An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-SA'ADHATU* *4-ASMA'U (MA'U)* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE1️⃣➡️2️⃣ _________________✍️ Dandazon mutune ne a k'ofar Wani maidaidaicin gida k'ofar gidan a kulle take gam k'ok'ari suke su bud'e ta amma sun k'asa kai daka kalle fusk'okinsu wadda suka fi koya shiga tashin hankali samari ne kusan su *SHADDA 6* sunfi koya shiga tashin hankali d'aya daga cikin su wadda yafi shuru-shuru da gyar ya bud'e baki saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki ya kira sunayansu gaba d'aya *"JAMIL!!, SULAIMAN!!, ABUBAKAR!!, KAMAL!!, MUSTAPHA!!"* amsawa sukai a tare cike da tashin hankali Kamal yace "ya dai ALIYU da magana a bakinka ya zamuyi mu shiga cikin gidan nan ace mutum tun jiya da dare amma gashi har yamma tayi ba labarin sa ga gidansa a kulle kodai karya k'ofar zamuyi ne?" Sauke ajiyar zuciya sukai jin Kamal ya kawo sha wara bud'awa sukai mutanan dake wajan suka kama bugun k'ofar da iya k'arfin su ai ko sunsha wuya kamin su b'alla k'ofar Ko wanne daga cikinsu k'asa shiga sukai zuciyar su na wata mahaukaciyar bugawa ALIYU ne yayi k'arfin kutsa kansa cikin tangamemen porlon wani irin jan birki yayi ganin Abokinsu kuma mafi soyiwa a garesu yashe a k'asa babu alamar rai a tare dashi Jikinsa yayi fari fat kamar an tsotse mai jini kalar jikinsa ta chanza ta koma bulu bikinsa na fitar da wani kunfa fari fat dashi jikinsa duk ya saddare, Wani irin uban ihu ya kwalla yana zubewa a k'asa sumamme da sauri sauran Abokan suka shigo ba shiri zan birki sukai ganin abinda Aliyu ya gani ya sashi sumewa suma dai zuciyar su kamar zata faso k'irjin su saboda tashin hankali Cikin wajan gari wani irin jeji ne tafe take tana b'ab'b'ak'a dariya iya k'arfin ta tana wata rausaya kai daka ga yadda take tafiya k'ugunta na jujjuyawa dukkan jikinta na launkwasa daka kalleta kasan ba cikakkiyar mutum bace zaunawa tayi jikin wani dutse kanta a duk'e d'ago wa tayi ta wani irin sauri (ni kaina sai da razana da tsananin kyawunta da kalar idanuwanta bulu shar dasu ga gashi ya sakko har yana so ya tab'a k'asa dariya ta k'ara shek'ewa da ita sai kuma ta fara wasu irin hawaye na jini jikinta ya fara sab'ulewa ya fara kumawa na maciji rabin jikinta ne daga k'asa ya koma na maciji wata irin uwar k'ara ta kwallah "inahhhh wllhy sai naga bayanku ku duka tunda kukai sana diyar shigata cikin k'unci kun jama kanku masifa da bala'i bazan barku ku zauna lafiya bahhhhh" ta ida maganar da murya mai k'arfi wadda har yasa dajin da tsintsayan dake rayuwa cikin dajin girgiza tsintsaya suka watse sama kasar dajin har wani tartsatsi take kamar zata rabe gida biyu......... ***************** Wani k'asur gumin boka ne zaune a wani k'aton kogo wasu macizzai ne durk'ushe a gabansa wadda ya kasance rabin jikinsu daga k'asa na maciya ne sai daga sama kuma na mutum ne kuka suke suna buga kansu a k'asa suna magiya da sauri cike da fushi bokan ya d'aga masu hannu da cewa "Matarka Alina tayi babban kuskure dole ne tabar wannan duniyar" yana nunata da yatsa d'ago fuskar tayi da duk ta b'aci da jini ga hawayen jini na shatata a idonta na tsananin tashin hankali da sauri na mijin wadda ya kasance mijinta zai bud'e baki domin magana bokan ya dakatar dashi "Bijay kasan cewa doka ce ba'a lamince muku shiga cikin bil Adam ba sai nan da shekara dubu biyar wadda zasu gaba shid'ewar zamanin nika amma Alina ta sab'a dole ne ta mutu" Kuka yake kamin yayi aune Alina ta fad'i a numfashi babu a jikinta da sauri ya tallafo ta yana kuka bokan ya shima cike da tausayin wannan masoya yace "nima ba yadda zanyi ne dole tunda ta k'arya doka amma karka damu nayi duba zamanin da zaka fito daga wannan kogo bayan shud'ewar zamanin nika za'ayo wata irin Alina sak babu banbanci sai dai za'ayo ta ne a jinsin d'an Adam" da sauri Bijay ya d'ago da kansa yana kallon boka "kware kuwa zata dawo gareka amma ba'a jinsinka ba kuma za'ayota ne a musulma wannan kogon da zaka shiga har sai zamanin da za'ayota zata bayyana a kusa da wannan kogon za'a gina wata makaranta wadda chan zamanin suna kiranta da jami'a ne zata zo cikinta dumin yin karatu a wannan lokacin ne zaka fito daga kogon kaje gareta".........✍️ *To Masoyana sai naga yanayin comment d'in ku zan cigaba da typing yayi kukaji salon book d'in* Nice taku *FATEEMAH RABI'U Ce (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-SA'ADAHTU* *4-ASMA'U (MA'U)* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE3️⃣➡️4️⃣ __________________✍️ Durk'ushewa sukai gaban gawar Abokinsu da Aliyu dake a Sume su duka hawaye suke mai cike da kunci da kuma rad'ad'in rashin dan uwansu da kyar mutane suka b'anb'b'are su daga gawar aka shiryasa aka kaisa gidansa na gsky, Koda Aliyu ya farfad'o a gigice ya farka yana kuka mai tab'a zuciya yana tabbayar shin ina HAIDAR (wadda ya mutu kenan) da kyar aka samu aka kwantar mai da hankali tunani ya fad'a, Sun kasance tare tsawon shekaru sun kasance basuda kowa su *TAKWAS* sun tasu a gidan Marayu sun gida kansu tabbas sunsha wahalar rayuwa amma kuskure d'aya yasa duk rayauwar jin dad'i da suke buri zata ruguje wadda ya kasance tsananin Abotarsu har gidajensu a jere suke inda Jamal yana da aure amma bashi da yara, sai Mustapha yana d'a d'aya namiji mai Suna *Al'ameen* k'arami ne wadda bai wuce shekara biyar 5 ba Matarsa ta mutu wajan haihuwar Al'ameen , Sai Sulaiman Shima yana Aure amma kamar dai Kamal basu da yara, Sai Abubakar bashida Aure, sai Aliyu wadda ya fisu yarinta shima baiyi aure ba, sai kuma Haidar daya mutu shima bai tara iyali ba. Wannan kenan Sai da aka kwana biyu da rasuwar wadda kwata-kwata zuciyar su bata kawo wai abinda suka aikata chan baya bane yake bibiyar su ba, Bayan kwana bakwai wadda da yawonsu sun dawo normal amma banda Aliyu dan har yanzu mutuwar bata bar jikinsa ba, Dare ne sosai wadda kowa ya kasance yana muhallinsa hadari ne sosai iska na kad'a wa mai k'arfin gaske ga wata irin walk'iya, Zaune Abubakar yake a gidansa yana d'an daddana computer windows gidan na kad'a wa da d'an k'arfi tashi yayi yana yatsine baki saboda duk a gajiye yake duk sai da ya rufe ko ina zai juya ya zaune kenan ya fara jin ana buga k'ofa da d'an k'arfi baiji wani tsoro ko fargaba ba ya nufi k'ofar, Bud'ewa yayi macece tsaye ta juye baya da sauri yace "wace a nan?" da sauri ta waigo tana Durk'ushewa k'asa cike da kuka da makyarkyata sanyi sanye take da kayan fulani tace "dan Allah ka taimaka min dare yayi ina tallar nono ga hadari", da kuka bai ban tausayi, Cike da tausayi da kuma dama Abubakar akwai san mata har wani d'an lashi baki yake yace "Ahh haba ba komai shigo" har wani rik'o hannunta yake da sauri ta fisge bayan ta shigo rufe k'ofar yayi juyowar da zaiyi yaga ta juya baya da sauri yakai hannunsa yana juyowa da ita da sauri ya sake ta cikin razana yana ja da baya yana nunata da yatsa bakinsa na kyarma, B'ab'b'ak'ewa da dariyar tayi mai amsa kuwwa runtse idanuwanta tayi sai kuma ta bud'e su sun rine sun koma bulu shar jikinta ne ya fara wani girgiza yana wani chanza kala daga k'asan ta ya koma maciji shar b'eb'e dashi, Da sauri Abubakar ya buga wata uwar k'ara yana zubewa k'asa da sauri kuma ya tashi da gudu yayi hanyar waje yana shirin bud'e k'ofa, Da saurin daya wuce misali tasa jelarta ta maciji ta yarb'er da k'afafunsa ya fad'i nannad'osa tayi tsakiyar cikinsa ta matso dashi kusa ta d'aga shi sama tana kallonsa cike da mugunta ta k'ara shek'ewa da wata mahaukaciyar dariya tana cewa "hhhhhhhhh ka shigo hannu kai har wani mai wayo ne da zaka iya tsallake kaidi na ne kunyi babban kuskure shigowarku rayuwa tahh" shi kuwa ya kasa magana sai mutsu-mutsu yake saboda ta matseshi tam bai aune ba yaji sara akan d'an yatsan sa babba ta sare shi sakinsa tayi ya zube a k'asa abinda bai wuce sakon d'aya ba jikinsa ya fara wata irin kyarma da chanza launi dafin macijin ya fara shigarsa jikinsa ne ya fara sandarewa bakinsa na aman wani farin kunfa na dafin da tana sa mai, Cike da jin dad'i ta bace bat daga gidan kamar ba'ai wanzuwarta a wajanba tabar gawar Abubakar yashe a k'asa....... ****************** Da gama maganar sa bokan ya bace da sauri Bijay ya tashi yana shafa kasan sa ya koma kamar mutum gaba d'aya kogon ya shiga wadda ya kasan kamar kukar aljanu k'atuwar gaske. *BAYAN SHEKARU ARU-ARU* Zaune take sai shagwaba take zubawa Momy "please ki barni nida Aamah mu cigaba da karatu mana tunda kina da hali kinji Momynah" cike da lallashin take lallab'a Momy tana turo d'an k'ara min bakinta mai d'auke da jan leb'e fuskarta doguwa ce tana da siririn hanci dogo har baka ga idanuwanta manya dasu, Cike da rashin son suyi karatu Momy ta kira sunan ta da cewa " RAYHA bank'i ba am hankali na bai kwanta ba sam" da sauri Rayha tace "inshallahu Momy ba abinda zai faru damu kedai kiyi mana Addu'a shine Momy" sauke ajiyar zuciya tayi dai-dai nan Aamah ta shigo tana cewa "ai nasani Momy zata barmu ne inshallah ko Momy?" Tana lek'a fuskar ta murmushin k'arfin hali ta sauke tana rungume su su kad'ai Allah ya bata Babansu ya dad'e da rasuwa tace "Allah ya albarkaci rayuwarku dama tuni an samar muku makarantar kawai dai hankali ne ya kasa kwanciya ji nake kamar wani abu zai faru da kune" ta ida maganar cike da sanyin murya suma duk jikinsu yayi sanyi cike da kwantar mata da hankali Aamah tace "babu wani abu Momy Addu'arki muke nema babu abinda zai faru sai alkhairi" sauke ajiyar zuciya tayi tace "inshallah tuni kun fara lecture inshallah zuwa gobe ko jibi sai ku tafi koh?" Cike da tsananin murna suka rungume Momyn........✍️ *Shin wai mi su Aliyu suka aikata ne yake bibiyar rayuwarsu ne yake san k'arar dasu?🤔* *Miye Momy taji game da yarinta shin wacce rayuwa zasuyi a jami'ar mi zai faru da Rayha ne,🤔 kudai ku kasance dani sannu a hankali zan warware muku chakwakiyar* *FATEEMAH RABI'U Ce (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-SA'ADAHTU* *4-ASMA'U (MA'U)* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE 5️⃣➡️6️⃣ __________________✍️ Washe sun tashi da sabon tashin hankali wadda fad'ar shi ma b'ata lokaci ne bare Aliyu dabai gama farfad'owa ba, Bayan akai gawar Abubakar zaune suke sunyi jigum-jigum wani mutum ne yayi masu sallama amsawa sukai hankalin su kwata-kwata jikinsu gyran murya yayi tukun yace "Gaskiya wannan aikin dana ga gawar Abubakar tabbas da akwai dafin maciji a jikinsa" da sauri suka waigo suna kallonsa cike da tsananin tsoro da kuma abinda suka aikata baya ya shiga tariyo masu, mutum ya cigaba da cewa "tabbas hakane amma zan had'aku da wani masanin macijzai zai iya taimaka muku inshallahu" da sauri su duka suka amince amma banda Kamal dake wani sham k'amshi dan shi kwata-kwata bai yarda da wannan abobuwan ba sam, Inda basu bata wani lokaci ba mutunan yayi masu jagora har wajan sarkin macijzain wadda mutane suke mai lak'ani da *D'AN MACIJIYA* Kamal kuwa yadai biyo su ne amma baya jin zai iya bin abinda za'a ce wajan da isarsu wani kogon dutse ne shiga sukai wajan cike yake da wasu layoyi da wasu y'an kwanduna kamar na saka dukansu macijzai ne ciki, Zaune yake duk layoyi cike da wiyansa da wasu irin abu irin na maciji a damtsan hannunsa da wasu kalar zobina masu zanan maciji, Tsaye suke a jere mutunan yayi masa mayanin mike faruwa da sauri D'an maciji yakai dubunsu a kan samarin su biyar a jere yace "tabbas kun shiga kaidin MACIJIYA wadda kwata-kwata ba imani a ziciyarta a yanzu tabbas ganin bayan macijiyar nan akwai jan aiki amma zan baku kariya tabbas indai kuna tare da wannan a d'aure a damtsen hannunku tabbas bazata iya koda tab'a ku ba" ya idasa maganar da d'akko wasu irin y'an hannu kamar laya ya bisu a jere yana sa musu dai-dai yazo wajan Kamal zai samai cike da rashin yarda da abin ya dakatar dashi ta hanyar d'aga mai hannu yana cewa "karka sake ka samin wannan shirmen babu abinda zai min" ya idasa maganar da iya gskyr sa su duka cike da kid'ima suke kallonsa dama duk cikinsu shine mai taurin kai da sauri Aliyu ya matso yana kama hannun Kamal yana cewa "haba Kamal kasan cewa muna cikin had'ari shin mi yasa zaka k'i ne please ka sa" yana amsar abin ya kamo hannunsa nufin ya samai, Kamal kuwa fisge hannunsa yayi bai ce komai ba ya juya ya fice daga wajan, cike da tashin hankali suka bisa da kallo, Da sauri D'an macijiya yace "lallai abokinku yana cikin hatsari" ya ida maganar cike da d'an b'acin rai yadda ya disga sa ya tsani mutum irin su Kamal sauke ajiyar zuciya sukai Jamil yace "yanzu dan Allah babu abinda zaka iya?" D'an macijiya yace "bari inada wani maciji mai fad'a dafinsa shima yana da had'ari sosai zan tura mata shi koh za'a samu nasara ya kashe mana itah" cike da gamsuwa Sukai godiya da mutunan daya kawosu ko wannan su gida ya wuce Mustapha yana shiga gidan sa da sauri Al'ameen d'ansa da dawowarsa school yahau cinyarsa yana cewa "Abbee" jin shuru bai amsa ba yasa Al'ameen d'an lek'a fuskar sa cike da damuwa shima yaron ya k'ara cewa "Abbee baka lafiya ne?" Da sauri Mustapha ya sawo d'ansa ya rungume sa yana tsoron rasa sa gara shi ya rasa tashi rayuwar, A wajan sauran ma Jamin da Sulaiman Matansu sun k'asa gane kansu saboda damuwar da suke ciki, A wajan Kamal kuwa yana shiga gidan sa yaga matarsa cike da mamaki yace "ba cewa kikai kwana zakiyi ba ya akai naga kin dawo?" Cike da wata irin rangwad'a ta tasu ta zauna a kan cinyarsa tana mai wani irin mayan kallo, cike da d'an mamaki yake dubanta matarsa bata saba mai haka ba anya kuwa kawar da zanchan yayi, Cike da kissa zata kai bakinta cikin nasa da sauri ya kawutar da fuskarsa cike da shagwaba da kissa tace "haba Honey" tana turo baki hannunta dake d'auke da wasu zak'o-zak'on farci tana shafa fuskar sa d'an karsar sa tayi, da sauri ya dafe wajan kanne mai hannu d'aya tayi cike da jan hankali ta fara gogamai mazau nanta da k'irjin ta hankalin sa ne ya fara tashi, Lura da haka yasa ta tashi zunbur da sauri ya rok'o hannunta bata juyo ba jawota yayi amma kamar dutse ya tsaye take wajan da d'an k'arfi ya sake jawota amma ina a tsaye take dai ta juya mai baya, cike da d'an tsoro daya fara d'arsar mai a zuciya Yasha gabanta da sauri da tashin hankali da bugawar zuciya yaja da baya, wata irin dariya ta kece da ita tana mai hiddo harshanta zungurere kalar na macijzai sai kuma ta tsaya da dariyar suffar tace ta koma asalin tata, shi kuwa Kamal kalar jikinsa ce ta fara chanza launi dafin maciji ya fara shigarsa dan kuwa ta rika ta samai tafin tuni wajan data karceshi fad'uwa yayi kasa yana shure-shure na zafin fitar rai, Ita kuwa wata dariyar ce ta sake yi tana cewa "kayi babban kuskure kai gaka mai taurin kai ko kayi kuskure kayi kuskureeeee rashin amsar wannan d'an hannun da aka baka suma kuma bawai tsallake kaidi na sukai ba daga su har wadda ya basu abin bai san wace ni bahhhh" ta ida maganar ta razananniyar tsawa wadda tasa gidan da duk wani gilassa dake cikin gidan faffashewa, Kamal kuwa kunfa ke fita ta bakinsa ga jini na shatata ta hancin sa kamin kace mi jikinsa ya saki dariya tayi tana sa jelarta ta maciji tana bubbuga fuskar sa ganin rai yayi halinsa cike da farin-ciki ta tashi sama kamar kububuwa ta bace bat Bata sauka a ko ina ba sai dajin da take rayuwa tana zubar da hawaye na rad'ad'in abinda akai mata da sauri kuma ta juyo jin kamar wani abu na bibiyar ta wani bakin maciji ta gani tsaye a gabanta wata irin dariya ta shek'e da ita tana cewa "lallai D'an macijiya kayi kuskure shigowarka cikin wannan sha'anin ni zaka turowa wannan k'aramin alhakin tabbas kayi kuskureeeee duk wadda yace zai dakatar Dani to zan d'au mummunan mataki a kansa........ ****************** Da gyar suka rabo da Momy kuka kam sun shashi ita kanta kasa daurewa tayi sai da tayi kukan tabbas tana ji a jikinta wata k'addara na shirin faruwa d'aya daga cikin yaran nata tabbas ita zata kaisu wannan makarantar ba yadda zatayi ne in k'addara tazo kai bawa baka isa dakatar ta ita ba fatan ta ko wacce iri ce ta zo masi da sauk'i, sun baro garin *gwambe* cike da kewa, Sun sha tafiya kana suka iso garin *RUMAN* mai cike da ni'ima da yawan shuke-shuke mai cike da kyawawan mutane wadda duk sun kasance fulani ne na Asali garin ya tara k'abilu da dama, school ce wadda ta amsa sunan ta wadda duk garin ba irinta sai d'an wane da wane keyita kai tsaye school d'in aka sauke su Rayha d'aga kanta Aamah tayi tana karanta sunan school d'in *UNIVERSITY OF RUMAN* kai tsaye school suka shiga babbar makaranta ce girmanta har ya wuce misali cike take da d'alibai Maza da kuma Mata kowa yana ji da kansa sunzo wuce d'akin da aka basu number d'akin tunda akai masu komai na school d'in ake baka number d'akin ku d'aki mutum Uku so yanzu mace d'aya ce a d'akin sai su sunzo gimta su maza ne sun kusan su biyar ko wanne sanye da k'ananun kaya sunsha askin y'an iska sai dizga y'an matan dake wuce suke su Rayha zasu gimta wajan kenan wani daga cikinsu yasha gabansu yana cewa "kai friend ga wasu zafafa" yana wani lumshi ido cike da shak'iyanci, Tsaki Aamah da Rayha suka ja suna mai ra rab'a ta gefe zasu wuce cike da jin haushin tsakin da sukai masu wadda yasha gabansu yasa hannunsa yajawo gyalan Rayha har yana zamowa kafad'arta cike da wani irin fushi ta waigo tana d'aukesa da mari lafiyayye tana nunasa da yatsa "shashasha kawai mararsa tarbiyya" su duka samarin tashi tsaye sukai cike da mamakin abinda tayi anya tasan shi waye kuwa? Shi kuwa huce yake cike da bakin kudiri a ransa lallai saya wargaza ma wannan yariyar rayuwa shi zatam mara kamar shi wacece ita, Da sauri Ikilima wadda d'akinsu d'aya ta shaidasu ta k'arasu wajan cike da tashin hankali ta kama hannunsu tana cewa "kai Rayha kunsan shi waye kuwa d'an gidan wani ne a cikin garin nan babansa babbane kwata-kwata Abdallah baya jin magana an sansa a cikin school d'in nan miya za maku tsayawa wajansu?" Tsaki Rayha taja tana cewa "yo saimi ko ma d'an gidan wane kinga mi yayi mana ne kwata-kwata basu da d'abi'a wallahi" Aamah kuwa har d'an tsoro ya fara shigarta ta kasa cewa komai Ikilima ta katseta da cewa "ai duk wadda zai shigo school d'in nan sai sunmai haka in kayi banza dasu zasu rabo dakai ne" "hmm lallai kuwa wa'innan sun kai to wallahi nidai indai sukai min saina rama" cewar Rayha da sauri Ikilima ta d'od'e mata baki tana cewa "ke Rayha ki rufa mana asiri" bige hannunta tayi tana turo baki, shi kuwa bayanta yabi da kallo yadda k'ugunta ke juyawa duk da tasa babban mayafi amma hakan baisa halittun jikinta rikita d'a namiji ba idonsa ne yayi jawur har wani lashe baki yake da sauri friend d'in sa suka k'araso d'aya daga cikin su yace "ya haka friend ka barsu suka wuce salin alin" juyowa yayi Yana watsa mai wani mugun kallo da idanuwansa wadda cike suke da jaraba da muryar sa irin ta gaggun y'an iska yace "kai kana zaton na hakura sai tasan kowani waye tayi babban kuskure da har ta d'aga hannu ta mare ni ko tsoho na na manta rabon daya sa hannu ya mare ni bare ni saina wargaza rayuwa ta saina aa rayuwarta cikin k'unciiiiiiii😳............✍️ *FATEEMAH RABI'U Ce (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE7️⃣➡️8️⃣ ___________________✍️ da gama maganar ta ta maida dubanta akan macijin da aka turo mata dumin wai ya kasheta wata shu'umar dariya tayi girgiza ta farayi jikinta ya fara rikid'a yana zama na macijiya gaba d'aya ta zama wata narkekeyar macijiya gadan-gadan macijin ya nufuta cikin fushi itama ta nufesa, Wata irin guguwace ta tashi fad'a suke suna sarar juna gani tayi zai wahalar da ita danda nan ta zama rabinta macijiya rabinta mutum nannad'osa tayi da jelarta ta yarb'asa a cikin k'ayoyi nan take macijin ya mutu, Wata shegiyar dariya ta kece da ita tana cewa "ni zaka turowa wannan k'aramin alhakin wadda tsafinsa baikai da ya rink'a zamowa mutum ba inahhh kayi kuskure D'an macijiya ganin zuwa gare kahhh" Bacewa tayi bata sauka a ko ina ba sai a kogon D'an macijiya zaune yake kawai yaga an wurgo mai macijinsa wadda ya aika, Da sauri ya mik'e abin busar maciji ne rataye a wiyansa kallon-kallo suke ganin abun busar da yake sasu bacci da maida su asalin suffar su ta macijzai juyawa zaitai nufin tabar wajan, ai da sauri ya fara busar iya k'arfin sa Tsayawa tayi tana dod'e kunwanta da iya k'arfin ta wata uwar k'ara ta kwallah tana zubewa k'asa "inahhh ka bari karkai min haka ka daina wannan busar nacehhh" ta fad'a da k'arfi, Shi kuwa D'an macijiya bai fasa busar ba abinda bai gaza y'an mintoci ba ta zama asalinta na macijiya tayi lagwas bata iya komai,. Da sauri yasa hannu ya d'auketa ya sata cikin wani d'an keji ya rufe yana murmushin nasara, Gama artabunsa da macijiya su Aliyu sukai sallama ganinsu yayi ko wannan su da tshin hankali a fuskar sa zasuyi magana ya dakatar dasu da cewa "nasan tunda na ganku a haka tabbas tayi galaba akan mai taurin kan nan" (Kamal kenan), su dukan su dakai suka amsa mai inda dawowarsu kenan daga kaisa makwancinsa na gsky, Cike da alhilin abun D'an macijiya ya k'ara da cewa "tabbas na jajanta muku kuna cikin uk'uba da kaidin MACIJIYA sai dai taimako d'aya ne zan baku shine ku tabbata wannan d'an hannun dana sanya muku ku tabbatar yana hannayenku a koda yaushe karku bari ya sub'oce maku" cike da gamsuwa da tsananin tashin hankali suka d'aga mai kai kwata-kwata baiyi gigin sanar dasu cewa macijiyar tana hannunsa ba dan suna iya cewa a fiddota a kashe ta sai dai kash wannan macijiya ko busar ba wani nasa take a jikinta ba yanzu haka ta sake ta dandai tana cikin abinda bazata iya fitowa ba, Bayan kwana biyu sun d'an samu kwanciyar hankali jin ba wadda ya k'ara mutuwa a cikinsu, D'an macijiya ne yaje cikin dajin d'ebo wani sassak'e dawowarsa ya nufi wajan daya kulle macijiyar nan zuciyar sa ce ta buga kamar zata fito girjinsa ji kake diff dumm diff dumm cike da tashin hankali yake kallon abinda ya kulleta a bud'e babu ita babu alamar ta, Juyowar da zaiyi ya hange ta zaune a suffar mutum ta hard'e k'afa d'aya kan d'aya cike da izza tace "kayi kuskure baka son wace ni ba da har kasa kanka cikin wannan lamarin da bakai gigin shugowarka gona ta bahhh" ta ida da macin rain abinda yayi mata shima, Cikin dagiya yace "bazaki tab'a cin nasara ba in...... Katse sa tayi a tsawace da cewa "har kai waye dazai dakatar dani?" Gama maganar ta zau juya ya d'akko abin busa da saurin d'aya wuce misali ta girgiza jikinta ta zama sharb'eb'iyar macijiya bai aune ba ta kai mai sara a agarar k'afarsa, Zubewa wajan yayi dai-dai ya d'akko abin busar fad'uwa abin busar yayi D'an macijiya ya fad'i yana shure-shuren mutuwa dan ita dafinta tana sama shi nan take ake mutuwa saboda hatsarinsa tashi tayi tana murmushin mugunta tana matsawa kusa dashi ta kece da wata irin dariyar data girgiza kogon gaba d'aya sai kuma ta turb'une fuska tana kai dubanta kan D'an macijiya dake futar da kunfa na dafin maciji idanuwansa sun kakkafe jikinsa ya saddare kamar yadda ya shekara da mutuwa ga kalar jikinsa ta zama kalar dafin macijiyar tace "lallai ka jama kanka mutuwa wannan shine kad'an daga cikin duk wadda zai rink'a shigowa gona tahhhh" murmushi take mai cike da zallar mugunta tana bacewa daga kogon........... ****************** Sai nasa rayuwar ta cikin kunci" ai da sauri friend d'in sa suka fara mai kirare, Bayan su Rayha sun shiga rom d'insu wadda yake a tsaftattace zaunawa sukai duk a gajiye Ikilima na kallonsu cike da tausayawa dan tasan tabbas Abdallah bazai bar wannan abun ba Rayha ta tashi tsaye tana nufar window tana zage labole d'an zaro ido tayi ganin wata gatuwar kuka kusa da window d'in da sauri ta waigo tace "amma Ikilima wannan kukar fa? Baki ganin akwai matsala kuwa" Ikilima tace "babu wata matsala mutum nawa suka zauna a d'akin kamin mu ba abinda ke cikinta na cutarwa naji ana cewa ta d'ad'e gaskiya shekaru da yawa" Aamah tace "Ahh ai daga ganinta kam" ita dai Rayha bata k'ara magana ba abinci suka ci sana suka kwanta a b'angaran Rayha kuwa wani mafarki ta fara mai cike da rikitarwa, Washe gari haka shi suku-suku bayan sun shirya suka nufi cikin makaranta da yake duk gurin lectures su d'aya duk abinda suke karanta saiya zamanto d'aya ne, Zaune su Abdallah suke ta hanyar da dole sai kabi ta wajan zaka hall d'in lectures sai zuk'ar sugari suke, Ikilima kuwa ganin su wajan yasa da sauri ta matso jikin Rayha tace "please Rayha kinga mutananchan ba mutumci ne dasu ba dan Allah mu wuce salin alin karki tanka masu" ita kuwa Aamah tunda ta hangosu tsoro ya k'ara shigarta, Rayha kuwa tabe baki tayi dai-dai sunzo gifta su cike dajan magana Abdallah dake gaf da ita yana shan sigari ya daddage ya fesu mata hayakin akan fuskarta da sauri ta dod'e hancinta tana tari sosae kamar zata shid'e da sauri Ikilima ta zasu suka bar wajan Aamah kuwa kuka ta fara waje suka samu suka zauna har yanzu Rayha tari take ba k'ak'k'autawa cike da tausayin ta Aamah matsa ta samu ruwa tana bata sha tayi tana jan wani irin numfashi kamar wadda ta suma idanunta sunyi jawur tana sauke numshin wahalahh.........✍️ *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE9️⃣➡️🔟 ___________________✍️ Tashin hankalin da ba'a sa masa rana wayewar gari su Aliyu suka samu labarin mutuwar D'an macijiya, lallai sun shiga tashin hankali wadda baki bazai fad'e shi ba, Tabbas suna cikin matsala babba yanzu saura wadda suka rage Mustapha, Sulaiman, Aliyu, Jamil, saira su hudu lallai suna cikin tsaka mai wuya wadda yake basu taimakon shima ta halaka shi, Zaune suke wajan gaisuwa kai daka kalle fusk'okinsu kasan sunfi koya shiga rud'u da tashin hankali kwana biyu sunji shuru ashe tana nan tana shirinta shin wane irin lefi sukai mata haka dahar take masu d'auke d'ai-d'ai, Da gyar suka bar wajan gaisuwar inda kowa yana k'ara jaddada ma d'an uwansa cewa yafa kula da d'an hannun da D'an macijiya ya basu lallai sun tuna kamar wasiyya ce yake masu kamar yasan zai tafi yabarsu cikin wannan duniyar mai cike da rud'u da tashin hankali kullum cikin zullumi suke basu san wane yanayi zatazo masu ba, Zaune matar Jamil take taci uban gayu ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya d'agowar da zatai tayi arba da mace tsaye kanta tayi gayo wadda yace uban nata, da sauri ta tashi zunbur cike da d'an kishi-kishi tace "wace ke ke tsayama taya akai kika shigo cikin gida nah eyee?" Ta idasa maganar tana b'alla mata wata uwar harara dakatar da ita tayi budurwar tana ware manyan idanuwanta bud'ar bakinta sai cewa tayi "ke ba matar Jamil bace?" Matar Jamil tace "kamar ya matar sace mana ji wata tabbayar reni" budurwar ta k'ara gyara tsayowarta da wani pictures babba a hannunta ta juya bayansa tace "to nima ai matarsa ce" Matar Jamil kuwa saddarewa tayi cike mamaki tace "anya kina da hankali kuwa kizo gida na da mijina kuma kice wai mijina mijinki ne" ta idasa maganar tana mata wani kallon banza, Murmushi budurwar tayi tace "nima haka zalika bansan wata matarsa ba inba niba amma nuna min shirdar cewa ke matarsa ce" cike da tsananin mamaki na wannan baiwar Allah tace "ki shigo har cikin gidan Jamil kiga ni ni matarsa kuma kice in nuna miki shaida amma tsama ai inada pictures d'in bikinmu"ta ida maganar tana juyawa ta bud'e wata dorowa dake cikin porlon ta zaro wani abu mai kamar littafi cike yake da pictures d'in bikin nasu ta wurga mata shi, D'auka tayi tana wani munafikin murmushi tukan ta mik'o mata taga dukkan abinda ke ciki ajiyewa tayi sana itama ta mik'a mata nata tace "nima ga nawa shaidar sunana *AMREETA*" da sauri matar Jamil ta amsa kallon pictures d'in take cike da tsananin mamaki da bugawar zuciya lallai kuwa ga hoto nan tana gani da mijinta da wata innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai take mai-maitawa, Zata k'ara magana kenan Jamil ya shigo kallon sa take cike da tsananin mamakinsa shi kuwa Amreeta yake ma kallon rashin sani ita kuwa matarsa ganin kallon da yake ma Amreeta gani tayi kamar na Soyayya ne da sauri ta matsa kusa dashi tana hawaye tace "Jamil dama yaudara ta kake ne ban sani ba?" Ta idasa maganar tana cin kwalar rigarsa cike da mamaki yake kallon ta yace "ban gane ba" tana kuka ta k'ara cewa "dama ya za'ai ka gane gata nan cewa tayi wai matarka ce" da sauri ya waiga yana kallon Amreeta kallo irin na tuhuma da rashin yarda, Ita kuwa Amreeta ko gezau batai ba ba alamar tsoro a idanuwanta saima tsayowa ta k'ara gyarawa tana aika mai da wani munafikin murmushi, juyowa yayi wajan matar sa yace "nifa ban ma santa ba ke ina kika sanni da har zaki ce waike matata ce?" Ya idasa maganar yana kallon Amreeta ita kuwa Amreeta takowa tayi cike kissa ta shafa fuskar sa tace "haba hubbyyy kodai kana tsoron matarka ne in...... Tukan ta ida matar Jamil ta k'ara fashewa da kuka tana k'ara ruk'unk'umeshi ita kuwa Amreeta D'an hannunsa take kallo ganin ya kusa cikewa wani irin shu'umin murmushi ta saki kallon su take yadda ta had'a husuma wani irin dad'i take ji basuyi aune ba d'an hannun sa ya tsinke ya wargaje a k'asa, Da sauri ya saki matar tasa yana furta "kin gani ko kinsan halin da muke ciki jibi kin katsi min abin kariyar kinji dad'i ai " wata irin dariya sukaji an b'ab'b'ak'ewa da ita da sauri suka waiga gaba d'aya cike da tsananin tsoro da bugawar zuciya suka za baya ganin Amreeta ta zama wata narkekeyar macijiya har wani huce take baitai wani sanya ba ta tashi sama kamar kububuwa bata saukar da sarinta a ko ina ba sai akan Jamil tsakiyar goshinsa nan take ya zube yana shure-shuren mutuwa kalar jikinsa ta fara chanzawa kunfa na fitowa daga bakinsa, Amreeta kuwa wata dariyar ta sake shek'ewa da ita har kujerin porlon na girgiza tace "lallai sunana Amreeta lallai sai naga bayanku d'aya bayan d'aya lallai kunyi kuskuren shigowa rayuwa ta hhhhhhhh" ta idasa maganar da wata mahaukaciyar dariya da sai tasa d'an Adam fisari a wando ta bace kamar ba'ai wanzuwarta a wajanba matar Jamil kuwa ganin mijinta a saddare babu alamar rai a jikinsa girgiza kai ta farayi tana ja da baya dod'e kunwanta tayi tana tana kwala wata uwar k'ara ta zube a k'asa sumammiya......... ***************** Da sauri Aamah tace "Rayha kina lafiya?" D'aga mata kai tayi kawai dan zuciyar ta cike take sa tsanar Abdallah, Ikilima tace "kin gani ko wallahi basuda kirki duk makarantar nan an sansu Allah dai ya rabaki da shirrinsu" tashi sukai suka shiga lecture Rayha kuwa kwata-kwata lecture ma ba wani ganewa take ba saboda damuwa koda aka tashi tare suka dawo d'akinsu, Cike da damuwa Aamah tace "bari naje na sayo miki magani naga kamar kanki na ciwo" Rayha tace "ai kuwa kaina nad'an ciwo" fita Aamah tayi dan sayo magani Ikilima kuwa abinci ta d'ora masu sana ta shiga wanka, Rayha kuwa jan numshi tayi tana d'agowa idonta bai sauka a ko ina ba sai a kan window d'in d'akin da sauri ta tashi tana ja da baya bakinta ya kasa furta koda kallama d'aya saka makon tozali da tayi da kan mutum sauran gaggar jikin kuwa ta maciji ne Bijay kenan bayan dubun nan shekaru ya fito daga kogon Da aka gindaya mai sharidd'in bazai fito ba harsar wannan zamanin da za'ayo matarsa kuma gashi ta bayyana garesa Rayha kamarsu d'aya da matarsa kallon ta yake cike da k'aunar ta da kuma kewarta na tsawon shekaru masu tarin yawa, Ita kuwa Rayha tunda take bata tab'a ganin tashin hankali irin na yauba maciji da kan mutum anya kuwa bata zareba hawaye take zuciyar ta na wata irin bugawa diff dumm dumm diff kamar zata faso k'irjin ta fito saboda tsananin tsoro numfashinta ne ya fara d'aukewa tana shirin suma ganin haka yasa Bijay gangarowa domin shigowa d'akin nufin ya rarrashe ta ganin yana nufo wajanta runtse idanuwanta tayi tana tsala wata uwar k'ara ta zube a sume............✍️ *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ ___________________✍️Su Mustapha kuwa dajin labarin mutuwar abokinsu ba k'ara min tashin hankali suka sake shiga ba dan kuwa Mustapha rungume d'ansa yayi yana durzar kuka shi kansa Al'ameen yana kallon Abbeensa yana hawaye duk da k'aramin yaro ne ya fahimci cewa Abbeensa yana cikin damuwa, Matar Jamil kuwa tunda ta farka take sanbatu kamar zararra dan har aka kai Jamin bata sani ba ai saida aka dan ganta ta da asibiti inda Matar Sulaiman sosai ta shiga tashin hankali kullum dama cikinsa suke, Mustapha da Sulaiman da Aliyu zaune suke sunyi jigum-jigum d'ago kyawawan idanuwansa Aliyu yayi a hankali cike da rauni yace "lallai chan baya munyi babban kuskure gashi abin yazo yana son shafe tarihin mu" ya ida maganar cike da rauni duk da ya kasan ko d'aya abinda friend d'in sa suka aikata ba hannunsa a ciki sai dai kash ai yana wajan akai abin, Su duka suka shiga tariyo abinda suka aikata chan baya wadda ya jaza masu rashin kwanciyar hankali da dana sani wadda bazai musaltu ba. *WAIWAYE* Lallai su Aliyu sun taso basa jin magana ko kad'an duk da sun kasance marayu dole tasa aka sallame su daga gidan marayun dan kuwa rukuninsu su TAKWAS kowa ya sansu a gidan marayun sai dai missa babin abinda yasa aka koresu gidan marayun ya kasance maza da mata ne sai dai b'angaran mata daban na maza daban a gidan marayun anyi wata yarinya kyakkyawar gaske mai suna *Khausar* tana nutsuwa sosai bata shiga harkar kowa rayuwarta kawae take tun Khausar na k'arama Amreeta ke tare da ita (Macijiya kenan) sai dai ita kanta Amreeta bata san Macijiya bace dan kuwa tun tana k'arama ta taba ceton Amreeta time d'in itama Amreeta k'arama ce akwai lokacin da Khausar ta fito domin zuwa islamiyar dake cikin gidan marayun ta hangi wata y'ar Macijiya y'ar k'arama da ita dutse ya danne ta sai nishi take saboda wahalar da tasha da sauri Khausar ba tsoron komai ta matsa kusa ta d'auke dutsan tana sa hannu ta d'auki macijiyar luf kuwa macijiyar tayi a hannun Khausar ita kuwa cike da rashin tsoronta ta ajiye ta a k'asa tana shafa bayan Macijiyar tana mai juyawa dan barin wajan, K'awayen tane taci karo dasu suna zare ido cike da mamaki d'aya daga cikin su tace "kai kai Khausar baki tsoron ta sareki ne?" Kama hannun su tayi suka fara tafiya dan suma y'an yara ne tace "bakwa ganin itama k'arama ce babu abinda zatai min" ta idasa maganar suna k'arasawa islamiyar. Ita kuwa Amreeta da barinsu wajan ta rikid'e ta zama mutum dama zo wajanne da kanta ta d'orama kanta dutsin tana so ta gwada cewa shin akwai wadda zai iya taimakonta, Cike da k'aunar Khausar a zuciyar ta lallai zata kasance tare da Khausar a matsayin k'awarta, To dayin wannan abu indai Khausar zata wuce islamiya saita rink'a ganin y'ar yarinyar mai kyan gaske wadda ita kad'ai ke ganinta ita kuwa Khausar kamar ana ce mata taje wajanta haka zata matsa wajanta tun basu kai da saboba har suka saba dan har bata lokaci take wajan zuwa islamiya mlm yayita fad'a kan cewa mi yasa yanzu bata son karatu ne ita dai sai dai tayi shuru dan bata da bakin cewa komai, Kamar kullum ma zaune suke ita da Amreeta tace "zanyi kewarki Khausar" tana mata wani irin kallo na kamar bazata k'ara ganinta ba cikr da tsinkewar zuciya da sanyin jiki da sauri Khausar ta kalle tace "wannan kallonfa kamar na bankwana to tukun ma ina zaki je ne" cike da kewar da xatayi tata tace "Khausar kamar yadda kika sani ni ba mutum bace kamar ke sana bawai yarinya bace kamar ke duk da yanzu kinkai shekara 13 kawai ina zo miki a yarinya ne domin kiji dad'in ma'amula dani yanzu haka zan koma chan wani jeji wadda muke rayuwa da mijina wadda yayi tafiya tsawon shekaru tabbas zan dad'e ban waiwaye ki ba" ta idasa maganar tana fashewa da kuka mai rauni da tsanin k'aunar Khausar d'in ita kanta Khausar matsawa tayi ta rungume ta tana hawaye tabbas zatai kewarta yanzu tana ganinta kamar wata y'ar uwar ta kuma danginta share mata hawaye tayi ta k'ara cewa "amma karki damu zan dawo gare ki komin daran dad'ewa" haka sukai ban kwana haka Amreeta ta tashi tafiya tana tafiya tana waigen Khausar ji take kamar bazata dawo ta sameta ba. Bayan Shekaru hudu tabbas yanzu Khausar ta fidda rai da dawowar Amreetar ta yanzu Khausar ta zama budurwa ta k'ara kyau komai na halittun jikinta ya k'ara bayyana tafe take kanta a k'asa cike da nutsuwa tazo gifta wa dai-dai su Mustapha na shirin wucewa layi suke daga alama a shaye suke banda Aliyu dashi bai bugu sosai ba, Cike da tsanin tsoro take kallon su ganin Kamal yana nufo wajan ta yana cewa "kai gayu kunga wata y'ar sakas dama gidan nan akwai zuk'a-zuk'an mata haka su dukansu har wani lashi baki suke Haidar ne da yaji abar girmarsa har wani tashi take zaboda zalama yace "kai Abokai bazan iya hakura ba ko d'akko mana ita muje cikin jeji da ita" dama ga duhun magaruba ya gabatu wajan ba kowa shi kuwa Aliyu a time d'in harya bingire da bacci danshi maganin mura ya sha, A kuwa haka suka sungume sai cikin jeji da ita tana kuka tana magiya amma ina shed'an ya buga masu ganga haka baiwar Allah tana ji tana gani suka rabata da mutumcinta na y'a mace cikinsu ba wadda baiyi anfani da ita ba haka suka tashi suka barta a yashe a wajan tana kuka mai tsayawa a rai ko numfashin kirki bata iyayi ga sanyin dare ga wani irin tsoro daya k'ara shigarta kuka take tana anbatar "Amreeta ina kika barni ki dawo gare ni" wannan ciwon abun da sukai mata yasa zuciyar ta bugawa dan ko safiya bata kai ba tace ga garinku nan A dai-dai wannan lokacin kuma Amreeta na zaune da mijinta zuciyar ta ce ke bugawa diff dumm diff da mugun k'arfi cike da damuwa da ruwan hawaye da take jin ya cika mata ido tace "mijina please ka barni naje wajan masoyiyata Khausar ina ji a jikina akwai matsala kaji dan Allah" ta ida maganar tana fashemai da kuka sauke ajiyar zuciya yayi yace "nima bank'i ta taki amma dai shikenan nan tare zamuje ki shirya" cike da tsanin murna ta rungume mijin nata, Washe gari gidan marayun suka tashi da tashin hankali wadda bazai musaltu ba ganin gawar Khausar basu wani bincike ba sun d'auka wani abun ya sameta har yayi ajalinta suka sallace ta suka kaita gidanta na gaskiya k'awayen sunsha kuka kamar ba gobe, Inda su Kamal kuwa ko a jikinsu saima wani shak'iyancin da saka sake b'ullowa dashi inda Aliyu daya ji labari yayi masu fad'a sosai amma sai ma tashi sukai suka rabo dashi, Amreeta kuwa tunda suka isu wajan gidan marayun dan a suffar mutune sukazo sai da suka bi k'a'ida kana suka shiga inda sukaga gidan duk a hargitse kamar ba lau ba nan Amreeta ta k'ara shiga rud'o da tashin hankali da gyar suka samu wata yarinya suke tabbayar ta cewa ina Khausar yarinyar kuwa kuka ta fashe dashi tana cewa Khausar ta rasu Amreeta kuwa jin maganar tayi kamar saukar aradu saman kanta gani tayi duniyar na juyya mata da sauri mijinta chan nesa da wajan mutane ya zaunar da ita yana share mata hawaye runtse idanuwanta tayi komai na rayuwar da Khausar tayi ba ita saida ta gani da sauri ta bud'e idanuwanta tana tashi tsaye tana cewa "inahhh bazai yuwuba wallahi bazaki mutu a banza ba inahhh wallahi wallahi sai sun san ke suka tab'a tabbas kun tab'o abinda yafi k'arfin ku" da sauri mijinta ya jawota jikinsa yana aikin rarrashi maciji ya zama yana kwantawa jikinta cike da tausayin matar tasa zata shafa jikinsa kenan taji harbin bindiga cike da tsanin tashin hankali jin mijinta ya fad'o jikinta da suffar sa ta maciji alamar ba rai a tare dashi shafu jikinsa tayi inda harbin ya sameshi innalillahi wa'inna ilaihir raju'un wacce irin k'addara ce ta same ta haka girgiza kanta take ta rasa shin kuka zatai ko kuwa, Ba kowa bane yayi wannan harbin sai Haidar tafe suke suna zagaye su duka suka ci karo da wata mace da maciji kanta kamar zai kai mata sari bai wani tsaya ba ya fiddo bindiga dan har ita garesu ya saita macijin nan sai dai sukaji harbi da sauri Aliyu ya jasu suka bar wajan cike da tashin hankali Aliyu yace "wai ku bakwa tunani ne in zaku aikata abu" da sauri Kamal yace "haba Aliyu baka ganin maciji ne kanta zai sareta" da d'an fad'a yace "kai baka da hankali kaida ka kallesu kasan ba mutane bane kasan itama kanta macijiyar ce suna zaune ne kawai" cike da kuma tashin hankali suka ce"yanzu ya zamuyi" sauke ajiyar zuciya yayi yace "tabbas kwana biyun nan kun aikata babban kuskure dama tuni an kuremu daga gidan nan dan haka kawai mubar wannan nahiyar kawai" ai kuwa da gama wannan maganar ko kayansu basu d'auka ba suka fice daga gidan gaba d'aya ma suka bar garin daga nan gidan marayun ba'a sake jin d'oriyar suba. A wajan Amreeta kuwa d'aukar mijinta tayi mata sauke shi ko ina ba sai dajin da suke rayuwa zuciyar ta saboda da tsanin k'unci da b'acin rai ta kasa kukan ma mijina da ya koma mutum ta matsa kusa da gawar sa ta bud'e idanuwansa duk abinda ya faru a idanuwan mijinta ta gani da sauri ta tashi zunbur cike da tsananin mamaki again wani irin uban ihu ta buga wadda har yasa dajin amsawa sai kuma ta zube a k'asa tana rushewa da kuka tana k'ank'ame gawar mijinta magani take cike da tsananin d'aukar *FANSA* "lallai kunyi kuskure shigowarku rayuwa tahh ni zaku raba da abinda nafi so har guda biyu shin mi suka tarewa rayuwarku lallai ba d'aya daga cikin ku dazan bari a raye ta idasa tana fashewa da wani kukan zuciyar ta zafi kamar ta had'e ta mutu.............. ***************** Tunda yaga ta sume ya ganka da sauri ya dafa kanta duk wani tsoro koh shakku ya cire mata shi san ya bace wajan, Ita kuwa Ikilima jin ihun Rayha yasa ta fito ban d'aki da sauri ganinta tayi tana bacci hankali kwance cike da mamaki take kallon ta to kodai ba ita bace ne taji ihun ta kauda maganar tayi ta cigaba da abinda take, Chan saiga Aamah ta dawo ranta a bace da sauri Ikilima tace "ya dai Aamah?" D'an tsaki Aamah taja tace "bari kedai fita ta na gamu da wa'inchan shashashun wai suna min gargad'in cewa sai sun illata Rayha" cike da tsoro. Ikilima tace kin gani koh wallahi zasu iya nidai Allah ya rabata dasu lafiya kawai" cike da sanyin jiki Aamah ta amsa da "Amin" kawai, Ganin cewa har yanzu Rayha bata tashi ba yasa suka zuba abinci suka ci, A wajan Rayha kuwa wani irin rikitaccin mafarki take wai gata a wani zami ni daya shud'e tana rayuwa da wannan wadda taga kansa kawai suna Soyayya mai tsayawa a zuciya ya kan ce mata "kin dawo gareni nine mijinki" tana cikin wannan mafarkin ta tashi a firgice da sauri su Ikilima suka matsa wajanta dafe take da kanta da take jin kamar zai rabe gida biyu da sauri Aamah tace "kanne ko? ga magani kisha" amsa kawai tayi tasha wanka tayi ta fito tana zaunawa da zaman ta d'aga kan da zaitai taga Bijay a dai wajan tagar yana mata wani irin kallo na k'auna a yanzu kuwa kallonsa take ba wani tsoro ko fargaba itama dai kamar kallon Soyayya take mai da kallon kamar ta tab'a rayuwa dashi, Ikilima nata mata magana amma bata jiba hankalin ta baya wajan kwata-kwata Aamah kuwa ganin inda take kallo tana murmushi cike da mamaki tabi wajan da kallo sai dai mi..........✍️ *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣ _________________✍️ Zuciyar Amreeta yadda kasan zata fito daga k'irjinta saboda tsananin hucen da take tundaga wannan lokacin Amreeta zuciyar ta bushe tsanin mugunta da d'aukar fansa, Tunanin su Haidar sun tserema abinda suka aikata wadda saida sukayi abinda suka fara tara iyali nanfa nadama da dana sani ta fara zuwar musu sai dai kash lokaci ya riga da ya gure masu dan kuwa duk abinda suke ciki da duk abinda suke Amreeta tana sane dasu babu inda zasuje domin tsere mata domin kuwa tayi masu dabaibayin da duk inda suka shiga a fad'in duniyar nan bazasu goje mata ba sai dai in mutuwa sukai kamin tayi sana diyar tasu mutuwar. Sauke ajiyar zuciya sukai su duka sun gama tunano abinda suka aikata chan baya tabbas saka makone suke gani, Aliyu ne ya fara tashi yabar wajan dan bakinsa ya kasa furta komai da shigarsa gida wayarsa tayi k'ara dubawa yayi sunan wata budurwarsa ya gani wadda yake burin aura wadda ita ta nace mai tana matuk'ar sonsa, Koda ya d'au wayar gaisawa sukai inda take mai ta'aziyya cewa zatazo har inda suke tayi masu gaisuwa sai dai ya hanata zuwa kan cewa basai tazo ba, sai dai bata bashi amsa ba sukai sallama. Washe gari bayan anyi addu'a mutane sun watse Aliyu zaune yana cin abinci tusawa kawai yake amma ba wani dad'insa yake jiba ji yayi an turo k'ofar parlo an shigo da sauri ya d'aga kansa Aliya idanuwansa sukai tozali da ita a zuciyar sa kowa mamakin ta yake shin baya ce karta zoba, d'an tsaki yaja yana k'ara kallon taci wani uban gayu sai wani yauk'i take takowa tayi har gaban sa sana ta zauna kujerar dake kallon tasa cikin karya murya tace "dear sorry nazo ban sanar da kai ba ya hakuri" d'an yatsine baki yayi ya amsa chan ciki, Ita kuwa cike da sonsa ta tashi ta k'ara matsowa kusa dashi lemon dake gabansa ta d'auka ta d'an kai bakinta d'an miyan dake bakinta ta tsirta ciki cike da kissa ta tako d'an shafa fuskarsa tayi gwarewa yayi ya fara tari idonsa yayi ja da sauri ya hankad'eta da cewa "ba nace miki bana so kina tab'a ni ke daina in ba haka ba kinsan hukuncin dazan yanke" yana magana yana tarin da sosai ya sark'esa da sauri ta tashi tana mik'a mai lemon da cewa "sorry dear amsa kasha naga ka gware" amsa yayi har yakai bakinsa sai kuma ya fasa d'an matsawa yayi chan kawai ya samu kansa da zubar da lemon ita kuwa bata lura ba ganin ya dawo da abin ba komai wani murmushin cin nasara tayi tana zama kan kojerar dake fesin d'in wani madubu dake parlon irin na kwalliyar parlo haka babba ne sosai sai wani yauk'i take tana rangwad'a shi kuwa Aliyu kamar ance ya matsa ta cikin madubin ta cikin madubin ya hangeta mi zai gani zuciyarsa ce ta buga da mahaukacin k'arfi kansa na sarawa cike da tsananin tashin hankali ya waigo inta take zaune tana latsa waya mutum yake gani a zaune a idanuwansa sai dai akasin haka a madubi k'ara waigawa yayi ta cikin madubin *MACIJIYA* Yake gani zaune innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai yake mai-maitawa cike da tsananin bugawar zuciya ya dawo ya zauna d'an cire tsoro yayi yana d'an tabbayar ta wasu abubuwa akan aihin Aliyarsa ga mamakinsa komi amsa dai dai take basa lallai ya shaida wannan macijiyar ba k'aramar hatsabibiya bace cike da kissa da yaudara ta d'an tashi tana zagaye parlon ganin har yanzu dafin data samai a lemo bai fara kamasa ba mamaki take can ta hango inda ya zubar da lemo zaro ido tayi cike da mamaki dan har wajan ya chanza kala ya koma bulu shar tunani ta farayi ya gano ta kenan tabbas dole ta sake shiri bace wa tayi daga gidan kwata-kwata shi kuwa juyowar da zaiyi ya nemata ya rasa wata irin ajiyar zuciya ya sauke da yanzu ya mutu koh? Da yanzu wani zanchan ake ba wannan ba "kai Allah na gode ma" ya idasa maganar yana dafe zuciyar sa da har yanzu take cike da tsananin tsoro. A wajan Amreeta kuwa ranta in yayi dubu ya b'aci har wani huce take na b'acin rai cike da wata irin murya mai cike da tsananin kuwwa tace "inahhh wallahi bazai yuwuba dole na sake shiri bazaku tab'a tsallake kaidi na ba in kunsan wata ai baku san wata bahhhhhhh" ta idasa maganar da k'arfi har bishiyoyin dajin na girgiza............... ***************** Aamah kuwa ganin inda take kallo tana murmushi cike da mamaki tabi wajan da kallo sai dai mi, ita bata ga komai ba cike da tsananin mamaki ta k'ara waigowa Sai dai har yanzu wajan take kalla tana murmushi mai k'ara ma fuskarta kyawu, Ikilima ma wajan takai dubanta itama dai window take gani bata ga komai ba da d'an mamaki Ikilima ta fara girgiza ta tana kiran sunanta da d'an firgice ta dawo hayyacinta tana dafe kanta, Ikilima tace "Rayha anya lafiyar k'alau kuwa shin mima kike kallo a wajan window?" Aamah itama tace "ashe kema kin gani har wani fa murmushi take irin tana tare da masoyinta d'in nan" da sauri Rayha ta kai mata duka kawucewa tayi tana dariya nan suka shashantar da abinda suka cigaba da fira. Washe gari bayan sun fito daga lecture tsaye suke su uku yamma tayi sosai ga gari yayi duhu hadari ya gaggami daka kalle hadarin kasan ko da yaushe ruwa na iya sakkowa, Da sauri suke tafiya domin isa rom d'insu suna cikin tafiya kawai sukaji mutum ya tsaya a gabansu cike da mamaki Rayha ke d'agowa idonta bai sauka a ko ina ba sai akan Abdallah dake layin giya sai wasu surutai yake marassa dad'in ji amai ya kwararo mata a kan jikinta mai warin giya da tsananin wari da sauri ta dod'e hancinta hawaye na b'alla mata su Aamah kuwa tsananin tsoro ya hanasu motsawa, Ita kuwa Rayha cike da tsanarsa ta d'aga hannu ta sharara mai mari lafiyayye har guda biyu da sauri Ikilima da duk ta rud'e ta jasu suka bar wajan shi kuwa Abdallah duk da cikin mayi yake saida ya wartsake idanuwansa saun kad'a sunyi jawur na tsananin bacin rai "Wardugu" ya kira wani abokinsa da sauri ya k'arasu wajan cike da tsananin b'acin rai yace "ku tabbatar kun sato min wachan yariyar kun kawo min ita kangon makarantar inda kowa bai shiga saita gane ni ta mara sai tayi dana sanin hakan da taimin" "an gama ya shugaba na" cewar Wardugu da wata bud'ad'iyar murya. Da isarsu d'akinsu Rayha tana kuka mai cin rai ta shiga wanka zuciyar ta sai tsinke wa take tana bugawa ga wani fad'uwar gaba da take ji a wajan Aamah ma haka take ji fashewa tayi da kuka haka kawai ko taji saukin zuciyar ta ta rasa mike mata dad'i dan har waya sukai da Momy ita ma dai fad'uwar gaba da tsinkewar zuciya da sanyin jiki duk sun hanata sukuni, Da sauri Ikilima ganin halin da suke ciki ta fara rarrashin su haka suka kwanta babu wani baccin kirki da suka yi Washe gari haka suka tashi Aamah kuwa cewa tayi bazata lecture ba sai dai Rayha duk da abinda take ji duk duniyar ta sire mata haka ta shirya ita da Ikilima suka fita, Ana cikin lecture kamar ance ma Rayha ta mik'e kawai ta fita daga wajan Ikilima na kallonta cike da tausayin ta a wajan Rayha kuwa tafiya take bata san inda take jefa k'afarta sai dai kawai taga dandazon in isaka a kanta kusan su hudu zuciyar tace ta sake bugawa da k'arfi kamin tayi wani yunk'uri suka shik'a mata wata farar huda gashi wajan ba kowa gashi dama babbar makaranta ce wani wajan ma ba shigarsa ake ba Basu sauke ta a ko ina ba sai a wani tsohon waje dake cikin makarantar wadda an fara gyara wajan aka barsa zaune Abdallah yake yasha wani askin y'an iska ajemai ita sukai wata irin dariya ya shek'e da ita nuna masu hanya yayi kan su fita suma zasusha garabasar cike da murna zasu kwashi dad'i suka fice haka bawan Allah nan Abdallah baiji tausayin ta baiji kunyar Allah ba baiji cewa Allah na kallonsa ba ya tub'e kayan sa haihuwar uwarsa ya keta ma Rayha mutumcin ta yana gamawa da ita ya tashi yana tufa mata yawu yana kiran sauran Abokan sa su hudu yana tsaye yasa suka rink'a keta mata mutumci har wani dariya yake zuciyar sa ta bushi da tsananin mugun ta ita kuwa Rayha duk da ba cikin hayyacinta take ba hakan baisa ta rasa gane wani irin hali take ciki ba wasu irin hawaye masu d'umi ne suka shiga bin fuskar ta, Aamah kuwa zuciyar ta ce ta kasa sukuni ta fito ta nufu cikin school d'in cin karo sukai da Ikilima da sauri Aamah tace "ina Rayha dan Allah?" Da sauri tace "bata dawo ba ai ana cikin lecture ta fita" wata irin bugawa zuciyar Aamah tayi bakinta ya kasa furta komai da sauri Ikilima ta jata suna dubawa ko Allah zaisa a ganta chan suka hange kamar d'an kunnan Rayha da sauri Aamah ta d'auka tana fashewa da kuka kamar ana tunkud'a ta wajan ta doshi wajan zuciyar ta na k'ara bugawa Ikilima na kiran ta cewa bafa zataje nanba babu wadda yake zuwa wajan amma ina bata ma jinta bare ta saurare ta ganin haka yasa Ikilima bin bayanta tana shiga wajan taga su Abdallah ga Rayharta kwace ba kaya da sauri ta nufi wajanta ta cire gyalanta ta rufe mata jiki rungume tayi tana fashewa da wani irin kuka numshinta ne ya d'auke ta zube a sume Ikilima ma na shigowa nan take ta zube ita ma sume Abdallah kuwa ko a jikinsa saima nufar k'ofar fita yayi shida y'an iskan Abokansa wata irin guguwace ta turnik'e wajan idanuwasu suka rufe bud'ewar da zasuji sukai tozali da wani irin narkeken maciji ba wadda hantar cikinsa bai kad'a ba a cikinsu ja da baya suka rink'a yi zasu ruga amma ina haka Bijay ya nannad'ossu su uku yayi masu sari lafiyayye nan take suka zube babu rai a tare dasu mutane ne suka fara shigowa wajan da hukumar makaranta jin ihu na fitowa daga wajan Abdallah kuwa da wani abokinsa da suka rage wani mai suna Shamsu ganin macijin ya nufu su gadan-gadan yasa su sume wa ba shiri jin motsin mutune yasa bijay bacewa yana wani irin kuka mai ban tausayi shikenan nan ya k'ara rasata a wannan karanma da k'afin yace "wallahi sai naga bayanku bazaku sha ba saina kasheku kai da kayi musabbabin abun saina gana ma azabar dasai ka gwammace mutuwa da rayuwa" yana kallon Abdallah cikin idanuwansa yana kallon duk abinda ya faru wata irin k'ara ya saki yana cewa "A'ahhh bazai yuwuba karkuyi mi yasa y'an Adam da yawansu basu tsoron Ubangiji ne" duk ya fita hayyacinsa kamar zararre............✍️ *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *KU KYAUTATA WA MATA INJI MANZON ALLAH S.A.W* Manzon Allah (SAW) yace: kuyi wasilcin alkhairi ga mata, domin ita mace an halicceta ne daga qashin haqarqari, wanda yafi karkata shine qashin haqarqari na sama, idan ka tafi domin ka miqar da shi sai ka karya shi, in ka barshi dai ba zai gushe ba yana nan a karkace, don haka kuyi wasilcin alkhairi ga mata". Bukhary da Muslim🙏🙏 *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣ __________________✍️ Amreeta wani murmushin mungunta tayi jin ta tuno wani shiri daban dariya tayi mai cike da zallar mugunta ta bace bat bata sauka a ko ina ba sai a gidan Sulaiman tsayawa tayi k'ofar gidan tana murmushin munguntar Shirin da tayi. Shi kuwa Aliyu d'akko wayarsa yayi ya kira Aliya koda ta d'auka ya tabbaye ta da ina da ina taje yau cewa tayi duk yau bata fita ba abinfa ya k'ara bashi tsoro ta ina tasan Aliya (ni ko Zahra nace kaima Aliyu yo abu da ba mutum ba taya za'ai ta kasa sanin komai kuma). Amreeta ta ko bacewa tayi ta sauka a d'akin matar Sulaiman ta juya baya tana sa kayan bacci dan dare ne wani murmushi tayi sana ta d'ora hannunta kan matar tasa nan take wani nannauyan bacci ya sure ta samun wani waje tayi ta b'oye ta inda ba wadda zai ganta sana ta rikid'e ta zama suffar matar Sulaiman komai da komai da kayan data sa sak ita babu wani mahaluk'in da zaice wai ba ita ba ce. Cike da takunta najan hankali ta nufi d'akin Sulaiman yana zaune yana shan shayi dan Matar tasa bata dad'e da kawo mai ba. Cike da kissa ta tak'o sai kuma ta d'an ja birki ganin d'an hannun nan wadda indai yana tare dashi bata ikon mashi komai. Cike da kissa da kisisina irin ta mata ko nace ta gaggun y'an duniya ta taku wajansa tana turo baki irin na shagwaba nan girgiza ta farayi da jikinta duk wani albarkatun jikinta ya fara motsawa da sauri Sulaiman ya runtse idanuwansa ganin ta fara tada mai hankali da sauri yakai hannunsa nufin ya kamota gocewa tayi da sauri ya tashi wajan tashi bai lura ba dan hankalin sa naga matar sa abin gado yaja abin hannun ya watse a k'asa amma hakan baisa ya lura ba dan kuwa d'an hannun dama ba kama hannun su yayi ba irin mai saku-sakun nanne. Ita kuwa cike da tsananin murna ta matso garesa tukan ya k'ara su tunda abinda yake mata shamaki dashi ya tsinke, Turasa tayi kan gado tana d'anewa jikinsa wani irin kallo yake binta dashi ganin matar tasa ta k'aro wani salo na daban, bai aune ta had'e bakin su waje d'aya wani irin kiss take mai cike wani salo wadda yasa bai shirya ba ya rink'a had'e miyan da take zubamai ji yake kamar sweet ce yake tsotsa da wannan damar tayi anfani ta samai tafin ta na maciji, Dai-dai wannan lokacin ta turesa daga jikinta da saurinsa ya rik'ota turesa tayi da k'arfin gaske fad'awa yayi kan gadon ya fara wani irin tari numfashinsa na tsark'ewa dariya Amreeta ta saki mai sauti tana zama ai nihin suffar ta tace "lallai zuciyata ta kusa samun salama na kusa k'arar daku a doran duniya tabbas *RUHI BIYU* Zai samu salama ruhin Amreeta da kuma mijina" ta idasa maganar tana fashewa da wani irin kuka zuciyar ta na sosuwa tunawa da wad'anda take so a rayuwarta amma babusu a duniya ita kanta duniyar bata mata dad'i. Shi kuwa Sulaiman dake kakarin mutuwa kunfa na fita daga bakinsa magana yake so yayi amma ina numshinshi ya fisga rai yayi halinsa, Amreeta ko a jikinta ta juya wata irin girgiza tayi ta bace bat........... ***************** Hukumar makaranta ganin abinda ya faru sun girgiza ainun da gyar aka samu su Ikilima suka farka Ikilima kuka kawai take kamar ranta zai fita Aamah kuwa tunda ta farka ta zama kamar tab'ab'b'iya da sauri ta matsa wajan Rayha dake mik'o mata hannu ta farka hawaye ne kawai ke shatata a idonta rik'e hannunta tayi tana fashewa da kuka mai ban tausayi Rayha da gyar ta iya bud'e baki tace "Aamah ki yafe min nasan mutuwa zanyi rayuwata bata da wani anfani kicewa Momy ta yafe min in....... Da sauri Aamah dake kuka tana girgiza kai cike da fitar hayyaci tace "bazaki mutu ba kuma insha Allah, Allah bazai barsu ba yanzu kam nasan ba wani mataki da za'a iya d'auka a kansu dan ya kasance d'an wani amma Allah yana gani dan Allah ki daina fad'ar wannan maganar" tari Rayha keyi numshinta na fisga tana hawaye masu ciwo da rad'ad'in abinda akai mata wadda yanzu a k'asa Najeria indai ka kasance kai ba d'an kowa bane akai ma abu to babu wani mataki da ake d'auka saima aima abun rufa-rufa abar zancan gaba d'aya ina kuwa rayuwa zata ci gaba shuwa gabanni ba adalci kowa cikinsu kansa kawai ya sani sai iyalinsa, Tace "kayya Aamah wannan rayuwar cike take da rud'u da abubuwan ban tsoro nikam nasan rayuwata ta k'are naji a jikina ki doba ki gani mutum nawa ya keta min haddi rayuwata bata wani anfani koda Allah baid'au raina ba kina ganin za iya rayuwa mai dad'i ne ina fata na zama mai k'arfin hali na rashina da zakiyi" ta ida maganar tarin na k'ara yawaita aman jini ta fara cikin tsananin tashin hankali wadda bazai musaltu ba garesu Aamah ta k'ara fashewa da wani marayan kuka tana k'ank'ame ta jin tana farta kalmar shahada jikinta ya saki lokaci guda da sauri Aamah ta fara girgiza kanta tana nunawa mutane cewa "bata mutu ba fa ku tasheta dan Allah Rayha karki min haka" kuka take magana kai da ka kalleta kasan bata cikin hayyacinta Ikilima kuwa kuka kawai take, Hukumar makaranta kuwa su duka aka kwasa sai asibiti sai dai tun a san nan aka shaida mutuwar Rayha tuburar Aamah haukace masu tayi itafa Rayhanta bata mutum ba inda hukumar makaranta taji wadda yayi abin zaima sukayi gum da bakinsu inda sai dai kawai gwamnatin jihar tasa aka kalle makarantar gaba d'aya amma dan wani d'aukar mataki akan su Abdallah babu ma wadda ya taso da zancan. A motar asibiti akasa gawar Rayha da Aamah da Ikilima da duk basu cikin hayyacinsu aka nufi gwabbe dasu. A wajan Momy kuwa tun jiya take jin fad'uwar gabanta ya tsananta ga jikinta dake k'ara sanyi haka nan sai taga hawaye na tarowa a idanuwanta haka yasa take ta kiran su Aamah d'in amma bata shiga gaba d'aya wayoyin nasu nanfa hankalin ta ya k'ara tashi sosai duk bayan wasu mintuna sai ta gwada kiransu amma dai amsar d'aya ce bata shiga tabbas tashin hankalin da take ciki bazai musaltu ba dan kuwa numfashinta har sark'ewa yake k'arar moto taji irin ta asibiti ta tsaya a k'ofar gidan da sauri ta mik'e zuciyar ta na lugude diff dumm diff dumm dumm hawaye ne ya tsinke mata tunkan tasan mike faruwa, Aamah ce ta b'alle murfin motar ta shiga cikin gidan da gudu tana shiga ta fad'a jikin Momy tana fashewa da sabon kuka Momy kuwa saddarewa tayi bakinta na b'ari tace "Aamah mi yasa mi y'ar uwarki ?" Ta jefa mata tabbayar kasa amsa mata tayi Ikilima ce ta shigo itama tana kuka to nan fa Momy hankalin ta ya k'ara tashi fiye da da, cike da kaushin murya tace "wai bada ke nake magana ba kiban amsa nace ko mutuwa tayi ku gaya min" gaba d'aya sun kasa furta koda kallama d'aya ce jin hayaniya a tsakar gidan da sauri Momy ta ture Aamah ta nufi waje da sauri Aamah ta bi bayanta ganin motar asibiti ta shigo har cikin gidan dan kuwa get ne kuma tsakar gidan akwai fad'i daskarewa tayi a wajan ganin ana fiddo da gawa lullub'e da farin mayafi (likkafani) bayani suke mata na k'arya da gaskiya suna ajiye gawar suka juya sukayi Tafiyar su Momy zuciyar ta cewa take ina ba Rayhanta bace ba ita bace bata mutum ba da kyar ta ja k'afa funta ta matsa kusa da gawar tashin hankalin da ba'a sa masa rana su duka Aamah Durk'ushewa sukai wajan gawar hannun Momy na kyarma ta kai hannunta akan gawar tana yaye abinda aka rufeta dashi saddare wa tayi tana zare ido wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga bin fuskar ta zuciyar ta na buguwa da mahaukacin k'arfi kawai saita rungume gawar tana fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciyar duk wani mai imani Aamah ma kuka take har yanzu fuskarta ta kunbura tayi sumtun zaboda da tsananin kukan data sha mak'otansu ko ta ina shigowa suke da y'an uwa gida ya riki ce da koke-koke da kyar Aamah ta bari aka yiwa gawar Rayha wanka Momy kuwa Suman ta yafi biyu data farka taga Rayha ba rai saita sake suma har saida wani limami yashigo yayi mata wa'azi mai ratsa zuciya cewa Allah ne fa ya bata Rayha kuma shiya amsa abinsa kuma komi akai mata Allah baya bacci tabbas subar su da Allah tun a nan duniya Allah yake fara hukuncin sa su basuda k'arfin shari'a dasu kam amma ai akwai Allah yanzu kawai abinda Rayha take so shine addu'a. Sosai nasihar limamin ta shigeta sai dai har yanzu kuka take kamar k'aramar yarinyar, Tofa tashin hankali sai da aka zo fita da gawar Rayha su duka uwa da y'a da kyar aka b'anb'are su suna kuka kamar ransu zai bar jikinsu Momy fad'i take inshallahu wadda sukai miki wannan cin kashin tun a duniya basai anje rahira ba Allah zai fara saka miki bamu yafe ba Ubangiji Allah ya isar mana, haka take ta maimatawa tana kusa da gawar gawar aka d'auka ganin cewa gadan-gadan za'a fita da ita Aamah da takasa jurewar cewa fa shikenan ita da k'ara ganin Rayhanta mutuwa mai yankan k'auna rigijif akaji fad'uwar Aamah a sume............✍️ *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* PAGE1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣ __________________✍️ Washe garin ranar aka tashi da labarin mutuwar Sulaiman matar sa kuwa kwata-kwata bata cikin hayyacinta tofa mutane da yawa sun d'iga ayar tabbaya akan wa'inna Abokai har an fara k'ananun maganganu kala-kala wasuma cewa suke ai k'ungiyar asiri suka shiga shine suka bijire ake masu d'auke d'ai-d'ai, Tofa maganar mutane tasa sun k'ara shiga rud'o da tashin hankali shida Mustapha da Aliyu wadda duk cikin Abokansu su TAKWAS su kad'ai suka rage sosai suka shiga tashin hankali inda suka tattauna cewa kar su k'ara yarda da kowa sana su rik'e d'an hannun nan da kyau dan kuwa ta ko wacce suffa zata iya zuwar musu dan Aliyu ya basa labarin zuwar mai da tayi lallai Mustapha ya k'ara shiga rud'o da dana sani sosai, Mustapha da kyar ya bud'e baki yace "koda na mutu Aliyu na tabbata zaka rik'e min yarona da kyau Amana Dan....... Da sauri Aliyu ya dakatar dashi da cewa baya son irin wannan maganar dan Allah ya daina. Mustapha kuwa tashi yayi kawai yana girgiza kai ji yake tabbas shima ya kusa mutuwa jiki a sanyaye ya shiga gidansa ganin kayan Al'ameen na school zube a k'asa da alama ya dawo school kiransa ya fara yi "Al'ameen!! Al'ameen!!!" Yana sama ya amsa da "na'am Abbee gani nan sakkowa" jin shuru bai sakko ba zai sake magana yaji ihun Al'ameen cike da tashin hankali yake kiran sunansa kuka yaron kawai yake ya kasa magana da sauri Mustapha har yana tuntub'e ya hauwara saman shigarsa d'akin yaron wani abun birki yaja zuciyar sa tayi wata mahaukaciyar bugawa zubewa yayi k'asa ganin Al'ameen Amreeta ta zama sharb'eb'iyar macijiya ta nannad'e yaron ta saita kansa sari kawai ya rage ta kaimai da sauri baikin sa har yana kyarma yace "kiyiwa Allah ki rabo da yarona karki cutar dashi ba abinda ya sani" ya idasa maganar yana fashewa da kuka Amreeta kuwa wata dariya ta saki tace "ashe kunsan Allah kunsan dashi kuma kuka cuci bayinsa har wani kai kasan imani a nan sana kuma indai kana son d'anka a raye to ka cire wannan d'an hannun inba haka ba zan kashe shi a madadinka" cikin tashin hankali yake kallon d'an hannun da d'an macijiya ya basa innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai yake mai-maitawa, Wata uwar tsawa ta daka mai "zakayi abinda nace ko kuwa baka son rayuwar d'an nakahhhh" ta ida maganar a tsawace har hannunsa na kyarma yakai hannunsa zai zare d'an hannun yana cewa "a'a a'a dan Allah ki bari zan cire" cirewa yayi ya wallar dashi wata irin dariya ta kece da ita tana sulalewa ta rabo da yaron bata wani bata lokaci ba tayi salle ta kaimai sara a dai-dai wuyansa ta b'ace ta bar gidan kwata-kwata, Zubewa yayi k'asa yana sakin wata k'ara da sauri Yaron ya matso kusa dashi yana kuka da ihu yana girgiza Abbeensa kukan yaron yasa har waje ana iya ji, Haka kawai Aliyu na zaune yaji yana so yaje gidan Mustapha dai-dai yana shigowa yaji kukan yaron a sama da sassarfa ya k'ara sa ganin abinda ke faruwa ya matuk'ar tada mai hankali da sauri ya k'ara so yana kama hannun Mustapha yana girgiza sa hawaye yake yana cewa "ya zakai min haka kaima karka tafi ka barni kagafa ni kad'ai na rage karka tafi kaimahhhh" ya idasa maganar yana fashewa da kuka kamar k'aramin yaro, Mustapha kuwa dake gab'ar mutuwa ya kama hannun yaronsa Al'ameen ya sashi a na Aliyu yace "Aliyu ga yaro na na baka shi halak malak ka rik'e min shi da amana nasan zaka iya tabbas nasan Allah yanzu bazai bata iko a kanka ba saboda baka da laifi ko a wajan Allah tabbas ina ji a jikina zaka kub'uta daga kaidin wannan maciji in...... Tari ne ya sark'esa jikinsa yana chanza kala idanuwansa sun fara kafewa aman kunfa da yake jikinsa ya sake rai yayi halinsa wata irin runguma Aliyu yayi ma Mustapha yana fashewa da kuka shi kansa Al'ameen kuka yake dan kuwa yasan mutuwa tunda ana masu wa'azi a isilamiya cewa duk wadda ya mutu bazai dawo ba ya tafi kenan inya tuna wannan abun sai ya k'ara sakin kuka mai tab'a zuciya shikenan bazai K'ara ganin Abbeensa ba da sauri Aliyu ya rungume Al'ameen suna kuka a tare kyar suka sanarwa mutune aka kaisa gidansa na gaskiya wajan fita da gawar sa kuwa da kyar aka b'anb'are Al'ameen ba wadda bai tausaya masu ba shida Aliyu sun tasu tare amma yanzu ba ko d'aya, Aliyu bayan an dawo kaisa a zuciyar sa ya yanke shawarar barin garin............. **************** Rigijif akaji fad'uwar Aamah a sume da sauri mutune sukai kanta da kyar aka samo likita ta farka tana kuka kamar zata shid'e ganin haka likita yayi mata allurar bacci dasa mata k'arin ruwa ita kanta Momy ganin bata cikin nutsuwarta yasa itama aka sa mata k'arin ruwan mutune tausayin su fal a ransu dan ita kanta makarantar abinda yasa suka shigeta suna da k'ok'ari sosai hakanne yasa tun a secondary hukumar makaranta ta biya masu zuwa wannan school d'in dan basuda kud'in da zasu iya biya masu kud'in wannan makarantar tabbas k'addara ce ta kaisu wannan makarantar. Bijay kuwa dashi aka kai Rayha yayi kuka harya gaji ba wadda yake ganinsa sai akai Addu'r uku yana garin sana ya koma Ruman domin shirin d'aukar FANSA dan bazai tab'a yafe masu ba har suyi rayuwar jin dad'i. Bai sauka a ko ina ba sai gidan su Shamsu Abokin Abdallah dan takansa zai fara Abdallah hukuncin sa na dabanne, ganin irin gidan mai kyan gaske da matakan tsaro a zuciyar sa yace taya za'ai kuwa a hukunta su suna y'ay'an jiga-jigai, Hango wani d'an aiki yayi zai shiga part d'an Shamsu da abinsha dan ba'a dad'e da sallamo su daga asibiti da sauri ya b'ace ya sauka kusa da d'an aikin jin kamar mutum yana binsa da sauri ya waiga ganin ba kowa yasa ya cigaba da tafiya Tafiyar dai ya k'ara ji a bayansa da d'an fad'a-fad'a yai waigo nufinsa ko wani cikin y'an aikinne ke binsa yana so yayi mai wasa wani abu Bijay ya fesa mai danda nan ya tafi dogon bacci chan wani lungu ya ajiyesa ya dafe kansa ya dawo suffar d'an aikin sak da d'an hanzari ya d'au abinda shan wadda za'a kaima Shamsun d'auka yayi yana kallon abin shiyi ne wani abu ya d'akko a jikinsa yasa a shayin danshi bazai sa masu dafinsa a'a saiya basu wahala a rayuwa inya so daga baya su mutu, Shiga yayi yana zaune yana kallon boll kamar ba abinda ya aikata jin an bud'e k'ofa yasa ya waigo ganin d'an aikinsa yasa ya tsine baki yace "ajeshi nan" yana nunamai wani teburi dake kusa dashi ajewa yayi kamar yadda yace sana ya d'an tsaya a kansa cike da isgilanci da raina talaka ya buga mai wata uwar tsawa cewa "kai miye na tsawa kuma kama hanya ka fice min daga gani sai wari kake ma" wani munafikin murmushi Bijay yayi yana juyawa ya fice kwata-kwata daga gidan, Shi kuwa Shamsu yana kallon boll yana murna wadda yake so sunci yakai shayin bakinsa duka ya shanyi saboda dad'i da gama shan shayin ya fara tari amma duk da haka ihu yake na kallon boll d'in jikinsa ne ya fara wata irin mika yana lallauyewa ya zube a k'asa bakinsa ya karkace hannuwansa sun lauye duk jikinsa ya shanye ihu yake yana k'ara wa ganin abinda yake faruwa dashi anya shine kuwa da sauri ahalin gidan sukayo parta d'insa jin ihunsa cike da tashin hankali ganin abinda yake faruwa da sauri aka kwashesa sai asibiti Daddy d'insa kuwa duk ya rud'e dan mahaifiyarsa ta rasu babban asibitin garin aka kaisa cikin sauri aka amshe sa iya bincike likitoci sunyi bincike amma basuga komai ba tashin hankalin iya tashin hankali Daddyn Shamsu ya shiga likitoci sunmai bayani sufa basuga komai ba kawai shanyewar jikinsa ya shanye wadda bazai K'ara moruwa ba sai dai zasu rik'e sa asibitin su d'ora sa a magani aga abinda Allah zaiyi Daddy sosai ya shiga rud'a ni ba kad'an ba haka aka ci gaba da jinyarsa ana basa mgani amma sauki sai wajan Allah kam jiki na nan a lallauye baki ya karkace har miyau ke jalala ya zama musaki tuburar. Kamar yauma bayan an basa magani kowa ya fita daga d'akin jinyar Bijay ya shigo d'akin a matsayin likita zama yayi yana murmushi kallonsa kawai Shamsu keyi ba bakin magana dan ko magana ba iyawa yake ba shafa fuskarsa yayi yana cewa "saka makonku kenan sai kuma na Allah in kunje can ai nasan bazaka manta da Rayha wadda kuka cutar da rayuwar ta ba kukai sanadiyyar mutuwar tahhhh" ya ida maganar da k'arfi har gadon da Shamsun ke kwance na girgiza Shamsu kuwa fitsari ya saki nadama ce ta dirar mai marar anfani kuka yake hawaye kawai ke zuba ga baki dake mutsi yana so yayi magana amma inah Bijay kuwa ya k'ara cewa "ai kaida magana har abada kaida tashi ma sai dai kaga wasu nayi" bat Bijay ya bace ganin abinda ya faru yasa jikin Shamsu k'ara rikicewa na'ururi jikinsa suka fara k'ara da sauri likitoci suka shigo ganin numshinsa na gaf da d'aukewa taimakon gaggawa suka fara bashi amma ina numfashi ya tafi saboda abinda ya faru zuciyar sa ta bugu likitoci suna share zufa suka fito lokacin Daddyn Shamsu ya k'ara so bayanin da likitoci suka mai ba k'ara min girgiza yayi ba da kyar aka samu ya dawo hayyacinsa aka d'auki gawar sa sai gida mutanan gidansu da ma'aikata kuwa wasu sunji mutuwarsa wasu kuwa ko a jikinsu dan kwata-kwata bashida kirki haka dai aka kaisa gidansa na gaskiya daga shi sai halinsa..........✍️ *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️ Comment and share Fisabilillahi🥰🙏 *🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉* MALLAKIN *©FATEEMAH RABI'U* *(ZAHRAH ROYAL STAR)* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Marubuciyar : *1-RAYUWA* *2-WATA RANA SAI LABARI* *3-ASMA'U (MA'U)* *4- SA'ADAHTU* *5-YAZDAD* *6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI* *7-RUHI BIYU* *NOW* *FANSAR MACIJIYA* *GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.* *بسم الله الرحمن الرحيم* *وصلى الله عل النبي الکريم* *PAGE D'IN K'ARSHE1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣* ___________________✍️ cikin k'ank'anan lokaci Aliyu da kuma d'ansa na yanzu Al'ameen ya gama had'a kayansu inda saura kwana biyu subar garin da yawan mutane na zomai gaisuwa Kamar yauma bayan wasu sun fita Al'ameen na zaune akan ciyarsa duk ya zama abin tausayi, tashi yayi yana kallon Aliyu yace "Daddy ruwa zansha" (da yake haka Aliyun yace daga yau ya rink'a kiransa da Daddy, Da sauri Aliyu cike da k'aunar yaron ya tashi ya zaunar dashi yaje d'akko mai ruwan dawowar da zaiyi ya hangi kamar gilmawar mutum da hanzari ya yunk'ura zai rungume Al'ameen yaga tashin abu sama ya nufi inda Al'ameen yake Allah yaba Aliyu sa'a har yana fad'uwa ya k'ak'k'ame Al'ameen a jikinsa waigawa yayi ganin wata narkekeyar macijiya sai uban huce take tsalle zata k'ara yi ta kaima yaron hari dan bata da ikon tab'a Aliyu saboda karinyar da yake da ita. Sai dai Allah mai rahama ne da yake Aliyu bashi hakki akan duk abinda ya faru, tsallan da tayo ta afkama window dake kallon waje, window d'in ya tararratse duk ya caketa (kunsan maciji indai wani abu yayi mai rauni to tabbas ba lallai ya tashi), to haka ta kasan ga Amreeta dan fad'awar da tayi duk gilas d'in window ya caketa sai kuma tayi rashin sa'a ta fad'a akan wasu k'ayoyi masu mugun tsini, Da sauri Aliyu ya fita yana kallon yadda duk k'ayoyin suka caketa shida Al'ameen kallon abun suke kamar almara, kwance take akan k'ayoyin sau wani irin huce take fiddawa na tsananin azaba rikid'ewa take a hankali har ta zama suffar mutum cikin tsoro Aliyu yaja baya Al'ameen dake jikinsa ya k'ara k'ak'k'ame sa, Ita kuwa dake gab'ar mutuwa tana kallonsu tana murmushi tace "tabbas baka da laifi zan tafi nabar wannan duniyar da farin-ciki na cika burina na d'aukar wa mutanan da sukafi soyuwa a gurina *FANSA*" daga kanta tayi sai ta rink'a hango Khausar d'in ta da Mijinta suna mata murmushi sanye da fararan kaya suna mik'o mata hannu, Murmushi tayi ta k'ara kallon Aliyu da cewa "ka gani suna kira nazo su tafi dani inda suka tafi" tana murmushi yaga ta muk'a hannunta gani yayi ta bace bat a wajan kamar ba'ayita ba. Ba k'aramin sauke ajiyar zuciya Aliyu yayi ba lallai Allah yana sonshi da rahma sujadda yayi ta godiya ga Allah daya karesa, Aliyu bai fasa barin garin ba dan kuwa Washe gari yabar garin da d'ansa ya sauka a garin da masoyiyarsa take wato Aliya garin KANO Take da zama yazo da uwar kud'in sa yasai gida madai-daici inda baiyi k'asa a gwaiba ya nemi auran Aliya ba'a wani ja lokaci ba aka basa auranta. Bayan aure da kwana biyu zaune suke ita da Aliyu Al'ameen nakan jiyarta zai zuba mata shagwaba yake inda Aliyu ya gama bata labarin irin abubuwan da suka fuskanta a rayuwa har kuka tasha jin wannan labari mai rikitarwa cike da kwanciyar hankali suke zamantakewarsu gwanin sha'awa inka kallesu da Al'ameen baka tab'a cewa wai basu ne iyayansa ba sosai Aliyu ya samu cigaba a rayuwarsa inda dukiyar Al'ameen ta mahaifinsa yana tattalamai yadda ya kamata inya girma yayi hankali ya basa abinsa zaune suke lafiya da matarsa Aliya data gansa cikin damuwa to yana tunowa da Abokansa ne zatayi iya bakin k'ok'arin ta wajan kawutar mai da damuwa rayuwarsu sun abin birgewa da Soyayya mai tsayawa a zuciya.................. ****************** Tofa koda Abdallah yaji mutuwar Shamsu lokacin yana masha'arshi tare da wata karuwarsa yad'an ji mutuwar kad'an ya jigaba da sha'aninsa ita kuwa karuwar sai k'ara wani narkemai take dan tasan abin ta kunsa mai dan kuwa d'auke take da cutar nan mai karya garkuwar jiki baccin nan d'auke take da wani mukuguwar cuta dake gabanta, Tunda yayi ma'amula da wannan karuwar tasa gabansa ya kama k'aik'ayi gaban kowa yana iya zura hannu a wando ya kama kartar gabansa yana lumshi ido saiya gama kuma wani rad'ad'in azaba ke ziyarceshi haka zai kama kuka tuburar koya tub'e kayansa a gaban kowaye, Tofa nan mutane suka zancen koya haukace ne wasu daga cikin su kuwa har video sukai mai ana dora a duniya innalillahi wa'inna ilaihir ahalin Abdallah bare Abbansa ya shiga tashin hankali Mamarsa kuwa yanke jiki tayi ta fad'i ganin videon d'anta a duniya tunb'ur haihuwar uwarsa yana susar gaba da alama bai san ana videon ba. Abu fa sai gaba-gaba yake dan kuwa saida aka dangana da asibiti to a asibitin ma dai sun d'ora sa a magani amma ina dan gabansa mazakuntarsa ta kunbura tayi sumtun ga kurajen sun fashe ga wani aban d'oyi da wajan ya farayi inda Bijay duk yana kallon miyasa meshi lallai ya k'ara yarda Ubangiji baya son mugunta gashi tunkan ya d'au mataki ta Allah ta sameshi duk da haka saida ya ziyarce sa har asibiti a matsayin likita ya basa Maganin daya ba Shamsu dan kuwa Aliyu na iya magana saidai yana cikin mawuyacin hali tofa bayan Bijay yaje ya basa wannan magani yasha da rashin sanin waye ya basa tashin hankalin da ahalin Abdallah suka sake shiga shine shanyewar jikinsa baki ya saki yana jalalar da yawu ga hannu a babbank'are Bijay kuwa ya bacewa cike da tsananin murna na sakama Rayha Ubangiji yayi tun kan aje ko Ina. Jikin Abdallah fa in gabansa ya tashi k'ak'ayi ba sauk'i gashi jiki ya shanye birgima yake kamar mahaukaci yo gara ma wani mahaukacin dan kuwa d'ankin da yake wani irin mugun wari yake wadda yasa mutane da yawa in suka shigo da gudu suke guduwa tsananin warin da d'akin yake mutane da yawa sun gujeshi ciki harda y'an uwansa daga iyayensa su kad'ai suma sai sunkai zuciya nesa suke shigowa in sun shigo ba wani dad'e wa suke iyayi ba to Mamarsa kuwa tun sadda ta fad'i hawan jini ya kamata bata iya komai asibitin ma kansa ganin sai korar masu mutane yake yasa suka sallame sa ba shiri koda aka kawosa gida can aka ware mai wani d'aki inda kowa bai shiga can wajajan masu aiki ko abinci za'a basa sai dai a warga mai ga gabansa sai k'ara ruwa yake har wasu tsutsotsi sun fara fitowa ta gabansa zuwa wannan lokaci yasan cewa alhakin Rayha ne ke bibiyar sa a yanzu ya gwammace mutuwa da rayuwa kullum cikin rok'on Allah yake daya d'au ransa dan mutu ai hutu ce da wannan bala'in da yake ciki duk da yasan koya tafi lahilar wani jan aikinne a chan Zaune su Momy suke da Khausar daka kalle su kasan farin-ciki yayi k'amari a rayuwarsu dan har yanzu basu dawo dai-dai ba Momy data g damuwar tayi yawa ta tashi ta kunna tibi dan rage damuwa dan rabonsu da wani kallo harsun manta tashar labarai ta kai dai-dai an hasko gawar Abdallah Allah yayi masa rasuwa bayan tsawon jinyar daya sha zaro ido Momy da Khausar sukayi ganin SAKAYYAR da Allah yayiwa Rayhansu lallai Allah buwayi ne gagara musali godiya suke ga Allah ga wasu irin zafafan hawaye na zuba ta idanuwansu tunuwa da Rayha Aamah tace "Momy kinga ni ko tun a duniya ma kenan" ta ida maganar cike da marin cikin wannan abu Momy kuwa hawaye take na tsananin godiya ga Allah daya sakawa d'iyarta tun a duniya. A wajan gidan su Abdallah kuwa da yawa farin-ciki suke da mutuwarsa dan duk ya ishesu da wari a cewarsu dama akan k'aya suke dan da kyar aka samu masu mai wanka sun dod'e hanci da kyar da kyar suka k'arasa mai duk da sun dod'e hancin haka aka sallace sa aka kaisa gidansa na gaskiya daga shi sai abinda ya shuka. Kai jama'a muji tsoron Allah mu daina biyewa sun zuciya da rud'in duniya miyasa dad'in da bai tab'a tsallake shekara ɗari na a duniyarka zai rud'eka ka manta da dubbunan shekarun dake gabanka na barzahu kawai?, miyasa dad'in dake k'alilan na duniya zai rud'eka ka manta da ranar hisabi ranar da bata da kwatankwaci ko misali😭?, ga dai Abdallah ji karshan sa, akwai ranar rarrabe gaskiya, ranar tonon silili, ranar da uwa ke gudun d'anta, ranar da d'a ke gudun iyayensa, ranar da kanka kawai ka sani, ranar bud'e b'oyyayun sirrika😭 (Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un) y'an uwana! Y'an uwana! Mi muke tunani haka da zurfine? Mi muke buri haka da yawane? Mi muke fatan samu haka da yawane? Mi muke k'ok'arin mallaka haka da yawa ne? Mi yake canjamu haka da yawane? Mi yake rud'armu haka da yawa ne? Mi muke tak',ama dashi haka da yawa ne ji Abdallah duk dukiyar sa data babansa yanzu tana ina ina tak'amar take? Da mi muka dogara haka da yawa ne? Suwa muke tunanin ko zaton sun tsaya mana haka da yawa ne? Ina mukabar imaninmu tafiya haka da yawa ne? Ina muka bar zukatanmu haka da yawa ne?😭😭. “🙏🏻😭Ya rabbi ka gafarta mana badan halinmu ba”. Allah ka tsaremu da mummunanr k'addara ya Ubangiji Allah ka tseratar da zukatanmu da gangar jikinmu aikata sab'onka ya Ubangiji.............. Alhmdllhi Alhmdllhi Alhmdllhi Allah na gode ma daka bani ikon kammala wannan d'an tak'aitaccen labari nawa Ubangiji Allah darasin dake cikin wannan book Allah ya bada ikon anfanuwa dashi illar dake ciki kuwa Allah yasa ayi watsi da ita Ina k'unar ku Masoya na irin sosai d'in nan a duk inda kuke fad'in duniya. Sai kun sake jina a wani sabon book nawa in sha Allahu. *FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)* PHONE NUMBER_08130479973 Email address_ rabiufatima43@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels