An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [2/28, 1:08 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 1* _Free page_ Misalin ƙarfe biyar da rabi shida saura na asuba, kyakykyawar baƙar budurwar ta isa ƙofar gidan Hakimin garin giwa. Mai suna Alhaji Haruna Musa giwa, wanda shine Hakimin garin kuma aminin mahaifinta marigayi Malam Mahmuda. Tana kuka wurjajan ta ci burki daga bakin zauren shiga gidan, tana faman raba idanu jin sautin karatun da ke fitowa daga masallacin kusa da gidan.Da alamu lokacin ake sallar asubi a masallacin,sai ta dawo da baya tana zama akan dakalin ƙofar gidan.Kuka sosai take yi iyakan ƙarfinta,baƙin kyakykyawar fuskarta gaba ɗaya ya tasa idanunta sun kumbura domin tun cikin dare take aikin kukan tashin hankalin halin da Innarta ke ciki. Tana nan zaune tana sharan hawaye da sauke ajiyar zuciya, su Hakimi suka fito daga cikin masallaci. Tun daga nesa yake hango wata da jan hijab zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasa, hakan ya sanya shi ɗaga ƙafa yana riga Yaransa isa ƙofar gidan domin zuciyarsa na gaya masa cewa ba lafiya bane. "Najmatu lafiya, ko jikin Mairo ne ya sake motsawa kuma? Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa ya furta hakan, a lokacin da ya isa wajen dakalin da take zaune akai ya fahimci cewa Ƴar amininsa ce zaune mai suna Najma. Wacce ya kira da Najma tayi saurin dubansa wasu hawayen na zarya akan fuskarta,taja ajiyar zuciya tana faɗin "Jikin ne Baba Hakimi, kwana mukai bamu runtsa ba.Yanzu haka na baro tana jin jiki." Ta kai ƙarshen maganar tana rushe masa da kuka mai motsa zuciyar mai saurarenta. Hakimi ya ja salati yana faɗin, "Subhanallah!" Ya waiwaya bayansa yana yafuto ɗansa Auwalu da hannu, wanda ya tsaya suna magana da wasu samari. Ganin Hakimi na kiransa ya sanya shi isowa da sauri yana faɗin, "Baba gani." Hakimi ya dubesa da zallar damuwa akan fuskarsa ya ce, "Maza shiga cikin gida ka ɗakko mukullin mota ka fito mu wuce asibiti, jikin Mairo ya sake motsawa." Auwalu ya ruga a guje zuwa cikin gidan yana jan salati a zuciyarsa, domin suna tsananin son Inna Mairo da ganin mutuncinta. Cikin hanzari ya fito daga cikin gidan hannusa riƙe da mukullin motar Hakimi.Ya isa garejin gidan ya fiddo motar, Hakimi ya shiga gaba yayinda Najma ta shiga baya tana faman jan ajiyar zuciya. Kamar yadda Najma ta sanar da Hakimi Inna Mairo na tsananin jiki, a haka suka sameta. Da taimakon Auwalu da Najma suka kamota zuwa mota, suka wuce da ita asibitin zaɓawa dake garin. Taimakon gaggawa aka bata har aka samu ta dawo hayyacinta.Likitan da ya dubata ne ya basu tabbacin cewa rashin shan magungunanta akan ƙa'ida shike maido da komi baya, don haka dole a kula da sayensu akan lokaci da zaran sun ƙare. Ya kammala dukkanin jawabinsa sannan Ya rubuta musu wasu magungunan kala biyu, Ya ce idan ta shayesu bata ji daidai ba su wuce da ita babban asibitin koyarwa dake shika domin ta samu ganin babban likita. Hakimi sukai godia bayan sun amsa takardan maganin. Najma da sai lokacin hankalinta ya fara kwanciya, ganin Inna ta dawo hayyacinta. Sai ta kama hannunta suka fito daga ofishin Likitan, wanda duk yawancin sanda za a kawo Inna Mairo shi ne ke dubata, kuma shi ne babban likita baki ɗaya a asibitin Zaɓawan. Suna tafe cikin mota don komawa gida Hakimi na mitan yadda ƴan uwan Inna Mairo da matar mahaifinta da suke kira Gwaggo suka juya mata baya. Ya cigaba da faɗin, "Yanzu saboda Allah Mairo idan su sun yanke zumunta dake sai ke ki biye musu ki daina zuwa inda suke? Karki manta fa kece ƙaramarsu Mairamu, duk yadda zasu gujeki su juya bayansu gareki don sun yi arziƙi, ke bai kamata ki yanke zumunta dasu ba. Ina giwa ina kaduna da za a ce kin yanke dukkan alaƙa da ƴan uwanki, kin zaɓi ki cigaba da rayuwa cikin tsananin maraici da ciwan zuci?" Ya dakata da maganar zuciyarsa na shiga ƙunci mai yawa, domin yana tsananin jin ciwon yadda Ƴan uwan Inna Mairo duka biyu suka wofintar da ita tun bayan rasuwan Mahaifinsu. Inna Mairo dake sauraren Hakimi ta kasa magana sai kuka, kukan da ke tasowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta yana ƙona ruhinta. Sanin da Hakimi ya yi Inna Mairo har da ciwon zuciya ke barazanar kamata,sai ya koma yin rarrashi da nusar da ita illar yanke zumunta koda ace an yanke maka, kai ance ka sadar ga wanda ya yanke maka ɗin. Har suka isa ƙofar gidan Inna Mairo Hakimi nasiha yake mata cikin rarrashi, Inna ta dinga saurarensa kalamansa na ratsa zuciyarta da sake raunatata. "Najma kamata ku shiga daga ciki,zuwa anjima Auwalu zai je ya samo magungunan da aka rubuta ɗin. Mairamu Allah ya ƙaro afuwa, ki daina sanya yawan damuwa a zuciyarki domin kin fi kowa sanin cewa ba a son mai hawan jini na yawan tunani da sanya damuwa a rai. Musamman ke da zuciyarki ke barazanar kamuwa.Na horeki da ki daina sanya yawan tunani ki maida dukkan lamuranki zuwa ga Allah. Na sani ke ɗin mai tawakkalice amma ki ƙara ninka jururiyarki domin shi komi na rayuwa NUFIN ALLAH ne Mairo, yadda duk Yaso haka yake kasancewa. Allah zai baki lafiya ya kuma ganar da ƴan uwanki da Gwaggo cewa sun yi kuskure, sun kuma ci amanar dattijon arziƙi marigayi Alhaji Muhammad da basu rungumi wasiyyarsa sun riƙe amanarki da ya bar musu ba." Hakimi ya dakata da maganar yana kallon Inna Mairo da hawaye ke gudu akan fuskarta, ta gyaɗa kanta murya a shaƙe ta furta, "Na gode Hakimi, Ubangiji ya biya maka buƙatunka na alkhairy duniya da lahira. Allah Ya duba gaba da bayanka Ya albarkaci zuriyya.In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na rage yawan damuwar." Ta kai ƙarshen kalamanta lokacin da Najma ta zagayo ta buɗe mata murfin motar ta fito. Hakimi ya sake mata fatan samun sauƙi yana jin tausayinsu ita da Ƴarta Najma na sake mamaye zuciyarsa. Tabbas Ya yi rashin amininsa mai ƙaunarsa, Yana kuma jin cewa kulawa da Iyalinsa tamkar tilas ne a garesa domin ba zai iya zuba ido rayuwar su Inna Mairo ya tagayyara ba. Shiyasa tun bayan rasuwar aminin nasa Malam Mahmuda shi ne yake ɗawainiya da su Inna Mairon,bai taɓa gajiyawa ko gazawa ba,da taimakon Ubangijinsa yake musu komi. Najma a hankali take takawa hannunta riƙe dana Inna Mairo har suka dangana da cikin gidan nasu, wanda ginin ƙasa ne da ya samu aka filascesa da siminti.Tsakar gidan ma an filascesa babu ƙasa sam a tsakar gidan,ko'ina fes yake don suna da tsanani tsafta da kula da muhalli. Ƙaramin ɗakin nasu mai ɗauke da falo da ɗakunan bacci biyu a jere suka buɗe, Inna Mairo ta zame hannunta daga na Najma tana nufan hanyar ɗakin baccinta.Najma tabi bayanta da kallo tana mata sannu cike da tausayi. Inna Mairo ta amsa ba tare da ta waiwayo ba, don burinta shi ne ta dangana ga tsohuwar katifarta ta yi kukan da take riƙewa na tunawa da gwarzon mijinta da Mahaifinta da suka kwanta dama. Domin tabbas da suna raye da sun share mata baƙin ciki mai yawa na rayuwa,da bata yi kukan rashin gata ko makusantar da zata kwanta a kafaɗunsu ta yi kuka ba. Sai dai dukkanin gatan nata sun ƙare, ta rasa uwa tun tana tsummar goyo. Gashi yanzu ta rasa miji da uba,duka sun tafi sun barta cikin wannan duniyar mai cike da tarin rikita-rikita da ruɗin zuciya. Ta kifa ciki tayi kuka mai yawa har Najma dake zaune a falo ta zabga uban tagumi, sai da ta jiyo sautin kukan da Innar ke yi. Ta nufo cikin ɗakin baccin Inna Mairo a rikice, tana mai durƙushewa a gaban katifar da take kwance ta ce, "Inna lafiya, jikin ne? Don girman Allah Inna ki tausayamin ki daina sanya damuwa a ranki, domin ke kaɗaice kika rage gatana a yanzu. Sannan lafiyarki ita ce abinda tafi komi muhimmanci.Ki dubi girman Allah karki bari lafiyarki ta salwanta akan baƙin cikin waɗanda basu san ma kina yi ba." Najma ta ƙare maganan tana riƙo hannun Inna Mairo ta saki kuka mai ban tausayi, hakan ya sake karya zuciyar Inna Mairo.Ta riƙe hannun Najma da kyau tana faɗin, "Ba don su nake wannan kukan ba Najma, ina kokawa ne don rashin Mahaifinki da nawa.Tuni na daɗe da cire damuwar su Gwaggo a cikin zuciyata,na danne dukkan ƙawazucinsu a raina.Bana ganin laifin su Yaya Kabeeru, laifin Gwaggo nafi gani Najma domin na san ita ce tayi musu katanga dani, ta kuma hana su raɓemu sabida da tsananin ƙiyayyarta garemu ni da Mahaifinki." Inna Mairo ta dakata da maganar zuciyarta na mata wani irin suya, ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da ke mata wani irin zafi. Ganin hakan ya sanya Najma taya ta dafe wajen tana mata sannu cikin tsananin jin tausayin Innartata. Sun ɗauki lokaci a haka hannunsu na dafe da ƙirjin Innar,kafin ta zare hannun Najma tana faɗin, "Tashi ki kunna wuta ki ɗaura abin karin kumallo Najma." Najma ta jinjina kai tana tashi tsaye ta zare hijab ɗin jikinta, idanunta akan Inna ta ce, "Sannu Inna, bari in je kicin ɗin in ga ko akwai ragowar gawayin da za a iya kunnawa." Daga haka ta fito daga ɗakin cikin takunta mai cike da nutsuwa ta halitta. Na dinga bin budurwar da kallo, wacce zata kai shekaru sha bakwai.Ina yaba kyawu da tsarin halittarta,domin babu ƙarya Allah Ya yi mata baiwar kyawu da cikar halitta mai asalin fisgar hankali. Baƙace sosai amma kyakykyawar da aka ƙera halittarta tamkar ita tayi kanta. Tana da tsayi matsakaici ba mai yawa ba, sannan tana da gaba da baya wanda suke a cike. Musamman ƙirjinta da yake a tsaye cir! Da cikakkun dukiyar fulani.Dogon hanci gareta har baka,sai manyan idanu farare tas! Masu turawan ƙwayar ciki baƙi siɗik! Ɗan ƙaramin bakinta so cute da cinkusassun gashin giranta baƙaƙe siɗik! Sun fi komi ƙawata kyawun fuskarta. Bata da jiki kuma ba za a kirata siririya ba, sai dai a kirata mai murjajjen jiki.saboda fatar jikinta a cike yake da tsoka babu alamar rama ko siranta a tattare da ita. Koda ta nufi cikin kicin ɗin kai tsaye wajen robar da suke zuba gawayin ta nufa, ganin akwai ragowarsa da ɗan yawa ya sanya ta ɗakko murahun gawayin guda biyu ta zuzzuba wanda zai isheta amfani. Bayan ya ruru ne ta ɗaura ruwan wanka a guda ɗaya, ɗaya kuma ta ɗaura ɗumamen ragowar tuwo miyar kuka da suka ci a daren jiya suka rage.......✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Najma# #Hot lovestory# Aysha Ɗansabo ce✍🏻 [2/28, 1:09 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH....!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 2* _Free page._ Kafin ruwan ya tafasa tuwan ya ɗumamu Najma ta kammala sharan ɗakinsu, wanda ba wani girma bane da shi. Bayan ta haɗa musu shayi ruwan bunu(ruwan lipton), ta juye ɗumamen a kula ta nufo ɗakin Inna Mairo da shi. A falo ta aje komi ta nufi bedroom ɗin wajen Inna Mairo, ta sameta a kwance har lokacin tayi lamo akan katifarta tana faman zurfafa tunani. Cikin sanyin murya Najma ta zauna daga bakin bed ɗin tana faɗin, "Inna na kammala, ga ɗumamen da ruwan lipton can a falo. Inna Mairo ta muskuta ta tashi zaune tana sauke manyan idanunta da Najma ta gada a kanta, ta sauke numfashi a hankali ta ce, "Sannu Najma da ƙoƙari, Allah ya yi albarka ya zaɓa muku mazajen aure na gari." Najma da tuni ta gane jam'u da Inna Mairo tayi tana nufin ita da su Luban gidan hakimi take wa addu'ar, sai ta kauda kai tana amsawa a zuci. Inna Mairo ta cigaba da cewa, "Da zaran mun kammala karin kumallon sai ki bani ruwan wanka, watakila idan nayi naji ɗan ƙarfin jikina." Najma ta murmusa ta ce, "To Inna!" Daga haka suka fito zuwa falon da Najma ta shareshi tsaf, ta goge yagaggen ledar tsakar ɗakin. Suna cin abincin suna taɓa hira akan ciwon Inna Mairo da irin yadda ake samun kuɗin sayen magungunan da ƙyar.Ba don Hakimi ba da tuni watakila Innar ta mutu,sabida rashin gata da wanda zai tsayawa lamuransu har ya ɗauki nauyinsu. Ba kuma don Innar ta rasa Ƴan uwa ba, sai don Ƴan uwan nata sun gujeta sun juya mata baya shekaru kusan bakwai kenan rabonta dasu.Tsakaninta dasu sai dai aiken kayan abinci da zanin sallah da suke mata duk shekara, amma baya ga haka babu mai takowa inda take domin sunyi arziƙin da suke ganin tamkar ci bayane su tako ƙauyen garin giwa su ce suna da ƙanwa bare har su ga halinda take ciki su tallafa mata. Wani irin abu mai ɗaci ya tsayawa Inna Mairo a maƙoshinta, lokacin da ta tuno zuwan Gwaggo na ƙarshe garin giwa, bayan rasuwar marigayi Malam Mahmuda. Najma ta kwashe komi ta kai kicin ta aje, ta ɗauki bokiti ta ɗebowa Inna ruwan zafi ta surka, ta kai mata banɗaki don tayi wanka ko zata ji daɗin jikinta kafin Baba Hakimi ya aiko da magungunan da zata sha. Ɗakinta da ke kusa dana Inna ta shiga ta share tare da gyara shinfiɗar lafaffiyar katifarta, wacce tun ta makarantar kwanan da suka yi ne ta dawo da abin ta tana kwanciya akai. Gefen katifar ta samu ta zauna ta sauke numfashin a hankali, zuciyarta na kwaɗaita mata son jin asalin tarihin Innarta da yadda aka yi ta auri Mahaifinta Malam Mahmuda. Tana matuƙar son sanin musabbabin da Gwaggon kaduna take nuna wa Inna ƙiyayyar da har ta kai ta rabata da Ƴan uwanta, ta hana su raɓeta ko ita Innar ta rabesu. Tana nan zaune tana zurfafa tunani har ta ji shigowar Inna ɗaki alamun ta dawo daga banɗaki yin wanka, tayi saurin tashi ta fito tana faɗin, "Inna har kin fito?" Inna Mairo ta dubi tilon Ƴarta da take duba ta ji sanyi a ranta ta bata amsa da faɗin, "Na fito Najma, ke ma sai ki je ki yo wankan kafin asan abin yi zuwa rana ko?" Najma ta jinjina kai tana faɗin, "To Inna, amma ina ga da rana ɗinnan da wuya mu samu abin girkawa domin babu sauran kayan abinci sun ƙare." Inna Mairo tayi shiru, kafin daga bisani ta dubi Najma tana faɗin, "To shikenan Najma, Allah zai rufa asiri. Ina ga Hakimi ya shafa'a ne ba a kawo kayan abincin wannan satin ba.Ki yo wankan ki fito akwai ɗari biyar sai ki je ki auno mana garin kwaki muyi kwaɗonsa da ƙuli muci kawai." Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa da maganar Inna ta ce, "To shikenan Inna, bari in je in yo wankan." Ta nufi ƙofar fita daga ɗakin ta bar Inna Mairo da bin bayanta da kallo, tana mai jin matuƙar tausayin Najmar na danne zuciyarta.A kullum ta tuna cewa Najma ita kaɗaice a gareta, kuma bata da sauran dangin uba a raye da zasu tallafeta sai ta ji hankalinta ya sake tashi. Domin ita kanta ya ta ƙare da nata Ƴan uwan bare har ta sanya ran watarana zasu tallafesu ita tilon Ƴar nata Najma. Ta ɗanɗana zafin rashin Ƴan uwa ko Ƴar uwa shaƙiƙai da bata da su, ta san zafi da illar hakan ga duk wanda ya taso cikin tsangwaman Ƴan uban da kansu ba a haɗe yake ba. Ta san illar ƙiyayyar matar uba, domin shi ne silar shigarta duk wani halin ƙuncin da take ciki a yanzu, bayan ƙasa ya rufe idanun Abbah da gwarzon mijinta Malam Mahmuda. Domin a lokacin Abbah na raye duk irin ƙiyayya da jin zafinta da Gwaggo ke yi, bata iya nuna mata wani abun sabida shakkar idanunsa. Amma tun daga randa ya kwanta dama, ta sake gane irin ƙiyayyarta da ke zuciyar Gwaggo, wanda bakomi ya sake assasa ƙiyayyar ba sai mugun riƙo da Gwaggon ke da shi. Inna Mairo ta faɗa ɗakinta don shafa mai ta sanya kaya, tana yi zuciyarta na sake tariyo mata da irin rayuwar da tayi a garin giwa ,tun daga zuwanta tana amarya, har kawo yau da wanda ya yi silar zuwanta garin bashi a raye. Ya tafi ya barta da tarin kewa da ƙuncin zuciya, Ya barsu a lokacin da ita da tilon Ƴarsa ke matuƙar buƙatar kulawarsa. Hawaye masu tsananin zafi da sam bata iya riƙesu a duk lokacin da tunaninsa ya bijiro mata suka silalo daga idanunta,ta kai hannu ta sharesu tana jin ƙunci mai yawa na sake mamaye zuciyarta. Cikin sanyin jiki ta kammala kintsa kanta ta sanya riga da zani na wata atamfar chiganvy, wanda ke ɗaya daga cikin irin zannuwan da ake aiko mata dasu daga hannun Ƴan uwanta su Yaya Kabeeru. Najma wanka tayo ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar atamfar roba, kalar atamfar ja ce da ta haska baƙar fatarta mai laushi.Fuskarta ya yi fayau babu ɗigon kwalliya illa tozali da ta zizarawa fararen idanunta, waɗanda ke da wani irin haske da ƙyalli tamkar ruwan hawaye na taruwa a cikinsu. Gashin kanta sassalka irin na asalin fulanin da ta gado wajen Inna, ta ɗaureshi a tsakiyar kanta kafin ta ɗaura ɗankwalin kayan nata. Lokacin da ta fito daga ɗakin ta samu Inna Mairo zaune a falo, ta nema waje ta zauna daga ƙasan ledar tsakar ɗakin ta ce, "Inna na kammala shirin, bani kuɗin siyan garin kwakin in je in dawo kafin rana tayi." Inna Mairo ta dubi Najma tana yaba kyawunta, wanda ta gado a wajenta. Baƙar fatarta ce kawai na Malam Mahmuda, amma kyawun fuskar da surar jikin duk nata ne, domin babu inda Najma ta barota a kamanni sai bambamcin kalar fata kawai. Ita Inna farace tas! Wacce a kallo ɗaya zaka gane cewa jinin fulanice sosai. Ta miƙa hannu ta ɗakko naira ɗari biyar ɗin da shi kaɗai ya rage musu a gidan ta miƙawa Najma, ita kuma ta sanya hannu ta amsa tana miƙewa tsaye ta tashi ta nufi ɗaki don ɗakko hijab. Lokacin da Najma ta dawo ta samu Auwalu ya kawo ma Inna magungunanta, sai dai ba a samu guda ɗaya ba sabida tsadarsa. Ta dubi Inna a lokacin da take mata bayanin ta ce, "Yanzu Inna to ya za a yi kenan?" Inna Mairo tayi murmushin ƙarfafa guiwa ta ce, "Allah zai kawo yadda za a yi Najma, ni burina ma mu sake samun jarin da zaki cigaba da toya ƙosannan tunda sana'ar ya amshemu dashi muke samun na rufin asiri." Ta kai ƙarshen maganar da sanyin murya. Najma ta jinjina kai ta ce, "To Inna ina zamu sama jarin? sai dai idan za a sake ɗaga wani abin a siyar ko?" Inna ta ɗanyi jim...Kamar ba zata tanka ba, sai daga bisani ta bai wa Najma amsa da faɗin, "Najma na yanke shawaran mu sai da katifar ɗakin Malam tunda babbace zata yi daraja." Najma da zuciyarta ke sake raunana ta dubi Inna ta ce, "Hakan ya yi Inna, Allah sa tayi darajar da za a samu jarin mai ɗan kauri." Inna Mairo ta amsa da cewa, "Ameen Najma, idan kin kammala ayyukan zuwa anjima sai ki je gidan Adama dillaliya ki yi mata maganar katifar." Najma ta ce, "To Inna!" Daga haka ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi kicin don haɗo musu kwaɗon garin kwakin. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin kwaɗon wanda yaji ƙuli dasu tumatir da albasa da ta yankasu gunin sha'awa a ciki, ta juyosa cikin baban faranti ta nufi ɗakin Inna dashi. Ta samu Inna ta shige ɗaki don yin sallar azuhur, hakan yasa ita ma ta fito ta ɗauki buta ta nufi bayi don kama ruwa da ɗauro alwala. Bayan sun idar da sallar ne suka haɗu suka ci kwaɗon cikin kwanciyar hankali. Najma ta ɗebo musu ruwan rijiyarsu mai daɗi suka sha suka yi hamdala,sannan ta ɗakko ma Inna magungunanta ta sha. Suna zaune suna ɗan taɓa hira Najma ta dubi Inna Mairo ta ce, "Inna don Allah ki sanar dani tarihinki dana aurenki da Babana, ina son sanin dalilin ƙiyayyar da Gwaggon kaduna ke miki." Ta dakata da maganar tana duban fuskar Inna Mairo don ganin yadda ta amshi maganarta. Inna da idanunta ke kan Najma tuni ta haɗe fuska, tana mata wani duba na mai yasa kike son sani? Kafin ta buɗe baki ta ce, "Najma sau nawa zan sanar dake babu ruwanki da sai kin san abinda ya faru? Ki rufe wannan maganar bana sonta." Najma da zuciyarta ke matuƙar son sanin cikakken tarihin Innarta da yadda aka yi aure ya wanzu tsakaninta da mahaifinta, sai ta narke murya tana matso hawaye ta ce, "Don girman Allah Inna karki gwaleni a wannan karon, wallahi ina matuƙar son sanin cikakken asalina da tarin yadda aka yi kika auri Babana? Ki taimaka ki sanar dani tarihin rayuwarki ko na ƙaru da wani abin." Inna Mairo ta jinjina kai cike da jin tausayin Najma, don ta san tana son jin tarihin baya ne ko zata gano ita ce mai laifi ko Ƴan uwanta su Yaya Kabeeru da suka wofintar da rayuwarta. Ta dubi Najma tana bata tabbacin zata sanar da ita tarihin rayuwarta baki ɗaya, da yadda aka yi Malam Mahmuda ya yi nasarar aurenta, har ya ɗakkota daga birni ya kawota ƙauyen garin giwa. Ta muskuta tana gyara zamanta sosai, ta fuskanci Najma da tayi zuru tana sauraren jin cikakken tarihin rayuwar Inna Mairo da Mahaifinta Malam Mahmuda...........✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Najma# #Luvstory# Ayshat Ɗansabo lemu😘 [2/28, 1:23 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!🤲🏻* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 3* _Free page_ *WAIWAYE...* Inna Mairo ta dubi Najma da take sauraren jin ta bakinta, ta saki murmushi mai faɗi kafin ta fara da faɗin, "Kamar yadda kika sani Babanki Malam Mahmuda haifaffan nan garin giwa ne.Ya taso cikin maraicin rashin iyaye,don Ya rasa iyayensa tun yana ƙarami.Hakan yasa ya taso a hannun ƙanin Mahifinsa mai suna Malam Lawal, Malam Lawal Malamin addini ne mai karantar da almajirai karatun addini anan babban zauren dake gidansa.Kasancewarsa Malamin addini ya sanya Babanki ya samu ilimi mai zurfi na addini a wajensa.Musamman karatun qur'ani da yafi zurfi a cikinsa, har ya kai ga haddacesa tun yana da shekaru goma sha biyu a duniya. Malam Lawal bai taɓa haihuwa ba, hakan ya sanya ya rungumi Babanki tamkar shi ya haifesa. Ya bashi dukkanin gata da kulawa, sannan Ya sanya shi a makarantar boko sabida bai yadda da zama cikin jahilci ba. Tun daga kan matakin primary Malam Mahmuda bai tsaya da karatun boko ba har sai da Ya kai matakin diploma,inda Ya yi karantun diploma ɗin nasa a jami'ar Ahmadu Bello dake zaria. Ya karanci fannin Business ne, don shi yafi sha'awar Ya zama ɗan kasuwa ba ma'aikacin gwamnati ba.Bayan Ya kammala karatun diploma ɗinsa ne Ya tattaro Ya dawo gida giwa, Ya cigaba da sana'ar yin ɗinkinsa na maza da ya ƙware akai. Don tun yana matakin sakandiri yake koyan ɗinkin har Ya ƙware, Ya mallaki keken kansa Ya buɗe shago anan zauren gidan Malam ɗin Yana sana'arsa. Sosai kuma yake samun rufin asiri da ɗinkin, domin Ya yi ƙwarewar da har daga birni yake samun ɗinkuna. Bayan Ya dawo gida ya cigaba da sana'ar ɗinkinsa ne, sai kuma tunanin son zurfafa iliminsa a ɓangaren addini Ya shigesa. Ya samu Malam Lawal Ya sanar dashi buƙatarsa, shi kuma sai Ya ji daɗi tare da bashi goyan baya har Ya yi masa alƙawarin danƙashi wajen wani babban amininsa wanda yake shi ma babban Malami ne garin kaduna. Malam Mahmuda ya yi farin ciki mai yawa, daga ƙarshe suka rabu da Malam ɗin akan cewa zai yi magana da aminin nasa mai suna Malam Muhammad Kabeer Dukku.Kwanaki biyu bayan sunyi maganar Malam Lawal ya kira Babanki ya shaida masa cewa ya fara shiri, don kuwa Malam Muhammadu ya yi na'am yana kuma maraba dashi a matsayin sabon ɗalibinsa. Kamar da wasa maganar tafiyar Malam Mahmuda karatu ya tabbata, ya yi sallama da dukkanin abokanansa su Haruna ɗan gidan Hakimi, da sauran abokanansa da suka tashi tare. Ya kama hanyar ya bar garin giwa bisa jagorancin Malam Lawal da matarsa Hanne da suka yi masa rakiya, suka kaisa har rigasa gidan babban aminin Malam Lawal ɗin..... Inna Mairo ta ɗan dakata tana duban yadda Najma ke saurarenta da dukkanin nutsuwarta, ta lumshe ido kaɗan tare da sake buɗesu akan Najma ta ce, "Kin san waye wannan Malamin da aka kai Babanki wajensa?" Najma tayi saurin girgiza kai alamun bata sani ba,hakan ya sanya Inna Mairo yin ƙaramin murmushi tana mai cigaba da faɗin, "Ba kowa bane sai mahaifina Malam Muhammad Kabeer Dukku. Shi ɗin ɗan asalin garin Dukku ne dake ƙaramar hukumar jihar Gombe. Bafulatani ne sosai domin uwa da ubansa duk fulani ne, neman karatun addini ne shi ma ya kawosa garin kaduna daga Dukku. Daga nan ne Ya ji daɗin zama har Ya fara sana'ar sai da zaruruwan ɗinki, yana kuma taya Malaminsa noma da kiwo. Sannu a hankali har Ya yi ƙarfi Ya buɗe ƙaramin shagon saida kayayyakin ɗinki a Kawo, gefe guda kuma yana kiwon kaji idan sun isa ci Ya fitar Ya sayar. Cikin hakan Ya haɗu da Gwaggo Hauwa,wacce take haifaffiyar ƴar cikin hayi rigasa ce. Bayan sunyi aure sai buɗi ya yi ta samuwar masa, samunsa na sake bunƙasa har ya kai Ya buɗe babban shago anan kawo. Shakerarsu biyu da aure aka haifi Yaya Kabeeru, bayan shekaru uku kuma aka sake haifo Yaya Ali. Daga nan sai haihuwar ta tsayawa Gwaggo, sai da ta share shekaru kusan takwas ta sake haifo ƴa mace. Sai dai ko kwana jaririyar bata yi ba ta bar gidan duniya, daga nan ne kuma Gwaggo bata sake haihuwa ba,har kawo yanzu da shekarun tsufa suka risketa.Abbah kamar yadda muke kiran mahaifinmu, Ya auro mahaifiyata ne bayan kusan shekaru talatin da aurensu da Gwaggo. A lokacin su Yaya Kabeeru har sun zama samari sun kammala deegree ɗinsu, don Abbah bai yi wasa ba wajen basu ilimin zamani dana addini. Hankalin Gwaggo ya tashi matuƙa da wannan ƙarin aure da Abbah Ya bijiro dashi.Ta dinga shuka tsiyataku kala da kala amma hakan bai sauya komi ba,don Abbah koda wasa bai ji cewa zai fasa auro Innata ba. wacce ya ganota a can Kaita mahaifarsa.Marainiyace da bata taso a hannun iyayenta ba duk sun rasu, ta taso ne a hannun wani ƙanin Babanta anan kusa da gidan Iyan Dukku, wato mahaifiyar Abbah kenan. Bafulatanace ita ma,uwa da ubanta duk fulani ne.Tausayin maraicin da take ciki da gallazawar da ake mata a gidan riƙonta, ya sanya mahaifiyar Abbah mai suna Iya bai wa Abbah ƙwarin guiwa akan Ya auri Innata mai suna Maryam. Ta kuma ƙara da kwaɗaitar dashi cewa watakila ya samu wani rabon,tunda haihuwa tuni ya ɗaukewa Gwaggo. Lokacin da aka yi bikin haukane kawai Gwaggo bata yi ba, sabida tsananin zafin kishi kamar yadda Iya ke bani labari. Malam bai aje Innata Mairo gida ɗaya da Gwaggo ba, sai ya kama mata haya a wata unguwa da ake cewa hayin banki. Wata ɗaya da auren Innata ta samu ciki, murna a wajen Abbah ba a cewa komi. Iya ma dake can Kaita da labari ya je mata murnar tayi sosai, tana taya shi addu'an Allah ya bashi ɗiya mace,don Iya na matuƙar son ƴaƴa mata domin ita Allah bai bata ba. Duka yaranta uku maza ne, Abbah kuma shi ne babba a cikinsu, sai ƙanninsa biyu Mansur da Salihu. Waɗanda suka rasu suna ƴan samari dasu, sun rasu ne sakamakon haɗarin mota da ya ritsa dasu akan hanyarsu ta komawa makarantar kwana da suke yi a bakori.Sai ya zamana Abbah shi kaɗai ya rage wa Iya, baya ga shi bata da kowa sai ƴaƴan ƴan uwa da take xagaye dasu.Abbah Ya yi juyin duniya ta dawo wajensa da xama taƙi, ba kuma komi ya sanya hakan ba sai rashin kirkin Gwaggo. Don ko kaɗan bata mutunta Iya da duk wasu dangin Malam,ƴan uwanta da ƴaƴanta kawai take gani da mutunci take kuma so. Gwaggo ji tayi kamar ta mutu don baƙin ciki, lokacin da maganar samun cikin Innata ya risketa.Ta sake ninka tsanarta da jin kishinta mai zafi a zuciyarta,duk da cewa ba gida ɗaya suke ba.Amma hakan bai taɓa sanyaya zuciyar Gwaggo ba,kullum cikin nuna kishi da ƙiyayyar da take wa Innata take. Tasha faɗi akan kunnuwar Abbah cewa ta tsani Innata, kuma ba zata taɓa son duk wani abu da zai fito daga tsatsonta ba. Malam ya yi nasihan ya yi faɗan ya yi rarrashin har ya gaji ya zuba mata ido, sai dai fatan shiriya da yake nema mata ba dare ba rana. Sabida a cewarsa zafin kishinta har ya yi yawa,dole a dinga roƙo mata sassauci a wajen Mahaliccinta. Da cikin Innata ya isa haihuwa ne Iya ta haɗo kayanta daga Dukku ta dawo kaduna, don Allah ya ɗaura mata son Innata tare da jin tausayin maraicinta. Daren ranar wata juma'a naƙuda ya kama Innata,kafin asuba an haifoni bayan Inna tasha matuƙar wahala.Ana murna ta sauka lafiya sai kuma jini ya ɓalle mata,kafin aje ga asibiti rai ya yi halinsa ta amsa kiran Ubangijinta.Faɗin irin tashin hankalin da Malam ya shiga bazai misaltu ba, hatta da samarin ƴaƴansa su Yaya Kabeeru mutuwar ya jijjigasu.Don duk irin ƙiyayyar da Gwaggo kewa Innata tana kuma cusa musu ra'ayin su ƙita,hakan bai yi tasiri a zuciyarsu ba sabida Innata bata taɓa yi musu koda kallon banza bane.Duk sanda zasu je wajen Malam idan yana gidanta,kyakykyawar tarba suke samu daga gareta.Take aka yi mini huɗuba da sunan mahaifiyata Maryam, bayan an kammala zaman makoki ne sai Iya ta tafi dani Dukku. Don ta ce bata amince a bai wa Gwaggo ko dangin uwata riƙona ba,tunda ita ma Innata marainiyace a cikin rashin gata ta rayu bare ace zasu iya riƙeni. Gwaggo kai tsaye dama ta ce ba za ta taɓa riƙon Ƴar kishiyar da kowa ya shaidi irin soyayyar da Abbah ya nuna mata,sabida ya aurota tana a ɗanya sharaf ɗinta. Iya ta tattara komi nawa muka wuce garin Dukku, na fara rayuwa a hannunta cikin tsananin gata da kulawa.Kusan koda yaushe Abbah na kan hanyar zuwa dubani,domin dukkanin soyayyar da yake wa Innata Mairamu sai ya koma kaina. Baya iya sati biyu bai je Dukku ya ga lafiyata ba, kuma baya zuwa hannu rabbana sai ya yi mana siyayya mai yawan gaske. Wannan sunturi da Yake yi a kaina da yadda ko a gaban Gwaggo ne Yake nuna tausayina da yake ji a cikin zuciyarsa, sai hakan ya haifar da ƙiyayyata a zuciyar Gwaggo. Ta juyar da dukkanin ƙiyayyar da take wa Inna zuwa kaina, bata taɓa yin kara tabi Abbah Dukku don ta dubani ba ko sau ɗaya.Wannan rashin karan da ƙiyayyar da take nuna mini akan idanun Iya idan munzo kaduna,sai ya sake haifar da rashin jituwa a tsakaninta da Iya. Sabida a lokacin duk wani mai son ganin ɓacin ran Iya to ya gwadamin rashin ƙauna, ko nuna min halin rashin kirki.Na taso da tsananin kyawu da shiga rai, sabida babu inda na baro kyawun Innata na asalin fulani. Jajir nake ga gashi har gadon baya, a haka na taso ina samun tattali da kulawa wajen Iya, wacce bata taɓa bari nayi kukan rashin uwa ba.Hasalima ita na taso na sani a matsayin Innata, sai dana fara girma nayi wayo har na shiga aji uku a primary, sannan Iya ta sanar dani cewa ita Kakata ce,Innata ta rasu tun ranar da ta haifeni. Sam banji komi a raina ba lokacin da take faɗa mini hakan, domin ni ita na taso na sani a matsayin uwata. Ban fara kukan rashin gata da rashin uwa da nayi tun ina tsummar goyo ba sai da Allah ya ɗauki ran Iya, a lokacin ina aji biyu na sakandiri. Nayi kuka kamar zan zautu sabida ita ce kaɗai gatana, da ita na rayu nayi sabon da bana iya ɓoye mata dukkanin abinda yake damuna. Ita kuma bata gajiyawa wajen yi min dukkanin abinda nake so matuƙar baifi ƙarfinta ba.Ban saba da Yayuna su Yaya Kabeeru ba, domin basa zuwa inda muke ni da Iya sai in wani abu ya faru, ko sallah tazo haka sai zo gaisheta.Sai kuma idan Abbah ya taso su a wasu lokutan, to shine zasu zo tare da shi. Amma baya ga gakan takanas dai su taka suje Dukku basa yi,musamman da ya zama sun kama aikin gwamnati a lokacin.Kuma dukansu ba a garin kaduna suke aikin ba, Yaya Kabeeru na NNRA Abuja ne.Wani abokin Abbah ne ɗan siyasa ya amshi takaddun Yaya Kabeerun Ya samo masa gurbin aiki wajen,wanda babban waje ne da ake biyan albashi mai tsoka matuƙa.Idan ba Ƴaƴan manya bama ba a cika bai wa wasu gurabin aiki a wajen ba, sai masu ƙafa da hanya kamar yadda ya kasance da Yaya Kabeerun. Shi kuma Yaya Ali ya samu aikinsa ne a gidan gwamnatin Kano, yana lallaɓawa da albashinsa yana kuma neman scholarship don yana da burin son fita waje ya yo masters deegree ɗinsa a can. Rasuwar Iya shi ya janyo mini dawowa hannun Gwaggo da zama,dawowar da ya zame mini tashin hankali da jefa rayuwata cikin ƙunci mai yawa.Domin Gwaggo ta amshi riƙona ne don babu yadda zata yi,sabida Abbah ya nuna bashi da wata mai riƙe masani, don haka dole in dawo ƙarƙashin kulawarsa tunda gata a raye matsayin matarsa. Tunda na dawo kaduna wajen Gwaggo ban taɓa ganin soyayyata a idanunta ko kan fuskarta ba, kullum na kalli idanunta tsanata nake hangowa a cikinsu. Abbah bai ɓata lokaci ba wajen nemo mini gurbin karatu a wata private secondary school, na cigaba da zuwa makaranta inda aka aje a JS3.Fara zuwa ta skull ɗin ne ya rage min ƙuncin da nake ji na xaman takura da bautar dani da Gwaggo ta fara yi, kuma da zaran na dawo daga boko ƙarfe huɗu zan shirya na wuce zuwa islamiya.Islamiyar a nan kusa damu ne bamu da nisa sosai,hakan yasa da ƙafa nake gangarawa na je.Bana shigowa gida sai ƙarfe shida na yamma,sai ya zama bani da wani lokacin kaina in ba alhamis da juma'a da bana zuwa islamiya ba. Shi ma kuma a ranakun Abbah ƙarfe huɗu yake baro shagonsa a Kawa,Ya dawo gida don karantar dani wasu littafan addinin. Duk wannan rashin lokacin da bani dashi, hakan bai hana Gwaggo nemo hanyar da zata cigaba da bautar dani ta ƙuntata mini ba.Sai ta koma tashina a bacci tun ƙarfe huɗu na asuba,a lokacin zan yi mata duk wasu ayyukan bautar gyaran ɗaki da wanke-wanken kayan da muka ci abincin dare. Ni zanyi abin karin safe kafin in tafi school, sabida tun a Kaita Iya ta horar dani ɗaura sanwa. Don ta sha ce mini Mairona iya girki shi ne martaba da adon mace, don haka ki dage wajen ganin kin iya sarrafa hatsi kar ki zama mai son jiki ta wannan fannin domin ke mace ce aure zaki yi. Hakan da Gwaggo ta gane ina da bai wa ta fannin iya girki,sai ya sanya ta sallami mai aikinta wacce dama Yaya Kabeeru ne ya ɗaukar mata ita, Ya ce lokaci ya yi da xata fara hutawa tunda sun kawo ƙarfi.Abbah bai san duk halin da nake ciki ba, don ta iya takunta a gaban idanunsa bata nuna min rashin ƙauna sosai. Sannan shi ba mazauni bane a kasuwa yake yini a shagonsa, sannan tun asubahin farko yake ficewa zaure don bai wa almajiransa karatu. Ba zai shigo gida ba sai anyi sallar asuba ya jasu jam'i, hakan ya sanya har in kammala dukkanin bautar da nake yi bai ma sani ba. Ina cikin wannan rayuwar aka kawo mahaifinki Malam Mahmuda Najma, na dawo daga makarantar boko na cidda mun yi baƙi ashe mahaifinki ne da ƙanin ubansa Malam Lawal da matarsa. Na gaidasu na wuce ɗakina da yake can ciki,bayan na sauya kayan jikina nayi shirin islamiya kamar yadda na saba yi.Na ci abincin rana da shi kaɗai Gwaggo keyi don dole tunda ina skull, na gabatar da sallar la'asar na ɗakko jakata na fito don tafiya islamiya. Anan na tadda baƙin da muka yi suma suna haramar tafiya, Abbah ya shigo har falo suna gaisawa da Inna Hanne. Na yi musu fatan sauka lafiya na fice don tafiya makaranta, a zaure naci karo da wani kyakykyawan matashin saurayi baƙi sosai dashi. Amma yana da kyawun fuska da suran jiki sosai,na wuce ina ayyanawa a zuciyata cewa tare suke da baƙin Abbah kenan. Bayan magriba mun kammala cin abincin dare tare da Abbah, wanda lokuta da yawa tare muke cin abincin dare dashi. Muna yi yana lallaɓani da yi min nasiha akan inyi haƙuri da rayuwa, da kuma duk halin da zan tsinci kaina a ciki. Ina matuƙar jin daɗin irin ƙauna da shaƙuwar dake tsakanina da Abbana, wanda hakan ne ke daƙile kaso mai yawa na jin zafin ƙiyayyar da Gwaggo ke mini, da kuma yadda sam babu shaƙuwa tsakanina dasu Yaya Kabeeru. Don ko sun zo gida tsakanina dasu gaisuwa ce kaɗai, baya ga haka basu taɓa jana a jikinsu sun nuna mini kulawa ko ƙauna ba.A matsayina na ƙanwarsu mace tilo da suke da ita, sam basu taɓa nuna min cewa suna maraba dani a matsayin ƙanwa garesu. Bayan mun gama cin abincin muka taɓa hira har aka kira sallar isha'i, Abbah Ya je sallar isha'i Ya dawo ne.Ya taramu ni da Gwaggo ya yi mana bayanin cewa ya samu baƙon ɗalibi da xai riƙa ɗaukar karatu a wajennsa, sai dai wannan ɗalibin yasha bambam da sauran ɗalibansa.Don shi wannan a matsayin ɗa yake a wajensa, sabida haka anan cikin gida za a riƙa zuba masa abinci sau uku a rana kamar yadda su Yaya Kabeeru zasu ci idan suna gari. Sannan yana da hurumin da zai iya shigowa ciki idan yana buƙatar wani abu ko don gaisawa da Gwaggo,Ya shaida mana cewa sam bai yi masa shamaki da hakan ba, matuƙar mu'amalar da zai yi a cikin gidan ba zai wuce tsakanin babban falo zuwa kicin ba. Muka yi shiru ni da Gwaggo muna sauraren jawabin Abbah, yayinda zuciyata ke hasaso mini cewa, ba kowa bane baƙon Abbah sai wannan black beauty ɗin matashin dana gani a zaure ɗazu. Gwaggo ta jinjina kai bayan ta gama jin jawabin Abbah, sannan ta buɗe baki ta ce, "Abbansu yanzu don kawai an kawo saurayi ɗan amininka shi ne har zaka bashi damar shigowa cikin gida ya yi mu'amala kamar yadda su Kabeeru zasu yi? Kana ƙoƙarin nuna cewa zaka daidaita matsayinsu kenan ko me?" Abbah ya dubi Gwaggo cikin nuna rashin jin daɗin maganar da tayi ya bata amsa kai tsaye da faɗin, "Hakane zan daidaita matsayinsu ne Hauwa, don inda kara ɗan da yake a matsayin ɗan aminina to nima yakamata na ɗaukesa matsayin ɗane.Don haka ki iya harshenki akan furta kalamai marasa kan gado akan Mahmuda, sannan zuwa da safe zan gabatar muku dashi..........✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Naj....AD# #Aysha Ɗansabo Lemu😘 [2/28, 2:19 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 4* _Free page_ Inna Mairo ta cigaba da cewa, "Washegari bayan mun gama karyawa da safe, Abbah ya gabatar mana da baƙonsa. Lokacin da baƙonsa ke gaida Gwaggo ido kawai ta zuba masa tana jifansa da wani mummunan kallo, wanda ni kaɗaine na kula da haka sabida shi da baƙonsa hankalinsu ba a kanta yake ba. Na gaida baƙon Abbah ya amsa da fara'a yana tambayata skull, na bashi amsa da cewa komi lafiya. Gwaggo ta fara barin falon zuciyarta na cika da jin haushin yadda ta kula baƙon Abbah ya shiga ransa farat ɗaya! Ni ma bayanta nabi don Abbah hira suka dasa sosai da baƙon nasa. Kwanaki biyu da zuwansa gidan na fahimci cewa Gwaggo bata ƙaunarsa, domin ko abinci aka gama aka zo zuba masa a kular da ta ware dominsa sai tayi ta mita tana faɗin Allah Ya yi wadaran ƴan karere. Sannu a hankali Mahmuda wanda Abbah yake kira da Malam Mahmuda ya fara jana a jiki, yana koya mini assignment idan an bani. Sannan mafi yawan lokuta shi Abbah ke sawa yana ɗaura min karatun littafan addini da nake ɗauka a wajensa.Hakan sai ya yi saurin haifar da sabo da shaƙuwa a tsakaninmu,musamman da ya kasance dama bani abokin hira, kuma bani da ƴar uwa ko ɗan uwa na jini da zasu zame mini abokan hira ko ɗebe kewa. Gwaggo bata sakar mini fuska, tsakanina da ita hantarace da sanyani aikin bauta.Baya ga haka ban isa ta zauna tayi hira dani ba, bare har taji damuwata ko sanin halin da nake ciki. Ko pad nake so idan ina period Abbah nake zuwa na faɗa mawa ya siya mini, sabida ban samu fuska a wajenta ba bare har na tunkareta da ire-iren waɗannan buƙatun nawa. Shiyasa da Malam Mahmuda ya fara nuna min kulawa, yana treating ɗina tamkar ƙanwarsa ta jini, sai nima nayi saurin sakin jiki dashi na ɗaukesa tamkar Yayana na jini. Lokutan da yake ɗaukar karatu a wajen Abbahna shi ne daga bayan sallar magriba zuwa isha'i ne, da anyi sallar isha'i shi kuma Babanki Malam Mahmuda sai ya karantar da almajiran Abbah. Haka suke yi kullum babu fashi, kuma sosai Abbah ke tsananin ƙaunar Malam Mahmuda a ransa sabida ya yaba da tarbiyarsa da nutsuwarsa. Wataninsa huɗu da zuwa garin kaduna, Abbah ya yi masa magana akan cigaban karatunsa,amma sai ya nuna baya ra'ayi yafi sha'awar business ga kuma sana'arsa ta ɗinki da yake matuƙar girmamawa. A lokacin Abbah ya san cewa ƙwararren tela ne shi, sai ya bashi umurnin zuwa gida giwa ya taho da kekunan ɗinkinsa biyu da ya mallaka.Abbah ya nema masa hayan ƙaramin shago, wanda zai aje kekunansa ya cigaba da sana'ar ɗinkinsa. Cikin sa a Babanki ya fara sana'ar ɗinki a garin kaduna, kafin wani lokaci ya zamana yana da tarin customers masu bashi ɗinki sabida ƙwarewarsa da cika alƙwari. Gefe guda yana cigaba da ɗaukar karatu a wajen Abbah, kuma yana cigaba da taimakon Abbah wajen karantar da almajiransa duk bayan sallar isha'i. Shi kuma Abbah ya ɗaura musu karatu da kansa bayan sallar asuba, haka suke yi har zuwa lokacin da Malam Mahmuda ya samu tsayin shekaru guda a gidan mu. Zuwa lokacin bazan iya misalta miki irin sabo da shaƙuwar da ya shiga tsakanina dashi ba, don ma shi yana matuƙar janye jiki da nuna takatsantsan a kaina.Musamman dana fara zama wata iriyar cikakkar budurwa,kyawuna ya sake bayyana kamar yadda duk wata baiwar ƙiran cikar halitta da Allah ya yi mini suka gama fallasa kansu.Gabaki ɗaya sai ya janye jikinsa daga gareni, baya son ko kaɗan ina raɓar inda yake sai idan Abbah na nan, ko kuma idan ya shigo cikin gida ɗaukar wani abu ko gaida Gwaggo sai mu gaisa. Idan ina da assignment sai dai in jira sai Abbah ya dawo mu baje a falonsa yana koya mini suna hira da Abbah, hakan da yake yi ya sake ƙara masa martaba a idanun Abbah. Ita kam Gwaggo zuwa lokacin Malam Mahmuda ya gama shaida irin tsanar da tayi masa, sabida hatta gaisuwarsa da take amsawa ta daina sabida jin zafin yadda ya yi kane-kane a zuciyar Abbah. Har ya kai kafin ya yi mata maganar su Yaya Kabeeru sau ɗaya,sai ya ambaci sunan Mahmuda sau goma. Sai ta fara cewa asiri ya yiwa Abbah don ya mallaki zuciyarsa, ta yadda zai cire soyayyar Ƴaƴansa a zuciyarsa. Waɗannan kalaman gaba da gaba Gwaggo ta tari mahaifinki Malam Mahmuda ta sanar masa, tun kuma daga ranar ya daina shiga cikin gida gaba ɗaya. Dama idan ba ruwan zafi ko wani abu yake so ba sam bai faye shiga ba, sai ya koma sanyani kai masa duk abinda yake da buƙata idan buƙatar hakan ya taso. Shi ma kuma ya hana in dinga shigar ɗakin nasa sai dai na aje masa abin da ya sanyani in kai masa daga bakin ƙofa, shi sai ya fito ya ɗauka. Duk yana yin hakan ne sabida gudun zargi, duba da yadda Gwaggo tayi mugun sanya mana idanu. Dukkanin ƙiyayyar da take gwada mini sai ta sake riɓanyashi, ta kuma haɗamu mu biyu dashi tana cusguna mana ta hanyar jifanmu da alkaba'i kala da kala. Ƴaƴanta su Yaya Kabeeru sam basa sakin ma Malam Mahmuda fuska,domin Gwaggo ta riga ta cusa musu ƙinsa ta hanyar sanar musu cewa basa gaban Abbah kamar yadda wannan ɗan almajirin maɗinkin ke gabansa. Yanayin yadda Abbah ke daidaitasu a komi yana kuma nuna musu cewa su ɗauki mahaifinki tamkar ƙani a garesu, sai hakan ya sanya suka gasgata maganar Gwaggo na cewa Malam Mahmuda ba ƙaramin shiga zuciyar Abbah ya yi ba, tunda har yake ƙoƙarin ganin ya cusa soyayyarsa a zukatansu. Hakan ya janyo suke jin kishinsa a zuciyarsu har ya kai basa ƙaunar suzo weekend su haɗu da shi a falon Abbah,bare har Abban ya tasa su da tarin nasihunsa yana kwaɗaitar dasu su haɗa kawunansu.Duk bayan sati biyu ko uku Malam Mahmuda ke haɗa shatara ta arxiƙi ya nufi garin giwa wajen ƙanin mahaifinsa Malam Lawal, ya kanyi kwanaki biyu ko uku sannan ya juyo kaduna. Sosai sana'arsa ta ɗinki da noma da ya fara gwada yi a gonar Abbah da ke cikin hayi ya bunƙasa, yana samun kuɗi sosai da gaske.Musamman da ya kasance Malam mai mutane ne kuma yana yawan tallata masa sana'arsa ta ɗinki, ta yadda yake samun ƙarin customers. Ina SS2 a secondary school wani cousine ɗin Gwaggo mai suna Fahad ya bijiro da zancen cewa yana sona, hankalina ya yi masifar tashi don na nafi kowa sanin Fahad bashi da kamun kai. Sabida akan kunnuwa na sha ji Gwaggo da ƴan uwanta idan sunzo suna zancensa. Yana da kuɗi domin matuƙin jirgin samane da ke ganiyan ƙuruciyarsa,don a shekaru ba zai wuce ashirin da biyar ba a lokacin. Gwaggo duk tabi ta gigice da wannan zance na Fahad don tana cikin irin matannan masu shegen kwaɗayi da son abin duniya.Ban taɓa sanin Gwaggo ta iya magana mai daɗi da nuna kulawa ba, sai da Fahad ya mato a kaina. Ta dinga sanyani a ɗaki tana min romon baka akan in amince da ɗan uwanta domin idan na aureshi ba ƙaramin hutawa zamuyi ni da ita ba. Ni dai bana iya ce mata komi domin tsoranta ya riga ya ginu a zuciyata, sannan ni sam bana sha'awar aure a wannan lokacin.Na fiso in zurfafa karatuna kamar yadda dukkanin ƙawayena ke da buri, amma abinda ban sani ba ni shine shi kansa Abbah bashi da burin barina nayi zurfin karatu a gabansa. Ban san hakan ba sai da Gwaggo ta tunkaresa da batun Fahad, sai ya sanya ta kirani don yaji ta bakina. Amma duk yadda yaso ince wani abu a gaban Gwaggo kasawa nayi, don ina tsananin tsoronta da kuma fargabar yadda zan sanar da Abbah cewa bana son Fahad ɗin. Gwaggo sai ta bamu waje tana cewa Abbah ya bini a hankali yaji ta bakina, a tunaninmu duka ni da Abbah ta bar falonsa baki ɗaya ta shige daga ciki.Ashe laɓe tayi tana sauraran dukkanin abinda muke tattaunawa da Abbah. Ban san hakan ba don dana sani ba zan taɓa iya buɗe baki in yiwa Abbah bayanin cewa bana son Fahad ne sabida bashi da kamun kai kamar yadda naji su Gwaggo na faɗi ba. Abbah ya kwantar min da hankali tare da sanar dani cewa bashi da burin nayi zurfin karatu a gabansa sai a ɗakin mijina, sabida haka idan har bana son Fahad inyi ƙoƙari kafin mu fara zana jarawar waec ya zama ina da tsayayye. Idan so samune nema in samu mijin da za a haɗa bikinmu ayi rana ɗaya dana Yaya Kabeer, wanda aka sanya masa ranar aure watanni biyu da suka wuce. Ƴar wani mai kuɗice ya samo a garin katsina daga zuwa ɗaura auren abokinsa ya haɗu da Yarinyar, Babanta mai kuɗine ɗan siyasa wanda ke riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi na garin katsina. An sanya ranar auren ne watanni biyar kacal, shi ma ba don iyayenta sun so hakan ba sai don Gwaggo da ta kafe ba za a sanya mata biki ba tare da an bata isasshen lokaci ta shiryawa bikin ba.Hankalina ya tashi da maganar Abbah, domin ni bani da wani saurayi don ban taɓa kula kowa ba, hasalima duk kyawun da nake dashi bani cikin irin masu farin jinin da za a ce duk inda suka shiga sai sun saurayi ba. Fahad shi ne na farko da ya fara tunkaroni da batun soyayya, kuma akai rashin sa a bai taɓa birgeni ba bare har naji cewa zan iya bashi zuciyata. Na fito daga falon Abbah bayan ya sallameni ina jin kaina na wani irin juya mini,na wuce zuwa ɗakina ba tare da na san cewa Gwaggo ta gama jin komi da muka tattauna da Abbah ba. Washegarin ranar ina cikin saka uniform sai gata kamar an jefota ta shigo mini ɗaki, kallo ɗaya nayi mata naji wani irin faɗuwar gaba da tsoro sun shigeni. Sabida gabaki ɗaya fuskarta a haɗe take babu ɗigon annuri.Ta samu gefen gado ta zauna tana cigaba da kiɗima zuciyata da mummunar kallon da take jifana dashi. Ko gaisuwata bata amsa ba ta fara buɗe mini wuta akan cewa ban isa na wulaƙantata nace ba zan aminta da jininta a matsayin miji ba, inda take shiga banan take fita ba tana zagina tana zagin uwar data kawo duniya.Daga ƙarshe ta bani umurnin cewa inje da kaina in sanar da Abbah cewa ina son Fahad, don Fahad ɗin ya matsa mata a kaina ya kuma ce yana so da zaran na kammala skull ne muyi aurene. Na rasa bakin magana sai kuka da nake yi tun fara balbalin faɗan da take mini.Ta fita ta barni cikin tashin hankali ina kuka mai yawa, domin bansan yadda zan ɓullowa lamarin ba. Daga ƙarshe dabara ta faɗon mini akan in samu mahaifinki in nemi shawaransa akan yadda zan ɓullowa lamarin Gwaggo har na kuɓuta daga tarkon da take son jefani ciki, na son in auri mutumin da tafi kowa sanin cewa bana gari bane. Bayan na dawo school sai duk na ƙosa su Abbah da Yaya Mahmuda su dawo kamar yadda nake kiran mahaifinki a lokacin, sabida har cikin zuciyata matsayin Yayana na jini na ɗaukesa. Don yadda nake jinsa a zuciyata ma bana jin su Yaya Kabeeru haka, sabida sam su basu taɓa nuna mini ƙauna ba bare su nuna kulawarsu a kaina ba. Shi kuwa har kuɗi yake kashe mini yana mini siyayyan kayan kwaɗayi dana ƙyale-ƙyalen mata kala kala. Bai jin ciwon kashe mini ko nawane matuƙar ya yi niyyar hakan. Dana samesa da batun shi ya bani shawaran in bida Gwaggo a yadda take so, in yaso shi Abbah sai inyi magana dashi mu haɗa baki ya nunawa Gwaggo cewa shi da kansa ya yi bincike ya gano cewa Fahad ba mutumin kirki bane,don haka ba zai bashi aurena ba koda ni ɗin ina ƙaunarsa. Wannan shawara ta Malam Mahmuda ya kwantar mini da hankali tare da jinjina hikimar da yake da ita, don koda na sanar da Abbah ga buƙatata shi ma ya yi mamaki har saida ya tuhumeni wanda ya iya shirya mini wannan dabarar. Na sanar dashi cewa Yaya Mahmuda ne, sai naga ya yi dariya mai yawa kafin ya sallameni ya ce in tashi in tafi zai yi magana da Gwaggon. Na tafi ɗakina zuciyata wasai tamkar an cire mini wani dutsen da ya danne zuciyata, domin kwana biyu da damuwar maganar Gwaggo nake kwana na tashi.Na dinga kasa kunni ko zan ji Gwaggo ta sake tarata da maganar Fahad amma sai naji shiru, sai dai ta ninka tsanar da take mini a baya don ko gaisuwata daina amsawa tayi. Abu kaɗan zanyi na kuskure zata kifeni da mari ta shiga zagina tana kirana dangin mayu masu baƙin hali. Abin na mini ciwo amma haka nake dannewa, sai dai in shiga ɗaki inyi kukana na share hawayena. Cikin kwanaki ƙalilan duk na rame sabida damuwa da shiga ƙuncin yadda Gwaggo ta uzzura mini, sam bani da sukuni inba ina makaranta bane. Amma da zaran na dawo gida bani da sauran kwanciyar hankali. Abbah da kansa ya fahimci ina cikin damuwa, kuma ya san ba zai wuce dai akan zancen Fahad bane da ya kashe maganar. Don ya sanar da Gwaggo ba zai taɓa bai wa ɗan giya auren ƴarsa ba koda ace zan mutu da soyayyarsa ne,sannan ya yi mata kyakykyawar gargaɗin ya daina zuwar masa gida ma baki ɗaya.Don da gaske Abbah ya yi bincike a kansa, ya kuma gano cewa ɗan giyane tantiri na gaske. Ya kirani Ya yi mini faɗa da nasiha akan muhimmancin maida lamura zuwa ga Allah, sannan ya nusar dani cewa a komi na rayuwa in dogora da cewa komi NUFIN ALLAH ne bana mutum ba. Kome kaga ya faru da bawa NUFIN ALLAH ne idan ya NUFA abu Ya kasancewa,kasancewa yake ko mutum naso ko baya so. Haka idan bai Yi NUFIN abu ya kasance ba ko duniya sun taru basu isa sawa ko hana wannan abun kasancewa ba.Don haka in sanya haƙuri da dangana In Sha Allah! Fahad ba zai zamo mijin aurena ba. Anan ne kuma ya sanar dani ya yanke shawaran zai zaɓa mini mijin da yake ganin ya dace dani, don yana so ya aurar dani don kawo ƙarshen ƙiyayyar da Gwaggo ke mini da kuma kawo ƙarshen wannan dambarwa na magana ɗan uwanta, domin ta gane cewa da gaske yake ba zai taɓa bashi aurena ba. Hankalina maimakon ya kwanta sai ma ya sake tashi Najma, domin na sanya zullumi a raina na waye zaɓin da Abbah zai mini alhali na sanar dashi bana ra'ayin aure karatu nake so. Haka nan dai na dinga ɓoye damuwata amma a tsaye duk na rame duk da cewa ba wani ƙibace dani ba dama, amma dai nayi rama don ada ina da murjajjen jikin da ko ƙashin wuyana ba a gani.Duk wanda ya ganni ya san ina da damuwa dannewa kawai nake yi, amma Gwaggo bata taɓa zama dani ta tambayeni miye damuwata ba. Burinta bai wuce in bijerewa Abbah in auri ɗan uwanta don biyan buƙatan kanta ba, ni kuma banyi yadda take so ba shiyasa ta ninka tsanata ni da mahaifinki don ta fito fili ta ce shi yake sake hure mini kunni. Bayan wani lokaci kaɗan Abbah ya gabatar mini da zaɓinsa....... Inna Mairo ta ɗan dakata kaɗan tana ɗaura manyan idanunta akan Najma,wacce duk ta ƙagara taji ƙarshen tarihin rayuwar Inna da mahaifinta. Ta dubi Inna cike da jin wani irin tausayinta ta ce, "Waye zaɓin da akai miki Inna?" Inna Mairo ta jinjina kai tana danne dukkanin raunin da ya bijiro mata na tunawa da gwarzon mijinta Malam Mahmuda. Ta dubi Najma tana mai cigaba da faɗin, "Mahaifinki shi ne zaɓin da Abbah ya yi mini Najma, wanda da fari na so na bijire domin ni a matsayin Yayana na jini na ɗaukesa. Amma daga baya sai naji zuciyata ta aminta dashi, muka fara fahimtar juna ni da shi. A hankali kuma soyayyarsa ta fara shigata wacce jigonta ƙaunace matuƙa da gaske, kamar yadda na fahimci shi ma ya jima yana ƙaunata da sona a cikin zuciyarsa. bai samu damar bayyanawa bane sai da Abbah ya furta masa ƙudirinsa na son ya haɗamu aure, anan ne ya amsa tayin Abbah cikin matuƙar farin cikin da Abbah bai taɓa gani akan fuskarsa ba. Malam Lawal takanas ya yo yazo ya yiwa Abbah godia mai tarin yawa, domin lamarin ya faranta ransa duk da cewa ba a kai ga sanya lokaci ba.Don Yaya Mahmuda ya ce sai ya kammala gininsa na zamani da ya ɗakko yi a garin giwa,sannan sai ayi auren hakan zaifi masa daɗi da kwanciyar hankali. Gwaggo a lokacin da hukuncin Abbah yaje kunnuwarta na cewa Malam Mahmuda ne zaɓinsa,kuma nima na amince da shi a matsayin wanda zan aura, sai taji tamkar ta haɗamu ta kashe ko zata huta da ƙiyayyarmu a cikin zuciyarta. Tun daga ranar ta ɗaura ɗammaran sake cusguna mana,daga ni har mahaifinki bamu sake jin daɗin zama da Gwaggo ba.Tsakaninmu da ita zagi da habaici ne kala-kala. Ta dinga jifan mu da kalamai marasa daɗi tana mugun fata,tare da kushe mahaifinki ba dare ba rana.Kullum sai ta tsinesa ta ce Allah ya yi wadaran zaɓin Abbah, Ya rasa wanda zai zaɓa mini sai baƙin munafukin almajirinsa wanda bashi da komi sai sana'ar ɗinki. Ta raina mahaifinki ta kuma raina arziƙinsa, don gani take duk abinda ya mallaka bai wuce ya zama mai wanki da gugan Fahad ba.Ni kuma abin na mini ciwo matuƙa,domin da gaske zuciyata har cikin zuciyata nake jin zafin yadda Gwaggo ke tsinan Malam Mahmuda. Ana cikin maganar sanya mana rana ne bikin Yaya Kabeeru da zaɓinsa mai suna Zainab ya zo, aka shiga hidima baji ba gani.Kan Gwaggo ya fara ɗaukar caji, hakan ya janyo ni da mahaifinki muka samu lafiya daga tujararta. Shiri ake wa bikin sosai domin ƴar masu dashi ne zai ɗakko, kuma shi ma ya tara kuɗi sosai tunda albashinsu mai tsokane. Tuni ya kama hayar gida mai kyau a cikin garin kaduna, wata unguwa da ake cewa Malali. Bikin na saura kwana biyar gidanmu ya fara ɗaukar baƙi, mutananan Dukku dangin Abbah tsiraru da suka rage duk sun sauka ana ta hidima. Haka ƴan uwan Gwaggo na kusa da nesa duk sun fara hallara, sai shiri akeyi na aurar da ɗan gaban goshin Gwaggo.Domin tana tsananin son Yaya Kabeeru sabida yana kyautata mata da bata kuɗi sosai. Sannan yana mata biyayya baya tsallake maganarta, duk abinda ta zana masa shi yake yi saɓanin Yaya Ali dake da zuciya da saurin hasala. Anyi biki lafiya an kawo Amarya daga katsinan Dikko.Mun yi kallon arziƙi a ɗakinta domin an kashe mata dukiya matuƙa da gaske.Taro ya watse cikin aminci sai kuma jiran namu lokacin wanda aka sanya rana watanni takwas masu zuwa.Ranar ɗaura auren Yaya Kabeeru aka bi ƴan uwa da minti da goron sanya rana. Aka dinga taya ni murna yayinda wasu dangin Gwaggo da suka san da zancen Fahad suka tasani da tsina da haibici kala-kala.Ni dai hakan bai dameni ba, don ji nake yi duk ma na ƙosa ayi auren na bar wa Gwaggo gidan kona huta da wannan ƙiyayya nata dana danginta.......✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma..AD# #Aysha Ɗansabo lemu🥰 [2/28, 2:30 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 5* _Free page_ Na cigaba da zuwa school ɗina bayan baƙi ƴan biki sun kama gabansu, muka maida hankali wajen shirya-shiryen jarabawar waec da zamu fara bada jimawa ba. Malam Mahmuda sai ya maida hankalinsa kan gininsa da yake yi a garin giwa, domin ya sanar da Abbah cewa yafi sha'awar ya kai Iyalinsa mahaifarsa ya zauna kamar yadda shi ma Malam Lawal yake da buƙata. Sabida bashi da ɗa shi kaɗai yake kallo a matsayin jininsa, don haka baya buƙatar ya aje Iyalinsa a bariki yafi sha'awar ya kawota gida in yaso sai ya dinga zuwa yana komawa kaduna wajen sana'arsa. Abbah bai yi musu ba bai kuma ji komi don za a ɗaukeni daga birni kamar kaduna a kawoni ƙauyen giwa ba.Ni ma da yake ƙauna da soyayyarsa sun rufe idanuna, ban taɓa jin cewa wai ci baya bane don na dawo ƙauye da zama na baro birni. Gwaggo na jin zancen cewa a ƙauye za a ajeni ta sake samun makamin yaƙata da kalamai marasa daɗi,tana mini gorin kaicona da zan ƙare a ƙauye,dama ta san tunda na liƙewa wannan baƙin almajirin matsiyacin Yaron, to lashakka sai ya gurɓa rayuwata domin a kyawuna da zubin halittar da Allah Ya yi mini ban dace da lusarin ɗan ƙauye kamar mahaifinki ba. Ranar da tayi mini wannan cin mutunci ɗaki na shiga nayi kuka tamkar ba zan daina ba, nayi kuka har dana rashin Iya da nayi don da tana raye tabbas ba zan fuskanci irin wannan ƙiyayyar da cin mutuncin da Gwaggo ke mini ba. Malam Mahmuda ya nuna mini zanen gininsa da yake har ya yi nisa an kusa yin rafta, gini mai kyau da tsari irin zamani yake yi.Babu wanda zai ce a ƙauye ne idan aka kammala shi,hakan dana gani sai hankalina ya sake kwanciya tunda naga cewa ba a mummunan waje zai aje ni ba bare burin Gwaggo ya cika na son ganin rayuwata ta tagayyara idan na auresa. Mun kammala zana jarawar waec ɗinmu a lokacin bikinmu saura watanni huɗu, zuwa lokacin Malam Mahmuda ya kusa kammala gininsa. Don har an rufa kwano anyi filasta da komi, saka tiles da sauran finishing ne kawai ba a ƙare ba,hatta ƙofofi da windows duk an sanya.Baya zama sam a kaduna yanzu sosai, kullum yana hanyar giwa don shirye-shirye. Yara ya zuba a shagon ɗinkinsa suna aiki kuɗi na taruwa, sai dai shi ya leƙo ya yi wasu ayyukan na manyan mutane da ke bashi ɗinki ya juya garin giwa. Ni kaina sai ya kasance munfi yin waya don baya ma son zuwa gidanmu sabida habaicin da Gwaggo bata gajiya da sakin mana, tunda a falon Abbah muke zama kuma sai ta san yadda aka yi ta shigo idan muna tare ta yada habaicinta ta fita. A haka lokaci ya ja biki ya gabato ya rage saura sati biyu, tun kuma ana saura sati uku jama'ar giwa suka kawo kayan lefe na gani na faɗa. Sabida Malam Mahmuda da kansa ya haɗa kayansa a nan garin kaduna, shi ya samu wata wayayyar mace cikin masu kawo masa ɗinkunan yaransu, ya roƙeta akan ta taya shi haɗa lefe aurensa ya tashi. Ta kuwa tsaya tsakani da Allah ta dinga zaɓar masa kaya masu kyau da nagarta.Shiyasa kayan suka zama a tsare daidai dana mai rufin asiri. Duk yadda Gwaggo taso kushe kayan bai samu ba, domin ƴan uwanta kansu da suka ga kayan sunyi mamaki sabida sun raina arziƙin Malam Mahmuda. Abbah ya kammala siya mini komi na kayan ɗaki, babu abinda bai siya mini ba tun daga kan kayan kicin har zuwa gadaje da kujeru. Yaya Kabeeru da Yaya Ali sun yi bajinta suma domin a wajensu Abbah ya amsa dukkanin kuɗaɗen da ya siya mini kayan, sabida ya ce musu sune zasu aurar dani bashi ba tunda Allah yasa sun kawo ƙarfi kuma suna da babban aikin da suka tara rufin asiri. Gwaggo sam bata san sune suka bada kuɗin da Abbah ya ragargaza mini siyayyar kaya na ƴaƴan gata ba, don da ta sani baƙin cikin da zata shiga sai yafi wanda tayi, sabida a hakan ma bata sani ba na sha tsina da zagi tana ce mini na zame mata baƙin ciki a rayuwa. Har taba cewa watakila uwata mayyace, kafin ta rasu sai da ta lashe kurwar Abbah ta yadda ko bata a raye abinda ta bari kawai zai dinga kallo da mutunci. Ni dai tun lamarinta na sanya ni kuka har na dake, don na gane cewa ƙiyayyata a zuciyar Gwaggo na musammance,duk kuma abinda zan mata na kyautatawa ba zai goge wannan ƙiyayyar ba. Wata Innar Abbah mai suna Inna Larai ita ce ta zo daga Dukku ta fara gyareni, don Gwaggo cewa tayi babu ruwanta da hidimar aurena kada ma a sanyata a komi na hidimar bikin don ba za tai ba. Tunda har naƙi ɗan uwanta na tozartata, to itama tabbas ba za ta taɓa shiga sabgar aurena da Yaron da take jin tsanarsa har cikin zuciyarta ba. Tunda tayi waɗannan kalaman a gaban Abbah ya ce kar a sake sanyata a harkar komi, a zuba mata ido tayi duk iya rashin mutuncin da taga dama aure ne dai babu fashi. Gwaggo sai ta sake tunzura ta kuma sake janye jikinta, ta zubawa dangin Abbah da wasu daga cikin na Innata da suka zo daga Dukku ido.Suka dinga hidimarsu cikin kwanciyar hankali domin Abbah ya sakar musu bakin aljihu sosai, don ya sake ƙuntata zuciyar Gwaggo. Ranar da aka tafi jere aka dawo kwana aka yi ana yaba kyawun gidana da irin dukiyar da Abbah ya zuba mini. Masu babbar waya a cikinsu har vedio suka yo, aka kuma samu wacce ta kunnawa Gwaggo ta gani. Aiko sai zuciyarta ta sake tunzura, ta dinga cewa wannan gini ba dai Malam Mahmuda ne ya yi ba,Abbah ne ya kwashe kuɗinsa ya bashi. Kuma kayan ɗakin ma tasan sai da aka matse ƴaƴanta aka amshe musu ƴan kuɗaɗensu, don kawai a tozartata a nuna mata cewa bare yafi ƴaƴanta matsayi. Babu wanda ya biye mata bare ayi tashin hankali da ita, aka barta tayi mitarta har ta gaji bata samu abokin tayi ba. Abbah bata ga fuska a wajensa ba, domin ya iya da ita baya sauraren duk wani shirmenta.Hakan ya sanya ta sake jin tsanar aurena da Malam Mahmuda ya sake ninkuwa a zuciyarta. Matar Yaya Kabeeru zuwa lokacin har ta samu ciki wata biyu, mace ce mai kirki da fara'a sam bata da damuwa domin ko irin rawar kai irin ƴaƴan masu kuɗi ita bata dashi. Duk yadda take mini fara'a na kasa sakin jiki da ita sabida Gwaggo, na sani ba za ta taɓa bari alaƙar aminci ya shiga tsakanina da matar Yaya Kabeerun ba sabida ƙiyayyarta a gareni. Don haka sam ban yaudari kaina ince zan dinga cusa kaina a wajent ba, tsakanina da ita gaisuwar mutunci ce sosai muke yi.Koda bikina ya gabato kuma ta kawo mini kayan decor na ɗaki masu tsada da kyawu, ta kuma sanya Yaya Kabeeru ya bani kuɗi masu yawa har nayi mamakin hakan. An ɗaura aure lafiya a babban masallacin da ke hayin rigasa, bayan ɗaure auren bada jimawa bane kuma aka ɗaukeni daga kaduna a kawo garin giwa, bayan na sha tarin nasihu da addu'o'in fatan alkhairy daga Abbah. Gwaggo koda wasa bata sanyawa aurena albarka ba bare tayi mana fatan alkhairy, koda aka kaini ɗakinta muyi sallama cewa kawai tayi in sauka lafiya tana mini kaicon rayuwar ƙauyen dana zaɓawa kaina. Nayi kuka tamkar zan haɗiyi zuciyata sabida kalaman Gwaggo sun raunata zuciyata matuƙa, na dinga ayyanawa a zuciyata wani irin ƙiyayyace Gwaggo ke wa Innata da har ƙiyayyar yake bibiyata? A haka muka iso garin giwa kaina na matuƙar ciwo sabida kukan dana sha. Mun samu kyakykyawar tarba daga ahalin Malam Mahmuda,akai ta shigowa ɗakin Inna Hanne inda aka saukeni don ganin Amarya. A gidan na kwana aka yi buɗan kai na al'adah kafin ƴan uwana da suka kawoni suyi haramar juyawa kaduna.Dama kuma mutum huɗu ne suka rakoni sai ƙawata Hafsa wacce da ita kawai nafi shaƙuwa a school. Da yamma sakaliya Inna Hanne da matar Hakimin giwa mai suna Gwaggo Salamatu suka yi mini rakiya zuwa ɗakina. Kowa ya ga gidana sai ya san cewa daga birni aka ɗakkoni, birnin ma kuma gidan rufin asiri da wadata domin an kashe mini dukiya a ɗaki sai dai maƙiyi ya kushe. Duka dangina da suka rakoni kafin su tafi dama sai da suka je ɗakina suka ga irin kyawun da ya yi, kowa ya tafi yana sambarka domin faɗi suke babu mai cewa a ƙauye nake idan yana cikin gidana don komi yaji sai sambarka. Inna Hanne da matar Hakimi sun tafi sun barni tare da wata budurwa mai suna Kausar, wacce Inna Hanne ke riƙonta, ita zata tayani zama kafin zuwa dare ango ya shigo ɗakinsa. Na dinga kuka ina sharan hawaye, kewar Abbah na rufar mini tamkar in rufe ido in ganni a kaduna. Misalin ƙarfe tara na dare su Haruna ɗan gidan Hakimi da sauran abokanansa suka rakosa, bayan sun sayi baki suka yi mana addu'o'in fatan alkhairy tare aje min ledojin kaji da kuɗi suka tafi abinsu. Malam Ya yiwa Kausar rakiya har zuwa gidan Inna Hanne, sannan ya dawo ya kulle gidan ya shigo cikin zumuɗi..... Inna Mairo ta sake dakatawa tana haɗiye wani abu mai nauyi da ya danne zuciyarta, sakamakon tuno ranar da ba za ta taɓa mantawa dashi a tarihin rayuwarta ba. Ranar da ya zame mata mabuɗin buɗe sabon shafin rayuwa mai cike da jin daɗi da tsantsar ƙauna da kulawar da ta samu daga Malam Mahmuda. Najma ta dubi Inna Mairo tana son jin ƙarishen labarin cike da zaƙuwa, hakan yasa Inna Mairo cigaba da faɗin, "Rayuwar aurena a gidan mahaifinki rayuwace da bazan taɓa mantawa dashi ba, domin na samu ƙauna da tarairaya daga garesa. Malam Mahmuda ya riƙeni da amana ya kuma nuna mini soyayya da kulawa.Ya gatantani shi da ahalinsa su Malam da Inna Hanne, haka ma Gwaggo Salamatu ba ƙaramin soyayya da ƙauna ta nuna mini ba.Suka zame mini tamkar ƴan uwa na jini.Cikin wata ɗaya da yin aurenmu na yi wani irin kyawu da cikar ɗaki, duk wanda ya dubeni yasan cewa ina cikin kwanciyar hankali da samun soyayyar miji. Bani da wata damuwa kullum sai na kira Abbah mun jima muna waya, haka shi ma yana kirana da kansa musha hira, daga ƙarshe ya yi ta mini nasiha akan muhimmancin haƙuri da biyayya wa miji a zamantakewar aure.Koda yaushe bana rasa Yara ƴan tayin hira masu shigo mini, hakama matar Haruna aminin Malam Mahmuda mai suna Karima. Koda yaushe tana zuwa mini hira mu jima tare,sannan kusan duk dare mu kan je gidan Malam muyi hiranmu sai wajen tara na dare mu dawo gidanmu. Malam Mahmuda tuni ya koma yana zuwa kaduna wajen sana'ar ɗinkinsa da sai da yadikan maza da ya fara yi, yana kuma samun ciniki da alkhairy mai yawa. yana dawowa garin giwa duk bayan kwanaki uku zuwa huɗu, ya yi mini kwana uku da ya juya kaduna. Kausar da ke matsayin ƴar ƙanwar Inna Hanne ita ke zuwa tana tayani kwana idan ya tafi, tana da hankali da kirki matuƙa. Duk aikin shara da mopping ita ke yi mini.Da zaran ta kammala take komawa wajen Inna Hanne tunda a hannunta take,sabida ita bata haihu ba shiyasa ta ɗakko riƙon Kausar ɗin.Anyi bikinmu da watanni biyu matar Yaya Kabeeru ta haihu, cike da zumuɗi na shirya muka tafi kaduna da Malam tunda dama an faɗi haihuwar daidai yana garin giwa.Da murnata da komi na shiga gida ina ɗokin son ganin Gwaggo da Abbah, amma tun a irin tarban dana samu daga Gwaggo cikin haɗe fuska da tsare gida jikina ya yi mugun sanyi. A tunanina zuwa yanzu Gwaggo ta gane cewa komi NUFIN ALLAH ne, Allah ne bai nufa Fahad shi ne mijina ba. Na gaisheta ta amsa a wulaƙance tana faman bina da kallon ƙirulla, zuciyarta cike da jin haushin yadda ta ga nayi shar abina. Bata ga makusa a tattare dani ba,domin komin hasadar mutum idan ya dubeni ya san nayi kyawu, irin kyawun da ana gani ansan mutum na cikin kwanciyar hankali da hutu ne. Koda Malam Mahmuda ya shigo gaidata bata amsa gaisuwarsa ba, sai ma tsaki da ta ja ta bar mana falon tana yada mana da ƙananun habaici. Abin ya yi matuƙar taɓa zuciyata amma na danne ban nuna a gaban Malam Mahmuda ba, shi ne ma ya dinga bani baki da nuna mini cewa inyi haƙuri watarana sai labari. Lokaci zai zo da Gwaggo zata yi nadamar duk irin ƙiyayyar da take gwada mana, domin bamu da wani abu da muka aikata mata na rashin biyayya. Mun samu tarba ta mutunci a gidan Yaya Kabeeru daga wajen Anty Zee da ƴan uwanta da suka zo barka. Ta dinga nuna masu ni tana sanar dasu cewa ni ɗin ƙanwar Kabeer ne, suka dinga yaba kyawuna wasu suce muna kama da shi yayinda wasu ke cewa nafi shi kyau nesa ba kusa ba. Sosai na ji daɗin karamcin da muka samu, na sake jin ƙaunarta ya shiga zuciyata. Bamu kwana ba a ranar muka juyo garin giwa, bayan mun bi Abbah har shago mun yi masa barka. Koda ranar suna ya zagayo ban je ba sabida nasan babu abinda zan tsinto sai danasani, don na san Gwaggo cin mutuncina zasu taru suyi ita da ahalinta. Malam ne ya yi siyayyar kayan suna ya haɗa da kuɗi ya kai wa Gwaggo, kayan yace in jini kuɗin kuma nasa. Amma Gwaggo sai ta rufe ido ta ce ba zata amsa komi ba don ba muyi arziƙin da zamu iya yi mata alkhairy ta amsa ba. Wannan abu ya sosa zuciyar Malam matuƙa da gaske, maimakon ya dawo da kayan gareni sai ya nufi gidan Yaya Kabeeru dashi.Ya sanya Mai gadi gadi ya yi masa kiran mai jegon ya bata kayan da kuɗin. Anty Zee ta amsa da murna tana godia, hakan sai ya faranta ran Malam ya wanke masa ɓacin ran da Gwaggo ta kimsa masa. Lokacin da yake bani labarin cin mutuncin da Gwaggo tayi masa, kuka na dinga yi ina sake jin tsoron irin ƙiyayyar da take gwada mana na sake ruɗa zuciyata. Ya dinga bani baki har sai da ya yi nadamar sanar dani abinda ya faru, sabida yadda ya ga na tada hankalina matuƙa. Ban sake tunanin in sake binsa kaduna ba tunda ko na je ba tarban arziƙi zan samu daga Gwaggo ba, sai kawai na rungumi su Inna Hanne da su Karima matar Haruna suka zame mini abokanan arziƙi masu ɗebe mini kewar rashin ƴan uwa na jiki da bani dashi. Abbah ya turo mini lambobin su Yaya Kabeeru ya ce lallai in dinga kiransu lokaci zuwa lokaci ina sadar da zumunci dasu,kada na yadda na ce zan riƙe ƙiyayyar da Gwaggo ke mini a zuciyata har na kasa yin zumumci da ƴan uwana. Kamar wasa watanni suka miƙa har akai ga shakera da yin aurenmu.Zuwa lokacin ne kuma bikin Yaya Aliyu ya gabato.A lokacin kuma ina tsaka da laulayin ciki mai wahala, hakan yasa ban samu zuwa ba sai Malam ne ya je ɗaura aure har Jos. Ya dawo yana bani labarin irin shagalin da aka yi, domin Yaya Ali akwai son ya ga Ya yi abinda zai birge mutane. Kano aka kai Amarya mai suna Safiyyah, don ya ce ba zai zauna a kaduna ba,zai dai dinga zuwa gaida su Gwaggo ya koma.A waya na kirashi na yi masa fatan alkhairy ya yi mini godia, bayan hakan na kira gwaggo ita ma nayi mata Allah sanya alkhairy tare da sanar da ita uzurina na rashin zuwa bikin da ban samu yi ba. Buɗan bakinta sai cewa tayi ai garama da banzo ba,tunda ko dani ko bani babu abinda za a fasa.Naji ciwon wannan maganar ƙwarai da gaske, don har kuka nayi ina jin tausayin kaina na sake kamani. Ko Malam ban faɗi masa yadda muka yi ba, nayi shiru da bakina tare da haɗiye baƙin cikina. Na cigaba da rainon cikin jikina cikin nuna juriya. Malam ba ƙaramin kula dani da tattalina yake yi ba, duk abinda nake so shi yake mini. Babu abinda na nema na rasa, kayan daɗi kuwa ko wata ƴar birnin sai mai auren mai hali kuma mai zuciya zata sameshi. Na sake fari da cika bayan laulayin ya tsaya mini, sai dai bana iya girki don sam bana son ƙamshin abincin dana girka. Inna Hanne ita ke zubo mini abinci tare da dafo mini abubuwan marmari da mai ciki bata rabo da son cinsa.Idan Malam zai dawo ita ke masa girki na musamman,a haka cikina ya kai watanni bakwai.Na samu sauƙin lamura da yawa,tunda har ina iya girki inci.Da haihuwa ya gabato ranar wata laraba na haifo ɗana namiji kyakykyawa babu inda ya baro kamannina, sai dai kwanansa biyu ya koma wajen Mahaliccinsa. Har kuka sai da nayi domin Yaron ya shiga raina sosai, haka ma Malam ya nuna alhininsa mai yawa. Daga ƙarshe ya dinga rarrashina da yi mini nasiha akan inyi haƙuri Allah zai bani wani rabon. Gwaggo Salamatu matar Hakimi ita ce ta kula dani tamkar mahaifiyata, sabida Gwaggo ta shafewa idonta toka ta ce ba zata taɓa zuwa ƙauye ta kula dani ba. Abbah ya ji zafinta matuƙa akan yadda take nuna masa cewa ƙiyayyar da take mini sake gaba yake yi ma,a maimaikon ya ragu.Amma duk yadda ya nuna mata ɓacin ransa hakan bai sanya ta sakko ta amince ta zo ta kula dani ba. Barka ma bata zo ba sai da akai wajen sati biyu da haihuwar,sannan Abbah ya tasota suka zo suka duba lafiyata. Sun kusa yini a garin giwa, sun samu tarba na alfarma daga gidan Malam Lawal da gidan Hakimi. Bayan kwana biyar da zuwansu Abbah ya sake taso ƙeyar Yaya Kabeeru da Yaya Ali suka zo garin giwa, karon farko kuma da ƙafafunsu ya tako inda nake. Dukkaninsu sun sake zama magidanta waɗanda hutu da jin daɗi ya fara zama musu, musamman Yaya Kabeeru da aka ce samunsa na sake bunƙasa don baya ga aikinsa yana taɓa harkar business sosai. Sun yi mini alkhairy sun bani kuɗi mai yawa suka ce na siyi abinda nake so.Na amsa nayi godia ina mai jin tsananin farin ciki, ina ji tamkar karsu tafi sabida yadda Abbah ya sanyamu a tsakiya muna hira cikin raha da nishaɗi. Na rakasu har wajen mota da zasu tafi ina hawayen da ban san kona minene ba, Abbah ya dinga rarrashina suka shiga mota suka tafi ina ɗaga musu hannu. Bayan na kammala wanka da sati biyu na haɗa kaya na Malam ya ɗaukeni sai kaduna.Kamar yadda Gwaggo ta saba tarbata babu raha bare murnar ganina haka ta tarbeni,hakan yasa jikina ya yi sanyi, naji cewa ba zan iya yin kwanakin da nayi niyya ba.Kwanana uku kacal nayi na samu Abbah nayi masa sallama, Malam yazo muka koma gida giwa cikin sabuwar motarsa 206 da ya siya.Don zuwa lokacin sosai shi ma samunsa ke bunƙasa, ga noma da yake yi mai yawa yana samun alkhairi. Tun daga wannan haihuwar da nayi ban sake samun ciki ba sai dana share shekaru biyar, na sake samun wani cikin amma watanninsa biyu nayi ɓarinsa. A ranar da nayi ɓarin cikin dare Allah ya ɗauki rayuwar Hakimi Alhaji Musa giwa. Mutuwar ta gigita dukkanin jama'ar giwa,domin kowa ya shaidesa mutumin kirki ne mai son jama'arsa. Bayan an share zaman makoki aka naɗa aminin mahaifinki Haruna a matsayin sabon Hakimi. Na tausayawa Gwaggo Salamatu, domin tayi rashin miji mai ƙaunarta, wanda suka rayu tsayin shekaru ba tare da ya yi mata kishiya ba har ya kwanta dama. Rasuwar Hakimi da watanni uku Abbah shi ma ya kwanta jinya, cutar hanta ta kamasa wanda ba a taɓa sanin yana da ita ba sai da cutar taci ƙarfinsa. Hankalinmu ya tashi matuƙa musamman ni da tsoron karna rasa shi ya shigeni.Da kukana muka isa kaduna muma dangana da asibitin kuɗi mai kyau da aka kwantar dashi.Muna shiga naga jikin da sauƙi sai sanya hankalina ya kwanta, amma da ya buɗe yana mini magana sai hankalina ya kuma tashi. Sabida dukkanin kalamansa sun yi kama da wasiyyace a fakaice, ya dinga mini nasiha akan muhimmancin zumunta da sadarda dashi a tsakanin ƴan uwa da makusanta. Yana mai nusar dani cewa ko bayan bashi a raye, karna yarda na yanke zumunta da ƴan uwana.In cigaba da bibiyarsu a matsayina na ƙaramarsu, karna taɓa damuwa da ƙiayyar da Gwaggo ke nuna mini. Na dinga kuka ina sanar dashi zan bi dukkanin nasihunsa amma ya daina ambaton ko bayan bashi, yana raye zan yi dukkanin abinda yake mini nasiha da aikatawa. A haka muka kamo hanyar komawa giwa ina kuka sosai Malam na rarrashina da bani baki. A she bayan barowarmu su Yaya Kabeeru na zuwa ya tasa su a gaba yana musu nasu nasihan akan su riƙe zumunci, su kuma riƙeni da amana, su maye mini gurbinsa domin bani da wani gata da ya wuce su da mijina. Hatta Gwaggo ya yi mata nasiha mai shiga jiki, ya kuma sanar da ita cewa ko bayan ransa bai amince ta raba zumuncin da ke tsakanina da ƴan uwana ba. Tun dana dawo garin giwa hankalina ya gaza kwanciya, sai in kira Abbah sau uku ina jin lafiyarsa. Duk sanda zan kira zan ji muryarsa garas kamar mai lafiya, sai hakan ya fara kwantar da hankalina ina jin daɗin cewa yana samun lafiya. Bayan kwana uku da zuwanmu muka sake komawa dubashi har dasu Inna da amininsa Malam Lawal.Mun ji daɗin ganin yadda ya samu sauƙi sosai, har suka dinga hira da amininsa cikin raha. Bamu kwana ba a ranar muka juya, a kuma ranar aka bashi sallama daga asibiti suka koma gida. Kwanansa biyu a gida ya rasu, rasuwar da ya gigita duniyata ya jefa rayuwata cikin ƙunci mai yawa. Wanda ba don na samu gwarzon miji mai ƙaunata da dukkanin zuciyarsa kamar mahaifinki ba,da tabbas sai zuciyata ta kamu da ciwo tun a wancan lokacin. Shi ya tsaya tsayin daka wajen ganin na rungumi ƙaddara na kuma fauwalawa Allah komi.Ya dinga yi mini rubutu ina sha don samun nutsuwar zuciya da dangana.A haka rayuwa ya dinga turawa har Abbah ya kwashi watanni da rasuwa, aka raba mana gadonsa aka damƙa komi na kasona a hannun mijina kamar yadda na buƙata. Sai da tafiya ta fara nisa na sake gane cewa tabbas na zama cikakkiyar marainiya mara gata, sai dai gatan miji kawai wanda Allah ya taimakeni ya sanya shi ya zame mini mijin marainiya. Gwaggo mutuwar Abbah bai sanya ya zame mata aya ko darasin da zata aje duk wata ƙiyayyar da take nuna ni da mahaifinki ba, sai ma abun ya ƙaru ta yadda ta fito fili ta nuna ko inda take bata so ina zuwa. Sannan suma ƴan uwana su Yaya Kabeeru daidai da rana guda basu taɓa kirana su ji lafiyata ba, bare har na saka rai zasu rungumeni su maye mini gurbin Abbah. Ni ce ke kiransu duk friday mu gaisa,shi ma wani lokacin ba a ɗaukar wayar musamman Yaya Ali yafi yin wannan wulaƙancin. A cikin hakan na sake samun ciki mai wahala, da dinga fama har cikin ya yi ƙwari. Watan haihuwa ya tsaya na haifoki ranar wata asabar da safe a asibitin zaɓawa. Kwana ɗaya aka sallamemu muka dawo gida,ƴan barka duk wanda ya shigo sai ya yi santin kyawunki da faɗin cewa babu inda kika baro ni. Gwaggo Salamatu da Inna Hanne su ne dai tsaye a kaina, suke kula damu suna bamu kyakykyawar kulawa. Gwaggo a waya ta kira tayi mini barka, ta kuma sanya su Yaya Kabeeru suma suka kirani.Yaya Kabeeru ya buƙaci na tura masa lambar asusun ajiyata ya saka mini naira dubu ɗari. Na kira nayi masa godia ina mai yaba masa a zuciyata, domin yafi mini Yaya Ali mutunci sosai.Kwanaki sukai ta ƙarewa Gwaggo bata tako ƙafarta ta zo dubamu ba, sai ana gobe zamuyi arba'in sai gashi drivernta ya kawota cikin sabuwar motarta da Yaya Kabeeru ya siya mata. Bata ɗauki lokaci ba ta ce zasu juya bayan ta aje mini turmin atamfa da dubu goma.Na yi godia tare da yi mata rakiya har waje na ga motar,na yi mata fatan alkhairy da addu'ar Allah ya tsare.A lokacin ne kuma take sanar mini cewa Yaya Kabeeru ya sayi wani gida zasu tashi a gidan hayan da suke su koma koma unguwar rimi. Nan ma fatan alkhairy na yi masa ina jin daɗin cigaban da yake samu har cikin zuciyata, sannan na dinga masa addu'ar Allah ya ƙaro masa buɗi ya raya masa ƴaƴayensa uku da aka haifa masa Adnan da Jiddah, sai ƙaramar da take sa'ar haihuwarkice mai suna Hameedah.Yara ƴan gaban goshin Gwaggon Kaduna kenan,waɗanda da sam bata son abinda zai taɓa su.Musamman Adnan da Gwaggo ke wa wani irin so na fitar hankali.Kusan ma ta ƙwatosa daga hannun uwarsa ne ta maido shi wajenta tana sakaltashi da goyon Kaka. Kina da shekaru bakwai Malam Lawal ya rasu sakamakon haɗarin mota da ya samu akan hanyarsa ta zuwa Daura.Mutuwar ta gigitamu musamman Malam da bashi da sauran gata da iyaye shi ma. Malam Lawal ɗin shi kaɗai ne gatansa kuma uba da yake gani yaji sanyi a rayuwarsa.Sai gashi ya goce mun zama cikakkun marayun da bamu wasu dangin da Zamu iya kamawa. Har gara ma ni ina da ƴan uwa, kawai dai babu shaƙuwa ne da ƙauna mai zurfi tsakanina dasu.Hakan kuma ba laifin kowa ne sai na Gwaggo,domin ita ce ta lalata komi ko ince take kan lalatawarma. Bayan rasuwar Malam Lawal da shekara guda Inna Hanne ta sake wani auren, ta bar garin giwa zuwa Yakawada,sabida ɗan Yakawadan ne mijin da ta aura. Hakan ya sake jefamu cikin maraici da alhini mai yawa. Lokaci ya cigaba da tafiya kina zuwa makarantarki tare da Yaran Hakimi, waɗanda kuke kai ɗaya dasu.Kinyi wayo ga kyawu tamkar ke kika yi kanki,kika zartani a kyawun halitta tun kina ƙaramarki. Sai ke ɗin kin biyo baƙin fatar Malam ne ziryan, wanda hakan bai ragi kyawunki da komi ba sai ma ƙarin kwarjini a gareki.Sannu a hankali buɗi sai ƙaruwar ma Mallam yake yi, har kuma lokacin bai aje sana'ar ɗinkinsa ba.Gadona shi yake juya mini zallar kuɗin, kadaran shanayena kuma yana kula dasu haɗe da dabbobinsa da yake kiwo. Sannu a hankali nima na fara tara kuɗi a asusun a jiyata. Sannu a hankali zama haka bana komi ya fara damuna, sai na fara tunanin ko makaranta zan koma? Amma dana tunkari Malam da maganar kai tsaye ya nuna bai amince ba. Na haƙura na fara kasuwancin sarin atamfofi da kayan Yara ina siyarwa, Allah kuma ya sanya wa sana'ar albarka. Idan zaki iya tuna kina da wayonki mun sha zuwa kaduna wajen Gwaggo ta wulaƙantamu, ko fuska bama gani bare har mu sanya ran zamu iya kwana a gidan. Haka zamu damu ina jin ciwo da damuwa mai tsanani a zuciyata.Zuwan da nayi lokacin da Yaya Kabeeru zasu tare a sabon gidansa, shi ne zuwan da Gwaggo tayi mini wulaƙancin da bani mantawa. Na je ɗaukar lemu cikin uban lemukan da aka jirge don rabawa baƙin da zasu taru a yi walima a gidan Innar, Inna ta tujarani a bainar jama'a.,har tana kirana da dangin mayu. Nayi kuka ranar kamar raina zai fita, na kuma yi murnar da Allah yasa ba dake naje ba na barki a gidan Hakimi ne wajen Inna Karima.Da aka je can gidan Yaya Kabeerun ma akan kunnuwana Gwaggo ke cewa da ƴan uwanta ita wallahi bata ƙaunar wannan naci da binbinin da nakewa ahalinta, domin sam ita ta kasa jin ƙaunata a ranta. Tafi sha'awar na nisanceta ita da ƴaƴanta, hakan kawai zai sanya ta manta dani bare har taji ƙiyayyata a zuciyarta. Jikina ya yi mugun sanyi da jin waɗannan kalaman, na samu wani lungu a gidan na zauna nayi kuka mai yawa ina tunawa da Abbah da tarin nasihunsa gareni akan karna yanke zumunci da ƴan uwana. sai gashi Gwaggo na faɗin waɗannan kalaman. Tun daga ranar na rayawa raina cewa dolene na nisanci zuwa inda suke, matuƙar ina so in tsira da mutunci idanun Gwaggo. Koda na dawo gida ban sanar da Babanki komi ba, naja bakina nayi shiru amma duk daren duniya saina tuna da kalaman Gwaggo na kuma zubda hawayen tausayin kaina. Kina da shekaru tara kika shiga aji uku a primary. A lokacin ne kuma in baki manta ba cutar ƙoda ta kama mahaifinki Malam Mahmuda,cutar da ta kayar dashi ta kuma lashe dukkanin arziƙin da muke dashi har sai da muka saida gidanmu mai ƙyau muka dawo wannan gidan ƙasar a lokacin da aka ce za a yi masa dashen ƙoda. Da ƙyar aka haɗa kuɗin bayan an siyar da dukkanin abinda muka mallaka ni da shi,hatta gadona tas sai da aka siyar da komi aka tattara kuɗin da ke asusun bankina aka haɗa dasu. Bayan anyi aikin ne kuma aka gano cewa hantarsa ita ma ta kamu da ciwo. Hankalin mu ni dasu Hakimi ya tashi,jinya ya da dawo sabo maimakon sauƙi sai abu ya sake taɓarɓarewa. A haka Ubangiji ya amsa kayansa a ranar wata juma'a da bazamu manta da ita ba.Duk wani mai ƙaunarmu ya tausaya mana akan wannan babban rashin da muka yi,musamman ke an tausaya miki matuƙa sanin cewa yana matuƙar ƙaunarki.Sannan kuma kinyi shaƙuwa da shi sosai,sabida irin yadda yake nuna miki gata.Bashi da burin da ya wuce ya kyautata rayuwarmu, amma sai mutuwa tayi mana yankar ƙauna, ta datse dukkanin farin cikin mu wanda har kawo yau bamu daina jin ɗaci da raɗaɗin mummunar rashin bango majinginin rayuwarmu da mukai ba...... Inna Mairo ta dakata da maganar tana kuka sosai. Najma ma kukan ta fashe dashi tana tuno irin shaƙuwarta da Babanta, da irin gatar da ya nuna mata.Ta dinga tuno lokacin rasuwarsa da irin mummunar yanayin da suka tsinci kansu a ciki. Wanda ba don Hakimi da Iyalansa da suka tsaya musu,suka zame musu garkuwa ba.Da tabbas baƙin ciki sai ya yi ajalin Inna Mairo. Inna Mairo ta ja numfashi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗaura da faɗin, "tun bayan rasuwarsa rayuwarmu ke cikin garari, bamu da mataimaki sai Allah sai kuma Hakimi wanda ya haifu cikin uwa da uba. Don ba don shi da Iyalansa da suka rungumemu tamkar ƴan uwansu na jini ba, da yanzu muna yawon bara sabida rashin galihu. Gwaggo idan baki manta ba bata tako ƙafarta ta zo gaisuwa ba sai da Malam ya share kwanaki ashirin a ƙasa, sannan ta zo mini ta'aziyya har da ɗan buhun shinkafarta da taliya da kuɗi. Waɗannan kayan da ta kawo mini suka zameni baƙin kaya domin nafi buƙatar kulawarsu ita da Ƴan uwana.Nafi buƙatar su ƙaunaceni su nuna mini cewa ni ɗin jininsuce da basu da kamata, ba wai su dinga jifana da abin duniyar da zai ƙare ya barni da su ba. Su Yaya Kabeeru kuwa a waya kaɗai naci arziƙin da suka kira suka yi mini gaisuwa, shima sai bayan da Gwaggo ta koma da kusan kwana goma sannan ta sanar dasu. Nayi kuka mai yawa na kuma sake jin sun fita a zuciyata, ba don bana ƙaunarsu ba sai don yadda suke treating ɗina tamkar ƴar riƙon da bata da galihu a wajensu. Sai ya zamana ko waya na kira don in sadar da zumunci dasu,sai suka daina ɗauka sai sun ga dama.Na fassara hakan da cewa suna gudun kar na roƙi wani abu ne daga garesu, ko kuma na sanya ran zasu tallafeni ni da ke. Tun ina kira da biyiyar Gwaggo jefi-jefi ina zuwa gaidata, tana gwado mini kwanon shinkafa da su taliya. Har na gaji na daina na rungumi maraicina, na kuma bar wa Allah komi, domin ba zan iya jurewa irin ƙasƙancin da Gwaggo ke mini ba. Gidan Yaya Kabeeru da kanta ta cewa mai gadin gidan duk sanda na je kada a barni na shiga, tunda ta fahimci cewa matarsa mai kirkice kuma tana sona. Sai ta toshe kafar da zan samu shiga cikin gidan bare har Anty Zee ɗin ta dinga nema mini taimako wajen ɗan uwana.........✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma AD# #Aysha Ɗansabo lemu🥰 [2/28, 2:36 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 6* _Free page_ Ban sake zuwa kaduna ba koda wasa,ina dai kiran Gwaggo mu gaisa idan naci nasarar ta ɗaga kirana.Suma su Yaya Kabeeru ko basu ɗaga wayata ba sai na tura musu saƙon gaisuwata ta message. A haka rayuwa ta dinga gara mana cikin ƙunci da danuwa.Hakimi da Iyalansa sune tsaye a kanmu wajen tausaya mana da nuna mana ƙauna.Basu taɓa gajiyawa damu ba har kawo yau, sai dai ajizanci irin na ɗan adam da kan saɓa maka a wasu lokutan koda cikin rasani ne. Bayan kun kammala primary ke da su Lubah ne Hakimi ya sameni da maganar cewa makarantar kwana zai sama muku, hankalina sai ya tashi domin bani da sha'awar kiyi nesa dani tunda ke kaɗaice gareni da nake kallo inji sanyi a rayuwata.Amma girman Hakimi a idanuna da yadda yake ƙoƙarin ganin bai bar rayuwarki ya tagayyara a bayan idon mahaifinki ba, sai hakan ya hanani nuna masa rashin jin daɗina. Nayi masa godia tare da addu'ar fatan gamawa lafiya,sai da ya tafi ne na samu zarafin share hawayen damuwar da zai riskeni na rashinki a kusa dani. Ban taɓa nuna miki bana son ki da makarantar kwana ba, musamman da naga irin ɗoki da murnan da kuke yi ke dasu Lubah.Sai na kasa nuna rashin jin daɗina domin bana so ki bijirewa tafiyar, alhali soyayya da ƙaunace ta sanya za a yi miki wannan gatan. Na fara shirin tafiyarki ta hanyar yi miku ƴan ƙananun siyayyar da ɗalibi zai nema a makarantar kwana.Bake kaɗai na yiwa siyayyar ba har dasu Hanne da Lubah, don ba zai yiwu ace banyi karaba kamar yadda ni ake mini. Na ɗauki wasu kayayyakina na siyar nayi muku siyayya ba tare da kinsan cewa wani abu na ɗaga na siyarba.Ranar da kuka tafi makarantar kwana na Ƴan mata dake garin Basawa, nayi kuka da dare kamar ba zan daina.Damuwa ya fara yi mini yawa a zuci,sabida kewar rashinki dana mahaifinki. Ga kuma kewar rashin iyayena duka dana rasa, sannan ga baƙin ciki da damuwar yadda na kasa samun soyayyar ƴan uwana.Damuwoyi suka haɗu suka yi mini yawa Najma, sai dai da safe bayan na gama hidimata in kulle gidan in tafi gidan Hakimi wajen Inna Karima,musha hira ina tayata da wasu ayyukan gida. Haka na dinga yi har zuwa lokacin da Hakimi ya jajibo maganar ƙarin auren da zai yi, bayan ya yi tayi mini naci in bashi dama ya aureni na nunar masa cewa hakan ba zai taɓa yiwuwa ba. Ya yi naci har ya gaji, shi ne ya samo wata bazawara ƴar garin gangara ya aura. Tunda ya sake aure saina janye jikina da yawan zuwa gidan, sabida gudun husuma tunda gida ɗaya ya haɗe kan matansa, dole akwai buƙatar ka iya takunka. Na duba naga zama haka bazai yiwu mini ba, domin kwabo sai yafi ƙarfina. Hakimi ba ko yaushe yake bani kuɗi ba sai duk bayan sati biyu yake aiko mini kayan abinci da kuɗi naira ɗari biyar. Kuɗin basa yi mini kwana biyar sun ƙare, sai dai nayi ta maze-maze ina shiga takura kafin ya bani wani kuɗin.Dibara sai ta faɗo mini akan na ɗaga kujerun ɗakina guda biyu na siyar naja jari,in yaso sai na bar ragowar guda biyun. Na tafi gidan dillayi nayi mata magana, cikin kwana uku aka samu shigar dasu aka bani ƴan kuɗaɗena. Ina ta murna na fara tunanin mai zan fara, sai Inna Karima ta bani shawarar in fara suyan ƙosai sabida babu mai yi anan kusa.Na amince da shawararta na fara suyan ƙosai kamar da wasa, sai ga ciniki ya buɗe mini ana saya sosai. Tun ina soya mudu a rana har na dawo soya kwano guda.Da tafiya tayi nisa ma dawo ina soya har kwano biyu a rana. Ke duk bakisan da yawan gwagwarmayar da nasha ba,tunda sai hutu kuke dawowa gida.Dukkanin siyayyar da nake aiko muku keda su Hanne a ranar zuwan duba ɗalibai, duk da kuɗin sana'ar suyan ƙosai da nake yi. Na samu alkhairy mai yawa da wannan sana'a domin nafi ƙarfin komai, a cikin cinikin nake yiwa kaina cefane mai kyau.Duk ranar cin kasuwa zan je in yo siyayyata ta sati in dawo gida. Hankalina ya fara kwanciya sosai, amma damuwa da yawan tunani basu bar zuciyata ba. Duk dare sai na share hawayen baƙin yadda ƴan uwana suka manta dani, ni kuma ina son zuwa amma da zaran na tuna kalaman Gwaggo da irin tarban da nake samu daga gareta sai naji na sare bazan iya sake tunkarar inda take ba.Watarana na tara cinikina da nayi na ƙosai,kuɗi sun haɗu har dana wake da mai da nake siya na tuya. Da tsakar dare ƴan iskan ɓarayi biyu irin ƴan taurinnan suka shigo mini, suka nuna mini wuƙa suka ce kuɗi ko suyi mini yankan rago. Jikina na ɓari na fiddo musu dukkanin kuɗaɗen suka tafi dashi. Ba zan iya misalta miki irin tashin hankalin dana shiga ba,domin na shiga tsananin ƙunci da ɗimuwa. Inna Karima na je da kukana na sanar mata tashin hankalin daya sameni.Ta tayani baƙin ciki, ta tayani kuka domin kuɗine da sai dana wahala na tarasu,ko ince ina ma kan wahalar. Ta je ta samu Hakimi ta sanar dashi abinda ya sameni, ya kirani ya yi mini jaje tare da min alƙawarin zai bani wani jarin ko kaɗan ne in cigaba da sana'ata. Kuɗin da ya bani ba wani bane dubu biyarce, na amsa nayi godia na cigaba da sana'ata cikin maneji da ƙarfin zuciya. Tunda suka shigo mini sai ya zamana bana iya bacci, duk dare ina cikin fargaban karsu dawo mini su sake rabani da ɗan kuɗin da nake juyawa. Kafin wani lokaci sai yawan tunani da damuwa ya fara haifar mini da wani irin ciwon kai na ɓari ɗaya, na dangana da asibiti don likita ya dubani. Bayan anyi mini gwajin BP na amsa ƴan tambayoyi sai Likitan ya sanar dani cewa jinane ya hau sosai, dole in daina yawan tunani da sanya damuwa arai domin idan na cigaba to lashakka abin zai dinga cigaba ne. Ya kwantar mini da hankali sosai tare da karanta mini tarin illolin da sanya damuwa da yawan tunani a zuci ke janyowa lafiyar bawa. Nayi masa godia bayan ya rubuta mini magunguna kala biyu yace lallai in siya in fara sha, zuwa sati biyu in dawo a sake gwada BP ɗin aga ko ya sauka. Na dawo gida na sake zurfafa a tunanin yadda rayuwa ke gara mini, na fita da kaina na je nemo maganin a wani babban chemist a cikin gari. Da na bada takaddar suka duba sai aka faɗa mini kuɗin maganin dubu biyu har da ɗari uku,nayi shiru ina tunanin idan na siya duka kuɗin da nake juyawa ne zai rushe.Hakanan dai na siyo na dawo gida na tasa maganin ina hawaye,tausayin kaina na sake kamani sannan kalaman Likita shi ma na dawo mini. Maimakon in cire damuwa da tunani sai ma abu ya sake yin gaba, don bansan ta yadda za a yi a halin ƙuncin da nake ciki ace in cire damuwa a raina ba.A hankali cutar hawan jinin dai da likita ke guje mini ya sameni,ban taɓa faɗiwa kowa ba sai da jarin hannuna ya kai ga rugujewa sabida siyan magani. Na samu Inna Karima na sanar da ita halin da nake ciki, ta tausaya mini ta kuma yi mini nasiha akan in daure in daina sanya damuwa a zuci.Ina cikin wannan halin azumi ya zo, lokacin kun dawo hutu idan zaki iya tunawa.Ana saura kwana biyar azumi Gwaggo ta yo mana aiken kayan abinci da turmin atamfa aka ce inji Yaya Kabeeru. Ni ce dana fita wajen drivern yake mini tsegumin cewa ai Yaya Kabeeru ya kuɗance sosai, har ya sake gina danƙareran gida ya ɗauke Gwaggo ta koma hannunsa da zama.Sannan babban ciki ɗansa ma ya fita dashi ƙasar waje karatu.Na dinga mamaki nayi musu fatan alkhairy, ina ayyanawa a zuciyata cewa zan yi ƙoƙari inje in yima Gwaggo Allah sanya alkhairy tunda drivern ya rubuta mini address ɗin gidan. Kayan abincin kinsan muka sai da rabi don na sake samun jari, sauran muka aje bayan na ɗibarwa gidan Hakimi taliya da shinkafa ƴar gwamnati. Bayan sallah da sati biyu na kama hanya naje kaduna, idan kin tuna har kinso muje tare na nuna miki cewa ki bari na fara zuwa idan na samu fuska sai muje dake watarana.Cikin rashin sa a koda naje bansamu tarba wajen Gwaggo ba, sai a wajen Anty Zee da ta tarbeni cikin fara'a. Ta dinga tambayata abinda yake damuna domin duk taga na lalace, nayi duhu alamun ina cikin damuwa da matsaloli. Ban sanar da ita komi ba sai dai murmushi da nayi kawai na yaƙe.Ban samu ganin Yaya Kabeeru ba don ance ya yi tafiya zuwa wata ƙasa.Ina nan zaune sauran yaran suka dawo makaranta, waɗanda biyu daga ciki ma bansan fuskarsu sosai ba don tun suna ƙananu rabona dasu. Suka gaidani na amsa da fara'a ina yaba kyawunsu, dukansu mata ne su biyu waɗanda babu inda suka baro kamannin Momynsu. Babar cikin wacce ta fara zama cikakkar budurwa kamarki,ta ce mini sunanta Nasreen shekarunta sha biyar. Sai ƙaramar ta ce sunanta Nabeelah, shekarunta sha biyu ita. Ita asalin babbar Yayarsu mace mai bima babban ɗan Yaya Kabeeru Adnan, mai sunan Gwaggo Hauw suna kiranta Jiddah.Hajiya Zainab ta sanar mini tana Abuja a can take karatu a jami'ar NILE. Shi kuma Adnan yana London shekarunsa biyu kenan, saura shekara guda ya kammala amma ba zai dawo ba har sai ya yo masters ɗinsa.Na yi fatan alkhairy na fito daga sashin Hajiya Zainab da tsayawa misalta tsaruwansa ma ɓata baki ne.Ta haɗa mini sha tara ta arziƙi,na na koma sashin Gwaggo wanda ya gaji da haɗuwa domin an kashe mata dukiya ba kaɗan ba ina murna sosai. Babban gidane na garari Yaya Kabeeru ya gina a unguwar Rimi GRA. Ganin abin arziƙin da Hajiya Zainab ta haɗa mini ya sanya Gwaggo sake haɗe mini fuska, ta dubeni cikin ɗaure fuska ta ce, "To Mairo ba kin zo kinga arziƙi an haɗa miki abin kirki ki ce zaki dinga ɗakko jikina kina zuwa ƙaf da ƙaf ba, a dinga ɗaga ƙafa ana haƙuri da halin da aka tsinci kai. Tunda tunda fari kece kika zaɓi baƙauyen mijinki kika ce kinji kin gani, sai gashi rayuwa ta juya miki kinyi rashinsu daga shi har Abbanki da ya ɗaure gindi ya zaɓa miki rayuwar ƙauye.Kin ga yanzu dole ki rungumi ƴarki ku rayu a inda Ubangiji ya zaɓa muku, tunda kun sha faɗi a gabana cewa komi NUFIN ALLAH, to kema haka ALLAH ya NUFA a ƙauye zaki ƙare rayuwarki. Sai kiyi ta haƙuri zamu dinga aiko miki da taimakon da ya samu, don haka karki ce sai kin dinga ɗakko jiki kina yawan gidan ɗan uwanki kina zubda masa mutunci a gaban matarsa, tana ɗaukan abin hannunta tana baki ba." Gwaggo ta dakata da maganar tana kallon yadda hawaye ke gudu akan fuskata.Domin tunda ta fara magana naji wani abu mai nauyi ya danne zuciyata, na dinga ji tamkar in rufe ido in ganni a giwa na bar gaban Gwaggo. Ta taɓe baki ta cigaba da faɗin, "Ba kuka zaki yi ba Mairo, gaskiya nake faɗi miki don bana ƙaunar ganin kina kusanto inda nake.Har yanzu zuciyata bata daina jin zafin yadda kika zaɓi bare kika bar ɗan uwana ba, ban daina jin kishin yadda Abbah ya fifita ƙaunarki dana bare akan ƴan uwanki ba. Don haka yanzu lokacin mune gara ki bamu dama muyi rayuwa cikin kwanciyar hankali, ba tare da kin cigaba da ƙuntata zuciyata da ganinki kusa dani akai-akai ba. Kiyi haƙuri ki zauna a inda Allah ya zaɓa miki, zamu dinga taimakonki da abinda ya samu lokaci zuwa lokaci." Daga haka ta miƙe ta nufi hanyar wani corridor ta shige ciki, bata jima ba ta fito hannun duntse da kuɗi. Ta iso inda nake zaune ina kuka tamkar raina zai fita, ta aje mini kuɗin akan cinyata tana faɗin, "Ga kuɗi nan ki riƙe, zan sanya a zuba kayan abinci a mota sai Adamu driver ya maidaki gida.Kin ga kin huta da wahalar bin motar kasuwa." Har ta dasa aya na kasa ɗagowa na dubeta tsabagen yadda na muzanta a gabanta,maganganunta suka dinga ci mini zuciya ina ji tamkar in mutu inbi su Abbah ko zan huta da gani wannan baƙin ciki da tozarcin na Gwaggo. Kamar yadda ta faɗi ta sanya aka zuba mini kayan abinci a bayan mota,aka haɗa harda su kayan tea masu yawa duk aka jibga mini.Ko kaɗan wannan kyauta bai yi mini daɗi ba, domin ba don kar Gwaggo ta ce na ci mutuncinta ba, tabbas da ko tsinke ba zan fito dashi daga gidan Yaya Kabeeru. Muna tafe ina kuka har muka shigo garin giwa sannan na share hawayena don bana so ki tambayeni mai ya faru,sabida naci alwashin ba zan sanar dake irin cin mutuncin da Gwaggo tayi mini ba..... Inna Mairo tayi shiru tana jin yadda wani abu mai tauri ya danne zuciyarta. Najma dake sauraren Inna Mairo zuciyarta na tariyota mata a halin da Inna ta dawo lokacin. Don a ranar kwana tayi tana kuka har sai da hawan jininta ya motsa sabida damuwa da rashin bacci.Kuma duk yadda taso sanin abinda ya faru da Innar taƙi sanar da ita, daga ƙarshema sai tayi mata kashedin cewa karta sake damunta da saita san meyafaru matuƙar tana son ganin kwanciyar hankalinta. Inna Mairo ta numfasa tana cigaba da faɗin, "Ba saina tsaya maimaita miki komi ba Najma, domin wannan zuwa da nayi shi ne zuwana na ƙarshe garin kaduna wajen Gwaggo. Na kife babinsu tare da danne dukkanin ƙawazucinsu a can ƙasan zuciyata.Kiran wayar ma da nake yi na daina, a ƙarshema wayar nawa ta lalace. Dukkanin abinda muke dashi a hankali ya dinga ƙarewa,tun ina ɓoye miki halin damuwar da nake ciki har kuka kammala karatu kika dawo gida baki ɗaya.Ta yadda komi ya cigaba da kasancewa akan idanunki.Hakimi dai shi ne gatanmu bayan Ubangijin da ya haliccemu. Shi ne komi namu hatta kuɗin maganina daga baya shi ya ɗauki ya dinga ɗaukar nauyin saye, tunda jarin sana'ar nawa ya jima da rushewa. Sannan likita ma ya hanani kusantar wuta tun wani kwanciya da nayi jinya nasha baƙar wahala. Dawowarmu gida ne kika ce kin ji kin gani ke zaki amshi sana'ar ki cigaba da yi, da ɗan ragowar kuɗin gadon ɗakina da muka siyar. Cikin maneji da ƙarfin zuciya muke cigaba da gudanar da rayuwarmu, har zuwa lokacin da lafiya yaƙi min hannu domin na kasa daina tunani da jin zafin wofintar dani da ƴan uwana suka yi. Shi Yaya Ali ma a bakin drivern Gwaggo da take aikowa duk azumi ya kawo mana hatsi da atamfa na ji cewa ya bar ƙasan,shi da Iyalinsa ya koma ƙasar Cairo da zama. Nayi masa fatan alkhairy a cikin zuciyata ko ke ban sanarwa ba, don banga amfanin sanar dake ɗin ba. Wannan shi ne tarihin rayuwata Najma, da irin baƙin ciki da ƙiyayyar dana fuskanta daga wajen Gwaggon kaduna.Har kuma kwanan yau ina cikin baƙin yadda na gaza samun soyayya da kulawar matar uba,na gaza samun soyayyar ƴan uwana da su ɗaine suka rage mini a duniya. Na kasa daina jin ciwon yadda na kasa cigaba da bin wasiyyar Abbah na cewa karna yanke zumunta dasu, amma zuciyata ba zata iya cigaba da kusantar Gwaggo da Ƴaƴanta suna ƙunsa mini baƙin ciki ba. Duk da cewa nafi ganin laifinta domin shi Yaya Kabeeru ina da tabbacin ba don Gwaggo ce ke yi mini katanga dashi ta hanyar nuna ƙarfin ikonta akan su bi dukkanin umurninta ba, da zan samu sassauci da kusanci dashi. Musamman da ya kasance matarsa mai zuciyar alkhairy da tausayi ce, ita ma babu yadda ta iya da Gwaggo ne shiyasa bata zaƙewa akan son daidaita tsakanina da ɗan uwana.Ba laifina bane Najma, dolece ta sanyani nisantarsu ba don zuciyata na son hakan ba, sai don na tsira da mutuncina na kuma gujewa zuciyata ɓacin ran da zai iya assasa ciwona ya sake munana. Sai gashi na barsu amma takaici da baƙin cikin yadda suka wofintar dani bai bar zuciyata ta huta ba, sai ma barazanar kamuwa da cuta da take shirin yi. Na horeki da karki sanya damuwar jin wannan tarihin nawa a ranki har ya zama kin riƙesu a zuciyarki, don zuwa yanzu na aminta na kuma tabbatar cewa tabbas haka ALLAH Ya yi NUFIN rayuwata ta kasance." Inna Mairo ta kai ƙarshen maganar tana kuka da hawaye. Dukkanin rauninta ya gama bayyana, domin ta famo mikin da ta jima da danneshi a ƙasan zuciyarta. Najma kuka sosai take yi tana mai jin tsananin tausayinsu na sake keta zuciyarta, sam bata san irin waɗannan cin mutuncin Inna Mairo ta fuskanta daga wajen Gwaggon Kaduna ba. Da tabbas ba zata matsa mata da son jin tarihin rayuwarta ba, sai dai kuma ta wani fannin taji daɗin hakan domin a yanzu ta gane cewa ba laifin Inna Mairo bane.Babban mai laifin ita ce Gwaggo, amma kuma shi ma Yaya Kabeeru a matsayinsa na babba da Abbah ya bashi amanar Innar ya ce su maye mata gurbinsa, bai kamata ace ya wofintar da wasiyyar Abbah ya biyewa son zuciyar Gwaggon ba. Da ace ya ji kulawa da ita zai dinga bibiyarta koda a wayane yana sanin halin da take ji, idan suna da buƙata ya taimaka musu yadda ya kamata ba tare da ya bari Gwaggo ta san yana yi ba. Koba zasu tako ƙauyen garin giwa ba, yaci ace suna kulawa da rayuwarta ya hanyar samar da wani da zai dinga zuwa yana duba musu ita ya kuma kawo mata tallafin da duk take da buƙata daga garesu.Amma sam bai yi hakan ba sai ya biyewa son zuciyar Gwaggo ta raba zumuntarsu, ta nesanta Innar daga zuwa gareta bare har ta raɓi ƴan uwan nata ko Iyalansa. Najma ta sauke zazzafan numfashi tana jin tsanar Gwaggon Kaduna na samun gurbi a zuciyarta. Hannu ta kai kan fuskar Inna Mairo tana share mata hawayen da suka kasa tsaya mata.Cikin sanyin murya take faɗin, "Kiyi haƙury Inna, tabbas baki da laifi domin koni ce iyakar matakin da zan ɗauka kenan na ƙaurace musu. Allah shi zai cigaba da zama gatanmu, ba zai taɓa bari mu tagayyara ba Inna In Sha Allah! Ki cigaba sa haƙuri tare da danne dukkanin baƙin cikinsu, koma ince ki cireshi baki ɗaya daga zuciyarki. Lafiyanki shi ne abin tattalawa a yanzu, ba wai sake sanya tarin damu da ƙuntata zuciyarki ba. Ba zan sake miki zancensu ba Inna, kamar yadda ba zan so kema ki cigaba da sanya damuwa a ranki ba." Ta kai ƙarshen magiyarta ga Inna tana duban fuskar Innar da ya yi jajir sabida kukan da take yi. Inna Mairo ta sauke hannuwan Najma daga kan fuskarta tana jinjina kai ta ce, " Na gode Najma! In Sha Allah zan kiyaye lafiyata ko dan ke dana mallaka, nake kuma burin rayuwa tayi mana tsayi tare da juna. Allah ya haska rayuwarki Najma,Ya yi miki albarka tare da shiriya na addinin musulumci, ke da ɗaukacin ƴaƴan musulmi baki ɗaya. Gwaggo ita ma ina mata addu'ar Allah ya ganar da ita, ya kuma juyo da hankalin ƴan uwana zuwa gareni." Najma ta amsa da cewa "Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum Inna!" Daga haka suka tashi sakamakon kiran sallar la'asar da aka yi, Inna ta nufi tsakar gida don ɗaukar buta ta yo alwala,yayinda Najma ta nufi ɗakinta tana ji zuciyarta na cigaba da yi mata rawa.Tausayinsu dana rayuwarsu na sake samun wajen zama a zuciyarta. Cikin ranta ta dinga jin ƙarin ƙaunar Hakimi da ahalinsa, domin sune suka zame musu haske a rayuwa,kuma sune suka zame musu bango majingina. Ba don su ɗinba da yanzu suna cikin halin ƙunci mai muni, musamman ita Najmar da yanzu bata samu feature mai kyau ta samu ilimin zamani dana addini da ta samu a yanzu ba. Wanda har take da burin cigaban karatun idan rayuwa ya zo mata da sauyin da hakan zai iya kasancewa.Inna na shigowa ɗakin ta fito ita ma ta nufi waje don ɗauro nata alwalar............✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [2/28, 2:39 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 7* _Free page_ Bayan sun idar da sallar la'asar ɗinne Najma ta sanya hijab ta nufi gidan Adama dillaliya. Ta taki sa a ta sameta a gida bata fita ba, don sam bata faye zaman gida ba sai yawon neman hajan saye da siyarwa. Najma na sanar da Adama maƙasudin zuwanta, tayi mata sallama ta kamo hanyar dawowa gida. Tafiya take yi cikin takunta mai cike da nutsuwa ta halitta, ko kaɗan bata kallon ko'ina sai inda ƙafafunta suke takawa. Kamar daga sama ta jiyo muryar Luban gidan Hakimi daga bayanta, sai tayi saurin waiwayawa fuskarta na haskawa da murmushi mai faɗi. Lubah ta ƙariso wajen da Najma ta ja tayi tsaye tana faɗin, "Hey! B beauty daga ina? Najma ta sake sakin murmushin da har fararen haƙoranta suka bayyana, sannan ta dubi Lubah tana bata amsa da faɗin, "Daga gidan Adama nake, wai ku kam ba za ku daina kirana da B beauty ɗinnan ba ko?" Lubah ta saki ƙaramar dariyar tana faɗin, "Yo ai sunan daidai da ke ne Najma, domin kowa ya yi miki kallo ɗaya zai shaida cewa ke ɗin black beauty ce ta gaske." Najma ta jefawa Lubah harara suna mai jerawa da juna suka cigaba da tafiya don komawa gida. Suna tafe suna hiran tuna baya na school ɗinsu da irin wuyar da suka daga farko farkon zuwansu makarantar kwanar. Najma ta dinga jin wani shauƙi da kwaɗayin son cigaban karatunta na kamata. Ta sani cewa a yanzu babu wannan halin, domin Baba Hakimi burinsa suyi aure ne ba karatu ba.Bashi da ra'ayin mace ta zurfafa karatu sai maza,hakan yasa ya bai wa su Lubah umurnin fiddo mazajen aure. Najma ce kaɗai bai matsawa ba don Inna ta sanar masa sam bata son ana mata maganar aure. Gashi akwaita da farin jinin samari, duk da cewa duk masu zuwa sai ta ce basu yi mata ba Sabida basu da wadatacciyar ilimi kamar yadda take da burin samun abokin rayuwar mai wayewa da ilimin addini dana zamani.Don haka sam bata sauraren dukkanin samarin ƙauyen giwa da ke nufota da ƙoƙon bararsu, don yawancinsu duk basu yi karatun kirki ba.Tun Inna na mata faɗa akan ta dinga sauraran masu zuwa gareta har ta gaji ta zuba mata ido, tana dai yi mata addu'a Allah ya yi musu zaɓi na gari, don komi lokacine ta sani idan lokacin auren yazo Allah xai kawo wanda zai sace zuciyar Najmar farat ɗaya har ta amince masa. Sannu a hankali suna tafe suna hira har suka iso ƙofar gidan Hakimi, wanda shi ne na farko kafin a yi can gaba sannan a isa gidansu Najma ɗin. Lubah ta dubi yadda Najma ta toge a tsaye alamun ba shiga gidan nasu zata yi ba,ta buɗe baki ta ce, "Najma yanzu muzo har ƙofar gida tare ba zaki shiga ku gaisa da Inna ba?" Najma ta ɗan saki murmushi tana narke fuska ta ce, "Afuwan my Lubcy! Sauri nake na je na sanar da Inna yadda muka yi da Adama, zan zo na musamman gobe na yini musha hira." Lubah ta harareta tana faɗin, "Allah ya kaimu goben, ki gaida min Inna Mairo ki sake mata sannu da jiki." Najma tayi gaba tana faɗin, "Zata ji In Sha Allah!" Daga haka ta cigaba da takawa har ta isa gida.A tsakar gida ta samu Inna Mairo ta shinfiɗa tabarma tana zaune tana lazumi da carbi riƙe a hannunta. Ta samu waje kusa da ita ta zauna tana faɗin, "Inna sannu da hutawa, na samu Adama ta ce zuwa da safe za ta zo ta ga girman katifar." Inna Mairo ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya kaimu Najma." ta ɗaura da cigaba da cewa, "Kina fita Babanku Hakimi ya aiko Ummaru da kayan abinci, gasu can an aje a madafi har da kuɗi dubu ɗaya ya haɗo dashi." Najma ta sauke nunfashi, girma da ƙaunar Hakimi na sake girma a zuciyarta. Cikin tsananin nuna farin cikinta ta ce, "Ma Sha Allah! Allah dai ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.Gaskiya Inna babu abin zamuce da Baba Hakimi sai dai addu'ar gamawa da duniya da lafiya. Allah ya ƙara masa nisan kwana mai albarka, Allah kuma ya duba bayansa a lokacin da ƙasa zata rufe idanunsa." Inna Mairo ta amsa da cewa, "Ameen!" Najma ta miƙe ta nufi kicin ɗin don duba abinda aka aiko musu dashi tunda ita ce mai sarrafawa, domin tunda aka hana Inna yawan kusantar ɗumin wuta sai ya kasance ita ce mai yin girkin. Kamar dai yadda ya saba aiko musu wake da shinkafa ce sai gero da garin tuwo da ake niƙo masa sai dai kawai ayi ta ɗiba ana amfani dashi. Ta sake gode masa cikin zuciyarta tana tunanin abinda zasu sarrafa suci da dare. Tunaninta ya tsaya akan ta dafa musu shinkafar manja da alayyu kawai, tunda da rana kwaki suka ci da ƙuli. Koda ta sanar da Inna abinda take da niyyar dafawar, sai ta miƙa mata dubu ɗayan ta ce ta je tayo cefanan ɗari biyar ta dawo da ɗari biyar. Najma ta sake fita tayo cefanan ta dawo tana mai fara shirin ɗaura girkin. Inna tana daga zaune ta taimaketa da gyaran kayan miya da alayyahun, ita kuma Najma ta nufi kicin don kiciniyar rura gawayin da zata yi girkin da shi. Washegari Adama dilalliya da safe ta zo ta duba katifar tayi masa kuɗi. Inna Mairo ta raina darajar da katifar tayi domin ta san cewa katiface mai nagarta irin ta da.Sai dai dagewa da Adama tayi akan cewa ba zata ƙara farashi daga yadda tayi masa kuɗi ba,sai kawai Inna tq amince domin a matse suke da son kuɗin. Zuwa yamma Adama ta zo da mai ɗaukar katifa ta biya kuɗi aka ɗauka, Inna Mairo sai da tayi ƙwalla lokacin da aka fita da katifar akan idanunta. Najma ta damƙawa kuɗin bayan tafiyar Adama tana mai cewa , "Gasu Najma, sake irgasu mu gani." Najma ta amsa kuɗin ta sake irgawa tana sanar da Inna Mairo yawan kuɗin. Suka zauna suka lissafa kuɗin wake dana mai da za a siyo don cigaba da sana'arsu da ya karɓesu na tuyan ƙosai, wanda Najmar ce zata jagorancin cigaba da yi tunda Inna ba damar ta cigaba sabida kiyaye lafiyarta. Ragowar kuɗin da ya ragu Inna ta amsa ta aje, da tunanin cewa washegari zata aika da kuɗin wajen Hakimi don a nemi ciko a sayo maganinta guda ɗaya da ba a samu saye ba sabida tsadarsa. Sai dai koda ta aika Najma da kuɗin Hakimi cewa ya yi a dawo mata da kuɗinta, yana sane da maganar da zaran ya samu hali za a sayo a kawo mata. Inna Mairo ta tasa kuɗin a gaba tayi zuru tana zurfafa tuni akan irin ɗawainiyar da Hakimi ke yi dasu, wanda ba kowani amini bane zai yiwa amininsa wannan halaccin da Hakimi ya gwadayi ba. Kuɗin sai ta sake rabashi biyu ta bai wa Najma rabi ta ce ta siyo musu mangyaɗa da manja na girki wanda zai jima musu, ragowar kuɗin kuma ta adana a hannunta don tsaran lalura. Najma ta cigaba da suyan ƙosai kamar yadda suke yi, kuma ana samun ciniki mai yawa don sana'ar ta amshesu da gaske. Sabida yadda suke tsaftace sana'ar da kyau, suke kuma yinsa da arha matuƙa basa bin mugun riba mai yawa,don albarkan suke nema ba wai yawan kuɗin da za a zare albarkarsa ba. Tun ƙarfe bakwai idan ta kafa yin tuyan bata tashi a wajen sai ƙarfe goma, sosai Inna ke tausayinta tare da jinjinawa ƙoƙarin Najma sabida irin wahalar da take sha.Inna ke ɗan taimakawa da yin ayyukan gida irin su shara da gyaran ɗaki don ragewa Najma wasu wahalhalun. A haka suke cigaba da sana'arsu suna manejin rayuwa, da daɗi babu daɗi haka nan suke nuna godiyarsu ga Allah kullum.A hakan suke samun ƙarin wadatuwan zuci a koda yaushe,wanda shi ne kuma babban arziƙin bawa. Ranar wata asabar da misalin ƙarfe sha biyu na rana, Najma ta fito daga wanka kenan tana shiryawa suka fara jiyo sallama daga bakin zauren shigowa gidan. Inna Mairo ta zari Hijab ta fice don ganin mai sallamar, duk da cewa kunnuwanta na jiyo mata murya kamar ta drivern Gwaggon kaduna ne. Tana fita kuwa tayi ido huɗu da Adamu driver,ta saki murmushi tana masa maraba da zuwa.A tsaye suka gaisa kafin ta juya zuwa cikin gida don ɗakko masa tabarma, ta shinfiɗa masa a nan zauren suna sake gaisawa cikin mutunci. Adamu ya dubi Inna Mairo cikin jin tausayin yadda duk ta lalace ya ce, "Hajiya Zainab ne ta aiko ni da saƙo, ta ce a gaidaki da kyau sannan idan na iso in kiraki zaku yi magana da ita ta wayata." Inna Mairo da ke sauraren saƙon Adamu driver, sai ta dubesa tana mamakin kalamansa. Ya cigaba da faɗin, "Bari a kwaso saƙon daga mota, in yaso sai na kirata kamar yadda muka rabu da ita akan ina isowa na kira kuyi magana." Inna Mairo ta jinjina kai tana faɗin, "To badamuwa Adamu, bari a kawo maka koda ruwan sha ne kafin a ɗaura sanwar rana ka ci." Adamu ya yi godia yana mai fita zuwa wajen ƙatuwar motar Hajiya Zainab Kaita da ya taho da ita. Inna Mairo kuma ta shiga cikin gida don kawo masa ruwan sha, tana mai sanar da Najma cewa drivern Gwaggo ne Adamu yazo. Ta cigaba da cewa, "Ya ce matar Yaya Kabeeru ce ta aikosa Najma, Allah dai yasa lafiya don ta ce idan ya bani saƙon ya kirata muyi magana. Naga dai ba azumi bane yanzu, ba kuma sallar layyane ya gabato ba bare ace saƙon da aka saba yo mini aike dasu ne suka iso." Inna ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya, hakan yasa Najma dubanta da kulawa ta ce, "Bakomi Inna,alkhairy ne In Sha Allah! Kai masa ruwan kiga abinda ya zo dashi, sannan kiji mai zata sanar miki ɗin." Inna ta jinjina kai tana gamsuma da kalaman Najma,ta juya ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da wani matsakaicin jug ɗin roba da ta ɗibarwa Adamu ruwan randarsu. Ta samu ya jibge manyan paper bags har guda uku daga gefe guda cikin zauren, ɗaya gefen kuma ya jingine buhun shinkafa da su taliya da kayan shayi. Ta ɗauke idanunta daga kan kayan tana mayarwa kan Adamu ta ce, "Adamu yanzu duk waɗannan kayan daga Hajiya Zainab suke? Kodai Gwaggo ce ta aiko ka ta ce ka ɓoye hakan?" Adamu ya yi murmushi, can ƙasan zuciyarsa yana sake jin tausayin Inna Mairo sabida yadda ƴan uwanta da Gwaggo basu damu da ita ba. Ga arziƙi can kamar yaci kansa, amma ita gata a cikin ƙauyen giwa da sam garin ya kula baya samun wani cigaba. Kullum yazo jiya iyau yake ganin garin, ba ya ganin wani sauyi na a zo a gani da garin ke samu. Ya sauke nunfashi yana faɗin, "Inna Hajiya ce ta aiko ni ba Gwaggo ba, don ita bata ma san nan nayo ba domin Hajiya Zainab cewa tayi ta ara mata ni zata aikeni wani waje. Don haka bata ma san cewa nan zan zo ba Inna, amma bari na kira Hajiyar kuyi magana." Daga haka ya zaro wayarsa daga gaban aljihun rigarsa yana mai danna kiran Hajiya Zee Kaita. Bugu biyu ana uku ta ɗaga wayar, Adamu ya shaida mata cewa ya iso, ta buƙaci ya sadata da Inna Mairon.Ya miƙawa Inna wayar ta amsa, hannunta na rawa ta kai wayar kunni bakinta ɗauke da sallama.Daga ɓangaren Hajiya Zainab ta amsa mata sallamar tana tambayarta lafiyarta dana ƴarta Najma. Inna ta bata amsa da cewa suna cikin ƙoshin lafiya. Hajiya Zainab sai ta tafi kai tsaye da tambayar Inna dalilinta na rashin zuwa wajen bikin manyan Yaranta biyu da aka yi wata ɗaya da ya wuce. Cike da kaɗuwa Inna Mairo ke duban Adamu tana sake damƙe wayar akan kunninta ta ce, "Yanzu kina nufin ki ce anyi auren Adnan da mai sunan Gwaggo banji labari ba?" Cike da tsantsar mamakin jin kalaman Inna Mairo ita ma Hajiya Zainab da bata tabbacin haka take nufi. Inna Mairo ta saki salati tana mai jin zuciyarta na matsewa da wani irin ɓacin rai mara misaltuwa. Mamakin halayyar Gwaggo da irin ƙiyayyar da take mata na sake tayar da hankalinta, domin bata taɓa tunanin hakan zai iya faruwa ba koda wasa. A ce wai anyi auren manyan Yaran Yaya Kabeeru ƴan gaban goshin Gwaggo, amma bata aiko an sanar mata ta halarci bikin ba sabida kawai Gwaggon ta nuna mata cewa har yanzu zuciyarta bata risina akan nuna mata ƙiyayyah da rashin son ta raɓi inda suke ba. Wasu hawaye masu zafi wanda bata shirya fitowarsu ba suka gangaro daga fuskarta, ta sanya hannu tana sharesu tana cigaba da sauraren kalamai na rarrashi daga bakin Hajiya Zainab ɗin. Wacce zuwa lokacin da suke wayar da Inna ta gama gane duk wani laifi na wuyar surukarta Hajiya Gwaggo, wacce ita ce bata son Inna ta raɓi ƴan uwanta bare har ta amfana da ni'imar da Ubangiji ya yi musu na tarin arziƙi. Domin zuwa yanzu arziƙinsu kullum sake bunƙasa yake, sun samu ɗaukaka a rayuwa matuƙa da gaske. Musamman mai gidanta Alhaji Kabeer Dukku,wanda ya gama zama babba sosai a wajen aikinsa, sannan ya zama ɗan siyarsa ɓoye dake ci da gwamnati.Yana samun manyan kwagiloli daga gwamnatin tarayya, sanadiyyar amininsu dake kusa da shugaban ƙasa sosai. Inna Mairo ta dinga sauraren maganganun Hajiya Zainab da irin ban bakin da take mata na cewa ta daure ta cigaba da kai musu ziyara,karta cigaba da biye Gwaggo ta zo don sadar da zumunci tsakaninta da ƴan uwanta ne. Ita dai Inna tana jin Hajiya Zainab ne kawai, amma zuwa lokacin zuciyarta ta riga ta kulle da tsananin baƙin cikin wannan tozarci da nuna mata iyakarta da Gwaggo tayi. Don bata yi zaton duk lalacewarta da yadda Gwaggon bata sonta zata iya bari ayi auren Ƴaƴan ɗan uwanta uba ɗaya amma ace wai bata sani ba. Tabbas dole zuciyarta ta girgiza, ranta kuma ya sosu domin iyakan tozarci da rashin ƙauna har ma da ƙyama duk an nuna mata. Ta danne zuciyarta har zuwa lokacin da suka kammala yin magana da Hajiya Zainab ɗin,sannan tayi mata godiya mai tarin yawa akan abin arziƙin da ta aiko mata da shi. Ta miƙawa Adamu wayarsa tana mai jin ƙaunar matar Yayan nata na mamaye zuciyarta, babu abinda zata ce mata sai godiya don ta fiye mata ƴan uwanta da Gwaggon.Tunda har ita taji ciwon rashin zuwanta bikin, ta kuma aiko takanas don a ga lafiyarta a kuma ji dalilinta na rashin halartan bikin. Bata bar ta haka ba kuma sai da ta aiko mata da tarin abin arziƙi, wanda take kyautata zaton kayan biki ne a waɗancan jakunan takardan.Sabida sai a yanzu take ganin tambarin sunan Yaran da aka aurar ɗin a jikin paper bags ɗin.Cikin wani irin sanyin murya ta dubi Adamu driver tana mai miƙa masa wayarsa ta ce, "Adamu ga wayar taka na gode, ka yi haƙuri ka jira Najma ta kammala abinci sai kaci ka yi sallah kafin ka juya." Adamu ya dubeta cike da sake jin zallar tausayin yadda yaga ɓacin rai kwance a idanunta ya ce, "Kiyi haƙuri Inna, komi na rayuwa mai wucewa ne." Inna Mairo ta jinjina kai tana kai wa matuƙa wajen sake danne damuwa da ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ta ce, "Bakomi Adamu, tabbas komi mai wucewa ne. Allah dai ya bamu ikon cin jarabawarmu ta rayuwa, domin kowa akwai ta inda ake jarabtarsa." Adamu ya jinjina kai yana sake kwantar da hankalinta da kalamai masu daɗi, don ya hango ɓacin rai mai yawa kwance a idanunta. Shi ya shigar mata da kayan abincin zuwa ciki, ita kuma ta ɗauki jakunan duka ta nufi cikin gidan, tana nufan ɗakinsu dashi zuciyarta na mata wani irin nauyi da zugi.......✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUKA AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DON SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/2, 1:57 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 8* _Free page_ Bayan Adamu ya ci abinci ya gabatar da sallar azuhur anan cikin zauren gidan Inna Mairo, sai suka yi sallama da juna ya juya don komawa garin kaduna.Inna Mairo ta juyo zuwa cikin gidan daga yi masa rakiya da tayi,tana ji zuciyarta na cigaba da yi mata matsananci zafi. A nan tsakar falonta ta samu Najma na fiddo kayan da ke cikin waɗannan paper bangs ɗin.Ta nemi guri ta zauna tana cigaba da kallon kayayyin da Najma ke fiddowa.Kayayyaki ne da aka raba wajen bikin irin cups da su plate, sai su towels na wanka da su mafitai masu kyau da sauran tarkace. Ɗaya bag ɗin kuma turmin atamfa ne mai tsada haɗe da wani laces mai shegen kyau, sai takalmi flat shoe product ɗin CHANNEL. Najma ta dinga juya kayan tana yaba kyawunsu, yayinda Inna Mairo da ke kallonta ta dinga ji zuciyarta na karyewa.Hawaye suka fara taruwa a idanunta ,ta dinga jin ƙaunar Hajiya Zainab na sake samun waje a zuciyarta. Cikin wani irin sanyin murya ta dubi Najma ta ce, "Watakila ta siya mini waɗannan kayan ne a tunaninta zan isa da wuri sai a ɗinka mini inci biki dashi.Ki taya ni yi mata fatan alkhairy domin yadda take nuna mini ƙauna ta fiye mini ƴan uwana da sam bana cikin zuciyarsu." Inna Mairo ta ɗan dakata da maganar wani abu mai mauyi na sake danne zuciyarta. Da ƙyar ta iya cigaba da faɗin, "Najma aurar Yara biyu fa aka yi amma ban yi darajar da zanji koda labari ba, wata iriyar ƙiyayyace Gwaggo ke mini har haka? Meyasa idan ita ba zata sanar min ba Yaya Kabeeru da kansa ba zai iya aikowa a sanar mini ba? Sabida ni ɗin basu damu dani bako? Suna ƙyamar na raɓi hidimarsu don za a nuna ni a ƙasƙance ace ni jininsu ce dana fito daga ƙauye ko? Meyasa zumunci ya yi lalacewar da ɗan uwanka na jini ke maida kai bakomi ba matuƙar aka ce kai ɗin ba kowa bane, ko wanda ka ke tare da shi ba kowa bane? Zafi nake ji sosai a cikin zuciyata Najma,na rasa yadda zanyi na cigaba da yin sabo da irin wannan tozarcin da ake yi mini don anga ba idanun Abbah a raye...." Inna Mairo ta kasa cigaba da maganar sakamakon kuka mai ƙarfi da ya taho mata, ta dinga yinsa har da shashsheka tana ji tamkar ƙirjinta zai buɗe sabida zafi da ciwon da take daga cikin zuciyarta. Hankalin Najma ya tashi da ganin irin yadda Inna Mairo ke kuka,wani irin tausayin Inna ya kamata. Hawaye suka dinga zarya a fuskar Najma tana rarrashin Inna Mairo.Tsana da jin zafin Gwaggo da Ƴan uwan Inna na sake zama a zuciyarta. Da ƙyar tayi nasarar tsaida kukan da Inna Mairo ke yi,ta sanya hannu tana share mata hawayen da suka kasa tsayawa. Cikin tsananin raunin muryar da tausayi da zallar damuwa suka kassarashi Najma ke faɗin, "Inna kiyi haƙuri, ki sake akan wanda ki ke yi.Komi zai wuce, zasu yi nadama wataran, domin sun cutar da zuciyarki a lokacin da kike matuƙar buƙatar su nuna tausayi da kulawarsu gareki. Kina dani Inna kuma In Sha Allah sai na share miki hawayenki na sanya farin ciki a zuciyarki,farin cikin da zai wanke damuwa da ƙuncin da suka cusawa zuciyarki.Don Allah Inna karki saka wannan baƙin cikin a zuciyarki ta yadda zai tada ciwonki, domin ni kaɗai kike sanyawa cikin firgici da ɗimuwa a duk sanda zan ganki cikin halin ciwo." Najma ta dakata da maganar hawaye na cigaba da zarya akan fuskarta. Inna Mairo ta dubi ƴarta tana sake jin tausayin kansu na kamata, ta miƙa hannu ta riƙo na Najma tana faɗin, "Ba zanyi hakan ba Najma, amma ki sani dole zuciyata da shiga ƙunci da irin wannan abinda aka yi mini.Ki tayani addu'a Allah ya danne zuciyata domin bana ji a yau zan iya koda rintsawa ne. Zuciyata zafi take yi ina jin ciwo mai yawa a cikinta Najma." Inna ta dakata tana zare hannunta daga riƙon da tayi wa Najma ta nufi ɗakinta jiri na ɗibarta. Hankalin Najma sai ya sake tashi,tabi bayan Inna da kallo wasu hawayen masu zafi na sake ɓalle mata. Duk yadda ta yi ƙoƙari wajen tausar zuciyar Inna Mairo ta kasa, domin ko abinci cokali uku Innar ta kai baki ta ce ta ƙoshi. Da ƙyar ta sha ruwa ta haɗiyi maganinta na rana ta kwanta,tana cigaba da jinyar zuciyarta da ke mata tsananin ciwo har lokacin. Zuwa yamma bayan Najma ta kammala yiwa Inna ɗan faten tsaki da yakuwa, sai ta juye a kula ta nufi ɗakin Inna dashi ta aje.Ɗakinta ta nufa ta zuro dogon hijab ɗinta har ƙasa kalar sararin samaniya,kalar ya yi mata kyau matuƙa tare da haske black beauty face ɗinta. Ta leƙa ɗakin Inna ta sameta a kwance har lokacin bisa katifarta,ta rufe idanunta tamkar mai yin bacci.Amma a zahiri idanunta biyu ta dai rufe idanun ne kawai, don bata buƙatar barinsu a buɗe sabida yadda idanun kansu sukai mata wani irin nauyi. Najma ta sanyaya murya ta ce, "Inna zan ɗan leƙa gidan Baba Hakimi, zan dawo yanzu bada jimawa ba." Kai kawai Inna Mairo ta gyaɗa wa Najma, ba tare da ta iya buɗe baki tayi mata magana ba. Najma ta juyo ta fice zuciyarta cike da damuwan halin da Innan ta shiga sanadiyyar kawai ba a sanar da ita bikin Ƴaƴan ɗan uwanta Yaya Kabeeru ba. Tafiya take yi cikin sanyin jiki har ta isa ƙofar gidan Hakimi, ta samu mutane zaune daga wajen zauren bisa shinfiɗu. Ta risina ta gaidasu ta wuce zuwa cikin gidan, tana ji ƙafafunta na faman harɗewa sakamakon idanun maza da suka yi mata rikiya. A tsakar gida ta samu Inna Karima na gyaran gyaɗar da za ta zuba a miyar taushe. Da fara'a ta ɗago tana amsa sallamar Najma tana faɗin, "Lale Najma, yanzu Hanne suka gama zancenki ita da Lubah." Najma ta ƙarisa inda Inna Karima ke zaune bisa kujerar tsugunno, ta gaidata cike da ladabi tana faɗin, "Alllah sarki, na tsaya na kammala yiwa Inna fate ne shiyasa ban fito da wuri ba." Inna Karima ta jinjina kai tana faɗin, "Ya jikin nata Najma, da fatan dai tana shan magungunan? Ɗazu Hakimi ya gama maganar cewa Auwalu zai je a sayo cikon ɗaya maganin." Najma ta saki murmushin yaƙe tana cewa, "Jiki da sauƙi Inna, tana shan maganin bisa ƙa'ida. Amma yanzu haka a kwance na baro ta, tana cikin ɓacin rai mai tsanani Inna." Inna Karima tayi saurin aje tray ɗin hannunta tana duban Najma ta ce,"Subhanallahi! Mai ya sameta Najma, ana murna jiki ya yi sauƙi kuma?" Najma ta sake narke fuska alamun tana cikin damuwa, ta dubi Innarsu Hanne cike da sanyin murya ta mayar mata da yadd aka yi. Inna Karima ta sauke zazzafar numfashi bayan ta gama sauraren Najma, ta buɗe baki cikin ɓacin rai ta ce, "Wannan Gwaggo wai wace iriyar zuciyace gareta? Meyasa ba zata mance abinda ya faru a baya ta gane cewa komi fa NUFIN ALLAH ne, yadda duk yaso hakan dole zai kasance. Mairo bata da laifi domin ba ita ce ta sanya mahaifinta auro Innarta ba, ba kuma ita ce ta zaɓawa kanta auren Malam Mahmuda ba. Allah ne ya yi nufin hakan zai kasance, don me ba zata saduda ta gane komi yin Allah bane? Ki kwantar da hankalinki Najma, zan yi magana da Hakimi domin lokaci ya yi da ya kamata ace ya shiga cikin wannan lamari ya daidaita tsakanin Mairo da Ƴan uwanta koda son ran Gwaggo ko babu. Domin idan aka cigaba da tafiya a hakan, tabbas watarana za a wayi gari baƙin cikinsu ya yi ajalin Mairo.Wanda mu ne za a yiwa asara basu ba, domin su ɗin basu san daraja da ƙimarta a matsayinta na mace tilo a cikinsu ba." Inna Karima ta kai ƙarshen maganar fuskarta na bayyan zallar ɓacin ran da ke zuciyarta. Najma da tayi zuru tana saurarenta,ta ɗaga manyan fararen idanunta tana duban Inna Karima ta ce, "To Inna da ko na gode idan ki kai wannan taimakon, domin ina cikin matsanancin damuwa. Ina jin tsoron ciwon zuciyar da ke barazanar samunta ya sameta, idan hakan ya faru na shiga uku Inna." Najma ta kai ƙarshen maganar cikin rawar murya. Inna Karima ta dinga rarrashin Najma tana kwantar mata da hankali, daga ƙarshe ta ce ta tashi ta isa ɗakin su Hanne suna nan a ciki. Ta ja ƙafa a hankali ta isa ɗakin amininan nata su Hanne, zuciyarta na yin sanyi da kalaman da Inna Karima tayi mata na kwantar da hankali. Shafin hira suka buɗe da ƙawayen nata su Hanne, waɗanda take kallo a matsayin ƴan uwa na jini da bata dasu. Sun ɗauki lokaci suna raha a tsakaninsu, sai da Najma ta kalli agogo ta ga lokaci ya ja sosai, sannan ta miƙe tana sanar dasu cewa zata wuce gida ta baro Inna ita kaɗai bata jin daɗi kuma. Cike da alhini suke tambayarta me yasamu Innar? Najma ta basu amsa da cewa jikin ne dai ya ɗan motsa mata, bata sanar dasu gaskiyar abinda ya kawo ɓacin rai a zuciyar Inna Mairon ba. Suka yo mata rakiya har zaure bayan tayi sallama da Inna Karima da Amaryar Hakimi mai suna Ladiyo. Ta isa gida ana daf da kiran sallar magriba, ta wuce direct ɗakin Inna Mairo don duba halin da take ciki. Bata sameta a ɗakin ba hakan ya bata tabbacin ta fita zuwa bayi ne, sai ta nufi ɗakinta tana zare hijab ɗin jikinta ta aje bisa katifarta. Fitowarta falo ya yi daidai da shigowar Inna Mairo, ta dubi Najma tana faɗin, "Sai yanzu ki ka dawo Najma?" Najma ta ɗan narke fuska tana faɗin, "Inna kiyi haƙuri, wallahi ban ankara ba naga lokaci ya tafi.Inna Karima suna gaidaki sun ce ai miki sannu da jiki, sannan Baba Hakimi ya bai wa Auwalu kuɗin maganinki da ba a sayo ba." Inna Mairo dake sauraren Najma sai tayi murmushin yaƙe tana faɗin, "Alhamdulillah! Allah ya biya shi da gidan aljanna Najma." Najma ta amsa da cewa, "Ameen." Tana mai wucewa waje don zuwa ta ɗauro alwala. Suna zaune tare da Inna Mairo bayan sallar isha'i suka jiyo sallamar Hakimi da Inna Karima. Najma tayi saurin fita tana musu barka da zuwa. suka ƙariso cikin ɗakin Inna Mairo Hakimi na amsa gaisuwar da Najma ke masa cike da kulawa. Inna Mairo tayi saurin shigewa ɗaki ta sanyo hijab, kafin ta fito ta zauna daga kusa da Najma tana yiwa su Hakimi barka da zuwa. Bayan sun gama gaisawa da tambayarta jikinta, sai Hakimi ya ɗaura da yi mata nasiha kamar ko yaushe akan ta cigaba da haƙuri da rayuwa. Inna ta dinga gyaɗa kai tana jin ƙarin nauyi a zuciyarta, musamman da ya ambato mata sunan Gwaggon kaduna. Hakimi ya cigaba da duban Inna Mairo yana faɗin, "Mairo lokaci ya yi da zamu je gani gaki gaban Gwaggo ta gaya mana mi kika yi mata da ta riƙeki haka a zuci? Meyasa ba zata gane cewa komi mai wucewa bane, sannan Ubangiji na son masu yawan yafiya da manta sharrin mutum su rungumi alkhairinsa.Zaki tasa ƴarki Najma mu je gani gaku domin kawo ƙarshen wannan ƙiyayya,don naga alamun lamarin kullum sake lalacewa yake yi maimakon ya gyaru. Bai kamata ace an kawo lokacin da har za a aurar da Ƴaƴan Kabeeru amma ace baki yi darajar da zaki sani ba, sabida an kai maƙura wajen nuna miki cewa ke bakomi bace. Abin ya yi mini ciwo matuƙa Mairo, amma ina miki nasiha da ki ɗauki dangana ki kuma maida komi ba bakomi ba. In Sha Allah! Komi zai daidaita, ni dai alfarmata kawai ki amince da buƙatata karki ce mini a'a." Hakimi ya kai ƙarshen maganar yana duban yadda hawaye ke gudu akan fuskar Inna Mairo. Cikin rawar murya ta saci duban Hakimi tana faɗin, "Ƙafi ƙarfin ka nemi dukkanin alfarma in kasa yi maka,sai dai ina matuƙar jin tsoron kar taci mutuncinka idan mun je gareta. Kayi haƙury abar maganar har zuwa lokacin da ita da kanta zata gane gaskiya ta nemeni." Inna Mairo ta ɗan dakata tana duban fuskar Hakimi, wanda ya kafeta da ido yana jin dukkanin ƙaunarta da yake binnewa tsayin shekaru na neman fallasa kansu. Ya yi gyaran murya yana faɗin, "Mairo ba za ai haka ba, ke ce ƙarama kuma ke ce kika yi fushin da kika daina bibiyarsu sabida gujewa tozarci.Wanda hakan ba cikakkiyar hujja bace da zaki yanke zumunta da ƴan uwanki, ko gurin Allah baki da hujja Mairo don shi ya faɗi cewa ku sadar da zumunta koda ga waɗanda suka yanke muku ne. Don haka zamu je gareta ki durƙusa ki bata haƙurin ƙauracewa zuwa garesu da kika yi tsayin shekaru, ni kuma nayi miki alƙwarin zan bi miki hakkinki wajen hutumarta ta sanar damu aibunki ko wani abu mara kyau da kika taɓa yi mata a rayuwa da har kika cancanci ta nuna miki irin wannan ƙiyayyar ta son zuciya da take nuna miki." Hakimi ya dakata daga maganarsa yana jin ciwo da zafin irin yadda tsohuwar take treating ɗin Maironsa, wacce tun bayan rasuwar amininsa yake ɗawainiya da soyayyarta a zuciyarsa. Ba don ta jima da sanar masa har abada ta haramtawa kanta aure in dai shi ne zai zamo mijin ba, da tuni ya jima da mallakarta a matsayin matarsa. Inna Mairo da zuwa lokacin take kuka har da shashsheka, sai ta ja hanci tana magana cikin rawar murya ta ce, "Allah ya kaimu lokacin da zamu je ɗin,Allah kuma ya fisshemu tozarci daga gareta." Hakimi da ya ji daɗin kalaman Inna Mairo, sai ya saki murmushin jin daɗin amincewarta cikin sauƙi yana mai faɗin, "Madallah Mairamu! Allah ya yi miki albarka ya ƙara miki juriya da haƙurin fuskantar dukkanin jarabawa ta rayuwa. Allah ya raya mana Najma ya yiwa rayuwarsu albarka. Ba zaki nadama ba Mairo domin Allah yana tare da masu yawan haƙuri da yawan yin yafiya ga bayinsa da suka zaluncesu. Zamu tafi a ranar asabar mai zuwa idan Allah ya kaimu, domin ina fata ya kasance mun yi sa ar ganin shi Alhaji Kabeerun tunda ƙarshen mako ne da ƴan boko ke zama tare da Iyalansu." Inna Mairo ta kai hannu tana share fuskarta ta dubi Hakimi ta ce, "Hakane kam, Allah yasa muyi farar tafiya.Ubangiji ya duba gaba da bayanka ya kuma raya Iyali. Bamu da bakin godiya bisa ga hidimar da ake yi damu tsayin shekaru ba tare da gajiyawa ba,tabbas samun amini na gari irinka sai an tona.Don haka tsakaninmu daku duka kai da Iyalanka sai dai addu'ar fatan gamawa lafiya." Inna Mairo ta juya ta dubi yadda aminiyarta Inna Karima ke tayata matsar ƙwalla ta cigaba da cewa, "Karime a tayani sake yin godiya, Allah ya biyaku da gidan aljanna domin kuma kun kasance mataye nagari,waɗanda ke ƙarfafa zuciyar mazajensu da basu goyan baya wajen aikata alkhairy ba tare da kushe ko hassada ba.Tabbas ku ɗin abin a yabeku ne a kuma gode muku, musamman ke da kika zame masa jajirtacciyar uwar gidan da kike tsaye wajen ɗaurashi akan hanya madaidaiciya." Inna Mairo ta ƙarisa kalamanta cikin raunin murya sosai. Hakimi ya bita da kallo yana jin wani irin yanayi na mamaye zuciyarsa, yayinda Inna Karima ta kama hannun Inna Mairo ta riƙe tana faɗin, "Kome muka yi muku bamu faɗi ba Mairo, domin duk ɗan halak ba zai mance alkhairy ba. Marigayi Malam Mahmuda ya kyautata mana a lokacin yana raye, ya kuma hidimta mana da dukkanin iyawarsa. Don haka idan ma bamu duba bayansa ba tamkar munci amanar zumunta da ƙaunar da ya nunawa Hakimi da mu kanmu ne. Ki daina gode mana Mairo domin abinda ya dace muke yi, kuma muna fata kada Allah ya nuna mana lokacin da zamu gaza. Allah ya ƙara miki lafiya, yasa wannan tafiya da zaku yi ya zamo silar yayewar baƙin cikinki da damuwarki. Allah ya daidai tsakaninki da ƴan uwanki su gane cewa ke ɗin amanace a garesu, kuma baki da waɗanda suka fisu kamar yadda suma har duniya ta tashi basu da tamkarki. Domin kece jininsu da zasu nuna suyi alfahari dake bayan ƴaƴansu da suka fito daga jikinsu." Inna Karima ta kai ƙarshen maganar cikin nuna tsantsar kulawa ga Inna Mairo, wacce ke jinjina kai dukkanin kalaman Inna Karima na ratsa jiki da zuciyarta. Cikin yin ƙasa da murya Inna Mairo ke zubawa Inna Karima godia, tana mai yi mata fatan alkhairy duniya da lahira. Sai wajen tara da rabi suka yi sallama da Inna Mairo don komawa gida,bayan Hakimi ya aje mata ledar maganin da Auwalu ya siyo a cikin garin shika.Inna Mairo ta sake yin godia tana mai yi musu rakiya har bakin zaure bayan Najma ta fito daga ɗakinta tayi musu sai da safe.......✍🏻 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/2, 2:43 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *_Arewabooks@ayshadansabo_* *Paid book:500 08167768704* *Chapter 9* _Free page_ Duk yadda Najma taso su tattauna maganar da Hakimi ya yi na zuwansu kaduna Inna Mairo taƙi bata dama. Shigewarta ɗaki tayi sabida yadda take jin kanta na wani sarawa da matsanancin ciwo, ga idanunta da sukai masifan yi mata nauyi tamkar an ɗaura musu bulo. Najma tayi zugum zaune a falon tana jin hankalinta na sake tashi.Dukkanin jikinta na yin tsananin sanyi,domin ta tsani ganin Innarta a cikin hali na damuwa. Taja ƙafa ta nufi ɗakinta hawayen da take riƙewa na ɓalle mata, ta jima zaune a bakin katifarta tana rasa irin tunanin da ya kamata ta faro ma.Sake fitowa tayi ta nufi ɗakin Inna don ganin a wani hali take.A kwance ta sameta hawaye na bin fuskarta, hakan ya sanya Najma ƙarisawa da sauri bakin katifar tana faɗin, "Inna don Allah karki sanya damuwa a ranki!" Inna ta sake rintse idanunta, kafin tayi magana cikin rawar murya ta ce, "Najma bani ruwa da maganin da aka kawo in sha." Najma ta fice a guje ta ɗakko ruwa da maganin ta bai wa Inna.Ta zauna kusa da ita tana faman sharan hawaye kamar yadda Innar keyi. Sai da ta ga bacci ya fara ɗaukar Inna Mairo sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta.Nan ma ta jima bacci bai ɗauketa ba sabida damuwar da ke cinkushe a zuciyarta. A ɓangaren Inna Mairo kuwa ba bacci ne ya kwasheta ba, tayi wa Najma lamfa ne don ta je ta kwanta.Amma ba don wai da gaske baccin ne ya kwasheta ba. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, kwana tayi cikin tunani da damuwa mai yawa. Sai bayan ta samu da ƙyar ta sallaci asuba sannan bacci ya sace ta, hakan yasa bata farka ba sai wajen goman safe. Ta tadda har Najma ta gama tuyan ƙosai ta gyara ɗaki.Tausayin Najmar ya kama zuciyarta don tabbas tana wahala matuƙa da irin bautar da take yi, shiyasa dole damuwa ba zai bar zuciyarta. Bayan tayo wanka ta sanya kaya sai Najma ta gabatar mata da koko da ƙosai ta karya, ta sha magungunanta bayan ta gama karyawan ta kishingiɗa daga tsakar ɗakin. Misalin sha biyu na rana sai ga sallamar su Hanne da Luban gidan Hakimi. Najma ta taryesu cikin farin ciki, suka isa ɗakin Inna Mairo hannun Lubah ɗauke da kular wainar shinkafa, ita kuma Hanne nata hannun riƙe da kular miya. Suka gaida Inna Mairo tare da yi mata sannu da jiki, ta amsa cikin fara'a tana tambayarsu mutan gidan suka ce lafiya lau. Suka aje kular waina da haɗaɗɗiyar miyan taushe da Inna Karima ta yisa, suna mai sanar da ita cewa gashinan in ji Innarsu. Inna Mairo tayi godia suka nufi ɗakin Najma don sakewa suyi hiransu irin ta ƴan mata, waɗanda suka shaƙu da ƙaunar juna tun daga yarinta har grima. Inna Mairo ta buɗe kular wainar tana yaba kyawun da suyan ya yi ,don ya yi fari tar dashi abin sha'awa. Ganin yawan wainar zai ishe su har dare ma suyi taci, sai Inna ta sanar da Najma cewa kar a ɗaura komi da rana don wainar zai ishesu watakila ma har ya yi musu yawan da sai dai suba almajirai sadaka idan ya ragu.Kusan yini su Lubah suka yi a gidan Inna Mairo, hakan sai ya kawo raha da annashuwa hatta a zuciyar Inna Mairo. Wacce ta tashi cikin ƙarin damuwa da tunanin yadda zata bi Hakimi su fuskanci Gwaggon kaduna, alhali rabonta da garin kaduna da Gwaggon shekaru kusan bakwai kenan.Zuwansu Lubah da Hanne suna hira da raha a cikin ɗakinta,sai ya sanyaya zuciyarta sabida wasu daga cikin hirarrakinsu dake sanyata cikin nishaɗi. Sai can bayan la'asar suka bar gidan bayan Najma ta wanke kular waina da miyar da suka kawo don su wucewa Inna dashi. Ta dawo daga yi musu rakiya tana ji zuciyarta na sake cika da ƙaunarsu,domin sune farin cikinta kuma ƴan uwan da take wa kallon tamkar jini ɗaya suke da juna. Kamar wasa sati ya zago ya rage saura kwana ɗaya su Inna su wuce kaduna tare da Hakimi kamar yadda ya faɗi. Da dare misalin ƙarfe tara Hakimi ya aiko Auwalu ya sake jaddadawa Inna Mairo su shirya da wuri, domin yana so su isa da wuri sabida ba kwana zasu yi ba. Inna Mairo ta aika Auwalu ya sanar da Hakimi cewa zasu shirya da wuri idan Allah ya yarda, sannan ya faɗi masa ta gode da dukkanin ƙoƙarinsa. Bayan tafiyar Auwalu Inna Mairo ta dubi Najma da ta zuba mata ido don son jin ta bakinta, ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "Najma to kinji dai saƙon Hakimi, idan Allah ya kaimu sai ki shirya da wuri. Ƙosan ma ayi kwano guda ne kawai yadda zai ƙare da wuri, sabida kar mu makara shirin akan lokaci." Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa da kalaman Inna, ta buɗe baki cikin sanyin muryarta ta ce, "To shikenan Inna, Allah ya kaimu goben lafiya." Inna ta amsa da cewa, "Ameen ya Allah!" Daga haka suka dinga tattauna matsalar Gwaggon,Inna na sanar da Najma irin fargabar da ke damun zuciyarta. Washegarin ranar misalin tara da rabi na safe Najma ta tashi daga gindin murhu. Wanka ta faɗa a gaggauce bayan ta kammala gyaran wajen da tsakar gidan ma baki ɗaya.Lokacin da ta fito ta samu Inna zaune a falo tana shan koko da ƙosai, ta wuceta zuwa ɗakinta don shiryawa bayan tayi mata sannu. Cikin wata straight gown na wata atamfa mai kyau Najma ta shirya, atamfar na ɗaya daga cikin waɗanda ake aikowa Inna Mairo dasu duk sallah. Kalar a tamfar mint green ce da akaiwa adon ƙananun zane da red and black.Sosai kalar ya haska black skin ɗin Najma ya yi mata mugun kyau. Ɗinkin ya zauna a jikinta domin telan da ya ɗinka kayan yana da ƙwarewa sosai, kuma shi yake musu ɗinkin sallah tare dasu Lubah sai Hakimi ya biya kuɗin ɗinkin. Ta ɗauki ƙaramin madubi ta kalli kyakykyawar fuskarta a ciki, wanda ya yi fresh dashi babu ɗigon finfus ko makamancinsa akan fatar fuskar. Kamar ta share karta shafa komi akan fuskar,sai wata zuciyar ta bata shawarar shafa powder. Ta shafa kaɗan tare da zizara baƙin kwalli a fararen idanunta,cute lips ɗinta ta gogawa lip balm mai arha daidai ƙarfinsu. Ta sanya wasu ɗan kunni masu faɗi a kunninta, waɗanda suka ƙawata kyawun fuskarta da shigar jikinta. Turaren Safeer oud mai ƙaramin kuɗi ta fesawa jikinta,tana aje kwalbar turaren daidai da ƙwalla mata kira da Inna tayi. Hakan ya sanya ta fito da sauri falon tana amsa kiran da Innar ke kwaɗa mata. Inna Mairo da ke daga tsaye yafe da mayafi, ta sauke manyan idanunta akan Najma tana yaba irin kyawun da tayi. Cikin murya mai cike da nuna kula ta dubi Najmar ta ce, "Najma me kike yi ne haka har gashi Hakimi sun iso shi da Auwalu suna mota a waje, maza ki ɗakko mayafi mu wuce kar a cigaba da ɓata masa lokaci." Najma ta buɗe baki cike da mamakin isowar su Baba Hakimin ta ce, "To Inna bari nayi sauri, ai dama na kammala shirin." Daga haka ta juya zuwa ɗakinta don ɗakko gyalenta mai kyau irin masu arhannan daidai ƙarfin talaka.Ta yafashi tana zura takalminta flat mai tudun ƙasa kaɗan, ta fito daga ɗakin zuciyarta na cika da ɗokin tafiyar. Ita ce ta kulle gidan ta fice ta samu su Inna a cikin mota, ta buɗe back seat inda Inna ke Zaune ta shige tana mai gaida Baba Hakimi dake kame a gaban motar. Ya amsa da tsananin kulawa yana yi mata ba a da cewa sai da ta ja musu aji kafin ta fito. Najma tayi dariyar maganarsa tana duban ɓangaren driver seat ,ta gaida Yaya Auwalu kamar yadda suke kiran babban ɗan Hakimin. Ya amsa shi ma da kulawa yana mai kallon fuskar Najma ta jikin madubi, tayi masa kyau matuƙa da gaske hakan ya sanya yaji zuciyarsa na sake dilmiya a ƙaunarta da yaketa binnewa tsayin shekaru biyu zuwa uku. Ya san cewa Najma matar manyance kuma baya cikin irin choice ɗinta, domin bai tsaya ya yi zurfin ilimi irin wanda take da burin samun mijin aurenta dashi ba. Sannan shi bai taɓa sha'awar ya bar garin giwa ba, bare a sanya rai idan ya shiga birni zai yi wayewar da zai sake zurfafa iliminsa. Hakan yasa yake ta danne soyayyarta yana gayawa zuciyarsa cewa basu dace da juna ba shi da Najma, domin ita kallo ɗaya za a mata a ɗauka cewa wata wayayyace da ta samu ilimi mai zurfi.Sabida yadda suke da wayewar kai ita da ƙanninsa su Hanne.Sannan daidai gwagwardo suna shiga mai kyau koda ace na robobin atamfa ne, zaka gansu masu kyau a jikinsu, sam basu yadda da mugun shiga don suna zama a ƙauye ba. Tunda sun sama ilimin boko mai kyau,kuma da wayayyu sukai cuɗanya ba ƴan ƙauye ba a makarantar kwanar da sukai.Shiyasa kansu a buɗe yake sosai, hatta turanci sun jisa daidai gwagwardo, sai dai kawai ace basu yi zurfi sosai wajen iya speeking ba sosai. Ya tashi motar bayan Hakimi ya bashi umurni. Suka kama hanyar baro garin giwa zuciyar Inna Mairo cike da zullumi,sabida bata san irin tarban da zasu tarar daga Gwaggo ba. Musamman daya kasance a bazata zata gansu bata san da zuwansu ba, sannan zata ganta tare da baƙin da bata taɓa tunani ba. Da wannan zullumi da fargaban a zuciyar Inna Mairo, Auwala ke ta falala gudu dasu a mota har suka baro garin giwa baki ɗaya suka ɗauki hanya.Najma tayi shiru a motar tana faman saƙe-saƙe a zuciyarta, ita ma zuciyarta na cika da tarin fargaba da tsoran irin tarban da zasu samu daga wajen Gwaggon kaduna. Lokacin da suka shigo garin kaduna daga Najma har su Inna Mairo, sake baki suka yi suna kallon yadda garin ya sauya.Ko'ina ya sauyawa Inna Mairo sabida irin cigaba da gagarumin sauye-sauyen da garin ya samu,a sakamakon samun nagartaccen shugaban da ya gyara birane da ƙauyakun jihar.Inna Mairo ce ta dinga yiwa Auwalu kwatance har suka isa unguwar Rimi GRA,bayan sun sha matuƙar wahala sabida gaba ɗaya garin kaduna ya sauya mata cikin shekaru bakwai da tayi bata tako ƙafafunta ciki ba. Da ƙyar ta iya gane street ɗinsu Yaya Kabeeru,suka isa ga tangameman gidan nasa da ke a farko-farkon shiga street ɗin. Daga bakin wani ƙaton black gate motarsu Hakimi ya faka, Auwalu ya danna horn har sau biyu amma shiru kake ji babu alamun za a buɗe gate ɗin. Hakan ya sanya ya kashe motar sukai zugum a ciki suna jiran ganin abinda zai faru.Zuwa kamar sakan biyar aka buɗe ƙaramar ƙofar dake manne da jikin gate ɗin shiga gidan, wani baƙin buzu ya danno kansa waje yana mai sauke idanunsa akan motar Hakimi samfurin 406. Ya tako zuwa wajen motar ya yi tsaye, cikin hausarsa da bata fita sosai yake tambayarsu wajen wa suka zo? Hakimi ya waiwaya yana duban Inna Mairo, hakan ya sanya ta gane abinda yake nufi.Ta buɗe baki ta ce da buzun, "Ka sanar cewa Mairo ce daga garin giwa tare da Hakimin garin." buzun ya juya ya koma daga ciki tare da rufo ƙofar gam. Inna Mairo ta sauke wani numfashi zuciyarta na cigaba da dakan lugude, yayinda ita ma Najma tayi tsumu a cikin motar tana taya Inna Mairo shiga zullumi. Mintuna biyar suka wuce shiru, sai daga bisani suka ga an wangale ƙaton gate ɗin gidan buzun na musu alamu da hannu akan su shiga da motar ciki. Hakan da Auwalu ya gani ya sanya shi tada motar tare da danna hancin motar zuwa cikin wawakeken harabar compound ɗin gidan. Tun shigar motar cikin compound ɗin, daga Najma har Hakimi da Auwalu sake baki suka yi suna ba idanunsu abinci,domin gini ne da ya gama tsaruwa matuƙa da gaske.Kallon ko'ina suke cike da birgewa yayinda Hakimi da Najma tunaninsu ya tafi iri ɗaya, wajen mamakin yadda mai kuɗi kamar wannan, amma ya iya barin ƴar uwarsa a ƙauye cikin wahala da ƙuncin rayuwa. Auwalu ya isa ga parking space ɗin gidan mai ɗauke da manyan motoci har huɗu ya faka tasu motarsu daga waje-waje. Duka suka fito kusan a tare, suna sake baza ido suna kallon kyawu da tsarun gidan Alhaji Kabeer Dukku. Adamu driver da tutir yana gidan sabida jiran aike ko fita da Gwaggo unguwa, shi ne ya hango cewa Inna Mairo ce da ɗiyarta suka iso garin. Ya taho cikin hanzarinsa yana musu barka da isowa cike da tsantsar farin cikin ganin Inna Mairo a garin.Shi ya yi musu jagora zuwa sashin Gwaggon kaduna da ke tsakiyar manyan apartment guda uku dake cikin gidan. Hakimi da Auwalu dai na tsaye jingine a jikin motarsu,zasu jira har a basu masauki ko izinin shiga daga ciki tukunna. Najma da Inna Mairo suka dinga bin bayan Adamu har zuwa sashin Gwaggo, wanda Inna Mairo ta dinga ganin tamkar an sake sauya komi ne na gidan sabida yadda gidan ke samun gyara duk ƙarshen shekara sai anyi masa wasu sauye-sauyen dake sake ƙawata shi. Cikin wata iriyar murya wacce zullumi da rashin karsashi suka sake kassara amonsa, su Inna Mairo suka rafsa sallama daga baƙin ƙofar shiga main parlor ɗin Gwaggo.Daga ciki muryar wata ta amsa musu sallamar tare da basu izinin shiga, hakan ya sanya suka kutsa kai cikin falon bakin Inna Mairo ɗauke da addu'ar samun nasara akan Gwaggo tare da fatan kada Allah ya bata ikon wulaƙantasu ko Hakimi.Najma dai zare idanu kawai take yi mamaki da wani irin abu mai girma na sake mamaye zuciyarta, ta kasa gasgata cewa ɗan uwan Inna ne keda wannan aljannar duniyar amma ya iya wofintar da rayuwar Innarta. Suka samu waje cikin kujerar 2 seater mai asalin kyau da nauyin kuɗi suka zauna, Inna Mairo ta gaida matar da suka samu a zaune cikin falon. Matar ta amsa da fara'a tana musu lale da zuwa tare da sanar dasu yanzu Gwaggon zata fito. Bata gama rufe baki ba sai ga Gwaggon ta fito daga cikin wani cooridor. Idanunta ta sauke akan Inna Mairo kamar yadda Inna Mairo ita ma ta sauke idanunta akan Gwaggon kaduna,tana mai yi mata cikakken kallo.Cikin nutsuwa Hajiya Gwaggo ke takowa zuwa cikin falon dukkanin jikinta na yin wani irin sanyi da ganin yadda Mairo duk ta lalace. Har ta ƙariso cikin falon ta kasa ɗauke idanunta akan Inna Mairo da ƴarta Najma, wacce Gwaggo ke hango tsananin kamanninta da Mairon. Sannan baƙin beauty face ɗinta ya tuna mata da Malam Mahmuda, mutumin da ko kaɗan bata taɓa jin ƙaunarsa a zuciyarta ba har ya koma ga mahaliccinsa. Yau ga ɗiyarsa da babu inda ta baro baƙin fatarsa a gabanta,tana kuma jin wani irin mutuwar jiki na kassara zuciyarta.Sabida wani irin kamanni na jini ta hango kwance akan fuskar Najma,wacce tayi mata kama da jikarta Nasreen......✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/3, 11:01 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshaɗansabo*_ *Chapter 10* _Free page_ Gwaggo na zama akan kujera Najma da Inna Mairo suka yi saurin zamowa ƙasa suna kwasan gaisuwa. Gwaggo ta zubawa fuskar Inna Mairo ido tana kallon yadda duk ta dishe ta fita hayyacinta.Ta amsa gaisuwarsu da fara'a, tana mai zubawa fuskar Najma idanu. Cikin sanyin murya Gwaggo tayi magana idanunta akan Inna Mairo ta ce, "Mairamu idonki kenan,dama kina sane damu a raye kika juya bayanki daga zuwa inda muke? Wani abu akai miki da har kika yi irin wannan zuciyar da kika zaɓi daina kusantar inda muke?" Inna Mairo ta ɗago a firgice sabida jin irin kalaman da suka fi dacewa da aka kirasu dana rainin hankali, da ke fitowa daga bakin Gwaggon kaduna. Wani abu mai nauyi ya taso ya danne zuciyarta, ta girgiza kai da sauri cikin harɗewar harshe ta ce, "Gwaggo kuyi haƙuri,na san nayi kuskure sai dai banyi don son raina ba, sai don ina ganin hakan shi ne kwanciyar hankalina da naki." Ta kai ƙarshen maganar da tsananin rawar muryar da ya sanya Gwaggo kafeta da ido tana jin wani irin yamm...! A cikin jinin jikinta. Tuni matar da ke zaune a falon ta kama gabanta, falon ya rage daga Gwaggo sai su Innar kaɗai. Inna Mairo ta ɗaura da faɗin, "Idan ba zaki damu ba Gwaggo tare muke da baƙi kamar yadda na ce mai gadi ya sanar.Don Allah a basu masauki don mun barsu ne a jingine jikin motar da muka taho." Gwaggo dake sauraren Inna Mairo sai ta jinjina kai ta ce, "Badamuwa bari a kaisu ɗakin baƙi." Daga haka ta miƙe tana sake nufan hanyar wani corridor inda matar ɗazu tabi. Ba a ɗauki lokaci ba ta dawo tare da wata matashiyar budurwa, da alamu ƴar aiki ce hannunta ɗauke da wani tray a hannu. Gwaggo ta zauna a inda ta tashi tana faɗin, "Na sanya a kaisu ɗakin baƙi, a kuma kai musu ruwa da lemu kafin a sauke girkin rana." Ta kai ƙarshen maganar lokacin da wannan matashiyar mai aikin ta aje tray ɗin da ke ɗauke da manyan juice na kwalaye da ruwan roba a gaban su Inna Mairo.Ta risina ta gaida su tana miƙewa ta bar wajen cikin gaggawa, alamun sam basu saba aje abu su tsaya kallon baƙo ko yin tsirku ba. Najma tabi bayan budurwar da kallo kafin ta dawo da dubanta kan Gwagggo n kaduna, wacce ta gama yin kyau cikin koriyar atamfar super holland da ke sanye a jikinta. Gaba ɗaya hutu da jin daɗin rayuwa gamida kwanciyar sun gama ratsata, babu mai dubanta ya ce ta doshi shekaru saba'in da takwas a duniya.Sabida yadda komi na jikinta yake ƙyas gunin sha'awa, fatarta ce kawai ta fara yin tauri na nuna alamun girma ya kamata.Gwaggo ta sake duban Inna Mairo dukkanin mafarkan da take yawan yi da Abbansu na dawo mata. Wasu irin mafarkai da ke birkita lissafinta da jefa zuciyarta cikin zullumi, don duk lokacin da zata yi mafarkin shi take gani riƙe da hannuwan Mairo yana tahowa gareta. Sai dai da zaran ya kusa isowa inda take sai ta dinga jiyo wani irin sautin murya daga bayansa ana faɗin, "Karka isa gareta domin ta kasance azzuluma bai yanke zumunta da raba tsakanin ƴan uwa." Sai taga Abbah ya juya cikin fushi Mairo na kuka tana waigowa baya tana kallon inda take. Ta sauke wani irin numfashi tana buɗe baki ta ce, "Mairo ku sha ruwa da lemu kuyi sallah kafin a kammala girki sai kuci ko?" Inna ta jinjina kai tana duban Najma ta ce, "Najma sha ruwa, ni kam bari na fara da gabatar da sallah tukunna." Gwaggo ta nuna wa Inna Mairo hanyar da zai shigar da ita zuwa ɗakin baccinta tana mai cewa, "Shiga daga ciki kiyi sallar Mairo, bari in aika a sanar da Zainab zuwanku. Kabeeru shi ma yana gari amma bada jimawa ba ya fita wajen wani ɗauri aure da aka gayyacesa, amma zan yi kiransa daga can ya wuto gida tunda gaki Allah ya kawoki a lokacin da nake buƙatar hakan." Gwaggo ta dakata da maganar ganin Inna Mairo ta shige corridor ɗin da zai sadata da ɗakunan baccinta. 3 bedrooms ne daga cikin corridor ɗin masu ɗauke da toilet a cikinsu,sannan duka akwai kayan alatu da aka zuba masu inganci da nauyin kuɗi. Inna Mairo ɗakin da ta gani a buɗe nan ta nufa, ta lalubi inda toilet ɗin yake ta shiga don ɗauro alwalar. Daga can falo kuwa Gwaggo ce ta dubi Najma ta ce, "Sannu Najmatu, kin zama budurwa sosai ina fata kin samu yin ilimi boko?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Na kammala secondary school ɗina, daga nan ne dai ban samu cigaba ba sai islamiya da nake zuwa,shi ma mun kammala ajin ƙarshe an yaye mu." Gwaggo ta gyaɗa kai idanunta har lokacin akan Najma suke, tana ganin kamar da Inna Mairo take magana a lokacin da take budurwa tamkar Najmar. Amma black beauty face ɗin Najma na tunasar da ita cewa wannan kyakykyawar budurwar ɗiyar Mahmuda ce bata Malam Muhammadu ba. Ta cigaba da yi mata tambayoyi game da zamansu a ƙauye, tana kuma bincikan wane ne ya ɗauki nauyin karatun Najmar? Najma da tarin baƙin ciki da jin haushin Gwaggo ke ƙaruwa a zuciyarta, sai ta dinga bata amsa a gajarce cikin rashin sakin fuska da walwala. Fitowar Inna Mairo ya sanya ita ma Najma ta miƙe ta shige don zuwa tayo nata sallar, Inna Mairo ta ƙariso ta zauna a inda ta tashi. Gwaggo ta miƙe ta fice don zuwa ta aika Sabeera mai aikinta ta yo mata kiran Hajiya Zainab, don bata faye zuwa sashinsu da kanta ba sai da dalili. Ita dai Hajiya Zainab ɗin da Yaranta ne ke shigowa duk safe su gaidata kafin su wuce school, idan sun dawo zuwa yamma ko dare Nasreen da ta fi shiri da Gwaggo ta kan shigo mata hira ita ma. Bayan ta aika Sabeera kiran Hajiya Zainab, sai ta bai wa Tabawa umurnin a shirya abinci a kai wa su Hakimi dake daga can ɗakin baƙi dake nan cikin part ɗinta. Suma su Inna abincin aka shirya musu a table, amma sai Gwaggo ta bada umurnin a sauke musu daga ƙasa don ba kowa ke jin daɗin cin abinci a sama ba.Tare da Gwaggo suka haɗu a tsakiyar falonta suka ci lafiyayyan shinkafa da miyar kaji,ga kuma haɗaɗɗyar haɗin salad daga gefe. Sosai girkin ya yiwa Najma daɗi matuƙa, musamman haɗin salad ɗin da bata taɓa cin irinsa ba.Suna kammala cin abincin Hajiya Zainab na shigowa ɗakin cikin tsananin fara'a da farin cikin ganin Inna Mairo.Cike da zallar farin ciki Hajiya Zainab suke gaisawa da Inna Mairo, idanunta akan Najma da fuskarta ke haskawa da ƙaramin murmushin ganin yadda Hajiya Zainaba ɗin ke nuna murnarta na ganin Inna Mairo. Ta risina ta gaida Hajiya Zainab ɗin cike da ladabi.Hajiya Zainab ta amsa da tsantsar kulawa tana yaba kyawu da nutsuwar da Najma ke dashi. Ta maida dubanta ga Inna Mairo tana faɗin, "Yanzu Najmar ce ta zama budurwa sosai haka? Koda yake ga tsararta can Nasreen ita ma ta zama budurwa har ta shiga aji biyu a jami'a." Inna Mairo tayi murmushi tana faɗin, "Ai girman Yara mata ba wuya Hajiya Zainab,musamman idan suna samun ingataccen abinci mai gina jiki." Gwaggo dake saurarensu ta dubi Inna Mairo tana faɗin, "Mairamu leƙa wajen baƙin idan sun kammala ki shigo dasu nan falo mu gaisa." Inna Mairo ta amsa da cewa, "Tuh Gwaggo." Ta miƙe ta fice daga ɗakin Inna zuwa waje tana raba idon gano inda ɗakin baƙin yake. Daga can hanyar fita part ɗin ta hango ɗakin,ta isa tana mai yin sallama daga baƙin ƙofar shiga. Auwalu da Hakimi suka haɗa baki wajen amsa sallamar, Inna Mairo ta sanar dasu cewa su shigo daga ciki inji Gwaggo. Tana tsaye daga bakin ƙofan suka fito, tayi musu jagora har zuwa falon Gwaggon kaduna. Cikin mutunci da girmamawa Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa suka gaisa da Gwaggo da Hajiya Zainab, bayan sun kammala gaisawa da tambayar lafiyar Iyali sai Hajiya Zainab ta janye Najma zuwa sashinta don su bai wa su Gwaggo damar tattaunawa. Shi ma Auwalu Hakimi sallamarsa ya yi ya ce ya koma ɗakin baƙi ya jira shi a can, don basu damar tattaunawa da Gwaggon kaduna da Inna Mairo. Gwaggon kaduna dukkanin jikinta a sanyaye yake lokacin da Hakimi ya buɗe zaman da addu'a tare da farawa da yi musu nasiha mai ratsa zuciya. Ya dubi ɓangaren da Inna Mairo ke makuye kanta a ƙasa ya ce, "Mairo ina so ki bai wa Gwaggo haƙuri akan yadda kika yi zuciya dasu kika yanke zumuntar da ke tsakaninki da ƴan uwanki, ta hanyar daina bibiyarsu da kawo musu ziyara." Inna Mairo ta ɗago manyan idanunta ta saci duban Gwaggo tana mai farawa da faɗin, "Ki gafarceni Gwaggo, tabbas nayi kuskure kuma daga bisani abin yana damuna domin na kasa cire ƙawazucin ƴan uwana a cikin zuciyata.Ina roƙo ki yafe mini akan dukkanin abinda ki ke zaton da gangar nayi miki Gwaggo, wallahi dukkanin abinda ya faru ya faruwa bisa ƙudurar Ubangiji.Banki Fahad don ya kasance jininki ba sai don haka ALLAH Ya NUFA ba shi ne zai zamo miji a gareni ba.Sannan ba laifin Baban Najma bane shi ma,domin shi kansa Abbah ne ya kira shi ya ce ya bashi aurena.Ki yafe mana Gwaggo ki sassauta mini irin ƙiyayyar da kike mini ko xan samu sassauci cikin rayuwata...." Inna Mairo ta kasa kaiwa inda take so takai a kalamanta,dalilin kukan da ya taho mata kai tsaye ya hanata ƙarisa kalaman da ta faro. Gwaggo da dukkanin jikinta ya gama sanyi, ta ɗago ido ta aza akan Mairo tana jin wani irin abu mai kama da nadama na ratsa zuciyarta. Murya can ƙasa ta soma da faɗin, "Mairo ki gafarceni, tabbas banyi miki adalci ba ban kuma yiwa kaina ba,domin na kasa cika wasiyyar Malam a kanki. Na biyewa son zuciyata ne kawai wajen raba zumunci da ƴan uwantaka,alhali nafi kowa sanin kinfi kowa buƙatar mu cikin rayuwarki domin mu kaɗai ne tilashinki.Nayi nadama Mairo tun daga sanda na fara wasu irin mafarkai da mahaifinku....Komi ya wuce Mairamu kamar yadda nake fata zaki yafe mini don ni ce mai laifi bama ƴan uwanki ba, sabida ni ce nayi miki katanga dasu na kuma hana ki cigaba da raɓanmu don na san tabbas da kin cigaba da zuwa garemu zuciyar Kabeeru dole ta amsheki,ya kuma cika wasiyyar mahaifinku ya kula dake.Ba sai na tsaya tone-tone ba Mairo, ki yi mini afuwa ki manta baya mu fuskanci gaba, don gyara abinda ya rushe." Gwaggo ta kai ƙarshen maganar tana duban Hakimi da Inna Mairo wacce ke kuka da hawaye. Ta cigaba da roƙon Inna gafarar abinda ta aikata mata na ƙiyayya a baya, tare da basu labarin irin mafarkan da take tayi da Abbah da Inna Mairon. Hakimi ya ɗaura da yiwa Gwaggo nasiha akan illar abinda ta aikata na son raba zumunci da nesanta tsakanin ƴan uwan juna. Wanda hakan babban kuskure ne wanda shari'a tayi tir da masu aikatashi, sannan aka yi musu albishir da azaba mai tsanani idan suka mutu a akan turban aikata irin abinda ta aikata ɗin. Gwaggo hawaye kawai take sharewa, dukkanin nasihun Hakimi na ratsa zuciyarta tare da kassara gaɓɓan jikinta. Lokacin da ya kammala nasiharsa tare da sanar da Gwaggo buƙatarsa na son ta rungumar Inna Mairo tamkar ƴar cikinta, sai ya rufe da addu'ar Allah ya haɗa kawunansu Inna Mairo da ƴan uwanta. Gwaggo ta share hawaye tana duban sashin da Inna Mairo take ta fara da faɗin, "In Sha Allah! Na ɗauki nasiha da shawarwarinka Hakimi, sannan ina baka tabbacin daga yau komi zai sauya don ba zan so na mutu da hakkin cigaba da ƙuntata rayuwar Mairo ta hanyar rashin kyautatawa ba. Kamar yadda Allah bai bani ƴa mace ba ina so a yanzu na riƙeta a matsayin ita ce makwafin ƴa macen da bansamu ba..... Ta ɗan dakata kaɗan tana duban yadda Inna ke share hawaye ta cigaba da cewa,"Kiyi haƙuri Mairo, ban baki wannan matsayin a lokacin da ya dace ba sai a lokacin da tsufa ya fara kamani.Lokacin da hakan ba lallai ne ya yi miki daɗi a zuci ya kuma wanke baƙin cikin dana cusawa rayuwarki ba, sai dai koma yaya ne ina so ki amshi wannan sabon matsayin don bani ikon kyautata rayuwarki da ta Najma ko yaya ne." Ta dakata tana duban yadda Inna Mairo ke faman gyaɗa kai hawaye na zarya akan fuskarta. Da ƙyar ta iya fisgo kalaman bakinta ta ce, "Na baki dama Gwaggo, sannan ina godiya da sabon matsayin da kika bani. Allah ya bani ikon yi miki irin biyayyar dasu Yaya ke miki koma na ninka.Allah ya jiƙan Abbah da Malam yasa suna cikin aljanna maɗaukakiya, Allah kuma ya haskaka makwancinsu tabbas da suna raye da yau sun yi alfahari da zuwan wannan ranar da suka sha kwaɗaita mini zata zo gareni. Amma gashi ranar ta zo a lokacin da ƙasa ya jima da rufe idanunsu...." Inna Mairo kuka ya kwace mata ta kasa ƙarisa kalamanta, ta dinga kukan sosai na tsananin zafin rashinsu Abbah da Malam Mahmuda da tayi.Gwaggo da Hakimi jikinsu ya sake yin sanyi, tausayin Inna Mairo ya dinga kassara zuciyar Gwaggo matuƙa da gaske. Suka haɗa baki da Hakimi wajen rarrashin Inna Mairo da kalamai na kwantar da hankali,har suka samu ta tsaida kukan da take yi ɗin. Gwaggo ta ɗaga wayarta a karo na biyu ta kira layin Alhaji Kabeer Dukku don jin ko ya kusa ƙarisowa gidan? Sabida da sukai waya da farko ya shaida mata cewa ba zai jima ba zai ƙariso gida daga wajen ɗaura auren da ya halarta a nan cikin garin kadunan. Ta aje wayar lokacin da ya bata tabbacin yana dab da ƙarisowa gidan nasa. ****** Daga can ɓangaren Hajiya Zainab kuwa, tasa Najma tayi da hira tana tambayarta akan abinda ya shafi karatunta. Najmar ta ɗan saki jiki da ita tana bata amsa a takaice,gefe guda kuma gaba ɗaya ta shagala a kallon tsaruwar falon Hajiya Zainab ɗin. A cikin zuciyarta take kisima suko wani irin dukiya suke dashi haka? Domin a falon kaɗai aka barka zaka san cewa ba ƙananun dukiya aka kashe ba. Kyakykyawar budurwa mai shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ce ta fito daga wani corridor. Ta sauke idanunta akan Momynsu da baƙuwar fuskar da ta gani tare da Momyn. Sannu a hankali ta cigaba da ratsowa zuwa cikin falon, idanunta kyam! Akan black beauty face ɗin Najma. Najma ita ma idanunta ne ya kai kan kyakykyawar farar budurwar dake tunkaro inda suke zaune, sai ta samu kanta da kasa ɗauke idanunta daga kan budurwar domin gani tayi suna satan kamanni da Innarta. Sai dai kawai wannan ɗin a yanzu tafi Inna fari da kuma dogon hanci, amma hatta yana yin tafiyarsu iri ɗaya ne dana Inna Mairo. Budurwar ta ƙariso cikin falon tare da samun waje kusa da Hajiya Zainab ta zauna tana faɗin, "Momy sannu da hutawa,baƙuwa muka yi ne?" Momy Hajiya Zainab sai ta dubi Ƴarta da murmushi akan fuskarta ta bata amsa da cewa, "Nasreen wannan ba baƙuwa bace, she's ur sister, ita ce Najmar dana taɓa baki labarinta na ce daughter ɗin Gwaggonku Mairo da suke zama a ƙauyen giwa kin tuna?" Wacce aka kira da suna Nasreen tayi saurin gyaɗa kai tana duban Najma sosai ta ce, "Wow! She's very black beauty Momy, and sunanta kuma ya dace da kyawunta. Nice to meet u sis!" Ta kai ƙarshen maganar tana sake ƙure kallonta akan Najma, wacce ta sakarwa Nasreen murmushi ita ma. Cikin sanyin muryarta kuma ta ce, "Nice to meet u too sis, thank u!" Ba Najma ba hatta Momy tayi mamakin yadda Najma tayi wa Nasreen magana da harshen turanci,don sunyi zaton koda tana ji ba lallai ta iya maida martanin magana da yarenba.Duba da cewa a ƙauye ta tashi, koda ace tayi karatu ba lallai ta iya turanci ko ta ji sosai ba sabida yadda ake faɗin lalacewar makarantun gwamnatin karkara da babu wasu ƙwararrun malamai.Cikin tsananin farin ciki Momy ta dubi Najma tana faɗin, "Very good daughter! Ashe dai makarantun karkara ma na ƙoƙari wajen koyar daku harshen english. Da alamu idan kika sake samun wanda zai koyar da ke harshen ba ƙaramin ƙwarewa zaki yi wajen iya speeking da shi ba." A kunyace Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Na gode Momy!" Ta faɗi sunan yadda ta ji Nasreen ta kira Hajiya Zainab ɗin dashi. Nasreen ta dubi Najma tana jin ƙaunarta na kama zuciyarta, cikin muryarta mai cike da iyayi irin na ƴan boko take tambayar Najma inda ta tsaya da karatunta. Najma ta sanar da ita cewa iyakarta secondary school, shi ma ba a garin giwa suka yi ba a wata makarantar ƴan matane dake garin basawa. Cikin nutsuwa da sakin fuska Nasreen da Momy suka dinga jan Najma da hira don ta ɗan sake dasu. Momy ta sanya an kawo mata tarin snacks da dambun nama an tasa mata a gaba, ga kuma lemuka kala har biyu na gwangwani an aje mata. A kan kunnuwarta kuma Momyn ta bai wa mai aikinta umurnin kai wa su Inna suma snacks da dambun naman, haka kawai sai Najma ta ji matar ta shiga ranta ta kuma kwanta a zuciyarta matuƙa da gaske. Don yanayinta da irin yadda take mu'amala da hatta masu aikinta zai baka tabbacin mace ce ita da tasan darajar mutunta ɗan adam! Sam bata fito a cikin irin matan masu arziƙin dake taka talaka suna wulaƙantashi ba. Sai da Alhaji Kabeer Dikku ya iso gidan ne Najma ta sulale ta koma sashin Gwaggo bayan ta gaida shi ya amsa da sakin fuska. Shi ma babban rigarsa da ta damesa a jiki kaɗai ya yarɓar akan kujera ya fice zuwa sashin Gwaggon. A can ya samu mai girma Hakimi da Inna Mairo suna ta hira da Gwaggo gunin sha'awa.Najma na daga gefe guda ta maida dukkanin hankalinta akan kallo TV, wanda yake a kunne an saita shi akan tashar Arewa24. Sallamar Alhaji Kabeer Dukku suka amsa yana mai ƙarisowa cikin falon ya zauna kusa da Gwaggo, idanunsa akan tilon ƙanwarsu Mairo ya saukesu yana mamakin ganin yadda ta lalace tayi duhu. Wani abu yaji mai tauri ya danne zuciyarsa, don ko kaɗan bai jin daɗin hakan a ransa ba. Bayan sunyi musabaha da Mai girma Hakimin giwa, sai ya maida kai wajen duban Inna Mairo tare da amsa gaisuwar da take masa cike da girmamawa. Najma sake gaida shi tayi tana mai miƙewa ta fita waje don basu waje, ba tare da ta san inda zata dosa ba kuma. Tunanin ya tsaya akan ta je ɗakin baƙi wajen Yaya Auwalu, sai kawai ta nufi hanyar wajen kanta tsaye tana mai rafsa sallama lokacin da ta isa ƙofar ɗakin.......✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/3, 11:27 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_ *Paid book:500* *Chapter 11* _Free page_ Auwalu ya amsa sallamar Najma yana mai bata izinin shiga ɗakin.Ta shiga ta samu wajen zama bisa kujerar da ke nesa da shi,ta dubesa da murshi akan fuskarta ta ce, "Sannu da hutawa Yaya Auwalu, an barka kai kaɗai kana ta jira shiyasa na ce bari in zo in tayaka zama kafin su Baba Hakimi su gama magana da Kawu Kabeeru. Auwalu ya aza mata idanunsa da ke cike da zallar ƙaunarta yana faɗin, "Kin kyauta Najma, dama duk zaman ni kaɗai ya dameni." Daga haka ya fara janta da hira yana mai jin tsananin nishaɗi a zuciyarsa. Daga can ɓangaren Gwaggon kaduna dasu Inna Mairo kuwa, Baba Hikimi ne kewa Alhaji Kabeeru Dukku nasiha mai ratsa zuciya. Yana mai tunasar dashi illar yanke zumunta da cin amanan ƴan uwantaka, domin tabbas sunci amanar zumunci da ƴan uwantaka akan yadda suka wofintar da Inna Mairo. Ya ɗaura laifin baki ɗaya akan Alhaji Kabeer yana mai sanar dashi cewa, "Amatsayinka na babban Yaya a garesu, kamata ya yi ace lokacin da ka kula cewa Mairo ta daina zuwa inda kuke wajen Gwaggo ka bincika da kanka ka gano miye matsalar, me kuma akai mata ko ke tayi da ta yanke hukuncin nisantarku da mahaifiyarku? Amma sai kayi biris ka cigaba da biyewa son zuciyan Iyayenmu mata, waɗanda dama sune ke assasa wutar irin waɗannan rashin jituwar da ke faruwa tsakanin ƴan uba.Domin kaso casa'in cikin ɗari na lalacewar zumunci a gidaje, Iyayenmu mata ne ke jagorantarsa, ba kuma sabida komi ba sai biye son zuciyoyinsu da mummunar kishin da ke rufe idanunsu. Idan ba anyi sa a da jajirtaccen uba mai sanya ido matuƙa da gaske ba, sai ka ga kafin kace kwabo sun raba kan ƴan uwa tare da jefa ƙiyayyar juna a zukatansu.Wanda wannan babban kuskure kuma babban zunubi, domin Ubangiji ya yi tir da bawan da ke yanke zumunta tsakanin ƴan uwan juna.Kana da laifi matuƙa da gaske wajen yin biris da lamuran Mairo, alhali kai ka fi girman hakkin kulawa da ita, sabida babban Yaya makwafin uba yake.Amma kai kayi watsi da amanar da Abbanku ya damƙa maka na riƙeta da amana ku kuma maye mata gurbinsa..... Hakimi ya ɗan dakata domin bai wa Yaya Kabeeru damar magana.Yaya Kabeerun da ya yi shiru yana mai faɗawa duniyar tunani da nadama, sai ya ɗago manyan idanunsa ya ɗaura akan Inna Mairo yana faɗin, "Ki gafarceni Mairo tabbas mun yi kuskure, sai dai fatan kada Allah ya maimaita.Sannan kema kina da kaso mai yawa wajen aikata kuskure Maryam, don bai kamata ace ko wani irin abu Gwaggo ke miki zaki iya yin zuciya ki daina zuwa inda take ba, koda ace ita ce ta buƙaci hakan da kanta.Domin su Iyaye ba a fushi dasu sai dai ayi ta binsu ana rarrashi da kwantar da kai har su gano kuskuransu.Amma ke sai ki ka nuna cewa tabbas ba ita ce ta kawoki duniya ba, domin da Inna ce ke raye kome take miki ai ba zaki iya daina zuwa gareta ba.Don haka kema kinyi kuskure bana buƙatar a gaba ki sake aikata makamancin hakan. Ki yafe mana baki ɗayanmu kuskuren da muka aikata wajen wofintar dake, alhali munfi kowa kusanci dake kuma mu ya cancanta mu riƙe ragamar rayuwarki a lokacin da kika rasa miji da mahaifi, amma ba muyi hakan ba duk da cewa Allah ya bamu arziƙi da damar yin hakan. Ki yafe mana wannan babban kuskuren Maryam, In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba.Zan yi amfani da bakina wajen roƙawa Ali gafararki shi ma, kafin ya zo ya roƙa da bakinsa idan yazo gari tunda a yanzu ya dawo ƙarsar yana can da Iyalinsa a garin Lagos." Inna Mairo ta jinjina kai tana sake share hawayen da ke zubo mata,wanda bana komi bane na farin ciki ne da Allah ya nuna mata wannan ranar da take zaune gaban Gwaggo da Yaya Kabeeru suna roƙon afuwa a gareta.Tabbas ta sake gasgata cewa mai haƙuri shi ke da nasara,sannan babu abinda ke dauwama a duniya walau jin daɗi ko akasin hakan. Baba Hakimi ya jima sosai yana nusar da Gwaggo da Alhaji Kabeer illar abinda suka aikata tare da sanar dasu lalurar da ta kama Mairo, duk kuma a sanadiyyar baƙin ciki da ƙuncin rayuwa ne da suka jefa zuciyarta a ciki. Don ba za a ce rashin ci ko sha ne ya sababba mata shiga ƙunci da yawan tunanin da har ya sanya ta kamu da cutar hawan jini ba, sabida iyakan ƙoƙari yana yi dasu wajen ganin basu nema abin ci ko abin sha da kuɗin cefane sun rasa ba. Illar ƙiyayyar Gwaggo gareta da kuma juya mata baya da suka yi ya janyo mata shiga halin ƙunci da yawan tunani. Jikinsu Gwaggo ya yi mugun sanyi, tausayin Mairo ya sake kamasu musamman Alhaji Kabeer da har wani ƙunci da kunyar Inna Mairo ya dinga ji. Ya sake bai wa Mairo haƙuri tare da yi mata albishir da cewa komi ya wuce a yanzu, don ba zasu sake barinta ba. Hasalima ta sanya a ranta ta dawo hannunsa kenan da zama ba za ta koma ƙauye ba ita da ƴarta, sai dai kawai su je suyi bankwana da mutanen garin su dawo.Inna Mairo ta dubi Yaya Kabeeru fuskarta na bayyana tsananin mamakin kalamansa, domin ba tayi zaton hakan ba cikin gaggawa. Kafin ta iya cewa komi ko Hakimi ya ce wani abu, Gwaggo ta rigasu da faɗin, "Tabbas Mairamu ba zaki koma ba kun zo kenan, muna godiya da tarin karamci da ƙaunar da Mai girma Hakimi da Iyalinsa suka nuna muku. Tabbas Hakimi ka cika amini na ƙwarai, kuma wanda yasan girman halacci a rayuwa. Mairo dawowarta garemu baki ɗaya shi yafi dacewa a yanzu, domin hakan ne kawai zai sake bamu damar kusanci da assasa ƙaunar juna a tsakaninmu." Mai girma Hakimi ya jinjina kai yana jin wani abu mai nauyi na son danne zuciyarsa. Cikin murya marar amo yake faɗin, "Alhamdulillah! Da wannan hukunci naku Hajiya Gwaggo, duk da cewa ni da dukkanin ahalina wannan hukunci ba zai mana daɗi ba. Amma a zahirin gaskiya hakan shi yafi dacewa, Mairo ta dawo ƙarƙashin kulawarku ko don ku kula da lafiyarta da samar mata magungunanta akan kari.Don a can ɗin wani lokacin kuɗin sayen magungunan kansa gagara yake. Zamu shiga alhini mai yawa idan ya kasance mun buɗe ido mun ga babu Iyalan Malam Mahmuda a kusa damu, amma hakan ba zai hana mu taya Mairo farin ciki ba domin wannan shi ne irin gatan da ya dace ta samu daga gareku. Allah ya haɗa kanku ya baku ladar zumunci,ke kuma Mairo ina fata barinki garin giwa ba zai zamo silar lalacewar zumunci da ƙaunar da ke tsakaninmu da juna ba ni da ahalina baki ɗaya?" Hakimi ya kai ƙarshen maganar fuskarsa na bayyana zallar alhini da irin kewar su Inna da zasu yi. Don sabo shegen abu ne, musamman su da suka riƙi juna tamkar ƴan uwa.Inna Mairo ta share hawaye tana duban Hakimi a karon farko ta ji wani irin abu na dukan zuciyarta game dashi, ta lumshe idanunta tare da sake buɗe shi akansa ta ce, "Har abada hakan ba zai taɓa faruwa Baban Hanne, domin ku ɗin kun zama wani ɓangare na rayuwarmu ni da Najma. Ba zamu taɓa manta halaccinku da ƙaunar da kuka nuna mana ba,domin kun tallafemu a lokacin da muka rasa dukkan gata.Kun riƙe mu tamkar jininku ba tare da nuna gazawa ko gajiya damu ba, wannan kaɗai ya isa ya sanya mu dauwama muna yi muku addu'ar gamawa lafiya tare da damƙe igiyar zumunta tsakaninmu da juna. Zamu yi kewar da zai wuce yadda zaku yi namu Hakimi, domin daku muka yi sabon da ku kaɗai ku ke sanin farin ciki ko damuwarmu. Ku kaɗai ke fara kawo mana ɗauki a dukkanin abinda ya taso mana, mai daɗi ne ko marar daɗi. Kune cin mu ku ne shan mu tare da suturarmu,taya zamu manta dukkanin wannan alkhairyn har mu kasa cigaba da sadar da zumunta tsakanin mu da juna? Hakan ba zai taɓa faruwa ba Hakimi, ina sake godiya tare da fatan alkhairy ga rayuwarka da ta Iyalinka baki ɗaya." Inna Mairo ta tsaida maganar hawayen tsananin kewar da zasu yi na baro garin giwa su dawo nan ɗin na wanke fuskarta. Gwaggo da Yaya Kabeeru ne suka cigaba da tataunawa akan Hakimi zasu tafi su bar Najma da Inna Mairo a nan ɗin. In yaso nan zuwa kwanaki uku shi da Gwaggo da su Inna Mairon zasu yi mota guda su yiwa Inna Mairo rakiya zuwa giwa, don su yo bankwana da Iyalan Hakimi su kuma ɗakko abinda suke so. Inna Mairo ta dinga sharan hawaye tana tuno fuskar Uwargidan Hakimi Inna Karima, tana ayyana irin kewar juna da zasu yi.Daga ƙarshe Yaya Kabeeru ya janye Hakimi zuwa ɓangarensa, ya yi masa masauki a ƙawataccen falonsa na ƙasa inda yake ganawa da baƙinsa. Sun tattauna muhimman lamura akan abinda ya shafi rayuwar Inna Mairo da ƴarta Najma. Hakimi ya yi masa dukkanin bayanin da ya shafi yadda hawan jinin Inna ke yawan tashi, ya kuma sanar dashi abinda likita ya faɗi na cewa zuciyarta na barazanar kamuwa. Alhaji Kabeer Dukku ya dinga yiwa Hakimi godia tare da jin ƙaunar dattijon na ratsa shi, don Hakimi ya fara zama dattijo don ya haura shekaru hamsin da takwas, kaɗan ya rage ya kai shekaru sittin a duniya.Suka yi sallama da Alhaji Kabeer bayan ya jaddadawa Hakimi cewa suna nan tafe nan da kwanaki uku. Daga shi har Iyalinsa duka zasu rako Inna Mairo garin giwa don tayi sallama da abokanan arziƙinta, shi kuma suyi godiya ga Iyalan Hakimin. Daga Inna Mairo har Gwaggo da Hajiya Zainab, dukkaninsu suka rako su Hakimi har bakin mota lokacin da zasu tafi. Najma na wani irin kuka mara sauti don ita ko kaɗan hukuncin cewa ba zasu koma garin giwa ba bai mata daɗi ba, domin da mutanan garin ta saba,sannan su ta taso ta sani a matsayin komi nata.Don haka a yanzu farat ɗaya ace za a rabota da ƴan uwanta su Hanne tana ganin tamkar rashin adalci ne da datse mata farin cikinta.Auwalu kansa kallon Najma ya dinga yi zuciyarsa na masa wani irin suya, hakanan yake jin bai ji daɗin yadda za a ce ba za su koma giwa ba. Ya dinga mita a zuciyarsa yana faɗin da can mai yasa suka yi watsi da lamuransu, sai a yanzu ne suka san da cewa Inna Mairo ba za ta cigaba da zaman karkara ba? Har Hakimi ya shiga mota Auwalu mita yake a zuciyarsa yana ji tamkar ya sanar da Najma sirrin zuciyarsa a kanta,ya haɗe fuska tamau lokacin da Gwaggo ke masa fatan su isa lafiya. Alhaji Kabeer Dukku kuwa matsawa ya yi daga jikin motar ya miƙawa Auwalu wata ƙaramar envilop, mai ɗauke da damin kuɗin ya ce su sha mai dashi. Auwalu ya amsa ya yi godiya fuskarsa sam babu walwala, sai ma ƙarin baƙin ciki da alhinin daina sanya Najma da zai dinga yi a idanunsa ke sake kassara zuciyarsa. Inna Mairo ta matsa har jikin motar tana sake yiwa Hakimi godiya tare da yi musu addu'ar Allah kiyaye hanya.Ita kam Najma ta kasa isa jikin motar sai tsayawa tayi daga nesa tana cigaba da kuka mai cin rai. Nasreen da ke tsaye daga bayanta ne ke faman rarrashinta akan tayi shiru, amma ko duban Nasreen ɗin ta kasa yi bare ta saurari rarrashinta da take yi. Dukkanin zuciyarta na ga su Hanne da Lubah, waɗanda ta san yau kwanan kuka zasuyi idan suka ji labarin za a rabasu da garin giwa su dawo nan ita da Innarta. Ita ko kaɗan hakan bai yi mata daɗi ba don duk yadda Gwaggo ke wani nuna nadamarta ba birgeta take yi ba, sai ma sake jin zafinta da take yi a cikin zuciyarta idan tana tuna irin yadda Inna ke kuka da idanunta na irin baƙin ciki da ƙiyayyar da Gwaggon ta nuna mata. Hannunta Inna Mairo ta kama lokacin da motar su Hakimi ta bar wajen,ta yi ƙasa da murya tana cewa da Najma, "Ki yi shiru ki tsaida wannan kukan Najma, nan ma gida ne kamar can kinji ko?" Najma ta ja ajiyar zuciya tana cewa, "Amma Inna meyasa zasu ce ba zamu koma can ba alhali ni nafi son can, duk talaucin da muke ciki a can wallahi nafi son can da nan ɗi....." Hannu Inna ta sanya ta rufe bakin Najma tana jifanta da wani kallo mai cike da gargaɗi ta ce, "Karna kuma jin kina faɗin hakan Najma, Gwaggo da Yaya Kabeeru sun yanke hukuncin mu dawo nan ɗin. Kuma hakan shi ne daidai domin sune tilashina ba Hakimi ba, shi halacci yake nuna mana amma ba don nauyin kulawa damu ya rataya a wuyarsa ba. Lokaci ya yi da za a barshi da Iyalansa ya hidimta musu, don koda kuɗin maganina aka cigaba da barinsa tabbas ana shiga rayuwarsa. Ki sani yau da gobe sai Allah Najma,sannan duk yadda zaki yi kewar su Hanne da Lubah bai kai yadda ni zanyi kewar baro garin giwa ba. Domin gari ne da tarihin rayuwar da nayi aciki da mahaifinki ba zai taɓa gogewa a zuciyata ba, sannan ban taɓa sha'awar baro garin ba koda wasa.Don haka ki daina faɗin komi da zuciyarsu ba zai so ba idan sun ji, shi komi NUFIN ALLAH ne Najma. Haka ALLAH Ya NUFA cewa lokaci ya yi ne da zamu baro garin giwa ba don mun gaji da garin ko mun daina son jama'ar cikinsa ba, sai don haka ALLAH Ya so Ya kuma yi NUFIN zai kansance." Inna Mairo ta kai ƙarshen maganar tana duban yadda hawaye ke gudu akan black beauty face ɗin Najmarta. Tuni su Gwaggo sun rigasu yin gaba don su suna takawa ne a hankali Inna na rarrashin Najmar, hakan ya sanya babu wanda ya ji dukkanin kalamai da rarrashin da Innar kewa Najma. Najma ta jinjina kai cikin sanyin muryarta ta ce, "Shikenan Inna, ba zan kuma magana ba amma ki sani zan jima ina kewar su Lubah." Inna Mairo ta gyaɗa kai tana sakin ƙaramin murmushi ta ce, "Na san hakan zai faru Najmata, amma a hankali zaki rage jin kewarsu idan ki ka saba da zaman nan ɗin. Ki yi addu'a ne kawai akan Allah yasa dawowarmu nan ɗin ya zame mana alkhairy kinji ko?" Najma ta jinjina kai ba tare da ta iya cewa Inna komi ba. A haka suka isa part ɗin Gwaggon kaduna, suka sameta zaune a falo alamun jiran shigiwarsu take yi...........✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/8, 1:05 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 12* _Free page_ Gwaggo ta dubi fuskar Najma da har lokacin da alamun hawaye ta ce, "Kiyi haƙury Najma nan ma gida ne,kuma sannan ga Nasreen nan tsararki ce sai kuyi ta hidimarku ba zaki yi zaman kaɗaici da rashin abokin hira ba kinji ko?" Najma ta gyaɗawa Gwaggo kai fuskarta sam babu walwala ta ce, "Tuh!" Daga haka bata sake cewa komi ba, ta takure jikinta daga gefe guda tana sauraran hirar da Gwaggo ke jan Inna Mairo da shi.Gabaki ɗaya hankali da tunanin Najma na ga ƙauyen giwa ne, tana ayyana ko yasu Lubah zasu amshi zancen barowarsu garin giwa a rana tsaka? Wasu hawaye suka sake cika idanunta tana ƙoƙarin maidasu don bata so ran Inna ya ɓaci. Gwaggo ko labarin bikinsu Adnan Dukku da Jiddah ta ke faman bai wa Inna Mairo, tana kuma sake bata haƙuri game da yadda ko bikin ba a sanar mata ba. Inna Mairo ta sanarwa da Gwaggo zancen zuwan Adamu drivernta da tarin abin arziƙin da Hajiya Zainab ta aika mata dashi. Gwaggon kaduna tayi shiru na wani lokaci,kafin ta dubi Inna Mairo da tsantsar mamakin da ke haskawa a saman fuskarta ta ce, "Yanzu dama zuwan da tayi ta ce in bata aronsa zata aikesa wani waje giwa ya tafi wajenki?" Inna Mairo ta gyaɗa kai cike da tabbatarwa ta ce, "Wajena ya je Gwaggo, kuma da tarin abin arziƙi babu abinda zance da irin ƙaunar da take nuna mini sai dai in yi mata fatan gamawa lafiya." Gwaggo ta jinjina kai ƙaunar surukarta na sake samum wajen zama a zuciyarta, sabida tabbas Momy mace ce ta gari da Alhaji Kabeer Dukku ya yi sa ar samu. Ta cigaba da kallon Inna Mairo tana faɗin, "Ai Zainab ta haifu Mairo, bani da abinda zan ce sai godia domin Kabeeru ya yi dace da macen ƙwarai mai ƙaunar dukkanin ahalinsa na birni da ƙauye.Don hatta mutanen Dukku hidimta musu take ba tare da gajiyawa ba.Shiyasa nake tsananin ƙaunarta a zuciyata,don tafi matar Ali sanin ya kamata, sannan ta fita son dangin miji da girmamasu." Inna dai jinjina kai tayi ta ce, "Allah sarki, gaskiya Yaya Kabeeru ya yi dace Gwaggo." Daga haka bata tofa akan irin yadda Gwaggo ke tsinan halayyar matar Yaya Alin ba, da alamu bata jin daɗinta sam! Ko kuma bata girmama Gwaggon irin yadda ita Momy ke mata. Sai dab da kiran sallar magriba Gwaggo ta yiwa Inna Mairo jagora zuwa ɗakin da ta ware musu ya zama mallakinsu. Bedroom ɗin na daga can ƙarshe ta wani corridor na daban bata cikin wanda ake shiga na ɗakin baccin Gwaggon ba, ta sanar da Inna Mairo cewa nan zasu ɗauka sabida yana da yalwa sosai.Inna Mairo ta dinga godia tamkar Gwaggo ta yi mata kyautar wani gagarumi. Ta shige daga cikin ɗakin tana ware idanu,tana kallon tsaruwar ɗakin da komi yake a tsare tsaf! Daddaɗan ƙamshi na tashi a cikin ɗakin don duk ranar duniya sai an gyare ɗakunan baccin duka an goge ko'ina. Najma sai daga baya tabi Inna Mairo zuwa ɗakin da aka ware musun, sosai ɗakin ya ƙayatar da ita amma ko a fuska bata nuna hakan ba. Ta samu saman sofa da ke ɗakin ta zauna ta mai zabga tagumi, don Inna Mairo ta shiga toilet ɗauro alwala lokacin da ta shigo. Koda Innar ta fito kallo ɗaya ta yiwa Najma tayi gaba zuwa wajen da ta shinfiɗa abin sallah.Ganin hakan ne ya sanya Najma tashi jiki a sake ta nufi toilet ɗin ita ma don ɗauro alwalar. Bayan Inna Mairo da Najma sun idar da sallar isha'i da suka jira aka yi, sai suka fito zuwa falon zuciyar Najma cike da jin haushin yadda zasu kwana basu da ko kayan canji, tunda bada shirin kwana suka zo ba bare har a riƙesu ace sun taho kenan. Gwaggo bata fito daga ɗakinta ba sai wajen takwas da rabi, suka haɗu suka ci abin dare tare da su Inna Mairo.Abinci kala biyu na sashin Gwaggo da Tabawa ce mai yin girkin, sai kuma wanda Momy Hajiya Zainaba ta aiko daga part ɗinta don karrama su Inna Mairon. Sun ci sun yi ƙat! Tare da yin godiya ga Allah, don ba ƙaramin sakin jiki Inna Mairo tayi ta kwashi farfesun kazar da aka yiwa wani irin haɗi na musamman.Najma ma da yake mai son naman kaza ce, ta ci abin ta sosai bata ƙwari kanta ba, sabida Gwaggo basu waje tayi bayan ta ci abu ba mai yawa ba don abinci kaɗan take iya ci ita. Hira sosai suka dasa tsakanin Gwaggo da Inna Mairo. Gaba ɗaya Inna Mairo sai take ganin komi kamar almara, don abu ne bata tayi sabo dashi ba tun ƙuruciya har girma, a ce wai Gwaggo ta zauna cikin raha da sakin fuska tana hira da ita,wannan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Suna tsaka da hiran nasu suka jiyo sallamar Nasreen da Momyn ta, Gwaggo ta amsa sallamar tana basu izinin shigowa. Nasreen ce a gaba hannunta riƙe da wani babban bag, sai Momy na biye da ita hannunta ita ma ɗauke da wani ƙaramin paper bag.Suka samu waje suna gaida Gwaggo tare da sake gaisawa da Inna Mairo cikin fara'a. Najma ta sake gaida Momynsu Nasreen tana duban ɓangaren da Nasreen ɗin ta zauna tana sakin mata murmushi. Momy ta amsa da kulawa idanunta akan Najma take tsokanarta da faɗin, "Mai kuka har kin share hawayen? Banda abinki Najma nan ma ai gida ne." Gwaggo tayi karaf ta ce, "Kema dai kya faɗi Zainab, ni gani nayi sam bata farin ciki da zancen dawowarsu nan ɗin." Najma tayi saurin duban Gwaggo tana mai ɗauke ido daga gareta ta mayar kan Inna Mairo, wacce ta zubawa Najma idanu tana jifanta da harara. Najma ita kaɗai ta ankare da irin hararar da Inna Mairo ke jifanta dashi,don haka sai tayi saurin maida dubanta ga Gwaggo tana faɗin, "Ba haka bane Gwaggo,ina tunanin ƴan uwana su Hanne ne, domin zasu ji babu daɗi idan aka ce zamu dawo nan ɗin." Gwaggo ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Karki damu zasu saba da rashinku kamar yadda kuma zaku saba, sannan zaku dinga zuwa kai musu ziyara ba wai za a rabaku da zuwa inda suke bane kin ji ko?" Najma ta gyaɗa kai cike da gamsuwa tana faɗin, "To Gwaggo mun gode!" Momy Hajiya Zainab kallon Najma kawai take yi tana jin ƙaunarta har cikin zuciyarta. Komi na Najmar birgeta yake yi, musamman nutsuwar da take gani tattare da ita.Nasreen da ke kallon Najma ita ma murmushi tayi tana faɗin, "Ai Gwaggo ni rarrashi ma nake mata ɗazu amma ko kallo ban ishe ta ba." Nasreen tayi maganar da wani irin salo na shagwaɓa, hakan yasa Najma zuba mata ido tana mamakin taɓararta ta ce, "Kiyi haƙuri gaba ɗaya hankalina ne ya tashi a ɗazu ɗin." Nasreen ta watsa hannuwa tana faɗin, "Alright! Sis ya wuce, but ni dai i like u, kuma ina so ki sake jiki damu mu zama tamkar twins ko Momy?" Momy ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Gaskiya kam da kun gama birgeni idan kuka haɗe kanku daughters ɗina." Tayi maganar da tsantsar nuna ƙaunarta ga Najma da ƴarta Nasreen. Gwaggo da Inna Mairo suka haɗa ido suka saki murmushi, kowanne cikinsu na sake jin ƙaunar Hajiya Zainab na sake yawa a zuciyoyinsu. Hajiya Zainab ta tura bag ɗin dake gabanta wajen Inna Mairo tana faɗin, "Innar Najma ga kayanan kala 2 mun siyo, kafin zuwa gobe ayi fita na musamman don samo muku kayan sawa da sauran abin buƙatu." Inna Mairo ta janyo bag ɗin tana nunawa Gwaggo ta ke cewa, "An gode da ɗawainiya Momyn Nasreen." Nasreen ma bag ɗin da ta shigo dashi ta miƙawa Najma tana faɗin, "Sister ga naki kema kafin mu fita shopping gobe." Najma ta amsa tayi godiya mai yawa tana mai nuna wa Gwaggo ta ce ta taya ta godia.Gwaggon kaduna ta dubi Momy ta ce, "An gode ƙwarai Zainabu, Allah dai ya saka miki da aljanna.Irin yadda ki ke hidimta wa ahalin Kabeeru da zuciya ɗaya, Allah ne kaɗai zai biya ki.Allah ya yi miki albarka na gode ƙwarai." Momy tayi ƙasa da kai tana cewa, "Bakomi Gwaggo ai an riga an zama ɗaya, Allah dai ya bamu ikon cigaba da yi muku biyayya." Inna mairo tayi saurin amsawa da cewa, "Ameen." Najma ta miƙe ta nufi ɗakin da aka saukesu da bag ɗin kayan,zuciyarta na cika da jin daɗin yadda Nasreen da Momy ke nuna musu kulawa. Koda ta buɗe bag ɗin kayan bacci ne ta gani kala biyu, sai wasu haɗaɗɗun ready made boubous na material masu shegen kyau suma kala biyu. Akwai undies da bra ma kala biyu,sai perfumes masu sanyi da daɗin ƙamshi guda uku. Abu na ƙarshe da ta ciro sune kayan wanka da su brush da toopaste masu kyau. Ta dinga jinjinawa Nasreen a ranta tana mamakin yadda tayi ƙarfin halin zaɓo mata har da bra, alhali gani ɗaya tayi mata a yau ɗin. Ta ɗago bra ɗin tana juyasu a hannu, tana kuma kisima cewa tabbas zasu yi mata daidai. Toilet ta shiga ta cire kayan jikinta ta gwada bra ɗin,sai gashi ya yi mata daidai har yaso ma ya ɗan matseta kaɗan.Amma ta san da zaran an wanke sau ɗaya zai iya ɗan saki,yadda zai mata normal ba takura. Rigar baccin da ta shiga dashi kalan milk ta sanya, ya yi mata kyau matuƙa tsayin rigar ya tsaya iya guiwarta ne. Ƙirjinta da babu bra ya fito sosai, hakan ya sanya tana futowa ta ɗauki hijab ɗin da tayi sallah ta zura. Falon ta sake fita daidai lokacin da su Momy suka miƙe suna wa Gwaggo sai da safe, ta ƙarisa tana duban Nasreen ta ga irin yadda take dubanta daga sama har ƙasa.Ta saki murmushi lokacin da Nasreen ta ƙariso wajenta tana yin ƙasa da murya ta ce, "Sis kin gwada bra ɗin?" Najma kunya ya rufeta ,ta ɗan lumshe manyan idanunta tana gyaɗa ta ce, "Sunyi Sis, na gode." Nasreen ta saki smile ta ce, "Thank god! Sai tomorrow zamu fita ki darji kaya masu kyau sosai, don so nake wannan black beauty skin ɗin naki su sama product masu kyau na body wash dana shafa,ta yadda fatarki zata yi sulɓi black skin ɗin ya fiddo da asalin kalarsa."Najma ta saki murmushi ba tare da ta ce komi ba.Momy ta tayi gaba tana faɗin, "Najma gud night, ko zaki taho mu je ki kwana tare da Sis ɗin naki?" Najma tayi saurin girgiza kai alamun a'a, hakan ya sanya Nasreen tsuke fuska tana magana cike da narkewa take faɗin, "Please! Muje Najma." Inna Mairo da idanunta ke kan Najma sai tayi mata alama da ido akan ta bisu ɗin. Sai Najma ta sakarwa Nasreen murmushi tana cewa, "To muje, amma da yin safe xan dawo wajen Innata." Duka suka saki dariyar yadda Najma tayi maganar cikin ƴar shagwaɓa.Nasreen ta ja hannun Najma suka fice bayan sun yiwa su Gwaggo sai da safe.Momy ta rigasu yin gaba zuwa part ɗin nasu,su Najma suna tafe tafiya ne a hankali Nasreen na mata hira har suka isa cikin haɗaɗɗan part ɗin nasu. Lokacin da suka dangana ga ɗakin baccin Nasreen ɗin, sake baki Najma tayi tana kallon tsaruwar ɗakin.Komi na ciki white ne babu surkin kowani kala, don ita white is her favourite colour. Komi a tsare yake a ɗakin,banda sassanyan ƙamshi da sanyin air condition babu abin ke tashi a ɗakin.Ta samu saman sofa ta zauna, idanunta akan Nasreen da ke amsa call ɗin da ya shigo mata. Najma sai ta ɗauke kai daga dubanta ta mayar kan ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na sake yaba kyawun komi na cikinsa. Daga yanayin yadda Nasreen ɗin ke wayar ta gane cewa da ƙanwarta Nabeelah ce, don ta ambaci sunanta sannan ta ji tana sanar da ita zuwansu har da koɗawa Nabeelah kyawunta. Ta sauke wayar a kunni tana blushing ta dubi Najma ta ce, "Nabeey na gaidaki, gobe ko jibi zata dawo.Ta je gidan wata friend ɗin Momy ne, age mate ɗinta tayi birthday yau." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Ina amsawa." Nasreen ta sake sakin mata murmushi ta ce, "Ki cire hijab ɗin mana Sis, kamar wata matar liman." Najma ta yi murmushi tana jin nauyin yadda za ta cire hijab ɗin Nasreen ta ga yadda rigar ta fiddo asirin cikar ƙirjinta da ƙasanta. Gane hakan da Nasreen tayi ne ya sanya ta faɗin, "Ni dai ai ƴar uwarki ce, kuma tare zamu rayu in ma baki cire yau na ganki da rigar bacci ba, watarana ma a gabana zaki sanya.So gara kawai ki fara yin komi kai tsaye,ke naga alama kunya tayi miki yawa Najma." Najma ta ɗan saki dariya tana kai hannu ta zare hijab ɗin jikinta. Nasreen ta kafeta da ido tana sake gano asalin kyawun da Allah ya yiwa Najma.Duk da kasancewarta baƙa sosai, Allah ya yi mata baiwar kyawu mai fisgar hankali da cikar halitta. Ta sauke numfashi a hankali tana faɗin, "Sis u are very black beautiful! Gaskiya na jima banga baƙar fatar da ta birgeni irinki ba. Najma tayi ƴar dariya tana ma rasa abin faɗi,don ba yau ne ta saba jin ana koɗa kyawunta ba duk da kasancewarta baƙace sosai. A karon farko Najma ta samu kanta da kwanciya akan gado da shinfiɗa na alfarma, wanda laushin katifar kawai aka bar bawa dashi ni'imace. Tunda tayi juyin farko bata kuma ba sai da kiran sallar asuba ya shiga cikin kumnuwarta.Don sosai ake jin kiran sallar da ake kwaɗashi daga cikin masallacin gidan Alhaji Kabeer Dukku dake daga waje. Ta tashi zaune tana mai karanto addu'ar tashi daga bacci, ta sauka daga gadon ta nufi tsararren toilet Nasreen da ya gaji da haɗuwa.Alwala ta ɗauro ta fito sannan ta tada Nasreen ɗin ita ma.Sai dai tana buɗe ta ɗaura akan Najma sai ta sake gyara kwanciya tana faɗin, "Ina period Sis,yi naki sallar ki dawo mu cigaba da bacci." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Ok to!" Daga haka ta nufi wajen sallar da aka saita shi ya kalli gabas, ta ɗauki hijab akan sofa ta saka ta tada sallar. Sai da ta gama yin azkar ɗinta gaba ɗaya sannan ta koma gado don sake kwanciya,amma abinka da rashin sabo duk yadda taso bacci ya sake ɗaukanta abin ya gagara. Ta riga ta saba aikin bauta a giwa, sam bata san wani zancen a koma baccin safe bayan anyi sallah ba. Haka ta dinga juyi tana tuno giwa da ayyukan da take gabatarwa a lokuta irin wannan. Wani abu ya tokare ƙirjinta, tana ji kamar ta buɗe ido ta ganta tana suyan ƙosanta ana mata layi ana saye. Wajen ƙarfe bakwai da rabi ta sakko daga kan gadon, don ta san babu wani bacci da zai ɗauketa don bata saba da hakan ba. Falo ta fito ta zauna tayi shiru tana faman tunanin mai zata yi ne? Ta miƙe tsaye tana nufan hanyar da taga mai aikin Momy jiya ta fito daga wajen, ta cigaba da takawa har ta shige cikin corridor ɗin. Daga can ciki ta fara jin karakainan masu aikin, sai ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da sallama. Rabi da Laure masu aikin Momy suka amsa sallamar suna duban Najma cike da mamaki.Ta samu waje tayi tsaye tana gaida su,don Rabi dattijiyace Laure ce kawai matashiya da bazata gaza shekaru ashirin da biyar zuwa da shida ba. Tambayarsu Najma tayi akan ko akwai aikin da zata iya kama musu? Rabi ta dubeta da kulawa tana faɗin, "Baiwar Allah da dai kin koma kin yi kwanciyarki kada Hajiya ta tuhumemu da sanya ki aiki." Najma tayi saurin girgiza kai tana sanar dasu cewa, kwanciyarce ba za ta iya ba don bata saba da ita ba, gara dai su bata wani abin ta kama musu matuƙar hakan ba laifi bane. Ganin ta dage sai Rabi ta bata ƙullun ƙosai da suka niƙa a blander ta ce ta buga, sabida Alhaji Kabeer Dukku mutum ne mai son yin karin safe da kayan gargajiya bai damu dasu chips ba. Don shi ake yin ƙosai da su waina duk safiya, matuƙar yana gari ba ya koma Abuja ko ya bar ƙasar bane.Ga tsananin mamakin Rabi gani tayi Najma har ta fita ƙwarewa wajen iya sakin ƙosai a mai,sannan yanayin yadda ta ƙarawa kullum ruwa ta ce zai cushe a yadda suka barsa. Sai suka ga tabbas hakan ne kuwa, domin kwasan farko da soya suaa ga irin taushin da ya yi.Kafin suce kwabo ta kammala soya lafiyayyan ƙosan da ya yi taushi matuƙa, ta juye shi a ƙawataccen kular da ake zubawa Daddy Kabeer Dukku a ciki. Ta wanke komi tas da tayi amfani ta dashi, ta kife a wajen adana kayan da aka wanke.Ta koma gefe guda tana kallon yadda suke yin soye-soyen su chips da haɗin lafiyayyen sauce irin na ƴan gayu. Take ƙaunarta da son girki ya motsa, ta dinga ayyanawa a ranta dolema ta riƙa zuwa tana taya su aiki, don ita ma ta koyi abubuwan da bata iya ba.Wajen ƙarfe takwas da rabi suka kwashi warmas ɗin da aka zuba komi ciki suna kai wa dining suna aje wa, na ɓangaren Daddy sun shirya shi a babban tray an aje daga gefe guda.Sabida basa shiga ɓangarensa, Momy ce da kanta ke zuwa ta ɗauka, wasu lokutan ma da kanta take tashi tayi masa girkin. Shi ne yake hanata tashin safen a wasu lokutan da yawa, sai ya zamana tafi amsar ragamar girka masa luch ko dinner. Ɗakin Nasreen Najma ta koma ta tadda Nasreen ɗin ta shiga wanka. Ta samu waje bisa sofa ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo a hasken safiya da ya haske ɗakin, domin windows ɗin a buɗe suke. "Sis ina kika shiga na tashi na ga baki a ɗakin?" Nasreen ta wurgawa Najma tambayar lokacin da ta fito daga bathroom. Najma ta saki ƙaramin murmushi ta ce, "Ina kitchen wajen masu aiki, na je taya su wani abin.Kinsan mu ƴan karkara ba muyi sabo da komawa baccin safe ba sai ku ƴan gayun birni." Yadda Najma tayi maganar bilhaƙƙi sai ta bai wa Nasreen tausayi. Ta narke fuska tana duban Najma ta ce, "Amma ai yanzu dole ki saba tunda kin dawo nan ɗin." Najma ta sake yin mirmushi tana cewa, "Bari in shiga wankan nima, idan yaso ina fitowa sai na tafi wajen Innata tunda kayan da zansa na can." Bata jira cewar Nasreen ba ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi toilet. Nasreen bata barta komawa part ɗin Gwaggo ba, sai ta bata wata rigarta ta saka na wani haɗaɗɗan batik kalar red and green.Ɗinkin free boubou akai ma rigar hakan ya sanya ya yiwa Najma daidai, sabida tafi Nasreen cikar jiki sosai. Tare suka nufi falo sukai breakfast a dining, bayan sun kammala Nasreen ta ja hannunta suka nufi side ɗin Daddynsu. Cikin sakin fuska da fara'a yake amsa gaisuwar Najma tare da miƙa mata hannu alamun ta isa garesa,ta isa ta zauna kusa da shi yana tambayarta yadda suka tashi. Najma ta gaida Momy Hajiya Zainab cikin ladabi,tana mai yaba kyawun da Momyn tayi cikin atamfar jullious holland da ke jikinta. Basu jima a wajen Daddy ba suka fice zuwa part ɗin Gwaggo.Sun samu Inna Mairo tare da Gwaggo sun kammala karyawa kenan, suna zaune suna hira cikin annushuwa.Har ƙasa Najma ta tsuguna ta gaida Gwaggon kaduna, Gwaggo ta amsa da sakin fuska tana tambayarta ya baƙunta? Najma ta yi murmushi tana ƙin cewa komi. Inna Mairo ko kallon Najma take yi tana yaba kyawun da kayan Nasreen suka yi a jikinta. Nasreen ta gaidasu Gwaggo ita ma cikin ladabi, tana mai duban Gwaggo ta sanar da ita fitan da zasu yi da Najma zuwa yin shopping zuwa ɗan anjima kaɗan. Inna Mairo a part ɗin Momy suka yi lunch, don tunda ta je gaida Yaya Kabeeru Momy ta hanata komawa part ɗin Gwaggo,suka zauna suna hiransu cikin nishaɗi. Labarin auren su Jiddah da Adnan Momy ke bai wa Inna, tana sanar da ita cewa Jiddar wani ɗan majalisa ta aura suna zama a Abuja.Amma yanzu haka ma bata ƙasar sun tafi yawon honey mun da mijinta, Shi kuma Adnan yana port harcourt da matarsa,a can yake aiki da ma'aikatan man fetur na ƙasa wato (refinery). Misalin biyu na rana Nasreen ta kwashi su Momy da Inna Mairo da Najma cikin ƙamar motarta KIA suka fita yiwa su Innar shopping,tunda ya kasance basu zo da kaya ba dole a nema musu kayan sawa da sauran kayayyaki na buƙata. Suna tafe Najma da ke zaune a front seat ta yane kanta da ƙaramin veil da Nasreen ta bata, tana faman kallon yadda Nasreen ɗin ke tuƙa motar cike da ƙwarewa. Siyayyan kayan sawa masu uban yawa dasu kayan shafa,zuwa su underwears kaɗai sun lashe kuɗi masu yawa. Daga Najma har Inna Mairo mamakin irin kaya masu tsada da ake ɗibar musu sukai tayi, bama kamar Najma da Nasreen ke jidarwa komi na gayu da ta ga zai dace da ita. Hatta body wash na wanka wasu irin product masu tsada na african black queens ta ɗaukar mata, waɗanda zasu gyara fatarta su fiddo asalin kyawun black skin ɗinta. Basu koma gida ba sai can yamma, domin sun biya gidan wata ƙawar Momy da ke saida ɗinkakkun kayan sawa na mata,aka zaɓarwa Inna Mairo wasu dogayen riguna masu kyau da tsada. A gajiye suka shigo gidan suka nufi ɓangaren Gwaggo gaba ɗayansu, don nuna mata siyayar da aka yo ɗin.Sabida Momy ta gama sanin halin surukartata, ta kuma karanceta tare da bida ita duk ta yadda take so. Gwaggo ta yaba da siyayyar har ma da cewa ba a siyawa Inna Mairo kaya masu yawan da tayi zato ba,don haka zuwa in an kwana biyu ita ce da kanta zasu shiga kasuwa da Inna Mairo ta zaɓi wasu kayan a bada ɗinki.Momy ta dinga dariya tana sanar da Gwaggo cewa ai dama wannan somin taɓi ne aka yi siyayyar, za a sake fita idan sun sake natsawa an je giwa an dawo. Inna Mairo da Najma suka dinga zubawa su Gwaggo godia tamkar ba zasu daina ba, har sai da Gwaggo ta dakatar dasu ta ce godiyar ya yi yawa ai abinda ya dace ne aka yi. Nasreen da Momy suka nufi part ɗinsu yayinda Najma ta maƙale wajen Inna Mairo, duk yadda Nasreen taso su wuce tare ƙi tayi sai ta ce mata sai zuwa dare zata je mata hira............✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/8, 1:07 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 13* _Free page_ Da dare misalin tara da kusan rabi Alhaji Kabeer Dukku tare da ƙwararren family doctor ɗinsa, suka shigo part ɗin Gwaggo kadua. Yana gaba doctor Bakory na biye dashi har cikin falon Gwaggo,bayan an amsa sallamarsu tare da basu izinin shiga. Najma da Inna Mairo da hankalinsu yafi karkata akan TV, sune suka waiwayo suna gaida Daddy da Likitan nasa.Yayin da Gwaggo da ke amsa waya ta aje wayar tana duban su Daddyn ta ce, "Barkanka da zuwa Likita bokan turai!" doctor Bakory ya yi dariya yana gaida Gwaggo cike da girmmawa. Daddy ya maida dubansa kan Inna Mairo yana sanar da ita cewa wajenta doctor ya zo, don haka sai ta taso ta dawo kusa da su sosai suna sake gaisawa da likitan a mutunce. Tambayoyi ya yi mata akan hawan jinin da ke damunta, ta dinga bashi amsa a nutse. Daga ƙarshe ya buƙaci ganin magungunan da take amfani dasu, sai ta sanya Najma ta tashi ta nufi ɗakinsu ta ɗakko ledar magungunan.Waɗanda suka taho da abinsu a jakar hannu da Inna ta riƙo. Ta dawo cikin falon tana mai miƙawa Daddy ledar ta juya ta koma can gaban TV, tana cigaba da kallon da ya ɗauke hankalinta. Likita na gama duba magungunan ya dubi Daddy yana sanar dashi cewa sai an canja wasu, don waɗannan ɗin sun yi mata kaɗan,sannan zata je asibiti ta sameshi don akwai test da ya kamata tayi.Inna Mairo tayi godiya mai yawa lokacin da ya kammala gwada BP ɗinta,ya kuma tabbatar komi normal ne a yanzu ɗin.Gwaggo ma godiya tayi masa tana sanar da shi cewa dole a goben Inna Mairo ta gansa a asibitinsu, domin a binciki lafiyarta da kyau tunda ance zuciyarta na barazanar kamuwa.Doctor Bakory ya jinjina kai yana tabbatar wa Gwaggo cewa dama dole ta je asibitin nasu, ya dai zo ne don fara duba mata da yi mata tambayoyin da suka kamata.Najma tayi musu sai da safe lokacin da Daddy da Likitansa zasu fice daga falon,Daddy ya amsa da kulawa yana sanar da ita cewa da safe akwai saƙon da zata amsa hannunsa nata dana Inna Mairo.Tayi godiya sosai tana mai maida dubanta ga kallon da take yi, har suka fice bata sake waiwayawa wajensu Gwaggo da ke hira duk akan ciwon Inna Mairon ba. Ƙarfe goma Gwaggo tayi musu sai da safe ta shige ciki don kwanciya, ita ma Inna Mairo tafiya tayi don ta kwanta sabida a gajiye take da fitar da suka yi ɗazu.Najma ce ta kai har goma da rabi kafin ta kashe kayan kallon ta wuce ɗaki ita ma,don bacci ya fara damunta dama kuma ita ba gwanar doguwar hira bace da wuri suke kwanciya bacci.Tana kammala sanya kayan bacci ta ɗauro alwala ta bi lafiyar gado, inda ta lafe a bayan Inna Mairo da har bacci ya yi awon gaba da ita tuni. Daga can ɓangarensu Momy kuwa tunda Nasreen ta ga goma tayi Najma bata shigo ba,ta san cewa ba za ta zo tayata hiran ba kamar yadda ta faɗi.Sai kawai ta shige room ɗinta suna shan vid call da wani course mate ɗinta,wanda ya nace mata shi a dole sonta yake gaske.Ita kuma kula shi kawai take yi sabida ƙoƙarinsa da kuma iya ɗaukar wankansa don guy ɗin ya haɗu ƙarshe. ******** *Port Harcourt,Rivers, State.* *11:30pm* Daga cikin ƙaton bedroom ɗin wanda ya gaji da haɗuwa,wata farar mace ce mai kimanin shekaru ashirin da biyar ke faman kai kawo a cikin tsakiyar ɗakin baccin nata.Tana sanye ne da wata haɗaɗiyar rigar bacci kalar red,wacce ta bayyana dukkanin surar jikinta.Hatta da shacin bra da ke jikinta ana kallo,komi nata a bayyane yake don rigar bata da maraba da babu.Kyakykyawace daidai misali,tana da surar jiki mai kyau don akwai gaba da baya tubarkallah! Hawaye ne ke zubowa daga idanunta suna sauka akan kyakykyawar fuskarta, a lokacin da take faman safa da marwa a tsakiyar bedroom ɗin tana duban agogon da ke manne jikin bangon ɗakin. Bai taɓa kai wa dare kamar haka bai dawo ba, ta san yana yawan darensa zuwa duk club ɗin da ya yi ra'ayi amma ko zai fitan sai ya dawo gida daga office ya ci abinci zuwa 10 na dare sai ya fice abinsa.To yau gashi tun fitan safe bata sake sanya shi a idanunta ba,sannan ta kira wayarsa har ta gaji amma bai yi picking call ɗin ba. Wasu hawaye masu tsananin zafi suka sake ɓalle mata,tana ji zuciyarta tamkar zata kama da wuta sabida irin zafi da turirin dake tashi a cikinta.Wani irin mahaukacin tsoro da kishinsa ke sake kassara zuciyarta,domin ba ƙaramin so take yiwa AD Dukku ba. Tun tana zubda hawaye tana duban agogo har ta gaji ta zame bisa sofa ta kwanta, bada jimawa ba kuma bacci ɓarawo ya lallaɓo ya saceta.Bata san lokacin da ya dawo gidan ba, ta farka ne kawai daga bacci ta ga ƙarfe biyu na dare har ta gota. Ta miƙe zumbur tana fita daga ɗakin cikin sassarfa,bata tsaya a ko'ina ba sai a ƙofar shiga bedroom ɗinsa.Ta tura ƙofar a hankali tana sanya kanta ciki, zuciyarta gaba ɗaya na yi mata wani irin nauyi.Idanunta ne suka sauka a kansa, yana zaune daga bakin bed yana faman danna waya.Sai ta ƙarisa shigewa cikin ɗakin hawayen da take riƙewa na sake kufcewa daga idanunta.Gaba ɗaya ɗakin ya rine da daddaɗan ƙamshinsa, ƙamshin da ke kassara zuciyarta da haifar mata da shauƙi mai tsanani a kansa.Ya ɗago manyan idanunsa ya zube a kanta lokacin da tayi masa tsaye, tana masa wani iri kallo daya tsana.Ya ɗauke kai daga dubanta yana faɗin, "Idan ba zama kika zo yi ba, kina iya bani waje please!" Hakan da ya furta ya sanya ta sulalewa ta zauna kusa dashi, har lokacin ta kasa ɗauke idanunta a kansa.Cikin rawar muryar dake bayyana dukkanin rauninta a kansa ta furta, "Why AD? Meyasa ba zaka gane cewa ina da girman hakki a kanka ba,meyasa ba zaka daina wannan yawon daren ba alhali kasan kana jefa zuciyata cikin baƙin ciki? Yau tun safe ka fita office amma ban ci arziƙin da ka dawo ba sai cikin wannan tsakiyar daren,hakan ya dace kenan a matsayinka na magidanci mai Iyali?" Ta tsaida tambayar iya nan tana sake kafeshi da idanunta dake zirarar da hawayen takaici da baƙin cikinsa.Ya yi mata wani malalacin kallo tare da taɓe bakinsa ya ce, "Hannah sau nawa zan gaya miki cewa irin lifestyle ɗina kenan? Ba zan iya daina zuwa club ba domin nayi sabo da hakan, kuma ina samun farin ciki mai yawa da zuwana wajen.Don me zaki riƙa damun kanki akan abinda baki da ikon hanawa ko sauya ra'ayina a kan hakan? Ba zance miki bana tarayya da mata ba idan ma kishi ne ke rufe idanunki.Sai dai Na sha gaya miki nishaɗi kawai nake dasu, amma bana kwanciya dasu.Iyakata dasu just romance ne kaɗai, amma bana tarayya dasu don ni mutum ne mai ƙyanƙyami.Ba zan taɓa iya zura gugata a kowani irin rijiya ba,sai wanda na san ni kaɗai ne na fara haƙashi,har na samar da gurbin da zan dinga zura gugata a ciki don samun tsaftataccen ruwa.Wannan ya zama karo na ƙarshe da zamu sake magana akan fitan dare, ko shigowar daren da nake yi Hannah,coz hakan ba abu ne da zai sauya ba." Ya dakata yana mai janyota zuwa jikinsa idanunsa fes akan ƙirjinta da ya fito sosai ta saman wuyar rigar baccinta.Sai ta lafe a ƙirjinsa tana sakin wani irin silent kuka mai motsa zuciya.Ya sake shigar da ita cikin jikinsa yana sunsunan wuyanta zuwa tsakiyar kanta,wanda ke fidda daddaɗan ƙamshin man gashin da take amfani dashi.A hankali ya kai hannu zai zame hannun rigarta tayi saurin dafewa tana ɗago idanunta da suka rine ta sauke a kansa,cikin wani irin raunin murya ta furta, "Bana so AD, bana son hakan domin na gama gane bani da wani saurin amfani a gunka sai na kwanciya dani, bayan kaje kun gama watsewa da ƴan matan naka a waje." Da idanunsa da suka sauya sosai ya dubeta, dukkanin haƙurinsa na fara ƙarewa.Don gaba ɗaya Remi ta gama kunna shi a club ɗinnan da salonta na son ta yaudareshi ya kwanta da ita, amma bata yi galaba a kansa ba.Ya fincike rigar da ƙarfi yana yin jifa dashi tare da haɗe bakunansu waje guda ya hanata dukkanin damar sakin masa kukan da tayi niyya.Da wani zafi-zafi yake haukata jikinta da salonsa, hannuwansa na kaiwa ko'ina cikin jikinta yana murza son ransa.Sai da ya tabbatar ya gama kashe dukkanin jikinta sa salonsa da sam bata iya tsallake tarkonsa,sannan ya kwantar da ita yana tashi ya zare wandon treequarter dake jikinsa.Sosai ya moreta cikin samun haɗin kanta kamar ko yaushe, don bata taɓa juya masa baya ba duk iya yadda ya ɓata mata rai, tana bashi haɗin kai domin shi ɗin shu'umi da ya san kan yadda yake tafiyar da ita a shinfiɗa.Ya iya gamsar da gangar jikinta irin gamsarwar da ake kira kankat! Hakan da ya gane tana da rauni a wannan fannin,kuma ta mato a kansa da yawa,shiyasa yake taka ta yadda yake so ba tare da ko sau ɗaya ya taɓa tunanin cewa yana cutar da ita da wannan banzar ɗabi'ar tasa ta yawan dare yana tarayya da mata suna rungume-rungume da tsotse-tsotsen juna ba.Sai dai kamar yadda ya faɗi ɗin ne iyakarsa dasu hakan ne kawai, bai taɓa kwanciya da kowace mace ba sai ita ɗin da ta kasance halilinsa wanda shi ya fara buɗeta a ledarta.Bai barta ba sai da ya tabbatar ita da shi sun samu cikakkaiyar nutsuwa, sannan ya zare jikinsa yana sauka daga bed ɗin ya nufi bathroom.Ta bi bayansa da kallo tana jin wata iriyar fitinanniyar ƙaunarsa na ninkuwa a zuciyarta.A kan idanunta ya fito ɗaure towel iya ƙugunsa, lafiyayyar fatarsa na zirar da ruwa don santsin fatar dake garesa yasa sam ruwa baya zama sosai akan fatarsa.Ta maida dubanta bisa kyakykyawar fuskarsa,tana sake tasbihi ga gwanin halitta wanda ya bashi baiwar kyawu tamkar shi ya yi kansa. AD Dukku kyakykyawa ne a jin ƙarshe, wanda ya mallaki cikar halitta da ƙira mai kyau da fisgar hankali.Fari ne sosan gaske don fatarsa har wani furu-furun ja yake yi.Yana da dogon hanci har baka,yana kuma da manyan idanu farare ƙal! Akwai shi da tsayi amma bashi da ƙiba sai murjewar jiki.A taƙaice dai yana da tsananin kyawun halittar da ke fusgar zukatan ƴan matan da suke hana rayuwarsa saƙat da bibiya.Shi a karan kansa ya san ya gama haɗuwa, musamman da Allah ya yosa cikin masu hannu da shuni.Kuma ya kasance wayayyen da samu buɗewar ido a turai, wanda boko da tsantar wayewa ya taka rawa wajen samar masa da wata iriyar rayuwa ta holewa.Hannah ta lumshe ido tana jin wani zafi-zafi a zuciyarta sakamakon irin baƙin cikin da take kwasa akan yawan darensa da kuma ƴan shaye-shayen ƙwayoyi da yake yi.Waɗanda take ganin suke sanya shi zafin kai da ƙeƙashewar zuciya yana zuba rashin mutuncinsa yadda yaso.Don ko kaɗan AD Dukku bashi da isasshshar kunya a idanunsa,ba kuma ya tsoron uban kowa.Yin kominsa yake kai tsaye cikin gadara da izzarsa tamkar wanda ya haɗa jini da sarauta.Hannunsa da ya kai ya ɗane idanunta ya sanyata sake narke fuska tana dubansa, ya balla mata wani irin harara yana faɗin, "Cinye ni zaki yi da wannan kallon ba zaki tashi ki tsarkake jikinki ba alhali kinsan bana son kwana da najasa ko?" Yadda ya yi maganar cikin tsare gida yana cigaba da banka mata harara ya sanya ta sakkowa daga bed ɗin.Ta kai hannu don ɗaukar rigarta dake yashe a tsakar ɗakin, amma kallo ɗaya ya yi mata ta fasa ɗaukar rigar, tana yin gaba ta nufi hanyar bathroom ɗin.Ji take tamkar ta kifa don tsananin kunyar dake ɗawainiya da ita,domin tasirin idanunsa da ke biye da ita take ji har cikin ɓargonta.Shi kam taɓe baki ya yi lokacin da ta ɓacewa ganinsa, yana sakin ƙaramin murmushi.Ya nufi closet ɗinsa yana ɗakko wata singlet da boxer ya sanya.Jin kansa yake fresh tamkar an wanke masa kwanya.Yana daga kwance ta fito ɗaure da ƙaramin towel,hanunta riƙe da wani tana tsane ruwan kanta da shi.Duba ɗaya tayi masa ta nufi hanyar barin ɗakin don drayer ɗinta na room ɗinta ne bashi anan ɗakinsa.Har ta kai tsakiyar ɗakin ya yi magana kai tsaye yana faɗin, "Dawo mu kwanta bana son ɓata lokaci please!" Zata yi magana ya banka mata wani kallo,hakan ya sanya ta juyowa tana dawowa ciki hawaye na biyo fuskarta sabida yadda ya yi maganar cikin tsawa tamkar bashi ya gama gigicewa har da sambatu a bed ba.Wutar ɗakin ta kashe kafin ta nufo kan gadon tana ji sanyi na shigarta, sabida kanta da yake a buɗe ga kuma uban sanyin AC da bata isa ta ce a rage ƙarfinsa ba don shi a haka ya saba kwana da ita komin sanyi ko zafi.Tana shiga cikin duvet ɗin ya janyota zuwa jikinsa tare da zare towel ɗin baki ɗaya ya wurgosu ƙasa.Gashinta mara yalwar cika da tsayi yake shafawa, damshin ruwan da ke jikin gashin da ƙamshin turaren wanka ta ɗauraye jikinta dashi na dukan hancinsa.Ya kai hannu ya shafo hawayen da ke sauka bisa ƙirjinsa yana yin ƙasa da murya ya furta, "Su hawayen na miye ne yanzu?" Bata yi magana ba sai sake manne kanta da ƙirjinsa da tayi tana baiwa breast ɗinta damar haɗuwa da nasa ƙirjin, hakan ya sanya tsigar jikinsa suka zuba ya sake matseta da kai hannu ya shafo abubuwan da suke tokaresan.Ya jima yana wasa da damshin ruwan da ke gashinta,har sai data fara tari alamun sanyi na shigarta sosai.Sai ya ɗan ɗago face ɗinta yana duban yadda duk ta narke masa.Murya ba amo ya furta, "Jeki busar da kan ki dawo, saura kuma kiyi zamanki tunda na ga alamun raini ya fara shiga tsakanina da ke Hannah!" Yadda ya yi maganar a dake ya sanyata dubansa tana jin wani maganaɗisu na yawo a cikin jininta.Bata san meyasa AD Dukku ya faye shegen son girma ba, sam shi baya son raini ko kaɗan.Yafi so koda yaushe a riƙa bashi girma ana shakkarsa,shi kuma ya riƙa tsula tsiyarsa yana taka ka yadda yaso.Bata jima ba kamar yadda ya buƙata, tana gama busar da gashinta da ba mai yawa bane ta dawo ɗakin nasa tana shigewa cikin duvet ɗin tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa.Ya zagayo hannuwansa duka biyun ya riƙo ƙugunta yana shinshinan ƙamshinta mai sanyi da daɗi sosai.Ya lumshe idanunsa baccin da ke ɗawainiya dashi ya fara fisgarsa har ya sacesa baki ɗaya. Ita kam Hannah ta jima baccin bai sureta ba, sabida tunanin halayyarsa da bata so da kuma yadda sam ta kasa samun cikakkiyar soyayyar AD Dukku ɗin.Tunda sukai aure tsawon watanni biyu da ɗuriya kenan,amma bata taɓa samun cikakkiyar kulawa da nuna ƙauna daga garesa ba.Idan har ta ga farin ciki da samun ƴar kulawarsa to a shinfiɗa ne idan ya dawo yana buƙatar kasancewa da ita, baya ga hakan bata isa ganin koda dariya akan fuskarsa ba sai ya yi ra'ayi ko kuma suna waya da Kakarsa mai ɓata shi.... Da ƙyar bacci ya sureta bayan ta gama tariyo tarin abubuwan takaicinsa,waɗanda take shaƙa tsayin watanni biyu da aurensu.Amma duk da tarin baƙin cikin da yake kimsawa zuciyarta, soyayyarsa da ƙaunarsa sake yawa yake a zuciyarta tamkar ta zautu. Washegari ƙarfe shida saura ta farka daga bacci, ta sauka cikin hanzari ta nufi toilet don ɗauro alwala.Sai da ta fito ta tada shi a nasa baccin, tana sanar dashi time ɗin sallah ya yi.Ya nufi toilet cikin sauri don mutum ne shi da duk iya rashin jinsa da buɗewar idanunsa baya wasa da sallah ko kaɗan, da zaran time ɗin sallah ya yi yake barin komi ya samu yinta akan lokaci.Wannan ɗabi'ar nasa ma na ɗaya daga cikin manyan ɗabi'un da suka siye zuciyar Hannah, har ta bari soyayyarsa ta rinjayi zuciyarta ta zaɓesa a matsayin abokin rayuwarta.Duk kuwa da cewa ba shi ne ya furta mata kalmar so ko ƙauna ba, hasalima ba don yana son ta aka yi auren ba, sai don ita data kafe ta kuma nuwa cewa soyayya da zazzafar ƙaunar da take masa kaɗai ya wadacesu.Aka kuma yi sa a ita ɗin ta fito a matsayin ƴar aminin Daddynsa da ya ɗauka tamkar uba mahaifi, wanda tasirin girman da Daddynta ke dashi a idanunsa, ya sanya ya amince da amsar tayin aurenta a lokacin da Daddynsa ya zaunar dashi, ya nuna masa kwaɗayinsu na son ganin aure ya wanzu tsakaninsa da Hannah.Domin tana tsananin ƙaunarsa,sai gashi bayan auren bada jimawa ba ta fara gane cewa tayi ganganci da kuskuren auren wanda bata gabansa.Domin AD Dukku bai taɓa fasa yin duk wani abu da ya yi niyya ba cikin rayuwarsa,bai taɓa fasa gudanar da tsarin rayuwarsa da ya yi sabo da shi ba, don tun tana da sati biyu a gidansa ya cigaba da fita yawan darensa zuwa club, yana harkansa da matan ƙabilu kala-kala.Don garin babu wasu hausawa sai tatattun ƙabilun da rabinsu ma ba musulmai bane, amma sun mato akan mijinta suna kuma ɗauke hankalinsa sosai wajen ganin ya kulasu koda ba zai kwanta dasu ba. Tunaninta ya katse lokacin da ya fito daga toilet ya nufo wajen da take zaune bisa sallaya tana azkar, ya yi tsaye yana jiran ta bashi waje ba tare da ya yi magana ba.Ganin hakan ya sanya ta sauka ta matsa daga gefe, shi kuma ya hau kan abin sallar yana tada sallarsa.......✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/11, 11:43 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 14* _Free page_ Ƙarfe takwas Adnan Dukku ya fito shirye tsaf cikin shirin fita office. A downstairs ya samu Hannah na ƙarisa shirya dining,don bata jima da kammala masa abinda zai yi breakfast da shi ba.Ya taka a hankali zuwa wajen dining ɗin,daddaɗan ƙamshin turarensa na cika wajen baki ɗaya. Hannah ta ɗago ta zuba masa ido tana kallon irin kyawun da ya yi,tayi ƙasa da murya tana gaida shi a narke.Ya amsa cikin basarwa yana jan kujera ya zauna,ita ma zaman tayi ta fara serving ɗinsa tana ji zuciyarta na sake narkewa a ƙaunarsa.Cikin nutsuwarsa yake cin abincin har ya kammala ya zari tissue ya goge bakinsa.Tashi ya yi yana dubanta kai tsaye ya furta, "Bola zai kai kai mana abincin lunch office, ina da baƙin da zasu iso daga lagos,so zamu muyi lunch tare da su a office." Hannah ta jinjina masa kai kafin ta furta, "Allah ya kaimu, but don Allah Hubby ka dawo gida yau akan time please!" Tayi maganar cike da magiya tana ji hawaye na cika idanunta.Ya yi mata duba ɗaya yana ɗauke kai ya fara takawa don barin wajen, ba tare da ya furta ko kalma guda ba.Bayansa tabi tana masa a dawo lafiya, ya ɗaga mata hannu kawai yana ƙarisa ficewa baki ɗaya.Ta juyo jiki a sanyaye ta nufi upstairs tana jin zuciyarta na sake yin nauyi, akan irin hakin ko inkulan da AD Dukku ke nuna mata.Watanni biyu da aurensu har wasu satukan asama, amma ta kasa samun soyayyarsa bare kulawar da ta dace daga garesa.Sam bashi da cikakken lokacinta sai na aikinsa da yawan zuwa club,idan dare ya raba ya dawo ba tare da jin shakka ko gudun ɓacin ranta ba.Idan yana da buƙatar kasancewa da ta ya kwanta da ita, idan baya buƙatarta kuma ko neman inda take ba zai yi ba.Wannan shi ne irin rayuwar da suke yi a cikin gidan shi, wanda sam ba haka tayi zato ko tsammani ba.Ta ɗauka duk irin yadda bai sonta a kai aurensu, da zaran ya kwanta da ita sau ɗaya zai fara sonta da tarairayarta kamar yadda ake rubuta musu a littafan hausa.Sai gashi saɓanin hakan take gani daga garesa, don duk yadda ta kai ga nuna masa kulawa da tarairaya ta kasa samun kansa.Sai ma ƴan matan waje da kullum suke sake zama barazana ga rayuwar aurensu, sabida yadda matan ƙabilu bama na hausawa ba ke matowa a kansa suna kuma binsa har club ɗin da yake zuwa suna sake dilmiyar dashi. Ta isa ɗakinta da ƙyar tana zama akan sofa ta zabga tagumi da hannu biyu, tana rasa abinda ke mata daɗi.Wayarta dake kan gado ta ɗauka ta dannawa Yayarta kira, wacce ita ce babba a ɗakinsu baki ɗaya mai suna Anty Laurat.Bugu ɗaya ta ɗaga wayar,sai kawai Hannah ta sanya mata kuka.Hakan ya ɗaga hankalin Anty Laurat ɗin,tayi saurin katse kiran tana sake kiran Hannah vid call don son ganin halin da take ciki.Kuka sosai Hannah ke mata tana sanar da ita irin baƙin cikin da AD Dukku ke kimsawa zuciyarta.Ta ƙare maganar da cewa, "Anty na rasa me zanyi na janyo hankalinsa gareni, duk wani abu da zan iya nayi amma bai yi tasiri ba don bashi da time ɗina kwata-kwata.Ina tsananin ƙaunarsa kamar na mutu,amma shi hankalinsa baya kaina Anty.Miye laifina don na mato a kansa da zai dinga wulaƙantani har hakan?" Anty Laurat da ke sauraren Hannah ta sauke numfashi mai ɗumi, zuciyarta cike da tausayin Hannah da irin muguwar soyayyar da take wa Adnan Dukku ta furta, "Hannatu abinda mukai ta jiye miki kenan tun farko da kika kafe ke sai shi.Shi namiji idan baya sonka takaici ne kawai a cikin tarayyarka dashi, sabida kome zaka yi ba lallaine ka samu zuciyarsa a lokacin da ka ke muradi ba.Musamman shi da ya kasance yana da kyawu da kuɗin da zai siye zuciyar kowace mace komin ajinta kuwa, sabida Allah ya yi masa baiwar kyau da zubin halitta.Ga kuɗi da waye da sukai masa zaman dirshan,hakan kaɗai ya isa ƴan mata su dinga binsa kamar jela,kuma hakan shi ke sake haifar masa da girman kai da jin cewa shi wani ne.Na sha gaya miki auren namijin da ya cika kyau ba ƙaramin tashin hankali bane Hannah, domin komin kamun kansa ba zai iya tsallake tarkon ƴan matan waje ba sai idan Allah ya yi mugun tsarewa.Takaicin su kaɗai ya isa bazarana ga rayuwar aurenki, don binsa zasu yi tayi office da duk inda suka san zasu samesa.Kiyi haƙury tunda kece ki ka zaɓesa,ki ka kuma nace sai shi ɗin duk da cewa kinfi kowa sanin bai taɓa kallonki da darajar da ya furta miki kalmar ƙauna koda sau ɗaya bane har aka ɗaura muku aure.Yawon bin club ɗinsa kuma dole shi ma haƙurin zaki cigaba da yi, tunda baki da ƙarfin iko da zuciyarsa tunda babu soyayyarki a ransa, bare kiyi amfani da ƙarfin soyayyar da yake miki wajen hanashi aikata dukkanin abinda zuciyarki bata so.Hannah koda ake cewa mace na sauya da yawa daga cikin munanan ɗabi'un namiji zuwa kyawawa, ki sani hakan na faruwa ne idan aka yi sa a an jarabci zuciyarsa da soyayyar macen.Amma idan babu so babu abinda zaki iya canjawa daga cikin munana ɗabi'unsa,sai ma dai ya cigaba da azabtar da zuciyarki don ya nuna miki cewa baki isa da shi ba." Anty Laurah ta dakata da maganar tana duban yadda Hannah ke cigaba da kuka sosai.Ta ɗago idanunta ta dubi Anty Laurat ɗin, tana ji dukkanin jikinta na mutuwa da kalaman Anty Laurat ɗin.Waɗanda kota ƙi ko taso dole sune iyakar gaskiyar, don kuwa gashinan AD na gasata son ransa ba tare da taci nasarar samun soyayyarsa ba.Cikin raunin murya ta furta, "Anty wallahi gaskiya kike faɗi, don ban taɓa tunanin zamu yi sati biyu ko uku da aure Adnan bai fara sona ba.Musamman dana sakar masa jiki ina masa dukkanin abinda yake so, amma shi burinsa ya ƙuntata mini.Idan nayi magana sai ya nuna ai shiɗin zaɓina ne,don haka ban isa hanashi gudanar da rayuwarsa a yadda yake so ba.Zafi nake ji a cikin zuciyata Anty akan yawan darennan da yafi komi baƙanta zuciyata.Ban taɓa damuwa da shan wasu ƙwayoyin da yake ba, don bai taɓa shigo min a buge ba tunda ba giya yake sha ba." Hannah ta dakata tana kasa cigaba da zayyano mata abinda ke mata ciwo akan irin ɗabi'un AD Dukku da ke baƙanta zuciyarta.Anty Laurat ta jima tana kwantar mata da hankali tare da bata shawarwarin da take ganin zasu amfani Hannah, daga ƙarshe sukai sallama da juna Hannah na aje wayar ta nufi toilet. Wanka tayo ta fito ɗaure da towel tana ji kanta na mata wani irin ciwo, a daddafe ta shafa mai ta zura riga ta kwanta ba tare da tayi tunanin sanya wani abu a cikinta ba.Dama tayi sabo da rashin karyawa da wuri, sam bata iya karyawar safe sai wajen 10am ko 11am haka.Don haka kwanciya ta yi don ta samu bacci sosai, ko ciwan kan zai faɗa mata idan ta tashi. ********* *Kaduna* Misalin ƙarfe goma na safe Najma ta isa part ɗin Momy bayan sun kammala yin breakfast.Tana sanye ne cikin ɗaya daga cikin boubous ɗin da aka siya musu ready made,kalar rigar dark pink ne wanda akai wa adon zane da blue black and white.Tayi kyau matuƙa fuskarta ya yi fayau babu kwalliya sai asalin natural black beauty face ɗinta ke haskawa,black skin ɗinta har ya fara samun sauyi daga fara amfani da sabulun african black soap ɗin da Nasreen ta ɗaukar mata.Bata samu kowa ba a falon, ko'ina tsit sai tashin ƙamshin turarukan wuta da roomfreshner's ke tashi.Cikin nutsuwa ta karya kwana zuwa hanyar corridor da zai sadata da falon Daddy,don tana da tabbacin suna can tunda bai koma Abuja ba yana gari.Ta tsaya daga bakin ƙofar ta tana doka sallama cikin siririyar muryarta,muryar Momy daga ciki ta jiyo tana amsa mata sallamar tare da bata izinin shiga.Ta shiga a nutse tana fara gaida Momy, don ita kaɗai ta samu zaune a falon. Momy ta amsa da fara'a tana sanar da Najma cewa Nasreen ta wuce school da sassafe ne.Najma tayi murmushi tana faɗin, "Ayyah! Shiyasa naji falon tsit! Nayi tunanin bata tashi bane ma." Kafin Momy tace komi Alhaji Kabeer Dukku ya fito daga ɗakinsa zuwa cikin falon, idanunsa akan Najma yake takowa zuwa ciki yana sake jinjina kamaninta da Inna Mairo da kuma baƙin fatar Malam Mahmuda da ta ɗakko. "Daddy ina kwana." Najma ta furta tana sake yin ƙasa da kanta lokacin da ya zauna kusa da Momy sosai har jikinsu na gugar juna.Ya amsa da fara'a yana faɗin,"Ya Innar taki ina fata kun tashi lafiya?" Najma ta amsa masa tana jin tsananin kunyar yadda ya wani mannewa Momy a jiki.Ita kuma tana ƙoƙarin fara serving ɗinsa abincin breakfast da aka shirya daga nan ƙasa akan ledar cin abinci.Ya dubi Momy da wani sassanyar kallo ya ce, "Zee tashi ɗakko min ledar dana shigo dashi jiya a bedroom." Momy ta aje serving spoon ɗin da take zuba masa farfesu a gefen chips da ta zuba a plate, tana mai faɗin, "Okay! Najma zo ƙarisa zuba ma Daddy abinci ko." Cikin nutsuwa Najma ta ƙarisa tana cigaba da serving ɗinsa,ita kuma Momy ta wuce zuwa bedroom ɗinsa don ɗakko saƙon. Daddy ya dubi Najma da ke faman loda masa soup ɗin ya ce, "Ya isa haka Najma, ko so kike Daddy ya aje jiki ya tsufa da wuri?" Ta yi dariyar maganarsa tana jin sanyi a ranta yadda yake sake mata fuskarsa tamkar su Nasreen.Leda Momy ta fito da ita riƙe a hannunta, ta aje a gabansa lokacin da ta ƙariso inda yake zaune tana faɗin, "Gashi Daddy!" Ya dubi Najma da tayi ƙasa da kaina alamun jin nauyi da kunya ya ce, "Ɗauki wannan ledar Najma ki je dashi, wayoyin hannu da layukansu ne na siya muku ke da Mairo.Babban cikin ita ce naki ƙaramar kuma na Innarki, idan Nasreen ta dawo skull sai ta koya miki yadda ake operating komi ko?" Najma ta ɗauki ledar cikin wani irin murmushi mai nuna tsantsar farin ciki ta ce, "Mun gode Daddy, Ubangiji ya ƙara arziƙi da wadata." Daddy cike da jin daɗin addu'arta ya furta, "Ameen Najma, abinda ya dace ne aka yi ai." Momy ta nunawa ledar tana cewa ta tayata su godiya, kafin ta ɗauka ta fice cikin tsananin zumuɗi ta koma part ɗin Gwaggo.Anan falo ta iske Inna Mairo tare da Tabawa mai aikin Gwaggo suna hira.Cike da zallar farin ciki Najma ta gaida Tabawa tana isa gaban Inna Mairo ta dire mata ledar wayoyin,tana sake faɗaɗa murmushinta ta ce, "Inna wayoyi ne Daddyn su Nasreen ya siya mana." Inna Mairo ta dubi Najma tana faɗin, "Ma Sha Allah! An gode masa,Allah ƙara arxiƙi da wadata." Gwaggo ce ta fito suka nuna mata tsadaddun wayoyin don ta tayasu godia. Nasreen na dawowa skull wajen 2 na rana, wanka kawai tayi taci abinci ta fita zuwa part ɗin Gwaggon, don a cike take da son ganin Najma don Daddy ya sanar mata ya siya musu waya.A ɗakinsu da aka ware musu ta samu Najma tana shirya musu kaya a drawer, ta isa da fara'a tana zama bisa sofa ta ce, "Idonki kenan Najma? Har na ganki jiya, kin kyauta." Najma ta saki smile tana sake jin ƙaunar Nasreen a ranta ta ce, "Yi haƙuri Sis, kallone ya ɗauke hankalina amma yau ai wajenki ma zan kwana." Nasreen ta saki ƙaramin dariya tana jin daɗin furucin Najma har cikin zuciyarta,ta sake narke muryarta ta ce, "Da ko kin kyauta beauty ɗin Inna,ina phone ɗin naki yake? Daddy ya ce zan koya miki yadda ake amfani da ita a kuma buɗe miki abubuwa masu amfani da zasu dinga ɗebe miki kewa." Najma ta isa saman madubi inda ledar wayoyin ke aje ta ɗakkowa Nasreen ɗin, ta miƙa mata tana faɗin, "Ya ce babbar ce tawa ƙaramar kuma ta Inna ce." Nasreen ta amsa ledar tana fiddo kwalin wayoyin ta furta, "Okey bari mu gani." Daga haka ta shigo fiddo wayoyin a cikin kwalayensu, tana yaba kyawunsu don Samsung ne na Najma mai muguwar tsada,sai na Inna Mairo kuma Nokia ce mai tsada ita ma android mai kyan gaske.Cikin ƙwarewa a iya sarrafa wayar hannu Nasreen ta sanya musu sim a wayar, tayi settings ɗin komi ta buɗewa Najma duk wata kafar sadarwa da take amfani da ita kamar su instagram,whatsapp,tiktok da kuma facebook.Ta miƙawa Najma wayar tana sanar da ita cewa akwai kuɗi da data mai yawa a wayar.Najma ta amsa wayar tana juyata a hannu tare da ganin komi tamkar a mafarki,"Wai yau ita ce da waya a hannu, kuma mallakinta? Ta tambayi kanta da kanta tana jin wani farin ciki na ratsa zuciyarta. Falon Gwaggo inda Nasreen ta baro su Inna Mairo suka nufa, Najma ta bai wa Inna wayar tana sanar da ita cewa Nasren ta saka mata layi anyi settings ɗin komi tare da sanya mata number ɗin su Momy da Gwaggo duk a cikin wayar.Inna Mairo ta amsa tayi godiya mai yawa, tana jin farin ciki na ratsa zuciyarta da samuwar wayar,don ta san waya babbar abu ce da ke taimakawa wajen sadar da zumunci a tsakanin ƴan uwa da abokan arziƙin da kukai nesa da juna dasu.Take ta sanya Nasreen ta sanya mata numbern Hakimi da akai saving a wayar Gwaggo,suna kiransa su gaisa duk safe da Inna Mairon har kuma yaba Inna Karima ita ma su gaisa.Kira aka danna masa don sanar dashi cewa ya yi saving number ɗin Inna Mairon.Sun jima suna gaisawa da juna bayan ya ɗaga wayar, Najma ma ta amsa sun gaisa ta kuma sanar da cewa Daddy tare da Inna ya siya musu wayar, don haka ya turo number ɗin Inna Karima ayi saving yadda zata dinga samun damar waya da su Hanne tunda basu da wayar.Ya taya su murna ya kuma yiwa Daddy fatan alkhairy, suka gaisa da Gwaggo daga ƙarshe sannan sukai sallama da juna.Ba a ɗauki lokaci ba ya turo lambar Inna Karima ta layin Inna Mairo, sai Najma ta kwashe a wayarta tayi saving kamar yadda Nasreen ta gwada mata yadda ake komi.Part ɗin su Nasreen ɗin suka kwasa suka koma, Najma na cike da ɗokin wayar sosai da sosai.Sun samu Nabeelah ta dawo kenan drivern gidan ƙawar Momy ya maido ta.Da fara'a sosai ta rungume Najma da tun a waya da Nasreen ta kira vid call ta ga Najma ta ji ita ma tana ƙaunarta. Najma ta dinga blushing tana yaba kirki irin na Ƴaƴan Momy da yadda suke nuna mata ƙauna, kamar yadda Momynsu ita ma take nuna musu ƙauna ita da Innarta.Hakan yasa hankalinta fara kwanciya da su, zuciyarta kuma ta fara samun nutsuwa tunda ta gane cewa su ɗin sun san darajan talaka .Basu fito a cikin irin masu arziƙin dake ƙyamar talaka koda ace jininsu ne ba. Suka zube anan babban falon suna hira, Nabeelah nata basu labarin yadda sukai shagwalinsu a birthday partyn ƙawarta Yasmeen.A haka Momy ta fito daga ɗaki ta samesu suna hiran gunin sha'awa, ita ma sai ta shige cikinsu ana yi da ita sabida so take Najma ta saki jiki da ita, ta ɗauketa tamkar yadda Ƴaƴanta suka ɗauketa suke sakin jiki da ita ta yadda take sanin dukkanin damuwarsu.Sai wajen biyar da rabi Momy ta bar cikinsu ta nufi ɓangaren Gwaggo don yiwa Inna Mairo rakiya zuwa asibitin su doctor Bakory.Koda ta shiga gaisawa kawai suka yi da Gwaggo ta sanar da Inna Mairo inda zasu tafin, Gwaggo tayi musu adawo lafiya tana jin daɗin yadda Momy ke ɗaukar komi na jinin Kabeerunta da muhimmanci. Lamiɗo driver ɗin Momy shi ne ya jasu zuwa haɗaɗɗen private hospital ɗinsu doctor Bakory, wanda ke da nisa sosai da unguwar rimi ɗin. Ana kiran magriba suka shigo gida don sosai aka duba Inna Mairo,sannan an sauya mata wasu magungunan na daban.Akwai kuma wani test da aka yi wanda sai a washegari result ɗin zai fita.Doctor Bakory ne da kansa zai amsa result ɗin,idan ya duba sai ya kira Momy ya yi mata bayanin abinda sakamakon ya nuna. ********** *Port Harcourt.* Hannah ce durƙushe a toilet tana faman kwara amai mai matuƙar wahalarwa. Tun tashinta wajen 11am na safe tayi breakfast ta sha maganin ciwon kai paracetamol, sabida sam bata ji sauƙin ciwon kanba koda ta tashi. Tana kwanciya kuwa ta sake komawa baccin, zazzaɓi na neman rufeta nan da nan.Bata tashi ba sai la'asar,ko sallar azuhur bata samu yi ba sai da ta tashi ta haɗa da la'asar ɗin tayi.Tana cikin cin lunch da Diana ta girka don ita ce tayi girkin tunda ita babu lafiya,already dama ta sanar da Diana ɗin Bola zai kai wa AD abinci office.Tana tsaka da cin abincin ne ta fara jin tashin amai,shine ta nufi toilet ɗin da ke nan cikin falon down stairs ɗin ta dinga kwarashi.Kakarin aman da take yi ne ya janyo hankalin Diana, ta iso da sauri tana mata sannu lokacin Hannah ta gama galabaita sosai, kai kawai take iya ɗagawa Diana.Hankalin Diana ya tashi sosai da ganin halin da Hannah ke ciki, ta riƙeta sosai tana taimaka mata ta wanke baki da fuskarta bayan aman ya tsaya mata.Cikin galabaita Hannah ta iso cikin falon ta zube bisa sofa tana sauke numfashin galabaita da wahala,ta baro Diana a toilet ɗin tana gyara inda aman ya ɓata ta kuma wanke wajen baki ɗaya. Lokacin da Diana ta fito da ƙyar Hannah ta iya buɗe baki ta sanar da ita ta miƙo mata wayarta dake kan table, ta ɗakko ta kawo mata tana sake mata sannu ta wuce zuwa kitchen don cigaba da aikinta.Saka kiran AD Hannah tayi tana fatan ya ɗauka akan lokaci, sai dai har kiran farko ya yanke bai ɗaga ba sai ana biyu sannan ya yi picking call ɗin.Da wani irin murya mai rauni ta sanar masa bata da lafiya ya zo ya kaita asibiti, don ba za ta iya driving da kanta ba.Bai ce komi ba sai kashe wayar da ya yi,hakan ya sanya Hannah rintse ido tana ji kuka mai ƙarfi na taho mata.Ta dinga yinsa anan cikin falon, tana ji zuciyarta na shiga ƙunci mai yawa da nadamar yadda ta mato akan soyayyarsa amma shi sam bata gabansa.Ba tayi tsammanin yadda ya kashe wayar zai ma dawo ɗin ba kamar yadda ta buƙata ba, sai kawai ta ji ƙaran buɗe gate da shigowar motarsa.Hakan ya sanya ta sake narkewa cikin sofan tana sake sakin sabon kuka ko zai ji tausayinta.Da ita ya fara cin karo naɗe cikin sofa tana faman shashshekan kuka, ya taka cike da nutsuwa da izzarsa ya isa wajen da take kwancen bisa sofa ya yi tsaye.Ƙamshin da ya cika hancinta na turaren CREED AVENTUS ya sanya ta gane yana kusa da ita ne, hakan ya sanya ta buɗe idanunta dake rufe ada tana kuka ta sauke akansa.Shi ma ya zuba mata ido zuciyarsa na ɗan harbawa.Cikin muryarsa mai cike da isa da aji ya furta, "What's wrong with u ?" Hannah ta matso wasu hawayen tana magana cikin rawar murya ta ce, "Amai da fever ke damuna,tun safe da ka fita a kwance na yini,please mu wuce asibiti Habibi!" AD Dukku sai ya ɗan kyaɓe baki yana miƙa hannu ya shafo saman kanta zuwa wuyanta yaji zafi rau! Hakan ya tabbatar masa da gaske zazzaɓin na damunta kamar yadda ta faɗi. Ya zauna daga gefen kujeran da take kwancen ya ɗagota baki ɗaya zuwa jikinsa yana faɗin, "Sorry! Bari in kira Doctor mu ji ko zai iya samuna gida ba sai mun fita zuwa asibitin ba." Bai jira cewarta ba ya saka kiran Dortor peter a wayarsa, wani likitan da sukai sabo sosai da shi,wanda ke zuwa har gida ya dubasa idan bashi da lafiya.Maganar mintuna uku zuwa huɗu suka yi,ya sauke wayar daga kunni yana kallon yadda Hannah ta nannaɗe a jikinsa tana goga masa zafin zazzaɓin da ya kama jikinta.Ya kai hannunsa saman ƙirjinta da suka ciko sosai ta samar rigar material ɗin da ke jikinta, ya shafosu da kyau yana jin yadda wajen ya ɗauki zafin zazzaɓin sosai.Ya ɗan lumshe idanunsa yana jin wani feeling mai ƙarfi, hakan ya sanya ya ɗauke hannunsa daga wajen ya kai bakinsa kusa da kunninta ya furta, "Let's go Hannah! Ba zai samu zuwa ba mu zamu samesa kafin ya tashi duty." Yana ƙare maganar ya miƙar da ita tsaye suna takawa zuwa upstairs tare.Hijab ta sanyo a ɗakinta shi kuma yana jiranta daga falon,don da gaske ya ji tausayinta don shi mutum ne mai tausayin mara lafiya.Sabida idan ciwo ya kamasa ya iya raki da shgwaɓa sosai, bayi son duk wani abu da zai taɓa lafiyarsa shiyasa idan mutum na ciwo yake tausayinsa musamman mace. Yana riƙe da hannunta suka sakko zuwa downstairs ɗin, sabida jiri sosai Hannah ke gani dole sai da taimakonsa za ta iya fita zuwa compound har ta shiga mota.Diana ta kira ta sanar mata sun fita asibiti, sannan ya cigaba da riƙon hannunta har zuwa wajen motarsa.Front seat ya buɗe mata ta shiga ciki, ya rufe murfin motar yana zagayawa ya shiga ɓangaren driver seat ya tashi motar suka fice daga gidan. Lokacin da suka isa asibitin basu ɓata lokaci ba suka samu ganin doctor Peter ɗin.Tambayoyi ya yiwa Hannah tana bashi amsa, daga ƙarshe ya sanyata ta yo test a lab ta kawo result ɗin.Yana buɗewa ya gano ciki ne da ita kamar yadda sakamakon gwajin ya nuna,hakan ya sanya shi ɗagowa da fara'a akan fuskarsa yana musu congratulation. AD Dukku da ya rasa murnar me Likita ke taya su,har sai da ya kasa daurewa ya tambayesa sannan likitan ya miƙa masa sakamakon gwajin,yana tabbatar masa da cewa cikine da madam ɗinsa na tsayin sati shida. Take dukkanin annurin da ke kan fuskar Adnan Dukku ya ɓace ɓat! Ya dubi Doctor Peter kai tsaye yana furta cewa, "No Doctor! Indai ciki ne bana buƙatarsa ciresa za a yi da gaggawa. Hannah da ke tsaye duk murnar samuwar ciki a jikinta ya gama kasheta, sai ta ɗago a tsananin razane tana duban Adnan Dukku da ke faman banka mata harara.Wani irin zufan tashin hankali ya rufeta lokacin da amon muryarsa ke ratsa kunnuwarta yana faɗin, "Yau nake so idan da hali a ciresa ba tare da ya sake kwana a jikinta ba, just 2 month kacal da yin auren ne zata yi ciki? No impossible! Ban shirya haihuwa ba yanzu doctor." Ya kai ƙarshen maganar fuskarsa da tai jajir don masifa na bayyana asalin ɓacin ran da albishir ɗin samuwar cikin ya haifarwa zuciyarsa.Ba Hannah kaɗai kalaman AD Dukku suka kaɗa ba, hatta doctor peter ya firgita da yadda ya nuna ƙin cikin kai tsaye haka.Ya dafo kafaɗun Adnan yana bashi baki akan ya amshi cikin tunda da aure suka samesa, sannan haihuwa is a big blessing da Ubangiji ke wa bayinsa. Amma maimakon Adnan ya ɗauki shawaran doctor Peter sai ma ya sake ɗaukan zafi yana tabbatar masa da cewa dole cire cikin za a yi don baya buƙatar haihuwa a yanzu.Fitar Hannah a guje daga office ɗin tana gunjin kuka shi ya ja hankalin AD Dukku, ya bi bayanta cikin hanzarin bayan ya sake jaddada kalmar roƙo ga Doctor akan ya bashi ko wani magani ne da zata sha cikin fita tunda sati shida kacal ne.Doctor Peter bai samu amsa masa ba, AD ɗin ya fice don rufawa Hannah baya. A jingine jikin motarsa ya sameta tana kuka sosai,ya ɓalla mata wani irin harara yana magana cikin tsawa yake faɗin, "Ni zaki fito ki bari a gaban likita ki zo nan kina kuka Hannah? Kukan cire cikin ki ke yi kona soyayyar da ki ke wa cikin da uban cikin? To bari kiji ko mutuwa zaki yi sai an cire cikinnan ban shirya haihuwa yanxu ba." Ya ƙare maganar yana komawa ciki ya barta a tsaye tana cigaba da kuka mai taɓa zuciya.Bata taɓa tsamannin Adnan zai ƙyamaci haɗa zuri'a da ita ba,duk da cewa ta san baya sonta amma hakan bai sa ta taɓa yin hasashen zai iya nuna bayason haihuwa da ita ba.Don abinda zuciyarta ta kimsa mata kawai shi ne ita ce da baya so, shiyasa ba zai so haihuwa da ita ba, ba wani maganar rashin son haihuwa yanzu bane ba yayi ɗin. Tana nan tsaye tana kuka ya dawo hannunsa riƙe da ledar magungunan da doctor ya rubuta ya saya,wanda a ciki har da takardan wani maganin zubda ciki da doctor Peter ya rubuta masa bayan ya tura masa kuɗi masu nauyi a account ɗinsa.Don da fari Doctor ɗin yaƙi bashi goyan baya akan a cire cikin,sai da yaji batun kuɗi sannan ya aminta da rubuta masa maganin da zai zubda cikin sauƙi idan ta sha. A jikinta ya yi wurgi da ledar magungunan yana bin ta da wani mugun kallon tsana, kai kace ita ce ta yiwa kanta cikin ba shi ba.Hannah ta sunkuyar da kai tana cigaba da kuka mai sauti, hakan ya sanya shi daka mata tsawar da ya tsaida kukan babu shiri.Ta ɗago idanunta dake zuban hawaye ta ɗaura a kansa tana faɗin, "Don Allah Adnan kar kace sai an fidda cikinnan,wallahi ina son sa tamkar yadda nake son ka.Ka barni da abuna domin ba zan taɓa iya zubda da kyautar da ba kowa Ubangiji ke yiwa ba, don wasu na can na nema da kuɗi ido rufe ba a basu ba.Amma kai an baka kana so ka yiwa Allah butulci sabida kawai baka sona, shiyasa ba za ka so haɗa zuriyyah dani ba ko? Miye aibun soyayyar da nake maka Adnan, miye laifi don an jarabci zuciyata da soyayyarka...." Kukan da ya sake taho mata ne ya hanata ƙarisa kalamanta, ta dinga yinsa tana ji tamkar ta shiɗe sabida yadda zuciyarta ke tsananin zafi.Ga zazzaɓin da ya sake rufeta dukkanin jikinta na ɗaukar rawar sanyi, wanda sanyin AC dake kunne ke sake tunzara rawar da jikin nata ke yi.Adnan da ke saurarenta har ta dasa aya tana cigaba da kuka, ya kasa cewa da ita uffan don a yadda zuciyarsa ke tafasa da ɓacin ran samuwar cikin yanzu, yana cewa zai yi magana to ba alkhairy zai faɗi ba. Sannan yana ganin tunda Doctor ya rubuta masa maganin zubda cikin, gani yake yi cikin ma ya zube ya gama.Don haka bashi da lokacin ɓatawa wajen sake jaddada mata ƙudirinsa. Ya yi biris da ita tana faman kukan da ke sake ƙona zuciyarsa,amma bai sake tanka taba har suka isa wajen wani babban pharmacy ya faka motar.Ya fita cikin zafin nama yana barin Hannah da bin bayansa da kallo, zuciyarta na sake matsewa da wani irin abu mai nauyin gaske.Bai jima ba ya fito hannunsa riƙe da wani ƙaramin leda, ya buɗe motar ya shiga ya tayar suna hawa kan kwalta.Kallo ɗaya ya sake mata ya ɗauke kai,bai sake duban inda take ba har suka isa gida.Ta rigashi ficewa daga motar ta nufi cikin gidan da gudu-gudu tana cigaba da kuka sosai.A ɗakinta da ke sama ta zube bisa bed tana ji tamkar kanta zai rabe gida biyu, ga zuciyarta da tayi mata mugun nauyin da take ji tamkar an ɗaura mata bulo.Dukkanin jikinta na sake ɗaukar rawar zazzaɓin da ke huda cikin ƙashinta.A haka ya turo ƙofa ya sameta, ya cilla ledar magungunan bisa kan gado yana magana cikin dakiya ya furta, "Ki tashi ki nemi wani abu kici sai ki sha magungunan zazzaɓin gasu nan,sannan ki tabbatar dukkaninsu kika sha zan yi wanka da sallah in dawo don ganin kinyi yadda nace ɗin.Daga haka ya fice daga ɗakin ya bar Hannah na cigaba rasgar kuka, tayi mai isarta kafin ta lallaɓa ta yo wanka ta fito ɗaure da alwala.Da ƙyar a zaune ta gabatar da sallar magriba da ya riskesu akan hanya,ta idar da sallar tana jan jiki ta koma gado.Wayanta ta ɗauka ta kira Diana ta ce ta kawo mata fresh milk mara sanyi, ta kuma yi mata warming meat pie da ke fridge.Koda Diana ta kawo mata kaɗan ta iya cin meat ɗin ta sha madarar mai yawa ta aje.Ledar magungunan ta janyo tana duba su ɗaya bayan ɗaya,ta tsaida idanunta akan ƙaramin ledar da ya fito dashi daga pharmacy ɗin da suka tsaya dashi a hanya.Haka kawai ta ji a jikinta maganin bai kwanta mata ba, sai ta ware shi daban tana ƙin shan sa, ta ɓalli sauran ta sha tana komawa ta kwanta hawaye na cigaba da kwaranyowa daga cikin idanunta........✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/11, 1:35 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 15* _Free page_ Tamkar wacce aka dallawa mari haka ta tashi zumbur ta diro daga bed ɗin, sabida tunawa da tayi da cewa zai shigo tabbas ya duba kota sha maganin.Ta san halinsa sarai duk abinda ya faɗesa sai ya cika shi, don baya magana biyu ko faɗin abinda ba haka yake a zuciyarsa ba.Ta janyo ledar maganin da bata sha ɗin ba ta ɓalli guda biyu kamar yadda aka rubuta,ta nufi toilet tayi flushing ɗinsu ta dawo ta kwanta. Koda da ya shigo ya sameta a kwance idanunta a lumshe hawaye na kwarara daga cikinsu,sai ya nufi inda magungunan suke yaba duba one by one.Ganin duka ta ɓalla ta sha ya sanya shi sauke a jiyar zuciyar da ta jiyo sautinsa,hakan ya sake tabbatar mata da cewa a kwai wata a ƙasa kenan.Sai ta sake rintse idanunta tana hana kanta yin duk wani motsi da zai gane idanunta biyu ne.Ya tako zuwa bakin bed ɗin ya yi tsaye yana ƙare mata kallo, kafin a hankali ya zame ya zauna daga bakin gadon.Hannu ya kai ya janye rufan da tayi sabida sanyin da take ji na zazzaɓi, ya aza hannayensa duka biyu ya tadota zaune.Har lokacin ta kasa buɗe idanunta da sukai masifar yi mata nauyi, sai da taji hannunsa cikin rigarta sannan tayi saurin buɗe idanunta da suka ɗan kumbura ta aza a kan kyakykyawar fuskarsa da ya tamketa sam babu annuri. Bai kalleta ba ya sauke rigarta zuwa ƙasa yana yin baya da hannunsa ya ɓalle huck ɗin bra ɗin da ke jikinta,tsayayyun ƙirjinta da suka sake cika suka bayyana a fili.Ya dinga binsu da kallo tamkar mai son gano wani abu a jikinsu,kafin a hankal ya kai baki ya sumbacesu yana faɗin, "Ban shirya bane Hannatu, sam ban shirya zama Daddy a daidai wannan time ɗin ba.Dole cikinnan a cireshi don ba zan iya amsarsa yanzu alhali duka ban gama morarki ta yadda za a ce har kin yi ciki ba." Ya ƙarisa maganar yana kai bakinsa kan ƙirjinta ya yi musu wani irin sumbatar da ya sanya ajiyan zuciya ƙwacewa Hannah.Kalamansa suka dinga ƙona zuciyarta tana ji sam bata ƙaunar ganinsa ma a gabanta.Ganin yana son raina mata wayo da salonsa ya sanya ta sakar masa kuka tana faɗin, "Banaso AD, please ka daina taɓani bana son hakan tunda kana ƙyamar haɗa jini dani, don kawai baka ƙaunata." Yadda tayi maganar ta motsa zuciyarsa da gaske,amma bai bari ta gane hakan ba don ya riga ya sanyawa ransa ƙin cikin da kuma ɗaukar alwashin rabata dashi.Don haka bai sake cewa komi ba ya tureta daga jikinsa bayan ya gama yamutsa ƙirjinta da tsotsesu son ransa.Ya fita ya barta tana kuka sosai mai asalin cin rai da motsa zuciyar duk wani mai sauraranta.Tunda ya yi wannan fitar bata sake jin ɗuriyarsa a cikin gidan ba har ta kwanta bacci, ta farka ne cikin tsakiyar dare sakamakon wani amai da ya tadata ta nufi toilet ta dinga kwarashi.Ta fito daga toilet ɗin kenan bayan ta wanko baki da fuskarta ta jiyo shigowar motarsa cikin gidan.Ta dubi agogon ɗakinta wanda ke nuni da ƙarfe biyu ne har da rabi na dare, ta janyo ƙafa zuwa bakin gadonta tana ji zuciyarta na sake ɗaukar zafi da ƙuna.Tana jiyosa ya hawo upstairs ɗin ya nufi ɗakinsa, tamkar ta bisa ta ga idanunsa amma takaicin yadda yake ƙin cikin jikinta da rashin ƙaunarsa gareta ya hanata yin hakan.Sai ta koma ta kwanta zuciyarta na kisima mata abubuwa da yawa a kansa, sannan batun cire cikin na zaune daram a zuciyarta tana tunanin yadda zasu kwashe dashi zuwa gobe idan ya gane bata sha maganin ba.Ta dinga faman tunanin hanyar da zata bi don ganin ta tseratar da cikin jikinta daga bazaranar da AD ke yi, na sai an zubda shi dole.Tunaninta ya tsaya akan ta kira Momynsa da safe ta sanar da ita halin da ake ciki, don ita kaɗaice ke sanya shi abu ya yi ko baya so.Amma baya ga ita baya jin magana ko shakkar kowa, yin kominsa yake gaba gaɗi musamman da ya samu kakarsa ta ɗaure masa gindi bata son ɓacin ransa ko ƙanƙani.Da wannan decision ɗin da ta yanke na sanar da Momynsa halin da ake ciki, ta samu bacci ya sace ta ba tare da tayi tunanin bi ta kan AD Dukku da ya dawo cikin wannan tsakiyar daren ba.Sabida ba yau ne karon farko ba,ya rigada ya zame masa sabo yawon dare zuwa club ya dawo cikin tsakiyar dare. ********** *Kaduna.* Najma a part ɗinsu Nasreen ta tare har dare, sai hiransu suke yi da Nabeelah wacce har tafi Nasreen son hira ma sosai. Sai around 10pm ta tashi zata koma part ɗin Gwaggo amma sai Momy ta hana, ta ce mata kawai ta kwana anan ɗin don Daddy ya ce ma gabaki ɗaya zata dawo side ɗin da zama ne wajen ƴan uwanta su Nasreen. Suka cigaba da hiransu rabi kuma suna kallo, gefe guda kuma su Nasreen hankalinsu na kan wayoyin hannunsu suna chart da friends ɗinsu.Kiran Anty Jiddah ne ya shigo wayar Nasreen vid call, ta ɗaga da murmushi akan fuskarta tana faɗin, "Sweethrt sai yau kika tuna damu? Ina ta kira wayarki a kashe so nake in nuna miki sabuwar Sis da muka yi a gidan fa." Nasreen tayi maganar da wani irin shagwaɓar da ya bai wa Najma mamaki.Ta dubi Nasreen ɗin lokacin da muryar Jiddah ya ratsa kunnuwarsu tana faɗin, "Sorry dear! Hubby ne ya kashe wayan ya amshesa don ya ce bani da time ɗinsa sai na kiran waya gida kamar a kaina aka fara nesa da ƴan uwa.Yanzu haka ya fita ne ya barni da ƙyar na gano inda ya jefa min wayar, shi ne fa yanzu na kira." Nasreen ta jinjina kai tana faɗin, "Lallai ne Uncle Muhsin, so ya london hope kina enjoying?" Jiddah ta furta, "Sosai Sis, ina Momy ne? Na kira wayarta busy." Nasreen ta bata amsa da faɗin, "Yanzu ta shige room may be suna waya da Daddy ne." Jiddah ta gyaɗa kai tana komawa kan batun Nasreen na cewa sunyi sabuwar Sis.Nasreen ta haska mata fuskar Najma da hankalinta ke kan TV tana faɗin, "Hey! Najma ɗago ku gaisa da Anty Jiddah." Najma ta waiwayo da murmushi akan fuskarta tana kallon allon screen ɗin wayar, suka gaisa da Jiddah cikin fara'a sosai,don ita ma yawan murmushi gareta tamkar Momy. Sun jima suna hira tsakanin Nasreen da Anty Jiddah, sannan Nabeey ta amshi wayar ita ma suka yi maganar tana sanar da Jiddah lallai a siyo mata tsarabar london.Najma ta dubi Nasreen bayan sun kammala wayar da Anty Jiddah ta ce, "Gaskiya Sis Anty Jiddah duk ta fiku kyau!" Nasreen ta saki murmushi tana faɗin, "Ita kuma duk kyawunta Yaya AD ya fita ba." Najma tayi murmushi tana jinjina kai ta ce, "Taɓ! Lallai kam kyakykyawane idan har yafi Anty Jiddah kyau." Nasreen ta saki smile tana faɗin, "Zaki gansa ai watarana da idonki Najma, daga lokacin zaki tantance cewa ya fita kyan.Amma fa Yayan namu ba ƙaramin tsoronsa muke ba, don fitinanne na bugawa a jarida." Cikin nuna halin ko'inkula Najma ta jinjina kai ta ce, "Dama su Maza haka suke idan sun ga sune manya a gida, sai suyi ta takurawa ƴan matan gidan da nuna musu shegen son girma da isa.Su Yaya Auwalun gidan Baba Hakimi ma haka suke wa ƙanninsu su Lubah mazurai, ni kaɗaice basawa hakan wallahi." Najma ta kai ƙarshen maganar tana tunowa da aminanta su Lubah, waɗanda suka gama shan waya dasu ɗazu suna ta taya ta murnar tayi waya.Nasreen ta sake sakin ƙaramin murmushi tana duban Najma kai tsaye ta ce, "Hmm! Sis ke dai kawai ayi shiru, amma duk yadda zamu kwatanta miki waye Yaya AD ba zaki gane ba." Daga haka suka rufe chapter ɗinsa Najma na basu labarin kalar rayuwar da suka yi a makarantar ƴan mata dake basawa.Nabeelah ta dinga tuntsura dariyar yadda Najma ta sha wuya a hannun jeniors kafin ta gyare, ita kuma Nasreen birgeta Najma ta dinga yi tana yaba sanyi da daɗin amon muryarta da ke fita a nutse.Sai ƙarfe 11pm na dare suka nufi room ɗin Nasreen don kwanciya, ita kuma Nabeey ta wuce nata room ɗin da ke manne dana Momy daga ciki. Washegary Nasreen na bacci Najma ta sulale ta koma part ɗin Gwaggo, ba tare da ta jira kowa ya tashi daga sashinsa ba.Ita ma kuma bata yi karanbanin sake zuwar ma su Rabi kitchen neman tayin aiki ba, duk da cewa abin na ranta tana kuma da burin son ta iya girke-girke kala-kala.Ko anan part ɗin Gwaggo ta tadda babu motsin kowa ya tashi a cikinsu,hakan ya sanya ta lallaɓa ta shige room ɗinsu ta samu Inna Mairo bisa gado ita ma tana faman juyi.Don ita ma ba gwanar komawa baccin safen bace, don haka sai suka ɓige da hiransu har gari ya sake wayewa sosai rana ya fito.Wanka suka yi duka suka shirya cikin shiga mai kyau na tsadaddun suturun da aka siya musu.Sosai Najma ta sha kyau cikin wasu skat da riga ƴan kanti masu shegen kyau! Rigar a sake take bata kama jikinta ba, amma kuma ta bayyana tudu da cikar ƙirjinta sosai.Waɗanda suke a tsaye cur cikin push-up bra da ya sake ɗagosu ya tsayar. Ba gwanar yin kwalliya bace don bata ma iya ba kai tsaye za a ce, tunda bata karambanin yinsa ma.Iyakarta shafa powder ta sanya kwalli da man baki, hodar ma fara tafi shafawa don ta kance baƙin fuskarta da farar powder zata fi dacewa.Sai dai a yanzu ta ƙaryata hakan, tunda ta shafa haɗaɗɗiyar powder ɗin mary kay mai tsadar da Nasreen ta saya mata. Sai ta ga tabi baƙar fuskarta tayi mata kyau,don kalar da aka zaɓar mata dama don irin su baƙaƙen fata aka yisa.A yanzu ɗin ma powdar kaɗai ta shafa ta goga man baki, ko tozalin ma bata sanya ba don babu shi a cikin kayan shafan da aka siya mata.Tare da Inna Mairo da tayi shar cikin jar doguwar rigar atamfar holland suka fito xuwa falon Gwaggon,sunyi xaman kamar mintuna goma sannan Gwaggon ta fito.Tayi kyau cikin riga da zani na wani irin material da suka kasa bambace voile ne ko kuma wani abin daban.Ta zauna a kujeran da tayi sabo da zama a kai, idanunta akan Najma wacce tayi mata mugun kyau da shigar jikinta, ta dinga kallonta tana amsa gaisuwar da Najmar ke mata.Inna Mairo ma suka gaisa da Gwaggo cikin girmamawa, Gwaggon na tambayar Najma amma dai gudowa tayi bata bari su Nasreen sun tashi ba? Najma tayi murmushi kawai ba tare da ta iya cewa komi ba.Suka haɗu sukai breakfast a nan tsakiyar falon Gwaggon, wanda aka shinfiɗa babbar ledar cin abinci kamar ko yaushe a saman carfet ɗin dake tsakiyar falon. Suna kammalawa Nasreen na shigowa cikin shirin fita skull,ta sha gayu cikin wani haɗaɗɗen gown na lace.Wanda kallo ɗaya zakai ma lace ɗin da ɗinkin da ya samu kasan cewa kuɗi sunyi kuka.Sannan colour ɗin lace ɗin da ya kasance black and silver ya haske farar fatar Nasreen ɗin, ya yi mata mugun kyau tamkar ka saceta ka gudu.Ta samu waje ta ɗosana ɗuwawunta tana gaida su Inna Mairo cike da ladabi,suka amsa da fara'a Inna na tambayar cewa halan skull xata wuce? Nasreen ta bata amsa da cewa, "Eh!" Najma ta dubi Nasreen tana ɗan yin ƙasa da murya ta ce, "Morning Sis, hope kin tashi lafiya?" Nasreen ta ballawa Najma harara tana faɗin, "Bansani ba ƴar rainin sense, kawai saina dinga tashi bacci bana ganinki kin ɓace ɓat a sashin baki ɗaya kin gudo nan kamar wacce ta kwana a ƙaya." Najma ta saki dariyarta mai kyau ta ce, "Sorry Sis! Ni ban iya wannan baccin safen bane shiyasa na gudu wajen Innata kawai." Nasreen ta sake hararanta tana miƙewa tsaye tare da gyara zaman veil ɗinta ta ce, "Ni xan wuce skull Sis sai 4 zan dawo yau,kinga kenan zanyi missing ɗinki." Najma da ƙaunar Nasreen ke sake kamata, sai ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Nima haka, but ayi karatu da yawa Sis sai kin dawo." Nasreen ta ɓata fuska tana cewa, "Babu ma rakiya kenan ko?" Najma da su Gwaggo suka sanya dariyar yadda Nasreen ɗin tayi maganar cike da shagwaɓarta na sabo.Najma ta tashi tana duban Inna ta ce, "Inna bari na rakata, daga can zan shiga mu gaisa da Momy." Inna Mairo ta jinjina kai ta ce, "Adawo lafiya, nima ki ce ina gaidata kafin in shigo." Daga haka Najma suka jera da Nasreen suka fito har zuwa parking space na gidan.Najma na sake yaba tsaruwar gidan da kyawunsa duk idan ta fito harabar gidan.Sai da motar Nasreen ta fice daga gate ɗin gidan sannan ta juya ta nufi part ɗin Momy ɗin. ********** *Port Harcourt.* Lafiya lau ta tashi ta gabatar da sallar asuba,jikinta bata jin ciwon komi sai kasala da tarin damuwa da tunanin da suka cunkushe zuciyarta.Don ji take yi sam ba zata yadda AD ya samu nasarar rabata da cikin jikinta ba,don tana tsananin son cikin da gaske. Wayarta ta janyo ta turawa Momynsa text tana sanar da ita halin da take ciki, ta dinga bin saƙon da kallo bayan ta tabbatar da tafiyarsa.Zuciyarta taji na ɗan yin sanyi,domin tasan matuƙar saƙon ya isa ga Momynsa ta kuma karanta to tabbas cikin ya tsira ya gama.Ta miƙe da ƙyar ta isa ga bed tana son sake rintsawa kafin 6:30am ta cika ta fita don sama masa abinda zai ci kafin ya wuce office.Wani irin bacci ne mai ƙarfi ya ɗauketa, bata tashi farkawa ba sai 7:30am.Ta diro a gigice daga bed ɗin tana kallon time, zuciyarta na bugawa da tunanin yana dab da fitowa don wucewa office. Kusan a guje ta sauka zuwa down stairs don shirya masa abu mai sauƙi da zai ci.Ta tadda Diana kusan duk ta kammala aikin gyaran downstairs ɗin,ko'ina na fidda sassanyar ƙamshi mai ratsa zuciya.Toasting bread tayi masa ta dafa ruwan tea ta soya egg, ta juye komi a inda ya dace ta ɗakko zuwa dining area dake nan ƙasa.Tana aje tray ɗin yana ƙarisowa wajen cikin shirinsa tsaf!Daddaɗan ƙamshinsa na cika wajen yana ratsa kafofin hancinta.Ta ɗaga idanunta tayi masa kallo ɗaya tana mai saurin yin ƙasa da kanta,don wani irin tashin hankali ta shiga da ganin kallon da ya jefo mata.Da ƙyar ta iya gaida shi ƙirjinta na faman bugun da ta kasa dubansa, sai ma ɗauke kai da ta sake yi tana jin wani fargaba na sake shigarta.Ya ja kujera ya zauna yana fara haɗa tea da kansa ba tare da ya jira ta haɗa masa ba,ganin hakan ya sanya ta saurin ɗago kai ta saci dubansa zuciyarta na sake shiga tashin hankali.Plate ɗin da ta zubo masa toested bread with egg ta tura gabansa,cikin aro jarumta ta furta, "Sorry na tashi late ne Hubby, wannan ɗin kaɗai na samu yi." Bai tanka ba sai ma siffing tea ɗinsa da ya fara yi hankali kwance.Ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ji bugun zuciyarta na ƙaruwa, don wannan shirun nasa ta san bana lafiya bane.Wajen ya ɗauki shiru sai ƙamshinsa da ke shiga hancinta ke sake haifar mata da shiga wani yanayi.Kamar daga sama ta jiyo muryarsa a dake yana kiran sunanta, "Hannatu!" Ta ɗago kanta da sauri tana duban fuskarsa, wanda ya haɗeta tamkar bai taɓa sanin wani abu wai fara'a bare dariya ba a duniya.Take taji ƙirjinta na sake sauya bugu da matsanancin tsoron abinda zai faru, ta amsa cikin karyewar murya hawaye na cika idanunta.Bai dubeta ba ya ɗaura da cewa, "Ki zaɓa ko cigaba da zama da AD Dukku ko kuma cikin jikinki,cikin biyu dole ki zaɓi ɗaya tunda har kika yi gangancin kai ƙarata wajen Momy!" Yadda ya yi maganan hankali kwance yana jifanta da wani irin kallon tsananin jin zafinta, sai hakan ya sake kiɗima zuciyarta.Hawayen da take riƙewa suka ɓalle mata,ta buɗe baki cikin harɗewar murya da rawar harshe ta ce, "Na zaɓi dukan ku AD, na zaɓi zama da kai sannan na zaɓi cikin jikina domin ina tsananin ƙaunarku kai da cikin.Don Allah kar hukuntani da abinda bani na bai wa kaina ba, Allah ya bamu wannan kyautar don haka kayi haƙuri mu am....." Tsawar da ya daka mata ne ya hanata ƙarisa kalamanta.Ya nuna ta da yatsarsa lokacin da yake miƙewa tsaye ya ce, "Sai kin zaɓa Hannatu, dole sai kin zaɓa koni ko cikin jikinki domin ban shirya amsarsa ba.Ina magungunan da aka baki, baki sha duka bako?To bari kiji tunda kika kai ƙarata kika haɗoni da Momy sai ki zaɓa koni ko cikin,idan kuma ba hakan ba karki bari ma na dawo daga office na sameki a cikin gidannan na taddaki yau!" Yana gama maganar ya kwashi wayoyinsa ya bar mata wajen ya yi tafiyarsa don wucewa office. Hannah da ta bisa da kallo zuciyarta na sake mutuwa a ƙaunarsa, bata san lokacin da wani gigitaccen kuka ya ƙwace mata ba. Ta nufi upstairs tana yinsa tamkar ba za ta daina ba.Kira da ke shigowa wayarta ya sanyata tsaida kukan tana ɗakko wayar don ganin mai kiran haka da safen nan,don ba a saba kiranta da sassafe haka ba.Sunan Momynsa da tayi saving da Momyn AD ta gani,hakan ya sanyata ɗaga wayar tana sake sakin wani sabon kukan mai sauti sosai.A cikin yin kukan take gaida Momyn tana sake faɗi mata abinda AD ya ce mata kafin ya fice daga gidan.Ta ɗauki tsayin mintuna shiru tana sauraren abinda Momyn nasa ke faɗi mata daga ɓangarenta.Zuwa wani lokaci ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "To Momy zan taho, kuma ba zan faɗiwa kowa ba In Sha Allah!" Daga haka ta sake yin shiru kafin ta sake furta, "To Momy zan yi duk yadda ki ka ce." Daga haka ta sauke wayar a kunni wasu sabbin hawaye na shatata daga idanunta.Hukuncin da Momy ta yanke akan tabi flight ta koma KD ya yi mata tsauri, amma ta san Momy ba zata faɗi abinda zai zamo aibu ba sai abinda zai sama mata fita daga wulaƙancin AD Dukku.Wanda ya gama fahimtar ta gama matowa a kansa, shiyasa yake taka ta da wulaƙantata son ransa.Ta ɗauki waya da sauri don sayen ticket ɗin jirgin da zata bi a yau zuwa KD ɗin idan zata samu.Cikin sa a ta sayi ticket ɗin jirgin da zai tashi a yau ɗin da misalin 3pm na yamma. Ta aje wayar lokacin da ta kammala da komi tana ji zuciyarta na mata nauyi matuƙa, sai ta tashi ta nufi bathroom tayo wanka ta fito.Cikin wasu riga da wando masu faɗi marasa nauyi ta shirya kanta, ta ɗaure gashinta da band tana fitowa zuwa downstairs domin cin abinci.Ita ma tea ɗin da ragowar bread ɗin da ya rage ta ci, tana mamakin yadda yau ta karya da wuri cikin jin matsananciyar yunwa.Sai dai tunawa da tayi ba ita kaɗai bace a yanzu sai mamakin hakan ya ragu a zuciyarta, ta kammala da cin abincin tana mai komawa zuwa upstairs ta nufi ɗakin baccinsa.Da kayan da ya cire ya barsu zube a tsakar ɗakin ta fara cin karo, sai ta nufi tsakiyar ɗakin hancinta na cika da ƙamshinsa da ya kama ko'ina da komi nasa.Kayan ta kwashe takai inda suka kamata,kafin ta fara gyaran ɗakin tana yi hawaye na zuba mata na tsananin kewar ganinsa da zata yi.Ta zauna daga kan sofa tana sharan hawayen da suka kasa tsaya mata,zuciyarta na cigaba da tunanin miye ne aibunta da AD Dukku ya kasa ƙaunarta? Me ta rasa da har yau ta kasa samun zuciyarsa bare kulawa da nuna mata tarairaya irin wanda ta sha mafarkin samu daga mijin aurenta? A hankali wani ƙaramin kuka ya ƙwace mata mara sauti sosai.Tayi mai isarta kafin ta rarrashi kanta, tana bai wa kanta ƙwarin guiwar tafiya ta barsa kamar yadda uwarsa ta ce.Hakan kaɗai ne mafita a gareta matuƙar tana son cikin jikinta da ita kanta su tsira daga fuskantar fushi da wulaƙancinsa.Bata baro ɗakin nasa ba sai da ta gyare ko'ina cikin dakiya da ƙarfin hali,domin ba za ta iya fita ta bar ɗakin a haka ba alhali tayi sabo ita ce mai gyara masa ko'ina ɗin.Diana ɗakunanta kawai take gyarawa, amma bata gyaran ɗakinsa wannan aikinta ne da take ganin ita kaɗai ta cancanta ta yisa.Kaya ta haɗa cikin madaidaicin akwati, wanda ya ɗaukar mata kaya masu ɗan yawa da duk wani abun buƙata.Kamar ta ɗaga waya ta kira Yayarta Anty Laurah ta sanar da ita komi, sai gargaɗin Momy na cewa karta sanar da Hajiyarta ko Anty Laurah ɗin ya faɗo ranta.Ta aje wayar tana ji damuwar duniya na rufar mata.Kanta ya fara ciwo babu ƙaƙƙautawa, hakan ya sanya ta tuna bata sha magungunanta ba.Sai ta ɗakkosu ta sha tana mai zuba su cikin tsadaddiyar hand bag ɗinta na BVLGARI,wanda ta shirya duk wasu ƙananun abubuwan da xata buƙata a ciki.Hatta da maganin da ya saya daban a pharmacy ɗin da suka tsaya, sai da ta saka su cikin bag ɗin, ta zuge jakar tana tunanin yadda zata isa gaban Momy ta nanata mata zancen zubda cikin da AD ɗin ke so ayi. Wayarta ta janyo ta tura masa saƙon cewa zata bi jirgin 3pm zuwa KD bisa umurnin Momy. Daga ƙarshen saƙon tayi amfani da kalamai na soyayya da ban haƙuri, tana sake jaddada masa irin soyayyarsa dana abinda take ɗauke dashi da ke bin jininta.Don haka ba za ta iya zaɓan ɗaya ta bar ɗaya ba, dukkaninsu take so ta kuma zaɓa. Lokacin da saƙon ya nuna ya tafi, komawa tayi ta zame kwance bisa sofa tana hawaye sosai.Idanunta a lumshe suke amma hawaye ne ke biyo fuskarta a guje, sabida tsananin zafi da wani irin karyewa da zuciyarta ke yi akan zazzafar ƙaunar da take masa.Ta miƙa hannu ta shafo lafaffan cikinta, tana jin wani irin feeling mai zafi na tsananin ƙaunar cikin da ke manne a haifarta na ratsata.Sosai ta hana kanta sukuni da kutsawa duniyar tunanuka kala daban-daban, har zuwa sanda ta ji ƙarar shigowar saƙo cikin wayarta.Hannunta har rawa yake lokacin da ta ga sunansa ne akan saƙon, alamun reply ya yo mata na text ɗin da ta tura masa ɗin. Koda ta buɗe saƙon wani irin zafi taji zuciyarta nayi,sakamakon baƙaƙen maganganun da ya gasa mata na cewa tafi ruwa gudu.Sannan ya sake jaddada mata cewa matuƙar tana son cigaba da zaman aurensa,to tabbas ta rabu da cikin jikinta don bai shirya haihuwa a yanzu ba. Jifa tayi da wayar lokacin da ta kammala karanta ɗatatan kalamansa, masu nuni da cewa ko kaɗan bata gabansa,bai kuma damu da maganar tafiyar da zata yi ɗinba kamar yadda Momyn nasa ta buƙata.Ta jima a kwance tana kuka har sai da wata uwar yunwar ta sakaɗota, sannan ta tashi tana sake janyo waya ta kira Diana.Tana ɗaga kiran ta furta, "Ki dafo min noodles, amma ya yi yaji sosai,ya kuma ya yi ruwa-ruwa." Ta kashe wayar tana ji duk ta ƙosa ta ga noodles ɗin a gabanta, ya kuma yi irin yadda take so ɗin. Koda Diana ta kawo mata shi har ɗakin baccinta, jikinta har rawa yake ta amsa plate ɗin tana sauke idanunta akan dahuwar noodle ɗin da ya yi mugun kyau, sai tashin ƙamshin pepe da mixed spices yake yi.Ta tsaida Diana tana sanar da ita zancen tafiyarta arewa a yau ɗin, tana mai bata umurnin haɗa kayanta don dole ita ma ta bar gidan a yau tunda anan cikin Port Harcourt ɗin take aka samo mata ita.Ko kaɗan Diana bata so wannan tafiya ta gaggawa da ta tasowa Madam Hannah ɗin kamar yadda suke kiranta da sunan ba, don tana jin daɗin aiki a ƙarƙashinta sabida bata da faɗa da hayaniya.Sannan tana kyautata musu sosai ita da duka ma'aikatan gidan, shiyasa suma suke bata girma da ƙaunarta sosai. Tana gama cin noodles ɗin wani bacci mai daɗi ya fara fisgarta, sai tayi kwanciyarta bisa sofa ɗin ba tare da ta hau bed ba.Bata tashi farkawa ba sai wajen 1:30pm, hakan yasa a gaggauce ta nufi toilet ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallah.Tana idarwa wanka ta sake yowa ta shirya cikin wani simple gown na swiss lace mai shegiyar tsada, ko kaɗan kayan basu da nauyi gashi ɗinkin ya amshi jikinta sosai.Kana kallonta za ka gano irin fresh ɗin da tayi gunin sha'awa, ga wani irin glowing da fatarta ke yi na samun hutu da kuma yanayin weather ɗin kudu mai kyau da ya taɓa fatar.Babu komi akan face ɗinta sai asalin natural face ɗinta, idanunta kaɗai ta iya sanyawa kwalli sabida kukan da ta sha idanun sun koɗe matuƙa.Sassanyar ƙamshin turarenta na LADY MILLION by PACO RABANNE ke tashi, duk ya buɗe ko'ina na ɗakin da sassanyar ƙamshi.Ta kammala shirin komi tare da aje bag da gyalenta bisa sofa,ta shiga neman layin driver ɗin da ya aje don fita da ita idan zata saloon ko mall.Sai da ta kira kusan sau uku sannan Bola ya ɗauka, wanda yake bayareban lagos ne zama ya kawo shi port harcourt ɗin. Allah ya haɗa shi da Adnan Dukku har ya ɗaikesa aikin driving ɗin da a sati bai fi su fita sau 2 ko 3 ba.Sabida Hannah bata san kan garin ba, kamar yadda bata saba da kowa ba har yau da take da watanni biyu da wasu kwankin a garin.Sanar dashi tayi ya taho zasu wuce airport, tafiya ta kamata zuwa gida arewa kamar yadda suke faɗi idan sun ji mutum zai irin garuruwan su Kaduna da sauran garuruwan da ke arewacin nigeria. Ƙarfe 2:30pm suka isa airport ɗin, ta gama duk abinda zata yi kafin ta jira lokacin da aka fara kiran passingers.Bola bai baro airport ɗin ba sai da ya tabbatar da tashin jirginsu,sannan ya juya don komawa gida ya aje motar. Tuni Diana dama ta riga Hannah barin gidan, bayan ta sallameta da kuɗi enough!Ta kuma bata tabbacin ba za ta jima ba zata dawo..........✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/12, 9:39 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!🤲🏻* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 16* _Free page_ *Kaduna.* Najma da Momy ne a kitchen suna hiransu tana taya Momyn aikin yankan su carrot da zata saka a filling ɗin samosa.Momyn ta kan amsa call akai-akai tana cigaba da yin sheet ɗin samosanta,gefe guda kuma zuciyarta sam babu daɗi da abinda surukarta ta sanar da ita tun safiyar yau ɗin.Ƙarfin hali kawai take yi tana dannewa, don bata so a fahimci halin da zuciyarta ke ciki akan irin baƙin cikin da Adnan ke cusa mata, tun kafin auren har aka yisa.Najma ta aje bowl ɗin da ta gama goge carrot ɗin a ciki tana duban Momy ta ce, "Momy na gama, sai kuma me zan kama miki?" Momy ta dubi Najma tare da kallon yadda ta yi komi tsaf cikin nutsuwa, ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Najma kin iya aiki a nutse gunin sha'awwa,da Nasreen ce da yanzu kinga ko'ina ya ɓaci.Babu abinda zaki yi yanzu sai ki nutsu ki ga yadda ake haɗa feeling ɗin da naɗesa a sheet ɗin." Najma ta jinjina kai cike da murnar yabon da ta samu daga Momy ta ce, "To Momy, bari in nutsu ɗin kuwa don ina so inga na iya irin waɗannan abubuwan zamanin." Daga haka ta dinga bin yadda Momy ke komi cike da ƙwarewa har suka kammala.Najma ɗin ta koyawa yadda ake naɗe samosan,cikin sa a kuma ta iya yinsa tsaf! Ita Momy ta barwa suyan ta fice daga kitchen ɗin lokacin da agogo ke buga 2:30pm na rana.Najma na aikin suyan tana yaba kirkin Momy da yadda take janta a jiki, tana nuna mata ƙaunar da bata yi zato ba.Tun shigowarta da safe bayan tafiyar Nasreen school, Momyn ta hanata komawa ɓangaren Gwaggo,suka yini suna hira da yin ƴan wasu aikace-aikacen a kitchen.Don yau ɗin ta kula sosai Momy ke jin motsa jiki da yin ayyukan kitchen kala da kala, hakan kuma sai ya yiwa Najma daɗi don ita indai a fannin son koyan girki ne bata da damuwa. Nabeela ita ma tun rana ta fita zuwa saloon da wankin ƙafa ,daga can kuma ta ji tana sanarwa Momyn zata biya gidan wata friend ɗinta. Tana kammala suyan samosan ta kashe gas ɗin tare da kintsa komi a mazaunin da ya dace,ta bar samosan a colander ya ɗige kafin a kwashe shi a mazubin da ya dace.Ta baro kitchen ɗin tana jin wani irin nishaɗi a zuciyarta,domin gani take yi ko yanzu aka kwaɓa mata dough ɗin samosan zata iya yinsa ya fita tsaf! In Sha Allah! A nan falo ta zauna don tun 1 suka yi sallah suka yi lunch tare da Momy a dining.Don haka bata jin yunwa ko gajiya tunda tayi sabo da aikin wahala a ƙauye,shiyasa take ganin ba komi tayi yau ɗin ba.Musamman da ya kasance a cikin lafiyayyen kitchen ɗin ƴan gayunnan suka yi aikin, suna yi sanyi AC na ratsa ko'ina a jikinsu. Wayar ta janyo daga lungun kujera inda ta aje sa, ta kunna data tana hawa online.Ganin Nasreen a online ya sanya tayi mata magana tana tambayarta ta kusa dawowa ko da sauran time? Nasreen tayo mata reply ta voice note tana sanar da ita sai 4 zata dawo kamar yadda ta faɗi da safe.Suka ɗan taɓa hiransu kafin Najma ta kashe datan tana kiran layin Inna Karima don tayi magana da mutanenta su Hanne.Bugu uku Hanne da wayar ke hannunta ta ɗaga, jin muryar Najma ce ya sanyata sakin ihun murna kafin su fara gaisawa Najma na tambayar ina Lubcy? Hanne ta bata amsa da cewa an aiketa ne,sai suka dasa hira tamkar ba credit ake janyewa ba.Sun jima sosai suna magana har Lubah ta dawo aiken da aka mata ta amsa wayar ita ma suka dasa hira.Daga ƙarshe Najma ta gaisa da Inna Karima sukai sallama da juna akan cewa nan da kwana biyu zasu iso giwa ɗin kamar yadda Daddy ya faɗi. Tana aje wayar fuskarta cike da murmushi,Momy ta fito daga ɗaki ta sauya shiga cikin wata boubou mai kyau na atamfar batik.Ta yafa babban gyale mai tsananin kyau da ya haska da kayan jikinta,fuskarta ɗauke da murmushi take duban Najma ta ce, "Naj! Tashi muje ɓangaren su Gwaggo ki ɗauki mayafi zaki rakani unguwa mu dawo, tunda gidan mu kaɗai ne karki zauna babu abokin hira gara mu riƙa zaga gari kina ganin ko'ina ko?" Najma ta gyaɗa kai ƙaunar Momy na sake zama a zuciyarta,ta miƙe tsaye tana faɗin, "To Momy, aiko dai zan zauna shiru babu Nabeelah babu Nasreen ta ce sai 4 zata dawo." Momy tayi murmushi tana duban Najma da kulawa ta ce, "Kema tare da Nabeela zaku shiga jami'a In Sha Allah! Don ita ma kin ga jamb kawai take jira a fara sayarwa ta zana, kinga sai a siya muku tare tunda kin ce takaddunki na waec da neco sunyi kyau ko?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Hakane Momy sun yi kyau." Suka fito zuwa sashin Gwaggon kaduna suna hiransu cike da nishaɗi. Bayan Momy sun sake gaisawa da su Inna Mairo ne ta sanar da Gwaggo cewa Najma zata rakata unguwa su dawo.Gwaggo da Inna Mairo suka yi musu a dawo lafiya, Najma ta isa ɗaki ta sanyo veil mara girma sosai don bata da hijab sai na sallarta kawai.Lokacin da aka je yi musu siyayya taso ta ce tana son a ɗinka mata su, don su ta saba sawa a giwa bata iya sanya gyaleba,amma kunya ya hanata faɗin tana so ɗin. Tayi kyau sosai da cream and silver colour ɗin veil da ta yano kanta dashi.Momy tayi mata duba ɗaya tana yaba tsantsar kyawun Najma da kyawun surarta, domin a yanzu kaɗai da suka samu kwanaki huɗu a garin har wani kyau ta ƙaro sabida hutu da kwana a cikin AC. Ga kuma lafiyayyan cima da suke ci suna wanka da sabulai masu tsada da kyawu,hakan ya sanya fatarta fara gogewa asalin black beauty colour ɗinta na wani irin haskawa. Sannu a hankali suka isa zuwa parking space na gidan,inda motoci uku suka rage a fake.Mommy ta aiki driver ɗinta can wani waje da motarta, hakan yasa dole a ɗaya daga cikin motocin Daddy biyu da suka rage zasu fita.Front seat ta buɗewa Najma ta shige, tana jinta a can sama cikin irin dalla-dallan manyan motocin da bata taɓa hasashen hawansu nan kurkusa ba.Motar ta birgeta matuƙa sai faman yaba kyawun ciki da wajen motar take yi a zuciyarta, amma a zahiri a kame take bata nuna ƙauyancinta afili sam! Momy dake mazaunin driver ta tashi motar suka dumfari bakin gate. Mai gadi ya buɗe musu gate yana yiwa Momy a dawo lafiya, suka fice tana ɗaga masa hannu fuskarta a sake kamar yadda ta saba. Sai da suka ɗauki hanya sosai Momy ta dubi Najma tana tana sanar da ita cewa airport suka nufa,domin ɗakko matar babban ɗanta da suke Port Harcourt.Ta cigaba da cewa, "Na aiki Lukman gashi kuma ta kira suna dab da sauka, dole yasa na fito don na ɗakkota da kaina Najma.Ban gayawa Gwaggo bane don zata yi surutu, ni kuna bana son ɓata lokaci don babu daɗi mutum ya sauka flight yana faman jiran azo a ɗauke sa.Don haka ko mun koma gida bana so ki sanar da ita ni ce na ɗakko Hannatun koda ta ganta,tunda muna isa direct wajena zamu wuce kinji ko?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Bakomi Momy ba zan faɗi ba, ai ba a haka, daga ɗaukata rakiya kuma sai naje ina faɗin abinda ba a tambayeni ba.Ko tambayata aka yi ma cewa zan yi bansani ba gaskiya." Momy tayi dariyar yadda Najma tayi maganar bilhakki cikin sassanyar muryarta mai daɗin amo,ta tsaida dariyar tana faɗin, "Das my gal! Allah ya yi muku albarka Najma." Najma ta amsa da cewa, "Ameen." Daga haka Momy ta cigaba da shara gudu a lafa-lafan titunan kaduna, waɗanda suka samu gyara na musamman daga ƙwararran gwamnar jihar mai shegiyar fasaha da fikrah. Sun isa airport ɗin dake mando daidai da saukar jirgin da ya ɗakko su Hannah daga jihar rivers.Lokacin da ta fito ta tadda Momy ce da kanta ta zo ɗaukarta sai jikinta ya sake yin sanyi, ƙaunar Momy da soyayyar da take wa aurensu da AD na sake kama zuciyarta.Cikin nutsuwa da sanyin jiki take ƙarisowa jaye da luggage da hand bag ɗinta, sai da ta kusa ƙarisowa Najma ta fice da sauri tana amsar luggage ɗin ta cigaba da jansa har wajen motar.Momy ta fito tana wa Hannah bar da isowa lafiya, tana mai duban tsakiyar idanun Hannah da ruwan hawaye ke taruwa a cikinsu.Murya cike da kulawa ta dubeta tana faɗin, "Hannah shige muje, bana son sanya damuwa a rai please! Kin dai san wace ce Gwaggo a wajen Adnan,don haka bana so ta gane rauninki a wannan karon don Allah!" Momy ta yiwa Hannah maganar cike da roƙo, don sam bata so Gwaggo ta samu kafar dagula lamuran, duk da cewa ta san komin ɗaurewa ƙarya gindi akan lamuran AD ɗin da ta saba,a wannan karon ba za ta yi hakan ba don ita ma ba za ta so a cire cikin shalelenta ba.Hannah ta gyaɗawa Momy kai, kafin tayi magana cikin sanyin murya ta ce, "In Sha Allah Momy!" Daga haka Najma ta gama sanya luggage ɗin a bayan boot,ta isa ga back seat ta shige don baƙuwar Momy a gaba ta kame.Momy ta ja motar suna cigaba da magana da Hannah, ita dai Najma na jinsu amma bata gane inda maganganunsu suka dosa ba.Koda ta gaida Hannah waiwayowa tayi ta amsata cike da fara'a, tana mai maida dubanta kan Momy ta ce,"Ina kuma kika samo wannan black beauty ɗin?" Momy ta saki murmushi tana bai wa Hannah amsa da faɗin, "Hannatu kenan, ƴar ƙanwar Daddy ne fa.A garin giwa suke da zama but yanzu sun dawo wajen mu zamu rayu tare In Sha Allah, so she's ur husband cousine Sis, ina fata zaki ɗauke ta tamkar su Nasreen?" Hannah da sam bata da wani damuwa, gyaɗa kai tayi tana faɗin, "In Sha Allah Momy! Amma gaskiy she's very black beauty and suna matuƙar kama da Anty Jiddah kuma." .Momy ta saki murmushi tana faɗin, "Tafi Jiddah kyau ai Hannatu, ita wannan photocopy ɗin Innarta ce sak! Sai dai ita Innar fara ce ita kuma sai ta fito a black beauty." Najma dai blushing take tayi tana sauraran yadda su Momy ke ta faman yaba kyawunta da black skin ɗinta. Sun iso gida daidai da shigowar motar Nasreen ta dawo daga skull, suka faka motocin kusan a tare suna mai ɓalle murafen motocin suka fito.Nasreen ita ce ta fara isowa wajen motar da Momy ta faka don ta hango fuskar wata kamar Anty Hannah ɗinsu.Tana ko isowa ta ga ita ɗince ta saki ƙaramin ihun murna tana rungumeta ta ce, "Welcome Anty Hannah! Ke kaɗai kika taho ina Yaya AD?" Hannah ta sake rungume Nasreen cike da fara'a da danne dukkanin ƙuncin zuciya ta bata amsa da faɗin, "Ni kaɗaice Nasreeny, AD zai zo may be a weekend." Najma Nasreen ta duba dake tsaye tana dubansu da murmushi akan fuskarta, sai ta saki Hannah tana faɗin, "Alright! Allah ya kaimu weekend ɗin lafiya, gwarama da ba tare kuke ɗinba ai." Hannah ta saki murmushi tana mamakin yadda su Nasreen ɗin ke tsoransa da rashin damuwa da lamarinsa, sabida ya iya musu faɗansa da baya ƙarewa.Sosai suke shakkarsa basa sakewa idan yana waje sam,don abu kaɗan zai rufesu da masifa ko ya mammakesu. Nasreen tana duban Najma ta ce, "Najma kice ke ce ƴar rakiyar Momy yanzu, so ya garin kinyi missing ɗina yauma ko kuwa waya ki kai tasha da mutanen giwar taku?" Najma ta saki murmushi tana ɗan narke face ta ce, "Nayi amma kaɗan, waya kam mun sha shi in gaya miki.Suna gaida ku da kyau ke da Nabeelah da duk nake ta basu labarin kirkinku." Nasreen ta sanya dariya suna yin gaba don tuni Hannah da Momy sun yi gaba zuwa ciki. A ɗaya bedroom ɗin Momy Hannah ta yada zango tana jinta a gajiye kamar wacce ta baro wata ƙasa zuwa KD ɗin.Wanka tayo da ruwa mai ɗumi, ta fito ɗaure da towel ta nufi bakin bed ta zauna tare da janyo luggage ɗinta.Doguwar rigar shan iska mara nauyi ta zaro ta saka, tana fesa turarenta mai daɗin ƙamshi da sanyi.Hijab ta nema ta saka ta tada sallah, tana idarwa ta fara jin dukkanin jikinta na ɗaukar rawar jin yunwa tamkar wata mai ulcer.Hakan ya sanya ta miƙewa da sauri ta nufi falo don neman abinci, tun kafin a kai ga gabatar mata dashi.Babu kowa a falon don Momy ta shiga yin sallar la'asar da ya riskesu a hanya,ita ma Najma sun ƙule a ɗakin Nasreen.Don haka kai tsaye ɓangaren dining da ba baƙonta bane ta nufa, don kuwa tun bata auri AD ba suna zuwa gidan su yini. Lafiyayyiyar fried rice da salad ta zuba ta fara ci, tana ci tana korawa da orange juice mai matsakaicin sanyi.Sai da yunwar cikinta ta fara gushewa,kafin ta ɗebo cinyoyin pepechicken ta ɗaura akan soyayyiyar shinkafar da ta ji veggies da hanta tana cigaba da zirawa cikinta. Momy ce ta fito daga ɗaki ta hangota kame a dining ɗin tayi nisa cikin cin abincinta, ta ƙarisa wajen dining ɗin fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin, "Sorry Hannatu! Ba a fara gabatar miki da abinci ba first, na ɗauka sai kin huta zaki buƙaci abincin sorry!" Hannah duk sai kunyar duniya ya rufeta, ta rasa bakin magana sai sunkuyar da kanta da tayi kawai.Momy dake dubanta tana gano dukkanin alamun mace mai juna biyu a tattare da ita, sai ta sake sakin murmushi tana faɗin, "Shi babyn mai ci ne kenan,tunda ya urunta min daughter!" Wani bahagon kunya ya sake rufarwa Hannah, ta sake ƙasa da kanta tana blushing cike da jin nauyin Momy.Momy ta baro wajen don bata damar kammala cin abincinta a nutse, zuciyarta na cigaba da kisima rashin mutuncin da Adnan zai zo ya tadda a gareta.Don tasha alwashin saɓa masa fiye da duk yadda zai yi zato, sabida ta ga rashin arziƙin nasa gaba yake yi maimakon ya yi baya. Koda Hannah ta kammala cin abincin sai kunya ya hanata tasowa daga dining zuwa cikin falo.Momy ce ta gane kunya ce ta hanata tasowa, sai ta ɗaga murya ta kirawo sunanta, "Hannatu!" Hannah ta amsa tana mai tasowa a kunyace ta iso cikin falon.Nesa da kujeran da Momy ke zaune ta zauna, tana sake sunkuyar da ƙanta ƙasa sabida tana jin idanun Momyn na yawo a kanta. Kamar saukar aradu ta ji Momy ta jefo mata tambaya tana cewa, "Hala sai da kika gaya masa na ce ki taho ɗin kamar yadda ya furta idan kin zaɓi cikin ki baro masa gidansa ko?" Hannah ta daburce da rasa abin faɗi, sai ta gyaɗa kanta kawai zuciyarta na karyewa da rauni mai yawa. Momy ta jinjina kai tana sake jefa mata wata tambayar ta ce, "Mai ya faɗi da ki ka ce ni ce na ce ki taho?" Hannah ta ɗago kai ta dubi Momy tana kallon yadda ta haɗe fuska alamun bata son wasa.Sai ta samu kanta da son miƙawa Momy wayar don ta karanta reply ɗin da ya yo mata, sabida ba za ta iya maida mata da baƙaƙen magangun da ya faɗi mata ba.Text ɗin ta buɗo iya inda ya aiko reply ɗin, ta miƙawa Momy wayar tana faɗin, "Gashi ki karanta Momy." Babu musu Hajiya Zainab ta karɓi wayar tana karanta abinda AD Dukku ya aiko.Ta jinjina kai bayan gama karanta saƙon,ta maida dubanta kan Hannah tare da miƙa mata wayarta ta ce, "Muje ɗakina muyi magana Hannatu!" Hannah ta miƙe ta rufawa Momy baya zuwa bedroom ɗinta, don bata buƙatar su Nasreen su fito suji me suke tattaunawa da Hannah ɗin. Bayan Momy ta zauna a bakin bed, sai Hannah ta zaɓi zama bisa sofa tana ji dukkanin jikinta na yin sanyi matuƙa. Momy ta dubeta cike da jin tausayin yadda take ɗawainiya da soyayyar gudan jininta, amma shi sam ba ita bane a gabansa wulaƙanci kawai yake mata son ransa.Tayi gyaran murya tana farawa da faɗin, "Hannatu shi namiji baka yadda ka nuna masa muguwar soyayyar da zai gane baka da wani abin so sai shi, ƙoƙari kake yi ka dinga dannewa soyayyarsa a gaban idanunsa tare da saita kanka ta yadda ba zai fahimci kayi nisa a ƙaunarsa ba,bare har ya gano lagonka da zai dinga ƙuntata zuciyarka da wannan soyayyar da kake yi masa ba.Adnan ɗana ne da ya fito daga jikina tabbas! Sai dai ki sani makauniyar soyayyar da ki ke nuna masa na rashin iya riƙe kai da ajinki sam baya birgeni, domin halin maza duka ɗaya ne indai akan mace ne. Dole ki koyi danne dukkanin soyayyar da kike masa, ki daina nuna masa sai dashi zaki rayu ko in bashi ba zaki iya rayuwa ba.Hakan da kike nuna masa ya sanya har ya fara baki zaɓin ko zama dashi ko kuma kiyi abinda shi yake so, ba tare da la'akari da girman zunubin da zaku aikata inda kin biye masan ba.Ki manta dashi ko sau ɗaya karki yadda ki kira wayarsa ko turo masa saƙo, ko shi ne ya kira ban amince ki ɗaga wayarsa ba.Ki bai wa banza a jiyarsa daga nan har ranar da zai kawo kansa garin da ƙafafunsa, idan Gwaggo ta tambayeki mai kika zo yi ki sanar mata cewa shi ne kawai ya ce kizo zai biyo bayanki daga baya.Ban yarda ki sanar mata komi ba sai idan shi ne ya sanar mata, nima kuma idan ta tambaya abinda zan sanar mata kenan.Ban amince ki sanarwa Hajiyarku ko Laurah ba, don wannan abin kunya ne da dariya a gareki ace miji ya baki zaɓin ko rabuwa da ciki ko zaman aurensa.Alhali watanni biyu kacal akai da auren bama shekaru biyu ba, don haka ban amince susan wannan maganar ba har zuwa sanda xaki koma ɗakinki ko kiyi zamanki a part ɗinku shi ya dinga zuwa miki weekend ko duk bayan sati biyu ne.Amma ciki da aurensa duka kin zaɓa zai kuma zo ya sameni,shi ma kuma Daddy yana jirace dashi ɗin don na sanar dashi komi jibi zai dawo daga Abujan." Momy ta dakata da maganar zuciyarta na matuƙar sosuwa da rashin kirkin AD, da yadda yake wulaƙanta Ƴar ƙawarta ta arziƙi Hajiya Halima.Wacce ke matsayin matar aminin mijinta da suke zuba abin arziƙi sosai da ita,amma ace ɗan cikinta da ta haifa ne ke wulaƙanta mata Ƴa ai hakan babban abin damuwa da tir ne a gareta.Ko kaɗan Adnan baya mata adalci akan wulaƙanta Hannah da yake don kawai an jarabci zuciyarta da soyayyarsa,ba don ta rasa tarin masoya ba sai don kawai shi ɗin ne ta mato a kansa har ta zaɓi aurensa ido rufe, ba tare da ta duba girman kuskuren auren wanda bashi ya ce yana ƙaunarka ba. Hannah ta jinjina kai hawaye na bin fuskarta, tana jin dukkanin jikinta na sake mutuwa da ƙaunar AD Dukku da bata taɓa ganin aibunsa ba.Duk yadda yake wulaƙantata ta kasa rage soyayyarsa a zuciyarta, sai ma gani take tamkar kullum kwanan duniya ninka mata a ƙaunarsa ake yi.Amma tabbas kamar yadda Momy ta buƙata haka za ta yi, dole ne ta koyi riƙe kanta da danne ƙarfin soyayyarsa a zuciyarta matuƙar tana son ta tsira da sauran mutunci a idanunsa,ta yadda zai fara shakkar yi mata wasu kalolin wulaƙancin nasa.Cikin rawar murya take wa Momy godia tare da tabbatar mata da cewa zata yi duk yadda ta buƙata ɗin. Daga haka Momy ta ce mata ta kwanta ta huta abin ta, za ta sanya yanzu a kawo mata snacks ko zata iya ci.Ta fito ta bar Hannah tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali, idanunta kuma na hasko mata kyakykyawar fuskar AD Dukku da yadda ya haɗe fuskar a ɗazu da safe yana mata masifarsa da ke kiɗima zuciyarta.Ta lumshe idanunta tana kai hannu ta shafo cikinta, wani irin sanyin ƙaunar cikin da uban cikin na sake keta zuciyarta da shigewa jinin jikinta baki ɗaya. Rabi Momy ta aiko da ƙaramin tray mai ɗauke da plate ɗin da aka zubo samosar ɗazu da suka yi tare da Najma,sai dambun naman kaza da aka yi ya ji spices.Gefe guda an ɗauro table water da sassanyar lemun abarba na gwangwani.Hannah ta gaida Rabi da girmamawa, kafin ta juyo ta fito daga ɗakin baki ɗaya.Hannah na yiwa dambun naman kallo ɗaya taji miyanta ya tsinke, ta kai hannu ta damƙoshi tana kaiwa baki ta fara ci.Daɗinsa da ƙamshin spices ya dinga ratsata,tana sake kai hannu ta damƙo ta kai baki. A haka Nasreen ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana sauke idanunta akan Hannah ta ce, "Anty Hannah hutawa ake a ɗakin Momy haka?" Hannah ta gyaɗa kai tana sakin murmushi ta ce, "Na gaji ne Sis,ga kaina da ke ciwo shiyasa Momy ta ce nayi kwanciyata na huta a nan ɗin." Nasreen tayi mata sannu tana zama kusa da ita ta ce, "But nayi mamaki zuwa ba sanarwa sai dai mu ganki daga sama, hala an tura Yayan aiki wani garin ne ya ce kiyi tahowarki?" Hannah ta sake sakin murmushi cikin son danne damuwarta ta ce, "Eh Nasreen,ina black beauty Sis ɗin naku ta shige?" Nasreen ta saki wide smile tana faɗin, "Najam wai? Ta gudu ɓangaren Gwaggo wajen Innarta." Hannah ta ɗan yi murmushi ta ce, " Nima zuwa anjima zan shiga wajen mutuniyar ai." Nasreen ta sake dariya tana faɗin, "Su Gwaggo manyan ƙasa, sweet heart ɗin na Yaya AD ba.Ayi tsiya ai daɗi, amma duk rashin kirkin da zai mata bata gani,kana magana abu ya juyo kanka." Suka saki dariya sosai, suna tuno kalar dramar da ake sha tsakanin Gwaggo da AD Dukku, wanda sam baya laifi a wajenta. Sai bayan sallar magriba Nasreen ta raka Hannah zuwa ɓangaren Gwaggo don ta kwashi gaisuwa.Sun samu Gwaggo na ɗaki bata fito ba, da alamu sai ta yi sallar isha'i zata fito su taru suyi dinner dasu Inna kamar yadda suka sabayi yanzu da suka dawo nan ɗin......✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/12, 10:48 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 17* _Free page_ Su Inna Mairo ne suka fara fitowa falon bayan sun idar da sallar isha'i kamar yadda suka saba.Sun tadda Hannah da Nasreen zaune a falon suna hiransu kafin Gwaggon ta fito.Nasreen ta gabatarwa da Inna Mairo Hannah,tana sanar da ita cewa matar babban Yayansu Adnan ne.Suka gaisa da fara'a tana tambayar Hannah ina shi Adnan ɗin? Ta sanar da Inna Mairo cewa yana can Port Harcourt ɗin bai zo ba.Hannah ta dinga satan duban Inna Mairo da Najma, tana kallon tsabagen kamanninsu da juna.Sai dai kawai bambamcin kalar skin da ke garesu, kuma ita sai Najma da take baƙa kyawunta yafi birgeta fiye da Inna Mairo da ke jinta jajir da ita.Gwaggo ta fito ta samesu suna ta zantawa da juna, ta ƙariso mazauninta da ta saba zama cikin 2 seater ta zauna.Da zallar mamakin ganin Hannah take amsa gaisuwarta tare da tambayarta ita dawa ta zo garin? Hannah ta yi ƙasa da kai tana bai wa Gwaggo amsa da cewa, "Ni kaɗai na taho Gwaggo, shi zai zo daga baya ina ga zuwa jibi weekend!" Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Kuma shi ne ɗazu da mukai waya bai sanar min zaki zo ɗinba? Ya sako ki a jirgi ke kaɗai kika taho ko tsoro baki ji ba?" Hannah da Nasreen suka saki murmushi,Hannah na duban Gwaggo da girmamawa ta ce, "Gwaggo ai babu wani tsoro,tunda ba daga wata ƙasa na zo ba ni kaɗai ɗin,koma wata ƙasar ce ai babu wata damuwa." Gwaggo ta jinjina kai tare da taɓe baki ta ce, "Eh! Lallai zamani ba ƙarya bane ai, ku Yaran yanzu baku san tsoro ba sabida buɗewar ido da ya yi muku yawa." Ta ƙare maganar tana bin Hannah da wani kallo na ƙurilla don son gano ko abinda take hasashe da gaske ne a jikin Hannar? Don tun kallon farko da ta yiwa fuskarta fa tara zargin da wuya ba ciki ne da ita ba.Kamar Hannah ta gano manufar Gwaggo sai ta juyar da fuskarta baki ɗaya tana facing su Nasreen da ke ta faman hira da Najma.Har aka shirya abincin dinner a tsakiyar falon suna nan zaune, Gwaggo tayi musu tayin in zasu ci a haɗu duka aci tare da juna.Nasreen da bata faye cin abincin dare ba sai wajen 10pm tayi saurin girgiza kai tana faɗin, "Sai dai ko Anty Hannah Gwaggo." Hannah ta ita ma ta girgiza kai tana faɗin, "No! Na ƙoshi wallahi, ni da abinci sai can anjima kuma." Daga haka Najma da Inna Mairo tare da Gwaggo suka haɗu suna cin abincin hankali kwance.Nasreen da Hannah sai suka yi musu sai da safe suka fice, bayan Nasreen ta jaddadawa Najma cewa tana jiranta a ɓangarensu idan ta gama. Kai kawai Najma ta gyaɗa mata amma ba don zata je ɗin ba,don bata son ta zama mai yawan shigewa musamman da yau ɗin Anty Hannah ta zo.Wacce tun daga kallon da Momy ke mata da irin yadda Nasreen ta nuna ɗoki da murnar ganinta, ta gano irin soyayyar da suke mata.Shiyasa take ganin gara ta ɗan ja jikinta yau ɗin, don basu damar sakewa da surukar tasu,kar taje tana takurasu da ganinta a kusa da su. Gwaggo bayan sun kammala da cin abincin sai ta koma daga gefe guda ta dannawa shalelenta AD Dukku kira.Bugu biyo ya ɗaga wayar cikin sassanyar muryarsa da yake haɗawa da ƴar shagwaɓar gata idan yana waya da ita.Bayan ta gama amsa gaisuwar da ya yi mata,sai kai tsaye ta jefa masa tambayar dake mintsininta, "Adnanu ya aka yi ka baro matarka ita kaɗai ta taho maimakon ku taho tare? Kasan fa nayi kewarka wata guda kenan baka zo dubamu ba,ince dai ko lafiya ta taho ita kaɗai ɗin." AD Dukku daga ɓangarensa ya lumshe idanunsa,yana sake gyara kwanciyarsa akan sofa dake ɗakinsa. Domin tunda aka tashi office ya dawo gidan.Ya buɗe baki cikin ƙasa da muryarsa ya sanar da Gwaggo cewa Momy ce ta bai wa Hannah umurnin tahowa, sabida sun samu ƴar hatsaniya tsakaninsa da Hannar. Gwaggo ta buɗe baki cikin matuƙar mamaki ta ce, "To hatsaniyar uban me kuma kuka yi? Nifa ka fara bani haushi da wannan ƙiyayya da kake nunawa salihar baiwar Allah.Miye aibun Hannatu ne wai da ba za ka rungumi matarka ku zauna lafiya ba?" Gwaggo tayi maganar da ɗaga sautin muryarta, hakan ya sanya su Gwaggo da ke daga can cikin falon suna jiyo duk abinda take faɗi ɗin.Ta ɗanyi jim! Da alamu tana sauraran abinda yake faɗi mata ne,zuwa can kuma ta sake ɗaga sautin muryarta tana faɗin, "To ai shikenan, ni yanzu zan je wajen Zainabun inji dalilin da zaisa ta ce wa matarka ta zo ba tare da izininka ba.In banda ma shiga uku ina ruwanta da faɗarku da har zata saka ƴar mutane kamo hanya tazo gari ita kaɗai kamar wata wulaƙantatta." Ta dakata da maganar tana sauraren yadda AD Dukku ke narke mata murya yana nuna cewa bashi da wani laifi, Hannah ɗince ta kira Momy ta sanar da ita ƙarya da gaskiya don Momy ta ji zafinsa.Gwaggo ta dinga jinjina kai kamar yana gabanta,kafin ta sake faɗin, "Karka damu zan je yanzu na ce na sameta, kai dai kawai kaxo zuwa ranar sati ɗin ina son ganinka Adnanuna.Amma kuma zamu giwa ranar asabar ɗin, Gwaggonka Mairo da na sha baka labarin tana can,to ta dawo nan kaduna da zama zamu rakata kwaso kaya suyi sallama da mutanan arziƙinta kuma.Amma hakan ba matsala bace, ka dai zo ɗin kaji ko?" Ta sake yin shiru tana saurarensa daga ɓangarensa,kafin ta sake furta, "To shikenan sai ka iso ɗin, ina fata dai yanzu duk kana rage shashancin shaye-shayen nan na zamani daka koyo a turai,don sam bana so Adnanu.Don Allah ka nutsu ka zama mutumin kirki,karka ga ina kareka idan Iyayenka na kyararka nima kaina abin yana damuna a zuci." Ta kai ƙarshen maganar tana sake manne wayar a kunni,tana cigaba da sauraran tsarin da yake mata.Ta sauke wayar a kunni bayan ya kashe,tana mai miƙewa tsaye ta kallo side ɗin dasu Inna Mairo suke.Sun maida dukkanin hankulansu akan kallon TV, Najma kuma ta kan duba wayarta jefi-jefi.Gwaggo ta ɗaga murya ta kira sunan Najma tare da bata umurnin zuwa ɗakinta ta ɗakko mata mayafi.Najma ta miƙe ta wuce don zuwa ɗakkowa Gwaggon mayafin nata, ita kuma Gwaggo ta maida hankali wajen Inna Mairo tana faɗin."Mairo ɓangaren Zainab zani yanzu in jiyo dalilin da zai sanya ta saka ƴar mutane kamo hanya tazo gari bada izinin mijinta ba, ina na taɓa ganin anyi hakan ni Hauwa! In banda dai zamani da ya lalace ma, ina ruwanta da surukar ɗan fari har da zata dinga zaƙewa a lamuransu? To bari in je mata don ba zan bari ma sai gobe ba." Inna Mairo tayi murmushi tana duban Gwaggo ta ce, "Allah sarki Gwaggo, watakila tana ganin hakan da tayi shi ne daidai ɗin.Amma dai gara kije ki ji ɗin zai fi." Gwaggo ta ɗan kyaɓe baki ta ce, "To ai hakan ma shine gaskiya da gaskiya Mairo, in je mata ɗin tun yanzu inji dalili da abinda ya faru ɗin." Najma da ta iso da mayafi a hannu,sai ta miƙawa Gwaggo tana faɗin, "Gashi Gwaggo." Gwaggo ta amsa mayafin tana faɗin, "Wuce mu je ki rakani ɓangaren Kabeeru Najma." Najma ta amsa da, "To." Tana bin bayan Gwaggo da bata bari ko mayafi ta saka akan rigar jikinta mara nauyi da ta saka ba. Suka isa ɓangaren su Momy tana cike da mamakin yadda Gwaggo ke ta faman mita ita kaɗai,don tunda suka fito take mita da magana ba tare da Najma ta ce komi ba. A nan main parlor ɗin suka tadda su Nasreen dukkansu har da Nabeela da ba a jima da maido ta gidan ba.Momy ta tarbi Gwaggo da kulawa tana faɗin, "Barka da shigowa Gwaggo, ga wuri nan zauna nan." Ta nunawa Gwaggo kujeran 2 seater ta zauna.Ta dubi Momy ɗin tana ɗan gimtse fuska ta ce, "Zainabu wajenki na zo, maza kai ni ɗaki muyi magana in kama kaina ba zama cikin Yara na xo yi ba." Momy ta dubi Gwaggo tana ji a jikinta cewa duk yadda aka yi Adnan ya kirata ya haɗosu kenan da Gwaggon.Ta miƙe tana duban Gwaggo ta ce, "To muje ɗakina Gwaggo." Daga haka suka yi gaba zuwa bedroom ɗin Momy ɗin, suka bar su Nasreen da bin bayansu da kallo, zuciyar Hannah na cigaba da doka mata. Gwaggo ta dubi Momy bayan shigarsu ɗakin ta ce, "Zainabu miye naki na cewa Hannatu ta kamo hanya ta taho,don kawai sun sami saɓani da mijinta?" Momy ta danne ɓacin ran Adnan da ya taso mata,ta dubi Gwaggo kai tsaye ta ce, "Au! Bai faɗi miki ɓarnar da yake shirin saka Ƴar mutane su aikata ba Gwaggo?" Gwaggo ta haɗe fuska tamau ta ce, "Ina tambayarki maimakon amsa sai kuma ki jefoni da wata tambayar Zainab? To bai faɗi mini komi ba, shiyasa ai na zo inji daga bakinki." Momy ta sauke numfashi mai ɗumi, cikin kwantar da murya ta ce, "Gwaggo so yake ta zubda cikin da ta samu, sabida wai shi bai shiryama haihuwa yanzu ba.Ni kuma tunda ta sanar mini, shi ne nace ta dawo gabanmu don kada ya tirsasata su aikata ɓarna, tunda ya fahimci ta mato a kansa zata iya aikata komi don ta faranta masa.Don Allah Gwaggo ki nuna masa ɓacin ranki a wannan karon,don na san kema ba za ki so a aikata wannan ɗanyan ɓarnar ba." Gwaggo da tunda Momy ta fara magana ta shiga shock! Sai ta riƙe haɓa tana magana a firgice ta ce, "Shi Adinanun ne ya faɗi hakan Zainabu, da bakinsa ya furta cewa bai shirya haihuwa yanzu ba don ubanshi? To wallahi ya yi kaɗan, idan ƙwayoyin da yake sha ne suke gaya masa gaibu,to ya sani sai Hannatu ta haife wannan rabon da Allan ya nufeni da rahamar zan ga jininsa a duniya." Gwaggo ta ɗan numfasa kafin ta cigaba da faɗin, "Au shine har da narke mini kamar wani mai gaskiya, lallai ko zai san cewa bana bayansa a wannan karon.Yanzu dai jeki kirawo min Hannatun ta zo inji zance dalla-dalla daga bakinta." Momy ta saki murmushi a sace tana miƙewa ta fice don kiran Hannah.Gwaggo kuwa sai faman mita take yi tana tsinewa shaye-shayen ƙwayoyin da aka ce Adnan ɗin nayi. Lokacin da Hannah ta shigo gefen da Momy ke zaune daga bed ta zauna tana yin ƙasa da kanta.Gwaggo ta zuba mata ido tana sake gano alamun mai ciki an tare da ita ɗin.Ta wanj yi ƙasa da murya tana duban Hannah kai tsaye ta ce, "Ke Hannatu da gaske ne Adnanu ne ya ce baya son cikin da kike ɗauke dashi?" Hannah ta gyaɗa kai cike da tsananin jin kunya.Gwaggo ta cigaba da faɗin, "To kuwa wallahi bai isa ba, ai duk laifinki ne da kike nuna masa shegiyar soyayyar da baki ganin duk wani aibunsa da tsiyar da yake shuka miki.Inba ya rainaki ya gano kin gama matowa a kansa ba, har ya iya kallon tsabar idonki ya ce baya son cikin alhali shi ya ɗirka miki,ko kuwa a ruwa kika sha cikin?" Hannah dai kunya kamar ta nitse, haka ta sake dankwafar da kai ƙasa tana sauraran masifar da Gwaggo ke mata.Daga ita har Momy suka yi har tayi mai isarta,ta miƙe tana duban Momy ta ce, "Ki sanar da Kabeeru da gaggawa, Yarinya ta dawo kenan har sai ta haife mana ɗan ko Ƴar sannan sai su ƙarata ta sake binsa can kudun.Amma yanzu tunda ya nuna baƙin cikinsa da hassadarsa akan samuwan cikin, ana bashi ita suka koma zai san yadda ya yi salwanyar da cikin tunda ita shashashace, ta riga ta nuna masa ta gama matowa a kansa gaba ɗaya.Ita ko irin ƴar jan ajinnan ta mata bata iya ba, kyawunsa gaba ɗaya na kula gigita yake,ta yadda idan waje duk take rasa nutsuwarta.Wallahi Hanantu ki yi hankali da zaƙewa a nuna wa namiji muguwar soyayya, inba haka ba kece a wahale a kuma gantale don duk iskancin da ɗebo a kanki zai riƙa saukewa." Gwaggo ta ƙare maganar tana yin gaba don fita daga ɗakin.Momy da Hannah sukai mata sai da safe, ta juyo tana makawa Momy harara ta ce, "Amma Zainab so kika yi ki rufeni,da tun farko baki je kin sanar min wannan iyashegenba.Yanzu gobe sai a buɗe mata ɓangarensu a gyare shi, tunda dama komi na nan kamar yau akai jeren wajen,tayi zamanta ta raini cikinta cikin salama.Ko Iyayenta ban yadda su ji wannan abin kunyar ba, sabida sai ai mata dariya gaskiya." Momy ta jinjina kai ta ce, "Dama nima shawarar dana yanke kenan Gwaggo, shi ma kuma Daddy haka ya ce tayi zamanta kawai." Gwaggo ta fice tana cewa, "To ai shikenan tunda basirarmu duk yazo ɗaya a nan,shi kuma Adinanun zai zo ya sameni har ɗakina." Ta ƙarisa ficewa tana barin su Momy da sakin dariya,don sun yi mamakin yadda Gwaggon ta rufe ido tana masifan jin zafin zancen zubda cikin. Falo Hannah ta koma ta samu Gwaggo ta tasa Najma sun koma ɓangarenta, don ta sanarwa Nasreen cewa gobe lafiyayyan ƙosan da Najma ta iya zata yi musu da safe.Don haka ba za ta kwana anan tana baccin asara da safe ba, har ta gagara komawa tayi musu ƙosan akan lokaci.Hannah ta zauna tana dariyar yadda Nasreen ke bata labarin abinda Gwaggon ta faɗi,ta cigaba da blushing tana cewa, "Nima har naji ina son naci ƙosan Sis,goben na je na samo wajen Gwaggon na ci." Nasreen ta taɓe baki cike da jin haushin hana Najma kwana da Gwaggo tayi ta ce, "Aiko dai zaki ci daɗi, don gaskiya ta iya suyan ƙosai sabida sana'arsu ce a can giwa ta ce." Hannah ta murmusa daidai wayarta na ɗaukar tsuwwa na shigowan kira ta ce, "Aiko da wuri zan aika a amso min ɗin." Daga haka ta ɗaga kiran ganin sunan Anty Laurah ce mai kiran.Sun ɗan jima suna magana, amma sam Hannah bata sanar mata cewa tana KD ba.Ta aje wayar tana kallo agogo zuciyarta na cike da tunanin kome yake can yana yi a yanzu? Ta ɗan lumshe ido tana jin wani zafi da kishi na sukan zuciyarta,don ta san yau ɗin watakila kwana ma zai yi a club tare da ƴan matansa tunda bata gidan baki ɗaya bare ya dawo mata cikin tsakiyar dare ya lalubeta kamar yadda ya saba.Ƙirjinta ta ji yana mata nauyi,sai tayi saurin tashi tana duban Nasreen da Nabeelah da hankalinsu ya koma kan wayoyinsu ta furta, "Gud night Sisis, zan kwanta bacci yazo." Nasreen sukai mata sai da safe ta nufi hanyar bedroom ɗin da Momy ta ce ta zauna a ciki.Su kuma suka cigaba da chart suna kuma kallo rabi da rabi.Kira da ya shigo wayar Nasreen na wani saurayinta Saheeb ya sanyata tashi ta wuce ɗaki, ta bar Nabeey a zaune tana kallo tana cigaba da chart. ********* *Port Harcourt.* Ƙarfe uku daidai na dare motar Adnan Dukku ya shigo gidansa.Ya ɓalle murfin motar ya fito bayan ya adanata a parking space, ya nufi cikin gidan yana jin kansa na sara masa sakamakon ƙwayar da ya sha da bai taɓa shan irin ta ba sai a yau ɗin da abokinsa US (Usman Sani) ya zo musu da ita.Shi ma kuma daga ingila ya taho da ƙwayar,wacce ba mai sanya buguwa bace sai dai ta sanyawa mutum ƙarfi da jin kansa a sama tamkar yafi kowa.Ƙarfin da take dashi ke sanya duk wanda ya fara shanta sai ya haɗu da ciwan kai mai tsanani kafin ta bi jikinsa ta fara aikin da ya dace.Ya kai kansa zuwa upstairs yana nufan room ɗinsa kai tsaye,domin burinsa bai wuce ya sakarwa kansa ruwa mai ɗumi ba.Kayan jikinsa da ke fidda mayataccen ƙamshin Leenah ya fidda,ya yi jifa dasu a tsakar ɗakin yana nufan hanyar bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi.Sai da sanyin ruwan ya gama ratsa kwanyarsa lafin ya sakarwa jikinsa ruwa mai ɗumi,yana jin wani irin yanayi na bin jikinsa.Koda ya fito kayan baccinsa ya sanya, ya nufi wajen ƙaramin fridge ɗinsa ya ciro table water, sai da ya sha rabin gorar ya dire yana nufan bed kai tsaye don kwanciya. Ya lumshe idanunsa lokacin da kansa ke warwarewa daga caji da ta ɗauka, feeling ɗin da yake ji na tsananin son kusantar mace na sake ratsashi.Ya sake lumshe idanunsa yana ayyanawa a zuciyarsa da Hannah na nan da yanzu tana cikin jikinsa, don amfaninta kenan a garesa da zaran ya shigo a irin wannan yanayin da yake ciki.Tashi ya yi ya nufi side drawer ɗinsa yana ciro kwalin wani magani da ya jima bai yi amfani dashi ba, tun bayan fara sanin Hannah da ya yi a mace.Ya ɓalli biyu ya jefa a baki yana takowa inda ya aje ragowar table water ɗin ya ɗauka ya kora ruwan maganin suka wuce,ya aje goran yana sauke numfashi tamkar wanda yaci babu.Da ƙyar ya iya rintsawa a ƙarishen daren,yana mai yankewa kansa cewa dole zuwa jibi friday ya wuce KD don tinkaran koma miye akan cikin jikinta. ********** *Kaduna.* Washegary da wuri Najma ta wuce zuwa kitchen ɗin Gwaggo,suka haɗu da Tabawa don haɗa abincin breakfast.Lafiyayyan ƙosai da kunun tsamiya suka dama, sai aka soya egg da irish tare da dafa ruwan shayin da yaji kayan ƙamshi a dahuwar.Sosai ƙosan da Najma ta soya ɗin ya yi kyau da taushi, gashi ganin akwai wadatan kayan gayu na girki sai ta yi karanbanin yanka green pepe da wadatacciyar albasa a cikin ƙullun,ta saka curry kafin a soya.Sai ƙosan ya bada kala da flavour mai daɗi don green pepe akwai shi da daɗi a cikin wasu soya-soyen ga duk wacce ta ganewa sirrin.Ƙarfe tara suka kammala da komi Tabawa na faman yaba ƙoƙarin Najma da son aikinta,don tana da zafin nama da himma matuƙa da gaske. Najma ɗakinsu ta wuce don yin wanka ta shirya kafin Gwaggo ta fito, su haɗu suyi breakfast ɗin tare.Ta samu Inna Mairo a zaune tana sauraran karatu a cikin wayarta, ta gaidata tana mai wucewa bathroom ta yo wanka ta fito.A tsanake ta shirya cikin wata free gown na atamfa, wanda ɗinkin ya yi mata kyau a jiki sosai tare da fidda kyawunta.Bata shafawa fuskarta komi ba sai man leɓe data gogawa lips ɗinta,fuskarta sai ya yi fayau da asalin natural black beauty face ɗinta.Sassanyar ƙamshin turaren MISS DIOR da Nasreen ta bata ke tashi a jikinta,kamar yadda dukkanin ɗakin ma ya buɗe da ƙamshin mai sanyi.Inna Mairo ta ɗaga ido ta dubi Najma tana faɗin, "Najma kinga yadda ki ke ta sauyawa kuwa? Anya zuwa nan gaba ba zaki dinga yawo da dogon hijab har da niƙab ba? Ina tsoron kyawun mace ya cika bayyana Najma, domin ya kan zamewa wasu ƴan matan mummunan bazarana ga rayuwarsu.Nasihata a gareki kullum shi ne ki zama mai matuƙar kamun kai da takatsantsan wajen kare mutuncinki ta ɗiya mace,sannan ki nisanci sanya tufafin da zasu dinga bayyana surarki domin hakan ba wayewa bace.Ko kaɗan kada ki bari ruɗin duniya da zaman bariki su sanya ki watsar da tarbiyar da muka ginaki akai, domin daga ni har Malam burin mu ki zama nutsatstsiya mai tayamu kare mutuncinki da namu.A kowani mataki na rayuwa ki riƙa tuna cewa mutuncinki dana addininki shi ne abinda zaki fara karewa sama da komi a duniya.Sannan ki ji tsoran Allah wajen kiyaye kanki daga mazan da ba muharramanki ba, karki ruɗu da kalar rayuwar wasu ki ce kema zaki koyi dasu a abinda zai taɓa mutunci ko tarbiyarki mai nagarta.Don Allah Najma karki sauya akan kyawawan ɗabi'u da halayen da aka sanki dasu, sannan karki dinga manta asali da tushenki duk yadda rayuwa zata zo miki da sauyi.Ki dinga tuna cewa ke ɗin ba kowa bace ba kuma ƴar wani bace, face ƴar ƙauyen garin giwa." Inna Mairo ta ɗan dakata da maganar tana duban yadda Najma ta nutsu tana saurarenta.Ta ɗaura da cigaba da faɗin, "Ba ina miki wannan nasihar da wata manuface Najma, sai don ina tsoron sharrin zuciya da ruɗin duniya.waɗanda suke saurin sauya tunanin ɗan adam farat ɗaya! Dole sai ana yi ana taro ku tare da yi muku nasiha,don duniyar dukkaninta babu tabbas a cikinta.Ki riƙe gaskiya da amana, duk rintse karki yarda mutanen da suka aminta dake, suke nuna miki ƙauna tsakani da Allah su sameki da rashin gaskiya ko cin amana.Ki taimakeni ki tayani kyautata musu da yi musu biyayya, sannan ki guji shiga cikin lamarin da ba a sanya ki ciki ba.Ki nisanci ƙarya da ha'inci,duk da cewa ba halayyarki bace,amma ina so kiyi matuƙar takatsantsan Najma domin zama a ƙarƙashin wasu abu ne mai matuƙar wahala.Ki ninka haƙurinki domin dole za a saɓa miki kamar yadda kema zaki saɓa musu cikin rashin sani koda gangan,ina fata zaki kiyaye ki kuma nisanci son abin hannunsu.Dukkanin abinda aka ɗakko aka baki kiyi godia, wanda ba a baki ba ko ya shiga ranki ki kauda da kai karki yadda ki taɓa abinda ba a baki ba.Na sani baki da kwaɗayi, amma ina miki matashiya da ki ninka akan kyawawan ɗabi'unki da na sanki dashi, hakan zaisa na cigaba da alfahari da ke Najma kin ji ko?" Najma da dukkanin jikinta ya yi sanyi da nasihun Inna Mairo, sai ta gyaɗa kai murya a sanyaye ta ce, "Naji Inna, kuma In Sha Allah zan kiyaye dukkanin nasihunki.Allah ya barmu tare har mutuwa mu je mu tadda Malam a aljanna cikin aminci." Inna Mairo ta yi murmushi wani abu na motsa zuciyarta.Cikin sanyin murya ta furta,"Ameen Najma! Allah ya cigaba da haskaka makwancinsu,tashi muje kada Gwaggo tayi ta jiran mu." Suka fito daga ɗakin jere da juna,zukatansu na tuno musu da rayuwarsu a garin giwa tare da mutanen arziƙinsu Iyalan gidan Hakimi. Sun tadda Gwaggo har ta fito tana zaune wajen da suka saba cin abinci ta fara serving kanta.Suka zauna suna gaida Gwaggo a tare,ta ɗaga ido tayi musu duba ɗaya tana yaba kyawun da dukkaninsu suka yi cikin suturu masu kyau da ke jikinsu.Idanunta akan Najma ta furta, "Jikata ya gajiyan suya?" Najma ta saki wide smile tana faɗin, "Babu gajiya Gwaggo, Allah dai ya sanya ya yi miki daɗi,don nayi miki karambanin ƙara wani abin a ciki." Gwaggo ta kai hannu tana buɗe kulolin har ta buɗo wanda ƙosan ke ciki, wani ƙamshi ya cika wajen mai daɗi.Ta ɗakko ɗaya ta kai baki tana faɗin, "To bari na ji wani karanbani ne kuma aka yi a cikin ƙosan." Ta tauna tattausan ƙosan da ke tashin ƙamshin green pepe da albasa tare da ƴar curry kaɗan da aka buga ƙullun dashi,wani irin daɗi ya ratsa harshenta zuwa kwanyarta.Ta lumshe ido tana buɗesu akan Najma ta ce, "Wayyo daɗi! Inji Yaro, gaskiya Najma kin iya ƙosai tamkar wata tsohuwar mace da hannunta ya nuna a iya tuya.Gaskiya dole Kabeeru ya yaba miki, aini ban taɓa sanin kin iya har hakan ba da kusan kullum dashi zan dinga karin safe,don ni Kabeeru ya gado a son karin safe da ƙosai ko waina da kunu." Daga Inna Mairo har Najma suka saki ƙaramin dariya, Najma na duban yadda Gwaggo ta sake jefa ƙosan a baki har da wani kanne ido.Ta sake sakin smile tana faɗin, "Allah sarki Gwaggo! Ai nima bansan kina so ba kuwa, da yake sana'arsa muke yi a ƙauye muke samun na rufin asiri lokacin." Gwaggo ta jinjina kai tana jin ciwon su dinga tuno rayuwar wahalar da sukai a baya,cikin kulawa da son kawar da maganar ta ce, "Gaskiya ni dai ke ce zaki dinga mana ƙosai ko idan watan azumi ya kamane, wannan irin ƙosai mai shegiyar daɗi haka." Najma suka sake sanya dariya,kafin tayi serving ɗinsu ita da Inna Mairo suka fara nasu karin. Suna dab da kammalawa Nasreen da Hannah suka shigo cikin falon Gwaggon.Hannah ke gaba Nasreen na bayanta cikin shirin fita skull,suka zauna suna gaida su Gwaggo cike da ladabi.Najma ta gaida Hannah ta amsa da fara'a tana faɗin, "U look so fresh and beautiful Najma! Gaskiya na jima banga black beauty da skin mai kyau irin naki ba." Najma ta saki murmushi tana duban Nasreen da ta tsareta da ido ta ce, "Sis wannan kallon kuma fa?" Nasreen ta saki smile tana cewa, "Kyau kika min ba kaɗan ba Najma, anya nan gaba ba goslow zaki dinga haɗa mana a layi ba?" Najma ta jefa mata harara tana faɗin, "Kai Nasreen, wallahi kin cika neman magana." Hannah ta taya su yin dariyar idanunta na sauka akan ƙosan da Gwaggo ke ci baji ba gani.Gwaggo ta ɗago suka haɗa ido da Hannah, sai tayi saurin faɗin, "Hannatu ko zaki ci ƙosai a zubo miki, ko kema ƴar gayunce irin mijinki da sai abincin turawa yake karyawa dashi?" Hannah tayi ƙasa da kai tana faɗin, "Gwaggo ni kam babu ruwana ina ci sosai ma, musamman wannan ɗin da nake ganin kyawunsa tun a ido." Gwaggo ta zuba mata plate ta miƙa mata tana faɗin, "Maza sakko kici tunda zafinsa, ga kunu nan ki zuba shi ma idan kina so." Hannah da dama ƙosan ta biyo, don tunda akai zancensa jiya ta ji shi kaɗai take son ci.Shiyasa Nasreen na shiryawa ta ce zata yo nan ɗin ita ma tace da Momy zata zo ta gaida su Gwaggon,suka fito suka yo nan ba tare da ta tsaya yin breakfast a can ba.Sosai ta ci ƙosan tana yaba daɗinsa da ƙwarewar Najma a iya sarrafashi, Gwaggo ta cigaba da kwarzanta daɗinsa suna kwasan dariya.Nasreen ce ta yiwa Najma magana cewar zata wuce skull, idan ta dawo kuma zata rakata wata unguwa.Ta raka Nasreen ɗin har wajen motarta ta wuce skull, ita kuma ta juyo zuwa side Gwaggon.Tana shigowa Hannah na fitowa zata koma side ɗin Momy, ta yiwa Najma kallo ɗaya da murmushi akan fuskarta ta ce, "Najma naci ƙosai mai daɗi da yawa, gaskiya kin sama ladana thank u beauty!" Najma ta sakar mata smile tana faɗin, "Laah! Bakomi Anty, na gode nima da yabawa." Daga haka Hannah ta wuce ita kuma Najma ta shige daga ciki.Sai wajen sha ɗaya suka fito daga side ɗin Gwaggo zuwa na Momy don gaidata.Sun sameta tare da Nabeelah da Hannah zaune suna hiransu, suka gaisa a mutunce idanun Momy akan Najma ta furta, "Idon ki kenan daughter? Na fito jiya kawai sai na tadda Gwaggo ta tasa ƙeyarki kun koma can ɗin,ai gobe dai Daddy idan ya dawo zai yi mata magana da kansa cewa nan zaki dawo da zama dai." Najma da haka kawai bata son hakan a ranta sai ta saki murmushin yaƙe ba tare da ta yi magana ba, sai Inna Mairo ce ta ce, "Ai dama kun barta kawai a can ɗin, indai Najma ce ba za ta iya zaman waje ɗaya alhali tasan ina cikin gidan." Momy tayi dariya tana faɗin, "Aiko hakanan zata dawo nan ɗin, gara ta zauna cikin ƴan uwanta su riƙa yin komi tare hakan zai sake haifar da shaƙuwa a tsakaninsu......✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/20, 5:14 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!*🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 18* _Free page_ Hira sosai suka sha a tsakanin junansu kafin Momy ta wuce kitchen,don fara shirya abinda zata tarbi Daddy dashi.Wanda a yau ɗin friday zai dawo weekend daga Abuja. Najma Momy ta kira bayan Inna Mairo ta koma ɓangaren Gwaggo domin taya Tabawa ɗaura girki.A hankali Najma ke taya Momy ayyukan da ta bata,don ta fahimci tana da son koyan girkin da gaske.Bayan sun kammala Najman ce dai Momy ta saka ta dinga kwasan warmers ɗin zuwa ɓangaren Daddy tana shiryawa akan dining.Cikin tsari da nutsuwarta na halitta take gudanar da komi nata,abinda ke sake birge Momy kenan don tana son mace ta kasance nutsatstsiya ba mai rawar kai ba. Hannah ɗaki ta shige tana chart da kuma karance-karancen novel da ta fara koya, don zaman kaɗaicin da take yi a port harcourt ɗin idan AD ya fita oficce, ya sanya ta fara koyan karatun novels da ake turawa a wani group da Anty Laurah ta sanya ta a ciki.Wani book ɗin Mamuhgee take karantawa mai suna IDON NERA,sosai ɗin book yake tafiya da zuciyarta take kuma jin daɗin karatun.Ta lunshe idanunta tana tunanin AD Dukku da son zuwansa a gobe ko yau ɗin, don da gaske kewar ganinsa take yi tsakanin jiya da yau da bata sanya shi a idanunta ko jin motsi ko muryarsa da ke kasheta ba. Momy ce ta kira wayarta time ɗin da ta idar da sallar zuhur da ta tashi ta gabatar da ƙyar, sabida kasalar da take ji.Ta ɗaga wayar tana sauraren Momy da ke bata umurnin fitowa tayi lunch tare dasu a dining.Ta aje wayar tana miƙewa ta canza rigar jikinta daga dogon shimi zuwa doguwar riga mai ƙaramin hannu.Rigar na wani haɗaɗɗan Indian material ne da yaji ɗinkin embroidery, wanda aka yisa tun daga wuyar rigar zuwa ƙasansa.Sosai tayi kyau da fresh irin na masu ciki, waɗanda hutu ya ratsa fatarsu babu wahala sam a tare dasu. Tare da Najma da Momy suka haɗu sukai lunch ɗin,bayan sun kammala Momy ta sanya Najma raka Hannah zuwa part ɗinsu da su Rabi suka kammala goge ko'ina.Sosai Najma ta yaba da tsaruwar part ɗin,wanda yafi na Gwaggon kaduna girma.Sannan tsarin ginin ma yafi haɗuwa, ga kuma rantsatstsun kayan ɗaki dana kitchen da aka yiwa Hannah irin na ƴaƴan gata,waɗanda iyayensu suka tada kai da naira.Don mahaifinta Alhaji Surajo ba ƙaramin mai kuɗi bane,don ma ya ɗan samu karayan arziƙin da har Daddy ya keresa,amma a baya ko Daddy ba zai nuna masa arziƙi ba.Ƴan asalin jihar kano ne su,aiki ne ya maida Alhaji Suraj ɗin Abuja da iyalinsa baki ɗaya.Sai dai yana da gida a kaduna da suke yawan hutu nan,daga nan su wuce kano a wasu lokutan.A hakane kuma ta hanyar yawan zuwa Kd da suke yi,suna ziyartan gidan Daddy da kuma yadda Adnan ɗin ke yawan ziyartan Alhaji Suraj ɗin idan ya shiga Abuja, Hannah ta ƙyalla ido ta gansa ta kuma maƙale masa.Babu kalar samarin da bata yi ba tsakanin Abuja da mahaifarta kano,amma ta watsar da kowa ta kama ɗan mutan Dukku.Wanda shi kuma zuciyarsa bata taɓa ƙaunarta ba, kawai auren nasu yazo a NUFIN ALLAH ne kawai.Wanda idan ya yi NUFIN abu ya kasance sai ya kasance ɗin,koda ace babu yarda da amincewar kowa ne. Duk yadda Hannah ta so Najma ta jira yi dawowar Nasreen daga skull anan side ɗinta ƙi tayi, ta matsa zata wajen Innarta ne ta dawo ne.Hakanan Hannah ta ƙyaleta ta wuce,tana jinjina rashin saurin sakin jikin Najma da mutane sosai.Gashi kuma ita Allah ya ɗaura mata son Najma a ranta tun ganin farko, sabida yadda kyawunta da sanyinta ya tafi da zuciyarta.Sannan yawan murmushin da baya rabo da fuskar Najmar abin na sake birgeta, yana kuma ƙarawa Najmar kwarjini da kyawu matuƙa. Najma na baro side ɗin Hannah ta wuce ɓangaren Gwaggo.A nan falo ta samesu suna hira,Gwaggo kuma na daga kishingiɗe tana amsa waya.Ta nema waje ta zauna tana sauraran yadda Gwaggo ke amsa wayar cike da ɗaga murya,wanda hakan ya zame mata jiki sam bata iya magana a hankali a waya ba.Bayan ta kammala wayar ne Najma tayi mata sannu da hutawa,ta amsa da fara'a tana faɗin, "Najmatu gobe fa sai garin giwa,tafiya babu fashi In Sha Allah! Don haka Nasreen na dawowa zaku je ku yo siyayyar tsaraban da za a wuce musu dashi.Duk dai na kammala tanadan abinda ya dace,amma su ƴan matan ƙawayen naki kece zaki san abinda zai fi birgesu." Najma godiya ta dinga wa Gwaggo bayan ta dasa aya a maganarta.Gwaggo ta nuna babu komi yiwa kaine, daga nan kuma sai ta sanya Najma zuwa kitchen ɗinta ta ɗakko mata kwanon nono da fura a fridge ɗinta. Nasreen sai ƙarfe biyu da rabi ta shigo gidan a gajiye, direct ɗakinta ta wuce tayo wanka ta saka riga mara nauyi.Dining ta fito ta nemi abinci don da yunwa ta shigo gidan,sabida bata ci komi a skull ɗin ba yau ɗin. Momy ce ta sanar da ita cewa Hannah na part ɗinta,hakan ya sanya Nasreen na kammala cin abincin suka nufi wajen Anty Hannah ita da Nabeela da tun rana ke ɗaki tana karatun books na skull don ita mayyar karatu ce. Daga can wajen Anty Hannah side ɗin Gwaggo Nasreen ta wuce wajen Najma.Ta samu Gwaggo da Inna Mairo tare da Tabawa a falo suna zantawa,ta tambayi Najma Inna Mairo ta ce tana ɗaki ta ɗan kwanta ta ce kanta na ciwo.Cikin hanzari Nasreen ta nufi ɗakin su Gwaggo bakinta ɗauke da sallama,ta hangi Najma kwance bisa bed da waya a hannunta. "Beauty baby ya aka yi ne da kwanciya da ranarnan haka?" Nasreen ta furta hakan tana zama daga bakin bed ɗin.Najma da ƙamshin turaren Nasreen ɗin ya bugi hancinta kafin isar muryarta cikin kunnuwarta, sai tayi saurin tashi zaune da murmushi akan face ɗinta ta ce, "Sis kin dawo? Wallahi kaina ke ciwo amma na sha magani ya faɗa mini,yanzu karatu nake yi a waya." Nasreen ta jinjina kai tana duban fresh black beauty face ɗin Najma da ke glowing ta ce, "Ayyah! Sannu Sis, wato kin fara koyan karatun novel ko? Ni kinga ban iya ba,karatun skull kaɗai ya isheni." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Wallahi Sis na fara koya, kuma ina ƙaruwa sosai,kawai luv ɗin cikin books ɗin ne yake bani kunya da mamakin anya ko ni zan iya wata soyayya kuwa?" Najma tayi tambayar bilhakki idanunta akan Nasreen ɗin.Nasreen ta tuntsire da dariya tana faɗin, "I don't know now,but idan lokaci ya yi zaki iya fiye ma da wanda kike karantawa." Najma ta ɗan ɓata face cike da shagwaɓe murya ta ce, "Ni dai gaskiya bana ji zan iya kam, yanzu dai bani labarin me kika taho min dashi?" Nasreen ta saki smile ta ce, "Nothing beauty! Amma zamu fita yanzu ai sai mu biya musha COLD STONE muci pizza." Najma da sam bata damu da irin abubuwannan ba,sai ta ɗan yamutse face tana faɗin, "Ni dai ban iya shan kayan sanyinnan ba, shi ma pizza ɗin baki ga ban iya cinsa sosai ba." Nasreen ta miƙe tsaye tana duba time a gogon dake ɗakin ta ce, "Oya shirya Najma, lokaci na tafiya gara mu fita yanzu koma dawo kafin Daddy ya ƙariso." Najma ta sakko daga bed ɗin ta nufi closet ɗinsu ta ɗakko rigar da zata saka su fita ɗin.Nasreen na tsaye tana dubanta ta saka doguwar rigar boubou na wata pink ɗin atamfa,rigar ya yi mata kyau kalar kuma ya haska black skin ɗinta mai sheƙi da fresh.Ga kuma sassanyar ƙamshin turaren Miss Dior da ta fesa kaɗan na tashi a jikinta.Ɗankwalin kayan ta ɗaura tana ɗakko wani ƙaramin hijab irin na makkah da Momy ta bata ta saka.Hijab ɗin tsayinsa duka iya cinyarta ya tsaya,amma ya rufe dukkanin hannayenta bai dai ƙarisa sauka zuwa cinyarta bane.Kalarsa milk ne da ya shiga da kayan jikinta,wanda akai wa touch da milk colour a jiki,sai ta fito tayi wani irin mugun kyau. Jere da juna suka fito zuwa falon Gwaggo, Nasreen nata yaba kyawun da Najma tayi.Daga Gwaggo har Inna Mairo idanunsu akan Najma suke,Gwaggo ta kasa shiru sai da ta furta, "Najma wannan kyawu da kike ta sake zabgawa haka." Najma ta saki murmushi ta ce, "Gwaggo a hakan?" Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Ƙwarai kuwa! Don baki ga yadda kyawunki ke sake fitowa bane shiyasa.Nasreen maza ɗakko min ƙaramar jaka akan gadona na sallameku." Nasreen ta wuce ta ɗakkowa Gwaggo jakan ta kawo mata.Ta amsa tana zuge zip ɗin ta ciro kuɗaɗe ta irga wanda zata basu tana miƙawa Najma tana faɗin, "Ungo Najma, ku siyowa ƙawayenki tsarabar da xaki kai musu gobe kin ji ko?" Najma ta amsa kuɗin tana godia Inna Mairo na taya ta ita ma.Sukai musu sai sun dawo suka fice don zuwa yiwa Momy sai sun dawo ɗin.Ita ma kuɗi ta ƙara musu ta ce Najma ta siya abinda take so,sannan ta sake ba Nasreen wasu kuɗin ta ce ta siya mata wasu abubuwan da zata wuce wa ƴan giwa dashi ita ma. A gaban motar Nasreen Najma ta kame,hannunta riƙe da wayarta da ke sake shiga zuciyarta.Suna tafiya suna hiransu cike da nishaɗi, Nasreen na faman tsokanar Najma da cewa akwai wani guy da za ta haɗata dashi.Najma ta bankawa Nasreen harara tana faɗin, "Don Allah Nasreeny ki rufamin asiri, nifa wallahi da gaske nake ba zan iya wata soyayya ba." Nasreen tayi dariya sosai kafin ta furta, "Ba za ki yi aure ba kenan?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Wannan kuma ai ana yinsa ko babu soyayyah, indai shi mijin zai soni ai shikenan ba dole sai nayi soyayya zan yi aure ba ai." Nasreen ta jinjina kai tana faɗin, "Gaskiya sai yau na yadda ke ɗin auta ce Najma." Najma cike da nuna halin ko inkula ta ce, "Hmmm! Ke wasa ki ke ganin komi Nasreen, ni kam da gaske nake furta dukkanin kalamaina." Nasreen tayi saurin faɗin, "Kar dai ki cika baki, don ita soyayya bata ƙwanƙwasa ƙofa, shiga kawai take yi duk zuciyar da ta so ba tare da bada notice ba.So kada Yarinya ta zo ta cika baki watarana in ji ana kuka ana faɗin Nasreen ya zanyi da soyayyar wane." Nasreen ta ƙare maganar ta bushewa da dariya, hakan ya sanya Najma sake narke fuska kamar zata saki kuka ta ce, "Allah dai ya yafe miki Nasreeny! Amma kin gama dani yau wallahi." Sosai suka ɗauki ɗauki lokaci a kasuwa suna siyayyar,Najma duk kuɗin da aka bata sai da ta ƙarar dashi wajen siyawa mutanenta su Lubah kayan gayu masu kyau. Kafin su wuto gida sai da suka tsaya suka sayi COLD STONE ice cream da Shawarma,suka sake tsayawa a wani waje suka sayi Chicken Kebab sannan suka wuto gida. Suna shigowa Nasreen ta hango motar AD Dukku da ake ɗakkosa daga airport idan ya zo gari a fake a parking space, ƙirjinta ya yi wani irin bugawa da jin haushin zuwansa garin.Ta isa ta raɓa motarta da nesa kaɗan da nasa suka fito daga cikin tasu motar.Najma na kwasan wasu kayan dake back seat take faɗin, "Ina muka nufa?" Nasreen da gaba ɗaya mood ɗinta ya canza da ganin motar Yaya AD ɗin, sai ta ƙaƙaro murmushi tana faɗin, "Mu nufi side ɗin Momy kawai Najma, idan mun yi magriba sai mu je wajen Gwaggo taga siyayyar ko?" Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa tana faɗin, "Okey to bari na kwashi waɗannan kayan." Najma ta ƙare maganar tana kwasan mafi yawan kayan da ke back seat ɗin ta nufi side ɗin Momy dasu.Nasreen ta rufe motar tana kwasan sauran kayan ta rufawa Najma baya, wacce har ta kusa isa ga ƙofar shigewa ciki.Kusan a tare suka isa bakin ƙofar shiga babban falon Momy, tun kuma kafin a amsa sallamarsu iska ya kwasowa Nasreen ƙamshin turarensa na CREED AVENTUS mai ƙarshen tsada ya buso hancinta.Muryar Momy da ta amsa sallamar da suka doka tare da basu izinin shiga, ya sanya suka kutsa kai cikin falon.Daddaɗan ƙamshinsa da ya haɗe dana ɗakin ya daki hancin Najma,hakan ya bata tabbacin akwai baƙo ko baƙuwar a cikin falon.Idanunta yakai kan wanda ke zaune ya baiwa ƙofar shigowa falon baya, kalar rigarsa da sassalkan baƙin gashin kansa irin na fulani kawai ake iya hangowa.Daga nesa dasu kaɗan Nasreen ta ce, "Mommy mun dawo bari mu wuce ɗaki." Momy ta jinjina kai tana musu sannu da zuwa, Nasreen kuma ta ɗanyi gaba kaɗan tana ɗaga murya yadda zai jiyota ta ce, "Yaya AD welcome!" Bai juyo ba sai hannu da ya ɗaga mata kawai.Hakan ya sanyata jan hannun Najma sukai ciki ba tare da Najmar ta ce komi ba ita.Momy tabi bayansu da kallo zuciyarta na sosuwa da yadda sam shi bai iya jan ƴan ƙanninsa a jiki yana nuna musu soyayya ba,tsakaninsa dasu gaisuwa ce sai idan ya ga dama ranar da ƴan kirkin ke kusa ya kwashesu zuwa shan ice cream ko cin abinci.Shi ma kuma zai yi wuya a dawo lafiya bai make wata ko ya yi musu faɗan da zasu shigo a tunzure ba,musamman Nabeelah da bakinta ba ya iya shiru.Shi kuma baya son yawan surutu da rawar kai.Anty Jiddah da ke bi masa,ita kaɗaice take ganin haƙoransa a waje har su zauna suyi hira suna kwasan dariya.Amma in ba ita ba ko Momy da wuya kaga ya zauna suna hira sosai cikin nishaɗi,sabida ita kullum cikin yi masa faɗa da nasiha take akan ya gyara halayensa ya kuma guje aikata saɓo a fili ne ko a ɓoye.Don dukkanin halayyarsa na shan ƙwayoyi da harka da matan banza ta sani, tana kuma yi masa addu'ar shiriya a koda yaushe. Ta dubesa fuska a haɗe bayan shigewar su Najma ta ce, "Adnan yanzu ko kallo Nasreen bata isheka ba bare ka buɗe baki ka amsa gaisuwarta, anya waɗannan halayen naka na banza zasu fissheka kuwa? Wasu ke dashi da ya kai ka, wanda zai jasu a jiki ya kula dasu ko bayan babu raina? Ina sha daga kai sai Jiddah garesu, kuma kai namiji kai ne jagora kuma uba a garesu.Idan baka basu fuska sunyi sabo da kai ta yadda zasu dinga iya tunkaranka da matsalolinsu ba wa kake so su tunkara? To wallahi ka shiga hankalinka tunda naga kai baka san kawaici da ya kamata ba.Saura kuma ka je ɓangaren Gwaggo ka kasa yiwa Inna Mairo gaisuwar mutunci kaga yadda zan saɓa maka." Ta ƙare maganar cikin nuna masa ɓacin ransa da take ji a zuciyarta.Ya ɗago manyan idanunsa da ke saye cikin baƙin eye glass ya dubi Momyn nasa mafi soyuwa a zuciyarsa,don yana mata wani irin soyayya da bai san iyakarsa ba.Sai dai duk da soyayyar da yake mata baya iya sakin jiki da ita yadda ya kamata,sabida bai shaƙu da ita kamar yadda ya shaƙu da Gwaggo da ta sangartashi ba.Ita Momy kullum cikin nuna masa kawaicin ɗan fari take yi, yanzu ne da take ganin tarbiyarsa ta ɓaci ita kuma Gwaggo ba wani cikakken kwaɓa masa take yi ba,sai hakan ya sanya ta fara sakin masa jiki tana nusar dashi hanyar da ya kamata ya bi wajen gyara ɗabi'unsa.Cikin sanyin muryarsa mai cike da aji da nutsuwa ya furta, "Ki yi haƙury Momy zan gyara,ni kinsan ban faye son raini bane shiyasa bana sake musu fuska,amma ai ina ƙaunarsu ina kuma ji dasu har cikin zuciyata." Momy ta taɓe baki ta ce, "In gani a zahiri ba a baki kaɗai ba,sannan ina fata ka ji maganata da kyau akan dawowar Hannatu nan da zama har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya ko?" Ya jinjija kai yana jin ciwo da takaicin samuwar cikin jikin Hannah na sake soya zuciyarsa, musamman da a yanzu ya tabbatar zancen fidda cikin ko maganar rashin ƙaunarsa da cikin sai dai ya zama tarihi.Don tunda magana ya zo kunnin su Momy,ya san sai Hannah ta haife cikin nan ko zai mutune da rashin ƙaunar hakan. Ya jinjina kai yana faɗin, "Naji Momy badamuwa!" Daga haka ya miƙe Momyn na binsa da kallo da yaba kyawunsa da cikar kamala da Ubangijin halitta ya yi masa.Don wani irin kyawu da fresh ya ƙaro na gaske, da alamu garin ya amshesa sosai.Ɗanyar gezner ce a jikinsa fara ƙal! Wanda akai wa ɗinki na musamman,ya yi kyau har ya gaji a cikin kayan.Fuskarsa dai kamar ko yaushe babu wani annuri,musamman a yanzu da ransa ya sake ɓaci da zancen cikin da kuma jin zafin Hannah da tun farko ta shigo da su Momy cikin maganar ba tare da ta biye masa an zubda cikin ba. Ya taka a hankali cikin tafiyarsa a nutse ya bar cikin falon bayan ya sanar da Momy cewa zai je ɓangaren Gwaggo. Yana tafe iskar alamun shigowar damina na ɗan kaɗa shi tare da baza ƙamshinsa a ko'ina,a haka ya isa ɓangaren Gwaggo bakinsa ɗauke da siririyar sallama.Gwaggo da suke zaune tare da Inna Mairo a falo suna zancen tafiyarsu garin giwa gobe, sai ta juyo muryar Adnan ɗin kamar daga sama.Tayi hanzarin amsa sallamar tana faɗin, "Shigo mana shalelen Gwaggo!" AD Dukku ya ɗage labulen tare da shigowa cikin falon baki ɗaya, yana mai sauke idanunsa akan Inna Mairo da ke facing ɗinsa.Ya cigaba da takowa zuwa cikin falon,ƙamshinsa na baje ko'ina tare da ratsa kafifon hancinansu Gwaggon.Inna Mairo ta ɗaga idanunta ta sauke akan kyakykyawar halittar da gaba ɗaya ya canza mata, don rabonta da ganinsa tun bai gama zama saurayi ba yana ɗan sakandiri.Ya sake yi mata kyawu a idanu tare da zama cikakken magidanci mai ji da aji da ƙuruciya,sannan a kallo ɗaya zaka fahimci ɗan gaye ne na gasken gasken,wanda hutu da kuɗi haɗi da jin daɗin rayuwa suka taɓashi matuƙa da gaske. Ta ɗauke kai daga dubansa lokacin da ya isa gaban Gwaggo ya zame ya zauna kusa da ita,yadda ya wani manne da jikin Gwaggon tamkar Yaron goye sai ya bai wa Inna Mairo mamaki.Gwaggo ta wani rungumo kansa ya haɗu da kafaɗunta tana faɗin, "Sannu da zuwa Adinanuna, barka da isowa shalelen Gwaggo.Ya hanya naga duk ranka a ɓace haka, ince dai lafiya lau ka iso ɗin ko?" AD Dukku ya sake narkewa a jikinta yana jinjina kai murya can ƙasa ya ce, "Lafiya lau Gwaggo, babu wata gajiyar hanya flight na biyo ai.Hope na sameku lafiya lau? Nima i really miss u sweetheart!" Gwaggo ta wani sake washe baki tana faɗin, "Ɗan nema kayi kewata shine baka fara isowa wajena ba, don tunda na ga ka shigo fuska a haɗe na gane wajen Zainab ka fara isa ta ɓato min ranka daga isowa ba za a bari ma ka huta ba." Adnan Dukku ya ɗan fidda ƙaramar murmushi yana ɗago idanunsa masu cike da kwarjinin da ke dukan zukatan ƴan mata ya ce,"Gwaggo ba wani faɗa tayi min bafa, ina fata kin aje min abu mai sanyi kamar fura ko zallar madarar shanu?" Tayi saurin gyaɗa kai tana faɗin, "Duka zaka samesu Adinanu,don jiya na saka aka kawo madara mai kyau don nasan kana tafe a satinnan.Ga Gwaggonka Mairo ku gaisa kafin a kawo maka furan yanzu." Sai time ɗin AD Dukku ya maida dubansa inda Inna Mairo ke zaune,duk mamakin yadda Gwaggo ke taɓara jikan nata da tun fil'azal kowa ya shaidi muguwar soyayyar da take masa.Ya yi ƙasa da murya tamkar wanda ake tilastawa yin magana,ya gaida Inna Mairon ba yabo ba fallasa.Ita ma ta amsa gaisuwar nata fuskar a sake tana sake yi masa barka da isowa, daga haka ta tashi ta bar musu falon zuwa ɗakinta.Yabi bayanta da kallo yana maida dubansa kan Gwaggo ya ce, "Gwaggo yanzu ita ce ƙanwar Daddy da ki ke bani labari? Tana matuƙar kama da Jiddah sosai." Gwaggo ta saki murmushi tana faɗin, "Jini kenan Adinanu, ai baka ga kama ba sai kaga yadda ƴarta Najma tayi kama da ita,kuma take kama da Jiddar sosai ita ma.Ina fata zaka girmamata ka kuma riƙe ƴar uwarka tamkar su Nasreen,domim nayi nadama iya nadama akan yadda na raba tsakaninta da mahaifanka a baya.Amma yanzu na gane kuskurena shiyasa na ce su dawo gareni domin in kyautata rayuwarsu ko Ubangiji zai yafe mini laifin dana aikata a baya.Sannan ina fata in tadda Kakanku Malam Muhammadu cikin salama a aljanna!" Gwaggo ta kai ƙarshen maganar cike da narke masa murya da nuna masa zallar nadamar da zuciyarta ke ciki.AD Dukku ya jinjina kai tare da ratsa hannuwansa a jikin Gwaggo ta yadda kansa ya samu kyakykyawan zama a kafaɗarta ya ce, "Sorry sweetheart! Komi ya wuce ai,zan yi ƙoƙarin hakan." Gwaggo ta saki ajiyan zuciya ta ce, "Yauwa Adinanuna,badon ba a shirya tafiyar da kai ba ai da mun je tare da ka gano garin giwa." Cikin sauri AD Dukku ya girgiza kai yana faɗin, "No Gwaggo! Bana son yawan tafiye-tagiye kema kin san hakan." Gwaggo ta taɓe baki tana ɗaga murya ta kira Tabawa, sai gata cikin hanzari ta iso cikin falon.Ganin AD Dukku manne a jikin Gwaggo ya sanyata sakin murmushi tana masa barka da zuwa.Ya ɗaga mata hannu cikin basarwa ya furta, "Tabawa sannu ko." Daga haka ya zame jikinsa daga na Gwaggo yana zama sosai kusa da ita.Gwaggo ta bai wa Tabawa umurnin kawo masa fura haɗe da soyayyiyar naman ragon da aka soya ɗazu,ta kuma ce ta haɗo masa da ruwa da lemu duka ta kawo.AD Dukku ya dubi Gwaggo cike da so ya ce, "Granny ina Hannah ne wai?" Gwaggo ta ɗan tsuke fuska tana hararansa ta ce, "Baka tambayi uwar taka ba sai ni ƴar kararen da aka so a ɓoye mini abinda ke faruwa, yanzu Adinanu sabida rashin tsoron mahalicci irin naka, ka ɗirkawa ƴar mutane ciki bayan duk ka gama nuna baka sonta akai auren,sannan yanzu kuma kace baka son cikin,don ƙaniyarka ba a haihuwa kai ka zo duniyar? To wallahi kar kaga ina wani lallaɓaka da shagwaɓaka, akan zancen cikin sai inyi maka tsirara a bainar nasi aji kanmu ni da kai.Kuma ba za ta koma garin ƙabilu ta haifo min jika ya yi kama dasu ba,anan zata zauna har ta haihu don tsakanina da kai akan cikinannan babu yarda babu amana.Tunda dai tun farko ka nuna baƙin cikinka akan samuwarsa, don haka ni babu ruwana da kai kama daina tambayata inda take ehe!" AD Dukku da dariyar drama ɗin Gwaggo ke cinsa arai, sai ya maze tare da sake haɗe face ya ce, "Au yanzu Gwaggo haka zamuyi dake, daga zuwa Momy ta rufeni da faɗa,bata ma sanar min inda take ba yanzu kuma nazo inda zan ji sanyi kema zaki juyemin?" Gwaggo nan da nan sai ta sassauta murya tamkar mai son yin raɗa ta ce, "Kwantar da hankalinka, tana can ɓangarenku da ina zata ka ke zato? Kai ɗin ne ka bani haushi sosai akan zancen wai baka son haihuwa." AD Dukku da sam bai kawo Hannah na ɓangarensu ba, sai ya sauke numfashi yana duban Gwaggo kai tsaye ya ce, "Sorry sweety! Ai yanzu babu zancen cire ciki tunda kuna son abinku, ni dai babu ruwana ne don ban shirya zama uba ba a yanzu da nake ganiyar cin lokacina." Shigowar Tabawa ya hana Gwaggo cewa komi.Tabawan ta aje tray ɗin da ta ɗauro dukkanin abinda Gwaggo ta lissafa, ta aje a kusa dashi ta juya ta bar wajen.Hakan ya bai wa Gwaggo damar faɗin, "Eh mu muna son abin mu, don haka ko kana so ko baka so saika zama uban kana ƙaryan iyashegene Adinanu." Bai sake magana ba ya ɗauki cup ya zuba sassanyar furan da aka dama da asalin nono kindirmo,aka haɗa da kwakwa da madara duk aciki ya kai bakinsa.Ya kurɓi furan sanyi da garɗin furan na ratsashi, ya wani lumshe ido yana sake siffing furan har ya shanye wanda ya zuba tas! Ya dire cup ɗin yana kai hannu ya ɗakko yankan naman ragon ya kai bakinsa.Ya jima sosai tare da Gwaggo har sai da aka kira sallar magriba sannan ya miƙe don zuwa masallaci.Ya fito yana duban side ɗinsu tare da sakin ƙaramin tsaki, amma can ƙasan zuciyarsa na cike da ɗokin son kasancewa da gangar jikin Hannah da yake samun tarin nutsuwa a tattare da ita.......✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/20, 6:23 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 19* _Free page_ Daga ɓangaren Momy kuwa Najma ce ta dubi Nasreen ta ce, "Nasreeny miye ne duk mood ɗinki ya sauya yanzu-yanzu?" Nasreen ta ɗan taɓe baki tana faɗin, "Wallahi banso Yaya AD yazo bane a week ɗinnan,sabida shegiyar takura da yiwa mutane masifa ya iya." Najma ta jinjina kai cike da basarwa ta ce, "To ina ruwanki dashi, ba sai ka shiga harkan mutum zai maka masifan ba.Ni kinganni nan bani da tsoron duk wata masifar mutum don bama zan shiga sabgarka ba bare har ka min ɗin, tsakaninku dashi ba gaisuwa bace da girmamawa, sai idan ya saka abu kuyi masa kuyi ɗin?" Nasreen ta sauke numfashi ta ce, "Hmm! Ba zaki gane bane Najma, shi fa Yaya AD daban yake wallahi.Sometimes shi da kansa zai saka kai masa abu, ƙarshe ya zama disgi a gareka,ni kawai bana son ma ganin yazo gara muna waya yafi mutunci ta waya." Najma ta saki dariya tana taɓe baki ta ce, "Hakanan za ku yi haƙuri da halinsa ai." Kafin Nasreen tayi magana kiran Momy ya shigo wayarta, sai ta ɗaga wayar tana faɗin, "Hello Mom!" Ta ɗanyi jim kafin ta furta, "Momy why Nabeey please!" Ta sake yin jim! Kafin ta ce,"Okey gamu nan ni da Najma please!" Daga haka ta kashe wayar tana duban Najma da ke danna wayarta ta ce, "Naj! Muje Momy na kira." Suka miƙe a tare suna fitowa falo, basu ga Momy anan ba sai suka wuce kitchen direct.Momy ta nunawa Nasreen basket da aka shirya warmers na abinci ta ce, "Gashi nan ɗauki wannan, ita Najma ta ɗauki tray ɗin can ku kai side ɗinsa.Ki cewa Hannatu idan tana son cin wani abu ta faɗi sai su Rabi su girka mata,kinsan masu juna biyu basa rabo da son kwaɗayi." Nasreen cike da zallar murna ta dubi Momy tana faɗin, "Momy wai dama ciki gareta?" Momy ta jinjina kai tana bata amsa da faɗin, "Yes! Maza ku je bana son surutu." Suka ɗauki basket da tray ɗin suka fice Nasreen na faman nuna murnarta ga samuwar cikin. Sun tadda babu kowa a falon Hannah har Nabeela da ke side ɗin basu gani ba a falon, sai suka aje komi bisa dining Nasreen na nufan hanyar bedroom ɗin Hannah.Najma ta zauna tana faman kallon tsaruwar ko'ina, tana kuma shaƙan daddaɗan ƙamshin da ke tashi a ko'ina na ɗakin. Nasreen bata jima ba suka fito tare da Anty Hannah,ita kuma Nabeey na biye dasu a baya.Basu jima sosai ba Nasreen ta janye Najma suka bar side ɗin,don bata son ya shigo ya samesu a side ɗin nasu. Ɓangaren Momy suka nufa daidai ana kiran sallar magriba, sai suka wuce direct ɗakin Nasreen suka ɗaura alwala suka gabatar da sallar. Lokacin da suka idar ne Najma ta marairaicewa Nasreen cewa zata gudu ɓangaren Gwaggo, Nasreen ta dubeta tana faɗin, "Haba Sis don Allah ki yi zamanki anan ɗin,ko kin je takura zaki yi idan Yaya AD na wajenta.Kin san shi baya rabo da manne mata,sabida yadda take sake taɓarashi yana abinda yake so." Najma sai ta ɗan yi jim...! Kaman ba za ta ce komi ba sai kuma ta furta, "To bari dai in bari sai zuwa can anjima saina koma can ɗin." Nasreen ta jinjina kai suka kamo hiran tafiya giwa a gobe,Najma na faɗin irin ɗokin da take ji a zuciyarta na son ganin su Lubah. Sai da suka sallaci sallar Isha'i sannan suka fito zuwa falo,suna zama motar Daddy na shigowa gidan.Sai sukai waje don tarbosa har da Najma da ke ɗan yin baya-baya na jin nauyi da rashin sabo.Da fara'a sosai Daddy yake amsa gaisuwar Najma yana jansu da hira har suka iso cikin falon.Momy ta fito cikin kwalliya na alfarma ta tarbi Daddyn,tana mai riƙo hannuwansa tana faɗin, "Welcome Daddy!" Alhaji Kabeer Dukku ya dubi matarsa cike da so ya ce, "Thank u luv!" Suka wuce su Najma zuwa side ɗinsa,Najma naji kamar ta narke a wajem don kunya.Nasreen ko sam bata ji komi ba ta dubi Najma tana faɗin, "Sis muje dining kiyi dinner, ni kinsan sai to 10pm zan saka wani abu a cikina.Ke kam kun saba cin abinci akan time." Babu musu Najma ta bi bayanta zuwa dining area suka zauna,Najam tayi serving kanta lafiyayyiyar tuwan semo da miyan ɗanyar kuɓewa da aka zuba naman rago da cat fish a ciki. Ga soyayyiyar man shanu a cikin bowl na tashin ƙamshi, sai ta zuba kaɗan ta fara cin abincin a nutse.Nasreen ko maida hankalinta tayi kan chart,suna ta magana da wata course mate ɗinta Rash Kagarko. Daga ɓangaren AD Dukku kuwa tunda ya shiga masallaci sallar magriba,bai fito ba sai da akai sallar isha'i sannan ya fito.Ganin motar Daddy alamun ya iso sai ya fasa nufan side ɗinsa ya wuce falon Daddy ta ƙofar waje.Ko kaɗan bai samu fuska wajen Daddy ba, don ko gaisuwarsa a daƙile ya amsa.Ya samu waje ya zauna kansa a ƙasa yana faɗin, "Daddy ya hanya?" Alhaji Kabeer Dukku ya dubesa fuska a haɗe ya ce, "Lafiya lau, idonka kenan sarkin marasa kunya? Yanzu Adnan ni kake neman tozartawa ka shiga tsakanin amincina da aminina ko?" Adnan ya sake ƙasa da kai cike da kwantar da murya ya ce, "Ayi haƙury Daddy kuskure ne." Daddy ya aika masa wani kallo yana faɗin, "Kuskure ko iyashege da rashin tsoron Allah? Wato bayan ka gama iskancin nunawa auren rashin ƙauna, yanxu kuma Ubangiji ya kawo rabo shi ne zaka butulcewa ni'imarsa ka nuna baka buƙatar kyautarsa a gareka.To ka buɗe kunni da kyau ka jini,wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zan ji anyi maganar cikin jikin matarka da sunan wai baka so ko makamancin hakan.Sannan ta dawo kenan har sai ta haihu,kuma duk weekend ko bayan sati biyu nake son ganinka a garin, ka zo duba lafiyar matarka dana abinda ke cikinta.Kar kaga bama gari ɗaya ka ɗauka duk iskancin da kake yi bana sani, ina da labarin komi sannan ina da masu sanya mini ido akan dukkanin motsinka.Kai ba ƙaramin Yaro bane Adnan, sannan ka wuce munzilin da za a zaunar da kai ana tisa maka cewa kabi Allah ka nisanci saɓa masa,domin daidai gwargwado na baka ilimin addini dana zamani.Sannan nayi maka irin tarbiyar da namu mahaifan sukai mana, don haka ya rage naka ka gyara rayuwarka wajen watsar da abokanan banza ka zama mutumin kirki.Duniya ta daina ruɗarka kana biyewa ƙawarta wajen tarwatsa rayuwar mutuncinka,don a yanxu ka shiga sahun uba wanda xai aje ɗan kansa ya kuma bashi tarbiyya.Idan har baka gyara yau ɗinka ba, a gobe wani irin tarbiyya za ka yiwa ɗanka ko ƴarka idan sun zo duniya?" Daddy ya dakata da maganar ta hanyar jefawa Adnan Dukku tambayar, yana tsareshi da idanunsa masu kaifi.AD ya sake risinar da kansa zuciyarsa na taɓuwa da kalaman Daddyn, ya cigaba da yin shiru bai ba tare da ya ce komi ba don bashi da abin faɗi ɗin. Hakan ya bai wa Daddy damar cigaba da faɗin, "Kana so ɗanka ko ƴarka su taso ace musu ubansu ɗan ƙwaya ne ko ɗan club dake yawon bin dare yana watsewa da matan banza? Ka ji tsoron Allah Adnan ka kuma ji tausayinmu ni da mahaifiyarka domin baka mana adalci, a matsayinmu na waɗanda suka tsayu wajen baka tarbiya mai nagarta.Ban ɗauke ka na kai ka ƙasar waje domin ka lalace ka koyi ɗabi'un banza ba, na kaika ne don nuna maka gata da kuma sauƙaƙa maka hanyar samun ingantaccen ilimi a sauƙaƙe ba tare da ka fuskanci matsalar yajin aiki ko wasu matsalolin ba.Amma kai sai ya kasance ka zaɓi mutanan banza su zama abokanka,aka kuma yi nasara sun ci galaba a kanka wajen dilmiyar dakai.Ka taimakemu ka dawo a mutumin kirki, nutsatstse kamar yadda aka sanka kafin barinka ƙasarka ta haihuwa.Ka watsar da duk wasu abokanan banza, ka kuma nisanci kusanta kanka da zuwa wajen da ake aikata masha'a.Kuɗi da wayewa ba hauka bane, domin mu bamu yi hakan ba don bamu zaɓi bin layin sakarkaru ba.Don haka ka shiga hankalinka ka dawo cikin hayyacinka tun lokaci bai ƙure maka ba." Daddy ya sake dakatawa idanunsa akan AD Dukku da jikinsa ya yi mugun sanyi,amma can ƙasan zuciyarsa gani yake Daddy yana matsawa rayuwarsa ta hanyar sanya masa ido ne kawai.Ya buɗe baki cikin muryarsa mai cike da aji ya ce, "Allah ya huci zuciyarku Daddy, ku cigaba da mini addu'a In Sha Allah zan gyara zuwa yadda kuke buƙata." Momy ta sake ɗaurawa da nata faɗan, ta koma nisiha sannan daga ƙarshe Daddy ya sallamesa ya ce sai da safe zasu haɗu kafin su wuce giwa. Ya fito daga ɓangaren Daddy yana ji dukkanin jikinsa nayin sanyi da nasihun iyayen nasa, waɗanda bashi da tamkarsu kaf faɗin duniya.Zuciyarsa ta dinga tuno masa da dukkanin kalaman Daddy,yana ji suna amsa kuwwa a tsakar kansa. "Da gaske idan ya haihu ɗan ko ƴar xa a iya musu gorin cewa yana shan ƙwanya da tarayya da matan club?" Ya tambayi kansa yana jin wani abu na sake tsayuwa a ƙirjinsa.Ya isa ɓangaren nasu yana jin wani irin yanayi na bin jinin jikinsa,kamar yadda wani ɓangaren ke ingizashi da tunasar dashi cewa wayewar kenan ya tafiyar da rayuwarsa kamar ya faro. Yana tura ƙofar falon ya shige yana fara cin karo da Nabeelah zaune bisa sofa tana chart.Jin shigowarsa da ƙamshinsa da baya ɓuya ya sanyata saurin waiwayowa,ta zuba masa idanunta tana miƙewa cike da murnar ganinsa ta ce, "Oyoyo! Ya AD." Ya ɗan sakar mata fuska yana faɗin, "Autan Momy ya kike?" Nabeey ta amsa da cewa, "Lafiya lau Yaya.Anty na ciki." Ya gyaɗa kai ba tare da ya yi magana ba ya nufi hanyar bedrooms ɗinsu.Har zai shiga nata sai ya fasa ya nufi nasa ɗakin, yana mai farawa da rage kayan jikinsa ya nufi bathroom.Wanka ya yo ya fito sanye rigar wanka,ya nufi bakin mirrow yana murza mai kaɗan a fatarsa.Blue black jallabiya mai asalin tsada ya ciro daga closet ɗinsa ya saka,ya ɗauki turarensa da baya rabo dashi a duk inda ya san yana zama ko sauka ya fesa a jikinsa.Aje kwalbar turaren ya yi daidai da shigowar Hannah cikin ɗakin, wacce gaba ɗaya tunda Nasreen ta sanar da ita isowarsa ta gaza samun nutsuwa.Ta taka zuwa cikin room ɗin sassanyar ƙamshinsa na dukan hancinta,zuciyarta na sake narkewa da jin ƙaunarsa mai zafi da ta yiwa zuciyarta yawa.Tana sanye ne da wata Ash colour ɗin rigar shan iska mara hannu,tsayin rigar da kaɗan ya wuce cinyarta.Sosai rigar ta fiddo surar gaba da bayanta da suka sake cika,musamman ƙirjinta da ya sake cikowa sosai.Ya zuba mata idanu lokacin da take takowa zuwa garesa, yana ji dukkanin jikinsa na saki.Bai ɗauke idanunsa a kanta har ta tako tayi tsaye daga bayansa tana faɗin, "Sannu da zuwa Hubby, zuwa babu sanarwa sai a bakin Nasreen na ji ka shigo garin.Miye laifina ne wai AD, mene ne laifina don zuciyata ta mato a ƙaunarka?" Bai yi magana ba ya yi taku biyu yana isa gareta ya juyo da fuskarta suna facing juna.A hankali ya haɗe fuskarsu waje guda yana mannata da jikinsa sosai, ta yadda tudun ƙirjinta ya mannu da nasa ƙirjin.Ya lalubo bakinta ya sumbata,kafin ya kai hannu bisa maranta ya shafosa.Hannah ta sauke wata shegiyar ajiyar zuciya tana lumshe idanunta tare da sake shigewa jikinsa.Murya can ƙasa ya furta, "Bana son yawan ƙorafi Hannatu, sannan baki da laifi don zuciyarki na ƙaunata.But ki sani wannan abin da aka ce kina ɗauke dashi shi ne bana so Hannah! Ban shirya zama uba ba amma babu yadda na iya a yanzu dole na amshi abinda bana ra'ayi tunda jin haɗani da iyayena fine!" Ya kai ƙarshen maganar yana cusa kansa a ƙirjinta ya shaƙo daddaɗan ƙamshin turarenta dana humran RUSS mai kashe jiki da sanya tsantsar shauƙi. Duk yadda Hannah ta so zamewa daga tarkonsa kasawa tayi domin da alamu a yunwace ya shigo garin,don bai barta ba sai da ya samu biyan buƙatar da ya sanar mata somi ne kafin ya ci abinci zuwa anjima tayi biyan bashin mai dalili.Ta nufi bathroom ɗinsa don yin wanka tana jin dukkanin jikinta na amsawa,don ya sameta sosai irin yadda yake buƙata. Sun fito falo sun tadda Nabeelah ta gudu abin ta, Hannah tayi serving ɗinsa abincin da Momy ta aiko.Yana cin abincin yana amsa call da ke shigo masa time by time,ita kuma Hannah na daga gefe tana dubansa tamkar mai gadin kada a zo a sure mata shi.Wani irin soyayyarsa take ji a zuci mai yawa, duk yadda ya kai ga haɗe mata face kyau yake mata tana jin zuciyarta na sake matowa a kansa.Tana son bashi haƙuri akan zancen cikin tana tsoron kalaman da zai gasa mata,hakan ya sanya ta ja baki tayi masa shiru har ya kammala cin abincin ya tashi.Ta dubesa cikin ido time ɗin da ya doshi hanyar fita falon ta ce, "AD fita zaka yi ne alhali baka jima da shigowa ba?" Wani kallo ya juyo ya aika mata,yana cigaba da takawa ya furta, "Wajen Gwaggo zani ko laifi ne yin hakan?" Hannah tayi ƙasa da kai zuciyarta na taɓuwa da yadda ya haɗe mata fuska tamkar bashi ya gama sambatu a bed ba ɗazu, tayi saurin faɗin, "Allah ya baka haƙuri ka gaisheta." Ya yi ficewarsa ba tare da ya sake tanka ta ba, don gaba ɗaya idan yana tuna tana ɗauke da cikin da bai shirya samuwarsa ba haushinta yake ji na rufe zuciyarsa.Sai dai ni'imar da ya kwasa a jikinta yau ɗin, ya sanya shi nishaɗi domin ta kaishi wata iriyar duniyar maji daɗi.Ya wani ja ƙaramin tsaki ƙasa-ƙasa yana cigaba da takawa ya fito daga side ɗin baki ɗaya zuwa na Gwaggo.Bai samu kowa a falon ba don 10pm ta gota, tuni Inna Mairo ta sha maganinta ta kwanta.Ita kuma Gwaggo na ɗaki na kintsa kayan da zata kai tsaraba giwa a gobe.Najma kuma Momy da Daddy sun ƙi bari ta dawo side ɗin Gwaggo, don Daddy cewa ya yi ma ta dawo kenan sai dai ta riƙa shiga gaida su tana dawowa nan ɗin.Hatta kayan sawarta ya ce suna dawowa giwa ta tabbatar komi nata ya dawo ɗakin Nasreen,don yana so kansu ya sake haɗuwa su kuma shaƙu da juna sosai. Direct ɗakin Gwaggo AD Dukku ya nufa, don ya yi mugun sabo da indai ya shigo garin baya iya kwanciya bai shigo ya yi mata sai da safe, sun ɗan taɓa hira tare da cin wani abu idan ya shigo dashi ba. Ya zauna saman sofa ya zauna yana faɗin, "Sweet granny shirin dai tafiya ƙauyen ne? Why not ki barsu Momy su wuce ke ki yi zamanki musha hira gobe kafin in wuce Abuja,daga can kuma zan wuce port harcourt ba xan dawo ta nan ba." Jin abinda ya faɗi ya sanya Gwaggo saurin dubansa tana faɗin, "Kana nufin gobe zaka wuce Habujan?" Ya jinjina kai tare da ɗage mata gira guda.Hakan ya sanya ta tsuke fuska tana faɗin,"Amma baka da tausayi Adinanu, inyi wata biyu ban sanya ka a idanuna ba amma ka zo sai ka ce min kuma gobe zaka tafi.Gaskiya baka kyauta mini ba, wannan ai dama baka zo ba kawai yafi." Adnan ya ɗan murmusa yana duban Gwaggo cike da so ya furta, "Karki damu sati na sama zan zo nayi one week, yanzu aiki ne zai kaini Abuja ɗin Gwaggo.Kuma dole in wuce a gobe ɗin babu yadda na iya,amma zan dawo karki damu tunda kun riƙemun mata anan ma ai xaki dinga gani na akai-akai don Daddy ya ce lallai na riƙa zuwa duk weekend ko bayan sati biyu." Gwaggo ta jinjina kai tana faɗin, "Har kunyi magana da Kabeerun ne? Amma shi ne da ya shigo bai ce min komi akan zancen ba.Sai ka kula dai ka aje duk wani shashancin banza na gaya maka,don duk wannan jinkan naka da tsare gida na banza ne tunda kana shan shegun ƙwayoyin da ke sake ƙonar maka da zuciya da sanyaka rashin kunya kala-kala ko?" AD Dukku bai shiryawa yin dariya ba amma sai da ya dara.Ya dubi Gwaggo da wani irin so yana mai faɗin, "Gwaggo dama akwai ƙwayar da take sanya rashin kunya ce?" Gwaggo tayi saurin gyaɗa kai tana faɗin, "Ƙwarai kuwa, haka naji ana faɗi kuma wallahi na yadda don idan kuka afa bakwa ganin kowa da mutunci ehe!" Wannan karon baki ya taɓe yana danne dariyar da ke cinsa ya furta, "To ni dai ba ita nake sha ba Gwaggo, yanzu dai ki aje maganar wata ƙwaya ki ɗakko min irin naman ɗaxu naci shi na shigo ci." Gwaggo ta harareshi tana cigaba da masa mita akan shan ƙwaya da illolin da yake janyowa mai yinsa,sannan uwa uba ɓarewar mutunci a idanun duk wani mai maka kallon daraja da cikar kamala.Adnan dai jinta kawai yake yi ba tare da ya tanka ba, suka fito falo ta nufi kitchen don ɗebo naman, ta haɗo da sassanyar madarar shanu da aka zuba zuma a ciki ba sugar ba.Ya ci naman mai yawa da madarar, yana ci suna hira har ya kammala.Ya yiwa Gwaggo sai da safe ya wuce side ɗinsa,yana ji zuciyarsa na sake cika da ƙaunar gwaggon nasa mai shagwaɓashi.Ya samu Hannah har ta gaji da jiran shigowarsa bacci ya kwasheta bisa sofa, ya bi rigar baccin da ke jikinta da kallo wanda babu maraba da babu.Ya ɗan lumshe idanunsa yana sake buɗesu akan tsayayyun ƙirjin da babu bra a jikinsu,sai wani tsokane idanunsa suke yi domin rabinsu sun bayyana a waje.Ya taka a hankali ya isa bakin sofa ɗin, yana mai rankwafawa ya basu wani light kiss kafin ya saɓata a kafaɗarsa zuwa room ɗinsa.Yana aje ta a tsakiyar bed ɗin tana farkawa, ta sauke idanunta a kansa lokacin da yake cire jallabiyar da ke jikinsa.Wani irin ƙishi taji tana ji,hakan ya sanyata sakkowa daga bed ɗin ta nufi ƙofar fita don ɗakko ruwan sha. Ganin zata fice ya sanya shi yi mata magana a kausashe,ta narke masa tare da sanar dashi ruwa kaɗai za ta ɗakko ta dawo.Tana fita hawaye suka cika idanunta,tana mamakin rashin kunyar AD Dukku.Domin ta gama gane gangar jikinta kawai yake so ba ita ba, ta gama sanin bata da wani amfani da ya wuce biyan buƙatar sha'awarsa.Sai kuma albarkacin soyayya da amintar da ke tsakanin iyayensu da ya zamewa aurenta da shi garkuwa,irin garkuwar da yake ɗaga mata ƙafa ya kuma amshi auren da hannu biyu amma ba don ƙauna ko soyayyah ba.Ruwan kaɗai ta sha ta yo fitsari tare da ƙaro turare akan wanda ta sanya time ɗin da ta saka rigar baccin.Tana shigowa ɗakin ta tadda ya kashe hasken ɗakin, sai mai duhu da ya bari.Ta lallaɓa ta hau bed ɗin zuciyarta na cigaba da matsewa da wani yanayi mai wuyar fassara.Tana jin sanda ya miƙo hannuwansa ya jata zuwa jikinsa yana shinshinan ƙamshinta kamar wani maye.Sai ta sauke ajiyar zuciya tana hana kanta shigewa cikin jikinsa sosai,amma duk yadda taso nuna masa gajiyarta kasawa tayi.Hakanan ta biye mishi ya sake samun cikakken gamsuwa daga gareta.Ko wanka bata iya yi ba baccin wahala da gajiya ya kwasheta, shi kam sai da ya yo wanka ya dawo ya kwanta don sam baya yadda ya kwana da janaba a jikinsa. *```WASHEGARI``* Koda AD Dukku ya shiga gaida Gwaggo, ita kaɗai ya samu ta gama karyawa kenan bata tashi a wajen ba. Inna Mairo tana ɗaki tana shiri don Daddy ya ce da wuri za a fita,don su samu su isa da wuri su kuma dawo akan lokaci.Ya samu kusa da Gwaggo ya zauna yana buɗeta da daddaɗan ƙamshin dake tashi a jikinsa,ya gama yin kyau cikin ƙananun kayan da ke jikinsa.Gwaggo ta amsa gaisuwarsa tana tsaida idanunta a kansa cike da ƙauna ta ce, "Ba dai har kayi shirin wucewa Abujan ba?" Adnan Dukku ya ɗan kwaɓe fuska cike da shagwaɓar da ya saba yi mata ya ce, "Eh na shirya Gwaggo, daga nan sai wajen Daddy zan wuce muyi sallama in kama hanya don ni zanyi driving da kaina." Gwaggo ta sauke numfashi tana faɗin, "To Allah ya tsare hanya,muma nan da lokaci kaɗan zamu gama shiri mu kama hanya.Don Allah Adinanu ka rungumi Hannatu ka bar wa Allah ikonsa,don da alamu aurenku da juna alkhairy ne tunda gashi zaku fara tara zuri'a.A hankali zaka ƙaunaceta kamar yadda take ƙaunarka,ko kaɗan bata da wani aibu kai nema mai aibun amma a hakanan take ƙaunarka da zuciya ɗaya.Don haka kaji tsoron Allah wajen sauke hakkinta dana abinda take ɗauke da shi, karka ga mun dawo da ita gabanmu hakan ya baka damar cigaba da sharholiyarka a can.Idan bama ganinka Ubangiji yana kallo,kuma zai yi mata sakayya gwargwadon yadda kaci amanarta kona namu ta hanyar saɓa mana da saɓama Ubangijinka.Ka taimakeni ka rabu da duk wasu abokanan banza da ke sake tunzuraka a aikata saɓo,domin ba tarbiyan da Kabeeru ya yi maka kenan ba." Gwaggo ta dakata tana duban yadda mood ɗin AD Dukku ya canza,don bai saba ta tasa shi tana masa irin wannan faɗa da nasihun ba.Ya ɗan haɗe fuska yana faɗin, "Gwaggo wallahi ni ba zina nake yi dasu ba,sune kawai ke manne mini amma ban taɓa kwanciya da ƴar kowa ba.Kin san ina da ƙyanƙyami so bana kusantarsu ta wannan hanyar da ku ke zargi,sannan kuma ni abinda nake sha ba buguwa nake yi kamar ɗan giya ba Gwaggo.Amma zan yi ƙoƙari na rage koma miye don na faranta muku, amma ba za a ce in daina gaba ɗaya a lokaci guda ba." Ya ƙare maganar yana ɗaura kansa a kafaɗarta.Ta kai hannu ta shafa lallausar suman kansa tana faɗin, "Naji Adinanu, amma shi saɓo duk sunansu ɗaya,koda baka kwanciya dasu tarayyarka dasu ɗin ai saɓo ne tunda ba matanka bane ƴan iskan bariki ne marasa tarbiyyya,ni dai ka nisancesu ka kuma nisanci zuwa inda suke domin komin son su da kai idan basa ganinka dole su ɗaga maka ƙafa.Ka daina ganin kyawunka na ruɗarsu,akwai lokacin da kyawun zai disashe." AD Dukku ya saki murmushi mai faɗi,kafin ya raba kansa da kafaɗarta yana miƙewa tsaye ya ce, "Na gode Gwaggo da nasiha, ni zan wuce tunda naga alamun wannan karon ba wani soyayya ki ke son nuna mini ba." Kafin Gwaggo tayi magana sallamar Najma cikin sanyin muryarta ya doki kunnuwarsu.Gwaggo ta amsa sallamar tare da bata izinin shigowa cikin falon, ta shigo kanta a ƙasa hancinta na shaƙan fitinannan ƙamshinsa da tun jiya ta gama saki cewa ƙamshin na musamman ne.Duba ɗaya ta yiwa inda suke ta ɗauke kanta tana tsugunawa nesa dasu ta gaida Gwaggo,Gwaggo ta amsa da fara'a tana faɗin,"Sannu Najma, yanzu nake cewa a raina sun riƙeki baki shigo da wuri ba." Najma ta ɗan saki smile tana faɗin, "Eh Gwaggo, wallahi Nasreen ce duk ta hanani shigowa tunda sassafe,bari in shiga mu fara shiri Daddy ya ce da wuri za a wuce." Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Haka ya ce kuwa, Mairo ma gata can a ɗaki nasan shirin take yi." Najma ta miƙe tana satan kallon gefensa taga hankalinsa na kan danna wayarsa,sam bai muna alamun ya san da wanzuwarta a falon ba.Har zata wuce sai taga rashin dacewar ƙin gaida shi,tunda ko banza shi ne babba a gidan kuma Iyayensa nada ƙima da mutunci a idanunta.Hakan yasa ta ɗan ɗaga sautin muryarta yadda zai jiyota ta ce, "Ina kwana,da fatan an tashi lafiya." AD Dukku da sassanyar muryarta ya bugi kunnuwarsa,sarai ya gane shi take gaidawa amma isarsa da zafin kansa ya hanashi ɗagowa ya dubeta.Hannu kawai ya ɗaga mata ta wuce yana cigaba da danna wayarsa, sai da ta shige corridor ɗin gaba ɗaya sannan Gwaggo ta dubesa tana jin haushin yadda ko kallon Najmar bai yi ba ta ce, "Yanzu ana gaidaka amma ko kallo bata isheka ba Adinanu, ita ce fa ƴar Gwaggonka Mairo da nake faɗi maka ka riƙeta tamkar su Nabeela.Gaskiya bana son wannan wulaƙancin naka,irin haka ne duk saika saka ta muzunta haba Adinanuna!" AD Dukku ya ɗago ya zubawa Gwaggo idanunsa yana faɗin, "Gwaggo mai zance mata tuh? kuma ko ban kalleta yau ba watarana zan ganta ai tunda sun dawon nan ɗin." Don haushi Gwaggo bata kulashi ba har ya yi mata sallama ya wuce side ɗin Daddy. A can ma side ɗinsu Momy bai daɗe ba ya yi musu sallama dasu, ya fito zuwa side ɗinsa.Ya samu Hannah ta tashi tana yin breakfast kenan.Tayi kyau sosai cikin ƙananan kayan da ta saka,waɗanda suka fidda suranta sosai da kuma bayyana fresh ɗin da tayi.Sallama ya yi mata akan zai wuce Abuja daga can kuma gobe zai koma PH ɗin,duk sai ta ji babu daɗi a ranta domin bata san cewa a yau ɗin zai juya ba.A sanyaye tayi masa fatan isa lafiya tana ji haka kawai hawaye na cika idanunta, domin bata san ranar da zata yi darajar da zata dinga sanin abubuwan da suka shafesa ba.Har ya kai ƙofa ya dawo da baya yana rankwafawa ya sumbaci fuskarta zuwa ƙirjinta,murya can ƙasa ya kai bakinsa bisa kunnuwarta yana faɗin, "Take care! Zan dawo zuwa next week okey!" Daga haka ya juya ya barta da lumshe idanunta hawayen da take riƙewa na sakkowa daga cikin idanunta.Wani irin ƙaunarsa ke sake huda kafan jininta,tana ji tamkar ta bisa su juya tare ko zata dinga ganin kaikawonsa da dakon jiran dawowar cikin tsakiyar daren da ya saba kaiwa ɗin.Don a nan ɗin bata da tabbacin zai dinga zuwa kamar yadda su Momyn suka faɗi.Da ƙyar ta iya ƙarisa cin abincin ta tashi ta nufi ɗakinta,ta sako hijab ta fito zuwa side ɗin Gwaggo don gaidata.Daga can ta wuce side ɗinsu Momy ta tadda suna ta shirin wucewa giwa, don Momy har ta gama cin ado cikin wani rantsatstsan lace mara nauyi mai shegiyar tsada.Nasreen ma ta sha ado cikin wani red and black jacquard voile mai kyan gaske.Ɗinkin straight gown ɗin da akai wa kayan ya amshi jikinta tare da fidda kyawun surarta matuƙa. Nabeela shadda ce a jikinta da yaji embroidery ɗinki ta ko'ina, tayi kyau har ta gaji ita ma don ita ma kyakykyawace wacce ta ɗakko kammanin Daddy sak! Ko kaɗan Hannah bata ji daɗin yadda za a barta ita kaɗai a gidan ba sai ƴan aiki.Ganin duk jikinta a sanyaye yake sai Momy ta ce idan za ta iya zuwa ta je ta shiryo kawai a wuce tare da ita ɗin.Aiko cikin zumuɗi ta koma ta shiryo cikin shiga ta alfarma cikin wani lafaya lace da ya amshi jikinta. Ƙarfe 11:30am suka kammala shiryawa aka loda tsarabar kayan abinci da kayayyaki masu yawa a bayan boot.A cikin ƙatuwar motar Daddy suka ɗunguma,inda Momy da Inna Mairo da Gwaggo ke ta seat ɗin farko.Yayinda Najma da Nasreen da Anty Hannah da Nabeey ke seat ɗin baya,sai Daddy da ya kame a front seat shi kaɗai. Wani irin tafiya aka yi mai cike da nishaɗi, ana hira tsakanin juna har suka isa garin giwa.Gidan Hakimi nan suka fara yin masauki,sun kuma samu kyakykyawar tarba daga kariman mutane irin ahalin Hakimi.Suka rasa inda zasu saka kansu da murnar ganin ahalin Inna Mairo da su kansu su Innar Mairon, waɗanda aka yi kewar rashinsu tsayin kwanaki bakwai kenan.Najma da Nasreen da su Nabeela suka ƙule a ɗakin su Hanne suna kwasan hira cike da nishaɗi,an cika gabansu da kayan cima da Hakimi ya fidda kuɗi aka yi cefane mai kyau don tarban su Gwaggo.Lafiyayyan wainar shinkafa da haɗaɗɗiyar miyau taushe da aka zuba naman kajin da aka yanka a ciki, gefe guda kuma an soya musu wasu kajin har da zabi guda biyu ma.An sayi soft drink da su ruwan sha,duk don a fita kunyar su Inna Mairo da hamshaƙan ahalinta waɗanda tun daga kan suturun jikinsu da kalar motar da suka zo a ciki zaka san cewa masu kuɗine ƴan gaske. Daddy da Hakimi tare da wasu cikin amintattun Hakimi ne ke zaune daga falon Hakimin, an baje abinci da kayan arziƙi ana ta hira cikin nishaɗi mai yawan gaske.Daga ɗakin uwargidan Hakimi Inna Karima kuwa,su Gwaggo da Momy ne suke ta shan shafta da tuno baya akan irin rayuwar ƙunci da Inna Mairo tayi bayan ta rasa gwarzon mijinta Malam Mahmuda.Inna Karima ta dinga basu labari,tana sanya Inna Mairo tuno memories ɗin tamkar a lokacin wasu abubuwan ke faruwa.Da hira ya yi hira akan irin kirki da karamcin Malam Mahmuda sai ga Inna Mairo na share hawaye akai-akai,tana ji dukkanin memories ɗin rayuwarta dashi a garin giwa na dawo mata.Sukai masa addu'ar fatan alkhairy suna rarrashin Inna Mairo da ke kuka har da hawaye,tana tunawa da Malam Mahmuda,wanda har a tashi duniya bata ji zata so wani ɗa namiji irin yadda ta so shi,ta kuma ƙaunacesa da dukkanin zuciya da gangar jikinta. Bayan sun gabatar da sallah sun ci abinci, sai Hakimi ya aiko aka yi kiran Inna Mairo zuwa falonsa.Suka tattauna batu akan gidansu da zasu bari a kulle tare da kawo shawaran ko zasu sanya ƴan haya a gidan ne? Inna Mairo ta dubi Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa ta ce, "Hakimi duk abinda kaga ya dace ayi shi za a yi In Sha Allahu!" Hakimi ya jinjina kai yana duban Alhaji Kabeer Dukku dake saurarensu ya ce, "Ni a ganina Mairo gara a saka ƴan haya bayan an yiwa gidan kwaskwarima,domin barinsa a haka xai cigaba da lalacewa ne ƙarshe ginin ya faɗi tunda damina za a shiga.Amma ga ɗan uwanki Alhaji nan kuyi shawara a tsakaninku." Alhaji Kabeer Dukku ya dubi Hakimi kai tsaye ya ce, "Shawararka ita ce abin ɗauka don barin muhalli babu kowa a cikinsa babban kuskure ne,gara ko yaya ne a saka waɗanda zasu cigaba da raya wajen.Don haka idan muka isa can ɗin naga yana yin wajen sai a san wani irin gyara za a yiwa wajen, idan so samu ne ma a bugesa ayi ginin bulo da bulo a saka ƴan hayan da zasu kula da wajen basu lalata ba.Tunda gadonsu ne da xasu yi alfahari da ganin wajen,yana tuna musu da marigayi Malam Mahmuda,wanda muke fata yana kyakykyawan matsayi a yanxu." Inna Mairo ta jinjina kai hawaye na taruwa a idanunta ta ce, "Na gode Yaya Kabeeru,Baba Hakimi kaji abinda Yaya ya ce." Hakimi ya jinjina kai ya ce, "Madallah Alhaji, wannan shawara ya yi, kuma In Sha Allah ba za a saka mutanen da za su lalata wajen ba." Daddy ya gyaɗa kai cike da gamsuwa yana faɗin, "Mun gode sosai Mai girma Hakimi, Ubangiji ya biya muku dukkan buƙatunku na alkhairy ya raya Iyali.Tabbas abinda ku ka yiwa Mairo Allah ne kaɗai zai biya ku,Allah kuma ya duba gaba da bayanku." Hakimi ya amsa da cewa, "Ameen." Inna Mairo na sake yiwa Hakimi godia ita ma. Gwaggo da Momy suma falon Hakimi suka fita aka sake gaisawa,su Najma da Nasreen suma tare da su Hanne suka zo zuwa falon suka gaida Daddy.Ya amsa da kulawa yana tambayarsu skull,suka sanar dashi sun kammala sakandiri shekaru biyu baya tare da Najma. Bayan sun koma daga ciki ne Daddy ya tambayi Yaya Auwalu da Umar matakin karatunsu,Auwalu ya sanar da Daddy cewa iyakarsa secondary school.Umar ne kaɗai yake NCE a garin Zaria yanzu,yana ma dab da kammalawa don shi yana son zurfafa karatu ba kamar Auwalu bane da sam yafi ganewa business da noma da kiwon da ya amshe sa. Daddy ya sanar da Umar cewa da zaran ya kammala ya nemesa,sannan shi kuma Auwalu lallai ya yi ƙoƙarin komawa makaranta don yanzu zamani ya sauya, dole mutum ya tashi ya nemi ilimi.Musamman su da suke maza majiya ƙarfi a yanzu, waɗanda ake da burin nan gaba su zama wani abu.Idan babu ilimin sai rayuwar ya zama koma baya,sabida haka lallai ya dage ya koma makaranta. Dukkaninsu suka ɗunguma zuwa gidansu Inna Mairo da suka rayu a cikinsa cikin ƙunci da damuwa.Daddy sai da ya share hawaye sabida tausayi da baƙin cikin yadda Mairo ta rayu a gida irin wannan, alhali su suna cikin arziƙi da wadatan da har yake iya kyautar gida da motar hawa.Amma ace sun bar ƙanwarsu ta rayu a cikin irin wannan gidan,sabida rashin bibiyanta da wofintar da rayuwarta da suka yi. Gwaggo hawaye ita ma take yi sosai,tana jin tsananin nadama da danasanin abinda ta aikatawa Mairo a baya.Nasreen da Hannah kuwa mamaki ne ya daskarar dasu,domin basu taɓa zaton a wannan gidan ƙasar Najma suka rayu ba.Inna Karima ita ce ke bai wa Momy labarin cewa, cutar da Malam Mahmuda ya yi fama dashi ne, jinya ya cinye komi nasu har suka saida asalin gidan da ya gini na zamani a garin,suka dawo wannan gidan suka cigaba da rayuwa har Allah ya karɓe rayuwarsa. Daddy ya shaidawa Hakimi cewa rusa gidan za a yi baki ɗaya asake sabon ginin bulo,don gabaki ɗaya gidan ya yi tsufan da ya kamata ace an sabunta gininsa koda na ƙasa ne. Inna Mairo basu ɗauka wasu kaya ba don Gwaggo cewa tayi karsu ɗauki komi duk su rabarwa jama'an gari.Daddy ma hakan ya faɗi yana mai jin tsananin kunyar Mairo da jin takaicin kansa da kansa,gaba ɗaya ji yake yi tamkar Abbah na can na Allah wadai dashi da rashin riƙe masa amanar Mairo da suka yi shi da Yaya Ali.Inna Karima, Inna Mairo ta ce ta kwashe duka kayan ɗakinta da suturunsu a rabarwa mabuƙata bayan ta zaɓi wanda take so a cikin masu ƙararin cikin.Suka koma can gidan Hakimi aka shiga fiddo kayan abinci da kayayyakin da Momy da Gwaggo suka saya don kawowa matan Hakimi da ƴaƴayensu.Hakimi da Iyalansa suka rasa bakin godia, don kaya ne da ba a taɓa sauke kamansu a gidan ba.Su Hanne kuwa rungume Najma suka yi suna kuka da hawaye,na tsananin murnar alkhairyn da ta zo musu dashi da kuma alhinin yadda zata bar garin giwa baki ɗaya.....✍🏻 *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 [3/20, 9:39 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book:500* *Chapter 20* _Last free pages_ Da suka tashi tafiya har bakin mota dukkanin jama'ar gidan Hakimi tare da maƙwafta,waɗanda Inna Mairo tabi gidajensu tayi musu sallama suka yo musu rakiya har bakin mota. Masu sharan hawaye irin su Inna Kareema nayi, masu kuka sosai irin su Hanne da Lubah ma nayi.A haka su Najma sukai sallama da kowa suka shige mota,tana ji tamkar tayi zamanta a ƙauyen garin giwa.Amma kuma can ƙasan zuciyarta tana son cigaban rayuwarta ta fannin samun ilimi mai zurfi da take da buri.Anty Hannah tausayin Najma ta dinga ji tunda Inna Kareema ta bayar da labarin wahalar da suka sha,ta kuma gane cewa marainiyace bata da uba.Daddy bayan uban kayan abinci da suturu da aka kaiwa Hakimi, sai da ya bashi kyautar kuɗaɗe masu yawa tare da yin alƙawarin ɗaukar nauyin karatun Yaya Auwalu har ya kammala idan ya samu addimision.Sun kamo hanya Najma na faman share hawaye,domin su Lubah sun gama karya zuciyarta da irin kukan da suke na rabuwa da ita,kai kace an rabu kenan har abanda ba za a sake ganin juna ba.Gwaggo dasu Momy har ma da Daddy ne suka dinga rarrashin su Inna Mairo,don ita ma lokaci bayan lokaci take kai bakin mayafi ta share hawayen dake zubo mata. Hawayen da ke fita tare da jin tarin kewa da alhinin rashin Malam Mahmuda tare da shafewar babin rayuwarta a garin giwa,wanda tsananin kewar da take ji a zuciyarta ke sanya hawaye tsere akan fuskarta. Ana dab da kiran sallar magriba suka iso kaduna,domin sunyi yamma a garin giwa basu fito da wuri ba.Dukkaninsu side ɗin Gwaggo suka nufa,amma banda Momy da Daddy da suka nufi side ɗinsu kai tsaye.Anty Hannah bisa sofan ɗakin Gwaggo ta zube tana sauke numfashin gajiya tamkar yau ta saba tafiyar mota,don sosai take jin gajiya ga wani irin yunwa da ke neman hargitsata.Ta rasa meyasa tunda ta samu ciki sai cin abinci,sam bata jure yunwa a ƴan kwanakinnan.Gwaggo ce da ta shigo daga ƙarshe ta dubeta tana faɗin, "Hannatu gajiyarce haka,ko kina buƙatar wani abu ne?" Hannah ta gyaɗa kai a kunyace ta ce, "Gwaggo ko akwai fura a fride ɗinki in ɗan sha?" Gwaggo ta ƙwalla kiran Tabawa da ke niyyar fitowa tarbansu dama, ta bata umurnin kawowa Hannah fura tana cewa a haɗo mata da soyayyiyan naman ragon jiya.Hannah ta ji wani daɗi ya ratsata,har ta ƙosa a kawo naman da furan gabanta.Nasreen da Nabeela basu wani zauna sosai ba suka nufi side ɗinsu don watsa ruwa,sabida yadda suke jin gajiya a jikinsu.Najma da Inna Mairo ma ɗakinsu suka nufa jikinsu a sanyaye,don hankulansu duka naga su Inna Karima da suka baro suna kukan rabuwa dasu.Wanka Najma tayo ta saka riga mara nauyi,tana tsaka da ɗaura ɗankwali aka kira sallah,sai kawai ta nufi wajen da suka keɓe domin sallah a ɗakin ta tada sallah.Inna Mairo ma toilet ta nufa ta watso ruwa,ta fito ɗaure da alwala ta saka riga da hijab ita ma don gabatar da sallah. Hannah ma tana gama shan furan da naman ta yiwa Gwaggo sallama ta nufi side ɗinta.Wanka da sallah ta gabatar,tana idarwa ta janyo wayarta zuciyarta na ingizata akan ta kira AD Dukku taji muryarsa da yadda ya isa garin Abuja ɗin.Sai dai tana danno lambar ta dinga tuna kalaman da Momy ke mata akan sai fa ta dinga daraja kanta da jan zarenta a kansa domin rawar ƙafar da take nuna masa har ya yi yawa.Wani sashi na zuciyarta ya dinga tuna mata cewa shi ya dace ya kirata ya ji lafiyarta dana babynsa,amma bai yi hakan ba alhali ya tafi ya barta tana kukan rashin samun kulawarsa da sam bata yi.Sai ta aje wayar tana ji zuciyarta na cika da wani irin ɓacin rai, ta dinga jin cewa yakamata ta ɗan ja zarenta a wannan karon wajen nuna masa baya gabanta ita ma.Koda ta sake janyo wayar line ɗin Hajiyarta ta kira suka sha hira,Hajiyar na tambayarta zamanta da AD Dukku ana samun cigaba ko kuwa tana nan tana sake zubda kanta yana takata don baya ƙaunarta? Hannah ta ɗan narke murya tana sanar da Hajiyar komi normal ne.Sam bata sanar mata da zancen tana da ciki ba, bare ta bata labarin iskancin da AD ɗin ya yi na cewa bayi son cikin.Bata sanar mata cewa tana kaduna ba,domin Momy ta roƙeta karta faɗa ɗin a yanzu. Ƙarfe takwas da rabi Najma suka haɗu tare da Gwaggo suka ci abincin dare kamar yadda suka saba,Inna Mairo ta ɓalli magungunanta ta sha kamar ko yaushe. Tana jin daɗin magungunan da aka canza mata fiye dana farkon,don yanayin yadda take ji a jikinta ada sam ba haka take ji yanzu ba.Suna kammala cin abincin bada jimawa ba Inna Mairo ta yiwa Gwaggo sai da safe ta wuce ɗaki,don ta gaji bacci kawai take son yi da wuri tunda dama ita bata saba da hiran dare sosai ba.Najma da Gwaggon ta bari a falo suna hira,Najma na baiwa Gwaggo labarai kala-kala nasu Hanne da gidan Hakimi.Wayar Najmar da ke kan jikinta ya ɗauki ruri, tana dubawa taga sunan Nasreen kamar yadda tayi saving sai ta ɗaga wayar da gaggawa. "Sis please ki taho yanzu,Momy ta ce ki ɗan zo mata da fura da ba a dama ba idan Gwaggo na dashi." Nasreen ta furta hakan daga ɓangarenta.Najma ta amsa mata da cewa gatanan xuwa ɗin,ta kashe wayar tana duban Gwaggo ta isar da saƙon Momy.Gwaggo ta ce taje kitchen cikin fridge zata ga furan a leda ta ɗiba,ta haɗa ma har nonon duk ta kai don tasan Daddy za a damawa furan, kuma shi ma yafi so adama da zallar nono kindirmo bada youghort ba.Sai da Najma ta koma ɗaki ta ɗaura zani akan rigar baccin da ta saka iya guiwa, sannan ta maida ƙaramin hijab ɗin da tafi zama da shi irin wannan lokutan idan ta sanya kayan bacci.Ta fito ta nufi kitchen ta ɗebi fura da nonon,ta yiwa Gwaggo sai da safe da fice zuwa side ɗin Momy ɗin. A falo ta samesu dukkaninsu suna ta hira har Hannah da ta kasa zama a side ɗinta ita kaɗai ta yo nan ɗin.Najma ta yiwa Momy barka da hutawa tare da tambayarta gajiyar hanya,Momy ta amsata da fara'a tana faɗin, "Babu wata gajiya sosai Najma,har kin gama kukan kin dangana?" Najma ta saki murmushi cike da jin kunya ba tare da ta ce komi ba.Furan da nonon Momy ta amsa ta wuce kitchen don damawa Daddy ta kai masa,domin dama abinda take jira Najmar ta kawo kenan.Najma ta samu gefen Nasreen ta zauna tana yiwa Anty Hannah ya gajiya cikin fara'a, ita ma ta amsa da kulawa tana faɗin, "Yau dai na ga garin giwa Najma, amma gaskiya garin baya samun cigaba yadda ya dace.Sam ciyamomin da ke riƙe garin basa yin ayyukan raya ƙasa da ya kamata, amma gari kamar giwa yaci ace ta samu cigaba sosai." Najma da ita ma rashin samun cigaban garin nasu ke damunta, sai tayi saurin gyaɗa kai cike da tarin takaici ta ce, "Bari kawai Anty Hannah, wallahi haka kowa ke wannan ƙorafin.Gaba ɗaya cin kuɗi kawai da gina Iyalansu da haram suka sani, amma sam babu wasu ayyukan raya ƙasa da garin ke samu.Kullum ka shiga garin giwa ba dai kaga wani ci gaban azo a gani ba sai ma koma baya.Gabaki ɗaya babu wani abin nunawa na azo a gani." Najma ta ƙare maganar fuskarta na bayyana takaicinta a fili.Haka suka zauna suna zantawa akan garin giwa da irin cigaban da ya dace ace garin ya samu,Nasreen ta dinga Allah wadai da rashin kishin garin da ciyamomin garin basayi.Nabeelah dake gefe tana karatun wani book na turanci a wayarta,ita ma baki ta sanya tana tsinewa rashin cigaban garin da lalacewar hanyoyi.Suka ɗauki lokaci mai tsayi suna zantawa kafin Hannah tayi musu sai da safe ta janye Nabeelah zuwa side ɗinta don taya ta kwana.Su Najma basu bar falo ba sai wajen 10:30pm bayan Nasreen ta ci abinci mara nauyi kamar yadda ta saba, bata cin abincin dare da wuri.Suna isa ɗakin Nasreen ɗin Najma ta samu saman sofa ta kwanta, ta kunna wayarta tana dialling lambar Inna Karima.Bugu biyu ta jiyo murya Lubah ta ɗauki wayar, cike da murna da sake jin kewar rashin juna suke wayar.Daga ƙarshe tayi sallama da su don har Hanne ta amsa wayar sun yi magana,Najma ta basu sallahun gaida Inna Karima.Alwala ta ɗauro bayan kammala yin wayar, tana fitowa daga toilet ɗin ta zare hijab ɗin da ke jikinta tare da kwance zanin data ɗaura akan rigar baccinta mara nauyi ta nufi bed don kwanciya.Nasreen da zuwa lokacin tana kwance daga gefen gadon tana faman amsa call ɗin Saheeb ɗinta, sai tabi Najma da kallo tana sake yaba kyawun surarta da ya bayyana a cikin rigar baccin. Najma ta shige duvet sabida sanyin AC da ya cika ɗakin yana ratsa fatar jikinta.Bata san lokacin da Nasreen ta kwanta ba, don ita tana kwanciya badajimawa ba bacci ya ɗauke ta. ~*BAƘIN DARE...!*~ Misalin ƙarfe biyu da wasu mintuna na tsakiyar daren,motoci biyu dake ɗauke manyan gawurtattun ƴan fashin suka shigo gate ɗin gidan Alhaji Kabeer Dikko.Mai gadin suka fara gamawa dashi ta hanyar ɗauresa tamau ƙafa da hannu,bayan sun zamge masa baki suka yi jifa dashi a gefe guda.Kusan rabinsu zagaye gidan suka yi baki ɗaya,hannunwansu riƙe da bindigogi da makamai.Yayin da asalin ogan nasu da wasu daga cikin Yaran nasa suka doshi side Gwaggo.Yanayin yadda suka doshi side ɗin kai tsaye zai baka mamaki,domin kamar dama sun san kan komi na gidan ne. Gwaggo da Inna Mairo har ma da Tabawa dake ɗakinta dake daga waje,sun farkane cikin wani firgici da tashin hankalin da basu taɓa riskar rayuwarsu a ciki ba.Tashin farko Gwaggo suka ɗaurewa hannu da ƙafafu,bayan ta sanar musu da inda take aje kuɗi da gwalagwalanta da su Daddy suka siya mata.Ita ma Inna Mairo da aka taso ƙeyarta daga ɗakinta cikin razani da firgicin da ya kusa tsaida bugun numfashinta,ɗaure mata hannu sukai da baki.Tabawa kuwa fitsari ta saki a wando tana faman zare ido tamkar ta shiɗe tsabagen tsoro da firgici.Sai da suka gama operation ɗinsu tas a side ɗin, suka tarwatsa komi na ɗakunan suka kwashi kuɗin duk da ke ɗakin Gwaggo da gwalgwalanta.Sannan ogan ya kwance bakinta dake ɗaure babu halin ihu ko magana,ya nuna ta da bakin bindigar dake hannunsa yana faɗin, "Mai gidan na nan ko?" Gwaggo da duk jikinta ke faman ɓari ta girgiza kai murya na rawa ta ce, "Mu kaɗai ne baya na....." Tsawar da ogan ya daka mata tare da ɗauketa da wani bahagon mari ya sanya Gwaggo tuntsurawa ƙasa tana sakin ihu.Ya ɗaga murya yana faɗin, "Karki raina mana hankali mana, bamu shigo ba sai da muka shirya muka kuma samu bayanan komi a kansa.Don haka maza mu je ku nuna mana asalin side ɗin da yake,domin shi muke da buƙatan gani yau." Gwaggo jiki na rawa ita da Inna Mairo da kanta gabaki ɗaya ya yi mata wani irin nauyi,haka aka tasasu suka fito zuwa side ɗin Daddy.Ta ƙofar shiga falonsa ta waje suka shiga cike da al'ajabin yadda ogan na dafa hannunsa a jikin ƙofa yake buɗewa ba tare da anyi amfani da komi ba.Har cikin ɗakin baccin Alhaji Kabeer Dukku suka tasa Gwaggon kaduna ta kaisu.Daddy da Momy dake manne da juna cikin Duvet suna sharan bacci,sai jin mutane sukai a kansu tamkar almara.Suka tashi a firgice sakamakon buga gadon da ogan ya yi da ƙafansa da ƙarfin gaske, ƙaran ya sanya dukkaninsu farkawa a razane suna yin ido huɗu da mala'ikun duniya.Wani irin frigici ne ya kama zuciyar Momy, ta wani zabura zata ƙwala ihu ogan ya yi saurin ɗaura mata kan bindiga akai yana hanata yi musu ihu.Sai ta sulale ta sakko daga kan gadon dukkanin jikinta na ɓari,gashi rigar bacci ne a jikinta da bashi da wani kaurin kirki.Daddy suka nunawa bindiga tare da sanar dashi cewa kuɗi ko rayuwarsa da ta Iyalinsa.Cikin matuƙar tashin hankali da shiga ruɗu yake roƙonsu karsu kashesa ko taɓa Iyalansa,indai kuɗi ne zasu samu ko nawa suke da buƙata.Ogan ya jinjina kai yana yima ɗaya daga cikin Yaransa magana akan ya fara da kashe dukkanin wayoyin su Daddyn,kafin su tasa ƙeyar Momy suna bata umurnin nuna musu sauran ɗakunan da ke side ɗin.Bayan sun gama da side ɗin Daddy ne, ogan ya taso su shi da Gwaggo da Inna Mairo zuwa babban falon gidan ya yi wurgi dashi a tsakar falon.Yana dubansa Yaransa yake basu umurnin shiga sauran ɗakunan suyi operation tare da fiddo ko su wayema a cikin ɗakunan.Inna Mairo da Daddy ji suke yi tamkar su haɗiyi zuciya,domin basu taɓa riskar tashin hankalin gamo da marasa imanin mutane irin waɗannan ba.Lokacin da aka taso ƙeyarsu Najma da Nasreen zuwa falon ne,hankalin Inna Mairo ya sake tashi sakamakon ganin yadda aka fito dasu cikin shigan da bai gama rufe tsiraicinsu ba.Don rigunan bacci ne a jikinsu waɗanda sam ba masu kauri bane na shan iska ne.Daga Najma har Nasreen ihu suke son yi amma an rufe bakunansu babu halin yin hakan,sai mazari kawai jikinsu keyi na tsabagen shiga tashin hankali. Ogan ya juyo ya sauke idanunsa akan su Najma yana waiwayawa ya dubi su Daddy ya ce, "Dama akwai ƴan mata a gidannan?" Daddy ya gyaɗa kai mummunan tashin hankali na bayyana a kan fuskarsa.Momy da aka taso ƙeyarta daga ɗakinta zuwa falon,bayan an gama yashe duk wani kuɗi da kadaransu na gwal da suke saye ita da Yaranta su Nasreen.Ta ƙariso cikin falon mummunan faɗuwar gaba na riskarta,domin tayi ta addu'ar kada Allah ya basu ikon shiga ɓangaren Yaran ashe har sun shiga sun fiddo mata su. Idanunsa ogan ya sauke akan Najma wacce ke dab da shiɗewa tsabagen yadda take cikin firgicin ganin waɗannan mutane da ake kira da mala'ikun duniya a gabanta.Wani irin kallo yake bin ta dashi daga sama har ƙasa, kafin ya ɗauke ganinsa a kanta ya mayar kan Daddy da hankalinsa yafi na kowa tashi a wajen ya ce, "Ranka ya daɗe naga kayan marmari mai ƙayatarwa a gidanka,don haka zan ɗan huta da ita kaɗan daga ciki." Ya ɗauke ganinsa akan Daddy ya mayar kan ɗaya daga cikin Yaransa da suka taso ƙeyar su Najma ya ce, "Shiga min da wannan black beauty ɗin kayan daga ciki." Yaran nasa ya janye Najma zuwa ciki tana wani irin fisga tamkar zata shiɗe.Nasreen da Gwaggo da Momy tare da Inna Mairo ma dukkaninsu jikinsu ya ɗauki rawa,bakunansu na son fasa ihu amma babu halin hakan don bakin a ɗaure yake.Ga kuma ƙattin da ke tsare dasu da bindigogi a hannunsu.A kan idanunsu ogan ya bi bayansu Najma zuwa ɗakin baccin Nasreen, aka yada ita bisa bed ɗin daidai da shigowar ƙaton mutumin da idanunsa ke rufe da baƙin masks ƙwayar idon kawai ake iya gani jajir a waje. Daga can falo Daddy Kabeer Dukku ne ke ji tamkar ransa zai fita sabida shiga tashin hankali,don bai taɓa ganin tashin hankali makamancin wannan da yake ciki a rayuwarsa ba.Ihun da Najma da tayi lokacin da yake cin galabar shiga mutuncinta,shi ne ya janyo hankalin Inna zuwa ga sulalewa ta sume gau a wajen.Momy da Nasreen ma sumewar sukai sabida yadda ihun Najma da aka kwancewa baki don sai da ya tsotse saƙo da lungun bakinta tas da salon kiss ɗinsa.Alhaji Kabeer Dukku tare da Gwaggo da tayi suman zaune bata gane komi a lokacin, sai ihun Najma da ke cika kunnuwanta yana mata amsa kuwwa.Sun kasa komi sai uban hawaye dake tsere akan fuskarsu,don babu halin kuka da sauti.Tsayin lokaci suka ji ta tsaya da yin ihun da take yi, sai ga mutumin ya fito daga ɗakin yana gyara zaman wandonsa.Fuskarsa na fidda wani irin murmushi,wanda ya sanya zuciyar Gwaggo sake shiga ƙunci.Ya taka zuwa gaban Daddy yana kai hannu ya fincike abinda aka ɗaure bakinsa da shi.Kamar jira Daddy yake yi ya saki wani irin kuka mai cin rai tamkar ƙaramin Yaron goye, domin tunda ya tabbatar an ɓata rayuwar Najma yaji komi ya kwance masa.Ogan ya kai hannu ya shafa kansa tare yi masa alamu da ya yi shiru.Ya buɗe baki cikin gadara ya ce, "Bar kuka Alhaji banyi ban ruwa a cikin gonarta ba, daga waje na zubda ruwan.Don haka bana tunanin ko mun tafi zan bar baya da ƙura,abinda kawai zaku yi ku kaita asibiti a ɗinketa da safe domin nayi ɓarna don taƙi bani haɗin kai.Tana da matuƙar daɗin da ban taɓa jin irinsa ba,da ƙyar na iya barinta ba don na gamsu ba." Ya kai ƙarshen maganar yana ɗane bakin Daddy da ya kasa cewa komi sai rawar baki yake,hawayen zallar baƙin ciki da takaici na cin zuciyarsa. Uku da mintuna kusan arba'in suka gama operation ɗinsu suka bar gidan,bayan sun kwance ɗaurin da sukaiwa hannu da ƙafafun Daddy.Jikinsa na wani irin rawa ya nufi Gwaggo ya kwance hannayenta dake zamge da bakinta,suka kwasa a guje zuwa ɗakinsu Nasreen ba tare da sun bi takan Momy da Nasreen da ke yashe a sume a tsakar ɗakin ba. Wani mugun jiri ne ya ɗebi Gwaggon kaduna lokacin da idanunta suka sauka akan Najma dake yashe daga ƙasan bed ɗinsu.Rigar jikinta a yage ana ganin tsayayyun ƙirjinta da suka sha matsa a hannun ɗan fashin,ga gabanta da ya yi face-face da jini,gefe guda ƙazantar da ya fitar ne daga gefe kamar yadda ya faɗi da bakinsa bai yi ban ruwa a cikin gonarta ba.A hankali ƙafafun Gwaggo suka murɗe,ta silale ƙasa tana sakin wani shegen kuka mai razanarwa.Daddy ma kallo ɗaya ya yiwa inda Najma ke kwance ya fice a guje yana kuka kamar ƙaramin Yaro.A falo yaja birki yana nufan wajen da su Momy ke yashe ya kwance musu ɗaurin da akai wa baki da hannuwansu.Ya nufi side ɗin masu aiki da nan ne kaɗai basu shiga ba ƴan fashin, ya samesu sunyi carko carko suna ɓarin jiki.Don tun shigowar Ƴan fashin side ɗin suka farka, tsananin tsoro ne ya hanasu yin ko wani irin motsi ko ihun da za a san dasu a wajen.Cikin wani irin tsawa Daddy ke basu umurnin kawo ruwa da gaggawa zuwa falon don kwarawa su Momy ko zasu dawo hayyacinsu.Rabi ce ta fito a guje riƙe da sassanyar ruwan gora ta nufi wajen da su Momy ke yashe,ta ɓalle bakin goran ta kwara musu ruwan a jiki da fuskarsu. Suka kawo numfashi kusan a tare,suna tashi zaune jikinsu babu inda baya ɓari.bin kowa da komi suke yi cikin son tantance daga mafarki suka farko ko kuwa? Sai dai daga sanda idanunsu ya sauka akan Daddy dake zaune bisa sofa,ya dafe kansa da hannu bibbiyu yana kuka tamkar ƙaramin Yaro suka gane cewa ba daga mafarki suka farkaba.Nasreen ta miƙe a guje ta nufi ɗakinsu zuciyarta na bugawa da wani tashin hankali da tsoro da firgici mai tarin yawa.Tana yin ido huɗu da Najma da Gwaggo dake kuka wiwi ta saki wani razanan ihun da ya kawo Momy a guje zuwa cikin ɗakin.Ita ma kallo ɗaya ta yiwa Najma da halin da take ciki ta sake wani irin ihu tana dafe kanta da hannuwa bibbiyu.Ya tabbata dai ɗan fashinnan yaci galaban yin raping Najma,irin raping ɗin da dole a tausayawa wanda aka yiwa shi.A hankali Momy ta isa wajen da Najma ke yashe babu alamun numfashi a tattare da ita, ta janyo duvet ta rufa mata a jiki.Cikin muryar kuka ta bai wa Nasreen umurnin kawo ruwa,Nasreen da jikinta ke rawa tana zuba wani irin kuka mai cin rai ta nufi falo a guje tana sake sakin gunjin kuka. Da ƙyar Najma ta kawo numfashi tana buɗe idanunta akan Momy,ta saki wani irin ihu tana jijjiga kanta tamkar a lokacin abin ke faruwa.Ta motsa ƙafarta tana jin wani azaba na ratsa cinyoyinta zuwa ƙasanta da take jin tamkar ba a jikinta yake ba.Take komi da ya faru ya sake dawowa kwanyarta,wani irin tashin hankali da ƙunci da bata taɓa sanin akwai irinsa ba ya dinga rufe zuciyarta.Kiran sunan Inna Mairo ta dinga yi tana wani irin jijjiga tamkar numfashinta zai sake barin gangar jikinta.Inna Mairo da ke kwance warwas a falo bayan farfaɗowarta, sam ta kasa motsawa sai zuciyarta da ke mata wani irin zafi,kanta na sake yi mata nauyi da wani irin ciwo mara misaltuwa. Ihun Najma da ta sake jiyowa ya sanya numfashinta sake barin gangar jikinta,ta sake somewa take don zuciyarta ba za ta iya ɗaukar baƙin cikin da ke tunkaro rayuwarta da ta tilon ƴarta ba.Daddy ya nufi kanta yana kuka sosai,irin kukan da ke bayyana halin ƙaƙanikayin da bawa ke ciki.Wayoyinsa ya tuna dasu,sai ya miƙe a guje ya nufi side ɗinsa.A kan table ya hango laf wayoyinsu babu wanda suka tafi dashi, domin sun samu kuɗi da kadaran gwalagwalan da ba za su yi wahalar ɗaukar waya ta zame musu kaya ko hanyar tonuwar asirinsu wajen sanyawa ayi tracking nasu ba.Ɗaukar wayarsa ya yi ya kunna cikin rawar jiki,yana mai fara laluban lambar doctor Bakory.Bugu biyu ya ɗauka cikin alhinin ganin kira da sassafe daga Daddy ɗin,cikin rawar murya Daddy ke roƙonsa alfarman yazo gidansa don bada taimakon gaggawa ga Iyalinsa,bayan ya sanar dashi dukkanin abinda ke faruwa.Ya kashe wayar bayan doctor Bakory ya bashi tabbacin gashinan bisa hanya nan da ɗan wani lokaci. Falon ya koma wajen Inna Mairo yana ƙoƙarin ganin numfashinta ya dawo amma bai yi nasara ba.Momy ita ma daga can ɗakin su Nasreen ƙoƙarin sake dawo da numfashin Najma da ya sake ɗaukewa suke yi amma abin ya faskara.Hakan ya sake jefa Nasreen cikin halin tashin hankali,tana ji dukkanin duniya na tsaya mata cak! Ta ɗakko wayarta da ke yashe a kashe bisa kan tiles ta kunna,tana mai jin relief da basu tafi da wayoyin kowa daga cikonsu ba.Layin Nabeelah ta soma kira,waɗanda su kaɗai ne suka tsira daga riskar wannan mummunan tashin hankalin.Domin sam ƴan fashin Allah bai basu ikon shiga side ɗin Yaya AD ɗin ba,don ga dukkanin alamu kamar suna tare da wani wanda ya san kan gidan da kuma mutanen da ke rayuwa a kowane ɓangare na cinkinsa ne.Basu ɗauka cewa akwai mutane a side ɗin ba tabbas da sai sun kai ziyara har nan ɗin.Bugu uku Nabeey ta ɗaga wayar cikin mayen bacci,Nasreen tayi saurin sake mata kuka tana sanar da ita mummunan yanayin da suke ciki.Bata bai wa Nabeelah damar magana ba ta kashe wayar, tana sake rushewa da kuka mai cin rai. Nabeey ta tashi Anty Hannah a firgice tana sanar da ita abinda Nasreen ta gaya mata,sai ta tashi a firgice tana ware ido da maimaita kalmar ƴan fashi da kuma raping a bakinta.Dukkaninsu cikin tashin hankali suka fito daga side ɗin nasu don isa nasu Momy.Suna fito wajen compound ɗin motar doctor Bakory na shigowa ciki.Bai yi mamakin ganin gate a wangale ba,domin Daddy ya sanar dashi komi a waya.Ya fito a gaggauce yana nufan wajen da Mai gadi ke yashe yana rawar jiki baki da hannuwansa a ƙulle.Ya kwancesa yana nufan cikin gidan a gaggauce,domin bada taimakon gaggawa ga wacce aka yiwa raping da kuma Inna Mairo da itama bata san inda kanta yake ba.Kusan a tare suka iso cikin falon tare dasu Nabeey,suka nema waje suka yi carko-carko suna kallon yadda Daddy ya fita a hayyacinsa tsabagen tashin hankali da ɓakin da yake ciki.Ɗakin su Nasreen suke shirin nufa amma sai Daddy ya dakatar dasu,suka dawo da baya suka tsaya akan Inna Mairo.Shi kuma ya yiwa doctor Bakory jagora zuwa ɗakin Nasreen ɗin.Basu jima da shiga ba su Gwaggo da Momy suka fito suna kuka wiwi na tausayin halin mummunar ƙaddarar data afkawa rayuwar Najma a dare ɗaya. Gwaggo ta nufi wajen da Inna Mairo ke yashe babu numfashi, ta fasa wani irin ihun tana jijjigata da kiran sunanta cikin ɗimuwa da tashin hankalin da bazai misaltu ba.Nasreen ma wajen Anty Hannah da Nabeey ta nufa tana wani irin kuka mai ɗaga hankali.Bakinta na faman furta, "Yayi raping ɗinta,wallahi ya yi raping ɗinta Anty Hannah!" Ta ƙare maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.Hakan ya sanya Nabeey durƙushewa ta saki wani irin kuka itama mai cin rai.Hannah ma jikinta rawa kawai yake yi, tana jin wani irin tausayi da tashin hankalin ƙaddarar da ya dirarwa kyakykyawar budurwa kamar Najma na ɗaga hankalinta.Suka rintse idanunsu baki ɗaya suna sake sakin kuka a tare, lokacin da kunnuwansu ya jiyo musu wani razananniyar ihun da Najma ta saki. Daddy ya fara futowa daga ɗakin yana sharan hawayen da suka kasa tsaya masa.Ya yiwa su Momy duba ɗaya yana yafutota da hannu alamun tabi bayansa zuwa ɓangarensa,hakan ya sanya ta miƙe jiri na ɗibarta ta rufa masa baya.Ta bar su Nasreen na cigaba da rasgar kuka,kowanne a cikinsu na cike da alhini mai yawa a zciyarsa.Lokaci kaɗan Daddy da Momy suka fito cikin shirin fita,Momy na sanye da hijab dogo har ƙasa.Ta dubi Anty Hannah ta ce, "Hannatu zaki zauna anan mu je asibiti mu dawo,don daga Inna har Najma dole su samu kyakykyawar kulawa daga wajen likitoci." Daga haka suka nufi ɗakin Nasreen don ganin halin da Najam ke ciki, wacce ta farfaɗo amma kuma ta sake sumewa lokacin da doctor Bakori ke ƙoƙarin duban wajen da kyau.Momy na shigowa doctor Bakory ya sanar mata dole sai an yiwa Najma ɗinki.Nasreen ce ta shigo ta roƙi Daddy cewa zata bisu, sai ya amince don hankalinta ya kwanta.Daddy ne ya saɓa Najma a kafaɗarsa zuwa mota,Inna Mairo ma doctor Bakory ne ya saɓota zuwa mota da ƙyar, don tana da ɗan jiki da nauyi. Daga Anty Hannah sai Nabeey dasu Rabi mai aiki da Tabawa aka bari carko-carko a side ɗinsu Momyn.Don Gwaggo ma bin su Daddy tayi zuwa asibitin domin ta ce ba za ta taɓa iya zama a gida ba Sun bar gidan bada jimawa ba aka fara kiran sallar asuba, hakan ya sanya su Rabi da Tabawa suka kama gabansu zuwa side ɗinsu Rabi don gabatar da sallah.Anty Hannah da Nabeey ma sai suka nufi ɗakin Momy,suna shiga suka tadda yadda akai batsa-batsa da ko'ina na ɗakin.........✍🏻 _Allah sarki baiwar Allah Najma! Ko ya rayuwarta za ta kaya cikin wannan mummunar ƙaddaran da ya afkawa rayuwarta?_ *Masu karatu duka anan na kawo ƙarshen free pages na NUFIN ALLAH...! Ga masu buƙatar karanta cikakken labarin domin jin ya rayuwar Najma za ta kasance? Sai ku zargayo don biyan kuɗinku domin karanta cikakken labarin,wanda zai zo muku da sabon salo mai taɓa zuciya haɗi da zazzafar soyayyar mai tsayawa a zuci.....! Yanzu ne labarin zai fara don kuwa yanzu zamu tsundima cikin labarin ka'in da na'in.Domin jin wace wainar za a toya? Wane ne gwarzon da zai samu nasarar aure Ƴar mutan giwa? Ya rayuwar auren Hannah da AD Dukku zai kaya? Shin auren zai ɗore ko kuwa rabuwa ce daga ƙarshe? Duka amsar na tare da ƴar mutan Zazzau! Don haka karku bari a baku labari.....!* ``` _NUFIN ALLAH....! Yazo da sabon salon da ya fi TAIMIYYAH taɓa zuciya,ga kuma tarin faɗakarwa tare da nuna muhimmancin yadda da ƙaddara...!_ ``` *Pay 500 in to this account number👇🏻* *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *OR* *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* *ACCOUNT NAME:OPAY* *Evidence of payment to this number:08167768704* 🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* *MTN* *GLO* *AIRTEL* *9MOBILE* *MONTHLY VADILITY 💃🏻* *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻 _Ina maraba da masu son a tallata musu hajarsu akan farashi sauƙi......!_ #Lovestory# #Najma# #Aysha Ɗansabo Lemu🥰 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels