An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_01_* *_MALAYSIA (SABAH)_* ..........A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani fara waige-waige a falon. Tabbas ba'a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine.             Takun sakkowa da stairs ɗin da'aka kawata adon falon da shi ya sani maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_* a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.          “Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fashi zuwa Nigeria ki zauna agareki, k idan ma kika ƙuleni ALLAH kin koma can da zama kenan keda ƙasar nan sai yawo”       Sautin kukan da aka sake fashewa da shi ya sani waigawa da sauri, ƙyaƙyƙyawar budurwa black beauty mai ɗaukar hankali da sam bata kama da matar a yanayin jiki sai na kamannin jini kaɗan. A ƙiyasi na yanayin jiki kai tsaye zance bata wuce shekaru sha bakwai ba. Sai dai a mizanin hankali da sanin masu irin yanayin jikinsu wajen ɓoye shekaru zan iya karyata zuciyata. Amma kai tsaye ban san shekara nawa zan bata ba. Dan sam bata da wani tsaho, tana nan dai ƴar cif-cif ga karamin jiki ga rashin tsayi kamar wata ƴar kanwata can (😂🤣ban dai faɗi suna ba ato😜). Tabbas kyaƙyawa ce, dan duk da kukan da idanunta suka nuna alamun taci hakan bai hana bayyanarsu dara-dara ba duk da suna a cikin farin siririn gilashi. Ga gashin gira da dogon hancinta (kamar na bilyn Abdull🙄 saura wani yace ba haka ba, bansan jealous😒😜). Kai atakaice dai yarinyar masha ALLAH. Sosai hawaye ke cigaba da bin kumatun ta tamkar an bude fanfo. Matar daketa masifar ta sake zuba mata harara a kausashe tace,           “Haɗiye min kukan nan kafin nazo na sassafa ki a wajen sakarar banza”.      Da ƙyar ta shiga ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Sai dai hawayen sunƙi riƙuwa. Cikin rawar murya ta dubi kamilar matar da take kamani da ita a ɗan fisge, “Mamie na tuba ALLAH na daina duk abinda baƙwaso ke da Abie ”.       “Dainawar taki ko cigaba bazai miki amfanin komaiba ai, dan zuwa Nigeria dai babu fashi tunda kin san abu mai muhimmanci ne zai kaiki. Dolene kije kiyi saves ɗinki a ƙasar haihuwarki kodan gaba zai miki amfani, dan nan ɗin da kika ɗauka ƙasar uwa da uba ta aro ce lokaci kaɗan ya rage mu barta muma ta ishemu”.        Kuka ta sake fashewa da shi tana daddaga ƙafa. “Ni wlhy bana son Nigeria, zafi, sauro ga shegen hayaniya. Ni basai nayi saves ɗin ba dan bazan taɓa rayuwar Nigeria ba balle har na damu dayin aiki saves yaymin amfani. Please Mamie....”       Cikin katseta Mamie taja wani tsaki. Kota kanta batabi ba ta nufi wata ƙofa a fusace tana faɗin, “Ki wuce driver ya kaiki wajen gyaran jiki dan Abie ɗinki yace da wuri zaku wuce, kin san kuma baya son wasa da lokaci”.      Kuka ta sake barkewa da shi kai kace Abie ko Mamie ɗinne aka aiko mata sun mutu. Harga ALLAH bata son zuwa Nigeria dan tana matuƙar wahala da yanayin zafinsu. Ga shegen sauro ɗinnan na kano tamakar kasuwancinsa sukeyi. Uwa uba zaman gidan Uncles ɗinta data tsana saboda mugun halin matar Daddy, na matar ma bai cika damunta ba dan sai ka shiga sabgarta take takuraka. Tafi tsanar babban ɗansa mai shegen baƙin hali da mugunta da har ya zarta uwar tasa. Sam bata ko ƙaunar ganinsa dan basa haɗa ko hanya bare shan inuwa guda, shiyyasa a mafi yawan lokaci idan taji zai zo malaysia take guduwa wajen Aunti Mimi. Da ance kuma zai je wajen aunty Mimi ɗin itama dake aure anan ƙasar malaysia ɗin sai ta gudo ta dawo sabah. Har ya gama zamansa bata yarda su haɗu. Kai itafa a kaf rayuwarta ma bai fi sau uku ta taba ganinsa ba. Tun kuma a ganin farko taji ta tsanesa saboda tsawa da yay mata dan ta fasa glass cup a mistake a gidansu, ita kuma ta murguɗa masa baki yako kama lips ɗin ya murje har sai da sukai kumburi duk da shekarunta basu wuci goma ba a lokacin ta kasa mantawa ta kuma kasa daina jin haushinsa. Hakama haɗuwarsu ta biyu sai da yay mata mugunta, kai idan bata mantaba ma dukansu yay ita da Aysha ƙanwarsa saboda sunje wajen bikin birthday na ƙawar Ayshan ba'a sani ba. Aiko dukan nan ya shigeta dan harda zazzaɓi kasancewar tunda ta tashi da wayonta da hankalinta ba'a taɓa dukanta ba sai shi mugu.........           Ta jima a wajen tana saƙa mai fishsheta kafin ta haura saman stairs. Cikin mintunan da basufi sha biyar ba ta fito sanye cikin wando da riga ta ɗaura jibgegiyar rigar sanyi data kai mata har gwiwa kasancewar lokacinsa ne, duk da veil data naɗo a kanta kamar yanda larabawa keyi hakan bai hanata jan hular rigar da bakinta keda gashi mai laushi har saman kanta ba. side bag dake hanunta ta saƙala cikin wuyanta sai faman tura baki take. Duk da Mamie na zaune a falon tana yanka tufa ko kallonta batai ba....       “Mamie na shirya kuɗin to”. Batare da Mamien ta tanka mata ba ta tura mata card ɗinta na ciran kuɗi. “Na gode ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”. Ta faɗa tana kama hanun Mamie ta sumbata tare da ɗagowa ta sumbaci kumatunta kamar yanda dai larabawa sukanyi. Mamie bata kulata ba, hakan yasa taƙi tafiya idanunta har sun cika da kwalla, dan tunda taga Mamien bata maida mata murtanin sunbar datai mata ba tasan har yanzun tana fushi da ita.        Haka kawai murmushi ya suɓucema Mamie, ta girgiza kanta da kamo hanun tilon ƴar tata da a kullum cikin jimamin ranar da aure zai rabasu take, dan ta tabbatar hakan na gab da faruwa. A ido zaka ɗauka Anam bata da wani shekaru saboda ƙaramin jiki da ALLAH ya bata. Sai dai kuma a zahiri shekarunta ashirin da uku kenan a duniya. Itama sumbatarta tai da ɗanjan kumatunta, hakan yasa Anam yin ƴar dariyar jin daɗi ta rungume Mamien. Mamie tai murmushi.         “To sarkin taɓara tashi kije ko ƙya dawo da wuri”.      “Okay Mamie bye”.       Batafi awa uku da fita ba sai gata ta dawo, ta kara wani irin ƙyau da kwarjini tabbacin taci gyara tako ina. Dan babu abinda fuskarta keyi sai shining da glowing, ga wani uban ƙamshi mai saka nutsuwar mai shaƙa. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufi ƙyaƙyƙyawan dattijon dake tsananin kama da ita dan shima black beauty ɗinne, amma kasancewar akwai jin daɗin rayuwa baka ganin komai tare da shi sai ƙwarjini da ƙyawun haiba. Ga baƙin sajen fuskarsa daya ƙara ƙawata ƙyawun nasa. Shima dai bashi da wani jiki, dan komai na Anam bashi da maraba da nashi, hakan na nufin dai kamaninta ɗaya da mahaifinta.       Zuwa tai ta rungumesa ta gefe tana dariyar farin cikin ganinsa. Shima fuskar tasa da murmushi ya riƙo hanunta cikin nasa. “Uhhm Mamana irin wannan ƙamshi haka kamar amarya”. Fuskarta ta ɓoye a kafaɗarsa tana dariya. “Nidai Abie ba wani amarya”. Dariya kawai yayi baice komai ba. A haka Mamie ta fito daga kitchen ta samesu. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon mijin nata abin sonta da ƴar tasu tilo ɗaya a duniya. Anam ta zame veil ɗin kanta tana nunama iyayen nata kanta daya sha gyara masha ALLAH, sai sheƙi yake da ƙamshi gashi da tsaho sosai. Gaba ɗaya kamaninta irin na Abie, gashin kai da gira zuwa gashi ido ne kawai irin na Mamie, sai ko maganarsu dake kama itama.     Sosai suka shiga yaba ƙyawun da gyaran nata yayi, cikin tsokana Abie ke faɗin, “Mamana kin zama kamar wata amarya da gaske, kodai kawai idan munje na aurar dake ma?”.     Idanu tai mugun zarowa, sai kuma ta kwaɓe fuska har hawaye na cikon mata ido. Lips ɗinta sai rawa suke tama rasa mizatace. Dariya Mamie da Abie suka shiga yimata, hakan yasata tashi da gudu ta haura sama. “Kin gani kin kunnata”.      “Na kunnata ko ka kunna abarka”. Cewar Mamie tana murmushi. “To aini abin na damuna, idan na tuna wataran aure zatai ta barmu hankalina na matuƙar tashi, gashi shekaru sunyi nisa, kamata yay ma data gama saves ɗin nan kawai a wuce wajen Humairah”.      Ajiyar zuciya mai nauyi Mamie ta sauke. Murya a raunane tace, “Hakane ya dace, sai dai kuma a kullum cikin korar samarin take ai taƙi bama kowa dama anan ɗin balle Nigeria. A kullum kallon kanta take a yarinya”.      “To ai yarinyarce, duka yaushe kika haifamin ita. Ni badan auren ya zama doleba dana bar abuta naita kallo kawai”.       Sosai Mamie ke dariya, cikin riƙe baki tace, “Lallai ashe mu iyayenmu basa sammu kenan da aka ɗakko aka baku. Lallai ashe lokacin auren munada kallo kenan dan za'a sha show rabuwar ƴa da uba”.      “A zakusha kam. Dan mijin nan zai sha gargaɗi, shiyyasa nafi son ma ta auri ɗan Nigeria dan ƙasar nan ta isheni haka”.         “To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Ya kawo nagari”.   Da amin Abie ya amsa cikin jimami da damuwar rabuwa da tilon ƴarsa. *_Washe gari_* kamar yanda Mamie ta faɗa hakance ta kasance. Dan kuwa dai Abie da Anam sun wuce ƙasar haihuwarsu Nigeria. Tasha kukan rabuwa da Mamie duk da tasan bazatai shekaran Mamie bataje ba tunda ita sunce bazata zo ba har saita kammala. A jirgi barci ta dinga ramuwa wanda ta gagara yi a daren jiya saboda alhinin yin nisa da iyayenta datai matuƙar shaƙuwa da su take mu'amula da su tamkar ƙawayenta. Sune abokan shawararta, sune abokan kukanta, sune abokan dariyarta, sune abokan rayuwarta. Bata da kamarsu dan su tafi sani fiye da kowa a duniya. *_04: 25pm_* jirginsu ya sauka ƙasar Nigeria Aminu kano international airport, a gajiye Anam take matuƙa duk da barcin da tasha, sai faman langarema Abie take, shiko lallaɓa abarsa yake dan yasan yanayinta bata son wahala sam. Abu ƙalilan ke galabaitar da ita tai laushi tiɓis. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali lokacin da suke fitowa idonsa ya sauka akan ƴan uwansa abin ƙaunarsa. Suma da alama idonsa na kansa, dan tuni suka nufosa fuskarsu ɗauke da murmushi. Abie yay azamar nufarsu shima suka rungume juna suna maijin farin cikin haɗuwa.        Sosai Anam take dubansu da murmushi, tana ƙaunar uncles ɗin ta kam, dan suma suna ƙaunarta. Matar big Uncle ɗin nata da ɗansa babba ne dai sai a slow, amma sauran matan small Uncle da yaransu duk bata da matsala da su musamman Aysha aminiya.       “Oh my Mah-mah welcome”. Uncle ɗin da suke kira da Daddy ya faɗa lokacin da suke sakin juna da Abie ya buɗe mata hannayensa alamar tazo garesa. Hanun trolley ɗinta ta sake da nufarsa a kasalance fuskarta ɗauke da murmushi ta matsa ya ɗan rungumeta ta gefe.         Small Uncle ɗinta da suke kira da Abbah yay murmushi tare da shafa kanta yana faɗin, “Ayya Mamana kina nan dai a ƴar ficikar ki ba tsaho ba girman jiki ga ragwantaka”. Fuskarta ta ɓoye jikin Daddy tana dariya da faɗin, “Lah Abbah na ƙara girma fa, kuma yanzu bana ragwanci”.      Daga Daddy har Abba da Abie dariya sukeyi, Daddy yace, “Nima dai ban gani ba, jibeki a galabaice a ƴar wannan tafiyar ta awoyi, shekara huɗu kenan ban ganki ba amma kina nan yanda kike fa”.      Sosai ta shagwabe masa ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta tana ƙyafta idanunta manya ta cikin glass ɗin da alamu suka nuna na ƙarin gani ne.       Ko amota ma Abie da Daddy da abbah dake a baya zaune tuni sun balle hira, itako kallon hanya kawai take dan tana gaba a gefen driver. Jikinta liƙis yake da gajiya, ga wani irin zafi dake shigar ƙofofin gashinta kamar ta fasa kuka dan bata ƙaunar zafi, shiyyasa duk sanda zasu zo Nigeria sai tai kuka bana wasa ba, idan sunzo kuma sam zaka sameta babu sakewa inhar lokacin zafi ne. Shiyyasa mafi yawan lokuta Abie yafi son shirya musu zuwa Nigeria a lokacin sanyi ko damuna saboda ita.         Sun sami tarba ta mutuntawa daga matan gidan guda biyu, wato aunty amarya da mom. Amma babu Big mom balle alamarta. Hakan ba sabon abu bane, shiyyasa daga Abie har Daddy da Abbah basu nuna sun damu ba. Yaran gidan dai duk sun wuce islamiyya, sai ma'aikatan ne keta shigowa suna mika gaisuwarsu domin duk wanda ya kwana ya tashi a gidan yasan muhimmancin Abie ga Daddy da abbah dama jama'ar gidan gaba ɗaya. Sai da suka kwashe kusan mintuna arba'in sannan Mommy ta shigo tana wani ciccin magani. Babu wanda yabi takanta harta samu waje ta zauna tana gaida Abie. Cikin sakin fuska ya amsa mata tamkar sauran ƴan uwanta, ya kuma tambayeta yara.      Duk wannan bidiri Anam na kwance a kujera lamo tana kallon kowa a galabaice, dan ma ta samu sauƙin zafin tunda suka shigo sanyin ac'n falon Daddy na ratsata. Gaishe da Mommy tayi itama a ɗan shagwaɓe, bata wani amsa mata da ƙyau ba. Sai taji duk babu daɗi har fuskarta ta nuna hakan dan ita yarinyace mai son kulawa. Hakan yasa Mom tai murmushi da shafa kanta cike da kulawa take faɗin, “Mamanmu har yanzu dai ke raguwa ce”.        A langabe Anam take dubanta har idanunta na nuna alamar tara kwalla. Murya a raunane tace, “Mom na gajine ga zafi”.       Dariya duk aka sanya a falon, aunty amarya cikin dariya tace, “Babbar magana. A haka za'ai saves ɗin kuma.....?”.       “Kema dai ƙya faɗa Hafsatu. Dan wannan ƴar taku ragwantarta harta wuce tunani, ina tausayama mijin da zaku mannawa”.            Mom da aunty Amarya suka shiga kare Anam da faɗin koma waye zasu iya dashi ai. Mommy kam sai faman taɓe baki take da yatsine fuska tamkar bata a falon ma....          A duk sanda suke a ƙasar gidansu dake jikin nasu Daddy ne masaukinsu, wannan karon kuma babu Mamie sai Daddy yace bai yarda su sauka anan ba duk da Abie ya nuna shi dai zai shiga can ɗin dan bazai so takura iyalan ƴan uwan nasa ba duk da kanine shi a garessu. Babu yanda su Daddy suka iya suka haƙura kawai suka barsa akan zuwa anjima sai ya shiga can ɗin yanzu masu aiki zasuje su gyara. Hakan kuwa akayi, masu aiki sukaje suka tsaftace ko'ina da taimakon aunty Amarya, ita kuma  ta koma sashen Mom ɗin kodan kawarta Aysha da basu san da zuwanta ba dan su Daddy sun ɓoyema kowa. Duk da jin zafinta bata wanka da ruwan sanyi, dan haka ta haɗa mai zafi sosai tai wankan a bedroom ɗin Mom kafin su Aysha su dawo islamiyya, tana fitowa kobi takan abincin da Mom ta ajiye mata bataiba ta ƙure ac ta kwanta sai barci. Yin barcin nata babu jimawa sai ga yaran gidan an dawo dasu daga islamiyya cikin katuwar bus ɗinsu ta zuwa makaranta. Kowannensu sashen uwarsa ya nufa, mazan kuma suka nufi sashensu na samari duk da kuwa babu wanda ya haura ashirin a cikinsu.      Basu san da zuwan Anam gidan ba sai bayan sallar magrib, samarin suka fara cin karo da Abie a massallaci, ana idar da sallar isha'i sai gasu da gudu sashen Mom. Sune suka fargar da ƴammtan gidan, aiko cikin ƙanƙanin lokaci suka hargitse ɗakin Mom da hayaniyarsu wadda ta tashi Anam ɗin dake tsaka da jin daɗin barci dan bata salla tana fashi. Tsawa Mom ta musu dan tana salla amma suke ihun nan, tsitt bedroom ɗin yayi suna sauraren faɗan da take musu na wannan shirmen nasu. Sai da ta gama suka bata haƙuri tare da janye ra'ayin ƴar uwarsu suka bar ɗakin.          Kai kawai ta ɗan girgiza fuskarta da murmushi, dolene yanda suke murna da ganin ƴar uwar tasu ya birgeka. Ita kaɗaice ware a cikinsu amma suna nuna mata tsananin so kamar yanda suma kawunansu yake haɗe duk da dai wataran Mommy kan birkita kan yaran idan tanajin fitinarta, musamman idan ta takalesu basu kulataba sai tabi duk hanyar son zuciya ta cusama yaranta ƙananun magana a zuciya da zakaga sun janye jikinsu da ƴan uwansu har wataran ma kaga an taɓah faɗa, a wasu lokutan faɗan nasu nayin nauyi, amma wani sa'in sukan fahimci juna da wuri musamman idan wanda suke shakka a gidan yana ƙasar dan shi babu ruwansa ubansu yakeci gwargwadon iko. Duk da mutum ne shi mai haƙuri da rashin son yawan magana, sam baya son raini da damuwa. Sannan duk da halin uwarsa bazaka taɓa ganinsa ya nuna banbanci akan yaran gidan ba, matan kuma yana girmama kowa yanda ya kamata duk ɗa nagari yayi........✍ KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE. DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300) BIYU (400) UKU (500) HUDU (700) KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE! ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN HAFSAT UMAR KABIR ZENITH BANK 2270637070 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 07040727902 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09134848107 KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* [10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_02_* .........Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu.       Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.      Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.      Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba'ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi, dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.      Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da matarsa mai suna Asiya haihuwarsu ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba sai fatan shiriya yake musu.       Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar saudia sunje aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa ragamar rayuwar ƙannensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da Mimi. A wannan gaɓar ƴan uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daɗi har cikin ransa.        Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai ɗan Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ƴan uwansa rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ƙanwarsa Mimi dake fama da ƙaramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ƴan uwan nasa dan kuwa su ko auran Mimi duk da ya basu hakkinsu ƙin zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta'aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane su manta kawai.         Ɗan shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk iyalansu, dan kuwa a baya basu taɓa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin ƴaƴansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila ɗiyar ƙanwar gwaggo nada yara huɗu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna kiransa da *_Shareff_*. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ƙaramin ciki da take kan laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta mugun tsanarsa saboda huɗubar Gwaggo, ƙinsa take tamkar itace ƴan uban nasa ba mijinta ba. a gefe tana matuƙar jin kishin yana rayuwa a ƙasar waje a ganinta kodai yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matuƙar takaicin ganin su Muhammad sun fara sakkowa akan ƙin ɗan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke ɗaurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai son jama'a da haƙuri, duk da ƙiyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin kishiya ta zama mai haƙuri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daɗin iyayen mijin nata takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai ɗiyar ƴar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haɗata fitinar da aka dingayi da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk maza. sai dai tana da ciki ɗan watanni biyar. Umar dai yaƙi aure, hasalima ya zama fanɗararre a cikinsu sai addu'a. Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba'a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.      Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba'a faɗaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.      Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.       Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri'arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al'amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya ɗauka yaƙi.      Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.          A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa....         Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.        A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su'ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma.        Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace. Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama. Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi. Yarinya taci sunan *_Juwairiyya_*, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da *_Anam (Blessings of GOD)._*          Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana maƙale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami'a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na'a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.        A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.      Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai.....       A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.      Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko'a mafarki bata fatar haɗa zuri'arta dasu Abie a duniya.....        Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa'aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna'a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da *_MM Shareff_* a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya Shareff bai yarda ya ɗauka ma'aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma'aikatansa damar yin wasan kuma.      Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo.         To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba.........✍ _Ko yaya wasan zai kasance🤔? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO...! MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taɓa zuwa muku da kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taɓo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki a yanzu da rawar da tarbiyyar ƴaƴanmu ke takawa a social media batare da saninmu ba ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da zafinsu suke😉🥰🥰😘🚶🏻._ KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE. DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300) BIYU (400) UKU (500) HUDU (700) KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE! ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN HAFSAT UMAR KABIR ZENITH BANK 2270637070 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 07040727902 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09134848107 KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽 [10/3, 10:44 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_03_* ..........Tuni sun tattare kansu a sashen aunty amarya idan ka cire ƴan manya-manyan yaran gidan samari da basu gama dawowa da ga wajen aiki ba da kuma masu shiga school lectures ɗin yamma. Zagaye suke da Anam suna kwasar dariyar hausarta da bata nuna da ƙyau ba. Dan cike take gwamutse da yaren malay da turanci, wai a hakanma Abie na matuƙar ƙoƙarin mata hausar ne shi da aunty Mimi dan Mamie ma ba wani iyawa tai sosai ba harma gara Anam ɗin, tunda dama acan itama ta tashi, ko Nigeria tazo tafi yin turanci da jama'ar gidan. Aysha dake naniƙe da Anam ɗin da suke sa'annin juna dan dama idan tazo bata da ƙawar data wuceta a Nigeria, cike da kulawa take tambayarta dalilin matsar ciki da take famanyi.        A yatsine Anam ta sanar mata tana jin yunwa ne, dan ta kasa cin duk abincin da aka shirya musu a gidan. Dama can idan sunzo Mamie ce ke musu girki shiyyasa Anam bata da matsala tunda abinda ta saba ci ne, a yanzu ko babu Mamie dole sai abincin Nigeria da har yanzu ta kasa iya ci, ƴan abubuwan da take iya cin ƙalilanne kuma babu su.       Idanu Aysha ta ɗan waro, cikin harshen turanci take cemata miyasa zata zauna da yunwa bayan abinci da akai domin su tunda sun iske tarin kwanika a sashen Daddy lokacin da sukaje gaida Abie. Sunada tabbacin kuma an shiryasune dan zuwan su Anam ɗin. Fuska a marairaice ta sanarma Ayshan ita bata iyacin duk abincin ba ai. Ba Aysha kaɗaiba duk yaran sai da suka dara, dan sosai ragwantakar Anam ke basu dariya, kodan tana ganinta da ƙaramin jiki ƴar ficika da ita yasa a kullum bata sanin ta girma? Sosai Aysha ta fita girman jiki, sai ma ta saɓeta ta goya dan ita ta kwaso tsayi da garin jikin Mommy mahaifiyarsu.     Sake ɓata fuska Anam tai kamarzatai kuka, sai faman matse ciki take da cizar lips dan da gaske yunwar takeji, shi kansa Abie yana canne amma hankalinsa na kanta dan yasan bazata iyacin kowanne abinciba da ya gani an tara masa.       “Am so sorry sweetheart. Kar kiyi kuka faɗi abinda kike so sai a samo miki, ko a kira Yaya ya sayo miki tunda shi yasan inda yake samo abincin naku, dan shima dai ya jima yana wahala kafin ya saba da abincin Nigeria, ko yanzu ma ba komai yake iya ci ba”.       Fahintar wa Aysha ke nufin za'ama magana ya samo mata abinci ya sakata girgiza kanta, a langwaɓe ta kamo hanun Ayshan cikin nata. “No don't worry rakani wajen Abie na nidai kawai”.     Batama bari Aysha tace wani abuba ta miƙe har lokacin hanunsu cikin na juna, ɗayan hanunta kuma nakan cikinta. Wando da rigane a jikinta marasa nauyi, wandon irin mai faɗin nan sosai da ƴan Nigeria ke kira a fantama😂, sai fingilar top da tabi jikinta ɗas kamar dan ita aka halicceta, sai siririn veil data sakaya gashinta a ciki sai dai hakan bai hanashi bayyana ta gaba ba saboda veil ɗin daya zama baya.        Itace ta farayin sallama a hankali cikin sassanyar muryarta, ta dora da faɗin, “Daddy mu shigo?”.      Murmushi Daddy da Abbah keyi idonsu akan ƙofar. Abba ne ya amsa da “Shigo mana Mamanmu”. Hanun Aysha taja zuwa ciki, sai dai taku uku kacal tai ta tsaya turus fararen idanunta da sukai laushi saboda yunwa tsaye ƙyam akan wanda ke zaune bisa lallausan carpet ɗin falon gab da ƙafafun Abie ɗinta, yayinda hankalin Abie kacokan ke akansa da alama ma bai san da shigowarta ba.      Sosai ƙirjinta ya harba dan ko kusa batai zaton ganinsa anan ɗin ba, tunma data duro gidan addu'arta shine karma su haɗu kwata-kwata. Zancen Aysha na ɗazun ya tabbatar mata yana ƙasar, hakan kuma na nufin dole su haɗu koda ba yau ba. Amma batai tsammanin yanzu ba. Kamar yanda tai masa kallo ɗaya ta ɓata fuska da gyara yanayinta haka shima yay mata kallo guda duk murmushin fuskarsa ya ɓace, har wani yamutse fuska yay tamkar yaci karo da tutun safiya na cikin sanyi......       “Mamanmu ƙaraso mana”. Daddy ya katsesu a tare dan duk yaga irin kallon tsanar da sukaima juna. Shikam ya rasa wannan ƙiyayya ta Anam da Shareff bayan kowa yasan irin dunbin son daya nuna mata tana jinjira har zuwa sanda ya wuce Indonesia, amma a yanzu baka ganin komai sai ƙin juna a tsakaninsu tamkar basu taɓa sanin juna ba. Yitai kamar bata gansa ba taje ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, cikin marairaice fuska tace, “Daddy ina jin yunwa sosai”.        “Ya salam mamana garin yaya haka? duk abincin dake gidan nan ga wasuma ko taɓawa ba'ai ba kuma dan k kawai aka shirya su”.       Kanta ta girgiza kamar zatai kuka. “Daddy bana son su ban iya ci ba ai”.           “Sai ki fara koya yanzu ai”. Abie ya faɗa kafinma su Abba suce wani abu yana hararar Anam duk da kuwa bai kai zuci ba, dan ransa cike yake da damuwar zamanta da yunwar tunda yasan da gasken ba iya cin tai ba.      Daddy yace, “A'a ba'ayi hakaba ai. Tunda tace bata iyaba da gaske bata iya ɗinba kuma bataso. A bita a sannu zata koya ci insha ALLAH tunda tana nan. Shareff ka ɗauketa kuje a sama mata abinci dan kaine kafi kowa sanin inda kake ciyo abinda ta iya ci”.        Tamkar saukar aradu haka Shareff yaji saukar zancen Daddy a kansa. Ya ɗago da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane. Harara Daddy ya zuba masa. “Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.        Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba. Sai dai fuskar ta sake rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa.           “Daddy ni dai nama ƙoshi kawai zansha ko tea to”. Anam da itama ta haɗe fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa ta faɗa baki a tunzure”.       Maimakon Daddy ya amsa mata sai ya kira sunansa a tsawace. “Shareff Are you daft?”. Kansa ya girgiza kawai yana miƙewa, idonsa a ƙasa yace, “Zanje na sayo kawai.....”       “Da ita zakaje ta zaɓa abinda take so”.      Dady yay saurin faɗa cikin katse masa hanzari. Wani irin rumtse ido yay da ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa uwa zai huda shi. Sai dai baice komai ba ya kama hanyar fita. “Basai kaje ɗakko key ɗin mota ba zo ka dauka wannan”. Abbah ya katsesa dan ya tabbatar Mommy ta gansa zata hana itama. Nanma baice komai ba ya dawo ya amshi key ɗin hanun Abban.        “Maza bishi mamana kuje, ki kuma zaɓo duk abinda kike so kinji”.     Kanta ta ɗagama Daddy tana murmushi, dan ganin yanda Shareff ɗin keyi yasata jin zama ta bisa kodan ta baƙanta ransa...         Kasancewar ya fita zafin nama sanda ta iso harabar gidan harya tada motar yana reverse, maimakon ya faka saitin inda take ya ɗauketa sai ya harba motar har bakin gate. Anam tai ƙwafa da taɓe baki, cikin kunƙuni da gurɓatacciyar hausarta tace, “Duk baƙin halin da kake sai naje saika mace idan kasha zuciyanka mugu mai baƙin rai”.        Oho baima san tanai ba. Cike da wani takun isa tazo ta buɗe murfin ta shiga kanta a gefe. Bawani duban kirki yay mataba a ciki, dan haka bai gama tantance kayan jikinta ba. Tana shiga ya fisga motar da ƙarfi har yanayi kamar zai taka mai-gadi ma, sai da yay tsalle gefe ya bashi hanya cike da mamakin mike damunsa. Dan shi shaidane Shareff mutum ne daya san mutuncin mutane, ko yaya kake a ƙasansa bai yarda ya ƙasƙantaka ba balle wulaƙantaka. Yayi imani da ALLAH ransa a ɓace yake bada son rai yay masa haka ba.                   ★ Sosai gidan abincin ya haɗu, ya samu waje yay parking batare da yace da ita komai ba ya fice a motar. Baki taɗan taɓe kaɗan da yima ƙeyyarsa gwalo, sai kuma ta zabura ta buɗe motar tamkar wadda ta tuna wani abu. Yana gab da shiga ta cimmasa saboda da ɗan gudu-gudu take tafiya. Cak ya tsaya, dan haka itama ta tsaya kanta a ƙasa dan duk fitsararta a bayan idone kawai dama.        “Idan kika bari ƙafarki ta shiga wajen nan sai na ɓallata”. Da yaren malay yay maganar, dan haka komai ya shiga kunnenta tsaf. Baki ta tura fuska a kumbure idonta na tara ƙwalla harya shige tana kallon bayansa ta ƙasan ido. Maimakon ta koma mota sai ta nema waje a gefe tai tsaye tana kallon mutanen dake. a ciki ta cikin glass da aka ƙawata wajen.....        “Hallo....”   Aka faɗa a bayanta cikin wani irin sallon daya tilastata ɗago idanunta masu haske, matashin saurayine ƙyaƙyƙyawa fari tas. Sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar karɓarsa ga wani ƙamshi na musamman a tare da shi. A hankali ta janye idanun nata ganin yanda ya tsareta da idanunsa birkitattu. Gefen data maida fuskar ya sake dawowa yana gyaran murya, ta sake ɗauke kanta gefe....       “Dan ALLAH ki kulani ƙyaƙyƙyawa ”. Ya faɗa cikin marairaicewa da haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Baki taɗan taɓe gefe tana yamutsa fuska da kai hannu ta gyara glass ɗin idonta dake ƙara fiddo ƙyawunta duk da tana sakawane badan gayu ba, kamar bazatace komaiba sai kuma dai ta tanka masa saboda ALLAH daya haɗata da shi. “Ka fara koyan sallama tukunna kamar zaifi bature”. Kansa ya dafe, cike da jimami yace, “Am sorry Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Nan ɗin ma bata amsaba sai da tasha masa ƙamshi tana wani ɗauke kai. “Wa'alaikassalam. kuma ni ba sunana ƙyaƙyƙyawa ba”. “Tabbas sunan shine ya dace dake, sai dai dazanji na yankan zanfi yin farin ciki”. Banza ta masa har kusan minti ɗaya, ganin yana neman matsowa jikinta tai saurin ɗagowa a masife......        A dai-dai nan Shareff ya fito daga wajen hanunsa ɗaukeda ledoji masu tambarin wajen abincin. Duk da idonsa a kansu ya fara sauka sanda yake buɗe ƙofar sai ya ɗauke tamkar bai gansunba. Sai dai ya sake tsuke fuska. Yazo zai giftasu a fisge yace, “Second ɗaya kika ƙara a wajen nan jikinki sai ya faɗa miki”. Daga ita har saurayin da sauri suka maida dubansu garesa dan ita bama ta lura da shi ba da farko. Ko kaɗan bazaka taɓa cewa shine yay maganar ba. Tuno dukan da sukaci ita da Aysha randa sukaje birthday party ya sata zabura da sauri tabi bayansa bakinta a tunzure tana hararar bayansa, da sauri shima saurayin ya take mata baya. Tana ƙoƙarin rufe murfin motar ya riƙe da hanzari..........✍        KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE. DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300) BIYU (400) UKU (500) HUDU (700) KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE! ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN HAFSAT UMAR KABIR ZENITH BANK 2270637070 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 07040727902 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09134848107 KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽 [10/3, 10:47 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_04_* ..........Kallon juna sukai cikin ido, tai saurin janye nata saboda wani irin harbawa da ƙirjinta yayi......      “Please Beauty ko details ɗinki ki bani mana”. Saurayin ya faɗa a marairaice. Ai kafimma ta bashi amsa mai gayya mai aiki ya fisgi motar da ƙarfi. Da sauri saurayin ya saki murfin yana mai yin tsalle gefe dan saura kaɗan ya takashi. Sosai yanzu kam Anam ta firgita, dan har hannunsa ta riƙo batare data sani ba. Tureta yay a jikinsa tare da mika hannu ya rufo ƙofar gefen da take ɗin. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana kiran sunan Mamie da Abie. Bai nuna yama san tanaiba, saima hankalinsa daya maida ga motar dake bin bayansu, sai da suka hau titi sosai hasken solar ya bashi damar ganin fuskar guy ɗin da suka baro ne. Lip ɗinsa ya ciza da ƙarfi yana wani fici-fici da idanunsa, sai ya koma tafiya a slow-slow harya zam saurayin ya ɗan gota su. Gefen titi ya gangara, sai da yaga saurayin na ƙoƙarin dai-daita nasa gudun danya sauka gefe titi shima saboda ganin sun tsaya sai kawai yay warming motar da wani irin karsashi ya sake harbata saman titi tamkar shikaɗaine a kansa. Tabbas da ace akwai ƙasa babu abinda zai hanashi bulama saurayin ita.        Wani irin duka saurayin ya kaima steering ɗin a ƙulle da kufcewar damar daya samu. Ya kife kansa yana furzar da huci mai zafin gaske, dan harga ALLAH yarinyar ta matuƙar tafiya da dukkan imaninsa.         Kamar yanda ya fita a fusace haka ya dawo a fusace, ko parking bai gama daidaitawaba da ƙyau ta ɓalle murfin motar ta fice da sauri. Wani irin mugun kallo yabi bayanta da shi, sai kuma ya janye yanayin ƙwafa ya kashe motar ya fito. Zaune ya sameta kusa da Abbah tana zuba surutu, dan har yanzu suna a falon suna hira. Sosai takaici ya riƙe masa maƙoshi, ya harareta yana ɗauke kai da zube ledojin hanunsa gabanta. Fuskarta ɗauke da murmushi kamar ba itace ta gama kuka a hanyaba yanzu tace, “Jazakallahu khairan Yaya Shareff”. Ta ƙare maganar da masa gwalo yanda su Abba basu luraba sai shi.          Yi yay tamkar baima gantaba duk da tsaurin idonta na bashi mamaki, sosai ƙanensa ke shakkarsa a gidan, amma sam babu irin wannan tsoron da yake gani a idon ƙanensa tattare da ita. Kai tsaye take abunta garesa, abunda ya fuskanta dukane kawai bata so, dan tun dukan da ya taɓa mata ita da Aysha ta shiga hankalinta a lokacin har tana wasan ɓuya da shi. Sallama yayma su Abie dake saka masa albarka ya fita fuskarsa ɗauke da murmushin daya saka Anam sakin baki tana kallonsa da mamaki. Dan inba Abie ɗin ba da wahala kaga murmushi a fuskarsa, kullum fuska a ɗaure kamar ɗan raka gawa....          Washe gari da ƙyar Aysha ta iya tashinta danta shirya. Haka tai wanka tanata mitar ita barci bai ishetaba. Shiri tai cikin wando da riga, sai dai anan babu maganar fita a haka duk da  zafi da ranar da akeyi a Nigeria, dole ta ɗaura abaya, Sosai tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. ɓata fuska taketa faman yi dan bada son ranta tasa abayar ba, sai dai yanda Mamie ta gargaɗeta ta dingayi tunda tasan kayan nata duk ba irin na sawar Nigeria ba ne. Shiyyasa ta zubo mata abayoyi kusan goma tanata mita bata kulata ba. Kasancewar akwai sanyin safiya sai bata damu da saka abayar ba sosai.        Sashen Mommy suka nufa ita da Aysha, sai dai daka kalleta kasan ba'a san ranta bane. To amma kodan Aysha da kunya tace bazataje ba. Mai aiki kawai suka samu a falon tanata aikin gyarawa, suka gaisa Anam na amsasu cike da fara'a, dan haka kawai ita dai Ladi ke birgeta. Bedroom ɗin Mommy suka nufa daga nan, bayan sallama aka basu iznin shiga. Zaune suka sameta a kujerar mirror tana murza ɗauri, ganin aysha ta rissina tana gaisheta itama saita ɗan rissina batare data yarda sun haɗa ido ba. Bata amsa na Anam ɗin ba, sai Aysha data watsama harara... “A ina kika kwana?”.       “A sashen Mom ne”. Aysha ta bata amsa cikin ɗari-ɗari dan tasan faɗa zata sha. Aiko kamar jira Mom ta rufeta da faɗa, ta inda take shiga batanan take fitaba. Itadai Aysha haƙuri kawai take bata. A tsawace tace. “Ɓacemin da gani shashasha da bata san ciwon kanta ba”.. Kafinma aysha tai yunƙurin fitowa tuni Anam tai waje ranta fal ƙarin mamakin masifar Mommy ɗin...       Da sauri tai baya jin suna neman yin karo da mutum. Ta tura baki gaba tare da ɗan matsawa gefe saboda hararar da yake watsa mata. Yana ƙoƙarin raɓata da nufin wucewarsa tai tunanin bugeta zaiyi, kamar ƙiftawar ido yaga ta zura da gudu ta fice. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da girgiza kansa kawai. Anan ɗin ma yana ƙoƙarin shiga ɗakin Mommy Aysha ta fito tana sharar hawaye, rissinawa tai ta gaishesa, maimakon amsa mata sai ya jeho mata tambaya idonsa kafe a kanta, “Mike damunki?”.      Kanta ta girgiza masa. “Ba komai Yaya Mom ce, dan naje sashen Mom na kwana shine taketa faman faɗa, ni kuma saboda naga Anam ne tunda nasan idan mukazo nan bazata barta ta kwana ba”. Shiru yay yana cigaba da kallonta kawai, batare da yace komaiba kuma sai ya raɓata ya wuce ɗakin Mommy ɗin.          Anam kam sai da ta tabbatar tabar sashen sannan ta ƙara kumbura baki, sashen Gwaggo ma da tun jiya batako kallaba sai da Abie ya korata sannan ta tafi fuska a haɗe kamar zatai kuka. Bata son kakar tasu dan itama tasan ba sonta take ba. Koda ta shigo sashen tsohuwar a ciccije take. Tamkar bama tasan Anam ɗin ba take kallonta, hakan yasa itama Anam ɗin tsumewa tai kamar bama wajenta tazo ba. Cikin ƙunar rai Gwaggo ta ture ƙaton kofin shayin da take sha gefe tana kallon Anam cike da tsana,         “Fitsararriya cokalin banza. K ko kunyar kanki bakijiba sai yau kike zuwa gaisheni? Da yake baki da mutunci. to in bakizoba k ai ubanki shi yazo dan uwarki”.    Shiru tai taƙi cewa komai, hakan sai ya sake tunzura Gwaggo ta fara bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ko motsi Anam bataiba ballema tai mata gaisuwar da akace tazo tayi, sai da ta tabbatar mintunan da Abie bazai zargi komai ba sun cika sannan ta gaida Gwaggo dake yayyafa ruwan bala'i da zage mata iyaye tai ficewarta batare da ta jira amsa ba. Biyota Gwaggo tayi tana ƙwala mata kira.       “Zuwairah!! Zuwairah!! yanzu nan ni kikema wannan ɗibar albarkan? To ko ubanki ai bai isaba, ke ko kakarki ma data haifi uban naki balle ke yarin....”       “Ki cinye kanki fitinanniyar tsohuwa”. Anam ta faɗa a hankali tana ƙara sauri dan ko muryarta bata buƙatar ji. Taji daɗin samun Abie harya shiga mota, dan haka ta buɗe wuf ta shige duk da bataji daɗin yin tafiyar da wanda ta gani zai jasu ba. Sai da suka fita a gidan gaba ɗaya Abie daya lura bata gaida Shareff ɗin ba ya dubeta ta mirror.....       “Anam!”. “Na'am Abie ”.    “Kin gaida Yayanki kuwa?”. Ido suka haɗa da shi ta mirror, ita ta fara ɗauke nata idon ganin kallon banzar daya jefa mata. “Abie na gaishesa tun ɗazun ma ai da muka haɗu a sashen Mommy”. Idanunsa da basu gama bajewar kumburin barci ba ya sake ɗagowa ya dubeta. Itako ta ɗauke kanta cike da basarwa. Abie kam daya yarda sai kawai yay murmushi da maida hankalinsa ga lap-top ɗin dake a cinyarsa yana dubawa, ta Shareff ɗince yake nuna masa ayyukan company duk da dama can komai za'ayi yana sanar masa. Sai dai a kullum cikin ƙara bashi wuƙa da nama yake da nuna masa duk yanda yayi dai-dai ne kawai. Koda suka iso inda zatai daidaita komai daya shafi hidimar ƙasar nata bata yarda tako kalla Ya Shareff ba, shima bai shiga sabgartaba dan koba komai yana jin nauyin Abie sannan shi sam baya wasa da yara dama can, itacema kawai za'ace ta ciri tuta a wajensa tana ƙarama.      Komai da taimakonsa shi da Abie ya kammalu, basu sami nutsuwa ba sai kusan azhar. Maimakon gida sai suka wuce company. Tunda akai Companyn Anam batazo Nigeria ba, dan haka ta ɗan nutsu a kallon tsarin wajen da yanda ma'aikata keta kaikawo na daidaita kansu tun shigowar motar tasa. Koda suka fitoma sai gaisuwa ake miƙa musu cike da girmamawa da mutuntawa har suka isa katafare kuma haɗaɗɗen office da yaji komai na more rayuwa da saka nutsuwa ga mazaunin cikinta.  Abayar jikinta ta shiga ƙoƙarin cirewa. “Wayyo Abie zafi”.       Yanda tai maganar ya sashi ɗan juyowa ya dubeta, ai da sauri ya ɗauke kansa ganin kayan dake a jikinta. Wando ne dayay matuƙar fidda surar jikinta da ƴar riga da itama bata ɓoye komai ba. Sun mata ƙyau sosai kuma dai-dai da halittarta ta masu ƙaramin jiki. Har veil ɗin data naɗa bata bari ba sai da ta yaye, ɗaurarren gashinta da yasha gyara ya bayyana, sai dai tuna gargaɗin Mamie yasata warware veil ɗin duk da ba wani girmane da shiba sosai taɗan yafa tana duban sashen da yake....        “Yaya Shareff Please kasa ac zafi”. Tayi maganar ne tamkar zata fasa kuka, dan da gaske zafine ya taso mata lokaci guda, har wani dimm kanta ke mata. Ta ƙasan ido ya harareta, sai dai baice komaiba ya ɗauka remote ɗin ac dake a desk ɗin office ɗin nasa ya kunna ɗin. Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin jin yanda sanyin ya wani buso mata da faɗin, “Alhmdllhi, Abie ALLAH da kamar ana dafamin fatar jikina fa”.      Ƴar dariya Abie yay yana mai girgiza kansa da kallon Shareff dake ƙoƙarin buɗe wajen da yake gudanar da duk ayyukansa na zane. Babu mai shiga wajen sai shi kaɗai, sai ko Fharhan da Khaleel da yakan bama dama a wasu lokutan su kuma Engineers ne, dan company ɗin nasu aikinsa kenan, mai buƙatar zane amasa, idan da gini duk a haɗa, kai dai kawai ka ajiye kuɗi ne kaga biyan buƙata.       “Babana kaji fa wani shirme, dama zafi na dafa fata ne?”.        Murmushi ya ɗanyi cikin sanyin muryarsa da shafa kansa yace, “Abie akwai zafinne ai”.      “Oh ka goya bayanta kenan dai kawai”.             Murmushi ya sake saki mai faɗi fiye dana ɗazun. Sai dai baice komaiba, saima ɗan hararan Anam data saki baki tana kallonsa ganin murmushi a fuskarsa yayi. Itako ko gezau kallonsa take kamar ta samu hoton bango. Fuska ya ɗan tsuke da ɗauke kansa daga saitinta. Itama sai ta janye tana taɓe baki.        Tare da Abie suka shiga, yayinda gaba ɗaya hankalin Anam ke ga littafin data ɗauka mai tambarin company ɗin nasu da alama samples ɗin ayyukan sune a wajen. Koda taji shigewar tasu bata maida hankali kansu ba, ta jima tana kalle-kalle, wasu su birgeta wasu ta taɓe baki harta fara hamma. Sai kawai ta zame ta kwanta a kujerar.........✍ KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE. DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300) BIYU (400) UKU (500) HUDU (700) KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE! ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN HAFSAT UMAR KABIR ZENITH BANK 2270637070 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 07040727902 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09134848107 KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽 [10/4, 1:29 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Ƙarshen free page_* *_05_* ...........Sun jima a ciki yana nunama Abie abubuwa, yanda yaketa faman bayani da murmushi saika rantse bashi baneba. Dan har dariya sukeyi tare da Abie. Kiran sallar la'asar ne ya fiddosu, hakan yayi dai-dai da shigowar ɗaya daga cikin ma'aikata office ɗin, sannan kuma dai-dai da farkawar Anam data sha barci hankali kwance sanyin ac ya gama ratsata.         Shigowar ma'aikacin mai suna Abeed tazo masa a bazata, dan hankalinsa gaba ɗaya nakan system ɗin gabansa, sai sallamarsa da buɗe ƙofa ne a lokaci guda suka shiga kunnensa. Da sauri ya ɗago idanunsa batare daya amsa sallamar Abeed ɗin ba ya kai dubansa gareta. Anam da bata san mike faruwaba duk da itama taji sallamar tai yunƙurin miƙewa tana laluben veil ɗinta da nufin ɗan lulluɓama jikinta. Abie ya riga ya shige toilet ɗin cikin office ɗin ɗaura alwala tunkan sallamar Abeed....        “You are vary stupid!! Zaka shigo min kai tsaye”. A yanda yayma Abeed tsawar da jefa mata rigar suit ɗinsa dake a jikin hanger ba shi Abeed ɗin ba hatta ita sai da ta zabura. Da sauri ta ɗane kujerar baki ɗaya ta ƙudindune kanta dan sam bata ƙaunar tsawa a rayuwarta. Cikin rufewar ido da manta Abie na'a office ɗin ya sake dakama Abeed tsawa da cigaba da masa masifa. Shi dai yay ƙasa da kansa dan bai san laifinsa ba anan har yanzu, tunda ya san ya yi sallama ya kuma yi knocking....         “Get out!!”. Ya sake faɗa a tsawace. Da sauri Abeed yay baya da rufe ƙofar. A fusace ya maida dubansa ga Anam da ke leƙosu ta cikin rigarsa. Ya watsa mata wata uwar harara, cikin gargaɗi mai kaushi,       “Idan kika ƙara fitowa da wannan ƴan iskan kayan saina kashe fuskarki da marukan da bazata ganuba. Stupid girl! An faɗa miki nan muna buƙatar sune”.     Baki ta tura gaba duk da ta mugun tsorata da yanayinsa. “To ni Yaya MM wannan duk sune kayana ai, kuma ni su na iya saw.......”     Ganin ya yunƙuro zai tashi ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera fuska a kwaɓe. Ƙwafa yay da sake watsa mata harara. Abie dake tsaye da ga bakin ƙofa yana kallonsu tun ɗazun basu lura da shi ba yay murmushi, domin kuwa wasu abubuwa masu ban mamaki ya hango a cikin ƙwayar idon ɗan nasa, ya girgiza kai kawai da ƙarasowa ciki. Sai lokacin Shareff ya lura da shi. Ƙasa yay da kansa dan shi gaba ɗaya yama manta Abie na'a office ɗin. Miƙewa yay sum-sum ya nufi toilet batare da ya yarda sun haɗa ido da Abie ba. Shima baice masa komai ba sai binsa da yay da kallo kawai. Anam dake a laɓe sai da taga ya shige sannan ta fito, cikin taɓe fuska ta ƙaraso inda Abie yake tana faɗin,      “Uhhm Abie ALLAH Yaya Shareff baida kirki, yanama staff ɗinsa ihu bai masa komaiba kuma”.     Nanma murmushi kawai Abie yay baice komai ba. Zata ƙara magana Ya Shareff ɗin ya fito tai saurin komawa bayan Abie ta ɓuya. Sai dai hakan bai hanata ganin hararar daya watso mata ba. ★★★★★          Washe gari su Abie suka wayi gari da shirin kai kuɗin auren Ya Shareff, wanda dama yana ɗaya daga cikin dalilinsa na zuwa Nigeria, dan data Anam ne kawai turota zaiyi tunda yasan akwai mai iya mata komai ai. Ita dai Anam bata san mike faruwaba ma, dan ta jima bata tashi a barcin safe ba kasancewar daren jiya tunda aka ɗauke wuta ta kasa komawa barci saboda zafi, duk da kuwa Mom ta kawo mata fan ta kunna mata saboda tsaki data dinga zubama su Husna kamar wata dangin tsaka, sai dai kuma fahimtar iya gaskiyarta ne yasa Ikram zuwa ta faɗowa Mom ɗin. Ganin akwatuna har set uku a falon Mom masu shegen ƙyau da tarin kayan sa rana ya sata tambayar Ya Khaleel first born ɗin Mom. Shima dai saurayine zangarere da shi dan yana shekara ta 26 a duniya. Khaleel ƙyaƙyƙyawa ne shima kuma nutsatstse. Sai dai akwai tsare gida da rashin son raini harma yafi Shareff zafi, dan shi Shareff inhar baka shiga gonarsa ba babu ruwansa da kai, sannan yana da sakewa da jama'a fiye da Khaleel. Shine na uku a haihuwa a gidan. Dan sanda Mom ta auri Abba haihuwar Mommy biyu ne. Daga Shareff sai Maheer da take goyo. Duk da Shareff ya bama Khaleel shekaru sosai hakan bai hana ƙaunar juna shiga tsakaninsu ba, dan tunda ya dawo daga Indonesia bashi da wani aboki a gidan kamar Khaleel. Da taimakonsa ya san wajaje da yawa daya manta, sannan tun a baya idan yazo hutu dama shine abokin yawonsa saboda nutsuwar yaron na birgesa. Yafi Maheer hankali sosai da sanin ciwon kansa, dan yanada himma da ƙwazon nema duk da ko maganar aure bayayi ma.        Duk ɗaurewar Khaleel suna ɗan shiri da Anam, sai dai itama ba wani sake mata yake ba dan miskilanci a jininsa yake. Kamar bazai tanka mataba yanata aikin danna wayarsa sai kuma ya kalleta. “Kayan auren Yaya Shareff ne”.       “Ya mi?! Dama aure zaiyi!?”. A yanda tai maganar ya tilastashi sake dubanta da ƙyau, haka kawai yaji dariya ta taho masa. Amma sai ya gimtse.        “Kinada matsala da auren nasa ne Granny”. (Dan haka yake kiranta mafi yawan lokaci).      “Kuji Ya Khalel ɗin nan da wani magana. Ni ina ruwana da wani aurensa da har zai zamar min wani damuwa. Ai sai dai nai murna zai tafi can ya barmu mu huta matan ta kwashi baƙin hal......”      Jin ta gagara ƙarasawa yasa Khaleel fashewa da dariya, dan dama dai tun ɗazun ya lura da Shareff daya fito daga bedroom ɗin Mom. Ita kuma sam ALLAH baisa ta lura ba sai yanzun da yaƙe ƙoƙarin baro corridor ɗin baki ɗaya dan dama kamar ya ɗan tsayane yana sauraren su, amma a zahiri waya yake dannawa. Duk da ba inda take yayo ba da gudu ta afka ɗakin barcin su harda murza key.      Shiko dama daba inda take yayo ba harara kawai yawatsama Khaleel da faɗin, “Dalla tashi muje ka zauna kana abu kamar wani yaro”.          Har yanzu dai dariya ƙunshe a bakin Khaleel ya miƙe. Idonsa na duban ƙofar da Anam ta shige. Suna ƙoƙarin fitowa yace, “ALLAH my best yariyar nan sam bata da wayo har yanzu. A hakan wai kuma ta kammala karatu. Bayan rashin wayon ƴan fari a jikinta harda taɓarama na ganin ita kaɗai ce a gaban su Mamie. Jiya fa harda kuka ta dinga yima su Mon wai zafi saida aka kawo fan aka kunna mata”.       “Mom ɗince ta biye mata mtsoww ”. Ya faɗa cikin halin ko in kula. Shi dai Khaleel yace, “Gara dai da aka kunna mata dan bata saba da zafin nan bane namu. Su da suke fama da dusan ƙanƙara ma wasu lokutan dan tsabar sanyi. Kaga ko tazo nan dole ta shiga wani yanayi dan kano ogace ta zafi..”       Komai bai ƙara cewaba yay gaba Khaleel ya bisa.      Kasancewar da Mom da Aunty Amarya sai wata ƙanwar Momy da yayarta za'aje yasa Anam maƙalema Mom sai taje. Mom bata hanata ba, dan ita tanada sauƙin kai sosai shiyyasa suke zaune lafiya da Mommy tsahon shekaru, duk da dai itama Mommy ɗin bawai tanada faɗa bane ko rikici, kawai dai ta tsani Mamie ne saboda tun farko akan hakan Gwaggo ta ginata, ta riga ta nuna mata shi Abie ɗan uba ne a cikin su Daddy duk da kuwa ba itace ta haifesu ba. Sai kuma ta kasance mace mai son komai ace itace sama da kowa, sannan a wajenta ake neman komai, a ganinta bazai yiyu ita matar farko a gidan ba, sannan mijinta shine babba ace wata a matan ta fita. Fin da Mamie ta mata kuma ya ƙara ƙiyayyar, itako Mom Abbah bai kai Daddy ba gaskiya, sai dai na waje bazai taɓa fahimtaba kasancewar ana ganinsu kansu a haɗe a koda yaushe kuma suna gida ɗaya ne.       Kasancewar matar da Shareff ɗin zai aura ɗiyace ga gwaggo halima (ƙanwar daddy), kuma mahaifinta yaya a wajen mommy gawurtaccen ɗan siyasa mai muƙamin babba a jihar ta kano gidane katafare suka iso. Komai yaji na more rayuwa. Fadwa shine sunanta, ɗiya ga Alhaji Sadiq Dakata. Mahaifinta kamar Yayane ga Mommy. Dan da mahaifiyarsa, da Mahaifiyar Mommy da gwaggo duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Zumincine mai ƙarfi a tsakaninsu, dan haka ita da Gwaggo suka zaɓama Shareff Fadwa matsayin mata tunkan ya dawo gida Nigeria. Sunyi hakane a cewarsu dan kar Abie yay tunanin basa auren Anam. Da farko dai Shareff bai maida hankali ba duk da baice baya sonta ba. Sai da Mommy ta masa jan ido sannan ya ɗan ke kula Fadwa ɗin. Fadwa ƙyaƙyƙyawar yarinya ce gwargwado kuma ƴar gata, sannan kuma sele (celebritie) a social media, musamman tictok da istagram harma da twitter. Idan zan zauna fayyace muku wacece Fadwa zamu cinye labarinne a kanta. Kuje zuwa dai lokaci zai nuna muku ainahin Fadwa Sadiq Dakata.      Sun sami tarba ta girma da girmamawa. Inda babu kunya Fadwa ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su Mom. Yayinda su Abie ke can suna tattaunawa da su Alhaji Sadiq domin tsaida rana. Dama dai shine yace baya son aita jeka ka dawo, su haɗo komai rana ɗaya su kawo har sadaki sai kawai a tsaida ranar ɗaurin aure.         Su dai su Mom wannan abu ya sakasu jin lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa ƴar gida ce dan sun san wasu a cikin halayenta saboda kowa yasan ƴaƴan gwaggo Halima basu da ƙwaɓa. har cikin rai suna jin tausayin Shareff ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba a mafi yawan lokuta. Amma sauran ƴan uwan Mommy da yake ƴan uwansune suma sai basuji komaiba a lamari, dan kuwa dai basu nuna a fuska ba sai dai in sun barma ransune suna nuna normal ne a zahiri.        Fadwa tasan labarin Anam a wajen Mommy da Gwaggo da mahaifiyarta. Sai dai bata santa a zahiri ba sosai saboda gwaggo halima ba shiga duk abinda ya shafi su Abie take ba, tasha jin sunzo ƙasar tabi duk hanyar datai mata ta toshe haɗuwarsu sai idan wata fitinar suka shirya da su gwaggo shima ita kaɗai take zuwa babu ƴaƴanta. Hakan yasa yaranta basu wani san Abie ɗin bama balle ƴarsa, shima kuma bawani gama sanin ƴaƴanta yay ba tunda bata bari su raɓesa. Hakan yasa Fadwa bata nuna damuwarta da ganin Anam tare da su Mom ba. Amma dai yanda Anam ɗin ta zama miskila a wajen tana kallon komai ya ɗan ja hankalin su Fadwa da ƙawayenta gareta. Har takai babu kunya Fadwa na tambayar su Mom ina suka samo Anam ɗin?. Murmushi kawai Mom tai da faɗin “Itama ƙanwarki ce”. Daga haka ta tsuke bakinta duk da tambayar bin ƙoƙwanto da ƙawayen Fadwa ke cigaba da jefamasu Mom ɗin. Aunty Amarya dama bata tanka ba dan ita bata da farin jini a garesu kasancewarta kishiyar Mommy.      Har dai suka baro gidan Fadwa da ƙawayenta basu san matsayin Anam ba. Ita kuma ta miskile ko ruwa bata sha ba a gidan har suka taho. Gwaggo halima ma duk da taga kamanin Abie a jikin ta kuma tasan sun zo bata tanka ba bata nuna komaiba. Anam ma sai da suka ɗakko hanyar gida ta fara yima su Mom mitar Fadwa da ƙawayenta masu shegen rawar kan tsiya da nuna wayewa. Murmushi kawai Mom da Aunty sukeyi dan mota ɗaya suke su uku, ƴan uwan Mom ma na nasu su biyu.       Bayan sun iso gida kowa yaji ainahin watan bikin a bakin su Abie. Nan da watanni biyu. Sauran yaran gidan nata murna duk da wannan ba shine karon farko da za'ai biki ba. Anyi bikin Rahma dake bima Khaleel, da Binta ƙanwar su Shareff dake bima Maheer. Yanzu Aysha ce a layi kuma sa'ar Anam ce dan watanni ta bama Anam ɗin kawai, itace ɗiyar Mommy ta biyar daga ita sai autoci su twins. Ga Anam kam babu dalili ta wani tsume sai kallonsu take da taɓe baki, har bayan magrib babu fara'a a tare da ita. Rashin walwalar tata yasa koda Aysha ta tambayeta. Sai tace ba komai.      Sai bayan magrib suna hira duk kusan yaran gidan a falon aunty Amarya, gaba ɗaya hirar tasu ta ta'allaƙa ne akan shirin biki. Sai dai Anam taƙi tako tanka sai faman game take bugawa a waya. Sai dai kuma kunenta duk yana a garesu ne. Jin sun cigaba da damunta ta tashi zaune tana wani taɓe baki da harar Nusaiba mai gwada rehearsal na rawan da zasuyi wai a wajen dinner....      “Kun wani dage sai tsara events kuke bayan amaryar ma ko aji bata da shi mtsoww!!”.    Lokaci ɗaya falon yay tsit duk suka juyo suna kallonta. Hussaina ta ɗan waro ido da ƴar tsiwa tace, “Aiko dai aunty Fadwa nada aji gata ƙyaƙyƙyawa ƴar babban gida bama son jealous”.        “Jealous!!. K! Hussaina dani kikeyi wai! kowa ma? Ni Juwairiyya ce zanyi jealous ɗin wancan farin ƙasan mai kama da ƴar tallan kasuwa. Baki da hankali”.       A yanda take maganar a fusace yasa Hussaina tsorata, dan in tsiwa takeji Anam kakartace a iyawa. Amma shirun nata badan tsoron bane kawai, harda wanda idonta ya hango ya shigo falon ne yasa tai shiru. Anam kam da sam bataji ko sallamarsa ba sai faman faɗa take da sule Fadwa iya gaskiyarta. Tsaki ta doka da fisgar tab ɗinta dake hanun Hashim da nufin barin wajen, karaf idonta ya sauka a kansa. Yana tsaye tamkar an dasashi ya kafeta da manyan idanunsa masu razana wanda ya shiga gonarsa. Sosai gabanta ya faɗi, amma da yake ƴar gagiyar bata yarda aga gazawarta a fuska ba sai ta ɗaukesu cike da wani irin sallo da kaɗasu kamar mai harara ta nufi hanyar kitchen domin bi ta baya, dan tana shakkar bi ta gabansa tunda a ƙofar falo yake tsaye. Duk da bai nuna yama ji abinda tace ɗin ba hakan bai hana su Aysha ƙara nutsuwa ba.          Washe gari Abie yay shirin komawa. Anam ta zauna taita kuka itafa sai dai su koma tare. Yasan halinta akan kafiya, baiyi da wasa ba yay mata fata-fata, sai su Abba ne da aunty Amarya keta lallashinta da Ya Khalel. Shareff kam duk da yana wajen ko tari baiyiba. Yamaƙi nuna yasan abinda akeyi. Sai da zai buɗema Abie baya zai shiga ne ya harareta. Ƙasa tai da kanta ta sake fashewa da kuka.         Daddy da yaga hararar Shareff na ƙoƙarin shiga mazaunin driver ya dakatar da shi. “Kaga ku wuce da Mamana tai rakkiyar itama”. Kansa ya duƙar ƙasa fuskarsa na sake tsukewa da satar kallon Mommy. Murya a rissine yace, “Daddy zanje wani wajene fa bayan airport ɗin”.     “Sai ku tafi tare da ita tama huce kafin ku dawo gida”.     Sosai takaici ya sake lulluɓesa. Sai dai baice komaiba. Daddy da kansa ya buɗe gefensa ya sakata dan Abie baya ya shiga. Koda suka bar gidan shi da Abie ne kawai keta hirarsu. Itako tai tsit kamar bata a motar, sai ajiyar zuciya take faman saukewa idanunta a lumshe sanyin ac na ratsata. A airport ɗin ma Abie shareta yay har sai da aka fara shelar masu tafiya a jirgin da zaibi sannan yaɗan fara lallashinta da ƙara mata nasiha. Daurewa kawai takeyi, amma ita dai bata ƙaunar zama a ƙasar batare da iyayenta ba. Da ƙyar ya ɓanɓareta a jikinsa domin amsa kira, tana ganin ya shige ta dirƙushe a wajen. Takaici ya saka Shareff buɗe motarsa yay shigewarsa. Jin ya mata key ya sata miƙewa da sauri dan ta tabbatar kaɗan daga aikinsa ya wuce ya barta a wajen.       Sunbar airport ɗin kaɗan kiran Momy ya shigo masa. Idonsa ya ɗan rumtse kafin ya kai hannu ya ɗaga. “Kana ina?”. Ta faɗa tunkan yay sallama. “Mommy can gidan mana”. Ya faɗa a tausashe. “What! Al-Mustapha kana da hankali kuwa? Da wannan yarinyar kake nufin kaje?! To ina mai tabbatar maka maza ka sakota a napep ta dawo gidan ko ranka ya ɓaci bansan iskanci”. Ɗan jimm yay na sakanni biyu. Sai kuma ya ɗan saki murmushi. “Okay Mommy ba damuwa”. Numfashi ta sauke a hankali da faɗin, “Yauwa ko kaifa. Bana son wannan karon naji abinda bai minba kaga dai yanzu akwai banbanci da da. Ka kula ka bita a yanda take so dan ALLAH”. Nanma murmushin kawai yayi batare da yace komai ba, sai dai har cikin kunnenta tajisa dan haka tai masa sallama ta katse kiran. Wayar ya ajiye shima ya cigaba da tuƙinsa a nutse har suka iso.        Da sauri ta waro idanu waje ganin inda suka zo, ta dubesa idanunta nayin ƙwal-ƙwal na tahowar kuka. “Yaya! nidai ka kaini gida bazanje wannan gidan ba”.        Harara ya zuba mata, batare da yace komai ba yay parking a ƙofar gate ɗin. Sanin abinda zatai nan gaba shine roƙonsa ko guduwa ya sashi dubanta, “Haɗiyemin wannan silly hawayen banzan kafin nai miki dukan mutuwa a wajen nan”.      Babu wasa a zancen nashi, dan haka ta haɗiye sautin kukan sai dai hawayen kam sun kasa tsayawa. Wayarsa data fara tsuwwa ya ɗauka, ganin mai kiran ya sashi ɗagawa da kaita kunne. “Ina waje”. Kawai ya faɗa tare da yanke wayar. Ko mintuna biyar basu gama cikaba Fadwa ta fito cikin yauƙi da yanga. Wando da riga ne a jikinta parkistan ƙirar Egypt. Sosai kalar kayan ya fidda mata ƙyawunta. Musamman yanda ƙaton gilashin data saka ya kusan mamaye rabin fuskar tata da haska farar fatarta. A hankali Anam taja guntun tsoki da ɗan laɓe baki. Sarai Shareff ya jita, sai dai komai baice mataba har Fadwa takusa ƙarasowa garesu.      “Fita ki koma baya”. Yanda yay maganar a dake batare da ya kalleta ba ya sata juyowa ta kallesa. “Are you daft?!”.      Maganar tasa tayi dai-dai da isowar Fadwa jikin motar tana ƙoƙarin buɗe gaban ta shiga dan batai zaton ganinsa da wani ba ma balle wata.  Da sauri Fadwa taja baya saboda yanda Anam ta buɗe murfin a fusace. Saura kaɗan ta bugeta ma ALLAH dai ya taƙaita abun. Ko kallon inda take Anam bataiba tai ƙoƙarin barin wajen maimakon baya daya bata umarnin komawa. Sai dai kuma Fadwa tasha gabanta da sauri....      “K! K! Dakata k! Ƴar uban wacece a motar mijina?”.      Ba kowacce hausa Anam ke ganewa ba, dan haka a yanzun ma bata fahimci furucin farko ba hakan yasata kasa haɗa ma'anarsa dana ƙarshe da ƙyau. Amma a yanda Fadwa tai maganar ta tabbata ba'abune mai ƙyau ta faɗa ba. Wani banzan kallo ta watsa mata kawai dajan tsaki ta ratseta zata sake barin wajen. Hannu Fadwa tasa ta fisgota ta maidota baya a wani irin fusace, kasancewarta mutum mai saurin zuciya da son yanke hukunci sai kawai ta ɗaga hannu da nufin zabgama Anam ɗin mari.........✍ *_Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Hajiya Fadwa daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. To ku garzayo cikin tafiyar zafafa biyar domin ganin yaya wannan wasan zai kasance😂. Dan tabbas akwai cakwakiya, idan nace cakwakiya ina nufin cakwakiya ƴar gaske. Yanda Fadwa take a tsaye Anam ɗin ma ba kanwar lasa bace. Littafine daya ƙunshi abubuwa da yawa. Rikicin zumunci, makirci, son zuciya, kishi, cin amana, kai harma da SARAN ƁOYE. Wasa ne kashi-kashi, dake da players daban-daban. Karku bari ayi babu ku, zafafa dabanne masoya, musamman na wannan ƙarnin da zasu zo muku a cikin zafi na musamman. Karna cikaku ku dai ku garzayo kawai._* _Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, dan girman ALLAH kizo ki mallaki halak ɗinki, idan baki da kuɗin saye ko baki da ra'ayin saye basai kin damu da karantawa ba dan baya cikin wajib. Mai tunanin siya ko mana mugunta ki fitar kiji tsoran ALLAH karki cutar damu bamu cutar dake ba, idan kinyi shirin haka da gayya ko izgilanci a garemu muna roƙon UBANGIJIN al'arshi mai rahama mai jin ƙai, mai sanya alkairi a zukatan dake ƙudurta sharri ya shiryeki ya ganar dake gaskiya ya kuma bamu kariya daga abinda zuciyarki ke ƙulla miki😊🙏🏻._ KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE. DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300) BIYU (400) UKU (500) HUDU (700) KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE! ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN HAFSAT UMAR KABIR ZENITH BANK 2270637070 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 07040727902 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09134848107 KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽 [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_07_* .........Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma ɗan uwansa magana. Yanata tuƙinsa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaɗi har suka iso. Motar ta buɗe tai ficewarta tana taɓe baki, sai da ta rufe masa ƙofar batare data kallesaba tace, “Jazakallahu khairan” tai gaba abinta. Fusgar motar yay da ƙarfi yay gaba har yana tada ƙura. Hakan yasata faɗin, “Kaji dashi in kayane dai”.         Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira da marmari har ranta ya fara ƙuna gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun. Sosai ranta yake a ɓace ga yunwa dake bala'in cin hanjinta dan bawani abun kirki taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da strawberry. Ganin yamma na ƙara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la'asar, sai dai ita zafi takeji matuƙa kodan inda ta fito akwai ac ne.         Ta tare abin hawa yafi sau huɗu amma ta rasa yanda zata musu misalin anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe ƙwalla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ƙaunar wulaƙanci shiyyasa bata wulaƙanta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na wulaƙanta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya ba. Hannu takai a hankali ta share ƙwallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da ƙaunarsu, waɗannan matsalolin na ɗaya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar ƙasa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta.......         Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruɗeba, dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.      “Beauty!”.   Ya faɗa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi.            Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta ɗago ba. Sai ma sake haɗe fuska da tai ta ɗauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda tai ɗin ya tabbatar masa ita ɗince. Buɗe motar yay cike da farin ciki ya fito. “A gafarce ni. Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya koma ta gabanta cikin sake raunana murya. “Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haɗamu daga ni sai k”. Karon farko ta ɗan ɗago ta dubesa, ya sakar mata murmushi. “Dan ALLAH kar kice baki ganeni ba”.      “Bamma taɓa ganinka ba”. Ta faɗa da ƙoƙarin barin wajen. Sauri bin bayanta yay. “Please dan ALLAH karkimin haka. Ni ne wanda muka taɓa haɗuwa a GJ restaurant da daddare”. Sarai ta ganesa tun kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake ɓata fuska aɗan fusace tace, “Bani bace Please kabar bina”.        “Kiyi haƙuri bazan iya daina binki ba wlhy dan kullum cikin addu'a da sadaka nake akan ALLAH ya sake nunamin ke. Ya kuma amsamin sai nayi sakaci da damata”.    Sosai ya bata dariya a wannan gaɓar, wai sadaka. Dan kawai ya ganta zaiyi sadaka. Hararsa tai zata sake wucesa ya babbake ko'ina. “Dan ALLAH ki saurareni”. Kanta ta dafe dan yanata faman haɗata da abinda bazata iya jayayya ba. Hakan yasa dole ta nutsu ta sauraresa. Bawata magana sukaiba damar kaita gida kawai ya nema. Bata da mafitar data wuce binsa, amma maimakon gida da yace zai kaita sai kawai ta buƙaci ya kaita inda zata sai layin waya. Bai musa mataba, dan a ganinsa hakanma wata damace.         Kai tsaye office ɗin mtn dake cikin wata plaza yakaita duk da yasan sun tashi aiki yanzu. Sai dai yanada alfarmar da za'a iya biya mata buƙatarta a wajen. Ilai kuwa tarba ta mutuntawa taga ana masa a wajen, yanda kuma suke gaisuwa da ogan wajen taji a ranta ɗan uwansane ko aboki.       “Mutumina wannan ƴar shilar fa haka?”.     Abokin ya tambaya cike da shaƙiyanci cikin zaurancen hausa da Anam ta kasa gane komai dan shima ya fahimci bata iya hausan ba, saboda yanda yay mata tambaya da hausa ta gagara bashi amsa mai ƙyau. Dole suka koma magana da turanci. Murmushi kawai yay batare daya bashi amsaba, sai ma danna waya da yake faman yi abinsa.      “Wai ka zama kurma ne?”. Abokin ya sake tambaya yana harararsa.        “Sarai ina jinka. Kai dai yi aikinka  kawai ba buƙatar tambayar ne”.    Dariya kawai abokin yay ya cigaba da ƙoƙarin ɗaukar Anam hoto. Tun a gurin ta ɗora layin akan wayarta, ta kuma tambayesu ko zata iya amfani da shi. Kasancewar abokin nasa babban ma'aikaci sai ya amshi wayar yay ƴan danne-danne ya miƙa mata. “Indai kiran gaggawa kike sonyi da shi bashi nan da mintuna talatin sai kiyi”.     Godiya ta masa tare da duban saurayin da har yanzu ko sunansa bata sani ba. “Zamu iya tafiya?”.      “Why note Beauty”.   Ɗan murmushi kawai tai da mikewa. Shima ya bama abokin nasa hannu suka cafke. “Friend ina zuwa ka jirani Please ”.      “Ba damuwa”. Cewar abokin nasa yana dariya.              Ganin sun ɗan gota plaza ɗin tace su ɗan tsaya mintuna talatin ɗin su cika. Bai musaba sai dai ya kalla agogonsa duk gudun kar lokacin salla ya shiga. “Beauty inaga muɗan matsa gaba akwai massallaci sai na shiga nai magrib ko”.      “Babu damuwa”. Ta faɗa hankalinta akan wayarta. Tun fitarsa a motar babu abinda take sai irga mintuna har ALLAH yasa suka cika. Kai tsaye number ɗin Abie tahau gwadawa dan ta loda kati daga kuɗinta na bank a ciki. Taƙi samunsa saboda network. Komawa tai kan Mamie itama dai yaƙi tafiya kiran. A take idanunta suka sake cika da ƙwalla, ta kife kanta a gwiwarta tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki. A haka ya dawo ya sameta. Sai dai tanajinsa tai azamar goge hawayen nata ta haɗiye kukan.      “Beauty ina muka dosa yanzu kenan?”.            “Abinda nake tunani kenan, dan kona maka kwatance ba lallai ka gane ba. Amma in ban takurakaba ka kaini restaurant ɗin nan kawai ka ajiye zan samu mafita”.         Kallonta kawai yake cike da nazari. “Na miki wani tambaya mana in bazaki damu ba?”.     Shiru kamar bazata amsashi ba. Sai kuma taja numfashi da jinjina masa kanta. Gyara zamansa yay sosai yana fuskantarta. “Harshenki ya tabbatar min idan ma ke ƴar Nigeria ce ba'anan kike rayuwa ba? Hakan na nufin ke baƙuwace shiyyasa bazaki iya gane inda zakije ba?”.        Nanma kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ɗan kallesa ta duƙar dakai. “Karka damu ka kaini inda nace kawai Please”.    “Baki son na sani ko?”. “No, kawai”. Ta faɗa a taƙaice. Bai sake magana ba ya ɗan rausayar da kansa da yima motar key yana murmushi.          Koda suka iso kamar yanda ta buƙaci ya tafi ya barta a wajen bai yarda yayi haka ba. Cikin lallashi ya sata suka shiga wajen. Yabi ya takura mata akan ta faɗi mi take son ci amma taƙi, dan Anam nada wani hali inhar bata saba da kai ba bata taɓa yarda ta sake da kai. Shi kansa badan tana neman mafitaba bazata bisaba tun farko ko wane irin naci zai mata kuwa. Haƙura yay ya amsar musu drinks kawai da snacks amma ko kallon natan bataiba balle yasan zataci.     Tunanin kiran Aysha ne yazo mata a rai. Ta sake zaro wayarta dake cikin bag ta hau lalubenta. Cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, sai dai harya katse ba'a ɗaga ba. Bata gajiba ta cigaba da kira har wajen 8missed call amma babu amsa. Da ƙyar ta iya ƙoƙarin danne kukan dake son taho mata...... _______________________       Ko kaɗan baiyi tunanin bazata iya maido kanta gida ba. Hasalima zuciyarsa raya masa take tuni ta dawo ɗin saboda yayi over time a office yau yana aiki, ga kansa na masa ciwo. Daya shigo gidan ma a ɗan gurguje ya shiga suka gaisa da Mommy ya fito. Wanka yayi a gaggauce shima saboda magrib dake kusantowa. Koda ya kammala shiri ya fito a compound ya haɗu da Abbah da Khaleel suma zasu massallaci. Tare suka fice, bayan an idar da magrib basu dawo gidaba sukai zaman jiran isha'i....        Tun kafin su ƙaraso suka hango Mom da Aunty Amarya tsaye cirko-cirko a ƙofar sashen aunty Amaryar. Dukansu sai suka nufi can dan da alama babu lafiya. Shidai kusan shine ƙarshe dama. Daddy da suka haɗu a massallacin ne ya fara jefama su aunty amarya tambayar “Lafiya kuke tsaye anan haka?”. Aunty amarya ta bashi amsa cikin damuwa da ruɗani. “Daddyn Shareff lafiya ba lafiya ba. Anam ce bata dawo gidaba har yanzun. Mubarak yaje har wajen aikin nata kuma maigadi ya tabbatar masa babu kowa a ciki ita ɗincema kusan ƙarshen fita, ta kuma jima a titi kafin yaga wani ya ɗauketa a mota”.       “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un”. Daddy da Abba suka faɗa kusan a tare. Shareff ma dake daga bayansu gabansa ne ya faɗi, suka haɗa ido da Daddy daya juyo yana masa kallon tuhuma. cikin son danne abinda keson taso masa yace, “Shareff nasan dai kaji mi mamarku ta faɗa ina ka baromin yarinya?”.       Sosai ƙirjinsa ke luguden duka. Ya girgiza kansa da risinar da idanunsa da sukai sirkin ja kaɗan saboda gajiya da ciwon kai.       “Ba girgizamin kai zakaiba ka buɗe baki kai magana!!”. Daddy ya sake faɗa a tsawace.             Kansa a ƙasa yace, “Ban baro office ba sai kusan 6, shiyyasa nai tunanin ta dawo gida”.     “Shareff are you out of your senses?!! Har kake gayamin kazata tama dawo gida. Kana da hankali kuwa? Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”.          “Wai lafiya mike faruwa ne?”. Mommy da Hassan yaje ya sanarma gidan babu lafiya ta faɗa tana ƙarasowa wajen. Babu wanda ya iya bata amsa saboda maganar da Daddy ya cigaba dayi a kausashe cikin kuma tsananin ɓacin rai....        “Wlhy na baka nan da zuwa ƙarfe sha biyun dare ka kawomin yarinyata gida, inba hakaba sai ranka yayi mummunan ɓaci Al-Mustapha!!”.            Cikin sauri Mommy ta dakatar da shi itama a fusace. “A'a Alhaji kamarya da wannan hukunci haka. Shine ya ɓatar da koma wacece ake neman da za'ace ya fita a wannan daren nemanta bay......”         “Babu ruwanki a wannan maganar, idan kuma kikace zaki shiga wlhy zan sakaki nadama ne!!”.       Gaba ɗayansu binsa sukai da kallo ganin yanda yabar wajen a matuƙar fusace. Banda Shareff da kansa ke ƙasa. Abba ne ya dubesa da damuwa shima, sai dai cikin sauƙaƙa murya dan bai kai Daddy zafi ba yace, “Son kayi kuskure. Ka manta Anam babu inda ta sani, ko anguwarnan bana zaton ta san sunanta ma, kag........”      A harzuƙe Mommy ta katse Abba “Anam!!. dama akan wannan tsifatar yarinyar ake wannan tada jijiyar wuyar? Shareff bance ka fita harkar yarinyarnan ba a gidan nan?”.       Bai iya ya ɗago ya kalleta ba, dan baisan wace amsa zai bataba. Tana ƙoƙarin nufosa isowar Gwaggo ya dakatar da ita. “Wai hayaniyar mi nakeji a gidanne haka kai?”. Duk juyawa sukai gareta. Ganin kowa ya kasa cewa komai Khaleel yace, “Anam ce bata dawo gida ba”.        “Shine miya faru kuma? Ita ɗin yarinyace?”.       “Haba Gwaggo ya zakice haka? Nawa Anam ɗin take? Sannan ina ta sani bayan kinsan kamar baƙuwa take a ƙasarnan bama garin kano ba”.           Harara Gwaggo ta zubawa Abba mai maganar. “Oh to kana faɗaminne ko kana tunamin Abubakar? Gallaƙeƙiyar budurwa da yanzu idan aka sakata ɗaki da namiji zata samo ciki kake sanarmin nawa take? Toni abindama ban ganeba mi'akema hayaniyar anan?”....       “Titsiye Shareff sukai yaje nemanta kamar shine yace ta tafi yawon tazubar ɗin, dan nasan bai wuci can ɗin ta tafi ba tunda an saba a inda aka fito..”        “A lallai kuna bukatar Addu'a Abubakar. Shi Mustapha ɗinne ya kaita ya ɓatar da zakuce yatafi nemanta a wannan daren bayan wahalar da yaje ya gama shawowa a wajen aiki ya dawo. Kai Mustapha muje naga ubanda zai saka fita ko nan da gate a daren nan dan.......”      Sauran maganar ta maƙale ganin kaf wajen babu alamar Shareff ɗin. Su dukansu babu wanda yasan yama sulale yabar wajen. Horn da ƙarar buɗe gate ya sakasu juyawa can gaba ɗayansu. Sai dai kafinma wani yay wani yunƙuri har motarsa ta fice.....          Wajen aikin nata ya fara zuwa, sai dai kamar yanda maigadin wajen ya faɗama Mubarak shima haka ya sanar masa. Lokacin da yake tafiya a hankali ya dinga tafiya kozai ganta a hanya. Amma ko alamarta babu duk da titin wajen tako'ina akwai hasken fitulun solar. Duk da hakan bai fasa sake bi a hankali yanzun ma yana dubawaba har ƙarshen titin. Ganin har tara ta gota na dare yay fakin gefen titi ya kifa kansa kan sitiyari dan ciwo yake masa matuƙa kamar zai faɗo ƙasa. Dama tuƙin yinsa kawai yake cikin dauriya.            A gida kowa ka kalla a cikin damuwa yake, idan ka cire Gwaggo da Mommy da suketa bala'i da kowa ya kasa fahimtar dalilin yinsa. Aysha harda kukanta. Dan ansan ko wayarta aka nema baza'a samuba tunda bata da layin Nigeria. Abba da Daddy da Khaleel ma sun fice police station.       “Aunty wayarki sai haske yake tun ɗazun”. Hassan ya faɗa yana duban Aysha data zuba uban tagumi tana sauraren masifar Mommy kawai daketa faman kai kawo tsakanin bedroom ɗinta zuwa falo. Kamar Aysha bazatabi takan wayarba sai kuma tacema Hassan “Ciromin daga cajin”. Ciro mata yay, ganin bata san no ɗinba tai tsaki ta ajiye. Duk kiran da aka cigaba dayi har kusan sau biyar bata kulaba. Sai ma ɗaukar wayar datai rai a ɓace zata kashe sai saƙo ya shigo da no din da aketa kiran nata. Guntun tsaki tai ta buɗe dan taga wai waye ma ya addabeta ya barta taji da damuwarta ma itakam. Zumbur ta miƙe da waro idanu, har zata fasa ihu sai kuma tai saurin gumtse bakinta da satar kallon inda Mommy take. Tai saurin haɗiye farin cikinta ta nufi bedroom ɗinsu da sassarfa. Jikinta har rawa yake ta maida ƙofar ta rufe harda saka key tana dailing number ɗin...       “Blood da gaske kece?”. Kamar jira Anam keyi ta fashe mata Aysha da kuka. “Ya ALLAH Blood Please kibar kuka, kina ina ne yanzu? Ga gida duk hankalin kowa a tashe da rashin dawowarki su Yaya dasu Abba duk sun fito”. Ta ɗanji sanyi, amma hakan bai hanata jin zafin Shareff ba. Da ƙyar tace, “Zan tura miki address ɗin yanzu bansan inaneba”..... Aysha na katse kiran tai kiransa.       Har yanzu kwance yake kawai akan sitiyari, yama rasa wane kalar tunani zaiyi shi kam. Ring na wayarsa ne ya katse masa tunani. Yay banza da wayar harta tsinke aka sake kira. Nanma bai ɗaukaba sai ana uku ya ɗago a fusace da nufin cin uwar mai damun nasa yaci karo da sunan Aysha. “Lafiya kika isheni da kira ke kuma?”.       “Kayi haƙuri Yayah. Anam ce ta kiranifa yanzu da wani number sai kuka take.”      Idanu ya rumtse da ƙarfi yana sauke wata irin bahaguwar ajiyar zuciya da har Aysha na jinsa. “Turomin number”. Ya faɗa a takaice kawai da katse kiran. Mintuna biyu kacal number ɗin da address ɗin data turo mata duk ta turo masa. Wayar ya cilla gefensa yayma motar key da fisgarta a guje yabar wajen. Tafiyar mintuna ƙalilance ta kawosa wajen saboda uban gudun daya zabga..........✍ _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107       *_ALLAH yasa yau a rama mana marinmu😹😹😜🚶🏻_* [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummarka. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar da ni da su. ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai. Ka ƙara mana lafiya da zaman lafiya a wannan ƙasa. Ka azurtamu da shugaba na gari mafi alkairi a garemu da ƙasarmu_* *_06_* ...........Kafin ta sauke nata data ɗaga Anam ta sauke mata lafiyayyen mari daya saka Shareff ɗago idanu a karon farko ya kallesu. Fadwa tai saurin dafe kuncinta tana kallon Anam dake jifanta da wani shegen kallo na gargaɗi tana huci. Mamaki, al'ajab da tsantsar ruɗanin daya haɗu da azabar zafin mari take kallonta ƴar ficit a gabanta. Ba ita kaɗai ba, hatta Shareff wutar kansa ta ɗauke dan mamakinta da ƙarfin hali dama tsaurin idanu.       A fusace Fadwa ta kai hannu da nufin shaƙota. Wani shegen kallo ta sake watsa mata da riƙe ƙugu, babu alamar tsoro kona sisi a idanunta cikin zafin rai da harshen nasara ta nunata da yatsa.        “Niba takalmi bace, ballantana ƙafafunki suyi tunanin takawa a duk sanda sukaga dama. Respect your self ok? Shashasha”. Ta ƙare faɗa tana barin wajen cikin takun izza...     Tamkar gunkin da aka dasa haka Fadwa ta kasance tsaye tana binta da kallo, dan da gaske wutar kanta ce ta ɗauke baki ɗaya har tama rasa hukuncin da zatai mata. Kusan taku biyar da barin Anam wajen Fadwa ta dawo hankalinta, zabura tayi zata bita  Shareff da mamaki ya hanashi motsin shima ya buɗe motar ya fito, cikin bada umarni yace, “Ƙyaleta”. Juyowa tai tana kallonsa idonta jajur, hakama fuskarta tayi ɗan ja abinka da fara. Tana bala'in jin shakkarsa, amma sai ta kasa daurewa cikin ɗaci tace, “Soulmate! Na ƙyaletafa kace?”.       Kansa ya jinjina mata cikin ɗan lumshe idanu da jingina da motar, sosai take masa kallon tunzura, amma tai ƙoƙarin haɗiye dukkan abinda ke bakinta. Batare da tace komai ba ta juya da nufin komawa gida. Hanunta yay saurin riƙowa, tai ƙoƙarin fisgewa amma ya hanata damar hakan. A jikin mota ya jinginata idanunsa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da hawaye ke sauka. Ba abinda Anam tai mata bane ya sata kuka, hanata ɗaukar matakin da yayi ne yafi ƙona mata rai.     Handkerchief ya mika mata, idanunsa na mata kallo cikin lallashi “Nace miki bazan ɗauka mataki bane?”. Idanunta dake ƙara cikowa da hawaye ta ɗago ta kallesa. Ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. “Bana son ɗaukar mataki cikin fushi akan kowanne irin abu ki kiyaye wannan. Shiga muje”.          Ƙara ƙuna zuciyarta tayi da kalamansa, kamar tace bazataje ba ta fasa sai kuma ta danne saboda shawaran su Mamanta akan ta danne komai dazai mata a yanzu har ta shiga gidansa. Sannan koba komai tana son sanin wacece yarinyar nan, amma cikin fushi tasan bazai sanar mata ba ɗin. Umarninsa tabi ta buɗe motar ta shiga, idanunsa da suka kaɗa sukai jaa ya ɗan bita da su, sai kuma ya janye dayima motar key yay reverse. Kasancewar anguwace da kakan daɗe bakaga abin hawaba yasa har suka cimmata. Tafiya take tana sharar hawaye. Duk da horn da aketa faman mata baisa ta juya ba. Ransa ya ƙara ɓaci, a fusace yay parking tare da fitowa yasha gabanta, kanta ta ɗauke gefe kamar bata gansa ba zata raɓashi ta wuce.       Hannayensa ya tura cikin aljihun wandon Jeans ɗinsa. “Idan kika ƙara step ɗaya a wajen nan sai jikinki ya faɗa miki!”. Cak ta tsaya iya taku biyun da tai, wasu irin hawaye masu zafi suka ƙara ciko mata idanu. Motar ya nufa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta. Duka kawai take tsoro, dan haka ta share hawayenta dan bata bukatar da ga shi har budurwar tasa su gani, motar ta buɗe ta shiga. Yay ƙaramar ƙwafa da buɗewa shima ya shiga, ya fisgeta da gudu zuwa kan titi batare daya ƙara kallon kowaccensu ba. Sunyi tafiya kusan na minti biyar dai-dai gidan wani abinci Fadwa ta dubesa, “Please Soulmate banyi breakfast ba”. Shiru yay kamar bazai tanka ba, bai kuma da alamar tsayawa, itama kasa ƙara cemasa komai tayi saboda yanda ya haɗe fuska matuka. Harma ta haƙura sai taga ya gangara gefen titi dai-dai wani restaurant da bama tasan da shi ba. Buɗe motar yay ya fita batare da yace musu komaiba, itama Fadwa sai ta fita tana harar Anam data maida hankali ga latsa waya kamar bata a motar. Suna ƙoƙarin barin wajen yakai dubansa gareta, dai-dai ta ɗago itama suka haɗa ido. Fuska ta sake ɗaurewa tamkar yanda shima ya sake tsuke tasa. A yanayin fusata ta janye nata da ɗan kallar gefen Fadwa. Har suna gab da shiga wajen bata da niyyar fitowa ita, sai da suka shige da kusan minti biyu sannan ta fito dan haka kawai zuciyarta ta raya mata ta bisu koba komai zata ragema Fadwa jin daɗi ai. Cikin taku a hankali ta shigo wajen, dai-dai yana magana waiter idonsa ya sauka a kanta harta ƙaraso inda suke, kujera taja ta zauna. Idanun nasa ya ɗauke gefe, tare da yin kamar bai ganta ba ya ɗauka wayarsa ya hau dannawa. Kallonsa ta ɗanyi tana tura baki, batare data kalli inda Fadwa take ba itama ta hau latsa tata wayar cikin kwaikwayon salon da yayi.       Ta gefen ido ya dubeta, numfashi ya ɗan ja a fisge tare da maida hankalinsa ga wayarsa a zuciyarsa yace (azababbiyar yarinya).       Kamar tasan mi yake ayyanawar ta ƙara ɗaure fuska tana hararsa shi da Fadwa da hankalinta itama gaba ɗaya ke kan wayarta da alama akwai abinda takeyi mai muhimmanci. Isowar waiter ɗauke da tray ya sakasu ɗagowa su duka. Har waiter ɗin ta gama shirya musu abincin tabar wajen idon Anam nakan nasa. Ya ɗau cokali zai fara ci tace, “ALLAH Yaya abincinka yafi nawa nama”.        Duk yanda yaso basar da ita ya kasa. Ya kafeta da idanu kamar mai harara “Kuɗinki ko kuɗina?”.   Fuska ta taɓe “Naka ne. Amma kuma ai ina cikin masu cin gadonka idan ka mutu, kaga banda laifi idan nayi magana”. Wani wawan tsaki Fadwa ta saki tsanar Anam na ƙara faɗi a ranta. “Shiga shanu ba sharo”Anam ta fada cikin sakin siririyar dariyar data sake kular da Fadwa (*Sharo ba shanu* bahaushiyar malaysia😹😆)      Tattausan murmushi kawai ya saki a karo na farko da cigaba da cin abincinsa. (Batun yanzuba ya fahimci bata da riƙo. Sai dai ya tabbatar wannan sauyawar tata lokaci guda ba'a banzaba akwai abinda ke ranta). Fadwa ta kafesa da kallon mamaki, sai dai shi yaƙi yarda ya kalla inda take. Saurayin dake kusa da su da drama ɗin tasu taja hankalinsa tun ɗazun yay ƴar dariya idonsa akan Anam shi kuma. Juyawa tai taɗan kallesa. Ganin shima ita yake kallo ta ɗauke kanta tana harararsa, abincin Shareff ta ƙara kallo, burinta kawai ta yanda naman kan plate ɗin nasa zai dawo nata, ganin hankalinsa nakan wayarsa tace. “Yaya!”.       “Uhhyim!”. Ya amsata batare da ya daina abinda yake ba. “Na faɗa maka wani abu?”.      “Uhhm” Nanma ya sake faɗa batare daya ɗago ɗinba. Ɗan shiru tai tana nazari. Bayan kusan sakan talatin ta dubesa sai kuma ta ɗan harari Fadwa ta maida dubanta ga ƙofar shigowa. “Lah Yaya wannan ba Aunty bace?”.      Kamar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin jin kamar tayi maganar a serious. Kallonsa ya kai ga ƙofar duk da bai san wace aunty take magana ba akai kamar yanda itama Fadwa da gaba ɗaya takaici ya turniƙe takai kallonta wajen. Wuff ta kwashi kusan rabin naman daya tsole mata ido ta maida a plate ɗinta. Lokacin da yake juyowa fuska a tsuke harta miƙe a table ɗin ta koma na kusa da su da guy ɗin da duk hankalinsa ke kansu yake.      Plate ɗin abincin nasa ya kalla sai kuma ya kalleta. Kauda kansa yay gefe saboda murmushin dake neman suɓuce masa. Ya ɗan jinjina kansa dayin ƙwafa. Fadwa dai kallonsa kawai take mamakin tsaurin idon yarinyar nan na nema shaƙureta.        Saurayin da gaba ɗaya komai na Anam ya gama tafiya da imaninsa shima fuskarsa ɗauke da mayataccen murmushi yake kallonta. Ya sake sakin murmushi ganin duk laumar abincin da zata kai sai da yankan nama. Cikin murya ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai zataji yace, “In ƙara siya miki wani gimbiya?”.         Kai ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta saci kallon Shareff. Ido suka haɗa, ya zuba mata hararar da hanjin cikinta suka kaɗa, amma saita fuske cikin dakewa. Ƙasa tai da idanunta Tana ƙoƙarin sake kai abincin bakinta kamar bata gansa ba, saurayin ya sake ɗan matsota cikin ranƙwafowa har tana jin hucin numfashinsa yace, “Queen Please”.       Wani irin cije baki Shareff yayi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe gaba ɗayansa. Gabansu ya iso ya ɗauka wayarta da saurayin ke ƙoƙarin ɗauka. A kausashe yace, “Tashi muje”.      Kamar bazata ɗago ba sai kuma dai ta ɗago tana kallonsa. “Ni banfa gama ba, ba yanzu muka fara ba, ga budurwarka ma bataci nata ba”.     “I will slap you in baki tashi ba”. Miƙewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba yayma waiter nuni tazo. Kuɗinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman rago. Fadwa da ko lauma ɗaya bataiba dama ta miƙe tsam da wayarta a hannu ta fice, bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko jikin mota ya sameta ta haɗe fuska tamau. komai baice mata ba ya buɗe ya shiga, a dai-dai nan aka kawo masa takeaway ɗin da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai saurin buɗewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buɗewa ya fito yana dube-dube. Wata shaƙiyyar dariya Anam ta ƙyalƙyale da ita harda kwanciya, tana ganin zai dawo ta haɗiye kayarta da gyara zama ta fuske... A dake yace, “Malama dawo nan”. Ido ta ɗan waro tamkar bata san mike faruwa ba. “Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari taje bane?”. Kallon banzar daya watso mata ya sata buɗe murfin ta fita tana danne dariya da ƙyar, ƙasa-ƙasa take faɗin, “Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai tasan ita ƙaramar ƴar iska ce”...... ★★★★          A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin ɓacin ran dake tattare da ita. Tunda Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma yaƙi shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba'aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa ɗauke da ledar takeaway. Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta waje.       “Yaya sannu da zuwa”. Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faɗin, “Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka”. A yanzu kam idanunsa ya ɗago yana kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai hannu ga ledar. “Bara na ɗauka maka to”. Harararta yay, babu shiri taja baya tana tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗagashi sama. “Oh my Friend ya kake?”.       “Lafiya lau Yayanmu. Good morning”.       Kumatunsa ya ɗan ja yana murmushi. Kafin ya ɗan kalla falon. “Gentlemen ina Mom ne?”.       “Tana ɗaki da aunty Rahma tazo”. “Okay! To kace ina gaisheta.”      Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef ɗin, cikin raɗa yace, “Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi”.           Idanu ya ɗan waro waje kamar yanda yaron yayi, “Haba dai?”.    “ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon ɗina”. “Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci tare”. Duk da ledar ta masa nauyi da ɗan gudunsa ya nufa ɗakin cike da murna yana ƙwala kiran “Aunty Anam! Aunty Anam!!”.         Idanu yaɗan lumshe a hankali da harɗe hannayensa duk biyu a ƙirji yana murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?.         Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haɗiye sauran gulmar da take faɗama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai saurin barin falon tana tura baki gaba.      “Shareff kai dawa kaje gidan Halima!!”. Mommy ta faɗa a fusace tunkan yace mata komai. Ɗan jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya ɗago yaɗan dubeta. “Mommy ni ban shiga gidanba ma balle naje da wani”. Harara ta watsa masa. “Wlhy Al-Mustapha ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai bazakajita da daɗi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka ɗauketa kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata walaƙanci a gabanta ko?! Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan haɗa zuri'a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan talla......”. Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ƙasan carpet ya zauna ya ɗora kansa jikin ƙafarta, hanunta ya riƙo cikin nasa murya a sanyaye, “First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaɓinki, idan ma hakane a ransu ai bani kaɗai bane ɗa a gidan ko?!.....”         “Ko kai kaɗaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane a ransu Maheer ma yafi ƙarfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel saina hana uwarsa yarda”.        Murmushi ya saki mai faɗi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar da suke masa ce ta sashi buɗe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma yace wani abu Hassan yay saurin faɗin, “Yaya daga aikan Gwaggo muke fa”. Komai baiceba ya miƙe ya fita a falon. ___________________         A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharɓa saboda jin daɗin ɗan sanyi-sanyin safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an ɗauke wuta bazata sake rintsawaba. Dan ƴar fan ɗin da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya taƙi ɗaukar caji. Gaba ɗaya Mom ta shafa'a da batun fara fitar Anam ɗin yau itama, shiyyasa batai tunanin tadata ba tanata ƙoƙarin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaɓeta da ƙyar..         Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma, bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haɓaka kamfani yake. Zamansa tsayayyen mutum yasa ma'aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani, dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu masu buƙatar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ƙanensa nata ƙoƙarin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ƙoƙarin kaiwa zaune a ɗaya daga kujerun falon dan bazaka taɓa ganinsa cikinsu yana cin abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining ɗin tana haɗa masa tea ta ƙaraso garesa. Tunkan ta ƙaraso ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mug ɗin. “Good morning First-luv”.       “Morning dear, how are you?”. “Alhamdulillahi”.      “Haka ake so ai. A saka maka Irish ɗin?”.     “No Mommy wannan ɗin ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight thirty”.         “To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight ɗin gab yake dayi”.       Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma'a da laraba zai sayo fruit bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ƙarshen wata zai sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai buƙata kananu yakai kowane sashe. Tun Mommy najin haushi da masa faɗa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan na damunta da ɓata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan haka ya maƙale daga ƙofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaɗa da take masa kuma ransa naso.       “Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida  Mom a kaimin mota”.     Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa school bus ɗinsu. Kafin ya ƙarasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi mai aikin Gwaggo ɗauke da ƙaramin basket. Tunkafin ya ƙaraso ya buɗe motar da key tai ƴar ƙara. “Ranka ya daɗe gashi inji Gwaggo”. Baice komaiba ya amsa basket ya ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yunƙurin shiga motar da yay niyya ya nufi Daddyn ɗin duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da asuba, tare kuma suka fita motsa jiki....        “Babana har an fito?”.    “Eh Daddy nama so makara dan inada meeting”.     “To ai yau da gobe sai ALLAH ko”. Daddy ya faɗa dai-dai da fitowar Anam daga sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka saceta ka gudu. Ta naɗa yololon veil ɗinta tare da ɗora p-cap ɗin samansa, saita goya bag ɗinta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta sauke hular daga kanta tace, “Good Morning Daddy”.      “Good Morning Maman Daddy. how are you?”.     “I'm fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daɗi”.          “Ayya mamana ba'akwai fan a ɗakin naku ba?”.   “Akwai Daddy, idan suka ɗauke nepa ɗinne fa, fan ɗin da Mom ta bani yaƙi ɗaukan cagi jiya”.      Kanta ya ɗan shafa da faɗin, “Am sorry insha ALLAH za'a saya miki wata to koda an ɗauke wutan, koma ac za'a sayo dai?”.       Ƴar dariya tayi da satar kallon  Shareff da tun zuwanta wajen ya haɗe fuska yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban Shareff ɗin, “Kun gaisa da Yayan naki ko?”.         Baki taɗan tura gaba da ɓata fuska, sannan tace, “Good morning”.       Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a aljihu da faɗin, “Daddy bara na wuce ina ƙara makara”.     Daddy yace, “Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce”.        Idanu ta waro da ƙyau tana ƙyaƙyƙyafta su. “Daddy Abie yace driver zai dinga kaini”.      “No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an ɗauka miki wani driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya ɗakkoki ba shike nan ba”.          Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai, sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata buƙatar haɗa sabgarta da shi. Duk miskilancin Khaleel tafi jin daɗin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai sauƙin kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daɗi.       Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa “To ALLAH ya bada sa'a. Sai ka wuce da Mamana ko”.  Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan rissinar da kansa ƙasa da fadin. “Mu yini lafiya”. Jinjina masa kai shima Daddyn yayi. “ALLAH yasa. Mamana bishi ALLAH ya bada sa'a”. “Amin Daddy” ta faɗa dabin bayan Shareff da tuni yay gaba abinsa kamar ta make masa ƙeya..........✍ _🤭🤗maza ki make to dan ALLAH_. _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*   [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_08_* ..........Tunda ya amsa wayar ya turama wadda ta kira da sister ɗinta address ɗin inda suke yaketa lallashinta ko ruwa tasha amma taƙi sai faman sharɓan hawayema takeyi. Hakan yasa yay tagumi kawai yana kallonta. Komai tai birgesa takeyi, Duk da ƙaramin jiki da take da shi kai kasan ba yarinya bace, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci lallai ƴar gatace a gidansu dan saurin karayanta yayi yawa. Hoto ya fara mata yana murmushi batare data sani ba.....          Tunda ya shigo idonsa ya sauka a kansu. Wani irin baƙin ciki da ɓacin ransa sai suka ƙara ninkuwa. Nufarsu yay rai a ɓace sai dai bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba duk da ya ciskulleta sam babu fara'a. Kamar ance ta ɗago idonta ya sauka a kansa. Babu shiri ta miƙe zumbur dan yanayinsa ya tsorarata, bata manta dukan da yay musu ita da Aysha ba. Wani irin mugun kallo yay mata ya ɗauke kansa ya maida ga saurayin da shima ya miƙe dan ya gansa. Kallon banza da tsana yake masa yayinda shi saurayin yay ƙoƙarin mika masa hannu suyi musabaha yana murmushi duk da yaga kallon banzar amma ya shanye.     Kallon hannun yay ya wani ɗauke ido da maidawa kan fuskarsa yana mici-mici da idanunsa dan sarai ya gane shine ranar yayta binsu daga wannan restaurant ɗin.....        “Kana buƙatar ka zauna lafiya?!!”.     Duk da a yanda yay maganar cike da isar gadara hakan bai hana saurayin sakin murmushi ba da jinjina kansa. Cikin sauƙaƙa tasa muryar yace, “Sosai kuwa babban Yaya. Ai magabatanmu kance zaman lafiya yafi zama ɗan sarki”.      Kansa ya ɗauke duk da shine ya buƙaci amsar kuma aka bashi. Wani ɗan juya harshensa yay cikin bakinsa cike da basarwa yana sakin murmushi mai harshen damo. Sai kuma ya jinjina kansa da sake maido dubansa ga saurayin fuska a haɗe. “To daga yau, daga yanzu, karka bari na sake ganin wannan fuskar taka a inuwa ɗaya da ita. Inba hakaba......”     Ya ƙarasa da wani shegen murmushi dimple ɗinsa na loɓawa, yaɗan bubbuga kafaɗar saurayin. Bai saurari amsar da saurayin zai bashiba ya fisgi hanun Anam dake maƙure waje guda zuciyarta kamar zata kifo ƙasa. Da tasan shine zaizo ɗaukar tata data aminta da shawarar saurayin daya buƙaci Aysha ta tura address ɗin gidan shi ya kaita amma taƙi. Jakkarta dake kan desk ɗin ya fusga itama tare da wayarta yay gaba da sake yima saurayin warning da idanunsa dake rine matuƙa fiye da yanda ya shigo wajen.....       Turata yay a motar ya rufe har saida ta zabura dan kaɗan ya hana ya datse mata yatsun hannu. Ya zagayo mazauninsa tare da figar motar a guje yabar wajen. Yanda yay ɗin yay masifar sake firgitata har sai da ta faɗa gefen hanunsa ta ƙudundune fuskarta tana kiran sunan ALLAH, dan ta zata gabzama motocin gabansu karo zaiyi ma. Ƙuwwww!!! Ya taka birki da daka mata wata razananniyar tsawa. Saurin sakinsa tai tai baya a firgice, sai kuma ta fashe da kuka dan gaba ɗaya ya sake firgitata ta tsani tsawa...          “Stupid! shut up!!. Idan baki rufemin shegen bakinki ɗin nan ba na fara kashe fuskarki da maruka sai kin suma. Wawuya kawai. K har idonki yay tsurin bin motar saurayi kuje restaurant?! Dama abinda kikazo yi kenan a Nigeriar?!!!”.       Yanda ya ƙare maganar a matuƙar tsawace ya sake birkitata. Amma sai ta danne cikin ƙarfin hali tace, “ALLAH ya kiyaye danni ba mayyar maza bace”. Ya sake watsa mata harara kai kace cinyeta zai da jajayen idanun nasa. Sai kuma yay ƙwafa da ɗauke kansa yana sake tada motar. Ko motsin kirki bata sakeyi tunda ta samu bai maketa ba. Kukan ma ta daina na zahiri na zucici takeyi. Gaba ɗaya jitake tama gama tsanar Nigeria, ita dai gaskiya bazata iya wannan masifar ba, tun farko abinda ta guda kenan amma su Mamie sukaƙi fahimtarta. Itakan duk ma yanda za'ai a satin nan sai tabar Nigeria hidimar ƙasar nan bazata yuwuba.....        Ko gama dai-daita parking baiyiba ta fita dan mutanen gidan duk suna tsakargida tsaitsaye Gwaggo da Mommy ne kawai babu sai irin su Fawwaz da sunyi barci tuni basu san abinda akeyiba. Aysha ce ta taho da gudu suka rungume juna, sai kuma ta saketa taje ta rungume aunty amarya da Mom. Su Daddy da tuni Aysha ta kirasu suka dawo gida zaman jiran isowarsu suma ajiyar zuciya kawai suke saukewa..       Mom dake shafa kanta da murmushi tace, “Kukan ya isa haka mana mamana. Tunda kuma an dawo gida sai muce Alhmdllhi. Jeki gaida iyayenki”.     Babu musu ta saki Mom tana share hawaye ta nufi su Abba. Gaishesu tai hawaye na sake silalo mata, abinka ga ƴan boko kasa daurewa Daddy yay sai da ya ringumeta. “Haba Mamana ina kika shige haka duk kin tada mana hankali”. Ya faɗa yana mai ɗagota a jikinsa. Murmushi tai tana share hawayen da suka ƙi tsayawa. “Daddy na kasa ganewane, idan na tsaida masu keke ɗinnan sai suce basu gane yanda nake faɗa musu gidan ba”. Tausayinta sosai ya ƙara kamashi, kanta Abba ya shafa yana murmushi. “Dole ki dage ki koya hausa a zaman nan Mamana, dan rashin iyawan ya taka rawar gani cikin accident ɗin nan”.       “A'a Abba dan ALLAH ni zan koma  Malaysia”.     “Tsit gurin yay babu wanda ya iya cemata komai. Sai Shareff ne ya wani taɓe baki da barin wajen ko uffan baicema kowaba balle bayanin yanda ya samota dan a matuƙar gajiye yake ga ciwon kan nasama zazzaɓi yake neman komawa. Daddy ya kashe shirun wajen da faɗin, “Kuje ciki tai wanka taci abinci dan tana buƙatar kwanciya da wuri. Mamana mayi magana da safe”.     Badan tasoba tabi Mom dan bata iya musu ba kuma. Duk da yanda Aysha ke tsoron faɗan Mom haka tabi Anam sashen Mom da ƙudirin su kwana tare, dan jitake kamar kafin safiya za'a ƙara cemusu ba'a gantaba ta sake ɓata.       Washe gari tunkan ma Anam ta kira Abie ɗinta ta sanar masa Daddy ya kirasa sukai magana. Yayma Shareff kuma faɗa sosai kamar zai ari baki. Daga ƙarshe ya kafa masa dokar hukuncinsa shine kai Anam wajen aiki kullum ya kuma ɗakkota. Idan ko wata matsala ta sake shigowa akan Anam to lallai ya kuka da kansa dan sai ya matuƙar ɓata masa rai a gidan.       Shi dai Shareff ɗin baice komai ba akan hukuncin. Sai Mommy ce tace sam bata yardaba ɗanta ba driver bane ba. Ko kallonta Daddy baiba, ya dai tabbatar mata idan Shareff ya isa yaƙi bin umarninsa.        Ai wannan magana ta dagula ran Mommy a safiyarnan. Dan tata masifa ita da Gwaggo data fito tana goya mata baya. Daga Daddy har Abba babu wanda ya sake tofa tasa dan sukam dai yanzu sai dai su kalla Gwaggo kawai tunda sun fahimci bata ƙaunar zaman lafiyarsu da ɗan uwansu, Halima ce kawai ta kasa fahimta sun kuma barta wataran zata gane da kanta musamman da suka san idan akai auren nan na Fadwa da Shareff.         ★★★★   Duk yanda Mommy taso hana Shareff ɗaukar Anam hakan bai yuwuba. Dan shi dai haƙuri kawai ya bata da nuna mata illar fushin mahaifinsa a garesa. Ya roƙeta ta kwantar da hankalinta a hankali zai janye jikinsa ya samama Anam ɗin driver kowa ma ya huta. Wannan magana tashi ce taɗan kwantar mata da hankali ta maida kanta ga hidimar shirye-shiryen bikinsa.       Daga ɓangaren Anam ma taci uban borinta akan malaysia zata koma ta fasa hidimar ƙasar su Mamie suka lallasheta da tabbatar mata cewar idan sukazo bikin Shareff zasu san abinyi. Hakanne yaɗan kwantar mata da hankali ta zauna zaman jiran lissafin kwanakin bikin. Yayinda ta cigaba dabin Shareff ɗin a takure. Shike kaita shike ɗakkota, daga gaisuwa babu abinda ke haɗasu sai harara. Ita kuma tata tura baki kenan da ɗaure fuska ita a dole haushinsa takeji duk da bata da riƙo sam wannan karon dai ta riƙe.            Yau a gurguje yay shirin tun 7 ma batai ba ya fito saboda wani babban uzirin dake gabansa a office ɗin. Ga baƙi zaiyi akan wani babban project da suke saran samu insha ALLAH. A tsaitsaye ya shiga sashen Mommy suka gaisa koma shayin bai zaman shaba yau dan yaran kansu duk suna ɗaki basu gama shiri ba. Baije sashen Gwaggo ba dan ya gaji da mitarta akan ɗaukar Anam da yake yasan zata ɓata masa lokaci. Aunty Amarya ma a tsaitsaye suka gaisa ya nufi sashen Mom. Bayan sun gaisa da Mom ɗin cikin raba ido da kallon ko'ina na falon yace, “Mom tana ina zan makara?”.       Da mamaki Mom ɗin ke kallonsa. “Wai kana nufin Anam?”.     Kansa ya jinjina mata. “Eh Mom, yau zan fita da wuri inada uziri shiyyasa na sanar mata tun ɗazun ta shirya da wuri”.       “Tab ɗi, to aiko banama zaton ta tashi a barci Babana. Ni kuma ban saniba ai da na tadata ta shirya”.         Cikin ɓacin rai ya ɗan sake duban agogonsa da rumtse idanunsa. Ganin Mom ta nufi ɗakin yaja ɗan siririn tsoki. “Mom bara naje idan Khalel zai fita su taho tare inada meeting ne mai muhimmanci”.       “To bara na tasheta dan nasan shima ɗin gab yake da fitowa kuwa”.    Komai baice ba ya juya ya fita.          Ba ƙaramin jan ido Mom taima Anam ba kafin ta tashi. A gurguje tai shiri saboda Khalel daya leƙo ya mata gargaɗi. Tasan halinsa shima ba mutunci ya cikaba shiyyasa tai ƙoƙarin shiryawa aɗan gurguje tanata kunƙuni dan barcin bai ishetaba. Tsaf ta shirya cikin kayan NYSE kamar koyaushe, sun mata cif kamar ka saceta ka gudu, ƙaramin baby hijjab tasa yau. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Khalel da gaba ɗaya yake ƙage da fitowar tata hanata zaman shan tea ɗin da Mom ta haɗa mata yayi.      “Mom Please ki barta tasha a hanya ko a office ɗin, ALLAH idan na makara Yaya zaimin faɗa duk da shine yace na ɗauketa, gashi meeting ɗin nan inada alaƙa dashi nima.”       “Amma Khalel ta fita bata karyaba? Bayan kasan bako wane abinci take iyaci ba. Kai da Shareff ɗin duk wutar ciki tamuku yawane kawai, amma duka ƙarfe nawane yanzu ɗin? An faɗa muku kowane zai dinga iya uban sakkonku da aiki kamar matching?”.     “Mom bazaki ganeba wlhy. Please ki barta nidai”.    Kafinma Mom ta sake magana Anam tace, “Kibari zansha a can ɗin Mom kinsan masifar wancan mutumin tafi ta Yah Khaleel”. Murmushi kawai Mom din tayi yayinda Khaleel ke hararta.        Sosai Khalel ya zumbuɗa gudu a hanya, lokacin da suka isa wajen aikin nata har bakwai da rabi ta kusa gotawa. Sai dai sauƙinsa ma babu nisa mai yawa da company ɗinsu dan duk titi ɗaya ne. Baki ta taɓe ganin yanda duk Khalel yabi ya damu kansa tunda suka taho yake mata masifa a mota wai idan tace lalaci zatai to zata dinga hawo motar kasuwa kuwa shi dai baza'a dinga sashi ya jirata ba. Ita dai komai batace ba sai faman ɓata fuska dai takeyi tana cin inibi ɗinta data taho da shi daga gida da buga game a waya har suka iso.       “Kije idan an fita break zan kawo miki abinci”.      Sosai ta waro idanu waje. “Har ƙarfe nawa kenan Yah Khaleel?”.        Harararta yay yana ƙoƙarin jan murfin data riƙe zai rufe. “Lokacin zuhur mana”.     “Haba Yah Khaleel one fa kenan? Kaga ƙilama yunwa ya halakani kawai”.     Dariya ta bashi amma sai baiyiba. “Naji zan roƙa Ya Shareff idan an tashi meeting zanyi squeezing time na kawo miki”. Kafia tace komai yaja motarsa yay gaba. Tabi motar da kallo tana tura baki gaba.          Kamarko yanda yay alƙawarin ya cika. Dan wajen sha ɗaya aka kawo mata saƙo. Koda ta buɗe sai taci karo da takeaway na abincin da take tsananin so. Daɗin da taji ya sata tura masa text message na godiya, dan hakan tamkar tarbiyyar su Mamie ne a gareta, indai an mata alkairi komin ƙanƙantarsa sai tayi godiya harma da addu'a.         Saƙonta ya shigo wayar Khaleel ne a dai-dai sanda wayar ke a hanun Shareff. Yazo nuna masa hoton wani zane da aka turo masa daga lagos sai kira ya shigo masa a ɗaya wayarsa, bazai iya ɗaukar wayar a gaban Shareff ba shine ya fita. Baiyi niyyar buɗe saƙonba, amma ganin sunan daya turo saƙon ya sashi buɗewa. Shiru yay na wasu sakkani yana kallon saƙon tamkar mai bitar karatunsa, sai faman cizar lip yake, sallamar Khaleel ta sashi danne saƙon ya aunashi a delete gaba ɗaya. Wayar ya miƙama Khaleel batare daya kallesa ba. “Kaje da shi zamuyi magana daga baya kawai”.         Ɗan jimm Khaleel yay yana kallonsa, dan sanin maganar tasu muhimmiyace, hasalima shine ya damesa da kira tun ɗazun akan yazo duk da yasan suna meeting ne. Amma kuma sai bai kawo komai a ransaba yace, “Okay Yaya. To koma dai na tura maka shi kawai saika sake nazari kafin?”.          “Okay yayi”. Ya faɗa a taƙaice kawai. Kasancewar shima Khaleel ɗin miskilin kansa ne sai bai sake tofa komaiba ya miƙe ya fita abinsa. Haka kawai ya samu kansa da binsa da harara harya fice. Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan. Ya sake jan tsaki ya miƙe gaba ɗaya yabar table ɗin. Can jikin ƙaton window da aka ƙawata office ɗin da shi wanda ake hango har titi da cikin compound ɗin company ɗin kasancewar a saman upstairs office ɗinsa yake yaje ya tsaya. Ya jima wajen a tsaye hannayensa duka a aljihu yana kallon kaikawon mutane daga titi zuwa cikin company ɗin...        Da lokacin tashi yay addu'a tai tayi ALLAH yasa Khaleel zai dawo ɗaukarta, har kiransa tayi dan taji sai dai bata samesaba network ya hana. Tun shigowar motarsa wajen tasan addu'arta bataci ba. Ɗan duban Yaseer abokin aikinta kuma shima ɗan hidimar ƙasa ne dake gefenta tai a sanyaye. Ya sakar mata murmushi dabinta da ƙyaƙyawan kallon da yake hanata sakewa da shi. “Ga Yayana yazo bye”.      Manyan idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta. Shima ya miƙe har lokacin idonsa a kanta. “Haba dai Friend haka ake Friendship ɗin anama juna rowan dangi? Kamata yay kice muje na gaida Yayanmu ai ko? Kullum sai dai naga yazo ɗaukarki baki taɓa gayyata ta na gaisar da shi ba”.       Murmushi kawai tai batare da tace komaiba. Ganin tayi gaba yay saurin bin bayanta har sai da tafiyarsu ta dai-daita. Kasancewar tinted glass ne yasa Yaseer knocking duk da sarai yasan wanda yake ciki ya gansu. Shiru babu alamar za'a sauke ya ƙara knocking fuskarsa faɗaɗe da murmushi. Zai ƙara na uku Anam ta girgiza masa kai a hankali, dama abinda ta gudar masa kenan shiyyasa taso hanashi tun farko. Tana ƙoƙarin buɗe baki ta bashi haƙuri aka sauke glass ɗin a hankali.           Kallon daya watsa mata ya sata kauda kanta tana taɓe baki, Ƙara ɗaure fuska yay da duban Yaseer daketa faman shafar ƙeya yana murmushi.... Kafinma yace wani abu Yaseer ɗin yay saurin faɗin, “Good afternoon Yayanmu”.        Kamar bazai amsaba sai kuma ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha, babu musu shima Yaseer ɗin ya basa suka gaisa, a mamakin Anam harda cema Yaseer ɗin, “Yaya aiki?”. Yaseer ya amsa fuskarsa na sake washewa ga sinne kai yana famanyi kamar wanda ke agaban surukai. Anam ta ɗan taɓe baki tana jinjina kanta, a ranta kuwa gulmarsa take. Tana son ɗagama Yaseer dake ɗago mata hannu nata hanun tanajin shakka, sai da taɗan faki idonsa ta ɗaga sau ɗaya ta fuske. Sai dai batasan yama rigada ya gantaba. Bai daiyi maganaba ya tada motar suka wuce.        Shiru babu wanda ke magana tsakanin shi da ita sai redion motar daketa karaɗi, ganin inda suka shiga saɓanin gida daya kamata su nufa ya sata kallonsa a sace tana muy-muy da baki alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa. Sai da ta karanta symbol ɗin wajen ta gane Saloon sukazo, mamaki ya sata dubansa dan batasan mi sukazo yi wajen ba. Ido suka haɗa yana ƙoƙarin kai waya kunensa tai saurin ɗauke nata. Shima janye nasa yay da cire wayar daga kunensa hango Fadwa na fitowa a wajen tamkar tarwaɗa. Tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfa, sai veil siriri data yafa iya kanta ta naɗesa a kafaɗa, ga wani uban glasess daya cinye rabin fuskarta sai dai ya mata matuƙar ƙyau kasancewarta fara ƙyaƙyƙyawa. Gefe da gefenta ƴammata biyune suma ƙyawawa kamarta farare tas da su. Yanda suke dariya zai tabbatar maka wata maganar sukeyi dan har ita Fadwan fuskarta cike take da murmushi. A hankali Anam taja siririn tsaki daya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai dai ta wani kauda kai gefe kamar wadda taga kashi. Sarai ya fahimci dasu Fadwa take, amma sai baice komaiba ya buɗe murfin motar ya fita fuskarsa sam babu walwala dan ya tsani taron ƙawayen Fadwa da suka zame mata kamar jela. Idan ka ganta da wannan yau gobe da waccan zaka ganta, na jibima daban ne...........✍ *_Haɗuwar iliya da wargaji😂 kunsan dai ba sauƙi😹😹, ku faɗama yarinyar nan taku yau sai mun rama marinmu ko shi Yayan nata bai isa dakatar damu ba ehe😜🤭._* _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*. *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_09_* .........Murmushi Fadwa ta sakar masa, cikin narke murya taima hannunta kiss da hura masa .       “I miss you my Soulmate”.    Kansa kawai ya jinjina da wani ɗan guntun murmushinsa iya laɓɓa. Cikin iyayi da feleƙe ƙawayen nata ke gaishesa idanunsu kamar zasu faɗo a kallonsa. Ɗan tsuke fuska yay yana amsa musu sama-sama.         “Baby am sorry na saka wahala”. Fadwa ta sake faɗa tana sake narke masa har tana saka tsigar jikinsa tashi. Nanma murmushi kawai yay mata da kauda kansa daga gareta dan shi kaɗai yasan halin da dama yake ciki ita kuma tana son sake kunnashi da wani. Cikin motar yay ƙoƙarin komawa da nufin ɗakko mata saƙonta, ita kuma batare da tunanin tare yake da kowaba ta nufi ɗayan side ɗin a zatonta anan ya ajiye saƙon nata ne, tana kuma son ƙara birge ƙawayenta da akaikaice tasa ake musu hoto acan gefe batare daya sani ba....         Sosai Anam ta cika tayi fam da takaici, tayi yunƙurin buɗe motar ta fita taji ya sakata a lock dan yasan dama abinda zata iyayi kenan tace zata fita kamar wancan ranar. Ya ɗakko ledar dake a back sit ɗin Fadwa ta buɗe ita kuma. Ido huɗu sukai da Anam, ta watsa mata wani kallon banza ta ɗauke kai dajan siririn tsaki da faɗin “Ballagaza” a hankali....         A yau kam tayi laƙawarin bazata ƙyale ƴar iskar yarinyar nan ba. Cikin jin ɗacin (ballagaza) data kirata dashi tace, “Kin yima ubanki dan uwarki.”     Duk da Anam bajin hausa take da ƙyau ba tasan zagi, amma sai tayi kamarma bataji Fadwa ɗin ba, taciro Bluetooth daga bag ɗinta ta fara ƙoƙarin maƙalawa a kunne Fadwa ta buge hanun Bluetooth ɗin ya faɗi ƙasa. Ƙafa tasa ta takesa da shegen takalminta mai tsananin tsini......        “Fadwa!”.     Shareff ya faɗa a ɗan kausashe..... “......Amma dai Soulmate kanajin tsakin da taimin ai, ranar na ƙyaleta daboda darajarka, amma yau gaskiya bazan iyaba, ban son raini..!”     Itama ta faɗa da sauri cikin tarar numfashinsa.           Anam data sake cika tai fam tai yunƙurin hanɓarata baya ta futa. (Yo dama a gayama kura gayyar cin nama bayan bidirin nasu ne🤣. Ba'a takali Anam ba ma yaya aka ƙare balle anzo har gida da goron gayyata😂).       “Idan kika fita a motarnan sai ranki ya ɓaci!!”. Yay maganar a tsawace da fisgota ya maida ya zaunar. Kuka ta fashe masa da shi dan zuciyarta tazo wuya. Baibi takantaba yay yunƙurin fita a motar sai ya hango Fadwa can ta nufi motarta a fusace ƙawayenta na take mata baya. Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma ya furzar da huci mai zafi yaja murfin a fusace ya rufe, na side ɗinta ma shine ya rufosa ya tada motar suka bar wajen dan tuni su Fadwa ma sun fice a wajen har tana bulama mutane ƙura.          Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi yaja birki da ƙarfi, firgita tai ta ɗago da sauri tana kallonsa. Harara ya watsa mata tare da gangarawa gefen titi ya kashe motar. “Nidai ka kaini gida, kuma saina sanarma Daddy mata na maka kiss a titi da rungumek....”      Bamm ya bige bakin nata, kukan ƙarya ta sake fashe masa da shi dan ko hawaye babu yanzu sai dai taji zafi sosai. “Har Abba ma saina faɗawa da Abie da Mamie da Mom da aunty Amarya”. Ta sake faɗa da ɓalle murfin motar zata fice. Riƙota yay ya maida murfin ya rufe yasa lock. Takaicinsa da haushin abinda Fadwa ta masa yasa takejin zafinsa batare data san dalili ba, cizo tai ƙoƙarin kaima hanunsa dake riƙe da nata....        “What!! Ni zaki ciza?”.    Bata kulashi ba ta sake kaima hanun cizo. Babu shiri tilas ya saketa, yana mai girgiza kansa. A hankali yakai kwance jikin kujera bayan ya kwantar da ita, hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa ya lumshe idanu yana mata kallon ƙasan ido. Tunba yanzuba yasan Anam fitinanniya ce dama, sai dai yayi zaton tabar tsiwa zuwa yanzu, amma tun tana ƴar ƙaramarta boss ce daman. Yasha zuwa hutu ya samu an kawo ƙarar Anam daga school ta naɗi ƴaƴan mutane babu dalili, idan kuma gidansu akazo nanma ta jibga, idan gidansu taje yaran ba tsira sukeba. Ƴaƴan aunty Mimi ba ƙaranar wahalar Anam sukaci ba duk da wasu sun girmeta bata ɗaga musu ƙafa........        “Nidai ka buɗemin, bazan sake shiga wannan motar ba da akeyin wannan abun....”       Duk yanda yaso danne murmushin dake son fita ya gaza hakan, gefe ya maida kansa yay murmushin kafin ya tashi zaune sosai fuska a haɗe ya riƙo hanunta dake jikin handle ɗin ƙofar, baki ta buɗe zata saƙi ƙara dan matse hanun yayi yasa yatsunsa biyu ya riƙe lips ɗin nata fuskarsa a tsananin haɗe. Sosai idanunta suka sake firfitowa, ga tsoro ga tsiwa......        “Haɗiyemin wannan kukan, ki kuma faɗi miye abunda akeyin kona tattakaki”.     Tsaf ta haɗiye kukan zuciyarta na bugawa da sauri dan kusancinsu yayi matuƙar yawa, kanta ta fara jujjuya masa a hankali. Idanu ya zare mata da sakin lips ɗin nata, “Ai saikin faɗa mara kunya”. A tsorace take amma bakin yaƙi mutuwa. Taja jikinta baya da maƙurewa a jikin ƙofa, “To ka bari muje gaban su Daddy ɗin basai na faɗa ɗin ba....”      Bakin ya sake kaima ɗalli tai saurin duƙewa da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Ƙwafa yay da komawa jikin kujerar ya lafe yana kallon waje,  kusan mintuna huɗu suna a haka ring ɗin wayarsa ya katse shirun nasu. Iska ya ɗan furzar da kallon wayar, ganin Daddy ya sashi ɗagawa yakai kunne a ladabce yay sallama.        “Shareff kuna ina?”.   Ɗan jimm yay saboda jin muryar Daddyn, sai kuma ya gyara zama da ƙoƙarin yima motar key yana bashi amsa. “Daddy gamu a hanyar tahowa gida”.  “To inna jiranku”. Kafin ya sake cewa wani abu ƙitt an yanke wayar. Shiru yay yana kallon wayar sai kuma ya sake furzar da numfashi. Ruwa ya ɗauka a baya ya miƙama Anam da itama ta ɗago tun ɗaga wayarsa. “Malama anshi ki wanke wannan banzan hawayen”. Baki taɗan tura gaba kafin ta amsa, ta buɗe murfin motar batare data fita gaba ɗaya ba ta wanke fuskar. Bag ɗinta dake kan cinyarta ya ɗauka ya buɗe, zatai magana ya harareta. Komai babu na kayan kwalliya da ƴammata kan ɗan fita da shi a bag sai lipsgloss kawai. Baice komai ba ya maida jakar ya rufe, tissue ya ɗiba guda uku ya miƙa mata sannan ya harba motar saman titi.       Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu gida, tunda aka buɗe musu gate ya sake tabbatar da babu lafiya, dan ganin masu baƙaƙen kayan nan yasan Aunty Halima ce a gidan. A karon farko yaji zafin hakan matuƙa, shikenan da abu ya faru tsakaninsa da Fadwa sai iyaye sun shiga ciki, to shikam idan anyi auren yaya kenan kuma?. Ita dai Anam ba fahimtar komai tai ba, dan tun kan ma ya gama kashe motar tai ficewarta sashen Mom a zatonta ma ko baƙi Abba ko Daddy wani yayi. Binta yay da kallo harta shige, ya sauke numfashi a hankali shima yana fitowa. Sashen Daddy ya nufa duk da yasan bai wuce ɓacin rai zai tarar ba.       Tun kafin ya ƙaraso yake jin hargowar Gwaggo Halima daketa masifa, ya girgiza kansa kawai ya shiga falon da sallama. Da Fadwa dake faman rusar kuka suka haɗa ido, ya ɗauke idanunsa fuskarsa na sake tsukewa. Sosai Mommy ke antaya masa uwar harara, hakama Gwaggo. Daddy dai kallonsa kawai yakeyi cike da nazari. Shiko Abba murmushine ma akan fuskarsa yana sauraren ƴar uwar tasu kuma yayarsa. Ƙasa ya zauna ya shiga gaishesu. Abba ne kawai ya amsa da daɗin rai, sai Daddy daya sauke ajiyar zuciya. Mommy kam da Gwaggo hayayyaƙo masa sukai da masifa kamar yanda Gwaggo Halimar ta rufesa da tata. Shi dai babu wanda yacema uffan a cikinsu, kansa a ƙasa ma yake. Sai da sukai mai isarsu sukai shiru duk da Abbah nata son dakatar da su sunƙi saurarensa.         “Ina ita mara kunyar dan ubanta? Kai yanzu Shareff ko kishinmu ma bakayi duk yawan ƴan uwanka da muka haifa karasa wadda zakai yawo da ita a motarka sai bare.....”         Haka kawai maganar ta bashi dariya, amma sai baiyiba yay murmushi kawai da ɗagowa ya ɗan dubi Gwaggon tasa datai maganar.     “Eh kalleni da ƙyau mara mutunci, ko kanada wata alaƙa da ita bayan ubanta dake matsayin ɗan uba a cikinmu da har kake wulaƙantamin yarinya akanta?”.           “Dan ALLAH ya isa haka Halima, maganar yarinya ko matsayinta duk bashi bane ya taramu anan. Kai Shareff miya haɗaka da ƴar uwarka?”.     Numfashi ya sauke a hankali da ɗagowa ya dubi Abbah da yay maganar ya sake sunkuyar da kansa. “Abbah ni bansan wani abu ya faruba. Ina office ta kirani tana buƙatar abu, duk da ina buƙatar zuwa na huta kuma tana ƙasa dani na ɗauka nakai mata har inda take badan ina jin tsoronta ba.......”      “Amma daka tashi zuwa ai da wancan bakwainin yarinyar kazo. Dama ranar da ita kaje gidanmu taimin rashin kunya da marina ka hana na ɗauki mataki kace zaka ɗauka da kanka, yau kuma harda zagina tayi tanamun kallon banza irin like akwai wani abu tsakaninku. Ni gara idan sonta kake ka faɗamin na barmata kai kawai dan bazan iya shearing ɗinka da wancan jakar ba....”        Idanunsa yay bala'in rumtsewa tare da dunƙule hanunsa da masifar ƙarfi. Daddy dake kallon hanun nasa ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, sai dai kamar yanda tun ɗazun baice komaiba yanzunma baice ba. Fadwa ta cigaba da sakin zance tana kuka har sai da Abbah ya ƙwaɓeta dan sai zagin Abie take da Anam....       “You're vary stupid. Baki san shi ɗin wanene ba a gareki? Ashe muma zaki iya zaginmu mara kunyar banza......”      A zabure gwaggo ta tare numfashinsa da faɗin, “Yo Abubakar wane matsayi Usman kedashi a wajenku bayan ɗan uba da zaka balbaleta danta zagesa?”.         “Haba Gwaggo wane irin magana ne wannan?”. Abba ya katseta ransa a ɓace. Gwaggo Halima zatai magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Bana sonji, daga yau kuma idan na sakeji a cikin ƴaƴanki wani ya zagi Usman to lallai ke kanki sai ranki ya ɓaci tunda akoda yaushe ke hankali baya isa miki cikin jiki. Wannan magana kuma na kasheta anan, sannan Mamana nine nace kullum Al-Mustapha ya sauketa a wajeb aikinta ya kuma ɗakkota tunda shine babba wataran sunan uba zai amsa a garesu. Bana son sake jin ƙananun maganganun nan daga yau, nakuma dawo da bikinsu baya zanje na samu Alhaji Sadiq ɗin, magana ya ƙare ok”.        Babu wanda ya iya sake cewa komai, sai dai har cikin rai maganarsa ta farko ta zafi wasu a cikinsu, ta ƙarshe kuma ta musu daɗi kusan su duka idan ka cire uban gayya daya shaƙa yay fam. A wannan gaɓar yaji mugun haushin Gwaggo a ransa fiye da koyaushe, dan ya gama gane itace ke assasa tsanar juna a tsakanin iyayensu da ƴan uwansu guda biyu kacal dan kawai suna matsayin ba uwarsu ɗaya ba. Shi ya fara ficewa a falon batare da ko kallon wani ya sakeyi ba.      Da sauri Fadwa ta mike tabi bayansa har tanayin tuntuɓe zata faɗi. Tana kiransa ko waugota baiyiba duk da sarai yajita. Duk da taji zafi haka ta cigaba da binsa har part ɗinsu, yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tai azamar shan gabansa ta tare ƙofar. Mugun kallo ya watsa mata, sosai hanjin cikinta suka kaɗa amma saita daure ta marairaice masa fuska.       “Haba My Soulmate yanzu ɗinma wulaƙancin zakamin?”.           “Bani hanya!!”.     Yanda yay maganar a tsawace idanunsa har suna firfitowa yasata saurin matsawa. Hannu yasa ya ƙarasa ingijeta ya buɗe ɗakinsa ya shige tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ta sake zabura....      Acan falo kuwa Daddy ne yay amfani da damar fitar su Shareff ya shiga yimusu nasiha musamman Gwaggo da Gwaggo Halima da Mommy da duk matsalar take daga garesu. Duk da a cikin lalama da son bada shawara yay maganar sai Gwaggo ta fashe da kuka tana matsar ido da fyatar majina wai ta fahimci laifinta suke gani dan bata haifesuba. “Shikenan Muhammadu nadai fahimci laifina kake gani, nidai ALLAH na gani ba inayi bane dan na rabaku da su kamar yanda kuke kallo sai dan kare martabarku da takaicin da uwarsu ta shaƙa mana a gidannan wajen mahaifinku. Babu annamimanci da kutungula da Zuwairah bataiba agaremu, akwai randa har sakinmu tasa mahaifinku yay a daren duk da ana ruwa yace mubar masa gidansa. Akwai randa ta ɗau hanun Halima ta turɓuɗa cikin murhu wuta naci wai dan ta zungurar mata icce. Kai har kusan jefa mahaifiyarku tai a rijiya lokacin tana goye da Umaru. Taya azzalumar mace irin wannan zanso ƴaƴanta kuma na baku goyon bayan kusota duk da abinda taima ƴar uwata. Ai shara'armu da Zuwairah sai dai a lahira, gashinan makirar jikarta ta gadota a komai na makirci. Dan haka bazaku taɓa samun nutsuwaba a gidannan tunda annamimiya tazo jinin munafukai.....” Fyaaaatttt. Ta face majina da ƙarfi da nufar hanyar ƙofa ta fita.      Mommy ma tashi tai a fusace tabi bayan Gwaggon tata. Cikin ɓacin Rai Gwaggo Halima ta dubi su Daddy. “Yaya kaji ko, duk da abinda uwarsa taima tamu uwar amma kuke nuna sonsa kamar.....”       “Halima!!”. Daddy yay saurin dakatar da ita shima ransa a bace. “Amma Yaya itafa gaskiya ɗayace daga ƙinta sai ɓata. Wlhy wlhy kaji na rantse bazan taɓa son su Usman ba a gidannan. Har duniya ta tashi sunansu ƴan ubane a gareni, bawai ƴan uwa ba”. Fuuu ta figi jakarta ta fice. Duk da kallo suka bita. Abbah ya fara sauke ajiyar zuciya da maido kallonsa ga Daddy da ransa ke matuƙar ƙuna. Ya rasa mizai fassara Gwaggo da shi. Tun basu san kansu ba take ƙulla raba kansu, ALLAH gafurun kuma rahimun ya ganar dasu gaskiya hakan taƙi yuwuwa, amma bata barsun ba har saida haƙanta ya cimma ruwa. Sukazo babu dalili suka tsani ƴan uwansu da basu taɓa masu komaiba su da mahaifiyarsu sai alkairi, ALLAH ya ƙara taimakonsu suka gane suka canja. Gashi yanzu tana son saka ƙiyayya kuma a tsakanin ƴaƴansu, wace irin fitinace wannan, kenan itama data haihu a gidan basu isa su jitu da nata ƴaƴanba......”            Taɓashin da Abba yayne ya maidosa hankalinsa. Ya sauke numfashi a hankali da ɗago idanunsa irin na Shareff da sukai jajur yana kallon ɗan uwan nasa. Cikin ɗacin murya yace, “Abubakar itace silar komai. Duk wata ƙiyayya tsakanin Umma da Mama itace taita haɗata. Bata barsu sun zauna lafiya ba muma ta hanamu gashi zata hana ƴaƴanmu ma. Yanzu ƴar ɗaya tilo da ALLAH ya bama Usman ma bazata barta tasha iskar farin ciki a cikin namu ƴaƴan ba. Kana ganin Maryamu ta daina zuwa da ƴaƴanta ƙasar nan saboda Gwaggo. Haka kuma zamu cigaba da zuba idanu kenan Abubakar?!”.       “Bazai yuwu ba yaya. Dolene a wannan karon mu ɗauki mataki. Yaya Halima tafi kowa bani haushi. Sam ta kasa fahimtar halin Gwaggo tamkar ita ɗin ba mace bace ba. A zatona da ake cewa mata sunfi kowa zuminci ita ya kamata ta fara farga da son ganin mun dunƙule abu ɗaya amma da ita ake makamin rusamu. Bazan ɓoye makaba ina tausayin Shareff akan wannan auren. Bazasu barsa ya zauna lafiyaba dan itama yarinyar nan da kake gani shaiɗaniyar kantace Yaya”.      Sosai zuciyar Daddy ke ƙara tafasa dan yasan duk gaskiya ɗan uwan nasa ya faɗa. Shi kansa yana tausayama Shareff dan yana cikin kwatankwacin irin halin da suke neman jefasane akan mommy. Tunda ya aureta Gwaggo ta hanasu su zauna lafiya saboda kawai tana taƙama ɗiyar ƴar uwartace......     ★★ Tunda ya shiga ɗakin bai sake fitowaba. Kwance kawai yake a gado ko takalmi bai cireba balle maganar wanka har aka kira magrib. Tashi yay ya nufi bayi yayo wankan a gurguje da alwala. Tsabar bai buƙatar haɗuwa da kowa ta baya yabi ya fita massallaci. Bai kuma dawo ba dan koda akai sallar isha'i can ya koma kan wani dakalin maƙwaftansu ya zauna.....               Tunda suka dawo gidan batabi takan kowaba. Tadai shiga ta gaida Mom sannan ta wuce ɗakinsu. Wanka tayi batare data ko shafa mai ba balle saka kaya ta kwanta da towel ɗin jikinta dan wani irin barci ke rinjayar idanunta kasancewar sanyin ruwan wankan dana jiƙar towel ɗin na ratsata. Barci sosai mai nauyi ya kwasheta, acikin barcin taji kamar abu na binta. A ɗan zabure ta farka ta hau dube-dube. Ganin jini ya sakata zaro idanu da dafe goshi. Shaf ta manta da batun zuwansa duk da sai jibi ya kamata ta gansa ma. Gadon ta ɗan dudduba, ganin bai ɓaciba ta nufi toilet da sauri, towel ɗin dai ya ɓaci kasancewarsa sky blue ya nuna sosai. Tasan yana mata zuba sosai shiyyasa bata wasa, gashi tanata son siyen audiga dama amma shiririta tasata mantawa dan ta saba sai da taga Mamie ta ajiye mata da lokacin yinsa yayi gareta. A gurguje ta gyara jikinta ta fito, baƙar abaya kawai tasa ta ɗauka atm ɗinta tayo waje. Ɗakin Mom ta leƙa ta samu tana salla, bazata iya jiraba dan akwai matsala zai iya sake ɓatata. Yanzunma handkerchief ɗinta sabo tai amfani da shi kafin. A falo ma duk sauran yaran sun fita massalaci kasancewar duk yaran Mom mazane aunty Rahma ce kawai mace, Husna ɗiyar ƙanwartace take riƙo bayan auren Rahama.         Su Daddy sun riga har sun shigo ciki, hakan yasa bata samu matsalar isa gate ɗin ba duk da batasan a ina zata samo audiga ɗin ba, kawai zatai dai tambaya ko gurin mai shagon layinne da sukan siyo ƙananan abubuwa wajensa koza'a samu kokuma ya faɗa mata inda zata samo....        Cak ta tsaya tare da saurin ja da baya saboda karo da sukaci, sosai gabanta ya faɗi, ta zabura da zummar komawa da baya tana kauda kai dan har yanzu haushinsa takeji akan abinda ya faru, Juyawa tai da sauri.....       “Idan kika ƙara stap ɗaya saina karya ƙafafunki”.            “Wayyo Anam kin mutu kawai”. Ta faɗa tana rumtse ido da cije lip ɗinta kamar zata fasa ihu. Sai kuma ta juyo tana wani tamke fuska batare data yarda ta sake kallonsa ba, ita ala dole bata son yaga lagonta..........✍ _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_10_* *_BABU SO....!! AREWABOOKS_* https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718 Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar ZEE ZEE Mai maida tsohuwa yarinya wadda ta shahara wurin hada kaya kamar haka ❤️kamar su Kaza Zabo Zakara Ciccibi Zuciya Tsimin kankana d rake Tsimin tabaje Zumar dabino d kwakwa Zumar gorun tula syrup Garuka masu kama jiki kamar su ❤️ Bita zai zai Dan wata bakwai Madarar mata Bata🤐🤐🤐 Ba kishiya ba Ko mugun mutan d mugun aljani sai sun barki Matsin kinfi budurwa Kalolin gumba dsauransu Address maberar jariri bayan FGC sokoto Phone 08068526455 Instergram Yar Zuru mamar ZEE ZEE kayan mata _________________ .........Ido ya ɗan tsura ma atm ɗin hanunta cike da nazari, kusan mintuna biyu harta ƙosa da tsaiwar sannan yay magana.      “Ina zakije?”.   Yanda yay maganar babu alamar wasa yasata ɗan ɗagowa a marairaice ta dubesa. “Abu zan siyo”.       “Shi abun bashi da suna?”.    Ƙasa tai da kanta tana tura baki batare datace komai ba. “Kin kurumuce ne?”.       Kamar zatai kuka tace, “Sirrine fa Yaya MM, kuma acan shagonne bada nisa bane”.             “Koma ciki”.     “Yaya zanfayi amfani da shine yanzu”.       Ƙoƙarin zagayeta yay zai wuce da faɗin, “Idan kin matsu da koma miye sai ki faɗa kafin ki fitan”.      Ƙafarta ta ɗan buga a ƙasa kamar zatai kuka sai kuma ta nufesa da sauri tasha gabansa. “Yaya Shareff dan ALLAH. Wlhy important ne”.      “Inda important ɗinne da baki tsaya raimin wayo ba. Tashimin a hanya ko nabi ta kanki”.     Matsawa ta ɗanyi ya raɓata zai wuce. Ganin da gaske tafiyar zaiyi tace “Audiga zan sayo”. Cak ya tsaya daga yunƙurin barin wajen, kamar wanda akaima tilas ya juyo yana kallonta. Sai dai ita nata kan a ƙasa sai faman ɓata fuska take dayin muy-muy da baki alamar akwai abinda take son faɗa koma take faɗar a zuciyarta. Harga ALLAH abinda ya fahimta zatai da audigan da ban. Dan haka ya dalla mata harara.        “Duk audigan dake cikin First aid box's ɗin gidannan kirasa audigan amfani sai kin fita saya? Bar nan kona mareki, mu nan ba'a mana fitan dare”. Kukane kawai ya rage bata saki ba. Har tayi niyyar yin zuciya sai kuma ta tuna halin da take ciki da wanda zata iya tsintar kanta kafin anjima kaɗan. “Yaya Please zanyi amfani da shine ALLAH”. Ransane ya ɓaci, ya ƙaraso inda take a fusace kamar zai kai mata mari ta zabura gefe. “Ina miki magana kina faɗamin zakiyi amfani da shine”. Ganin ya ƙaraso kanta ta zabura da gudu sai sashen Mom. Baiyi niyyar binta ba, sai dai kawai zuciyarsa ta kitsa masa ya amshe atm ɗin hanunta shiyyasa yabi bayanta. A falo ya sameta tana kumbure-kumbure Mom da su Salim zagaye da ita ana tanbayarta lafiya? Dan babu wanda yasan tama fita.          “Wai bazakiyi magana bane Anam ana tambayarki kinyi shiru?”.      Shigowarsa ta hanata bama Mom amsa, duk suka maida hankalinsu garesa yaran na gaishesa. Amsawa yay idonsa a kanta. Batare da yayi magana ba ya miƙa mata hanun fuska a tsuke. Ta fahimci mi yake nufi ta bashi dan haka ta zabura zata gudu.      “Kika tashi a wajen nan sai kinyi kukan da baki taɓa yin irinsa ba bani”.      Mom ta kalla idanunta cike da ƙwalla. Mom data kasa fahimtar inda suka dosa tace, “Babana miya faru ne?”.     A taƙaice ya faɗama Mom abinda ya faru. Cikin mamaki Mom ɗin ta kalleta dan tasan dai Anam da tsoron dare, itada da dare yayi ko'a cikin gidan akace taje wani sashin aika saita nema ƴan rakiyya. “Anam”. Mom tai kiran sunanta. Ɗagowa tai ta dubeta sai kuma ta maida kanta ƙasa.      “Ina zakije?”.    A hankali tace, “Audiga zan siyo”. Ɗan jim Mom ɗin tayi na nazari. Sai kuma ta girgiza kanta “Yanzu Anam har sai kin tafi siyen audiga basai ki tambayeni ba, idan ma babu ai za'a bada a sayo miki. Amma ko fitama bansan kinyi ba”.     “Kiyi haƙuri Mom naje naga kina salla”.     Girgiza kai kawai mom tayi, ta maida kallonta ga Shareff, “Ƙyale shashancin wannan Babana, nasan yanda zatai maka bayanin ne yay mata nauyi”.      Janye idanunsa yay daga harar Anam ɗin, komai bai sake cewa ba ya fice. Binsa tai da kallo tana taɓe baki, sai dai shi baima san tanai ba.                      ★★★★★★    Kamar yanda Daddy ya faɗa game da matso da auren Shareff ɗin hakane ta kasance. Dan shirye-shirye aka cigaba da yi babu kama hannun yaro. Dama ankai komai gidan su Fadwa, sai gidansa daya rage a ƙarasama ayyuka wanda dama kamfaninsa keyin ginin shi kuma ya zana kayansa da kansa. Sosai yay busy a tsakanin, Anam ma wataran sai Ya Khaleel take bi ya sauketa ya kuma ɗakkota. Tana dai shan masifa idan ta makara. Ita dai yitake kamarma batasan hidimar da akeba a gidan, ko anko da aka fitar nata cewa tai bataso ita batason kayan zafin nan sai da Mom ta mata faɗa sosai randa zasuje wajen tela sannan ta yarda tabi su Aysha tanata kumbure-kumbure.        ★Yau data kasance alhamis daya rage 1week bikin Shareff ƙarfe sha biyu ta baro wajen aiki sakamakon mura da take fama da shi. Dama cikin dauriya ta fita aikin har Khaleel na mata faɗa. Zazzaɓi daya rufeta ya hanata sukuni ga ciwon kai, Yaseer ne ya samu shugabansu yay complain aka bata damar zuwa gida. Karan farko data yarda ta shiga motarsa, dan tayi ƙoƙarin zame masa amma ya ɓata rai. Maimakon ma gida sai ya fara nufar asibiti da ita, taso masa magana ciwon da kanta keyi yasata hakura ta zuba masa ido kawai.     Basu wani samun tangarɗar ganin doctor ɗin ba, kasancewar akwai sanayya tsakaninsa da Yaseer ɗin. Da ɗan mamaki Dr Jamal ke duban Anam ɗin, daga ƙarshe dai ya kasa daurewa ya jeho mata tambaya. “Anam baki ganeniba ko?.”        Ɗagowa tai daga kwanciyar datai akan desk nasa ta ɗan dubesa, sai kuma ta maida kanta ta kwantar tana ɗan girgiza masa kai. Shiru yay yana kallonta na wasu daƙiƙu kafin ya cigaba da rubuta musu maganain ya bama Yaseer da tun tambayar da yayma Anam ɗin ya shiga tunani. “Babu wani damuwa Yaseer murane kawai kuje a sai waɗannan drugs ɗin tasha insha ALLAH fiver da headache ɗin zai sauka”.    Godiya Yaseer yay masa da basa hannu sukai musabaha. Ya bisu da kallo lokacin da suke fita kansa a matuƙar ɗaure. Jiyay bazai iya haƙuriba ya ɗauka wayarsa domin lalubo abokinsa dan tabbatarwa. A kiran farko dai ba'a ɗaga ba, duk da yasan daliline ya hana hakan sai ya kasa daurewa ya sake kira....       “Ai harna fara tunanin bazaka ɗaukaba nai tracing naka ninazo inda kake”.       Daga can aka amsa da “Saikace wani ɓarawo”.     Dariya Dr Jamal yay dakai hannu ya shafi gemunsa. “My Man ai baka da maraba da ɓarawon da ake nema ruwa a jallo yau a wajena. Dan nasan bazan iya haƙuriba”.         “Ai dama koda yaushe kai ba haƙurinne da kai ba. Miya faru?”.      “Muje a hakan bani da haƙurin. Wai dama mutuniyar ta shigo Nigeria amma ko labari?”.             “Malam jeka kai tsaye kan maganarka waye mituniyar? Dan na kula kai baka gajiya da kwashe-kwashe”.     “Oh ALLAH shaidar da kai min kenan? To Anam nake nufi. Dan yanzu suka bar wajena ita da wani yaro Yaseer ya kawota a dubata”.           Ɗiff yayi kamar wanda ruwa ya cinye har Dr Jamal na tunanin kota yankene, wayar ya cire a kunnensa ya kalla, ganin yana online ɗin dai ya shiga faɗin “Hello! hello! Bakajina ne?”.      Ɗin! Ɗinn! kiran ya yanke, bai wani kawo komai a ransa ba ya ajiye wayar da tabbacin bayaji ɗinne, shawarar daya yanke a zuciyarsa na anjima zaije har gida kawai ya sashi ƙin sake kira.            ★★         “To Alhmdllhi, indai banyi kuskure ba nan shine gidan”. Yaseer ya faɗa yana duban Anam da tunda suka baro asibiti ta kwantar da kanta jikin sit ta lumshe ido. Shiru bata motsa ba, yaɗan leƙa fuskarta yana murmushi da ɗan bubbuga gefen kujerar. Idanun ta buɗe a hankali ta kallesa. Kamar yanda yake mata murmushi itama saita ɗan sakar masa mai kama da yaƙe....       “Nan ne ko?”. Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa da narke mata idanusa. Janye nata tai daga garesa a ɗan daburce ta kalli gate ɗin. “Nan ne, na gode sosai ALLAH ya bada ladan zuminci”. Murmushi ya mata kawai ya buɗe ya fita. Side ɗinta ya zagayo itama ya buɗe mata. “Thanks”. Ta faɗa a hankali da ziro ƙafarta ƙasa zata fito idonta ya sauka akan Shareff da shima fitowarsa kenan daga gida hanunsa riƙe da key ɗin motarsa dake anan waje fake, ita sam bama ta lura da motar ba sai yanzu daya danna key tai ƙara. Ganin yanda ya kafeta da idanunsa ya sata yin ƙasa da nata ta ƙarasa fitowa gabanta na faɗuwa. Ɗan baya tai kamar zata faɗi saboda jiri Yaseer yay azamar kai hannu zai riƙota, dafe motar tai da sauri ta tsaya da ƙafafunta. “Ayya sorry Friend”. Yaseer ya faɗa a hankali yana janye hanunsa da bai kai ga taɓata ba.      Ɗan satar kallon inda Shareff yake tai, yanzun kam zaune yake cikin motar sai dai ƙafafunsa a waje yana danna waya tamkar bai san da wanzuwarsu a wajen ba.....      “Wancan ba Yaya bane?”. Yaseer ya katseta yana fuskantar inda Shareff yake. Kanta kawai ta jinjina masa. “A to bara naje mu gaisa ko?”. Nanma batace komai ba, ganin ya nufi inda Shareff ɗin yake ita kuma gashi kwanciya kawai take buƙata, ga hararar daya mata sai kawai tai shigewarta gida...          Shiru gidan babu gittawar kowa. Ta nufi sashen Mom da tunanin ko barci suke. Nan ɗinma shiru har ɗakin Mom ta leƙa bata samu kowaba, kitchen ta nufa inda take ɗan jin motsi. Iyami kawai ce tana ƙoƙarin ɗaura girkin rana. Gaisawa sukai kafin ta tambayi su Mom da hausarta da Iyami bawani fahimta take da ƙyau ba. Iyami ta bata amsa da cewar dukansu sun fita harsu Gwaggo amma batasan ina suka tafi ba. Fitowa tai ta shige ɗaki ta kwanta, ko mintuna biyu bata cika ba aka buɗe ƙofar, a tunaninta Iyami ce, sai dai kuma ƙamshin turaren da taji ya sata buɗe idanunta da sauri...        Ido suka haɗa tai saurin janye nata ta maida ta rufe.    “Tashi”.   Sake buɗe idanun tai kamar zatai kuka, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasata kasa musa masa ta tashi zaunen. Hanyar ƙofa ya nuna mata. Saita waro idanunta da suka canja launi na mura ga ƙwalla a cikinsu.     “Banda lafiya fa Yaya. Ina zanje?”.    Ganin ya nufota ta miƙe da sauri hawaye na sakko mata saman kumatu. A falo ta kusa faɗuwa saboda jirin dake ɗibarta, a bazata taji tattausan hanunsa cikin nata. Gaba ɗayansu sai da tsigar jikinsu ta tashi, sai dai babu wanda yay yunƙurin cirewa musamman ita dake buƙatar taimako dama. A haka suka fito har waje, ya taimaka mata da kansa ta shiga mota sannan ya zagaya nasa mazaunin, tana sonyin magana tana jin shakka dan haka tai shiru, saima ta kwanta abinta jikin sit ta lumshe idanu..        Wani clinic ya kaita dan a dubata. Data sanar masa sunfaje asibiti wata muguwar harara daya wulla mata bata sake magana ba. Doctor ya rubuta musu magani fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsu da faɗin, “To amarya ALLAH ya ƙara afuwa kafin biki”.      Idanu taɗan waro da kallon Shareff da shima kallonta yake, zatai magana ya harareta yana miƙama doctor hannu. “Thanks you doctor”.      “No babu damuwa ango ALLAH ya ƙara lafiya sai ranar ɗaurin aure kuma”.       Shareff ya saki murmushi yana jinjina masa kai. Yanzu kam bama ta jira sun jera ba tai gaba da sauri, koda ya fito harta buɗe mota ta shiga abinta. Sai da suka baro anguwar gaba ɗaya ya tsaya a wani babban pharmacy ya sayi magungunan da aka rubuta, ya kuma shiga gidan abincin dake gefen pharmacy ɗin yay mata takeaway. Duk batasan hidimar da yake ba saboda tunda suka baro asibitin barci ya ɗauketa, dan haka batasan inda suka dosa ba har sai da suka iso. Gefen kujerar yaɗan bubbuga, a hankali ta buɗe idanunta, ganin har ya fita ta yunƙura ta tashi, fitowa tai tana dube-duben inda suke “Yaya MM ina ne kuma nan?”. Bai tanka mataba, ya rufe inda ta fita yay gaba abinsa. Ƙara bin gidan tai da kallo, dagani dai sabone dan duk ma ga botikan fenti nan a tsakar gidan da kayan aiki, gabanta ya shiga faɗuwa, cikin zuciyarta take tambayar kanta (ina kuma ya kawota nan?).....        “Idan kika bari na dawo nan ALLAH sai kinyi kuka”.      Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafa ta nufi inda yake, koda ya buɗe ƙofar da key matsa mata yay ta fara shiga, ƙamshin sabon fenti dana sabbin furnitures ya daki hancinta. Sosai falon yay mata matuƙar ƙyau, danma ciwon kai ya hanata damar kallon komai da ƙyau. Ganin tana neman kaiwa kwance ya dakatar da ita. “No tashi kici abinci kisha magani first”.        “Yaya banajin yunwa kadai ban maganin kawai”.      “Dole kici abinci, kin taɓa ganin ansha magani ba'aci abinci ba”. Yanda yay maganar babu wasa yasata yin shiru. Ya buɗe mata abincin tare da tura mata gabanta, “Kafin na fito ki tabbatar kinci”. Da kallo kawai ta bisa harya shige ƙofar daya buɗe..... Kusan mintuna goma sai gashi ya fito, ganin ya canja kaya yasa ta kasa haƙuri. “Yaya Shareff ina ne nan?”.       Batare daya kalleta ba yakai zaune cikin kujera da faɗin, “Gidan ƴan shan jini”. Shiru tai, dan tasan baƙar magana ya mata. Ɗagowa yay yaɗan kalli abincin, ganin taci sai baice komaiba yaja ledan magungunan. Da kansa ya ɓalla ya bata, duk ta amsa tasha dan sam bata tsoron allura bare ƙin magani. Ganin zata kwanta a kujerar ya sashi faɗin, “Tashi kije ciki ki kwanta”. Kallonsa tai kamar zatai magana sai kuma ta haɗiye abunta ganin yanda kicin-kicin da fuska. Ya bita da kallo ta ƙasan ido harta shige, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido ya buɗe yana furzar da ɗan huci. Sai kuma ya miƙe ya fita.       Gidan ya shiga zagayawa, dan jiya masu fenti suka ƙarasa na katanga. Bai kuma samu shigowaba sai yanzu. Komai yayi masa yanda yake buƙata, shi kansa ya yaba da gidan duk da shine ya zana abinsa companynsa kuma ya fidda kayan aikin ginashi. Yanzu amarya kawai gida yake buƙata nanda kwanaki bakwai insha ALLAH. Motarsa ya nufa ya ɗauka lap-top ya koma ciki. Haka kawai yake jin nishaɗin zama a cikin gidan yau, saɓanin ƴan kwanakin nan da duk yake jin ransa a dagule, dan kayan sashen nasa ma sai da Mommy ta masa jan ido ya bada damar shirya masa su dan ita da kanta tai order ɗin komai tamkar itace mai aurar da macen ba namiji ba. Komai saida ta haɗa masa. Tunda kuma aka shirya kayan baizo ya zauna kamar haka ba......     Ring da wayarsa tai ya sashi katse aikin da yake famanyi a laptop ɗin ya ɗaga. A tausashe yace, “Mommy barka da rana”. Daga can Mommy ta amsa masa da “Barka dai son kana ina ne?”. Ɗan jimm yayi kafin yace “Mommy kina son ganina ne?”.       “Eh to kusan haka, amma idan zaka iya aika wani gidanka ya kai mana keys ma basai kazo ba. Dan gamu a hanya zamuje dasu gwaggo gidan, sannan Halima tai kirana ma danginmu na wajen baban Fadwa zasuzo da masu Company da zasu shirya kayanta su auna komai, shiyyasa muka yanke shawarar muzo muma ɗin kawai dan babu daɗi dangin uba kawai ko?”.         Tun fara maganar tata zuciyarsa ke faman bugu da sauri, ya ture laptop ɗin cinyar tasa gefe, cikin dauriya da danne halin daya shiga yace, “Okay Mommy! kuna inane yanzu haka?”.        “Ai gamu ma mun shigo street ɗin gidan naka kamar dai in ban mantaba”.      Goshinsa ya dafe yana ambaton “Ya ALLAH a hankali”.          “Mi kace?”.   “No Mommy, canai ALLAH ya kawoku lafiya ai inama gidan nima na shigo ganin aiki daga nan na ɗan huta”.      “Kaji ja'iri, bama ka bari iyayen naka su kaika ganɗoki muje biki”.     Ƴar dariyar yaƙe kawai ya mata da faɗin, “Sai kun iso”.         Da sassarfa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Ya duba Anam dake barci hankalinta kwance harda naɗewa cikin lallausan duvet nashi dako shi bai taɓa lulluɓa da shi ba. Nufarta yay yakai hannu kamar zai tadata sai kuma ya fasa, ya ɗan furzar da huci tare da dafe goshinsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya tabbatar su Mommy suka ganta ya shiga uku, dan baima san kalar ƙurar da zata iya tashi a family ɗin MD Shareff ba yau. Jin horn ya sashi sake ambaton “Ya ALLAH”. Tare da fita a ɗakin domin buɗe musu tunda babu maigadi har yanzu sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu yake saran Fharhan zai kawo shi.....          Tunda ya buɗe musu gate bakin Mommy da Gwaggo ya sake washewa. Suma dai su Mom fuskarsu da murmushin jin daɗin ganin yanda ɗansu ya gina wannan gida dako maƙiyi ya gani zai yaba ko'a zuciyane.       “Kai-kai! Anya kuwa Alhaji ƙarami bazan dawo nan ba irin wannan gida haka?”.     Gwaggo ta faɗa tana riƙe haɓa dabin ko'ina da kallo. Murmushi yay mata da shafa kansa. “Indai bazaki dinga damuna da kwakwazonki ba sai na dawo dake”. Dariya su Mom sukasa, yayinda Gwaggo tai masa daƙuwa. Nanma murmushi yayi kawai. Da kansa yay musu jagora suka shiga ko'ina suna mai yabawa da masa addu'a, bakin Gwaggo da baya iya yin shiru tace, “Toni abinda ban ganeba anan, Alhaji ƙarami yanaga sashe biyu, gidan kamar na zaman mace fiye da ɗaya! Kar dai kacemin kaima halin Kakanka da ubanka zakai tara mata?”.       Ganin duk su Mom sun juyo suna kallonsa, har fuskar Mommy ta sauya ya sashi ɗan hararar Gwaggo ta ƙasan ido. “Kai tsohuwarnan kedai bakinki bai iya shiru, kawai dan mutum yayi wadataccen waje a gidansa sai yazam na aure? Nayine saboda ke in kinzo kwaɗayin jar miya”.         Dariya su Aunty Amarya suka sanya. Mommy ma ta ɗan saki fuska tana murmushi dan tun farkon fara ginin gidan da tazo ta gani ta masa irin wannan maganar ganin sashe biyu da nasa na uku, amma sai yace yayine kawai saboda baƙi. Haka kawai zuciyarta taƙi aminta da shi taita masa bin.....        “To shikenan muje ka kaimu naka sashen muga namai gida”.    Gwaggo ta katse mata tunani. Gabansane ya faɗi, zaiyi magana Gwaggo ta nufi ƙofar sashen da basu shiganba wanda tabbacin nasan ne, itama Mommy saita take mata baya. Hakan yasa dole su Mom ma binsu. Da ƙarfi ya rumtse hanunsa da cije lip ɗinsa. Ganin har Gwaggo ta shige yay saurin bin bayansu shima dan ya tabbata target ɗinta na biyu shine bedroom ɗinsa. Kamar yanda yay hasashen kuwa hakane. Dan ko falo bama tagama nutsuwa ta ganiba ta nufi ƙofar bedroom acewarta da nan zata fara a sashen. Shigowarsa tayi dai-dai da ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar.............✍     *_🙆🏻Yau munga idi wagga tsohuwa babu man kai zata ɓaro aiki. Dangin Anam kuna ruwa, maganin masu bin mazan mutane kenan🚶🏻😂🤭_*       _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_12_* ..........A karon farko ta ɗago ta kallesa da mamaki ganin inda yay parking. Magana take so tayi, sai dai ta kasa. Shi kuma yaƙi cemata komai, sai ma wayarsa daya ɗauka yay ƴan danne-danne yakai kunensa. “Fito”. Kawai ya faɗa ya yanke wayar. Ba'a rufe minti uku ba wata budurwa mai tsananin iyayi ta fito daga shagon saloon ɗin tana tafiya kamar tarwaɗa. Haka kawai abin nata ya bama Anam haushi, taja siririn tsaki da taɓe fuska ta janye idonta. Duk da tayine a hankali sai da yaji, sai dai bai nuna yajinba balle ya tanka, sai ma faman daƙilar waya yake, amma ya buɗe murfin kafarsa ɗaya a waje take.       “Assalamu alaikum Yah Musty barka da zuwa”. Budurwar ta faɗa murya a lanƙwashe lokacin da take isowa wajen. Kansa kawai ya jinjina mata yana janye kunne ɗaya na earpiece dake a kunnensa. Kamarma bata damu da abinda yay matan ba. Murya ta ƙara tausasawa cike da iyayi tace, “To Bismillah muje ko”.        Nan ɗinma bai tankaba, sai da yaja wasu sakanni ma sannan yay yunƙurin fita a motar.     Baƙin ciki, haushi da takaicin ballagazanci na wasu mata ya tokare maƙoshin Anam. Lokaci ɗaya taji tama tsani budurwar.          “Sai an fito da ke ne?”. Ya faɗa cike da gatse idonsa akan Anam. Jitai kamar karta fita ɗin, amma sai yaci darajar Yaya da yake gareta tabi umarninsa. Yanda budurwar batai mata magana ba itama bata nuna tama san da zamanta a wajen ba. Gaba sukai tana binsu a baya, budurwar sai ƙoƙarin dai-daita tafiyarta take da shi tamkar dole, ga baki ta saki sai surutu kai kace hanyar kasuwar wanbai aka buɗe da safe. Sosai wajen Saloon ɗin ya haɗu dan yaɗan birge Anam kaɗan, sai dai bata nuna a fuskaba saima kicin-kicin data sakeyi da fuska duk da gaisuwa da ma'aikatan wajen ke musu na girmamawa daya bata mamaki matuƙa. Wajen zama aka basu, harda ajiye musu abinsha kafin budurwar da taji ma'aikatan sun kira da aunty Deena ta dubesa cike da yauƙi da shauƙi.           “Sir za'a mata kitso ne?”.     Bai jita ba, saboda earpiece dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne ɗaya, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska. “Am sorry, nayi magana ne bakaji ba, nace za'a mata kitsone?”. Idonsa ya ɗauke daga gareta ya maida ga Anam datai kicin-kicin da fuska fiye da yanda suka shigo dan ta fahimci ita ya kawo kenan. “Komai ma daya dace kumata”. Ya faɗa a taƙaice da maida earpiece ɗinsa.         “Ni wlhy bance inaso ba. Kuma kaina a wanke yake, hakama......” Hararta yay yana mai zare kunne ɗaya na earpiece ɗin, tai saurin sake haɗiye maganar tana matso hawaye. Ɗauke idonsa yay kamar baima ganta ba. Tanaji tana gani aka kwance mata kalbar kanta aka saka mata relaxer aka wanke fes. Bayan an rage ruwan da towel akai steaming ɗinsa. Wadda take mata gyaran tambayarta tai tana son kitso ne? Amma tai mata banza. Ganin haka ta juya ga Shareff dake zaune komai anayi gaban idonsa.       “Sir za'a mata kitson ne ko a barta?”.         “Barta kawai a mata lalli”. Yay maganar batare da ya kalleta ba yana maida earpiece ɗin kunensa.        Ana fara wanke mata ƙafa da gyaran farcen hanunta ya miƙe ya fita, Anam ta bisa da harara ƙasa-ƙasa tana tura baki. Cikin ƙunƙunai tace, “Gwarama da zakai aure mu huta da baƙin halinka”.     Murmushi mai mata wankin ƙafa tai saboda jin abinda tace. Lokacin da aka fara zana mata lalle harda ɗaukar video, dan tana son lalli sosai kitsone dai kam saida dambe da Mamie tsaye kanta, dan ko Mamie ce tace zata mata ba yarda take ba da arziƙi. Abie kam lallaɓata yake ko yace a barta sai wani lokaci tunda bata so.        Sosai ta fito ras tai ƙyau tamkar wata sabuwar amarya. Sai faman kallon kanta take a manyan mirrors na wajen tana murmushi da ɗaukar hoto kamar ba'itace ta gama rikiciba yanzun. Sai da tai mai isarta sannan ta fito waje kamar yanda Deena ta tabbatar mata Yaya Shareff na nan na jiranta a waje. “Okay”. kawai tace mata tai ficewarta. Deena da yaranta suka bita da kallo baki taɓe. Fuska ta haɗe tamau tana cika baki da iska lokacin da take fitowa, ta buɗe motar ta shiga tana wani kauda kai taƙi kallon inda yake.         A jiyar zuciya ya sauke a hankali yana ɗagowa daga kwanciyar da yay jikin kujerar, murmushin daya tsaya iya laɓɓansa ya ɗan saki ganin yanda taketa faman kauda kai gefe wai ita a dole haushi take da shi. Hanunsa ya kai ya zame veil ɗin, tai saurin riƙewa tana tura baki. Kallon daya wulla mata ya sata sakin masa babu shiri, sai da ya gama ƙarema gashin kallo cikin ɗan lumshe ido da buɗewa ya maida mata ya rufe. Sosai gashin nata yasha gyara sai ƙamshi mai daɗi da ƙyalli yake.       Koda suka iso a gate yay parking, tana fita yaja motar yay gaba abinsa. Da harara ta raka motar, sai kuma ta kalli hanunta da ƙafa da sukasha lalli tai murmushi. Gidansu tai shigewarta. Dan cikin gida tun daga waje kana iya jiyo hayaniyar daya sake ɗauka alamar baƙi sun ƙaru kenan. Gidan nasu ma cike ta sameshi da baƙin da suka iso bayan fitarta. Sai su Aysha dake shirin komawa gidansu amarya bayan magrib Arabian night. Tambayarta wanda yay mata ƙunshi suka shigayi kowa na yaba ƙyan da yayi. A takaice tace musu Yayane ya kaita wani waje kawai. Koda suka buƙaci jin wane Yaya a ciki bata amsa musu ba tama shige toilet dan son watsa ruwa kasancewar gab ake da kiran sallar magrib saboda sun jima a wajen ƙunshin nan ba laifi, gashi ko sallar la'asar batayi ba.           Ana idar da sallar magrib ƴammatan gidan suka sake ficewa wajen event na arabian da aka shirya amma banda Anam yanzu ma. Dan kwanciyarta taima tana kallo a lap-top hankali kwance kamar bata san bikin da akeyi ba. Har magana Amrah tai mata amma tace karta dameta. Yanda tai maganar cikin masifa yasa kowa bai sake magana ba sukai shirinsu suka fice.           ★★★★★ Washe gari kam gida ya sake cika danƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa dana kusa. Abokan Yah Shareff na Nigeria da wajenta duk wanda ya iso anan ake saukarsa gidansu Anam a sashen Shareff ɗin da tuni Abie ya ware dominsa duk da ba zama yake ba a hanunsu yanzun. Duk hidimar da ake Anam na ɗaki batako fitowa sai yunwa ta isheta. Bamai ganin ko fara'arta. Mamie tayi faɗan harta watsar da lamarinta, hakama Aysha fushi take da ita dan ita bataga mi Anam ɗin kema fushe-fushen ba tunda babu wanda ya mata wani abu ai. Aima gaba ɗaya ta tsame kanta daga shagalin bikin tamkar Shareff ba ɗan uwanta ba. Da yamma kusan rabin jama'ar gidan suka wuce gidansu Fadwa amarya kamu amma nanma Anam bataje ba. Kai barci ma suka wuce suka barta tana sha hankali kwance. Koda suka dawo kuma su Aysha nata labarin yanda kamu ya kasance da ƙayatarwa Anam sai tai tsaki tama fice a ɗakin gaba ɗaya. Da kallon mamaki duk suka bita, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da al'amarin nata tunda ansanta da miskilanci da kuma tsanar da sukaima juna ita da ƴan gidan su Fadwa batun yanzu ba.         *_WASHE GARI* ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa, duk da ba'ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya koma tamkar a hanunsu ne.       Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa'ointa ma na family ɗin sunata zuwa nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.      Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin yabawa.      Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu tafi masallaci”.       Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi  tace, “ALLAH yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa'a, kuma yasa abokiyar arziƙinka ce har a aljannah”.     Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa, hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye.     Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.       Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”. Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.       Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.    Dariya tayi da faɗin, “A'a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a ɗaura a sa'a.”      “Humm” kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan Humm ɗin bata magani Yarona”.        Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan da suka rage na take masa baya..        Bayan ficewarsu Aunty Mimi bin bayan Anam tai. Ganinta zaune tana kallon su Aysha daketa faman shiryawa ta korata itama tai wanka. Ta kuma tabbatar mata idan har ta sake shigowa ta ganta bakamar kowaba saita ɓata mata rai matuƙa. Babu yanda ta iya dole tabi umarninta, su dai su Aysha sai faman dariya suke. Bata kulasuba ta shiga tai wanka, ta fito ta shiryawa a ɗaya daga cikin kayan fitar biki da su Daddy sukai musu. Sai dai kalar nata daban tasa saɓanin ƴan uwanta da duk suka saka atamfa. Sosai lass ɗin yamata ƙyau kasancewarsa skirt da riga kuma bata saba sakawa ba. Tai ɗas abinta kamar itama amaryar ce (Anam team😜). _________________________________         Alhamdulillahi bayan idar da sallar juma'a dake massallacin juma'a na anguwarsu ɗunbin al'ummar musulmi daga sassan daban-daban na Nigeria da wajenta suka shaida ɗaurin auren *_Al-Mustapha Muhammad Shareff_* da amaryarsa *_Fadwa Sadiq Dakata_* akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Ɗaurin aurene daya tara manyan mutane masu alaƙa da ango da iyayensa harma da ɓangaren amarya.         Kamar yanda nan gidan su  Shareff ke cike da ƴan uwa da abokan arziƙi acan gidansu amarya Fadwa ma hakane. Taci ado na faɗa aji daya amsa suna ado irin na amare ƴan ƙwalisa masu ji da lokaci (😘😍Sai dake tawan😂😉). Tana tsakkiyar ƙawayenta daketa aikin zuba hotuna da videon ɗorawa a tiktok. Tun kafin yau amarya Fadwa ta roƙi angonta da zarar an ɗaura aure ya taimaka ya kirata ya fara sanar mata da kansa. Da farko bai amsaba, sai dai yanda ta dinga nacin damunsa da maganar tsahon lokaci yace zaiyi. Shi mutum ne dabai ɗaukar alƙawari bai cikaba, sai dai hakan ta kasance bisa akasi. A yanzun ma harya shafa'a alƙawarin ya faɗo masa a rai. Yana tsaka da gaisuwa da abokansa yay excusing kansa ya koma gefe yana mai ƙoƙarin cikawa. Ga amarya Fadwa kam harta fidda rai zuciyarta sai faman kaikawo take kamar ta fasa kuka. Ta riga ta gama shiryawa da ƙawayenta domin jiran wannan lokaci, sai dai shiru kakeji sun fara jin kishin-kishin na cewar an ɗaura auran. Dama tasan itama gangancine kawai, Shareff ba irin mazan da ke ɗaukar kowane kalar shirme bane, hasalima ita har yanzu bai san tana harkar yanar gizo ba, da tana da tabbacin sai sun kwashi ƴan kallo da shi.......       Ring ɗin wayarta ya katse mata tunani, tamkar maijin tsoro ta ɗauka wayar tana dubawa badan ta saka ran ganin shi ɗin bane. Kasa ɗagawa tai har sai da babbar aminiyarta Sima ta ɗaga mata tasa a hansfree dan sunada tabbacin abinda suke zaman jiran ji ne daga angon dama. Sassanyar muryarsa data ratsa cikin wayar ta saka ɗakin ƙarayin tsitt, masu video recording na faman ɗauka. Cikin rawar murya ta amsa, dan haka kawai taji kuka ya taho mata batare data san dalili ba. Daga can yay murmushi saboda jin yanayinta, ashe da gaske aure yaƙin mata ne, dan yasan abinda zai saka Fadwa karaya ba ƙarami bane. Yay ɗan gyaran murya da sake kwantar da murya. *_“Habibtie kin zama Matar Al-Mustapha, ina roƙon UBANGIJIN daya nufemu da ganin wannan rana ya bamu lafiya da zuri'a masu albarka, tare da haƙurin zama da juna, mai cike da kulawa da soyayya na har abadan. Finally Al-Mustapha ya zama naki”._* Kalamansa sun ratsata daga ita har ƙawayenta da abun yay matuƙar burgesu, sai kawai ta sakar masa kukan da taketa faman haɗiyewa. Murmushi yayi, da sake faɗin, “Congratulations once again dear, i love you”.        “I love you too”. Ta amsa masa da sake fashewa da kuka. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin ihu da sowa harda masu guɗa. Jama'a dake waje kuwa har ture juna ake wajen son shigowa aga mike faruwa.       Cikin ƙanƙanin lokaci video ɗin da ƙawayenta suka ɗauka suka ɗaura a tiktok, istagram ya fara yawo fiyema da yanda sukai zato ko tsammani a kowane shafi na sada zumunta kamar yanda sauran hotunan da suketa ɗaurawa na sauran kwanakin ke yawo dama . Wanda ma followers ɗinsu basu kaiba tuni ƙaruwa suke. Comments da like kam ai bama a magana. Ƴammata sai alwashi ake ɗauka da zuwan tasu makamanciyar wannan rana. Wanda ko bikinsu ke shirin zuwa next week dama cikin satin tuni sun fara neman angunan nasu da ƙawaye yanda zasu tsara nasu suma. (Hummm media-media gidan kashe ahu😣).       ★★★      Daga wajen ɗaurin aure gayyar abokan ango da abokan su Daddy dama sauran jama'a suka ɗunguma hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci domin su. Anci ansha anyi hotuna kafin ango da tawagarsa su nufo gida. Yanzun kam sai da suka fara shiga gidansu yakai kansa ga Mommyn sa. Rungumesa tai cike da farin cikin yaronta ya zama babban mutum yau burinta ya cika. Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tayasa murna da masa fatan alkairi. Anyi hotuna shida dangin Mommy dama sauran jama'a har da wanda ke a tsakar gida na kusa. Daga nan gidan su Anam suka nufa da gayyar abokansa tunda dama nan ne masaukin nasu, Mamie kuma tama sake shirya musu wasu abincin anan dama.        Nan ɗin ma gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziki. Shigowarsu ta saka wasu fara sakin guɗoɗi, yayinda maroƙa keta aikin kirari na al'adar biki. Su Aysha da duk suke zaune a harabar gidan suma kan kujerun roba da aka zube miƙewa sukai cike da farin ciki suka nufi Yayan nasu dan tayasa murna suma. Anam dake faman latsa waya duk hayaniyar da ake gidan batako ɗaga kanta ba taja siririn tsaki, tare da gyara zamanta dan babu alamar zata bisu.        Har aka fara ɗaukar hotuna bata  ko kalli sashen da suke ba. Sai ma mikewa tai da nufin barin wajen taji an riƙo hanunta. Juyowa tai a fusace da tunanin cikin su Amrah ne, sai tai arba da aunty Mimi. Baki ta tura idonta na tara hawaye, aunty Mimi ta girgiza kanta da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Mamana”. Hanunta taja har cikin taron, ta kaita har gaban Shareff ta tsayar.       Ƙoƙarin haɗiye hawayen dake son zubo mata ya hanata iya ɗagowa ta kalli kowa take, ga idanu tanaji a kanta da maganar da aunty Mimi ke mata akan ta ɗago mai hoto zai ɗauka. Aunty Mimi zata ƙara magana Shareff ya girgiza mata kai, tare da yima camara man ɗin nuni daya dauka kawai. Aiko ɗaukar ya farayi abinsa, bayan an musu su kaɗai kusan kala uku mutane suka fara shiga, daga haka aka cigaba da ɗauka batare da ko sau ɗaya Anam ta kalli camara ba. Daga ƙarshe ma ƙoƙarin zame jikinta a wajen ta shiga yi dan kukan da take dannewa ƙoƙarin fin ƙarfinta yakeyi. Taku ɗaya tai taji an riƙo hanunta, cak ta tsaya, tare da juyowa da sauri zuciyarta na ƙara zuwa wuya. Ɗaukewa numfashinta ya nemayi a dalilin shigar idanunta cikin nasa, ya kuma sarketa da su da iyakar ƙarfin ikonsa. Ga hanunta har yanzu yana riƙe a cikin nasa. Tuni camara man ya maida hankalinsa a ɗaukarsu hoto. Ƙoƙarin janye hanunta tayi ya hana hakan, ga idanunta ma sun gagara fita a cikin nashi. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo a fuskarta a hankali, ta fisge hanunta da sauri tabar wajen harda ɗan haɗawa da gudu. Waɗanda hankalinsu ke kansu duk suka bita da kallo kamar yanda shima ya bita har sai da ta ɓace. Ido suka haɗa da aunty Mimi yay saurin ɗaukewa shima yana barin wajen..........✍ *_Ko anƙi ko anso, aure dai ya ɗauru, murna muke daga zuciya har zuwa ranmu💃🏻😍😜. (Anam team ya take ne🤣😂😉😜?)_* _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 0913484810_ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 ko *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽 [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_11_* .......Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.       A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya saka aljihu sannan yabi bayansu...                Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan karon.      Ko'ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma'aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba'aiba ya tsolema kowa ido.     Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa.       “Soulmate!”. Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.       Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa da buɗewa a lokaci guda.....           “Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama'a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.       Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.        Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.       “Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi'ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.            “To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma'auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.     “Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.      “Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet Please”.      Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.            Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a jikina”.       Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.            “Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.     “Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.        Addu'arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa.      Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa.... Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a jikinta....         “you are vary stupid!!”. Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne.      “Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka.......     “Shut up! Stupid!”. Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.       Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.         A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.            ★★★★    Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan ɓuya da Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta shirya tabi bus ɗin su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta faɗama kowa abinda ya faru ba, sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa aiki ta daina samun number ɗinsa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu'amula a wajen aikin nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata. A yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani abu ya samesa ai.         Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya ɗauke mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za'aje tarbo iyayenta airport sai dai batasan waye zaije ɗakkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman jiransu a gida. Aiko ƙarfe huɗu da rabi na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal abokinsa ɗauke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta harda kukan daɗi su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk wannan kaikawo da ihun yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin ɗansu. Hasalima duk wani ɗawainiyar biki Abie da Mami suka ɗauka. Acewarsu Shareff ɗansu ne, sune suka cancanci yimasa aure ba kowa ba. Hatta lefe da duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu nuna sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma dan uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra'ayin ayi bikin nan da ita, duk da kuwa katanga ɗayace tasan wasuma zasu shigo gidansu a ƴan bikin, amma dai ko yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun gara bane ta faɗa gidan zago😚.           ★★★     Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da taren ƙawayenta wayayyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da amaryar ta tara ɗunbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin celebrities da akeji dasu. Amarya tasha ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba'ai mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.       ★★★     Bayan sallar isha'i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah ɗiyar Aunty Mimi dake kusan sa'anni dasu Anam ɗin tana can itama za'ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da ta langaɓe wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan ɗin ma faɗa Mom tai mata akan batun ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni huɗu bata cikaba da gama murnar isowar su Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe idan ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta ɗin can ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.        Washe gari wajen sha biyu yaran gidan kowa da ƙunshi abin sha'awa amma banda Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka shirya suka fita hausa day itako tace bazataje ba. Sai faman baƙin rai takeyi na babu gaira babu sabar. Mamie dai tunda taimata tambaya ɗaya tace bakomai bata sakebi takanta ba. Sai aunty Mimi ce ke faman lallaɓata da lallashinta. Sai tace kawai ita bata da lafiya ne.        A wannan lokacin Shareff dake gidan batare da Anam ta sani ba ya shigo. Gabantane yay masifar faɗuwa. Ta miƙe zaram da nufin guduwa aunty Mimi ta dakatar da ita cewar ta kawo masa breakfast ɗinsa dake kitchen wanda Mamie dakanta da girka abinta kuma irin abincin ƙasar Malaysia ne. Jitai kamar ta fashe da kuka dan takaici, koda ta kawo ta ajiye masa ƙoƙarin juya tai zata bar wajen ya watsa mata mugun kallo saboda ido da suka haɗa by mistake. Baki ta murguɗa masa itama ta haura sama da gudu.       “Kai kaji shasha lafiyarki kuwa Mamana?”. Aunty Mimi da bata lura da abinda ya faru ba ta faɗa da mamaki tana kallon hanyar da Anam ɗin tabi. “Babana wai kaga mi yarinyarnan tayi kuwa? Sai kace mai tsoron wani anan?”. Murmushi kawai yay baice komaiba. Ta hararesa. “Kaifa tsiyarka kenan ai magana ka bama mutum amsa da murmushi”.      “Oh ALLAH small Mom rigima. Ni yanzu mikike so nace anan kuma? Ina ruwana da shirmenta”.          Hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kai. Yay dariya da shafa kansa yana buɗe kwanikan. Ƙamshin ya sashi lumshe ido murmushinsa na ƙara faɗaɗa. “Lallai na shaida Mamie na kusa dani”.      Dariya aunty Mimi ta sanya masa da faɗin, “Makwaɗaicin banza”. Dariyar yayi shima da faɗin “Naji ɗin”. Haka ya fara cin abincin cike da nishaɗi suna hirarsu har Mamie ma ta fito daga sashen Abie ta samesu. Zama tai itama suka ɗora, daka gansu kasan akwai shaƙuwa mai faɗi a tsakaninsa tun ba yanzu ba. Anam na jiyo dariyarsu daga sama taƙi sakkowa har saida ya wuce massalaci sallar azhur. Aunty Mimi kuma ta fita zuwa can cikin gida ita da Mamie.      Ta idar da salla tana shirin sakkowa ƙasa ta samu abinda zataci suka kusa cin karo da Fawwaz.     “A'a autan Mom daga ina haka da gudu?”.          “Yaya ne yace na kiraki”. Kafin tace da shi wane yaya ya kwasa da gudu ya fice. Ta girgiza kai tana murmushi. Ɗaki ta koma ta ɗauka abaya kasancewar kayan jikinta wando da rigane marasa nauyi. Duk zatonta Khaleel yake nufi, shiyyasa ta fito hankalinta kwance. Harta nufi gate ɗin shiga cikin gida motar dake fake a tsakanin gidansu da cikin gida tai mata horn. Kamar bazata juyaba sai kuma ta dubi motar ganin an sakeyi alamar da ita ake, tunanin ko Yah Khaleel ɗin ne a ciki ya sata nufar can duk da tasan ba motarsa bace, bama tasan motar ba dan kamar ma sabuwa.        “Tofa, wai su Yah Khaleel sabuwar mota akayine halan?”. Tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi tana shafa motar har side ɗin mazaunin driver. Kanta tsaye ta buɗe murfin. Duk abinda take dama idonsa a kanta, kuma yana jinta dan ya ɗanyi ƙasa da glass kaɗan. Da sauri ta saki murfin tana ambaton ALLAH tamkar wadda taga wani shaiɗan ko aljani. Ɗaga kafa tai da nufin juyawa ya dakatar da ita.       “Idan kika bar wajen nan sai na mareki”.    Tsayawar tayi, sai dai taƙi ta juyo. Hasali ma auna yanda zata arta da gudu takeyi.....             “Zagaya ki shiga”      Ta tsinkayi muryarsa a dake. Shiɗin ba abun wasanta bane, musamman a yanda yay maganar babu alamar wasa a cikinta. Ta haɗiye ƙwallar da suka taru mata a ido cikin cije lip tabi umarninsa. Sanyin ac da kamshi na musamman suka ratsata a cikin sabuwar motar da ko leda ba'a cirema kujerunta ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da lafewa cikin kujerar ranta fal tunanin ina zai kaita? Bata da mai bata amsa dan haka taja bakinta ta tsuke ta zubama sarautar UBANGIJI idanu..........✍      _🤣Tofa, su Shareffudden ango ko'an fara kidnapping ne bamu sani ba😣, to magana ta gaskiya ƴan team ɗinsa ku faɗa mana gaskiya mu fara rigakafin killace kammu kar'a sakamu a ruɗani😂😆?._ _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 0913484810_ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 ko *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_13_* ..........Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka, Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya kaimu za'a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya fara shirin tafiya dinner.      Bayan sallar isha'i aka fara kwasar mutane inda za'a gudanar da dinner, sai dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa. Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a barta ta shana😜). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama'a aka dawo gida.     WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma, dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai bayan sallar azhar. Anayin la'asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau. Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba...        Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran abokan ango.....       ★★   “Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka kanata jamana aji”.         Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay yana harararsa da miƙa hannu, Isma'il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima yana dariya. “ALLAH baza'a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”        Isma'il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu ragowa”.       Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu. Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom.         Jin gidan ya rage hayaniya sosai ta sakko downstairs. Su Mamie ne kawai zaune da ƙannenta, gaishesu tai kowa na tambayarta ya ƙarfin jikinta. Tace da sauƙi tana zama gefen Mamie ta kwantar da kanta a kafaɗarta. Ko mintuna uku batai da zama ba suka shigo da sallama. Shine a gaba cikin ɗanyar shadda milk color sai ƙyalli take harda hula a kansa. Sai su Fharhan biye da shi. Jitai kusan su dukansu idanunsu akanta suke kamar ta tashi ta arta da gudu, sai dai ta dake dan bata fatan sake tafka abin kunyar datai a ranar ɗaurin aure😝.        Sai da suka gama gaisawa da su Mamie Dr Jamil dake jin kamar ya haɗiyeta fuska ɗauke da murmushi yace, “A'a Anam banda ke a kai amaryar kenan?”.       Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi batare data kallesu ba. “Banda lafiya ne shiyyasa”. Ta faɗa a hankaki tana ƙara sinne kanta jikin Mamie.           “Ayya ai ban sani ba dana kawo ɗauki. Yaya jikin yanzun?”.   “Na samu sauƙi”. Ta faɗa a taƙaice tana ɗan ɗagowa. Cikin idonsa natan suka shige, tai saurin janyewa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi....       “My son kuje kar dare yayi an bar ɗiyata ita kaɗai, ALLAH yay muku albarka, ya bada zaman lafiya na har abada. Ayi haƙuri ayi haƙuri ayi haƙuri. Mu mata a duk inda muke haƙuri ake damu akan komai dan halittane masu wahalar sha'ani. Banda yanke hukunci cikin fushi, duk abinda aka gani ba dai-dai ba abu asannu a ruwan sanyi a kawo maslaha a cikinsa. Ayi ƙokurin sauke duk hakkin da ALLAH yace duk da bani da damuwa a kanka game da wannan. ALLAH ya azurtaku da zuri'a masu albarka”.       Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Anam dai ma ta maida hankalinta ga wayarta kamar bata jinsu. Ƴan uwan Mamie ma sun masa tasu nasihar suka sallamesu dan dare na ƙarayi. Dai-dai yana mikewa suka ƙara haɗa ido da Anam data ɗago itama. Wani kasalallen kallo suka sakarma juna. Ta kauda kanta tana taɓe baki zuciyarta na mata zafi. Shima iska ya ɗan furzar yana janye nasa a wani yanayi. Bata sake yarda ta ɗago ba har suka fice Dr Jamal na faɗa mata sai yazo dubiya ta musamman. Bata tankasa ba, sai Aunty Nasara dake kamar ƙanwar Mamie ta bashi amsa cikin dariya.       Tsam ta mike tabar falon dan ji take wani ɗan zazzaɓi ma na neman rufeta, ta nufi ɗakinta da fatan su Aysha su kwana a cikin gida yau bata bukatar su anan...... *_MONDAY MORNING_*           Tana tsaka da barcinta na safe mai daɗi kasancewar bata samu yin na dare ba sosai saboda zazzaɓi mai zafi data sake kwana da shi aunty Mimi ta tasheta akan ta tashi ta shirya za'a aiketa.       “Wayyo aunty ina su Aysha ki aika a kira miki su suna cikin gida fa ALLAH bana jin daɗi”.          Hararta Aunty Mimi tayi. “Ai nasan dasu Ayshan na tasheki. Maza tashi kina ɓatamin lokaci. Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi kamar zatai kuka. Wanka tai da ruwa mai ɗumi dan duk son sanyinta kuma bata wanka da ruwan sanyi. Gudun masifar aunty Mimi ya sata shiryawa a ɗan gurguje cikin shigar da tafi so a ko yaushe wando da riga ta ɗaura abaya pink a sama ta naɗa veil ɗin abayar. Tayi ƙyau sosai sai zuba kamshi take duk da bawani kwalliya tai mai yawa ba. A falon ƙasa ta sameta har su Mamie wanda suka makara nata breakfast. Gaishe dasu tai tana karasawa inda Aunty Mimi take.       “Yauwa ɗiyar albarka. Ai jeki kawai waje ga Ikram can na jiranki a mota da driver ”.     “To aunty saƙon fa?”. “Yana wajensu a motar”. Kai kawai ta jinjina taima su Mamie sallama ta fita. Baya ta buɗe ta shiga yayinda Ikram ke gaba tanata zubama driver surutu da hausanta da bata iyaba wai ita a dole koyan hausa takeyi. Itace autar aunty Mimi shekararta goma sha uku, kasancewarta girman turai sai take abu kamar wata yarinya ƙarama ga tabara ta autoci.       “Good morning aunty Anam”. Ta faɗa lokacin da Anam ke ƙoƙarin rufe murfi. “Morning dear how are you?”.     “Am fine, sai ƙafana dake ciwo saboda rawan da mukai a wajen dinner ranar”.          “Good for you”. “Kai aunty maimakon kimin sorry”.     “Tunda ni na aike ki”. Dariya Ikram tayi. Sai kuma ta shiga bata labarin yanda shagalin dinner ya kasance. Shiru Anam tai mata, da taga zata isheta sai ta buɗe bag ta ɗakko bluetooth ta saka waƙa har suka iso gidan da bazata taɓa iya mantawa ba. Kasa motsi tai balle magana har driver yay horn maigadi ya buɗe masa gate suka shige. Jitai kanta na juyawa, ta dafesa tana ambaton sunan ALLAH. Da tasan nan aunty Mimi zata aikosu da duk ma yanda zatai taƙi zuwa ALLAH da sai tayi. Yanzu kuma tana ƙin shiga wannan akku sarkin zancen zataje ta bazata a fassarata a mai baƙin ciki. Siririn tsaki taja da buɗe motar a fusace ta fita dan Ikram tuni ta fice har driver ya buɗe mata booth suna fidda kayan breakfast da sukazo da shi. Ƙin daukar komai tai sai driver da ikram ɗinne suka kwasa.         Daga can baya ta tsaya Ikram ta shiga yin knocking tana kiran sunan Yaya Shareff. Sun kai kusan mintuna goma sha sannan aka buɗe har ta gama yanke shawarar juyawa ta koma. Shine ya buɗe ƙofar Ikram ta riƙo hanunsa cike da shagwaɓa. (Wayyo Yaya ƙafafuna har zafi suke da hannuna”.       Kanta ya dafa da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya tashi yana buɗewa. Ya matsa mata alamar ta shigo yana maida dubansa ga Anam datai tsaye tana kallon wani waje daban. Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yay magana.     “Tsaiwar ta miye?”.   Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufosa. Harta ƙaraso idonsa na kanta yanzu ma. Ya ɗan matsa mata alamar ta shiga itama. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janyewa da raɓashi ta shige tana murguɗa baki. Shine ya shiga da kayan cikin falon da kansa, Ikram sai faman yaba falon take dan babu ƙarya naira tayi kuka. Itako tana tsaye tamaƙi zama, ta dai jingina da bango tana daƙilar wayarta.     “Ina kwana”. Ta faɗa batare data yarda ta kallesa ba. Bai amsata ba, sai hankalinsa daya maida ga Ikram da bakinta yaƙi shiru. Haushi ya ƙara kume zuciyarta, gashi ta fara gajiya da tsaiwar, amma sai ta cigaba da daurewa. Kusan mintuna biyar yana biyema shirmen Ikram tamkar ma ya manta da ita a falon. Ƙaton agogon dake bangon falon ya duba, tare da dawo da kallonsa gareta.       “Bani plate a kitchen”.    Kallonsa tai da mamaki, sai kuma ta sake ɓata fuska. “Ni ban san kitchen ɗin ba”. Da hannu ya nuna mata ya ɗauke kansa. Kitchen ɗin ta nufa wani haushi na ƙara turniketa, cikin taɓe baki take bin ko'ina na kitchen ɗin da kallo. Tabbas yayi ƙyau, sai dai hakan ba yana nufin wani abu na cikinsa ya burgeta ba. Abinda ya aikota ta nufa ta ɗauka, sai dai ta nufi sink dan ta ɗauraye, sai ƙunƙuni takeyi da bazaka iya sanin mitake faɗa ba. Juyowa tai tana jan tsaki, da sauri taja baya har plate ɗin na neman suɓuce mata. Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba, ga idanunsa masu kaifi daya kafeta da su. A hankali ya tako gabanta duk hannayensa cikin aljihun jallabiyar jikinsa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin numfashinsa. Sai taji gaba ɗaya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi a wadace...       “Ya jikin ki?”.    Yay maganar cikin taushin muryar da bata taɓa ji daga garesa ba. Kasa jurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa. Har yanzu idanunsa a kanta suke, tai saurin janye nata tana girgiza kanta. Muryarta da ɗan rawa tace, “Alhamdulillahi”.       “Kin tabbatar?”.    “Nifa zazzaɓi ne dama kawai Yaya MM”.        Jin baice komaiba ta ɗago ta dubesa, still dai har yanzu idonsa a kanta. (Ya ALLAH! lafiyarsa kuwa?) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin son barin wajen. Amma sai furucinsa ya sakata dakatawa babu shiri.           “I'm sorry”.     Kasa yarda tayi daga bakinsa furucin ya fito, musamman da babu alamar shi ɗin ya faɗa a yanayinsa. Sannan bata san dalilinsa na faɗarba. Kamar ya fahimci ƙarin bayani take buƙata sai ya bar wajen cike da basarwa. “Zoki dafamin lipton”. Shiru bata motsa ba, da alama bata tare da tunaninta ma. Ya juyo ya dubeta fuska a tsuke. “Badake nake magana ba!”. Itama fuska ta haɗe, sai dai cikin sanyin murya tace, “Yaya matarka fa?”.  Ido ya tsura mata na wasu sakanni, sai kuma ya janye. “Nasan da ita ai na sakaki. Sannan ganin amarya a kicin irin wannan ranar kema kin san bamai yuwuwa bane”.       Da hausa yay maganar, dan haka ba komai ta fahimta da ƙyau ba. Amma sunan amarya kawai daya shigo ciki ya saka yanayinta ƙara canjawa. Sai dai bata sake cewa komai ba, ta ɗauka tunkuyar daya fiddo mata domin dafa shayin ta ɗauraye, ruwa ta zuba dai-dai shan mutum ɗaya, tana ƙoƙarin rufewa taji tsaiwarsa a bayanta, kafin tayi wani yunƙuri ya janye hanunta da sake buɗe murfin ya buɗe fanfo ya ƙara ruwan.       “Nadai bazan dafama wata ƙatuwa shayi tana kwance tana barci ba”.   Karon farko ya saki murmushi, sai dai komai baice ba ya rufe mata tukunyar. Zata sake magana ya dakatar da ita. “Zakimin abinda na saki ko tsiwa? Trouble maker!”.       “Ga babbar Trouble maker can ka bari a ɗaki”. Tai maganar ƙasa-ƙasa yanda bazaiji ba. Da kansa ya kunna mata gas ɗin, ta ɗaura tukunyar sannan ta ɗiba kayan ƙamshi da lipton da duk ya fiddo da kansa ta zuba. Flask daya fiddo a kwali shima ta ɗauka ta ɗauraye tare da kofi duk yana tsaye yana kallonta. Baiyi mamakin yanda take komai a tsaftace da kuma tsari ba, dan sai dai ya bama wani labarin Mamie badai a bashi ba, yasan kuma hakan duk tarbiyyar data samune daga gareta. Yana kitchen ɗin harta kammala komai, ya sake ɗaukar kofuna uku ya ɗauraye da kansa ya haɗa da wanda ta wanke. Bata tanka masa ba, ta ɗauka flask ɗin kawai ta fita. Shine ya ɗauka sauran kayan ya fito da su, samunta yay tanama Ikram masifa akan ta tashi su wuce gida, ashe da wayarsa ya haɗata shi ya tafi neman magana kitchen..       “Sai kun karya, tunda tace bakuyi breakfast ba kuka fito”.     Ranƙwashi takaima Ikram ɗin, amma sai ta kauce tana dariya da faɗin, “Wlhy Yaya ita a barci ma aka tasota gara ni nasha tea”. Wani ranƙwashin zata sake kaimata ya zuba mata hararar data sata dakatawa, sai dai tayi gefe da kanta tana ƙunƙuni.        “Oya zauna ki haɗamin yunwa nakeji”. Ya faɗa yana ajiye ledar dake ɗauke da kayan tea da abokansa suka rako shi da su a daren jiya tare da kaza. Batai magana ba, shima kuma bai sake maganar ba ya nufi ƙofar fita yasa key sannan ya wuce kitchen. Harara ta dinga zubama Ikram tana haɗa tea ɗin, tsabar mugunta ta zabga masa sugar. Ikram ta mikama nata tana faɗin, “Makwaɗaiciya kawai, daga zuwa gidan mutane”.      Ikram tace, “Ni banyi kwaɗayiba tunda gidan Yaya ne”. Fitowarsa ta hanata bama Ikram ɗin amsa, ya dire babban plate dake ɗauke da kaza sai turiri take alamar ɗumamata yay. Zata miƙe yace, “Koma ki zauna.” babu wasa a lamarinsa dole tabi umarni, sai dai idonta harya fara tara ƙwallar takaici. Hanyar corridor ɗin da take ƙyautata zaton bedrooms ne ya nufa, cikin jin haushin da babu dalili ta raka bayansa da harara. Wayarta ta ɗauka ta cigaba da daƙila, kusan mintuna uku sai gashi ya fito, zama yay a ƙasan carpet ɗin shima kamar yanda take zaune. Yace, “Bani tea”.     Batai magana ba, ta ɗauka flask ta zuba masa ruwan zafin akan kayan tea ɗin data haɗa a kofin. Sai da ta juya ta tabbatar sugar ɗin ya haɗe sannan ta miƙa masa. Duk da yaga bata haɗa nata ba sai baice komai ba yaja nasan gabansa da ƙyau, kaɗan ya ɗiba a cokali yakai baki dan yaji yaya test ɗin. “Ya ALLAH!”. Ya ambata da sauri. Tasan tsiyar da tai dan haka taƙi ɗagowa. “Kina hankalinki ƙuwa zaki saka min wannan sugarn?”.      “Toni Yaya nasan yanda kake so ne?”.    Idanu ya zuba mata kawai tsahon wasu sakanni. “Idan ma mugunta ce harda kanki zaki mawa, ba wadda take cikin gidan kawai ba, dan duk dodo ɗaya zaku yima tsafi”. Komai bata fahimta a zancensa ba. Wani kofin ya ɗauka ya raba shayin biyu, ya ƙara kayan tea ɗin banda sugar ya sake zuba ruwan zafi. Ikram dake ta faman latsa waya tana shan nata tea ɗin yace ta sakko.      Duk yanda Anam ta so nuna ta ƙoshi bai saurareta ba. Haka ya tilasta mata karyawa tare da shi da breakfast ɗin da suka kawo da kazar daya ɗumama. Sai dai ita taƙi cin kazar ko sau ɗaya. Ikram kam komai sai da taji yakai mata sannan tai hamdala. Tayi niyyar suna gamawa su wuce, amma sai taga babu dacewar barin kwanikan, ita ta kwashe komai zuwa kitchen, ta ɗauraye kwanikan da suka ɓata. Koda ta fito bata samesa a falon ba, tacema Ikram ta tashi su wuce gida.        “Lah aunty Anam Yaya yace mu jirashi zai fito muje tare”.      Harara ta zuba mata, “Shi kuma driver daya kawomu fa yake zaman jiranmu?”.       Fitowarsa ta hana Ikram bada amsa. babu abinda ya canja a jikinsa sai key ɗin mota daya ɗakko, ta ɗauke kanta gefe harya ƙaraso ya amsa wayarsa a hanun Ikram. Suna gaba tana binsu a baya har wajen mota, bataga driver ba, ba kuma ta tambaya ba. Ganin Ikram ta shige baya itama tai yunƙurin shiga....         “Waye driver ɗinku?”.    Fuska ta tsuke tana hararar Ikram kamar itace tai maganar. “Malama koma gaba”.      “Ni dai aunty ki barni anan nafi son baya cikina ya cika da yawa zan kwanta”. A fusace ta ƙara yunƙirin yin magana ya dakatar da ita. “Bana son shirme fa kina ɓatamin lokaci nabar matata tana barci kowane lokaci zata iya tashi, ganina kusa da itane kuma abinda tafi buƙata a yanzun”.       Tamkar saukar aradu haka furucinsa ya daki ƙirjin Anam saboda da yaren malay yay maganar yanda zata jisa ta fahimta da ƙyau. Idanunta ta rumtse ta buɗe motar ta shiga batare datace masa komai ba. Shima bai sake cewarba ya harbar motar zuwa waje dan maigadi dama ya wangale masa gate tuni........✍     *_🚶🏻🤕😣askiya kuyima ƴar mitsilarnan taku kashedi ta fita sabargar angonmu.😚_*       _ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 0913484810_ZAFAFA BIYAR_ *_INAYAH_* _MamuhGee_ *_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_ *_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_ *_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_ *_BABU SO_* _Billyn Abdul_ _*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_* YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾 ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902 IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 ko *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* [10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_* *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_* _(Miya kawo kishi?)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_14_* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels