An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH! (Tarihi, Karamomi, Darajoji da Baiwar Jagoran Harka Islamiyyah A Afirka, Shaikh Ibraheem bin Ya'aqub Al-Zakzaky H). Na: CIBIYAR WALLAFA DA YAXA JAWABAN SHAIKH ZAKZAKY (H). (Institute For Completion And Publication of Shaikh Zakzaky's Works). AUTHENTIFICATION: Copyright©: Institute For Completion And Publication of Shaikh Zakzaky's Works. Haqqin Mallaka: Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H). ISBN: 978-978-959-905-9 TUNTUBA: +234-80-32-58-57-34. +234-70-68763600. +234-80-37023343. MASANIYA: Littafi: Shaikh Zakzaky Ikon Allah! Rubutawa: Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H). Jigon Batu: Tarihin Rayuwar Sayyid (H). Shekara: 1438-Hijira. 2017-Miladi. Wallafa: 12-Stars Multimedia. Kanu: Babi 7, Fasali 83. Kalmomi: Ya Qunshi Kalma 47,650. Farashi: Daidai da Kasuwa. Adireshi: Nigeria, WestAfrica. Tuntuba: 080-325-857-34. KYAUTARWA: Muwafaqa a Wannan Littafi, Hadiyya ce ta Musamman Ga Ma'abucin Alfarma Da Daraja, Baqiyyatullahi Fil-Ardh, Sahibul Asr Waz-Zamaan, Imamul Hujjah, Al-Qa'im, Al-Mahdiy Bin Hasan Al-Askary (AF). IZINI: Ya halasta a yi amfani da sashen wannan littafi ko dukkansa wajen yada manufa kyakkyawa, kamar yadda ya halasta a sake bugawa don yadawa, amma bai halasta a canza wani abu ko a sake masa fasali ba sai da izinin marubutan. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ GABATARWA Da sunan Allah mai Rahama mai Jinqai. Tsira da Aminci su ci gaba da dauwama ga fiyayyen halittu, Annabin Rahama Muhammad xan Abdullahi (S), da Iyalan gidansa tsarkaka ma’abuta daraja, wanda ba sa kuskure ko savo. Babban dalilin da ya haifar da rubuta wannan xan littafi shi ne, lokacin da gwamnatin Nijeriya qarqashin shugaban qasa Muhammadu Buhari ta abkawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa a birnin Zariya ranar 12 ga watan 12 na shekarar 2015, inda ta kashe almajiransa kusan Dubu xaya, ta raunata xaruruwa, ta kuma tsare xaruruwa, ciki har da yi wa Shaikh Zakzaky da mai xakinsa ruwan harsashi, da raunata su a wurare da dama, da kuma kama shi da tsare shi ba bisa qa’ida ba, wanda hakan ya jawo gangami da Muzaharorin Allah wadai a qasashen duniya da dama. Hakan ya sa al’umomin duniya a xaixaikunsu da jama’ance suna ta tambayar waye Shaikh Ibraheem Zakzakin nan? Meye tarihinsa? Ya labarinsa yake? Ta yaya za su san wani abu a kansa? Duk xan uwan da ke mu’amala da ‘yan qasashen waje ko da kuwa ta “Social Media” ne, zai iya zama shaida na qishin ruwansu ga neman sanin tarihin Shaikh Zakzaky (H). Wannan ne qashin bayan da ya zaburantar da mu don samar da wani xan abin da zai ba mutane haske game da wannan Jagora mai albarka. Tarihin Jagoran Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Bin Ya’aqub Al-Zakzaky (H) abu ne mai faxin gaske, da wuya wani marubuci ya iya rubuce tarihin Shaihin Malamin baki xaya saboda faxinsa. To amma Larabawa suna da karin maganar da ke cewa; “Abin da ba za a iya yinsa duka ba, to, bai kamata a qi yinsa kwata-kwata ba”. Wannan ne ya sa muka ga dacewar yin tsokaci game da wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar wannan Jagora a gurguje kuma a taqaice, domin hakan ya zamo manuniya ga masu sha’awar faxaxa sanin tarihinsa ko yin rubuta a kansa, kuma ya bai wa wasu haske game da tarihin wannan babban Malami Jagora a Afirka. Ko kaxan, wannan xan littafin ba zai zamo ya wadatar ga sanin tarihin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba, domin akwai abubuwa da dama da ba a tavo su ba don gudun tsawaitawa, sa’annan waxanda aka tavo xin ma sama-sama aka tava su, an ambaci sashensu ne kawai ba dukkansu ba. Dan haka, mai son sanin faffaxan tarihin shugaban Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sai ya koma zuwa ga wasu littattafan da aka rubuta a kansa, da waxanda za a rubuta nan gaba. Ximbin mutane sun bada gudunmawa mai yawa ta vangarori daban-daban wajan haqqaquwar wannan littafi, ta yadda ba zai yiwu a iya jero ko ambato sunayensu duka ba, amma tattare da haka muna matuqar miqa jinjina da godiyata garesu, Allah ya saka musu da mafificin sakamako. Dukkan yabo da godiya ga Allah suke tuqewa, kuma duk wata dacewa daga Allah take, gare shi muka dogara, kuma gare shi muke neman taimako! Bissalam. Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H). 080-325-857-34. 070-687-636-00. 080-370-233-43. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ BABI NA FARKO TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) A TAQAICE Salsalar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) : Tarihi mafi inganci da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da kansa, ya faxi cewa asali iyayensa sun fito ne daga Magrib (Moroko); Daga nan suka zo birnin Shingixi na tsohuwar daular qasar Mali, amma yanzu birnin na Shingixi mai tsohon tarihi yana qasar Mauritaniya ne, daga garin Shingixi kakanninsa suka yo qaura zuwa birnin Mabruk da ke qasar Mali, daga nan kuma suka zauna a birnin Timbuktu, daga birnin Tumbuktu ne kuma suka taho wannan qasa Nijeriya cikin qarni na 12. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 09 zuwa 11). Nasabarsa : Salsala ko nasabar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta jero ne kamar haka; Shaikh Ibraheem xan Ya’aqub, xan Aliyu, xan Muhammad Tajuddeen, xan Liman Hussain Batoronke, shi Liman Hussain Bafulatani ne daga qabilar Toronkawa wanda ya zo qasar Hausa daga Mali a zamanin Shehu Usman bin Fodiye, inda ya zama babban limami a garin da yake zaune a yankin Sakkwato. Daga bisani sai xansa Malam Tajuddeen wanda almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne ya biyo tawagar wakilin Xanfodiye na Zazzau, wato Sarkin Zazzau Malam Musa suka taho Zariya tare dan ya riqa karantarwa. Mafi yawan tarihin da ake rubutawa na salsalar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) yana tuqewa ne akan Liman Hussain, wataqil don gudun tsawaitawa, domin jerin nasabar Shaikh (H) tana tuqewa ne ga Imami na biyu cikin limaman shiriya na Ahlul-Bait (AS), wato jikan Manzon Allah (S) Imam Hassan Al-Mujtaba bin Aliy bin Abiy-Talib (AS), xan Sayyida Fatimah Azzahra (SA), wan Imam Hussain shahidin Karbala (AS). Mahaifinsa : Sunan mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam Yaqubu Aliyu, ana masa laqabi da Malam Magaji, tarihi bai ambaci takameme shekarar da aka haifi Malam Yaqubu Aliyu ba, amma ana kyautata zaton an haife shi ne a shekarar 1902. Ya taso a gidan malanta da ilimi, dan haka ya taso ne da karatu da riqo da addini, tun tasowarsa mutum ne mai haquri da sanin ya kamata, an shaide shi da kyawawan xabi’u da aiki da abin da ya karanta. Sana’arsa ita ce koyarwa da kuma Noma da Kiwo. Ana kyautata zaton ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 70 daidai (1902 – 1972), ko shekaru 72 a qidayar Hijiriyyah. Allah ya yi wa mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam Yaqubu Aliyu rasuwa ne a watan Fabarairu na shekarar 1972, ya rasu ne a wani kududdufi da ke bayan unguwar Qwarbai cikin birnin Zariya, a lokacin da ya je ceto wata Akuya da ta faxa cikin kududdufin lokacin da ta je shan ruwa, kuma an yi masa jana’iza aka binne shi a maqabartar da ke kusa da kududdufin, yanzu haka qabarinsa yana wurin. Ya rasu ya bar ‘ya’ya 16, maza takwas, mata takwas. Mahaifiyarsa : Malama Salaha Muhammad Gixaxo, wacce aka fi sani da Hajiya Hari Jamo ita ce mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Bafulatanar usuli ce daga qabilar Fulani Toronkawa, kakanta Malam Abdulqadir ya taho ne daga qasar Mali ya yaxa zango a Zariya. Laqabinta na “Hari” a harshen Fulatanci yana nufin “Wacce aka haifa a Damina”. An haifi Hajiya Salaha ne a shekarar 1924 a cikin birnin Zariya. Ta haifi ‘ya’ya 12 da mijinta Malam Yaqubu, amma 5 daga ciki sun rasu tun suna qanana, kuma Shaikh Zakzaky (H) shi ne xa na biyar a wurinta. Mahaifiyar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) Hajiya Salaha (Hari Jamo) malama ce mai ilimin addini, ta kasance tana karantar da mata maqwabta da matan unguwa da kuma qananan yara a cikin gida. An shaideta da yawan ibada, musamman karatun Alqur’ani da yawan addu’a. Ta rasu ranar 17 ga watan Nuwamba na qarshen shekarar 2014 (25-Muharram-1436), sakamakon jinyar da ta yi fama da ita, kuma ta rasu tana da shekaru 90 daidai a qidayar Bature (1924-2014), ko shekaru 93 a qidayar Hijira. Ta bar ‘ya’ya 6 da jikoki masu yawa, qabarinta yana Hubbarenta da ke unguwar Jushi a cikin birnin Zariya. 'Yan Uwansa : Mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wato Malam Yaqubu Aliyu, ya rasu ya bar ‘ya’ya goma sha shida ne cif a duniya, takwas maza, takwas mata, su Shaikh Zakzaky (H) su bakwai ya bari ta wajan mahaifiyarsu Hajiya Salaha, wato wanda suka haxa uwa xaya uba xaya, maza huxu, mata uku, ga su a bisa jerinsu; Abdulqadir Yaqub, Maryam Yaqub, Fatimah Yaqub (Goggon Qaura), Ibrahim Yaqub (Sheikh Zakzaky), Badamasi Yaqub, Yahya Yaqub, sai ‘yar autarsu Maimunatu Yaqub. Ta vangaren sauran ‘yan uwan Shaikh Zakzaky guda 9 kuwa, sun haxa mahaifi ne kawai da su, wato mahaifinsu xaya, amma mahaifiyarsu ita ce Hajiya Aminah wacce ake qira (Iya mai Manja), su tara ne, maza huxu, mata biyar, ga su a bisa jerinsu; Muhammad Sani Yaqub, Ramatu Yaqub, Karimatu Yaqub, Usman Yaqub (Sarkin Malaman Fadar Zazzau), Maryam Yaqub, Abubakar Yaqub, Salihu Yaqub, Zaliha Yaqub, sai ‘yar autarsu Hajara Yaqub. A jumlace, waxannan sune ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) na jini, kuma Shaikh (H) ne xa na shida a wajan mahaifinsu, amma na biyar a wajan mahaifiyarsa, (bisa lissafawa da wansa Zubairu Yaqub, wanda ya rasu yana qarami). Haihuwarsa : An haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne gab da hudowar Alfijir na ranar Talata 15 ga watan Sha’aban 1372 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da Talata 5 ga watan Mayu shekara ta 1953 Miladiyya. An haife shi ne a bayan Fada da ke unguwar Kwarbai cikin birnin Zariya jahar Kadunan Nijeriya. Suna da Laqabinsa : Sunan jagora shi ne Ibraheem, laqabinsa kuma Al-Zakzaky, wanda fassararsa ke nufin mutumin Zariya, wato mutumin qasar Zazzau, ko Bazazzagi a taqaice. Laqabin Al-Zakzaky ya samo asali ne a lokacin yana makaranta, sai ya zamo su biyu sunansu ya zama iri xaya (Ibrahim Yaqubu), sai aka ce kowa ya qara suna xaya a jikin nasa, sai Shaikh ya qara Zakzaky a jikin sunansa, daga nan ake qiransa Al-Zakzaky. Wani laqabinsa da ya shahara shi ne laqabin da Shaikh Usman bin Fodiye ya laqaba masa tun sama da shekaru 200 kafin haihuwarsa, wato laqabin Sharafuddeen, wanda fassararsa ke nufin “Mai Xaukaka Addini”. Sai kuma laqabin Ibraheemul-Magriby, wanda ke nufin “Mutumin Yamma” wanda shi ma laqabi ne da ya samo asali daga zantukan waliyai magabata. Sannan akwai laqabin “Khaleel” wanda iyalinsa Malama Zeenatuddeen ce kaxai take kiransa da wannan laqabi. A taqaice Shaikh (H) yana da laqubba guda uku, wato Zakzaky, da Sharafuddeen, da Al-Magriby, sai kuma na khass da iyalinsa ke kiransa da shi, wato Khaleel. Siffofinsa : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baqin fata ne mutumin Nijeriya a Afirka ta yamma. Matsakaici ne a tsawo amma ya fi kusa da gajarta. Yana da matsakaiciyar qiba. Kyakkyawa ne mai kyan sifa da kyan diri. Yana da manyan idanu matsakaita girma. Yana da faffaxan goshi, da faffaxan qirji, da karan hanci. Yana da hasken fata da madaidaitan kunnuwa. Yana da mayalwacin gemu amma bai da qasumba. Yana da tsaga bibiyu a kwivin idanuwansa biyu, wanda hakan ke alamta cewa shi Bamalle ne a qabilar Fulani. Ta ko ina bai da naqasa a halitta. Yana da cikar kwarjini da Haiba. Yana da izza a cikin tafiya da zamansa. Haziqi ne mai fikira da hangen nesa. Fasihi ne mai fasahar magana. Xan baiwa ne a ilimi, Fikira da sanin fannoni. Yarintarsa : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso a gida na addini da tarbiyya, dan haka tun yana yaro qarami ya gudanar da yarinta ce mai tsabta, sam ba a san shi da qin jin magana, ko faxa da yara, ko mugunta da qeta, ko nuna fin qarfi ga wanda ya fi ba. An san shi ne a matsayin yaro mai dattaku, mai tarbiyya, mai girmama na gaba, mai ladabi ga iyaye, mai tausayin qanne, mai taimakon tsofaffi, mai son karatu, kuma mai qwazo da rashin kasala. Iyaye da ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da cewa tun yana qaramin yaro bai tava zuwa neman qarin miya ba, wato in an zuba masa abinci komai qarancin miya ba zai ce a qara ba, kuma in yana cin abinci miya ta qare, to ko bai qoshi ba haka zai haqura, amma ba zai je ya ce a qara masa miya ba. Wannan yana nuna halin dattaku da Makarimul-Akhlaq xin Shaikh (H) ne tun yana qaraminsa. Wanda suka san tasowa da yarintar Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da kyawawan halayensa na yarinta. Dattijo kuma xan Sarkin Zazzau Aliyu Xan Sidi, wanda aka fi sani da Alhaji Basiru Aliyu Xan Sidi ya faxi cewa; “A wancan lokaci (na yarinta), sanin da na yi wa Malam Ibraheem Zakzaky yaro ne mai hankali da biyayya ga na gaba da shi, tare da dattako, ban kuma tava jin wani abu na laifi ko kuma aibu akansa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 84). Shi ma Magayaqin Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya faxi cewa; “Ni dai na san shi (Ibraheem Zakzaky) yaro ne mai kawaici, sannan bai cika maganganu haka barkatai ba… A makarantun da ya yi yana da ladabi da biyayya ga duk na gaba da shi a yawan shekaru, domin mu nan ba mu samu wani abu da za mu soka game da shi ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82). Wata dattijuwa ‘yar kimanin shekara 100 daga zuriyar gidan su Shaikh Zakzaky (H), wacce ake kira Goggo Fatimah, ta bada kyakkyawar shaida akan yarintar Shaikh xin, ta ce; “Shi dai lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki… tun farko mun ga alamar zai zama wani abu. Yana da biyayya qwarai da gaske. Mutum ne mai zumunci, ya san nasa, duk inda suke zai sa qafa ya bi su da alheri, dama (tun asali) da alherinsa ya taso, ba yanzu ne ya fara ba, tuntuni haka yake… Tun yana yaro bai san faxace-faxacen nan na yara ba, ba ruwansa, shi ya taso kamar Dattijo ne, tun yana yaro kamar dattijo yake, irin sakarcin nan ma na yara shi ba ya yi, sai ma idan yara sun yi abun da bai dace ba, sai ka ga ya tsawatar musu” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 68). Wani abokin Shaikh da suka taso tare, mai suna Malam Wadan Mai Raqumi yana cewa; “Ibraheem mutum ne wanda tun yana yaro ba ya son wasa ko wulaqanta addini, (sannan) shi ba ya irin mugun wasannin nan da yara kan yi, ko a unguwa ko a makaranta, idan mun zo muna yin (mugun wasa) sai ka ga ya koma gefe guda abinsa” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24). A taqaice, Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun tasowarsa ya taso ne a matsayin kamili mai halin dattaku, duk wani shexanci na yara bai yi shi ba, da kamala da kyawawan halaye ya taso. Kenan halaye da xabi’un Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun ran gini ran zane ! Karatuttukansa : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ma’abucin ilimi ne da ya yi karatu mai zurfi a fannonin ilimi guda biyu, wato karatun addini da kuma na zamani (Boko), kuma a lokacin yin waxannan karatuttuka ya bi ta hanyoyi biyu ne da aka saba bi bisa al’ada, wato tsarin karatun gida (karatun Zaure), da kuma tsarin karatun Nizamiyya na makarantun zamani. Karatunsa na Zamani : A fannin karatun zamani na Boko, ko mu ce karatun Nizamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara karatun ne yana da shekaru 17 a duniya, dan haka bai yi karatun Primary kai tsaye ba. Ya fara shiga makarantar horar da malaman Larabci da ake qira “Fada Provincial Arabic School, Zaria” ne a shekarar 1969 zuwa 1971. A shekara huxu ake gama wannan makarantar, amma saboda basirar Shaikh da hazaqarsa ya kammala ta ne cikin shekaru biyu kacal. A lokacin da yake karatu a wannan makaranta ta FPAS yana koyarwa a makarantun Islamiyyah har guda huxu, xaya a unguwar Kwarbai, xaya a unguwar Kakaki, xaya a unguwar Lemu, xaya kuma a Rimin Tsiwa duk dai a cikin garin Zariya. A tsakiyar Shekarar 1971 ya tafi makarantar koyon harshen larabci “School for Arabic Studies” da ke birnin Kano don zurfafa karatun harshen Larabci, amma bayan an yi masa gwaji (Interview) an ji ya iya turanci, sai shugaban makarantar ya canza masa ra’ayi daga karatun harshen Larabci zuwa karanta darussan Turanci. Ya kammala wannan makaranta ne a shekarar 1975. A lokacin da yake karatu a S.A.S Kano ya gwama karatun “Grade Two” xinsa ne da karatun darussa huxu na “Advance Level”, darussan kuwa sune; Economics, Government, Islamic Studies, da kuma Hausa, dan haka bayan ya kammala jarabawar “Grade Two” sai kuma ya zarce da ta “Advance Level” a lokaci guda. Da jarabawowin guda biyu suka fito, sai ya zamo duk ya ci su, takardunsa duk sun yi kyau, wannan ne ya ba shi damar samun karatun digiri kai tsaye a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya kasance yana halartar karatuttukan addini a zaurukan manyan malamai da dama na birnin Kano a lokacin da yake xalibta a can. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zariya) ne a shekarar 1976, inda ya karancin fannin tattalin arziqi (Economics). Ya kammala digirinsa a shekarar 1979, amma a lokacin da yake jarabawarsa ta qarshe ta kammala karatun, sai jami’an tsaro suka kama shi suka tsare bisa tuhumar hana wasu mashaya giya yin taronsu na fasadi a harabar makarantar, wannan ya sa bai samu damar yin wasu takardu (Papers) na jarabawarsa ba, har sai da aka sako shi daga kurkukun Inugu a 1984, sai hukumar makarantar ta ba shi damar qarasa jarabawar tasa, amma bayan ya rubuta jarabawar suka ga ya yi nasara, sai suka riqe sakamakon suka hana shi, wato har zuwa yau hukumar jami’ar ba su ba Shaikh Zakzaky (H) digirinsa ba. Amma rahotanni sun tabbatar da cewa shi ne xalibi mafi hazaqa a wannan shekarar, wato ya fita da “First Class” ne. A jumlace, za mu iya cewa, karatun Boko daga fara shi zuwa kammala digiri, ana yinsa ne a tsawon shekaru goma sha tara (19), amma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya kammala karatun zuwa digiri ne a tsawon shekaru Goma (10) kacal! Domin karatun shekaru bakwai na Firamare, ya yi shi ne a shekaru biyu kacal a FPAS Zariya. Karatun shekaru shida na Sakandire kuma, ya yi shi ne a shekaru huxu kacal a S.A.S Kano. Sa’annan ya yi digirinsa a ABU Zariya cikin shekaru 4. Wannan zai nuna baiwa da hazaqa ta musamman da Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) ne. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokacin xalibta ya riqe muqamai a qungiyoyin xalibai na cikin makarantun da ya yi, amma mafi fice shi ne muqaman da ya riqe a Jami’a. A shekarar 1978 ya zama babban sakataren qungiyar xalibai musulmi “Muslim Students Society” (wato MSS a taqaice) a jami’ar Ahmadu Bello, sannan daga baya ya zama mataimakin shugaban qungiyar ta MSS na qasa baki xaya mai kula da harkokin qasashen waje a 1979. Karatunsa na Addini : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso ne a gida na ilimi da addini, gidansu gidan malamai ne masu riqo da addini da koyarwar musulunci, dan haka Shaikh ya taso ne da karatun addini wanda ake kira “Karatun Zaure”. Ya fara karatun Alqur’ani ne a gaban mahaifinsa tun yana xan shekara huxu da haihuwa, ya kuma fara karatun ilimin Nahwu ne a wajan kakarsa Malama Hajara, wacce ake wa laqabi da “Mai Karatu”. Tun Shaikh yana qarami ya yi karatun addini mai zurfi, domin ya kasance yana haddace duk karatun da aka yi masa, har ma yana haddace karatuttukan na gaba da shi da aka yi a gabansa. Ya yi karatu a gaban manyan malamai da dama a birnin Zariya. Kusan ya karanta duk wani littafin addini da ake karantawa bisa tsarin karatun zaure, kuma ya karanta dukkanin fannonin ilimi da ake karantawa a Zaure, kama daga karatun Alqur’ani, Fiqhu, Usul, Hadisi, Tarihi, Luga, Sarf, Aroud, Nahwu da sauransu. Ya yi waxannan karatuttuka ne a gaban mahaifinsa Malam Yaqubu, da kakarsa Malama Hajara Mai Karatu, da fitattun gidajen ilimi na Zariya, daga ciki ya yi karatu a gidan Ladanai, da wajan Malam Sani Abdulqadir Fateh, da Malam Sani Na’ibi, da Malam Isa Kwarbai, da Malam Ibrahim Nakakaki, da Malam Aminu na Madaka da sauransu. Sannan ya zurfafa karatun fannonin ilimi a zamansa na Kano a gaban Shaikh Nasiru Kabara, da Shaikh Isa Waziri (babban limamin Kano), da Malam Nuhu limamin Unguwar Yola, da Malam Datti Ahmad (qwararren malamin Luga da Adabi), da Malam Ibrahim Babarbare, da kuma Shaikh Abdur-Ra’uf Usman (wani malami xan qasar Masar). Duk waxannan masana Shaikh (H) ya yi karatuttukan fannonin addini ne a wajansu. Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ci gaba da halartar gaban manyan masana da malamai yana zurfafa bincike akan mas’alolin addini da faxaxa Bahasi a qasasen waje. Misali; ya yi karatu na tsawon lokaci a qasar Ghana, a gaban wani babban masani xan qasar Iran Sayyid Tabataba’i. Sannan tun a shekarar 2000 har zuwa 2015, kusan duk shekara yana zuwa qasar Iran na tsawon wata biyu dan zurfafa karatu a gaban manyan malamai da masana fannonin ilimi daban-daban. Yana karatu mai zurfi a fannonin nazari da bahasi akan wasu mas’alolin addini, tare da zurfafa karatu a fannonin ilimin Falsafa, Irfani, Manxiq, Usoul, Shari’a, da sauransu. Shariftakarsa : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sharifi ne, wato jikan Manzon Allah (S) ne ta nasabar mahaifinsa, wannan dalilin ne ya sa ake ce masa ‘Sayyid’ wato Sharif kenan a Hausance. Salsalar nasabar Shaikh Zakzaky ta tuqe ne ga jikan Manzon Allah Imam Hassan Al-Mujtaba (AS), kamar yadda Shaikh xin da kansa ya tabbatar a “Decumentry” da gidan talabijin xin qasar Indiya ‘MAULA-TV’ ya yi a kansa a shekarar 2015. Ya ce “Asalin iyayenmu sun fito ne daga Magrib (Morocco kenan ta wancan lokacin)…. Sun tashi daga sassa zuwa sassa har suka zauna a Mali, Malin da ba Malin yanzu ba. Ana cewa suna daga cikin Sulala xin Imam Hasanil-Mujtaba (AS), wanda suka zauni nan qasar Magrib tukuna suka gangaro suka zauni Mali, sannan suka gangaro suka zo nan (Nijeriya)”. Tun kafin Shaikh (H) ya bayyana shariftakarsa a fili, an samu wasu masana da suka sha cewa shi jinin Manzon Allah (S) ne, sai dai Shaikh Zakzaky (H) bai shelanta Shariftakarsa ba sai a wajajen shekarar 2004, bayan ya yi tafiya takanas zuwa qasar Mali don sada zumunci ga danginsa da kuma qarasa bincike akan nasabarsa mai alfarma. A ranar da Shaikh Zakzaky (H) ke ayyana siyada ko shariftakarsa a wajan wani taron Maulidin Sayyida Zahra (SA) da ‘yan uwa mata suka shirya a Fudiyya Islamic Center (F.I.C Zaria), ya karanto ruwaya da ke cewa; “Allah ya la’ani wanda yake shi tsatson Annabi (S) ne amma ya voye nasabarsa, sannan ya tsinewa wanda ya nasabta kansa ga tsatsontaka da Manzon Allah (S) alhali qarya yake yi”. A fakaice, Shaikh (H) ya nuna cewa lalura ce ta sa zai ayyana Shariftakarsa ba don alfahari ko neman xaukaka ba. Tattare da haka, Shaikh (H) ya nuna cewa ba zai sa baqin Rawani ba, saboda a al’adar mutanenmu (Hausawa), baqin Rawani bai da kima, domin bayin Sarakunan gargajiya ne ke sanya shi, dan haka mu anan ba zai dace jikan Annabi (S) ya sanya baqin Rawani ba, maimakon haka, sai Shaikh (H) ya ce zai riqa anfani ne da “Koren Qyalle” na ratawa a wuya, wanda zai zama shi ne alami na Siyadar jikokin Manzon Allah (S) a wannan qasa tamu. Wannan shelanta Shariftaka ta Shaikh Zakzaky (H) ta vuvvugo da abubuwa da dama na raya al’amarin nasaba ga Manzon Allah (S), da bada kima ta musamman ga jikokin Annabi (S) a wannan al’umma tamu. Istibsarinsa : Duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tsatson Manzon Allah (S) ne, to amma yanayi na Biy’a (Inviroment) ya sa an haife shi a cikin Sunni, kuma hatta karatuttukan addini da ya taso da su na Mazhabar Malikiyya ne ta Ahlis-Sunnah. Babu tabbataccen batu game da takameme lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi riqo da Mazhabar Ahlul-Bait (AS), to amma ta bayyana ga mutane cewa Shaikh yana bin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne a shekarar 1980, a lokacin yana da shekaru 27 da haihuwa. Almajiransa (wanda kusan baki xayansu Ahlis-Sunnah ne) sun soma gunaguni game da yadda suka ga Shaikh xin ya soma yin wasu abubuwa sabbi da ba su sani ba a cikin Alwala da Sallarsa a wancan lokacin. Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya tava bada labarin wannan rashin fahimta da sashen almajiransa suka nuna a wancan lokaci, wanda hakan ke tabbatar da cewa ya fara fitowa fili yana aikata koyarwar Ja’afariyya a ibadarsa ne tun a 1980, ya ce; “Na san tun 1980 lokacin da aka yi “Funtua Declaration” akwai waxanda suka zo suka same ni, cewa sun ga na yi Alwala amma na shafa qafa ne, sai na qyale, sai wani ya ce musu; ai shi Shi’a ne, shi ya sa yake shafa a qafa, amma ni ban ce musu komai ba, (sai) wani ya ce ya ga ina Qunuti ina xaga hannu, shi ma na qyale ban ce masa komai ba, wani kuma ya ce ya ji ni ina Tasbihi a Ruku’u a bayyane, shi ma sai na qyale, duk dai na qi in amsa masu. “Wani lokaci kuma mun tafi Sakkwato a dai cikin shekarar 1980, sai nai Sallar Azuhur da La’asar, sai na karanta “Bismillahir-Rahmanir-Raheem” a bayyane, wani sai ya tambaye ni, ya ji a cikin Sallah na yi Bisimilla a bayyane, sai na ce masa e, Manzon Allah (S) ya kasance yana yin haka, saboda su mutane akan wannan, sai su yi faxa, ko kuma su ce addininka daban ne, saboda haka ni ban so tun farko mu fitinar da mutane (ba)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 154). A wani zama na Khass da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi da wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori a wancan lokaci, ya bayyana musu cewa; “Ana jira in ce ni Shi’a ne domin a tarwatse, to, ni Shi’a ne! Tun da can ni Shi’a nike akai, a Shi’ar ka sanni, in ba ka sanni a haka ba to ba ka da basira! Saboda haka a Shi’a nike, kuma Insha Allah a Shi’a zan mutu, kuma ina fata Allah ya tasheni da Shi’a a ranar Qiyama, ya kai ni mokomar Shi’a!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 155). Kenan, a bisa wannan jawabi, duk wanda ya fahimci Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), to ya shigo ne ya samu Shaikh (H) a bisa aqidar Shi’a da Wila’a ga Ahlul-Bait (AS) da kuma biyayya ga koyarwarsu, amma saboda maslaha ta Biy’ar da yake rayuwa a ciki, da kuma tausayin kar mutane su fitinu su nesanci tafarkin tsiransu, ya sa Shaikh (H) bai bayyana wannan aqida da Mazhaba ta Ahlul-Bait (AS) a fili ba, ya bar abin ga kansa kawai, sai da yanayi ya kyautata sannan ya shelanta tare da ayyana tafarkin da yake riqo da shi a fili, wanda sakamakon hakan ya sa miliyoyin almajiransa suka rungumi aqidar ba tare da qyama ba. Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya zama mutumin da ya fi kowa nasarar canza akalar aqidar miliyoyin mutane daga Sunnah zuwa Shi’a a tarihin Musulunci baki xaya! Uwargidansa : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da mace xaya, wannan kuwa ita ce Malama Zeenatuddin Ibraheem, ita ce mahaifiyar duk ‘ya’yansa, wato daga gareta zuriyarsa ta samu. An haifi Malama Zeenatuddin ne ranar 14 ga watan Ogusta na shekarar 1961, a unguwar Sabon Gari da ke cikin garin Zariya. Sunan mahaifinta Malam Ibrahim, sunan mahaifiyarta Malama Maryam, su huxu ne a wajan mahaifiyarsu kuma dukkaninsu mata, Nafisa Ibraheem, Maryam Ibraheem, Zeenatuddeen Ibraheem da Khadija Ibraheem. Malama Zeenatu ta fara karatun firamare ne a wata firamare ta Mishon da ke Sabon Gari Zariya, daga baya ta koma Firamaren Jafaru, wato St, George Primary School Zaria, daga 1967 zuwa 1973. Daga nan ta tafi “Commercial College, Zaria” a shekarar 1977, ta kammala a 1979, sai ta tafi CAST Katsina, ta shekara biyu a can, daga nan sai ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 inda take karanta fannin aikin Banki, amma ba ta samu damar qarasawa ba sakamakon korarsu da makarantar ta yi saboda harkokin addini a sekarar 1982. Daga nan Malama Zeenatu ta tafi karatu a wata “Hauza Ilmiyyah” da ke qasar Iran, daga shekarar 1982 zuwa 1984. Malama Zeenatu baiwar Allah ce ma’abuciyar hidima ga addini da tsayuwa akan hadafi, mace ce haziqa mai tsananin riqo ga karantarwar addini da fikirar Harka Islamiyya. An shaideta da yawan ibada da kishin addini da tsananin tausayawa mata. Aurensa : Malama Zeenatuddeen Ibraheem ta fara sanin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne a shekarar 1977 lokacin da take karatu a makarantar kwalejin koyon sana’o’i, “Commercial Collage Zaria”, a lokacin Shaikh Zakzaky (H) yana xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, kuma kasancewar yana xaya daga cikin jagororin qungiyar xalibai musulmi MSS (wato Officials), kuma yana xaya daga cikin masu gabatar da jawabai da wa’azozi na qungiyar, a irin wannan jawabai da yake gabatarwa ne Malama Zeenatu ta san shi. Amma Shaikh Zakzaky (H) bai san Malama Zeenatu ba sai a shekarar 1979, lokacin da aka je taron “Islamic Vocation Course” (IVC) na qungiyar MSS a Legos, a nan ne ya fara ganinta, saboda ta zo taron ne daga Zariya, amma ba wata mu’amala da ta shiga tsakaninsu a lokacin. Mu’amala ta fara shiga tsakaninsu ne a birnin Bauchi a wannan shekarar ta 1979, lokacin da aka zo wani taron IVC na musamman, Malama Zeenat ita ce kaxai mace da ta zo wannan taro daga wata jaha, kasancewar daga taron IVC na Legos aka wuce Bauchi kai tsaye, kuma xalibai da yawa ba su san da wannan shiri na wucewa Bauchi daga Lagos ba. Dan haka da Malama Zeenat ta wuce Bauchi daga Legos sai kuxin mota da na guzurinta ya qare a Bauchi, da aka kammala taron, sai ta nemi ganin Shaikh Zakzaky a keve a matsayinsa na xan garinsu (Zariya), ta koka masa qarewar kuxinta, ta nemi ya bata aron kuxin mota, in sun koma Zariya za ta biya shi, sai Shaikh ya bata kuxin da zai wadaceta komawa Zariya da cin abinci da sauran buqatu. Bayan sun koma Zariya da ta samu kuxin ta mayar masa sai ya qi karva, ya ce tun asali kyauta ya bata ba bashi ba, wannan ce mu’amala ta farko da ta shiga tsakaninsu. Kasancewar Malama Zeenat haziqa ce mai basira da qumaji, sai aka riqa gayyatarta taron kevantattun membobin MSS na musamman waxanda Shaikh Zakzaky (H) yake karatun gina fikira (Ideology) da tarbiyyar addini da su. Wannan ganawa ta kevantattu da ake kira EED ana yin ta ne a duk taron IVC da aka je, kuma Shaikh Zakzaky ya fara gayyatar Malama Zeenatu zuwa wannan taro na EED ne a IVC na Wudil cikin shekarar 1979, sai kuma na Funtuwa (wanda Shaikh xin ya shelanta Bara’arsa ga tsarin kafirci) duk dai a shekarar 1979/1980. Bayan tafiya ta yi nisa ne, Shaikh Zakzaky ya bayyanawa Malama Zeenatu cewa yana sonta da aure, wannan ya faru ne a shekarar 1980, to amma sai Malamar ta nuna cewa ba ta fara tunanin yin aure yanzu ba tukunna, sai Malam ya haqura da batun. Amma bayan wani lokaci mai tsawo, sai ta yi ta ganin isharori ta hanyar mafarki na dacewar aurenta da shi, wannan ya sa ta canza shawara, ta niqi gari ita da babbar qawarta a lokacin (Fatimah Yunus), suka je har Kurkukun Enugu (inda Shaikh xin ke tsare a lokacin) a 1981, ta nemi afuwarsa kuma ta nuna amincewarta ga aurensa. An xaura auren Shaikh Zakzaky (H) da Malama Zeenatu ne a watan July na shekarar 1984, wanda ya yi daidai da watan Shauwal 1404 hijira, bayan dawowarta daga karatu na tsawon shekaru biyu a qasar Iran. Zuriyarsa : Allah Ta’ala ya yi baiwa ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta hanyar azurta shi da zuriya mai albarka, domin ya haifi ‘ya’ya har guda tara (9), bakwai daga ciki maza ne, yayin da biyu kuma mata ne. Sai dai azzaluman hukumomin Nijeriya ba su bar mafi yawan ‘ya’yan nasa sun yi rayuwa mai tsawo a duniya ba, domin sun kashe shida daga cikin ‘ya’yansa maza guda bakwai a cikin shekara xaya, kenan, a cikin ‘ya’yansa guda 9, yanzu 3 suka rage, mata biyu da namiji xaya. MUHAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Muhammad shi ne babban xa wato xa na farko a wurin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne a shekarar 1985 (a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban qasa na lokacin Janar Buhari ya yi masa). Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya da qasar Ingila, kuma ya je qasar Iran inda ya karanta darasin “Fasahar Gine-gine” da ake kira “Architecture” a babbar Jimi’ar Tehran (wato University of Tehran) da ke birnin Tehran. Sayyid Muhammad qwararre ne a yaren Turanci, Farisanci da Hausa. Mutum ne mai tsananin shiru da kawaici da rashin son hayaniya, yana da xabi’ar kauda kai ga abin da bai shafe shi ba, yana da kaifin basira da hangen nesa, kuma mutum ne mai taka tsantsan akan al’umuran rayuwa. Ya yi aure a watan Mayu na shekarar 2016, a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya sake yi masa a 2015. NUSAIBA IBRAHEEM ZAKZAKY : An haifi Sayyida Nusaiba ne a ranar 21 ga watan Afirilu na shekarar 1987 bayan fitowar Shaikh Zakzaky daga gidan kurkuku, ita ce ‘ya mace ta farko ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma ta biyu a jerin ‘ya’yansa. Ta yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, ta fara karatun Jami’a a qasar Malesiya, daga nan ta wuce Jami’ar qasa da qasa da ke birnin Dubai na haxaxxiyar daular Larabawa (United Arab Emerate). Sayyida Nusaiba haziqa ce mai basira da hangen nesa, an shaide ta da yawan haquri da kawaici. AHMAD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Ahmad shi ne xa na uku a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 1990. Ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi jami’ar Kimiyya da Fasaha ta “Xhenyang University of Technology” da ke birnin Zhenyang a qasar Chaina, inda yake karanta darasin fasahar sarrafa sinadarai, wato “Chemical Engineering”, yana shekarar qarshe ta kammala karatu a Jami’ar ya yi Shahada. Sayyid Ahmad ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 23 kacal, kuma ya yi shahada sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Qudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya. Sayyid Ahmad ne kwamanda na Mu’assasar Abul-Fadal Abbas. Haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira, yana kama da mahaifinsa sosai a yanayin halitta da hazaqar qwaqwalwa, da yanayin xabi’u. Mutum ne mai tsananin son qananan yara, an shaide shi da jarunta, yawan ibada, da hidima ga addini. HAMEED IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Hameed shi ne xa na huxu a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 17 ga watan Janairu na shekarar 1992, ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi Jami’ar “Zain University of Technology” da ke birnin Xain a qasar Chaina, inda yake karanta darasin qera jirgin sama wato “Aeronautical Engineering”, yana shekarar qarshe ta kammala jami’ar ya yi Shahada. Sayyid Hameed ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra, ya rayu a duniya tsawon shekaru 22 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Qudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya. Sayyid Hameed haziqi ne xan baiwa irin wanxanda ake kira “Genius”. Kafin rasuwarsa an tabbatar da cewa zai iya qera jirgin sama saboda hazaqa. Mutum ne mai tsananin natsuwa da kawaici, ya fi sha’awar rayuwar shiru da kaxaici, yana da qarancin magana, kuma ba ya son hayaniya. SUHAILA IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyida Suhaila ita ce ‘ya ta Biyar a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amma ta biyu a ‘ya’ya mata. An haifi Sayyida Suhaila ne ranar 8 ga watan Agusta na shekarar 1993. Ta yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, ta fara karatu a Jami’ar “Usman Xan Fodiyo” da ke birnin Sakkwato a Nijeriya, amma daga baya sai ta tafi wata Jami’ar qasa da qasa “International University” da ke qasar Malesiya, inda ta karanta darasin “Halayyar xan Adam” wato “Sociology”. Sayyida Suhaila haziqa ce mai fasahar magana, an shaideta da kawaici, qwazo, da himma a fagen addini. MAHMOUD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Mahmoud shi ne xa na Shida a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a makarantarsu xalibai suna kiransa “Gentle Man”, a gida kuma jama’a suna masa laqabi da “Shehu” saboda natsuwarsa da sauqin kansa da riqo da addini. An haifi Sayyid Mahmud ne ranar 20 ga watan March na shekarar 1995. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kafin ya yi Shahada yana aji uku a jami’ar “Al-Mustapha International University” da ke birnin Beirut na qasar Lebanon. Sayyid Mahmud ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan July na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 19 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Qudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya. Sayyid Mahmud mutum ne qwararre a fagen ilimin kwanfuta da sadarwar zamani, haziqi ne mai tawali’u da tsananin riqo da addini, ya fi sha’awar karatun addini fiye da na zamani. An shaide shi da sauqin kai da kyawun hali da kyawawan xabi’u da yawan ibada. An yi hasashen da ya rayu, da shi zai gaji Shaikh Zakzaky (H) a fagen ilimin addini mai zurfi. HAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Hammad shi ne xa na Bakwai a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 1997. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa. Ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da ranar uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 18 kacal. Kafin shahadarsa shi ne kwamandan rundunar qananan yara masu tasowa da ake kira “Kasshafa”. Ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, iya mu’amala, da kula da qananan yara. ALI HAIDAR IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Aliy-Haidar shi ne xa na Takwas a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 15 ga watan Satumba na shekarar 1999. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa. Sayyid Ali yana cikin waxanda waqi’ar Qudus ta 2014 ta rutsa da su, tare aka kama shi da ‘yan uwansa guda biyu aka tafi da su barikin soji aka yi ta azabtar da su, shi ne kaxai ya kuvuta da ransa a cikinsu bayan an yi masa harbi da dama tare da dagargaza qafarsa ta hagu, wanda ya jaza dole sai da aka fita da shi waje aka yi masa aiki. Sayyid Aliy-Haidar ya yi shahada ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 16 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Sayyid Aliy-Haidar haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, son karatu, son wasannin motsa jiki, da sauqin kai a mu’amala. HUMAID IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Humaid shi ne xa na Tara kuma xan auta a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 2001, kuma ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 14 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, sannan ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa. Haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira, an shaide shi da jarunta da rashin tsoro, ga sakin fuska da girmama na gaba. A taqaice, wannan ne tsokaci akan rayuwar ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) guda tara, wanda shida daga ciki suka yi shahada, uku ne kacal ke raye, xaya namiji biyu mata. Muna roqon Allah ya wanzar da zuriyar Shaikh Zakzaky ta cikinsu, Ilahiy Ameen. Fara Da’awarsa : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wa’azi a bainar jama’a ne a wani babban taro da aka yi a makarantar “Provincial Arabic School” da ke unguwar Kwarbai a cikin birnin Zariya. Wannan taro an yi shi ne a watan Afrilu na shekarar 1972 don kafa qungiyar samarin Musulmi, kuma ya haxa manyan mutane ciki har da sarakunan gargajiya. Wannan shi ne wa’azi na farko da Shaikh Zakzaky ya fara yi a bainar jama’a, a lokacin yana da shekaru 19 kacal a duniya. To, amma Da’awa ta fikirar Harka Islamiyyah, wato kiran mutane zuwa ga bin koyarwar addini da qauracewa tsarin jahiliyya, ya fara shi ne a shekarar 1977, wato tun bai fi shekara xaya a Jami’ar ABU ba, sai dai a lokacin yana Da’awa ta sirri ne ba tare da shelanta manufarsa a fili ba (Da’awa Sirriyya). Ya shafe shekaru uku a wannan mataki na Da’awa ta sirri (1977-1979), sa’annan daga baya ya shelanta manufar Da’awarsa a fili a farkon shekarar 1980 a Funtuwa. Shaikh Zakzaky (H) ya shelanta Da’awarsa da manufarta a fili ne cikin watan Jimada-Ula na shekarar 1400 Hijira, wanda ya yi daidai da watan Yuli (?) na shekarar 1980. Ya shelanta wannan Da’awa ne a wani babban taro na qungiyar xalibai musulmi ta qasa “Muslim Students Society” (MSS) a garin Funtua. A jawabin ya shelanta miqa wila’arsa ga Allah da Manzo (S), tare da Bara’a ga duk tsarin da ya savawa nasu, ya kuma shelanta qyamarsa ga zalunci da azzalumai. Wannan bayyana Da’awa da ya yi ita ake kira “Shelar Funtuwa” wato “Funtua Declaration” a turance. Bayan shelanta Da’awarsa a taron xalibai na Funtuwa, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi wa’azinsa na farko ga al’umma ne a wani gangamin wa’azi da aka yi a masallacin Kwarbai dake Zariya a cikin watan Rajab na shekarar 1400 Hijira (1980), wanda shi ne wa’azi na farko xauke da fikirar Harka Islamiyya da Sheikh Zakzaky (H) ya gabatar wa mutanen gari. Bayan shelanta wannan qira nasa ya fuskanci tsangwama mai tarin yawa ta fuskoki da vangarori da dama, kama daga azabtarwa daga vangaren hukuma, da kuma matsin lamba daga dangi da makusantansa. A wani jawabinsa yana cewa; “Wani ma ya ce min “ba za ka koma Jami’a ka yi karatu ba!” (sai) na ce masa; to ai wannan aikin da kake so na yi akwai masu yi, amma wannan (Da’awa) da nake yi ba mai yi! Saboda haka gara wannan shi ma a tsaya a yi shi” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 18). Dalilin Fara Da’awarsa : Kowa zai so sanin yaya aka yi Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) ya fara wannan Da’awa tasa, wato meye dalili, ko ya aka yi tunanin fara yin Da’awar ya zo masa? Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha amsa wannan tambaya ga ‘yan jaridu, yakan ce, shi a farko bai tava tunanin zai zama mai Da’awa ko ya zama malamin addini ba, tunaninsa shi ne in ya gama karatunsa na boko zai zama ma’aikacin gwamnati ne ko malamin jami’a, domin rayuwar ma’aikatan gwamnati da ta malaman jami’a tana burge shi, rayuwa ce ta natsuwa wacce ba hayaniya a cikinta, kuma shi yana sha’awar rayuwa ta kaxaici da natsuwa, ba ya son a san shi ko ya zama wani fitaccen mutum, domin ba ya son hayaniya da xawainiyoyi da yawa. To, ya aka yi tunanin Shaikh Zakzaky (H) ya canza daga zama ma’aikacin gwamnati ya koma malamin addini mai Da’awa da gwagwarmaya? Shaikh Zakzaky ya amsa tambayar kamar haka; “Ina iya cewa (zama mai Da’awa da na yi) qaddara ce ta Ubangiji da kuma ayyukan waxanda suke ganin za su ga bayana, su lalata ni, su hana ni magana….. Domin lokacin da na shiga jami’a, akwai qalubale da yawa da suke fuskantar Musulunci, akwai masu aqidar gurguzu a wancan lokacin, (yanzu babu su ya’alla a harabobin jami’a ne ko a ko’ina), a wancan lokacin suna caccakar duk wani abu da ya shafi Musulunci da shi kansa addini gaba xaya. “To, sakamakon na taso da ilimin addinin musulunci, na san suna sukar Musulunci ne kan abin da bai da laifi, suna da aqidar cewa addini kamar qwaya ce mai bugarwa ga mutane, kuma da shi ake fakewa ana zaluntar jama’a, suna kawo misali da sarakunan da suke da mata barkatai da saxakoki, kamar wannan kawai Musulunci ya qunsa, sai muka ga bai kamata mu yi shiru kan irin wannan zarge-zarge ba, dan haka muka fara kare addini, ta haka wannan Da’awa ta fara, wato kare addini, kuma a lokaci guda da koyar da mutane haqiqanin manufofin addinin. “(Domin) mun gano akwai ‘ya’yan musulmi da ba su san mene ne addinin Musulunci ba, wanda masu wannan farfaganda za su iya yaudararsu da waxannan aqidu, hasali ma da dama ko mafi rinjayen (masu aqidar Gurguzun) ‘ya’yan musulmi ne suka dawo suna zargin Musulunci da zaluntar xan adam, alhali a xaukacin tarihin xan adam ba wata aqida ko tunanin da ya tseratar da xan adam kamar Musulunci. “Wani vangare da suka fi kwarmato akai shi ne batun mata, sun zargi Musulunci da tauye mata, amma bisa xan ilimin da muke da shi, mun san wannan ba gaskiya bane, duk da cewa abin da waxansu musulmi suke yi ga mata za a ga kamar haka (musulunci yake), amma wannan ba yana nufin Musulunci ne ya koyar da hakan ba. To, zan iya cewa da haka muka fara (wannan Da’awa) a jami’a, kuma ga alama (abin da muke yin ba ya yi musu daxi), ba su son wannan ci gaba da aka samu, don haka suka fara musguna mana tun muna xalibta, ta kai ga an kama mu an tsare… “Kuma ina iya cewa wannan (Da’awa xin) qaddara ce daga Allah, idan muka karanta tarihin Annabi Musa (AS), za mu ga yana qoqarin kare xan qabilarsa ne (ta kai ga) ya banke ma’aikacin tsaro na Fir’auna ya mutu. Wannan ya tilastawa Annabi Musa (AS) yin hijira, kuma akan hanyarsa ta dawowa ne Allah ya yi masa wahayi da Annabta, wannan qaddara ce ta Ubangiji cewa hakan zai faru. A nawa gefen ma ina iya cewa qaddara ce ta Ubangiji cewa hakan za ta faru, amma ban tava tunanin faruwar hakan ba, ban tava tunanin zan zama malamin addinin Musulunci ba, abin da kawai na yi tsammani shi ne ko dai in zama ma’aikacin gwamnati, ko malamin jami’a, sai na tsinci kaina a abin da nake kai a yanzu”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 02 zuwa 03). Bayan Shaikh Zakzaky (H) ya soma gwagwarmaya da masu aqidar Gurguzu da ke sukar fikirar addini, tare da tuhumar musulunci da kushe shi kan abubuwa da dama, wanda kuma cikin qanqanin lokaci suna ta gurvata aqidun ‘ya’yan musulmi ta hanyar falsafa da hikimomi irin nasu, sai ya zamo in Shaikh Zakzaky (H) ya xauki Alqur’ani yana karantawa sai ya ji kamar da shi ake magana, kamar Allah Ta’ala yana umartarsa ne da ya tashi ya kare addini ta hanyar karantar da mutane haqiqanin addini da nuna musu hanyar shiriya. A wata hira da “Mujallar Gwagwarmaya” Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “A lokacin in na karanci Alqur’ani sai in riqa fahimtarsa ta wata mahanga da ada can ni ban gane ba. Ba zan manta ba, a lokacin har nakan riqa kallon aya sai ina ganin kamar a lokacin aka sauqar da ita… wato sai Allah sanya mini fahimta, in na karanta (aya) sai in ga kamar ana magana da ni ne!” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 09). Kenan, idan mun lura da waxannan bayanai, za mu ga cewa abubuwa biyu ne suka zamo asasin wannan Da’awa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), qoqarin kare addinin Musulunci da fikirarsa, don ceto al’ummar musulmi daga gurvacewar aqida, da kuma qaddarawar Allah Ta’ala wacce ya riga ya zartar, wannan su ne tushe ko mu ce asalin abin da ya sa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wannan qira na Harka Islamiyyah a Nijeriya. Manufar Da’awarsa : Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani yunquri ne na sauqe haqqin Allah Ta’ala, ta hanyar biyayya ga umarninsa da hanuwa ga hane-hanensa, da kuma qaqarin kawo gyara a cikin al’umma don a gudu tare a tsira tare a gobe qiyama. Al’umma ta yi nisa cikin ximuwa da rashin sanin haqqoqin Allah a kanta, an ajiye umarnin Allah a gefe ana ta rayuwa cikin son zuciya da makanta, wannan ya jaza ximbin matsaloli a tafarkin rayuwar al’umma, kama daga munanan xabi’u da halaye, qeta da fin qarfi, zalunci da danniya, jahilci da makanta, rashin sanin addini da rashin sanin alqibla, da kuma uwa uba fuskantar mummunar makoma a gobe qiyama. Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya tashi don kiran mutane zuwa ga addini wanda a cikinsa ne kawai mafitarsu ta ke, a cikinsa ne kawai al’umma za su samu duk abin da suke nema na kwanciyar hankali, yalwar arziqi, tarbiyya da kuma kyakkyawar makoma a gobe qiyama. Dan haka manufar Da’awar Shaikh Zakzaky (H) ita ce xora mutane akan koyarwar addinin musulunci da kyautata hali da xabi’unsu. A jumlace kuma a dunqule, manufar Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne kawo gyara don kyautata rayuwar al’umma, da kuma neman uzuri da tsira gaba ga Allah a ranar alqiyama. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ BABI NA BIYU BAIWA DA XABI’UN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) HAZAQARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun tasowarsa a yarinta fasihi ne haziqi, Allah ya wadata shi da hazaqa da fasaha, domin duk a cikin ‘ya’yan mahaifinsu ya fi su hazaqa. Malam Badamasi Yaqubu shi ne qanin da ke bin Shaikh Zakzaky, ya faxi a wata hirarsa da ‘yan jarida cewa; “Malam ya taso da son karatu, kuma lalle kam duk a cikin ‘ya’yan mahaifinmu ba haziqi kamarsa, domin zan iya tunawa, yana da yayye kamar guda biyu maza, akwai Malam Abdulqadir Yaqubu, akwai Malam Sani Yaqubu, lalle akan gaya musu karatu su manta, mahaifinmu yakan koyar da su karatu su manta, shi Malam bai kai inda suke ba, amma idan sun manta (karatun) shi suke tambaya ya tuna musu… kuma ya iya karatun boko ba tare da ya yi firamare ba, sannan kuma duk wani littafi da ake yi a (karatun) zaure, lallai Malam ya yi shi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 63). Wani lokaci mun kai wa Shaikh Zakzaky (H) ziyara, yana mana hira cikin raha, sai magana ta biyo ta kan yaranta, sai yake cewa: “Lallai ni ina tuna abubuwan da na yi lokacin ina xan shekara huxu zuwa biyar da haihuwa, nakan tuna abubuwa da dama”. A raina sai na ce “Ku kenan masu ‘Extra Ordinary’ Qwaqwalwa, amma mu kam ai sai a hankali!. A wani jawabi Sayyid Badamasi Yaqub ya faxi cewa; “Wani lokaci in ana hirar yarinta, Malam (H) yakan ce mun a lokacin da aka haifeka kaza da kaza ya faru, wato, yana bada labarin wasu abubuwan da suka faru a lokacin da aka haife ni, wanda ya gani da idonsa, alhali tsakani na da shi shekara uku ne kacal”. Tabbataccen abu ne cewa, kaifin qwaqwalwa da hazaqar Shaikh Zakzaky (H) ba su misaltuwa, domin a wani jawabi da ya yi wa qananan yara a taron IVC na shekarar 2013 a Darur-Rahma, ya faxa musu cewa; “Lokacin da ina yaro xan shekaru goma sha, qwaqwalwata kamar mayen qarfe take game da xaukar karatu. Na yi qidaya a Kano a 1973 a (qaramar hukumar) Fagge ta kudu, ta kai ma da a ce wani abu zai samu takardun (su vace), to, duk mutanen unguwar zan iya rubuta su da sunayensu da shekarunsu!” (Al-Mizan, bugu na 1093, shafi na 18). Ba shakka wannan bayani zai haska mana waye Shaikh Ibraheem Zakzaky a qwaqwalwa da fasaha da hazaqa da zalaqa, domin duk wanda zai iya haddace sunayen xaruruwan mutanen unguwa, da yawan shekarun kowannensu, da lambar gidajensu, da kalar addininsu a lokaci guda, to ba shakka zalaqa da fasaha da hazaqarsa ta kai maqura! Haka nan, sakamakon da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a kammala digiri xinsa a shekarar 1979, har zuwa wannan shekara ta 2016 ba a samu xalibin da ya samu irin wannan sakamako a darasin “Economics” a jami’ar Ahmadu Bello ba. Magayaqin Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya ce; “Muna da labarin cewa a jami’a sakamakon digiri xinsa ya yi kyau sosai! Domin ya samu “1st –Class” (daraja ta xaya) ne akan sanin tattalin arziqi (Economics), wanda kusan shi ne mutum na qarshe da ya tava samun irin wannan takardar digiri xin. Domin an ce tun daga kansa ba a qara samun xalibin da ya samu sakamako irin nasa ba har zuwa yau (2016) a wannan jami’a (ta Ahmadu Bello da ke Zariya)”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82). Hazaqar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baiwa ce daga Allah, amma wannan baiwar tasa ta xanfaru da naci na son sanin komai a haqiqarsa. Madaucin Zazzau Alhaji Ahmad Shehu, wanda tare suka yi yarinta da Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “Malam Ibraheem a cikinmu ya banbanta a tsakaninmu, tunda shi ya taso ne da neman ilimi da kuma neman sanin tarihin kowane abu da sanin asalinsa!... Malam shi mai son yin nazari ne akan kowane abu, don duk abin da bai san shi ba, in dai yana da alheri, za ka ga ya nemi iliminsa, sannan ya yi nazari akansa” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 80). Malam Abdulqadir Yaqubu, wanda shi ne babban wa ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cewa; “Muna masu alfahari da wannan qane namu, ya kasance wanda ya fara haddace Alqur’ani a zuri’armu tun bayan kakanmu Malam Aliyu, shi ya cikata addu’a da babban burin da kakanmu ya mutu da shi”. (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24). Wani abu da zai qara nuna hazaqar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne yadda ya iya haddace Alqur’ani da qira’o’i biyu, wato bayan ya dace Alqur’ani da qira’ar ‘Hafs’, sai kuma ya sake dawowa ya haddace shi da qira’ar ‘Warshu’. Wannan ba qaramar baiwa bace, marubucin littafin ‘Malam, Malam ne’ yana cewa; “Malam hafizi ne na Alqur’ani, kuma Alaramma ne, don kuwa da hannunsa ya rubuta Alqur’ani a lokacin da ya zauna a kurkukun Fatakwal na farko daga 1986 zuwa 89”. (Malam, Malam Ne, shafi na 11). Da marubucin littafin “Mujaddadin Wannan Qarnin” ke magana game da hazaqar Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Malam (H) bai tava shiga aji ya koyi “Computer” ba, amma ya san “Computer” fiye da wanda ya shekara biyar yana karanta ta. Kuma duk wani fanni na ilimin zamani in Malam (H) yana magana akai sai ka rantse da Allah a kansa ne ya yi digiri, saboda kawai yadda ya san fannin!” (Mujaddadin Wannan Qarnin, shafi na 49). FIKIRARSA : Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Duk wanda ka gani, to zantukansa da ayyukansa da kuma xabi’unsa sakamakon fikirarsa ne, wato tunaninsa. Ashe kenan fikira sahihiya kuma salimiya, wadda ta yi daidai da koyarwar addinin musulunci tana da gayar muhimmanci ga mutum, tunda zantukansa da ayyukansa sakamakonta ne”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 25). Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani bawa ne da Allah ya keve shi da wata irin baiwa ta sahihiyar fikira ta musamman, duk wanda ya nazarci rayuwar Shaikh Zakzaky (H) zai tabbatar da cewa bawa ne da Allah ya azurta shi da salimiyar fikira da ingantaccen tunani, domin ba ya tufqa da warwara a cikin zantuka da ayyukansa, kullum akan tafarki xaya yake tafiya. Sau da yawa wasu abubuwa kan bijiro bagatatan ba zato ba tsammani, jama’a su ruxe kowa yana neman mafita, amma shi sam baya ruxewa, duk abin da ya bijiro, to Shaikh yana da ingantaccen tunani akansa, kuma yana da qwaqqwarar mafita a game da shi. A shekarar 1990 lokacin yaqin Tekun Fasha tsakanin Iraqi da Amurka, kan al’ummar Nijeriya ya rabu gida biyu, suna ganin yaqi ne tsakanin Musulunci da kafirci, dan haka suka sava kan waye mai gaskiya tsakanin shugaban Amurka Gorge Bush da kuma shugaban Iraqi Saddam Hussain. Wannan ya jawo varaka a tsakanin musulmi ya su- ya su, wanda har ya kai qungiyar Izala ta rabu kashi biyu, masu goyon bayan Amurka, da kuma masu goyon bayan Saddam Hussain. Adaidai lokacin da ake wannan ruxani, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fito fili ya yi wa al’ummar musulmi bayani cewa wannan yaqi bai da wata alaqa da Musulunci, kawai savani ne aka samu tsakanin karen farauta da ubangidansa, faxa ne na kare muradi da kuma qoqarin cimma wani muradin, ba faxa ne tsakanin musulunci da kafirci ba. Wannan abu ya jawowa Shaikh Zakzaky (H) hujumi daga malamai, amma daga qarshe bayan kammala yaqin sai jama’a suka gano lallai matsayar da Shaikh Zakzaky ya xauka ita ce gaskiya! ,Haka nan a shekara 1999, bayan kafa mulkin farar hula a Nijeriya, gwamnonin wasu jihohi na Nijeriya qarqashin jagorancin gwamnan Zamfara Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, sun qirqiro batun Shari’a, inda suka ce za su riqa hukunci da Alqur’ani maimakon hukunci da Kwansitushin a jihohinsu. Wannan ya ja hankalin ximbin al’ummar Nijeriya, musulmi suka fito qwansu da qwarqwata suka nuna goyon bayansu kan hukunci da Alqur’ani, su kuma Kiristoci suka ja daga a gefe guda suka ce ba su yarda ba. A tsakanin wannan hayaniya, Shaikh Zakzaky (H) ya fito ya yi wa al’ummar Nijeriya jawabi, ya nuna musu cewa sam ba ta hanyar siyasa ake kafa gwamnatin musulunci ba, shari’a da Alqur’ani yana da matakai da marhalolin da ake bi kafin a samar da shi, dole sai an bi sunnar Manzon Allah (S) kafin a samar da duk wata gwamnatin musulunci a kowane zamani. Ya ce wannan siyasa ce kawai ta yaudarar mutane da xauke hankalinsu daga abin da ya kamata a yi musu na kyautata rayuwa da samar da cigaba, domin Shari’a a qarqashin tsarin kafirci mai cikakken iko, abu ne da ba zai tava yiwuwa ba! Nan da nan malamai suka yi masa caa suna sukarsa da aibata matsayarsa, amma bayan shekara xaya kacal da qaddamar da Shari’ar, sai mutane suka gane cewa ashe lallai an yaudare su ne an wawaitar da qwaqwalensu, ba wata shari’ar musulunci da ake yi a jihohin sai shegantakar ‘yan siyasa kawai. Daga baya wasunsu suka gaskata Shaikh Zakzaky (H) suka jinjinawa matsayarsa da zurfin fikirar da Allah ya yi masa. A lokacin da Amurka ta kai hari kan tagwayen benayen cibiyar kasuwanci ta duniya (World Trade Center), da cibiyar tsaro ta Pentagon a 2001, da yake kafafen yaxa labarai sun xora alhakin harin kan wasu musulmi qarqashin Usama bin Ladin, al’ummar musulmin duniya musamman Nijeriya sun yi tsalle suna murna da farin ciki, malaman addini musamman Wahabiyawa suka rinqa kwatanta aikin a matsayin babban jihadin addini, suka rinqa yabawa Usama tare da nuna goyon baya da jinjina a gare shi. Amma ta vangaren Shaikh Zakzaky (H) tun washegarin ranar da abin ya faru, wasu sashen almajiransa suka kira shi a waya don jin matsayinsa game da abin da ya faru, nan take ya ce masu; Ai kar ku ruxu da wannan abin, wani makirci ne na yaqi da musulmi da Musulunci Amurka da Isra’ila suka kitsa! Shiryayyen shiri ne na yaqi da addini, su suka kitsa harin, ba wani wanda ya kai musu hari!”. Wannan ya nuna yadda Allah Ta’ala ya kimsa shiriya a fikirar Shaikh Zakzaky (H), ta yadda ba a ruxarsa balle a wawitar da qwaqwalwarsa. Haka nan, a shekarar 2009, ba zato ba tsammani, sai ga wani makirci na qoqarin rage yawan musulmin Nijeriya ta hanyar kisa. Kwatsam wata qungiyar ta’addanci da ta kira kanta da suna “Ahlis-Sunnah Lidda’awati Wal-Jihad” wacce aka fi sani da “Boko Haram” ta bayyana, wai manufar qungiyar shi ne kafa gwamnatin musulunci. Amma maimakon qungiyar ta yi jahadin kawar da gwamnatin zalunci ta Nijeriya, sai kawai ta vuge da ayyana arewacin Nijeriya inda musulmi ne tsantsa a matsayin cibiyar jihadinta ! Kuma a jihadin ta’addanci da ‘yan qungiyar ke yi, suna kashe kowa da kowa ne, suna kashe manya da yara, maza da mata, jarirai da marassa lafiya, suna kashe dabbobi da lalata gonaki da qone duk garin da suka kama qurmus! Suna kai hare-haren Bom a masallatan Juma’a da na “Khamsu-Salawat” adaidai lokacin da ake Sallah, su kashe duk masallatan. Suna kai hare-haren Bom da na kisan gilla a kasuwanni, da asibitoci, da tashoshin mota, da wuraren cin abinci, da wuraren bukukuwa, da gidajen Sinima, da wuraren qwallon qafa, da gidajen mai, da bankuna, da duk inda mutane ke taruwa, kuma a dukkan hare-haren da suke kaiwa sama da kashi 90 na mutanen da suke kashewa musulmi ne, amma wai jihadin Musulunci suke yi! An ruxi mutanen Nijeriya cewa da gaske wata qungiyar musulmi ta “Ahlis-Sunnah” ce ke yin wannan aika-aika, kuma jama’a duk sun yarda. Amma sai ga Shaikh Zakzaky (H) ya fito fili ya yi wa mutane jawabi, inda ya ce “Boko Haram” qarya ce! Dirama ce kawai jami’an tsaron Nijeriya da haxin guiwar CIA da MOSSAD na Isra’ila suka shirya don shafe al’ummar musulmin Nijeriya daga samuwa, da mallake kafofin arziqin Nijeriya, da kuma vata musulunci a idon duniya, ba ruwan musulunci da wannan aikin, aiki ne kawai na ‘yan mulkin mallaka da masu shan jinin raunana! Shaikh Zakzaky (H) ya ambaci misalai da shaidu masu yawa da ke tabbatar da cewa “Boko Haram” shiri ne tsararre na kafircin duniya da ke samun goyon bayan gwamnatin Nijeriya, wannan ya sa ximbin al’ummar Nijeriya sun farka daga mayen da aka sa qwaqwalensu a ciki, suka gane cewa “Boko Haram” qarya ce, wani makirci ne kawai na zaluntar musulmi da sabon salon mulkin mallaka. Wannan misali ne kawai na irin baiwa ta ingantacciyar fikira da Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H), ta yadda shi ba ya ruxuwa da ruxin masu ruxi, ba a iya yaudarar tunaninsa ko cusa masa wahami, ba a iya wawitar da fikirarsa ko a gina shi akan holoqo. A wata magana tasa yana cewa, bisa baiwa ta Allah Ta’ala gare shi, tunda yake bai tava samun matsalar fikira ba, ya ce; “Wannan fikira ba wai wani qoqari ba ne, ko ilimi ko jarunta ko kuma dabara ba, a’a, baiwa ce daga Allah Ta’ala wacce ya yi mana”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 25). Marigayi Dakta Kalim Siddiqy (shugaban majalisar musulmin Birtaniya) ya tava cewa; “Bai tava haxuwa da mutumin da cikin ‘yan mintoci zai gaya maka manufarsa, kuma ka fahimce shi, kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky ba”. (Malam, Malam Ne, shafi na 30). TSABTARSA : Duk wanda ya san Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya san shi da tsananin tsabta da qin qazanta da datti. Mutum ne da tsabta ta zamo xabi’a tamkar jinin jikinsa, duk inda yake rayuwa za ka ga wuri ne gyararre mai tsafta da ban sha’awa, hasali ma Shaikh Zakzaky (H) ne ya raya xabi’ar ado da kwalliya da Fulawa a cikin al’ummar Hausawa, domin akan yi ado da fulawa a motarsa, da wuraren wa’azozinsa, da wuraren zamansa, da ma ko’ina a cikin gidansa. Kuma Shaikh Zakzaky mutum ne da ke tsananin adawa da wari ko qarni ko duk wani abin da ba qamshi ba. Shaikh Muhammad Turi (RA) ya labarta tsananin tsaftar Shaikh Zakzaky a wata hirarsa da ‘yan jarida, ya ce, bayan an kama su tare da Shaikh Zakzaky a lokacin mulkin Abacha, sai aka kai su kurkukun Kaduna, aka sa su a wani waje mummuna mai matuqar qazanta; “Wurin ga shi da qazanta qwarai da gaske, sam wurin ba shi da kyawu, wurin shi ne mafi muni (a cikin kurkukun), sai mutum ya yi (babban) laifi a cikin kurkukun ne za a kulle shi a wurin… nan da nan Malam ya tura waje aka zo da farin fenti (aka fente wurin baki xaya), aka zo da fulawowi da sauransu, wurin babu ko wutar lantarki, aka jawo wuta, nan take dai aka gyara wuri, sai ga shi ya fito fes-fes. “Ina iya tunawa, wata rana (ko Konturola Janar ne) ya kawo ziyara kurkukun, yana shigowa wurin, sai ya cika da mamaki, ya ce; “Ah, wurin nan kamar za a kawo Amarya!” Saboda shi ya san wurin a baya can, shadda ne kawai za a iya cewa wurin, amma sai ya ga yanzu an yi fenti har da Fulawowi da sauran kayan qawata wuri, nan fa ya jima yana cike da mamaki, to shi ne sai Malam yake cewa; “Shi wannan bai san akwai mutanen da idan aka sanya su a shadda, shaddar nan sai ta yi qamshi ba?”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 100). “Ka duba ka ga yadda Malam ya gyara inda ya zauna a gidan yarin Kaduna, ya yi fenti a wurin, ya shuka filawa, ya ja wutar lantarki, har wadoji na cewa wurin ‘Presidencial Villa’ wato “Fadar Shugaban Qasa”. (Malam, Malam Ne, shafi na 11). Rayuwar Shaikh Zakzaky (H) gaba xayanta cike take da qamshi da tsafta, xakinsa qamshi, falonsa qamshi, gidansa qamshi, motarsa qamshi, duk inda zai zauna sai an qamsashe shi. A duk sa’adda ya yi “Brush” sai ya yi anfani da “Mouth Freshner”. Komai nasa mai qamshi kuma tsaf-tsaf gwanin ban sha’awa, sam ba ya son wari da datti da rashin tsafta. “Malam mutum ne mai yawan anfani da turare, don Malam ko wucewa ya yi ta wuri za ka sani saboda qamshin turarensa, balle a ce wani abin da ya fito daga hannunsa, qamshi za ka ji yana yi, duk abin da ya tava sai ya yi qamshi. Wata rana matata, Malama Zeenat ta sa ta zubar da ‘Dustbin’ (shara) na xakin Malam, to wallahi qamshi (sharar) take yi!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 10). Mai karatu ka ji fa! Sharar xakin Shaikh (H) ma qamshi take yi! Editan jaridar Almizan Malam Ibrahim Musa ya ce; Shaikh (H) ya tava bani kyautar rediyo qarama ta xaukar magana, rediyon ta daxe a wurina tana qamshi”. Wannan misali ne kawai na tsabtar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H). TAWALI’UNSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) fitacce ne a fagen Tawali’u da qanqantar da kai, sam ba a shaide shi da girman kai ko jiji da kai ba, sai wanda ya kusance shi ne zai iya sanin zurfin tawali’unsa. Misali, duk wanda ke zuwa gidan Shaikh Zakzaky (H) a Gyallesu zaman yamma, ya san cewa Shaikh xin ne da kansa ke zubawa mahalarta zaman Shayi a kofuna a mimmiqa musu su sha, kuma wannan ya zama xabi’arsa. Shaikh Muhammad Turi (RA) yana cewa; “(A zaman da muka yi tare da Shaikh Zakzaky a kurkukun Kaduna), duk lokacin da aka kawo abinci, shi Malam ne ke raba mana abincin. Ba ni mantawa, akwai wani shugaban Wadoji a nan kurkuku xin, wata rana ya shigo haka kwatsam, a daidai lokacin Malam yana rabon abinci, sai ya yi ta mamaki, har yana cewa “Leadership by Example”, yana ta mamaki….. “Kuma wata rana a lokacin irin tarukan makon haxin kan nan, akwai wani malami daga cikin waxanda aka gayyata ya zo, a irin lokacin cin abincin nan, sai ya ga Malam shi da kansa yake xiban nasa abincin yana zubawa a kwanon da zai ci, sai shi malamin yana ta mamaki, har yake cewa; “Ah, ya za ku bari Malam yana xiban abinci da kansa, ba za ku amsa ku zuba masa ba? Haka nan, wata rana mun yi tafiya a cikin dare a wata jar mota, lokacin ina ga ‘Bluebird’ ce, sai muka kafe, sai duk muka sassauko domin mu tura motar, kafin mu ankara, ashe har malam ya sauko ana tura motar tare da shi”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 101). Daga cikin Tawali’un Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yakan ziyarci majinyata daga dangi ko maqwabta ko almajiransa, kuma yakan je ta’aziyyar rasuwa, ko dubiyar marassa lafiya, ko ziyara ga waxanda ke tsare a gidan yari. Xaya daga cikin manyan almajiransa, ya bayyana irin farin cikin da ya ji lokacin da Shaikh xin ya tava kai masa ziyarar ba-zata a kurkukun Benin lokacin da yake tsare, ya ce; “(Daxin da na ji lokacin da Shaikh (H) ya ziyarce ni a kurkukun Benin), Wayyo Allah, ai ban san ma yadda zan misalta abin ba, ai daxin da na ji ba kaxan bane, mance ma inda nake na yi, na manta da komai da komai, kuma har na baro gidan yarin nan tasirin wannan ziyara tana nan”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 111). A wani misali na tawali’un Shaikh Zakzaky (H), Malam Yaqubu Yahya yana cewa; “Akwai wani wuri da ake ce ma Zawiyya (a gefen gidan Malam), Malam yakan xan sauqar da baqi a wurin, ni ma ina daga cikin baqin da ake sauqarwa. To, akwai wani zuwa da na yi, Malam da kansa ya shinfixa mani Katifa, ya xauko zanin gado ya sanya mani, ya kukkunna mani fitila, abin ya ba ni mamaki! Haka kuma in na yi bankwana zan tafi, sai Malam ya yi mani rakiya, sai in ji kamar in nutse qasa (saboda jin nauyi)”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 112). A wata hira da jaridar Al-Mizan, xaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) Malam Dawud Aliyu ya ambaci wani misali na Tawali’un Shaikh xin, ya ce; “Zan iya tunawa, akwai wani lokaci, tun Malam yana Kwarbai, na zo na sami Malam (H) ya fito, akwai wani gida da yake tafiya can wajen yana yin abubuwa na karance-karance da wasu hidimomi, Malam ya xauke ni a mota muka tafi wancan gidan, muka je muka shiga, akwai kayansa da ya jiqa zai yi wanki, na nemi in karva in wanke masa, amma ya hana ni, da kansa ya wanke kayansa ya shanya”. (Shekaru 60 masu Albarka, shafi na 158). Wani tsohon hadimin Shaikh Zakzaky (H) mai suna Abdullahi Manu, ya faxi cewa tun asali Shaikh Zakzaky (H) da kansa yake wanke tufafinsa, ba ya bari wani ya wanke masa; “A bisa al’adarsa, yakan jiqa wanki a bokiti tun safe, sai da yamma sai ya wanke, to in ya jiqa ya fita sai in wanke in shanya masa kafin ya dawo, sai ya yi mun magana cewa ba buqatar hakan, to amma ni sai na kasa bari. Washegari da ya jiqa sai na sake wankewa na shanya, da ya dawo ya gani sai bai ce komai ba, bayan kwana biyu da wankin ya sake taruwa, da ya jiqa sai ya xau bokitin ya shigar da shi cikin falonsa ya kulle, ala tilas na haqura ina gani yana wankinsa da kansa, a garin wannan wankin da yake yi ne ma ya tava samun hatsari da bokiti har ya karye a hannu”. Shi ma Malam Nuraddeen Aliyu Alqaleri (xaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky) ya labarta mana cewa; “A lokacin da Shaikh ke zaune a unguwar Kwarbai a Zariya, na tava zuwa na same shi yana xibar ruwa a bokiti daga Zawiyya yana kaiwa gidansa, sai na je zan karva, na yi na yi in karva amma ya hana ni, ya ce; “Ba damuwa, na gode!”, ya ci gaba da xiban ruwansa da kansa”. Shaikh Zakzaky (H) yana ban ruwa ga filawowin gidansa da kansa, kuma yana bawa tsuntsayen gidansa abinci da kansa, kamar yadda yake shara da dafa abinci ga iyalinsa. Tabbataccen abu ne cewa zurfin tawali’un Shaikh (H) ya kai ga yana yin aikace-aikacen da suka shafe shi ne da kansa, kama daga wanki, xiban ruwa, shara, renon yara, har ma da dafa abinci. Wannan yana nuna sauqin kai da qanqantar da kai irin na Shaikh (H). ZUHUDUNSA : Kamar yadda yake qa’ida cewa, duk wani Malami na Allah ba a rasa shi da zuhudu (wato gudun duniya, ko xaukar duniya ba a bakin komai ba), to shi ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) haka yake, zahidi ne da dukkan ma’anar zuhudu, domin dukkan xabi’unsa na zuhudu ne, tattare da irin yanayi na qasa da al’ummar da yake rayuwa a cikinta. Ga wanda ya san haqiqanin rayuwar da Shaikh Zakzaky ke yi, ya san cewa bawan Allah ne mai zuhudu, ga abin da xaya daga cikin manyan xalibansa ke cewa; “La’alla za ku ga Malam haje-haje da shaddodi, ga mota Marsandi (ko Jif), sai mutum ya zaci ko Malam baida zuhudu, ka tambayi na kusa da shi ka ji, sai a kwana uku ko huxu ba a hura wutar dafa abinci a gidan Malam ba, ba a samu abin da aka xan tava ba, ba kuma za ka gane ba, kuma har yanzu ma maganar nan da muke yi wani lokaci haka ne!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10). Xaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) ya tava labarta cewa; “Wata rana ya samu Rogo, sai ya ga ya kamata ya kai gidan Malam, da ya kai Rogon sai Malam yake cewa; “Allah ya saka da alkairi, yau kwana uku kenan gidan nan ba wani motsi”. (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10). “Kuma sau xaya yake cin abinci a rana, wannan ko ka yarda ko kar ka yarda haka ne, musamman ma mafi yawancin lokuta ranar Juma’a, sai wajan qarfe uku sannan ya karya kuma sai gobe, in kuma tafiya za a yi, za a tafi tunda safe kamar qarfe shida, to ko ma ina ne za a, Malam ba ya karyawa sai an je wannan garin, ko za a kai faxuwar rana ne!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10). Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Malam shi ko abinci bai dame shi ba, don sau da yawa Malam a gida yakan yi wasu kwanaki bai ci abinci ba. Na san wata rana za mu je Maulidi da daddare, sai ya ce; “Ku xan jira ni in jefa wasu ‘yan lomomi, saboda rabo na da abinci tun shekaran jiya”. (Malam, Malam Ne, shafi na 15). “Sannan Malam a gidansa a xakinsa ba ya da katifar da yake kwanciya, ba kuma don bai da kuxin da zai saya ba ne, amma dai shi ba ya zo kwanciya (a duniya) ba ne!”. (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10). Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Malam Zahidi ne mai gudun duniya, ba ka bi na bashin rantsuwa, amma Wallahi! Malam bai da ko katifa a xakinsa na kwana balle Gado! A qasa yake kwana. Da ya je ziyara wata jaha a arewa maso yamma, sai Gwamna ya je masaukin Malam da sassafe don ziyara, da gwamna ya shiga xakin da Malam ke kwance, sai ya tarar da shi kwance a qasa, wannan abu ya yi wa gwamna tasiri ba kaxan ba, shi ganau ne ba jiyau ba, ya ce; “Wannan irin sauqin kai haka!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 28). “Wani mai kuxi ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) tayin gina masa gida mai kyau, sai Shaikh ya ce shi ba ya fatan ya bar komai (na duniya) wanda wani xansa zai gada. Fulotin da xan uwan ya ba shi ma, sai ya ce ba nasa ba ne, na al’umma ne, ko ya mutu ‘ya’yansa ba su da gado akai, to, ka ga ni fa!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 11). Akwai lokacin da a wani jawabi (Shaikh Zakzaky) yake cewa; “Duk wanda ya fuskantar da zuciyarsa ga Allah Ta’ala, zai ga komai (na duniya) wulaqantacce ne, zai ga sutura wulaqantatta ce, zai ga komai a wulaqance, kai, duniya baki xaya ba za ta kai darajar fuffuken quda a wajensa ba”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 32). “(Shugaban qasa na mulkin soja), Janar Ibrahim Babangida, ya shahara da rufe bakin Malamai da kuxin rashawa, watarana sai ya tura wa Shaikh Zakzaky (H) saqon magudan kuxi, amma sai Shaikh (H) ya yi musu gatse irin yadda Annabawa da Mujaddadai suke wa Xagutai. Ya dubi kuxin ya cewa wanda ya kawo saqon; “Ai kuxin ba su kai yadda suka ambata ba”, wanda ya kawo saqon jiki na rawa ya ce; “Wallahi Malam ba a tava komai a ciki ba”, sai Shaikh (H) ya ce; “Na duba ne ban ga Aljannar Allah a cikin abin da ka kawo ba”. Nan take xan saqo ya gane abin da Shaikh (H) ke nufi, sai ya ce; “Allah gafarta Malam, wannan kam babu”, sai Shaikh (H) ya ce; “To, a maida masa abinsa tunda babu Rahamar Allah a ciki, dama ni ita nake nema”. Xan saqo ya kwashi saqon Ubangidansa cikin kunya da qasqanci, yana tambayar kansa ashe akwai Malamin da zai qi kuxi irin wannan?”. (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 21.). Wani abu da zai qara nuna mana zuhudu da tsantseni na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne; wata rana ya yi tafiya zuwa wata qasar waje, bayan ya kammala abin da ya kai shi, da zai dawo gida sai ya je qaton shagon sayayyar kayayyaki na komai da ruwanka, wato “Super Market” don siyo tsaraba da sauran kayayyakin da yake buqata. Ashe lokacin da ya shiga “Super Market” xin wani daga cikin almajiransa na qasar ya gan shi, sai almajirin nasa ya zaga wajen mai karvar kuxi na “Super Market” xin wato “Cashier” ya ba shi katin cirar kuxi na ATM xinsa, ya ce masa “Duk abin da Malamin can ya xauka, ku yi lissafi ka cire a akawunt xina, kar ka karvi ko kwabonsa”, sai ya juya ya fita ya tafi don ma kar Shaikh (H) ya ganshi. Shi kuma mai kula da shagon “Super Market” da yake yana so ya yi babban ciniki, sai ya je ya samu Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; Ya Shaikh, wani mutum ya biya maka kuxin duk abin da za ka xauka, dan haka ka kwashi duk abin da kake so!” Da Shaikh (H) ya ji haka, sai ya fasa sayan duk abubuwan da ya zo da niyyar saya, ya xauki abin share zufa “Handkerchief ” guda xaya rak, ya je wajan “Cashier” ya ce; “Ga iyaka abin da nake buqata!” Mai shago ya ce; “Yallavai ko ba ka fahimci bayanin da na yi ma ba ne?” Shaikh (H) ya ce masa; “Na fahimta sosai”, sai mai shago ya buxe baki yana kallon Shaikh Zakzaky (H) yana mamaki! Ataqaice waxannan abubuwa suna nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya xauki karikitan duniya a matsayin shirme, tattare da cewa a zahiri yana mu’amala da wasunsu, amma baida “Ta’alluq-Qalbiyya” wato xanfara zuciya garesu. TAWAKKALINSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai matuqar tawakkali ga Allah Ta’ala da siqa gare shi, duk wanda ya san zantukansa, to ya san shi da yawan maida al’amarinsa ga Allah. A farkon-farkon Da’awarsa, wani malami ya tava ce masa wannan Da’awa da yake yi gara ya dena ta ya nemi wani abin yi, domin abin da yake kira a kai na kafa gwamnatin musulunci, abu ne da ba zai tava yiwuwa ba samsam! Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; “To, kana nufin akwai abin da ya gagari Allah ne, wanda shi wannan abin Allah ba zai iya yinsa ba samsam? Da ma ba cewa na yi ni ne zan yi ba, cewa na yi Allah Ta’ala ne zai yi, in kuma akwai abin da ya gagari Allah to ka faxa mani!” wannan amsa tana nuna zurfin siqar Malam da Allah Ta’ala ne. Wani abu da zai qara nuna mana zurfin tawakkalin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da tsananin dogaronsa ga Allah shi ne, a shekarar 2014, lokacin da Jami’an leqen asiri na Nijeriya da haxin gwiwar na qasashen waje suka tsananta xane-xanen tarko na qoqarin kashe shi a hanyarsa ta zuwa Hussainiyya wurin karantarwarsa, sai almajiransa na “Dandalin Ahlid-Duthour” suka zartar da shawarar saya masa motar da harsashi ba ya hudawa (Bullet-Proof) don samun kariya daga harsashin maqiya. Har sun tuntuvi kanfanin sayar da motocin a qasar Jamus, sun ma yi ciniki sun gama za su biya, sai labari ya iske Shaikh Zakzaky (H) kan wannan yunquri da sashen almajiransa ke yi na saya masa motar da harsashi baya hudawa don sama masa kariya. Sai Shaikh (H) ya ce musu; Lallai yana godiya bisa yunquri na bada gudunmawarsu ta kariya a gare shi, Allah Ta’ala ya saka musu da alkairi, amma ba buqatar saya masa mota “Bullet-Proof”, domin Allah Ta’ala ne mai kariya kuma yana nan, Insha Allah zai ci gaba da karewa har zuwa wa’adi”. A haka ya rufe wannan batu na saya masa mota “Bullet-Proof”. Babu shakka wannan matsaya ta Shaikh (H) zai nuna mana zurfin tawakkali da tsagwaron dogaronsa ga Allah! A shekarar 2015 jami’an tsaron Nijeriya da haxin gwiwar na Amurka da Isra’ila sun tsananta xana tarko na qoqarin buxewa Shaikh Zakzaky (H) wuta a hanyarsa ta zuwa zaman makokin Ashura na tsawon kwanaki 50 da yake gabatarwa a “Hussainiyyah Baqiyyatullah” da ke birnin Zariya, don ganin sun kashe shi ko ta halin qaqa. Sun yi ta xana tarko don cimma wannan buri nasu, to amma sai Allah ya yi ta kunyata mummunan shirin nasu, duk lokacin da suka ajiye ‘yan ina da kisa akan hanyarsa, sai ya zo ya wuce ba tare da sun yi la’akari ba. Sai suka qara yin wani mummunan shiri na musamman, suka tsara ajiye makasa a wurare da dama, ta yadda in ya wuce waxannan to ba zai wuce na gaba da su ba. Da rahoton hakan ya zo ga Shaikh Zakzaky (H), sai ya yi jawabi ya fallasa shirin nasu, sannan ya tabbatar musu cewa; “Zan ci gaba da zuwa zaman makokin Ashura sai na kai har qarshen watan! Zan nuna muku cewa; AKWAI UBANGIJIN DA KE KARENI! Ba zan tava fasawa ba! kuma hanyar da nake bi nan zan dunga bi (ba zan canza ba)!” (Yaumus-Shuhada, 1436-2015). Mai karatu, kalli zurfin tawakkalin Shaikh a wannan matsayar! Haka nan, a lokacin waqi’ar 2015, bayan sojoji sun kashe xaruruwan almajiran Shaikh Zakzaky (H) da ke ba shi kariya, sun tunkaro gidansa, sai xansa Shahid Hammad ya shiga wajansa ya ce masa; “Mun qiyasta cewa nan da awa xaya sojoji za su shigo cikin gidan nan”. Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; “Mu wannan ba a hannunmu yake ba, mu abin da ke kanmu shi ne mu dogara ga Allah kawai, ba mu san me zai faru nan gaba ba, namu shi ne mu yi iyakar qoqarinmu, kuma mu dogara ga Allah, amma batun yaushe sojoji za su shigo, ba namu ba ne, saboda haka duk wanda ba ya wani abu musamman na taimakawa, to ya ci gaba da addu’a kawai”. Zuwa xan lokaci kaxan sojoji suka iso qofar gidansa suna kisa ba ji ba gani, sai sashen almajiransa suka shiga wajansa suka nemi ya amince su fita da shi ta baya don tseratar da shi daga mummunan nufin sojojin; sai ya yi murmushi, ya ce “Ai ba batun gudu ko vuya, su yi iyakar nasu qoqarin, mu kuma mu dogara ga Allah… in Allah ya tsara mutanen nan za su shigo su qarasa mu ne, to shi ne nasararmu, idan kuma ya kasance za su tsaya ne, to haka Allah ya tsara. Mu dai muna neman afuwa ne a wajen Allah, kuma mu yi addu’a da tunanin muna neman afuwa a wajen Allah. Idan Allah ya tsara zai bar mu mu ci gaba da aiki a tafarkinsa, za mu tsaya, idan kuma za mu tafi ne (mu yi Shahada), to hakan ya tsara mana”. (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1240, shafi na 7). Ana cikin haka, sai wani ya kira shi a waya daga qasar Iran don jin halin da yake ciki, sai ya ce shi yana cikin gidansa bai je ko ina ba, kuma anan zai tsaya ba zai je ko ina ba, Allah ne kawai zai kare shi! “Only Allah Alone Can Deliver me!” Lallai waxannan zantuka na Shaikh Zakzaky (H) suna nuna zurfin tawakkali da maida al’amuransa zuwa ga Allah Ta’ala ne a kowane yanayi. YAQINI DA SIQARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai tsananin yaqini da siqa ga Allah Ta’ala. Yawancin marubuta da manazarta rayuwar Shaikh Zakzaky (H) suna jinjinawa da qarfafa batu akan zurfin yaqini da siqarsa ga Allah Ta’ala. A mafi yawan jawabansa yana tabbatar da cewa ba wanda ya isa ya dakatar da tabbatar addinin musulunci, wato duk da tinqaho da qarfin kafircin duniya, bai isa ya hana kafuwar addinin Allah a wannan zamanin ba, domin a yanzu Allah ya ga damar addini ya xago. A wani jawabinsa na “Yaumul-Arba’in” yana cewa; “Su (azzalumai) suna ganin za su iya hana Allah tabbatar da abin da ya so, saboda suna da bindiga sun iya kisa! To da kisa yana hana addini tabbata da tun a Karbala an kashe Musulunci!” Haka nan, a jawabin “Yaumus-Shuhada” na 2015 yana cewa; Insha Allah kamar addinin nan ya kafu ma daram an gama!” Wato Shaikh Zakzaky (H) sam bai da shakku ko kokwanto akan tabbatuwar addini. Wani abu ma da zai qara nuna mana siqar Shaikh Zakzaky (H) da Allah shi ne; A lokacin waqi’ar Abacha, yana tsare a gidan yari, sai mutanen gidansa suka aika masa cewa, masu gidan haya sun matsa musu cewa su tashi daga gidansu, (wato sun shiga halin da ake cewa halin Lahaula wala Quwata), amma amsar da ya ba su ita ce cewa, “Tunda ku ka ga an matsa mana akan gidan (haya), to insha Allah muna gab da mu soma ba da kyautar gidaje!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 06). Wannan yana nuna siqar Shaikh (H) da Allah ne, domin a lokacin da ake karanta masa tsanani, qunci, matsi, da qalubalen da ake ciki, shi kuma yana bushara da albishir na farin cikin da zai biyo bayan quncin ne! Wannan halin sai waliyyan Allah! Yaqinin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai taqaita akan al’amuran yau da kullum kawai ba, a’a, hatta a ibadarsa yana yin ta ne da cikakken yaqini. A lokacin da gwamnatin Nijeriya ta sa hannu kan wani shirin kashe shi a shekarar 2009. Shaikh Zakzaky (H) ya yi nasiha ga almajiransa a qoqarinsa na kwantar da hankalinsu, a ciki yake cewa; “Alhamdulillah! Allah ya yi min wannan baiwar, na san ko mutum ya qi ni, in dai mun yi yarinta (tare), ya san tun ina yaro na taso ina ibada ne, kuma na san yau shekaru 40 cur ina ibada da YAQINI kamar ina ganin zahiri! Saboda haka tafiya in ta zo ‘Falillahil-Hamd’, an kashe waxanda suka fi ni!”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 176). Wannan jawabi na Shaikh Zakzaky (H) ya nuna zurfin xanfaruwarsa da Allah Ta’ala, da irin siqa da yaqininsa cikin bautar da yake yi, ba mai iya faxin wannan magana in ba salihin bawa ba. HAQURI DA JURIYARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da aka shaide shi da haquri da juriya, misalan haquri da juriyarsa suna da ximbin yawa, amma ataqaice za mu bada misali guda uku kacal; A tsawon shekarun Da’awar Shaikh Zakzaky (H), gwamnatin Nijeriya kai tsaye ko a fakaice ta hanun ‘Yan tauri, ‘Yan Banga, zauna gari banza, Sarakunan gargajiya ko ta hannun malaman Fada, sun sha rusa makarantun almajiransa a wurare daban-daban! An sha abkawa a raunata ximbin almajiransa a garuruwa daban-daban, an sha qona dukiyoyin mabiyansa ba iyaka a lokuta daban-daban, an sha xaurewa kuma ana ci gaba da xaure almajiransa a gidajen kurkuku daban-daban, an kori ximbin almajiransa a wuraren aikin gwamnati, an kori xalibai almajiransa daga manyan makarantun da suke karatu, an mayar da dubban ‘ya’yan mabiyansa Marayu, an mayar da dubban mata almajiransa Zawarawa, an mayar da ximbin masu arziqi a cikin almajiransa faqirai! Amma duk waxannan abubuwa da aka yi masa a tsawon waxannan shekaru kusan 40 bai tava ramawa ba, bai tava cewa almajiransa su xau fansa ba. A shekarar 2014 sojojin Nijeriya qarqashin mulkin shugaban qasa Goodluck Jonathan bisa jagorancin Kanar M.S Oku suka kashe haziqan ‘ya’yan Shaikh Zakzaky (H) guda uku, tare da almajiransa guda 30, sun yi hakan ne da nufin su fusata Shaikh Zakzaky (H) su ingiza shi ga yin bore da tada hankali, amma sai Shaikh Zakzaky (H) ya yi bayani cikin natsuwa da mayar da al’amari ga Allah, ya lallashi almajiransa cewa kada kowa ya mayar da martani ko ya yi wani abu da sunan xaukar fansa. An ce, a ranar da sojoji suka kashe ‘ya’yansa uku, labarin Shahadar biyu daga cikin yaran ya zo masa ne bayan sallar Isha, kuma adaidai lokacin da ya zauna don yin buxa baki da almajiransa. Ya tsiyayi ruwan shayi zai sha kenan sai wayarsa ta yi qara, yana xauka sai aka ji yana cewa “Innalillahi wa Innaa’ilaihi Raji’un!” ya maimaita sau uku. Bayan ya sauqe wayar sai ya shaidawa almajiransa cewa an qara kashe ‘ya’yansa biyu Ahmad da Hameed, nan take gun ya kaure da kukan baqin ciki, amma shi Sheikh (H) babu ko xigon hawaye a idanunsa, ya yi shiru na tsawon lokaci bai motsa ba (alamun yana munajati da Allah), har ya tashi ya shiga gida ba a ga hawaye a fuskarsa ba, duk da tsananin so da qauna da shaquwar da yi da yaran nasa. Wannan juriya da ya nuna sai da ta zama abin tattaunawa a tsakanin almajiransa. Shekara xaya rak bayan haka, wato a shekarar 2015, sai ga bataliyar sojojin Nijeriya qarqashin Janar Tukur Yusuf Burtai, sun zo Zariya takanas suka aiwatar da mummunan ta’addanci akan Shaikh Zakzaky (H) da iyalansa da al’majiransa, inda suka kashe xaruruwan almajiransa, suka qara kashe ‘ya’yansa uku maza, suka kashe yayarsa Goggo Fatimah, suka yi masa ruwan harsashi shi da matarsa Malama Zeenatu, suka qona gidansa bayan sun harbi gidan da Gurneti, suka rusa masa cibiyon karantarwarsa irin su Hussainiyyah Baqiyatullah, Darur-Rahma, Fudiyyah Islamic Center, da Hubbaren mahaifiyarsa da ke unguwar Jushi. Sannan suka kama shi suka tafi da shi a mummunan yanayi, amma bayan ya farfaxo ya samu sauqi daga raunukan da suka yi masa, sai ga shi ya aiko gaisuwa da jinjina ga almajiransa da suka dake akan wannan tafarki na gwargwamaya. Kuma ya yi musu Wasiyya cewa su tsaya akan nizamin Harka Islamiyyah, kar a ce za a xauki fansa, kawai a ci gaba da abin da ake yi da kuma addu’o’in neman sakayyar Ubangiji. Wannan ya nuna yadda Shaikh (H) ke da zurfin haquri da qarfin juriya ne. AFUWARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai yawan afuwa da shanye laifi, yana da yawan kauda kai da bada tazara. Duk wanda ya san shi zai iya bada shaida ga yawan afuwarsa, misali; A lokacin fitinar ‘yan Zuhudu, akwai waxanda suka yi (munanan) maganganu ga Shaikh (H), wasu ma suka yi rubutu. To, daga baya wasu sun farga (da kuskurensu), saboda haka sai suka zo wajen Shaikh (H) domin ya yi musu afuwa, sai ya yafe musu, shi ne ma lokacin da ya zo jawabin rufe Ijtima ya yi magana, a ciki yake cewa; Duk wanda ya san ya ce wani abu gare shi, ba sai ma ya zo ya ce ya yafe masa ba, shi ya yafe masa!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 30). Haka nan, wasu daga cikin almajiransa sun valle masa a shekarar 1993, suka yi masa tawaye, suka riqa sukarsa da aibata shi da yi masa qazafi da sharri iri-iri, amma da ya zo jawabinsa na cikar Harkar Islamiyyah shekaru 25 da kafuwa, sai ya ce; “Ina ‘yan Tawayiyya ku dawo! Duk wanda ya fita (daga cikin Harka Islamiyyah) to muna kiransa ya dawo, qofar da ya gani a wangale ya fita, to yanzu ma tana buxe a wangale ya dawo, in dai ni ne (game da qazafofi da cutarwar da kuka yi mani) na yafe!” “Ka duba ka ga ‘yan Tawayiyya yadda suka cutar da Malam, kai sun yi niyyar kashe shi ma a masallacin Juma’a na Jami’ar Bayero da ke Kano, to amma Malam da me ya saka musu? Lokacin da ya je aikin Hajji, addu’a ya yi musu a Ka’aba, ya ce, “Ya Allah in waxannan suna da rabo a lahira, to ka dawo da su mu ci gaba da abin da muke yi tare, kuma ni na yafe musu duk abin da suka yi mini”. (Malam, Malam Ne, shafi na 16). Haka nan, a wajajen shekarar 2010, an kawo wa Shaikh Zakzaky (H) muryar da aka naxa ta wani mutum da yake nuna yana tare da shi, amma a gefe kuma yake sukarsa yana aibata shi, yana faxin munanan maganganu akansa. Bayan Shaikh ya ji maganganun sai bai ce komai akai ba, ya kauda kai daga abin. Sai sashen almajiransa da ke tare da mutumin suka nuna rashin amincewarsu ga abin da mutumin ya yi, aka soma samun rashin jituwa a tsakaninsu har dai batun ya zo gabansa. A jawabin da ya yi wa almajiran nasa ya nuna musu cewa, wannan abin da mutumin ya yi ba komai ba ne, “Na so a ce ni kaxai na ji waxannan maganganu da mutumin ya yi a kaina, da ba wanda zai san an yi su! Zan xaga qasan filona ne kawai in jefa kaset xin, ba wanda zai ji labari balle a samu rigima, domin ba shi kaxai ne ke irin wannan maganganu ba, suna da yawa, muna da labarinsu, amma ba mu tava cewa komai a kansu ba, mun kauda kai daga garesu, ba za su cutar da mu da komai ba, kowa yana aiki ne don kansa”. Wannan jawabi na Shaikh Zakzaky (H) yana nuna mana zurfin kauda kansa ga al’amura. Sau da yawa in aka yi anfani da wasu wawayen mutanen gari suka abkawa ‘yan uwa, ko suka lalata dukiyar ‘yan uwa, sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce, “In ba don tausayi ba, da sai mu yi musu addu’a” amma don gudun lalacewa da asarar lahirarsu, Shaikh (H) ba zai musu addu’a xin ba, sai dai ya yi akan azzaluman da ke ingizo su. A shekarar 2011 wani xan jarida ya tambayi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ko ya yake ganin mutanen da suka cutar da shi ta hanyoyi daban-daban? Sai Shaikh (H) ya ce: “Ni ina ganin (waxanda suka zalunce ni a matsayin) su mutane ne da sam ba su son canji, suna ganin hakan zai shafe su, mu a namu gefe muna qoqarin jawo hankalinsu, amma su kuma suna son murqushe mu (su kashe mu)… wannan shi ne tunaninsu, a ce ba mu nan, mu kuma a gefe guda ba mu fatan xaya a cikinsu ya mutu, mun fi son su rayu, su fahimci abin da muke qira akai, muna so mu jawo ra’ayinsu ne, amma su suna so su murqushe jikkunanmu ne, mu (kuma) muna son mu rinjayi ruhunansu ne”…Saboda haka in mutum ya lura da mu, mu ba mu xauka wani ne muke faxa da shi ba, gaskiyar magana kenan, mu muna qira (Da’awa) ne, amma wasu ne suke faxa da mu… suna faxa da abin (da muke yi) ne” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 04 da 14). Wannan ya nuna yadda zuciyar Shaikh Zakzaky (H) ke cike da hasken alkairi ga kowa, sam ba ya nufin kowa da sharri, hatta masu gaba da shi, da waxanda suka cutar da shi fatan alkairi yake masu, madalla da irin wannan zuciya ta bayin Allah na gari. ADALCINSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai adalci a komai nasa, sam bai da son zuciya ko fifita kai ko wani abu nasa, misali; A shekarar 1993 wasu sashen almajiransa sun juya masa baya suka yi masa tawaye saboda zargin cewa yana qoqarin Shi’antar da su da canza musu alqibla daga mabiya Sahabbai zuwa mabiya Ahlul-Bait (AS). Bayan sun shelanta valle masa, sai suka lashi takobin sai sun wargaza wannan Da’awa tasa ta kowane hali, suka shiga yin wa’azozi unguwa-unguwa na cin zarafi da aibata Shaikh Zakzaky (H) da Da’awarsa. Da Shaikh (H) ya zo yin magana akansu, sai ya faxi manufofinsu da dalilansu na valle masa, a qarshe sai ya yi addu’a ya ce; “Ya Ubangijin Musa da Haruna! Idan abin da waxannan mutane suke akai, shi ne daidai, shi ya fi soyuwa a gareka, to ka wargaza nawa ka tabbatar da nasu, idan kuma abin da nake yi shi ya fi kusa da daidai, ya fi soyuwa a gareka, to ka wargaza nasu ka tabbatar da nawa!”. Idan mun lura a wannan addu’a ta Shaikh Zakzaky (H) akwai tsabar adalci da rashin son kai a cikinta. Harwala-yau, a wata ganawa ta keve da ya yi da mawaqa a tsakiyar shekarar 2015, Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ba mu ce wannan Da’awa tamu ita ce kaxai hanyar tsira ga mutum ba, shi ya sa ma ba mu kafirta mutane ba, amma abin da muke cewa shi ne, in za ka bar Harkar, to ka tabbata inda za ka je xin ya fi nan inda ka bari, abin da ka bari a nan za ka samu wanda ya fi shi a can inda ka je!”. Ba shakka a cikin wannan zance na Shaikh (H) akwai babban abin la’akari na adalci! HAIBARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bawan Allah ne mai matuqar kwarjini da Haiba, wani mawaqi yana cewa, “Kwarjininsa wane Zaki!”. In kana magana da shi ba za ka iya kallon cikin idonsa ba saboda tsabar Haiba. Sau da yawa mutane kan kasa magana da shi in sun zo gabansa. Ni kaina haka ta tava faruwa da ni, da ma na daxe ina jin ana cewa magana da Shaikh (H) sai an samu Sabati, domin kwarjininsa yana rikita mutane su mance muhimman bayanan da suka zo da su. To, wataran da za mu je ganawa da shi, sai na gama tsara abubuwan da zan faxa masa, na haddace abubuwan tsaf, sannan na yi ta addu’o’in samun Istiqama da rashin ruxewa, amma bayan mun isa falonsa, da ya zo ya zauna ya kalle ni ya ce bismilla, duk sai na manta abin da zan faxa, ina ta kame-kame, ba ya jin ma abin da nake faxa, Haiba da kwarjininsa duk sun lulluve ni!”. Haka nan, wasu da suka je ganawa da Shaikh (H) kan wasu matsaloli, sai mai gabatar da batutuwan ya kasa gabatar da su yadda ya kamata, bayan sun fito sai wasu suka ce masa ya ba ka ambaci kaza da kaza ba? sai ya ce musu; “Hmnn, ba ku san magana da Shaikh (H) ta fi dutsen Uhudu nauyi ba ne? Ai Haibarsa tana rikitawa mutum lissafi”. Wani xan uwa cikin kundin adana bayanansa (Diary), ya rubuta labarin yadda ya fara ganin Shaikh Zakzaky (H) a rayuwarsa, da irin Haiba da kwarjinin da ya kama shi. Ya ce; “Na daxe ina jin labarin wannan Malamin, amma ban tava ganinsa ba, sai na ce lallai ina so in gan shi tunda an ce anan cikin Zariya yake zaune… Da isata gidansa na tarar da wasu mutane (a falo suna zaune)… zuwa can sai Malam ya fito, ina ganinsa jikina ya xau rawa, na ji numfashina ya xauke, wani sanyi ya sauqa a zuciyata. Malam ya zauna ya kalle ni ya yi mani sallama, na amsa masa… tun daga wannan haxuwa ne na ji wani Ruhi na sanin waye ni ya shige ni, wata tsima ta neman ‘yanci ta shige ni, wani so ga Allah da sallamawa dokokinsa ta lulluve ni, na ji ba ni da buqatar in tuna baya!” (Wakilin Manzo a Doron Qasa, shafi na 24-26). Wata rana wani Laccara na “Islamic Studies” ya shigo aji, ya yi karatu akan nazarin ingancin hadisin da ke cewa; Ubangiji na da wasu bayi waxanda da zaran an ambace su sai a girmama Allah (a ce ‘Allahu Akbar’)”. Laccara ya ce; Wasu Hadisai da bayanan Malamai sun tabbatar da cewa, sai “Waliyan Allah na qoli ne ke kai wa wannan matsayi, domin kuwa su Allah ne ke son su har ya mayar da lamarinsu da an ji sunansu ko an gan su sai a tuna Allah”. Sai Laccara ya tambayi xalibai, “A cikin malaman da kuka sani, wa ke da wannan matsayin?” Sai wani xalibi ya ce “Allah gafarta Malam sai shugaban ‘yan Shi’a xin nan! Shi ne saboda sadaukarwarsa ga addini daga an faxi sunansa ba ka sanin lokacin da bakin ka zai girmama Allah”. Sai Laccara ya tambayi xalibin, “Ya sunansa?” xalibin ya ce “Sunansa Shaikh Ibraheem Zakzaky!” ai yana faxin haka sai baki xayan xaliban ajin suka xauka “Allahu Akbar!” daga ranar Laccara ya shiga nazarin rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) don sanin sirrinsa. (Tasarrufi daga littafin Wakilin Manzo (S), 01-27). MARTANINSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne Fasihi mai hikima da hangen nesa cikin maganganu da furucinsa, sam ba ya fusata a yayin da ya fahimci an yi abu ne dan a tunzura shi. Tarihin rayuwar Shaikh Zakzaky (H) cike take da suka da kai farmaki ga Da’awarsa da ra’ayoyinsa da aqidunsa daga Malaman hukuma da duk masu adawa da shi, amma abu mafi armashi shi ne irin raddi da martanin da yake mayar wa masu sukarsa daga lokaci zuwa lokaci, domin martani ne mai cike da Fasaha da Hikima da Juriya, wannan yana cikin abin da yake burge jama’a game da shi. Misali; A shekarun farko-farko na Da’awarsa, malaman hukuma sun yi ta suka da aibata shi da kushe fikirarsa, wani babban Malami ya tava aibata shi a kafafen yaxa labarai cewa; “Su Al-Zakzaky masu cewa sai an yi shari’a da Alqur’ani ‘yan yara ne qanana, kuma ba malamai ba ne ba su da wani ilimin addini mai zurfi!”. Da Shaikh Zakzaky (H) ke mayar da martani ga malamin sai ya ce; “To, ai waxannan abubuwan da aka aibata mu da su ba aibi ba ne, kuma ba su ne ma’aunin da za su nuna mutum yana kan vata ba, domin yarinta ba laifi ba ne, tunda muna raye ai wataran za mu girma, da ma ba a haihuwar mutum a tsoho, daga yaro yake girma har ya tsufa. “Sannan rashin zurfin ilimi ma ba aibi ba ne, ba dai muna karatu ba? To, da sannu wataran za mu zama malamai, aibi shi ne a ce ba ma karatu, kuma muna gaba da ilimi, in mun ga littafi ma yagawa muke yi, wannan shi ne laifi, amma in dai muna karatu, to ai da sannu nan gaba za mu zamo malamai!”. Ba shakka akwai hikima da basira a wannan martani na Shaikh (H), ka yi nazari! Wahabiyawa da Salafawa a shekarar 2002 sun cika kunnuwan jama’ar qasa da farfaganda cewa wai shugaban qasa na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya naxa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a muqamin ‘Shugaban Zaman Lafiya’ na tarayyar Nijeriya, sun yi ta shelanta wannan magana a wuraren wa’azozinsu da kafafen yaxa labaru. To, a wata hira da gidan Rediyon tarayya na Kaduna suka yi da Shaikh Zakzaky (H) sai suka tambaye shi ko zai mayar da martani ga masu wancan iqirari? Sai Shaikh (H) ya ce; “Akwai wani abu da na yi ta ji irin wannan, sai daga baya na fahimci asalin maganar. Akwai Ibrahim Musa Gashash, yana da wata qungiya wacce da turanci ake ce mata “National Tranquility Movement” da Hausa sai aka fassara ta da “Qungiyar Wanzar da Zaman Lafiya”. Wani qila sunan Gashash xin bai saba ji ba, kuma Zakzaky ma bai saba ji ba, sai ya xauka shi Gashash xin shi ne Zakzaky, duk kuma akwai Ibrahim a sunanmu, ina tsammanin daga nan fa aka ce ai Al-Zakzaky shi ne shugaban zaman lafiya! “Har nake cewa waxannan surutan da ake yi, ya kamata in har da gaske ne gwamnatin qasar nan ta yi wata qungiya mai suna “Qungiyar Zaman Lafiya” kuma har ta naxa Al-Zakzaky a matsayin shugabanta. To, ai ya kamata a taya ni murna ne, ba a yi ta yi min surutu ba, sai a ce Alhamdulillah, ka ga yanzu za ka samar da zaman lafiya a qasa. Amma sai ya zama suka suke yi, ma’ana yanzu sun fahimci cewa ita hukuma abin da take yi ba daidai ba ne, bai kamata ya zama wani mutumin kirki yana tare da ita ba, ina tsammanin haka suke kallo, shi ya sa ma suke neman su aibata ni akan cewa ina yi wa hukuma aiki!” (MujaddadinWannan Qarnin, shafi na 36). Kalli yadda Shaikh ya mayar da martani cikin ruwan sanyi da hikima kan wannan batu. Lokacin da aka fara “Tattakin Arba’een” daga kusurwowin Nijeriya guda huxu zuwa Hussainiyya Baqiyyatullah Zariya a shekarar 2011. Qasar ta xau xumi ta hanyar surutai da aibatawa kala-kala daga malaman Wahabiyawa, suka yi ta cewa wannan abin da ‘yan Shi’a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke yi na Tattakin xaruruwan kilomitoci cikin yunwa da qishin ruwa, suna tafiya da qafa suna dukan qirjinsu sanye da baqaqen kaya, bautar da kai ne da azabtar da jikinsu ga aikin banza, wanda baida lada balle la’ada! Da Shaikh Zakzaky (H) yake mayar musu da martani a wani jawabinsa sai ya ce musu; “Ina ruwanku! Me ya dame ku da abin da muka sa kanmu? Da qafar wa muke takawa a Tattakin? Ba da qafar mu bane? Qirjin wa muke duka? Ba qirjinmu ba ne? Cikin wa yake shan yunwa? Ba cikinmu ba ne? A jikin wa muka sa baqaqen kayan? Ba a jikinmu ba ne? Waxanne idanu ne suke yin kuka? Ba idanunmu ba ne? To, meye naku a ciki? Meye naku na qorafi da surutu? Kusa mana ido mana kawai?” Mai karatu, kai ya ka gani? KYAUTARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tamkar ruwan sama yake a fagen kyauta, duk abin da ya mallaka, to na kyautarwa ga al’umma ne. Kyautar Shaikh Zakzaky (H) tana buqatar a yi wallafa ta musamman a kanta, amma tunda komai taqaitawa muke yi, bari ita ma mu taqaita da ‘yan misalsali; A shekarar 2014 sojojin Nijeriya suka kashe manyan ‘ya’yansa guda uku, to, a lokacin da ake zaman karvar gaisuwa ta shahadar yaran, wata tsohuwa ta shigo ta yi wa Shaikh Zakzaky (H) ta’aziyya, bayan ta yi masa ban haquri tare da yi wa yaran addu’ar samun rahama, sai ta sa hannu ta xauko xari biyu ta bayar ta ce a miqa masa. Da Shaikh ya karva ya yi godiya, sai ya sa hannu a aljihu ya ciro adadin wasu kuxi masu yawa ya miqa mata, ya ce ga shi ta sai goro. Tana qirgawa sai ga Naira dubu Ashirin cif! Da wani jikanta ya samu labarin abin da ya faru sai ya ce mata; Da xari biyar kika ba shi, da dubu 50 za ki samu! Domin “Man’jaa’a Bil-Hasanati, Falahu Asharu Amthaliha”. Wani xalibi ya samu takardar izinin shiga jami’a “Admission”, amma sai ya zamo shi da iyayensa ba su da kuxin yin rijista, ga lokaci yana ta qurewa, sai aka shawarci xalibin cewa ya je ya kai kukansa ga Shaikh Zakzaky (H), sai kuwa ya zo ya samu Shaikh ya nuna masa takardar ‘Admission’ xin da ya samu na shiga jami’a amma baida kuxin yin rijista. Sai Shaikh (H) ya ce masa, “Bari in shiga gida in gani ko Allah zai bada mafita”, zuwa can Shaikh ya fito da ambulan a hannu, ya ce ina xalibin nan? Aka ce ga shi nan, ya miqa masa ambulan ya koma cikin gida. Da xalibin ya buxe ambulan xin sai ya ga Naira dubu xari biyu cur! Ya rinqa tsalle yana murna. Ya je ya yi rijista sannan ya sayi mashin na zuwa makaranta, sauran canjin kuma ya kai wa iyayensa. Kyauta a wurin Shaikh Zakzaky (H) ta zama tamkar jinin jiki, domin hatta manyan mutane in sun ziyarce shi ba ya bari su tafi hannu rabbana, sai ya ba su kyautar da ta dace da su, misali; da Ambasadan Iran ya ziyarce shi a gida a shekarar 2014, sai ya ba shi kyautar Alqur’ani rubutun hannu. Da Ambasadan Swiss ya ziyarce shi, shi ma ya ba shi kyautar Alqur’ani don ya yi nazari. Haka nan idan manyan malaman Ahlis-Sunnah sun ziyarce shi, yakan ba su kyautar littafin “Sahifa Sajjadiyya” da sauran muhimman littattafai. Duk dai wanda ya ziyarce shi yakan masa kyautar da ta dace da shi ne. A shekarar 2007 ya sayawa Sarkin Makafin Zazzau da mutanensa makeken gida a unguwar Tudun Wada Zariya, sannan duk lokacin da dandazon makafin suka kai masa ziyara sai ya ba kowannensu magudan kuxaxe. Shaikh Zakzaky (H) ya kasance yana ba matan da yake karatu da su a F.I.C kyautar kuxi akai-akai, kuma suna karatun ne a ranar Talata ta kowane mako, amma bai tava gajiyawa ba, daga lokaci zuwa lokaci sai ya ba kowaccensu kuxi mai kima. Haka nan matan da yake gudanar da karatun Daura da su duk bayan wata biyu, ya kasance yana ba duk wacce ta halarci Daurar kuxi masu kima, har ta kai ga mata sukan ci bashi su biya wasu buqatunsu in sun lura lokacin Daurah ya kusa, ko su ci bashin kuxin mota su zo, don suna da tabbacin samun kuxi muddin Shaikh Zakzaky na gari. TAIMAKONSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya zama babban Bango majinginar bayi a Nijeriya, ya zama Baya mai goya marayu, Shaikh ya zama gatan al’umma baki xaya! Babu mai musun hidimar Shaikh Zakzaky ga al’umma ko da kuwa hassada da qiyayya ta makantar da shi, domin gudunmawar Shaikh ga al’umma ya shafi kowa ta zahiri ko ta baxini, ta kai tsaye ko a fakaice. Shaikh Zakzaky (H) ya koyar da xalibansa hidima ga al’umma, ya nuna musu cewa wajibi ne su yi hidima ga raunanniyar al’ummar da suke zaune a cikinta, domin al’ummar tana buqatar masu yi mata hidima, kuma ya zo a hadisi cewa, “Mafi alherin mutane, shi ne wanda ya ke anfanar da mutanen”. Albarkar wannan karantarwa ta Shaikh Zakzaky (H), dubban almajiransa a garuruwa da dama ke bada gudunmawar jini a manyan asibitoci da qanana don tallafawa marasa lafiya da majinyata. A kowane taro (musamman na Ashura da Maulidi), almajiran Shaikh Zakzaky a duk inda suke suna zuwa asibitoci su bada jininsu kyauta a xiba a sanyawa majinyata maza da mata, yara da manya, kiristoci da musulmi ba tare da nuna banbanci ba. Wannan gudunmawa da suke badawa ta sha tseratar da ximbin rayuka daga salwanta. Haka nan, Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya zayyana wasu ayyukan da ya kamata almajiransa su riqa yi don taimakon al’umma, kama daga gyara maqabartun musulmi, kwashe bola, tsabtace kwata, gyara hanyoyin ruwa, feshin maganin sauro da na kashe qwayoyin cututtuka, bada gudunmawar abinci da kayan masarufi ga raunana da waxanda wani bala’i ya shafa, gina hanyoyin ruwa don magance ambaliya da sauransu. Waxannan abubuwa kuwa sune muhimman ayyukan da wasu Lajanoni na almajiran Shaikh Zakzaky irinsu “Youth Forum” da “Lajanar Hurras” ke aiwatarwa a ko da yaushe cikin al’ummah, wanda hakan ba qaramin kyautata rayuwar jama’ar qasa yake ba. A gefe guda, Shaikh Zakzaky (H) ya sha daqile fitina da tarzoma a tsakanin mutanen gari. Farkon zuwansa unguwar Gyallesu ya samu qungiyoyi biyu na matasa ‘Yan daba suna gaba da juna da faxace-faxace, wanda kusan kullum sai sun yi kisan kai a junansu. Sai Shaikh (H) ya sa aka qira su gidansa, ya yi zama da su, ya yi masu nasihohi masu ratsa jiki, ya sasanta su suka dena kashe junansu. Sannan Shaikh (H) ya hana abkawa kiristoci a lokutan zave ko na hargitsin addini, duk inda almajiransa suke, sukan baiwa kiristoci kariya da ba su mafaka don tseratar da rayukansu a lokacin rikici ko na hargitsi. Haka nan a shekarar 2011 lokacin zaven shugaban qasa, duk da cewa Shaikh Zakzaky da almajiransa ba sa zave, amma ya umarci almajiransa sun ba jami’an zave kariya daga abkawar mutane a duk runfunan zaven da ke kewaye da unguwar Gyallesu da wasu sassa na birnin Zariya. Shaikh Zakzaky (H) ya zamo gatan marar gata a cikin al’umma, misali; A shekarar 1994 wani Sarkin gargajiya a yankin Kudan ta jahar Kaduna ya qwacewa wata tsohuwa makekiyar gonar da ta gada, sai ta kai qara wurin manya amma suka kasa qwato mata gonarta, ta kai qara kotu, kotu ta tabbatar da cewa lallai gonarta ce, amma kawai ta yi haquri dan wanda ya qwace gonar ya fi qarfinta. Tsohuwar nan ta rasa inda za ta sa kanta, alhali tana da ‘ya’ya da jikokin da take so ta barwa gadon gonar. Sai mutane suka ba ta shawarar ta zo Zariya ta sanar da Shaikh Ibraheem Zakzaky halin da take ciki, kuma ta nemi taimakonsa. Da ta zo ta gabatarwa Shaikh Zakzaky (H) shaidunta, da kwafin takardun hukuncin kotu, sai Shaikh da rakiyar ximbin almajiransa ya je garin na Kudan ya ziyarci gonar, sannan ya yi jawabi mai girgiza azzalumai, kuma ya ce ya dawo wa da tsohuwar nan gonarta tunda kotu ma ta tabbatar da cewa gonarta ce. Daga nan azzalumin sarkin garin bai qara iqirarin qwace gonar ba, haka ya haqura! Haka nan, almajiran Shaikh Zakzaky (H) a garuruwa da jihohi da dama sun zama gatan raunana marassa gata a yayin da aka zalunce su ko aka yi musu danniya akan wani muhimmin haqqinsu, wannan ya nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya zama gata ga wannan al’umma. CIYARWARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da ba abin da yake son yi fiye da kyautatawa al’umma, musamman al’ummar wannan qasa tamu da ke fama da quncin rayuwa a vangarori daban-daban. Tun asali Shaikh Zakzaky (H) ya taso ne da burin kyautatawa mutane musamman ta vangaren ciyarwa, domin tarihinsa ya nuna tun yana Jami’a yake ciyar da xalibai da abokansa. Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” a shafi na 94 ya kawo cewa; A lokacin da Shaikh Zakzaky (H) yake xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, xalibai dare da rana suna yin Safa da Marwa zuwa xakinsa don su sha Shayi, ko su ci cincin da dai sauran nau’ukan abincin da yake samarwa, domin a lokacin Shaikh (H) yana sawa a yo cincin kwalla-kwalla a kawo xakinsa, domin xalibai ‘yan uwansa ba sa rabuwa da zuwa xakinsa komai dare don neman abin sawa a bakin Salati. Haka nan, a zaman kurkukun da ya yi a Inugu, ya kasance yana ciyar da sauran ‘yan Fursuna da abincin da ake kawo masa daga maziyarta, xaya daga cikin almajiransa Shaikh Yaqubu Yahya ya labarta cewa; “A wani lokaci mun ziyarci Malam a kurkukun Fatakwal, kuma mun je masa da xan guzuri haka, soyayyen nama ne da sauransu, (bayan mun shigar masa xaki, da ya gani) sai ya ce a maida shi waje, aka dawo da shi waje, su Madara da Bonbita da sauran kayayyaki duk ya sa aka raba wa mutane, har wani (Inyamuri xan fursuna) yana cewa; “Alhaji No Dey Chop, No Dey Sleep!” wato Malam ba ya cin abinci kuma ba ya bacci!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10). KARAMCINSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sarkin karimci ne da Baiwa ga duk wanda ya rave shi, yana da halin girma na kyautatawa kowa fiye da zatonsa. Misalai akan karimcin Shaikh Zakzaky (H) ba su qirguwa, amma bari mu ambaci ‘yan qalilan. Malama Jameela Auwal (uwargidan Malam Mukhtar Sahabi) ta ba mu labarin wani karimci da Shaikh Zakzaky (H) ya yi mata, ta ce; “Lokacin da zan raka ‘yata Maryam Iran bayan xaura aurenta, mun je yin Sallama ga su Shaikh (H), sai ya tambayeni ta ina za mu tashi? Sai na ce masa ta Legos ne, sai ya ce; Gobe da sassafe za ku bar Kaduna kenan tunda qarfe 2 jirginku zai tashi” sai na ce ai yau ne ma za mu kama hanya zuwa Legos, don ta mota za mu tafi, sai Shaikh ya ce; A’a, ai mota akwai wahala, a ce wa Malam Mukhtar ya yi muku bukin na jirgi gobe sai ku tafi, zan turo masa kuxin!” haka kuwa aka yi, ya biya mana kuxin jirgi muka tafi Legos ta jirgin sama, anan na qara tabbatar da cewa; “Sayyidul Qaumi Khadimuhum”. (Dandalin Khairul-Amal na Whatsapp, 2016).  A watan Maulidi na shekarar 1437 Hijira, rundunar sojojin Nijeriya suka farwa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa da ke unguwar Gyallesu a cikin birnin Zariya, kafin su kai ga Shaikh xin sai da suka kashe xaruruwan almajiransa maza da mata har da jarirai. A lokacin wannan ta’addanci na sojoji da ya shafe tsawon yini uku suna yi, sashen mutanen wannan unguwa wacce ke cike da jami’an leqen asiri, sun bada gudunmawa sosai da goyon baya ga ta’addancin da ake yi wa Shaikh xin da almajiransa, wanda hatta wasu marubuta sai da suka kwatanta mutanen unguwar ta Gyallesu da mutanen Kufa, wanda suka ci amanar Imam Hussain (AS). Amma abin mamaki, bayan watanni shida da faruwar abin, watan Ramadan ya shigo, sai ga Shaikh Zakzaky (H) ya aiko daga inda ake tsare da shi cewa; Lallai a rabawa talakawa da raunanan mutanen Gyallesu buhunan abinci na tallafin watan Ramadan da ya saba ba su duk shekara! Hakan kuwa aka yi, aka bi su gida-gida kowa ana ba shi abin da aka saba ba shi na Shinkafa da Masara da Gero da Sukari da sauran kayan masarufi. Wannan ya nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ke maida sharri da alkairi saboda karamcinsa. Wani xan uwa ya labarta mana cewa;  “Wata rana da yamma muna zaune a falon Shaikh Zakzaky (H), sai wani xan uwa mai hali ya ziyarci Shaikh, bayan sun daxe suna hira muna saurarensu, da ya tashi zai tafi, sai ya miqawa Shaikh makullin mota, ya ce; “Ga wata ‘yar mota can na kawo muku Hadiyya ko yara za su yi anfani da ita”, sai Shaikh ya karvi makullin motar ya ce; “Masha Allah, Allah ya saka da alkairi”. Bayan mutumin ya tafi, sai Shaikh (H) ya ce; Motar kuwa ta yi kyau, ina ganin za ta dace da Malam wane (ya ambaci sunan wani xalibinsa da ke zaune a wurin)”, sai ya ce wa wannan xalibi; “Ai wannan motar za ta yi tafiya a Sahara ko?” Kafin xalibin ya amsa sai ya miqa masa makullin, ya ce “To a je a yi ta fama da kuxin mai”. Wannan ba qaramin karimci bane musamman ga wanda ya san cewa ‘ya’yan Shaikh baki xayansu ba wanda ke da motar hawa a lokacin, amma maimakon ya ba su, sai kawai ya ba wani almajirinsa. Haka nan Shaikh Zakzaky (H) duk shekara yana yanka wa almajiransa Ragon layya, wato duk shekara yana yanka Rago ko Saniya a madadin miliyoyin almajiransa da Allah bai nufe su da yin layya a wannan shekarar ba, kuma yana yankawa dukkan raunanan al’ummar musulmin duniya da ba su samu damar yin layya ba Raqumi, kamar dai yadda Manzon Allah (S) ya yi wa al’ummarsa marassa galihu layya. Marubucin littafin “Malam, Malam Ne” yana cewa; “Na san duk sallar Layya sai Malam (H) ya yanka Rago, wato ya yi wa duk “Brothers” (‘yan uwa maza da mata) Layya, kuma ya ba su naman Ragon sun ci” (Malam, Malam Ne, shafi na 10). JARUNTARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) jarumi ne da dukkan ma’anar jarunta, tun asali bai da tsoro, bai da fargaba bare razana, domin tarihi ya tabbatar da cewa tun yana yaro qarami bai san tsoro ba. A wani biki na cikarsa shekaru 45, Shaikh Zakzaky (H) yana cewa, bai san me ya sa shi tun yana yaro baida tsoro ba, duk wani abu mai razanarwa shi ba ya razana shi, ko irin abin da ke faruwa bagatatan xinnan, wanda ke firgita mutane, to shi gabansa ba ya faxuwa. Marubucin littafin ‘Tarihin Harkar Musulunci’ yana cewa; “Akwai ma lokacin da yake cewa idan Akuya za ta ba shi tsoro, to arne ko Azzalumi zai ba shi tsoro, wato tunda Akuya ba za ta ba shi tsoro ba, to, babu wani abu da ya isa ya ba shi tsoro (a duniya!)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 29). A wani jawabi da Shaikh Zakzaky (H) ya yi a ranar “Yaumus-Shuhada” na shekarar 2003 yana cewa; “(Mahukunta) su kan riqa yin wani gadara wai su ce; Wa ya fi qarfin gwamnati?’ To, mun fi qarfin gwamnati! In ta ce qarya ne ta zo! Iyaka dai kurkuku ne da kisa, ya wuce haka ne?....(ba ta yi harbin bane? Ba ga mu ba! Ba ta yi kamun bane? Ba ga mu ba!). To, ba ma kurkuku ba, wallahi tallahi ko da kuna da Jahannama, kuma ko da Jahannamar taku ta kai zafin ta Allah Ta’ala, a shirye muke mu shigeta! Don mun san ita Jahannamar taku mai qarewa ce, ta Allah ko ba ta qarewa. Ta Allah muke jin tsoro ba taku ba!” Ba shakka Shaikh Zakzaky (H) ya gaskata wannan iqirari nasa, domin duk kamun da ake yi masa bai tava gudun kar a kama shi ko ya yi rakin kamun ba, maimakon haka ma, shi nuna jin daxin kamun yake yi. Misali, lokacin da aka kai Shaikh Zakzaky (H) gidan yarin azabtarwa na Kirikiri da ke Legos a shekarar 1984, ya rubutowa ‘yan uwa almajiransa wasiqa, a ciki yake cewa; “Lokacin da ake tuqani zuwa Kirikiri, na ji wani daxi da farin ciki wanda ban tava jin irinsa ba!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 42) Ka ji irin wannan jarunta! Kirikiri fa; Waje ne da ake kai mutanen da ake so a musguna masu, ko a azabtar da su, domin akwai karikitai na azabtarwa daban-daban a ciki. Malam yake cewa; ko sauro mutum ya kashe sai an masa bulala, za a ce masa wai ya damu yaran gwamnati” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 43). Amma da aka kama hanya za a kai shi wurin, shi ne yake cewa ya ji wani daxi da farin cikin da bai tava jin irinsa ba! Wannan wace irin jarunta ce? Sannan bayan fitowarsa daga kurkukun Inugu, cikin jawabin da ya yi wa ‘yan uwa yana cewa; “Wani abu wanda yake shu’uri ne (wato a jiki ake jinsa), wanda sai in kai ma ka ji ne za ka iya fahimta, shi ne abin da na gani a zamana na kurkuku. (Amma) tunda ba a yarda mutum ya je ya qwanqwasa gidan kurkuku ya ce a buxe masa ya shiga ba, (da ana haka da na yi, to, amma tunda ba a yi), duk ran da aka zo aka kamani zuwa can zan yi farin ciki!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 44). Mai karatu, ka ji mai neman shiga kurkuku, wanda bai tava tsoron xauri a gidan fursuna ba, da me za ka kwatanta jaruntarsa? Shaikh Zakzaky (H) jarumi ne da dukkan ma’anar jarunta, domin lokacin da gwamnatin Nijeriya qarqashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kama shi ta gurfanar da shi a gaban kotu, alqalin kotun Justice Karibi White ya yanke masa hukuncin xaurin shekaru huxu a gidan kurkuku. Bayan an karantawa Shaikh Zakzaky (H) laifinsa da irin hukuncin da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu irin wannan laifi, kafin a zartar da hukuncin, sai alqali ya tambaye shi cewa; “Ko kana da wani roqo (na neman sassauci) da za ka yi ga kotu?” Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ina roqon kotu ne da ta zartar mun da mafi munin hukuncin da za ta iya, ta zartar mun da mafi tsananin hukunci na iya qurewarta! Kar ta sassauta mini!” Sa’annan Shaikh Zakzaky (H) ya fuskanci alqali Karibi White ya ce masa; “Idan kana da zavi tsakanin harbi ko xaurin rai da rai, to ka zartar mun da hukuncin harbewa!” Wannan jawabi ya girgiza alqali da duk waxanda ke cikin kotun, dan ba su tava jin wanda ke fuskantar hukunci ya faxi haka ba a tarihinsu! Jaruntar Shaikh Zakzaky (H) za ta qara fito maka fili ne in ka san cewa; “(Saboda yawan) kame-kame na ba zata (da ake yi masa), sai da ta kai ga Malam a wani lokaci ya kai ga aje wata jaka, a cikinta ya sa sabulun wanka da na wanki, man shafawa, turare, (Makilin da Brush), da tufafi na canzawa da dai makamantansu, yake cewa jakar ba ya tava ta, tana aje ne kawai, da an zo kama shi sai dai ya xauketa (ya rataya) ya ce mu je!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 44). A lokacin mulkin sugaban qasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2007), labaran asiri sun yi ta zuwa cewa ana shirin abkawa da kashe jogaran Harka Islamiyyah Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da rahotannin suka yi qarfi sai wasu suka shawarci Shaikh Zakzaky (H) cewa ko zai xan yi hijira zuwa wata qasa kafin abubuwa su daidaita, sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ko Janar aka ce masa Zakzaky zai yi gudun hijira zai ce qarya ne!!” wannan ya nuna jaruntar Shaikh Zakzaky (H) ne a fili qarara! Tabbas Shaikh Zakzaky (H) ya gaskata wannan iqirari nasa, domin lokacin da gwamnatin shugaban qasa Umaru Musa Yar’adua ta shirya jefa Bom a gidansa cikin dare a shekarar 2010, an shawarci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ya bar gidan, amma ya ce wallahi ba inda za shi, sai dai su kashe shi a cikin gidansa, kuma haka aka yi, a cikin gidan ya kwana, Allah Ta’ala ya wargaza mummunar aniyarsu. Haka nan, mummunan harin da bataliyar sojojin Nijeriya qarqashin Hafsan sojoji Janar Tukur Yusuf Burtai, bisa umarnin shugaban qasa Muhammadu Buhari suka kai gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a watan Disamba na shekarar 2015, inda suka kashe kusan mutum dubu kafin su iya kaiwa gare shi, tun kafin su ci qarfin ‘yan uwa an buqaci a fita da Shaikh Zakzaky (H) don tseratar da shi, amma ya ce ba inda zai je, yana nan a cikin gidansa, sai dai su zo su yi masa duk abin da za su yi! Hakan kuwa aka yi, sai da aka shafe sama da awowi 48 ana ruwan wuta, har aka cimma gidansa, aka harbawa gidan Gurneti, gidan ya kama da wuta ya qone qurmus, amma Shaikh Zakzaky (H) yana cikin wani qaramin xaki na dakin shi da iyalansa, qarshe har suka zo kansa suka yi ruwan harsashi suka kashe ‘ya’yansa uku, suka harbi matarsa a sama da wurare goma a jikinta, shi ma suka harbe shi a wurare goma sha xaya a jikinsa, ciki har da cinya da qirji da goshi da idanuwansa biyu har sai da idonsa na hagu ya zazzago ya fito waje, sa’annan suka xauke shi suka tafi da shi rai a hannun Allah! Wannan jarunta irin ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tarihi ya daxe bai ga irinta ba! AMSA ADDU’ARSA : Allah Ta’ala ya yi alqawarin amsa addu’ar bayinsa a yayin da suka roqe shi, tattare da haka bayin Allah managarta addu’o’insu sun fi karvuwa cikin gaggawa da sauri. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin bayin da Allah ke gaggauta karvar addu’o’insu da biya musu buqatar abin da suke nema. Misalin hakan shi ne; A shekarar 1991 an yi waqi’a a birnin Katsina, inda jami’an tsaro suka farwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suka fito muzaharar Allah wadai da zagin Manzon Allah (S) da wata jarida mai suna “FunTimes” ta  kanfanin “Daily Times” ta yi. Jami’an tsaron sun farwa ‘yan uwa suka yi ta dukansu da kulake da gindin bindiga, inda suka raunata da dama, suka kwashe su cikin jini suka je suka kulle ba tare da sun kai su asibiti don magani ba. Bayan kwana biyu da faruwar lamarin, sai ‘yan jarida suka tuntuvi kwamishinan ‘yan sanda na Katsina a lokacin, wato Saminu Daura dan jin halin da ‘yan uwan da ake tsare da su suke ciki. Sai Saminu Daura ya ce duk waxanda ake tsare da su suna cikin qoshin lafiya da aminci, alhali a lokacin ‘yan uwa suna tsare a hedikwata da barikin ‘yan Sanda cikin tsananin galabaita da raxaxin ciwuka da raunukan da aka yi musu ba tare da ba su magani ba. Da Shaikh Zakzaky (H) ya ji wannan hira sai ya yi raddi ga Saminu Daura, ya ce; Idan halin da ‘yan uwa ke ciki shi ne halin qoshin lafiya da aminci, to yana roqon Allah ya ba Saminu Daura irin wannan qoshin lafiya da amincin! Ba a daxe da wannan addu’a ba Saminu Daura ya kamu da matsananciyar jinya wacce wasu rahotanni suka ce har haushin Kare yake yi, zuwa xan wani lokaci ya sheqa barzahu. Har wala yau, a Shekarar 1992, jami’an tsaron Nijeriya sun kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a birnin Kano lokacin da zai je wani taro a qasar Ingila. Suna kama shi suka yi awon gaba da shi zuwa kurkukun Dodon-Barrack na Legos, da nufin tsare shi har illa masha Allah. Shi kuma Shaikh (H) a lokacin yana cike da shauqin halartar wannan taro na London. Dan haka yana shiga kurkukun ya xaga hannu ya roqi Allah cewa ya tabbatar masa da wannan buri na tafiya London don halartar wannan taro da kuma haxuwa da ‘yan uwa na Ingila. Addu’ar da ya yi tana da ma’ana kamar haka; Ya Allah, ka sani na yi zaman kurkuku a wuri kaza da kaza, amma daidai da rana xaya ban tava roqonka ka fitar da ni daga cikinsu ba, sai dai da kanka kake fitar da ni a lokacin da ka ga dama. Amma a wannan karon ina shauqin haxuwa da ‘yan uwa na Ingila da ganawa da su, ina so in halarci wannan taro da za a yi, ina roqonka ka fitar da ni da ikonka, “Ya Allah ka gaskata zatona gareka”. Yana yin wannan addu’ar sai kawai umarni ya zo na sakinsa, kuma aka ba shi takardunsa na izinin tafiya, ya kama hanya ya fita zuwa Ingila, duka-duka tsarewar da aka masa a lokacin ta ‘yan kwanaki ce. Sannan, a shekarar 1994, bayan wasu almajiransa sun valle sun yi masa tawaye, sai suka yi gangami suka kafa qungiyar yaqarsa da bishe hasken Da’awarsa mai suna “Jama’atu Tajdeedil Islam” wato JTI ataqaice. Sai ya yi jawabi game da su, ya fayyace musu abubuwan da suke zarginsa da su na aqidar Shi’anci daki-daki. Sannan daga qarshe sai ya roqi Allah Ta’ala cewa; Ya Ubangijin Musa da Harun, idan abin da waxannan mutane suke akai, shi ya fi soyuwa da zama daidai a gareka, to ka rusa nawa ka tabbatar da nasu, idan kuma nawa ne ya fi soyuwa gareka da zama daidai, to ka rusa nasu ka tabbatar da nawa”. Bayan yin wannan addu’ar ba daxewa Allah ya rusa wannan gungu na ‘yan Tawayiya, ya shagaltar da su da kawukansu, suka tarwatse suka dena batun Tawayiyanci suka shagaltu da neman duniya da neman abinci, ya zamanto su da qungiyar ta su ta JTI ba su da wani tasiri a cikin al’umma, hasali ma mafi yawan jama’a ba su san da qungiyar tasu ba. Wannan ‘yan misalai ne kawai na yadda Allah Ta’ala ke amsa addu’ar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). KARAMOMINSA : Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) karamomi masu yawa, waxanda aka sani da waxanda ba a sani ba, domin Shaikh Zakzaky (H) ya kasance mai voye karama da rashin son nuna ta, amma tattare da haka wasu karamominsa kan bayyana ba tare da nufi ba. Misali; Kamun da aka yi masa na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya cikin shekarar 1979, an kulle shi a ofishin ‘yan sanda ne na Zariya, ya shafe kwana uku ba ci ba sha, suka hana shi cin komai, bayan kwana uku sai suka fito da shi da nufin zai amsa wasu tambayoyi, da suka ba shi takarda ya rubuta jawabinsa (Statement), sai da ya rubuta musu shafi tara na amsoshin abin da suka tambaye shi, har su jami’an tsaron suna mamaki, suna cewa dubi rubutunsa mai kyau kamar wanda bai sha yunwa ba! A wata hira Shaikh Zakzaky (H) ya ce, duk da ya shafe tsawon kwanakin bai ci abinci ba, amma shi kwata-kwata bai ji yunwa ko qishin ruwa ba. Wannan karama ce babba! (Rairayowa daga Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 42) A farkon shekarun 90s, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je Umrah, a hanyarsa ta dawowa sai jirgin samansu ya samu matsala, (wasu sun ce da gangan aka so a halakar da shi). Jirgi ya rinqa tangal-tangal, fasinjoji suka rikice suna ihu da neman taimako, amma Shaikh Zakzaky (H) yana zaune a natse akan kujerarsa yana ta karatun Alqur’ani, sam babu alamar damuwa a tattare da shi kamar bai san abin da ke faruwa ba. Da matsalar ta qara muni, hankalin fasinjoji ya tashi matuqa, sai Shaikh cikin natsuwa ya xaga hannu sama ya yi wata gajeruwar addu’a, nan take jirgin ya daidaita, sai ga sanarwa daga matuqa jirgin cewa komai ya yi daidai. Wannan ya sa mutane da yawa a jirgin suka rinqa neman tabarrukin Shaikh (H), har wani a cikin mahajjatan ya ce “Daga yau na zama xan Buraza!” (Tasarrufi daga Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 09). A shekarar 1992, lokacin da aka kama Shaikh Zakzaky (H) a filin jirgin Malam Aminu Kano sa’adda zai tafi Ingila, an kai shi wani wuri ne aka tsare shi ya kwana, washe gari sai aka zo da sabuwar mota aka sa shi a ciki, aka kama hanya ba tare da an ce masa uffan ko an sanar da shi inda za a kai shi ba. To, tun ba a fita daga cikin Kano ba, sai Shaikh Zakzaky (H) ya cewa jami’an tsaron da ke tafiya da shi; “Ku me ya sa ba za ku yi xabi’a irin ta mutane ba! Wannan xabi’a taku ta sava da xabi’a irin ta mutunci, domin ni mutum ne kuka xauko ba Akuya ba, idan za ka saka Akuya a cikin mota ka kai ta Legos, ba ka buqatar ka yi mata bayani, ka ce Akuya zan kai ki Legos. Haka nan idan za ka xauki buhun shinkafa, ba ka buqatar ka ce masa zan kai ka wuri kaza, sai dai ka kai shi kawai. Amma ni mutum ne (ba Akuya ko Buhun shinkafa ba), menene ya hana a jiya ku ce min, an umarceku ne ku hana ni tafiya, kuma yau ku ce, an umarce mu da mu kai ka Legos? Shi kenan!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 45, da tasarrufi kaxan). A wannan abun da ya faru akwai nuna Karama a ciki, domin ba wanda ya ce wa Shaikh Zakzaky (H) Legos za a kai shi, sai ga shi cikin hikima ya faxa musu cewa Legos za su kai shi, kuma Legos xin suka kai shi kai tsaye. Wannan menene in ba Karama ba? A shekarar 1994 a wani gari da ake kira Lushi a kusa da birnin Bauchi, qasa ta kama hannun wani yaro saboda ya qaryata Shaikh Zakzaky (H). Musu suke yi da ‘yar uwarsa, shi yana cewa Shaikh Zakzaky vatacce ne kuma Da’awarsa halaka ce. Ita kuma yarinyar (wacce ‘yar Baffansa ce) tana cewa lallai Shaikh Zakzaky akan shiriya yake, kuma yana kira ne zuwa ga hanya madaidaiciya. Sai suka yi ittifaqi cewa su yi ‘yar qasa-qasa, (wata al’adar Hausawa ce da yara ke anfani da ita don gane marar gaskiya a tsakanin mutane biyu, za a tara yashi ne ko qasa, sai wanda ake tuhuma ya cusa hannunsa iya wuyan hannu a ciki, sai ya yi rantsuwa cewa in ba shi ne akan gaskiya ba to qasa ta kama hannunsa). Sai yarinya mai gaskata Shaikh Zakzaky ta fara sa hannunta a cikin qasa, ta yi rantsuwa, kuma ta ce in ba haka bane qasa ta kama hannunta, tana zarowa sai hannu ya fito. Sai shi ma yaro ya cusa hannunsa cikin qasa, ya yi rantsuwa cewa Shaikh Zakzaky (H) akan vata yake, kuma Da’awarsa halaka ce, in ba haka bane qasa ta kama hannunsa. Abu kamar wasa sai hannu ya maqale, qasa ta riqe hannunsa qam, har sai da aka kawo masa xauki, aka yi aka yi a cire hannu ya qi fita, yaro sai kuka yake yi, sai aka ce masa sai in ya warware wannan rantsuwar ya gaskata Shaikh Zakzaky ne kawai hannun nasa zai fita. Haka kuwa aka yi, yana gaskata shiriyar Shaikh Zakzaky (H) da ya zaro hannun sai kawai ya fito. Jaridar Al-Mizan ta wancan lokacin ta hakaito wannan labari na karamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Haka nan, a wajajen shekarar 1997, an yi wata gobara a gidan wani xan uwa a birnin Gombe, inda gobarar ta cinye komai na xakin gidan amma ta bar hoton Shaikh Zakzaky (H) da ke rataye a xakin, hatta katakon da aka sanya hoton a jikinsa bai qone ba, kuma wannan hoton shi kaxai ne ya tsira a xakin, komai ya qone qurmus. Wannan karama ta qarawa mutane da dama yaqini game da sha’anin Shaikh Zakzaky (H). Haka nan, wani xan uwa da yake neman wata budurwa da aure, ya yi tsananin kamuwa da so da qaunarta, sai ya yi ta yin Istihara yana roqon Allah cewa; Ya Ubangiji, in aurena da wance alheri ne, ka qaddara mun shi cikin sauqi da yalwa, in kuma sharri ne, to ka rusa abin ka hana shi yiwuwa”. Yalai kuwa sai abu ya rushe, yarinya ta kawo sunan wani wanda take so, ya turo iyayensa suka biya sadaki aka sa ranar xaurin aure. Sai wannan xan uwa ya shiga halin qunci mai tsanani saboda son wannan budurwa da yake yi, ya kasa jurewa rabuwa da ita saboda xanfaruwar zuciyarsa da ita, ba ya iya bacci balle cin abinci, komai nasa ya dagule, ya rasa abin da ke masa daxi. Watarana sai ya ce bari ya je majalisin yamma na gidan Shaikh Zakzaky (H) da nufin ko zai manta da damuwar da ke damunsa, kuma ya yi Tawassuli da nufin Allah ya yaye masa qaunar yarinyar nan da ya addabi zuciyarsa. Ya je gidan Shaikh (H) da wuri ya samu wuri a gaba ya zauna, zuwa can sai Shaikh (H) ya fito ya zauna a wurin zamansa, yana gama gaisawa da mutane sai kawai ya kama magana akan Istihara da yadda ake yinta, ya ce; “Da yawan mutane ba su iya Istihara ba, sai su roqi Allah cewa “In abin nan alkhairi ne ka tabbatar mun da shi, in kuma sharri ne ka wargaza shi ka hana shi yiwuwa”. Wani lokaci in abin ba alheri ba ne sai Allah ya hana shi yiwuwa, amma ya bar ka da son abun a ziciyarka. Kamata ya yi mutane su riqa cewa “Ya Allah in wannan abin alkhairi ne ka qaddara mun shi cikin sauqi, in kuma sharri ne gareni ka kore shi daga gareni, kuma ka cire mun qaunarsa da sonsa a zuciyata”. Xan uwan yana jin haka sai kunya ta kama shi, ya duqar da kai qasa yana matuqar mamakin wannan al’amari, domin shi dai bai faxawa kowa abin da ya kawo shi ba, bai kuma faxawa Shaikh (H) wannan labarin ba, amma ya aka yi Shaikh (H) ya iya fahimtar damuwarsa? Wannan tambayar har zuwa yau bai samu amsarta ba, amma dai daga wannan rana ya samu waraka daga ciwonsa na soyayya. Babu shakka duniya shaida ce cewa Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) karamar Kashafi, wannan karama ta Kashafi wani abu ne da ke bayyane ga ma’abuta nazari, misali; duk wani qulle-qulle da makirce-makircen da maqiya suka qulla masa, ko suke qullawa Harka Islamiyyah, to za ka ga ya tona asirin shirin. Wani lokaci za a qulla abin cikin tsattsauran matakan tsaro don kar abin ya fita, amma sai ka ji yana bada labarin yanda abin ya gudana, wani lokaci ma mutum biyu ne ko uku za su qulla abin, amma sai ka ji ya tona asirin shirin, har ma ya fito da takardar “Blueprint” xin shirin. Wannan hatta su maqiya da jami’an leqen asiri abin yana matuqar ba su mamaki, wani lokaci ma ba a Nijeriya ake shirya abin ba, amma zai sani, misali kwangilar da aka ba wani qwararren kanfanin kisan kai da ke Amurka, na wani xan asalin Birtaniya mai suna Patrick Williams a shekarar 2012. ALBARKARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani xan baiwa ne mai wata irin albarka wacce ba ta voyuwa ko kaxan! Komai nasa cike yake da albarka komai qarancin abin kuwa, duk wanda ya san Shaikh Zakzaky (H) zai iya zama shaida kan wannan abu da muke faxa. Misali; qanwar Mahaifin Shaikh Zakzaky wacce ake kira Goggo Fatimah, ta faxi cewa; “Lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki, akwai jama’a da kuma abubuwan gudunmawa da aka samu, duk cikin ‘ya’yanmu ba a samu wanda aka samu falala (ta cikar jama’a da samun gudunmawa) irinsa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 67). Anan, Goggo Fatimah tana cewa ne tun daga haihuwar Shaikh Zakzaky (H) aka ga albarkoki masu yawa a tattare da shi, ximbin jama’a suka halarcin bikin sunansa, kuma ba qaramar gudunmawa mahaifansa suka samu daga abokan arziqi, makwabta da dangi ba, kenan Shaikh (H) tun asali da albarkarsa ya shigo duniya. Kamar yadda muka faxa, ba kawai Shaikh Zakzaky (H) ne ke da albarka a tattare da shi ba, duk ma wani abu mai alaqa da shi ba qaramar albarka yake da shi ba. Misali; masu sana’ar buga fosta ta hotunan manyan malamai, ba fostar da suke cinikinta kamar ta Shaikh Zakzaky (H), sam ba sa tsoron buga fostar Shaikh komai yawanta, domin sun san za ta qare, an qiyasta cewa xaruruwan mutane ne ke cin abinci ta hanyar sayar da zallar hotuna, sitikoki, littattafai da fostocin Shaikh Zakzaky (H). Haka nan, duk lokacin da aka rubuta littafi akan Shaikh (H) ko akan wani abu da ya dangance shi, to ba a samun kwashe na wannan littafin, ko da za a yi ta maimaita bugawa, to kuwa zai yi ta maimaita qarewa! Sau da yawa idan Shaikh (H) zai je wani gari, har hanyar garin ake bi a gyara wuraren da suka lalace, dan haka hatta masu bin hanya sukan samu albarkar wucewar Shaikh (H). Idan Shaikh Zakzaky (H) zai je wa’azi ko ziyara wani gari daga cikin garuruwan qasar nan, masu sana’o’i na abinci, da abin sha, da sauran kayan buqatu, da masu motocin haya, da masu gidajen man fetur, ba qaramar darawa suke yi ba. An tava ruwaito wani mai sayar da Shayi yana cewa; “Da Shaikh Zakzaky zai riqa zuwa garin nan duk shekara, to da zan yi arziqin da zan fi qarfin sayar da Shayi!” Wani abin da ke qara tabbatar da cewa duk wani abu da ya shafi Shaikh Zakzaky (H) albarkarsa ba ta misaltuwa shi ne abin da ya faru a zauren “Marital Solutions” na ‘Whatsapp’ a cikin watan Yuni na shekarar 2016, inda wata ‘yar uwa ta faxi laqabin da uwargidan Shaikh Zakzaky (H) Malama Zeenatu ke kiransa da shi, wanda a sakamakon haka sai da membobin zauren suka yi mata hadaya ta wuridin Salatin Annabi (S) dubu xari biyu da hamsin a matsayin tukuici. Mai karatu, idan faxin laqabin Shaikh Zakzaky (H) na “Khaleel” kawai zai sa a yi wa mutum Salatin Annabi (S) kwata Miliyan a matsayin tukwici, to, lallai wannan mafificin shaida ne cewa duk wani abu da ke da alaqa da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) albarkarsa ba ta da iyaka! Wani mawaqi yana cewa; Mai albarka, xan albarka, Al-Zakzakiyu kogin albarka! TASIRINSA :  Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin zavavvun bayin Allah qalilan da Allah Ta’ala ya yi wa baiwar tasiri a zukatan al’ummar da yake rayuwa a cikinta, domin a fili yake cewa zantukan Shaikh Zakzaky (H) da ayyukansa ba qaramin tasiri suke yi ga almajiransa da ma al’umma baki xaya ba. Misali; Tun bayan lokacin da mutane suka fahimcin cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana yin azumomin watanni uku masu alfarma (Rajab, Sha’aban, Ramadan) a jere, sai ya zamo ximbin jama’a sun tasirantu da hakan, sun lizimci yin azumomin watannin a jere, duk da cewa Shaikh xin bai tava umartar wasu da yin hakan kai tsaye ba, kuma abin bai tsaya ga almajiransa kawai ba, har da sauran jama’ar gari. Haka nan, a ranar tunawa da waqi’ar Ashura na shekarar 1434 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da shekarar 2012 Miladiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sauka a motarsa ya yi tattaki da qafafuwansa ba tare da takalmi ba daga qofar Doka zuwa babban masallacin Idi na Zariya. Ya yi wannan Tattaki ne akan kwalta kuma a lokacin ana tsananin zafin rana. Wannan tattaki da Shaikh Zakzaky (H) ya yi ya zama wata Sunnah abin xabbaqawa ga almajiransa da dama, ta kai ga akwai waxanda suke Tattakin Arba’een tun daga garuruwansu har zuwa Husainiyyah Baqiyatullah Zariya, wanda tafiya ce ta kwanaki, amma ba tare da takalma a qafafunsu ba, dan kawai koyi ga aikin jagora (H). A wasu lokutan baya, Malam ya ziyarci garin Lokoja, inda ya ziyarci qaburburan wasu sarakunan Musulunci da Bature ya kai su garin Lokoja suka rasu a can, irin su Sarkin Kano Aliyu xan Abdullahi, da Sarkin Zazzau Aliyu xan Sidi, da su Sarki Kwasau da Sarkin Bida da na Gwandu. “Sadda Malam ya je da farko duk waxannan qaburbura sun zama Bola da wurin kewayawa da gidajen vera da burgu, an manta da su, musamman ma Sarkin Kano. To amma cikin hukuncin Allah zuwan Malam ke da wuya sai kowace masarauta ta tashi haiqan da gyara maqabartar Sarkinsu, misali, na Kano sun gine wurin, an yi azuzuwa, kuma an kewaye wurin da gini, mai buqata ya je ya gani. “Na Zazzau su ma ba a bar su a baya ba, sun gina masallaci a wurin qabarin Aliyu xan Sidi, da wasu azuzuwa. Kafin ziyarar Malam Zakzaky waxannan qaburbura lallai an manta da su, don kafin mutum ya shiga wurin sai ya rufe hanci don wari da qazanta. Wannan abu da na gani a Lokoja na sanya shi a cikin nasarorin Malam Zakzaky!” (Malam, Malam Ne, shafi na 36). Tasirin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai tsaya ga almajiransa da sauran al’umma kaxai ba, hatta gwamnatin Nijeriya a wasu lokuta in ta fito da wani tsari da ya shafi al’umma wanda take so ta cimma nasarar aiwatar da shi, ba mutumin da take sauraron tsokacinsa akan shirin nata kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin da zaran ya yi magana akan abu, to al’ummar qasa sukan samu waraka game da abin, idan ya kushe abin ko ya nuna illarsa, to al’umma za su bijirewa abin, gwamnati ba za ta tava iya cimma nasarar aiwatar da shirin ba (allrar Poliyo ta isa misali), amma idan ya yi shiru akan lamari, to, gwamnati kan samu qarfin gwiwar aiwatar da shi. Wannan tasiri na Shaikh Zakzaky (H) ga al’umma yana xaya daga cikin abin da ke xagawa gwamnatin Nijeriya hankali, domin tana ganin ya za a yi a samu wani mutum ya fi hukuma tasiri ga al’umma? Tasirin Shaikh Zakzaky (H) ya haifar da canje-canje da dama a sassa da vangarorin al’umma masu yawa, kama daga vangaren Malamai ta sashen wayewarsu, ‘yancinsu, da salon tsaronsu. Zuwa vangaren xalibai, talakawa da sauran vangarori. Tasirin da Shaikh Zakzaky (H) ya yi a sassa na rayuwar jama’a ne ya sa manazarta ke cewa ya riga ya yi nasarar juyin juya hali “Ravolution” a Nijeriya. A taqaice, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi matuqar tasiri a kowane fanni na rayuwar al’ummar qasarsa, domin za ka ga jama’a suna matuqar koyi da shi a dukkan sassa na rayuwarsa, kama daga tsabtarsa, adonsa, zamantakewarsa da iyali, har ma da kwaikwayon salon kalmomi na maganarsa. Wannan tasiri da Allah Ta’ala ya ba Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana xaya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci da suke jan hankalin hukumomi da manazarta akan rayuwar Shaikh Zakzaky (H) da dalilan da suka sabbaba masa wannan tasirin. RAHARSA : Babu shakka, wasu mutanen da ke hangen Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daga nesa, za su xauka mutum ne mai kaushi da tsanani, amma ga duk wanda ya kusance shi, zai gane cewa shi mutum ne mai tsananin sauqin kai da raha, ba yadda za a yi ka zauna tare da shi na tsawon mintuna 15 ba ka mance da duk damuwowin ka ba, domin mutum ne mai matuqar hikima da raha, duk inda ka gan shi a cikin jama’a muddin ba lokacin juyayi ba ne, to za ka ga annuri da alamar fara’a a fuskar duk na tare da shi, domin tabbataccen abu ne Shaikh (H) zai sanya nishadi da farin ciki ga kowa ta hanyar raha mai cike da ilimantarwa da hikima. Shaikh Zakzaky (H) mutum ne mai sauqin kai matuqa, wani Fasto da ya tava kawo masa ziyara gida, bayan sun daxe suna tattaunawa cikin raha da nishaxi, sai ya ce; Gaskiya Malam yadda muke hangenka daga nesa ba haka kake ba, mu ba mu xauka kana da sauqin kai haka ba, da a musulmin qasar nan na tsane ka fiye da kowa, amma yanzu na ji ina son ka fiye da kowa!”. Shi kuwa Fasto Meter Peller na cocin Abuja, cewa Kiristoci ‘yan uwansa ya yi; “Kiran da zan yi ga al’umma da sauran Fastoci shi ne, ya kamata kowa ya buxe qofa ga waxannan jama’a (‘yan Shi’a almajiran Shaikh Zakzaky) don a fahimci juna, abin da ke tsakaninmu shi ne rashin fahimta, duk wanda ya nazarci kiran Malam (Zakzaky) to ba zai tava muzanta shi ba, dole ne ya yarda da kiran Malam! Wasu za su ji kamar ina siyasa ne ko wani abu mai kama da haka, amma (na tabbata) idan har suka samu ganawa da Malam, to lallai su ma sai sun zama ‘ya’yan Malam kamar yadda na zama!” (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 08). Marubucin littafin “Malam, Malam Ne” ya labarta cewa; “Wani xan jarida, bayan saduwarsu da Malam ya ce; “(Wannan) ko cutar da quda ba zai iya ba” (He can hardly wound a fly)” (Malam, Malam Ne, shafi na 15). Wannan xan jarida ya ga sauqin kan Shaikh (H) ne da zurfin ilimi da fikirarsa. WASIYYARSA : Bisa al’ada akan ambaci Wasiyyar mutum ne bayan ya bar duniya, to amma babu laifi ga ambatar Wasiyyar mutumin da ke raye a duniya ma, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi buxaxxiyar Wasiyya aqalla guda biyu. Buxaxxiyar Wasiyyarsa ta farko ta faru ne a watan Ramadan na shekarar 1430 (2010), lokacin da rahoton sirri ya zo masa cewa an gama duk wani shiri na halaka shi a wannan dare da zai shigo, har ma ya samu kwafin takardar “BluePrint” da shugaban qasa Umaru Musa Yar’aduwa ya sawa hannu na zartar da “Operation” xin a wannan dare. Shaikh Zakzaky (H) ya yi Wasiyya ga vangarori uku na al’umma, ya yi Wasiyyar gargaxi ga azzalumai, ya yi Wasiyyar juriya ga almajiransa, ya yi Wasiyyar farkawa ga al’ummar musulmi, sa’annan a qarshe ya yi albishir ga almajiransa, ya ce; “Ba zan qarqare maganar nan ba sai na yi muku albishir, ko an qi ko an so addinin Allah zai tabbata! Ba yadda za a yi a ce wai bakin bindiga ko bom zai tarwatsa Da’awa zuwa ga Allah!” Wasiyya ta biyu ta Shaikh Zakzaky (H) ita ce wacce ya yi wa ‘ya’yansa uku da suka rage a duniya, wato Sayyid Muhammad, Sayyida Nusaiba da Sayyida Suhaila, a ranar da sojoji suka kai hari gidansa, suka kashe kusan mutum dubu daga almajiransa, kuma suka kashe ‘ya’yansa maza uku, da babbar Yayarsa, suka harbi matarsa, shi ma suka yi masa ruwan harsashi, da yake bai xauka zai rayu ba, ya yi kevantacciyar Wasiyya ga ‘yarsa Sayyida Suhaila wacce yake tare da ita a lokacin. Ta ce, daga cikin Wasiyyarsa gareni ya ce; “In kula da Sallah, sannan mu xau fansar abin da aka yi mana, kar mu qyale abin da aka yi mana ya tafi (a banza), kar mu yi shiru akan abin da aka yi mana. Sannan in yi haquri, in kalli rayuwar Sayyida Zainab (SA), in yi haquri irin nata, in yi rayuwa irin yadda ta rayu. Ya yi batun komawa makaranta, yana wannan halin ya riqa qarfafamu ni da Sajida akan muhimmancin ci gaba da karatunmu, ya ce in mun rayu mu tabbata mun koma makaranta, kar mu ce ba za mu koma ba, kar mu tsayar da komai namu dan abin da ya faru, amma kar mu qyale abin ya tafi a haka nan (siddan)” (Jaridar Al-Mizan, bugu na 1240). Jumlatan a waxannan Wasiyyoyi na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shiryar da al’umma ne a cikinsu, za mu ga yadda ya yi Wasici da kula da Sallah, da dagewa da neman ilimi, da rayuwa tare da ruhin gwagwarmaya da zaluncin azzalumai. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ BABI NA UKU ALAQAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) DA YAWAN IBADA IBADARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bawan Allah ne mai tsananin ibada, mutum ne da duk wanda ya san shi ya shaide shi da yawan ibada musamman salloli da azumomi da Azkar da yawan zuwa aikin hajji da umrah (kafin kafircin duniya ya sa shi a tarko). Yakan ce, awa 24 na yini da kwana sun yi masa kaxan, da da yiwuwar a qara da zai so haka, ya ce “Duk duniya ba abin da ya kai Sallar dare daxi, da azzalumai sun san daxin da muminai suke ji (a Tahajjud), da sun ce ba su yarda (a riqa yi) ba!” (Malam, Malam Ne, shafi na 07). Bari mu ambaci ‘yan misalai na yawan ibadarsa a fagen Sallah, Azumi, Hajji da sauransu. SALLOLINSA : A fagen sallolin nafilfili Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun yana qarami ya lizimci yin “Nawafilil Yaumiyyah” wato nafilolin da ake yi tare da kowace sallar farilla kafinta ko bayanta. Wato duk wanda ya san Shaikh Zakzaky (H), ya san shi da yin Nafilfilin dare (Tahajjud) raka’a 13, Nafila raka’a 8 kafin Azahar, raka’a 8 kafin La’asar, raka’a 4 bayan Magriba, raka’ar Wateera bayan Isha’i, in an haxa da raka’o’i 17 na sallolin farilla guda biyar, zai zama kenan a kullum Shaikh (H) yana yin Sallah Raka’a 51 a qalla. Wannan banda kevantattun Salloli na kowane dare da na kowane yini da yake yi, kuma banda raka’a biyun da yake wa iyayensa, da raka’a biyu ga ‘ya’yansa, da raka’a biyu hadiyya ga shahidai, wannan a kowane dare ne, kuma banda salloli na musamman a ranar Juma’a da ranakun Idodi da sauransu. Kenan, a kowane wata Shaikh Zakzaky (H) dubban raka’o’i yake yi na sallar Nafila. Sannan yana yin kevantattun nafilfili na dararen watanni uku a jere (Rajab, Sha’aban, da Ramadan) kamar yadda aka ruwaito su a littattafan ibada, sannan yana yin kevantattun salloli na darare na musamman a kowane wata. Lokacin da ya saba tashi don yin sallar Tahajjud shi ne qarfe 2 na dare, wannan shi ne “Normal Time” xinsa a kullum, xaya daga cikin manyan almajiransa yana cewa; “Ta vangaren Mujahada kuwa, wannan kam ko yau daren nan ko gobe, Malam qarfe biyu na dare ya tashi, kuma ba zai kwanta ba har sai bayan rana ta fito, ni ban san iyakar shekarun da ya xauka yana yin wannan ba” (Malam Zakzaky, Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 08). Amma a darare masu falala da alfarma ta musamman (kamar daren Juma’a, dararen haihuwar Ma’asumai (AS), dararen Mab’ath, Dahwil-Ardh, Nisfu-Sha’aban, Ghadeer, da kusan gaba xayan dararen watan Ramadan), ba ya ma bacci kwata-kwata a cikinsu. (Tasarrufi daga Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 07). Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Yana da yawan Sallah, musamman da dare, kai barcinsa in ma yana yi, to fa kaxan ne, sau da yawa za ka ji yana cewa; “Rabo na da barci tun kwana kaza”, ya ambaci wasu kwanaki” (Malam, Malam Ne, shafi na 08). Shaikh Zakzaky (H) yana da wata alaqa ta musamman da Sallah, domin a rayuwarsa ba abin da yake son yi kamar Sallah, na tava ji a wata ziyara da aka kai masa yana cewa; “Da za a tambayeni, me ka fi so? Zan ce Sallah! Da kuma za a tambaye ni, me ka fi jin daxinsa, zan ce Sallah!” wannan da kunne na na ji Shaikh (H) yana faxin haka. Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Akwai wani mutumin Iran da ya ga Malam Zakzaky (H) yana Sallah, ya ce; “Wannan yana Sallah irin ta Annabawa da Waliyyan Allah” daga nan suka shaqu da Malam” (Malam, Malam Ne, shafi na 08). Za ka tabbatar da alaqar Shaikh Zakzaky (H) da Sallah in ka karanta labarin waqi’ar Maulud ta 2015, cewa, duk ruwan wuta da sojojin Nijeriya ke yi suna kashe almajiransa (a lokacin da suke qoqarin isa gare shi don kashe shi), shi ba abin da yake yi a falonsa sai Sallah. ‘Yarsa Sayyida Suhaila tana cewa; “Daga lokaci zuwa lokaci ana sanar da mu abubuwan da ke faruwa, mu kuma sai mu shiga mu sanar da Abbah (Shaikh Zakzaky) haqiqanin halin da ake ciki, da yawan lokaci in na shiga sai in tarar Abbah yana Sallah, sai in sanar da Ummah akan in ya yi sallama ta faxa masa” (Al-Mizan, bugu na 1240). AZUMINSA : A fagen Azumi, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ginu akan lizimtar Azumin Litinin da Alhamis na kowane mako, (tun daga watan Shawwal zuwa qarshen Jimada-Thani), kenan yana yin Azumi 77 na waxannan raneku. Sannan yana azumin kwanaki tara na farkon watan Zulhajji, kuma yana yin azumin baki xayan watanni uku a jere, wato Rajab, Sha’aban da Ramadan, kenan yana yin azumin kwana 90 a jere. Shaheed Hafizu Dauda (xaya daga cikin masu rakiya ga Shaikh Zakzaky), ya faxi cewa, “A bisa al’ada, in Shaikh (H) zai gabatar da Muhadhara (jawabi) yakan zo da ruwan shansa, in ba mu gan shi da ruwa ba, to mun san a ranar yana azumi. To, kuma mun lura, daga ranar xaya ga Muharram ba ya zuwa wurin zaman makokin Ashura da ruwa har sai ranar Arba’een (20 ga Safar) muke ganin ya zo da ruwan sha a tare da shi”. Wato yakan yi azumin watan Muharram baki xaya (in banda ranar Ashura), da kuma kwanaki 20 na Safar, jimilla yakan yi azumin kwana 49 kenan a jere. Sannan yana yin Azumi na dukkan ranakun haihuwar Ma’asumai 14 (AS), yana kuma azumtar muhimman ranakun idodi na shekara, irinsu ranar Mubahala, ranar Ghadeer, ranar Mab’ath, ranar shinfixa qasa, ranar Nuzuri da sauransu. Jumlatan, a kowane kwanaki 360 da ke cikin shekara, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana azumtar tsakanin kwanaki 230 zuwa 260 a cikinsu. Kenan, in dai Shaikh Zakzaky (H) yana zaune a gida ba tare da tafiya karatu ba, yana azumi aqalla na sama da wata takwas a cikin watanni 12 na shekara. Qanin Shaikh Zakzaky (H) wato Malam Badamasi Yaqubu yana cewa; “Na san Malam (tun) sama da shekaru 40 barcinsa qanqani ne, kuma na san cewa tunda ya taso ya ga mahaifinmu yana yin azumin wata uku a jere, wato Rajab, Sha’aban, da Ramadan, (shi ma) tunda ya taso yake yi, kuma har yanzu Malam bai daina ba, tun kamar shekaru 40 da suka wuce yake yi, kuma har yanzu yana ci gaba da yi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 64). A wani jawabi Malam Badamasi ya ce; Tun Shaikh Zakzaky (H) bai balaga ba yake azumin wata uku a jere. Wani da suka yi zaman Fursuna tare da Shaikh Zakzaky (H), ya faxi cewa; Lokacin da suka yi zaman gidan kurkuku, Malam ya kwashe wata tara cur yana Azumi, kuma abinci kimantacce yake ci!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10). KARATUN QUR’ANINSA : A fagen karatun Alqur’ani za a iya cewa Shaikh Zakzaky (H) mutum ne na musamman, domin shi ba ya gajiya da karatun Alqur’ani, sai dai kawai sauran hidimomi su tilasta shi ya ajiye, uwargidansa Malama Zeenat tana cewa; “Na san a da (Shaikh) yana sauqe Alqur’ani ne cikin kwana bakwai (wato mako guda)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 130). Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Sayyid (H) ya kasance mai yawan karatun Alqur’ani, akwai ma lokacin da yake cewa, lokacin da yake zaune a kurkuku, yakan so ya sauqe Alqur’ani a qasa da kwana uku, amma tunda Sunnah shi ne qarancin sauqa kwana uku ne, to yakan tsaya akan hakan” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 26). Idan muka nazarci wannan magana ta Shaikh Zakzaky (H) za mu ga zurfin xanfaruwarsa da karatun Alqur’ani mai girma, domin yana cewa ne, da ba don Sunnar Annabi (S) ta koyar da mu sauqe Alqur’ani cikin kwana uku zuwa sama ba, to da shi zai riqa sauqe Alqur’ani ne a qasa da kwana ukun, wato a kullum zai riqa sauqe Alqur’ani, amma tunda abin da Sunnah ta koyar kwana uku ne, to ya tsaya a haka! ADDU’ARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ma’abucin yawan addu’o’i ne, ya yi imani da addu’a fiye da komai a rayuwarsa, komai nasa sai ya yi addu’a kafin ya yi shi da bayan kammala shi. Yana bin dukkanin ladubba na karanta addu’a akan komai, kama daga addu’o’in Alwala, wanka, bacci, sanya sutura, zama, tashi, hawa abin hawa da komai na rayuwarsa. Sa’annan ya lizimci yin addu’ar kowane dare, da addu’o’in ranakun mako, da addu’o’in kwanakin wata, da kuma addu’o’i na musamman a wasu lokuta na musamman, ko a wasu fitattun ranaku masu alfarma. Ya wallafa littafi ma na nafila raka’a dubu da addu’o’insu na musamman da ake yi a watan Ramadan, mai suna “Ad’iyaati Nawafilir Ramadan”. Shaikh Zakzaky (H) ya yi fice wajan yawan karanta sashen addu’ar nan ta Iftitah daga daidai “Allahummah Innaa Narghabu Ilaika Fiy Daulatin Kareemah…” zuwa qarshen addu’ar, da kuma addu’ar Sabati da Istiqama ta “Yaa Allahu, Yaa Rahmanu, Yaa Muqallibal Quloub Thabbit Qalbiy Aladeenika”, da sauran addu’o’in tuba da na neman shiriya da taimako ga Allah, sannan ya lizimci yin addu’ar “Allahummah wa Qadshamalana Zaigul Fitan” a Alqunut xinsa na Sallah. A fagen addu’o’in murqushe kaidin azzalumai da ganin bayansu kuwa, Shaikh Zakzaky (H) ya yi amanna da addu’ar “Al-Qamah”, da addu’ar “Sahmul-Lail” da addu’ar “Ahliththugour” da kuma addu’ar “Xairal Ababeel”. Sannan yana yawan karanta addu’o’in halaka azzalumai musamman na Imam Zainul Abidin (AS). Shaikh Zakzaky (H) yana da yawan addu’o’in alkairi ga almajiransa, malamansa, iyayensa, al’ummar musulmi da kuma Shahidai, duk wanda ya san Shaikh ya san ba abin da yake roqon a yi masa sai Addu’a, saboda zurfin imaninsa da ita. MUJAHADARSA : Mujahada na nufin qoqari ko wani qarfin hali na musamman a fagen ibada. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mujahidi ne na musamman a fagen ibada, domin banda yawan ibadar da yake da, a gefe guda kuma yana da naci da dagewa a tsawaita ibadar, wato ba ya hanzari ko shaf-shaf a lokacin ibada, yakan tsawaita tsayuwar karatu, da Ruku’u, da Sujjada da sauransu a tahujjud xinsa. Misali; Shaikh Zakzaky (H) ya shafe shekaru masu yawa yana aiwatar da dukkanin azumin watan Ramadan a Haramin Makka ko masallacin Annabi (S) da ke Madina, wato duk shekara yakan tafi Umrah tun a cikin watan Sha’aban, ba ya dawowa sai bayan Sallah (Idil-Fitr), yakan shafe gaba xayan watan Ramadan ne a cikin masallacin Harami, ba abin da yake yi sai ibada. Wani mutum ya labarta yadda ya ga ibadar Shaikh Zakzaky (H) a masallacin Annabi (S) dake Madina. Akwai wani ginshiqi a cikin Raudha na masallacin Madina da ake qira ginshiqin Abu-Lubaba, anan Shaikh Zakzaky ke zama ya yi ta ibada, lokacin da mutumin ya ga Shaikh a wurin, sai ya yi ta zuwa sawu-sawu dan yana so ya samu damar yin magana da shi, amma duk sa’adda ya je wurin sai ya tarar yana ibada, hatta lokacin tsayawa cin abinci ma bai da shi, sai dai ya xan ci Dabino ya sha madarar gwangwani ko xan wani abu marar nauyi, amma ba ya fita waje don neman abinci. Mutumin ya ce; “Wallahi duk sadda na je sai in iske shi yana Ruku’u, ko ya yi Sujjada, ko yana karatun Alqur’ani, sam ba ya zama haka nan (shiru), akwai ranar da na ga ya yi Sujjada da tsakiyar dare, har aka fara qiran sallar Asubahi bai xago ba, har na yi tunanin in je in qwanqwasawa Askar su zo su xauke shi ko ya rasu ne, (na yunqura zan je) sai na ga ya taso ya zauna ya maida nunfashi, a lokacin ba dan tsoron Askarawa ba da na ce “Labbaika ya Al-Zakzaky!” (Malam Zakzaky, Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 09). Wani xan uwa daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) ya rubuta labarin mujahadar Shaikh xin kamar haka; “Na daxe ina samun matsaloli na rashin fahimta tsakani na da Babana, lamarin bai yi sauqi ba sai da wata rana wani abokin Baban nawa ya dawo daga aikin Umrah, suna zaune suna hira sai ga ni na zo wucewa, sai na ji yana faxa masa cewa; “Kai Alhaji, a wannan shekarar na ga shugaban ‘yan Shi’a (Shaikh Zakzaky) a Umrah, yana ibada kai ka ce Mala’ikan mutuwa ke jiransa, yana ibada ba ji ba gani, da ka gan shi sai ka ji so da qaunarsa ta shigar maka rai” ya ci gaba da ba Babana labarin cewa “Larabawa sai zuwa suke zunxensa, ana faxin ga wani baqin fata yana ibada ganga-ganga, da wata irin baiwa wacce samunta sai a kundayen tarihi” sai na ji Babana ya yi shiru, daga lokacin ya fara canzawa, yana saurare na da hujjojina” (Wakilin Manzo (S) a Doron Qasa, juz’i na xaya shafi na 26-27). Daga cikin Mujahadar Shaikh Zakzaky (H) akwai cewa, shi ba ya umartar wani da yin wani aiki na ibada har sai wannan aikin ya zamo jiki a wurinsa. Misali; a lokacin da ya fara yi wa almajiransa magana akan falalar yin Sallah Raka’a xari a wasu darare masu alfarma, irinsu daren Nisfu Sha’aban da dararen “Layaliyal Qadari” da sauransu, to shi ya fi shekara goma yana yi. Haka nan, sai da ya shafe sama da shekara goma yana yin sallar nafilar nan mai raka’a Dubu ta tsakanin Magriba da Isha’i a watan Ramadan, kafin ya sanar da ‘yan uwa muhimmancin yin wannan Sallar, har ma ya wallafa xan qaramin littafi na yadda ake yin sallar da addu’o’inta. Sannan tarihi ya nuna cewa shi ne mutumin da ya raya I’itikafi a aikace a qasar nan, kafin tasowarsa ana karanta batun I’itikafi ne kawai a littattafan fiqihu, amma ba a san wani mutum na shiga I’itikafi ba. Kenan, a sama da qarni guda da ya gabata Shaikh Zakzaky ne ya fara shiga masallaci ya yi I’itikafi tun yana yaro xan shekaru 15, daga nan sannu a hankali yin I’itikafi ya bazu a cikin al’umma, yanzu yin I’itikafi ya zama jiki a wurin dukkan vangarorin musulmin Nijeriya. Yayar Shaikh Zakzaky Shaheeda Fatimah Yakubu (Goggon Qaura) ta faxi cewa; Tun yana yaro yake shiga masallaci ya yi I’itikafi, tun 20 ga watan (Ramadan) sai Sallah yake fitowa. Ni dai ban san wani da yake shiga I’itikafi ba a lokacin sai shi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 71). ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ BABI NA HUDU WASU SASSA NA RAYUWAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) TAFIYE-TAFIYENSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tafiye-tafiye zuwa qasashe masu yawa a sassa da dama na duniya, kusan ma ba wani sashe na duniya da bai je ba, kama daga Asiya, Turai, da qasahen Afirka. Misali, a yankin Asiya ya je qasashe kamar su; Iran, Iraqi, Saudi Arabiyya, Dubai, Lebanon, Malesiya da sauransu. A qasashen Afirka kuwa ya je Sudan, Ghana, Saliyo, Mali, Habasha, Nijar, Kenya, Afirka ta Kudu, Libiya da sauransu. Sannan ya je manyan qasashen duniya masu tinqaho irinsu Birtaniya, Amurka, Rasha, Faransa da sauransu. Dukkanin waxannan tafiye-tafiye ya yi su ne ta hanyar gayyata bisa dalilai na addini, ko halartar tarurrukan qarawa juna ilimi. “Haka nan in muka dawo nan cikin gida za mu ga cewa Sayyid Zakzaky (H) ya je birane da qauyuka masu yawa a cikin qasar nan don isar da wannan Da’awa da yake yi, kai mutum ma zai iya dukan qirji ya ce a jihohin qasar nan musamman ma na arewawacin qasar, to, ba jihar da bai je domin isar da wannan saqo na Allah Ta’ala ba” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 23). ALAQARSA DA AL’UMMAH : MUSULMI : Abu ne sananne ga kowa cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fi kowane malami a Nijeriya kyakkyawar alaqa da sauran musulmin da ba fahimtarsu xaya ba, domin ko kaxan ba ya qyamar musulmi na kowace Mazhaba ko Aqida, hasali ma ya fi kowa jin zafi bisa rashin jituwar da ke tsakanin qungiyoyin musulmi. Kullum a cikin sa’ayi na haxa kan musulmi yake, damuwarsa ita ce, aqalla musulmi su yarda su dena aibata juna da sukan juna da kafirta junansu. Daga cikin qoqarin Shaikh Zakzaky (H) na haxa kan musulmi ya sunnantawa kansa da almajiransa ziyarar Malamai na qungiyoyin musulmi daban-daban, daga lokaci zuwa lokaci Shaikh (H) yakan tashi takanas ya je gidajen manyan malamai ya ziyarce su don neman kusanci da fahimtar juna. Sannan duk garin da ya je don wa’azi ko halartar wani taro, yakan je ziyara ta sada zumunci da neman kusanci da fahimtar juna ga manyan malamai na garin, yakan ziyarci malamai ne mabanbanta na qungiyoyin musulmi. Sannan ya hana almajiransa warewa ko gina masallatansu na qashin kansu, don hakan zai qara kawo rarraba da farraqa ne a tsakanin musulmi, wannan ya sa duk inda almajiran Shaikh Zakzaky (H) suke, suna Sallah ne a masallatai na al’ummar musulmi, kuma a bayan limamai na waxannan sassan musulmin, tattare da cewa suna riqo ne da tafarkin Ahlul-Bait (AS) wato Ja’afariyyah. KIRISTOCI: Ko ba a faxa ba duniya shaida ce game da kyakkyawar alaqar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Kiristoci da ma sauran mabiya addinai a Nijeriya, domin in banda Shaikh (H) ba wani malami da Kiristocin Nijeriya ke yabawa salon Da’awarsa kamarsa. Qungiyoyin Kiristoci daban-daban sun sha rubutawa Shaikh Zakzaky (H) takardar yabo da godiya bisa gudunmawar da almajiransa suka ba su, na tseratar da rayukansu, ko na kariya ga dukiyoyinsu ko ga wuraren kasuwancinsu a lokutan rigingimun addini ko na qabilanci ko na siyasa. A wurin Shaikh Zakzaky (H) hanya mafi dacewa ta yin jihadi ga Kiristoci ita ce hanyar isar musu da saqon musulunci na haqiqa ta kyakkyawar hanyar da za su fahimta su gamsu, ba wai ta hanyar hantara ko far musu da kisa ko qona dukiyoyi da wuraren ibadarsu dan kawai sun zavi su zama kiristoci ba. MUTUNTAWARSA GA MATA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne alami mafi girma na ‘yancin mata da tausaya musu a wannan al’umma ta wannan nahiya, domin ya kawo gagarumin sauyi akan yadda al’ummar wannan nahiya suka xauki mata, da yadda suke kallonsu, da irin mu’amalar bawa da maigidansa da ke gudana a tsakanin mata da mazajensu. Sannan a gefe guda Shaikh Zakzaky (H) ya yaqi munanan al’adu na qasqanta mata da mayar da su haja ta biyan buqata kawai. Wanda ya san rayuwar Bahaushe da iyalinsa, da yadda Shaikh (H) ya kawo sauyi a cikinta ne kawai zai iya fahimtar abin da muke faxa. A matakin farko, Shaikh Zakzaky (H) ya darajta mata ne ta hanyar koya musu sanya suturar Musulunci (Hijab), wanda kafin Da’awarsa ba a san sanya hijabi a wannan nahiya tamu ba. Daga nan sai ya fito da su daga zaman dirsham na hidimar mazaje a gidajensu, zuwa fagen addini da sa’ayi kafaxa da kafaxa da maza wajan neman yardar Allah da gwagwarmayar ceto al’umma, wanda kafin Da’awarsa, a wannan nahiya tamu an manta cewa mata suna da wata damar bada gudunmawa a harkokin addini. Albarkacin Da’awarsa ne har mata suka samu damar riqe sifika su yi wa’azi, suka samu ‘yancin yin karatu suna gidajen aurensu, wanda kafin Da’awarsa an takura damar matan aure ta yin karatu da neman ilimi a makarantu. Shaikh Zakzaky (H) ya bada gudunmawa sosai ta hantar mutunta mata da raya darajarsu a cikin al’ummar Hausawa ta aqalla fuskoki uku; NA FARKO : Ya kare su daga yawan saki barkatai ba tare da bin qa’ida ba, domin a wani jawabin da yake matuqar nuna damuwarsa game da yadda maza ke yawan sake mata ba bisa qa’ida ba a Nijeriya, Shaikh Zakzaky (H) ya tava cewa; “Da ina da iko, to da na sa wata qa’ida a sakin aure, idan mutum zai saki matarsa, sai an sa rana, ya buga katin gayyata ya raba, an yi ta sanarwa a gidan rediyo, cewa wane xan wane, ya sa ranar kaza ga watan kaza a matsayin ranar da zai aikata abin nan da Allah Ta’ala ke qi, wato Saki! A taru kamar yadda ake xaura aure, mai shela ya yi shela cewa; Ga wane xan wane, ba tare da jin kunyar Allah ba, ba tare da jin kunyar Manzon Allah (S) da Mala’uku da Muminai ba, zai aiwatar da abin nan da Allah ba ya so, wato zai saki matarsa! NA BIYU : Ta vangaren aure ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya qarawa mata kima da daraja a wajan maza, domin kuwa a bisa al’ada, a Nijeriya da qasashe maqwabtanta ana biyan kuxi ‘yan qalilan ne a matsayin sadakin mace, kai akwai ma al’adar bayar da ‘ya mace kyauta ko sadaka ga namiji ya aureta ba tare da wata wahala ko xawainiya ba, hatta sadakinta ma ubanta ne ke biya masa, shi kawai a siddan za a kawo masa matar! Wannan al’ada ta tsananin arhar aure ta haifar da matsaloli masu yawa a zamantakewar auren al’ummarmu. Na farko ta haifarwa auren rashin kima, ta yadda an mayar da shi kamar wasa, daga mace ta xan savawa miji ko da bisa kuskure ne sai kawai ya saketa, domin ya san zai samu wata sabuwa cikin sauqi. Na biyu kuma hakan ya sabbabawa mazaje auren mata barkatai, alhali ba sa kiyaye haqqoqin matan kamar yadda musulunci ya tanada, hakan ya taimaka qwarai wajan jefa mata cikin halin tagayyara da qaqanikayi a gidajen aurensu. Don taqaita wannan mummunar xabi’a ta wulaqanta mata, sai Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raya sunnar biyan Sadaki mai kima ga mata, don aqalla mace ta samu darajtawa daga namiji, kuma hakan ya rage yawan saki barkatai ba tare da bin qa’ida ba, sannan ya taimaka wajan daqile tara mata rututu ba tare da kiyaye haqqoqi da dokokin Shari’a ba. NA UKU : Shaikh Zakzaky (H) ya tarbiyyantar da al’umma (musamman almajiransa) dangane da tausayawa iyayen ‘ya mace, ya nuna cewa; Idan iyaye suka haifi ‘ya mace, sukan kula da rayuwarta da tarbiyyarta baki xaya, su yi ta xawainiyar ciyar da ita, tufatar da ita, kula da iliminta da lafiyarta da sauransu har ta girma. To kuma in an zo batun aurenta, sai iyayen sun sha wata baqar wahala ta kashe magudan kuxi, wani lokaci ko iyaye ba su da hali sai sun ci bashi sun yi xawainiya. Dan haka, kamata ya yi su masu neman aure, su riqa tausayawa iyayen yarinya suna hutar da su daga manyan xawainiyoyi a lokacin biki. Ma’ana, ya zamo wanda zai auri mace ya biya sadaki mai kima sosai, wanda zai isa iyaye su yi wa mace duk abin da ake buqata a gidan mijinta, sai ya zama a qalla iyaye ba su riqa wahala sosai a lokacin aurar da ‘ya’yansu mata ba, an taimakawa iyaye kenan wajan hutar da su daga xawainiya mai galabaitarwa a lokutan bikin ‘ya’yansu mata. Madalla da wannan darajtawa ta Shaikh Zakzaky (H) ga matan al’ummar nahiyarsa, madalla da wannan cigaba da ya samarwa mata, kuma madalla da wannan hutu da ya nemawa iyayen ‘ya’ya mata ! TAUSAYINSA GA MATA : Shaikh Zakzaky (H) mutum ne mai matuqar tausayawa mata bisa halin da suka samu kansu a wannan al’umma tamu, yana yawan nuna damuwarsa game da cutar da mata da mazaje ke yi. Kullum yakan yi kira ga maza da su riqa tausayawa mata, su dena cutar da su, su dena bautar da su, su riqa musharaka da su cikin ayyukan gida, su riqa biya musu buqatunsu na rayuwa, su riqa kyautata musu har su shagwava su. A wani jawabinsa na “Ranar Mata ta Duniya” wato “Makon Zahrah”, ya yi nasiha ga mazaje da su shagwava matansu ta hanyar tsananta kyautata musu, a ciki yake cewa, maza su riqa sayawa mata gwalagwalai na ado, in suna son mota ku saya musu, in suna son zuwa Hajji ku kai su, duk abin da suke so ku yi musu, ya ce idan maza suka yi wa matansu haka, sai kuma ya zamo matan sun nuna butulci, to a lokacin shi kuma zai yi wa matan faxa ya ba su rashin gaskiya. Kullum Shaikh yakan tausayawa ‘yan uwa mata idan ya wuce ya gansu akan titi suna tafiya da qafa za su je wurin taro, musamman idan wurin taron da nisa, wani lokaci ma har tsayar da tawagar motocinsa yake yi ya umarci matan da ke tafiya a qafa da su shiga a rage masu hanya, in kuma suna da yawa yakan cire kuxi ya ba su ya ce su hau Tasi. Wani xan uwa ya bada labarin yadda Shaikh Zakzaky (H) ya tava taimakawa wata mace mai ciki tun a shekarun baya, ya ce; “Ina da wasu dangi a cikin garin (Zariya), kullum suna gargaxi na game da bin Malam Zakzaky (saboda shi Shi’a ne). Ran nan sai kawai na ji mahaifiyar mai gidan ta ce ita ma ta zama ‘yar Shi’a, na ce meye dalili? Sai ta ce “Ai ran nan xaya daga cikin ‘ya’yanta mata sun dawo daga unguwar Ban Zazzau (a cikin garin Zariya), ga goyo kuma ga ciki ruqu-ruqu, (tana tafiya da qyar da wahala), sai Malam ya zo wucewa a motarsa Bitil, ya tsaya ya xauko ta da xanta har zuwa kusa da gida. Ta ce yana tuqi sai karatun Alqur’ani yake… Wannan shi ne dalilin xaura xamarar neman sai ta koyi karatun Qur’ani ta iya kuma ta haddace shi” (Wakilin Manzo (S) a Doron Qasa, Juz’i na xaya, shafi na 26). Tausayin Shaikh Zakzaky (H) ga mata bai taqaita ga mata ma’abuta addini ba, hatta mata masu zaman kansu Shaikh (H) yakan tausayawa rayuwarsu qwarai, “Akwai lokacin da na ji yana cewa, lokacin da yana zaune a kurkukun Kaduna, yana sauraron BBC sashen Hausa, sai ya ji ana tattaunawa da wasu ‘yan mata musulmi, waxanda suka maida fasiqanci a matsayin sana’a, suka ce kuma da abin da suke samu ne suke xaukar xawainiyar kansu da ma na iyayensu, shi ne Sayyid (H) ya ce da ya ji hirar, saboda tausayinsu sai da ya zubar da hawaye” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 31). HIDIMA GA IYALANSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da hali irin na Manzon Allah (S) na taimakawa iyali a ayyukansu na cikin gida da hidimta musu, domin ya kasance yana yi wa iyalinsa wanki da guga, yana xiba mata ruwa ya cika randuna, yana sharar xaki da gyara shinfixar kwanciyarsa da kansa, kuma yana dafa abinci ga iyalansa. A wata hira da ‘yan jarida, uwargidansa Malama Zeenatu ta shaida musu cewa; “Qila kuna da labari cewa; Malam yakan girka abinci da yin sauran ayyukan gida. Tunda muka yi aure muna raba aiki ne ni da shi, ba wai komai ni nake yi ba, bilhasali ma wasu abubuwan shi yake mani, kamar wanki, (guga), da sauransu, sai ya ce in tara kayana in sun yi datti, shi sai ya wanke… kuma yakan ce kar a tava masa girkinsa, wato in yana girki ba ya so a sa masa hannu, ya fi so ya yi abinsa ya gama” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 41). A wani jawabi Malama Zeenat tana cewa; “Shi (Malam) bai yarda mu ce komai mu za mu yi, shi ba zai yi ba, kuma Malam bai tava cewa in ba shi kaza ba, bai tava cewa xauko min kaza ba, kai ba ma ni ba, har yaransa ba ya aikensu, har da su Zainab (Hameed) in za su gyara masa xaki, to sai in ya fita za su shiga su gyara. Bai tava ce mun xauko min kaza ba, ko bani ruwa ko menene ba, shi kawai yana so ya yi komai da kansa ne” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 128). Haka nan Malama Zeenatu ta tava bayyanawa ‘yan uwa mata misali na hidimar da Shaikh Zakzaky (H) yake mata hatta a cikin barcinta, ta ce; “Kun ga ni mai yawan jin zufa ce, waxanda muke tare sun sani, kuma ana yawan xauke wuta, kuma idan aka xauke wuta ba mu kunna AC da Janareto, don kar mu matsa masa, sai dai mu kunna fanka. To, duk lokacin da NEPA suka kawo wuta zai zo ya kunna min AC, ya kulle min windo, sannan ya koma (vangarensa), wani lokaci yana komawa sai a qara xauke wuta, shi kuma ba shi da nauyin barci, ko canza wuta aka yi yana tashi, sai ya zo ya kunna min fanka, ya kashe AC xin, ya bubbuxe windunan, kuma har yanzu yana yin hakan. Sannan kuma da abubuwa da dama, wanda mutum zai yi mamaki (in ya ji su)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 129). Shi ma Shaheed Sayyid Ahmad xaya daga cikin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya faxi yadda Shaikh xin ya rene shi tamkar uwa, wato yana masa duk wata hidima da xawainiyar da uwa ke yi wa xanta, ciki har da reno da sauransu. Ya ce; “Da yake ni ina da qani, sai ya zama an haife shi shekara xaya bayan an haife ni, sai ya zama ni an yaye ni tun kafin lokacin da ya kamata ya zama an yaye ni, sai ya zama Umma tana ji da qanina, sai ya zama ni kuma Abba ne yake ji da ni, sai ya zama da wanka da duk wasu abubuwa da ka san uwa tana yi wa yaro, to ni Abba ne yake min, har ya zama na fi sabawa da shi Abban fiye da Umman” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 55). Malama Maryam Sani, wacce makusanciya ce ga Malama Zeenat (uwargidan Shaikh Zakzaky) tana cewa; “Malam har girki yana yi (a gidansa), da yawanmu in ana wani “Programme” mun sha cin girkin Malam. Akwai ma lokacin da wata Yayata ta zo guna, amma sai ta sauqa a gidan Malam, sai ta ga malam ya shiga kicin ya yi wanke-wanke ya dafa abinci, aka kawo musu suka ci, ba ta ga Malama (matar Malam) ta shiga kicin xin ba ma, da ta komo take ce min ashe haka malaminku yake? Wannan ba qaramin tasiri ya yi mata ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 196). Ita ma Malama Maimunatu Abdullahi (uwargidan Shaheed Shaikh Muhammad Turi), ta labarta yadda Shaikh Zakzaky (H) ke hidimar gida ga iyalansa, ta ce; “Shi Malam rayuwarsa ta sha banban da yadda ‘yan uwa suke… Malam yana girki, sannan yana kula da ‘ya’yansa. Akwai wani xansa ma da yakan kwana a xakinsa, shi ne yake kula da shi, ya yi masa wanka da sauransu, ko kuma idan ana goyon yaro Malam yakan fito falo wurin ‘yan uwa ya canza masa nafkin, ya yi masa tsarki, ya nuna ma ‘yan uwa yadda ake wanke nafkin, da yadda ake saka shi… (Mun tava ziyartar Malam a gidansa) Sai muka samu yana girki, ya xora miyar taushe da tuwon shinkafa, har ma ya dafa mana shayi (muka sha), sai muka ga duk al’amuran da Malam ke yi addini ne” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 206). Wannan shaida ta iyalan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa, game da hidimar da yake wa iyalansa na ayyukan cikin gida da reno da kula da sauransu, babbar shaida ce ta koyi da halayyar Annabi (S) da Shaikh Zakzaky (H) ke da ita. Kuma a gefe guda, hakan na nuna karimci da maxaukakan halaye da xabi’unsa managarta, lallai rayuwar Shaikh Zakzaky sanfur ce ga al’ummah. KARANTARWARSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da ya yi fice a fagen karantarwa, domin bai da aiki a rayuwarsa face karatu da karantarwa ga ximbin xalibansa. Yana da tsarin karantarwa na dindindin a vangarori biyar, kama daga tafsirin Alqur’ani mai girma, karatun Nahjul-Balagah, karatun Daurori, da kuma Muhadharorin da ya saba gabatarwa a kusan ko da yaushe. Tunda farko dai, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya assasa Harka Islamiyyah ne akan karantarwa ta gina fikira da kyawawan xabi’un musulunci. Wannan karantarwa wacce ake kira ‘TA’ALIM’, ta cikinta ne ake sanin jauharin manufa da hadafin Harka Islamiyyah, ita ce asasi ko matakin farko da ake so kowane xan Harka Islamiyyah ya bi ta kai kafin isa ga sauran karatuttukan Shaikh (H). TAFSIRIN ALQUR’ANI : Shaikh Zakzaky (H) yana gabatar da tafsirin Alqur’ani mai girma a kowace ranar Laraba ta mako, wato yana da zaunannen tsari na yin tafsirin Alqur’ani wanda ba wani abu da ke sa ya xage tafsirin in ba tafiya qasar waje ya yi ba, hatta a lokutan gudanar da taruka da suke xaukar tsawon mako guda ana aiwatarwa, akan ware ranar Laraba a matsayin ranar tafsirin Alqur’ani ne a jadawalin, haka nan, ko ana ruwan sama ba ya xage tafsirin sai ya gudanar da shi. Salon tafsirin Shaikh Zakzaky (H) ya sha banban da na dukkan malamai, misali; A tafsirin Alqur’ani na farko da ya yi, tun daga “Suratul Fatiha” har zuwa “Suratun-Nass”, ya yi shi ne a salon Tarjama, inda ya riqa gabatar da taqaitattun bayanai game da ma’anonin ayoyin Alqur’ani ba tare da kawo ra’ayoyin masu tafsiri ko savaninsu ba. Amma da ya zo zagaye na biyu na tafsirin, sai ya riqa yin tafsirin a bisa doron bayanan Ahlis-Sunnah game da ma’anar ayoyin, wato idan ya karanto aya, sai ya yi tafsirinta ta mahangar Shi’a, sa’annan sai ya karanto tafsiri ko ruwayoyi da zantukan malamai da jagororin Ahlis-Sunnah da suka dace da wannan fassara ta Shi’a. Sa’annan, da ya sake dawowa zagaye na uku na tafsirin, sai ya zamo a wannan karon, yana tafsirin ne kawai da zallar ruwayoyi da hadisai na Ahlul-Bait (AS), da kuma zantuka da fahimtar jagorori da malaman Shi’a (Radhiyallahu Anhum). Wannan ya nuna wata baiwa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na Ihaxar iliminsa da kuma salon da yake bi wajan shiryar da al’umma.  NAHJUL BALAGAH : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gabatar da karatun littafin “Nahjul-Balagah” a duk ranar Litinin ta kowane mako, shi ma karatun “Nahjul-Balagah” kamar na tafsirin Alqur’ani ne, ba abin da ke kawar da shi sai in tafiya qasar waje ne. A wannan karatu na “Nahjul-Balagah” Shaikh Zakzaky (H) yana faxaxa bayanai sosai, tare da zurfafawa wajan hallale ma’anoni na kalmomin da littafin ke qunshe da su, kuma yakan zo da littattafai daban-daban dan faxaxa bayani ko qara bada haske kan wani abin da yake magana akansa, wannan ya sa zuwa yau an kwashe tsawon shekaru da dama Shaikh xin bai iya kaiwa ga sauke littafin ba har yanzu. DAURAR AMIRAI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gudanar da karatu mai zurfi a fannonin ilimummukan addini da dama tare da manyan almajiransa daga lokaci zuwa lokaci, shi tsarin wannan karatu da ake kira “Daurah”, ya kevanta ne kawai ga manyan almajiransa, musamman wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori, da sashen masu wasu Mas’uliyya a Harka Islamiyyah, da makamantansu. Shaikh Zakzaky (H) yana gudanar da wannan karatun Daurah ne ga manyan almajiransa duk bayan wata uku, kuma yakan shafe makwanni uku ne yana musu karatun a keve, a lokacin Daurar akan tattauna tare da zartar da muhimman shawarwari. DAURAR ‘YAN UWA MATA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yakan gudanar da irin wancan karatun Daurah ma ga ‘yan uwa mata masu Mas’uliya a Harka Islamiyyah. Ita ma wannan Daurah ta ‘yan uwa mata akan gudanar da ita ne tsawon makwanni uku, kuma akan shigeta ne da zarar an kammala ta ‘yan uwa maza, wakilan ‘yan uwa mata daga dukkanin Da’irori na faxin qasar sukan halarta. MUHADHARORI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gabatar da Muhadharori masu yawan gaske a rayuwarsa, kusan a kullum ba ya rasa gayyata ta gudanar da wata Muhadhara a wani taro, sannan a gefe guda yana da zaunannun Muhadharorin da yake gabatarwa shekara-shekara. Kamar zaman makokin Ashura na tsawon kwanaki 50, da Muhadharar Yaumu-Arba’een, da wafatin Manzon Allah (S), da Maulidin Shaikh Usman bin Fodiye, da Maulidin Manzon Allah (S), da Wafati da Maulidin Sayyida Zahra (SA), da Maulidin Imam Ali (AS), da Yaumul-Mab’ath, da Nisfu-Sha’aban, da Wafatin Amirul-Muminin (AS), da Dahwil-Ardh, da Eedul-Ghadeer da sauransu. Sannan a kullum yana cikin gabatar da Muhadharori ga Lajanoni da vangarorin Harka Islamiyyah, da halartar Mu’utamarori, da zuwa taruka da sauran gayyace-gayyacen da ake masa a ciki da wajan qasa. A taqaice, waxannan abubuwa suna daga cikin aikace-aikace da hidimar yaxa ilimi da koyarwar addini da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke gudanarwa a rayuwarsa. WALLAFE-WALLAFENSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai yi fice a fagen rubuce-rubuce da wallafe-wallafen littattafai ba, wataqil hakan yana da alaqa da yawan ayyukansa da qarancin samun dama da lokaci na zaman yin rubuce-rubucen. A wata magana da ya tava yi game da wallafa, ya yi ishara cewa a kowane fage da kowane fanni an yi ximbin rubuce-rubuce masu kima da gamsarwa, sun wadatar wajan sanin duk abin da ake neman masaniya a kansa, wataqil wannan falsafa ce ta sa Shaikh (H) ya fi maida hankali wajan tafiyar da lokutansa ga ibada fiye da zaman yin rubutu. Amma tattare da haka, Shaikh Zakzaky (H) ya rubuta littattafai guda uku da hannunsa, xaya na Turanci, xaya na Larabci, xaya kuma na Hausa, littattafan su ne;- “THE MISSION OF MAN ON EARTH”, wato “Manufar Halittar Xan Adam a Bayan Qasa”. “TARIHIN ZAZZAU” wato “The History of Zazzau”, wanda yake rubutawa da harshen Hausa. “AD’IYAATU NAWAFILIR-RAMADAN” wato “Addu’o’in Nafilfilin watan Ramadan” wanda ya rubuta da Larabci. A cikin waxannan littattafai guda uku, xaya ne aka samu damar kaiwa ga xab’insa, wato “Ad’iyaati Nawafilir-Ramadan”, sauran biyun zuwa yanzu bai iya samun damar kammala rubuta su ba. Amma a gefe guda, akwai ximbin littattafan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin harsunan Turanci da Hausa, wanda laccocinsa ne da yake gabatarwa a wurare da lokuta daban-daban ake rubutawa a maishe su littafi. Ba za mu iya ambatarsu gaba xaya ba saboda yawa, amma daga cikin fitattun akwai; “Nasihohi ga ‘Yan Uwa Musulmi”, na xaya zuwa na biyar, sai “Nijeriya Ina Mafita?” (wanda an ce har wani gwamna ya tava ba shi lambar yabo akan wannan littafin), sai “Rayuwar Imam Khumain (QS)” da sauransu. Sannan akwai jerin laccocin da yake yi a ranar tunawa da Shahidai “Yaumus-Shuhada”, wanda kowace lacca ana mayar da ita littafi xauke da sunan “Shahada Maganin Mutuwa”, akwai kuma laccocin da yake gabatarwa a zaman makokin Ashura da ake mayar da su littafi xauke da sunan “Jawaban Ashura”, akwai laccocin da yake gabatarwa ga matasan Harka Islamiyyah a lokutan taronsu na shekara-shekara, wanda ake mayarwa littafi xauke da sunan “Zuwa Ga Matasa”, akwai laccocin da yake gabatarwa a makon tunawa da Imam Khumain (QS), wato “Imam’s Week” da ake mayar da su littafi xauke da sunaye daban-daban. Akwai laccocin da yake gabatarwa a ranakun Maulidi da ake mayar da su littafi xauke da sunan “The Meassage”, akwai jerin laccocin da yake gabatarwa a wa’azozin dare a garuruwa, da laccocinsa na rufe tarukan Mu’utamar, da laccocinsa na tarukan qarawa juna ilimi da ake mayar da su qananan littattafai ana rabawa jama’a a bisa kulawar cibiya mai suna “Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky”, akwai ma jerin littattafai na zavavvun zantukansa da ake tattarawa wuri guda ana maishe su littafi da dai sauransu. HAUSARSA : Harshen Hausa shi ne yaren da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke magana da shi a rayuwarsa ta yau da kullum, duk da cewa yana jin harsuna aqalla huxu, wato Hausa, Turanci, Larabci da Fulatanci. Kamar yadda aka sani, Shaikh Zakzaky (H) xaya ne daga cikin bayin Allah waxanda Allah Ta’ala ya yi wa baiwar faxaka da lura da la’akari cikin komai na rayuwa, domin hatta a  furuci Shaikh (H) yana anfani ne da zavavvun kalmomin Hausa a jawabai da mu’amalolinsa, ba kawai yakan yi anfani da kalmomin da ya ji Hausawa suna furtawa ba ne, a’a, kafin Shaikh ya yi furuci da wata kalmar Hausa sai ya tantance ma’ana da kamalar kalmar, wato yakan yi anfani ne kawai da kalmomin da suka dace da koyarwar addini da tarbiyya. Kullum Shaikh (H) a faxake yake kan Hausar da yake furtawa. A wasu lokuta yakan yi magana kan rashin dacewar furta wasu kalmomi ko ‘Karin Magana’ na Hausa, a wasu lokuta kuma nazari da la’akari ne zai tabbatar maka cewa baya anfani da wasu kalmomi na Hausa. Ga ‘yan misalai akan haka;- DODO GUDA SUKE YI WA TSAFI : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana” a yayin da yake magana kan mutanen kirki, ko ma duk wani musulmi mai aqidar Tauhidi, wataqil kai ma za ka iya fahimtar rashin dacewar anfani da kalmar in ba ga maguzawa ma’abuta tsafi ba. RIGA MALAM QALU-BALE  : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana” a yayin da yake so ya kushe gaggawar wasu mutane, domin riga Malam zuwa masallaci abu ne mai kyau a musulunci, dan haka bai kamata a kushe yin hakan da “Karin Magana” ba.  QALU-BALE : Shaikh (H) ba ya nafani da kalmar Qalu-bale a yayin da yake so ya nuna ko ya yi wani “Challenge” ga wasu, domin in an bi zirin ma’anar ‘Qalu-bale’ za a taras kalmar ba ta da wani ma’ana in an kwatanta ta da ma’anar da aka xorata a kai, yakan yi anfani ne da kalmar “Kule” a madadinta.  IN GEMUN XAN UWANKA YA KAMA DA WUTA, TO, KA SHAFAWA NAKA RUWA : Wannan “Karin Magana” ma Shaikh (H) ba ya anfani da ita, ya sha faxi cewa karin maganar bai dace ba, domin musulunci yana qarfafa ‘yan uwantaka ne da taimakon juna. Don haka, in gemun xan uwanka ya kama da wuta, kamata ya yi ka kawo masa gudunmawar ruwa ka taya shi kashewa, in kun kashe wutar, to, kai da shi duk sai ku shiga shafawa gemunan naku ruwa don kar wani a cikinku ya sake samun gobarar gemu! Amma in gemun xan uwanka ya kama da wuta, sai ka ja gefe ka shafawa naka ruwa, ai ka nuna halin ko in kula gare shi da son kanka kenan, alhali musulunci ya yi hani ga hakan. Ko ba a lura ba?  SO DUK SO NE, AMMA SON KAI YA FI : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana”, domin ya savawa karantarwar addinin musulunci. Hafizahullah ya nuna cewa cikar imanin mutum shi ne ya so wa xan uwansa abin da yake so ga kansa, ayar Alqur’ani a “Suratul Hashr” Aya ta 9 ta nuna cewa mumini cikakke shi ne wanda zai hana kansa ya baiwa xan uwansa abin da yake so. Sannan musulunci ya haramta son kai, dan haka wannan karin maganar ya savawa koyarwar addini, domin yana koyar da son zuciya ne da handama. Shaikh (H) ya canza wannan “Karin Magana” da wani sabo, inda yake cewa “So duk so ne, amma son xan uwa ya fi”.    WAL-BANI WAL-BAKA, WAL-HANANI WAL-QEMEME : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana”, domin ya savawa koyarwar addini. Wannan karin maganar yana koyawa mutane rowa ne da son kai a fakaice, don yana cewa ne, in mutum yana baka abin hannunsa, to, kai ma sai ka riqa ba shi naka, in kuma yana hana ka na shi, to, kai ma kar ka ba shi naka ko da yana cikin matuqar buqata! A Hadisai da yawa Manzon Allah (S) ya yi umarni ga musulmi cewa; “Ka rika yin kyauta ga mai yi maka rowa, ka rika kyautatawa mai munana maka”, dan haka karin maganar “Wal-bani Wal-baka…” ya savawa karantarwar addini. Shaikh (H) ya canza wannan “Karin Magana” da wani sabo, inda ya ce; “Wal-bani wal-baka, Wal-hanani Wal-baka!”. Ko ba a lura ba?   IN KA YI MUN KAN KARA, ZAN MAKA NA ITACE : Shaikh Zakzaky (H) ba ya cewa azzaluman da suke cutar da shi, “Duk wanda yai mana kan kara, za mu yi masa na itace”, domin yin hakan ya savawa karantarwar addini. Addini bai hana ramuwa ba, amma ya hana wuce gona da iri akan ramuwa. In aka yi maka wani abu to ya halasta ka rama daidai yadda aka yi ma ne, amma xaukar fansa fiye da laifin da aka yi maka laifi ne a musulunci, kuma yin hakan ne abin da wannan “Karin Magana” ke koyarwa.  YA TAKA MUHIMMIYAR RAWA : A yayin da Bahaushe ke so ya bayyana girman gudumawar da wani ya bayar, yakan ce; “Wane ya taka muhimmiyar rawa a abu kaza”. Sheikh (H) ba ya anfani da wannan karin maganar, domin taka rawa ba wani abu ne kyakykyawa a musulunci ba, sannan ko a al’adance ma mutum mai kima da daraja ba ya rawa, dan haka bai kamata a kwatanta wani abu maras kima ga wani mutum mai daraja da kima ba, maimakon “Ya Taka Rawa”, Shaikh (H) yakan ce “Ya Bada Muhimmiyar Gudunmawa” ne, ko ba lura ba? more_vert RefreshRate ApplicationMore Application SHAIK IBRAHEEM ZAKZAKY (H) Jagoran harka islamiyyah a Afrika  homeGidashareKyautarwapeopleMasaniyahelpIzinimailTuntuba   BABI NA BIYAR RAYUWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) A QANGIN AZZALUMAI GWAMNATOCIN DA SUKA XAURE SHI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha kamu da xauri a hannun hukumomin Nijeriya, an sha kama shi da azabtar da shi da xaure shi a lokuta daban-daban, ya zuwa yanzu hukumomin Nijeriya sun kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) har sau 10, kuma jumlatan shekarun da ya yi a tsare sun doshi shekaru 15. Ya zauna a gidajen kurkuku na jihohin Nijeriya daban-daban, daga ciki ya zauna a kurkukun Zariya, Kaduna, Sakkwato, Inugu, Fatakwal, Lagos da Abuja, kuma an sha tsare shi a wuraren azabtarwa da bincike, daga ciki akwai inda ake qira “Interrogation Center” a Lagos, da kuma wuraren tsaro na musamman na jami’an leqen asirin DSS a Abuja. Bisa abin da ke tabbace a zahiri, daga lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara Da’awarsa a shekarar 1980 zuwa yanzu, mafi yawan gwamnatocin Nijeriya sun xaure shi a gidan yari, wasu gwamnatocin ma sun masa xauri ko kamu fiye da xaya, yayin da wasu gwamnatocin ke gadar ci gaba da xaure shi da gwamnatocin da suka gabace su suka yi. Gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo ta tsare shi a shekarar 1979 a Zariya, ta kuma sake kama shi a Sakkwato ta tsare a farkon shekarar 1981. Gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari ta kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta xaure shi tun daga wajajen tsakiyar shekarar 1981 zuwa 1984. Gwamnatin mulkin Soja ta Janar Muhammadu Buhari, ta xaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wajajen qarshen shekarar 1984. Gwamnatin mulkin Soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta xaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1987 zuwa 1989. Gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sake kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1992. Gwamnatin mulkin kama karya ta Janar Sani Abacha ta xaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1996 zuwa qarshen shekarar 1998.  Gwamnatin mulkin danniyar farar hula ta Muhammadu Buhari, ta kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta tsare shi a qarshen shekarar 2015 wanda har zuwa rubuta wannan littafi a farkon shekarar 2017 ba a sake shi ba. JADAWALIN KURKUKUN DA YA YI : Ga tsarin gidajen kurkukun da Shaikh Zakzaky (H) ya yi, da daxewar da ya yi cikin kowannensu;  Bisa wannan jadawali, za mu ga cewa gwamnatocin Soja ne suka fi yawan kamawa da tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma zuwa yanzu an tsare Shaikh (H) a wuraren tsarewa aqalla goma sha bakwai, daga cikin tsarewar da aka masa, an tava tsare shi a “Dungeon” wani wurin tsarewa na qarqashin qasa wanda mutum ba ya iya banbance dare da rana. A wata hira Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “(An tsare mu) a wani wuri wanda yake shi wannan wurin ba akan gane dare ko rana ba, amma wani lokaci akan fito da mu (dan suna yarda mutum ya yi wanka sau xaya a mako), sai a fito da mutane wajan su hamsin duk a wuri xaya, a sa musu bokitai (su tuve su yi wanka), sai su ga ni ban fito ba saboda suna yin tsirara, har wani ya ce mun; kai ba za ka yi wankan ba ne? Sai na yi masa shiru, sai ya ce; oho, don kai musulmi ne ko? To, sai ya yarda ni in dinga yin wankana ni kaxai” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 16). Saboda tsabar tsarewar da aka yi ta yi wa Shaikh Zakzaky (H), an haifi uku daga cikin ‘ya’yansa ne a lokutan da yake tsare a gidajen kurkuku, misali, an haifi xansa Muhammad ne yana kurkukun Kirikiri a Lagos, an haifi Nusaiba yana kurkukun Kaduna, an haifi Hammad yana kurkukun Fatakwal. An sha azabtar da shi da nau’o’in azaba a kurkuku, wanda wasu azabobin har yanzu tasirinsu yakan motsa a jikinsa daga lokaci zuwa lokaci. YUNQURIN KASHE SHI : Bisa lura, za mu ga an samu tazara mai yawa ta kimanin shekaru 17 (1998-2015), (wato tun fara aiwatar da mulkin farar hula na jamhuriya ta uku) ba a kama Shaikh Zakzaky (H) ba sai a qarshen shekarar 2015, wanda wasu ke ganin kamar an qyale shi ne; “A a, sun lura ne cewa duk kame-kamen da aka yi wa Sayyid Zakzaky a baya, ya daxa havaka abin da yake kira akai ne. Bisa asasin haka, sai suka ga cewa wannan kamun da xauri bai da wani anfani ga manufarsu, saboda haka sai suka canza salo da kuma makirci. “Wannan sabon salon shi ne yunqurin kashe Sayyid Zakzaky (H). Shi ya sa in muka duba a cikin waxannan shekaru da aka samu tazara na rashin kama Malam, babban abun da suka sa ma gaba shi ne kashe Malam xin ko ta halin qaqa! Za mu ga sun yi qulle-qulle da makirce-makirce iri-iri domin su cimma wannan manufa tasu, amma Allah Ta’ala bisa ikonsa duk ya wargaza shirin nasu!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 22).  Misali; Shugaban qasar Nijeriya a Alhaji Ummaru Musa Yar’adua a shekarar 2008 ya bada umarnin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin mako uku, amma sai Allah Ta’ala ya tona asirin shirin, wanda daga qarshe ya wargaje sakamakon kamuwa da mummunar jinyar da Yar’aduwan ya yi, wacce ta yi ajalinsa cikin qanqanin lokaci. Bayan mutuwar Yar’adua, sai aka rantsar da shugaban qasa Goodluck Ebele Jonathan, sai shi ma ya xora a inda Yar’adua ya tsaya kan batun kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), inda jami’an tsaron gida da haxin gwiwar na qasashen waje (musamman Amurka da Isra’ila) suka duqufa ka’in da na’in na ganin sun kashe Shaikh Zakzaky (H). Sun yi ta tsara hare-hare da nufin kashe shi a hanyarsa ta zuwa Hussainiyyah Baqiyatullah ko a gidansa ko a hanyarsa ta zuwa wa’azi wani gari, amma Allah Ta’ala ya riqa wargaza duk qulle-qullen nasu yana ba shi kariya, har ta kai ga a cikin duhun wani dare na shekarar 2012 sun zo da wani jirgin sama da zai yi ‘Bombing’ xin gidan Shaikh Zakzaky (H), amma Allah ya hana su ganin gidan, suka yi ta shawagi suka koma. Haka nan, a shekarar 2012 gwamnatin Jonathan ta ba fitaccen kamfanin kisan kai (Assasins) na wani shararre kuma qwararren makashi mai suna Patrick Williams kwangilar kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Kanfanin mai mazauni a Amurka kwararre ne a fagen kashe mutane a duniya. Lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu labarin wannan shiri, ya yi jawabi ga ximbin jama’a a filin Idi na birnin Zariya lokacin rufe muzaharar maulidi ta 17 ga watan Rabi’ul Auwal na shekarar 1433. A ciki yake cewa, “Na farko, kai Patrick Williams sai in ce maka ‘Raina yana hannun Allah ne ba yana hannunka ba ne!’ Kuma Allah Ta’ala na yi imani da shi, ya ce “Ba ya yiwuwa ga rai ta mutu sai da izinin Allah, abu ne yankakke rubutacce!”.  Haka nan, a farkon shekara 2015, qwararrun ‘yan ina da kisa daga cikin sojojin Amurka da aka xauko hayarsu musamman don kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun xana masa tarko a hanyar zuwa Hussainiyya inda ya saba gabatar da Tafsiri, amma sai Allah Ta’ala ya aiko da ruwan sama mai tsanani ya wargaza shirinsu. QOQARIN HALAKA SHI A KURKUKU : A wasu kurkukun da aka tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) an yi ta haxa shi da qwararrun makasa da masu shaye-shaye da mahaukata, (duk dai dan su kashe shi, sai su kuma hukumomi su fake da cewa hatsaniya ce ta haxa shi da wani a kurkukun suka yi faxa har ya kai shi ga rasa ransa). Misali; A kurkukun Sakkwato, an haxa shi da wani qwararren xan ta’adda, wanda kuma xan sanda ne na ‘Mobile Police’, wanda shaye-shaye ya juyar masa da qwaqwalwa, ana kiransa Jasper, qato ne qaqqarfa. Da Shaikh Zakzaky (H) yake magana game da Jasper ya ce; “Ya tava xaukar Alqur’aninmu haka, sai muka ce masa; kai Alqur’ani ne, sai ya wurgar! Kuma sai ya kama gilas xin ido na wani xan uwa da bai gani sosai, kafin ka ce haka ya mutsuttsuka shi ya watsar… kuma sai kawai ya malala fitsari (a cikin xakin da muke), kuma in ya doki bango sai ka ji ya yi motsi! Haka dai Allah ya kiyaye mu, amma mun zauna tare da shi a xaki xaya” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 16). Shaikh Zakzaky (H) ya sake bada labarin wani mahaukaci da aka haxa su zama a wani kurkuku, ya ce; “Haka kuma wata rana aka zo da wani tuburan, ina ga shi mahaukaci ne ma tuburan sosai xaure cikin sarqa a qafafunsa, …To, haka dai (muka zauna) ya yi ta haukatakunsa, har kashinsa yana ci, sai ya xauko fo wai zai yi kashi ya ci in gani, sai na ce masa in ka kuskura zan mangareka, to, sai na nuna masa nima mahaukaci ne, na ce masa ina fasa kan mutane! To, sai ya ji tsoron fasa kai xin, to yadda na qwaci kaina kenan, daga baya dai Alhamdulillah aka xauke shi, ban san inda aka kai shi ba”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 17-18 da Tasarrufi). A kurkukun Fatakwal kuwa, an haxa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a xaki xaya da wani qwararren xan ina da kisa na CIA, Ba’amurke ne baqar fata, yana kiran kansa “Jew” wato Bayahude, amma a kurkukun suna ce masa Tony ko Sony, kuma ya daxe a hukumar ta CIA yana aiki, har ma ya tsufa. Ya yi aikin leqen asiri da na kisan kai a qasashen duniya da dama, a wata hirarsu ya faxawa Shaikh Zakzaky cewa; Bari in gaya maka gaskiya, ni an bani kwangila na kashe mutane da yawa, kuma har yanzun akwai waxanda aka ce in kashe su, kuma zan kashe sun!” Shaikh Zakzaky (H) ya ce; Ko saboda ni suka kawo shi, wallahu’a’alamu, to in ma don ni ne Allah Ta’ala dai ya hana shi (zartar da mummunar manufarsa), bai samu cimma burinsa ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 19-20, bisa taqaitawa). AZABTAR DA SHI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi na azabtarwa a hannun azzaluman mahukunta a lokuta daban-daban a tsawon wannan Da’awa tasa ta Harka Islamiyyah. Za a iya wallafa manyan littattafai akan zallar azabtarwar da ya sha da irin jarabawowin da ya fuskanta a hannun hukumomin Nijeriya, amma bari mu xan yi tsokaci kawai a matsayin misali. Duk da cewa Shaikh Zakzaky (H) ma’abucin tsabta ne da tsananin qin datti da dauxa, amma da aka kama shi a Sakkwato cikin shekarar 1981 aka tsare, an hana shi yin wanka da wanki na tsawon makwanni masu yawa, a wani jawabinsa yana cewa; “Lokacin da muke tsare a Sakkwato, an haxa mu Sel guda da mahaukaci, an buqatar da mu ga rashin wanka na makwanni, wankanka shi ne ka xauko hannunka ka mulmula dauxa ka jefar, muka yi makwanni a haka, ba wanka ballantana wanki, riga ba ta sawuwa sai dai na dole”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 213). A wani misali da yake bayarwa na jarabawar da ya fuskanta a gidajen kurkukun ya ce; “An buqatar da ni tare da wasu ‘yan uwa da muke tsare ga qwarqwata a jiki tare da kuxin cizo, ko’ina ka shafa a jikinka kuxin cizo ne da qwarqwata, har ta kai ma lokacin da aka kai ni kurkukun Inugu sai da aka yi min aski qwalkwabo, domin duk qwarqwata ta cinye kan! Kuma an buqatar da ni zama da faxe (takalma irin na danqo), ina ta yi masa faci har shekara uku, kuma an buqatar da ni a kurkukun Inugu in yi wanka ba sabulu har tsawon wata shida, kuma ba man shafawa, har jini na ketowa (a jikina saboda bushewar fata)” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 214). Sannan an tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a kurkukun Kirikiri dake Legos tsawon watanni, shi Kiriri wuri ne na azabtarwa da sunan bincike, akwai karikitai na azabtarwa iri-iri a wurin. Shaikh Zakzaky (H) ya ce ko sauro ka kashe a Kirikiri sai an yi maka bulala, wai kana kashe yaran gwamnati, kuma hatta tufafi riga da wando ba a yarda mutum ya shiga da su ba, sai dai a shigar da mutum daga shi sai Pant. Lokacin da aka kai Shaikh Zakzaky (H) suka ce ya tuve tufafinsa, ya ce wannan kam ba zai yiwu ba, dole da tufafinsa zai shiga, su kuma suka ce bai isa ba! suka kama shi da kokawa za su tuve masa tufafi da qarfin tsiya, kawai sai jinsa ya yi a cikin xakin tare da tufafinsa, dole suka haqura suka qyale shi da tufafin, har waxanda ya samu a cikin wurin suna ta mamaki, shi kansa Shaikh Zakzaky (H) yana cewa yana ganin shi ne mutum na farko da ya shiga Kirikiri da tufafi a jikinsa. A Kirikirin akwai wani sashen azabtarwa na musamman, wanda sel ne a qarqashin qasa, a wajan ba a gane banbancin dare da rana, wuri ne mai tsananin duhu, wanda ko tafin hannunka ba za ka iya gani ba, a cikin wurin aka cusa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na tsawon lokaci, Shaikh (H) ya bada labarin wurin a wata laccarsa, ya ce; “A wancan lokacin yadda na riqa yi nike gane lokutan Sallah shi ne; Suna kawo abinci da rana, in za su kawo abincin to gab da Azuhur suke kawowa, to in na ci da yake kofin ruwa guda xaya ne za a ba mutum, to sai in sha rabi in yi Alwala da rabi. “To, sallar Magriba yadda nike gane ta shi ne, in an kawo abincin yamma, saboda galibi sukan kawo (abincin) gab da Magriba ne, to jim kaxan sai in yi sallar Magriba. To, sallar Asuba ba yadda za a yi in gane, yadda nikan yi wani lokaci (shi ne), in na yi sallar Asuba bisa tsammanin ta yi, sai in zauna in yi ta yin Azkar har lokacin da suka zo da safe suna qwanqwasa qofa suna tambayar mutum nawa ne cikin wannan xakin, to qarfe bakwai ne suke wannan, to sai in yi ‘Estimate’ (in qiyasta) daga lokacin da na zauna zuwa yanzu an yi awa nawa? To wani lokaci sai ta bayyana na yi sallar asubar ne qarfe ukku na dare, ko ma qarfe xayan dare” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 136). Haka nan a waqi’ar Maulud ta 2015 wadda sojoji suka kashe almajiransa kusan mutum Dubu kafin su kai gare shi, da suka isa xakin da yake ciki suka yi masa ruwan wuta, harsashi ya farfasa jikinsa har sai da idonsa na hagu ya zazzago ya fito waje, shi ya kama idon ya mayar da kansa, idon dama kuma harsashi ya sauqa a samansa shi ma ya samu matsala. An yi masa harbi a wurare daban-daban aqalla goma sha xaya a jikinsa, suka xauke shi ba rai suka tafi da shi, sai bayan kwana 4 Allah Ta’ala ya dawo masa da ransa ya farfaxo. Tattare da cewa bayan tsawon lokaci ya yi ta samun sauqin raunukan da aka masa, amma idonsa na hagu yana masa tsananin ciwo da zogi, ta kai ga ba ya iya karatun Alqur’ani saboda ba ya ganin rubutun, kuma a hakan gwamnati ta hana a fita da shi waje don yi masa aikin idon, burin da jami’an tsaro ke da shi shi ne lalacewar duk idanuwan nasa guda biyu. Wannan kaxan kenan daga gallzawar da Shaikh Zakzaky (H) ya sha a hannun azzalumai, a taqaice, Shaikh Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi na azabtarwa sosai daga vangaren azzaluman mahukunta, sun sha kama shi da xaure shi da gallaza masa ta hanyoyin azabtarwa daban-daban, amma tattare da haka bai tava saranda ko miqa musu wuya ba, hasali ma qarin yaqini da sabati yake samu akan abin da ya sa a gaba na ceto al’umma daga qangi. YUNQURIN KASHE SHI : Allah ne kaxai ya san iya yawan yunqurin da aka yi ta yi na kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokuta da wurare daban-daban, kama daga yunqurin kisan gilla na zahiri zuwa kisa ta hanyar sihiri da tsatsuba. A matsayin misali, ga jerin yunqurin kisan da aka yi masa wanda suka bayyana a zahiri. NA FARKO : Yunqurin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) karo na farko da ya bayyana shi ne wanda aka shirya shi tun Shaikh xin yana xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, wato farko-farkon Da’awarsa, wanda aka shirya yin anfani da wasu xalibai da za su je xakin da yake cikin dare su kashe shi, an samu labarin wannan shiri ne daga wani xalibi mai suna Alpha Bolaji. NA BIYU : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Ibraheem Babangida ta yi a lokacin da aka kai shi Kirikiri a 1992, lokacin an shirya za a yi masa kwaf xaya ne kawai a gama da shi, to amma sai Allah ya wargaza shirin, sai suka sake shi da gaggawa. NA UKU: Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da ‘yan Tawayiya suka yi, bayan sun rutsa shi a masallacin Jami’ar Bayero dake Kano, a shekarar 1994. NA HUXU : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Abacha ta yi a shekarar 1996 a kurkukun Kaduna, inda aka shirya kashe shi ta hanyar allurar mutuwa kamar yadda aka yi wa Janar Shehu Musa Yar’adua a lokacin. NA BIYAR : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin farar hula ta Ummaru Musa Yar’adua ta yi a shekarar 2010, wacce ta tsara “Bombing” xin gidan Shaikh da kashe duk waxanda ke cikin gidan, an samu kwafin “BluePrint” ne na umarnin yin hakan. NA SHIDA : Yunqurin kashe shi da hukumar CIA ta Amurka ta yi a ranar bikin cikarsa shekaru 63 a duniya cikin shekarar 2014, wanda suka turo qwararrun makasa jar fata rufe da fuskokinsu da “Mask” irin na “Ku Klu Klax”. Suka voye a hanya da nufin aiwatar da mummunan nufinsu, amma sai Allah Ta’ala ya aiko da ruwan sama mai tsanani ya rusa shirinsu. NA BAKWAI : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Ebele Jonathan ta yi ta yi a shekaru biyunta na qarshe (2013-2015), wanda a qarshe suka yi nasarar kashe ‘ya’yansa uku a shekarar 2014 a madadin gagararsu kasuwa da ya yi. NA TAKWAS : Yunqurin kashe shi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a qarshen shekarar 2015, wanda ya janyo kashe almajiransa maza da mata kusan mutum Dubu da ke ba shi kariya, da kuma yi masa ruwan harsashi a goshinsa da qirjinsa da cinyoyinsa a qoqarinsu na halaka shi, amma Allah ya raya shi da ikonsa. Waxannan sune yunqure-yunquren kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da aka sha yi, wanda suka bayyana a fili qarara kamar hasken rana, wanda duniya ta shaida kuma ake da dalilai da hujjoji na zahiri a kansu. Amma kamar yadda muka faxa a baya, ba suke nan ba, yunqurin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Allah ne kaxai ya san iyakarsa, mun ambaci fitattu ne kawai a matsayin misali. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ BABI NA SHIDA NASARORI DA XAUKAKAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) KEVANTATTUN NASARORINSA : Baki bai isa ya iya faxin dukkanin nasarorin da jagoran Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a rayuwarsa ba, haka nan, alqalami ba zai tava iya rubuta waxannan nasarori ba, domin sun fi qarfin iyakancewa balle kewayewa da sani, amma tunda tsokaci muke yi akan komai na rayuwar jagoran, wannan ma bari mu yi tsokaci kaxan akai. NASARA TA XAYA: Nasara ta farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a rayuwarsa ita ce Shiriya! Babu shakka Allah Ta’ala ya so shi ya zave shi ya kuma fifita shi da shiriya a birbishin sauran malamai. A duk tarihin Shaikh Zakzaky (H) bai tava yin riqo da tafarkin vata ba, ya fito ne daga tsatso mai daraja, gida na malamta, zuriyya ma’abuciyar addini, da kuma tarbiyya ta gari. Duk wata nasara da xan adam ke samu a rayuwa a bayan shiriyar Ubangiji take. NASARA TA BIYU : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi nasarar canza rayuwar ximbin mutane daga vata zuwa shiriya, daga kuskure zuwa ga daidai, ya ‘yanto tunanin mutane daga ximuwa zuwa tunani mai kyau, ya raya zukatan da suka mutu, ya farfaxo da waxanda suka suma. Ta sanadin Da’awarsa da dama daga masu aqidar kwaminisanci sun canza zuwa aqidun Musulunci, masu kwana barci sun koyi raya dare da Tahajjud, masu yini cin abinci sun koyi azumomin nafilfili, masu mugayen xabi’u sun canza zuwa kyawawa, masu rowa sun koyi kyauta, masu son kai sun koyi Iythari, mata masu tabarruji sun koyi suturtuwa da Hijabi, mazajen da ke wulaqanta mata sun koyi mutuntasu, matsorata sun zama jarumai, jahilan addini sun zama malamai, ‘yan Malikiyya sun zama ‘yan Ja’afariyyah, nasarar Shaikh Zakzaky (H) wajan sauya al’umma ba ta qidayuwa! NASARA TA UKU : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi nasarar canza Miliyoyin mutane daga aqidar Sunnanci zuwa na Shi’anci, wanda tarihi bai tava ganin irinsa ba. Domin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne kawai mutum xaya tilo da aka yi qiyasin ya yi nasarar canza sama da mutum miliyan Ashirin da Biyar (zuwa yanzu a nahiyar Afirka) daga aqidar Ahlis-Sunnah zuwa tafarkin Ahlul-Bait (AS). Wannan irin nasara tarihin xan adam bai tava ganin irinta ba tun bayan bayyanar Shi’anci a bayan qasa. Batun nasarorin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya cimma a rayuwarsa abu ne da bai da iyaka, dan haka za mu taqaitu da wannan a matsayin misali. NASARORINSA GA AL’UMMAH : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya cimma ximbin nasarori ta fuskoki da dama na kawo sauyi a al’ummar da yake rayuwa a cikinta, mafi yawan nasarorin Shaikh Zakzaky (H) nasarori ne na baxini, nasarori ne na raya zukata da canza tunane-tunanen al’umma da wasu I’itiqadodinsu iri-iri zuwa sahihan tunanuka ta fuskar addini. Amma tattare da haka, akwai ximbin nasarori na kawo sauyi a zahirin rayuwar al’umma da ido zai iya shaidawa ta fuskar addini, al’ada da “Social Issues”, wanda Shaikh xin ya samar ga al’ummar da yake rayuwa a cikinta, ga wasu kaxan daga ciki. SANYA HIJABI : Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ce ta zo da sanya Hijabi ga mata musulmi a Nijeriya, domin kafin Da’awarsa, ba wanda ya san mata da sanya Hijabi a Nijeriya. Tun bayan Jihadin Shehu Xan Fodiye (RA) mata suka watsar da sanya Hijabi. Duk wanda ya wanzu kafin bayyanar Shaikh Zakzaky (H) shaida ne cewa bai ga sanya Hijabi a gidansu ba. Mata sun fara suturtuwa da kammalallen Hijabi ne sakamakon Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). MATA A ADDINI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara shigo da mata fagen addini a wannan nahiya. A baya a wannan al’umma tamu ba a san yin hidimar addini da mata ba, abin da kawai aka sani shi ne fitar tsofaffin mata tuguf-tuguf zuwa masallacin juma’a da na Idi. Amma sakamakon Da’awar Shaikh Zakzaky (H) yanzu duk wata hidima ta addini da mata ake yi, kama daga wa’azozi, tarukan qarawa juna ilimi, muzaharori, I’itikafi da duk wata hidima ta addini. Sannan Da’awarsa ce ta fara ba matan aure ‘yancin ci gaba da karatun addini daga gidajen aurensu, shi ya fara samar da makarantar mata kafin Wahabiyanci ya mamaye fagen daga baya. MUZAHARA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya koyawa al’ummar musulmin wannan nahiya yin Muzahara ta fuskar addini. A baya ba a san yin Muzahara don nuna farin ciki, ko tallata wani abu na addini, ko dan nuna rashin yarda da rashin amincewa kan wani abu da ya shafi cutar da Musulmi ko Musulunci ba. Shaikh Zakzaky (H) ne ya fara yin Muzahara da sunan addini a tarihin Nijeriya, yanzu ta kai ga kusan duk qungiyoyin addini suna yin Muzahara ko gangami dan nuna farin ciki (kamar Muzaharar Maulidi), ko dan nuna rashin amincewa da tozarta addini, ko dan bayyana wata manufa tasu. I’ITIKAFI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara yin I’itikafi a Masallaci a watan Ramadan a tarihin Nijeriya. Tun Shaikh yana matashi yake shiga I’itikafi shi kaxai a masallaci. Kafin ya aikata I’itikafi a aikce ba a san I’itikafi a zahiri ba, an dai san bayanin I’itikafi a babuka na littattafan Fiqihu. Dan haka, duk wanda yake I’itikafi a Nijeriya ya kwaikwaya ne daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa. Wannan wani abu ne sallamamme da ba wanda ya jahilce shi sai mai qarancin masaniya da rashin lura da al’amura. KARE ANNABI (S) : Kafin bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), al’ummar wannan nahiya ba ta san hanyar da ya kamata a bi wajan kare martabar Manzon Allah (S) ba. Ko da wani ya ci zarafin Annabi (S) musulmi sukan ji takaici ne kawai a ransu, amma ba sa iya yin wani katavus na nuna rashin amincewa da hakan. Hatta a farkon lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara kare martabar Annabi (S) ta hanyar nuna rashin amincewa da zagi ko cin zarafinsa, sai da ya fuskanci tsattsauran martani daga waxanda ake kallonsu a matsayin malamai da jagororin addini. A nahiyar Afirka ta yamma baki xaya, Shaikh Zakzaky (H) ne ya koya wa musulmi yadda ake kare martabar Annabi (S) ta hanyar mayar da martani, rubuce-rubuce, da Muzaharorin Allah wadai na nuna rashin amincewa. Ta haka musulmin wannan nahiya suka koyi kare martabar Annabi (S) da martabar addini idan an tava shi. HAXIN KAI : Kusan kowa shaida ne cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi ta fafutukar wayar da kan al’ummar Nijeriya wajan ganin sun fahimci juna tare da sanin tushen matsalarsu maimakon gaba da faxace-faxace da juna. Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta fara yaxuwa ne a daidai lokacin da Wahabiyanci ke ganiyar mamaya da yaxa munanan aqidunsa na kafirta musulmi da dasa gaba da qiyayya a junansu.  Shaikh Zakzaky (H) ya yi ta fafutukar kawar da gaba a tsakanin musulmi da kuma hana faxace-faxacen qabilanci da na addini da ya addabi al’ummarmu. Bayan tsawon shekaru ne Shaikh (H) ya yi nasarar daqile habaqar gaba tsakanin Izala da Xarika, da kuma kashe-kashen qabilanci tsakanin Musulmi da Kirista. Ta kai ga Shaikh (H) ya samar da “Makon Haxin kan Musulmi” wanda ake haxa malaman musulunci na qungiyoyi daban-daban su yi jawabai. Da kuma bikin “Sallah Feast” wanda ake haxa shugabannin Kirista da na musulmi waje xaya su tattauna don samun kusanci da fahimtar juna. Ta haka Shaikh (H) ya yi nasarar kashe kaifin hargitsin Qabilanci da na Addini da Siyasa da ma rage gaba a tsakanin al’umma. DOGARO DA KAI : Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta koyawa qungiyoyin addini dogaro da kai wajan qoqarin samar da kuxaxen gudanar da ayyukansu da kansu. Domin a baya qungiyoyin addini sun dogara ne kacokam ga tallafin gwamnati da gudunmawar gwamnatoci da qungiyoyi na qasashen waje wajan tafiyar da al’amuransu, sam ba su iya yin abu da kansu ba, komai yi musu ake yi, a gina musu Masallaci, a saya musu motocin zuwa wa’azi, a ba su kuxin gudanar da taruka da sauransu. Malamai sun zama Banbaxawa yaran masu mulki, suna jurewa kowane wulaqanci daga mahukunta don su ci gaba da samun abin da za su rayu da shi. Sai Shaikh Zakzaky (H) ya zo da Da’awar da ba ruwanta da kwabon wani, ba ta buqatar tallafin gwamnatin qasa balle na qasashen waje, ba ta buqatar gudunmawar masu kuxi balle na qungiyoyin qasa da qasa. Da’awa ce da ta dogara kacokaf da gudunmawar membobinta kaxai, duk abin da za a yi za a haxa taro sisi ne daga membobi a yi shi, ba a neman gudunmawar gwamnati ko ta qasashen waje. Wannan ne kuma sirrin da ya ba Da’awar Shaikh Zakzaky cikakken ‘yanci, ba wani mai ikon juya Harka Islamiyya daga waje ko daga cikin gida, domin bai da tasirin da zai iya sawa a yi wani abin da yake so, ko ya hana yin abin da ba ya so. RAYA MASALLACI : A bisa al’adar al’ummar wannan nahiya, masallaci wurin yin Sallah ne kawai, ba a komai a cikinsa sai Sallah. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara raya masallaci ta hanyar yin ayyukan addini a cikinsa, a lokacin da yake xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello ya maido da dukkan tarukan qungiyar MSS zuwa masallaci. A wani jawabinsa yana cewa;- “Ni na tabbatar ba mun gani a aikace a wajan wani bane, mun karanta ne a littafi muka ga cewa a lokacin Annabi (S) masallacin Annabi nan ne cibiyar addini, a nan ne Annabi (S) yake koyarwa, a nan ne yake wa’azi, a nan yake alqalanci, a nan yake sasanta tsakanin mutane, a nan yake karvar baqi daga qasashe daban-daban. Wato masallaci a lokacinsa cikakkiyar cibiya ce ta dukkan ayyukan addini, a nan ake yin taro a yi Mashwara a tattauna shawarwari, haka nan ma tattauna dabarun yaqi da komi da komi duk a masallacin Annabi (S) ake yi a wancan lokacin. “To, sai muka ce ai a karatu muna karantawa (cewa) komai a zamanin Annabi a masallaci ake yi, amma mu ba mu yin komai a masallaci (sai Sallah). Sai muka ce to harkokin da muke yi na addini mu koma da shi Masallaci. To, sai muka qira lacca irin wanda za a gayyato Malami a ba shi wani Maudhu’i ya yi magana akai, sai muka yi a masallaci, to (ai kuwa) sai muka sha surutu, wai yin lacca a masallaci ba a ‘Assambily Hall’ ba! (Saboda su mutane ba su saba da ganin haka ba a wancan lokacin)”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 71-72). Hatta wa’azin da yanzu ake yi a kusan dukkan masallatai ranar Juma’a kafin zuwan liman, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara assasa shi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kafinsa ba a san da wannan ba, wanda a yau za mu ga cewa masallatai da dama har da na Wahabiyawa suna yi. Amma yanzu saboda yadda abin ya zamo jiki sai a xauka tun asali ma haka abin yake, alhali a 70s ne Shaikh Zakzaky ya sunnanta hakan. RAYA SUNAYE : A bisa al’adar al’ummar wannan nahiya (duk da kasancewarsu musulmi), amma ba su cika qiran mutane da cikakkun sunayensu na addini ko na yanka ba, sun fi qiransu da sunaye na al’ada. Za ka ji suna qiran Ibrahim (Iro), Idris (Idi), Usman (Manu), Abdullahi (Audu), Abubakar (Garba), Dawud (Dauda), Adamu (Ado), Salihu (Salele), Mahmud (Mudi), Muhammad (Mamman), Zakariyya (Ya’u), Sulaiman (Sule) da sauransu. Haka abin yake ga mata, Ruqayya (Rakiya), Bilkisu (Balki), Maimunatu (Munari), A’ishatu (A’i), Khadija (Dije), Zainab (Abu), Maryam (Mairo), Hajara (Hajjo), Fatimah (Fatsuma), Lauratu (Laure) da dai sauransu. Haka nan sunan mutum na al’ada yakan shafe asalin sunansa na yanka daga samuwa, sai ka ji sunan mutum Sallau, Mati, Lado, Tanimu, Gambo, Barau, Gagare, Rabe, Makau, Kwasau, Datti, Xandunawa da sauransu. In kuma mata ne ka ji Kyallu, Kande, ko ka ji mutane xauke da sunayen ranakun da aka haife su irinsu Xan Liti, Xan Jummai, Asabe, Ladi, Talatu, Larai, da sauransu, ko ka ji mutane xauke da sunan lissafi da dai makamantansu. Amma albarkacin wayewar addini musamman qarqashin tasirin Da’awar Shaikh Zakzaky (H), yanzu duk waxannan abubuwa suna kwaranyewa sannu a hankali, galibi yanzu ana kiran yara ne da sunayensu na addini ba na al’ada ba. Sannan ana sa wa yara sunaye da inkiya masu daxi da ma’ana, musamman yadda Shaikh xin ya koyawa al’umma sa sunayen jikokin Annabi (S) da ‘ya’yayensu, kuma abun ya ratsa gidan kowa har da Wahabiyawa. Yanzu maimakon sunayen su Mati da Lado, za ka riqa jin sunaye ne daxaxa, irinsu Al’ameen, Haneef, Munzir, Ma’aruf, Faisal, Sadiq, Arafat, Zahra, Yaseera, Afrah, Humaira, Sajida, Muslimah, Suhaila, Zeenat da sauransu. YAXA MANUFA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara koyawa musulmin wannan nahiya yadda za su dogara da kansu wajan bayyana ra’ayoyi da manufofi da aqidunsu da kansu ga al’umma ta kafofin yaxa labarai da na sadarwa, ba wai su shantake ta hanyar dogaro da kafafen yaxa labarai na gwamnati da masu zaman kansu su tallata su ba, domin kayan aro ba ya rufe katara, kuma maqiyinka ba zai ma kyakkyawan wakilci ba. Shaikh (H) ya nunawa qungiyoyin musulmi muhimmancin samar da kafar sadarwa ne ta hanyar samar da jaridar ALMIZAN da Mujallar GWAGWARMAYA, waxanda ke bayyana saqon Da’awarsa da manufarta, don al’umma su san manufar Da’awarsa daga bakinsa ba daga bakin wasunsa ba, daga baya an qara samar da jaridar “POINTER EXPRESS” da Mujallar “MUJAHIDAH”. Sakamakon wannan darasi da Shaikh Zakzaky (H) ya nuna, sai ga qungiyoyin addini su ma sun shiga koyi da shi, Wahabiyawa suka samar da jaridar “AS-SUNNAH” da Mujallar “SAUTUS-SUNNAH”. ‘Yan Tijjaniyya suka samar da Mujallar “AL-QIBLAH”. ‘Yan Qadiriyya suka samar da Mujallar “SAUTUL-WAHDA”. ‘Yan Jama’atut-Tajdeedul-Islam suka samar da Jaridar “ATTAJDEED”. ‘Yan Salafiyya suka samar da jaridar “ATTATBEEQ”. ‘Yan Shi’a Taqleedi suka samar da Mujallar “AL-MAUZOON”. ‘Yan Shi’a ‘Commercial’ suka samar da jaridar “AHLUL-BAITI” da dai sauransu. Wannan yana nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya cimma nasarar dasa ingantattun tunanuka a cikin al’umma. RAYA SUNNONI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tasiri sosai cikin al’umma a fagage da dama, musamman a fagen raya wasu sunnonin da aka yi watsi da su, misali; Shi ya raya al’amarin sanya Zobe, wanda bayan Istibsari ta kai ga maza suna sanya zobba masu alfarma. Shi ya raya taron addini da ake qira “Goron Sallah”, duk wata qungiyar addini da take taro da sunan ‘Goron Sallah’ ta kwaikwaya ne daga gare shi. Shi ya raya yin Tafsiri ba tare da Alaramma mai jan baqi ba, kafinsa ba a san yin hakan a matsayin Sunnah ba. Shi ya raya ziyarar malamai mabanbanta ra’ayi ga junansu, kafinsa ba a san malamai da ziyarar juna in ba ‘yan qungiya xaya ba. Shi ya raya batun Shariftaka, har ta kai ga yanzu al’amarin Shariftaka ya zama muhimmin al’amari a cikin al’ummarmu. Shi ya raya Maulidin Annabi (S) ta hanyar qirqiro yin Muzahara a ranar, wanda yanzu ya zama bikin addinin da ya fi kowanne armashi a Nijeriya. Shi ya raya mutunta Rawani, domin a baya kowa ma yana naxa Rawani in ya ga dama, amma yanzu an barwa malamai yin Rawani saboda mutuntawa. Kuma ga shi yanzu yana raya maqarbartu da qaburburan mamata, ta hanyar gyara su da qawata su da yi musu ado da kwalliya da fulawowi, ta yadda maqabartun sun soma zama wurin ziyara mai ban sha’awa, maimako yadda a da suka zamo dazuka na ban tsoron Fatalwa, da ramukan Macizai, Veraye, Buragu da qwari. Wannan sauyi da Shaikh Zakzaki (H) ke ta samarwa a cikin al’umma, yana qara tabbatar da baiwar da Allah yai masa ta musamman. A taqaice, waxannan abubuwa suna daga cikin fitattun nasarorin da Shaikh Zakzaky (H) ya samar a cikin al’umma, madalla da wannan Jagora! MATSAYINSA A DUNIYAR SHI’ANCI : Babu tantama ko ja-in-ja game da matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci, domin memba ne a Majalisar Ahlul-Bait ta duniya, wato (Ahlul-Bait World Assambly). Memba a Majalisar Taqreeb na Mazhabobin Musulunci, wato (The World Forum for Proximity of Islamic Thoutht). Memba a majalisar haxin kan Shi’a ta duniya, wato (World Federation Shi’a Khoja). Memba a majalisar goyon bayan Palasdinawa ta duniya, wacce Dr. Zahra Khumaini ke wa jagoranci. Memba a qungiyar taimakawa Intifadar Palasdinawa ta duniya, wato … Memba a qungiyar kare haqqin xan adam ta musulunci ta duniya, wato (International Islamic Human Right) mai hedikwata a birnin London, sannan shi wakili ne a wasu majalisu da qungiyoyi da dama na duniya. Kamar yadda ba buqatar tsawaita bayani game da karvuwarsa da martabawar da duniyar Shi’anci ke masa, domin waxannan wasu abubuwa ne da ke bayyane a fili qarara, musamman ga wanda ke bibiyar kafafen sadarwa na zamani. Misali; A duk lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fita zuwa wata qasar waje, musamman Iran, Iraqi, Lebanon da qasashen Turai, Asiya, ko Afirka, za ka ga irin tarba ta girmamawa, da liyafofin karramawa, da gayyace-gayyacen jawabi, da neman ganawa a keve, da sauran abubuwa na gayar karamci da ake masa, wannan kawai ya isa ya tabbatar da abin da muke faxa. Wata babbar shaidar da ta bayyana matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci shi ne waqi’ar Muzaharar Qudus da ta auku a birnin Zariya a shekarar 2014, inda sojojin gwamnatin Nijeriya suka kashe almajiransa guda 33 a lokacin wannan Muzahara, ciki har da ‘ya’yansa guda uku. Yadda duniyar Shi’a ta tankawa wannan ta’addanci da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya nuna ko waye Shaikh xin a duniyar ta Shi’anci, domin kusan ba wani babban Marja’i a duniya da bai yi Allah wadai, tare da rubutowa Shaikh Zakzaky (H) wasiqar jaje da ta’aziyya ba. Maraji’ai da manyan malaman Shi’a daga kowane sashe na duniya sun rubuto wasiqun jaje da ta’aziyya ga Shaikh, wasu ma sun tado jakadu ne musamman daga qasashensu, inda suka zo takanas ta Kano don jajantawa Shaikh Zakzaky (H), ciki kuwa har da Marja’il A’ala Ayatullah Sayyid Ali Hussain Khamna’i (DZ), wanda ya tado wakili na musamman Ayatullah Muhammad Hassan Akhtari don jajantawa. Abu na biyu da ya ja hankali ga matsayin Shaikh Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci shi ne, yadda manyan Maraji’ai sanannu a duniya suka riqa kiran Shaikh Zakzaky (H) da sunaye na daraja da girman matsayi ta fuskar ilimi, malanta, jihadi da jagoranci, kamar kiransa da Al-Mujaheed, ko Al-Muslih, ko Ayatullah, ko Allamah da sauransu. Daga cikin wasiqun da Maraji’ai da manyan malaman Shi’a suka kira Shaikh Zakzaky (H) da “Samahatul ALLAMAH Al-Mujaheed Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)” mafiya jan hankali sune na Hujjah Muhsinul Araky, shugaban majalisar haxin kan Musulmi ta duniya, wato “Majma’ul Aalamy Littaqribi Bainal Mazahibil Islamiyyah”. Sai wasiqar Sayyid Aliy Qadhiy Askar, Amirul Hajji na qasar Iran, kuma Wakilin Sayyid Qa’id kan al’amuran Hajji. Sai wasiqar Ayatullahil Uzmah Alawy Karkany, fitaccen Marja’i a duniya. Sai wasiqar Jami’ar Al-Mustapha ta duniya, wato “Jami’atul Mustapha Al-Aalamiyyah, Lebanon” da sauransu, (duba kwafin wasiqun a shafin Harka Islamiyya na Intanet, ko ka duba Al-Mizan bugu na 1142 shafi na 7, da bugu na 1144 shafi na 5). Nasabta Kalmar “Allamah” da fitattun Maraji’an duniya da suka cika sharuxxan Ijtihadi suka yi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta nuna daraja da girman da yake da shi ne a da’irar Shi’anci na duniya, kuma ya nuna mustawar ilimin Mujaddadin wannan qarnin! Amma abin da ya fi nuna girman daraja da zurfin matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar xan adam baki xaya, da duniyar musulmi ta wata fuska, da kuma duniyar Shi’a a fuska ta musamman, shi ne, faruwar waqi’ar ta’addancin sojojin Nijeriya na abkawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa a farkon watan Maulidi na shekarar 1437, wanda ya yi daidai da 12-12-2015. A wannan waqi’ar, wacce aka kashe xaruruwan almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ciki har da qarin ‘ya’yansa guda uku, aka harbi matarsa Malama Zeenatuddeen a wurare da dama na jikinta, sannan shi kansa Shaikh xin aka yi masa ruwan harsashi da nufin kashe shi, amma Allah ya qi xaukar ransa, daga qarshe suka kama shi suka tsare. Wannan abu da aka yi wa Shaikh Zakzaky (H) ya girgiza duniya, wanda nan da nan duniya ta yi Allah wadai da abin da sojojin Nijeriya suka yi, qasashe da dama sun yi tir da Allah wadai, wasu a gwamnatance kai tsaye, wasu ta hannun jakadun Nijeriya da ke qasashensu. Ta vangare guda kuma, al’ummomin qasashen duniya daban-daban ne suka fito kan tituna don yin tir da Allah wadai, tare da nuna rashin amincewarsu ga abin da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin shi. An yi zanga-zanga da muzaharori da gangamin ximbin mutane a qasashe kusan 80 na duniya, ciki har da Iran, Iraqi, Lebanon, Indiya, Amurka, Ingila, Denmark, Norway, Afirka ta kudu, Malesiya, Ghana, Phakistan, Mali, Philipines, Kashmir, Moroko, Dubai, Nijar, Yamen, Kamaru, Bahrain, da sauransu. Wannan martani na bai xaya da duniya ta mayar dangane da kama Shaikh Zakzaky (H), ya qara nunawa duniyar girman matsayin Shaikh xin da gayar tasirinsa a duniyar Shi’anci baki xaya. A jawabi na musamman da shugaban Shi’a na duniya Ayatullah Sayyid Qa’id Aliyul Khamna’iy (DZ) ya yi wa manyan malaman Shi’a a ganawar musamman da ya yi da su a falonsa cikin watan Janairun 2016, ya nuna cewa wajibi ne duniya ta yi tir da abin da ya faru ga Shaikh Zakzaky (H). Ya ce; “Me ya sa al’ummar musulmi su ka yi shiru akan abin da ya faru ga wannan Shehin Malami, Mumini, mai kawo Gyara, mai son Zaman Lafiya, mai haxa kan (musulmi) Shi’a da Sunnah waje guda! An kashe aqalla kusan mutum dubu da ke tare da shi, sannan ‘ya’yansa sun yi Shahada!” (Sayyid Qa’id ya yi wannan jawabi ne ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2016). KARRAMAWA (AWARDS) DA AKA BA SHI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin muhimman mutanen da aka yi ta karramawa da muhimman kyaututtuka a duniya, an ba shi kyauttuttukan karramawa masu yawa a qasashe da cibiyoyi daban-daban, kaxan daga cikin muhimman karramawar da aka yi masa sune; NA XAYA : A watan Janairu na shekarar 1980 Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amsa gayyatar halartar wani taro akan Musulunci a qasar Iran, bayan kammala taron an karrama Shaikh (H) da ganawa ta musamman da Imam Khumain (QS), wanda ke kwance a gadon asibiti yana jinya a lokacin. A qarshen ganawar, Imam Khumain (QS) ya xauki Alqur’aninsa da yake karatu da shi ya ba Shaikh Zakzaky (H) a matsayin kyautarsa ta karramawa gare shi, inda ya umarce shi da cewa; ya je ya kira mutane zuwa ga aiki da Alqur’ani.  NA BIYU : Gwamnatin mulkin soja ta jahar Kaduna a Nijeriya cikin shekarar 1996 ta karrama Shaikh Zakzaky (H) da “Award” a matsayin mutum mafi tasiri da ya fi kowa son zaman lafiya a qasa. Gwamnan soja na wancan lokacin Kanar Lawal Ja’afaru Isah ne ya jagoranci karrama Shaikh (H) da wannan kyauta, kuma Shaikh Zakzaky ya kafa shaida da wannan “Award” xin a kotu a lokacin da ake shari’arsa a 1998. NA UKU : Qungiyar Hizbullah da ke qasar Lebanon qarqashin jagorancin Sayyid Hassan Nasrullah, ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar Haramin Imam Hussain (AS).  Wannan muhimmiyar karramawa ta baqar Tutar da ke filfilawa akan Qabarin Sayyidish-Shuhada (AS) mai xauke da kalmar “Labbaika Yaa Hussain!” an yi ta ga Shaikh (H) ne a shekarar 2012. NA HUXU : Haramin Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala a qasar Iraqi, ya Karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar da ke filfilawa a saman Haramin garkuwan Imam Hussain (AS) wato Abul-Fadal Abbas (AS), wanda ake wa laqabi da “Qamaru Bani Hashim”. An karrama Shaikh (H) da kyautar Tutar Hubbaren Abul-Fadal ne a shekarar 2013. NA BIYAR : Qungiyar tara gudunmawar jini ta qasa, wato “National Blood Transfussion Services” ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Award” na musamman don jinjina masa da godiya gare shi bisa umartar miliyoyin almajiransa da ya yi da taimakawa majinyata da gudunmawar jini a duk faxin qasar, kuma wannan gudunmawar jini da ximbin almajiran Shaikh ke bayarwa ta dindindin ce a kowace Munasaba ta bikin haihuwa ko juyayin wafatin wani Ma’asumi (AS). An karrama Shaikh Zakzaky (H) da wannan kyauta ne a shekarar 2013. NA SHIDA : Qungiyar Kiristoci ta Nijeriya wato “Chirisian Association of Nigeria” (CAN) vangaren matasa, a shekarar 2014 ta Karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Award” na gwarzon Malami mai qaunar al’umma da samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ma’abuta banbancin addini. NA BAKWAI : Qungiyar kula da iyayen gwarazan Shahidai ta Duniya mai hedikwata a qasar Iran, ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyauta ta “Uban Gwarazan Shahidai”. An shirya babban taro ne a Iran, inda aka gayyaci iyaye da dangin gwarazan Shahidai daga qasashe daban-daban na duniya aka karrrama su. Kuma Shaikh Zakzaky (H) ne ya zamo gwarzon uba a wannan taron, don shi ne ya rasa haziqan ‘ya’yansa uku a rana guda. An karrama Shaikh (H) da wannan kyauta ne a shekarar 2014. NA TAKWAS : Haramin Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad a qasar Iran ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da matsayin “Hadimin Imam Ridah (AS)”, inda aka ba shi “Award” haxe da koriyar Tutar da ke filfilawa a saman qabarin Imam Ridha (AS), wanda aka tara manyan Maraji’ai don su shaida bikin wannan karramawa da aka yi ga Shaikh (H) a Hubbaren Imam Ridah (AS) a watan August na shekarar 2015. NA TARA : Haramin Sayyida Fatimah Ma’asuma (SA) da ke qasar Iran, ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar da aka lulluve Hubbaren na qanwar Imam Ridah (AS), a wani qwarya-qwaryan biki a babban ofishin Haramin da ke birnin Isfahan na qasar Iran cikin watan Zulhajji na shekarar 1436, wanda ya yi daidai da qarshen watan August 2015. NA GOMA : Haramin Sayyida Zainab (SA), da ke birnin Dimashqa a qasar Siriya, ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyautar Tutar da ta shekara tana lulluve da qabarin Sayyida Zainab bint Amiril Muminin (SA), wanda aka shirya biki na musamman a xakin taro na Mahdiyyah da ke birnin Mashhad Iran don karrama Shaikh xin da wannan Tuta mai alfarma. An yi wannan karramawa ga Shaikh (H) ne ran 20 ga watan Janairu na shekarar 2016, lokacin yana tsare a hannun gwamnatin Nijeriya, wasu almajiransa ne suka wakilce shi a bikin. NA 11 : Qungiyar kula da al’adu ta qasar Iran mai suna “Iranian Cultural Caravan” wacce ke qarqashin cibiyar “Under The Shade of The Sun”, wacce kuma kula da Haramin Imam Ridah (AS) ke qarqashinsu, sun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyautar Tutar da ke filfilawa a saman Hubbaren jikan Manzon Allah (S) kuma Khalifa na 8 a jerin Khalifofin Annabi (S) na Shari’a (wato Imam Aliyur-Ridah (AS)). An yi wannan karramawa ne ranar Juma’a 04 ga August 2016, kuma duk da cewa Shaikh Zakzaky (H) yana tsare a kurkuku a lokacin, amma an iya isar masa da tutar don Tabarruki. NA 12 : Gamayyar qungiyoyin kare haqqin xan na jihohin kudancin Nijeriya, wato “Southeast Based Coalition of Human Rights Organisations” (SBCHRO’s) a taqaice, wacce ta qunshi qungiyoyi 12 na kare haqqin xan adam a Nijeriya, sun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Prestigious Award” na “Prisoner-of-Conscience” wato (POS) a taqaice. Sun yi wannan karramawa ne ranar 17 ga watan August na shekarar 2016 a birnin Ummuahia na jihar Abia. Shugaban gamayyar qungiyoyin Mr. Emeka Umeagbalasi ya ce; Mun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky da wannan “Award” da ya ginu akan cika qa’idojin Majalisar xinkin duniya na wanzar da zaman lafiya da yaqi da wariya ne, bisa irin al’ummar da ya samar mai tsananin hangen nesa da aiki da hankali, “Domin an tsare shi tsawon lokaci bayan an harbe shi da kashe masa ‘ya’yansa da ximbin mabiyansa, amma har zuwa yau ba a samu yamutsi ko hargitsi ko tashin hankali da sunansa ko na mabiyansa ba!” Sun karrama shi ne duk da cewa yana tsare a kurkuku a lokacin. Waxannan jerin “Awards” da karramawa guda 12 da muka ambata ba suke nan ba, an ba Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) “Awards” da dama a wurare da qasashe da dama, mun ambaci waxannan ne a matsayin misali. YABO DA JINJINA A GARE SHI : Tirqashi! Idan mutum yana so ya varo aiki, to ya nemi sanin yawan yabon da mutane daban-daban suka yi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin linzami ya fi qarfin bakin kaza. Za a iya wallafa manya-manyan littattafai akan yabo da kyawawan zantukan mutane akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amma da yake komai muna taqaitawa ne, bari mu bada ‘yan misalai na yabon vangarorin al’umma gare shi. YABON KIRISTOCI : Kiristocin Nijeriya na vangarori daban-daban sun sha yabawa Shaikh Zakzaky (H) a lokuta da dama, wannan yabo sukan yi shi a qungiyance da xaixaikunsu, sun sha kwatanta halayensa da na Annabi Isa (AS), sukan ce shi ne “Small Jesus” ko “The Saviour” ko “The Mesiah” da sauransu. Rebaran Musa D. Musal na cocin Angilika a Gombe, ya faxi a wani jawabinsa cewa; “Xabi’un Shaikh Zakzaky irin na Annabawa ne. Kusan shekaru 20 ina tare da Shaikh, ina jin karatuttukansa, har ta kai ga na xauki Shaikh a matsayin jagorana! Akwai Shehunnai a qasar nan, amma Shaikh Zakzaky ya fita daban a cikinsu… dan haka addu’ata da zan yi ga Shaikh shi ne, Allah ya qarfafe shi, Allah ya sa shi ne wanda zai zama sanadin tsiranmu a wannan nahiya” (Rebaran Musa ya yi wannan jawabi ne a taron Mu’utamar na Matasa na qasa da aka yi a Bauchi, ranar 7-Zulqa’ada-1436). Wani Fadan kirista, kuma shugaban qungiyar yaqi da cin hanci ta “Anti Corruption Network” a Nijeriya, Mr. Ebenezer Onyetekan ya faxi cewa; “Yadda na ga xabi’un Shaikh Zakzaky da halayensa, da kuma salon Da’awarsa, ko da Musulunci zan yi, to Shi’a zan yi!” (Ya faxi wannan ne a taron tunawa da Shahidan Qudus karo na farko, ranar Lahadi 26 ga watan Yulin 2015, a Sheraton Hotel Abuja). Fasto Meter Peller na Cocin Anglican Abuja, ya faxi a wata hirarsa da ‘yan jarida cewa; “Malam Zakzaky ba irin sauran malamai ba ne da za su ce abu su kuma kasa aikatawa, Malam yana faxa ne da aikatawa, kuma muna gani a zahiri. Kuma lallai wannan mutumin ya kamata ya zama Uba ga kowa, kuma ya kamata ni in zama xa gare shi daga cikin ‘ya’yansa!” (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 08). “Malam ya zama ‘Bridge Builder’ mai gina gadar fahimtar juna tsakanin kudu da arewa, da kuma tsakanin Kirista da Musulmi, Ibo da yawa sukan ce in dai za su yi Musulunci, to irin na Zakzaky za su yi, wani ma cewa ya yi “This man na freedom fighter” wato wannan mutumin mai qwatarwa raunana ‘yancinsu ne”. (Malam, Malam Ne, shafi na 18). YABON QADIRIYYA : Limamin Qadiriyya na Afirka, Shaikh Muhammad Nasiru Kabara (RA) tun yana da rai aka ruwaito cewa, wata rana da Shaikh Zakzaky (H) ya ziyarce shi, a jawabinsa ya ce; Duk xan Qadiriyar da ya soki Da’awar Shaikh Zakzaky ya ci amanar Qadiriyya!”. Sannan kusan baki xayan ‘yan gidan Qadiriyya ba wanda bai ya bi Shaikh Zakzaky (H) da yabo kyakkyawa ba a lokuta daban-daban. YABON TIJJANIYYA : Shaikh Murtadha Abul-Fathi, wanda xa ne ga babban jagoran Tijjaniyya a Nijeriya, kuma xaya daga cikin jigoginta na duniya, wato Shaikh Abul-Fathi Maiduguri, a jawabinsa na wani taron “Makon Haxin Kan Musulmi” da aka yi a Zariya, ya ce, duk wata kamala (Qualities) na Annabawa (AS) to Shaikh Zakzaky (H) ya siffatu da su, “Da ba don na riga na yi wa Shaikh Ibraheem Inyas mubaya’a ba, to da na miqa hannuna na mubaya’a ga Shaikh Zakzaky!”. YABON GWAMNATI : Abin mamaki game da Shaikh Zakzaky (H) shi ne, hatta gwamnatocin da suke adawa da shi, sun sha yabonsa a fili da voye, misali; Gwamnatin jahar Kaduna ta tava ba shi takardar karramawa (Certificate) a matsayin gwarzon mutumin da ya fi kowa kawo zaman lafiya a qasa, wanda gwamnan jahar Kaduna na mulkin soja Laftanar Kanal Lawal Ja’afaru Isah ya ba shi a shekarar 1996 kafin Janar Abacha ya kama shi a wancan lokacin. Haka nan, wasu daga cikin manyan Sarakunan gargajiya mafiya daraja a Nijeriya, sun sha yabawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), misali, marigayi Sarkin Kano Dr. Alhaji Ado Bayero CFR, ya sha yabawa Shaikh Zakzaky, har ma ya tava fitowa fili ya yi kiran da a sake shi lokacin da gwamnatin Janar Abacha ta kama shi, kuma ya yi Allah wadai da gallazawar da ake masa. Haka nan Sarkin Zazzau Dr. Alhaji Shehu Idrees CFR, ya tava jinjinawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wata hira da aka yi da shi lokacin da ya cika shekaru 30 akan gadon Sarauta, an tambaye shi ne me zai ce game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)? Sai ya ce; “Malam Ibraheem Zakzaky yana cikin ‘ya’yanmu masana masu albarka, shi xan mu ne mai albarka!” (Al-Mizan, bugu na 657, shafi na 3, 10-Muharram-1426). YABON ALMAJIRANSA : Yabon almajiran Shaikh Zakzaky (H) gare shi abu ne da bai misaltuwa, wani almajirinsa a littafin da ya rubuta mai suna “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Akwai sunnoni da yawa na Manzon Allah (S), Shukran Laa-fakhran, Sayyid Zakzaky (H) shi ne asasin raya su a wannan nahiya ta mu da muke ciki, wanda ba ‘yan uwa kawai ba, a’a hatta sauran jama’ar gari, da yawa sun kwaikwayi waxannan sunnoni”. RUBUCE-RUBUCE AKANSA : Ta xaya janibin kuma, akwai littattafan da aka rubuta akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da rayuwarsa, wanda littattafai ne qanana, amma sun yi tsokaci akan wasu muhimman janibobi na rayuwarsa. NA XAYA : Littafi na farko game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne; “Kitabul Bushra” wanda littafi ne da ya yi magana akan albishirin bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Waliyi kuma mujaddadi Shehu Usman Bin Fodiye ya yi tun fiye da shekaru 200 kafin haihuwarsa. An buga littafin ne a shekara ta 1416 Hijira, Edita Malam Ibrahim Musa ne ya wallafa littafin. NA BIYU : Littafin “Malam Zakzaky (H) Rayuwarsa da Karamominsa”, wanda shi kuma laccocin wasu malamai guda biyu ne akan rayuwar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) aka mayar da su littafi, ya qunshi tsokaci akan vangarori daban-daban na rayuwar Shaikh Zakzaky (H). An buga littafin ne a shekarar 1416 Hijira, malaman da suka gabatar da jawaban littafin su ne Shaikh Ya’aqubu Yahya Katsina, da Malam Abubakar Abdullahi Sokoto. NA UKU : Littafin “Tauhidin Kalma Daga Rayuwar Mujaddadai”. Shi wannan littafin littafi ne na falsafa, wanda ya qunshi salo da kalmomi masu sarqaqiya, yana kwatanta dacewar salon rayuwar bayin Allah ne ma’abuta Tajdidin addini, inda ya kwatanta dacewar rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da sauran Mujaddadan addini da suka gabace shi. An wallafa littafin ne a shekarar 1997, marubucin littafin shi ne Malam Ibrahim Muhammad Potiskum. NA HUXU : Shi ne littafin; “Yusufuz-Zaman”. Shi wannan littafin ya fito da darussa ne na dacewar rayuwar Shaikh Zakzaky (H) da ta Annabi Yusuf (AS), ta yadda ya gaji halayya da xabi’u da yanayin rayuwar Annabi Yusuf (AS) musamman ta fuskacin jarabawar garqamewa a gidan kurkuku. An wallafa wannan littafi ne a shekarar 1998, marubucin littafin shi ne Malam Ibrahim Muhammad Potiskum. NA BIYAR : Shi ne littafin “Wakilin Manzon Allah (S) a Doron Qasa”. Shi wannan littafi an gina shi ne akan hujjoji na nassi da na hankali da na zahiri da ke nuna cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) magajin Manzon Allah (S) ne a wannan nahiya, domin ayyukansa da xabi’unsa da halayensa suna kama da na Manzon Allah (S). Littafin na xaya da na biyu ne, kuma an buga su ne a shekarar 1997 da 1998 Miladiyya, marubucin littafin shi ne Malam Xanjuma Katsina. NA SHIDA : Shi ne littafin “Bayyanar Sharafuddin”. Shi wannan littafi shi ne irinsa na farko a fagen hallale bayani akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daki-daki. Littafin ya qunshi magana akan Shaikh Zakzaky (H) tun daga wasiyyoyin bayyanarsa, zuwa asalin zuriyya da nasabarsa, har zuwa yarinta, karatu, gwagwarmaya, kulen da ya fuskanta, da sauran vangarorin rayuwarsa. An buga littafin ne a shekarar 2001 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Malam Al-Ameen Isa Al-Sakkwaty. NA BAKWAI : Shi ne littafin “Malam Malam Ne”. Wannan littafi ya qunshi muhimman bayanai game da wasu vabgarori na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da baiwar da Allah Ta’ala ya yi masa a vangare daban-daban. Asalin littafin rubuce-rubuce ne da mawallafin ya yi a jaridar ALMIZAN, shi ne aka tattara su wuri guda aka maishe su littafi. An buga littafin ne a shekarar 2007 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Marigayi Malam Haruna Shelleng. NA TAKWAS : Shi ne littafin “Shekaru 60 Masu Albarka”. Shi wannan littafin ya qunshi hirarraki ne da mutane daban-daban akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun daga yarintarsa har zuwa cikarsa shekaru 60 a duniya. An yi hira da iyalansa, da ‘ya’yansa, da abokansa, da danginsa na jini, da almajiransa, da sauran jama’ar da suka san shi, kuma a qarshen littafin an kawo wasu rubuce-rubuce akansa. An wallafa littafin ne bayan bukin cikar Shaikh xin shekaru 60 da haihuwa a shekarar 1433, wanda ya yi daidai da farkon shekarar 2012 Miladiyya. Mawallafin littafin shi ne Edita Malam Ibrahim Musa. NA TARA : Shi ne littafin “Mujaddadin Wannan Qarnin”. Shi wannan littafi ne da ya qunshi bayanai akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da hujjoji akan zamowarsa Mujaddadin addini a wannan nahiya. Marubucin ya kawo hujjoji na naqali da na hankali da ke tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky (H) Mujaddadin addini ne. An buga littafin ne a shekarar 2013 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Muhammad Nasir Miji Gombe. NA GOMA : Shi ne littafin “Sallah Mafificiyar Ibada”. Shi wannan littafi ya xauki janibi xaya ne kacal, wato sallolin Shaikh Zakzaky (H) ya yi bayani akai, cike yake da hotunan Sallolin Shaikh Zakzaky (H) tun daga na Yaumiyya har zuwa Idi da sallar Jana’iza. An kawo dukkanin karance-karance, da addu’o’i, da Azkar, da Alqunut xin da Shaikh Zakzaky (H) ke yi ne a cikin sallolinsa, da surar yadda yake wasu ayyukansa na Sallah a cikin hotuna masu kala. An wallafa littafin ne a shekarar 2014. Marubucin littafin shi ne Abdullahi A. Hamza. NA 11 : Shi ne littafin “Tarihin Sayyid Ibraheem Yaqub Al-Zakzaky da Harkar Musulunci”. Wannan littafi shi ne irinsa na farko a bisa salo da usulubinsa, domin littafin ya qunshi vangare biyu ne, vangaren tarihin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma vangaren tarihin Da’awarsa ta Harka Islamiyyah. A irin wannan usulubi, za a iya cewa shi ne littafin tarihin Harka Islamiyyah na farko. An wallafa littafin ne a shekarar 2015 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Malam Muhammad Sulaiman Kaduna. NA 12 : Shi ne littafin “Shaikh Zakzaky Ikon Allah!” wato wannan littafin da ke hannun mai karatu, shi ya qunshi tsokaci ne akan vangarori da dama na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da tarihinsa ataqaice. An kammala rubuta littafin ne a shekarar 2017 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Adamun Adamawa. A taqaice, waxannan sune littattafan da aka rubuta kacokam akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da abubuwan da suka shafe shi, amma akwai littattafai da dama da suka ambaci wani sashe na rayuwarsa a wasu babukansu. Sannan wannan littatafan da aka rubuta da Hausa ne kawai, banda na Larabci, Turanci, Projects, Mujallau da sauransu. WAQOQIN DA AKA YI AKANSA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin mutane qalilan da tarihi zai ayyana cewa an yi ximbin waqoqin yabo a kansu, domin zuwa yanzu abu ne mai matuqar wahala a iya qiyasi ko kirdadon adadin waqoqin yabon da aka yi a kansa. Tun a qarshen shekarun 70s waqoqi akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Da’awarsa suka soma karaxe sassa da lungunan Nijeriya da qasashe maqwabta, kuma har ya zuwa yanzu sai abin da ya qaru. An yi waqoqi marassa qirguwa akan Shaikh Zakzaky (H) da Da’awarsa, hasali ma akwai qungiyar mawaqa na Harka Islamiyya mai suna “Ittihadus-Shu’ara Lil Harkatil Islamiyyah”, wanda suke taimakawa da fasaharsu wajan wayar da kan jama’a game da manufar Da’awar Shsikh Ibraheem Zakzaky (H). Babu shakka mawaqa da daman gaske sun yi waqoqi da yawa akan Shaksiyyar Shaikh Zakzaky (H), wanda zai yi wuya a iya qididdige su, to amma mawaqan da suka fi kowa yin fice akan yi wa Shaikh Zakzaky (H) waqoqi sune Alhaji Mustapha Gadon Qaya, da Malam Ammar Muhammad Xan Tinka. Shi Alhaji Mustapha Gadon Qaya ya yi waqoqin yabon Shaikh Zakzaky (H) da dama, daga cikin wanda suka yi fice akwai; “Yaa Sharafaddeeni Maraba”. Da “Imamul Bara’ati Labbaika!”. Sai “Ya Malam Zakzaky, Ibraheemu Baban Nusaiba Tsayayye”. Sai “Ibraheem Zakzaky, Labbaika ya Zakzaky”. Sai “Ya Zakzaky qara yin Juriya Jagoran Addini Babba”. Sai “Akan Zakzaky Mu Ba Mu Shakkar Uban Kowa!”. Sai “Ya Allah Kare Al-Zakzaky Qara Mana Yin Biyayya”. Sai “Ya Hasken Allah Imamu Zakzaky Mai Alfarmaa”. Sai “Al-Zakzaky Kogin Baiwa, Sirri na Allah sai Kallo!”. Sai kuma “Sannu-sannu Dattijo, Wila’armu na gurin Allah, Bai’armu na a hannunka”. Sai kuma “Babu inda ba Allah, in akwai ku kai Malam” da dai sauransu. Shi ma Malam Ammar Xan Tinka Zariya, ya yi waqoqin yabo da jinjina ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da dama, daga cikin fitattun waqoqinsa akwai; “Yaa Mujaddadi”. Da “Labbaika Zakzakiy Shehu!”. Da “Gaskiya Malam Malam ne”. Da “Haske ya Bayyana Al-Zakzaky Muna nan Bayanka”. Da “Zakzaky Taka da Laafiya!”. Da kuma “Zakzaky Aarifum-Billahi” da dai sauransu. A gefe guda, akwai wasu fitattun mawaqa da suka yi waqoqi na yabon Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suka yi tashe a cikin al’umma, daga ciki akwai; Alhaji Mustapha Limanci da waqarsa ta “Gaisuwa nake Jagorana Shehu Ibraheem Zakzaky”. Sani Aliyu Katsina da waqarsa ta “Lallai-lallai Mun yi Nasara, Malam Zakzaky shi Muka Riqe!”. Bello Shehu Mafara da waqarsa ta “Zakzaky Malamin Ulama’u”. Nura Shahidi da waqarsa ta “Barka da Fitowa Maulana Al-Zakzaky mai Gulbin Baiwa”. Shaheed Shafi’u Kazaure da waqarsa ta “Ni na maka Bai’a Baban su Nusaiba Zakzaky mai Haiba”. Abdullahi Andu da waqarsa ta “Imam Khumaini da Malam Zakzaky Mun Faxi Xa da Uba ne”. Marigayi Malam Rabi’u Tudun Iya da waqarsa ta “Labbaika Shehu Imam Zakzaky”. Sai Gambo Xankaka da waqarsa ta “Mu dai Al-Zakzaky Muna Son ka Qwarai-qwarai”. Shareef Uzairu Badamasi da waqarsa ta “Kada Mage ba Yanka ba, Yaa Shehu Ibraheem Labbaika Zakzaky Mazajen Fama!”. Abdullahi Xan Lushi da waqarsa ta “Yaa Shehu Zakzaky”. Sa’idu Saqafa Potiskum, da waqarsa ta “Malamina da na yi wa Mubaya’a Jagorana, Zakzaky na!”. Sani Xan Auta da waqarsa ta “Zakzaky Kainuwa Dashen Allah, mun ji mun Gani”. Musa Qasida Gombe da waqarsa ta Fulatanci “Shehu Zakzaky Modibbo, Wala bamaxa Nder Moxivve”, da dai sauran ximbin mawaqan da ba za su qirgu ba. Wani tabbataccen abu da nazari ya nuna shi ne, duk waqoqin da ake yi akan Shaksiyyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba qaramin farin jini da tashe suke yi ba, wataqil wannan yana da alaqa da xanfaruwar zukatan al’umma ga Shaikh Zakzaky (H) xin ne. KYAWAWAN MAFARKAI AKANSA : Babu shakka kowane bawan Allah akan samu wasu alamomin da za su zamo shaida akan Khususiyya da darajarsa, ta irin wannan salo ne aka samu isharori da dama game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) musamman ta hanyar mafarkai, kasancewar mafarki wata hanya ce daga cikin ingantattun hanyoyin Bushara, kenan hakan zai zama abin la’akari ga ma’abuta hankali. Mafarke-mafarke da ke ishara ga darajojin Shaikh Ibraheem Zakzaky ba su da iyaka, domin jama’a da dama sun sha yin ayyuka “A’amal”, ko su yi wasu addu’o’i na neman ganin Manzon Allah (S) a mafarki, amma maimakon haka sai su yi mafarki da Shaikh Zakzaky a madadinsa, wanda hakan ke nuna wata alaqa mai qarfi da ke tsakanin Shaikh da Manzon Allah (S). Haka nan, jama’a da dama sun yi mafarke-mafarke da Manzon Allah (S) ko wani Imami daga cikin Ma’asumai (AS), ya umarce su da riqo da yin biyayya ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wannan ya sha faruwa hatta ga waxanda ke qiyayya ga Shaikh Zakzaky (H) kamar Wahabiyawa da wasu mabiya xariqun Sufaye. Misali; A shekarar 1995, wani Bawahabiye a birnin Bauchi ya yi Mafarki da Imam Mahdi (AF), ya ce masa; “In na bayyana kana cikin wanxanda zan yaqa!”, sai Bahwahabiyen ya fashe da kuka yana roqon Imam ya yafe masa laifinsa kuma ya faxa masa mafita. Sai Imamul-Asr (AF) ya ce masa; “In kana son tsira daga wannan, to ka yi mubaya’a ga mai Da’awar nan na Zariya Malam Ibraheem Zakzaky!”, Da sassafe Bawahabiyen ya yo sammako zuwa cibiyar ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) ta Bauchi, ya faxi mafarkin da ya yi, kuma ya nemi a miqa bai’arsa ga Jagora (H). Sannan a wajajen shekarar 2000, wani xan Ahlis-Sunnah a Sakkwato ya yi mafarki game da Shaikh Zakzaky (H), wanda ta sanadinsa ya zama almajirin Shaikh Zakzaky (H). An buga labarin mafarkin nasa a jaridar Al-Mizan. Ya ce;- “Na yi mafarkin an gina wani sabon masallacin juma’a babba a garinmu, sai na ji ana sanarwa cewa za a yi gagarumin taro na bikin buxe masallacin, kuma babban bako mai buxe masallacin, wanda kuma zai jagoranci sallar farko a masallacin shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky! “Sai abin ya bani mamaki, a raina na ce; Zakzaky shugaban ‘yan Shi’a ne zai buxe mana masallacin garinmu, alhali mu Ahlis-Sunnah ne? Na yi ta tambayar kaina, me ya sa aka gayyato shi? Me ya sa ‘yan kwamitin masallacin ba su ga dacewar gayyatar kowa ba sai shi? Me ya haxa mu da xan Shi’a? A haka dai na haqura, na yi wanka na sa farar jallabiya, na tafi wajan bikin buxe masallacin. “To, inda ake taron buxe masallacin qaton wuri ne kewaye da wata doguwar katanga, ta qofa xaya ake shiga wurin, gun ya cika maqil da jama’a, sai aka yi shela cewa kowa ya daidaita sahu za a yi Sallah, na ga Shaikh Zakzaky (H) ya wuce gaba zai ja sallah, sai na riyawa zuciyata cewa; Ni ba zan bi shi Sallah ba! “Sai na kama hanya zan fita, ina zuwa qofa, da na hangi waje, sai na ga mugayen namun daji ne ta ko’ina! Duk wata muguwar dabba akwaita a wurin, Kura, Zaki, Damisa, Gwanki, Dorina, Aladu da sauransu, ga su nan ba iyaka! Suna ta hargowa, suna jiran in fito su cinye ni! Nan take sai na juya da hanzari na koma na shiga sahu na bi Shaikh Zakzaky (H) Sallah! Kawai sai na farka daga barcina. “Daga nan na sallamawa Shaikh Zakzaky (H), na ce wannan ishara ce ake yi min ta yin biyayya gare shi. Alhamdulillah, yanzu ina cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H). Allah ka tabbatar da mu a bayansa har abada! Dan darajar Manzon Allah (S) da iyalansa tsarkaka!”. Haka nan, wani mabiyin xariqar Sufanci, ya yi mafarki da Manzon Allah (S), inda ya nuna masa cewa abin da Shaikh Zakzaky ke tafiya akai shi ne shiriya, kuma ya umarce shi da biyayya gare shi muddin yana son tsira cikin sauqi a gobe qiyama. Haka ma wani babban malami daga qasar Senegal, mai suna Shaikh Sayyid Haidar Muhammad Shamsuddeen ya yi mafarki har sau uku da Sayyida Fatimah Azzahra (SA) tana ce masa ya je birnin Zariya a Nijeriya ya yi mubaya’a ga xanta Shaikh Ibraheem Zakzaky, a karo na ukun har gargaxi ta yi masa. Shi ne a shekarar 2014 ya niqo gari daga Senegal ya zo Nijeriya ya miqawa Shaikh Zakzaky (H) mubaya’arsa don yin biyayya ga umarnin ‘yar Manzon Allah (S). Ire-iren waxannan mafarkai akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba su da iyaka, mun kawo waxannan ne kawai a matsayin misali, kuma duk da cewa ba kowane mafarki ne hujja ba, to amma ire-iren waxannan mafarkai bushara ce ingantacciya. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ BABI NA BAKWAI BUSHARORIN BAYYANAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) BUSHARA A TARIHIN XAN ADAM :  Tarihi ya nuna cewa kafin a haifi duk wani mutum na musamman, mai baiwa ta musaman, wanda zai yi wani aiki na musamman a duniya, ko zai wanzu ya shahara, to, akan samu wasu bayin Allah masu hangen nesa da za su yi busharar bayyanarsa, kamar dai yadda aka samu wasu bayin Allah da ke busharar bayyanar Annabawa (AS), da yadda aka samu waliyan da suka yi busharar bayyanar Mujaddadi Shehu Usman xan Fodiye (RA), kuma aka samu zantuka masu busharar bayyanar Imam Khumain (QS). To, haka nan shi ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) an samu bayin Allah da suka yi busharori na bayyanarsa da girman sha’aninsa. Bushara ta farko da ake alaqanta ta game da bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ita ce wacce ta zo daga Imam Muhammad Baqir (AS) wacce Imam Jalaluddin Suyuxy ya ruwaito a cikin littafinsa, wacce kuma wani manazarci ya yi fashin baqi akanta ya nuna dacewarta da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Bushara ta biyu ita ce Busharar Imam Ja’afar Assadiq (AS), wacce ta zo cikin hadisinsa mai tsawo, inda ya bayyana mataimakan Imam Mahdi (AF) guda 313, ya ambaci sunaye da wasu daga cikin siffofinsu, daga cikin sunayen akwai Ibraheem Al-Magriby, wanda ake kyautata zaton Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne. Bushara ta uku wacce waliyin Allah kuma Mujaddadin addini Shaikh Usman bin Fodiye ya yi, wacce a ciki ya bayyana siffofin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekarar haihuwarsa. Shaikh Usman bin Fodiye ya yi wannan bushara ne a wata waqa tasa mai Baiti Ashirin, wacce ya yi ta da harshen Fulatanci, waqar tana cikin littafin “Bushral-Ahbab” na Shaikh Usman bin Fodiye, wanda littafi ne da aka tattara waqoqin da ya yi ga waliyyan Allah na zamaninsa da wanda za su zo nan gaba. Wani malami mai suna Shaikh Bayero ibn Muhammadu Sambo Kulwa ya fassara waqoqin littafin “Bushral-Ahbab” daga Fulatanci zuwa Larabci, bayan ya yi naqalinsu daga littafin mahaifinsa Malam Muhammadu Sambo Kulwa (wanda ya rasu a shekara ta 1248 bayan Hijira) mai suna “Kanzul-Aulaad”, shi kuma mahaifin nasa almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne kai tsaye. Bushara ta huxu ita ce Busharar da waliyiya Nana Asma’u bint Usman bin Fodiye ta yi akan bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Nana Asma’u ta yi busharar bayyanar Shaikh Ibraheem ne a wata waqarta mai Baitoci 40 cikin harshen Fulatanci, kuma an kawo wannan Bushara a cikin kundin waqoqinta da wasu Turawan Ingila suka tattara wuri xaya aka maishe su littafi mai suna; “The Collected Works of Nana Asma’u” na Jean Boyd da B.B Mark, wanda kanfanin wallafa na Sam Bookman Publishers da ke birnin Ibadan a Nijeriya suka wallafa a shekarar 1999. Sannan akwai busharar da wani babban malamin xariqa a Zariya ya tava yi, wanda bawan Allah ne sufi taqiyyi, kafin rasuwarsa ya tava bayyana cewa “Wasu matasa daga Jami’ar Ahmadu Bello ne za su yi tajdidin addini a wannan qasa”. Wanda a fili qarara za a iya xanfara wannan bushara ga Shaikh Zakzaky (H) da almajiransa, domin tushen da’awarsa ya samo asali ne daga wannan Jami’a. Bari mu kawo uku daga cikin waxannan Busharori biyar da muka ambata, tare da yin taqaitaccen sharhi a kansu. BUSHARAR IMAM BAQIR (AS) : Malam Ishaq Muhammad Xan’adany (malami, manazarci mazaunin birnin Zariya), ya fitar da wani nazarinsa akan ruwayar Imam Baqir (AS) da Imam Jalaluddin Suyuxy ya ruwaito a fitaccen littafinsa mai suna “ALHAAWY LIL-FATAAWA” juz’i na uku shafi na 99, inda ya ce lallai wannan ruwaya tana Busharar bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne, ga abin da ya rubuta. Imam Suyuxy ya ruwaito hadisi a littafinsa mai suna “Al-Haawy Lil-Fataawa” cikin zantukan jikan Manzon Allah (S) Imam Baqir (AS), ya ce; daga Abiy-Qubail (daga Imam Baqir (AS)) ya ce; “Wani jagora zai kasance a AFIRKA, (zai yi jagoranci) na shekaru sha biyu, kuma a bayansa Fitina za ta kasance. Sa’annan wani namiji wankan Tarwaxa (launi tsakanin fari da baqi) zai mulketa ya cikata da adalci. Sannan ya tafi zuwa ga Mahdi (AF) ya miqa masa biyayyarsa (Bai’a), kuma ya yi yaqi a qarqashinsa” (Al-Haawy Lil-Fataawa” Juz’i na 03 shafi na 98-99). Abubuwan la’akari da lura a wannan ruwaya sune; Mutum biyun da aka yi Busharar zuwansu ‘yan Afirka ne. Na farkon zai yi Mulki na tsawon shekara sha biyu, sai Fitina ta biyo bayansa, sai wani namiji ya zo (a bayansa) ya tabbatar da adalci, kuma shi wannan mutumin zai riski Imam Mahdy (AF) ya miqa masa Bai’a, sa’annan zai yi yaqi a qarqashinsa. To, a bisa nazari, za mu ga cewa wannan ruwaya ta Imam Baqir (AS) kamar tana magana ne akan Shaikh Usman Bin Fodiye (RA) da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin na farko; Shehu Usman bin Fodiye da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) duk ‘yan Afirka ne. Na Biyu : Shehu Usman da almajiransa sun fara samun Nasara a jihadinsu ne a shekarar 1805 Miladiyya, wanda kafin nan Shehu da almajiransa sun ci karo da wahalhalu sosai, kama daga tsananin yunwa da rashin wurin zama, wanda saboda tsananin yunwa har ta kai ga hijira ta gagari wasu saboda hatta dabbobinsu ba za su iya wannan tafiyar ba, sai da wani Buzu ya taimaka da raquminsa wajan kwasarsu zuwa garin Gwandu, inda Shehu da almajiransa suka tare don yin Noma da Kiwo. Shehu Usman ya samu cikakkiyar nasarar kafa Gwamnati da ikon gudanarwa ne a shekarar 1805, sannan ya yi wafati ne a shekarar 1817. Kenan, in mun lissafa daga 1805 zuwa 1817 za mu samu shekaru 12 ne daidai. Na uku ; Bayan wafatin Shehu xan Fodiye fitina ta biyo baya tun daga kan wanda zai gaje shi (kamar yadda tarihi ya tabbatar), wanda hakan ya kawo rarrabuwar kai a almajiran Shehu, har ya yi sanadin raunanar Musulmi, a qarshe (babbar fitina, wato) Bature ya zo ya ci su da yaqi ya rusa xan sauran abin da ya ragen. Na huxu ; Bayan tsawon lokaci, sai ga wani namiji a wannan nahiya ta Afirka ya tashi yana Da’awa da fafutukar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma, qiransa ya ratsa qasashe da dama na nahiyar Afirka, wannan kuwa shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda kuma shi mai cikakkiyar xa’a ne ga Imam Mahdi (AF), kuma akan biyayya ga Imam xin yake gina almajiransa. Na biyar ; Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai da burin da ya wuce Allah ya sanya shi cikin mataimakan da za su yi yaqi a qarqashin Imam Mahdi (AF), ba ma shi ba, hatta almajiransa ba su da burin da ya wuce haka. Sannan wasu Busharori na Waliyan Allah sun nuna yana cikin mataimakan Imam Mahdi (AF) 313, kamar yadda ya zo a hadisin Imam Sadiq (AS) da zantukan su Shehu Xan Fodiyo (RA). Kenan, in mun duba da kyau za mu ga wancan hadisi na Imam Baqir (AS) tamkar yana bushara ne na bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin kusan dukkanin abubuwan da hadisin ya ambata sun dace da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Allah ne masani ga haqiqanin al’amura. (Ishaq Xan’adani Al-Rafidhiy, rubutunsa a Wattsapp ranar 04/09/2016). BUSHARAR IMAM SADIQ (AS) : Bushara ta biyu wacce ake kyautata zaton Busharar bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ce, ita ce busharar bayyanar wani Ibraheem Al-Maghriby cikin jerin mataimakan Imam Mahdi (AF) da Khalifan Manzon Allah (S) na shida, wato Imam Ja’afar As-Sadiq (AS) ya yi, marubucin littafin “Bayyanar Sharafuddin” ya yi bayani akan wannan Bushara kamar haka;- “Akwai wata daxaxxar Bushara wadda Imam Ja’afar ibn Muhammad Assadiq (AS)- watau Imami na shida daga zuriyar gidan Manzo mai tsarki (SAW)- ya yi kan zuwan Malam (H). Wannan busharar kuwa ya yi ta ne tun shekaru xaruruwa da suka shuxe kafin bayyanar Shehu Xan Fodiyo (RT). Wannan busharar ta fito ne a cikin littafi mai suna “BUSHRAL ISLAM” wanda yake littafi ne da ya yi bayanai a kan bayin Allah waxanda za su bayyana a duniya tun bayan wafatin Manzo mai tsarki (SAW) har zuwa qarshen duniya. “Yadda lamarin ya kasance kuwa, wani ne ya zo wajen Imam Sadiq (AS), yana neman sanin ilimi kan bayyanar Imam Mahdi (AS), sai Imam Sadiq (AS) ya fayyace masa bayanai daki-daki har ya kai ga ambata masa sunayen mataimakan Imam Mahdi (AF) su 313, daga ciki ya ambaci sunan Ibraheem Al-Maghriby, watau Ibraheem na yammacin duniya, wanda kai tsaye za a iya cewa yana nufin Malam (Ibraheem Zakzaky) (H) kenan!” (Bayyanar Sharafuddin, Babi na 6, shafi na 40). Marubucin bai tsawaita bayani akan wannan Bushara ba, sai dai nazari zai iya tabbatar da haka, domin ya zuwa yanzu ba wani Ibraheem da aka yi a Magrib (wato Afirka) da ya fi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) zama kusa da kasancewa cikin mataimakan Imam Mahdi (AF). Domin na farko dai yana riqo ne da tafarkin Imam Mahdi (AF) wato Shi’a Imamiyyah, kuma ayyukan da yake aiwatarwa tamkar shinfixawa Imam Mahdi (AF) hanya ne, wato yana gwagwarmaya da zalunci da azzalumai, da kuma qoqarin wanzar da adalci a cikin al’umma. Kuma hatta Husainiyyarsa ma wacce ta fi kowace Hussainiyyah girma a nahiyar Afirka, sunan da ya sa mata shi ne “Hussainiyyah Baqiyyatullah”, wato ‘Hussainiyyar Imam Mahdi’ wanda wannan babban alami ne na alaqa da kusancinsa ga Imam Mahdi (AF). BUSHARAR SHEHU USMAN XAN FODIYE (RA) : Shaikh Usman bin Fodiye (RA) ya rubuta waqa Baitoci goma da ke bayani akan wasu manyan waliyyan Allah da suka gabata da kuma waxanda za su zo nan gaba, to a ciki sai ya ambaci wani waliyi Ibraheem da zai bayyana, wanda ya ce sunansa na baxini shi ne Sharafuddeen, kuma za a haife shi ne a shekara ta 1370 bayan hijira. Ga sashen Baitukan nasa:- (Waliyai) masu zuwa a bayan waxancan sune; Ibraheem wanda shi ne Sharafuddin da kuma Jamalul-Badry Husamuddini. Shi Husamun nan da aka ambata shi ne; Wanda aka ba cikamakon Waliyai Kamilai akan muqaman addini. A shekara ta 1370 bayan hijira zai bayyana, Wato shi Ibraheem mataimakin Imam Mahdin. Shaikh Bayero Sambo Kulwa ya yi taqaitaccen sharhi ga waxannan Baituka guda uku, ya ce; “(Ibraheem xin da zai bayyana), Sharafuddeen shi ne laqabinsa wato sunansa na baxini, saboda addini zai xaukaka a lokacinsa…” “Shi kuma Husamuddin xin nan da aka ambata, shi ne wanda aka ba muqamin cikamakon waliyai kamilai akan muqaman addini. An tambayi Shehu Usman dangane da wannan Husamuddin xin, sai ya ce shi ne Imam Mahdi da ake jira… shi shugaban kowa ne a zamaninsa…” “An tambayi Shehu Usmanu da ya yi qarin bayani akan (abin da zai faru a shekara ta 1370) sai ya ce; “Wannan shekarar ita ce shekarar bayyanar Ibraheem, wanda shi ne mafi girman mataimakan Imam Mahdi da ake jira, amma Allah ne kaxai ya san lokacin jihadi da yaqi na sojojinsa tare da kafirai, fajirai, fasiqai da ma’abuta munafunci” (Kitabul-Bushura, shafi na 04). To, bayan Shehu Usman bin Fodiye ya kammala waqar, sai aka tambaye shi qarin haske game da Ibraheem xin nan da ya ambata, shi ne sai ya qara rera wasu baitoci goma sabbi, inda ya hallale bayani daki-daki game da Ibraheem xin da siffofinsa, ya nuna cewa zai zo da albarkoki masu yawa. Ga yadda baitukan na Shaikh xan Fodiye (RA) suke bayan an tambaye shi qarin bayani game da Ibraheem Sharfaddeen; Wani mutum zai bayyana a qasar yamma, Yana kuma da jama’a masu taimakon Mahdi. Wannan mutumin da zai fito daga yamma manisanciya, Da mabiyansa sune mutanen (Imam) Mahdi. Duk lokacin da wannan mutumin ya bayyana, Ku da shugabanninku ba za a muku xa’a ba sai dai ga Mahdi. Cikin shekarar 1370 ne wannan mutumin zai bayyana, Shi ne kuma babban mataimaki (ga Imam) Mahdi. Wannan mutumin yana da faffaxan goshi tare da alama, Ka fahimci haka ya kai mai tambaya akan siffofin (mataimakin) Mahdi. Shi wannan mutumin fatar jikinsa baqa ce, Gemunsa da qirjinsa kuma mayalwata ne (Nasirul Mahdi). Kuma yana da idanu kamar na Mussa (Mage). Wannan mutumin zai yawaita ziyarar mafi alherin halitta (SAW). Laqabinsa shi ne Sharafuddeeni, Ibraheem kuma shi ne sunan mataimakin (Imam) Mahdi. Waxannan Baitoci na Shehu Usman bin Fodiye (RA) sun hallale bayani akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), tare da tabbatar da cewa lallai shi ake nufi a wannan Bushara, domin ba wani Ibraheem da ya tattara waxannan siffofi in ba shi ba. DACEWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) DA BAITOCIN XAN FODIYE : Manazarta sun yi nazarin waxannan Baituka na Shehu Usman bin Fodiye (RA), inda suka yi sharhohi masu faxi ta fuskoki da dama. Marubucin littafin “Kitabul-Bushura” da mawallafin “Bayyanar Sharafuddin” da marubucin littafin “Mujaddadin Wannan Qarnin” duk sun yi dogayen bayanai da suke tabbatar da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne kawai ya cika waxannan siffofi da Shehu Usman xan Fodiye ya zayyana. NA FARKO : Shehu ya ce za a haifi Ibraheem mataimakin Imam Mahdi (AF) ne a qasar yamma manesanciya. To, idan mutum ya duba hadisan da suka yi maganar bayyanar Imam Mahdi (AF), zai ga cewa duk sun tabbatar da cewa Imam Mahdi (AF) zai bayyana ne a Makkah, kuma mataimakansa guda 313 za su je can ne su yi masa Mubaya’a. To, in aka yi dubi ga Makkah a matsayin wurin da Imam Mahdi (AF) zai bayyana, kenan za a iya cewa qasar da mataimakinsa zai fito wato Nijeriya “Qasar Yamma Manesanciya”, domin in dai za a auno Nijeriya daga Saudiyya, za a iya qiranta qasar yamma mai nisa. NA BIYU : An ce Ibraheem xin zai bayyana a shekarar 1370 bayan Hijira, sai ga shi an haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1372 bayan Hijira. Wannan ya dace sosai da zancen Shaikh xan Fodiye, domin in za a fassara abin da Shehu ya faxi daga Fulatanci ko daga Larabci zuwa Turanci, to cewa za a yi; “Za a haifi Ibraheem Sharafuddeen ne a shekarun saba’inoni wato (Seventes) bayan Hijira” wanda hakan yana nufin ba lallai ne sai an haife shi a 1970 daidai ba, a ko da yaushe aka haife shi daga 1970 zuwa 1979 duk a 70s aka haife shi. Sannan kuma, in ma mun tafi akan cewa yana nufin za a haife shi ne a 1370 daidai, to dole mu yi la’akari da cewa Shehu Usman bin Fodiye waliyyi ne ba Annabi ba, Ma’asumi ne kawai in ya faxi magana take tabbata cif da cif, su waliyai ana iya samun abin ya gaza da kaxan ko ya qetare da kaxan. NA UKU : An faxi siffofinsa kamar cewa shi baqin fata ne, kuma mai faxin goshi, mai alama a fuska, mai mayalwacin gemu, mai faxin qirji, kuma mai manyan idanu farare kamar na Mage. Waxannan siffofi suna iya xaukar ma’anoni biyu, na zahiri da na baxini, kuma duk biyun sun dace da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Misali;Duk mutumin da ya san Shaikh Zakzaky (H), ko ya ga hotonsa, to zai ga cewa a zahirin halittarsa baqin fata ne, kuma yana da faffaxan goshi, kuma yana da alamar Sujjada a fuskarsa, kuma yana da mayalwacin gemu, kuma yana da faxin qirji, kuma yana da manyan idanu farare, da dai sauransu. Amma a fassara ta baxini, ba zahirin halitta Shehu Usman bin Fodiye ke nufi da waxancan siffofin ba, aron kalma ne ya yi a matsayin lamiri. Kenan, da ya ce mai faxin goshi, yana nufin mai yawan Sujjada na bautar Allah ne. Da ya ce mai alama a fuska, yana nufin mai Haiba ne da kwarjini da hasken fuska. Da ya ce mai yalwar gemu, yana nufin dattijo ne a maganarsa, (wato duk abin da ya faxa gaskiya ne kuma zai tabbata). Da ya ce mai faxin qirji, yana nufin mai tarin masaniya da zurfin ilimi na fannoni daban-daban ne. Da ya ce mai manyan idanuwa, yana nufin mai ganin shiriya ne a haqiqarta, da kuma xora mutane akan tafarkin shiriya madaidaici. Duk waxannan siffofi kuwa sun dace qwarai da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ka yi nazari ka gani! BUSHARAR NANA ASMA’U ‘YAR XAN FODIYE (R) : Waliyiya Nana Asma’u bint Usman bin Fodiye (R) wacce ta rayu tsakanin 1793 zuwa 1864, ta jaddada Busharar bayyanar mujaddadi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ita kam ma bayan ta ambaci sunan waliyi Ibraheem, da shekarar haihuwarsa, da dangantakarsa da Imam Mahdi (AF), sai ta qarfafa zance akan yadda wa’azinsa zai sha banban da na sauran malamai, da kuma uwa-uba nau’in sabon ilimin da zai bayyanar a cikin al’ummarsa, wanda wannan ke nuna ilimin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne, wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke yaxawa yanzu haka a wannan nahiya. Ga nassin Busharar Nana Asma’u a waqenta mai Baiti 40, amma mun naqalto daga Baiti na 17 ne zuwa na 30 kamar yadda mawallafin littafin “Bayyanar Sharafuddeen” ya yi, wanda sune ke qunshe da batutuwa akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H); A cikin shekarar Hijira ta 1400 (1979) ne, Wani Mujaddadin Musulunci zai bayyana. Usman (Xan Fodiye) ya faxi zuwansa, A lokacin da yake maganar Mahdi. Zukatan da suka haskaka za su fahimci wannan, Waxanda kuwa ke a cikin duhu ba sa fahimta. Ana jiran lokutan (bayyanarsa) tun, Shekaru xari uku da suka shuxe. Haqiqa an haife shi a shekarar hijirar, Annabi ta 1370 zai bayyana. Yana da matsayi mai girma, Don haka dole ne a girmama shi. Littattafansa sune hujjarsa, In kana musu to ka karanta su (ka jiya). Ganinsa kawai zai iya bayyanar maka, Da ko shi wanene (idan har ka kula). Kowa (ya kamata) ya so shi, Ya kuma kula da amfanonin da zai zo da su. Ba ko shakku cewa akwai alamomi, Musulmi ku kula kuma ku fahimta. Ka da ku kula da ‘yan qananan abubuwa, Ku kula da hankali kuma ku karanta littattafansa. Ka da ku ce, “Mu ba mu gaji wannan ba”, Sannan kuma mu (sam) ba mu fahimce shi ba. Duk yadda lamari ya kasance ku karanta littattafan, Kuma ku sanya zukatanku a cikin aminci. Ya Allah Ta’ala ka tsare mu daga jahilci, Ka kuma kare mu daga wahalhalun (Duniya). (The Collected Works of Nana Asma’u. Na Jean Boyd & B.B Mark, naqali daga; “Bayyanar Sharafuddin”, shafi na 48, bisa tasarrufi da tsari). NAZARIN BUSHARAR NANA ASMA’U (RA) : Idan muka nazarci waxannan Baituka da kyau, za mu ga akwai qwararan shaidu na zahiri da ke tabbatar da cewa Nana Asma’u (RA) ta qara bayyana wasu siffofi ne na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wannan Bushara tata, kuma ta fito da abin a fili qarara ta yadda ba za a iya kore dacewar waxannan siffofi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba. Misali, bayan ta faxi shekarar da za a haifi Mujaddadin a 1370, tare da tabbatar da cewa zai jaddada addinin Musulunci, da kuma cewa zukatan da Allah ya nufa da haske za su fahimci Da’awar wannan mujaddadi da aka shafe kusan shekaru 300 ana jiran bayyanarsa. Sai ta faxi wasu sabbin abubuwa guda biyu wanda Shehu Usman bai faxe su a tasa Busharar ba. Abubuwan kuwa su ne; Bayyanar Mujaddadin a shekarar hijira ta 1400 wacce ta yi daidai da shekarar 1979 Miladiyya, sai kuma yawan littattafan Mujaddadin, da kuma sabon ilimin da zai zo da shi, wanda ta ce lallai mutanen zamaninsa su karanta littattafan, kuma kada su ce wa sabon ilimin da ya kawo “Mu ba mu gaji wannan ba”. Sannan ta qarqare da cewa, lallai mutane su yi anfani da hankali wajan nazarin rayuwa da ayyukan wannan Mujaddadi idan ya bayyana, kar su riqa la’akari da ‘yan qananan abubuwa. Waxannan muhimman abubuwa guda biyu ba wani Malami a Afirka da ya siffatu da su sama da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin a shekarar 1979 ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana, wato a shekarar ne ya shelanta Da’awarsa a wani babban taron qungiyar xalibai musulmi da ya gudana a garin Funtuwa, kuma a shekarar ne duniya ta fara jin xuriyarsa da sunansa a karon farko, sakamakon rikicin “K-GUYS” da ya faru a Jami’ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya, lokacin da Shaikh xin ya jagoranci matasa musulmi suka wargaza taron qungiyar mashaya giyar kwakwa da suka saba yi duk shekara. A lokacin manyan jaridu (ciki har da na qasashen waje) da sauran kafafen yaxa labarai duk sun yaxa wannan abu da ya faru, tare da ambatar sunan Shaikh Zakzaky (H) a matsayin wanda ya jagoranci abin. Sannan da Nana Asma’u ta ce zai kasance mai yawan littattafai, wanda take cewa ya kamata mutane su karanta su, wannan zai iya xaukar ma’anar yawan wa’azozi, da laccoci, da huxubobi, da Muhadharorin da Shaikh Zakzaky (H) ke ta yi ne, wanda yanzu kusan shekaru 40 kenan yana yi, amma da yawan mutane ba su ma sauraron jawaban, balle su ji me yake faxa, balle su fahimce shi. Na’am, idan ma tana nufin littattafai ne na zahiri, to akwai ximbin littattafan Shaikh Zakzaky (H) akan batutuwa daba-daban, wanda laccoci da muhadharorinsa ne aka maishe su zuwa littafi. Abu na uku shi ne nau’in sabon ilimin da zai bayyanarwa musulmi a zamaninsa, wanda Nana Asma’u take gargaxin cewa kar mutane su ce su ba su gaji irin wannan ilimin a wajan iyayensu ba. Wannan a zahiri yana nufin ilimin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne, wanda ake qira Shi’a, domin shi ne nau’in sabon ilimin da Shaikh (H) ya bayyana a wannan nahiya, wanda kuma sashen musulmi ke faxa da shi bisa hujjar cewa su ba su yarda da shi ba don ba akansa suka tarar da iyayensu ba. Kenan, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne mujaddadin da Shehu Usman bin Fodiye da ‘yarsa Nana Asma’u suka yi Busharar bayyanarsa, domin shi ne kaxai ya cika sharuxxa da siffofin da waxannan waliyyan Allah suka zayyana a Busharorinsu, amma idan wani na da ja, sai ya kawo nasa gwanin a xora shi akan waxancan sikelin a gani! more_vert RefreshRate ApplicationMore Application SHAIK IBRAHEEM ZAKZAKY (H) Jagoran harka islamiyyah a Afrika  homeGidashareKyautarwapeopleMasaniyahelpIzinimailTuntuba   KAMMALAWA Alhamdulillahi Auwalan wa Aakhiran, a wannan xan qaramin littafi, mun yi tsokaci a vangarori da dama na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kama daga busharorin bayyanarsa, zuwa haihuwa da yarintarsa, zuwa Da’awa da salon gudanar da rayuwarsa, zuwa gallazawar azzalumai gare shi, har zuwa kan sauran abubuwan da ke xanfare da rayuwarsa, muna fatan Allah ma ji roqon bayi ya tabbatar da mu tare da shi Abadan wa Sarmadan! Muna roqon Allah cikin qasqantar da kai, ya qara kariya mai yawa da tsaro ga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya tsawaita rayuwarsa tsawaitawa, ya qara masa garkuwa da kariya daga makirce-makirce da mugun nufin maqiya da azzalumai, ya fisshe shi sharrin zamaninsa, ya qara masa qoshin lafiya da inganci, ya qara masa daraja da xaukaka da martaba, ya qara masa yarda da kusanci gare shi, ya qara masa Nasara akan mahassada da abokan gabarsa, Yaa Allah ka cika burin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a rayuwarsa, ka hutar da zuciyarsa da cikar burinsa, ka kwaranyar masa da damuwa da qunci a zuciyarsa, ka zamo gatansa akan komai ya Rabbal Alameen! Bihaqqi Muhammadin wa Aailihix-Xahireen! “Allahummah Swalli Ala Muhammadin, wa Aali Muhammad!”.  more_vert RefreshRate ApplicationMore Application SHAIK IBRAHEEM ZAKZAKY (H) Jagoran harka islamiyyah a Afrika  homeGidashareKyautarwapeopleMasaniyahelpIzinimailTuntuba   MANAZARTA 1. BAYYANAR SHARAFUDDIN: SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H). Al’Ameen Isah Al-Sakkwaty, I.M Publications, 2001. 2. TARIHIN SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY DA HARKAR MUSULUNCI. Malam Muhammad Sulaiman. GDP-Printers, 2015. 3. MALAM ZAKZAKY (H): RAYUWARSA DA KARAMOMINSA. Mal. Yaqubu Yahya, da Mal. Abubakar Abdullahi, 1994. 4. SHEKARU 60 MASU ALBARKA NA SAYYID ZAKZAKY (H). Mal. Ibrahim Musa (Edita), I.M Publications, 2012. 5. MALAM, MALAM NE. Malam Haruna Shelleng, Sauqi Press Kaduna, 1428 – 2007. 6. MUJADDADIN WANNAN QARNIN: Sayyid Ibrahim Zakzaky (H). Nasir Miji Gombe, Babu Maxaba’a, 2013. 7. KITABUL-BUSHRA: Busharar Bayyanar Sheikh Zakzaky (H). Mal. Ibrahim Musa (Edita), I.M Publications, 1416 Hijra. 8. WAKILIN MANZO (S) A DORON QASA (Malam Zakzaky). Muhammad Danjuma Katsina, I.M Publications Zaria, 1998. 9. Jaridar ALMIZAN, da Mujallar GWAGWARMAYA. 10. KASETOCI Da INTANET Da SOCIAL MEDIA. ✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳ TALLA Mai karatu ! Kana son sanin tarihin Harkar Musulunci a Nijeriya cikin sauqi kuma daki-daki dalla-dalla? Maza tanadi kuxinka don mallakar sabon littafi mai fitowa, mai suna “TARIHIN HARKA ISLAMIYYAH”. Shi wannan sabon littafi ya hallale bayanai akan Harka Islamiyya ne zalla, da munufarta, da ayyukanta, da qudurorinta da kuma bayyana ayyukan kowace Lajana ta Harka Islamiyyah. Littafi ne da zai fito daga Cibiyar Wallafa da Yada Jawaban Shaikh Zakzaky (H), wanda zai haskakawa mutum masaniya game da tushen Harka Islamiyyah, Manufarta, Ayyukanta, Lajanoninta da inda ta dosa. Ku dai ku tanadi kuxinku kawai kafin littafin ya shigo kasuwa! An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels