An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 *_💋 TRIPLETS 💋_*      *_( ROMEO )_* *Story & Written*            ⬇️      *Star Lady* The writer of *DUK KARFIN IZZATA*     And now *_💋 TRIPLETS 💋_*             *_( ROMEO )_* _Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu masoyana masoyan *DUK KARFIN IZZATA* masoyan Hiyana da Brigadier general Safras ina muku fatan alkhari da godiya mai tarin yawa ba zan taɓa mantawa da kuba har kullun kuna rai na ya Allah ya tsaremin ku daga sharrin duk wani abun halitta_. Da farko dai wanna littafi book 1 sadaukarwa ne ga My dear Amira My sister kuma my P.A😹ina kaunar ki lodi lodi 🥰 BOSS BATURE!!!much kauna 💖 masoyiya munarh much love ❤️ Kamar Yadda na fara littafin nan lafiya ina rokon Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon Kammala shi lafiya Allah ya bani ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abunda bazai amfani al'ummar Annabi ba. 🤲Ya Allah ina rokon da ka tsaremum alkalami na daga rubuta abun da zai lalata tarbiyyar ƴa'ƴan mutane Allah ka bani ikon isar da sakon da nake son isar wa *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a haɗamun document ko amin Edit Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ San nan ina jiran daɗaɗan comments naku masu karamin karfin gwiwa ta hanyar daddaɗar comments naku ne zan iya gane ya kuka ɗauki littfin Ina godiya Allah ya bar zumunci 🥰 Share fisabilillah👏👏 Mai neman karin bayani ya min magana ta wan nan number 09162620621 or 09075846926 Please iya WhatsApp ban da kira 💋THE BEGINNING 💋 Let's get started Episode 1 KATSINA STATE Unguwar farin yaro Misalin karfe 4 na yamma anguwar tayi shiru babu wani motsin kirki kyakkyawar yarinya ce Chocolate colour doguwa tana da kyakkyawar fiska ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da dogon kyakkyawar hanci mai tsini har baka ga manya manyan dara daran idon ta masu design na kifi farare ne tas kamar madara masu ɗauke da dogayen gashin ido kamar wadda tasa eyelashes bakin ta ɗan karami dai dai da face nata lallausan laɓɓan ta launin pink color, lips nata nasama design of heart ne tana da baƙi lallausan saje kwance a gefen lalausan kumatun ta lallausan kwantaccen bakin gashi siɗif a goshin ta kamar na larabawa tana da gogayen yatsun kafa masu ɗauke da kunba (farce) farare tas kamar madara sanye take cikin blouse gown pink color mai bala'i kyau ta sanya ɗan karamin hijabi baki a kanta a shekaru bazata wuci 13 years ba kallon ɗaya zaka mata ka san tafito daga gidan hutu da jin daɗi amma sai dai ga fuskar ta ɗauke da bushesshen hawaye alamar tasha kuka. Rike dake da matches (ashana) a hannun ta kyakkyawar kafar ta na sanye cikin kyakkyawar flat shoe baki kalan hijabin ta kyakkyawar gaske ce dan idan nace zan tsaya zayyana muku kyan yarinyar nan to sai mu kwana mu wuni bamu gama ba dan ta ko ina ta haɗu. Sauka tayi daga kan titin da take tafiya ta keta ta cikin wani lungu taci gaba da tafiya tana tangal tangal alamar ta gaji. Dai dai zata shiga wani kwana wani matashin saurayi yace "Jimana ƴanmata" Juyowa tayi tana kallon sa zaune yake cikin motar sa kofar motar a buɗe ya zuro kafafunsa waje, Ji tayi kamar kar taje sai kuma ta tuna da zancen mum ɗin ta in da take cewa "Ba kyau wulakan ta ɗan adam dan baka san in da zaka haɗu da shi gaba ba" tuna hakan ya sanya ta nufesa tana ɗaure fuska. Da ga ɗan baya ta tsaya da zazzakar voice nata tace "Gani nan" tayi maganar rai a ɓace fitowa yayi daga cikin motar ya juya gabas ya juya yamma lungun babu kowa shiru cikin sauri ya zaro handkerchief daga aljihun sa ya kaɗa mata a fuska, nan take ta yake jiki zata faɗi cikin zafin nama ya taro ta ya turata cikin mota gidan baya, ya shiga gidan gaba ya tada motar da gudun gaske ya fito daga lungun ya miƙi hanyan. Gudu yake zubawa sosai kamar zai tashi sama yara uku ne a cikin bayan motar da ita 4 dukkan su a sume kuma dukkan su mata ne. Agogon Nigeria karfe 4:30pm ta buga. Gidane ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da ɗan ƙaramin kofar shigowa, bazaka kira gidan da gidan talakawa ba haka zalika bazaka kirashi da gidan masu kuɗi ba, za dai a sashi a layin gidan masu rufin asiri sai dai duk anguwar gidan tafi kyan gani da tsari da fasali. Ɗakuna biyu ne a cikin gidan sai yar karamar kitchen dake tsakar gidan ta ɓangaren hagu, daga gefen dama kuwa toilet ne awajen, gidan yana da ɗan filin tsakar gida mai ɗan girma. Kyakkyawar mace ce zaune a tsakar gidan saman tabarma, kallo ɗaya zaka mata kaga jikin hutu ta mike kafa tana tsintar shinkafa a bai bai kana kallon yadda take tsintar shinƙafar kasan bata iya ba sanye take cikin dankareriyar lace baki mai ratsin ja hannun ta da wuyar ta sanye suke da sarkan gold mai matukar kyau da tsada farace tas kyakkyawa ajin farko, cikin sanyin murya ta ɗago kai tace"Jehan!! Jehan!!!"daga cikin ɗaki wata zazzakar murya ta amsa da "na'am Mum" "Kizo ki je ki dubamin Rimsha tun ɗazun da ta fita siyo matches bata dawo ba kin san dama ba wani sanin hanya sosai tayi ba, kiyi sauri dan mu samu mu ɗaura girkin nan yamma tayi sosai" "Mum ni gaskiya na gaji shekaran jiya fa tare da ita mukaje shagon na nuna mata hanya ba daman kince tafini ƙwaƙwalwa ba to sai ta gane hanya da kan ta ba sai na nemota ba ta dawo gida" tayi maganar cikin harshen turanci ta kai karshen maganar tare da fitowa waje daga cikin ɗakin. ```Jehan``` Kyakkyawa ce ajin farko farace tas doguwa mai kyakkyawar fuska dake ɗauke da dogon hanci har baka ga manya manyan idanun ta masu design na kifi farare tas kamar madara gashin idon ta dogaye a tsai tsaye bakin ta ɗan ma dai dai ci tana da lallausan laɓɓa pink color,sanye take cikin blouse gown pink color kanta ba ɗankwali ta zubo gashi har baya bakin kirin mai tsantsi da laushi an mata kananan kalba a kan nata a karshen kitson an sanya mata bit manya manya kowani kitso ɗaya bit uku aka sa idon ta abushe yake bata da tsoro ko kaɗan a shekaru ba zata wuce 15 years ba. Jehan yarinyace shagwaɓaɓɓiya a jin farko ga rashin tsoro iyayi rashin kunya rashin ji izza ba'a mata ta kyale rashin hakuri saurin fushi rashin son mutane. ***** "Ina ɗankwalin ki Jehan?" Cewar mum tayi maganar da ɗan karfi, turo baki Jehan tayi cikin shagwaɓa tace "Mum nifa nagaji da sanya ɗankwalin nan ni yanzu ma Mum fruits nake son sha" tayi maganar da harshen turanci "Jehan!! Jehan!!! Saunawa na kira sunan ki? Ki wuce kije ki sanya hijabi kije ki nemomin Rimsha kin san yarinyar nan ba in da ta sani tun da muka dawo nan bata taɓa fita ba sai shekaran jiya idan kika bari na mike Allah sai jikin ki ya gaya miki" "Kai Mum ni wlh kin takuramin yanzu fa mun kai 5 days da zuwa garin nan idan ma ban da dakikanci irin na Rimsha ko ba'a taɓa nuna miki waje ba ba zakije ki dawo ba bare mun taɓa zuwa to ni waye ma ya nunamin ba da kai na naje ba?" tayi maganar cikin kwaɓaɓɓiyar Hausar ta, Shiru Mum tayi bata sake cewa komai ba, ita kuwa Jehan waje ta samu saman dakalin soak away dake kusa da windon toilet ɗin ɗakinta ta zauna tana tura baki. Wata kyakkyawar farar mata ce mai ɗan kiba ta fito daga cikin ɗaya ɗakin tana faɗin "Haba Jehan ɗin daddy yi hakuri kije ki dubo yar uwarki kinji idan ta ɓata fa? Ya zaki yi?" Tsaki Jehan taja kafin tace "Goggo ni fa I can't go anywhere ta ɓata mana ni ina ruwana da ita? Please Mum let's go back to our real house I don't like this house it's too local, I want to see my dad I miss him" Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi ɗaki tana faɗin "Tunda kun dame ni na shige ɗaki" kallon mum goggo tayi, yayin da mum ta ɗaure fuska tana zancen zuci "Koma me Jehan tayi baku kuka batata ba baku kuka mai data hakan ba" wucewa goggo tayi tabi bayan Jehan dan taje ta rarrashe ta miƙewa Mum tayi ta nufi kitchen tare da shinkafar da take tsinta. Shiru shiru har karfe 6 na yamma gari ya fara duhu Rimsha bata dawo ba Mum ta fara tsorata ta ɗauko mayafinta ta fito wajen gidan dan ta dubo Rimsha kallon gabas tayi ta kalli yamma ita kan ta bata san ko ina ba a unguwar dan tun da suka zo bata leka ko kofar gida ba. A hankali ta zuro kafafunta ta fara takawa ta rasa ina zata bi Jehan ce kawai ta san unguwar chan ta hango majalisan samari suna zaune suna hira cikin sauri ta karisa wajen tare da yi musu sallama, cikin fara'a uku daga cikin su suka amsa mata Sallamar har suna haɗa baki, sauran ukun kuma fiska a ɗaure "Dan Allah bayin Allah baku ga ƴata ba wallahi tun ɗazun na aiketa siyo ashana shiru shiru har yanzu kuma bata dawo ba mu sabbin zuwa garin ne batasan ko ina ba sai shagon shima sau ɗaya ta taɓa zuwa" ɗaya daga cikin sune ya miƙe yana faɗin "Kai subhanallah yadda siyasa ta gabato dinnan satar yara ake sosai kamar me ya Allah yasa ba gaba da ita akayi ba bari mu duba miki ita Mama ya take yarinyar ina nufin tsawon ta da kalar kayan da tasa tayu ko ta ɓata hanyane tun da sabon zuwa garin ne ku" da sauri Mum tace "Chocolate color ce shakarun ta 13 tana sanye cikin dogon riga pink color da karamin hijabi baki sunan ta Rimsha" "Yusuf, Sha'aban kuzo mu rabu mu duba ta ko Allah zai sa mu ganta Mama ke kuma ki koma gida idan mum ganta zamu kawota har gida kinji?" Mum bata da zaɓi dan in tace ba zata koma gida ba bata san ko ina ba bata san ta ina zata fara neman Rimsha ba dole tabi maganar Sadiq hakan yasa ta gyaɗa masa kai ala'mar to sanna ta wuce jiki ba kwari ta nufi gida zuba mata ido Sadiq yayi har sai da ya ga gidan da ta shiga sanna yace "Sha'aban Yusuf muje mu duba mata ƴar nata mana" a tare Sha'aban da Yusuf suka mike kallon sauran Sadiq yayi yana faɗin "Hafeez kufa muje mana me kuke jira" a gatsale Hafeez yace "babu in da zamuje gayyan soɗi neman gindin zama daga ganin baki har ka fara shishshige musu to dai kabi a hankali dan da ganin matar nan wlh batayi kama da talaka ba me ya kawota anguwar talakawa?" Shiru Sadiq ya yi bai sake magana ba ya wuce tare da Sha'aban da Yusuf suka kutsa cikin anguwar neman Rimsha. Lokacin da Mum ta koma gida an fara kiraye kirayen Sallar Mangariba, a tsakar gida ta isko Jehan da goggo suna zaune wuce su tayi zata shiga ɗaki goggo tayi saurin cewa "Maryam lafiya ina Rimsha ɗin take?" Mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "Mum I'm feeling hungry I want to eat something very soft" Kallon Goggo mum tayi kafin tace "Aunty Aisha ya kamata ki sanar da Jehan yanzu fa mum shiga halin rayuwa ko mutuwa ne dan na lura tafi jin maganar ki batun Rimsha kuma bamu ganta ba yaran unguwar nan sun fita tayani neman ta" kallon Goggo Jehan tayi dan ita ba wani jin Hausa sosai take ba iya mum ce ka ɗai ke musu magana da Hausa sai kuma goggo da take musu kaɗan kaɗan time to time Daddyn su turanci da Larabci kawai yake musu" goggo where is Rimsha? I'm seeing like Mummy is not happy why is she talking like this everyday she's shouting and abusing me?" "Jehan you have to be very very careful now kina jina? Our life now and before is very very different" cewar goggo shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "okey na gane kaɗan now ina Rimsha take nake son sani kafin na tambayi Daddy" Hararar wasa Goggo ta mata kafin tace "Ba tun ɗazun akace kije ki nemo taba kika ki maybe ta ɓata hanya ne" Mikewa Jehan tayi ta nufi waje tana faɗin "Bari nayi checking nata mu gani ko zan ganta amma fa sai ta sha very very good slap idan na ganta dan ta ɓatan rai" ita dai Goggo bin ta da ido kawai tayi har ta fice. Tana fita sukayi karo da su Sadiq suna kokarin shiga gidan "Who are those peoples kuma?" ta tambayi kan ta tare da ruke haɓa da hannu ɗaya ta tsaya a bakin kofar shigowa ta tare musu hanya, cikin nitsuwa sadiq yace "Sannun ki bari mu wuce" a wulakan ce ta masa kallon uku goma kafin tace "From where to where?" kallon su Sha'aban dake bayan sa yayi san nan ya dawo da kallon sa kan Jehan dake tsaye ta rike kugu tana musu kallon banza "Yi hakuri ni bana jin turanci kiyi magana da Hausa" cewar Sadiq dogon tsaki taja kafin tace "daga ina? kuma ina zaku je?" tayi Hausar a kwaɓe kallon ta Sadiq yake a ransa yana mai mai ta yadda ta kwaɓa hausar wai ita a dole tayi magana "wajen mamanki muka zo" cewar Yusuf, kallon wulakanci ta masa kafin ta musu nuni da hanyar komawa da hannu ta a wulakance tace "Ku wuce ku bani waje wasu dirty Boyz daku ne zakuce wajen Mum kuka zo to Mum ta muku me please leave this place before I open my eyes" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki tana tofar da yawu. Har ga Allah yadda take magana ba karamin tafiya da Imanin Sadiq tayi ba dan shi a rayuwar sa yana son mace mai izza tana burge shi sosai. ```Sadiq``` Sadiq matashin ne mai jini a jiki wadda ba zai wuce shakara 24 ba ba laifi yana da kyau dai dai gorgodo yana da hali mai kyau baki ne amma irin bakin nan mai shegen kyau yana da ɗan ma dai dai cin hanci da manya manyan ido Fusata iya fusata Yusuf ya fusata da abun da Jehan ta musu yarinya yar karama zata tsaya tana faɗa musu magana cikin kunan rai yace "Yaya Sadiq muje dan Allah idan ba haka ba zan iya sumar da yarinyar nan" kallon banza Jehan ta watsawa Yusuf ba tare da tayi magana ba, juyawa Sadiq yayi yana kokarin yin magana, Mum ta fito dan duba su tun da taji shiru shiru gashi har an gama sallar mangariba, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan sunkuyar da kan sa kasa dan tun da yaga Jehan ya ji ya fara jin kunyar mum "Mama wallahi mun duba bamu ga yarinyar nan ba" Salati Mum tasa tana kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "They are lying Mum ina zata je da za suce basu gan taba" Yusuf ji yake kamar ya kwashe ta da mari dan haushi ita kuwa sai kallon rai ni take musu ko shakkan su babu a idon ta bare tsoro "Bayin Allah ina ne police station na ku bari na kai Report tun wuri, cikin nitsuwa da girmamawa Sadiq yace "Mama kiyi hakuri zuwa da safe sai muje amma da zakiji shawara ta da baki je police station ba dan last 2 weeks aka sace wata yarinya a nan kin san zaɓe ya kusa haka iyayen ta sukayi ta yawon zuwa police station ƴan sanda suna anshe musu kuɗi basa masu aiki kin dai san yadda kasan nan ya zama yanzu sai a hankali ba talakawan ba ba masu kuɗin ba kowa baya son gaskiya mafi yawancin su kan su kawai suka sani amai ma kon ki kwashi kuɗi ki kai wa yan sanda gwara ki ɗau kuɗin ki kai masallaci a sayi buta ayi sallah ayiwa yar ki addu'a sanna ki biya kuɗi a miki saukan Qur'ani mai girma dan Allah shi ka ɗai ne mafita, a yan kwana kin nan an sace yara zasu kai 3 a layin nan" Jin haka yasa hankalin Mum ya kara tashi sosai dan atunanin ta Rimsha sai dai ta kauce hanyar gida ta sauya hanya bata taɓa tunanin za'a iya sace ta ba amma jin bayanan Sadiq yasa hankalin ta yayi mugun tashi cikin ruɗu da fargaban in da Rimsha take tace "Yaro muje yanzu nan afara yi mata addu'a ka kai ni in da malaman ku suke mu baki ne a garin nan bamu san kowa ba" "Mama ki bari sai da safe mu kara dubata zuwa azahar tun da ku baki ne tayu ba sace ta akayi ba ɓata hanya tayi idan mun dubata gobe zuwa azahar bamu ganta ba sai mu fara rabawa malamai kuɗi su fara addu'a" shiru Mum tayi kamar mai tunani zafafan hawaye ne suka fara bin kuncin ta da yake wajen ya fara duhun mangariba su Sadiq basu lura da hawayen da take ba, ita dai Jehan sai kallon ban za take musu a duhu tana yamutse fuska tare da ɗage dogon hanci tan nan dan bata gane abubuwan da su Sadiq ke tattaunawa da Mum ba dan ba wani jin Hausar kirki take ba sama sama ta iya shi ma sai idan ita tayi kayan ta take gane me take faɗe idan Hausa ta wuce zo tafi zauna ina zuwa zansha ruwa da sauran kananan word to ba wani ganewa take ba. Da kyar mum ta iya cewa Sadiq "Bawan Allah ya sunan ka? kuma inane gidan ku dan gobe nazo muje neman nata tare" Murmushi Sadiq sarkin murmushi yayi kafin yace "Ga gidan mu can mai kofar kwanon nan sunana Sadiq wayan nan biyun kanne nane Yusuf da Sha'aban Yusuf Maman mu ɗaya Sha'aban kuma ɗan kanin Baban mu ne" "Na gode kwarai da gaske Babana dan sunan babana gare ka Allah ya biyaku da gidan Aljanna" murmushi Sadiq yayi yana faɗin "Ba komai Mama sai da safe" ya kai karshen maganar tare da juyawa suka bar wajen, Hannun Jehan Mum ta riko dan su koma cikin gida "Where are we going mum?" harara cikin duhu Mum ta wurga mata kafin tace "cikin gida" "Mum which kind cikin gida kuma? Where is Rimsha what about her?" Shiru Mum tayi dan bakin ciki ji take kamar ta wanke Jehan da mari haka Allah ya kaddara amma ko mai ya faru Jehan da Goggo ne sila "Mum please talk to me now" "Jehan wallahi ki fita ido na idan zaki rabu da wanna shegiyar yaren turawan ki kama Hausa gara miki ki kama yaren ki kina yar fulani shuwa arab Daddyn ku cikakken bafulatani ni cikakkiyar shuwa arab amma dan iskanci baki iya yaren mu ko ka ɗan ba sai aron yare ki bi ki addabi mutane to wallahi tun wuri ki fita harkan yaren yahudawan nan ki kama yaren uwar ki da uban ki kai kaji min ƴa" "Mum what are you saying? why are you shouting anytime everyday" Dogon tsaki mum taja ba tare da ta sake magana ba ta ja hannun ta suka wuce cikin gida dan tasan idan ta biyewa Jehan haukata ta ta zatayi. A tsakiyar gida suka isko Goggo na alwala sallar issha sakin hannu Jehan Mum tayi tare da wucewa ɗaki abun ta kallon Goggo Jehan tayi tace "My Goggo please where is Rimsha" da sauri Goggo ta ɗago kai tana faɗin "What are you saying Jehan? You mean up til now they didn't see Rimsha?" gyaɗa mata kai Jehan tayi ba tare da tayi magana ba ta nufi cikin ɗaki "Jehan kizo kiyi alwala" cewar goggo "No goggo ba yanzu zan yi sallah ba sai an jima" daga cikin ɗaki mum tace cikin harshen turanci "Wannan ne kuma wane uwar ki baki isa ba wallahi ko ki wuce kije kiyi alwala kizo kiyi sallah a gaba na ko kuma na fito na same ki a wajen" Shiru Jehan ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya dan mum bata taɓa mata magana a irin wanna sigar ba juyowa tayi ta kalli goggo "Ni ma dai Jehan awan nan gabar ba zan bi bayan ki ba duk wanda baya sallah bai da wata amfani a duniya da kuma lahira sanna idan baki sallah a kan lokaci idan kin mutu kunama da maciji ne zasu yi gadin ki a cikin gabari ki kuma wutar jahannama zaki tafi saɓanin mai sallah akan lokaci da Mala'ikun rahma ne zasuyi gadin sa a kabarin sa su buɗe masa kofar aljanna ya rinƙa shakan kamshin aljanna sanna ya shiga aljanna" Ta kai karshen maganar tare da mikewa ta wuce ɗaki. Ɗaki Jehan ta shiga ta ɗauko wayar ta kirar iPhone 14 ta kunna wutar wayar ta dawo tsakar gida ta ɗauki buta tana bin butar da kallo aranta tana faɗin "Disgusting gaskiya ba zan iya wannan rayuwa ba dole na koma asalin gidan mu" kitchen ta nufa ta ɗebo ruwa a butan ta dawo wajen da goggo tayi alwala, ita ma tayi alwala ta wuce ɗaki tana turo baki kamar biro tana kunkuni. Tana shiga ɗaki ta ajiye wayar saman yar gadon su ta ɗauki ɗan karamin hijabi ta shifiɗa dadduma ta tada Sallah abun mamaki a nitse tayi sallar tare da karanta manya manyan surori a Qur'ani irin su suratul Yusuf da Aaraf a nitse tayi sallar nata sai dai hijabin nata ne bai gama rufe mata hannu ba a haka tayi Sallar. Bayan ta idar ta ɗaga hannu sama tayi addu'a mai tsawo sanna ta shafa ta mike ta cire hijabin ta mai da saman trolley ta tare da naɗe daddumar ta ajiye saman hijabin nata ta ɗauki wayar ta, ta fito waje nan tsakar gida ta isko mum da goggo sun tasa abinci a gaba sun kasa ci dukkan su sun buga uban ta gumi suna tunani ga wayar mum a gefen ta kirar I phone 13 ta kunna wutar wayar tana haska musu wajen. Kallon Abincin Jehan tayi shinkafa'ce da miyar steew da naman rago yaji ganye irin su lettuce cucumber cabbage da dai sauran su dogon tsaki taja ta nufi hanyar fita gidan babu hijabi" Jehan ina zaki je? Cewar mum "mum I'm feeling hungry kuma ni gaskiya i can't eat this dirty food I want to go and withdraw money from my Account to buy something that I will eat" "Jehan karki kashe kuɗin cikin Account na kin nan saboda bamu san me gobe zata haifar ba kiyi hakuri ki ci abincin nan yau kam kinji? Cewar mum kallon goggo Jehan tayi tana faɗin "ni gaskiya I can't wallahi" "Ok naji bazaki ci ba na yarda amma karki fita da daddaren nan kinga yanzu ma bamu ga Rinsha ba ko? Ki bari na je na ciro kuɗin na sawo miki ko me kike son ci" girgiza kai Jehan tayi kafin tace "No mum bana so, ki zauna i will go by myself" tana kai karshen maganar ta fice da sauri mum na faɗin "To ki dawo ki sa hijabi" ina kan mum tayi magana ma Jehan ta fice abun ta kallon mum goggo tayi tace "Maryam kiyi hakuri kici Abincin ki kinji ko?" girgiza kai mum tayi tana faɗin "Aunty Aisha ba zan iya cin Abincin ba bakina ba daɗi ina Rimsha take? Wani hali take ciki? Hannun su wa take? Mutane na gari ne ko na banza? Taci Abinci ne? ko bata ci ba? Wanna tunani ba zai barni na iya cin Abinci ba Aunty A'isha" dafa kafaɗar ta goggo tayi cikin tausayin uwa da ƴa tace "Na sani Maryam dole ki shiga tashin hankali muma muka shiga tashin hankali bare ke amma ki daure ki ci Abinci nan In Sha Allah babu abun da zai samu Rimsha zata dawo gare mu cikin koshin lafiya" da kyar mum ta iya cewa "Aunty A'isha ina ji ajikina duk in da Rimsha take bata lafiya tana cikin tashin hankali da damuwa" "A'a Maryam ki dai na faɗin hakan ki mata Addu'a domin Addu'ar Uwa bata faɗuwa haka kasa banza kinji? Yanzu dai dan Allah kici abincin" miƙewa Mum tayi ta nufi ɗaki tana faɗin "Aunty A'isha sai da safe ba zan iya cin komai ba" ta kai karshen maganar tare da shigewa ɗaki dafe kai goggo tayi tana salati da ambaton sunan Allah a ranta. Tana kokarin miƙewa Jahan ta shigo gidan babu ko sallama, kusa da goggo tazo ta miƙa mata ledoji biyu farare masu ɗauke da takeaway da drinks a ciki ta wuce da leda ɗaya ɗakin ta in da sabo goggo ta saba tun da su kazo garin nan Jehan bata cin Abincin da suke girkawa sai dai taje restaurants tayo musu takeaway kuma bata taɓa saya ita kaɗai guda huɗu take saya kullun goggo tasha ruman mamakin ganin yau ta sayi guda uku sai daga baya ta tuna ashe Rimsha bata nan, jiki ba kwari goggo ta mike taje ta rufe musu kofar gida sanna ta dawo ta wuce ɗakin mum saman gado ta isko mum kwance kamar mai barci ajiye mata wayar ta da kuma leda ɗaya daga cikin ledojin da Jehan ta sawo musu abinci goggo tayi, ta juya ta fita ta nufi ɗakin Jahan kasan cewar ɗakuna biyu ne a cikin gidan mum da Rimsha take kwana ita kuma goggo da Jehan zaune a tsakiyar ɗaki ta isko Jehan tana cin abinci fried rice da pepper chicken ajiye nata Abincin goggo tayi ta haye gadon su ta kwanta dan ita ma bata jin yinwa ko kaɗan ɓatan Rimsha ya tsaya mata a rai sosai, Addu'a tayi ta yiwa Rimsha akan duk in da take Allah ya tsare ta da haka har barci ɓarawo yayi awon gaba da ita. Ita kuwa Jehan sai da taci tayi nak sanna ta kwanshe kayan ta gyara wajen dan ita mace ce mai son tsabta bata son datti ko kaɗan. Sai da ta gyare wajen tsab ta sauya kayan jikin ta izuwa na barci ta haye gado kusa da goggo ta kwanta tare switch off na wayar ta ba jimawa barci yayi awon gaba da ita dayake ba tare da Rimsha suke kwana ba sai bata wani damu da rashin Rimsha ɗin sosai ba. Misalin karfe 1 na dare duniya duk sunyi barci Mum na zaune tsakiyar gadon ta ta kifa kai da gwiwa tana sharar kuka tana cikin matsanancinyar damuwa da tashin hankali ɓatan Rimsha, sosai take kuka damuwa sun haɗu sun mata yawa ga yanayin Jehan ga ɓatan Rimsha har karfe 2 na dare tana zaune tana sharar kuka. Sai 2:30 ta mike ta ɗauro alwala a toilet na ɗakin ta tazo ta fara sallah tana kai wa Allah kukan ta. Kamar yadda ta ga rana haka taga dare dan ta kasa rintsawa gani take kamar Rimsha zata dawo komai dare. Washegari tun karfe 6 mum ta fita ta nufi gidan su Sadiq yayin da ita kuma Jehan ke sharar barcin ta goggo na fama da Aikace Aikace gida tana kokarin ɗunɗuma musu abincin daren su na jiya da basu samu damar ci ba dan suci da safen. Da sallama mum ta shiga gidan su Sadiq yana tsaye a tsakar gida shi da maman sa da alama wani magana suke jin sallamar mum yasa suka juya a tare, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan saki murmushi yana faɗin "Sannu da zuwa Mama ina kwana?" "Lafiya lou babana" kallon Mum Maman Sadiq tayi cikin mutuntawa tace "Sannu ki da zuwa yanzu Sadiq ke faɗa min abun da ke faruwa na ɓatar ƴarki Allah sarki Allah ya bayyana ta" da sauri mum tace "Amin ya Allah" "Mama bari na kira su Sha'aban muje mu duba gidajen masu anguwanni ko Allah zai sa mu dace muga yarinyar" "To Sadiq Allah Ubangijin yasa ku ganta Allah ya bada Sa'a" "Amin" Sadiq ya amsa da shi sanna ya dubi mum yace "Mama ki koma gida zamu dubata gidajen masu anguwanni da dai duk in da ya dace" girgiza kai mum tayi cikin sauri tana faɗin "A'a babana muje tare ba zan iya zama a gida ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba". Ba yadda Sadiq bai yi da Mum akan ta koma gida ta jira su ba amma taki har Maman Sadiq ta sa baki amma mum taki haka Sadiq ya hakura suka tafi cikin jin kunya ya jera da mum suka fito ya shiga ɗakin su dake zauren gidan ya kira Sha'aban da Yusuf suka fito suka jera a tare suka fice daga gidan. Gidajen masu anguwanni suka fara zuwa suna tambaya, duk in da suka je ace musu ba'a ganta ba sunje gidajen masu anguwanni 5 amma shiru shiru ba labari mum ta gaji iya gajiya dan bata saba tafiyar kafa ba ga yinwa da take ji tun jiya da rana rabon ta da Abinci amma saboda tana da yakinin za'a iya ganin Rimsha ko da a hanya ne yasa ta danne duk wani abun da take ji ta jure ta cigaba da bin su Sadiq. Duk in da Sadiq yake tunanin za'a ga Rimsha sunje amma shiru daga karshe sai ya yanke shawarar suje su kai wa malamai kuɗi afara yi musu addu'a. Haka kuwa akayi malamai biyar mum ta rabawa dukka kuɗin hannun ta akan ayiwa Rimsha saukan Al Qur'ani mai girma sanna tayi sadaka da ɗan kuɗin da suka rage mata, jiki ba kwari ga gajiya da yinwa suka juya suka dawo anguwar su cikin mutunci da girmama juna sukayi sallama dasu Sadiq ta wuce gida da kyar take jan kafar ta duk kafar nata sun kunbura sun yi ja. Da sallama ta shigo gidan a tsakar gida ta isko Jehan da goggo suna zaune goggo tayi jugumi tana tunani, ita ma jehan tana zaune gefe ta buga nata tagumin, ganin mum yasa sukayi saurin miƙewa Jehan ta fasa kuka tana faɗin "Mum whare is my Rimsha?" "Maryam ina Rimsha ɗin take?" Cewar goggo wuce wa mum tayi ta zauna saman tabarma tana mai da numfashi kamar zatayi kuka cikin sauri goggo ta koma ta zauna tare da dafa kafaɗar mum tana faɗin "Maryam ki faɗa mana ina Rimsha kar ki sa zuciyar mu ta buga" shiru mum tayi tana mai da numfashi ta kasa magana. To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💋Star Lady💋 Share fisabilillah 👏 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* daga farko har karshe yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please STAR 🌟 LADY..✍️ *💋The beginning💋* Episode 2 ____Komawa itama Jehan tayi ta zauna ta dafa mum kamar zata yi kuka tace "Mum please where is Rimsha?" Har lokacin mum bata samu damar yi musu magana ba hasali ma dukar da kanta kasa tayi tana sauke ajiyar zuciya, hawaye Jehan ta farayi dan duk wan nan rashin shiri da suke da Rimsha tana bala'i kaunar kanwar nata. Almost 30mins mum ta ɗauka san nan ta ɗago kai ta kalle su cikin karyewar zuciya ta fara magana "Aunty A'isha banga Rimsha ba babu ita duk in da muka san zamu ganta mun duba bamu gan taba" tashin hankali iya tashin hankali goggo da Jehan sun shiga cike da matsanancinyar damuwa da tashin hankali goggo tace "Ai zama bai ganmu ba tashi za kuyi mu wuce police station mu kai Report" girgiza kai mum tayi tana faɗin "Aunty A'isha kin manta abun da Alhaji Shitu yace mana ne?" "A'a Maryam ban manta ba amma ai yanzu ya zama dole ne muje police station dan wan nan ba karamin case bane kin san dai idan Allah yayi Nawazudden ya zo yanzu ba zasu kare da shi ta daɗi ba ko?" "Nasani Aunty A'isha na sani amma to ya zamuyi bamu isa muje police station ba jiya ma da nace muje ido na ne ya rufe gaba ɗaya ban da haka da ban isa in yi wani zancen police station ba" "Maryam yanzu to me abun yi?" "Aunty A'isha sai dai fa mu zubawa sarautan Allah ido mu ci-gaba da yiwa Rimsha addu'a amma batun muje police station ko mu fita neman ta ma ya kare daga yanzu dan gudun ukubar da zamu shiga kin ji dai abun da Alhaji Shitu yace mana ko?" Shiru goggo tayi tana tunani ita kuma Jehan sai ruwan hawaye take wani na bin wani tana mai dana sanin kin zuwa aikan da tayi har a ka aiki Rimsha yanzu gashi yar uwar ta ɗaya tilo a duniya ta ɓata innalillahi wa inna ilaihir rajiun, jugum jugum sukayi dukkan su ba mai iya yiwa ɗan uwan sa magana kowa da abun da yake tunawa a ran sa amma kallo ɗaya zaka musu kaga tsananin tashin hankali a kan fuskokin su. KANO STATE Katafaren two storey building gida ne mai matukar kyau da tsada iya haɗuwa gidan nan ya haɗu kai da ganin gidan kasan masu rayuwa cikin wan nan gidan ko dai wani babban kusa daga gomnati ko wani babban ɗan kasuwa gate ɗin gidan kawai abun kallo ne ɓangaren biyu ne a cikin gidan ga wani ɗan ma dai dai cin pool a tsakar harabar gidan daga gefen hagu katafaren parking space ne mai ɗauke da katon rumfa ga dankara dankaran motoncin uku a wajen kirar *Mercedes-Benz* *McLaren solus GT.* *Roll-Royce boat Tail* motocin kawai abun kallo ne daga gefen dama kuma shuke shuken fulawowi ne awajen masu matikar kyau da ban sha'awa launin ja da yellow daga ɗan gefen parking space wani Katafaren wajen hutawa ne dake kewaye da glass wajen ɗauke yake da tampatsa tampatsan kujeru masu numfashi set ɗaya launin sky blue a tsakiyar kujerun wani haɗaɗen sofa table ne mai ɗan girma a wajen da gefe guda kuma ga makeken fridge a wajen dake ɗauke da lemukan sha kai ko ta ina gidan nan ya haɗu ba karya. Wani kyakkyawan puppy dog ne fari tas mai yalwataccen gashi a jikin sa ya fito da gudu daga katafaren kofar da zata sadaka da babban palo na gidan da Da gudu wata yar matashiyar yarinya ta fito daga kofar wadda a shakaru ba zata wuci 13 to 14 years ba tana sanye cikin wandon jeans guntu zuwa guiwa da yar riga baki mara nauyi kanta ba ɗankwali ta saki gashi har zuwa bayan wuyar ta, an zuba mata kananan kitso a kan nata kyakkyawace sosai chocolate color tana da dogon hanci da kyakkyawar fuskar ga manya manyan idon farare tas kamar madara yar siririyace ba kuma siririya sosai ba yar ma dai dai ciya, da gudu ta biyo puppy dog ɗin tana faɗin "My Dolly ki tsaya mana haba Dolly na so ki ke nayi kuka ne" gudu Dolly take sosai yarinyar tana bin ta a baya har sai da suka kai wajen wasa dake gidan waje ne mai girma ga gefen buga basket ball a gefe ga wajen lilo ga wajen hawa dokin wasa da motoci na yara na wasa da dai sauran su wajen ya haɗu iya haduwa. Saman lilo Dolly ta hau ta zauna da gudu yarinyar ta kariso wajen tana haki tana mai da numfashi ta tsaya ta rike kugun ta da hannun ta dukka biyu tana kallon Dollyn ta yayin da itama Dolly ita take kallo "Why Dolly kika wahalar da ni me na miki?" Tsalle Dolly tayi ta faɗo jikin ta hannu yarinyar ta sa tana shafa jikin dolly ɗin tana kallon face nata. Dai dai lokacin wani babban Alaji ya iso wajen kai da ganin sa kasan Naira ta zauna masa kyakkyawa ne sosai fari tas da shi kamar balarabe ga kyakkyawar saje da gemu dogo da ka ganshi kaga Ustadz yaji hutu fatar jikin nan nashi ta kwanta luwai luwai da shi, yana sanye da jallabiya Brown a jikin sa ya kariso wajen yana faɗin "Baby jelly kizo muje kiyi breakfast a gaba na kafin na fita" make kafaɗa jelly tayi cikin shagwaɓa da murya kamar mai kuka tace "Dady ni ba zan iya cin komai ba dan dolly na tun jiya taki cin abinci fushi take da ni fa dady" ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka rungumota dady yayi tare da dollyn nata yana ɗan bubbuga bayan ta cikin sigar rarrashi yace "Haba babyn dady muje ki ci abinci zan kira doctor Sadiq ya duba dolly ɗin sai muga meke damun ta yasa taki cin abinci" make kafaɗa tayi tana faɗin "Ni dady idan baka kira dr yazo ya fara dubata ba bazan iya cin komai ba" "Okey muje na ɗauki waya ta na kira dr ɗin ko dan ki samu kici abinci nima na samu na fita ana ta kirana a office tun ɗazun kuma nasan inna tafi ba cin abinci zaki yi ba" to tace masa ya kama hannun ta tana rungume da dollyn ta suka wuce cikin palon. Katafaren palo ne mai girman gaske mai ɗauke da manyan sofa set, set 2 launin Milk da Brown sai wani kyakkyawan table ɗin cin abinci mai ɗauke da kujeru 6 daga gefe ga wani makeken Tv plasma manne a bangon. Palon yaji komai da ake buƙata. Saman kyakkyawar table ɗin dady ya wuce rike da hannu jelly sai faman turo baki take table ɗin cike yake da kayan abinci kala kala zama yayi tare da zaunar da ita saman kujerar kusa da shi ya ɗauko wayar sa dake saman table ɗin ta gefe ya shiga contact ya laluɓo wata number da a ka yi saving da Dr ya fara kira. Bugu ɗaya dr ya ɗaga cike da cikin nitsuwa dady yace "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Dr yace "Waalaikumussalam Alhaji Ya gajiya?" "Lafiya lou dr daman nace idan kana kusa ka zo ka duba mana dolly taki cin abinci tun jiya" "To alhaji gani nan zuwa" "Ok sai ka zo" ya kai karshen maganar tare da katse kiran ya mai da wayar ya ajiye a gefen sa ya ɗauki spoon da ya fara cin abincin sa da shi kafin ya fita kiran jelly ya ɗibo abincin ya kai sai tin ɗan bakin jelly yana faɗin "Ci ko my baby" turo baki tayi tana faɗin "No dady ni ba zan ci ba gaskiya sai Dolly na taci" "Haba my baby kinji fa dr yace zai zo ya duba ta, to ki ci naki ke ma kafin dr yazo ya dubata kinji? Yauwa babyn dadyn ta" a hankali ta buɗe ɗan bakin nata ya zuba mata ta fara tauna a hankali hankali tana turo baki a haka har ta haɗiye ya sake ɗebowa ya kai mata bakin ta, ta ansa ta fara ci haka ya rinƙa lallaɓata har taci ta koshi san nan shi ma yaci ya koshi kafin ya miƙe ya riƙo hannun ta suka haye sama tana rungume da dollyn ta suka shige wani haɗaɗe bedroom mai ɗauke da katafaren gadon kwanciya dake shinfiɗe da white bed sheet na alfarma sai makeken drawer sanya kayan su, Sai da suka isa tsakiyar ɗakin ya saki hannun ta ya nufi toilet yana faɗin "Let me bath my baby ki zauna idan kinji dr ya shigo sai ki kai masa dolly ya fara dubata kafin nazo, wucewa tayi ta haye saman katafaren gadon su ba tare da tayi magana ba shi ma ya wuce ya shiga toilet Da zaman ta ba'afi 10mins ba dr yazo jin dr yazo yasa ta fito da gudu tazo ta miƙa masa Dolly tana faɗin "Uncle ka dubata taki cin abinci kwata kwata" tayi maganar kamar zata yi kuka tun daga nesa dr ya kura mata ido yana kallon ta har ta kariso gaban sa tana miƙa masa Dolly hankalin sa na kan kyakkyawar face na ta bai ma san tana miƙa masa wani abu ba sai magana take masa amma bai ji taba hankalin sa yayi nisa kallon face nata kawai yake, tana kokarin sa masa kuka dady ya fito yana faɗin "dr Sadiq har ka iso?" Yar firgigit dr yayi kafin yace "Eh na iso" yayi maganar tare da ansan dolly da jelly ke miƙa masa cikin sauri ya fara dubata da gudu jelly ta wuce ta rungumi dady tana faɗin "Dady bana son a yiwa Dolly ta allura" rungumeta dady yayi suka koma saman kujera mai zaman mutun 2 suka zauna shi ku ma dr yana aiki yana satar kallon jelly `````Dr````` Babban mutun ne wadda a kalla zai kai 35 year a duniya yana da kyan sa dai dai gwargwado ɗane ga abokin dady suna shiri da dady sosai. Miƙewa dady yayi yana faɗin "My baby zauna ki kalli Dolly ki dr na duba ta bari na yi shirin zuwa office ko" jinjina masa kai tayi tana faɗin "To dady" wucewa dady yayi yana faɗin "Sadiq dan Allah ka duba mana dollyn nan da kyau muji ainihin meke damun ta yasa bata cin abin ci kaga kwana ki ma haka ta mana to dan Allah wan nan karon kam ina son sanin asalin a bun da ke damun ta" ya kai karshen maganar tare da hayewa saman ya shiga bedroom na shi dan shirin zuwa office. Dady na tafiya dr Sadiq ya dubi jelly da ta buga takumi ta tsare sa da manya manyan idon ta tana kallon yadda yake duba dollyn nata ɗaga ido yayi ya kalli sama ganin cameran palon a kunne ne yasa ya ɗan ɓata rai tare da mai da kan sa kan dolly ya ci gaba da yan dube duben sa ita dai jelly ta zuba masa ido tana kallon sa. Wacece jelly Jalila kenan ya ɗaya tilo ga Alhaji Abdul Malik Salman Sultan tun jelly na da shekara biyu mahaifiyar ta ta rasu dadyn ta kuma yaki kara yin wani auren ya ci gaba da zama da yarsa su biyu suke rayuwa cikin wan nan Katafaren gidan sai masu musu girki Nana da Zuwaira Alhaji Abdul Malik bai cika zama sosai a gida ba wan nan dalili yasa ya sanya camerori a gaba ɗaya longu da sako na gidan sa dan ya rinƙa ganin halin da yar sa ɗaya tilo take ciki yana bala'i son jelly sosai fiye da ran sa, duk abun da take so shi ma shi yake so yana son farincikin ta kasan cewar ita ka ɗai ke garesa yan uwan maman ta sunyi sunyi ya bari su ɗauke ta su rike ta a wajen su amma yaki san nan anyi anyi da shi ya kara wani Auren nan ma yaki karawa dan gani yake duk wadda zai auro ba zata rike masa jelly yadda ya dace ba shi yasa yayi zaman sa daga shi sai ita sai masu aiki. Wan nan shine ta kai taccen wacece jelly. Shirye cikin wata dakakkiyar shadda sky blue dady ya fito ya sanya hula da takalma farare sai kamshi yake zubawa yayi kyau sosai, in da ya bar jelly nan ya dawo ya same ta ta buga tagumi tana kallon dollyn ta kusa da ita dady ya dawo ya zauna yana faɗin "My baby kar ki damu dolly zata samu lafiya ta dawo normal" kwantar da kan ta tayi saman cinyar sa tana faɗin "Dady ina jin kamar zan yi kuka" kallon dr dady yayi kafin yace "Dr Sadiq ya ake ciki meke damun dolly ɗin namu" satar kallon jelly dr yayi kafin ya fara magana "Alhaji zaka fitane?" Gyaɗa masa kai dady yayi "To muje tare sai na sawo mata magungu nan da suka dace ko? Dan gaskiya dolly bata da lafiya tana da matsala a zuciya amma In Sha Allah tana shan maganin nan zata samu sauki" "Okey to muje mana amma ni zan wuce Office idan ka sawo maganin sai kazo ka bata" "Miƙewa dr yayi yana faɗin "Ba damuwa zan dawo na bata maganin jelly a kula da dolly sai na dawo yanzu zan zo na bata magani ta warke taci abinci kin ji ko? Da fara'a ta amsa da "To uncle sai kun dawo" . A tare dady da dr suka fice daga palon kowa ya shiga motar sa driver yaja dady shi kuma dr ya ja kan sa suka fice daga gidan suka bar jelly rungume da dolly tana jiran dr. KATSINA washegari haka su mum suka tashi cikin kunci da jimami a kwana biyu da ɓatan Rimsha har mum tayi mugun rama saboda tunani. Yauma kamar kullun zaune suke tsakar gida saman tabar ma sunyi jugum jugum kamar wayan da aka aikowa da sakon mutuwa Jehan na zaune daga ɗan gefen su saman yar ƙaramar kujera tana rike da wayar ta tana kokarin yin posting na hoton Rimsha a shafin ta Facebook. Tana gab da ɗora hoton sai maganar mum na jiya ta faɗo mata a rai in da take cewa Aunty A'isha kin san dai Alhaji Shitu ya gargaɗe mu kan zuwa police station ko, tuna hakan yasa gudun karta jawo wata matsala yasa ta ɗago ta kalli mum murya cike da damuwa tace "Mum ina son in shearing hoton Rimsha ya shiga duniya ko Allah zai sa in samu wan da ya gan ta" waro ido waje mum tayi kafin tace "Ki dai tona mana asiri ina ga Jehan kin gaji da zaman duniya ne shi yasa" cikin sauri goggo tace "Karki kuskura kiyi wan nan ganganci yanzu duk wani old account naki na media ma ki sauke sa ki buɗe sabo kuma karki kuskura kiyi posting na face na ki dan kin san dai ba wan da bai san face naku ba a kasar nan" jiki ba kwari Jehan ta sauke hoton Rimsha ta fasa ɗaurawa tayi shiru tare da buga takumi tana tunanin yar uwar ta "Jehan ki tashi ki ɗauki bokiti kije gidan su Sadiq ki ɗebo mana ruwa mu ɗaura girki dan yau duk gidan nan ba mai cash ko biyar" cewar goggo, a sukwane Jahan ya ɗago kai tana kallon goggo mamaki ma ya hana ta magana sai tambayar kan ta take a cikin ran ta "Wai shin mafarki nake ne ko da gaske ne ni Jahan zanje ɗebo ruwa ya Allah idan mafarki nake kasa nayi gaggawar farkawa" ganin tayi shiru ne yasa goggo tace "Jehan dake fa nake ki tashi mana" a kule tace "Wai goggo mafarki kike yi ne? Ni Jahan ɗin ne zanje ɗebo ruwa kina jin me kike faɗe kuwa goggo?" Tayi maganar cikin harshen turanci Kallon ta da kyau goggo tayi kafin tace "Kiyi hakuri Jehan kinga kuɗin hannun mu ya kare ne yau duk gidan nan ba wanda ta tashi da ko sisi" "To goggo ba akoi kuɗi a Account ba? Ai bani ATM zaku yi naje na ciro muku" "A'a Jehan yanzu kuɗin da suka rage manan nan lallaɓasu zamuyi ɗan su ɗan rike mu na wani ɗan lokacin kafin muga me Allah zai yi yanzu duk abun da bai zama dole ba ba zamu rinƙa fitar da kuɗi dan sayan sa ba" Cewar mum "Maryam wai nawa ne ma ya rage a account nakin?" Cewar goggo "Aunty A'isha kuɗin ba yawa kinga mun saya gidan nan mun sayi gado da sauran kayan buƙata bai fi 300k bane ya saura a ciki kinga idan muka ce komai saya zamu yi a yadda zamanin nan ya zama komai ta ninka kuɗin sa wallahi kafin nan da next week kuɗin zai kare" "Hakane Maryam shi yasa nace tun da akoi rijiya gidan su yaron nan Sadiq sai Jehan ta rinƙa ɗebo mana ruwan aiki ko?" Gyaɗa kai mum tayi tana faɗin "Haka ne Aunty A'isha kuma ruwan rijiyar tasu ba laifi wallahi maman Sadiq na da tsabta sosai" mum na rufe baki Maman Sadiq ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta a tare mum da goggo suka haɗa baki wajen amsa mata sallama, ita dai Jehan ta buga tagumi tana tunanin yar uwar Rimsha duk wan nan zancen da su mum suke baya shiga kunnen ta, saman tabarmar da suke Maman Sadiq ta zauna suka gaisa cikin girmama juna san nan tayiwa mum jaje tare da fatan Allah ya bayyana Rumsha "Jahan ɗin dady ki tashi ki je mana" cewar goggo kallon sama da kasa Jehan tayiwa goggo kafin tace "Wai ke meyasa goggo baki son zaman lafiya ne? Wai da gaske kike ni zan je ɗiban ruwa?" Tayi maganar cikin harshen turanci goggo na kokarin yin magana mum ta riga ta da cewa "To shike nan Jehan tun da ba zaki je ba bari ni na tashi naje da kai na" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi kitchen ta ɗauko wata yar bokiti baki na roba ta fito ta ɗauko mayafi a ɗaki, ta na kokarin nufan hanyar fita Jehan tayi saurin miƙewa ta rike bokitin tana faɗin "are you serious mum? yanzu daman da gaske sai kije ɗiban ruwa da kan ki? Haba mum wai me yasa kuke yin hakane okay let me go and withdraw money from my account sai na sawo ruwan ko?" Kallon ta da kyau mum tayi tana mugun tausayawa yaran nata rayuwar da baka saba da ita ba rana ɗaya ka tsinci kan ka a ciki akoi wahalar ɗauka cike da tausayi mum ta fara magana cikin harshen turanci "Jahan bana son ki sake taɓa kuɗin Account na kin nan kinji? Kinga bamu san in da dadyn ku ya ke ba kuma kin san muna cikin haɗari a gaban ki Alhaji Shitu ya faɗimana komai kin san komai kin san meke faruwa kina dai ji Alhaji Shitu cewa yayi mu ɓoye kan mu karmu bari a san in da muke idan muka kashe kuɗin hannun mu waye kike tunanin zai bamu a wan nan wahalar rayuwa da ake ciki ko so kike mu fita nema har a ganmu a kashe mu ne eh? Ina son ki zama mai godiya ga Allah a duk halin da kika tsinci kan ki kin ji ko? Wan nan rayuwa da muke yanzu ma wata aya Allah ya nuna mana da muna zaune cikin daular dukiya da jin daɗi bamu taɓa sanin halin da yan kasan nan suke ciki ba amma kin yanzu ko ba komai mun samu karuwa munga halin da talakawa suke ciki idan Allah ya bayyana dadyn ku kuma Allah ya cika masa burin sa ya ci zaɓe kinga ai zamu faɗa masa halin da talakawa ke ciki ba sai na kusa da shi sun rinƙa masa karya ba" shiru Jehan ta ɗan yi hawaye na bin kuncin ta da kyar ta iya buɗe baki ta fara magana cikin harshen turanci "Mum yanzu shike nan dady ba zai dawo ba wai ma ina yaje ne mum kinga kafin ya fita fa yace min yana zuwa zai dawo da wuri kuma naji da uncle yazo yana ce miki bayi da tabbacin dady zai iya kuɓuta mu dai mu gudu Please mum ki faɗa min meke faruwa menene gaskiya abun da ya faru da dady na ko dai dady ya rasu ne?" "No Jehan ban san in da dadyn ku yake ba amma koma me ina da tabbacin bai mutu ba kuma ina sa ran zai dawo gare mu zai nememu ina jin hakan a jiki na" ta kai karshen maganar tare da sanya hannun ta ta gogewa Jahan hawayen dake bin kumatun ta tana faɗin "Ya isa kukan haka kiyiwa dadyn ku da Rimsha addu'a kin ji ko? In sha Allah zasu dawo gare mu komai zai wuce" rungume mum tayi tana faɗin "Mum ba zan iya dai na kuka ba sai dai na tsagaita" ɗan bubbuga bayan ta mum tayi tana faɗin "Hakane Jehan na san ba zaki iya dai na kuka ba dan uba da yar uwa ba wasa ba amma addu'a shine best thing da zaki rinƙa yi musu yanzu dai ansa bokiti kije ki ɗebo mana ruwa muyi abinci kin ji" ba musu ta ansa bokitin ta saki mum tana goge hawaye ta nufi hanyar fita "Jehan ki dawo ki ɗauki hijabi kin ji ko?" Cewar mum ɗin girgiza kai Jahan tayi kafin tace "No mum ni ban son hijabin nan gaskiya" "Jehan nan fa ba Abuja bane" Cewar goggo shiru Jahan tayi kamar bata ji me suka ce ba ta fice daga gidan kan ta ba hijabi sai wani ɗan karamin ɗankwali mai kama da handkerchief ta ɗaura a kan ta haka ta fice. Sai da ta fita san nan tace "bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah" بِسْمِ اللهِ، تَوَكَّلْتُ عَلَى اللهِ، وَلاَحَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ kallon goggo mum tayi kafin ta dawo kusa da maman Sadiq ta zauna tana faɗin "Jahan kenan" murmushi maman Sadiq tayi tace "Ai yara sarakuna ne" da yake cikin harshen turanci mum da Jahan suka yi magana hakan yasa maman Sadiq bata ji me suka ce ba girgiza kai kawai mum tayi bata sake magana ba shiru wajen yayi kamar ba mutane dukkan su sun shiga duniyar tunanin. ```Jahan``` Tana tafiya tana yamutse fuska tana kallon dattin unguwar kasan cewar Anguwar talakawa ne sosai akoi datti ta ko ina kallon banza ta fara yiwa mutane dake wucewa a harabar unguwar duk in da ta wuce sai ta tufar da yawu ko ta toshe hanci. Tun daga ɗan nesa ta hango su Sadiq da wasu samari saannin sa suna buga kwallo dogon tsaki taja kafin tace "Dirty people" ta kai karshen maganar tare ta tufar da yawu a ranta tana faɗin "Allah ya kiyaye naci abincin da su Goggo zasu girka da ruwan gidan su kazaman yaran nan" Ta shagala cikin tunani da zancen zuci bata ma san ta iso wajen su sadiq ba sai ji tayi kwallo ya bugeta a kafaɗa da karfi har sai da tayi tangal tangal kamar zata faɗi kasa, a zafafe ta juyo tana kallon matashin da ya bugo kwallon, matashi ne mai jini a jiki yana da ɗan kiba da tsawo wadda akalla zai kai 24 to 25 years. Kallon banza mata shin mata kafin yace "Ke ki wuce ki bamu waje kinzo kin tsayawa mutane a waje" Bata ma fahinci me ya faɗa ba ta dai fahimci faɗa yake mata, A kule ta fara magana cikin harshen turanci "Kai banza kazami idan ban da kai wawa ne ma taya za'ayi kuzo kuna buga ball a kan hanyar wuce wa jibeka wani katon banza da kai cikin yara duk kafi su girma kazo kana shiga cikin yara ko kunya baka ji" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki fusata iya fusata matashin nan ya fisata kasan cewar yana jin turanci sosai a fusace ya nufota gadan gadan tana tsaye ko motsi ba tayi ba sai ma kallon rai ni da take masa,.Yana iso wa wajen ta bai yi wata wata ba ya ɗaga hannu zai wanka mata mari cikin sauri Sadiq ya rike hannun sa yana faɗin "Haba Fadil me yayi zafi zaka yi yunkurin marinta" Fadil na ƙoƙarin yin magana muryan Jahan ya katse su cikin harshen turanci tace "Lallai kuwa wani kaza mi da kai ne kake yunkurin taɓani aiko da kayi kuskuren marina da baka sake mafarkin marin wata ba da kayi nadamar zuwan ka duniya" A fusace Fadil ya kwace hannun sa daga rikon da Sadiq ya masa yana kokarin kai mata mari Sadiq ya sake rike sa yana faɗin "Ki tafi in da zaki je kiyi hakuri" kallon banza tayiwa Sadiq kafin tace "I can't go anywhere please ka sake shi ya mare ni idan ba shi da hankali wani wawa kazami da shi sai wari yake" tayi maganar da kwabaɓiyar hausar ta, ta kai karshen maganar tare da tufar da yawu tana yamutse fuska, a fusace Fadil ya ture Sadiq har sai da yayi baya baya ya faɗi kasa cikin zafin nama ya ɗaga hannu zai mare ta Share fisabilillah 👏 To Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💋Star Lady💋 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please STAR 🌟 LADY..✍️ *💋The beginning💋* Episode 3 ....cak ta riƙe hannun sa tana tsaye ko alamar tsoro babu a idon ta bare shakkan sa cikin fushi ya sanya kafar sa yana kokarin kwashe kafar ta ta faɗi kasa batayi wata wata ba ta wanke masa fuska da mari cike da izza tace "Da Jehan kake magana first born a wajen...sai kuma tayi shiru tare da wurgi da hannun sa da ta riƙe tana jan tsaki ta wuce ta nufi hanyar shiga gidan su Sadiq mamaki ya hana Fadil motsawa daga in da yake ya dafe kumatun sa yana kallon ta har ta shige gidan su Sadiq shi kan shi Sadiq dake baje a kasa mamaki ya hana shi miƙewa sai zancen zuci yake "ƴar ƙaramar yarinya kamar wan nan har ta iya sa hannu ta mari namiji babba kamar Fadil babu shakka ko tsoro a idon ta wace ce wan nan yarinyar gaskiya ina son sanin wace ce ita dan wannan irin ƙarfin gwiwar da ƙarfin halin nata ba haka kawai ba daman kuma yan unguwar nan suna ta magana a kan su akan basu yi kama da talakawa ba to suwaye su wace ce ita?" haka Sadiq yayi ta jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su shi kan shi Fadil tambayar da yake wa kan sa kenan wace ce Jehan da har zata iya marin sa babu ko shakka bare ɗarɗar, gaba ɗaya matasan dake wajen suna buga kwallo sun sha mamakin Jehan ba kaɗan ba kasan cewar sun san halin Fadil bai da wasa yana da zafin rai ga cinzali da mugunta dayawan ƴan unguwa suna tsoran sa yau mace ta mare sa a gaban jama'ar unguwa tab yarinya kin shiga uku sai dai muce Allah ya jikan ki. A gefen Jehan kuwa tana shiga gidan su Sadiq tayi karo da kanwar Sadiq a bakin kofa zata fito hannun ta rike da murhun da take suyar awara a kofar gida ɗan baya kaɗan yarinyar tayi tana faɗin "Sannun ki da zuwa" ko kallon in da take Jehan bata yi ba ta wuce ta shige cikin gida. Tana shiga ta tufar da yawu ganin gidan caɓa caɓa da ruwa shiru ta tsaya kusa da rijiyar ta kasa ɗibar ruwan dan bata iya ba kuma taga abun ɗiban ruwan yana da girma shiru tayi tana karewa gidan kallo tana kwaɓe fuska. Tana tsaye Amaryan baban Sadiq ta fito daga ɗakin ta shirye cikin atamfa doguwar riga tayi kyau ba karya kallon sama da kasa Jehan ta mata kafin tace cikin harshen turanci "Ke zo ki ɗiba min ruwan" waro ido waje Amaryan baban Sadiq tayi ta ɗan juya baya dan taga ko dai ba da ita Jehan take ba akoi wata a bayan ta, ganin ba kowa ne yasa ta dawo da kallon ta kan Jehan kallon banza Jehan ta mata tana faɗin "Ke dake nake ai kizo ki ɗiba min ruwa nace" kallon uku goma amaryan baban Sadiq ta mata kafin tace cikin harshen turanci ita ma tace "Ke kina da hankali kuwa ni kike cewa na ɗiba miki ruwa kin san wace ce ni kuwa?" Dogon tsaki Jehan taja kafin tace "Thank God ashe dai akoi masu ɗan jin English a kauyen nan ke ni ban tambaye ki ke wace ce ba kuma ban nemi sanin ke wace ce ɗin ba, ruwa kawai nace kizo ki ɗeba min ban son hayani ya" a fusace Amaryan baban Sadiq ta nufo Jehan da nufin wanka mata mari dan ta mata rashin kunya zuba mata ido Jehan tayi tana mata kallon mahaukaciya har ta ƙariso wajen, ganin babu alamar tsoro a face ɗin Jehan ne yasa Amarya taja birki tana kallon ta dai dai lokacin Sadiq ya shigo gidan, da sauri ya kariso wajen yana faɗin "Amarya lafiya?" Kallon sama da kasa amarya tayiwa Sadiq ɗin kafin tace "Ban sani ba" san nan ta juya harshen cikin harshen turanci tace da Jehan "Ke ɗauki bokitin ki, ki bar gidan nan kuma daga yau karna sake ganin kafar ki wai da sunan kinzo ɗiban ruwa gidan nan kina jina ko?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Da ba a son rai na nazo ɗiban ruwan nan ba amma tun da kika ce haka to ki sani daga yau kullun sai nazo ɗiban ruwa in ga uban da ya isa ya hanani" ganin Jehan bazata daku a hannun ta bane yasa ta juya fuuu ta wuce ɗaki tana masifa "Wallahi bari shi ma baban Sadiq ɗin ya dawo dole ya hanaki zuwa gidan nan har kaman ni ina faɗa yau wata tana bani amsa ni da duk gidan nan shakka ta ake nasan maganin ki" kallon Sadiq Jehan tayi kafin tace "Who is she?" "Kin mantane nace miki bana jin turanci" sadiq ya bata amsa guntun tsaki taja kafin tace "waye ne ita" murmushi Sadiq yayi yana faɗin "Cewa zaki yi wace ce ita" kallon sama da kasa ta masa kafin tace "To koma me tun da ka gane nufi na just amsa me kawai" "ita ma maman mu ne" waro dara daran idon ta waje Jehan tayi ta sanya hannu ta tana gwada tsawon Amarya a iska tana faɗin "How? Za ace wan nan yar Small yarinyar ta zama maman ku ba ma sister ku ba" hannu Sadiq yasa ya ɗauki guga ya fara ɗiban mata ruwan yana faɗin "Eh matar baban mu ne itama da ita da maman yarinyar da take waje tana tuyan awaran nan dukka matan baban mu ne" "Why baban ku zai Auri wan nan small girl ɗin I think fa ka girme ta ko?" "Eh na girme ta kawai dan iyayen ta na da kuɗi ne sai tace baban mu take so shi ne aka aura masa ita bana jin yana son ta amma dai ni ban sani ba tun da ba shiga har kan su nake ba" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da yake juye mata ruwa gugan karshe a bokitin nata, Shiru Jehan tayi dan ba abun da ta gane a zancen Sadiq bayan cewa Amarya maman su ne matar baban su. Ɗaukan mata ruwan yayi yana faɗin "Muje na kai miki gida" wucewa gaba tayi da sauri ta fice daga gidan tana tufar da yawu bayan ta Sadiq ya bi yana mai farinciki ko ba komai yau Jehan ta masa magana, ko da ta fito duk matasan dake buga kwallo da Sadiq ɗazun basa nan sun watse kowa ya kama kan sa wuce wa tayi abun ta tana hararar masu wucewa a hanya Babu ko sallama ta faɗa cikin gida yadda ta bar su mum da goggo da maman Sadiq haka ta dawo ta same su saman kujerar da ta tashi ta koma ta zauna tana turɓune fuska "Jehan ina ruwan kuma?" Cewar mum turo baki tayi kamar biro kafin tace "wan can dirty boy ɗin yana kawo wa" ruƙe haɓa goggo tayi zata yi magana Sadiq ya shigo bakin sa ɗauke da sallama da fara'a mum ta amsa masa tana mamaki yanzu daman Sadiq Jehan ke cewa dirty boy oh Allah "Mama ai na zan juye muku ruwan?" Sadiq ya tambaya kakalo murmushi dole Mum tayi kafin tace "Ajiye min a kitchen babana" da azaman sa ya karisa cikin kitchen ɗin ya ajiye ruwan ya fito dai dai lokacin goggo ke tambayar Jehan "Wai babyn dady me ya faru kike ta ɓata rai haka ne?" Murmushin Sadiq yayi yace "Ita da Amarya ce ban dai san me ya haɗa su ba na shigo na samu amarya ta nufo ta zata bugeta" mum na kokarin yin magana goggo ta rigata a kule tace "Wace amarya kuma? Giya ta sha ne da zata ce zata bugi baby Jehan?" Kallon maman sa Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri gwaggo" miƙewa gwaggo tayi tana faɗin "Ba wata zancen hakuri sai naji dalili, akan me zata ce zata bugi Jehan" shiru maman Sadiq tayi ita kuwa mum mamaki take wai duk wahalar da suka shiga gwaggo bata sauya ba akan Jehan, cikin sanyin murya mum tace "Aunty A'isha kiyi hakuri mana tun da bata bugetan ba" a fusace gwaggo tace "A'a gaskiya ba zan hakura ba idan na barta gobe ma zata sake yunkurin tabata ne gwara na dakatar da abun tun yanzu kai Sadiq muje in ga wace isashiya ce wan nan" "Matar baban mu ne" Sadiq ya bata amsa yana kallon maman sa "Dan matar baban kune sai ta yi yunkurin taɓa Jehan tana da hankali kuwa?" Shiru suka yi gaba ɗayan su ita dai mum idan da sabo ta saba da halin gwaggo da Jehan dawo da kallon ta kan maman Sadiq gwaggo tayi tana faɗin "Zan hakura ne kawai saboda mutuncin ki da kirkin ki amma ku faɗawa baban Sadiq ya jawa matar sa kunne idan ta kuskura hannun ta ya taɓa jikin Jehan to zata yi danasanin mai girma a rayuwar ta" ta kai karshen maganar tare da komawa ta zauna tana ɗaure fuska "Mum zan iya tafiya ko in karo muku ruwan?" Cewar Sadiq girgiza kai mum tayi tana faɗin "A'a babana ya isa muna godiya sosai Allah ya albarkaci rayuwar ka" "Amin mum amma dan Allah mum idan kuna buƙatar ruwa ku kirani zan ɗebo muku ban son Jehan ta rinƙa zuwa gida dan amarya bata da mutunci ko kaɗan gashi duk gida ba wan da ya isa ya mata magana dan tana takama baba zai iya komai akanta zai iya koran kowa a gidan saboda ita shi yasa take abun da ta ga dama" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya fice daga gidan kallon maman Sadiq da kyau mum tayi damuwa ne karara a bayyane a kan face ɗin ta Allah sarki gata mace mai hakuri da kamala "Maman Sadiq abun da Sadiq ya faɗa haka ne?" Gyaɗawa mum kai maman Sadiq tayi kafin tace "Haka ne" miƙewa Jehan tayi ta wuce ɗaki a ranta tana faɗin "Ko me su gwaggo kuma suke cewa oho" "Maman Sadiq me ya sa hakan to? Ba kece uwar gida ba? Ko dai akoi wata ce kafin ke?" Cewar gwaggo shiru maman Sadiq ta ɗan yi kafin ta fara magana a nitse "Da farko ni ka ɗai ce a wajen baban Sadiq daga baya ya auro maman Hanan lokacin da tazo gidan ba irin cin kashin da bata min ba shi kuma baban Sadiq yana biye mata ranar girkin ta zata yi girki ta hana ni, ni da Sadiq haka ina ji ina gani idan na masa magana sai yace to shi ina ruwan sa na ansa da kai na mana ni ba mace bace kuma yana sane ba iya faɗa da ita zan yi ba dan tafini tsawo da kiɓa wani lokaci Sadiq idan yaga abun da take min yayi yawa sai ya shiga ɗaki yayi ta kuka dan yana tsoron yin magana yasan halin baban sa zai iya korin sa daga gidan shi ba korin sa da za'ayi ne damuwar sa ba a'a tafiya da zai yi ya barni bai san me zai iya faruwa da ni ba gwara masa ya zauna yana kallo na idan wani abun da yafi karfi na yazo sai ya tare min, haka muka ci gaba da rayuwa cikin wahala ga talauci har ta kai ta kawo baban Sadiq ya dai na bani abinci ya dai na shiga ɗaki na ya dai na kulani kwata kwata, saboda haka Sadiq ya ajiye makarantar sa daga class 5 ya fara koyan aiki a garejin bayan layin nan yana aiki idan ya samu kuɗi yana ciyar da ni Allah da ikon sa Allah ya bani ciki na sake haifan Yusuf daga nan ban sake samun Haihuwa ba har yau dan tun daga lokacin har izuwa yanzu baban Sadiq bai sake kusan tata ba, shi ma Yusuf haka ya taso cikin wahala da ukubar maman su Hanan tun yana yaro take bashi wahala har Allah yasa ya girma gwara Sadiq ma ya samu karatu kaɗan zuwa class 5 shi Yusuf ko kaɗan bai samu ba kasan cewar baban sa bai da karfi daman bai da karfi rike mata biyu kawai jaraba ce ni kaɗai ɗin ma da kyar yake iya ciyar da ni sau biyu a rana amma haka ya rufe ido ya kara Aure, Sadiq yana iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kula dani da kanin sa muna a haka har maman Hanan ta samu cikin Hanan yarinyar nan dake tuyar awara a kofar gidan mu, ita ma tun daga kan Hanan bata sake Haihuwa ba sai dai abun mamakin ita Hanan tana da hali mai kyau ba kamar maman ta ba, muna cikin wan nan wahalar yazo mana da wata zance wai an bashi mata wata yar mai kuɗi ce ta ganshi tace shi take so dan haka Aure zai kara a lokacin nayi kokarin nuna masa illar hakan yaki yarda dana matsa yace to na tafi gidan mu jin hakan yasa nayi shiru na kyale sa kasan cewar bani da uwa mahaifiyata ta rasu kuma ba zan iya tafiya na bar su sadiq ba, yarinyar da yace zai aura yarinya ce karama bata wuce Sa'a Sadiq ba dan bata wuce 23 years ba Sadiq ma ya ɗan girme ta na nuna masa illar abun amma ya rufe idon sa yaki shi yaga kuɗi daman gidan da muke cikin nan gidan hayane alokacin sanadiyar Auren yarinyar baban ta ya sai masa gidan ya dawo mallakin sa yarinyar nan tun da tazo shikenan baban Sadiq ya tattara mu daga ni har maman Hanan ya watsar daman ni ya dade da watsar da ni ya tattara ya koma ya tare a gindin yarinyar sai abun da tace ya keyi ko waje idan tace karya fita tofa baya taka ko ina daman ba wani sana'a yake ba itace yake sayarwa a ɗan bayan layin mu baban yarinyar ya saya masa kaya dayawa da abubuwan amfani san nan ya gyara ma yarinyar ɗakin ta an mata ciki da palo har da fenti gashi yarinyar tazo da abubun ta dayawa har da su kayan kallo da su gas da kayan abinci na zamani kullun zata girka kaji da shinkafa bata taɓa tsanmana ba sai dai taci ta ragewa baban Sadiq ya fito waje idan ba wuta yana cin ragowar ta yana washe baki ni ko ajiki na dan Sadiq yana iya kokarin sa wani lokaci idan ya samu kuɗi a garejin su sosai har kaza nima yake sawomin gasashe muci da shi da Yasuf mu ɗebawa maman Hanan da Hanan ɗin ta, maman Hanan ma ta kasa jurewa shi ne suka fara sana'ar awara a kofar gida ɗan su ciyar da kan su baban Sadiq ya sallama mu ba ruwan sa da mu baya bamu ci baya bamu sha bare sutura ko idan bamu da lafiya ya nema mana magani kwata kwata ba ruwan sa da mu damu da babu duk ɗaya ne awajen sa daga ni har maman Hanan ya fita sabgar mu, ko mutuwa zamu yi mu mutu shi ba ruwan sa kullun yana wajen amaryan sa gashi yarinyar bata da kunya ga masifar bala'i idan rashin Kunyar ta ya motsa sai Sadiq na min wanki kaya na sai ta kwaso nata ta zuba masa tace ya wanke idan yaki sai ta sa baban shi, shi kuma gudun ta sanya babansa yasa sai ya ansa wankin nata ya wanke mata Yusuf ne dai baya ɗaukan iskancin ta shi yana da zafin rai sosai ga saurin fushi sau biyu baban sa na korin sa daga gidan saboda ita sai naje na bawa amarya hakuri san nan tasa babansa ya hakura ya barsa ya dawo gidan sau biyu wallahi yana korin sa ni kuma ba zan iya ganin sa yana yawon neman wajen kwana gidajen abokai ba gwara dai duk wuya ya zauna a gaba na ina kallon sa yadda rayuwar yanzun nan ya lalace yaro na gaban ka ma ya kacika bare baya ganin idon ka shi yasa ma bana damuwa nake zuwa na zube a kasa na roki amarya ta sa babansa ya hakura ya bar shi ya dawo, Sadiq da kuke ganin nan sai dai in ce Allah ya bawa yaron nan aljanna wan nan murmushi dake kan fuskar sa kullun dan dole yake yin ta idan kuka tona ciwon dake zuciyar yaron nan sai kunyi masa kuka" ta kai karshen maganar tare da goge hawayen dake idon ta "Tab ɗijam lallai maman Sadiq kina cikin jarabawa to Allah ya baki ikon ci, wannan wani irin zalunci ne duniya ina zaki da mu ya za'ayi ba zamu rinƙa fuskantar fushin Ubangiji ba irin wan nan zalunci har ina, ace mutun sai son abun duniya ka haifi yara ba ruwanka da su ba ruwan ka da cin su shan su suturan su bare tarbiyyar su ka zubar da su har ma da matan ka wan nan wani irin abu ne wan nan zamani Allah ka kawo mana sauki" cewar Mum "Amin" maman Sadiq ta amsa da shi ita dai gwaggo shiru tayi abun duniya sun taru sun mata yawa akai shiru wajen yayi ba wanda ya sake magana ita kuma Jehan tana ɗaki tana latsa waya. KANO da sallama Dr ya dawo palon, jelly na zaune a wajen da ya barta rungume da dolly har barci ya fara ɗaukan ta, jin sallamar tasa ne yasa tayi saurin waro idon ta waje tana faɗin "Welcome Uncle" murmushi ya sakar mata kafin yace "Yauwa jellyn dady" ya kai karshen maganar tare da zama gefen ta ya sanya hannu ya ansa dolly ya haɗa allura ya fara mata, kuka jelly tasa tare da runtse idon ta tana faɗin "Wayyo Allah na" da sauri dr ya ɗago kan sa yana faɗin "Lafiya jelly?" Cikin kuka tace "Uncle dan Allah kayiwa dolly allura a hankali kaji? Nasan yanzu tana jin zafi" kallon ta da kyau yayi tsabar haushi kamar ya kwashe ta da mari a ransa yana faɗin "Wallahi ba dan cameran dake palon nan ba da kin sha mari yan iskan yara iyayen ku sun lalata ku dan rashin aikin yi irin na iyayen naku yanzu uban ki ya sa kuɗi ya sawo wan nan hauka ga talakawa can suna kwana da yinwa ba irin kuɗin da baya kashe wa kan wan nan ɗan iskan karen duk saboda ke, shigiya da wani fuska kamar anyi ɓarin kunu a cikin kasa" da sauri ɗayan ɓangaren na zuciyar sa yace "A'a Sadiq kai kan ka kasan Jelila kyakkyawa ce ajin farko" tsaki yaja a ransa tare da danna alluran da karfi yayiwa dolly har sai da ta fasa ihu da sauri jelly ta miƙe jin kukan dolly idon ta a rufe ta nufi staircase tana kuka tana faɗin "Uncle idan ka gama ka kirani" yana kokarin jan tsaki sai ya tuna akoi camera a palon hakan yasa yayiwa dolly aiki mai kyau ba dan yaso ba. Bayan ya kammala komai ya sake dolly da gudu ta haura sama tabi bayan Jelly tana yar ƙara miƙewa dr yayi ya fice daga palon yana jan tsaki a ransa yana tunano irin kyan jelly. Ita kuwa jelly tana shiga bedroom ɗin dadyn ta, ta haye katafaren gadon sa ta kwanta tana kuka tana yiwa dolly addu'a, bata san lokacin da dolly ta shigo ɗakin ba sai jin ta tayi a jikin ta cikin sauri ta buɗe ido tare da miƙewa zaune nan take murnushi ya kubce mata ta rungumi dollyn ta suka kwanta tare tana murna da murmushi a face nata har barci ya ɗauke ta. KADUNA zaune suke cikin wani katafaren palo na alfarma mai ɗauke da manya manyan sofa set masu numfashi, set 2 launin Ash da milk palon ya kawatu iya kawatuwa yaji komai da ake buƙata idan nace zan tsaya zayyana muku kyan palon nan to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba, tsala tsalan yan mata ne su biyu kamanin su ɗaya, sai dai babban farace tas karamar kuma chocolate color ce jikin su jikin hutu ne suna sanye cikin shiga iri ɗaya wandon jeans baki da t-shirt pink color kayan sun matse su babban cikin su zata kai 20 years ta zuba kitson uban attachment kanana a kan ta wadda yazo mata har bayan ta, ita kuma ɗayan bazata wuce 18 years ba bata yi kitso ba ta tara gashin ta ɗaure a tsakiyar kai ba laifi tana da gashi har bayan wuya ga gashin nata bakin kirin mai tsantsi da sheki dukkan su ba ɗan kwali a kan su babban cikin su na rike da wayar ta kirar iphone 13 ita kuma karamar tana rike da Samsung A72 suna zaune saman sofa mai zaman mutun 3 ko wacce kan ta na kan wayar ta tana latsawa, da sallama wata yar matashiyar mata ta shigo palon ta sauko daga sama bene tana sanye cikin wata dakakkiyar lace blue da ratsin fari ɗinki bubu gown wuyan ta da hannun ta sanye suke da dankareriyar sarka da abun hannu mai matukar kyau da kyalli tayi kwalliyar ta sosai ta fita ras yar cakwai da ita wankan tarwaɗa ce matar a shekaru bazata wuci 24 years ba kafar ta na sanye cikin takalma flat shoe fari duk in da ta taka sai takalmin yayi kwas kwas har ta kariso cikin palon kai tsaye ta nufi saman katafaren dining table dake shirye da kayan abinci kala kala tana faɗin "Aafia kuzo mu fara breakfast Abbin ku na fitowa yanzun nan" ko kallon in da take basu yi ba suka ci gaba da latsa wayar su suna turɓune fuska idan da sabo ta saba bata damu ba, dan basu tanka taba ta wuce ta zauna saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin tana kokarin buɗe kulolin abinci wani kyakkyawan mutun ya sauko daga saman benen mai ɗan jiki kaɗan fari tas da shi kamar balarabe gashi da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo yana da manya manyan ido kamar bull ga dogon hanci, kaman sa ɗaya da wadda aka kira da Aafia, suna ganin ya sauko suka miƙe da gudu suka nufe sa suna faɗin Abbi oyoyo rungume su yayi tana faɗin "Good morning my Angle's" "Good morning Abbi how was your night?" Cewar Aafia kafin ya amsa cikin shagwaɓa Umaisha tace "Abbi I'm feeling hungry let's go and eat" shafa lallausan gashin kanta yayi kafin ya riko hannun Umaisha suka nufi table ɗin Aafia tabi bayan su lokacin Aunty su ta gama zubawa kowa abincin sa a plate ɗin sa ta zauna tana jiran su kariso, cikin nitsuwa Abbi ya zauna saman kugeran dake kusa da Auntyn su yana faɗin "Amarya barka da safiya har kin tashi?" Turɓune fuska Aafia tayi a kule tace "Ke Umaisha ni zan zauna kusa da Abbi fa" turo baki Umaisha tayi a shagwaɓe tace "Wallahi ba zan yarda ba ai nice karama" taɓe baki Abbi yayi yana faɗin "Ke Aafia baga waje kusa da ni ta ɗayan gefen nan ba ki barwa Umaisha gefen daman tun da itace karama" kallon gefen ido Aafia tayiwa gefen hagu na Abbi in da yake nuna mata ta zauna kara turɓune fuska tayi a ranta tana faɗin "Allah ya kiyaye na zauna kusa da wan nan stupid ɗin" ganin tayi shiru yasa Abbi yace "Umaisha na yi hakuri kizo ki zauna ta site ɗin nan kinji? Ki bar mata nan ɗin" ba musu Umaisha ta dawo ta gefen hanun nasa kusa da Auntyn su ta zauna ita kuma Aafia ta zauna gefen daman sa a tare su suka jawo plate na abincin su gaban su ita da Umaisha shi ma Abbi ya jawo na shi a nitse ya ɗauki spoon Aafia sai satar kallon sa take ta kasan ido, yana kai abincin bakin sa a sukwane ya miƙe tsaye tare da fitar da abincin yana faɗin "A uzubillahi Halima menene haka?" waro ido waje Aunty tayi tare da miƙewa tsaye ita ma tana faɗin "Me ya faru?" Cikin fushi yace "Tambaya ta kike ki ɗan ɗana abin cin mana kiji yau shi ne ranar ki ta farko da kika fara girki a gidan nan a matsayin ki na amarya mai makon ki farantawa mijin ki rai shi ne zaki min wan nan shirme? Idan kin san baki iya girki ba tun farko me yasa kikace min baki son masu aiki sumin girki zaki min kamar abun kirki eh? Wannan wani irin abune buhun gishiri nawa kika zuba a cikin abincin nan saboda Allah?" Hannu na rawa Aunty ta sa hannu ta ɗauki spoon ta ɗebi abincin dan ta ɗan ɗana taji tana kai wa bakin ta ta fitar a sukwane tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun me hakan kuma wallahi Abbi Ni bansaka gishiri ba a girkina kwata kwata" a fusace Abbi ya juya ya bar palon ba tare da ya sake magana ba miƙewa Aafia tayi cike da rashin kunya tace "Ke idan kin san baki iya girki ba me zaki wani ce zaki yi eh? Yanzu duba asarar abincin da kika yi fa wato dan baki san darajan abincin bako? Dan ba tsohon ki ke nemowa bako? To wallahi kibi a hankali bazaki zo nan kimana shirmen ƴaƴan talakawan nan ba daman ance ku baku iya samun waje ba to ki shiga hankalin ki, ki nitsu ki dai na rawan jiki dan kinga abinci Available a nan babu a house kizo ki fara mana ɓarna kamar wata rat" zuba mata ido Aunty tayi tana kallon ta idan da sabo ta saba da rashin kunyan Aafia sai dai a sati ɗaya da tayi a gidan Aafia bata taɓa mata rashin kunya mai muni da zagi irin na yau ba kasan cewar iyayen ta basu da karfi talakawa ne yasa take hakuri da rashin kunyan Aafia dan kar taje ta kulata Abbi ya sake ta dan tun kafin suyi Aure ya sanar da ita akan ƴaƴan sa zai iya komai saboda sune ma yasa ya jima bai yi Aure ba, Fuuu Aafia ta wuce ta haye saman bene tana surfa masifa, miƙewa Umaisha tayi ta nufi saman bene tana faɗin "Sorry Aunty sarkin iya girki" ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya ta haye sama, shiru Aunty tayi ta kasa motsawa daga in da take tsaye tunani take yaza ta ɓullo wa matsalar gidan nan waye kuma ya zuba mata gishiri a girki ita dai tasan kwata kwata ma bata sanya gishiri a girki ta ba, tana tsaye a wajen har Aafia ta fito sanye da wandon jeans ja da riga fari mai dogon hannu ta ɗaura wani ɗan karamin handkerchief a kan ta wadda ya tsaya mata iya goshi kawai ta zubo kitson huɗu gaba biyu ta gefen nan biyu ta gefen nan ta sanya high heel fari a kafar ta tana riƙe da makullin motar ta da jakar ta da waya tazo ta wuce Aunty ta fice daga palon taje ta shiga dan kareriyar motar ta kirar discussion continue ta figi motar da gudu ta bar gidan, Share fisabilillah 👏 💋Star Lady 💋 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf STAR 🌟 LADY..✍️ *💋The beginning💋* Episode 4 .....Still Aunty na tsaye a wajen har Umaisha ta fito shirye cikin atamfa ɗinkin doguwar riga kayan sun mata kyau sosai kuma basu wani matse ta sosai ba sun dai zauna cif cif a jikin ta, ta ɗaura ɗankwalin kayan ɗaurin ture kaga tsiya ta yafo gyale yar karama fari a kafaɗa, ta sanya flat shoe fari a kafar ta hannun ta ɗaya riƙe da yar jakar ta fara, ɗayan hannun kuma riƙe da wayar ta da key ɗin motar ta tayi kyau sosai, har ta kai bakin kofar palon zata fita sai kuma ta juyo tace "Aunty idan Abbi ya fito kice masa na wuce School" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta fice daga palon taje ta shiga motar ta kirar continue continue ta bar gidan, Jiki a mace Aunty ta koma ta zauna saman kujerar table ɗin tana mamakin waye ya sanya mata gjishiri a abinci ta, shirye cikin suit Abbi ya fito hannun sa riƙe da jakar computer sa kai tsaye wajen da Aunty take zaune ya nufa a takai ce yace "Zan fita kina bukatar wani abun ne?" Da sauri ta miƙe tsaye tana faɗin "Dan Allah Abbi kayi hakuri" guntun murmushi yayi kafin yace "Shike nan komai ya wuce amma dai ki kiyaye gaba zan sa akawo wasu masu aikin tun da kin sa mun sallami wayan can kuma gashi kin zo baki iya girkin ba dole nasa a nemo wasu" ya kai karshen maganar tare yin hugging nata ya manna mata kiss a goshi kafin ya sake ta ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin "Ki kula min da kan ki na baki amana" "To mijina sai ka dawo Allah ya tsare min kai yauwa Abbi Umaisha tace na faɗa maka ta wuce School" jinjina kai yayi kafin yace "okey ki musu addu'ar Allah ya tsare min su" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palon murmushi tayi tana godewa Allah daya sa Abbi shi mutun ne mai saurin sauko wa idan yayi fushi, cike da kwarin gwiwa da fara'a ta kwashe kayan abincin ta mai da su kitchen ta haɗe abincin waje guda ta zuba cikin kwando ta wanke kwanikan ta gyare ko ina san nan ta fito ɗauke da kwandon abincin taje ta miƙawa baba mai gadi akan yaje waje ya zubar sannan ta dawo ta haye sama ta koma bedroom nata ta haye gado ta kwanta tana mai da numfashi. RIMSHA Gudu yake da motar sosai kamar zata tashi sama a tsakiyar dokar daji mai cike da dogayen bishiyoyi masu ganye kore shar, saboda cikan ganyen bishiyoyin yasa wajen yayi duhu sosai kamar dare, baka jin motsin komai a wajen wajen shiru, gudun bala'i yake shararawa da motar nan wadda da ka gan shi kasan gudun cetan rai yake ko kuma na rashin gaskiya, Sun shafe 2 hours suna sharara gudu a dokar dajin nan suna keta bishiyoyi kafin su isa wani katon waje mai girman gaske wan da ke cike da yashi fari tas mai laushi har kyalli yashin yake, suna shiga wajen yashin ya rage gudun motar kasan cewar yashin yayi yawa tayar motar ba zata iya wani gudu sosai a wajen ba waje ne mai girman gaske dan sai da suka safe 1 hour suna tafiya cikin yashin kafin su fita ya keta ta cikin wasu bishiyoyin masu ban tsoro sun kewaye wajen sun yi kamar raun ta cikin su ya biyo duhune mai tsananin gaske a wajen haka ya kutsa motar sa ya wuce su ya ɓullo gaban wani katon gunkin kan mutun wadda jini ke zuba daga bakin gunkin kasan gunkin an kewaye kamar rijiya a nan jinin ke taruwa kamar kogi, gunkin shi kaɗai ma mutun ya gani ya isa ya sa shi mutu ko suma saboda ban tsoron sa idan ka ganshi kai kace yana da rai dan an gina idon sa a buɗe ga fari da baki irin na idon mutum ga kuma hawayen jini da ke fita daga idon na shi da baki da hanci yana da hanci mai girma gari guda girman kan gunkin nan ya kai girman kan traila ga tsawo ga faɗin daga saman goshin gunkin an rubuta *DAULAR MUTUWA* da manyan baki sun fito ɓaro ɓaro san nan aka zuba jini a wajen ya dawo ja kai da ganin wan nan ko ba'a faɗa maka ba kasan gidan mutuwa ne ba gidan zaman lafiya ba, Yana zuwa dai dai gaban gunkin motar su ta ɓace ɓat ta fito cikin wani katafaren gida mai girman gaske kamar gidan fursina kashe motar yayi a tsakiyar gidan ya fito yana miƙa kamar wadda ya taso daga barci, wasu kartin mutane su biyu masu kama da samudawa bakaƙe kirin kamar wayan da aka yiwa fenti da gawayi kai da gani kasan wayan nan cin namar mutane suke idon nan nasu jawur kamar jini ga katon hanci kamar tukunya suna da tsawo ga kiɓa wayan nan idan suka ɗaura maka hannun su ɗaya a kan ciki to fa sai dai wani ba dai kai ba, gashin kan nan nasu a tsai tsaiye kamar ƙawo gashi dogo ya musu kamar jijiyar bishiya suna da bala'i muni kamar a yanka a ɓuye wuka, duk in da suka yi taku ɗaya sai kaji kasa ya bada dim ɗim saboda girman su, matashin saurayin nan na tsaye har suka kariso wajen sa ɗaya daga cikin sune yasa hannu ya shafa kan mata shin, nan take matashin ya riƙiɗe ya dawo jibgegen kato baki mummuna mai katon hanci sai dai bai kai su girma ba ɗayan ne ya buɗe kofar motar cikin wata iriyar murya mara daɗin ji mai bada sautin amo mai kara kamar ganga da yaren su na matsafa yace "Barbushi yau ma yara huɗu ne aka samu fa" wadda aka kira da Barbushi ne ya kalli matashin da ya rukiɗe yanzu ya zama kato yace "Zaka iya tafi aikin ka ya kammala sai mun haɗu a aiki na gaba" ba musu Saurayin ya wuce ya nufi cikin gidan yana taku kasa na bada dum dum kamar ganga saboda girman ƙafarsa, dawo da kallon sa Barbushi yayi kan ɗayan daya buɗe motar da murya kamar an tada injin markaɗe in jin ma irin lalataccen nan mai kara mara daɗin ji mai rikita ƙwaƙwalwa yace "Kai Santilago ka kwashe su ka kai su ɗaki daban daban zuwa gobe da safe idan gimbiya ta fito sai muji me zata ce" Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar komawa cikin gidan yana taku ƙasa na bada dum dum har ya shige ta wata ƙatuwar kofa mai ɗauke da tambarin wata mata tsaye ba kaya a jikin ta, ga malalen jini nan kwance cikin idon matar ga idon nata sun yi ja bakin nonon ta duk jini ke zuba aka zana ta, shi kuma Santilago ya sanya hannu ya ɗauko Rimsha dake sume da hannu ɗaya ya ɗauko ɗaya daga cikin yaran ma da hannu ɗaya ya saɓa su a kafaɗar sa san nan ya ɗauko saura biyun yariko kafofin su kan su na lilo na kallon ƙasa haka ya wuce da su ta wata faffaɗar hanya dake ɗan gefe da kofar da Barbushi yabi yana tafiya kasa na amsawa nan ya rinƙa wuce ɗakuna masu burglaries kamar gidan fursina ba abun da ke tashi daga ɗaku nan face bala'i warin jini wani ɗakin kuma kaga akoi yara a ciki wani kuma sai dai kaga kashi ko wani sassa na jikin mutane, dai dai wata katafaren gate dake wajen ya tsaya, da gudu wani mutun wadda da ka gan shi kasan cikakken bil adama ne, yazo da gudu ya ɓuɗewa Santilago gate ya wuce da su Rimsha ciki, yana shiga wasu kantin mutane kusan kamar sa suka rufa masa baya su uku, ko wacce ɗaki daban ya kai ta Rimsha itace ta karshe suka kai ta wata ɗaki dake karshen ginin suna kokarin buɗe kofar ta farfaɗo daga doguwar sumar da ta faɗa kafin tayi wani yun kurin Santilago yayi wurgi da ita cikin ɗakin suka jawo kofar dafaffiyar karfe mai karfin gaske suka kulle suka sa key suka juya suka bar waje. Ɗaki ne mai matikar duhu baka iya ganin komai a ciki ko yatsun hannun ki baki iya gani, ga bala'i wari jini mai sa tashin hankali da tashin zuciya dake fitowa daga cikin ɗakin. Da kyar ta iya miƙewa zaune jiri na ɗibar ta sabida bala'i yinwa da take ji a sukwane ta toshe hanci lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta waro dara daran fararen idon ta waje tayi ko zata samu daman ganin wani abu sai gwale idon take tana bin ɗakin da kallo tana toshe da hanci da hannu ɗaya ko tsillin tsinke idon ta ya kasa iya gane mata a ɗakin saboda tsananin duhu, motsin ta fara ji daga ɗan nesa da ita, a sukwane ta takure jikin ta waje guda saboda tsoro ta runtse dara daran idon ta tana ambaton sunan Allah ji tayi an ɗan taɓa ta a bayan ta hankali tashe ta yi saurin waro idon ta waje tare da juyawa a sukwane tana faɗin "wanene? akoi wani a nan ne?" ji tayi an kwashe da wata mahaukaciyar dariya da wata murya mara daɗin ji kamar na aljanu, daga ɗan gefe kuwa wata iriyar siririn murya mai kama dana baby's taji ana kuka da shessheka kasa kasa, a razane tamike tsaye tana ja da baya tana faɗin "Dan girman Allah idan akoi mutane a ɗakin nan kumin magan kar ku haukatani ku dai na kukan nan mu rungumi Allah, Allah zaiji kukan mu zai kawo mana ɗauki" tayi maganar cikin harshen turanci ihu aka kurma da wata katuwar voice irin na yan shaye shaye, a sukwane ta toshe kunnuwan ta da hannayen ta dan ihun mai rikita ƙwaƙwalwa ne ba zata iya ji ba kan ta zai fashe nan take ta fara hawayen tsoro. kamar daga sama taji an cire hannayen nata daga kunnuwan ta ana mata kukan mage a kunne, ihu ta fasa tare da bazama cikin duhun kamar mahaukaciya. muryoyi uku uku ne suka fara fita lokaci guda ɗaya na dariya ɗaya na kuka ɗaya na wani irin abu kamar wakar shaiɗanu aljanu daga gefe guda kuwa kukan mage ne mai sautin gaske ke tashi, idan ta toshe kunne sai a buɗe mata idan tayi ihu suma abubuwan su kara sautin nasu ihun idan ta zauna shiru taji ana taɓata ga ɗakin duhu baka ganin komai. Hawaye ta fara yi sosai wani na bin wani tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta daga ciki har da addu'ar san ya sabon kaya wato اَلحَمدُ لِلهِ الَّذِي كَسَانِي هَذَ (الثَّوْبَ) وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَولٍ مِنِّي وَ لَا قُوَّةٍ Haka ta rinka gero Addua'o'i sai ta kama wan nan bata kai karshen ba ta sake ta kama wani ga hawaye wani na bin wani a kuncin ta ga bala'i yinwa da take ji lokaci guda ta fita hayyacin ta ta zama kamar zautatciya, tun tana iya jero addua'o'i har ta fara jin duniya na juya mata harshen ta yayi mata nauyi saboda yinwa a hankali ta sulale kasa warga jam ta baje bata ko motsi, tana faɗuwa suma abubun sukayi shiru tsit kamar babu su a ɗakin. Aafia Zaune take saman kujerar table dake cikin E,library dake cikin Greenfield university kaduna tayi shiru, kan ta na kan wani book da take karan tawa ga wayar ta da key motar ta a gefen ta jakar ta kuma yana ɗayan gefen nata, cikin takun ƙasaita wasu haɗaɗun yanmata su uku suka shigo cikin Library'n dukkan nin su suna sanye cikin wandon jeans da t-shirt sun zubo gashin dokin nan har baya kamar nasu, kai tsaye wajen Aafia suka nufa suka zauzzauna saman sauran kujerun dake table ɗin da Aafia ke zaune kallon su ta kasan ido Aafia tayi kafin ta ɗago kai tare da cire katon glass ɗin dake face nata tana faɗin "Yan mata ya kuke?" Ɗaya daga cikin sune tace "Yar Alaji ko in ce hajiya da kan ta tun ɗazun muke neman ki bamu gan ki ba can muka haɗu da Umaisha wajen Masallaci shi ne take faɗa mana kina nan" guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Ku dai bari ina da Exam on Wednesday ne that's why nake karantun" ɗaya daga cikin sune tace "Ke dalla Rufee ba wan nan ba mu yanzu Afi baby ki faɗa mana ya kika yi da wan nan shegiyar kwailar Amaryan Abbin ku nan?" Turɓune fuska Aafia tayi tana turo baki kamar biro tace "Rabu da shegiya wai ni zata wa iskan ci jiya har da wani zuwa bedroom na dan munafurci tana wani cemin wai mu haɗa kai mu zama abu guda mu zama friend hmm zata yi bayani ne Allah sai ta bar gidan nan because I don't like her at all I hate this woman over wallahi shi kuma Abbi har da wani cewa zai kawo wasu masu aiki dan yau na zuba mata gishiri a abinci Allah ba wata house girl da zan bari ta zauna a gida duk wadda aka kawo sai na san yadda zan yi na koreta ita Amaryan ita zata yi girki kuma mu rinƙa bata girkin duk wani aikin da tayi sai na ɓata a haka har Abbi ya gaji ya sake ta mu huta Allah ba wata mai aikin da zata sake zuwa gida tayi aiki ita zata rinƙa aiki dan daman gidan su ai ba bu house girl" ta kai karshen maganar tare da zan dogon tsaki bushewa da dariya Rufee Anisa Amal suka yi suna tafa hannu "Wallahi Aafia karki bata wani dama karki kuskura ki bari ta samu sake a gidan ku idan ba haka ba zata samu ciki ta haihu da Abbi kuma hakan babban abun kunya ne a gare ku a ce kamar Abbi mutun mai manya manyan companoni wadda ake ji da shi a kasar nan ya auri yar talakawa kuma har sun haihu tab kofa ina zaku je in faɗa miki sai an rinƙa dan ganta ku da yaron da zata haifa wani lokaci ma sai kiga ana kwatan cen ku da gidan su amaryan ba da gidan Abbi ba" cewar Rufaidat buga table da karfi Aafia tayi tare da miƙa wa tana faɗin "it can't happen Rufaidat dole Halima ta bar gidan mu ko tana so ko bata so" Amal na kokarin yin magana Umaisha ta shigo da gudu tana faɗin "Aunty Afi, today your famous had accepted the invitation and he spoke on the Tv _CNBC Tv 18 Robin Roberts_ for almost one minute" ta kai karshen maganar tana nunawa Aafia wayar ta dake hannun ta a sukwane Aafia ta ansa wayar tana faɗin "What are you saying Umaisha do you mean yau TGA yayi magana har tsawon minti ɗaya bai tsaya ba" tayi maganar tana zaro ido gyaɗa mata kai Umaisha tayi tana faɗin "Duba ki gani yanzu nima na kunna data na gani sai sharing na video mutane suke yau TGA ya amsa tambaya har tsawon 1min yana magana" waro ido waje Aafia tayi tana kallon video kyakkyawan baturen dake magana cikin kyakkyawar turanci yana sanye da facemark a face na shi "Wow" Aafia ta furta tare da mayar da video daga farko ta sake gani a sukwane Anisa da Rufaida suka mike suka dawo kusa da Aafia suna kallon video taɓe baki Amal tayi tana makakin yadda su Aafia ke mutuwar son wan nan mutumin da wata kila ma bai san da zaman su ba a duniya kullun basu da wani zance sai zancen sa, ganin Aafia bata da niyar dai na mai da video daga farko tana sake kallo ne yasa Amal tace "Wai Aafia ni kam wanene TGA nan ne kullun sai kin dame mu da zan cen sa" cikin sauri Anisa tace "A'a sai ta dame ki dai dan ni ina ga ba wan da ya kai ni son ganin TGA wallahi kome nake idan lokacin kallon News akan Tga yayi sai na bari nazo na kalla ina bala'i son kallon face na guy ɗin nan sai dai kullun idan yan jarida na ɗaukan sa zakiga hoton ko video yana sanye da facemark ban taɓa kallon real face na shi ba sai dai dara daran idon sa light ash masu ɗaukan hankali masu kama da glass dan in ya waro idon na shi ko ya ɗago su ya kalli abu sai kiga kamar glass yana walkiya suma fa idon na shi wani lokaci yana sanya bakin glass ya rufe su, kai amma guy nan lamba ɗaya ne ya haɗu ta ko ina ba abun da yafi burgeni da shi ma irin sai yan jarida sun tasa shi a gaba sun sanya masa camera suna tambayar sa sai sufi 20mins suna jero masa tambayoyi suna jiran jawabi sai ya tattara gaba ɗaya tambayoyin nasu ya basu amsa ɗaya da batafi maganar 5 second ba shi ma sai ya ja musu aji sai yafi 2 mins kafin su samu amsan duk wanda zai ce miki ga kalan voice na guy ɗin nan a Nigeria kai bama a Nigeria ba har kasashen waje to ya miki karya dan ko magana yake ciki ciki yake magana kuma ga face mark a face na shi maganar tasa bata fita sosai kuma ni ban taɓa ganin in da yayi magana na tsawon 1min ba idan ba yau ba yanzu haka ki shiga media kiga yadda jama'a zasu yi ta rushing na kallon video yau yayi magana har na tsawon minti ɗaya" taɓe baki Amal tayi tace "To wan nan kam a wani gari yake? Abuja ko? Kuma ɗan waye a kasan nan? Mawaki ne ko ɗan film? Ni fa tun da kuke wan nan hauka ban taɓa sanin akan waye ma kuke ba kuma ni ba mai kallon News bace ni ko kallon film ma bana yi bare wani News" ta kai karshen maganar tare da gyara zaman ta, girgiza kai Aafia tayi tare da komawa ta zauna tana faɗin "Amal ni zan baki wan nan amsan ni zan faɗa miƙi who is TGA kina jin labarin *The General of the Army* ko baki ji shi ma?" guntun tsaki Amal taja tana faɗin "To ni ina ruwana da army's nifa ba abun da na sani kawai ki bani labari idan zaki bani amma ni bani da wata masaniya game da army's" gyara zama Aafia tayi kafin ta fara magana "TGA The General of the Army kenan namijin da ni banga kamar sa ba a duniya cikkaken gwarzo jarumin maza kaifi ɗaya ne shi ba mai iya tankwara shi Bature ne ɗan ƙasar *UNITED STATE OF AMERICA* a babban birnin*WASHINGTON DC* babban sojane da babu kamar sa duk wani sojoji da kike gani a *Usa* to a karkashin sa suke bafa wani babba bane, bai da shekaru sosai, kawai baiwa ce daga Allah ya ba shi he is 28 years amma akoi shi da farin jini ga kuɗi mulki tarin masoya Allah ya bashi amma fa Kirista ne ba musulmi ba gashi da bala'i izza kafin yayi magana sai ya ɗau wasu mintoci ina ganin kamar shi kaɗai ne wajen mum da dad ɗin sa, dan ɗan gata ne sosai kafin manya manyan gidan Tv su samu damar yin hira da shi suna shan wahala, wan nan gidan Tv da sukayi hira da shi yau ɗin nan ma a ka ce miki sau biyar suna tura masa takardan gayyatar nan, da kyar suka samu yayi accepted na gayyatar ta su yanzu ki shiga media kiga yadda media ta ɗauka an yi hira da TGA, kuma yayi magana har na tsawon 1min amma time to time yan jarida suna ɗaukan sa hoto wani lokaci a church ɗin su wani lokaci kuma a Airport haka idan yayi tafiya ya dawo" Aafia na kokarin ci gaba da magana Amal tace "Shirmen banza to ai na ku kuma kuka san shi iyayen gayyan soɗi ae, na kuka san shi da har kuke mutuwar kaunar sa haka? Mutumin da ba bahaushe ba, Bature kuma Kirista fa wata kilama bai san wata kasa Nigeria ba ku kuna nan kuna haukan banza bai san da ku ba" Cikin sauri Aafia tace "Ni dai a gidan Tv na fara ganin sa sai kuma a wani News da muke kallo ranar an ɗauke sa hoto yana saukowa daga jirgi ni ba ma abun dake burgeni da shi irin idan yana tafiya kiga jibga jibgan Bodyguards suna take masa baya ga wasu jibga jibgan sojoji a gefen sa wow ai na a jiye wan nan video nasa kullun sai na kalla na kasa goge ta kuma na faɗa miki wani lokaci yan jarida na ɗaukan sa a church na su wan nan hirar da kikaga anyi da shi ma kusan sau biyar a kace gidan Tv na tura masa takardan gayyata amma bai yi accept ba sai yau yayi musu bazata ko in ce ya mana bazata amma fa akoi wani guy a tik tok dake posting na video sa time to time har gidan Tv na ɗauka su ɗaura idan zasu yi labarai a kan sa sai su ɗaura wannan short ɗin video nasa karki ga jama'ar dake followed na Account na guy ɗin dake posting na shi a tik tok ɗin nan sunan sa Johnson yana da followas sama da 10 millon duk kuma saboda posting na TGA da yake yi kuma karki ɗauka kullun yake posting na shi a'a wani lokaci yana yin sati bai yi posting na TGA ɗin ba da zarar yayi kan kice me zaki ga viewers sama da 1 million kamar jira suke hmmm wan nan ma ba kowa ya taɓa kallon face ɗin TGA ba kina leƙa comments section na Johnson zaki ga jama'a suna faɗin handsome of the world ba mata kaɗai ba har maza faɗe suke kuma fa ba fuskar sa suka gani ba dan na faɗa miki kullun da facemark yake yawo ba abun da zaki gani sai idon sa light ash ɗin nan mai kyalli kamar madubi shima idon time to time yake zama ba glass amma a haka jama'a ke mutuwar son sa musamman hausawan mu sai kiji suna faɗin wan nan anya ba aljani ba kuwa dan kyan sa ya wuci ɗan adam tun ma basu karisa kallon ainihin kyan face nashi ba" shiru Amal tayi ta zubawa Aafia ido har ta kai karshen maganar san nan tace mata "Dan Allah Aafia nuna min wan nan The general of the army nan in ganshi dai yau kam cikin sauri Aafia ta ɗauko wayar ta, ta shiga gallery sauri sauri ta fito da video Tga jikin ta har rawa yake tace zo ki kallesa a gidan Tv a na hira da shi duk da ya sanya face mark zo kiga asalin kyau shi fa ko a cikin turawa ma number 1 yake" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa Amal wayar ta da sauri Amal ta ansa wayar ta fara kallon kyakkyawa Bature ne zaune saman wata haɗaɗiyar kujera mai matukar kyau da laushi face na shi sanye da face mark baki sai dara daran idanun sa kamar ball masu kyalli kamar glass kasan cewar kwayar idon nasa light ash ne, zubawa surar jikin sa ido Amal tayi yana da murɗaɗen jiki sosai ga faffaɗar kirjin kamar wani zaki duk da yana sanye cikin kaya ya ɗaura jaket mai matukar kyau da tsada a saman kayan na shi hakan bai hana faffaɗar kirjin sa bayyana ba, sau uku Amal na mai da video daga farko tana sake kalla ganin Amal bata da niyar dai na kallon TGA ne ya sanya Aafia ta anshe wayar ta tana faɗin "Ke ni bani karkije kiyi mafarkin sa" waro ido waje Amal tayi tana faɗin "Dan girman Allah Afi ki turamin duk wani videos nasa da kike da shi kuma ki faɗa min sunan account da ake posting na shi a tik tok da kuma gidan Tv dake News a kan sa time to time ɗin kinji?" Ta kai karshen maganar cikkin sigar rarrashi ba musu Aafia ta tura mata video TGA da take da shi dukka ta WhatsApp san nan ta an sa wayar ta tayi searching account ɗin Johnson tayi followed na sa sai murna Amal take da farinciki da haka sukayi sallama dan time ya tafi sosai Aafia da Umaisha suka wuce wajen motocin su kowa ta shiga nata Aafia na kokarin kunna motar ta Rufee ta kariso wajen da yar gudun ta tana kiran sunan Aafia sauke glass ɗin motar Aafia tayi tana faɗin "Lafiya Rufee kika yi wan nan gudun haka?" Girgiza kai Rufee tayi kafin tace "A'a ba lafiya ba daman ina son in ɗan tambaye ki kuɗi ne ɗazun sai na manta sai yanzu na tuna" jinjina kai Aafia tayi kafin ta ciro kuɗi daga jakar ta ta kirga 10k ta miƙa wa Rufee tana faɗin "Ban da sayan kayan haɗin shisha" Ansa Rufee tayi tana faɗin "In Sha Allah abu mai mahimmanci zan saya" tada mota Aafia tayi ba tare da ta sake yiwa Rufee magana ba ta figi motar ta bar wajen da gudu already ita Umaisha ta jima da tafiya Aafia na barin wajen Rufee tayi tsaki kana tace "Yar wahala uwar muce ke da zaki rinƙa hana mu shan shisha kema In Sha Allah sai na koya miki ba shan shisha kawai ba har da sha kwayoyi da bin maza sai kin koya sai na lalata miki rayuwa san nan na auri uban ki na mori dukiya duk na koreku daga gidan kin ɗauka a banza nake saki kike wa matar baban ki abun da kike matan nan ne yarinya dan kawai ki fitar min da ita ne ni kuma na shiga dan banson zama da kishiya wawayen yara kawai" ta kai karshen maganar nata tare da juyawa tana kaɗa 10k da Aafia ta bata tana murmushi ta bar wajen ta koma cikin department na su. KATSINA. Tafiya take hannun ta riƙe da leda baka mai ɗauke da kayan miya irin su tomator tattasai attarugu sanye take cikin doguwar riga abaya baka ta yafa gyalen rigar a kanta tana tafiya tana kwaɓe fuska kamar wadda taga kashi tun daga nesa Sadiq dake tinkarar majalisan su shi da wani mutun ya hangota murmushi ya saki yana faɗin "Nasir kaga waccan yarinya dake zuwa? Wallahi haka kawai yarinyar nan ta shiga rai na kome nake tunanin ta nake" kallon Jehan dake tin karo su Nasir yayi kafin yace "Lallai yarinyar nan tayi Sa'a kai da baka kallon mata baka taɓa kula ya mace ba har faɗa muke maka shi ne yau....bai kai karshen maganar ba ya dakata tare da kara waro idon sa waje yana kallon Jehan da ta kusa isowa in da suke dai dai lokacin su kuma suka isa majalisar tasu "Nasir lafiya kake kallon ta haka lafiya ka tsaya da magana?" Cewar Sadiq da kyar Nasir ya iya zama saman bencin majalisar tasu still idon sa na kan Jehan muryan sa har sarkewa yake yace "wan nan ba yar Alhaji Nawazudden Salman Sultan bane?" Da sauri Sadiq yace "Wanene kuma Alhaji Nawazudden?" Dai dai lokacin Jehan tazo zata wuce su cikin sauri Nasir yace "Jehan Nawazudden Salman" cak jehan ta tsaya kamar zata juyo sai kuma ta tuna abun da uncle Shitu yace musu akan su ɓoye kan su tuna hakan yasa cikin sauri ta wuce ba tare da ta juyo ba, cikin ƙaguwa Sadiq yace "Nasir meke faruwa ai na kasan Jehan?" Girgiza kai Nasir yayi yana faɗin "Sadiq shi ne matsalar ku, ku yan nan unguwar ba masu manyan wayoyi sosai awajen ku shi yasa baku ganin News da sauran su amma ina da tabbacin kasan Alhaji Nawazudden ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Apc ko?" Cikin sauri Sadiq yace "Eh ina jin labarin sa ance mutun ne mai adalci da kaunar talakawa salihin bawa bai da hayani ga taimakon na kasa da shi bai da girman kai" "Good to bari kaji Sadiq wan nan yarinyar da kake gani sunan ta Jehan Nawazudden ina followed nata a tik tok dasu Instagram Twitter dukka ina followed account nata i think itace kaɗai yar sa akoi ta da jiji da kai ga izza bata kula mutane bata ɗauki halin baban ta ba gata yar karama da ita sai izzan bala'i da rashin kunya" shiru Sadiq yayi yana tunanin to me ya kawo su Jehan nan kenan dafa shi Nasir yayi yana faɗin "Kasan cewa tun last week zancen baban ta ne ke trending a media wasu sunce ya ɓata wasu kuma sunce ya janye takarar sa ya barwa abokan hamayya to duk ma ba wan nan ba ajiye zancen Jehan a gefe ya maganar mu? ya kamata fa kai ma ka shiga irin sana'ar nan tamu akoi samun kuɗi over" dogon numfashi sadiq yaja tare da saukewa a hankali kafin yace "Wai wani irin sana'a ce wan nan da ka dameni tun satin da ya wuce?" Ɗan wawwaigawa Nasir yayi dan yaga ko akoi mutane, Ganin babu kowa ne yasa ya matso kusa da Sadiq sosai kasa kasa yace "Mutane muke kamawa mu kai su daji mu ɓoye su mu kira yan uwan su akan su kawo kuɗi mu basu yan uwan su idan ba haka ba zamu kashe su muna faɗa musu zamu kashe yan uwan su zakaga sun tsorata sun haɗo kuɗi da wuri sun kawo mana sai mu basu yan uwan su" kallon Nasir da kyau Sadiq yayi kafin yace "Wan nan ai sata ce Nasir ba sana'a bace kuma bai kamata kuna yiwa ƴaƴan talakawa haka ba" kara kasa da murya Nasir yayi yace "Haba Sadiq ya kake abu kamar wawa ne wannan ba sata bace amsan hakkin mu muke wajen masu kuɗi dan ba mu kama ƴaƴan talakawa ai sai ƴaƴan masu kuɗi dan mu ansa hakkin mu tun da basu bamu saboda Allah kaga ai hakan ba laifi bane kayi tunani ka gani yadda rayuwan yanzun nan ya zama ba mai taimakon yan uwan sa ko yana da hali kowa kansa kawai ya sani ko dan saboda maman ka da kanin ka suji daɗi su huta ya kamata ka fara wan nan sana'ar kuma kaga idan ka samu kuɗin nan zaka iya saya wa mamanka har gida da duk wani abun da zata ji daɗi ta buƙata" Jin Nasir ya ambato maman sa zata ji daɗi ne yasa ya tuna irin cin kashin da baban sa da amaryan sa ke mata saboda kuɗi hakan yasa yaji yana bukatar samun kuɗi shiru ya ɗan yi kafin yace "Ba komai Nasir na gode Allah ya bar zumunci In Sha Allah zanje na shirya sai musan ya zamuyi nan da gobe dai zan gama shiri" da murna Nasir yace "To abokina haka ake son namiji da zuciyar nema sai nazo gobe zan zo maka ma da babban waya ta yadda ma zaka san ba karamin kuɗi nake samu a harkan ba amma fa karka yi maganar nan da kowa kar ka faɗa wa kowa" ya kai karshen maganar tare da miƙewa yace "To sai mun haɗu gobe" hannu Sadiq ya ba shi sukayi musabaha san nan Nasir ya bar wajen ya miƙi hanyar fita daga unguwar, shiru Sadiq yayi yana tunani a kan Jehan shi ma Nasir yana tafiya yana tunanin ta yadda zai yi bincike a kan Jehan me ya kawo ta nan ta ɗayan ɓangaren na zuciyar sa kuma murna yake da ganin Jehan a nan sai ayyana wa yake a ransa kuɗi fansa da zai ansa idan ya sace Jehan ɗin a matsayin ta na yar ɗan siyasa, da wan nan tunani ya bar unguwar su Sadiq ya tare ɗan a caɓa ya hau ya bar layin gaba ɗaya To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please Share fisabilillah 👏 💋 Star Lady💋 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 *💋 TRIPLET'S💋* https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf STAR 🌟 LADY..✍️ *💋The beginning💋* Episode 5 Nasir na tafiya ba jimawa Sadiq ya miƙe ya bar wajen ya nufi gidan su Jehan. A ɓangaren jehan kuwa gudu gudu sauri sauri ta shiga gida babu ko sallama tun daga kofar gida take kwalawa mum kira da sauri mum ta fito daga cikin kitchen tana tabayar ta lafiya take kwala mata kira haka da sauri gwaggo dake zaune saman tabarma a tsakar gidan ta miƙe tana faɗin "Jehan are you okey?" A ruɗe Jehan tace "Mum yanzun nan kafin na shigo na haɗu da wancan dirty boy ɗin shi da wani dirty boy ɗan uwan sa kuma wancan ya gane ni har ya kira sunana da na daddy" waro ido waje mum tayi tana kokarin yin magana gwaggo ta riga ta da cewa "What? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun what are we going to do now?" shiru mum ta ɗan yi kafin tace "Jehan as from today kar ki sake fita ko ina just stay at home" gwaggo ne tayi saurin taran numfashin mum da cewa "Hakan yayi daman duk cikin ku nice face na bai zama popular ba so zan rinƙa zuwa cefene da sauran su" girgiza kai mum tayi tana faɗin "A'a Aunty A'isha hakan kuma ba zai yiwu ba gaskiya dole dai mu samo mafita batun kije ki rinƙa yo mana cefene da kan ki kam bayyi ba" "Mum why not na rinƙa using face mark to?" "Gaskiya Aunty A'isha munyi ganganci tun farko da muka manta da waye mu, muka saki face namu ga kowa muka bar Jehan tana zuwa in da ta ga dama lokacin da take so" jinjina kai gwaggo tayi cike da tashin hankali da damuwa tace "Maryam ina ganin Jehan ta rinƙa using face mark ko kuma mu sai mata face na roba da zata ɓatar da kamanin ta ko ya kika gani?" Jinjina kai mum tayi tana faɗin "Duk yadda kika yanke yayi" dawo da kallon ta gwaggo tayi kan Jehan tace "Go and wear face mask and go to market buy fake face" cikin sauri Jehan ta wuce cikin ɗaki, ta buɗe trolley ta ta ɗauko face mark ta sanya ta fito ta wuce ta fice daga gidan ta nufi kasuwa, tana fita sukayi karo da Sadiq zai shiga gidan nasu ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce yana ce mata sannu ko kallon sa ba tayi ba ta wuce murmushi yayi shi ko kallon ta ma yayi daɗi yake ji tsayuwa yayi ya suba mata ido tana tafiya har sai da ta kurewa ganin sa san nan ya wuce ya shaga gidan bakin sa ɗauke da sallama zaune ya isko gwaggo a saman tabarma a tsakar gida ita kuma mum ta koma cikin kitchen dan ci gaba da aikin ta saman kujerar da Jehan ke zama ya zauna yana faɗin "Ina wuni gwaggo?" Da fara'a gwaggo ta amsa da "Lafiya ya kake ya gida ya maman ka" "Lafiya Lou Alhamdulila ina mum?" "Tana kitchen" gwaggo ta bashi amsa "To bari na jirata magana nazo muyi da ita ne" jinjina kai gwaggo tayi ba tare da ta sake magana ba mum na kitchen bata san da zuwan Sadiq ba yana zaune shiru ita ma gwaggo na zaune shiru har Jehan ta dawo hannun ta riƙe da leda kasan cewar kasuwar nasu bai da nisa da gida kuma ta hau abin haka ne wato mashin shi yasa tayi sauri dawowa ba ko sallama ta shigo gidan ganin Sadiq zaune saman kujera da take zama ne yasa taja guntun tsaki ta wuce kusa da gwaggo ta zauna tare da kwanto da kan ta saman cinyar gwaggo tana faɗin "My gwaggo I'm tired" shafa curly hair ta gwaggo tayi tana kokarin yin magana mum ta fito daga cikin kitchen tana faɗin "Har kin dawo Jehan?" Gyaɗawa mum kai tayi ba tare da tayi magana ba "A'a babana yaushe kazo" kasa yayi da kai yana murmushi "Yanzu nazo mum ina wuni" da fara'a mum ta amsa masa tare da karisowa wajen ta zauna gefen gwaggo saman tabarma "Mum daman ina son yin magana da ke ne idan ba damuwa" ba tare da ta kalli in da yake ba hankalin ta na kan Jehan tace "To babana in taso muje gefe ne?" Girgiza mata kai yayi yana faɗin "A'a a nan ɗin ma yayi" "To ina jin ka" nan Sadiq ya kwashe yadda sukayi da Nasir akan kidnaping da yake son Sadiq yayi join na shi ya sanar wa mum san nan ya ɗaura da cewa "Naga ku kunyi karatu kuna da ilimi boko da na islamiya shi yasa nake son ki bani shawara shin yin hakan abune mara kyau ko kuma dai kamar yadda Nasir ya faɗa ba laifi hakkin mu zamu ansa" cike da tashin hankali mum tace "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunallahu wani'imal wakil haka fa mutanen nan suke amfani da wayan da basu yi karatu ba kuma talakawa masu neman na abinci su cucesu su lalata musu duniyar su da lahiran su kayi kyan kai babana da kazo ka tambaya da wani ne yaji kuɗi haka zai faɗa halaka wa iya zubilla ni yanzu gashi ban isa da zuwa police station ba kuma bamu da hujjan report na shi da mun sa an kama shi wan nan babban laifi ne babana, wadda idan aka kama mutun yana aika tashi kashe shi ake har lahira shawaran da zan baka a rayuwar ka kawatsar da duk wani aboki kayi rayuwan ka daga kai sai ɗan uwan ka san nan da kai da ɗan uwan naka duk ku rinƙa zuwa idan kun samu time Aunty A'isha ta rinƙa koya muku karatun Arabic har ma da boko dan ku fita cikin duhun jahilcin nan jahilci babban ciwo ne babana, babban bala'i ne jahilci yanzu ba yace maka zai dawo gobe ba idan yazo kace ya kara maka lokaci karka nuna masa kayi maganar ma da wani kuma karka nuna masa bazaka ansa tayin nasa ba idan kayi kuskuren nuna masa hakan tofa zai iya maka wani illar koma ya kashe ka dan gudun karka tona masa asiri a kama sa kabi da taka tsantsan kana ja masa rai duk lokacin da ya kawo maka maganar kace yayi hakuri kai ma kana son sana'ar amma ya ɗan kara maka lokaci a haka har ka rabu da shi san nan idan yazo anguwar nan ka rinƙa ɓuya karka na bari kuna haɗuwa kowani lokaci karkuma karinƙa gudun sa sosai har yazo ya gane In Sha Allah hukuma zata kama shi" da sauri Sadiq yace "Hukumar da bata da adalci bata wani yi mana Aiki basa son gaskiya bayan masu kuɗi kawai suke bi" girgiza kai mum tayi kafin tace "A'a babana falyakul Kairan auli yasmut karka haɗa hukuma dukka ka musu kuɗin goro ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba akoi na kirki kamar yadda a ko ina akoi na kirki da na banza suma hukuma haka suke idan kayi Sa'a ka haɗu da na kirki zaka ji daɗi, kuma zancen gaskiya hukuna na iya bakin kokarin su wajen ganin su gudanar da aikin su yadda ya dace wani lokaci abun ne yake fin karfin su amma suna kokari bance akoi wayan da basa aikin su yadda ya dace ba sai dai kasani su mutane ne ba Mala'iku ko aljani ba dole suna da a jizanci irin na ɗan adam wan nan shi ne kawai" ta kai karshen maganar tare da yin shiru tana kallon Jehan shiru wajen yayi ita dai gwaggo ta kasa magana saboda ganin abun take kamar a mafarki ita kuma Jehan bata ma san me suke cewa ba ta lumshe dara daran idon ta har barci ya fara ɗaukan ta can kome ta tuna tayi saurin waro dara daran idanun nata waje tana faɗin "Gwaggo this dirty boy he know everything about me because that stupid guy that talked about me is his friend they are together the time that the guy talked about me and dad" kallon Sadiq gwaggo tayi tace "Sadiq kasan wace ce Jehan yanzu ko?" Kasa yayi da kan sa kafin yace "Eh gwaggo" "Okey to kabar maganar iya tsakanin mu" jinjina kai yayi san nan ya miƙe yana faɗin "Mum Nagode sosai kuma zan yi yadda kika ce In Sha Allah" murmushi mum tayi san nan tace "To shike nan Allah yasa mufi karfin zuciyar mu" Amin ya amsa da shi san nan ya fice daga gidan miƙewa mum tayi ta nufi kitchen "Maryam ina son muyi magana a kan issue da Sadiq ya kawo yanzu" cewar gwaggo "To Aunty A'isha mu bari sai dare yanzu bari na ƙarisa girkin nan tukun nan" shiru gwaggo tayi bata sake magana ba ita kuwa Jehan barci ya ɗauke ta kan cin yar gwaggo. 💞💞💞💞💞💞💞💞 KADUNA Lokacin da Aafia ta dawo gida babu ko sallama ta shigo palon Auntyn su na zaune saman sofa mai zaman mutun 3 tana kallo a makeken Tv plasma dake sama TV stand sanye take cikin doguwar riga na dakakkiyar shadda blue color yasha aikin daga sama har kasa ta yi ɗaurin ture kaga tsiya tayi kyau sosai reras da ita tana zaune tana jiran Abbi ga kayan fruits a gaban ta time to time tana ɗauka taci, kallon sama da kasa Aafia ta mata cikin mutunci Aunty tace "Sannun ki da dawowa Aafia" dogon tsaki Aafia taja ta nufi bene tana faɗin "Babu a house ba dole a ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya a na ɗurawa ba dan ba tsoho ke nemowa ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi ɗakin su babu ko sallama ta banko kofar ɗakin tashige tana jan tsaki Umaisha na kwance saman gado har tayi wanka ta sauya kaya zuwa wando mai ɗan faɗi kamar palazo da yar riga mai karamin hannu kanta babu ɗankwali tana riƙe da wayar ta tana chatting, ta tada kai da pillow "Ke Umaisha yau kin yi magana da Yaya Irfan ne?" Aafia ta tambaya miƙewa zaune a tsakiyar gadon Umaisha tayi tana faɗin "A'a bamu yi magana da shi ba me ya faru?" Wurgi da jakar hannun ta Aafia tayi a saman gado tare da ɗaura key din motar ta da wayar ta saman bedside drawer ta nufi toilet tana faɗin "Babu komai naji kishin kishin kamar zai dawo ne" waro ido waje Umaisha tayi tana faɗin "who told you?" "I'm on my way coming back to hause Abbi called me dan yaji mun koma gida ne or not nan yake ce min wai kamar yaya Irfan zai dawo" da sauri Umaisha tace "Allah yasa karya dawo yanzu" daga cikin toilet Aafia tace "A'a karma ya dawo gaba ɗaya" "Haba Aunty Afi ya zaki ce karya dawo kuma?" "Eh mana Umaisha karya dawo, uban me yake mana idan ya dawo in ba ya takura mana ba ya samu sanya katon hijabi muje School gashi sai ya samana ido ya hana mu sanya attachment a kai ya hana mu sanya eyelashes wai shi ustaz duk wani jin daɗi na rayuwa sai ya hana mu shi yasa nake masa fatan karma ya dawo yayi zaman sa a can dan ni dai bana bukatar sa" taɓe baki Umaisha tayi tace "A'a ni kam ina son ya dawo amma ba yanzu ba sai mun samu hutu" dogon tsaki Aafia taja dai dai lokacin da take shiga cikin baf na wankan tayi shiru bata sake ce da Umaisha komai ba ita ma Umaisha komawa tayi ta kwanta ta ci-gaba da chatting da take yi 💞💞💞💞💞💞💞💞 KANO Karfe 5 na yamma dai dai dady ya shigo gidan jelly na zaune a palo tana rungume da dolly ga Nana da Zuwaira masu aikin girkin su nan suna zaune suna kallo a makeken Tv plasma dake saman TV stand, da sallama daddy ya shigo palon a gajiye da gudu jelly ta miƙe ta nufe sa tana faɗin "Oyoyo dady na" rungumota daddy yayi yana faɗin "My baby ya baki yi wanka ba?" Turo baki tayi kamar biro a shagwaɓe tace "Daddy kai nake jira ka dawo kamin ai" "Haba my baby na faɗa miki yanzu da kan ki zaki rinƙa yin wanka dan kin girma baki ganin ko su Nana na hana su miki wankan bane na faɗa miki tun last week bazan sake yi miki wanka ba ke da kan ki zaki rinƙa yi wato kenan kwana biyu da suka wuce ba kiyi wankan ba ko?" Kukan shagwaɓa ta sa masa a ruɗe yace "Haba my baby me abun kuka to yi shiru muje na miki" ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun ta tana rungume da dollyn ta suka nufi bene cikin girmamawa su Zuwaira suka gaida daddy tare da masa sannu da zuwa fuska a ɗaure ya amsa musu suka haye sama yana riƙe da hannun jelly, jelly ta fara girma amma taki yarda ta rinƙa wanka da kan ta ba yadda daddy bai yi da ita ba da suka shiga ɗaki akan tayi wanka da kan ta amma taki sosai daddy yayi nadamar saba mata da wanka da yake mata da tun farko ya bar su Zuwaira suna mata da duk haka bata faruba yanzu gashi ta fara kirgan dangi, dafe kai yayi ya zauna a gefen gado yana neman mafita dan gaskiya ba zai iya cigaba da yiwa jelly wanka ba a halin yanzu ta fara girma, "Daddy yaushe Yaya Imran zai zo" tayi tambayar cikin shagwaɓa jin ta ambaci sunan Imran yasa yayi saurin ɗago kai yana faɗin "Yauwa my baby jeki yi wanka da kan ki Yaya Imran naki na hanya" tsalle tayi tana dariya ta nufi toilet da gudu tana faɗin "Daddy ka kula min da dolly bari to nayi wankan" shiru yayi ya kasa magana yana tunanin yadda zasu kwashe da ita idan yau Imran bai zo ba zata iya kin cin abinci ma ta kwana da yinwa in dai Imran bai zo ba gashi Imran baya kasan ma gaba ɗaya, tunanin mafita sosai daddy yake yadda zai yi da jelly da kuma yadda za'ayi ta yarda ta rinƙa wanka da kanta kullun. Yana zaune awajen yana tunani ya kasa motsawa har jelly tayi wanka ta fito jikin ta duk kunfa bayan wuyan ta duk sabulu bata fita ba zuba mata ido yayi yana kara dana sani a ran sa "My baby jeki sake zuba ruwa da kyau a jikin ki sai ki dawo" turɓune fuska tayi ta juya tana turo baki ta koma cikin toilet ɗin a fili ya furta "dole mu dena kwana ɗaki ɗaya da ke kar nazo na miki aure nan ma kice sai da ni zaki kwana a gidan mijin naki" sosai daddy ya rinƙa dana sani a ransa yana kokarin miƙewa wayar sa ta fara kara a nitse ya fito da wayar tare yin picking ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Alhaji Zahraddeen yace "Hello maik Ya kake ya baby jelly" "Jelly tana lafiya amma yaya ya naji muryan haka?" Dogon numfashi Alhaji Zahraddeen yaja tare da sauke wa a hankali kafin yace "Dole kaji murya na haka ba, nashi ga damuwa ne sosai a kan gawar da a ka nuna a News jiya wai ta Nawazudden ne Allah sarki bawan Allah mutun ne mai adalci da kaunar talawa duk wani mai adalci a kasar nan sai miyagun ɓarayin gwamnatin nan sun san yadda sukayi suka kayar da shi" shiru daddyn jelly ya ɗan yi kafin yace "Hakane amma nifa abun yana bani mamaki yadda ya ɓata lokaci guda sannan daga baya a kawo gawa a ce mana yayi haɗari ne ya rasu bayan shi bai sanar da kowa zai yi tafiya ba mutane ma sai cewa suke bashi bane duk da fuskar gawar tayi jaga jaga ba'a ganewa amma jama'a sun ce ba shi bane ni abun da yake kara bani mamaki ina family'n sa? Ina suke ya a kayi sukayi ɓatan lokaci guda?" Jinjina kai yaya yayi kafin yace "Maik kadai na wannan tunanin na banza Nawazudden fa abokan hamayya suka kashe sa shi ne kawai family sa kuma Allah ne kaɗai yasan In da sukayi ko suma an kashe su an ɓoye gawan sune oho Allah dai shi ne masa ni a kan komai In Sha Allah gaskiya zata yi halin ta ai amma ko ni gawar da aka fitar jiya a kace gawar Nawazudden ne ban yarda ba gaskiya dan Nawazudden bai da jikin wan can gawar san nan farine tas kamar balarabe kamar sa ɗaya da first born na shin nan ina rokon Allah daya sanya family'n sa suna raye na haɗu da su na taimaka musu kamar yadda ya min ya taimake ni a rayuwa ta sosai" shiru daddyn jelly yayi ya faɗa doguwar tunani "Maik baka jinane?" Yar firgigit daddyn jelly yayi kafin yace "Ina jin ka yaya" "Ya batun Jelly da Imran?" "Eh yaya ka tun Jelly na da 2 years a duniya Imran yace itace matar sa kuma ba wanda zan bawa ita In Sha Allah sai shi" "Imran yana da kirki sosai in dai yazo kasar nan sai yazo har gida ya gaida ni" "Sosai ma yaya yana da kirki, Alhadulillah ita ma Jelly tana son shi duk da bata san me soyayya yanzu ba amma tana bala'i son ganin sa suyi hira sun saba kaga bani da wata matsala ta wan nan ɓangaren sai dai ɓangaren Hajiya Umaiya bana jin zatayi accept Imran ya auri Jelly ni na sani gidan nan ma a ɓuye yake zuwa idan ta sani bazata taɓa yarda ba" "Hmmm kai dai Maik ka ci gaba da addu'a amma Umaiya ta wuci tunanin mai tunani yanzu zan wuce gida zamu yi waya in na kai gida ban son ina driving ina waya" to daddy yace tare da katse kiran ya ɗago ya kalli Jelly dake zaune saman mirror chair ta tsaresa da manya manyan idon ta kamar ball "My baby lafiya? Yaushe kika fito wankan?" Murmushin tayi kafin tace "Daddy da uncle kayi magana ko?" Gyaɗa mata kai yayi ba tare da yayi magana ba "Daddy me yasa Umaiya ɗin ba zata bari ka aura min yaya Imran ɗin ba? Ita muguwa ce ko? San nan me auren da yasa ba zata bari ba me auren ke nufi" girgiza kai Daddy yayi kafin yace "She is your mother also don't call her wicked" turo baki tayi tana faɗin "She is a wicked daddy i don't like her she has a big head and nose she don't like people to come close to her everyday she's shouting and abusing people" dafe kai daddy yayi daman yasan halin Jelly kwata kwata bai lura da ita a wajen bane yasa yayi ta hira da yaya da yaga fitowar ta ai da bai zagi Hajiya Umaiya a gaban idon ta ba "Daddy what are you thinking?" "Go and wear your clothes first my baby" "No daddy ni gaskiya kai ne zaka samin" tayi maganar kamar zata yi kuka yana kokarin yin magana suka jiyo sallamar Zuwaira a bakin kofar shigowa a takaice daddy ya amsa mata sallalar da "Waalaikumussalam" daga ta waje Zuwaira tace "Daddy kana da bako a palo" "bako kuma?" Daddy ya tambaya da mamaki a face nashi dan shi dai bai yi da kowa zai zo gidan sa ba "Eh daddy bako" Zuwaira ta ba shi amsa "Okey gani nan zuwa" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya dubi jelly dake tsaye ɗaure da yar towel da bata gama rufe mata cinya ba "My baby ki sa kaya ki zo palo ki same ni muci abinci" bai jira amsar taba ya fice dan ya san halin ta yanzu idan ya tsaya jiran amsar tama wata rigimar zata tsayar masa. Yana fitowa palo idon sa ya sauka kan wani matashi dake zaune saman sofa mai zaman mutun 2 sanye yake cikin wando jeans crazy da riga t-shirt fara yayi wata iriyar aski irin na shararrun yan duniya bakin nan nasa bakin kirin yasha sigari yayi tatul gashi fari tas da shi hakan yasa baƙin bakin nasa ta kara fitowa sosai lokacin guda face ɗin daddy ta sauya daga annuri zuwa ɓacin rai ya kariso cikin palon ya zauna saman kujera 1 sitar yana faɗin "Muneer yaushe ka dawo?" Cikin wata iriyar katon murya kamar na yan shaye shaye Muneer yace "Yau da safe na iso tun ɗazun naso zuwa office naka amma ban samu dama ba sai yanzu nace bari nazo gida mu gaisa" "Okey yayi kyau ka kyau ta ya baban naka?" Muneer zai yi magana Jelly ta fito sanye cikin doguwar riga zuwa gwuiwar ta kayan sun ɗan matse ta kaɗan kan ta babu ɗankwali tana tafiya tana yauki tana kwaɓe fuska har ta kariso wajen daddy ta zauna saman cinyar sa a shagwaɓe tace "Daddy ya har yanzu yaya Imran bai zoba?" Kallon Muneer daddy yayi kafin yace da Jelly "My baby je ki fara cin abinci ina zuwa yaya Imran kuma yana hanya" "To daddy amma ka faɗa wa yaya Imran dan Allah yau kam yazo tare da Akila kaji?" Gyaɗa mata kai daddy yayi ba tare da yayi magana ba miƙewa tayi ta nufi table tana faɗin "Daddy dolly tayi barci" shiru daddy yayi bai amsa mata ba dan bai son jan magana da Jelly yanzu miƙewa Muneer yayi ya nufi table ɗin shima yana faɗin "Daddy nima abincin zan ci ai" ji daddy yayi kamar ya koresa daga gidan amma ba hali, hakan ya sa ya kakalo murmushi dole yace "To Muneer kai da gidan ku bismillah kaci mana" ya kai karshen maganar tare da miƙe wa shi ma ya nufi table ɗin Nana ce tazo tayi serving na su a tare suka ci abinci daddy na ci yana bawa Jelly a baki shi kuma Muneer yana cin na shi. Bayan sun kammala cin abincin ne Muneer ya musu sallama ya fice daga gidan ba karamin daɗin tafiyar sa daddy ya ji ba dan bai son Muneer bai son ganin sa ko kaɗan riƙo hannu jelly daddy yayi suka koma sama shi ya wuce toilet dan yin wanka ita kuma ta wuce ta haye saman katafaren gadon su ta kwanta kusa da dollyn ta dake barci. 💞💞💞💞💞💞💞💞 KADUNA Bayan Aafia ta fito wanka ɗaure da towel a kirjin ta wadda a iya cinya yazo mata kai tsaye gaban mirror ta nufa ta zauna saman mirror chair ta fara shafa lotions ɗinta masu kamshi da kyau da tsada "Aunty Aafia ina son in miki wata magana" cewar Umaisha ba tare da Aafia ta juyo ba tace "To sarkin magana ina jin ki" miƙewa zaune Umaisha tayi kafin ta fara magana "Dan Allah Aunty Afi ki dai na kula Rufee da Amal wallahi duk ba class naki bane gwara ma Anisa ba kuma ina faɗa miki hakan dan Rufee da Amal sun fito daga gidan talakawa ba a'a ina gaya miki hakan ne sai dan nasan ba dan Allah suke tare da ke ba ni ban hana ki ki kyautata musu kamar yadda kike yi ba dan nasan kece karfin su saboda ke Abbi ya ɗauki nauyin karatun su kiyi hakuri ki dai ma yawo da su a cikin School kin sani halin su ba mai kyau bane kowa yana gulman su a School nan amma sai ki rinƙa biye musu zaki jawa Abbi zagi a wajen jama'a dan Allah ba dan ni ba ki fita har kan su sam basu da ce da ke ba" miƙewa Aafia tayi bayan ta gama shafa mai ta nufi drawer kayan sawan su cike da izza tace "Umaisha har kinyi girman da zaki faɗamin da wan da ya dace nayi abota?" Cikin sauri Umaisha ta girgiza kai "To daga yau idan kika sake shiga harkata sai na ɓallaki ba ruwan ki da friends na kiyi harkan ki a School nima nayi nawa idan mun dawo gida shine muke sister's kin gane ko?" Gyaɗa mata kai Umaisha tayi dan daman tasan halin Aafia ma wuyacin abune ta yarda da shawarar ta komawa tayi jiki ba kwari ta kwanta ta ɗauki wayar ta tana latsawa tana tunanin yadda zata raba yar uwar ta da su Rufaidat ita kuma Aafia shiryawa tayi cikin doguwar riga bubu tana ja mata a kasa ta feshe jikin ta da perfume sannan ta ɗau wayar ta, ta fice daga ɗakin ta nufi garden na gidan dan shan iska. 💞💞💞💞💞💞💞💞 KATSINA Karfe 6 dai dai mum ta gama girki ta fito tayi wanka ta shirya musu abincin a saman taburma kamar yadda suka saba, sannan ta fito musu da daddumar da hijabi ita da gwaggo dan gabatar da sallar mangariba idan lokacin ya cika zama tayi saman tabarman tana faɗin "Jehan kizo ki ɗauki abincin nan ki kaiwa babana gidan su" Jehan dake zaune cikin ɗaki saman gado tana kokarin kunna wayar Rimsha tace "did you heard what you said mum? do you mean I should come and take food to that dirty boy place?" A kule mum tace "Jehan don't allow me to come and catch you, Allah ko kizo ki ɗauki abincin nan ko in zo in same ki" turo baki Jehan tayi tana jin bakin cikin yadda mum ke zubar mata da daraja, haka ta miƙe ba dan ta so ba ta ajiye wayar duka biyu daga nata har na Rimsha ɗin tana kunkuni ta fito babu hijabi tazo ta tsaya a kan mum tana faɗin "where is the food?" Da hannu mum ta mata nuni da ɗan ma dai dai cin foodflask dake gaban ta hannu jehan tasa ta ɗaki kulan ta nufi hanyar fita "Where is your hijab Jehan?" Cewar mum kara turo baki tayi kamar biro cikin murya kamar zata yi kuka tace "Mum I told you I don't like hijab please mummy stop talking to me about hijab" ta kai karshen maganar tare da ficewa daga gidan tana turo baki, sai da ta fita gaba ɗaya san nan tayi addu'ar fita daga gida ta nufi gidan su Sadiq tana kwaɓe fuska. A dakalin kofar gidan su ta isko sa tana isa wajen Yusuf ya iso ko sannu bata ce masa ba ta ajiye masa kulan abincin a gaban sa ta juya yana faɗin sannu ki na gode kamar bata san da mutun awajen ba ta wuce ta koma gida kallon sa Yusuf yayi kafin yace "Yaya Sadiq kaji labarin da naji kuwa?" Waro ido waje Sadiq yayi yana faɗin "Me kaji" girgiza aki Yusuf yayi kafin yace "Sudais kanin Fadil ne naji yana Faɗe wai Fadil yace sai yabi dare yayi wa Jehan fyaɗe tun da ta mare sa ba zai barta ba sai ya ɗau fansa" zumbur Sadiq ya miƙe dan yasan halin Fadil zai iya ai kata fin hakan ma mugu ne sosai "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun yanzu Yusuf me mafita?" Miƙewa shi ma Yusuf yayi yana faɗin "Mu bari zawa da safe muyi magana da mama muji me zata ce" komawa Sadiq yayi ya zauna shi ma Yusuf ya koma a zauna tare da jawo kulan da Jehan ta kawo musu ya buɗe tuwon shinkafa ne da miyar ɗanyen kuɓewa yaji nama da kayan haɗi sai kamshi ke tashi mayar wa Yusuf yayi ya rufe yana faɗin "Muje muci da mama ko?" Gyaɗa masa kai Sadiq yayi suka miƙe a tare suka shige cikin gida To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please Share fisabilillah 👏 💋Star Lady💋 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 *💞 TRIPLET'S💞* https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf *STAR 🌟 LADY..✍️* *💋The beginning💋* *Episode 6* Jehan na komawa gida babu ko sallama zata wuce ɗaki Mum tace "Come here" ba musu ta koma ta zauna kusa da mum tana faɗin "here I am" kallon tsab mum ta mata kafin tace "Whare is your fake face?" Sai lokacin Jehan ta tuna da furkar roban da ta sawo hakan yasa ta miƙe da sauri ta shiga ɗaki ta ɗauko ta dawo ta zauna kusa da mum dai dai lokacin gwaggo ta fito daga wanka ta zo ta wuce su ta shiga ɗaki dan shiryawa, mum da kan ta, ta taya Jehan sanya fuskar roban tana faɗin "Ko barci zaki yi karki yarda ki cire kinji" gyaɗa mata kai Jehan tayi, mum ta sanya mata fustar nan take kamannin Jehan ya ɓata, baka taɓa cewa ita ɗin bace, abinci mum ta zuba mata tuwon shinkafa da miyar ɗanyen kuɓewa ta tura mata gaban ta tana faɗin "Dauka ki ci" girgiza kai Jehan tayi kafin tace "Mum I can't eat this food, the food will not be delicious" kasa kasa mum tayi da murya cikin sigar rarrashi tace "My Jehan kina son farincikina na?" Gyaɗa mata kai Jehan tayi ala'amar eh "To buɗe bakin ki kici abincin nan kin ji ko? Idan kika ci I will be happy, idan kuma baki ci ba I will not be happy", a hankali Jehan ta buɗe ɗan bakin ta mum ta sanya mata abincin ji tayi kamar zata yi amai haka ta daure dan farincikin mum ta fara taunan abinci tana yamutse fuska ita kan ta mum tasan Jehan bata saba cin irin abincin nan ba kullum bata da abinci sai kayan zaki da snacks shinkafa ma sai jefi jefi take ci, haka ta rufe ido mum na bata abincin tana tauna kamar mai cin magani, har ta kai ta fara hawaye tana cin abincin, mum na ganin ta, amma ta kawar da kai dan tana son ta saba mata da rayuwar daɗi da wahala, suna wan nan hali gwaggo ta fito shirye cikin atamfa Holland mai matuqar kyau da tsada ɗinkin zani da riga ta ɗaura ɗankwalin atamfar a kan ta, gwaggo na zama Jehan ta faɗa saman jikin ta tare da sakin kuka mai tsuma rai sai lokacin gwaggo ta gane ashe Jehan ce ta sanya fake face ta sauya kamar ba ita ba "Why are you crying baby Jehan?" Sarai gwaggo tasan me takewa kukan, da gangan taki biye mata dan ita ma tana son Jehan ta saba da rayuwar da suke ciki yanzu. Da kyar gwaggo ta rarrashe ta, tare da lallaɓata, haka ta hakura ta ci abincin har ta ƙoshi, sosai mum taji daɗi cin abincin da Jehan ɗin tayi a ranta ta rinƙa godewa Allah tana addu'ar Allah yasa ta ɗore a haka kullun ta rinƙa ci Cikin shagwaɓa tace "Mum gobe zanje na wanke kai na a saloon" shiru mum ta ɗan yi kafin tace "A'a da safe zan wanke miki" kwanciya kan cinyar gwaggo Jehan ɗin tayi kamar za tayi kuka tace "My gwaggo ina kewar yar uwata ina so ganin ta ina take? Wani hali take ciki yanzu? Taci abinci ne? Ko bata ci ba Ina daddy na yake? Na san dukkan su shi da Siha na suna kewata suna son ganina su ma" ta kai karshen maganar tare da sakin kuka mai tsuma rai "Jehan ashe baki manta sunan da daddyn ku ke kiran Rimsha ba siha" cewar mum ita kuwa gwaggo hannu tasa tana gogewa Jehan hawaye ta tana kokarin danne nata hawayen kar su zubo ita kan ta mum dannewa take Jehan ta fama mata babban ciwo mai tsanani dake zuciyar ta, sosai Jehan ke kuka tana jero sunan da daddy ke kiran Rimsha idan taci mark ko wani gift a school "My siha My misha My sima My Rasha ina kike a halin yanzu? Me kike yi? Baki san muna kewar ki bane? Da ba zaki dawo gare mu ba haba my Rashi ki dawo ko zafi zai ragun min a rai" da sauri mum ta miƙe ta bar wajen saboda hawayen da take riƙe wa sunfi ƙarfin ta ba zasu riku ba ita kan ta gwaggo hawayen cubce mata su kayi suka fara bin kuncin ta, Jehan ta fama musu ciwon dake zuciyar su, sosai Jehan ta sha kuka na kin ƙarawa, da kyar gwaggo ta iya sai ta nata kukan ta rarrashi Jehan ɗin, ita ma mum sosai ta murji kukan ta a cikin ɗaki har ya isshe ta, kiraye kirayen sallar mangariba ne yasa mum fitowa idon ta duk sunyi ja sun kunbura saboda kukan da tasha haka ta wuce su Jehan ta ɗauro alwala ta shinfiɗa dadduma ta tada Sallah, da kyar gwaggo da Jehan suka iya miƙe wa dan yin alwala jikin su duk ya mutu saboda kukan da suka sha, a tare suka yi alwala har lokacin hawaye bai dai na bin kuncin Jehan ba, haka tana Sallah tana kuka zuciyar ta na mata tsananin zafi kamar zai fashe ya fito waje tana matukar kaunar yar uwar ta sosai. Bayan sun idar da sallah suka zauna saman dadduma sukayi addu'a sosai san nan sukayi karatun Al Qur'ani mai girma har a ka kira Sallar issha sukayi Sallah san nan suka naɗe daddumar Jehan ta ɗauka da hijaban su ta mai da ɗaki daga nan ta haye gado tana hawaye ta runtse ido tana tuno rayuwar su a baya sosai ta kara shiga damuwa, su mum kuma da kyar suka tsakura abincin sama sama suka ci mum ta tattara sauran abincin ta mayar kitchen, yau ba wani hira da suka yi saboda tuna musu da daddy da Rimsha da Jehan tayi, gwaggo taje ta rufe musu kofar gida kowa ya wuce ɗakin sa zuciya ba daɗi, Ko da gwaggo ta shiga ɗaki ganin idon Jehan a runtse yasa tayi tunanin ko tayi barci dan lokaci ta dai na hawayen, hayewa gadon gwaggo tayi ta musu addu'a san nan ta kwanta gefen Jehan ɗin tare da kashe wutar wayan nata, duk abun da take Jehan na jin ta dan bata yi barci ba kuma bata jin alamar barci ko kaɗan kawai tayi shiru ne tana tunanin yar uwar ta. 💞💞💞💞💞💞💞💞 RIMSHA Tana sume a wajen da ta faɗi su barbushi suka buɗe daffafiyar kofar karfen ɗakin, nan take haske ya gauraye ɗakin cikin takun irin na samudawa Barbushi ya shigo ɗakin yana wani irin nishi kamar gurnanin zaki duk in da ya taka sai kasa ta bada dum dum haka ya iso in da Rimsha ke jefe tana sume, da hannu ɗaya ya damko ƙafofin ta dukka biyun ya ɗago ta sama kan ta na lilo a kasa ya nufi waje da ita, a tsakar mummmunar gidan wadda duk in da ka juya gunkin wancan matar ne ta bakin kofar shigo ga hakoranta manya manyan fato fato, gidan ne mai kama da gidan sheɗanun aljanu ga gidan a tsakar dokar daji mai matukar haɗari da ban tsoro da duhun gaske, da karfi Barbushi yayi wurgi da ita kan sauran yaran da aka fito da su, yara 8 ne a wajen ciki harda yaran da a ka kawo su tare da Rimsha jiya, dukkan su yaran a sume suke, wani katon bikiti Santilago ya ɗaga mai cike da ruwa mai kaman jini jawur da shi, ya ɗaga bokitin sama ya juye ruwan a kan yaran nan a firgice suka farka, dukkan su da wata iriyar gigitatchiyar ihu suka farka saɓanin Rimsha da ta farka da sunan Allah a bakin ta, cikin tsawa da muryan sa kamar lalataccen injin markaɗe Barbushi ya daka musu tsawa "Kuyi mana shiru!!!" da gudu ɗaya daga cikin yaran da a ka kawo su tare da Rimsha ta miƙe jikin ta sanye cikin riga da skit na atamfa ta bazama cikin gidan ba ta san ina ma take takawa ba da alama ta fita cikin hayyacin ta, wata mahaukaciyar dariya Santilago ya kwashe da shi yana faɗin "Ga gawar farko dan ina da tabbacin ta haukace" dama al adar gidan ne idan sun kawo yara zasu zuba su cikin irin wan nan ɗakin da suka sanya Rimsha sai dodannin tsafin su suyi ta basu tsoro suna rikita musu kwakwalwa wadda ta haukace ita suke fara yankawa su bawa dodon tsafin su jinin, kai da kafa da kayan ciki kuma su bawa wasu manya manyan dodannin dake cikin kejin su a wata ɗaki, su kuma su ci naman jiki, idan kuma da safe suka fito da ke da sauran kwarinki baki fita cikin hayyacin ki ba to zasu kai ki mataki na biyu, idan nan ma kika tsira baki haukace ba to zasu ajiye ki su samo mai sayan sassan jikin ki dan dodon tsafin su wato Queen na su jinin mahaukata kawai take sha shiyasa sai sun hausata yara suke yanka su, idan kika cerewa ihun abubuwan tsafin su a rana ta farko to rana ta biyu zasu kai ki ɗakin gurnani daga shi sai ɗakin suma kafin mutuwa sai kin tsalle wan nan dukka sai su ajiye ki su nemo wan da zai sayi sassan jikin ki idan sun samu sai su yanka ki su cire masa abun da yake buƙata a jikin naki idan kuma ba su samu ba to a nan zasu yi ta ajiye ki suna baki namar mutane har ki dawo irin su. Kallon Barbushi Santilago yayi cikin tsawa yace "kamota!! Taku biyu Barbushi yayi da wan nan katon kafar tasa kamar na samudawa ya damko gashin kan yarinyar dake ta gudu a cikin gidan ta rasa ina zata je dan bata cikin hayyacin ta ta haukace, ɗaga ta sama Barbushi yayi da gashi ya wulwula ta kamar fanka wadda sai da gashin kan nata wasu suka tsitsige tuni ta sume, sai da ya jijjiga ta sosai san nan ya wuce da ita saman wata katuwar benci da ke tsakar gidan wadda suke yanka mutane a kai, dukka sauran yaran basa cikin hayyacin su Rimsha ne ka ɗai take cikin hayyacin ta kuma tana kallon duk abun da suke idon ta a bushe ta kasa yin kuka, da hannu Barbushi ya tsigewa yarinyar nan gashin kan ta dukka, yana tsigewa jini na malala kamar fanfo yana zuba cikin wata katotuwar kwano dake kasan bencin, haka Barbushi ya tsige gashin kan yarinyar nan dukka, yarinyar bata ko motsi da alama ta mutu ko ta suma, bayan Barbushi ya gama tsige hashin kan yarinyar shi kuma Santilago yazo ya ɗauko wata katuwar wuƙa mai girman gaske ga kaifin bala'i da hannu ɗaya ya ɗaga yariyar ya kwantar da ita flat a saman bencin ya ɗaga wukar da karfi ya datse mata wuya nan take gidan ya amsa da kururuwan muryoyin dodanni mai bala'i rikita ƙwaƙwalwa, wata guguwar iska mai karfin gaske ne ya taso daga cikin gidan kan kace me gaba ɗaya gidan yayi duhun kamar duhun hadari sama guguwar nan tayi, tayiwa gidan runfa tana juyawa kamar fanka tana bata wata iriyar gigitatchiyar sauti kara kamar na wakar shaiɗanun aljanu abun dai ba'a magana abun tsoro abun rikitar da mai rai nan take jinin yarinyar nan ya fara feshi kamar fanfo ya fashe ya wanke wa Santilago fuska, fito da harshen sa yayi ya fara lashe jinin yana ɗage hanci sama kamar kofar shiga gari, saboda zafin fitar rai yarinyar ta fara shure shure, tana shure shure Santilago ya fara yanka sassan jikin ta gunduwa gunduwa yana fitar da kowani joint yana ajiyewa a gefe, duƙawa Barbushi yayi ya ɗauki kwanon dake kasan tebur ɗin wadda jinin ya taru a cikin sa ya nufi wajen dodon tsafin su yana dariya kamar mahaukaci, ɗago ido Santilago yayi ya kalli abokan aikin sa dake gere a wajen cike da bada umarni yace ku ɗaure sauran yaran nan dukka ku tsige musu gashin kan su dan ina ga dukkan su ba sauran mai hankali ku ɗaure su ku tsigemin gashin kan su bari na gama yanka namar nan sai kuje ku fara girka mana ku kaiwa kannen mutuwa kai da kafa da kayan ciki ni kuma na yanka sauran yaran" da hanzari suka amsawa Santilago da to sannan suka nufi wajen su Rimsha, duk abun da suke idon Rimsha kar a kan su ko kyabta ido ta kasa ta kasa hawaye tayi mutuwar kwance dara daran fararen idon ta a buɗe reras amma da alama ta suma ido a buɗe ne, haka matsafan nan suka zo suka ɗaure su tam da igiya ta yadda ko motsi ba zasu iya yi ba sauran yaran sai ihu suke kamar mahaukata ita dai Rimsha shiru kamar bata a wajen, ɗaya daga cikin matsafan ne yace "Oga wan nan yarinyar kamar tana cikin hayyacin ta fa" yayi maganar yana taɓa Rimsha da hannun sa, ganin ko motsi bata yi ba ga kuma idon ta a buɗe ne yasa ya sanya katon mummunar koren yatsar sa a cikin dara daran idon nata ya tsole mata ido, nan ma ko motsi bata yi ba jujjuya kwayar idon nata yayi da yatsar sa, ko kyabta su ba tayi ba hakan yasa ya ɗago kai yace "Oga yarinyar nan fa ta mutu" a kule Santilago yace "Daman idan sun mutu ai sunfi daɗi ku tsigemin gashin kan su nace ko?" Cikin sauri suka fara aikin su dan cika umarnin ogan su. masu karatu mu leƙa jelly mu dawo 💞💞💞💞💞💞💞💞 KANO Karfe sha biyu na dare jelly ta farka daga barci tare da juyawa tana laluɓan daddy, abun mamaki sai ta ga daddy zaune idon sa biyu ya buga uban takumi sai zufa yake duk da sanyin Ac dake ɗakin kwata kwata ya manta da wutar ɗakin a kunne, sau uku jelly na kiran sunan sa amma bai ji ta ba yayi nisa cikin duniyar tunanin da ya faɗa, da kyar jelly ta iya miƙewa zaune ta rarrafo tazo wajen da yake zaune ta kwantar da kan ta saman cinyar sa cikin muryan barci tace "Daddy what are you thinking?" Firgigit yayi yana kallon face nat,a da kyar ya iya kakalo murmushi wadda yafi kuka ciwo murya a dashe kamar mai mura yace "My baby yaushe kika tashi?" hannu ta sa tana mutsuƙe ido tace "Tun ɗazun daddy kuma ina kiran ka kaki amsa mani ba me kake tunani?" shafa kan ta yayi ji yake kamar yasa ihu ko zai samu sauki a ransa ya rasa meke masa daɗi a duniya, da kyar ya iya buɗe baki kamar zai yi kuka muryan sa har sarkewa yake yace "My baby jeki kwanta kiyi barci" girgiza kai tayi tana faɗin "No daddy sai ka faɗa min what is wrong with you, what is happening?" nan take hawayen da yake kokarin ɓoyewa suka fara zuba a idon sa kawar da kan sa gefe yayi yana kokarin shanye hawayen amma ina sunci karfin sa da gudu gudu suke zuba wani na bin wani a razane jelly ta miƙe zaune tare da sanya hannunta, ta riƙo kumatun sa ta juyo da face na shi suna fiskantar juna tace "Daddy please tell me what is happening why are you crying?" tayi maganar tana hawaye tana goge masa nasa hawayen rungume ta yayi ya saki kuka mai ɗan sauti yana faɗin "Ki yafe min my baby yau na karya alkawarin da na ɗaukar wa umaima kafin ta rasu jalila kiyi hakuri na bada Auren ki ga Muneer gobe za'a ɗaura" cikin kuka tace "Daddy saboda auren kake kuka? to me shi auren?" Sake ta daddy yayi ya mai da ta saman gadon ya zaunar da ita still hawaye na bin kumatun sa nan ya shiga yi mata bayanin abun da ake nufi da aure, a iya 14 years da take da shi a duniya ta ɗan fahimci me ake nufi da aure, riko hannun sa tayi da kyau tana hawaye tace "Daddy to me yasa zaka yi haka? Ni yaya Imran nake so" kasa jure kallon raunanniyar face nata daddy yayi cikin sauri ya kawar da kan sa yana faɗin "Jalila dole a ka min ba zan iya ja da baban Muneer ba, ba zan iya yi masa musu ba muddin ina son rayuwa cikin salama to dole nayi abun da yake so dan na rufawa kai na asiri na cece mutuncina jelly ki ceci rayuwar daddyn ki nasan na cuce ki na cutar da rayuwar ki bazan taɓa yafe wa kai na ba idan hakan ta faru na ci amanar da Umaima ta bani ban cika mata alkawarin da na ɗauka mata a kan ki ba, lokacin da take gargaran mutuwa hannu bibbiyu ta haɗa tana rokona a kan kada na bari kiyi kuka sai gashi yau da kai na zan saki kuka innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya kai karshen maganar tare miƙewa da sauri ya bar ɗakin saboda kuka mai karfi da yazo masa, tabbas yasan Muneer ba dan Allah yace dole a aura masa jelly ba yana da tabbacin jelly ba zata yi sati a gidan sa ba zai sake ta dan yara uku yayiwa hakan gashi ɗan giya ne lamba ɗaya duk macen da ya gani sai yace yana so zai aura haka baban sa zai sa a aura masa ita kwana biyu yayi yawa yake sakan mace idan ya ansa budurcin ta shi dai baya zina da matan banza idan yana so aura masa ake, da kuka daddy ya isa palo ya zauna saman sofa, Shiru jelly ta ɗan yi kafin ta miƙe ta biyo bayan sa da gudu, ganin ta yasa yayi saurin goge hawayen sa, faɗowa jikin sa tayi tana faɗin "Daddy na ka dai na kuka kayi shiru muje mu kwanta na yar da zan aure sa dan farincikin ka" rungumeta yayi yana faɗin "Shikenan muje mu kwanta" ya faɗa mata hakane dan ya samu tayi barci amma shi dai ya san barci ya kauracewa idon sa, miƙewa yayi ya ɗauke ta cak suka wuce bedroom ya ɗaurata saman gadon ta shima ya haye nashi yana faɗin "Saura idan nayi barci ki sake biyo ni gado na" murmushi tayi tana faɗin "Ba zan zo ba, good night" Jinjina mata kai kawai yayi ya kasa magana. Shiru yayi yana tunani, ita ma shiru tayi ta rintse ido kamar mai barci ta shiga duniyar tunani dan nemewa kan ta mafita, dan ta san dai karya ta yiwa daddyn a kan ta yarda zata auri Muneer ta faɗa masa haka ne kawai dan ya samu yayi barci amma ba wai dan ta yarda ɗin ba hasali ma tunanin yadda zata gudu ta koma gidan su Imran take, daga daddy har ita ɗin ba wan da yayi barci ranar haka suka kwana cikin tunani. Bari mu leƙa Jehan mu dawo 💞💞💞💞💞💞💞💞 KATSINA Misalin karfe 1 na dare farin wata na nan tas a tsakiyar duniya kasan cewar daren goma sha huɗu ne na wata, wasu kartin maza su biyu suka diro cikin gidan su Jehan kai tsaye suka wuce kufar da zata kai su ɗakin gwaggo kamar sun san hanya ɗaya daga cikin su ya sanya yar makulli safaya key ya buɗe kofar ɗakin, suka kutsa kai cikin ɗakin kasa kasa ɗayan yace "Fadil ina take sai fa mun kunna haske" Fadil na ƙoƙarin yin magana suka ji diran wasu mutanen cikin gidan nan take suka tsorata har suna rige rigen shiga toilet dake ɗakin wadda babu kofa, suka ɓuya wadda su Jehan suka mai da wajen a jiye kayan datti dan basu amfani da toilet ɗin dana waje suke amfani kasan cewar wan nan yayi karami sosai, shiru suka laɓe suka kasa kunne dan jin su wanene suka shigo gidan su Jehan ɗin, takun tafiyar manya sukaji hakan ya tabbatar musu ba kananan mutane bane suka shigo gidan, sunyi shiru suna jan mumfashi a hankali sun kasa kunne, can kasa kasa suka jiyo muryan ɗaya daga cikin wayan da suka shigon yana faɗin "Nasir ai kofar ma abuɗe take" Nasir Fadil ya mai mai ta sunan a ransa yana mamaki, suna tsaye har su Nasir suka shigo cikin ɗakin, sai da suka gama shigowa san nan suka fara magana kasa kasa dan sun san gwaggo da Jehan sun yi barci a irin wan nan lokacin, jin motsin mutane yasa mum ta farka daga barci da kyar ta iya miƙewa zaune ta ɗauki wayar ta, ta kunna wutar wayar, ta sauko kasa daga gadon, ta ɓuɗe kofar ɗakin ta fito ta nufo ɗakin su gwaggo dan tanan take jiyo motsin ta sha ruwan mamaki ganin ɗakin su Jehan ɗin a buɗe, sosai ta kara haska kofar wajen ganin germ lock ɗin dan dama daki su Jehan da germ lock suke rufewa ba sakata a ɗakin, cikin tsoro ta ɗaga haske wayan nata ta haske cikin ɗakin sai kan face ɗin ɗaya daga cikin abokan Nasir dake tsaye ta bakin kofa, ga idon nashi jawur kamar jini manya manyan kai da gani kasan wan nan yana shaye shaye over ganin shi ba karamin tsorata mum tayi ba nan take numfashi ta ya ɗauke ta zuɓe kasa sumammiya Tashin sense masu karatu mu koma mu leƙo daddy da jelly ya suka tashi sai mu dawo 💞💞💞💞💞💞💞💞 KANO Washegari da safe daddy ya sha ruwan mamaki ganin yau jelly ita da kan ta tayi wanka tun kafin ya dawo sallar asuba ta tashi ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata riga fari da wando ash da ɗan karamin farin hijabi zuwa kirji, hakan ba karamin mamaki ya ba wa daddy ba dan bata taɓa kwatatan ta hakan ba, amma sai ya ɓoye mamakin sa ya yaba mata sosai sai dariya take fararen hakoran tannan sai kyalli suke, wucewa shi ma yayi ya je yayi wanka, ko da ya fito bata ɗakin ta fice palo sauri sauri ya shirya cikin suit sannan ya ɗauki jakar computer sa da wayar sa ya duba time 7:02 sauri sauri ya fito zaune ya iskota saman sofa tana ta murmushi kamar ba ita ba a wan nan karon daddy ya kasa ɓoye mamakin sa yace "My baby what is happening ne?" Miƙewa tayi ta rungume sa tana faɗin "My daddy I want you to be happy everyday that's why" rungume ta yayi kawai amma bai yarda da maganar ta ba dan yasan halinta sarai, kafin ya sake ta yana faɗin "Muje muyi breakfast mu tafi kar lokaci ya kure" ba musu ta bishi suka zauna saman kujerar table, Nana tazo tayi serving na su sauri sauri suka yi breakfast, bayan sun gama daddy ya riko hannun ta suka nufi waje, suka je suka shiga mota gidan baya idi driver ya shiga gidan gaba ma zaunin driver yayiwa motar key suka bar gidan, a bakin gate na school na su suka tsai da motar daddy ya juyo ya kalle ta yace "Yau ba zamu shigar da ke ciki ba nayi late sauka ki shi ga school ina kallon ki" ba musu ta sauka daga motar da murmushi tace "Daddy na, ina kaunar ka sosai ka kula min da kan ka sannan kayi min alkawari ba zaka sake kuka ba komai zai faru da ni" daddy bai kawo komai a ransa ba yace "Na miki alkawari my baby ba zan sake kuka ba" sako kan ta tayi ta glass ɗin motar ta manna masa kiss a kumatu bata jira reply na shi ba ta wuce da sauri saboda hawaye da ya gangaro mata, zuba mata ido daddy yayi yana kallon ta, ya sha ruwan mamaki ganin yau bata juyo ta masa bye bye ba saɓanin kullun da take juyowa wani lokaci ma tafiyar baya baya take tana kallon sa, ganin su daddy basu tada mota bane yasa ta fahimci daddy na kallon ta dan haka sai ta kara sauri ta shige cikin school, tana shiga school Idi driver ya tada motar suka bar wajen sai mamaki daddy yake nan take yaji jikin sa ya mutu gaban sa na faɗuwa, haka ya daure dan bai kawo komai a ran sa ba har suka isa office na shi, Ita kuwa jelly tana laɓe a wajen gate sai da taji motar su daddy ya bar wajen tayi Sa'a mai gadin ya zaga bayan gida su daddy na tafiya ta fito da sauri ta kariso bakin hanya ta tari abun hawa ta hau tana sauke ajiyar zuciya "Ina zan kai ki?" Mai mashin ɗin ya tambaye ta cikin sauri tace masa "In da ake hawa mota" ɗan juyowa yayi ya kalle ta kafin yace "Motar zuwa ina?" Sai lokacin ta tuna ita bata ma san a wani gari gidan su yaya Imran yake ba shiru tayi tana tunanin hiran da suka yi a baya da Imran "Motar zuwa ina nace?" Mai mashin ɗin ya sake gefo mata tambaya nan ta tuna last zuwan yaya Imran yace mata daga Kaduna ya fito da ta tambaye sa daga ina ya fito tuna haka yasa cikin sauri tace wa mai mashin ɗin "Motar zuwa Kaduna" ba tare da ya sake magana ba ya buga mashin ɗin sa suka nufi park sai sauke ajiyar zuciya take, Ko da suka isa bai sauke ta ba sai da ya kai ta har wajen motocin Kaduna tayi Sa'a kuwa motar saura mutun ɗaya ya tashi, mai mashin ɗin yace "Kawo kuɗi na biya miki kuɗin mota" ba musu ta sauke jakar school dake bayan ta, ta zaro dollar dubu ɗaya tana faɗin "Nawane kuɗin?" Waro ido waje mai mashin yayi yana kallon kuɗin dake hannun ta nan take jikin sa ya fara rawa kasa kasa yayi da murya yace "Ki mai da kuɗin nan idan kina da kuɗin Nigeria ki kawo" miƙa masa dollar tayi tana faɗin "To kai riƙe na baka dan kana da kirki ina da kuɗin Nigeria" ta kai karshen maganar tare da sanya dayan hannun ta ta zaro dubu dubu guda biyar ba musu mai mashin ɗin ya ansa dollar da ta bashi ya mata godiya san nan ya ansa 5k da ta ciro ya sauka ya biya mata kuɗin motar zuwa Kaduna ya mata sallama tare da bata canjin ta ya wuce, shi kan sa driver ya sha ruwan mamaki ganin yarinya kamar jelly tazo hawa mota hakan yasa ya tambaye ta ina zata je dan ya tabbatar tana cikin hayyacin ta yarinya 14 years, cikin sauri ta sanar da shi Kaduna zata je da mamaki a face na shi na jin tana cikin hayyacin ta haka a ka loda kayan passengers a bayan mota, driver ya shiga kowani passenger ya shiga mazaunin sa jelly ta zauna kusa da wata tsohuwa mota ta tashi zuwa Kaduna. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💋Star Lady💋 *💞TRIPLET'S💞* 💞💕 💕💞💕 💕💞💕💞 💞💕💞💕💞 STAR 🌟 LADY..✍️ *💋The beginning💋* Episode 7 💞💞💞💞💞💞💞💞 *3 years back* *Abuja* *7:10 am* Wata haɗaɗiyar Hajiya ce zaune saman sofa mai zaman mutun 2 cikin wani katafaren palo, palo ne mai girman gaske mai ɗauke da sofa set manya manyan set biyu kowani set da kalan sa sai makekiyar Tv plasma dake manne a bango, daga gefe kusa da kyakkyawar staircase ɗin haurawa sama table ɗin cin abinci ne awajen mai bala'i kyau mai kujeru 8 daga wajen table ɗin kofar kitchen mai girma gaske mai ɗauke da duk wani abun da mace ke bukata a kitchen, ga manya manyan gas cooker guda biyu. Sanye matar nan take cikin dan kareriyar Swiss lace pink color da ratsin baƙi, ɗin kin bubu gown ta sha kwalliya sosai, wuyar ta da hannun ta sanye da dankara dankaran gold tayi kyau sosai ta yi ɗaurin Zahra Buhari a kan ta da ganin ta kasan naira ta zauna mata sosai jikin ta jikin hutu yayi luwai luwai da shi gata fara tas kyakkyawa a jin farko, shiru ta zauna tana kallon News a makeken Tv plasma dake manne a bango, hankalin ta yayi nisa a kallon da take wani kyakkyawan Alajine ya sauko daga saman bene fari tas da shi kamar balarabe yana shirye cikin wata dakakkiyar shadda ash color kyakkyawa ne sosai yana da kwantatciyar saje da gemu bakin kirin ga gashin kan sa na fulani har wani curly yake yana nannaɗewa ya gangaro masa har gaban goshi ga wata kyakkyawar gashi da ta kewaye ɗan bakin sa tayi masa kamar raun ba karamin kyau hakan ta karawa face na shi ba, a hankali ya tako ya kariso cikin palon ya sanya hannu ta baya ya rufe idon hajiyar dake zaune sofa, cool murmushi ta sake har sai da fararen hakwaran ta suka bayyana ga wani siririyar wushirya a tsakanin hakwaran nata gwanin ban sha'awa cikin shagwaɓa tace "Barkama (sunan girmamawa ne na fulani) kayi latti ai to" murmushi ya saki wadda yasa dimple na shi lotsawa slowly ya zame hannun sa daga kan face nata tare da zagayowa ta gaban ta yana faɗin "bongel am (kyakkyawa ta) barka da tashi" murmushi tayi tana kokarin yin magana wata kyakkyawar yarinya chocolate color ta sauko daga saman benen da gudu, kyakkyawace ajin farko doguwa tana da dogon hanci har baka ga dara daran ido kamar ball farare tas kamar auduga idon nata design of fish ne san nan kuma sleeping eyes gare ta wadda idan ka ganta zakayi tunanin barci take ji amma ba barci bane gasu da girma idon kamar ball bakin ta ɗan karami launin pink lip nata na sama design of heart ne kanta ba ɗankwali curly hair ta ya nannaɗe kamar indomie ga gashin nata dark black sai kyalli yake kai kace an tsomashi cikin baby oil ne saboda curly da kyalli da yake gashin nata har gadon bayan ta duk da yana nannaɗe hakan bai hana shi kai mata tsaliyar bayan ta ba tana da dogayen gashin ido sosai kamar tasa eyelashes ga saje mai kyau dark black kwance a gefe da gefen kumatun ta tana sanye cikin wando skin tight baƙi da white T-shirt mai dauke da bajel ɗin makaranta kyakkyawan kafofin ta ba ta kalma, hannu ta na riƙe da wani katuwar teddy kamar jaririn mutun a shekaru ba zata wuce 10 years ba, Da gudu ta sauko bene tana faɗin "Daddy kace wa Jehan ta kyaleni" tayi maganar cikin harshen shuwa arab ta kai karshen maganar tare da rungume sa, shafa curly hair ta yayi kafin yace "My Rimsha My siha where is your Abaya? Ko so kike muyi latti ne?" Girgiza masa kai tayi tana faɗin "Daddy this teddy is it not my own?" Tayi maganar sai da dimple nata irin na shi ta lotsa sosai, ta kai karshen maganar tare da ɗago masa teddy'n dake hannun ta tana nuna masa, yana kokarin yin magana Jehan ta sauko da gudu tana faɗin "I'm I playing with you? I'm I your mate?" A lokacin Jehan tana da 12 years, tana sanye cikin uniform riga me dogon hannu light blue se doguwar riga a saman ta dark blue mai hannu a kafada rigar ta tsaya a dai dai gwiwar ta se wandon uniform dark blue ƙafar ta sanye da Black socks ba takalmi a ƙafarta da gudu tayo kan daddy tana kokarin fisgo Rimsha, ihu Rimsha ta fasa tare da kanka me daddy tana faɗin "Daddy save me" fararen hannun sa yasa ya riƙo hannun Jehan yana faɗin "Haba Jehan yau fa Graduation ɗin My siha mai kuma ya haɗa ku faɗa a kan teddy kullun baku da aiki sai faɗa kan teddy ba kalan teddy da ban sawo na kawo gidan nan ba ni narasa meke damun ku" bai kai ga rufe baki ba mum ta miƙe ta amshe teddy tana faɗin "This teddy is for Rimsha whare is your own Jehan?" Turo baki Jehan tayi tana faɗin "Mum This is mine, is not for Rimsha" kallon mum daddy yayi san nan yace "bongel ɗauko min sauran kayan su yau ba ma zamu yi breakfast ba haka zamu wuce dan munyi latti, sayi breakfast ɗin a school ɗin na su ko idan mun dawo" ya kai karshen maganar tare da ruƙo hannun Rimsha ɗaya na Jehan ɗaya suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3 yana kallon face na Rimsha, har cikin ransa yake bala'i son yaran nan nashi gashi Jehan ita ce mai kama da shi sai dai bata da dimple irin nashi ita kuma Rimsha da mum take kama sai kuma ta ɗauko dimple ɗin dad wushiryan mum, miƙewa mum tayi ta haye sama sauri sauri dan ɗauko musu sauran kayansu Kallon daddy Rimsha tayi cikin harshen shuwa arab tace "Daddy ni zanzo first class In Sha Allah" murmushi daddy yayi ya sanya hannu yana tara mata curly hair ta da baya kitsuwa idan a ka mata kitso sai ya warware ga gashin nata da tsowo sosai a nannaɗe kamar indomie duk da naɗuwar sa kuma bai hana tsowon gashin nata bayyana ba dan a nannaɗen ma ya kai mata har tsakiyan baya "In Sha Allah my siha ke zaki zama first class" ya kai karshen maganar tare da ɗaure mata gashin nata da kyar dan sai ya kamo sai su zame shi yasa ma bata cika ɗaurewa ba dan ko ta sanya rebon fita yake shima daddy yanzu kulle mata yayi kamar igiya da gashin ya kullu, ita dai Jehan ko a jikin ta hankalin ta na kan Tv, a tare mum da gwaggo suka sauko hannun mum riƙe da Abayar Rimsha Black colour da Hijab fari da takalmin ta da Black socks ita kuma Gwaggo na shirye cikin Abaya fari tas ta yafa gyalen abayar a kan ta idon ta sanye da glass ɗan siriri mai matukar kyau da tsada, hannun ta rike da Hijab ɗin Jehan light blue Dan Karami kalar T-shirt ɗin uniform ɗin, mum ta shirya Rimsha Gwaggo ta shirya Jehan bayan mum ta gama shirya Rimsha ne ta ɗago ta kalli daddy tace "Yanzu Barkama da gaske kake ba zan biku ba?" Dogon hancin ta yaja yana faɗin "Duk abun da zai faru a School ɗin daga farkon har karshen zaki gani ki kunna TV kuma in muka dawo nayi alkawari zan biya" hararar wasa ta masa tana musu addu'a, riƙo hannun Rimsha yayi gwaggo kuma ta rinƙo hannun Jehan suka nufi hanyar fita daga palon "eyeeee My siha yau ba zuwa da jaka kenan" mum tafaɗa tana dariya, dariya ita ma Rimsha tayi kafin tace "Mum yau hutu za'ayi ai" komawa mum tayi ta zauna saman sofa tana faɗin "Allah ya bada Sa'a kuzo min da first class" a tare gwaggo da daddy suka amsa da Amin dai dai lokacin suka fice daga palon suka nufi parking space na gidan, da gudu wani ɗan sanda ya nufo su ya buɗe wa daddy da gwaggo kofar motar daddy kirar Roll-Royce boat Tail a tare suka shiga gidan baya daddy ya ɗaura Rimsha saman cinyar sa ita ma gwaggo ta ɗaura Jehan saman cinyar ta, ɗan sandan ya shiga ya tada motar yaja suka nufi gate, tun basu kariso wajen gate ɗin ba iliya mai gadi ya wangale musu tampatsetsen gate ɗin cikin kwarewa da iya tuki ɗan sandan nan ya danna hancin motar waje suka miƙi titi, Cikin kankanin lokaci suka isa bakin katafaren gate ɗin Great Heights Academy horn ɗaya ɗan sanda yayi mai gadin ya wangale musu gate ɗin, ɗan sandan ya kutsa motar sa cikin school ɗin. Makarantar cike take makil da jama'a ga manya manya baki da manya manyan yan siyasa da sarakuna sunzo taya yaran su murna masu kammala primary da jss 3 da ss 3 Rimsha na cikin wayan da za su kammala primary 6 na su tana cikin wayan da suka zana common entrance while Jehan na jss 2 yanzu, sai murna Rimsha take ita ma zata shiga secondary zata kamo Jehan. Ɗan sanda na parking a parking space na school ɗin ya fito ya buɗewa daddy da gwaggo suka fito nan take manya manyan alhazawan dake tsaye a wajen suna jiran fitowar daddy suka kariso cikin murna da fara'a suka fara bashi hannu a kan su gaisa, kasan cewar shine babban bako a wajen hakan yasa director makarantar da sauran malamai suka kariso wajen da sauri dan tarban sa, cikin girmamawa director ya miƙawa daddy hannu yana faɗin "Barka da zuwa gaskiya munji daɗi da amsa gayyatar mu da kayi muna alfahari da hakan" murmushi daddy ya saki har sai da dimple na shi ta lotsa yace "Ai dole nazo ko dan siha ta" ya kai karshen maganar tare da shafa kan Rimsha cool murmushi ta saki har sai da dimple nata ya lotsa siririn open teeth dake tsakanin fafaren hakoran ta ya bayyana hakoranta fafare tas da su kamar gonan audiga, manya manyan Alhazawan dake wajen dukkan su Rimsha ta matikar burge su sosai. Malamar su Rimsha ce ta ƙaraso ta gaida daddy cikin girmamawa ta kama hannun Rimsha tana faɗin "let's go and get ready" a hankali ta lumshe sleeping eyes nata ta sake buɗe wa kafin tace "Bye daddy see you in the Hall" ta kai ƙarshe maganar tana yi masa bye bye da hannunta shima bye bye ɗin ya mata ita dai Jehan tun saukowar su ba ta jira kowa ba ta wuce wajen friends nata, Director ne yace "sir please let's go in" Kallon Gwaggo daddy yayi yace "Anty A'isha muje Koh" a tare suka ranƙaya zuwa cikin katafaren hall ɗin dake cikin School ɗin a nan za'ayi taron ƴan jarida sunzo ɗaukar new gidan TV kala kala gaba ɗaya student na ciki kowa na zaune saman kujera an kawata hall ɗin sosai da kalar makarantar Dark blue da light blue an rubuta Sunan Makarantar da ballons dark blue da light blue idan nace zan tsaya zayyana muku haɗuwar da hall ɗin nan yayi to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba kawai ku kawata shi a ran ku, hall ne mai girman gaske an cike sa da kujeru da student suka zazzauna, ta gaba kuma inda aka tanadar na ɗaliban da sukayi graduation ɗine, daga saman staircase wani ya opposite ɗin students ɗin, a ka shirya wasu haɗaɗu kujeru masu kyau sun kawatu iya kawatuwa ga wata doguwar table a gaban kujerun an jera drinks a sama da ruwan faro masu sanyi wadda daga ka gani kasan wajen baki na musamman ne daga tsakiyar kuren a kwai wata haɗaɗiyar kujera golden color an mata kwalliya sosai kamar kujerar sarauta daga gani kasan mutun na musamman a ka tana dawa, manya manyan alhazawa da sarakuna ne zazzaune saman sauran kujerun da a ka jera layi sai wan nan ɗayan mai kama dana sarakuna shi da na kusa da shi ne babu kowa a kai, saman sa daddyn su Jehan yaje ya zauna ita kuma gwaggo ta zauna a kujerar kusa da na shi, nan take student suka miƙe suka fara kwasan gaisuwa daddy na amsa musu da fara'a a face na sa, duk school nan ba wanda bai san shi ba sai dai in new comer amma student ɗin school ɗin sun san shi dan mutun ne shi mai fara'a da kyauta gashi da son yara duk kuɗin da yake da shi, shi da kan sa yake kawo su Jehan school kuma ya dawo ya ɗauke su dan gani yake kamar idan ya bari driver ya kai su ba zai kula masa da su sosai ba, shi yasa ko abu suke so yake ɗaukan su suje shopping tare da shi komai aikin da yake zai ajiye yazo yayi attended nasu, yana bala'i kaunar su sosai, Bayan sun gama kwasan gaisuwa ne suka koma suka zauna. Mike director ya ɗauko ya sanya a saitin bakin sa ya fara magana cikin harshen turanci "Ina mai farincikin zuwan wan nan rana mai albarka Jehan Nawazudden Salman kizo ki buɗe mana taro da Addu'a" shiru hall ɗin yayi, gaba ɗaya manya manyan bakin da suka halakci taron sun zubawa Jehan ido wadda ta taso tana tafiya a nitse, a hankali ta tattaka saman staircase ɗin ta hauro sama taje ta tsaya kusa da director, miƙa mata mike ɗin director yayi ta ansa cikin kyakkyawa turancin ta da zazzakar voice nata mai sanyi da daɗi ta fara da yi musu sallama san nan ta fara jero addu'a "We take refuge with Allah, The Supreme and with His Noble Face, and His eternal authority from the accursed devil In the name of Allah, and prayers and peace be upon the Messenger of Allah O Allah, open the gates of Your mercy for us Amin" ta kai karshen Addu'ar tare da rufewa da Ayatul kursiyyu, sosai jama'a suka yi ta kabbara ciki hadda daddy da gwaggo sosai daddy yaji daɗi, ji yayi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, bayan Jehan ta sauka ta koma mazaunin ta ne director yace a shigo da ɗaliban da sukayi graduation ɗin, a cikin layin suka shigo cikin tsarin suna sanye Cikin graduation gown kalar uniform ɗin makarantar daga bayansu kuma malaman sune kowa fuskarsa cikin annashiwa da tsantsar farin ciki, kai tsaye inda aka tanadar domin su suka karasa sannan sukayi Anthem ɗin makarantar aka basu iznin zama Director ne fara kiran graduates ɗin ɗaya bayan ɗaya sukazo su gabatar da kan su san nan suyi jawabi tare da nuna farincikin su sai suyi karatun al Qur'ani mai girma, ba laifi yaran sun iya kira'a daddy ya kosa a kira Rimsha ɗin sa haka ita ma gwaggo ta kosa taji karatun Rimsha, duk yarinyar da tazo a kace ta karanta Al Qur'ani mai girma bata wuce karanta sura daga nasi zuwa amma ko sabbi, Rimsha itace yarinya ta goma da a ka kira cikin nitsuwa ta taso tana tafiya a nitse ta hauro saman wajen ta ansa mike ɗin da zazzakar voice nata ta fara da bilmillah san nan ta karanta suratul fatiha daddy yaji ba daɗi a tunanin sa a suratul fatiha zata tsaya sai yaji ta sake wata Bismillah ta fara karanta Suratul Baƙara, shiru hall ɗin yayi ba abun da ke tashi sai zazzakar voice ɗin Rimsha dake tashi, gaba ɗaya kowa ya nitsu tsit suna sauraron baiwar da Allah ya mata farincikin a wajen daddy da gwaggo ba'a magana, hawaye Rimsha ta fara yi tana karatu ko da tazo In da Allah ke magana a kan itaciyar da ya hana Annabi Adam ci Annabi Adam yaci ta sanadiyar haka Allah ya fito da shi daga aljanna, sau uku tana mai mai ta ayoyin san nan ta ci gaba tana karatu tana kuka, tun muryan ta na fita sosai har ya fara sarkewa saboda kuka da take idan ta tuna girman Allah ta tuna mutuwa kwanciyar kabari gadar siraɗi hisabi sai ta kara fashe wa da kuka shi kan sa daddy sai da kwalla ta cika masa ido duk wani mai imani a wajen sai da idon sa ta kawo kwalla dan kukan da Rimsha ke yi tana rero kira'ar nan, masu saurin kuka kam ma tuni sun fara rera nasu kukan cikin harda Jehan, da kyar Rimsha ta iya kai karshen suratul bakara tana kokarin durkushewa kasa a wajen daddy da ya kasa hakuri ya taso da sauri yazo ya rungume ta yana faɗin "It's okey my siha" cikin kuka tace "Daddy me mutun zaiyi a dunuyyar nan da ya wuce bautan Allah daddy mutuwa gaskiya ce kwanciyar kabari gaskiya ce gadar siraɗi gaskiya ce hisabi gaskiya ce haka zalika wuta da aljanna gaskiya ce daddy, duk wani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa daddy, duk lokacin da na kalli kwayar idon ɗan Adam daddy ina kara jin tsoron Allah da ganin girman Allah a rayuwata dan idon ɗan adam ma kawai ya isa yasa bawa mai hankali ya kara jin tsoro Allah, duk lokacin da na tuna da mutuwa hisabi kwanciyar kabari gadar siraɗi wutar jahannama daddy ina shiga tashin hankali sai in ji gaba ɗaya duniya ta fitamin a rai na daddy, me ya rage bawa yake so bayan yayi bautar Allah dan ya samu ya tsira ranar gobe kiyama, daddy ban taɓa kwaciya barci na sawa rai na zan farka a duniya ba, ban taɓa lissafin me zai faru gobe na ba kullu lissafi na iya yau nake dan bana sawa rai na zan kai goben mutuwa gaskiya ce kuma tana ɗauka duk lokacin da kwanan mutun ya kare ba ruwan ta da abun da kake ko in da kake zata ɗauke kane kawai, daddy duk wani musulmi kamata yayi ya sawa ransa iya yau kaɗai garesa ba zai kai gobe ba dan ya samu damar aikata aikin Allah, daddy duk lokacin da na samu dama har tsawon kwana na ya kai nayi sallar issha, ji nake tamkar an sauke min wani katon dutse a kai na dan kullun ina cikin fargabar kada na mutu gab da wata sallar ko azahar ko la'asar kuma a ce ban samu damar yin wan nan sallar ba" ganin maganar da Rimsha take babban magana ne yasa director ya kawo mata mike ɗin sai tin bakin ta dan kowa yaji maganar nata, sosai hall ɗin gaba ɗaya suka ɗauka da kuka babban magana miƙewa manya manyan sarakuna irin su sarkin Zazzau Sarkin kano Gombe Bauci da dai sauransu suka yi, ba karamin tashin hankali magangun Rimsha ta jefasu ba yariya yar karama kamar wan nan amma tana da karfin imani har haka shi kan shi daddy yayi shocked da jin maganar Rimsha yasan dai tafi Jehan ilimin addini dan ita kullun tana tare da mum tana koya mata karatun addini ban da Jehan da a iya islamiyya kawai take ɗauka bai taɓa tunanin girman ilimin Rimsha ya kai haka ba, ba wanda bai yi mamaki da jinjinawa Rimsha ba ta girgiza gaba ɗaya hall ɗin ta karawa mutane da dama imani a ran su dayawa daga cikin wayan da suka halakci wajen sun kudurci niyar gyara ɗabiun su marasa kyau ta dalilin maganganun Rimsha, sosai suka shiga tashin hankali duk wanda ya manta da lahira yau sai da Rimsha ta tuna masa wani ma ji yayi kamar yaje ya sadakar da dukiyar sa dukka ya koma ga Allah yayi ta ibada, da gudu Jehan ta miƙe ta hauro saman wajen ta rungumi Rimsha tana kuka tana faɗin "Kinyi gaskiya yar uwata duk abun da kika faɗa gaskiya ne amma jama'a da dama sun shagala da duniya sun manta da mutuwa da kwantatciyar kabari sun manta duhun kabari da siraɗi da hisabi idan ka dace ka shiga aljanna idan baka dace ba ka wuce wutar jahannama bayan ka gama ansan azabar kabari dana siraɗi ga tsayuwa kafin hisabi tsayuwar shekara ɗai ɗai har shekara dubu saba'in ga kuma rana a dai dai sai tin kan ku babu dare babu inuwa sai wan da yayi aikin Allah ne kaɗai zai shiga inuwar al'arshin Ubangiji Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun tuba mun tuba ya Allah" sosai jama'a suka ciro wayoyin su suka rinƙa yi musu video ciki har da director. Da kyar daddy ya iya rarrashin Rimsha sai da tayi shiru san nan ya riƙo hannun ta suka miƙe ya dubi director yace "Mu zamu wuce gida ba zamu iya jira a gama taro ba dan jikin siha ya fara zafi saboda kukan da tayi" ya kai karshen maganar tare da kallon gwaggo dake zaune saman nata kujerar tana goge kwallan dake idon ta yace "Aunty A'isha muje ko?" Da kyar gwaggo ta iya miƙewa dan gaba ɗaya Rimsha ta kashe mata jiki, gaba ɗaya manya manyan baki da sarakunan dake wajen suka miƙe dan raka su daddy zuwa wajen mota, sunyi sunyi a kan daddy ya bari suyi hoto da Rimsha amma yaki haka suka hakura ba dan sun so ba suka bar su Rimsha suka tafi ba tare da sun yi hoton ba, da haka taron ya watse dan dukkan su sun kasa gudanar da komai jikin su ya mutu da har da kayan kiɗa suka kawo amma jin zancen Rimsha yasa suka manta da wani kayan kiɗa da suka kawo, kowa ya wuce gida taro ya watse 💞💞💞💞💞💞💞💞 KANO Zaune jelly take saman mirror chair daddy na tsaye a kan ta yana ɗaure mata gashin kan ta da roba irin na kitson yara kasan cewar gashin nata yayi tsantsi sosai baya kitsowa sai dai a ɗadɗaure mata shi da roba, sai murmushi take fararen hakwaranta masu kyau suna jere kanana da su sai kyalli suke, shi ma daddy sai murmushi yake yace "My baby kinyi kyau over" kara murmushi tayi sosai a wan nan karon har fararen hakoran ta suka kara bayyana sosai "Daddy amma dai yaya Imran zai zo school na mu ko?" Tayi maganar cikin shagwaɓa "Eh my baby yace min zai zo In Sha Allah" tana kokarin sake yin magana daddy yace "Sauko na gama kuma surutun nan ya isa dan 07:00 am tayi yanzu taso na sanya miki uniform dan karmuyi late" make masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy kai fa ka ɗaurani saman chair ɗin yanzu kuma kace na sauko da kai na ni ban iya ba" girgiza kai kawai yayi ya sanya hannu ya ɗagota cak suka nufi wajen gado dan bai son biye mata idan ya biye mata ba zasu wuce school da wuri ba, saman gado ya ɗaura ta san nan ya wuce ya ɗauko mata uniform nata riga fari da wando blue sai ɗan hijabi fari ya dawo ya sanya mata sharp sharp san nan ya ɗauko perfume ya feshe ta da shi nan take ta fara zuba kamshi wuce wa yayi ya ɗauki suit nasa da zai sanya ya shige toilet, tana zaune har ya fito shirye cikin bakin suit da ya ɗauka ya dube ta yace "Let's go my baby" shiru ta masa kamar bata ji me yace ba, sake mai mai ta maganar yayi dai dai lokacin da yake ɗauko jakar computer sa nan ma sake masa shiru tayi kamar bata san da mutun a ɗakin ba, da sauri ya juyo dan yaga wai ko barci tayi ne ganin idon ta kar a kan sa ta turo baki kamar biro ne yasa ya dafe kan sa da hannun sa yana faɗin "Yanzu kuma menene? haba my baby zamu makarafa" kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "Ni daddy yanzu ka dai na sona baka ɗauka na sai kace na tafi da kafata" "Haba my baby yanzu fa 11 years kike da shi gaskiya kin min katuwa ba zan iya ɗaukan ki ba" sauka kasa tayi daga saman gadon ta kwanta a kasa ta fara birgima tana masa kuka girgiza kai yayi ya ratiyo jakar computer sa ya kariso wajen tare da sanya hannu ya ɗauke ta cak kamar yar baby suka nufi waje, ganin ya ɗauke ta yasa tayi shiru kamar an kashe gen. Ko da suka fito palo su Zuwaira sun kammala shirya musu breakfast ga kuma basket na school ɗin Jelly sun shirya mata abincin ta a ciki roban cool Yoghurt ne mai ɗan girma da snacks a cikin wata kyakkyawar transparent roba sai pepper chicken a cikin foodflask, daddy bai tsaya yin breakfast ba dan time ya tafi basket na lunch nata kawai ya ɗauka mata suka nufi waje lokacin 7:45 am yayi. Suna fita harabar gidan wata dankareriyar mota kirar Mercedes-Benz ta danno hanci cikin gidan ihu jelly ta fasa mai rikita ƙwaƙwalwa tana faɗin "Daddy ka sauƙe Ni" ba musu ya sauƙe ta da gudu ta nufi motar zata runguma ba ruwan ta da tafi motar yake, saura kaɗan yabi ta kan ta dan irin shigar da tayiwa motar, a sukwane mamallakin motar ya taka birki, ba karamin tsorata daddy yayi ba ganin saura kaɗan motar ya take ta, ita ko, ko a jikin ta bata ma san me tayi ba da gudu ta karisa wajen marfin motar tana faɗin "Yaya Imran nayi kewar ka" gently a ka buɗe kofar motar a hankali ya zuro kyawawan kafafun sa dake sanye cikin cover shoe baƙi waje kafin ya fito gaba ɗaya, cikakken namiji ne chocolate color yana da dogon hanci da dara daran idon ga kyakkyawan saje kwance a face na shi kaman sa ɗaya da daddyn Jelly sai dai shi chocolate color ne sosai, yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara tas da hula baki sai cover baki a kafar sa kyakkyawa ne a jin farko, da sauri Jelly ta faɗa jikin sa tare da sakin kukan shagwaɓa, ɗagata sama yayi yana faɗin "Rabin rai na nima ai nayi kewar ki yanzu dai a dai na min kukan haka ya isa kin san ban son kukan ki ko?" kwantar da kan ta tayi saman kafaɗar sa tana yar dariya kamar ba ita ke kuka yanzu ba, wucewa Imran yayi ɗauke da ita a jikin sa ya nufi daddy dake tsaye sai murmushi yake bakin sa yaki rufuwa yana bala'i kaunar Imran sosai, Risinawa kasa Imran yayi ya gaida daddy, da fara'a daddy ya amsa yana murna "Daddy muje ko lokacin ya tafi" cewar Imran yayi maganar tare da ansan basket ɗin Jelly dake hannun daddy, a tare suka ranƙaya zuwa wajen motar Imran, daddy ya shiga gidan gaba tare da ansan Jelly shi kuma Imran ya koma mazaunin driver ya zauna tare da yiwa motar key yana satar kallon face ɗin Jelly yaja motar suka bar gidan suka nufi School ɗin su Jelly Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu 💞Star Lady💞 *💞TRIPLET'💞 *💞The beginning💞* STAR 🌟 LADY..✍️ Episode 8 *KADUNA* Zaune Abbi yake saman sofa a cikin palon sa ya buga uban tagumi yayi shiru, kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa, duk da sanyin Ac dake cikin palon hakan bai hana shi zufa ba, jikin sa sanye da jallabiya baki gaba ɗaya a hargitse yake, da sallama Irfan ya shigo cikin palon, Abbi yayi nisa cikin tunani bai ji sallamar da Irfan ɗin yayi ba, ````Irfan```` Cikakken namiji ne yana da tsawo dai dai san nan yana da ɗan kiba kaɗan yana da faffaɗar kirjin ga hancin sa dogo har baka idon sa dai dai ne basu da girma sosai kuma ba kanana bane yana da ɗan karamin baki laɓɓan sa na sama brown color na kasa pink color kyakkyawa ne sosai fari tas da shi kamannin sa ɗaya da Umaisha sai dai shi fari ne a shekaru ba zai wuci 26 to 27 years ba sanye yake cikin shadda brown color ɗinkin half jomfa ba karamin kyau kayan suka masa ba kasan cewar fatar sa na da haske. ......Jiki ba kwari ya kariso cikin palon, ya shiga damuwa sosai ganin halin da Abbi ke ciki, kusa da shi Irfan yazo ya zauna ya ɗan taɓa shi yana faɗin "Abbi lafiya?" Yar firgigit Abbi yayi ya ɗago idon sa da suka sauya launi zuwa ja, dogon numfashi yaja tare da sauke wa a hankali, "Abbi me yasa kake yawan sa kan ka cikin damuwa ne? Karfa wani ciwo ya kama mana kai" jinjina kai Abbi yayi murya a dashe yace "Irfan dole na shiga damuwa Alhaji Ma'azu ya cuce ni yaci amanar yarda" riƙo hannun sa Irfan yayi cike da tausayawa yace "Abbi ba komai Allah zai saka maka yanzu dai ina son ka dai na sawa ranka damuwa muyi hakuri muga me Allah zai yi" girgiza kai Abbi yayi kafin yace "A'a Irfan dole mu sai da Company nan, mu fara business da kuɗin dan kar muzo mu rasa na cin abinci" shiru Irfan yayi yana tunanin mugun ta da Aminin Abbin ya masa, duk wani abu mai amfani a company su na sarrafa shinkafa sai da ya kwashe cikin dabara, saboda yadda da shi da Abbi yayi yasa bai farga da wuri ba, har injuna da sauran kayan amfani bai bari ba Abbi yayi reported na shi a police station amma ba wani abun da ya samu sai ma kuɗin da ya rinƙa kashe wa kuma ba'a masa adalci ba saboda Alhaji mu'azu ya saye jami'an tsaron, Alhaji mu'azu ba abun da ya barwa Abbi a company sai kangon gini kawai duk wani abun da ya sace kuma sai da yaje ya musu takardun karya wadda zasu tabbatar da nashi ne, "Irfan tashi muje muyi Sallah azahar lokaci yayi idan muka dawo sai kaje ka ɗauko su Aafia a school" a lokacin Aafia na ss2 ta rubuta waec and neco yau suke graduation Abbi bai samu daman zuwa ba saboda damuwa da ta masa yawa shi kuma Irfan baya nan ya manta ya tafi wajen friend na shi a cikin Zaria City, Umaisha kuma tana ss1, a lokacin Aafia na da 17 years Umaisha na da 15 years "Amma Abbi me yasa ba zaka tambayi bappa Yaya ya baka kuɗi ba ko da bashi ne sai ka tayar da company namu" cewar Irfan yayi maganar yana kallon cikin idon Abbi "A'a Irfan ko na tambaye sa Hajiya Umaiya ba zata taɓa bari ya bani ba kasan halin ta shi kuma Abdul Malik yanzu haka yana cikin matsala ba zan iya tambanyar sa ba, na san idan na tambaye sa ko bai da shi zai nemomin bashi amma bana son sashi cikin damuwa in kara masa damuwa kan wadda yake ciki" waro ido waje Irfan yayi yana faɗin "Abbi Bappa maik ɗin ne yake cikin damuwa? To damuwar me kuma?" Gyara zama Abbi yayi san nan ya fara magana "Akoi wani abokin Takarar sa a fagen aiki su da ya sako sa a gaba a kan company sa *filman Nigeria limited* wai sai dai maik ya sai da masa da company kuma mutun ne mai haɗari sai barazana yake wa maik, kawai dan company maik yafi nasa sanuwa a duniya maik ya fisa farin jini shi yasa yake son dole dole sai ya tankwarar da maik yanzu haka a koi wani aiki da company maik dana abokin takarar nasa dana wasu su kayi applying, aikin gina wani katafaren asibiti ne a Villa to shi Alhaji Auwal ɗin yasan duk in da aiki ya fito kuma company maik ta nuna sha'awar sa a kan aiki to shi a ke bawa shine ya ɗaga masa hankali dan aikin babban aiki ne sosai duk company da tayi Sa'a ta samu aikin to zata samu makudan kuɗaɗe shiyasa ya sako maik a gaba da baraza a kan dole maik ya janye neman wan can aikin kuma ya sayar masa da company sa" kara waro ido waje Irfan yayi cike da damuwa yace "Abbi to me yasa daddyn jelly ɗin ba zai yi report na shi ba" girgiza kai Abbi yayi yana faɗin "No Irfan idan baka iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ka ai wan nan mutumi baka isa ka kai karan sa ba Alhaji Auwal ya wuce tunanin ka yana da wani ɗan iskan yaro mai suna Muneer wan nan yaron har gida yake zuwa yayi wa maik abun da yake so ba yadda maik zai yi da su, addu'a ita ce kaɗai zata raba su dan haka ka taya bappan ka da addu'a Allah ya raba shi da su, amma kuma Maik ɗin ya ce min ya turawa Nawazudden later a kan matsalar kuma na san in dai Nawazudden ya samu later nan to ba makawa zai taimaka wa Maik sosai dan shi ɗin mai yi ne yana da zuciya mai kyau kuma kaga yanzu sune gomnatin gaba ɗaya, In sha Allah zaɓe mai zuwa sai ya zama shugaban kasa dan yace tabbas zai tsaya takara ku tayasa da addu'a" dogon numfashi Irfan yaja tare da saukewa a hankali yace "Abbi duniyar yanzu mutane ba abun yarda bane yanzu dubi yadda kayiwa Alhaji mu'azu gata ka jawosa inuwa ya turaka rana ashe ba ma kai ka ɗai ba har da bappa maik ga kuma maman su Imran ta hana bappa Yaya taimakon ku ta raba zumunci ta rabamu da yan uwan mu gashi Bappa yaya yana da kuɗi na fitan hankali amma ta hana kowa yazo kusa da shi yanzu fa bappa yaya ma ina ga ya manta da ku gaba ɗaya a rayuwar sa nifa idan ba Imran ba ba wan da na sani a gidan shima Imran ɗin dan yana da son zumunci yana zuwa nan kuma muna waya da shi shiyasa amma ba dan hakan da shima ba zan san shi ba" ajiyar zuciya Abbi ya sauƙe san nan yace "Ba kai ka ɗai ba nima nan iya Imran kawai na sani ban san sauran yaran yaya ba amma naji daddy'n jalila yace ƴaƴan yaya uku ne bayan Imran a koi Akil da Akila amma ni ban san su ba ban taɓa ganin su ba ko shi maik ɗin ai sau ɗaya na taɓa kallon jalilan sa lokacin tana yar shekara biyu yanzu ko a hanya muka haɗu ba gane ta zan yi ba ni ma kuma bana jin maik ya san su Aafia kai kaɗai ya sani dan kai kaɗai ne mai zuwa wajen sa" cikin sauri Irfan yace "Ae, kuwa dole wan nan hutun na kai su Aafia wajen sa dan ya san su suma su san shi dan zumunci nima daga nan naga jelly dan rabon da na ganta tun tana da shekara 6 duk lokacin da zanje gidan tana School kuma ban taɓa kwana ba amma wan nan karon zan kira Imran ya zo mu haɗu a can gaba ɗaya muyiwa bappa koda 1 week ne muga juna su Aafia su ga jelly ita ma ta gansu nima kuma na ga su Akila ɗin dan zance Imran yasan yadda zai yi yazo da su" kakalo murmushi Abbi yayi kafin yace "Wallahi har kasa naji daɗi ba dan ina cikin wan nan matsalar ba ai da tare zamu tafi dan nima rabona da ganin maik wajen shekara 6 kenan yanzu sai dai muyi waya kawai" murmushi shi ma Irfan yayi yana faɗin "Abbi karka damu komai zai warware yanzu dai muje muyi Sallah gashi nan har an tada Kabbara" A tare suka miƙe suka nufi waje suna yar hira suka nufi masallaci. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *ABUJA* Da sallama ɗauke a bakin daddy ya shigo palon da sauri Mum dake zaune tana kallon abun da ke faruwa a school ɗin su Rimsha a Tv ta tashi ta nufo su tare da buɗe hannu ta rungumi Rimsha tana murmushi, rungumarta Rimsha tayi tana ɗan murmushi ita ma "My Siha Allah ya miki albarka, Allah ya inganta min rayuwar ki Allah ya dafa muku gaba ɗaya daga ke har babayn daddy" tayi maganar tare da jawo Jehan ta haɗe su ta rungume, sai murmushi daddy da gwaggo suke, mum ta ɗan jima rungume da su tana zuba musu Addua'o'i daddy da gwaggo na amsawa kafin ta sake su ta riƙo hannun su suka haura saman bene dan taje tayi wa Rimsha wanka ita kuma Jehan tayiwa kan ta wanka, duk wan nan dukiya da Allah ya bawa daddy bai yarda da yar aiki ta kula masa da yara ba mum ɗin su ke musu komai dan gani yake ba wadda zata musu abun da ya dace kamar mum, ko itama mum ɗin wani lokaci idan tana musu wani abun zuwa yake ansa da kan sa ya musu sai yace bata musu yadda ya dace sai dai ta girgiza kai kawai tana masa dariya. Wucewa shi ma daddy yayi ya haye sama dan yaje yayi wanka ya shirya yazo ya ci abinci ita ma gwaggo ta wuce nata bedroom ɗin dan yin wanka ta huta. After some hours Mum na zaune saman sofa ita da daddy da gwaggo suna hira a palon, sai murmushi suke suna anna suwa da alama hiran na musu daɗi, da gudu Jehan da Rimsha suka sauƙo suna rige rige zuba musu ido daddy yayi yana kallon ikon Allah ita kuwa mum da ta saba sai ta ɗaga ido ta kalli agogon dake manne a bangon palon ta saman Tv 2:30 pm dai dai girgiza kai kawai mum tayi tana faɗin "Bismillah" da sauri Rimsha ta ɗauke remote ɗin Tv ta canza tasha zuwa news, nan take murmushi ya bayyana a kan face nata ta koma saman sofa ta zauna tana faɗin "Allah na gode maka da kasa TGA ya yarda ya amsa wan nan gayyatar yauma dani za'a fara hira da shi kuma har a gama" tayi maganar cikin harshen larabci, bata gama rufe baki ba Jehan ta anshe remote ɗin ta canza tasha tana faɗin "Daga yau kin dai na kallon wan nan kafurin Krista a gidan nan" a kule Rimsha ta miƙe kamar zata yi kuka tace "Dan Allah Jehan ki bani remote nan wallahi yanzu fa TGA zai shigo kin hanani kallo a bedroom na hakura na dawo nan to dan Allah a nan karki hana ni ki bar ni na kalli jarumi na" kallon sama da kasa Jehan tayi mata kafin tace "eyee ina cewa ɗazun ba cimawa kika gama mana jawabi a school like good girl shine yanzu zaki zo ki fake da kallon wan nan kafurin da ma bai san da zaman ki a duniya ba, gaskiya ne wan nan magana do what I say don't do what what I do" su daddy dai sun zuba musu ido suna kallon ikon Allah "No Jehan wan nan abun da nake kallo ba hara mun bane a musulci kuma dan na faɗi magana a school hakan ba yana nufin ni bazan yi nishaɗi a rayuwa ta ba ko kuma wasu ba zasu yi nishaɗi a rayuwar su ba abun da nake nufi kar ku shagala da duniya ku manta da lahira kuma ai ni ban shagala da duniya ba kema sheda ce a kan hakan kiyiwa Allah ki bani remote ɗin nan" ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka duk wan nan magana da suke cikin harshen larabci suke yin sa, a kule Jehan tace "Ba zaki sake kallon wan nan mummunar mutumin mai kama da zunubin a gidan nan ba" a fusace Rimsha ta wanke mata fuska da mari tare da sanya hannun ta ta fisge remote ɗin ta canza tasha ta mai da News, ta koma ta zauna saman sofa ta ci-gaba da kallon ta, cikin zafin nama da ɓacin rai Jehan tayi kanta da niyar dukan ta da sauri daddy ya miƙe ya ɗauki Jehan ɗin cak suka haura sama ihu ta fara yi masa tana wuntsilo kafofin ta, Kallon Rinsha mum tayi cikin harshen shuwa arab da kakkausan murya ta fara magana "Daga yau idan kika sake marin sister ki Rimsha sai ranki ya ɓaci koma me ta miƙi ba muna zaune a wajen ba ai kin san ba zamu bari ta hana ki kallon ki ba zamu ansan miki, karki sake yin wan nan kuskure ko da sunan wasa kada ma ki sake tana magana kina bata amsa gaba take da ke, ki rinƙa mata biyayya kuma ki gama kallon idan daddyn ku ya rarrashe ta kije ki bata hakuri kina jina?" Cikin ladabi da biyayya tayi kasa da murya tace "Naji mum kiyi hakuri ba zan sake ba" har cikin ranta mum taji daɗi Rimsha yarinya mai biyayya ga hakuri kamar damo bata son yawan hayaniya, A ɓangaren daddy kuwa kai tsaye bedroom na shi ya wuce da Jehan dake ta wuwwuntsilo masa kafofin ta sama tana masa ihu, saman katafaren gadon sa ya sauƙe ta san nan ya zauna gefen ta tare da ɗaure fuska ya fara magana cikin harshen turanci "Why Jehan you always look for troubles, amid you are a senior, you know Rimsha is patient, but you vividly push her to fight you at most?" Shiru tayi tana turo baki "As from Today kar na sake ganin kina neman Rimsha da faɗa kina ji na ko?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh ba tare da tayi magana ba. Miƙewa Rimsha tayi zata bar palon mum tace "A'a Rimsha kin fasa kallon ne kuma?" Turo baki Rimsha tayi kamar za tayi kuka tace "Mum hankali na ya kasa kwanciya ne zanje na bawa Jehan hakuri sai na dawo na ci-gaba da kallon" "No my Rimsha zo kiyi zaman ki karki damu ki bari sai kun shiga ɗaki sai ki bata hakuri" ba musu Rimsha ta dawo ta zauna ta kafe Tv da dara daran sleeping eyes nata masu ɗaukan hankali, sosai ta kafe Baturen dake magana a Tv da idon ta yana sanye da face mask a face na shi, farine tas yana sanye da kananan kaya sai jacket da ya ɗaura a saman kayan nasa kasan cewar sanyi dake wajen nasu, duk da rabin face nashi a rufe da face mask hakan ba zai hana ka gane kyakkyawa ne ajin farko ba yana da murɗaɗen jiki ga faffaɗar kirjin kamar wani zaki kirjin nasa a cike ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda training da yake, "Rimsha ni ko in da tambaya a kan wan nan boss ɗin naki" cewar gwaggo ɗago sleeping eyes nata tayi ta kalli gwaggo, calmly tace "To gwaggo Allah yasa na sani" "Jarumin nan naki mutun ɗaya ne ko biyu?" Cikin sauri Rimsha tace "Shi kaɗai ne wajen mum da daddyn sa dukka" shiru gwaggo ta ɗan yi kafin tace "Amma wani lokaci zaki gan shi da ido ligh ash wani lokaci kuma ligh blue shi yasa nace ko su biyu ne" girgiza kai Rimsha tayi tana faɗin "Eh gwaggo nima ina ganin hakan sai dai ina tunanin sanya kalar idon nasa yake dan shi kaɗai ne wajen mum da dad na sa bai da wani ɗan uwa i think yana using eye contact ne" mum ce ta ansa zancen da cewa "Ni ma tun da jimawa nake son mata wan nan tambaya ban samu dama ba amma fa dukka idon da light blue da light ash ɗin duk suna masa kyau sosai" da sauri Rimsha tace "A'a mum light blue nan yafi masa kyau idan ya sanya ta zaki ganshi idan ya ɗago idon nasa har wani kyalli take kamar madubi, tana ɗaukan hankali idan kikaga idon nasa zaki yi tunanin light ash ne amma kuma light blue ne ni kasa ganewa ma nake har sai ya ɗaga idon nasa ko yana kallon mutun ko yana kallon wani abu a nan ne nake iya gane light blue ne amma idan kika gan shi at the first time zaki yi tunanin light ash ne" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi bene tana faɗin "Mum an gama shirin dan shi baya wuce 15mins yake badawa a cikin time na sa, yace kowani second a rayuwar sa tana da matukar muhimmanci" girgiza kai kawai mum tayi tana mamaki irin kaunar wan nan Christan da Rimsha keyi, mutumin da bai san hanyar Nigeria ba ma amma ita tana nan tana fama da kaunar kallon face na shi da labarai a kan sa. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *UNITED STATES OF AMERICA* *WASHINGTON DC* *HARVARD UNIVERSITY* *Allotment garden* Babban filine mai girman plot 10 filli ne mai matikar kyau da kawatuwa, wajen cike yake da shuke shuke kanana kanana da manya manyan flowers masu bala'i kyau da ɗaukan hankali launin yellow da kore, wani wajen an yi design of heart da flowers wani wajen kuma an rubuta Harvard University, daga bakin katafaren gate ɗin shigowa an rubuta Welcome to *Allotment garden* da flowers kore da yellow an kawata wajen sosai da sosai gwanin ban sha'awa sai kamshin furanni ke tashi a wajen, gaba ɗaya garden ɗin shinfiɗe yake da wasu kanana ƙanana grass masu bala'i kyau kai kace grass carpet ne a shifiɗe a wajen ga wasu Gumaka da a ka kawata su suna zubar da ruwa, ƙatuwar Giwa a ka gina ta a tsakiyar wajen ta ɗaga hancin ta sama ruwa na zuba ta kofar hancin nata kasan ta kuma an kewaye shi kamar rujiya ruwan na taruwa a wajen daga gefen Giwa ga kuma maciji shima ya ɗaga kai yana fesa ruwa daga bakin sa, ko ta ina ka zaga a wajen fitullune masu haske gaske ke haske wajen ga wasu tamtsama tamtsaman kujeru na alfarma masu numfashi, launin Milk color cike a wajen, daga karshe karshen ginin dogayen bishiyoyi ne masu ganye ja da kuma yellow, Allotment garden ya kawatu iya kawatu wa, duk girman wajen shiru babu mutane sai wani haɗaɗen Bature dake zaune saman sofa fari tas da shi jikin nan nasa ka rantse da Allah bai taɓa taka kasa ba saboda laushe da kyau gashi a kwance luwai luwai Kyakkyawan farin matashi ne mai jini a jika, sosai yake da hasken fata da kallo ɗaya zaka masa kasan asalin 𝑩𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆 ne, dogone cikakken namiji, yana da faffaɗan kirji da yasa muscles ɗinsa Fito wa sosai cikin baƙar top din Salvatore ferragamo da ya Fito da kakkarfar farar surar jikinsa, kyakkyawan fuskarsa ɗauke take da dogon hancin da ya ƙara wa fuskarsa kyau, ɗan karamin bakinsa ɗauke yake da kyakkyawan laɓɓa dark purple da yayi wa karamin bakinsa kawanya , a hankali ya ɗago da dara daran eyes dinsa masu shegen kyau kamar yasa musu kwalli, kwayar idanuwansa da ta kasance light brown mai ɗaukar ido, idan kayiwa idon na shi kallo a fusge sai kaga kamar idon damisa (tiger) a hankali ya fara motsa idanuwansa dogayan eye Lashes dinsa suka kara fitowa sosai , daga saman idanunsa kuwa sosai girarsa take a cike da taso haɗewa sabida cikarta, gefe da gefen fuskar sa duk gargasar gashi ne da yasha gyara, kyakkyawar dark brown hair sa har gadon bayan sa ya kai masa sai curly gashin kan nasa keyi, zaune yake shiru fuskar nan tasa a ɗaure take tamau kamar bai san me dariya ba, daga gefen da gefen sa wasu mahaukatan karnuka ne jibga jibga guda uku masu gashi sosai a jiki, biyu daga cikin su farare ne kal ɗayan kuma ja gashin jikin su har ja yake a ƙasa saboda yawa manaya manya ne sosai karnukan sun samu kiwo nai kyau. Wan na shi ne *Michel* wasu matasan Turawa ne su uku suka shigo wajen suna tafiya suna kwaɓe fuska kusa da Michel suka zauna, ɗaya daga cikin su yasa hannu yana shafa gashin jikin karen dake kusa da shi, cikin harshen turanci Michel yace "Dest me ya tsayar da ku sai yanzu kuka zo?" Guntun tsaki Dest ya ja kafin yace "Wan nan ban zan uncle da a ka kawo sabon nan ne mana wai yaji labarin mune marasa ji a School nan dan haka zai sa mana ido kullun idan yazo mana lecture bai gammu a class ba sai ya hukun tamu" dogon tsaki Michel yaja ba tare da ya sake magana ba "Michel muje mu sha giya ko? Ina jin yinwa" Cewar ɗayan dake daune ta ɗayan ɓangaren Michel ɗin, ata kai ce Michel yace "As from Today na dai na shan wine" waro ido waje Dest yayi kafin yace "Michel kana jin me kace kuma? Ka dai na shan giya?" Shiru Michel yayi bai sake magana ba, a ƙule Johnson ya buɗe baki zai fara magana kenan wani Bature ya shigo wajen jikin sa sanye da suit kallo ɗaya zaka masa kasan lecturer ne, miƙewa tsaye gaba ɗaya guys ɗin suka yi amma ban da Michel dake zaune kamar bai da mutumin a wajen ba, kasa da murya Johnson yayi dai dai sai tin kunnen Michel yace "Wan nan shine sabon teacher'n shi bai san mu ba zai iya sanar da Romeo idan muka masa taurin kai" kallon sama da katsa Michel yayiwa Johnson kafin ya mai do da kallon sa kan uncle ɗin dake tsaye yana musu kallon tuhuma kasa kasa Michel yace "Romeo baya kasar nan tun jiya" bai karisa rufe baki ba uncle ɗin ya daka musu tsawa "Kai dest dana ce kuje ku zauna kuyi karatu shi ne kuka zo kuka zauna a nan kuna shirme ko? To yau zaku yi bayani, ba kunce ku baku ji ba tun da na shigo makarantar nan ko wani malami sai yace min kar na shiga har kan ku kuna da haɗari, ku gaku tantirai to nima tsohon ɗan daba ne kafin daga baya na ajiye dabanci na rungumi bairo da takarda, ku fara frog jump daga wajen da kuke, yau sai kun kewaye min garden ɗin nan sau hamsin" ya kai karshen maganar tare da dawo da kallon sa kan Michel yace "Kai ne ogan su ko to naka hukunci daban ne kukace ku yan iskan gari ba?, ba zaku yi karatu ba sai dai ku zauna kuna jagaliyanci ku addabi masu karatu parents naku na kashe makudan dukiya a banza, to ni zan gyara muku zama" duk wan nan magana da su cikin harshen turanci suke yin sa, ganin wan nan uncle ɗin ba zai dai na wan nan surfa uwar masifa da yake bane gashi ya toshe masa kunne yana da mun sa yasa Michel ɗin ya miƙe tsaye tare da shafa kan ɗaya daga cikin jibga jibgan karnukan sa kasa kasa a sai tin kunnen karen yace cikin harshen turanci "Lucky ko ya masa hankali" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna saman sofa ɗin, dirowa kasa lucky yayi tare da girgiza jikin sa wani jibgege da shi ya ɗaga wuyan sa sama ya fara takowa a hankali hankali ya nufi uncle, baya baya uncle ya fara ja yana faɗin "Ku dakatar da karan nan" kamar jira lucky yake uncle yayi magana ya rufa masa, a guje uncle ya juya yana ihu, da ɗan ma dai dai cin gudu lucky ya bi bayan sa ta yadda ba zai kama sa ba zai kuma hawalar da shi, kwashewa da dariya su Johnson suka yi suna faɗin "New uncle ma ya shiga layi" suka kai karshe maganar tare da tafa hannu shi dai Michel yana zaune shiru, Shi kuwa uncle gudu yake kamar zai tashi sama yana ihu a kawo masa ɗauki amma ina duk in da yazo wucewa sai student sun tashi sun gudu dan sun san halin lucky duk wan da ya kwana ya tashi a Harvard University to yasan da zaman Lucky da Winston Copper karnukan nan bala'i ne basu da mutunci gashi sun samu horo da kyau wajen Michel, duk abun da Michel ɗin yace suyi shi suke idan yace su rikita mutun zasu bi mutun amma ba da gudu sosai yadda zasu kama mutumin ba sai su bishi da gudu kaɗan kaɗan dan su galabaitar da mutun san nan duk in da ka shiga sai sun bika ba wanda ya isa ya raba ka da su sai shi Michel ɗin da ya haɗa ka da su, Tsabar gudun da uncle yake har sai da wandon sa ta cire ya rage daga shi sai Short sai uban zufa yake yana ihu yana neman tai mako, a guje ya shiga Harvard Community garden wajen cike yake da student, ganin uncle da gudu yana ihu ga kuma lucky na bin sa a baya ne yasa gaba ɗaya student ɗin suka fara gudun cetan kan su suma, uncle dai yanzu karfin sa ta fara karewa ya rage gudu daker yake nishi girgiza jiki Lucky yayi tare da yin haushi mai firgita kwakwalwa nan take uncle ya ji sabon karfi yazo masa ya kara kwasawa a guje ya nufi wajen garden ɗin yana ihu kamar mahaukaci, a guje ya shiga wajen Harvard swimming pool dake kusa da goro place watermelon, manya manyan swimming pools ne a wajen wadda a kalla zasu kai 20 an kawata wajen sosai da sosai, a sukwane uncle ya faɗa cikin pool ɗaya, a tunanin sa ya tsira sai nishi yake sama sama kamar zai mutu, lucky na shigowa wajen shi ma ya faɗa cikin ruwa ihu uncle ya fasa tare da fita a sukwane jikin sa duk ruwa tsantsin tiles ya kwashe shi ya faɗin ƙasa ya buga kai a tiles, rage gudu lucky yayi har sai da uncle ya miƙe ya ci gaba da gudu san nan shi ma lucky ya rufa masa baya. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu shin ya uncle zai ƙare da *Lucky* wayyo ni *Princess Teema* Michel na sha'anin sa 🤣🤣🤣🤣🤣 💞Star Lady💞 *💞TRIPLET'💞 *💞The beginning💞* *Episode 9* .....Idan uncle yayi kamar zai tsaya sai Lucky ya girgiza jikin sa yayi haushi mai rikita ƙwaƙwalwa, uncle kuma da yaji haka sai yayi tsammanin lucky ya kusa kama shi ne sai ya daure ya kara karfin gudun nasa, gaba ɗaya student da ke ganin halin da uncle ke ciki sun tausaya masa ba kaɗan ba dan ya fara manya ta a kalla zai kai 45 years ba yaro bane, ga abun dariya ga kuma abun tausayi, Shi kuwa Michel yana zaune hankalin sa kwance, kallon sa test yayi cikin muryan neman alfarma yace "Please Michel ku ɗauke ni aiki mana a gidan ku koda goge muku takalma ne idan zaku fita ina son in ganni dai na zauna a cikin gidan ku" shiru Michel ya ɗan yi kafin yace "Babu wan da ya isa ya kawo wani Mai aiki gidan mu idan ba Romeo ba shi kaɗai yake iya ɗaukan masu aikin da yake so, ko daddy bai isa yace ya ɗauko mai aiki ba kuma shi Romeo kafin ya ɗauki mai aiki yana da doka, dokar kuwa itace idan har yaga ka dace ya ɗauke ka aiki tofa zaku yi agreement da shi ne zai rubuta maka takarda kasa hannu misali idan zai ɗauke ka aiki zai faɗa maka aikin wata kaza ko Shekara kaza zaka masa idan ka amin ce to zai rubuta maka takarda kasa hannu, idan kuma kasa hannu tofa ka sani komai zai faru sai ka cika adadin shekarun da kukayi da shi ko da baban kane ya mutu a ranar sai kazo aiki baka da wani iko da kan ka sai abun da yace kayi kuma shi aikin sa bata da time ko wani lokaci yana iya saka aiki koda cikin dare ne, babu wan da ya isa ya tinkari Romeo yace ya ɗaga maka kafa, ko daddy ka sani tsoron sa yake, kuma mu ai kasani dukka gidan mu sojoji ne masu aiki har abinci sojoji su ke girkawa wan nan tsarin Romeo ne" "please Michel ka ɗan roƙe sa mana ya ɗauke ni ko da mai goge muku takalma ne" kallon sama da kasa Michel ya masa kafin yace "Ko daddy bai isa ya ce da Romeo ga abun da zai yi ba shifa abun da ya ga dama yake, kai mutun ma ya isa ya tinkare sa yace masa yayi wani abun hmmm ka tambayi Johnson ya faɗa maka, kai bama sai an faɗa maka ba ni zan baka 1 million $ idan ka iya tinkarar Romeo ka gaida shi ma kawai" ya kai karshen maganar tare da miƙa wa ya bar wajen cikin sauri dest da test da John ɗin suka rufa masa baya, da sauri karnukan sa biyu Winston da Copper suka diro kasa tare da girgiza jikin su wasu jibga jibga da su cikin takun ƙasaita suka rufa masa baya, A ɓangaren uncle kuwa kasa cigaba da guduwa yayi ya zube kasa a dai dai Allston dake kusa da hanyar tafiya community garden, ya kasa ci gaba da numfashi, numfashi ta masa wahalar jawuwa hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya sume, da guduwa Lucky ya kariso kansa yana kokarin kai masa cizo a kafa Michel da ya iso wajen yanzu yace "Wait Lucky" ba musu lucky ya tsaya tare da juyawa da gudu ya koma wajen Michel ɗin shafa kan sa Michel yayi kafin ya juya ya bar wajen Lucky Winston Copper suka sufa masa baya san nan su dest suka rufawa su lucky baya, Su Michel na tafiya sauran uncle's ɗin suka zo suka ɗauki uncle dake sume suna ta masifa "da ma ai mun faɗa maka karka shiga sabgar wayan nan kaƙi yanzu gashi kaji a jikin ka ai" haka sukayi ta surfa masifa har suka wuce da shi cikin *(HUHS) Harvard University Health Services* Shi kuwa Michel kai tsaye ya wuce *Harvard Square Parking Garage* yaje ya shiga dankareriyar motar sa kirar *Aston Martin* a guje Winston Copper suka shiga gidan baya shi kuma Lucky ya shiga gidan gaba, Johnson ma wucewa yayi ya shiga motar sa, kuɗi Michel ya ɗebo dollars ya miƙawa su dest yana faɗin "Kai test zaka iya zuwa ka gaida Romeo ne gobe na zo maka da kuɗin ka cash 1 million dollars zan baka idan ma sun maka kaɗan zan karama" cikin sauri test yace "A'a ni nama fasa batun aikin ai" turɓune fuska Michel yayi kafin ya miƙa musu kuɗin hannun sa yana faɗin "See you next time guy's" ba musu dest da test suka ansa kuɗi, Michel ya kunna motar sa da gudun gaske ya figeta ya bar School ɗin dama shi Johnson tun isowar su parking space ɗin yaja motar sa bai tsaya wani magana ba, su ma dest da test kowa ya shiga motar sa ya wuce gida dan yau ba zama a School sun san sunyi tsiya kar aje a faɗa wa daddyn su gwara shi Machel shi da Johnson ba mai karfin gwiwar iya nufan hanyar gidan su ma bare ya kai karan su. John wadda kuka fi sani da Johnson ɗane ga uncle ɗin su Romeo, mai suna uncle herry a gidan su Michel ɗin yake da zama da shi da ɗan uwan sa jay. Gudu sosai Machel ke shararawa a kan makekiyar titin *beach drive* duk motar da tazo sai dai ta kauce ta bashi hanya ba dai shi ya kauce ba, mutane na girmama shi saboda tambarin dake gaban bambam motar sa wadda a ka rubuta *William jacop Family* saboda wan nan suna yasa suke kaucewa su bashi hanya, *Washington DC* Birni ne mai matukar kyau da ɗaukan hankali kuma shi ne babban birnin Usa gaba ɗaya garine na manya manyan masu kuɗi ta duniya, garine mai cike da dogayen gine gine na alfarma ga wurare daban daban na wasanni da kayatar da ɗan adam, duk ta in da ka juya irin wayen nan kyawawan jirgin kasa na masu shiga har cikin anguwa nan ne (Portland train) ma su kama da luckgerious bus, ko wani bakin titi zaka samu kyawawan kujerun zama wadda passenger zai zauna ya jira jirgin kasa ko Asalin Bus, kowani wajen da kujera yake an sanya masa runfa mai matukar kyau saboda ruwan sama kowa harkan gaban sa kawai yake ba ruwan wani da wani, *Washington DC* garin ya haɗu ta ko ina ya kayatar matuka, kawatuwar sa ba zai faɗu a baki ba, Sosai Michael ya kunna kiɗar sa ya kure volume yana sharara gudu yana kaɗa kai su lucky na tayasa, cikin kankanin lokaci ya iso katafaren unguwar su mai suna *lot 33*, anguwa ce ta manya manyan masu kuɗi da masu mulki ma'ana yan siyasa da sarakuna, ko ta ina a anguwar the most billion dollars gidaje ne a wajen wata gidan ma idan ka ganta kace da gold a kayi ta, anguwar tsab tsab take babu alamar datti ko kaɗan kamar mutane basa rayuwa a waje saboda hasken da tsabtar unguwar tayi, har kan titi babu alamar datti ko kaɗan duk wani lungu da sako na anguwar titi ne mai matukar kyau shifiɗe har bakin kofar gidaje, gaba ɗaya gidajen dake wajen babu hawa 2 daga uku yayi sama dogayen gini ne sosai a unguwar kai dagani ba tambaya kasan anguwar na masu shi ne. Wata dankareriyar hanya Michel ya miƙa kai da ganin hanyar kasan ta musamman ce, kai tsaye wata aljannar duniya ya tinkara, dan wan nan gida itace aljannar duniya, tun daga nesa ya fara danna horn na motar sa, a guje wasu jibga jibgan sojoji masu jini a jika lafiyayyu masu razana mai rai suka wangale masa tampatsetsen gate ɗin wadda da ganin gate ɗin kai kasan ba gidan wasa bane a wajen, dan haɗuwar gate ɗin gidan kawai ma abun lallo ne, yana kari sowa wajen ya danna hancin motar sa cikin gidan ya nufi second gate sai sara masa jibga jibgan sojojin suke, in da second gate ɗin yake, kafin ka karisa wajen sai ka shiga ta wani waje kamar ɗaki wadda a ka rubuta scanning a wajen, cikin wajen yana bada wuta launin purple, wajen bai da nisa da gate 2, wajen cike yake da na'urorin da a ka haɗa su da jikin bangon wajen, san nan wajen babu kofa zaka shiga ta nan idan wajen ya gama scanning naka sai ka fita ta can haka wajen yake ko da Michel ya isa wajen, dai dai wajen da a ka rubuta scanning place ya tsaya, yana jira, sai da na'uran dake wajen tayi scanning na motar sa tsab dan tabbatar da ba wani mugun abu a motar tasa, bayan na'uran ta gama scanning sai da ta ɗauki 2mins san nan gate 2 yayi kara kiii kafin ya buɗe kansa da kan sa alamar motar Michel babu komai dan gate ɗin an haɗata da nauran ne idan a koi wani mugun abu a tattare da kai to gate ɗin bazata buɗe ba zatayi kara kamar jiniyar motar yan sanda su kuma jibga jibgan sojojin dake bakin gate na farko suzo su kamaka su binciki me kazo da shi yasa nauran ke kara shiyasa a gate ɗin farko a kasa sojoji na biyu kuma gate mai aiki da na'ura mai buɗe kan ta kuma ta rufe kanta. Da gudun gaske Michel ya figi motar sa zuwa cikin gida ````Wow```` Gida ne mai girman Hectare 4 wato plot 24 kenan, gida ne gari guda, gaba ɗaya gidan har jikin bango da kasa, tiles da glass ne kai kace ginin tiles da glass ne kawai, hawa huɗu ne gidan, ginin ya tsaru iya tsaruwa ya fita iya fita ko gidan shugaban kasa albarka parking space na gidan kawai taci 3 palo san nan shi kan shi parking space ɗin a keɓe yake waje guda an sa masa katafaren gate da na'urorin da zasu wanke motar da a ka fita da ita idan an dawo, kamar ɗaki a ka gina parking space ɗin motocin ne kala kala jere a wajen, a tsakiyar harabar gidan wani gini a kayi kamar rijiya a ka kewaye wajen san nan a kayi wanin gini a tsakiya kamar fai fai ruwa na zuba a wajen, garden na gidan ya kai girman plot 2 cike yake da kana kanan flowers masu kamshi launin je da kore a dai dai kofar shiga garden ɗin daga ɗan gefe an rubuta *Romeo da flowers*, ga manya manyan kujeru masu numfashi na hutawa shirye a wajen, ga fitillu masu hasken gaske sun haske ko ina, gaba ɗaya garɗen ɗin kewaye yake da glass ƙasan sa kuma tiles ne wani gefen kuma grass carpet, tsayawa zayyana muku haɗuwar garden ɗin nan zai cimana lokacin sosai, wajen lambun daddy kawai yaci 2 plot, dan daddy mutun ne mai son lambu sosai, kowani ɗaki a gidan yana da balcony ta gaban sa an kawata wajen da furanni masu ɗaukan hankali, gaba ɗaya gidan kewaye yake da jibga jibgan sojojin masu jini a jika suna tsaye rike da manya manyan bindigu fuskar nan tasu kamar an aiko musu da sakon mutuwa, idan ba kana da dakakkiyar zuciya ba ka kalli face ɗin sojojin nan to zaka iya sumewa dan babu alamar annuri a face nasu ko kaɗan, kowani lungu da sako na gidan jibga jibgan sojoji ne riƙe da manya manyan bindigu kai kace wajen yaki zasu tafi, kai daganin hakan kasan ba gidan wasa kazo ba, manya manyan swimming pools uku ne a gidan ɗaya na Romeo ne shi kaɗai ba mai zuwa wajen sai shi, biyun kuma na sauran yan gida, haɗuwar wan nan gida ba zai faɗu a baki ba dan gidan nan gari ne guda, Kai tsaye parking space Michael ya nufa yana zuwa wajen, daga saman gate ɗin wata yar na'ura kamar yar baby ta fara karanto number motar sa daga farko har karshe san nan ta kira sunan wadda ya fita da motar, nan take gate ɗin ta buɗe kan ta, Michael ya shige, duk wani kofa na gidan sai da Romeo ya sai tata da nauran sa dan ya rinƙa samun information a kan waye ya fita waye ya shigo, ko mota zasu ɗauka sai yasan da wani mota suka fita kuma waye ya fita da motar, ko wani kofa a koi matakan tsaro a jikin ta, idan ba gate ɗin farko na shigowa gidan ba bawani waje dake da mai gadi shi ma gate ɗin farko ya bar shi ne dan criminal ya samu ya wuce gate ɗin farko ya shiga gidan, gate na biyu ya tonasa asiri, kuma ba halin guduwa sojojin dake gate na farko zasu yi ram sa shi wan nan shi ne dalilin da yasa ya bar jibga jibgan sojoji a wajen, Michel na shigar da motar sa ya kashe ta ya fito tare da su lucky, ya danna wani waje kamar remote san nan ya fice daga wajen su lucky na biye da shi, nan take ruwa ya fara sauƙowa yana wanke masa motar tasa, a she ruwa ya danna dan ta wanke masa motar. Yana fita ya wuce wajen ɗakin su lucky dake kusa da garɗen, ɗakin karnukan ma duniya guda ne har da katon gado a ka sanya musu kai kace ba kuɗi a ke sawa ake sayen abubuwan nan ba, yana kai su ɗakin su ya rufe su ya fito Kai tsaye katafaren kofar da zata sada shi da cikin gida ya nufa shi kan shi kofar ma abun kallo ne, yana zuwa wajen ya buɗe yatsun sa ya ɗaura saman finger scanner yana kwaɓe fuska yana jin haushin wan nan matakan tsaro irin na gidan, ba karamin fama ya shaba kafin Romeo ya yarda ya dai na haɗa shi da bodyguard suna raka shi School har rashin lafiyar karya yayi dan a barshi ya rinƙa fita shi kaɗai yana shanawar sa, bayan finger scanner ta gama scanning na hannun sa ne katafaren kofar mai girman ta wangale kan ta, guntun tsaki yaja tare da kutsa kan sa cikin, wani aljannar duniya ne a wajen palone mai girman plot 1 da rabi shi kansa palon yayi girman gidan wani, palon ɗauke yake da tampatsa tampatsan kujeru na alfarma masu numfashi set huɗu ko wani set kuma yana da nisa da ɗan uwan sa kai kace ma kujerun ba a palo ɗaya suke ba saboda ratan dake tsakanin su zaka ce palo huɗu ne kusa da juna amma kuma ba haka bane dukka palo ɗaya ne girman palon ne yasa a kai wa kowani set da mazaunin sa, kowani set da kalar sa sky blue fari milk golden color shine colors ɗin kujerun, wajen table ɗin cin abincin su ma duniya ne guda, table ɗin yana da tsawon 2meter ga haɗanɗun kujerun sa launin golden color masu ɗaukan hankali da ɗaukan ido guda 24, gaba ɗaya curtains na falon farare ne kal kamar yanzu a ka fito da su daga kwalin su saboda haske, Makekiyar Tv ɗaya ne a palon mai bala'i girma wadda idan kana kallon mutun sai kaga kamar ka kira shi ya amsa saboda girman Tv, fentin palon gaba ɗaya golden color ne sai ɗaukan ido yake kamar gidan gold, daga kusa da sofa set milk color nan wata iriyar tampatsetsiyar staircase ne mai kamar indomie raun haka kamar maganain sauro haka staircase ɗin yake, daga farkon staircase ɗin a miƙe yake straight daya ɗan yi nisa kamar nisan tsawon mutun daga nan sai ya tafi sama a nannaɗe kamar maganin sauro, shi kan shi staircase ɗin abun kallon ne duniya ne guda fentin jikin sa golden color ne kamar gold san nan ga wasu kwayaye fitillilu a jikin sa dake haske stair ɗin da kyau sai walwali yake yana kwalli kamar gold, staircase ɗin nan ya haɗu iya haɗawa sosai, gashi tsab da shi kamar kafa bai taɓa taka kan shi ba, a kasan iya palo da katafaren kitchen ne kawai a wajen sai wajen dining table wadda shima duniya guda ne wajen, kitchen ɗin kawai kusan 1 plot ne a wajen babu abun buƙata da babu a kitchen ɗin jibga jibgan sojoji ne ke musu girki da duk wani aiki na gidan gaba ɗaya gidan daga farkon ta har karshen ta babu alamar mace a cikin ta gaba ɗaya palon kasan kewaye yake da tsadaddun curtains masu bala'i kyau da ɗaukan hankali farare tas ko ta ina hasken gaske ne a palon saboda kyawawan fitullin dake bada haske daga sama POP, palon nan a gyare yake tsab kai kace ba a taɓa taɓa komai na palon nan ba saboda tsab ɗin da yake, sai wani fitinan ne kamshi ke tashi a palon kamar an yi ɓarim turare, Wan nan gida dai sai dai muce Masha Allah dan ta ko ina yayi ne Kai tsaye staircase ɗin Michel ya nufa sai kwaɓe fuska yaƙe, yana hawa wani kyakkyawan Bature ya sauko wadda kallo ɗaya zaka masa kasan daddyn su ne dan kammanin sa ɗaya da Michel sai dai shi kwayar idon sa blue ne, ko kallon in da yake Michel bai yi ba ya wuce, cikin sauri daddy yace "Welcome My tiger" da yake haka daddy ke kiran sa a cewar daddyn wai idon Michel ɗin na shining like Tiger eyes shi yasa yake ce masa tiger "Thank you dad" ya faɗa tare da wucewa ya karisa hawa saman, a mai makon ya shiga palon saman sai ya kauce hanya ya shari kwana ya nufi wajen wata kofa wadda daga bakin kofar kana iya leko palon kasa, kofar ya sanyawa fingerprint na shi na tsakiya, nan take kofar ta buɗe ya shige abun sa, shi kuma daddy ya wuce ya sauƙa palon kasa ya nufi wajen sofa sky blue ya zauna tare da kunna News a makeken Tv plasma su. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *KANO* Sai 04:00 pm su jelly suka dawo gida a motar Imran, sauri sauri Imran ya sauƙe su a gida tare da yin sallama da daddy dan lokacin jelly tayi barci a jikin daddy sauri sauri ya juya kan motar sa ya bar gidan dan tsoron kar dare ta masa a hanya ba shi da amsan da zai bawa Ammie sa idan ta tuhume sa a kan ina yaje, wucewa cikin gida daddy yayi kai tsaye bedroom na shi ya wuce su Zuwaira na gaida shi amma bai kula su ba saboda bai son amsa magana jelly ta tashi daga barcin da take, saman gadon ta dake bedroom na shi ya kwantar da ita a hankali dan karta tashi, sai bayan ya kwatar da ita ya tuna sun manta basket na ta a motar Imran, wucewa yayi ya ajiye jakar computer sa ya nufi toilet dan yin wanka. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *👹 DAULAR MUTUWA 👹* Yan sanda mota biyu ne suka shiga wajen wan nan dajin dan sun samu labarin akoi gidan magicians a wajen, tun daga ɗan nesa suka kashe motocin su, suka sauka suna tafiya da kafa a hankali hankali kamar wasu ɓarayi sai sanɗa suke suna tafiya, suna addu'ar Allah yasa nan shine address ɗin da a ka basu kuma Allah ya basu Sa'a su samu su tarwatsa wan nan gidan dan an sanar da su waje ne mai haɗari ga kuma a saran rayuka da basu ji ba basu gani ba da ake a wajen, a na zaluntar bayin Allah a wajen, Sunyi tafiya mai nisan gaske sunayi suna duba map har sun gaji wasu daga cikin su suka cire takalmin kafarsu suka ci-gaba da takawa da tafin kafar su, Dai dai wasu bishiyoyin masu tsawo ga wajen da ɗan duhu saboda cikan ganyen bishiyoyin, suna shiga wajen sun ɗan fara tafiya kenan suka fara jin wata iriyar gigitatchiyar takun sahu dan duk in da a ka taka sai kasa ta bada dum dum, a guje suka nemi wajen ɓuya kowa yayi ta kansa suka laɓe suna ɗan leƙowa wasu sun laɓe wajen bayan bishiya wasu kuma sun shige cikin ciyayi, suna tsaye sunyi tsurutasu suna jiran su ga wanene zai bayyana, ba karamin girgiza sukayi ba ganin barbushi basu taɓa ganin irin wan nan halitta mai girma da muni har haka ba nan take tsoro ya bayyana a face nasu wasu daga cikin su fitsarin tsoro suka saki a wandon su, wasu kuma sumewa sukayi a wajen dan halittar Barbushi sai mai karfin imani zai iya kallon sa kuma yasha lafiya, wani ɗan sandan ma har da kashi yayi a wando saboda tsoro, jikin su sai kerma yake ido ya rena fata sai zufa suke sun kasa riƙe bingun hannun su wasu daga cikin su sai kalmar shahada kawai suke furtawa a ran su, shima kalmar shahadar basu iya furtashi dai dai ba dan akoi masu ɗauko farkon kalmar shahada su karasa da wata sura ko nasi ko falaki saboda tsoro, ɗaya daga cikin sune yayi ta maza ya saita Barbushi da bindiga, hannun sa sai rawa yake haka ya daure ya danna kunamar bindigar ya harbi Barbushi a sai tin hannun sa, abun da ya kara rikita ƙwaƙwalwa su shine da bullet ɗin yaje sai ya daki hannun Barbushi ya faɗi kasa kamar wadda ya daki karfe, ihu ɗan sandan da yayi harbin ya saki saboda tsorata dan bai taɓa ganin in da aka harɓi mutun kuma bullet ɗin taje ta daki jikin sa kuma ta dawo kasa ta faɗi kamar ta daki karfe ba, jin ihun ɗan sandan yasa Barbushi juyo da idon sa masu kama da wuta dai dai sai tin in da yaji ihun, kasan cewar wajen da ɗan duhu baka gani sosai yasa nan taƙe idon Barbushi ta rikiɗe ta zama kamar torchlight mai hasken gaske kai tsaye sai kan ɗan sandan da ya harbe sa hasken idon nasa yaje, a guje ɗan sandan ya fita daga maɓoyar sa yana kokarin guduwa Girgiza jiki barbushi yayi ya fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa da wan nan katuwar muryan tasa san nan ya zuro harshen sa waje wata iriyar doguwa harshen nasa tayi kamar igiya, yana tsaye a wajen ya aika harshen nasa ta capko masa ɗan sandan nan, ya kawosa gaban sa ɗago katuwar mummunar hannayen sa yayi ya damki ɗan sandan nan ya murɗe masa wuya ya ji kake kakas kas wuyar ta karye nan take rai tayi halinta ɗan sandan ya mutu, buɗe mummunar bakin sa duk wari kamar shadda yayi ya jefa ɗan sandan a cikin ta ga hakoran san nan zabga zabga kamar block a ka jera masa gasu da tsini kaifi kamar wuƙa nan take ya fara tauna ɗan sandan da gabza ganzan hakoran sa, kan kace me jinin ɗan sandan ya fara gangarowa daga bakin Barbushi hancin sa har ta ido ihu sauran yan sandan da suka rage suka fasa tare da fita a guje suka bazama, suna neman cetar ransu, girgiza jikin sa Barbushi yayi kafin ya durkusa a wajen nan take ya rikiɗe ya zama katuwar maciji mai katon kai kamar faranti, ihu yan sandan nan suke basu san in da suke takawa ba guduwa kawai suke masu kashi a wando suna yi masu fitsari suna yi, kwanciya Barbushi da ya rinkiɗe ya zama katuwar maciji yayi ya kutsa ta cikin grass dake wajen yabi bayan yan sandan, duk wanda ya kama haɗiye su yake kamar paracetamol, yan sanda Shabiyar ne suka shigo cikin dajin Barbushi ya cinye uku yanzu biyar sun sume a wajen da suka fara ganin barbushi bakwai kuma suna gudun cetar rai sai kalmar shahada suke shima kalmar shahadar ba dai dai suke faɗe ba saboda tsoro da suke ciki Sai da Barbushi ya cinye yan sanda biyar daga cikin su san nan yaji ya ɗan koshi sai ya fara kamasu yana murɗe musu wuya idan sun mutu sai ya goya su a bayan sa, har ya gama kashe su dukka ba tare da ya lura da biyar ɗin da suka sume a wajen bishiyoyin ba ya ɗauki gawar wayan da ya kashe san nan ya rikiɗe ya koma asalin mummmunar halittar sa ya wuce ya koma in da ya fito Su kuma biyar ɗin suna sume a in da suke. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *WASHINGTON DC* *Harvard University* Kamar kullun zaune suke saman kyawawan fararen kujerun dake gore place, Michael yana latsa wayar sa Johnson na riƙe da drinks shi da test, dest kuma na shafa gashin jikin lucky, basu da aiki kullun in sunzo school sai su zauna suyi ta shaye shaye suna addabar ƴaƴan mutane, School ɗin ma dan dole suke zuwa Michel bai isa yace ba zai zo school ba saboda Romeo zai ɓallasa duk wan nan iya shegen da suke Romeo bai sani ba kuma ba wan da ya isa a School ɗin ya tunkari Romeo yace zai sanar da shi dan bala'i tsoron sa suke ji, shi yasa Michel keyin abun da ya ga dama kuma dole a masa biyayya ko ana so ko ba'a so Wani lecturer ne yazo wucewa ta in da suke zaune bai lura da su a wajen ba yazo zai wuce cike da iya shege John yace "Dr Simon kwana biyu baka watsa jini ba kenan da har zakazo ka wuce baka gaida mu ba" kafin Dr Simon yayi magana John yace "Copper punish him" ihu Dr ya fasa yana faɗin "I'm sorry I'm sorry Johnson please karku haɗani da wayan nan tashin hankali" ya kai karshen maganar tare da duƙawa kasa yana kuka, hannu kawai Michel ya ɗaga masa ala'mar ya tafi ya basu waje, a guje Dr Simon ya miƙe ya bar wajen shi kuma Copper yana zaune ko motsawa bai yi ba dan daman idan ba Michel bane ya basu umarnin basa taɓa yin abu umainin Michel kawai suke bi To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 Share fisabilillah 👏 *💞TRIPLET'💞10 Masu son magana dani su min magana ta wan nan number 09075846926 wan can layin ya samu matsala *💞The beginning💞* *Episode 10* Masu tambaya ta menene ma'anar sunan Rimsha da Jehan to gashi nan *Rimsha means Beautiful or face like moon* *Jehan means the world* san nan duk wan da na kira sunan sa a book nan zanyi kokari na rubuta muku ma'anar sunan Nagode Princess Teema Musa...✍️✍️ 💞💞💞💞💞💞💞💞 💞ABUJA💞 *RIMSHA* Kwance Rimsha take a ɗakin su saman katafaren gadon ta taja lallausar blanket ɗinta ta rufe daga ƙafa zuwa cikin ta tana sanye da rigar shan iska zuwa gwiwa fari kal da shi mai laushi, tana rungume da ƙatuwar teddy ɗin ta, ɗaki ne na Alfarma komai na ɗakin bibbiyu ne kama daga kan katafaren gadon su wardrobe dressing mirror komai bibbiyu ne na Rimsha pink color na Jehan ash color toilet ne kawai guda ɗaya, dressing mirror su cike yake da lotions kala kala masu kyau da tsada ga perfume masu bala'i kamshi komai a jere tsab sai kamshin ɗakin ke zubawa, daga saman dressing mirror glass ne wadda kana iya hango sarkakunan gold da abubuwan hannun su dake cikin drawer mirror, daga cikin drawer mirror kuma a kwai fitilla mai bada haske yana haske sarkoki da abun hannun nasu, sai ya karawa wajen kyau da ɗaukan hankali, kwance take tana Chatting da friends nata a Telgram Group nasu na makarantar su, suna magana akan *Prize-giving* day daza suyi a makarantar su Ranar Saturday mai zuwa Auntyn su ta basu zaɓi akan kayan da zasu saka Black and white ko Black and blue kowa na faɗar ra'ayin sa basu yarda akan abu ɗaya ba daga ƙarshe tace za su yi voting waɗanda suka fi yawa shi zasu ɗauka haka akayi ƴan Team na *First lady*(Rimsha) da ƴan Team *Miss Assistant*( Maryam). Abun da yasa suke kiran Rimsha da first lady saboda kaman da take da mum, idan dad yaci zaɓe mum ce zata zama first lady shiyasa suke kiran Rimsha da first lady dan kamannin mum ....Tun kafin Rimsha ta zaba duk suka ce zaɓin First lady shi ne nasu, Black and White ta zaɓa sabida sune favorite color ɗin ta. Bayan Auntyn su taji zaɓin ta shi ne ta ce kowa yayi dressing in Black and white. Daga ƙarshe ta masu nasiha akan karsu bar karatu su dinga duba littattafai lokacin hutu sannan tace masu akwai online lesson da zasu fara Friday, Saturday and Sunday su sanar ma Iyayen su. Da jin ɗadin suka amsa mata da In Sha Allah zasu Rinƙa karatun suka nuna mata farin cikin su akan lesson daza su fara. Aunty na Sallamar su Rimsha ta miƙe aguje ta fice a ɗakin nasu rungume da ƙatuwar teddy ɗin ta, ta nufi office ɗin daddy dake palour ɗin ƙasa wajen da yake zama yana duba mahimman abubuwa sa. Zaune yake a saman 2 Sitter dake office ɗin yana duba wasu takardu, Da sallama ta shiga office ɗin tana nishi kaman wacce kare ya biyo, ɗago wa yayi da sauri ya sauke idanunsa akan ta kara waro ido waje yayi yana faɗin "My sima kiyi a hankali don't hurt yourself am about to come and surprise you ai and then you came" ya faɗi yana kamo hannun ta ya zaunar da ita a gefen sa "Daddy let's go to the shopping now I want to be the best among everyone" ta faɗi tana mai da numfashi, miƙewa Daddy yayi ya ɗauko mata ruwa a fridge ɗin da ke office ɗin ya dawo ya ɗauke ta ya dorata saman cinyarsa ya buɗe ruwan ya kafa mata a baki, kaɗan tasha ta janye bakin ta "Haba my Siha you are now a big girl stop running anyhow like that is not proper kinji" ya faɗi yana shafa curly hairs ɗinta daya gangaro mata har bayan ta, gyaɗa masa kai tayi ta kwantar da kanta a kirjinsa tana mai da numfashi tare da jujjuya dara daran sleeping eyes nata. After some minutes Jehan ta shigo office ɗin bako sallama ta ƙaraso gun daddy ta zauna a gefen sa tare da kwantar da kanta a kafadar sa, hannun sa ya kai ya shafa lallausan gashin kan ta, cikin shagwaɓa tace "Daddy our party outfit is black and white" "same as ours" Rimsha ta faɗi tana ɗago kanta daga chest ɗin daddy "Alright go and make the lists of all you need well go to shopping later" ya kai karshen maganar tare da rungumar su a jikinsa, kiss suka manna masa a kumatunsa har suna rige rigen tashi su fita suna faɗin "That's why we Always love you daddy" Suka faɗi suna ficewa a ɗakin murmushi yayi shi ma yana mai jin kaunar yaran nasa har cikin ransa, ci-gaba da duba takardun da yake yi yayi. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *KADUNA* A yaune Abbi ya kira dillalai masu sayan filaye da gidaje, a kan suzo su sai company'n sa, yana tsaye sanye cikin shadda nevy blue kayan sun masa kyau sosai ɗinkin full jompa, while Irfan na tsaye a gefen sa sanye cikin wandon jeans baki da t-shirt blue gashin kan nan nashi yasha gyara sosai, dukkan su fuskokin su babu annuri kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin damuwa da tashin hankali, su kuwa dillalan sai kewaye company suke suna dubawa, har zufa Abbi yake haɗawa shi Irfan ma ba'a magana dan tashin hankali sa yafi na Abbi yawa saboda abun ya haɗun masa biyu ne na farko a baya Abbi bai da kuɗi yasa Ummin su ta gudu ta barshi, bayan tafiyar ta Allah ya azurta Abbi har company ya saya yanzu kuma wani yazo ya zalince sa, ga zafin ciwon abun da Ummi tayiwa Abbi ga kuma zafin ciwon abun da ya samu Abbin yanzu. Suna tsaye a wajen har dillalai ɗin suka gama kewaye kewayen da dube duben su suka dawo wajen su Abbin, Shiru Abbi ya zuba musu ido yana jiran yaji nawa zasu fara taya masa wajen, da buɗar bakin ɗaya daga cikin dillalan sai cewa yayi mun saya 5 million a sukwane Irfan yace cikin tsawa "What!! 5 million fa kukace ai ko wan nan fillin kawai yafi karfin 20 millon, company guda mai girman filli plot 15 shine zaku ce 5 million bayan har da gini a wajen kuji tsoron Allah bayin Allan" dogon tsaki ɗaya daga cikin dillalan ya ja kafin yace "Kai da kake mana wani lissafin banza da na wofi mu ina ruwan mu da abubuwan da kuka kashe kuka saya yanzu dai sayarwa zaku yi, kuka kiramu to mu kuma 5 million muka ce zamu saya idan ya muku, mu baku kuɗin ku cash mu ansa takardu idan kuma bai muku ba sai mu wuce ku nemi wasu, a zamanin yanzun nan waye ma yake ta wani filli ko gida kowa ta abincin da zai ciwa cikin sa yake na rantse muku ba wanda zai sayi wan nan kangon 6 millon!!" Ya kai karshen maganar cikin faɗa, kallon Irfan Abbi yayi yace "Muje gefe mu ɗan yi magana" ba musu Irfan ya wuce sai huci yake dan yadda suka taya wajen ba karamin ɓata masa rai suka yi ba filli mai girman gaske har ka kuma a cikin garin kaduna ba'a kauye ba kai wan nan ma ai rai nin hankali ne. Kasa kasa da murya Abbi yayi ya fara magana dan kar dillalan suji "Irfan suna da gaskiya yanzu ba kowa yake da kuɗin sayen gida ba al'umma ta abincin da zasu ci suke dan haka mu hakura da asarar kawai mu sallama musu" riƙo hannun Abbi Irfan yayi yayi kasa da murya cikin girmamawa yace "Abbi wallahi karya suke ta haka suke fakewa suce ba kuɗi kowa na ta abinci ne sai su kashewa mutun jiki susa ya sallama musu kayan sa kamar kyauta ina da tabbacin suna mutuwar son company nan dan haka Abbi ka rabu da su idan ba zasu bada 20 millon ba wallahi su bar mana abun mu ni zan ɗauki degree certificate na naje neman aiki, ai ta Allah bata karewa kuma bai kamata bawa ya yanke tsammani daga samun Rahman Ubangijin ba" "Hakane Irfan to ni dai zan koma cikin motar ka najira ku ka yi magana da su kaji kai na ciwo yake ba zan iya tsayawa a wajen ba" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya bar wajen ya nufi motar Irfan ɗin, shi kuma Irfan ya koma wajen dillalan a ƙule yace musu "Zamuyi tunani idan mun gama zamu nemeku" ya kai karshen maganar tare da juyawa zai bar wajen, cikin sauri ɗaya daga cikin su yace "To mujira zaku sayar mana ne ko dai" Irfan ba tare da ya juyo ba yace "Zamu neme ku idan mun gama tunani" yana kai karshen maganar ba tare daya jira amsar su ba ya bar wajen cikin sauri yaje ya shiga motar sa, suka zauna shiru shi da Abbi har sai da dillalan suka tafi san nan su Abbi ma suka fitar da motar su waje, Irfan ya kashe motar ya fito ya rufe gate ɗin company nin ya koma mota suka bar wajen A takaice dai dillalai har kala uku su Abbi suka kira amma duk wadda suka zo tayin wulakanci sukewa wajen ba wanda ya taya sama da 7 millon a cikin su, dukkan su Irfan yaki sallama musu ya ɗauki takardun sa ya fara naman aiki, 💞💞💞💞💞💞💞💞 *KANO* Zaune take saman tsakiyar gadon daddy tana latse latse a system na shi da ya ajiye saman bedside drawer ya fita, sai latsa masa take bata ma san in da take shi ga ba kawai duk in da ta samu latsawa take, da sallama daddy ya shigo bedroom ɗin, ganin abun da take masa da system yasa ya kariso wajen da sauri yana faɗin "Jelly me kike min a system kuma? Ke da nace ki cire kaya ina zuwa in miki wanka" turo baki tayi kamar biro cikin shagwaɓa tace "Daddy amma yau tare zamuyi wanka ko?" Waro ido waje yayi yana kallon ta cike da mamaki yace "A'a ba dani ba" kuka ta sa masa tana faɗin "Daddy ni gaskiya idan ba da kai ba ni ma bazan yi wankan ba" kara waro ido waje yayi yana kallon ta, ganin da gaske take kukan ga hawaye sun fara bin kuncin ta ne yasa yayi kasa da murya yace "My jelly Allah ya hana mutane biyu su shiga toilet" cikin sauri tace "Daddy ai to tare muke shiga ba kai kake min wankan ba kaga kenan mu biyu muke shiga ai" ɗaure fuska yayi sosai kafin yace "Ni ai daddyn ki ne zan iya yi miki wanka amma ba muyi tare ba Allah ya hana hakan" kara turo baki tayi tana faɗin "Daddy nima zan iya maka wankan ke nan ai" saura kaɗan dariya ta kubce masa amma sai ya danne ya wuce ya nufi toilet yana faɗin "kiyi sauri kizo namiki wanka anjima kaɗan su Yaya Irfan dash yaya Imran zasu zo" ya kai karshen maganar tare da shigewa cikin toilet ɗin yana mamaki wai zata masa wanka ita da ko brush bata iya yiwa kan ta ba ne zata ce zata masa wanka, ita kuwa jin daddy ya ambaci su yaya Imran zasu zo ne yasa ta miƙe da sauri ta diro kasa daga gadon ta shige toilet ɗin da yar gudun ta tana dariya, After some minutes. Daddy ya fito ɗauke da ita a saman kafaɗar sa ya naɗo ta a towel mai laushi sai murmushi take, kai tsaye saman chair ɗin gaban mirror ya ɗaura ta tare da ɗauko karamin towel ya goge mata jiki tsab, san nan ya fara shafa mata lotion nata masu kamshi da daɗi da tsada, bayan ya kammala ya shafa mata mayukan gashin ta masu kyau da tsada ya gyara mata gashin ya feshe ta da perfume masu bala'i kyau da kamshi, san nan ya sauƙo da ita kasa ya wuce ya nufi drawer sanya kayan su ya ɗauko mata wani dankareren blouse gown ja mai manya manyan flowers fari daga ta kasan rigar, rigar kasan ta a buɗe yake kamar umbrella, san nan ya haɗo mata da pant, ya dawo bakin gadon, ba tare da ya mata magana ba ya fara sanya mata pant ɗin, bayan ya gama sai ya sanya mata rigar a wuyar ta yana kokarin sanya mata hannu tayi sauri cirewa tana faɗin "Daddy baka samin wan nan abun da nagani a film matan suna sawa ba" tayi maganar cikin shagwaɓa cikin nuna ko in cula yace "Wani abu kenan?" Hannu tasa saman kirjin ta tana faɗin "that thing that looks like ball a kirji naga suke sawa and then the thing is big" sai lokacin daddy ya gane breziya take nufi hakan yasa yaja dogon tsaki a kule yace "Sai kin girma" kuka ta sa masa tana faɗin "Ni yanzu ma na girma ai, kuma da suka sa suma sunyi kyau ni kasa min nima nayi kyau" dafe kai daddy yayi yana nadamar barin ta ma da yake tana kallo India film, ganin yayi shiru ya kyaleta ne yasa ta fasa masa ihu tana kokarin sauka daga gadon, cikin sauri ya riƙota cikin muryan rarrashi ya fara magana "To ai my Jelly baki da abun sai naje Shopping sai in sawo miki yanzu dai kisa rigar ki karsu yaya Imran suzo su ganki haka, kuma kinga har da su Umaisha yaya yace min zasuzo, ko so kike su fiki kyau ne?" Cikin sauri ta girgiza masa kai tana faɗin "A'a daddy banson su fini kyau" da murmushi a kan face na shi yace "Yauwa my Jelly to kisa kayan naki idan ba haka ba zasu fiki kyau" ya kai karshen maganar tare da sanya mata rigar, ba musu ta tsaya ya sanya mata tsab ya riƙo hannun ta yana faɗin "Muje kasa na baki abinci" maƙe masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy what about make up fa? Baka min ba ai" girgiza kai kawai yayi tare da sakin hannun ta ya koma gaban mirror ya ɗauko lipstick da powder da kwalli yana tafiya yana tunanin ya za'ayi kwalliyar tayi kyau dan wancan karon ma daya mata kwalliyar kamar dodo ta zama, haka dai ya karisa wajen ta da tunani fal ransa gefen ta ya zauna ya fara shafa mata powder, sai murmushi take, shiko sai rawa hannun sa keyi, sosai ya lapka mata powder a face nata kafin ya ɗauko kwalli ya sanya mata, a mai mai kon yasa mata kwallin a cikin ido sai ya sanya mata a kasan ido dan gani yake kamar zai tsole mata ido idan ya sanya mata a cikin ido, kamar wata matsafiya haka ta dawo haka ya labka mata lipstick ja a baki har ma gefe da gefen bakin, nan take bakin nata ya kara girma, shi kan shi ya tsorata da kallon ta amma ba yadda ya iya da ita, yana kokarin miƙewa tayi saurin cewar "Daddy baka sanya min a saman gerata ba, a na sawa a wajen ma mummy'n su hudan School na mu tana sa musu" ba musu ya koma ya fara zana mata lapka lapkan gera yana tunanin waye zai samu ya koya masa yadda ake wa mace make up dan ya rinƙa sanya Jelly farinciki dan tana bala'i son make up musamman idan taga friends nata a School iyayen su sun musu sai ta yi ta damun sa sai ya mata, da wan nan tunani ya kammala mata make up ɗin, kamar wata aljana haka ta dawo ya zana mata gerar lapla lapka har kusa da ido ga shi sama da kasa ya zana mata gerar, ɗaya yayi kasa ɗaya yayi sama, ita kuwa sai washe baki take tana dariya, cikin sauri ya kawar da kan sa dan idan tayi dariya kamar boka ko wani katon mummunar aljani take dawowa, haka ya kama hannun ta ya ɗau wayar sa suka fice palo Ko da sukaje palo sai kallon ta su Zuwaira suke, sun kasa gane ta sun san dai ba wadda daddy zai riƙo haka in ba jelly ba, kallon sama da kasa tayiwa su Zuwaira kafin tace "Ku idan mutun yasha make up sai kuyi ta kare masa kallo to ni karku kwashe min kyan make up na yaya Imran nayiwa duk wadda ta sake kallo na sai na kwakwale idon ta" cikin sauri suka yi kasa da kai shi kuwa daddy ko ajikin sa ya ja hannun ta suka wuce saman table, Nana tazo tayi serving nasu suka fara cin abinci, idan tana taunar abincin kai kace rakumi ne ke cin abinci saboda yadda daddy ya lapka mata lipstick a baki, sai kau da kai daddy yake bai son ganin ta a wan nan yanayi ita kuwa sai murmushi take tayi make up. 👹DAULAR MUTUWA👹 Ruwan sama mai karfi ne ya ɓarke a dajin a firgice yan sanda da suka suma suka farfaɗo, tare da fara ihu mai tarwatsa kwakwalwan ɗan adam, a sukwane suka bazama cikin dajin basu san in da suka dosa ba kwata kwata gudu kawai suke sun rarraba hanya kowa ya kama nashi hanya, Abun da ya basu mamaki ya kara ɗaure musu kai sai kawai ganin su sukayi dukkan su a cikin asalin *Daular mutuwa* a ruɗe suka tsaya suna zazzare ido kamar ɓera a tarko, suna tsaye suna waige waige suna karewa gidan kallon, sai ganin wasu jibga jibgan wasu halitta masu kama da shanun daji wayo ɓauna amma sai dai wayan nan sunfi ɓauna girma jibga jibgan gaske ne wadda zasu kai girman giwa, a guje wayan nan halittu sukayi kan yan sandan nan alama a yin wace suke, kafin yan sandan suyi wani yunkuri wayan nan halittun sun farmusu, sun fara yin kaca kaca da naman jikin su suna gurnani kamar wasu mayin watan zakuna, tas suka cinye yan san dan nan ko kashi basu bari ba har jinin da ya zuba a kasa sai da suka lashe tas, san nan suka girgiza jikin su tare da sakin wata mahaukaciyar ihu mai tarwatsa kwakwalwan ɗan adam san nan suka riƙiɗe suka zama mutane matasa kyawawa kamar larabawa, suka wuce suka shige wani ɗaki mai kama da keji. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *KANO* Da sallma su Irfan suka shigo palon, daddy da Jelly suna zaune saman sofa suna buga game a system ɗin daddy, daman kullun idan daddy ba zai je office ba sai ya zauna ya kunna musu game ɗin kwallo suyita bugawa tare, Jelly ta iya buga game ɗin kwallo sosai, wani lokaci ma har winning ɗin daddy take, Jin sallama yasa ta ɗago ido ta kalli bakin kofar da kwalliyan ta kamar boka, ganin su Imran ne yasa ta miƙe a guje tana ihu ta nufi Imran, ta faɗa jikin sa tana dariya, ba tare da ya lura da face nata ba ya ɗaga ta sama yana faɗin "Oyoyo rabin rai na" yayi maganar yana kokarin zama saman sofa, dai dai lokacin idon sa ya sauka kan face ɗin ta, ihu ya saki tare da sauke ta daga jikin sa yana faɗin "Wace ce ke? Wa innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanin rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba bappa wace ce wan nan?" Saboda dariya Irfan har da faɗuwa kasa yayi, dan duk da bai san face ɗin Jelly ba ya fahimci ita ɗin ce tasha make up dan Irfan yana da ƙwaƙwalwa sosai ga dogon tunani, Aafia Umaisha Akila Dukka sai dariya suke ban da Akil da face na shi a ɗaure kamar hadari AKILA kanwar Imran ce itace autar su yanzu haka tana da 15 years kamar Umaisha, kyakkyawa ce sosai irin ta ɗaya da Imran. Akil Matashin saurayi ne mai jini a jiki kanin Imran ne shima daga Imran sai shi a yanzu yana da 22 years while Imran nada 28 years dukkan su kamannin su ɗaya sai dai shi Akil farine tas, da yake family su daddy ruwa biyu ne fari da chocolate. Shi kan shi daddy sai da dariya ta kubce masa, ita kuwa Jelly cikin shagwaɓa tace "Yaya Imran me ya faru?" Miƙewa tsaye Imran yayi ya fasa zama a kujerar cikin tsoro yace "Bappa wallahi muryan ta irin na Jelly ce, dan Allah ina Jelly ta me ya kawo aljana gidan nan" yayi maganar yana kallon daddy, kashe masa ido ɗaya daddy yayi kafin yace "Kai Imran yanzu sai da ka bari kyan baby Jelly ya rikitaka dama na faɗa mata sai tafi kowa kyau, na faɗa mata bazaku gane ta ba dan kyau ɗin da kwalliyar ya mata" sai lokacin Imran ya gane matsalar komawa yayi ya zauna tare da jawota jikin sa yana faɗin "Kai baby Jelly duniyar kyau, irin wan nan kyau ai dole ki rikita yaya Imran kaiii chanchaɗi" kallon gefen ido daddy yayi wa su Irfan nan take suka tsaya da dariyar dan kar jelly ta hassala, cike da farinciki suka kariso suka zazzauna saman sofa tare da ɗagawa daddy gaisuwa, cikin hanzari su Nana suka zo suka ɗauka musu trolley's dasu ka zo da shi, kallon Akila Imran yayi kafin yace "heartbeat jeki gyarawa Auntyn ki make up ɗin ta ya ɗan ɓaci" cool murmushi Akila ta saki tana faɗin "Yaya wan nan ne daman Auntyn mu? Ita ce kullun kake faɗa mana?" Gyaɗa mata kai yayi ala'mar eh cike da jin daɗi Akila tace "Yaya Akil yau dai ga rabin rai ɗin da yaya Imran ke ta magana a kan ta" kwaɓe fuska Akil yayi har suna haɗa baki da Aafia wajen cewa "Wan nan mummunar" a sukwane Irfan ya ɗago kai yana mamakin rashin kunya irin na Akil da Aafia a gaban baban yarinya kuce mata mummuna, Irfan na kokarin yin magana Jelly ta rigashi da cewa "Ku da kuke maganar kyawawane ku? Da wasu fuskan ku kamar an gasa big (Alade) ya kone tayi baki" shi dai Imran shiru ya musu dama bai tanka musu bane dan yasan Jelly zata kwatarwa kanta yanci dan ba'a mata ta kyale, tsawa Aafia ta daka mata "Ke mara kunya idan kika ce zaki min rashin kunya sai na fasa miki baki!!" shi dai daddy yau yaga ikon Allah, girgiza kai kawai yayi dan baruwan sa da faɗan su yan uwan juna su karata can, Irfan zai yi magana Imran ya ɗaura yatsa a saman lips na shi alamar yayi shiru, murmushi Akila sarkin fara'a da kaunar mutane musamman yan uwan ta tayi cike da fara'a a face nata tace "Aunty Aafia abun ai bai kai ga haka ba, dan Allah ku bari, ni fa tun jiya da yaya Imran ya faɗa min zanzo wajen yan uwan Abba wallahi ko barci banyi ba saboda murna zanzo naga yan uwana da ban sansu ba, ban taɓa ganin su ba kuma nake mararin ganin nasu, ni ada duk tunanina Abba bai da wasu yan uwa sai jiya da yaya Imran ya sanar da ni to dan Allah karku ɓata mana wan nan farin cikin" Akila bata gama rufe baki ba Jelly tace "Ke ce mara kunya kuma wallahi ba'a haifi wadda zai fasa min baki ba" a fusace Aafia ta miƙe da niyar ta bugi jelly, sai dukan uku uku kirjin daddy ke yi dan da a dakar masa Jelly gwara a sanya shi frog jump, gashi kuma bai son shiga faɗar nasu kar a ce ya shigarwa yarsa kar su ce dan sun zo gidan shi ne dama ga yadda zumuncin nasu ke rawa, Aafia na zuwa ta sanya hannu zata fisgo Jelly daga jikin Imran a fusace Irfan ya ɗaga hannu zai mareta Imran ya riƙe masa hannun nasa yana faɗin "Ke Aafia kuce kije ki zauna heartbeat jeki gyara min babyna" ya kai karshen maganar tare da sakin hannu Irfan, shiru Irfan yayi sabida Imran yayan sa ne duk kan su ya girme su, shi dai Akil ko ajikin sa sai kwaɓe fuska yake a ransa yana faɗin "Wan nan gidan talakawan ne za'a ce mu zauna har one week wallahi ba zan iya ba kuma sai na faɗa wa Ammie sai dai yaya Imran ya kashe ni, amma sai Ammie taji in da ya kawo mu gida sai wari yake gashi ɗan karami kamar keji tsuntsaye na" ita kuwa Aafia a fusace ta juya ta koma ta zauna saman sofa tana kunbura kumatu, miƙewa Akila tayi ta riƙo hannun Jelly ta kalli daddy tace "Bappa ina ne ɗakin ta" murmushi ya saki har cikin ransa yake jin kaunar Akila saboda kirkin ta ga kuma fara'a ga son yan uwanta, yau tazo gidan amma har ta rungumi Jelly ta riƙe ta hannu bibbiyu, da hannu ya nuna mata bedroom na su da murna ta ja hannun Jelly suka wuce sama, dawo da kallon sa daddy yayi kan su Irfan kafin yace "Ku tashi kuje ɗaki kuyi wanka kuzo kuci abinci" ya kai karshen maganar tare da kiran Zuwaira da Nana a kan su zo su kai su masaukin su miƙewa Akil yayi, yayi gaba yana faɗin "Ni banga abincin ci a gidan nan ba haka kuma ban ga wajen kwana ba dan haka hotel zan tafi na kama" yayi maganar cikin harshen turanci murmushi daddy yayi yana mamaki Akil, Abban su Imran yana da kuɗi na fitar hankali haka ita ma Ammie su dan tafi Abban su ma kuɗi nesa ba kusa ba, to amma shi ma daddy Jelly bazaa kirashi talaka ba koda kuwa a gaban su Ammie ne ya wuci su kirasa da talaka kuma wan nan gidan nashi yafi karfin a ce ba'a ga wajen kwana ba, kawai dai Ammie su ta ɓata su da kuɗi ne suna abun da suke so shi dai Imran yana da kyakkyawar zuciya ne kawai shi yasa baya biyewa abun da Ammie ke yi musu baya damuwa da kuɗin da suke da shi shi dai Irfan gaba ɗaya sai yaji babu daɗi sai ma yaji da bai sa Imran ya tawo da su Akil ba gashi sunzo suna yiwa bappa rashin kunya, jiki ba kwari shima Imran ya miƙe Zuwaira ta musu jagora zuwa boys quarters su Aafia kuma Nana ta kai su ɗakin kusa da na daddy Aafia Umaisha Akila, ita kuma Jelly daman gadon ta na bedroom ɗin daddy Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 *💞TRIPLET'💞11 *💞The beginning💞* *Episode 11* *🛫WASHINGTON DC🛬* *LOT 33.* *07:30* Iskan sanyin safiya na kaɗawa yanayin weather garin gwanin ban sha'awa, iskan na kaɗawa a hankali hankali, duk da cewa a koi sanyi hunturu amma hakan bai hana kaji daɗin iskan dake kaɗawa ba, a hankali Michael ke tattako staircase yana saukowa jikin sa sanye yake da wando 3 cutar blue da t-shirt mai laushi mara nauyi fari kal kamar yanzu ya fito da ita daga kwalin ta saboda haske ta ya ɗaura jacket blue color mai ɗan girma a saman kayan nasa, hannun sa na ɗaure da dankareriyar gold watch mai bala'i kyau da tsada sai kyalli yake yana ɗaukan ido, ya tara kyakyawan dogon gashin can nan nashi daya sha gyara ya ɗaure a bayan wuya ya zubo kaɗan ta gaban goshin sa kamar mace, fuskar nan a ɗaure tam kai da ganin sa kaga Tiger ne da gaske, katafaren palon su a gyare tsab sai daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac ke tashi, kai kace yanzu a ka zuba komai na palon saboda yadda suke tsab kamar hannu bai taɓa taɓasu ba, kai tsaye wajen table ɗin cin abinci Michael ya nufa, wasu jigba jibgan Bodyguard ne tsaye a wajen table ɗin sanye suke cikin suit baki da glass baki a face nasu fuskar nan tasu kamar hadari a ɗaure tamau babu alama imani ko ɗigo a ransu, sun jeru yali gefe da gefe sun sanya table ɗin a tsakiyar su, bodyguard 12 ta gefen nan 12 ta gefen nan, tun Michael bai iso wajen ba suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba ya nufi saman kujerar table ɗin, a sukwane ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ja masa kujerar baya, ya zauna, cikin sauri ɗaya daga cikin su yace cikin harshen turanci "Sir me za'a zuba maka?" Da hannu ya musu nuni da wata dan kareriyar warmer mai ɗauke da Nasville hot chicken, nan take suka fara serving na shi, nan daddy da Uncle Herry suka isko sa, da sauri bodyguard suka ja musu kujera suma suka zauna, suna zama sai ga John da Jay suka iso wajen, suma haka bodyguard suka ja musu kujera suka zauna Cike da so da kauna daddy yace "My Tiger where is James?" ba tare da ya kalli in da daddyn yake ba yace "I don't know" cikin sauri John yace "he had gone out" shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "Why two days ɗin nan James ke fita since morning kuma baya dawowa sai can dare" shi dai Michael bai tanka daddy ba abincin sa kawai yake ci hankalin sa kwance waya daddy ya ɗauko ya shiga contact ya fara kiran number da a kayi saving da my lion, sai ringing wayar take amma ba'a ɗaga ba, har wayar ta katse ba'a ɗaga ba, sake kira daddy yayi, a karo na biyu ma ba'a ɗaga ba, sai a karo na uku shima sai da wayar ta kusa katsewa san nan a ka ɗaga, kara wayar a kunne daddy yayi ya tattara nitsuwar sa cike da so da kauna yace "Hello my lion" shiru a ka ɗan yi na 40 second kafin wata zazzakar voice mai tashin kai mai bala'i daɗi yace "Good morning dad" nauyayyar ajiyar zuciya dad ya sauke kafin yace "my lion how are you doing this morning?" Shiru ya ɗan yi, su Michael duk sun nitsu, shi Michael ma har abincin ya dai na ci yayi shiru ya nitsu dan yaji ko karar sa daddy zai kai, shi kam John har kerma jikin sa keyi Uncle Herry sai zazzare ido yake, Jay kam ba'a magana, ba su kaɗai ba har ta jibga jibgan Bodyguard dake tsaitsaye a kan su dan basu kulawa sai da suka kara shiga hankalin su kowannen su sai zazzare ido yake sun kasa kunne suna sauraron daddy, kowa sai addu'a yake Allah yasa ba wani abu a kan sa daddy zai faɗa ba "What's going on daddy you called me this early morning hope there is no problem?" Lion yayi maganar cikin sanyin muryan ga sexy voice nashi mai bala'i daɗin sauraro ciki ciki yake magana kamar bai son buɗe bakin sa, cikin sauri dad yace "I want you to investigate for me where James is out every early in the morning and coming back home in the evening" shiru lion yayi kamar bai ji me dad yace ba, bin wayar da kallo daddy yayi dan yaga ko lion ya katse kiran, bai kuma katse kiran ba ganin haka yasa daddy ya gane lion na nufin ko a koi wata matsala bayan wan nan, hakan yasa cikin sauri dad ɗin yace "There's no other problem" dad na kai karshen maganar ɗif lion ya kashe wayar sa, dogon numfashi daddy yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya ɗago ya kalli su Michael da suka zuba masa ido suna jiran suji ko lion ya bashi wani sako a kansu, su kuwa bodyguard sai sauke ajiyar zuciya suke tun da sunji ba karan su dad ya kai ba Kallon Uncle Herry daddy yayi cikin harshen turanci suke magana "Herry ina mamakin Romeo sosai yanzu, ba ma shi kaɗai ba dukkan su suna bani mamaki over" cikin sauri Uncle Herry yace "Nima dai gaskiya ina mamakin Romeo da James how comes yanzu yake ɗan respecting naka how? why?" Shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "Tun last 5 Month ago Romeo ya fara ɗaukan kirana in yayi tafiya har ma ya min magana cikin girmamawa har ma ya tambaye ni ko a koi wani problem abun da a baya ko zan shekara ina kiran sa sai ya ga damar ɗauka kuma ban isshe shi kallo ba to why? Why suka canza haka? Ina son sanin dalili" guntun tsaki Michael yaja tare da cire hannun sa daga cikin abincin ya ajiye spoon da yar karamar wukar hannun nasa, da sauri ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ciro masa tissue paper ya goge masa bakin sa, sai kwaɓe fuska Michael ɗin yake ya miƙe ya nufi hanyar fita daga palon "My tiger what about church?" Daddy ya tambaya, ba tare da Michael ya juyo ba yace "I can't go" cikin sauri daddy ya miƙe tsaye yana faɗin "Are you mad? Are you heard what you said?" A fusace Michael ya juyo a ƙule yace "I'm not mad, I knew what I said, let me repeat it again maybe you will understand what I mean, I said i can't go anywhere, in fact as from today i can't go to the church again" tashin sense cikin sauri Uncle Herry ya miƙe yana faɗin "William ina ganin mu kira Pasto yazo yayiwa Michael addu'a dan ina ga ya samu matsala a brain nashi" Johnson ne ya cabki zancen da cewa "Yes daddy saboda ya faɗa a School wai ya dai na shan wine" jiki na rawa daddy ya ɗauko wayar sa ya shiga contact tsabar ɓacin rai har idon sa baya gani sosai, ganin daddy zai yi kirane kuma yasan mutun ɗaya zai kira yasa Michael saurin cewa "Sorry dad rai na ne ya ɓaci amma I'm sorry today i have an exam so ba zan samu damar zuwa church ba amma gobe zanje" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palon yana mai jin haushi, shi ba wani abu yasa bai son zuwa church ɗin ba pace Pasto su daya tsani gani, bai son pasto ko kaɗan tun yana yaro sai an sha fama da shi yake zuwa church ɗin, Jin abun da Michael yace yasa daddy sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna sai ajiyar zuciya yake ta faman sauƙewa a ran sa yana faɗin "Thank you Jesus" *Michael* Kai tsaye School ya nufa, sai sharara gudu yake a kan shinfiɗaɗiyar titin mai laushi wadda babu kwarzane ko kaɗan, da motar sa kirar *Aston Martin*. Yana shiga school ya kashe Motar sa a parking space na *Harvard Square Parking Garage*, ya fito tare da Lucky Copper Winston, kai tsaye office na dr tyrian ya wuce, babu ko excuse bare jiran umarnin haka ya faɗa cikin office ɗin fuska a ɗaure, tsabar tsorata Dr har yana kokarin guduwa dan banyi expecting ganin kowa a lokacin ba, kai tsaye wajen sa Michael ya nufa fuskar nan tasa a ɗaure tam kamar hadari dan dad ya ɓata masa rai over, Yana zuwa ya damko wuyar rigar Dr cike da bada umarni ya fara magana cikin harshen turanci "Idan har this time ma ka faɗar dani baka bani Mark ba kasa na kara samun carry over kasa Romeo ya bani punishment idan... Michael bai kai karshen maganar ba Dr yace "A'a ni na isa ai kana rubuta Exam nan dole na baka mark" kallon banza Michael ya masa kafin yace "Chemaka a kayi zan rubuta Exam ɗin? Ni ba wani Exam da zan rubuta kai zaka rubuta min da kan ka, kuma kayi marking ka bani mark full" ya kai karshen maganar tare da sakin wuyar rigar dr ya juya ya fice daga office ɗin yana wani kwaɓe fuska, nauyayyar ajiyar zuciya Dr ya sauƙe kafin yace "Oh wan nan bala'i da me tayi kama dole muyi meeting na malamai mu san yadda zamuyi mu bawa Michael result mai kyau dan ya bar School nan mu huta" haka dai Dr ya rinƙa surutan sa shi kaɗai, Shi kuwa Michael yana fita kai tsaye gore place ya wuce yaje ya zauna su lucky suka zauna kusa da shi. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *KANO* Bayan sallar issha zaune suke gaba ɗayan su a palon daddy amma ban da Akil, sai Jelly da Akila da basa wajen suna cikin ɗaki suna can Akila tasawa Jelly wan nan ta canza mata wan nan sai shiri suke kamar wayan da zasu je party Daddy na zaune kusa da Imran da Irfan suna hira, wayar sa tayi kara alamar shigowar kira, cikin sauri ya duba wayar dan daman yana expecting na kira, Engineer Muhammad Imam shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar jikin daddy har kerma yake wajen picking na call ɗin ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Engr ya ake ciki" tsabar zumuɗi ya manta da sallama ma, daga ɗayan ɓangaren Engr yace "Congratulation sir company mu gomnati ta bawa contract na aikin nan" miƙewa tsaye daddy yayi tare da dukawa ya ajiye wayar yayiwa Allah sujudur shukur yana zubawa Allah kirari da godiya mai tarin yawa, ganin daddy yayi sujudur shukur yasa Irfan da Imran suma suka sauko suka taya sa yiwa Allah godiya ta hanyar yin sujudur shukur ɗin suma duk da basu san me ya faru ba me daddy ke wa sujudur shukur ɗin, Daddy ya ɗan jima yana yiwa Allah godiya kafin ya ɗago ya ɗauki wayar sa yayi ta zubawa Engr Muhammad Imam godiya da fatan alkhari, san nan sukayi sallama ya katse kiran, cike da murna ya sanar da su Imran abun da ya faru, sosai suka taya shi murna da yi masa fatan alkhari, sosai suka ji daɗi su Aafia duk sun masa addu'ar fatan alkhari yaji daɗi sosai, Cikin wan nan farincikin Jelly da Akila suka fito daga bedroom suka same su, jelly tasha make up mai bala'i kyau Akila ta sanya mata wandon jeans blue mai stone a jiki sai yar karamar riga mai karamin hannu pink color tayi kyau sosai da sosai, wow shi ne abun da Imran ya iya furtawa kenan, kyau iya kyau Jelly tayi Akila ta tsantsara mata kwalliya, sosai Aafia da Umaisha suka zuba mata ido dan Jelly ba baya ba wajen kyau bare kuma kyan ya haɗu da make up kai Masha Allah, kasa jurewa Imran yayi yana bala'i son Jelly tun tana yar jaririya, miƙewa yayi ya riƙo hannun ta yana jin kamar yace daddy ya ɗaura musu Aure yanzu sai a barta sai ta girma sai yazo ya ɗauki matar sa dan gani yake kamar za'a kwace masa ita tun da shi ba'a kano yake ba, shi ma daddy ya lura da halin da Imran ɗin ke ciki da kuma abun da yake so sai dai ba zai iya yiwa Jelly aure a haka ba har sai ta mallaki hankalin kan ta ta girma ta faɗa da bakin ta a lokacin tana son Imran ɗin, dan tayu yanzu soyayyar yarinta ne kar ta girma tazo ta canza raayi, shi dai Irfan sai murmushi yake yi abun sa yana yiwa Imran fatan alkhari shi da Jelly a zuciyar sa, sai shagwaɓa Jelly ke zuba musu Imran na biye mata ita kuwa Akila na musu video, sai murmushi dad yake yana addu'ar Allah ya cika masa burin sa ya aurar da Jelly ga Imran, Aafia tayi nadamar cewa Jelly mummuna da tayi ashe kwalliyar da daddy ya matane yasa tayi muni ashe kyakyawace ajin farko, Akila na tsaka da yi wa su Imran video wayar ta ta fara kara alamar kira ya shigo, Yaya Akil shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, cikin sauri ta ɗauki call ɗin tare da kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello yaya Akil" a ta kai ce yace "Bawa yarinyar nan wayar" shiru ta ɗan yi kafin tace "Wace yarinya kuma yaya Akil?" Dogon tsaki yaja kafin yace "Wan nan mai kama da Abba mana" ɗago ido Akila tayi ta kalli Aafia da Umaisha dan ta ga waye kuma mai kama da Abban su a cikin su, sai taga ashe Umaisha ce mamaki ne ya kamata ko yaushe yaya Akil ya ga Umaisha har yasan tana kama da Abba kuma ohon masa mutun kaman wani mai juju a kai, tayi nisa cikin tunani sai jin muryan Akil tayi yana faɗin "Ba da ke nake bane?" Yar firgigit tayi tare da miƙawa Umaisha wayar, ba musu Umaisha ta ansa tare da mannawa a kunnen ta tana faɗin "Waye ne?" Cikin tsawa Akil yace "Ni kike tambaya waye Ni?" Kallon Akila Umaisha tayi dan ita har lokacin bata san da wa take magana ba bata ɗauki muryan sa ba tun da yau suka taɓa haɗuwa kuma yau ɗin ma ba wani magana sosai yayi da su ba, Kasa tayi ta murya cikin girmamawa tace "Kayi hakuri ni ban san waye kai ba ne shiyasa nake tambaya" a ta kaice cikin faɗa yace "Mijin kine to, idan kin koma ki sanar da mahaifin ki idan na samu time zan zo a ɗaura aure!!" tashin sense shi kuma Akil kalar nashi soyayyar kenan, waro ido waje Umaisha tayi muryan ta na sarkewa tace "Akila amma wan nan mahaukaci ne kika haɗani da shi ko?" Waro ido waje Akila tayi su daddy kuma sun zubawa Umaisha ɗin ido hannu Irfan yasa ya amsa wayar, yana bin screen ɗin wayar da kallo, ganin an rubuta Yaya Akil ne yasa Irfan ya sanya wayar a hand-free, cikin tsawa Akil yace "Ke ni kike cewa mahaukaci dan zan rufa miki asiri to wallahi ko kina so ko baki so sai kin aure ni gwara ma ki sani tun wuri idan kin koma ki sanar da mahaifin ki idan na samu time zanzo na kawo sadaki na ɗauke ki, amma kafin nan dole kullun sai munyi waya kuma idan na kira baki ɗaga ba wallahi zakiyi dana sani, gobe kafin na tafi zan sayo waya na kawo miki dan naga kamar baku da karfin sayan waya kina jina ko? Idan kika kuskura kika min taurin kai Allah zan sa a ɗauko ki a kawo min ke a daren nan na kira limamin masallacin mu a waya ya fita ya tara jama'a ya daura mana aure kuma zama dani ya zama maki dole!!" Tashin sense shi dai daddy abun ma dariya ya bashi yau ga ikon Allah soyayya dole aure dole, yau Aafia taji abun da yafi karfin ta shi kan Irfan ya rasa bakin magana dan Akil yafi karfin sa, Imran ne yayi ta maza ya amsa wayar yana faɗin "Sannu Akil idan ma son ta kake ta haka ake ansar soyayya?" cikin masifa Akil yace "Yaya Imran babu ruwanka dani ni ba son ta nake ba Auren ta zan yi kuma dole a aura min ita dole kuma ta zauna dani tana min aiki da biyayya dan daman da yar aiki take kama yar datti ma irin ta!!" ita dai Umaisha yau taga tashin hankali shiru tayi ta sunkuyar da kan ta kasa, a kule Imran yace "Okey yar datti ko to ka bar mana yar dattin mu idan ka sake kiran ta a waya Allah sai na ɓallaka zan ga wanda zai nema kama auren nata wallahi ko bappa ya baka ita sai na hana" cikin fushi Akil yace "Kai yaya Imran waye yace maka ni ina neman izin daga wani wai bappa ya bani Auren ta? Kai ka san wani abu wai izini ni ban san shi ba, ni abun da na sani shine dole a bani ita ko anki ko anso idan ba haka ba kuma muzuba mu gani kasan sauran" ya kai karshen maganar tare da katse kiran salati dad yasa yana faɗin "Anya Akil baya shan wani abu kuwa?" Girgiza kai Imran yayi yana faɗin "Wallahi daddy baya shan komai shi dai haka yake komai da karfi da izza yake cewa zai ansa shi bai san wani abu wai bada hakuri ko lallaɓa mutun ya baka abu ba, a'a shi yana ganin kamar komai kuɗi na iya saya shi yasa sai yace komai da izza da kuɗi zai ansa" jinjina kai daddy yayi kafin yace "Yarantace zai daina idan yayi hankali" shiru Imran yayi yana tunani, dafa kafadar Imran ɗin Irfan yayi yana faɗin "Karka damu my bro ni nasan yarinta ke damun Akil" kallon su Umaisha da sukayi mutuwar zaune Imran yayi kafin yace "Sister kuje daki ku kwanta ko tun da already kun ci abinci" ba musu suka miƙe suka wuce bedroom nasu palon ya rage daga daddy Irfan sai Imran ita ma Jelly ta wuce bedroom na daddy dawo da kallon sa kan Irfan Imran yayi cikin nitsuwa ya fara magana "Irfan tun da kaji Akil yace zai auri Umaisha to tabbas da gaske yana son tane kuma in har ya kai wa Ammie da Abba maganar nan tofa mai iya hana wan nan auren sai dai Allah, dan ko bappa yace ba zai bawa Akil Umaisha ba Abba yana iya sawa a ɗauko ta kuma a aure mata Akil a gaban bappa ba yadda ya iya, ni duk wan nan bashi ne damuwa ta ba Akil yaro ne bai wani mallaki hankalin kan sa sosai ba 22 years yake da shi san nan bai san yin abu a hankali ba shi komai da izza da karfi yake kwata bai san girman nagaba da shi ba baya girmama mutane ba zai taɓa ganin darajar sister ba a wulakance zai riƙe ta na san halin sa sosai tabbas yana son ta tun da har ya iya cewa zai aureta amma duk da wan nan son da yake mata ba zai taɓa riƙe ta da daraja ba dan bai san darajar ɗan adam ba kullun cikin faɗa muke da shi a kan hakan, nike gaba da shi amma saboda wan nan banzan hali na sa yasa na sallama masa girman yana da jiji da kai ga izza da masifar faɗa ga ɗaukan zafi zuciya da rashin kunya duk ya haɗe komai, zan yi iya kan bakin kokari na wajen naga na gyarashi ya zama mutun, nasan zai sai wa Umaisha waya kamar yadda ya faɗa to dan Allah Irfan ina neman alfarman da ku kyaleta ta rinƙa magana da shi a hankali hankali har mu samu ya sauya tun da yana son ta In Sha Allah idan suna waya zamu iya samun wani sauyi" jinjina kai Irfan yayi yana faɗin "Karka damu ɗan uwana" sai murmushi daddy ke yi yana yabawa Imran a ransa, daga haka suka miƙe suka nufi table ɗin cin abinci daman already su Aafia sun ci nasu abincin tun kafin su daddy su dawo sallar issha. 💞💞💞💞💞💞💞💞 *KADUNA* Wata hajiya ce zaune cikin wani katafaren palo na alfarma mai ɗauke da manya manyan sofa set, set 2 launin Ash da baki ga Makekiyar Tv plasma manne a bango, daga ɗan gefe hadaɗiyar table ɗin cin abinci ne mai matikar kyau mai ɗauke da kujeru 6, daga kusa da table ɗin staircase ne mai kyau a wajen ɗan gaba da staircase ɗin kofar kitchen mai girma gaske ne a wajen, gaba ɗaya curtains na palon launin Ash da ratsin baki ne kalar sofa ɗin, daga tsakiyar sofa set ɗin wata kyakkyawar Chinese carpet baki ne sai sofa table saman carpet ɗin, duk wan nan haɗuwar palon babu gyara dan ko ina a watse yake kaca kaca duk datti ga kwanikan abinci saman table ɗin duk anci an bar ragowa shi kan shi kitchen ɗin a watse yake sai warin ruɓaɓen abinci ke tashi ta ko ina a cikin kitchen ɗin gaba ɗaya ya buɗe palon da wari, ta ko ina a cikin palon ledojin takeaway da su kan su takeaway ɗin ne, palon dai ba kyan gani, zaune hajiyar nan take saman sofa mai zaman mutun 2, ba karya kyakkyawace ajin farko fara ce tas har hasken nata ma yayi wani iri kamar bata da jini a jikin ta saboda hasken da tayi, sanye take cikin wata mahaukaciyar bubu irin na larabawa masu manya manyan mayafan nan, gaba ɗaya rigar duk datti ita kan ta hajiyar warin datti take, babbar mace ce wadda a kalla zata kai 45 years sai dai tana da ɗan ƙaramin jiki wadda idan ka ganta zaka yi tunanin 25 years ko 30 years take da shi duk da bata gyara jikin nata amma yana da kyau sosai, ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana latsawa wayar ta kirar Samsung A72, da sallama wata hajiya ta shigo palon tare da wani Alhaji na biye da ita a baya, tun daga bakin kofar shigo hajiyar ta toshe hanci tana faɗin "Subhanallah me haka kuma Hajiya yana ji wari palon" ko kallon in da suke Hajiya bata yi ba ta ci-gaba da latsar wayar ta, karisowa cikin palon suka yi suka zauna saman sofa shi kan shi Alhajin sai kwaɓe fuska yake ya tara yawu a baki ya kasa haɗiyewa "Hajiya dan Allah me ya mutu a palon nan?" Cewar hajiyar da ta shigo yanzu cikin faɗa Hajiya tace "Ke Zainab ban san iskanci fa waye ma ya gayye ku gidan nan?" Kallon Alhajin Zainab tayi kafin tace "Baban Farooq kaji ko? Sai da nace maka ba zan zo gidan nan ba ka dage sai munzo mun duba abokin ka to ga irin ta nan" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta fara tattara palon tana faɗin "Ni ba zan iya zama a kazantar nan ba" shi dai Alhaji ya kasa magana sai mamaki kazantar Hajiya yake ita warin ma baya damun ta tab lallai abokina na kokari wai irin wan nan abu haka, ita dai Hajiya ko kallon in da suke baya yi ba kan ta na kan wayar ta, ita kuma Zainab ta ci-gaba da da tattara palon har ta kai kitchen, wani warine ya bugo mata hanci wadda yasa ta yin baya ba shiri, cikin masifa tace "Ke dai Hajiya wallahi kinji kunya, ga yaranki nan tsab tsab da su basa son kazan ta amma ke sai uban kazan ta kamar zai kashe ki thank God ma da Allah yasa Part na yaran daban ai da kunyar da zakiji sai tafi haka" ita dai Hajiya bata tanka ba, da dai taga surutun Zainab ya ishe ta sai ta miƙe ta haura sama abun ta, dogon tsaki Zainab taja tare da wucewa ta koma cikin kitchen ɗin ta ci-gaba da aikin tana toshe hanci, girgiza kai kawai Alhaji yayi tare da ciro wayar sa ya fara latsawa ga uban yawu da ya tara a baki, Ihu mai gigita kwakwalwa Zainab ta saki daga cikin Kitchen ɗin, a guje Alhaji ya miƙe ya nufi Kitchen ɗin, kwance ragajab ya iskota a kasa ga jini na zuba daga gakin ta idon ta sun ɗagu sama bakin ciki gaba ɗaya ya bace idon nata ya zama fari zalla, zaro ido waje Alhaji yayi tare da karisawa wajen ta yana ihu yana kiran sunan ta amma ina bata ko motsi, duƙawa yayi yasa hannu yana kokarin ɗaga ta nan take idon ta ya sauya launi zuwa Pink color san man ya sake komawa purple kafin ya koma maroon kamar jini, ihu Alhajin ya fasa sai da Hajiya ta sauko kasa da gudun gaske tana faɗin "Lafiya nake jin Ihu?" A guje Alhaji ya fice daga cikin Kitchen ɗin ya bar gidan ma gaba ɗaya, kamar wani mahaukaci haka ya dawo sai baza babban riga yake a kan titi yana gudu, daga karshe ma cire babban rigar yayi yayi wurgi da ita a kan hanya ya ci gaba da guduwa Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 *💞TRIPLET'💞 *💞The beginning💞* *Episode 12* Ganin abun dake faruwa da Zainab yasa Hajiya ta fasa ihu tayi waje tana kiran mai gadi, da gudu mai gadi ya fito da toilet ba tare da ya ɗaure wandon sa ba saboda yasan halin Hajiya da bala'i masifa karta masa wani hukuncin, a ruɗe ya nufota yana faɗin "Hajiya lafiya" cikin tsawa tace "Kai malam ka ja wandon sama tukun nan" jikin sa sai kerma yake, dai dai lokacin Abba ya danna horn a bakin gate ta waje, a tsorace Hajiya tace "Wayyo Allah Alhaji ya dawo ban gyara gidan ba dama da gaske yake da safe zai shigo gashi na aiki Lami kasuwa Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kaga baba mai gadi karka buɗe masa kofa tukun nan ka bari ina zuwa ka koma toilet ɗin kaji?" Ta kai karshen maganar tare da wucewa da gudu ta koma cikin gida, ta shiga ruɗani ta manta da Zainab dake baje a kasa, tana shiga palo ta hau tattare tattare sharp sharp taje ta jawo kofar kitchen da karfi ta rufo ta wuce ta haye sama sauri sauri ta canza kayan jikin ta ba tare da tayi wanka ba, ta dawo Palo hannun ta riƙe da perfume na jiki, tsabar ruɗewa a tunanin ta air freshener ta ɗauko ashe perfume na jikine, haka ta feshe palon da body perfume nata gudu gudu ta mayar sama ta sauko ta nufi wajen, baba mai gadi yana bayi kamar yadda ta umarce sa bai fito ba, ita da kanta taje ta buɗe wa Abba gate tana faɗin "Sorry yana bayine" sauƙe glass ɗin motar Abba yayi cike da fara'a a face nashi yace "Ai nasan halin sa da yawan shiga toilet shi yasa ma ban damu ba" Abba kyakkywa ne sosai kaman sa ɗaya dasu Imran ba marabe shi suka ɗauko dukkan su, amma Hajiya Umaiya tafi su kyau tsabar kyan ta kamar ita tayi kan ta gata fara tas kamar baturiya, Kutsa motar cikin gida Abba yayi kai tsaye ya nufi parking space, yana kashe motar ya fito ya rungumi Hajiya Umaiya yana faɗin "Umaiya tun da na tafi baki cin abinci sosai ko?" Girgiza masa kai Hajiya tayi kafin tace "In ci mana me ka gani" "Naga kin kara ramewa ne ai kuma kinyi duhu" ya kai karshen maganar tare da jan dogon hancin ta, raba jikin su tayi suka jera zuwa cikin Palo, lokaci da suka shiga palon sai da mood na Abba ya canza dan shi mutun ne mai bala'i tsab ta ita kuma Umaiya kazama ce lamba ɗaya gashi duk yan aikin da aka kawo mata sai sunki zama saboda mugun tan ta bata da mutunci ko kaɗan ga wulanta ɗan adam ita idan datti zai shekara yana zaune kusa da ita bazata taɓa damuwa da shi ba, ta riga da ta saba, har namiji mai aiki sai da Abba ya kawo a baya amma haka Hajiya Umaiya ta sako mutumin a gaba da kazantar ta ga zagi da cin mutuncin yaga ba zai iya ba ya kama kan sa, yanzu mai aiki ɗaya ce ta rage mata Lami ita kuma kullun kashe ta da aika zuwa kasu Hajiya take dan akoi ta da ciye ciyen kwalama gata da son jiki kamar wata mage. Ganin face ɗin Abba ya sauya ne yasa Hajiya wayan ce masa da cewa "Muje kayi wanka sai muje restaurant mu ci abinci ko?" Jinjina kai kawai yayi dan in da sabo ya saba Umaiya bata girki kullun sai dai suje su sayo abinci shi yasa ta ko ina a gidan ledojin takeaway ne da su kan su takeaway ɗin, haka Abba ke hakuri dan yana bala'i kaunar Umaiya fiye da komai a rayuwar sa "Ina su Imran banji motsin su ba?" Abba ya tambaya yana hawa saman benen, bin bayan sa tayi tana faɗin "Imran ya ɗauki Akil da Akila sun tafi Uk hutawa yace one week zasu yi" ta kai karshen maganar dai dai Abba zai buɗe kofar ɗakin sa, jinjina kai da mamaki yayi lokacin da ya ga cikin bedroom na shi kamar yadda ya tafi ya bari haka ya dawo ya samu yau satin sa ɗaya da yin tafiyar zuwa Abuja amma yadda ya fita ya barɗakin ba wani gyara da a ka masa ga short na shi da ya cire tun ranar da zai tafi ya barshi saman bed bata taɓa ba yana wajen baya jin ma tun da ya tafi Umaiya ta shigo ɗakin, yana ɗaya daga cikin abun da yasa yan aikin ta ke kin zama su gudu sai tace su zasu sanya mata kaya idan tayi wanka ita bata son taɓa komai sai wayar ta kawai wankan ma sai bayan kwana uku uku take Girgiza kai Abba yayi tare da wucewa ya ajiye yar jakar sa kamar jakar system a saman bed ɗin ya fara ƙoƙarin gyara gadon yana faɗin "Alhaji Mustapha ya kirani ina hanya yace min zai zo shi da Hajiya Zainab su duba jikina waye yace musu bani da lafiya? Ko kece? Na dai am sa musu da to basu kariso bane?" Sai lokacin Hajiya Umaiya ta tuna da zancen Hajiya Zainab dake baje a Kitchen, ihu ta fasa tare da nufar waje da gudu, a razane Abba yabi bayan ta yana faɗin "Umaiya lafiya?" kai tsaye kitchen ta nufa tana salati, Abba na shigowa ya ja birki cike da tashin hankalin suke kallon Hakiya Zainab dake kwance a kasa an kwakwale mata ido dukka biyu ga jini nata malala kamar kogi, san nan an yanke mata nono dukka biyu an cire hancin ta, mutuwar tsaye sukayi shi Abba tsabar tsorata ya kasa karisa shigowa cikin kitchen ɗin, suna tsaye sunyi tsuru tsuru ita kam Hajiya Umaiya ma suman tsaye tayi a wajen, wani guhuwa me mai karfin gaske ne ya shigo cikin kitchen bakin kirin da shi yana bada sautin kamar wakar shaiɗanu aljanu, sun razana ainun sun kasa gaba sun kasa baya ita dai Hajiya Umaiya suman tsaye tayi shi kuma Abba yana ganin meke faruwa amma ya kasa motsawa, yana ganin guguwar nan tazo ta mamaye Hajiya Zainab ta rufe ta ruf na wasu yan mintoci kafin daga bisani guguwar ya mulmule ya zama kamar ball san nan ya fice ta window da ya shigo, guguwar na fita Abba ya duba babu Hajiya Zainab babu labarin ta guguwar ya tafi da ita ko alamar ta babu a wajen jinin ta daya zube ma babu shi a wajen, wajen ya koma clean, tashin hankali ba'a saka maka date yanke jiki Abba yayi ya sume a wajen ita dai Hajiya Umaiya a tsaye ta sume. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Gidan Abbi* Sosai Abbi ya shiga damuwa gani yake Irfan ba zai samu aiki ba kasan cewar yadda kasar ta zama yanzu, jiki a mace ya ɗauki waya ya kira dillalan da suka taya company 7 millon a kan suzo su saya kawai su bashi kuɗin ya fara wani business kafin su Irfan su dawo dan yasan idan Irfan na nan ba zai bari ya sayar ba shi yasa ya sallama musu shi tun kafin Irfan ya dawo an gama komai. Cikin kankanin lokaci dillalan suka zo kofar gidan Abbi, cike da rashin jin daɗi Abbi yace su shigo, ba musu suka shigo su biyu hannun su riƙe da jaka baka mai yar girma kaɗan, kai tsaye palo Abbi ya wuce da su, bayan sun zauna, har da ruwa Abbi ya kawo musu suka amsa suka sha san nan suka gaisa, bayan sun gama gaisawa ne Abbi yake sanar da su a kan su kawo 7 millon ɗin ya sallama musu company, ɗaya daga cikin sune yace "Alhaji ae yanzu ba zamu iya sayan wan nan kangon 7m ba aa ya mana tsada 5m shine last abun da zamu iya saye idan ka sayar mana" shiru Abbi yayi ya kasa magana saboda ɓacin rai, ɗaya daga cikin dillalan ne ya sake cewa "Alhaji ka sayar ne ko baka sayar mana ba mu tashi muyi tafiyar mu" kamar daga sama a bakin kofar shigowa suka ji an ce ba'a sayar ba kuma ba za'a sayar ba ku tashi ku fice daga gidan nan" a sukwane suka juyo ciki har da Abbi dan ganin wanene, wani matashi ne tsaye a bakin kofar shigowar hannun sa riƙe da katuwar jaka jikin sa na sanye da riga baki da wandon jeans blue ya daura rigar sanyi mai hula ya kuma sanya hular rigar a hansa baka iya ganin face nashi sosai, a yanayin jikin sa dai ba zai wuci 25 years ba, Ganin dillalan basu tashi bane yasa ya daka musu tsawa yana faɗin "Bazaku tashi bane?" Cikin sauri ɗaya daga cikin su yace "Alhaji mun saya 7 millon ɗin ga kuɗin bamu takardun mu tafi da shi" a fusace matashin nan yace "Wan nan fillin bazaa sayar ba ku fice daga gidan nan tun kan ranku ya ɓaci" jiki ba kwari suka wuce sumui sumui suka fice daga palon suka bar gidan Bayan dillalan sun tafi ne matashin ya kariso cikin palon ya zauna saman sofa dake fuskantar na Abbi san nan ya buɗe jakar da ya zo da ita "Bawan Allah waye kai? Me ya kawo ka gidana" cewar Abbi, shiru saurayin yayi bai tanka Abbi ba har ya gama buɗe jakar ya ciro wasu takardu guda biyu ya miƙawa Abbi yana faɗin "Irfan ya shirya next week zai wuce London *UNITED KINGDOM* karatun master's nashi su kuma Aafia da Umaima ance na canza musu makaranta, kuma na canza ɗayan takardan nasu ne na canza musu school, san nan wan nan kuɗin 100 million ne akace na kawo maka ka tayar da company ka san nan idan kana da wata buƙata a kace ka faɗa min" ya kai karshen maganar tare da ɗago kai ya zubawa Abbi ido yana jiran yaji ko Abbi na da wata buƙata "bawan Allah waye ya aiko ka?" Abbi yayi maganar cikin sanyin murya "No Alhaji wan nan bai shafeka ba kawai dai kafaɗamin idan kana da wata damuwar dan zan wuce aiki na ya kare" shiru Abbi ya ɗanyi kafin yace "Bani da ita amma zan so sanin wanda ya aiko ka da kuma kuɗin zuwa kwanana nawa ko sati nawa zan biya" rufe jakar saurayin yayi tare da ɗauka ya ajiye kusa da Abbi saman sofa, ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin "Bawan Allah ne ya baka kuma ba ya baka dan ka mayar bane no kyauta ne daga Allah sauran bayani a kan karatun Irfan a Uk yana cikin aljihun jakar nabarka lafiya" ya kai karshen maganar tare ficewa daga palon ya bar gidan gaba ɗaya, shi dai Abbi a tsorace yake jiki na rawa ya buɗe aljihun jakar dan yaga sauran takardun Irfan ɗin, nan ya ci karo da wata farar takarda mai ɗauke da sako later warware takardan yayi ya fara karantawa kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu ɗan uwana barka dai fatan kana lafiya ina maka fatan alkhari da fatan gamawa da duniya lafiya, nasan zakaji tsoron an san kuɗin nan shi yasa na haɗa maka da wan nan takardan, karkaji tsoro ka ansa kuɗin mallakin kane na baka har abada idan ma kana baƙatan kari zai iya karoma, yasu Aafia na canza musu school Masha Allah naga result na Aafia tayi kokari jamb ɗin ta yayi kyau tana da ilimi sosai ni ta ɗauko ashe, ita ma Umaisha ba laifi tana kokari ranar Monday Irfan zai iya wucewa Uk an gama shirya masa komai yaje yayi master degree ɗin sa ka gaida min da yarana idan sun dawo kasa musu Albarka, sako daga Hussain" zubur Abbi ya miƙe yana faɗin "Hussain daman Hussain yana raye? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun haba ɗan uwana me yasa zaka mana haka zuciya bata da amfani in dai har zaka iya sanin halin da nake ciki ka kawomin ɗauki to nasan zaka iya jin abun da nake faɗa yanzu ma dan Allah Hussain ka dawo garemu shakara 18 fa kenan rabon mu da kai zuciya bata da amfani karka biyewa zuciya kadawo mu haɗe kan mu, mu ci-gaba da yiwa iyayen mu addu'a, saboda ni da Maik zaka dawo ba dan yaya ba karka duba abun da yaya ya maka a baya ka ki dawowa dan Allah ka dawo mu muna son ka ai" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna ya fara fitar da abubuwan cikin jakar wai ko zai samu address ɗin Hussain, har ya kammala fito da komai na jakar babu komai sai wayan nan kuɗin da takardun sai kwalayen wayoyi kirar I phone 13 guda uku ko wani waya an rubuta sunan mai shi a jikin kwalin Umaisha Aafia Irfan, haka Abbi ya tattara komai ya mai da cikin jakar, yayi farinciki sosai ya kuma yi bakin ciki sosai yana bala'i son ganin Hussain amma ba dama tunda bai san in da zai same su ba, kwashe komai yayi ya mai da ya ɗauki jakar kuɗin ya fito dan ya tafi banki, nan ya ci karo da sabbin masu gadi ga wasu matasa tsaye a harabar gidan yasha mamaki sosai a tuanin sa ɓarayi ne har yafara kiran sunan Allah daya karesa, ɗaya daga cikin matasan ne ya kariso in da yake cikin girmamawa ya gaida shi san nan ya ɗaura da ciwa an ce suzo su rushe wasu ɓangarori daga gidan nan su gyara ginin san nan su kara gina abubuwan da babu, cikin sauri Abbi yace "Waye ya turoku?" A tunanin sa kila sun san address ɗin wadda ya aiko su, amma sai yaji akasin haka domin kuwa suma a waya a ka kirasu a ka basu wan nan aikin basu san daga in da a ka kira su ba, wucewa Abbi ya yi rai a ɗan ɓace ya nufi yar motar Irfan yana faɗin "Kuyi aikin ku" cikin sauri suka fara aikin su shi kuma Abbi ya shiga motar Irfan ya tayar ya nufi gate, tun bai kariso ba wani jibgegen mai gadin da aka kawo masa sabo yazo ya buɗe masa gate ɗin ya kutsa motar waje ya nufi bank su kuma masu aiki suka fara aikin su. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *KANO* Zaune daddyn Jelly yake cikin katafaren office na shi na Engineer dake company nin sa filman Nigeria limited sai murmushi yake yana murna a kan aikin nan da suka samu dan ba karamin aiki bane contract ne na billions of Naira, da sallama P.A ɗin sa ta shigo hannun ta ɗauƙe da kyakkyawan plate mai ɗauke da Tea da snacks, har kasa ta duƙa ta gaida shi sai murmushi yake ya amsa mata gaisuwar san nan ta miƙe ta ajiye masa plate ɗin a saman table ɗin ta fice daga office ɗin tana yaba kyan hali irin na daddy, cikin nitsuwa daddy ya ɗauka tea ɗin ya fara sha ya ture snacks ɗin gefe dan bai jin yinwa sosai kawai ma dan ya saba shan tea ɗin ne idan yazo office amma ban da haka yau baya jin yinwa dan yayi breakfast dasu Irfan kafin su fito tare shi ya wuto office su kuma suka tafi ganin gari a kan da yamma zasu biyo masa su koma gida tare, bai karisa shan tea ɗin ba barci ya ɗauke sa a wajen yana zaune. After some hours Da kyar daddy ya iya buɗe manya manyan idanun sa da suka masa nauyi, da kyar ya iya waro su waje ya sauke su saman katafaren agogon bangon dake manne a bangon ɗakin sa dake cikin office ɗin, zubur ya miƙe tare da goge idon sa yana kallon time ɗin da kyau 4:45 pm, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi abun da kawai yake iya furtawa mamaki yake yaushe yayi barci haka shi da yake zaune yake shan tea lokacin kuma 10:00 am me ya faru da shi haka? Haka ya zauna yana jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su jiki ba kwari ya yunkura zai miƙe a sukwane ya koma ya zauna ganin jikin sa babu kaya innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya faɗa tare da kara waro idon sa waje sai yanzu ma ya lura ashe a cikin bedroom na shi na cikin office ɗin yake, yasha ruwan mamakin waye ya cire masa kaya gaba ɗaya haka, wai mekeke faruwa ne ya kai karshen maganar tare da miƙewa a fusace ya fara sanya kayan sa dan yaje ya tambayi P.A dan ba wadda ya isa ya shigo office na shi ba tare da sanin ta ba, Bayan ya gama sanya kayan sa tsab da tunani fal ransa ya nufi waje yana jan kafa da kyar da kyar dan gaba ɗaya jikin sa ya masa nauyi, Haka ya fito daga office ɗin gaba ɗaya ya nufi wajen P.A, turus ya tsaya ganin office nata wayan babu komai har desktop computer ta babu a wajen, ta kwashe komai ta tafi, ganin haka yasa daddy ya fahimci a koi wani abu a kasa akoi makarkashi ya, cikin sauri ya juya ya koma cikin office na shi ya ɗauko wayar sa dan ya kira P.A ɗin, nan yaci karo da saƙo guda biyu ɗaya na P.A ɗaya kuma na Baban Muneer wato Alhaji Auwal abokin takarar sa sun turo masa, jikin sa har kerma yake wajen buɗe sakon baban Muneer, yana shiga sai yaga video ne cikin tsumuwa ya buɗe video, wata iriyar mahaukaciyar yarazana yayi lokacin da idon sa ya sauka kan Video, har sai da wayar tasa ta faɗin ƙasa a wajen, kasa motsawa yayi ya kurawa wayar ido yana kallon ta dan koda wayar ma ta faɗi kasa bata ɗauke ba video nayi, tashin hankali kwance daddy yake saman gado sa na cikin bedroom ɗin office ɗin kwance yake jikin sa ba kaya shi da P.A, abun da ya kara rikitashi shi ne gashi kuma ba barci yake ba a video idon sa biyu suke sheke ayar su sai dai shi ya kasa tuna lokacin da a kayi hakan a video dai gashi nan ita P.A tana nuna bata so shi kuma yana tilasta mata, dogon salati yasa muryan sa har rawa take ya durkushe kasa a wajen nan take hawaye wani na bin wani suka fara bin kuncin sa, ganin abun yake tamkar a mafarki, a hankali ya buɗe bakin sa muryan sa na kerma yana kuka yace "Ina saurayi matashi ma ban yi zina ba sai yanzu why why P.A zaki min haka Alhaji Auwal kacuci rayuwata ka gama da ni Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" yana cikin surutan da yake, kiran Alhaji Auwal ya shigo wayar nasa, cikin sauri jikin sa har ɓari yake wajen ɗaukan wayar tare da yin picking na call ɗin, Daga ɗayan ɓangaren Alhaji Auwal ya bushe da dariyar mugun ta yana faɗin "Ka gama kukan ne ko baka gama ba, dan ina da tabbacin ka gama kallon video yadda kaci amarcin ka a karo na biyu dan kaci na farko kam da marigayya matar ka, amma fa gaskiya na jinjina maka ashe kai ma jarumin namiji ne ba rago ba ashe kai ma ɗan hanune ji yadda ka farwa yar mutane daman yinwar abun kake kawai dannewa kake kakiyin aure, to ni dai ba zan iya ganin abokina cikin yin wan nan ba shi yasa na bugar da kai dan ka biya bukatar ka nasan yanzu zam zam kake jin ka ko? Tun ɗazun nake ta kallon video nan naka ina koyar wasu style nima" ya kai karshen maganar tare da kara bushewa da dariya, shi dai daddy hawaye kawai yake yana tuanin mafita dan dai yasan hujjar sa ɗaya shine camera dake cikin office ɗin to amma yasan Alhaji Auwal bazai bar camera a kunne ba, ba zai bar wata hujjaba "Kasan me nake so da kai?" Cewar Alhaji Auwal cikin sauri daddy ya girgiza kai yana faɗin "A'a" da sarkakkiyar murya "Good yaron kirki, kayi kuskuren shiga gonata da kayi yanzu duk ba ma wan nan ba, zan ajiye video nan a waje na ni kaɗai bazan tura ko ina ba amma da sharaɗi, sharaɗin sune kamar haka idan ka kuskura ka sanar da wani abun da ke faruwa wallahi zaka tsinci video nan a duniya, abu na biyu wan nan contract ɗin ya zama dole kasan yadda zakayi ka sallamawa company na, abu na uku kuma duk abun da nake so shi zaka gudanar a company ka, abu na huɗu zan faɗa maka gaba idan ka gudanar da wayan da na faɗa maka yanzu a kan tsari ba tare da kuskure ba, san nan ina son ka sani kuskure kaɗan zakayi na saki video ka ga duniya jama'a su kalli chaskalewan Engineer Abdul Malik maik nasu, zanga har lokacin ma zasu ci gaba da yabon kane ko dai ya abun zai kasan ce amma kuma akoi dayawa da zasu ɗauki style fa dan kai ɗin ba na wasa bane duk da cewa na kara maka karfi da kwaya" ya kai karshen maganar tare da shekewa da dariyar shakiyanci, shi dai daddy ban da hawaye ba abun da yake, sake bushewa da dariyar iya shege Alhaji Auwal yayi kafin yace "Bari na barka kaɗan huta zuwa anjima sai muyi magana ko? Dan na lura yanzu a zauce kake" yana kai karshen maganar ɗiff ya kashe wayar, kuka sosai daddy yake yana tuanin ta ina zai fara sallamawa Alhaji Auwal contract ɗin nan sai dai ya zauna da gomnati ya sanar da ita company sa ta samu matsala ba zai iya aikin ba kenan, innalillahi wa inna ilaihir rajiun kara rushewa yayi da kuka mai ɗan sauti, daman shi daddyn Jelly yana da sauri hawaye. To muleko su Rimsha mu gani 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *ABUJA* zaune a saman katafaren gadon ta dake cikin bedroom nata gwaggo take tana zaune tana latsawar ta jikin ta sanye da gown mai kama da abaya black color ta sanya turban cap mai kyau fari a kan ta, baki ɗauke da sallama Rimsha ta shigo ɗakin jikin ta sanye da wando zuwa gwiwa black color da riga mai karamar hannu pink color ta zubo dark black curly hair ta daya sha gyara sai sheki yake gwanin ban sha'awa, gashi a nannaɗe kamar indomie ta sake shi har tsakiyar bayan ta, sai faman lumshe dara daran fareren sleeping eyes nata take tana buɗe wa kamar wadda barci bai ishe ta ba fuskar ta fayau ba kwalliya amma sai sheki fatar ta keyi kamar fatar jariri, lallausan pink lips na tan nan kamar ta sanya lipstick pink, hayewa saman gadon tayi tare da kwatar da kan ta saman cinyar gwaggo cikin shagwaɓa tace "My gwaggo Jehan tace min wai Uncle Shitu ba kanin daddy bane da gaske ne?" kallon kyakkyawar face nata gwaggo tayi cike da so da kaunan tace "My siha da kikayi wan nan maganar kin tunamin da wani abu, bari na ɗauko in nuna miki amma gaskiya ne Alhaji Shitu ba ɗan uwan mu bane kawai zumunci ne ya haɗa" ta kai karshen maganar tare da miƙe wa ta sauƙo kasa daga kan gadon ta nufi drawer san ya kayan ta, Rimsha na kwance tana kallon ta Wata yar karamar akwati ta ɗauko ta dawo saman gadon tana kokarin buɗe wa Jehan ya shigo ɗakin tana faɗin "Ke Rimsha tun ɗazun nake neman ki, ki wuce kije ki shirya mu tafi Shopping daddy na jiran mu, san nan na gama mana list ɗin abubuwan da zamu saya" ta kai karshen maganar tare da zama gefen Gwaggo tana kwaɓe fuska Buɗe ɗan akwatin gwaggo tayi ta ciro wasu abubuwan hannu guda biyu masu bala'i kyau, da alama na tarihine dan an yi su da kauri irin na da kuma da gani na azurfa ne, sai kallon abun Jehan da Rimsha suke ba karamin kyau abun ya musu ba, ajiye abun gwaggo tayi san nan ta fito da wasu neck chain sirara suma guda biyu sai kyalli suke da alama na gold ne, ajiye ɗaya tayi kusa da abubuwan hannu, ta buɗe ɗayar ta sanyawa Rimsha a wuya tana faɗin "Lokacin da nake yammata ne nake kwalliya da su" ta kai karshen maganar tare da ɗauko ɗayan ta sanyawa Jehan tana faɗin "Ko da yake har yanzu ni yanmata ne" murmushi Jehan tayi kafin tace "Gwaggo kece yan matan? Bayan kin girma zaki kai 50 years fa" gwaggo na kokarin magana Rimsha ta rigata da cewa "Ai kuwa gwaggo ba tsohuwa bace dan mum ta faɗa min gwaggo bata taɓa yin Aure ba kinga kuma wanda bai taɓa yin aure ba ai bazai tsufa ba" tsaki Jehan taja kafin tace "Ke dalla idan masu ido da kwalli suna magana ki dai na sako idon ki duk kwantsa dan mutun bai taɓa yin aure ba sai a ka ce miki ba zai tsufa ba gwaggo fa ta girmi daddy Auntyn daddy ce su biyu maman su ta haifa daga gwaggo sai daddy to daddy ma yanzu ya kai 40 to 45 years haka bare gwaggo, to bari kiji gwaggo kam ta tsufe ta yagalgale dan kawai tana gyara jikin tane badon haka ba da yanzu da sanda take tafiya" ta kai karshen maganar tare da jan tsaki ta miƙe zata fice daga ɗakin, hannun ta gwaggo ta riƙo ta sanya mata abun hannun ko a jikin ta bata damu ba dan in da sabo ta saba da iyashegen Jehan, ita dai Rimsha shiru tayi bata sake magana ba Gwaggo na gama sa musu abun hannun suka miƙe har suna rige rigen fita gwaggo nace musu "karfa ku cire abun hannun nan da sarkan dukka, ku barshi a jikin ku har ku haifi yara kuma ku basu dan nima wajen maman mu na gado" ina ai tun kan gwaggo ta faɗin word ɗaya ma sun yi waje basu ji me tace bama sun tafi shirin zuwa shopping. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 *💞 TRIPLET'S💞 *💞The beginning💞* *Episode 13* *KANO* Da murna da farinciki su Irfan suka shigo office ɗin daddy, jin shigowar su yasa daddy saurin goge hawayen face nashi ya miƙe ya shiga toilet ɗin cikin bedroom ɗin, sauri sauri ya wanke face nashi ya ɗan gyara jikin sa ya fito, zaune ya same su saman kujerar da yake zama, Irfan na zaune saman kujerar, Imran na zaune saman visitor chair, suna ganin daddy ya fito suka kara faɗaɗa murmushin su Imran na faɗin "Bappa bamu zo da wuri bako?" Kakalo murmushi dole daddy yayi wadda ake cewa tafi kuka ciwo, yana kokarin yin magana Irfan sarkin basira ya rigashi da cewa "Bappa me ya sameka meke damun ka?" Cikin sauri daddy yace "babu komai Just I'm feeling headache ne" cikin sauri Imran yace "Bappa muje hospital mana to" girgiza kai daddy yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "No muje gida kawai naji sauki" kallon Irfan Imran yayi, yayin da shima Irfan ɗin shi yake kallo, shiru sukayi sai da daddy ya fice san Imran yace "Irfan me ka fahimtar game da Bappa dan ni ina ganin kamar a koi wani damuwa bappa bai taɓa yimin haka ba ka duba fa ka gani yau office nashi muka zo amma ya fice ya barmu a ciki, ni da wani lokaci ma idan nazo garin nan wallahi saboda son da yake min ajiye aiki yake a ranar ya ɗau hutu dan muyi hira koda kuwa bai da lafiya baya taɓa kyaleni na zauna shiru amma yau har ya fita ya barmu a office na shi kai a koi matsala" jinjina kai Irfan yayi kafin yace "kayi gaskiya Imran duk da ban san halin bappa sosai ba amma tabbas yana cikin wata damuwar yanzu dai tashi muje, ma karasa maganar a gida" miƙewa Imran yayi ba tare da ya sake magana ba, shima Irfan ya miƙe suka gera suka fice waje, yau daddy ko system na shi bai ɗauka ba haka suka wuce gida. AKIL Tsaye yake a tsakiyar palon daddyn Jelly, sanye yake da wando jeans baki da riga fari tas ta ɗaura cardigan mai hula a saman kayan nasa, ya sako hulan a kan sa, tsaye yake yana fuskantar makekiyar Tv plasma dake manne a bango ya bawa bene baya, ya duƙar da kai kasa ya zura hannu a aljihun sa da alama wani abun yake jira. Da sallama Akila Aafia da Umaisha suka sauƙo daga sama suka shigo palon, wucewa Akila tayi taje ta rungume sa ta baya cikin shagwaɓa take faɗin "I missed you yaya Akil" juyowa yayi ya rungumeta yana faɗin "Missed you too heartbeat" yayi maganar dai dai lokacin da idon sa ya sauƙa kan Umaisha da Aafia dake tsaye kusa da centre table, nan taƙe ya ɗaure fuska tare da sakin Akila cikin tsawa yace "Waya baki izinin fita? Ina kuma kuka je nazo gidan nan ɗazun baku nan?" Ba Umaisha kawai ba har Akila sai da ta tsorata da yadda yayi maganar, nan take Umaisha jikin ta ya fara ɓari dan tana da tsoro sosai kirjin ta ya fara dukan uku uku tsawa ya kuma daka mata "Ke bada ke nake bane?" Murya na rawa tace "Kayi hakuri mun bi su yaya Imran ganin gari ne shine yanzu suka dawo damu suka wuce office ɗin daddy" "Zo nan!!" Ya faɗa yana kare mata kallo, cikin tsoro ta kariso gaban sa zata tsugunna ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata baya buƙata da hannun sa, hannu yasa ya riƙo kunnan ta ya murɗe da ɗan karfi, cike da bada umarni ya fara magana "Daga yau sai yau idan kika kuskura kika sake fita ba tare da ni na baki izinin ba Allah ba zan yi kaffara ba daga ranar zaki dawo ɗaki na da zama kuma karki yi tunanin idan kin dawo ɗaki na ɗin daɗi zaki ji, no rufeki zan rinƙa yi ko palo ba zaki leƙa ba kin ji na gaya miki" hawaye Umaisha ta fara yi saboda murɗe mata kunne da yayi yana mata zafi sosai, ganin tana hawaye ne yasa ya saki kunnen nata tare da ciro handkerchief daga aljihun sa ya goge mata hawayen yana faɗin "Idan kika sake bari hawayen ki suka zuba ranki zai ɓaci ban son ganin su in ma na farinciki ko na bakin ciki dukka bana son gani" shiru tayi ta sunkuyar kanta kasa ita kunyar sa ma take ji tsawa ya daga mata "Ke ɗago ido ki kalle ni ban son munafurci sai kuyi ta wani sunkuyar da kai idan mutun na muku magana a waje amma da zarar anyi aure duk sai ku riƙiɗe ku zama tantiran yan iska masu lasisi sai ka rasa ina sunkuyar da kai lokacin da ba'a yi auren ba yake, sai ku watsar da komai ku ɗauko rayuwar dabanci da hauka to ni bana son munafurci komai na a fili nake dan haka na san komai game da halin mata karki fara min munafurcin kun nan tun yanzu, ki nunamin true color ki kawai a wuce wajen!!" ikon Allah ita dai Aafia zubawa Akil ido kawai tayi babu ko kyabtawa ita kuwa Akila in da sabo ta saba da halin sa, cike da jin kunya Umaisha ta ɗago kai tana ɗan kallon sa kasa kasa "Ke nace ban son munafurci ko, ki kalli cikin ido na kawai tun yanzu yafi min a kan kiyi ta ɓoye fuska sai munyi aure kizo kina tsayamin a kai kina min wallahi tallahi kina kallo na cikin ido, shi abokina ma da yayi rashin Sa'a har ce masa ake idan ya isa yace tak al halin lokacin da yake neman auren ta tsabar kunya da biyayya irin nata itace Amyra a islamiyar su, amma daga yin auren su ta dawo rikakkiyar yar daban cikin gida to ni ban yarda da wan nan iskanci idan mace ta min abu dukan mutuwa zan mata" Allah Sarki Umaisha bai war Allah ko kala bata ce masa ba tayi shiru tana jin surfan da yake "Zan wuce Kaduna yanzu ina son ki faɗa min me kike da buƙata" cikin sauri ta girgiza kai tana faɗin "Bana buƙatar komai" tayi maganar cikin sanyin murya, guntun tsaki yaja tare da sanya hannu ya ɗauko ledar da ya ajiye sama hannun sofa tun shigowar sa, ya miƙa mata yana faɗin "Na miki setting na komai na wayar karki kuskura naga number wani a wayar nan naki idan ba na family ki ba, san nan zan kara ja miki kunne a kan maganar fita ko nan da kofar gida ban yarda ki taka ba, bayan haka ban yarda ki rinƙa yawan magana ba kina hira da mutane ban yarda da wan nan ba banso" ya kai karshen maganar tare da ciro wrafer sabbin ɗari biyar biyar daga aljihun wandon sa wadda a kalla zasu kai 50k ya miƙa mata yana faɗin "Ki sai kati idan na cikin wayar ta kare san nan zan sa azo a ɗauke ki aje a buɗe miki Account dan nasan baki da shi" girgiza kai tayi cikin sanyin Murya tace "A'a yaya Akil ka bar kuɗin ka nagode wayar ta isa" a fusace ya ɗaga hannu zai wanka mata mari Akila tayi saurin riƙe hannun sa tana faɗin "Ansa kuɗin Umaisha ki tafi ɗaki idan kinje ki tashi Jelly daga barcin ya isa haka yamma yayi sosai" jiki na kerma Umaisha ta ansa kuɗin da gudu ta haura sama Aafia tabi bayan ta. Kallon face ɗin Akila yayi cike da so da kauna yace "Heartbeat me yasa kika riƙeni?" Murmushi ta saki tana faɗin "Yaya Akil bakaga yarinya bace? Kamar ni fa take shi is 15 years fa, yanzu zaka iya dukana?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a kafin yasa hannu yana shafar kan ta a hankali yace "Heartbeat ai ba wanda ya isa ya taɓa ki a kasar nan ya kwana lafiya babu shi wallahi" faɗawa tayi saman kirjin sa tana dariya tana faɗin "that's why I love you my lovely brother" duƙo da kan sa yayi ya manna mata kiss a goshi ta tare da raba jikin su ya nufi hanyar fita yana faɗin "Sai kun dawo ni na wuce Kd ki kula min da kan ki san nan ki faɗa wa yarinyar nan karta kuskura na sake bata abu taki ansa, zan iya karyata a kan hakan kin san bana son hakan" kafin Akila tayi wata magana ma ya fice daga palo, bin sa kawai tayi da ido tana mamakin irin halin sa. Akil yana kutsa motar sa waje gate ɗin, su kuma su daddy suna kutso motar su cikin gida, ko kallon in da su daddy suke bai yi ba yaja motar sa ya bar layin gaba ɗaya ya miƙi hanyar airport. Daddy kuwa yana kashe motar sa a parking space ya fito ya nufi cikin gida, kai tsaye bedroom nashi ya wuce ya rufo kofar ya sanya key, Ko da su Irfan suka shigo palon, babu kowa shiru palon ganin haka sai suka kara sanin ba lafiya ba dan haka sai suka wuce masaukin su dan suje suyi wanka anjima suzo su tambayi daddy ko zai faɗa musu meke damun sa. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *ABUJA* Shiryawa sukayi Rimsha cikin Abaya doguwar riga blue color, kayan sun ansa jikin ta, kyanta ya kara bayyana, da kyar mum ta iya ɗaure mata dark black curly hair tan nan saboda tsantsin gashin, tayi light make up a face nata, kamar ka sace ta ka gudu saboda kyau da tayi, ga dara daran fararen sleeping eyes nata nan sun sha kwalli sai kyan su ya kara bayyana sai ɗaukan hankali suke, su gwaggo dukkan su sai da suka yi magana a kan kyan idon Rimsha, idon nata a koi ɗaukan hankali da kyau sosai, idan ka kalleta in the first place zaka yi tunanin barci take ji koda kuwa daga barci ta taso sabo idon nata kamar zata lumshe su haka suke, gasu dara dara fafare tas kamar auduga kwayar idon nata kuma dark brown ne mai ɗaukan hankali gwanin ban sha'awa, sai faman lumshe su take tana buɗe wa, mum na fama da ɗaure mata kai. Ita kuma Jehan sanye take da wandon jeans Ash color da top fari tas, ta tara gashin kanta tayi parking har baya, Mum na ce mata ta sanya hijabi sai faman turo baki take tace "mummy I told you I don't like hijab" shiru mum tayi bata sake magana ba dan tasan daddy ba zai ɗauke ta haka nan ba hijabi su fita ba Tsab suka kammala shirin su ita dai Rimsha ta sanya mayafin rigar ta a kan ta, sun yi kyau over musamman Rimsha dake da wata iriyar jiki wadda ko wani kaya ta sanya sai ya zauna a jikin ta kamar dan ita a ka yi shi sai ya lafe yabi shape ɗin coca colar ta ya lafe kamar dan ita a kayi su, koda kuwa kayan Jehan tasa sai yabi shape ɗin coca colar ta ya zauna dai dai kamar nata ne while Jehan kuma tafita ƙiba kaɗan Zaune a palo suka isko daddy yana jiran su, da sauri Rimsha ta tafi ta rungume sa tare da manna masa kiss a kumatu tana faɗin "Sorry dad for keeping you waiting" manna mata kiss shima tayi a goshi yana faɗin "No don't worry about that, have you done?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh sun gama, ɗago kai yayi ya kalli Jehan dake tsaye tana latse latsen wayar ta, "Where is your hijab Jehan?" Daddy ya tambaya yana kokarin miƙewa, turo baki tayi kamar biro cikin shagwaɓa tace "Allah daddy i don't like the hijab at all" kallon Rimsha yayi kafin yace "Kawo min Hijabin ta" da sauri Rimsha ta wuce ta nufi sama, Jim kaɗan ta dawo hannun ta ɗauke da Malaysian hijab mai kyau fari tas yasha kwalliya da stone masu kyalli, ansa daddy yayi da kan sa ya sanya mata hijabin san nan ya riƙo hannun su suka fice mum na ta musu addu'ar dawowa lafiya da Allah ya tsare hanya Sai faman kwaɓe fuska Jehan take haka suka wuce parking space, da sauri ɗan sandan dake tuƙa daddy yazo ya buɗe musu kofar motar suka shiga gidan baya, daddy ya zauna a tsakiyar su, Ba tare da ɓata lokaci ba ɗan sandan ya shiga mazaunin driver yayiwa motar key suka bar gidan. Direct *Jabi Lake Mall* suka nufa a parking space ɗan sandan yayi parking ya fito ya buɗe masu motor, suka fito suka nufi cikin Mall ɗin suka shiga suka wuce Boutique (wajen sayar da kayan sawa) Rimsha ta gwada wan nan ta cire wan nan, ta gwada kaya yafi a ƙirga duk wanda tasa se tayi complain a kan bai mata ba. Se daga baya tayi final choice akan wata wedding dress (kayan Amare) doguwar riga ce fara kal me high neck ga ƙasan ta ya buɗe sosai yana jan ƙasa daga saman kuma fitted da dogon hannu ne Amman net ne hannun, rigar ta zaɓa tare da ɗauko high heel black color sai crown sima black color, Sai ɗankwali wanda zata daura shi ma black. Wani ma'aika ci ne ya nufa Rimsha da irin abun da Amare ke sawa wanda ake rubuta Bride To Be, cikin natsuwa ya fara magana "Me zan rubuta maki anan" yayi maganar cikin harshen turanci yana nuna mata abun, da murmushi ɗauke a face nata tace abata inda zata rubuta. shi dai daddy ya zuba mata ido duk matsin ta akan idonsa, Jehan kuma kamar ba ta a wajen tayi shiru hankalin ta na a kan wayar ta tana latsawa, Miƙa mata Memo aka yi da pen, ta ansa tayi rubutu ta miƙa masa, 5mins ya dawo da abun black anyi rubuta da farin zare an rubuta ta gaban * Happy graduation First lady Rimsha* ta baya kuma aka rubuta *Finally done with primary school*. Amsa tayi ta nufi daddy tace "look daddy how does it look?" Tayi maganar tana miƙa masa, zaunar da ita yayi a saman cinyar sa sannan ya amsa abun cike da so da kauna yace "It looks beautiful" murmushi tayi tana kwantawa a ƙirjin sa karaf dara daran sleeping eyes nata suka sauka akan Jehan dake zaune tana latsa waya kaman ba ita a gurin "Jehan aren't you buying the clothe" Rimsha ta faɗi cikin kulawa tayi maganar tare miƙewa daga cinyar daddy ta nufi Jehan ɗin ta zauna a gefen ta, tana kallon face nata Miƙa wa shima daddy yayi ya nufo su yana faɗin "My Jehan what's wrong bazaki sayi kayan bane?" Ya faɗi cike da kulawa yana ƙaraso wa wajen nasu, tsaki tayi tace "Daddy kayan da nake son saya I can't find the picture on my phone" tayi maganar cikin sanyin murya, buɗar bakin daddy sai cewa yayi "kinga kayan da Rimsha ta ɗauka?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a tana faɗin "No daddy am busy looking for the picture, my mind wasn't there" jinjina kai daddy yayi kafin yace "okay take a look at that outfit there" yayi maganar yana nuna mata irin rigar Rimsha dake rataye a matsayin sample, zumbur Jehan ta miƙe tana murmushi wanda ya kara fito da kyan ta, "Yeah daddy it's, it looks more beautiful in reality" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi wajen rigar, sosai ta kurawa rigar ido tana kare masa kallo kafin ta juyo tace "Daddy what about the rest of the stuff?" Tayi maganar tana zuba masa dara daran Idon ta "zasu yi maki irin kayan da Rimsha ta zaba ai" Cewar daddy ya kai karshen maganar tare da juyowa ya kalli ɗaya daga cikin ma'aikatan yace "Get her what to write what she wants for you to write for her" ya ƙai karshen maganar yana nuna mata gefen sa akan tazo ta zauna, ba musu ta dawo ta zauna kusa da shi, ma'aikacin ya kawo mata, ita ma tayi nata rubutun tagama ta miƙa masa Miƙa wa daddy yayi tare da riƙo hannun su yana faɗin "muje mu karasa shopping ɗin kafin suyi packaging ɗin, it's getting late now" miƙewa sukayi suka nufi kofar fita, juyo wa daddy yayi yace "package everything in less than 30 minutes we'll be back in a while" Ya kai ƙarshen maganar tare da fice wa ɗan sandan sa ya rufa masu baya, tun kafin su fice ma'aikatan suka amsa da "Alright Sir" Jiki na rawa suka fara haɗa masu kayan suka yi packaging suka saka a leda suka yi bill ɗin. A bangaren su Rimsha kuwa direct cikin mall suka nufa suka sassayi kayan da zasu kai na party, ko mai kayan ciye ciye na students, abubuwa sosai suka saya kama daga Capri-son, Happy hour, Munchit, Cocopops sweets kala kala komai seda suka saya daga ƙarshe suka sayi leader ɗin party park, Jehan ta ɗauki na Barbie Rimsha ta ɗauki ta Sofia, the first suna fitowa dara daran idon Rimsha ya sauka akan Ice cream cikin zumuɗi tace "Daddy i want this Ice cream" tayi maganar tana nuna masa Ice cream ɗin "No my Siha sanyi yayi yawa" marairaice masa face tayi kamar zata yi kuka, cikin sauri yace "A'a My Rimsha me abun kuka kuma ɗauki dole ma ai na sai miki kefa Jehan zaki sha?" Turo baki Jehan tayi tana faɗin "Ni Smoothie nake so" jinjina kai daddy yayi Rimsha ta ɗauki ice cream ɗin daddy ya biya suka fice daga wajen suka koma Boutique aka yi masu Bill na kayan da suka ɗauka, daddy ya bada ATM nashi, suka ansa suka sanya a POS na su san nan suka miƙo masa POS ɗin dan ya saka pin nashi, a tare Jehan da Rimsha kowa ya miƙa hannu suna rige rigen wai su zasu saka kowa yaƙi bari ɗaya yasa, mamaki ne ya kama daddy, a mall da zai biya kuɗin ice cream shi ya sanya pin da hannun sa basu damu ba sai a nan ne zasu ce su zasu sa. Da dai daddy ya ga basu da niyar bari ɗaya yasa pin ɗin sai ya ansa ya sanya pin ɗin ya raba gardama. Ɗan sandan su na tsaye yana riƙe da kayan da suka sayo a mall ɗin, zai ɗauki kayan Boutique ɗin ɗaya daga cikin ma'aikatan yayi saurin ɗauka yace "Its my duty lemme take it to the car" haka akayi ya kai masu kaya har mota daddy ya ciro rapper na 500 ya bashi godiya ya rinƙa zubawa har suka bar wajen ya juya ya koma bakin aikin sa. Ko da suka koma gida su mum na palour suna jiran su. Daddy da Rimsha ne kawai suka yi sallama, Jehan kuwa cinyar Gwaggo ta haye ta fin cike Hijab ɗin kanta tana faɗin "My Goggo am tired am hungry" shafa kanta Gwaggo tayi tace "sorry let's go and have dinner daman ku muke jira" ta ƙai karshen maganar tana kama hannun ta suka nufi dining. Ita kuwa Rimsha gun Mum ta nufa ta zauna a gefen ta ta kwantar da kanta a kafadar ta "let's go and have dinner" mum ta faɗi tare da kama hannun Rimsha takai ta kan dining gun su Gwaggo ta dawo wajen daddy ta masa Sannu da zuwa tace suje su ci abinci tun da yayi wanka kafin su fita in yaci abinci se yayi wankan kwanciya. Jinjina kai yayi san nan suka wace dining ɗin suka fara cin abinci. After some hours. RIMSHA & JEHAN Zaune suke a Palon sama Kowa Cikin kayan bacci. Sun baza tulin kayan da suka sayo suna aikin sassakawa a leda, se kusan 11 pm Suka kammala sannan kowa ya nufi makwacin sa kamar yadda suka saba sai murna da farinciki suke. *PRIZE-GIVING* DAY A yau ne ranar ƙarshe da zasu makaranta zasu yi hutu sunyi shirin su kaman amare komai irin daya Gwaggo ta daura masu ɗankwali kaman gwaggoro suna sanye da danƙara danƙaran gold kaman larabawa, sun fito sun yi kyau over. Daddy na sanye Cikin danƙareriyar getzener ɗinkin babbar riga Fara kal anyi mata Aiki na Manyan Mutane da Blue ɗin zare ya saka Hula ita ma blue takalmi ma blue se kamshi yake zubawa kaman sabon ango. Bayan sun yi breakfast se wurin 9:30am suka bar gida kasan cewar 10:00am ne partyn Rimsha ta matsa su tafi shiyasa suka tafi da wuri. Tun daga bakin gate ɗin an tsara komai anyi adon da ballons kalar uniform ɗin makarantar, a cikin Hall ɗin makarantar za'a yi partyn kowa yayi shiga ta alfarma. Daddy a motor sa ya tsaya yace da ɗan sandan ya rakasu ajujuwan su ya kai masu kayan su, haka akayi tun daga nesa da ajin su ƴan ajin su Rimsha suka rinƙa mata kirari "Our first lady is now our Princess" aji ta shige suka fara gaisuwar rungume rungume juna da students yadda suka saba, Aunty ta fito ta amsa kayan da ɗan sandan ya biyo Rimsha dasu. Jehan kam tuni ta wuce zuwa class ɗin su tace ma ɗan sandan ya fara kaima Rimsha se ya kawo mata na ta kayan, bayan Aunty ta amsa kayan Rimsha sai ɗan sanda ya nufi ajin su Jehan ya kai mata nata kayan, san nan ya dawo parking space wajen daddy ya tsaya a gefen motor. 10pm Dukkanin ɗalibai da malamai duk sun hallara a Babban Hall ɗin makarantar wasu parents ma duk sun shigo Jehan da Rimsha se zuba ido suke suga shigowar daddyn su bama su kaɗai ba kowa jira yake yaga shigowar Nawazuddeen amma shiru bai shigoba. Sai 10:30am ya shigo yana tafiya ta ƙasaita irin na manyan mutane kana ganin shi ko baka san wanene ba zaka san ba ƙaramin mutum bane. Malamai ne cike harda me makarantar duk suka miƙe don girmama shi, ɗalibai ganin Malaman su sun miƙe yasa suma suka miƙe sauran parents ma haka, shi mai makarantar ne ya zo ya taro daddy ya miƙa masa hannu sukai musabaha. San nan ya masa jagoranci zuwa inda aka tanada domin shi, kafin ya zauna ya buƙaci a bashi mike zeyi magana, jiki na rawa MC ya bashi aka kashe kiɗan dake tashi saman sama, Cikin natsuwa da wannan zazzakar voice nashi yayi Sallama dinbin al'umma dake wajen suka amsa masa sannan ya buɗe musu taro da addu'a da turancin, daga ƙarshe ya musu godiya ga karrama shin da suka yi sannan ya buƙaci kowa ya zauna kamin shi ma ya zauna. Duk abinda ke faruwa akan Idon mummy da Gwaggo ne da sauran dubban al'umma waɗan da suka kalla live a TV ciki harda abokan takarar daddy. Mai makarantar ne ya amsa mike ɗin cikin girmamawa yace "ku tafa masa" gaba ɗaya Hall ɗin ya dauki tafi raf, raf, raf, na kusan tsawon minti biyu, san nan mai makarantar ya yi Godiya ya gabatar da speech akan makarantar ya gabatar da Malaman makaranta gaba ɗaya sannan daga bisani ya nemi daddy da ya bama students gifts nasu da award nasu. Amsa masa daddy ya yi. makarantar ya fara kiran students ɗaya bayan ɗaya suna zuwa amsar gift nasu da award nasu, da aka zo kan Rimsha Ita kaɗai Awards Guda huɗu taci Best in Islamic Studies, best in English, Best in Mathematics, se best in home economics. Sannan aka bata wani medal na The person with the Highest points. Daddy sabida murna seda ya mata hawaye a cikin bainar Jama'a, ta ƙara so gabansa ta share masa hawaye tace "Daddy In Sha Allah we'll keep making you proud" murmushi yayi yana kokarin tsaida hawayen sa, Jehan ta ƙara so wajen cikin harshen turanci tace "Daddy please stop crying" ta faɗi kaman zata yi kuka murmushi shi ne ya kubce masa ya haɗe su gaba ɗaya ya rungume yace "Am proud of you my daughters Allah ya yi wa rayuwar ku Albarka" gaba ɗaya Hall ɗin suka amsa da Amin Amin, shi bema san yayi maganar da ƙarfi ba har suka ji. Miƙewa yayi ya ciro check a aljihunsa wanda already ya rubuta tun a gida ya miƙama me makarantar yace "gashinan Sadaƙatul Jariya school fees ne na Mutane 500 complet har su gama makarantar nan, ku sanar da marasa ƙarfi da suke son ƴaƴan su suyi karatu basu da halin biya musu gashinan na biya" "Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar" Hall ɗin ya dau Kabbara, Mutuwar tsaya da ta zaune manya manyan masu kuɗi da sukazo taron domin ƴaƴan su suka yi, sun sha ruwan mamaki irin kyautan da daddy yake, baya jin kyashi ko kaɗan, shi kuwa daddy bai jira cewar kowa ba yace su Rimsha su ɗauki stuffs ɗin su su wuce gida, haka kuwa a kayi suka ɗauka suka nufi mota sai sauri daddy yake dan bai son jama'a su tsaida shi suce zasu yi hoto. Yana zuwa parking space ɗan sandan sa ya buɗe kusu mota suka shiga, da sauri ɗan sandan yaja motar suka bar school ɗin. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 *💞 TRIPLET'S💞 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *💞The beginning💞* *Episode 14* *KADUNA* *Unguwar sarki* Hajiya Umaiya na sume a tsaye, shi kuma Abba yana sume a kwance har sai da Lami ta dawo daga kasuwa, ta isko su a sume, ihu ta fasa tayi kan Hajiya tana kiran sunan ta, tana taɓa Hajiya, Hajiya ta zube kasa wanwar, kara tsorata Lami tayi ta nufi fridge ta ɗauko ruwa jikin ta sai kerma yake ta buɗe ruwan, tsabar kiɗimewa da tayi bata san lokacin da ta juyewa Hajiya ruwan gaba ɗaya a kan taba, Ihu Hajiya ta fasa mai razaba kwakwalwa tare da miƙewa zaune tana zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko, waige waige ta fara yi kamar mai neman wani abun, can idon ta ya sauka kan Abba dake sume cikin tsoro tace "Ke Lami me yasami Alhaji? Yaushe ya dawo?" Kara zaro ido waje Lami tayi murya na rawa tace "Nima a nan na dawo na same ku kuna sume" kara waro ido waje Hajiya tayi, tayi shiru tana kokarin tunano me ya faru, amma ta kasa tuna komai, jiki ba kwari ta yunkura tana son miƙewa, sai ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya mata nauyi sosai, dafe kan ta dake sara mata kamar zai fashe tayi da kyar ta iya miƙewa tana faɗin "Kawo min ruwa" da sauri Lami ta miƙe ta ɗauko wani ruwa a fridge ta dawo ta miƙewa Hajiya, ansan ruwan Hajiya tayi tare da duƙawa kusa da Abba ta tarfo ruwan a hannun ta ta shafa masa a face nashi, dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali, ya waro idon sa waje ya fara bin saman da kallo kafin ya sauko da idon sa kan face ɗin Hajiya, a hankali ya miƙe zaune yana kallon Hajiya "Alhaji yaushe ka dawo?" Hajiya ta tambaya tana zaro ido, shiru yayi yana bin ta da kallo, "Alhaji kayi magana mana" da kyar ya iya motsa bakin sa yace "Hajiya yaushe na dawo? Ba ina Abuja ba?" tashin sense shiru Hajiya tayi tana kokarin tunano yaushe Alhaji ya dawo, amma ina ta kasa tuna komai, shima Alhaji shiru yayi yana kokarin tunano yaushe ya dawo bayan shi dai yasan yana Abuja wajen meeting to ya akayi ya dawo gida Almost 30mins sunyi shiru suna tunani daga karshe suka hakura da kokarin tunano me ya faru da su, haka suka miƙe suka wuce sama ran su cike da tunani fal. Hayewa saman gadon Abba Hajiya tayi ta kwanta ta dafe kan ta dake tsananin sara mata kamar zai fashe, shi kuma Abba yaja kafar sa a hankali da kyar da kyar ya shiga toilet dan yin wanka, a ta kaice dai su Hajiya sun manta komai da ya faru sun manta da abun da ya faru da Hajiya Zainab. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *WASHINGTON DC* *LOT 33* *06:00am* Sanye yake da short mai ɗan girma zuwa gwiwar sa sky blue kyakkyawar cinyoyin nan nasa a waje ga kyawawan gashi dark brown kwance a cinyar nasa daga sama har zuwa idon sahu na kafar sa, jikin sa na sanye da farar riga mara nauyi mai karamin hannu, kyau iya kyau Tiger na da shi kyakkyawan Bature ne sosai sai iskanci kala kala, ba kalan da bai iya ba rashin kutunci ne cike fal a kan sa, A hankali yake takawa har ya haura sama gaba ɗaya, ya tura kofa ya shiga wani waje mai kama da ɗaki, sai dai gaba ɗaya wajen da glass a kayi shi, kasan wajen kuma kyakkyawar grass carpet ne a wajen launin kore, waje ne mai girman plot 1, an kawata wajen sosai ga luntsuma luntsumar kujerun hutawa san nan ga injunan motsa jiki kala kala a wajen, da gani kasan wajen training na su ne, ga in juna da mashuna kala kala masu kyau da tsadar gaske, wajen dai ba'a chewa komai sai dai masha Allah. A hankali Michael ya kariso cikin wajen, kusa da wani mashin na motsa hannun ya tsaya, yayin da wani matashi ke kwance a wajen yana ɗaga wasu kana kana nan karafuna. Kallon tsab Michael yayi wa matashin kafin yace "Good morning photo copy" Ajiye karafunan hannun sa guy ɗin yayi tare da miƙe wa zaune, subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangiji dayayi wayan nan halittu, guy nan kamannin sa ɗaya sak da Michael ba abun da ya raba su sai kwayar ido da gashin kai, Michael gashin kan sa dark brown ne, shi kuma guy nan gashin kan sa ya rina ta ya sanya mata color ta dawo light brown mai kama da golden, sai kuma kwayar ido Michael kwayar idon sa light brown ne shi kuma guy ɗin nan nashi idon light ash ne masu kyau, ban da ido da gashi komai nasu ɗaya ne. Kallon tsab guy ɗin yayi wa Michael kafin yace "how are you doing this morning?" "I'm going well" ya faɗa tare da wucewa ya nufi wajen motsa kafa, har ya kai wajen sai kuma ya juyo yana faɗin "James yaushe Romeo zai dawo?" Komawa James yayi ya kwanta ya ci-gaba da ɗaga karfen da yake yana faɗin "I don't know maybe this week" shiru Michael yayi ba tare da ya sake magana ba, shima James shiru yayi ba tare da ya sake magana ba suka ci gaba da motsa jikin da suke. 07:00am dankareriyar gold watch dake ɗaure a hannun su tayi kara lokacin guda alamar awa ɗaya ta karu a kan lokaci, kallon juna suka yi, kusan a tare suka ajiye karafunan hannun su, kowa ya sanya hannu yana kokarin kashe karar watch ɗin, dankareriyar gold watch ne mai bala'i kyau da tsada iri ɗaya ba abun da ya raba watch ɗin, ko ina zasu je watch ɗin na hannun su basa rabuwa da shi sai dai in zasu yi barci ko zasu yi wanka shi ne suke cirewa, Tsai da karar watch ɗin sukayi a tare, dai dai lokacin jibga jibgan Bodyguard na su guda huɗu suka shigo wajen hannun su ɗauke da plate masu ɗauke da cup na ruwan lemon wadda masu motsa jiki ya kamata su sha idan sun kammala motsa jikin nasu, Rabuwa bodyguard ɗin suka yi, biyu suka nufi wajen Michael biyu kuma suka nufi James, cikin girmamawa suka miƙa musu plate ɗin, ba musu kowan nen su yasa hannu ya ɗauki cup ɗin suka kafa a ɗan karamin bakin su. Cikin ƙan ƙanin lokaci suka shanye lemon ɗin tas, tare da mai da cups ɗin saman plate dake hannun bodyguard ɗin, daman ka idar motsa jikin kenan shan 1 cup na lemon idan an kammala. Bayan bodyguard ɗin sun fice ne Michel ya kalli James yace "Photo copy zan je na shirya na wuce school yanzu" ba tare da James ya kalle sa ba yace "Ba za dai ka dai na ce min photo copy ba ko?" Miƙewa Michael yayi yana faɗin "To ai kai photo copy ne da gaske dama aikin sojan kawai kai ma ka shiga da ya fima yawon ban zan da kake ɗin nan kullun gaka wajen partyn abokai, ka gama school kana zaune" shiru James yayi ba tare da ya sake magana ba, sai mamaki yake wai Michael ne yake ce masa mai yawon banza to ba gwara shi ba ya samu ya kammala school ɗin, aiki ne dai kawai bai fara ba kuma baya ra'ayi yin koma ne hutu kawai yake sonyi a gida shi kuma fa, wuce wa Michael yayi ya fice daga wajen ya nufi bedroom na shi. A hankali shi ma James ɗin ya miƙe ya wuce nashi bedroom ɗin dan yaje yayi wanka. After some hours. James ya fito sanye da wandon jeans baki da t-shirt navy blue masu bala'i kyau da tsada sai kamshi yake zubawa, kai tsaye parking space ya nufa, yaje ya shiga motar sa kirar *Bugatti centodieci* ya tayar ko da yazo fita parking space ɗin sai da wan nan na'uran ta faɗi sunan motar da number ta da kuma sunan wanda ya ke cikin motar, san nan gate ɗin parking space ɗin ta buɗe, James ya danna hanchin motar waje. Yana fita ya saki kiɗa mai tashin kai yana kaɗa kan sa yana tuƙi cikin kwanciyar hankali. Kai tsaye *medina Hotel* ya wuce, horn ɗaya yayi a bakin gate ɗin masu gadi wajen suka buɗe masa, ya kutsa hancin motar sa a ciki ya nufi parking space, yana kashe motar ba tare da ɓata lokaci ba ya fito tare da sanya fake face a face na shi dan kar kowa ya gane sa san nan ya shige cikin katafaren hotel ɗin. Manya manyan Alhazawan kasar ne a wajen sunyi cincirindo shi kaɗai a ke jira daya iso gaba ɗaya sun zauna saman luntsuma luntsumar sofan dake cikin ɗakin hotel ɗin, cikin taku irin na jaruman maza ya kariso wajen, ya kara ɗaure fuakar nan tasa tamau, zama yayi gefen wani jibgegen Bature wadda da ka gansa kaga wadda Naira ta zauna ma sosai, ba tare da ɓata lokaci ba suka fara tattaunawa. Almost 40 mins suna tattaunawa nawa kafin daga bisani wan nan jibgegen Baturen ya jawo trolley dake gefen sa ya buɗe zip ɗin ya fito da wasu pistol gun ya fara rabawa mutanen dake wajen, ko wan nan su yana amsa yayi godiya amma da a kazo kan James sai yaki ansa, kallon sa Baturen yayi tun kafin yayi magana James yayi saurin cewa "Ba zai yiwu na shiga gidan mu da gun nan ba, idan nace zan shiga da ita tofa sai an kama ni dan gidan mu na da tsaro sosai" jinjina kai Baturen yayi kafin ya mai da gun ɗin cikin a kwanakin ya ajiye yana tunanin wai ma James ɗan waye ne dan bai san asalin wanene James ba kawai harkalla ta haɗa su, Cike da tunani fal ransa ya fito musu da wani abu kamar daskararren jini ne a ka yayyan ka, ko wan nan su ya amsa da fara'a amma ban da James shi fuska a ɗaure ya amsa, kallon su Baturen yayi san nan ya basu umarnin a kan su cinye abun, ba musu suka sanya a bakin su suka cinye, shiru ogan nasu yayi na yan mintoci kafin yace zasu iya tafiya sai a zama na gaba kuma, da sauri James ya miƙe kamar mara gaskiya ya bar wajen ya nufi motar sa ya shiga ya bar hotel ɗin da gudun gaske. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *ABUJA* Zaune Rimsha take saman sofa mai zaman mutun 2 a palon kasa tayi shiru ta kura idon ta a kan makekiyar Tv dake kunne ana labarai a kan wan nan Baturen, da sallama daddy da mum suka shigo Palon sai murmushi suke kai da ganin su kasan suna cikin farin ciki da annashuwa. My siha a na kallon labarai a kan TGA ne?" Cewar daddy yayi maganar tare da zama kusa da ita, a hankali ta kwanto jikin sa tare da ɗago dara daran sleeping eyes nata cikin shagwaɓa tace "Daddy yau ba TGA nake kallo ba na asalin nake kallo GAR shi ne asalin General of the army R ɗin kuma ban san ma'anar ta ba" shafa kan ta yayi yana murmushi, zama mum tayi gefen ta tana faɗin "Ni Rimsha wlh bana gane wa mutanen nan naki yau kiga wan nan gobe wan nan to shi kuma GAR ɗin waye shi?" Miƙewa tayi zaune daga jikin daddy cikin sauri tace "Mum GAR shine asalin jarumi na ai shima TGA ɗin yana burgeni amma ba kamar GAR ba" jinjina kai mum tayi tace "Ni kam Rimsha ba abun da na gane game da wan nan bayanin naki kyale ni kawai muje a kina san kallon TGA" komawa Rimsha tayi ta kwanta jikin daddy tana faɗin "Nima mum ba wani gane wa nake ba suna rikita min kwakwalwa sai yau na lura da mai light blue eyes ɗin nan da mai light ash eyes ɗin ashe ba mutun ɗaya bane na gano gakan ne ta sunan su, mu kullun bamu duba suna kawai idan mun ga hoton shi kenan ban taɓa tunanin GAR su biyu bane sai yau sun caza min kai, mai light ash ɗin idon nan shi ne TGA mai light blue idon kuma shi ne GAR wato General of the army kenan kuma shi ne jarumi na, ban taɓa luraba sai yau, suna kama over idon su ne kawai ya ban ban ta su" shi dai daddy shiru yayi yana jin ta amma ba wai dan ya fahimci kan zancen nata ba, dan shi ba wani zama yake yana kallon labaran Usa Army's ɗin nan ba, ita dai mum amsa mata kawai tayi amma ba wai dan ta gane kan zancen nata ba, shiru gaba ɗayan su suka yi suka zubawa Tv ido suna taya Rimsha kallo, while ita kuma Jehan tana ɗaki tana zubawa Gwaggo shagwaɓa da iya shege. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *KADUNA* Abba da Hajiya Umaiya sun manta komai da ya faru da su da rana a cikin gidan, sosai abokan Abba ke kiran sa a waya suna tambayar sa Alhaji Mustapha sai dai yace musu tun da ya dawo basu haɗu ba domin kuwa tabbas babu abun da Abba da Hajiya suka iya tunawa, shi Abba ma ya kasa tuna lokacin ma daya kamo hanyar Kaduna shi iya sanin sa yana Abuja bai san ya akayi ya dawo ba. Kamar kullun bayan sun gama cin abincin dare suka wuce bedroom na Abba dan su kwata, da kyar Hajiya ta iya samu tayi wanka saboda kasala da take ji jikin ta duk zafi yake mata kamar wadda a kawa mugun duka, a ɓangaren Abba shima hakan ne gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, haka dai suka lallaɓa suka yi wanka tare da shirin barci suka kwanta. Cikin dare sai juyi suke dukkan su sun kasa barci, dafe ciki Hajiya tayi kamar zata yi kuka tace "Abban Imran yinwa nake ji sosai kamar zan mutu" da mamaki ya miƙe ya kunna lamp na gefe da gefen gadon, abun ya ɗaure masa kai cikin kasalalliyar murya yace "Hajiya yinwa kuma?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh, yasha ruwan mamaki sosai dan basu taɓa jin yinwan dare haka ba A hankali ya koma ya kwanta yana faɗin "Muna da sauran takeaway a palo ai kije kici ni zan sha Yoghurt dan nima yinwa nake ji kuma banson cin abinci da tsohon daren nan, idan kin gama cin abincin naki ki tahomin da L&Z Yoghurt mai sanyi guda ɗaya" to kawai Hajiya tace tare da sauƙo wa daga gadon ta nufi Palo. Ko da ta shigo palo wutar palon a kashe, kai tsaye ta wuce wajen switch ta kunna wutar palon nan take haske ya gauraye ko ina a cikin Palon, Waro ido waje tayi kamar idon ta zai fito waje ya faɗi kasa, nan idon ta ya mata arba da tashin hankali da kwakwalwa ba zai ɗauka ba, jibga jibgan mutane su uku ne zaune saman sofa jikin su duk jini idon nan nasu launin jini ga fuskokin su bakake kirin abun tsoro, wata yar kyakyawan matashiyar yarinya ce zaune a tsakiyar palon ta na fukantar kofar palon ta bawa Hajiya baya, ta dukar da kai kasa kamar tana cin wani abun, cike da ruɗu da tashin hankali murya na rawa Hajiya tace "A..Ab..Abla" cikin sauri yarinyar ta ɗago tare da wayan nan dodan nin dake zaune saman sofa, tabbas Abla ce ke zaune tana cin namar mutane ɗanye idon Hajiya ya gane mata, kai kallon ta hajiya tayi kan abun da Abla ke ci, razanannen ihu Hajiya ta fasa ganin namar jikin mutun Abla ke ci, sai lokacin Hajiya ta iya tuna abun da ya faru ɗazun, dan kuwa naman Jikin Zainab Abla ke ci, Hajiya na kokarin guduwa ta koma sama idon ta ya sauka kan wasu dodan nin dake zaune saman kujerun table suna cin ɗanyen nama ga face nasu abun tsoro idon nan nasu kamar zai fito waje, ga launin idon jawur kamar jini suna da katon hanci Kamar kofa ga girman baki kamar masai ga idon na su ma manya manya masu firgitar da ɗan adam, ihu Hajiya ta kuma fasawa kamar makoshin ta zai fashe amma ina gaba ɗaya gidan ba wan da ya kawo mata ɗauki, a guje ta juya kamar zata mutu ta koma bedroom nasu. Tana shiga tayi arba da wani tashin hankali, dan kuwa wayan nan dodan nin ta gani suna tsere da Abba sun hana shi fita, shima sai ihu yake amma ba'a iya jiyo sautin ihun nashi, ga dai bakin sa na ihu amma ba wanda ke jin komai, tsabar tsorata Hajiya yanke jiki tayi a wajen ta sume. Shi kuma Alhaji ya daɗe yana tsere da wayan nan sheɗanun dodan nin gashi sai zane sa suke da wasu zabga zabgan bulalu a bayan sa, duk ta in da ya gudu sai yaji sun zabga masa wan nan bulala mai baki biyu dake hannun su a tsakiyar bayan sa, sai ihu yake amma ba mai iya ji. Gaba ɗaya gidan sai rugugi yake kamar tashin sautin gangan sheɗanu amma ba mai iya jiyo rugugin sai Abba shi kaɗan dan Hajiya kam ta jima da sumewa Tun Abba na iya gudun cetan ransa har ya kasa ya zube a kasa a bakin toilet ya sume a wajen, yana suma komai ya tsaya chak dodannin suka ɓace, amma kafin su ɓace sai da suka zanawa Hajiya wani karfe a bayan ta suka fasa mata baya, sai jini ke malala, san nan suka ɓace. Tashin sense ba'a sa maka rana wai meke faruwa gidan Abba ne? Muje zuwa yanzu wasan zai fara. Abba da Hajiya dai a wan nan daran a haka suka kwana, abun mamaki kuma ko da suka tashi da safe sun manta komai sun kasa tuna komai sai mamakin ciwukan da sukaji a jikin su suke, sai tambayar junan su suke wan nan ciwon fa, dukkan su ba mai bawa ɗan uwan sa amsa dan basu da amsan sun manta komai basu iya tuna komai. Da kyar Abba ya iya miƙewa ya ɗauki wayar sa ya kira doctor sa dan yazo ya duba su. Baa ɗauki lokacin sosai ba sai ga dr yazo, koda dr ya duba su sai yace shi bai ga komai ba, mamaki ne ya kara bayyana a face nasu Abba da kan sa ya sanya hannu dai dai sai tin in da dodannin nan suka zanawa Hajiya karfen nan yake ta jini, yasa hannu a wajen yana nunawa Dr, amma dr yace shi bai ga komai a wajen ba, clean yake kallon wajen, sun shiga ruɗani sosai daga su har dr, domin kuwa shi dai Abba shi da Hajiya ga ciwo na nan suna gani a jikin su amma a ce musu ba ciwo, ga jinin su nan sai zuba yake dr yace musu bai ga komai ba, shi Abba ma a face nashi ciwon yafi yawa duk dodannin nan sun zazzane masa face nashi da wan nan zabga zabgan bulalu nasu sai jini fuskar keyi amma shi dr baya ganin komai very smooth yake ganin face ɗin Abba, tashin hankali ba'a sa maka date Abba da ya ga dr ya dage a kan shi bai ga komai ba sai ya fara tunanin to ko dai dr ya samu taɓin hankali ne, dan haka sai ya sallame sa, ya ɗauki waya ya kira driver sa a kan yazo ya kai su hospital, nan driver ke sanar masa ai yana Abuja a hotel ɗin da suka sauƙa tun jiya yake jiran sa bai gan shi ba ya kira layin sa bata shiga, zaro ido waje Abba yayi tare da dafe kan sa yana kokarin ko zai tuna wani abu da ya faru, yaushe ya dawo Kaduna meke faruwa da shi ne, sai jerawa kan sa tambayoyin da bashi da amsan su yake, hakan yasa ya gane ba dr ke da matsala ba shi ne ke da matsala ita dai Hajiya ta kasa magana tana kwance shiru sai hawaye da take saboda azaban zafin da bayan ta ke mata in da dodannin nan suka yanke ta, gashi kuma dr yace bai ga komai ba alhalin ga ciwo nan karara kwance a bayan ta yana mata raɗaɗin azaba san nan ga jinin ta sai zuba yake amma dr yace bai gani ba kuma har ma da jinin dake zuba dukka bai gani ba wan nan wani irin masifa ne? Haka ita ma ta rinƙa jerowa kan ta tambayoyin da bata da amsar su, tana yi tana hawaye. Wunin ranar dai haka suka wuni cikin tashin hankali da damuwa, Abba ya kira likitoci daban daban amma duk wanda yazo sai yace bai ga komai ba, tun abun na basu mamaki har suka dai na mamaki suka rungumi kaddara suka lallaɓa suka taimakawa junan su wajen yiwa kan su dressing na wajen, sunayi suna hawaye dukkan su. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *After some day's* su Akila kowa ya koma gida sun gama yiwa daddyn jelly hutu, kafin su koma ba yadda su Imran basu yi da daddy ba a kan ya faɗa musu damuwar da amma yaki sai yace musu ba komai, da suka matsa masa da tambaya sai ya ɓata rai ya ɗaure fuska cikin umarni yace karsu sake tambayar sa, haka suka hakura ba dan su rinƙa so ba. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *KADUNA* Irfan yasha ruwan mamaki ganin yadda aka gyara masu gidan su ga kuɗin da Abbi ya samu, san nan ga karatun master's degree nashi da zai je yayi a uk wow abun ya masa daɗi over har azumi godiya ga Allah sai da yayi, su Aafia kuma an samu babban waya ga babban makaranta nan rashin mutunci ya karu dozin dozin, ita kam Umaisha wayan ta biyu ga wan da Akil ya saya mata san nan ga wadda a ka kawo mata, murna awajen su ba'a magana cikin kurna Aafia ta kira Kawar ta Rufaidat da suka gama secondary tare, ta sanar da ita abubuwan da suka samu na alkhari, sosai a fili Rufaidat ta nu mata farincikin ta san nan ta dora mata da cewa tana taya ta murnan samun babban makaranta, suma Allah yasa su samu mai dafa masu, da murna Aafia tace In Sha Allah zata faɗa wa Abbin ta zai taimaka musu, sai godiya Rufaidat ke yi sukayi sallama dukkan kawayen ta da sukayi secondary sai da ta kira ta sanar musu da abun alkharin da ya same su, sosai suka rinƙa taya ta murna, ita kam Umaisha daman bata da kawaye. Wan nan kenan *WASHINGTON DC* zaune Michael yake a *Harvard community garden* ga lucky Copper Winston a gefen sa, kan sa na kan wayar sa yana latsawa, su John suka iso wajen suka same sa, zama suka yi gefen sa Test na faɗin "I'm feeling hungry bro's" ya faɗa yana kallon Michael dake faman latsa waya, John ne yace "Okey kuje super restaurant mana kuyo oder sai a kawo muku nan" satar kallon Michael Dest yayi hakan yasa John ya gane me suke nufi, basu da kuɗi kenan, kallon Michael ɗin John yayi kafin yasa hannun a aljihun sa ya fito da kuɗi yana kokarin basu kenan wasu turawa su biyu suka iso wajen, ganin yan matan yasa su John juyowa a sukwane suna kallon Michael da kwata kwata hankalin sa baya kan su, cikin sauri Dest yace da yan matan "Kuzo muje" yayi maganar a tsorace dan bai san hukuncin da Michael zai masa ba idan ya ga yan matan a wajen, tsawa ɗayar yarinyar ta daka masa tana faɗin "babu in da zanje har sai ka bani kuɗin zubar da cikin nan" tashin sense jin muryan mace yasa Michael ɗagowa da sauri yana kallon su, ihu Dest ya fasa yana ja da baya, ba Dest kawai ba har John sai da ya ja baya, nan take idon Michael ta canja launi zuwa ja cikin tsawa yace da yarinyar "leave this place before I open my eyes!!" Kallon sama da kasa tayi wa Michael kafin tace cikin faɗa "Kai ba da kai nake ba tukun nan kuma idan kaga na bar nan to na samu abun da nake so ne" girgiza kai kawai John yayi yana yiwa yarinyar addu'ar Allah ya ceceta, shi kuwa Michael a fusace yace da Copper "give her a good punishment" zaro ido waje Dest da Test suka yi, shi kuwa John godiya ma yayi ga Allah dan Michael bai bata horo sosai ba, yayi mamaki sosai, dan kamar yadda su Michael su ka tsani Mum ɗin su haka suka tsani duk wata mace a duniya shi yasa duk masu aikin gidan su sojoji ne kuma maza, mace bata zuwa ko in da inuwar su take dan suna ganin dukka mata irin ɗaya suke da mum ɗin su, hakan yasa duk wata macen da tayi gigin zuwa in da suke to kuwa ta shiga uku, sun tsani mata over kuma duk mum tasu ce silar komai. Dirowa kasa Copper yayi tare da girgiza jikin sa, yana miƙa, durkusawa kasa Dest yayi ya riƙe kafafun Michael yana faɗin "Please Michael forgive my wife bata san kai wanene bane shiyasa kaga ba'a School nan take ba, bata san ka ba da bazata zo kusa da kai ba please she's pregnant kuma ina bala'i son cikin nata sosai" shiru Michael yayi kamar bai san da mutun a wajen ba, shi kuwa Copper tun da ya riga ya ansa umarni sai ya daka haushi mai razanar da kwakwalwa wadda yasa matan fasa ihu suka watsa a guje, kamar jira Copper yake yabi bayan su, yana gudu yana girgiza jikin sa, kuka sosai Dest ya fara ya ci-gaba da rokan Michael a kan ya dakatar da Copper kar cikin jikin matar sa ya zube, shi kuwa John da gudu yabi bayan su Copper duk da yasan ba zai iya dakatar da Copper ɗin ba, dan ba wanda ya isa ya dakatar da shi sai Michael ɗin da ya haɗa su da shi, shima Test duƙawa yayi suka haɗu suna rokan Michael dake zaune yana latsa wayar sa hankalin sa kwance. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *💞The beginning💞* *Episode 15* _____gudu sosai yan matan suke kamar zasu yi hauka suna kurma ihu, shi kuma Copper yana biye da su, haka suka bazama cikin school ɗin basu san in da suka nufa bama. Suna gudu suna waigowa su kalla ko Copper ya kusa kamo su, matar Dest bata an karaba ta juya tana kallon Copper sai ji tayi ta bugu da mutun, baya baya tayi ta faɗi kasa, tare da fasa ihu, ba shiri ɗayar yarinyar ta ja birki da gudun da take ta waigo dan ganin ko dai Copper ne ya kama matar Dest ɗin yasa take ihu, a guje Copper yayi kan ta da niyar cizon ta, a guje ta miƙe dan ta gudu bata lura da mutumin da tayi karo da shi ɗa zun ɗin ba, still yana tsaye a wajen tana kallon su, tana kokarin gudu ta sake yin karo da shi tayi baya zata faɗi, da sauri yasa hannu ya riƙo hannun ta tare da janta tayi ta bayan sa, daka sufa Copper yayi yayi kansu, a fusace James ya kai masa bugu a kai sai da yayi baya ya faɗi kasa, a sukwane ya miƙe tare da daka haushi mai karfi yayi kan James ɗin yana buɗe baki kamar mayin wacin zaki, duƙawa kasa James yayi ya damko makogoran Copper ɗin tare da zaro manya manyan light ash eyes ɗin sa, cikin tsawa yace "put your eyes into my own!!" Ganin James ne yasa Copper daka haushi mai tashin kai kana ya dukar da kan sa kasa, sakin makogoran nasa James yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsawa yace da Copper "Muje in da ka fito" juyawa Copper yayi ya wuce ya mufi *community garden* ba tare da James ya yiwa su matar Dest magana ba ya wuce yabi bayan Copper, cikin sauri suma su matar Dest ɗin suka bi bayan sa. Michael na zaune sai rokan sa Dest da Test suke amma bai kula su ba, da suka dame sa sai ya miƙe a fusace ya fara jibgan Dest kamar an aiko sa, fuskar nan tasa kamar hadari, gaba ɗaya student dake wajen sun tsorata dan basu taɓa ganin Michael ya daki Dest ba, yanzu tsawon shekara 5 kenan suna tare basu taɓa ganin wani abu makamancin haka a tsakanin su ba. Dest kuwa ganin Michael zai iya yi masa illa ne yasa ya miƙe da gudu ya nufi hanyar fita daga community garden ɗin, da sauri Michael ya damko kafar sa ya jawo sa, ya sanya kafa ya take masa wuya ga kafar nasa sanye suke cikin Booth na yan kwallo masu karfin nan, haka ya takewa Dest wuya ya zaro belt ɗin wandon sa ya fara zabgawa Dest ta ko ina a jikin sa, sai zaro ido waje Dest yake dan numfashin sa na gab da ɗauke wa baya mumfashi da kyau saboda take masa wuya da Michael yayi, da gudu Test yazo ya duƙa ya riƙe kafar Michael ɗin yana kuka yana bashi hakuri karya kashe masa ɗan uwa, ina Michael yayi nisa baya jin Test, kawai saukewa Dest belt nashi yake ta ko ina a jiki kamar wani zararre ga belt ɗin na shin da tauri sosai, duk ya fashewa Dest jiki, duk da hakan kuma bai kyalesa ba gashi kuma ya take masa wuya gaba ɗaya student dake wajen sun tsorata sosai sun san halin Michael da zuciya amma basu taɓa ganin sa cikin ɓacin rai har haka ba, su kansu Lucky da Winston sai haushi suke suna goga kan su a jikin Michael ɗin kamar suna dannan sa yayi hakuri. A wan nan halin James ya iso ya same su, cikin nitsuwa ta baya ya anshe belt ɗin da Michael ke zane Dest da shi, a fusace Michael ya juyo dan ganin wani isasshene ya anshe belt, yana juyowa karaf idon sa ya sauka kan James dake tsaye fuskar sa babu alamar wasa ko kaɗan, ganin haka yasa Michael cire kafar sa daga wuyar Dest ya koma saman sofa ya zauna yana huci kamar wani zaki, kallon jama'ar dake wajen James yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Micheal "John Take him to *(HUHS) Harvard University Health Services*" yayi maganar tare da muna Dest dake ta kokarin bawa kan shi mumfashi, ma'ana yana kokarin jawo mumfashi sa ya saitata, da sauri John da Test suka ɗauki Dest ɗin suka wuce da shi HUHS, da sauri matar Dest da kawar ta suka bi bayan su kallon tsab James ya yiwa Michael kafin yace "did he offend you?" Shiru Michael yayi sai huci yake kamar mayin wacin zaki "am I not talking to you?" James ya sake jefo masa tambaya, yayi maganar yana karasowa wajen sa, cikin fushi da tsawa Micheal yace "Why zai kawo min wancan banzan abun na shi a nan?" "Which Abu?" James ya tambaya da mamaki a face na shi "Matar sa mana" Michael ya bashi amsa, girgiza kai James yayi kafin yace "Wajen ka matar tazo?" Miƙe wa tsaye Michael yayi cikin fushi ya fara magana "Ba waje na tazo ba kuma bata isa tazo waje na ba amma ai yasan bana son hakan, bana son wayan nan azzaluman su raɓeni" zuba masa ido James yayi har sai da ya kai karshen maganar tasa san nan yace "Why kake haɗe mata dukka kace basu da kirki This is not good, ya kamata ka sani mummy daban suma sauran daban kamar dai yadda muke ɗin nan", gigitatchiyar tsawa Micheal ya daga masa a fusace yace "Stop James, stop talking about that human hare, she's not my mother at all, i came this world true my dad only, i hate that human i hate her more than your expectations, i don't have any mother in my life!!!" Kasa da murya James yayi cikin muryan rarrashi ya fara magana "I knew it Michael, i know you hate mum and I, and i hate her because she had done bad thing to us, but this is not the reason, da zaka ce you hate all ladies in this world" dogon tsaki Michael yaja tare da komawa ya zauna yana faɗin "I hate all ladies I don't want to see tham close to me" shiru James ya ɗan yi kafin yace "Okey I agreed, know let's go back home i want to see you there, I want us to be discuss something" yayi maganar cikin sanyin murya Tsaki Michael yaja kafin ya miƙe ya fice daga wajen rai a matuƙar ɓace, bayan sa James yabi yana mai matukar jin tsanar mum na su a ransa na karuwa. Da sauri Copper Winston Lucky suka bi bayan su, sai mamaki student dake wajen suke Kowa motar sa ya shige, kamar yadda suka saba haka lucky ya shiga gidan gaba Copper da Winston suka shiga gidan baya na motar Micheal, James na tsaye sai da yaga motar Micheal ta miƙi shinfiɗaɗiyar titin fita daga School ɗin san nan, shi ma ya tada motar sa yabi bayan Michael ɗin. ________________________________ *KADUNA* Unguwar Malali Kwance Umaisha take saman gadon su dake bedroom na su, tayi nisa cikin tunanin a kan Akil, while ita kuma Aafia tana ta fama da shirya kayan ta cikin drawer sanya kayan su, wayar Umaisha dake gefen ta ya fara kara alamar shigowar kira, sai da gaban ta ya bada dukan uku uku, tun ma bata ga mai kiran na taba, cikin sauri jikin ta har kerma yake ta ɗauko wayar, My pleasure shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin, mamaki ne ya kamata wato shi Akil har suna ya zaɓawa kansa yayi saving number sa da shi, dan tana da tabbacin shine duk da bai taɓa kiran taba sai yau ɗin, ta san shi ɗin ne dan bayan shi bawan da ya taɓa mata waya, ko Aafia taki ɗaukar wayar dan tsoron Akil ɗin, My pleasure ta mai mai ta sunan, cike da fargaba ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunnen ta, cikin sanyi murya tace "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Waalaikumussalam" "In wuni yaya Akil" tayi maganar cikin girmamawa "Me ya same ki?" Ya tambaya da ɗan tsawa, murya na kerma tace "Babu komai" "zaki faɗa min me ya same ki ne kosai na tashi na ɗauki mota nazo na same ki" kallon time tayi 11 na dare kuma ta san halin sa zai aikata, hakan yasa tace "Kayi hakuri zan faɗa maka" shiru yayi yana sauraron ta "Daman a kan School ne naji kace kar na sake fita ko ina kuma wlh ina bala'i son nayi karatu" ta kai karshen maganar kamar za tayi kuka "Ni kin ji nace kar kiyi karatu ne?" Cikin sauri ta girgiza kai kamar tana gaban sa, "A'a yaya Akil" "Kin iya mota?" da sauri tace "A'a ban iya ba" "Wan can dirty brother ɗin naki fa ya iya ne?" Gyaɗa masa kai tayi kamar a gaban sa tana faɗin "Eh ya iya" "Good zan sanya a kawo muku mota guda biyu ke ɗaya sister ki ɗaya sai ya koya muku ko?" Kasa ta kara yi da murya a nitse cikin fargabar abun da zai je yazo tace "Yaya Akil ka bar shi mun gode" wani gigitatchiyar tsawa ya daka mata wadda ya sa har wayar hannun ta ya kusa faɗuwa "Ke har kin isa in ce abu kuma kice na bari? To gobe da safe ina zuwa gidan, kai yanzu ma gani nan zuwa sai ki kalli cikin ido na ki faɗa min ko?" Kallon Aafia dake tsaye ta Zuba mata ido Umaisha tayi, kamar zata yi kuka tace "I'm sorry yaya Akil ba zan sake ba, sai ka kawo motar muna godiya Allah ya kara arziki" dogon tsaki yaja tare da kashe kiran sa, ajiye wayar Umaisha tayi tare da sakin kuka mai tsuma rai, haurowa saman gadon Aafia tayi tana faɗin "Ya isa haka Umaisha kiyi shiru" rungume Aafia tayi cikin kuka tace "Aunty Aafia wai shi kam wani irin mutun ne yaya Akil ɗin nan? Kullun cikin masifa da faɗa bashi da hakuri ga zafin rai" Aafia na kokarin magana wayar Umaisha ta kuma yin kara, a kule ta furta "Wai har da wani sawa number sa my pleasure, to yana sanin farincikin ne?" Ta kai karshen maganar tare da ɗaukan kiran ta kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Daman nasan kuka kike ai shi yasa na sake kira, bana hana ki kuka ba? Me yasa bakyaji ne? Tun yanzu kike yin abubuwan da na hana ki ko? Kina son ki ɓata min rai kenan ko?" Mamakin sa ne ya kara kama Umaisha wai shi wan nan wani irin mutun ne, ji yadda yake wani Magana kamar ba shi ya sanya ni kukan ba, "Ba dake nake magana bane?" Cikin sauri tace "Kayi hakuri" "Aikin ku kenan sai kun yiwa mutun abu ku rinƙa bashi hakuri kuna cutar sa, to dai ki shirya gobe za'a kawo muku motocin guda biyu discussion continue and continue continue, ki ɗauki karamin ki barwa sister ki babban ku rinƙa zuwa school, zuwa gaba zan canza muku motar kina jina?" Da sauri tace "Eh muna godiya sosai da sosai" "Idan kinje School babu ruwan ki da kowa, karatu kawai nace kije kiyi, idan kika kuskura nasami labarin kina kula wani ba sai nayi magana ba kin san me zai biyo baya, san nan ina son ki mai da hankalin ga karatun sosai dan ni ina son wayayyiyar mace wadda tayi karatu sosai Allah ya ba da Sa'a" yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar taba ya katse kiran Wurgi tayi da wayar gefen ta kamar zata yi kuka tace "Wai wan nan wace irinyar musifa ce" gyara zama Aafia tayi cikin nitsuwa ta fara magana "Umaisha kar ki ɓoye min ki faɗa min gaskiya kina son yaya Akil?" Ɗago ido Umaisha tayi tana kallon Aafia kafin tace "Eh ina son shi, amma bana son abubuwan da yake min, shi fa ba ruwan sa da wani soyayya umarni kawai ya iya bayarwa, sai shegen masifa da izzan na banza" dariya Aafia ta kwashe da shi har da riƙe ciki, a kule Umaisha tace "Me abun dariya kuma?" Cikin dariya Aafia tace "No wonder shi yasa mana kike bin umarnin nasa kuma kika nitsu ashe dan kina son shi ne, hhhhh lallai Umaisha nayi mamakin yadda kike masa biyayya kike biye masa ashe ashe, to zan baki shawara tun da har kina son shi so mai tsanani, dan wan nan so mai tsanani kike masa wadda yake sanya ki jure duk wani haukar da zai miki, to shawarar dai a nan shi ne a hankali ki rinƙa shi gar masa da kalaman soyayya a kan sa ki dai na zama shiru idan kuna waya ki rinƙa yi masa shagwaɓa In Sha Allah zai zo ya fara biye miki yana mayar miki da martani" shiru Umaisha ta ɗan yi kamar mai tunani Can kuma ta ɗauko wayar ta cikin hanzari tana faɗin "Bari na gwada wani abu mu gani ko zatayi aiki" zuba mata ido Aafia tayi tana kallon ta, layin Akil ta kira, amma bai ɗauka ba sai ya katse kiran nata ya kirata, yana kira ta ɗauka cikin zumuɗi tare da shagwaɓe murya tace "Hello" "Lafiya kika sake kirana?" Ya jefo mata tambaya still dai da wan nan voice na shi mai kamar faɗan, kara shagwaɓe murya tayi kamar wata yar baby tace "Kai yaya Akil to na kira ne naji muryan ka, naji ina kewar kane" da sauri yace "Ke me kuma ya samu voice naki ban fa son munafurci ki ware murya ki min magana hai" zaro ido waje tayi tana kallon Aafia da ta zuba mata ido tana jiran taji ko zasu yi nasara ta ɓangaren shagwaɓa, tunani Umaisha ta shiga yi "wai shi yaya Akil shagwaɓar ma bai sani bane shi dai ko mai da karfi karfi ya sani innalillahi wa inna ilaihir rajiun" tayi nisa cikin tunani ya daka mata tsawa "Ke zaki faɗa min me yasa kika kirani ne ko kuma na kashe waya ta dan ina da abun yi!!" Haɗe rai tayi ciki ciki tace "Sai da safe" bai jira ta karisa ba yace "Idan kika sake kirana babu wani dalili sai ran ki ya ɓaci, dan ba aikin ki nake ba, da zaki rinƙa kirana babu dali kina ɓatamin lokaci bayan ina da abun yi!!" Ya kai karshen maganar tare da katse kiran, ɗaura wayar tayi saman bedside drawer ta kwanta kamar zata yi kuka, tun da Aafia ta ga yanayin face nata tasan basu dace ba dan haka ba sai ta tambaye taba ta kwanta a gefen ta kawai, suka jawa kan su bargo suka lukkuɓu, ba jimawa barci ya ɗauki Aafia ita kuma Umaisha ta jima tana tunanin Akil kafin daga baya barci ya ɗauke ta, asuba ta gari. ________________________________ *KANO* Kamar dai kullun zaune Jelly take saman mirror chair daddy na gyara mata gashin kan ta, ya mata make up a fuskarta, ba laifi wan nan karon kam make up ɗin ya ɗan yi kyau, dan ya fara iya make up ɗin yanzu, sai murmushi take shi kuma daddy kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa da tashin hankali duk ya rame ya sauya kamar ba shi ba, ya shiga tunani da damuwa, abubuwa biyu sun haɗu masa waje guda, abu farko contract da ya samu dole baban Muneer yace ya ajiye, Abu na biyu kuma baban Muneer yace dole duk abun da yake so shi za'a gudanar a filman na daddy, ma'ana company daddy, sosai daddy ya shiga damuwa a kan hakan dan yasan shi kenan time na rushewar company sa yazo, tun jiya ya rubutawa gomnati takarda a kan ba yason contract ɗin nan amma har yau babu reply, yana kuka yana rubuta later, duk ya rame yayi duhu kamar ba shi ba, babban abun da yafi damun sa ya ja masa raman nan, shi ne zina da a ka sashi yayi, wa iya zubilla san nan kuma har da video a ka ɗauke sa jama'a suna girmama shi suna kallon sa da mutunci, Allah ya sani shi mutumin kirki ne bana banza ba, yanzu idan video nan ta fita yake nan, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wan nan tunanin yasa shi yake ramewa ya shiga damuwa over. "Daddy what are you thinking?" Jelly ta tambaya tana kallon hotuna a wayar sa dake hannun ta, kakalo murmushi dole yayi wadda yafi kuka ciwo yace "My Jelly ina tunanin kalar kitso da zan miki gobe ne" dariya tayi zata sake magana idon ta ya sauka kan hoton wani kyakkyawan puppy dog dake wayar daddy fari kal da shi, yar kara ta saki tare da furta "wow daddy I love this puppy dog please will you buy for me?" Kallo hoton daddy yayi kafin ya dawo da kallon sa kan face nata, sai zuba murmushi take hakwarar ta kamar gonar audiga saboda hasken su tas suke ganin murmushi da ke kan face nata yasa shi jin sassauci a ransa yaji sanyi a zuciyar sa cike da so da kauna yace "Yes I will my Jelly" juyowa tayi ta rungume sa tana dariya, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa kan ta, yana mai tausaya mata ya zata ji idan ta girma by mistake taji abun da baban ta ya aikata, Da tunani cike fal ran sa ya ɗauke ta cak suka wuce wajen drawer kayan su, ya ciro mata wasu riga da wandon jeans, sauri sauri ya shirya, tsab suka wuce palo, dan cin abinci. Already su Zuwaira sun gama shirya musu komai zama yayi ya ɗaura ta saman cinyar sa ya fara bata abincin a baki, tana ci tana wasa haka ya rinƙa biye mata har ta koshi san nan yaci na shi, sai da ya koshi san nan ya miƙe suka koma saman sofa ya jawo system nashi dake saman sofa table ya kunna musu suka fara buga game kamar yadda suka saba, shi dai buga game ɗin kawai yake ba wai dan hankalin sa na wajen ba, baya ma sanin me yake taɓa wa ba, kawai yana yi ne dan jelly taji daɗi tayi farin ciki, ita kuwa sai murmushi take abun ta. ________________________________ *KADUNA* Cikin dare yinwa mai tsananin gaske ne ya tada Hajiya daga barci, tayi kokarin ta danne yinwan tayi barci, amma ina abun ta ci tura dan yin wa sosai take ji fiye da tunanin mai tunani kamar zatayi kuka haka ta taso ta kunna wutar ɗakin, ba karamin tsorata tayi ba ganin Abba a zaune a tsakiyar gadon "Alhaji lafiya?" Tayi maganar murya na rawa, kamar zai yi kuka yace "Yinwa nake ji Hajiya" shiru Hajiya ta ɗan yi kafin tace "To muje palo muci abincin mana" kasan san cewar sun manta komai ne yasa basu damu ba suka jera a tare suka nufi palon. Ko da suka isa palon wutar a kunne babu komai shiru palon, kai tsaye table ɗin cin abincin suka nufa, suka zauna, sai bayan sun zauna suka lura da abincin dake saman table ɗin zaro ido waje sukayi suna kallon abincin, kayatattun girke girke ne masu bala'i kyau ga daddaɗar kamshin da abin cin ke dubawa, ga fruits kala kala an yayyanka su an jera a plate ga gasassun gaji sun ji kayan kamshi, wani abincin ma basu taɓa ganin irin sa ba, duk girman table ɗin nan sai da a ka shake sa tab da abinci na alatu masu kamshi da haɗuwa, har da gasassun pig (Alade) gasu ɓera da zomo duk an gashe su sai turirin zafi suke, Hajiya ce ta fara fasa ihu tana kokarin miƙewa, wayan nan dodannin suka bayyana a sauran kujerun table ɗin suka mai da Hajiya suka zaunar da ita, shi kam Abba daman ban yi yunkurin rashi bama Nan take Hajiya jikin ta ya fara kerma, ta rintse idon ta bata son haɗa ido da dodannin bata son kallon su, dan fuskokin su babban tashin hankali ne sai mai irin zuchiyar Sahabbai zai iya ganin su ma'ana sai mai karfin imani Kamar daga sama Abba da Hajiya suka ji an fara ɗura musu abincin a baki, a sukwane Hajiya ta wari idon ta, kai tsaye idon ta ya sauka kan mummunar hannun ɗaya daga cikin dodannin nan yana dunbutso shinkafa yana danna mata a baki, kallon hannun nasa tayi da kyau, bakin kirin kamar gawayi ga hannun duk datti sai bala'i wari yake ga hannun nasa da girma kamar samudawa Wage baki Hajiya tayi zata fasa ihu, kamar jira dodan yake, tana waje baki ya danna mata shinkafa a baki, wadda ya sata ba shiri ta haɗi saboda daya danna mata shinkafar ya toshe mata hanci, hakan yasa tayi saurin haɗiye abincin dan ta samu tayi mumfashi, yau ga ɗuren dole, haka dodannin nan suka rinƙa yiwa su Abba ɗuren abinci da wan nan mummunar hannun nasu kamar kwata. Da sauri Imran ya shigo palon daga Part nashi yana faɗin "Abba kune daman a palon? Sai jin motsin nake ina ɗaki shi ne nace bari nazo na duba" wage baki Hajiya tayi tana ihu dan Imran yaji ya taimake su amma ina Imran baya jiyo komai, shi ma Abba sai magana yake wa Imran amma Imran baya jin komai, sai ganin bakin su yake suna motsi "Abba lafiya kuke motsa baki kuma baku magana? Ko nazo ne" Imran ya faɗa da mamaki a face nashi, ya kai karshen maganar tare da kallon saman table ɗin, zaro ido waje yayi yana faɗin "Abba me nake gani hakan? Ya naga kamar ɗan yen nama da kwari kuke ci?" Ya kai karshen maganar tare da karasowa wajen, sai magana su Abba ke masa shi kuma baya jin komai ganin su Abba sun ƙi yi masa magana ne yasa ya sanya hannun sa yana kokarin cire hannayen su daga kan abincin da idon sa ke gane masa shi suke ci, dan shi ɗanyen nama da kwari da tsutsotsi yaga su Abba na ci, su kuma ganin abinci masu kyau suke a saman table ɗin. Tashin sense Da karfi Imran ya ja hannun Abba da niyar cirewa daga plate ɗin, kamar daga sama yaji saukan bulala a tsakiyar bayan sa, ihu ya fasa bai san lokacin da yace "bura uban nan kai uban waye ya dake Ni?" Bai gama rufe baƙi ba aka sake shinfiɗa masa wata bulalar a wuyar sa da karfi, razanannen kara ya saki, cikin fitar hayyaci yace "Bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah kulhuwalkahu ahad kulya ayuhal kafirun Alhamdulilahil laji an zala fi hil Quran" tsabar azaban bulalar ne yasa shi furta wayan nan kalamai, da bai san me bakin sa ke faɗe bama, Abba da Hajiya Suna kallon meke faruwa da Imran ɗin har wanda ke zane sa suna kallo amma ba halin magana, shi kuma Imran baya ganin komai sai saukar zabga zabgan bulalu kawai yake ji a jikin sa, sai ihu yake yana sambatu, amma duk gidan ba mai jin sa sai su Abba, Kewaye palon Imran ya farayi ya rasa gane kofar fita sai ihu yake su kuwa dodannin ba tausayi ba imani haka suka rinƙa shin fiɗa masa wan nan zabga zabgan bulalun nasu mai bala'i zafi a jiki, duk sun fashe masa jiki, duk in da yayi sai saukar bulala zai ji da kyar ya samu ya gane kofar fita a guje kamar wani zararre yayi waje yana gudu yana ihu ya ɗage jallabiya sama, yana wurga dogayen kafofin sa bai san ma in da ya nufa ba, kai tsaye sai toilet ɗin baba mai gadi ya shige, ya samu bayan kofa ya tsaya yana mai da numfashi tare da jan majina. Su kuwa dodannin yana fita suka kyalesa suka koma kan Abba da Hajiya, Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara....✍️ 💞TRIPLET'S💞 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 EPISODE 16 ________________________________ Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara zabga mata bulalun sai ihu take, sauran dodannin kuma suka damko Abba suka kwantar da shi kusa da Hajiya suka hau zabga musu bulalun, dai dai lokacin Akil ya shigo palon yana sauraron kira'ar sudais a wayar sa ya kure volume, shi ma yinwan dare ta tashe sa, jin kira'ar yasa dodannin ɓacewa ɓat, kamar kuma yadda suka ɓace haka suka ɓace da tunanin su Abba. Ganin su Abba kwance a tsakiyar palon ne yasa Akil karisowa wajen da sauri yana faɗin "Abba Ammie lafiya kuka kwanta a palo yau kuma?" Shiru sukayi basu amsa masa ba, mamaki ne ya kara kama shi yasa hannu yana taɓa su, yana kiran sunan su. Hajiya ce ta fara tashi a nitse kafin Abba ma ya tashi, "Abba me yasa kuka kwanta a Palo?" Akil ya jefo musu tambaya, kallon juna sukayi kafin su ɗaga ido suna kallon Palon, da mamaki har suna haɗa baki wajen cewa "Me ya kawo mu palo kuma?" Miƙewa Akil yayi tare da rage volume na kira'ar da yake ji ya nufi table yana faɗin "Kila barci kuka yi a wajen kuna hira" ya kai karshen maganar tare da zama saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin, ya fara bubbuɗe takeaway ɗin dake saman table ɗin, dan ya duba wani abunci ya dace yaci. Jiki ba kwari su Hajiya suka miƙe suka nufi bedroom nasu ransu cike da mamaki yaushe suka zo palo kuma, da kyar suke jan kafar su, har suka wuce Bedroom na su. Shi kuwa Akil abincin sa ya fara ci yana yatsine fuska After some minutes. Wayar sa ta fara kara, dogon tsaki yaja kafin ya ɗauki wayar ya kawo ta sai tin face nashi Abla shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin sake jan dogon tsaki yayi kafin ya ɗauki kiran ya sata a hand-free ya ɗaura saman table ɗin. Daga ɗayan ɓangaren cikin sanyin murya a kayi sallama, rai a ɓace Akil yace "Wai Abla baki ganin time ne da zaki kirani yanzu?" Murya kamar zata yi kuka tace "Kayi hakuri yaya Akil wallahi tun karfe 10 nake kiran yaya Imran yaki ɗaukan waya ta" "To naji me kike so yanzu kuma?" "Kuɗi nake so yaya Akil" guntun tsaki yaja kafin yace "Za'a turo" ya kai karshen maganar tare da katse kiran yana faɗin "Da daren nan zaki kira mutun kice masa wani kuɗi gari ba zai waye bane ku baku da aiki sai takurawa mutun, ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗau wayar sa ya fice daga palon ya koma part na su. _____________________________ *WASHINGTON DC* Motar Micheal na gaba motar James na bin sa a baya, har suka kai babban titin da zata sada su da unguwar su, wayar James ta fara kara, a hankali yayi parking na motar sa a gefen titi dan hakan yana daga cikin dokan Romeo ya hana su ɗaukan waya suna tuƙi. Sai da ya kashe motar san nan ya ɗauki wayar tare da picking call ɗin ya manna wayar a kunnen sa, Jim kaɗan ya cire wayar daga kunnen sa, sauri sauri ya tayar da motar tare da juya kan motar da wata mahaukaciyar gudu ya figi motar ya bar layin ya sauka daga titin ya canza hanya, yayin da shi kuma Michael ya ɗauki shinfiɗaɗiyar titin gida. Kai tsaye unguwar *Adams alley* ya wuce, ka ta faren unguwa ne mai cike da dogayen gine gine, na alfarma masu kayatarwa, kai tsaye wajen wani katon guest house ya nufa, tun bai kariso ba suka wangale masa gate ɗin gidan kamar daman sun san da zuwan sa, da gudun gaske ya kutsa hancin motar cikin gidan kamar mara gaskiya, yana shiga masu gadin suka mai da gate ɗin suka rufe, kai tsaye parking space ya wuce. Yana kashe motar ya fito ya shige cikin gidan da yar gudun sa. Still wan nan ogan nasu ne a wajen shi da wasu mutane, da alama wani abun mai muhimmanci suke tattaunawa, wucewa James yayi yaje ya zauna kusa da ogan nasu. Cikin harshen turanci ogan nasu ya fara magana "Lokacin yayi da zamuyi Oder makamai a China dan kayan aikin mu sun yi kasa, san nan karku manta Jams kai zaka ja ragamar sayo makaman kamar dai yadda muka saba, ina son mu kai hari mumbai mu tura wa gomnatin su gargaɗi ta hanyar boom, sai magana ta gaba, manyan mutane daga sama sun aiko mana da hoton wani matashin soja mai ji da karfin iko, a yanzu shi yake juya gomnati, suka ce mu kawar da shi dan babban barazane a gare su kasan cewar sa a raye, dan yana aiki da gaskiya kuma shi ci-gaba mutane yake so, mu kuma kun san bama son hakan, mun fi so muga talakawa cikin ukubar rayuwa, James na naɗa ka a kan wan nan aikin, kai zaka kashe sojan, dan nasan kai kaɗai zaka iya, zan tura maka hoton sa a WhatsApp sai kayi kokarin cika aikin, idan ka gama aikin kashe sojan ne sai ka jagoranci sayo makamai ɗin daga nan sai mu fara shirye shiryen meeting a kan cocaine da zamu shigo da su this year, sai muga container nawa ya kamata mu kawo kuma kasashe nawa ya kamata mu sayarwa" jinjina kai James yayi tare da miƙe wa tsaye yana faɗin "I'm leaving now, saboda ina da meeting da brother na a gida, kuma bana son su fahimci abun da nake suna jirana ne" gyaɗa kai ogan nasu yayi kafin yace "Okey see you next time" sauri sauri James ya fice daga wajen, dan kar Michael yaje gida yayi ta jiran har ya fara tunanin wani abu, motar sa yaje ya shiga ya ja da gudun gaske ya bar wajen. Yana cikin tafiya wayar sa ta ɗan yi yar kara alamar shigowar sako, sauke hannun sa ɗaya yayi daga kan staring ya ɗauki wayar yayin da ɗayan hannun nasa ke tuƙa motar, Ganin sakon ogan sune yasa cike da zumuɗi ya buɗe sakon dan yaga menene zai kashe, a sukwane ya taka wata irinyar mahaukaciyar birki wadda tasa sai da ya buga kan sa da jikin staring motar, waro light ash eyes ɗin sa waje yayi yana kallon wayar, a fili cikin tsawa yace "GAR zan kashe kai ina never" lokaci guda yaji kan sa na sara masa kamar zata fashe, jikin sa har tsuma yake saboda ɓacin rai shiru yayi yana tunanin mafita, dan magana ta gaskiya ko wani ya gani zai cutar da GAR sai in da karfin sa ya kare, yau shi za'a cewa ya kashe GAR da kan sa, ina hakan ba zata yiwuba, gashi duk wanda ya shiga wan nan aikin nasu tofa bai isa yace zai fita ba, yana cewa zai fita to fa kashe shi suke har lahira, shi bama fitar bace a gaban sa ya za'ayi ya ceci GAR ya za'ayi ya sauyawa ogan su ra'ayin a kan su rabu da GAR, dan ya san yanayin aikin su, duk wanda a kasa hoton sa a layin wayan da za'a kashe tofa ba makawa sai sun kashe sa, sosai James ya shiga damuwa da fargaban ya za'ayi ya samu mafita. Yana tsaka da tunani sai zufa yake yi yayi tsuru tsuru da shi lokaci guda, wayar sa dake hannun sa ta fara kara ala'mar shigowar kira yar firgigit yayi tare da ɗago wayar dan yaga wanene, blood Shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, jikin sa har kerma yake wajen yin picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen sa, ya tattaro dukkan nitsuwar sa waje ɗaya, cikin girmamawa yace "Hello" shiru a ka ɗan yi na yan sakanni kafin wata zazzakar murya mai batikar daɗi da sanyi yace "I'm on my way" zaro ido waje James yayi muryan sa har sarkewa take wajen furta "Wow, remain how many hours?" Shiru a ka sake yi kamar ba za'ayi reply ba, sai zaro ido waje James yake, can wan nan sexy voice ɗin yace "Few minutes" "What? James ya faɗa da karfi, katse kiran a kayi ba tare da an sake magana ba, a sukwane James ya ja motar kamar wani zararre ya bar wajen ya nufi gida. Yana shiga gida ya wuce parking space, yana kashe motar ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu ya nufi cikin gida, gaba ɗaya jubga jingan sojojin nan sai da suƙa tsorata ganin yadda James ke rikice sun san ba lafiya ba Tun daga kofar babban Palon kasa James ke kwalawa daddy ƙira, a ruɗe daddy da Uncle Herry suka sauko daga sama, suna tambayar lafiya James ke kwala musu wan nan uban kira haka, dai dai lokacin Michael da John da Jay suka sauko suma a ruɗe James yace "Romeo is back" daddy da Uncle har suna haɗa baki wajen cewa "What?" Shi kuwa John ihu ya fasa ya nufi hanyar fita a guje "where are you going John?" Daddy ya tambayi John dake kokarin nufar kofar fita, tsaki Jay yaja kafin yace "School zai je mana ina da tabbacin shaidar exam da Hangout zai je ya nemo" shiru Michael yayi yana tunanin yadda zai yi a ransa, wuce su James yayi ya haye sama ya nufi bedroom na shi, kallon Uncle Herry daddy yayi kafin yace "Let's go in, ko?" Girgiza kai uncle yayi yana faɗin "No let me check first, what and what I did last week might be i did something wrong, i don't know, I want to correct my mistake before lion reach here" wucewa daddy yayi dan shi ma yaje ya duba ko ya aikata wani abun da ba dai dai ba, shi kuma uncle ya nufi waje kallon tsab Jay yayiwa Micheal kafin yace "To kai me ya tsayar da kai? Ko dai kai ma zaka je ka duba ko kayi wani abun ne?" wucewa Micheal yayi ba tare da yayi magana ba, wucewa shima Jay yayi ya koma bedroom na shi. _______________________________ *KADUNA* A toilet din baba mai gadi Imran ya kwana, a nan wajen barcin ya ɗauke sa, saboda donanin nan na ɓacewa dukkan su barcin ya ɗauke su, suma su Abba Akil ne ya tashe su ba dan shi ba da a haka za su kwana, shi kuwa Imran sai da baba mai gadi yazo shiga bayi da asuba san nan ya samu a ka tashe sa, yana fitowa ya rinƙa tikar amai kamar zai mutu ga jikin sa duk ciwo yake masa, sai dai shima ya manta komai yayi kokarin ko zai iya tuna abun da ya kawo shi toilet ɗin mai gadi amma abun yaci tura dan ya kasa tuna komai, shiru sukayi suna ta mamaki, ita dai Hajiya duk da ta kasa tuna komai hakan bai hana tasa su Imran su mata saukan Al Qur'ani mai girma ba dan tana ji a jikin a koi matsala, haka ko a kayi Hajiya da Abba suka shirya suka tafi yiwa yan uwan Alhaji Mustapha jajen ɓatan Alhaji Mustapha da Hajiya Zainab, su kuma su Imran suka zauna shi da Akil da Akila suka fara karatun Al Qur'ani mai girma dan su sanu saukin matsalar su. Bari mu leƙa KANO mu dawo kila kafin nan sun gama karatun. _______________________________ *KANO* Daddy na zaune saman sofa shi da Jelly ɗin sa sai buga game suke a Palo, Jelly sai winning na sa take tana ta dariya, shi daman bai san ma me yake taɓa wa ba, saboda damuwa da suka masa yawa Yayi nisa cikin tunanin da yake wayar sa ta fara kara alamar shigowar kira, da sauri Jelly ta miƙe ta ɗauko masa wayar ta dawo ta miƙa masa, gabyin Engineer Muhammad ne yasa yayi saurin ɗaukar kiran tare da kara wayar a kunnen sa, da kyar ya iya furta "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Engr yace "Waalaikumussalam barka da safiya sir" "barka Engr ya aikin? Ya office ɗin?" Yayi maganar da murya irin na marasa lafiya, cikin zumuɗi Engr yace "Sir gomnati tayi rejected na later da muka tura a kan rejected na contract ɗin nan da muka yi, to suma sun yi rejected sun ki ansa san nan sun haɗo mana da nasu later" zubur daddy ya miƙe tsaye tare da zaro ido waje yana faɗin "Me suka ce a later?" "Sir ban buɗe later ba ai" tsabar sauri har daddyn Jelly na haɗe words wajen cewa "Ɗauko later ka buɗe ka karanta muji" da sauri Engr ya ɗauko later ya buɗe ya fara karantawa kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu ɗan uwana fatan ka na lafiya, ya kake ya yata Jalila? Ina fatan komai normal Allah yasa haka, ban san dalilin ka na yin rejected na contract nan ba amma koma ne bazakayi rejected ba korafin ka ba zai ansuba dan na sha wahala sosai kafin na samun maka contract nan dan haka dole kayi aikin nan, ka kula kayi aiki da amana kamar tadda na sanka, ban da ha inci na barka lafiya sako daga Hussain" "What? Sako daga wane" daddyn Jelly ya faɗa a razane "Sako daga Hussain" Engr ya mai mai ta masa, "Husaini daman kana raye ina kake? me yasa ka guje mu please ka dawo gare mu muna son ganin ka kaman ta da abubuwan da suka faru a baya dan Allah" "Sorry sir" Engr ya faɗa cikin girmamawa, a sukwane daddy yace "daga ina sakon ya fito?" "Kamar fa daga Dubai ne sir dan ga tambarin kasar a jikin later" cikin sauri daddy yace "a jiye min later da kyau gani nan zuwa yanzu" ya kai karshen maganar tare da katse kiran sauri sauri yace "Jelly ɗauki system ɗin ki shiga bedroom bari naje office ina dawowa yanzu kinji?" Gyaɗa masa kai kawai tayi san nan ta miƙe ta haye saman kujera ta kara tsayi ta manna masa kiss a kumatu, shima ya manna mata a goshi san nan ta sauƙo ta ɗauki system ɗin ta wuce bedroom, shi kuma ya fice daga palon daga shi sai jallabiya amma haka ya fice saboda sauri ba zai iya tsayuwa ya shirya ba, haka ya shiga mota ya bar gidan ya nufi office. _________________________________ *WASHINGTON DC* *03:00 pm* Agogon Washington ta buga, wasu dankara dankaran motoncin 6 ne masu numfashi wadda suka amsa sunan su motoci, a jere motocin nan su danno hancin zuwa cikin gidan su Michael, sai da suka wuce gate 1 gate 2 tayi scanning na su tsab san nan suka wuce suka nufi parking space na gidan, koda suka je bakin gate ɗin parking space ɗin, sai da suka tsaya a nan ma wan nan na'uran ta gama kiran numbers ɗin motoncin san nan gate na parking space ɗin ya buɗe suka shiga suna kashe motocin wasu jibga jibgan sojoji suka fito da yar gudun su, suka kewaye ɗaya daga cikin moton cin wadda ke a tsakiya, sojoji ne masu jiki a jika jibga jibga da su, sun samu horo mai kyau fuskokin nan nasu masu firgitar da zuciyar maza babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da su, jeruwa sukayi a bakin wata dankareriyar mota kirar *Bugatti La voiture noira* wani jebgegen soja ne ya fito daga nashi motar, jibgege da shi mai kiran basawa shima fuskar nan tasa babu alamar wasa, sai sara masa wayan nan sojojin suke, bai kula suba ya wuce ya nufi wan nan motar *Bugatti La voiture noira* ya sanye hannun sa dake cikin hand gloves baka ya buɗe kofar motar tare da komawa bayan kofar motar ya tsaya ya ɗaga hannun sa ɗaya sama ya ɗaura saman goshin sa alamar respect, cikin nitsuwa mamallakin motar ya zuro kafafun sa dake sanye cikin bakaken Booth waje, kafin daga bisani ya fito a hankali yana fitowa sojojin nan suka buga kafa a tare har sai da kasa ya amsa da dum san nan suka ɗaga hannun suka sara wa matashin da ya fito daga cikin motar, sanye matashin nan yake cikin wandon jeans blue da t-shirt ya ɗaura kyakkywan jacket mai ɗan girma zuwa gwiwar hakan yasa t-shirt nasa na cikin bai samu damar bayyana ba, ya ɗaura wani abu mai kama da rawani mai kauri a wuyar sa, san nan ya sanya black face mask a face nasa tare da black glass a idon sa, hannun sa na cikin hand gloves baki, a ta kaice dai baka iya ganin komai na shi sai dark black curly hair sa mai tsawo sosai, ya tara curly hair ɗin ya kulle a bayan wuyar sa ya nannaɗe jelar da kyau ta yadda ba zata masa yawo a bayan sa ba, duk da yana cikin jacket mai girma hakan ba zai hana ka gane cikakken jarumin Namiji bane, yana da tsawo sosai, dan yafi duk sojijin dake wajen tsawo san nan yana da ɗan giɓa kaɗan yana da murɗaɗen jiki sosai, wadda da gani kasan cikekken jarumin sojane. Zura hannun sa yayi cikin manya manyan aljihun dake jikin jacket ɗin cikin takun ƙasaita irin na jaruman maza ya nufi hanyar fita daga parking space ɗin, a sukwane wayan nan jibga jibgan sojojin suka take masa baya, wow abun gwanin ban sha'awa, taku yake suna take masa baya, duk in da ya saka kafa ɗaya sai suma sun saka, duk wani sojan da suka zo wucewa kusa da shi sai ya sara musu cikin rawan jiki, su Michael suna tsaye a bakin kofar shiga palo suna jiran sa, suna ganin sa tun daga ɗan nesa, nan take suka kara nitsuwa shi kam John jikin sa har kerma yake saboda tsoro, duk cikin su Jay da James ne masu ɗan kwari sune tsoron su bai tsanan ta sosai ba. Har wajen da su Michael ke tsaye sojojin nan suka rako matashin nan san nan suka tsaitsaya a wajen yayin sa shi kuma matashin ya nufi cikin palo kamar bai ga su Michael ba, murya na rawa har suna haɗe baki wajen cewa "Welcome lion" kai kawai ya ɗaga musu ba tare da yayi magana ba ya wuce cikin palon, da sauri suka bi bayan sa, su kuma sojojin suka tsaya a wajen kamar wasu saƙaguna. Koda suka shigo palon lion baya nan ya wuce bedroom na shi dan a gajiye yake, kallon juna sukayi kafin daddy da Uncle Herry su wuce bedroom nasu "What is wrong with you John?" James ya tambaya dan yaga yadda jikin John ke rawa kamar mazari, tsaki Jay yaja kafin yace "An fara Exam a school kuma basu yi ba mana shi yasa ya fara kuka tun yanzu tun lion bai damke saba" shi dai Michael ko a jikin sa dan yasan ya riga da yasa uncle na su ya rubuta masa Exam ɗin, shi kuma John ba ɗaya kanin biyu wucewa James yayi ya nufi bedroom nashi yana faɗin "Johnn you are in big trouble I pity you" tsaki Michael yaja kafin shi ma ya wuce bedroom na shi, kallon sama da kasa Jay yayiwa John kafin ya wuce shina ya nufi bedroom na shi yana faɗin "ina fatan lion in ya damke ka ya maka hukunci da sai ka gwammaci mutuwa tun da kunce ku bakuji" durkushewa kasa a wajen John yayi ya dafe kan sa yayi shiru kamar bashi a wajen, ya shiga damuwa sosai mafita. After some hours 08:00 pm zaune suke saman katafaren table ɗin cin abincin su dake cikin Katafaren palon su, gaba ɗayan su suna wajen kama daga Uncle Herry, daddy Michael, James, John, Jay, sai jibga jibgan Bodyguard masu basu tsaro tsaye a kan su suna aikin su wato basu tsaro da kula da abubuwan da zasu ci da kuma in suna bukatar wani abun sai su kawo musu, kamar irin su tissue paper idan zasu goge hannu ko baki, sai idan suna bukatar shan ruwa ko wine sai su zuba musu, wan nan shi ne aikin wayan nan jibga jibgan Bodyguard ɗin masu lafiya da jini a jika, masu fuska kamar wasu zakuna. "Where is Romeo?" Cewar daddy shiru palon yayi ba wanda ya amsa sai John ne yace "he is inside his room" kallon Michael daddy yayi kafin yace "Michael go and call him, yazo muci abinci mana" "I can't go anywhere dad because I'm tied" ba ƙaramin tsorata duk wani halitta mai rai dake cikin palon suka yi ba jin daddy ya ambaci a kira Romeo, nan take wayan nan jibga jibgan bodyguard ɗin suka kara nutsuwa tsit kamar basu a wajen daddy na kokarin yiwa Michael magana Jay ya miƙe yana faɗin "let me call him dad" jinjina kai daddy yayi ba tare da ya sake magana ba yana mamakin halin yaran sa kwata kwata basa girmama shi ko kaɗan abun da suka ga dama kawai suke, ɗan gara James ma shine mai ɗan tausayi da saukin kai a cikin su, Michael kam sai dai Allah ya shirya, lion kuma ba'a magana dan nashi yafi na kowa shi karshe ne wucewa Jay yayi ya haura sama ya nufi wata katafaren kofa launin golden color mai bala'i kyau wadda kamar da gold aka yi ta. A hankali cikin tsoro Jay ya tura kofar ya shiga, wani katafaren palo ne gari guda, girman palon nan ya kai 1 plot da ɗori, tampatsa tampatsan kujeru ne masu mumfashi set uku a cikin palon launin sky blue, fari, da kuma milk, ko wani set na gefe guda, ga wani haɗaɗiyar sofa table mai bala'i kyau a tsakiyar kowani sofa set, manya manyan fridge uku ne a palon masu shaƙe da kayan drinks da sauran abubuwa, daga gefe kuma ga wani makeken Tv plasma zaune saman Tv stand, shi kan shi Tv stand ɗin abun kallo ne, dan ya tsaru iya tsaruwa, gaba ɗaya palon gauraye yake da haske kwayayen wuta dake manne a saman POP palon, ba abun da ke tashi a palon sai sanyin Ac da wani fitinannen kamshi mai bala'i daɗi da ratsa zuciya, gaba ɗaya curtains na palon farare ne kal kamar hannun bai taɓa taɓa su ba, saboda haske ma kamar yanzu a ka fitar da su daga cikin ledar su, san nan su kan su curtains ɗin abun kallo ne, dan sun tsaru kai da gani kasan ba wajen wasa kazo ba, kowani sofa set a koi Chinese carpets mai bala'i laushi kamar audiga a tsakiyar su, kowani sofa set Chinese carpet kalan sofar a ka sanya masa, tiles na kasan palon da kuma na jikin bango dukka farare ne kal a ka sanya, tsayawa zayyana muku haɗuwar palon nan lokaci guda ba zai yiwu ba sai dai a rinƙa sako abubuwan a hankali, dan wan nan palon ya wuce tunanin mai tunani, wan na palon shi a ke wa laƙabi da aljannar duniya, a hankali Jay ke taka kasar palon kamar mai tsoron wani abu haka ya tura wani katafaren kofa ya shiga yana faɗin "excuse" Wow Aljanar duniya part 2 bedroom ne mai girman plot 1, ga wani makeken gado mai girman gaske, tsawon saman kayin kadon nan ya kai 2.1m (miter) kusan girman gini, dan ma dai ginin suna da tsawon 3m ne shi yasa, shi kan sa kayin gadon abun kallo ne, an kawata shi da kwalliya golden color kamar gold ga wasu hasken fitullu masu bada wuta launin sky blue a jikin kayin gadon, kayin gadon round ne (arp) while jikin gadon kuma 4 kwana, daga farkon kayin gadon har karshen sa duk kyawawan fitillun ne masu kyan gaske ke bada wuta sky blue, wan nan katafaren gadon shin fiɗe yake da lausasan bedside da kuma bargo masu laushi kamar audiga, daga bed sheet ɗin har bargon farare ne kal kamar hasken audiga, gaba ɗaya kyawawan bedside drawer, nan wasu kyawawan lamp ne ɗaure a saman su, mirror dake cikin ɗakin nan ma kawai ya isa mutun yayi kauyanci a wajen, kwalliyar saman mirror iri ɗaya ne da kwalliyar kayin gadon wato kamar kwalliyar gadon manya manyan sarakuna ta duniya, haka aka kawata wan nan bed ɗin da artists na shi, saman mirror shaƙe yake da lotions da perfumes kala kala masu kamshi da tsada, ga combs for combing hair and hair cream kala kala shake a wajen kai da gani kasan tsabtar mamalakin bedroom nan ya wuci tunanin mai tunani, mutun ne mai son gyara dan ko ta ina kayan gyara jiki ne saman mirror. Gefe da gefen mirror wasu haɗaɗun show glass ne a wajen ma su ɗan tsawo, ɗaya cike yake da air freshener da perfume na ɗaki kala kala masu daɗin kamshi, ɗayan kuma shake yake da takar su irin su Christian Bible, da dai sauran takardun su, floor tiles na ɗakin farine kal, kamar kafa bai taɓa taka tiles ɗin ba saboda hasken sa, da gani kasan mamallakin ɗakin nan yana son white color sosai dan kusan komai nasa na ɗakin fari ne, kusa da katafaren gadon nan wani hamshakin Chinese carpets ne mai bala'i lausi ga gashi a jikin sa kamar gashin mage wadda kana takawa kafar ka na nitsawa cikin gashin saboda laushi, tsadaddun curtains na ɗakin launin white color ne suma masu bala'i kyau da tsada, a koi ƙofofi guda uku a cikin bedroom ɗin, dukkan su kuma ƙofofin glass ne, ɗaya na toilet ɗaya kuma na balcony, while ɗayan kuma na dressing room ne, bedroom nan ya kawatu iya kawatu wa, ga wani sky blue haske da fitillun jikin furniture ɗin ke badawa hakan ba karamin kara kawata ɗakin yayi ba, kwayayen fitillun dake manne a POP bedroom ɗin ma dukka hasken wuta launin sky blue suke badawa, hakan ba karamin karawa ɗakin kyau da ɗaukan hankali yayi ba, ko ina a gyare tsab kamar sabon waje, sai daddaɗar kamshi da sanyin Ac mai ratsa zuciya ke tashi a cikin bedroom ɗin gwanin dadi da ɗaukan hankali. Kallon saman katafaren gadon Jay yayi, lion na kwance ya rufe jikin sa har izuwa wuyar sa da lallausan bargon sa mai kama da audiga saboda laushi, while long dark black curly hair sa ya barbazu ya rufe masa kyakkyawan face nashi, baka iya ganin komai na jikin sa, sai wan nan dark black curly hair ɗin nasa da ta rufe masa face, da alama barci yake, ya lafe luf a lallausan gadon, yabi lafiyar gadon, ganin haka yasa Jay ja da baya a hankali, kamar mara gaskiya ya fice daga bedroom ɗin ya koma Palon kasa wajen su daddy. Yana komawa ya zauna saman kujerar table ɗin yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo ɗin ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 💞 TRIPLET'S💞 17 *💞TRIPLET'S💞* https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 EPISODE 17 *KANO* _______Daddyn jelly na zuwa office jikin sa har rawa yake wajen amsan later ya fara dubawa ko zai samu address ɗin Hussain a jiki, sai dai kash bai samu ba, ba karamin haushin hakan ya ji ba, jiki ba kwari ya juya ya koma gida cike da dana sanin abubuwan da suka faru a baya, sun yasar da ɗan uwan su gashi shi kuma bai yasar da su ba yana bibiyar al amuran su yana taimaka masu, gaskiya basu kyau taba, da wan nan tunani ya koma gida. Zaune tsakiyar gado ya isko jelly tayi ɗai ɗai abun ta ta sanya system a tsakanin kafafun ta sai buga game nata take bata san me duniya ke ciki ba. Zama yayi gefen gadon yana faɗin "My Jelly har yanzu baki gaji da buga game ɗin bane?" A sukwane ta ɗago kai da alama bata san da shigowar sa ba, ture system ɗin tayi gefe guda ta rarrafo ta faɗa jikin sa tana dariya, shafa kan ta yayi cike da so da kaunar ta, yana kokarin yin magana wayar sa ta fara kara Cikin sa ya ciro wayar daga aljihu sa, dum dum gaban sa ya bada dukan uku uku ganin sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, Baban Muneer cike da damuwa ya ɗauki kiran tare da kwantar da Jelly saman gadon ya miƙe ya nufi waje Murya na rawa yace "Hello" dogon tsaki baban Muneer yaja kafin yace "Naji duk abun da ya faru wai gomnati sun yi rejected na later da ka tura ko? To ai ba damuwa in sun san wata basu san wata ba, ka buɗe kunnen ka da kyau ka saurare abun da zan faɗa maka, ina son duk wani abun da zaku saya na aiki, ka raba kuɗin biyu ka bani rabi, ma'ana idan zaku saya abun 10k sai ku sayi local na 5k sai ka turomin ragowar 5k ɗin a Account na, na san duk wani abun da zaku saya a wajen aikin nan kuɗin original gwamnati suka baku, to kai kuma da fake ko in ce local zaka musu amfani da shi, sai ka rinƙa turomin sauran kuɗin, kai engineer ne nima engineer ne nasan komai so baka isa ka cuceni ba kana jina ko?" da kyar daddy ya iya buɗe baki yace "Dan Allah Baban Muneer kayi hakuri wan nan abun da kake son nayi zalunci da ha inci ne kuma zan zubar da nutunci na da kuma darajar company ni nane, kowa yasan ni mutumin kirki ne dan girman Allah karka sa na zama maha inci karka zubar min da mutunci" ya kai karshen maganar hawaye na bin kuncin sa, bushewa da dariyar shakiyanci baban Muneer yayi sai da yayi dariyar mai isar sa san nan ya tsagaita, cike da iya shege ya fara magana "Yanzu maik har wani mutunci ne da kai? Ko ka manta abun da ka aika tane? Kai fa mazina ci ne number ɗaya ko shima ka manta ne? To in ka manta na tuna maka, wlh ko kayi abun da nace maka ko kuma ka tsinci video ka a media" yana kai karshen maganar ya katse kiran, dafe kai daddy yayi yana mai dana sanin zuwan sa duniya, wan nan masifa da me tayi kama, yanzu da hankalin sa da ilimin sa na addini zai cuci mutane, sun yarda da shi su bashi aiki a kan ya sayi kaya masu quality amma dan zalunci baban Muneer zai sanya shi cin amana zai sanya shi sayan fake kaya, why baban Muneer, sosai daddy ya shiga damuwa da tashin hankali mai tsanani, a wajen zaune saman sofa barcin wahala ya ɗauke sa, dan kwana biyu kenan baya samun barci tunani da damuwa sun hana sa rintsawa, ita ma Jelly barcin ne ya yi awon gaba da ita rungume da system a hannu tana latsawa. ________________________________ *ABUJA* Kwance Rimsha take saman sofa 3 seater a palon su na kasa, ta kurawa wayar ta wan nan dara daran sleeping eyes ɗin nata tayi shiru tana kallon hoton GAR sanye da face mask a face nashi, shi kullun cikin face mask yake ba wanda zai ce ga kalar face na shi na asali, ko a gida bai cika cire face mask na shin ba, duk wanda zai baka hoton sa to cikin face mask za ka ga face nashi Kamar wadda a ka muntsina ta miƙe da sauri ta haye sama, jim kaɗan ta dawo hannun ta riƙe da cardboard paper da kayan design irin su color da pencil da dai sauran su Saman sofa table ta ɗaura ta karawa wayar ta hasken sa ta kurawa hoton GAR ido, tana kallo tana zanawa, ta dage yau sai ta cire face mask ɗin nan nasa da design nata dan taga asalin face na shi A wan nan halin gwaggo ta fito ta same ta, zama tayi gefen ta tana faɗin "Rimsha anya ba zamu dakatar da ke daga kallon wan nan Christan ba kuwa? Ɗago dara daran kyawawan sleeping eyes nata tayi ta kalli gwaggo da kyau kafin tace "Gwaggo me ya muku kuma?" Girgiza kai gwaggo tayi tana faɗin "A'a Rimsha abun ne naga ya fara yawa kar abun yazo ya zame miki matsala kin san kwakwalwan yaro da riƙe abu" shiru Rimsha tayi ta ci-gaba da zana GAR ɗin ta, kamar daga sama sukaji murya daddy yana faɗin "Nima nayi wan nan tunani, kaunar da Siha ke wa wan nan mutumin yayi yawa kar yazamo mata wani matsalar dan haka dole a dai na kunna shi a gidan nan daga yau na dakatar" a razane Rimsha ta ɗago dara daran sleeping eyes nata ta kalli daddy, yayin da shi ma ita yake kallo, a hankali tayi kasa da kan ta kamar zata yi kuka, ta ci-gaba da zanen ta wucewa daddy yayi ya nufi waje yana faɗin "Aunty Aisha zan je meeting na yan takara shugaban kasa na zaɓe mai zuwa" da fara'a gwaggo tace "Allah ta bada Sa'a" Amin ya amsa da shi san nan ya fice Rimsha na tsaka da zanen ta bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata a idon ta ba, sai dai kawai taga hawayen a kan cardboard paper ɗin suna zuba, cikin sauri ta sanya hannu a firskar ta dan taji da gasken kuka take, jin da gaske hawaye ne yasa tayi saurin gogewa ta ci-gaba da design nata, nan take taji kan ta na sara mata kamar zai fashe, idan ta tuna daddy yace kar a sake kallon GAR sai taji kan ta ya kara sara mata da karfi kamar zai fashe, a haka ta jure ta ci-gaba da zanen yayin da ita kuma Gwaggo ta kafe Tv da idon ta, tana kallon Arewa 24, Sosai Rimsha ta kawata kyan GAR a ranta kuma haka ta fito da shi fili ta zana a cardboard paper ta, wow gashi daman ta kware a fannin zanen, abun ba'a cewa komai, zanen yayi kyau over ta tsara kyan sa iya son ranta har da sanya masa pink lips, da pink color na zane ta zana shi ya fita kamar ki kirashi ya amsa, nan take murmushi ya kubce mata ta kura masa ido cikin ranta tana kawata kayan sa yafi haka Babu ko sallama Jehan ta shigo palon ta fito daga wajen motsa jiki, sanye take cikin wando skin tight baki da riga irin na yan kwallo shi ma baki, sai zufa take haɗawa da alama ta motsa jiki sosai, ko kallon in da su gwaggo suke ba tayi ba ta wuce zata haura sama, cikin sauri gwaggo tace "Jehan ke dai ba zaki dai na wan nan abin ba ko? Wai ma da kika dage kike wan nan shirmen waye ya faɗa miki a gidan nan a koi wan da zai kyaleki kiyi aikin ɗan sandan?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Wai ke gwaggo ina ruwan ki da ni? To sai ki hanani yin abun da nake so ɗin mu gani, aikin ɗan sanda nake so ko kuma aikin jarida, kai ni nafi son aikin ɗan sandan ma kuma zanga wanda zai hana ni, Kinga gwaggo wlh ki fita sabgata idan ba haka ba ina fara aiki kece mutun na farko da zan fara sanyawa a cell in ce kina dillancin kwayoyin maye kuma ba wanda ya isa ya fitar da ke dan har kwayar sai na nemo na sanya miki cikin jaka dan a ji daɗin kama ki" waro ido waje gwaggo tayi tana faɗin "Sabon topic yau kuma, tohh a ina kuma kika koyo wan nan sabon topic ɗin kuma yau? A ba shakka dole ne kiyi aikin ɗan sanda, tun yanzu kin iya shirya sharri kiri kiri a'a Allah ya bada Sa'a Allah baki hakuri ni Aishatu jeki yi wanka da yamma ma ki kara motsa jiki abun ki daga nan sai koyan harɓi, daga nan sai kaki dan duk wani muna furci na yan sanda kam kin iya shi ba sai kin koya ba kai tsaye kawai zaki shiga aiki" sai murmushin dole Rimsha ke musu dan gwaggo da Jehan basu rabuwa kuma basu haɗuwa Tsaki Jehan taja ta nufi sama tana faɗin "Ai na zaci zaki yi wata magana ne da kin ga yadda ake tsiya kuwa" shiru gwaggo tayi dan tasan halin Jehan ba sauki yanzu sai ta sa hawan jinin ta ya tashi, miƙewa Rimsha tayi tana faɗin "Gwaggo let me go and sleep I'm feeling headache" zaro ido waje Gwaggo tayi tare da jawo ta jikin ta tana faɗin "Sorry Allah ya baki lafiya" ta kai karshen maganar tare da manna mata kiss a goshi, kakalo murmushi Rimsha tayi kafin ta miƙe daga jikin gwaggo ta haura sama ta nufi bedroom nasu Ko da ta shiga bedroom ɗin nasu Jehan na toilet tana wanka, hayewa saman gadon ta tayi ta kwanta ta shige lallausan bargon ta ta rufe jikin ta dukka har kan ta, san nan ta rungumi zanen GAR da tayi ta fara ruwan hawaye kasa kasa tana faɗin "Me yasa daddy zaka hana ni kallon sa?" Sosai take hawaye wani na bin wani, nan take zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ga bala'i ciwon kai mai tsanani, a haka barcin wahala ya ɗauke ta, koda Jehan ta fito daga toilet, bata ma lura sa Rimsha ɗin ba, ta wuce taje ta shirya cikin jallabiya irin na shan iska nan Black colar, ta saki gashi har baya san nan ya haye saman gadon ta, tajawo wayar ta ta shiga latsawa tana murmushi tana addu'ar Allah ya cika mata burin ta na zama yar sanda. _______________________________ *KADUNA* 03:00 pm Gaba ɗaya su Abbi suna zaune a Palo Irfan ya gama shirye shiryen tafiya Uk on Monday zai wuce, sai murna yake while su Aafia na taya sa, sai hira suke cike da kaunar juna, kowan nan su fuskar sa ɗauke da murmushi. Da sallama mai gadi ya shigo palon, Abbi da Irfan har suna haɗa baki wajen amsa masa sallamar tasa "Lafiya mai gadi" cewar Irfan, cikin girmamawa mai gadi yace "Wani bako ne yazo yace na kira masa matar sa, shine na tambaye sa waye yace bai sani ba idan naje kawai nace a na kiran matar Akil tasan kan ta" tashin sense kallon su Aafia Abbi yayi kafin yace "Yau she ku kayi aure ban sani ba? Dan ku kaɗai ne mata a gidan nan" Jinjina kai Irfan yayi kafin yace da mai gadi "Je kace ya shigo" da sauri mai gadi ya wuce ya koma bakin gate, shi kuma Akil ya dawo da kallon sa kan Abbi cikin nitsuwa ta fara yiwa Abbi bayanin abun da ke faruwa ta sigar da zai fahimter, shiru Abbi ya ɗan yi kafin ya ɗago yana kokarin yin magana mai gadi ya dawo bakin sa ɗauke da sallama. "Ina yake?" Irfan ya tambayi mai gadi, Mai gadi yace "Oga yace wai in ce muku idan shiga gidan yake son yi ai ba sai an masa iso ba, ba sai an bashi izini ba yasan hanyar shigowar dan haka bai da niya kawai in ce matar sa tazo yanzun nan ya bata 2mins" shiru Irfan ya ɗan yi na yan seconni kafin yace "Shike nan jeka abun ka, ke kuma Umaisha ta shi kije" Abbi zai yi magana Irfan yayi saurin cewa "Dan Allah Abbi kayi hakuri na yau kawai zan ga gudun ruwan sane" shiru Abbi yayi bai yi magana ba, miƙewa Umaisha tayi jiki a mace cike da jin kunya ta haye sama. Jim kaɗan ta fito sanye da yar karamar gyale a jikin ta tazo ta wuce su Abbi kunya kamar ta shige cikin kasa haka ta nufi waje, ba karya da Abbi yaji Akil na son Umaisha yaji daɗi sosai ko ba komai zasu kara dankon zumunci, amma sai dai yana tausayawa Umaisha ɗin dan yasan zama surukar hajiya Umaiya ba karamin abu bane sai wanda ya shirya dan masifaffiyar mace ce lamba ɗaya, sai dai duk masifar ta sai ka taɓo ta san nan kuma idan tana son ka zaka ji daɗi dan tana da kyau ta over ga wadda tayi niya, kuma tana da kirki ga wadda take so. Baki ɗauke da sallama Umaisha ta isa wajen sa, yana tsaye jikin motar sa ya bawa gidan nasu baya ya Kifa kan sa a jikin motar kamar mai tunanin wani abu, yau sanye yake cikin dakakkiyar shadda milk color mai bala'i tsada ɗinkin ta zauna a jikin sa sosai, half jomfa a ka masa yasha hula kamar ustaz, jin sallamar ta yasa ya juyo cikin nitsuwa, kallo ɗaya ya mata ya ɗaure fuska sosai kamar bai san Menene dariya ba, a kule yace cikin tsawa "Ki koma kije ki sanya hijabi!! Kuma idan kika kuskura na sake ganin ki ba hijabi sai ranki ya ɓaci!!" Ya karisa maganar kamar zai wanka mata mari saboda haushi, murya na rawa tace "Kayi hakuri yaya Akil bani da hijabi ne shi yasa, duk wanda yaya Irfan ya saya mana na kyautar da yaya Irfan ya koma Zaria lokacin" a fusace ya ɗaga hannu har zai mareta sai kuma ya fasa cikin fushi yace "Shiga mota muje" cike da tsoro tace "Ina zamuje?" Shiru ya mata kamar bai ji me tace ba, ganin haka yasa tace "To bari na faɗa wa su Abbi sai nazo mu tafi...bata kai karshen maganar ba taji saukan mari a kumatun ta, rai a matukar ɓace yace "A matsayin kanwa na mareki ba mata ba, ke har kin isa nace muje kice min ina zamuje, san nan kuma daga yau idan nace kiyi abu kika ce min bari ki tambayo wani Allah sai ran ki ta ɓaci, dan ba wanda zaki tambaya ida zakiyi abu sai nine, nine mijin ki ke mallaki nane, ni kaɗai nake da iko da ke, ba wanda ya isa ya nuna min abun da zan yi a kan ki, dan ke ɗin mata tace!!" Ya kai karshen maganar tare da ciro handkerchief daga aljihun sa ya miƙa mata a kan ta goge hawaye, a hankali ta sanya hannu tana hawaye zata ansa handkerchief ɗin, ganin tana abu a hankali zata ɓata masa lokaci ne yasa, ya sanya hannun sa da kan sa ya goge mata hawayen yana faɗin "A matsayin kan wa nake miki hakan" bayan ya goge mata hawayen da kan sa ya buɗe mata motar ta shiga gidan gaba san nan shima ya zagaya ta ɗayan gefen ya shiga ya tada motar suka bar wajen. Kai tsaye *ABC supermarket* suka nufa, yana tuki yana zuba mata kashe di da dokokin irin kayan da zata rinƙa sawa, gaba ɗaya yayin cancel ɗin gyale a cikin kayan ta, haka riga da wando yace kar ta sake sawa sai tazo gidan sa, san nan attachment da eyelashes duk ya hana yayi cancel, hijabi har kasa ya yarje mata tarinƙan sawa idan zata je school, dokoki kala kala iri iri ya kafa mata, tare da kashe din idan ta karya masa doka ɗaya zatayi bayani sai ranta ya ɓaci, ita kuwa cikin ranta cewa take "zan dai na duk abun da ka hana amma wlh ban da sa gyale, sai na sa in dai gyale ne sai dai ka kashe ni" shiru yayi bai sake magana ba har suka isa super market ɗin cike da bada umarni yace "Ki zauna a nan karki yarda ki leka waje" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga Motar ya nufi cikin super market ɗin, sai tsaki take ja, a kule tace "Sai an sa gyale mugu kawai" Haka tayi ta surutan ta ita kaɗai, har ya dawo hannun sa rike da ledoji manya manya guda biyu, ba tare da ya mata magana ba ya ajiye a gidan bayan motar san nan ya shiga gidan gaba, ya tada motar kai tsaye suka wuce *kasuwar barci* a nan yaje da kan sa ya zaɓa mata manya manyan hijabai wadda yana da tabbacin zasu kai mata har kasa, dan a wan nan karon ma a mota ya barta ya hana ta fita, hijabi 12 ya saya mata manya manya har kasa san nan ya sayawa Aafia ma 12 ya wuce ya dawo mota, yana zama wayar sa ta fara kara, guntun tsaki yaja tare da ɗauko wayar ya duba, a nutse yayi picking call ɗin yana faɗin "Sorry Abla na manta ne amma bari na sa miki yanzu, sai yaushe zaki zo ne?" Daga ɗayan ɓangaren Abla tace "Yaya Akil wai ina yaya Imran ne? Sai kiran sa nake amma baya ɗagawa" kallon face ɗin Umaisha yayi ta cikin mirror motar kafin yace "Abla ni bana gida na fita da Auntyn ku amma idan na dawo zan duba miki me yasa baya ɗaukan kiran, amma dai koma me kin dai san ba da gan gan yaki ɗauka bako?" Da sauri Abla tace "Yaya Akil Auntyn mu kuma? Jinjina kai yayi yana faɗin "Eh Auntyn ku" cikin zumuɗi tace "Dan Allah yaya Akil ka bata waya mu gaisa" "Me zaki faɗa mata?" Shagwaɓa murya tayi kafin tace "Kai yaya Akil gaisawa kawai zamuyi" girgiza kai yayi yana faɗin "A'a ai na sanki ne da iya yi" "Kai yaya ba wani iyayi Allah" sanya wayar yayi a hand-free san nan ya miƙa wa Umaisha, jikin ta har kerma yake wajen ansar wayar tana faɗin "Assalamu alaikum" da murna Abla tace "Waalaikumussalam Auntyn mu ina wuni?" Kallon sa ta kasan ido Umaisha tayi kafin tace "Lafiya lou Aunty Abla yasu mama?" kunna motar sa yayi ya ɗauki hanya yana sauraron hirar tasu Sai murmushi Umaisha ke yi, Abla tace "Auntyn mu waye baban ki? Yar gidan sarki ne ke ko yar governor? Dan nasan yaya Akil ba zai zaɓo mana yar gidan kananan mutane ba" nan take face ɗin Umaisha ta sauya ta dai na murmushi jiki a mace tace "Ni ba...bata karisa ba ya ansa wayar cikin faɗa yace "Abla abun da zaki tambaye ta kenan? Wan nan tambayar ni zaki yiwa ai ba ita ba" murya na rawa Abla tace "Kayi hakuri yaya Akil" tsawa ya daka mata "Abla kullun ina faɗa miki ki ɗauki duniya da sauki ki dai na jin zancen Ammie a kunnan ki baki ji ko? Kullun sai na faɗa miki ki dai na cewa kina kyamar talakawa amma baki ji ko kaɗan ko? Ya miki kyau to ba yar kowa bace yar talakawa ce, kuma a haka nace nake so ko akoi wadda ya isa ya hanani auren zaɓin rai na ne?" Murya har sarkewa yake tace "Kayi hakuri yaya Akil tuba nake" dogon tsaki yaja tare da katse kiran, shiru Umaisha tayi tana tunani "Ashe daman yaya Akil yana da hankali, ashe kawai zafin rai gare sa ba wai rashin hankali ba Allah sarki, Allah ya sassauta masa zafin kan nan da zuciyar nan tasa" shiru sukayi dukkan su, ba wanda ya sake magana har suka isa kofar gida, ya kashe motar sa ya fito ya ɗauka mata ledojin dan yasan ba zata iya ɗauka ba suna shiga harabar gida a nan suka isko Abbi da Irfan da Aafia, suna tsaye cirko cirko saboda da sukaji Umaisha shiru bata dawo ba shi sukazo su leka ko tana wajen ganin bata nan shine suka tsaya suna tattaunawa ta ina Irfan zai je neman ta ganin su yasa Umaisha ta tafi da sauri ta faɗa jikin yaya Irfan tana ɓoye fuska dan ita a koi ta da kunya sosai, har gaban su Abbi yazo ya ajiye mata ledojin cikin girmamawa yace "Sannu ku ina wuni uncle" da fara'a Abbi yace "Lafiya lou Alhadulillah ina kuka je ne na fito ban same ku ba?" Juyawa Akil yayi ya bawa Irfan hannu yana faɗin "Yanzu dan na fita da matata sai na faɗa wa wani in da na kai ta, wan nan sirrin mune ai" tashin sense kallon Irfan Abbi yayi kafin yace "Ni kam Irfan ko dai ka aurar da Umaisha ban sani bane?" Wuce Akil yayi abun sa ya nufi gate yana faɗin "My wife sai mun yi waya" kallon sa Irfan yayi har sai da ya fice san nan yace "Umaisha ku kwashe kayan kuje ciki" cikin sauri suka kwashe kayan da sauri suka wuce ciki Aafia tana ta kallon Umaisha tana jiran suje ɗaki ta tambaye ta ina Akil ya kai ta Gyara tsayuwa Irfan yayi cikin nitsuwa ta fara magana "Abbi kayi hakuri haka halin Akil yake muna masa fatan yayi hankali ta dalilin Umaisha mun yi magana da Imran a kan hakan san nan kuma Abbi idan ka lura yaro ne fa 22 years yake da shi" cikin fushi Abbi yace "A'a wlh bai isa ba wan nan iskanci ba zan ɗauka ba, bai isa yazo ya min wan nan iskanci a gida ba ya ɗauki yata lokacin da yake so ya fita da ita san nan ya dawo da ita lokacin da yake so in masa magana yace min shi da matar sa to a yau she ta zama matar sa? Wlh idan yamin tsiya sai na haramta masa auren Umaisha in ga wanda ya isa ya sa na bashi ita, ya koma ya tambayi yaya cikin kannen sa waye mai zafi ma faɗa ci zai faɗa masa, daga yau ka sanar ma sa idan ba zai shigo cikin Palo yayi hira da Umaisha ba to ya bari bana bukata daman bance masa tana neman mijiba kwata kwata ma nawa tace 15 years fa gare ta zai fara koya mata wasu ɗabiun ya sauke min ya daga tarbiyar dana ɗorata to bai isa ba yaya ma yayi kaɗan a kan wan nan zance bare shi, kuma nayi cancelled fita da Umaisha suje wani wajen, idan wani abun yake son nuna mata ko ya saya mata to sai dai yaje shi kaɗai ya dawo ya kawo mata nan!!!" Shiru Irfan yayi dan yasan halin Abbi yana da saukin kai da fara'a amma idan a ka taɓosa yana da zafi sosai, yana da faɗa kuma wan nan karon a kan gaskiya yake faɗar sa dole su nunawa Akil Umaisha na da daraja dole su saya mata kima Wucewa Abbi yayi ya shige cikin palo ransa a matukar ɓace, jiki ba kwari Irfan yabi bayan sa, ko da ya shiga palon Abbi ya wuce bedroom na shi, shi ma sai ya wuce bedroom na shi jiki a mace. A ɓangaren su Aafia kuwa, suna shiga bedroom na su da murna Aafia ta fara watsa kayan tana fitarwa, ganin manya manyan hijabai ne yasa taja dogon tsaki ta ture ledojin, ta jawo wan da ya sawo daga super market tana faɗin "Lallai Umaisha kina da babban aiki a gaban ki wan nan hijabai dukka lallai kina ruwa" da sauri Umaisha tace "A'a Aunty Afi muna dai ruwa, dan hijabai ɗin ba nawa ni kaɗai bane, nawa 12 naki 12 ne ai" zaro ido waje Aafia tayi kafin tace "Sannu Uban na wlh bai isa yace zai sani sanya hijabi ba, ina ruwan sa ma dani tab aiko gyalen ma sai na ga daman sawa in ga uban da ya isa ya sani sawa, shegen idon sa kamar na duji" dariya Umaisha tayi tana faɗin "Ni fa da yace naje na sanya hijabi har karya na masa nace bani da su, na ɗauka zai kyaleni yace na ci-gaba da sa gyalen, amma sai na ga akasin haka ya tasani a gaba mukaje kasuwa ya kwaso min wan nan abubuwan dukka dan iskanci" ta kai karshen maganar tare da kwanciya saman gadon, tsaki Aafia taja tana fitar da abubuwan cikin ledojin super market ɗin, chocolate ne kala kala dasu hollandia milk su biscuits sweet da sauran kayan kwalama, nan Aafia ta ware wanda zata ci lokacin ta tattara sauran ta zuba su cikin bedside drawer, ta tasa wadda ta ware a gefe kuma tana ci suna yar hiran duniya. __________________________________ *WASHINGTON DC* Jay Yana komawa ya zauna saman kujerar table ɗin yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo ɗin ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su. Kallon Micheal James yayi cikin kulawa yace "My bro bana son ka rinƙa yin irin abubuwan nan da kake yana da kyau kayiwa sauran mata adalci, mum daban suma sauran mata daban, ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba, ba wai ina faɗa maka haka bane dan ka kula mata ko wani abu no nima bani da lokacin kula mace kwata kwata a rayuwa ta, ba kuma ina faɗa maka hakan bane ko dan ka yarda da mace ko kuma mum batayi laifi ba, no mum tayi babban laifi, wadda ta cancanci mu tsaneta kuma dole mu kasa yarda da mata saboda abun da mun tayi ta cutar da zuciyar mu ta sa mana tabon da ba zai goge ba, amma yana da kyau ka cire tsanar su a ranka, dan wani lokaci suna da amfani, kuma ina son kayi hakuri ka shirya muje New York mu gaida mum gobe, please na san bata da burin da ya wuce ta gan mu, ba wai dan wani abu zamu je gaishe ta ba sai dan sada zumunci, ba wai dan muna son ta ko zamu yafe mata ba a'a kawai yana da kyau ne muje ɗin, shekara 18 kenan rabon mu da mugan ta fa tun da tazo sau ɗaya daddy ya koreta bata sake zuwa ba why mu ba zamu je ba?" Miƙewa Michael yayi tare da buga table ɗin cikin fushi yace "I told you to stop talking about that human for me!! I said I don't like, wai a na dole ne? Nace bana son jin zancen wata mata ni bani da uwa daddy shi ne kawai duniya ta, karka sake cewa muje wajen wata mummy idan kuma ka sake wlh barin muku gidan zanyi!!!" a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 💞 TRIPLET'S💞 18 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 EPISODE 18 *Washington DC* a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya, girgizar kai James yayi kafin ya miƙe tsaye cikin fushi ya bar palon, yana jin haushin abun da mum ta musu da kuma irin tsanar da Romeo, daddy, Michael, Tga, uncle herry, suka mata. A gefen su Michael kuwa komawa daddy yayi ya zauna shi ma Michael ya koma ya zauna, "Micheal where is your exam card?" cewar Jay yayi maganar yana tsare Michael da ido, a kule Michael yace "Wai Jay meye ruwan ka da ni ne? A koi wani business ne tsakanin mu?" Dariya Jay yayi yana faɗin "Michael baka da gaskiya" a fusace Michael ya buga table ɗin ya fara sunfa uwar masifa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba sai dannan sa su daddy suke, cikin wasa John yace "Kai Micheal is it not our brother? kake masa tsawa haka" cikin fushi Micheal ya danko wuyar rigar John yana kokarin yin magana sukaji takun tafi daga bayan su, wadda ko basu juya ba sun san mai wan nan takun, a sukwane Michael ya saki wuyar rigar John ɗin tare da tattara nitsuwar sa waje guda, gaba ɗaya palon yayi tsit, duk wani halitta mai rai a palon sai da ta nitsu tsit kamar ba kowa. A hankali yake sako kafar sa yana taka staircase ɗin kamar bai san taka kasa matashi ne mai jini a jiki farine tas farin Bature dogo ne sosai mai faffaɗar kirjin kamar wani zaki yana da murɗadɗen jiki wadda kallo ɗaya zaka masa kasan yasamu training mai kyau ya koshi da training, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda horon da ya ke bawa kan sa, sanye yake da wando guntu 3 cutar hakan ne ya bawa kyawawan kafofin sa bayyana ga wasu gashi dark black mai tsantsi da laushi kwance a kyawawan fararen kafofin nasa har izuwa idon sahu na kafar sa hakan ba karamin kyau ya kara masa ba, yana sanye da riga mai ƙaramin hannu hakan ya bawa tuma tuman ɗamtsen hannun sa damar bayya kamar zasu fashe saboda horo, ga wasu kyawawan gashi dark black sai sheki suke kwance a hannun na sa har izuwa idon sahu na hannun sa, kasan cewar a komai face mask a face nashi baka ganin face na shin sai dai dara daran light blue eyes na shi masu bala'i kyau da ɗaukan hankali gwanin burgewa, yana da dogayen gashin ido kamar ya sa eyelashes, gashin geran sa kuwa a cike suke kamar zasu haɗe saboda cika gasu a kwance luf kamar an zana masa sai sheki da kyalli suke, sai faman lumshe dara daran light blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan dark black curly hair sa da ya sha gyaran nan kuwa ya ɗaure a bayan sa, kaɗan ya zubo masa ta gaban goshin sa, hakan ba karamin kyau ya kara wa face nasa ba, ya kara kawata kyan sa sosai ya fito da face ɗin gwanin ban sha'awa da burgewa, soft skin nasa nan kamar ka taɓa jini ta fito saboda kwanciya da laushin da yayi yaji hutu kamar bai taɓa fita waje ba, kyawawan fararen kafofin sa na sanye cikin wani haɗaɗiyar bedroom slippers mai bala'i kyau da laushi jikin takalman duk gashi kamar gashin jikin mage, san nan yana da dogayen yatsun kafa da na hannu farare tas mai ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga yatsun nashi a koi lallausan bakin gashi mai tsantsi kwance a kan su haka zalika yatsun hannun sa dogaye ne sosai suna da ɗan kauri kaɗan masu ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga, yana da kwantatciyar lallausan bakin saje a gefen kumatun sa har izuwa gemun, sai dai bai bar gemu ba, a hankali yake takowa kan sa na duƙe kan wayar sa kirar *falcon Supernova IPhone 6 pink diamond* wadda a kalla kuɗin ta ya kai ($48.5 million) a hankali yake latsa wayar kamar baya son taɓa screen ɗin wayar, hannun sa na ɗaure da dangareriyar gold watch irin na hannun su Michael sak. Duk in da ya sanya kafar sa, sai wani kyakkyawan ƙaton karen sa dake gefen sa mai suna Brady ya sa na shi kafar. Brady irin manya manyan karen nan ne masu gashi ajiki sosai wadda yake har kasa duk in da Romeo yayi taku ɗaya sai Brady ma yayi taku ɗaya, tun bai karisa shigowa palon ba wan nan daddaɗar fitinanniyar kamshin perfume na shin ta kauraye ko wani lungu da sako na cikin palon, sai shakan kamshin bodyguard nasu ke yi suna lumshe ido, dan kamshin perfume na shi number ɗaya ne a duniya wajen daɗi ```````ROMEO``````` Cikakken namijine mai Jini ajika, lafiyayye kuma kakkarfan jarumi., kaifi ɗaya ne ba mai iya tan kwara shi idan ya faɗi abu tofa ya faɗa ne kome za'ayi baya sauya magana miskiline na karshe baya shiga harkan kowa baya son magana, idan ma yana waje tofa kome zai faru shiru ake ba wadda ya isa yayi magana har sai ya tashi a wajen dan bai san hayani ya, idan baka san shi ba sai kace kurma ne, bai son kallon mace a Area da yake saboda Mahaifiyar sa ya tsani kalmar mace a rayuwar sa kamar yadda ya tsani jin sunan mahaifiyar sa, Allah ya masa farinjinin da mata da maza ke haukan son shi, daga kasashe daban daban yayan manya manyan masu kuɗi na duniya na son shi, ta ko ina mata son shi suke suna burin ko sau ɗaya ne suga face na shi, sai dai kuma babu macen da ta isa tayo area da yake, saboda ba shi da sauki basu ga alamar face ɗin wasa a tattare da shi ba, baya dariya kullun face nashi a ɗaure take tamau kamar hadari kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ganin face na shi kawai yana sa hantar manyan maza ta kaɗa bare ku ma mata, ganin face na shi kawai tana jirjiza daula, yaci sunan sa da daddy ke kiran sa wato lion, lion ɗin ne da gaske, ...Taku yake cikin nitsuwa da kwanciyar hankali Brady na gefen sa suna saukowa tare. Nan take su Johnson suka kara shiga hankalin su, suka nitsu ba su Johnson kawai ba har su daddy uncle Herry duk sun nitsu numfashi ma a hankali suke fitar wa dan gudun kar wani sauti da zai sa Romeo ɗago kan sa daga kan wayar sa ya fita. Saukowa yayi yazo ya wuce su bai ko kalli in da suke ba kamar bai san da zaman mutane awajen ba ya fice ya nufi waje, Brady na biye da shi a gefen sa. Yana fita suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya a tare, miƙewa Johnson yayi ya ɗan leƙa kofar palon dan yaga Romeo yayi nisa ne ko bai yi ba, ganin babu alamar sa awajen ne yasa ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali ya dawo ya zauna, kasa kasa ya dubi Michael cikin harshen turanci yace "We're finally saved Michael it seems like kana da rabon yin tsere da doki kwanan nan" harara Micheal ya watsa masa kafin ya miƙe ya bar palon yana huci kamar wani zaki shi a dole an ɓata masa rai, miƙewa daddy yayi ya nufi waje yabi bayan Romeo, a ransa yana faɗin "na sanya maka sunan Romeo da murnana, a tunani na zaka girma kamar Romeo sai kuma nayi rashin Sa'a ka girma kamar lion kwata kwata baka san wani abu wai shi felling ba ba ruwan ka da wani abu wai shi kaunar yan uwa da iyaye kai dai umarni kawai ka iya badawa gaskiya sunan Romeo bai dace da kai ba da tun kana yaro na fahimci haka da na jima da canza maka suna, amma yanzu time ya kura wayyo ni William sai na gama kamar sabon rashin mutunci ya karo tafiyar san nan to ko dai an sake ɓata masa wani aikin ne ya dawo ya sauya gaba ɗaya" da tunani cike fal ransa ya nufi in da yake zaton zai samu Romeo, wato garden Haka ko a kayi Romeo na zaune a wajen yana latsa wayar sa ya ɗaura hannun sa ɗaya a saman wuyar Brady yana shafa lallausan gashin Brady ɗin, hasken fitullun dake wajen masu bada wuta launin sky blue ba karamin karawa face ɗin Romeo kyau suka yi ba, wutar tayi dai dai da kalar idon sa, hakan gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, ga wajen ya kawatu iya kawatu, gwanin kyau. Kusa da shi daddy yazo ya zauna cikin nitsuwa yace "Welcome My lion" shiru ya ɗan yi kafin yace "Tnks" yayi maganar ba tare da ya kalli daddyn ɗin ba, "My lion, i want us to discuss something" shiru yayi tare da ajiye wayar dake hannun sa a gefen sa alamar yana sauraron daddy kenan, cikin ɗari ɗari daddy ya fara magana "About your mum i want you to.... Bai kai karshen maganar ba ya dakata saboda juyowa da Romeo yayi a sukwane har sai da kwayar idon sa suka kara shining saboda ya waro su waje sosai, nan take daddy yaji harshen sa ya masa nauyi over, ya kasa ci gaba da maganar kallon tsab Romeo ya masa kafin ya kau da kan sa gefe, murya kasa kasa kamar mai raɗa yace "get out!!" cikin sauri daddy ya miƙe ya bar wajen, ya koma cikin gida, jingi na kai da jikin sofar Romeo yayi tare da ɗaga kan sa sama kamar mai tunanin wani abun, zuciyar sa na masa zafi daddy ya tuno masa da babban ciwo dake zuchiyar sa wadda baya son tunawa kwata kwata a rayuwar sa, a wan nan hali wayar sa ta fara ringing, yana ji amma bai ɗago ba ma bare ya ɗauki wayar, har kiran ta katse, kira ta biyu ta shigo, hannun sa ya cusa cikin curly hair ɗin sa, yana ɗan shafawa a hankali tare da sauke ajiyar zuciya, kira na biyu ya yanke na uku ya sake shi gowa, a hankali ya ɗauki wayar kamar bai son taɓa wayar haka ya kawota sai tin face nashi tare da waro blue eyes nashi masu kwalli, zubawa wayar kyawawan eyes nashi yayi, na yan wasu sakan ni, sai da wayar ta kusa katsewa san nan ya sanya kyakkyawar yatsan hannun sa yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru bai yi magana ba, daga ɗayan ɓangaren TGA yace "Hello" shiru Romeo ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba, A hankali ya furta "What is going on T?" Daga ɗayan ɓangaren TGA yace "tomorrow I will be on my way" jinjina kai kawai Romeo yayi ba tare da ya sake magana ba, shiru shima TGA yayi yana jiran yaji me GAR zai kuma cewa Har Tga ya cire rai da GAR zai amsa masa sai kuma yaji cikin wan nan sayyar muryan nasa yace "safe journey" ya kai karshen maganar ya ajiye wayar a gefen sa ba tare da ya kashe kiran ba, Tga da yaji shiru sai ya katse kiran, shiru GAR yayi tare da lumshe dara daran kyawawan blue eyes ɗin nan nasa, kamar mai jin barci yayin da hannun sa ke saman wuyar Brady yana shafawa a hankali. Lokacin da daddy ya koma palo duk sun gama cin abinci sun watse kowa ya wuce bedroom na shi, yana kokarin wucewa ya haura sama, James ya sauƙo, shirye yake cikin wani ɗan iskan crazy jeans baki sai t-shirt fara tas, ya zuba gold chain a wuya, ya sanya wata haɗaɗiyar Booth a kafar sa baƙa kalar wandon sa a kafar sa, daman shi gashin kan sa bai da tsawo sosai, ba ta kai ya tara ya ɗaure ba dan haka sai ya barta zube kawai, tasha gyara sosai, sai kamshi yake zubawa, kai da gani kasan wan nan wani waje mai mahimmanci a gare sa zai je, "Where are you going James?" daddy ya tambaya yana duba time a jikin agogon hannun sa, 09:30 pm, a ta kai ce James yace "Party" yayi maganar tare da wucewa da sauri, yana kokarin ciro wayar sa daga aljihun wandon sa, hoton da ogan su ya turo masa a waya ta faɗo, dan yaje ya wanke hoton ya mai da ta na cati, ɗaukan hoton daddy yayi ya zubawa hoton ido yana kallon face ɗin Romeo sanye da face mask "what are you going to do with this pic James?" a sukwane James ya juyo tare da dawowa ya ansa hoton ya nufi hanyar fita yana faɗin "is it not my blood brother picture?" Shiru daddy yayi ya haura sama abun sa bai kawo komai a ran sa ba, shi kuma James ya wuce ya fice daga palon ya nufi parking space. Sauri sauri ya ɗauko motar sa ya fice dan kar Romeo ya tambaye sa ina zai je. Yana fita kai tsaye *Flash dancing club* (gidan rawa) ya nufa, sai da ya kusa isa wajen san nan ya tsai da motar sa a bakin titi ya cire kayan da ya sako daga gida, ya sanya nasu na yan ta'adda, wato irin kayan mai kama da na yakin nan mai ɗauke da wukaken ko ta kwana a jikin su, haka ya shirya tsab a kan titi ya cire duk wasu chain da ya sanya a wuya da hannun sa, ya bar agogon su kawai, san nan yasa face mask dan kar wanda ya san shi ya gane sa yazo ya faɗa wa daddy da Romeo. Yana gama shiri ya ja motar sa ya wuce club ɗin, yana parking a parking space na su ya fito ya shige ciki, kai tsaye wani keɓaɓɓen ɗaki ya wuce, a nan ya isko wasu fafaren Indiyawa suna jiran sa, zama yayi a saman kujerar dake wajen suka fara tattaunawa a kan abun da ya tarasu, Good 3 hours suka ɗauka suna tattaunawa kafin daga karshe James ya miƙe ya nufi wani ɗan karami kofa dake wajen ya buɗe ya shige, suna zaune suna jiran sa. Jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata jaka yazo ya miƙa musu san nan ya basu hannu sukayi musabaha tare da yin sallama, ya wuce ya fice daga wajen ya nufi motar sa. A wan nan karon ma yana fita daga club ɗin ya ɗan yi tafiya kaɗan ya tsaya ya sauya kayan jikin sa ya mai da wanda ya fito da su daga gida, ya shirya tsab kamar yadda ya fito daga gida san nan ya wuce ya nufi gida. Yana shiga gate na biyu tayi scanning na shi san nan ya wuce parking space, lokacin karfe ɗaya sau ra minti 20 na dare. Ko da yayi parking na motar ya fito sai ya fara lallaɓawa a hankali kamar mara gaskiya, musamman ma da ya shigo palon kasa, a hankali yake sanya kafar sa a floor ɗin dan kar wani yaji takun sahun sa. Kamar daga sama yaji zazzakar voice an ce "where are you coming from?" A razane ya ɗago kan sa sama, dan ta saman kan sa yaji voice ɗin, ganin Romeo tsaye a saman benen a bakin kofar shi ga part na shi ne yasa James sauke nauyayyar ajiyar zuciya a hankali, cike da tsoro yace "from my friend party" shiru Romeo ya masa tare da tsare sa da dara daran kyawawan blue eyes na shi, sanye yake cikin kayan barci riga da dogon wando farare kal masu laushi da kyau da tsada, kayan sun zauna a jikin sa sun anshe sa sosai kamar dan shi a kayi su, a wan nan karon ma a koi face mask a face na shi, dan shi idan ba barci zai yi ba baya rabuwa da face mask dan bai son jama'a su iya tantance face na shi, bai son su iya gane banbancin sa da TGA, dan kwarai suna kama amma suna da ban ban ci ta abu huɗu kawai, wan nan dalilin yasa bai son cire face mask ɗin, har ya saba abun ya zame masa jiki, ya zamo idan bai sanya face mask ba ma baya jin daɗi. Da wan nan daddaɗar sexy voice ɗin nasa mai kwantar da hankalin mai sauraro cikin nitsuwa yace "From today i forbide any body in this house going to party anymore" cikin girmamawa da rawan jiki James yace "Okey bro" sai kerma irin na marasa gaskiya jikin sa ke yi, duk a ruɗe yake, sai zufa yake duk da sanyin Ac dake ta shi a palon kirjin sa sai dukan uku uku yake, tsabar tsoro har kan sa na sara masa kamar zai fashe. Juyawa Romeo yayi cikin nitsuwa ya taka ya koma cikin part na shi, ba tare da ya sake yiwa James magana ba, da sauri James ya haura sama har yana haɗawa da gudu, kallon ɗaya zaka masa a wan nan yanayin da yake ciki kaga asalin mara gaskiya, yana shiga bedroom na shi ya faɗa saman gadon sa ko takalman kafar sa bai cire ba kirjin sa sai dukan uku uku take, yana murna da ya samu ya kubcewa Romeo, dan yasan ba dan dare bane yanzu da sai Romeo ya kama shi sai ya gano shi, saboda Romeo a koi shi da kaifin kwakwalwa da basira, ga saurin gane abu, ba'a banza yake The general of the army gaba ɗaya ba. Saboda tsorata da James yayi da kyar barci ta ɗauke sa ko takalmin kafar sa bai cire ba bare aje ga zancen wanka da sa kayan barci, ya tsorata sosai dan ya san halin Romeo bai da wasa, kana wargi kaɗan zai kama ka. *NIGERIA,* *ABUJA* Wasa wasa zazzaɓi ne mai zafi ya rufe Rimsha tana rubgume da zanen da tayi na GAR haka mum ta shigo ta same ta, a tsorace ta kira daddy, lokacin already ya dawo yana gida, yana zuwa ya taɓa jikin ta zafi kamar wuta, hannu yasa yana kokarin ansan zanen da ta rungume, cikin magagin barci da zafin zazzaɓi ta fara sambatu ta kankame zanen sosai tana faɗin "Jehan dan Allah ki kyale min zane na daddy ya hanani kallon GAR a Tv yanzu zanen kawai ya rage min duk wani video sa dake wayata zan goge dan ba zan iya kin bin maganar daddy ba, dan Allah ki kyalemin zanena idan kika ansa Allah zan iya mutuwa, ni GAR yana matuƙar burgeni dan Allah ki kyaleni" Cike da tashin hankali daddy ya ɗago ya kalli mum wadda ita ma shi take kallon, tashin sense ja da baya kaɗan yayi murya kasa kasa yace "Munyi kuskure, mun yi kuskure tun farko da muka bar Rimsha tana kallon wan nan kafurin yanzu saboda na hanata kallon shi ne har zazzaɓi ya kamata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun tab ɗi jam a koi matsala" matsowa Mum tayi ta dafa sa tana faɗin "To yanzu me mafita?" Girgiza kai yayi yana faɗin "Mafita shi ne mu kyaleta ta ci-gaba da kallon sa, a hankali mu raba ta da shi, idan muka ce zamu raba ta da kallon sa lokaci guda zata iya cutuwa kin dai ga alama yanzu to, ba zai yiwu mu ce lokacin guda ta dai na kallon sa ba, idan mukayi hakan mun zalunce ta, kuskure dai mun riga mun yi sai dai mu kiyayi gaba ki san yadda zaki yi kina zare mata abun a ranta a hankali hankali har ta rabu da abun dukka, yanzu zai wuce da ita hospital kome yake ciki zamuyi waya" ya kai karshen maganar tare da komawa wajen ya duƙa ya sameta cak a kafaɗar sa suka nufi waje sai sambatu take ga jikin ta zafi kamar wuta jiki a mace mum tabi bayan su ta wuce bedroom nata, while gwaggo da Jehan kuma suna ɗakin gwaggo basu san meke faruwa ba, ita ma mum tazo dubasu ne ta samu Rimsha cikin wan nan hali. Kai tsaye hospital daddy ya wuce da ita, suna zuwa a ka anshe ta hannu bibbiyu, a ka fara bata taimakon gaggawa, shi kuma daddy sai yawo yake a bayan A&E yana tunanin mafita. *KADUNA* zaune suke gaba ɗayan su suna hira while Imran yana aikin latsar waya yana kallon hotunan Jelly, cikin natsuwa Abba ya fara magana "Imran yaushe zaka koma school?" Ɗagowa Imran yayi daga kallon wayar nasa da yake cikin girmamawa yace "Next week zan koma" jinjina kai Abba yayi kafin yace "Kai kuma fa Akil?" "Tare zamu wuce da Yaya Imran In Sha Allah sai mu rabu a Germany ya wuce nima na wuce namu School ɗin" Abba na kokarin yin magana Akila ta rigasa cikin shagwaɓa tace "Abba dan Allah nima zan bi yaya Imran, na gaji da karatu a Nigeria" Shafa kan ta Abba yayi tare da jawota jikin sa yana faɗin "Ba komai heartbeat zaki je amma ba yanzu ba sai kin kammala secondary ki san nan kije kiyi jami'a a can" kara lafewa tayi jikin Abba tana mai kaunar iyayen ta da yan uwan ta, Akila kenan heartbeat na kowa dake cikin gidan, har da masu bawa flowers ruwa da mai gadi duk kaunar ta suke, kowa son ta yake, ba iya gidan ba duk wan da ya zauna da ita sai ya so ta saboda kyan halinta da kaunan jama'a ba ruwan ta da rigima ga girmama mutane, tana son zaman lafiya, ga fara'a kowa na tane Tana kwance jikin Abba ta jiyo wayar ta na ringing a bedroom na ta, da gudu ta miƙe ta haye sama ta nufi bedroom ɗin, wayar na gab da katsewa ta shigo, hannun ta har rawa yake wajen yin picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen ta cike da zumuɗi tace "Bappa ina wuni" daga ɗaya bangaren muryan Jelly ta daki dodon kunnen ta cikin kauɗi tace "Aunty Akila ni ce ba daddy ba" daɗi kamar Akila tayi ihu sai murmushi take bakin ta yaki rufuwa, ta kasa ɓoye murnar ta, cike da kaunar yan uwa ta tace "Jelly na ya kike ina kewar ki sosai yar uwata" a bangaren ita ma Jelly bakin ta ya kasa rufuwa saboda murna da farinciki ji take kamar tayi tsuntsuwa tazo ta kalli Akila, tana matikar son Akila over, haka suka rinƙa hira Jelly na zuba mata shirme ita kuma tana biye mata, almost 1 hour suka ɗauka suna hira sai murmushin da dariya Akila keyi ji take kamar ta koma gidan su Jelly kawai da zama, sun kasa yin sallama da juna har sai da daddy ya anshe wayar suka gaisa da Akilan san nan ya katse kiran Yana katsewa Akila ta fara ƙoƙarin neman layin su Umaisha dan su gaisa, sai dai kash a rufe tasamu layin, haka ta hakura ba dan taso ba, tana bala'i kaunar yan uwan ta sosai, rashin samun su Aafia a waya bai mata daɗi ba ko kaɗan amma haka ta hakura ba dan taso ba, ta miƙe jiki ba kwari ta fice ta koma Palo Ko da ta dawo palon, yaya Imran da Akil duk sun tafi basu a palon sai Ammie da Abba, da suka zubawa Tv ido sosai suna kallon, yanzu sun samu saukin wayan nan dodannin dake zuwa musu kasan cewar su Imran na yawan yi musu karatun al Qur'ani mai girma a gidan, shi yasa tun ranar da suka ɓace basu sake dawowa ba, daman saboda tafiyar su Imran kano ne yasa abubuwan ke zuwa dan ba'a karatu kuma ba'a kunna kira'a, daman Abba da su Imran ke kunnawa, to shi Abba ya dawo ya samu bala'i ne shi yasa bai samu damar karatun ba, dan ita dai Hajiya Umaiya bata wani yin karatu Al Qur'ani sharholiyar ta kawai take, san nan faruwar wan nan abun yasa Hajiya Umaisha ta yi hankali sosai, ta rage wasu abubuwa yanzu duk wani hakkin miji tana kokarin ta sauke sa dan tsoron dodannin, yanzu ta dai na masifa da faɗa ta koma so silent kamar ba ita ba, daman shi kam Abba shiru shiru ne baya shiga har kan kowa abun da ke gaban sa kawai yake, haka suka koma ratuwar farincikin su kamar yadda suka saba. *ABUJA* Sosai a ka bawa Rimsha kulawa har sai da suka tabbatar ta dawo dai dai, daddy ya shiga damuwa over ji yake kamar zai yi kuka saboda kaunar da yake wa Rimsha gashi ta jefa kan ta cikin wahala. Basu bar hospital ba sai da daddy ya tabbatar da tasamu lafiya sosai san nan ya ansa magungu nan ta ya wuce ya suka shiga motar sa suka bar hospital ɗin, Rimsha ta samu sauki dan da kafar ta ta taka zuwa wajen motar daddy. Suna isa gida, suka isko mum gwaggo da Jehan a Palo zaune cikin damuwa ko wani hali Rimsha ke ciki, mum na ganin su ta miƙe tana faɗin "Ya jikin nata dai?" kallon face ɗin Rimsha daddy yayi kafin yace cikin zolaya "GAR ya bamu magani ai" cool murmushi Rimsha ta saki har sai da dimple nata ya lotsa open teeth nata ya bayyana ga hakoran nata a jere tsab sai kyalli suke kamar gonar audiga, hakan ba karamin kyau ya karawa kyakkyawar face nata ba, duk da cewa ta ɗan rame saboda zazzaɓin, sleeping eyes nata sun kara haske sosai sun kara girma saboda yar ramar da tayi. Riƙo hannun ta gwaggo tayi suka haura sama dan taje ta mata wanka ta huta, wucewa daddy yayi ta nufi bedroom na shi yana faɗin "Ina son magana da ke boɗɗi" cikin sauri mun tabi bayan sa ita kuma Jehan tabi su gwaggo. Zaune bakin gado ta isko sa yayi shiru kamar mai tunani wani abun, "lafiya daddyn Jehan?" Mum ta tambaya dai dai lokacin da take zama a gefen sa, dogon numfashi yaja tare da sauke wa a hankali ya ɗan juyo suna fiskantar juna "Wallahi ba lafiya ba" zaro ido waje mum tayi tana faɗin "Meke faruwa to?" Riko hannun ta daddy yayi ya fara magana cike da damuwa "kwana ki na ta tafiya zaɓe na ta kara gabatowa ni kuma sai kara samun baraza nake daga abokan ha mayya, baraza ta ko ina nake samu abun ya fara affecting ɗina na fara karaya, dan wasu ma ban san daga ina suke min barazanar ba, ina tsoron kada na jefa rayuwar ku a cikin haɗari bana son abun da zai taɓa min ku bana son tashin hankali ku, ina ganin zan hakura da siyasar nan kawai" cikin sauri mum tace "A'a barkama ni ban yarda da ka hakura da siyasa ba, kasan cewar adalin mutun irin ka mai gaskiya a siyasa babban nasara ne ga yan kasa, kana da tausayi kuma zaka taimakawa talakawa, na sani siyasa babban haɗari ne dan ba kowa yake son cigaba al'umma ba, amma jajirtattun mutane ire iren ka masu son tai makon talakawa bai kamata ku rinƙa karaya kuna sarewa haka ba, kama ta yayi ku rinƙa karawa kan ku kwarin gwiwa, na san cewa rayuwa a matsayin mai gaskiya yafi komai wahala a duniyar da muke ciki yanzu, dan dayawa daga cikin mutane sun ajiye gaskiya sun bi karya da ha inci a guje suna son kamawa su runguma, wasu ma har sun kama sun runguma ɗin sun yar da gaskiya, kayi rayuwa ba tare da cutar da wani ko tauye hakkin wasu ba yafi komai wahala a duniyar yanzu, babu mai tai makon ɗan uwan sa, jama'a da dama sun manta lahira sun rungumi duniya hannu bibbiyu, jama'a da dama sun manta cewa wanda ka bayar shi zaka tarar a lahira wanda kuma kaci a nan duniya zaka barshi, dan Allah barkama ka karawa kan ka karfin gwiwa wajen ganin ka tsaya tsayin daka ka ceto mana kasar mu, muna bukatar adalin shugaba irin ka, kasar mu na bukatar jajirtattun maza irin ka, aikin Allah na da wahala, ba'a shiga aljanna a na kwance a gado, duk wanda Allah keso da Rahma to sai ya jarrabe shi da wani abun, to ka ɗauka duk wan nan barazana da abokan hamayya suke maka jarabawa ce daga Allah, kuma ka dage ka ci jarabawar, san nan ka zauna da kowa zuciya ɗaya" duk wan nan hiran da suke cikin harshen turanci suke yin sa, dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin yace "Kin san me?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a "Meeting da naje ɗazun sai da nayi dana sanin shiga ta siyasa, saboda a fillin Allah wasu daga cikin manya ke min baraza a kan na janye tun yanzu abun ya tsorata ni, shi yasa nake tsoron kar na jefa rayuwar ku cikin haɗari" kwanciya mum tayi a jikin sa cikin sigar soyayya ta fara magana "Barkama ka sani fa kafin mutun yaji daɗi sai ya sha wahala, musamman ma mutun mai zuciyar gaskiya irin naka to fa sai ka daure ka kawar da kan ka daga kan wasu abubuwan idan ba haka ba bazaka taɓa cin ma nasara ba, a zamanin yanzun nan duk wanda yace zai fito fili ya nuna cewa shi gaskiya yake so tofa makiya ba zasu taɓa bari ya kai labari ba sai ya dage da kai wa Allah kukan sa, yanzu dai ka manta da komai ka ci-gaba da gwagwarmayan ka kana addu'a muma zamu taya ka, In Sha Allah ba dai ɗan adam ba, sai Allah ya cika maka burin ka na ganin ka taimaki talakawa kuma ka raya mana kasar mu ta girma kamar sauran manya manyan kasashe na duniya In Sha Allah" ta kai karshen maganar tana riƙo hannun sa, murmushi ya saki har sai da dimple nashi ya lotsa, cike da so da kauna yace "Shi yasa nake son ki matata duk lokacin da na shiga damuwa kin san yadda zaki yi ki kwantar min da hankali, duk wata natsala ta idan na kawo miki, ba za'a fi 10mins ba kike samo mana mafita, Allah ya miki albarka ki taya ni da addu'a In Sha Allah burin mu zai cika bari naje nayi wanka yanzu na fito sai mu ci-gaba da hirar ko?" Gyaɗa masa kai tayi tana faɗin "Amin ya Allah" ta kai karshen maganar tare da tashi daga jikin sa, miƙewa yayi ya nufi toilet ita kuma ta miƙe ta wuce wajen drawer kayan sa ta ciro masa kayan sawa da duk wani abun da zai buƙata ta dawo ta ajiye masa a bakin gado san nan ta haye saman gadon ta kwanta tana tunanin rayuwa. After some days *KADUNA* A yau Akil yazo yin sallama da Umaisha zai koma makaranta, sanye yake da manyan kaya wato wata dakakkiyar yadi navy blue mai bala'i kyau da tsada, ɗinkin half jomfa, kayan sun masa kyau, yau ma kamar kullun tsaye yake a kofar gida bai shiga ba, ya bawa gidan baya ya kifa kai da jikin mota kamar dai kullun, ya aiki mai gadi da ya kira masa matar sa, ko da mai gadi yaje Abbi baya nan ya tafi company shi kuma Irfan ya wuce Uk tun kwana biyu da suka wuce, gidan ya rage daga Umaisha sai Aafia, koda mai gadi ya sanar da su sakon Akil sai Umaisha tace "Kaje kace masa Abbi yace ya shigo ba zan kara fita ba" tayi maganar cike da tsoron abun da Akil ɗin zai mata sai dai kuma ta sawa ranta ko kashe ta zai yi bazata ki bin umarnin Abbin ta tabi na Akil ɗin ba. Ko da mai gadi ya isar masa da sakon da Umaisha tace, ko kaɗan Akil bai damu ba, ba musu ya shigo cikin gidan, kallon ɗaya zaka yiwa face nashi kasan yana cikin damuwa yau he look so silent kamar ba shi ba, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo palon already Aafia ta bar palon tun tafiyar mai gadi. Cikin sanyin murya Umaisha ta amsa masa sallamar, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kan sa tare da zama saman sofa, murya kasa kasa kamar mara lafiya yace "Jeki sanya hijabin ki kizo" da sauri tace "Yaya Akil a cikin gida ne fa ba waje ba" tsare ta yayi da ido na yan mintoci kafin yace "Ban isa in ce kiyi abu bane?" Girgiza masa kai tayi tare da miƙewa ta nufi bedroom na su, ajiyar zuciya ya sauke tare da jingina kan sa da jikin sofa, Jim kaɗan ta dawo cikin hijabi yana ja har kasa ɗan nesa da shi ta zauna tana faɗin "Ina wuni" tayi maganar tana kunbura kumatu, ɗagowa yayi ya zuba mata ido kasa kasa ya fara magana "Dan nace ki sanya hijabi ne kike ɓata rai haka?" Shiru ta masa tana jin haushi a zuciyar ta "Ina son ki sani duk macen da bata ɗauki hijabi a matsayin sutura ba ni a waje na da ita da dabba duk ɗaya ne, bana son mace da bata suturta jikin ta, bana son macen da bata daraja kan ta, hijabi shine darajar ya mace, ina son mace wayayyiya amma ba ballagaza ba, idan nace wayayyiya ina nufin mai wayewa irin ta addinin musulunci, ina matsayin yayan ki, kuma mijin ki, amma a yadda muke ni ban yarda da na rinƙa kallon ki haka ba hijabi ba, kuma ban kawo sadakin ki ba koda kuwa a cikin ɗakin uncle ne ba a palo ba, ina son kullun na ganki da hijabi har kasa idan nazo, yau bana jin daɗi jikina, bana son yawan magana dole ne yasa nazo miki sallama, ina son ki sani wallahi idan na tafi kika karya doka ɗaya daga cikin dokokin dana sanya miki wallahi 6 hours ya isa ya kawo ni in da kike, idan kuma nazo in ran ki yayi dubu sai na ɓata miki, san nan ki faɗa wa Uncle idan na dawo na nitsu zan kawo sadakin ki na ɗauke ki mu koma tare, abu na gaba ki faɗa wa Uncle ya dai na samin wasu dokoki tsakani na dake dan ke ɗin matata ce ko suna so ko basu so, dole ke matata ce, yanzu ma na shigo gidan nan ne ba dan komai ba sai dan bani da lafiya banason yawan hayaniya, amma daga yau ni ba zan sake shigowa ba, shi yasa ma ina dawowa zan kawo sadaki na ɗauke ki dan ba zan iya wan nan abun da uncle ke min nan ba" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ciro kuɗi daga aljihun sa masu yawa rafar 500 ya ɗaura mata saman hannun sofa ya nufi hanyar fita "Yaya Akil meke damun ka?" Cak ya tsaya tare da juyowa ya zuba mata ido, ganin bai amsa mata ba yasa ta sake mai mai ta tambayar, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Nima ban sani ba kawai bana jin daɗin jiki nane gaba ɗaya na rasa meke min daɗi" miƙewa tsaye tayi ta nufo sa tana faɗin "To kasha magani ne?" Zuba mata ido yayi ya kasa ɗauke idon sa daga kan ta, tun da yake bai taɓa tsayuwa ya kalli face nata da kyau ba sai yau, wow shine ka ɗai abun da yake furtawa a ransa, har ta iso gaban sa bai sani ba, cikin girmamawa tace "In kawo maka maganin zazzaɓi" girgiza mata kai yayi ala'mar a'a san nan ya juya ya nufi hanyar fita. Kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "To shi ne zaka tafi kuma bayan idan ka tafi yau sai bayan kusan shakara kafin na sake ganin ka" mamaki ne ya kama shi, a sukwane ya juyo cikin tsawa yace "Ke ni bana son munafurci yanzu kukan me kike?" Cike da tsoro tace "To ba kai ne zaka tafi ba kuma ni ban gan ka sosai ba idan ka tafi ya zan yi?" A fusace yace "A baya da baki sanni ba ya kike yi?" cak ta tsayar da kukan nata ta zuba masa ido, guntun tsaki yaja tare da wucewa abun sa, ya bar ta nan tayi mutuwar tsaye. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 19 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 EPISODE 19 Kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "To shi ne zaka tafi kuma bayan idan ka tafi yau sai bayan kusan shakara kafin na sake ganin ka" mamaki ne ya kama shi, a sukwane ya juyo cikin tsawa yace "Ke ni bana son munafurci yanzu kukan me kike?" Cike da tsoro tace "To ba kai ne zaka tafi ba kuma ni ban gan ka sosai ba idan ka tafi ya zan yi?" A fusace yace "A baya da baki sanni ba ya kike yi?" cak ta tsayar da kukan nata ta zuba masa ido, guntun tsaki yaja tare da wucewa abun sa, ya bar ta nan tayi mutuwar tsaye. Kai tsaye motar sa wuce, ko da ya shiga motar ya kasa tafiya ya zauna shiru kamar mai tunani, ba abun da ke masa yawo a kai face muryan Umaisha mu samman in tana masa shagwaɓa yana bala'i son ganin tana zuba masa shagwaɓa sosai, sai dai iyashege irin nasa ya hana ya rinƙa biye mata wai a cewar sa idan ya biye mata zata raina sa hakan yasa baya sake mata fuska. Almost 1 hour yana zaune cikin motar, ya kasa tafiya ji yake kamar ba zai iya komawa school ya bar ta ba, duk da zasu rinƙa waya hankalin sa bai kwanta ba, gani yake kamar zai yi nisa da bugun zuciyar sa, gani yake kamar idan ya tafi zai rasata, wan nan dalili yasa har zazzaɓi ta kama shi. Sai da ya kara 30 mins a wajen san nan ya kunna motar sa, da kyar ya iya jan motar ya bar wajen, ya nufi gida. A ɓangaren ita ma Umaisha sai da tayi tsayuwar 20 mins a wajen san nan ta ja kafar ta jiki ba kwari ta wuce bedroom na su, tana shiga ta kakalo murmushi dole tana faɗa wa Aafia yaya Akil ya koma school, guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Allah ya raka taki gona yan damuwa kawai, shi sa yaya Irfan ai ɗaya suke shi ma yaya Irfan har da wani cewa kar mu kuskura mu fita ba hijabi, wlh yanzu ma ina tashi in tafi gidan su Rufaidat in je in mata albishir Abbi yace zai biya mata School fees ta shiga school namu ita ma, kuma wlh babu hijabi babu gyalema zan tafi sai nafa uban da zai sani sawa" ta kai karshen maganar tare miƙewa ta hau shirin zuwa gidan su Rufaidat, ita kuma Umaisha gyara kwanciyar ta tayi a saman gado ta ɗauko wayar ta, ta shiga massage ta fara tsara massage na kalaman soyayya masu daɗi, dan ta turawa Akil, kirjin ta sai dukan uku uku yake tsoro take ji karya zageta ko ya mata faɗa dan ta san halin sa komai ba burgeshi yake ba shi, haka ta daure ta tsara masa kalamai masu daɗi da kwantar da hankalin masoyi, tana kammalawa ta tura masa ta kwanta tana jiran ko zai mata reply. Lokacin message ɗin ya shigo wayar sa yana tuƙi, da hannu ɗaya ya ɗauki wayar dan ya duba, ganin sakon ta yasa ya fara karanrawa cikin sauri, lokacin guda cool murmushi ya bayyana a kan face nashi har cikin ransa ya ji daɗin sosai, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kai wayar sai tin bakin sa ya mannawa wayar kiss nan take yaji zazzaɓin nasa ta gudu jikin sa ya ɗan warware, a hankali ya mayar da wayar ya ajiye, ya ci-gaba da tukun sa ba tare da ya mata reply ba, ita kuwa tana can tana jiran ko zai yi reply tana fargaban shin yaji daɗin massage ɗin ne ko bai ma karanta ba ne, har barci ya ɗauke ta Akil bai yi reply ba, ita kuma Aafia ta shirya cikin atamfa doguwar riga ɗinkin ya ɗan kama ta haka ta fice babu ko gyale, ta nufi gidan su Rufee, taxi ta shiga dan lokaci basu gama iya motar tasu ba, lokacin suke koya shi yasa ta shiga taxi. *KANO* Jiki ba kwari Imran yazo yin sallama da Jelly duk ya damu sosai dan bai son yin nisa da ita, ita kuwa sai murnar ganin sa take, sai faman washe baki take kamar wata zararriya, yaki faɗa mata zai koma ne daddy kawai ya faɗawa ita kuma yace mata kawai yazo ganin tane, sosai tayi murna, sun sha hira sosai, sai 3 na yamma san nan ya musu sallama ya kama hanyar Kaduna kamar zai yi kuka bai son rabuwa da Jelly ɗin sa, haka ba yadda ya iya, ya wuce Kd. *ABUJA* Zaune suke a palo dukkan su sai Jehan ita kaɗai ce bata nan, suna zaune suna yar hiran su, yayin da shi kuma daddy yake latsa wayar sa yana kallon yadda mutane ke accepting na shi a media kowa sai faɗi Nawazudden yake, ko ina sunan dake treading a media kenan, sai murmushi daddy yake yana jin daɗin hakan, ita kuwa Rimsha ta tada kai da cinyar mum tana karatun littfin husnul Muslim, ita kuma Gwaggo ta zubawa Tv ido tana kallon Sunnah Tv. babu ko sallama Jehan ta faɗo palon sai kwaɓe fuska take kamar wadda taga kashi ko wani abun kyamar. "My Jehan lafiya? Daddy ne ya tambaya yana kallon face ɗin ta, zama tayi gefen sa tana faɗin "Daddy ina kewar School ne" shafa kan ta yayi yana faɗin "To ai next week zaku koma ko? Gyaɗa masa kai tayi kafin tace "Daddy yau azumi saura kwana nawa?" Cikin sauri Rimsha tace "Remain 12 days fa" "did I ask you?" Cewar Jehan tayi maganar tana hararar Rimsha ɗin, murmushi Rimsha tayi tana faɗin "Sorry ASP Jehan or DPO or commission" turo baki Jehan tayi tana kokarin yin magana suka ji sallamar mai gadi, miƙewa daddy yayi ta nufi kofar palon yana amsa sallamar, kallon Gwaggo mum tayi kafin tace "Da alama barkama ya san da zuwa mai gadin nan fa" murmushi gwaggo tayi tace "Ni dai ba ruwa na kun fi kusa ai" mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "Mum i need to see your previous pictures before you got married to my dad nan take face ɗin mum ta sauya, nan take taji ba daɗi taji zuciyar ta na mata ciwo Jehan ta tuna mata baya, shiru tayi bata yi magana ba. Da sallama daddy ya dawo palon hannun sa ɗauke da carton irin na turo sako daga kasar wajen nan, a tsakiyar palon ya ajiye, da sauri Jehan ta miƙe ta kariso wajen tana faɗin "What is this daddy?" Miƙewa zaune Rimsha tayi ta zubawa daddy dara daran sleeping eyes ɗin nan nata ba tare da ta je wajen ba. Buɗe kwalin daddy yayi ya fara fito da kayan yana faɗin "Kaya na saya muku daga Dubai" ya kai karshen maganar tare da fitowa da Jehan wasu kayan masu kyau na yan kwallo dan Jehan a koi ta da son kayan yan kwallo sosai, daddy na kokarin yin magana Jehan ta ansa kayan daga hannun sa tana dariya ta wuce ta haye sama ta nufi bedroom na su dan taje ta gwada, girgiza kai kawai daddy yayi ya ci gaba da fito da kayan, ita dai Rimsha ta zuba masa dara daran sleeping eyes nata tana kallon yadda yake fitar da kayan, ɗago kai yayi yace "My siha close your eyes, i want to surprise you" ba musu ta ta rufe idon na ta, wani leda ya ɗauko daga cikin kwalin ya nufe ta, ya zauna gefen yana faɗin "now open your eyes" da sauri ta buɗe idon nata dan ta ƙagu ta ga me daddy zai mata surprise a kai, miƙa mata ledar yayi yana kallon face nata, cikin zumuɗi ta ansa tare da buɗewa a sukwane ta miƙe tsaye tana faɗin "What? Daddy am I dreaming or not?" Sosai daddy ke murmushi dan bashi da wani burin da ya wuce yaga farincikin yayan sa, wan nan murmushi dake kan face ɗin Rimsha ya fi masa abubuwa kaso 80 cikin ɗari na rayuwar sa. Fito da kayan Rimsha tayi tana ta dariya kamar bakin ta ba zai rufu ba, kyakkyawan dimple nata sai motsawa yake ga open teeth nata dake tsakanin fararen hakwaran ta kamar gonar audiga, cikin zumuɗi ta zuje zip ɗin jacket ɗin ta sanya a jikin ta tana faɗin "daddy ai na ka samu irin jacket ɗin GAR dan Allah" "Saya na yi mana, My siha daga Dubai na sai miki saboda son da kike wa guy ɗin shi ne na ga kuma yana yawan sanya irin jacket ɗin shiyasa na ɗauki hoton na tambaya wurare daban daban da kyar na samu a Dubai, na ɗau wajen 2 weeks ina neman jacket nan company company, su kan su company da suka buga jacket ɗin na tuntunɓe su ta number su na WhatsApp, amma sai suka ce min gaskiya iya shi kaɗai su kayiwa shi ya kawo sample suka masa dan haka ba zasu iya yi min ba, wan nan ma na hannun ki ba sak irin nashi bane copy ne babu irin na sa shi kaɗai suka bugawa" shiru Rimsha ta ɗan yi kafin tace "Daddy to shi ma copy ɗin yana da tsada ne? Dan naji a Tv sun ce Jacket ɗin na shi na da tsada sosai, gashi kuma yana da su kala kala, sai dai duk design ɗaya ne color ne daban daban" jinjina kai daddy yayi kafin yace "Hmmm My siha kuɗin da na sayi jacket nan ba zai faɗu ba ke dai kawai ki saka irin jacket na GAR ɗin ki ba sai kin ji kuɗin copy ɗin ba ma" juyawa tayi ta kalli mum kafin tace "Mum ya min kyau?" Mum da gwaggo har suna gaɗa baki wajen cewa "Ya miƙi kyau over Rimsha sai dai ya miki yawa sosai, Jacket ne har kasa gaskiya ki ajiye sai kin kara girma" make kafaɗa tayi tana faɗin "Ni ko yana ja a kasa ma ni sai na sa" shi dai daddy sai murmushi yake abun sa burin sa ya cika tun da Rimsha da Jehan sun yi murna, wuce wa ita ma Rimsha tayi ta nufi bedroom na su da jacket ɗin sanye a jikin ta wadda ya kai ma har idon sahu na kafar ta. Fito da sauran kayan daddy yayi ya bawa gwaggo nata san nan ya bawa mum nata wadda ya kasance irin ɗaya ne dana gwaggo Dubai jallabiyas ne masu kyau da tsada, shi ma ya sai wa kan sa Dubai jallabiya na maza masu kyau da tsada, miƙewa yayi da na shi ya wuce bedroom na shi, miƙewa ita ma mum tayi tabi bayan sa, ita kuma Gwaggo ta wuce bedroom nata dan taje ta ajiye kayan. "Washington DC* *08:00 am* Zaune suke gaba ɗayan su a palon kasa, Micheal, James, Jay, ko wan nen su kan shi na kan wayar sa yana latsawa yayi da shi kuma daddy yana hira da uncle Herry. A buge John ya shigo palon kwata kwata ya manta da Romeo ya dawo, Sanye yake da Bluetooth a kunnen sa, jikin ne sa sanye da wando crazy irin na shararrun yan duniya nan, yau yayi kitso bibbiyu ta gefe da gefen kan sa, yayin da jikin sa ke sanye da t-shirt baka mai zanen horo da jan kala a gaban, hannun sa wuyar sa duk sanye suke da chain na maza masu kyau da tsada, kallo ɗaya zaka masa ka san yau a cike da iya shege yake, taku yake ta baya baya ya shigo palon yana tafiya yana girgiza kai da jiki yana bibbiye wakar da yake ji daga ta cikin Bluetooth ɗin, kasan cewar su basa jin wakar da yake ji sai dai wanda yake bibbiyewa suke ji sai hakan ya musu ban bara koi saboda wakar yan china yake ji, shi dai Jay kallon tsantsar mahauakci ma yake masa, dan wakar da yake bi ɗin ma basu taɓa jin irin ta ba, idan yayi taku ɗaya sai ya tsaya ya tiki rawar sa iya son ransa kafin ya ci gaba da tafiya, gaba ɗayan su sun zuba musa ido suna kallon sa, ba karamin tausayi ya basu ba, dan da alama yau wine ɗin nasa tasa ya manta da Romeo ya dawo, shi ko ko ajikin sa dan daman mayen son rawa da waka ne kamar Michael Jackson, kai tsaye saman bene ya nufa ko kallon in da suke bai yi ba. Dai dai lokacin Romeo ya fito daga part na shi jikin sa sanye da wando jeans guntu zuwa gwiwar sa sai riga fara mara nauyi mai karamar hannu, yau ma kamar kullun ya ɗaure dark black curly hair sa da ta sha gyara sosai sai kyalli da kamshi take, ya ɗaure ta a bayan sa, kaɗan ya zubo masa ta gaba goshin sa kasan cewar gashin gaban goshin nasa ya ɗan yanke ta bata kai tsawon na bayan sa ba, hakan yasa bata iya kai wa ya haɗa da ita ya ɗaure shi yasa ko ya ɗaure gashin na shin nasa wan nan na gaban goshin bata shiga ya ɗaure da ita sai ta zubo masa a kyakkyawar face na shi, hakan kuma ba karamin kyau yake kara face na shi ba, kamar kullun yau ma a koi face mask a face nashi, wan nan daddaɗar fitinanniyar kamshin perfume nashi ne ya kai wa su Michael karo a hanci hakan ya sasu ɗagowa a sukwane kuma a tare har da su daddy, dan ko ina kamshin perfume ɗin ya gauraye gaba ɗaya duk girman palon, tun ma bai shigo cikin palon ba a sukwane su Michael suka kara nitsuwa kowa ya ajiye wayar sa dake hannun sa suka zubawa John dake rawa yana tafiya yana tinkarar Romeo dake kokarin sauko wa kasa, ganin John na zuwa a buge yasa Romeo tsayuwa ya zuba masa dara daran blue eyes na shin masu ɗaukan hankali nan yana kallon sa, duk wata halitta mai rai dake cikin palon sai da ta nitsu tsit ka ke ji ko numfashi a hankali suke fitar wa dan gudun shiga matsala, shi ko John sai kaɗan kai da hannu yake yana tafiya yana wani bouncing, ya sanya hannun sa ɗaya ya rinƙo wandon sa ta tsakiya dai dai sai tin gaban sa irin yadda gayu keyi, zuba masa ido gaba ɗaya palon suka yi yayin da shima Romeo ya zuba masa ido yana kallon gudun ruwan sa John bai an kara ba sai ji yayi ya daki kirjin mutun sai da yayi baya yayi tangal tangal ya faɗi kasa, a sukwane ya ɗago kai cikin muryan yan maye yace "Who is this?" kara waro ido sa waje yayi yana kallon Romeo, sai dai kash saboda shaye shayen da yayi ta sa bai gane ko wanene a wajen ba hakan yasa ya ja dogon tsaki tare da banko uban ashar yana kokarin miƙewa Raɓawa ta gefen sa Romeo yayi a nitse ya nufi hanyar fita ba tare da yace komai ba, har su James suna haɗa baki wajen cewa "Good morning Lion" jinjina musu kai yayi ba tare da yayi magana ba, ya wuce ya nufi waje dai dai lokacin Tga ya sauko daga saman benen shima face na shi sanye da face mask san nan kayan jikin sa kusan iri ɗaya da na Romeo, dai dai tsakiyar palon ya tsaya ya kalli su daddy cikin harshen turanci yace "Good morning daddy and uncle" da murna daddy da uncle Herry suka amsa masa, san nan suma su Micheal suka gai da shi a ta kaice ya amsa musu san nan ya nufi waje yabi bayan Romeo har ya kai bakin kofa ba tare da ya juyo ba yace "I want to see all of you know in my place, excluding uncle and dad, James come with John" ya kai karshen maganar ya fice daga palon tun da sukaji Tga yace su sa me sa a wan nan filin, jikin su ya fara kerma dan sun san shike nan horasu zai yi, dan wan nan fili daɗi baya kai mutun sai wahala, filline gari guda da Romeo ya saya kusa da gidan su wajen yake daga gidan su ta baya a koi kofa ta wajen zaka buɗe ka shi ga wajen, Musamman Romeo ya sayi fillin yasa a ka kawata masa wajen dan ya rinƙa basu horo a wajen, da sauri Michael, Jay, suka rufawa Tga baya, shi kuma James ya wuce yaje ya damko wuyar rigar John ya jawo sa suka nufi waje, sai zagi da sambatu John ke tayi amma James bai kula sa ba, komawa daddy da Uncle sukayi suka zauna, suna masu tausayawa John. Filline mai girman gaske an kawata wajen, ga wasu kyawawan kujeru a saman stair an sanya kyakkyawar runfa a wajen kujerun, kamar dai wajen hutawa, an raba wajen gida biyu rabi an sanya masu tiles, rabi kuma an sanya grass carpet mai kyau, fillin bai da faɗi sosai sai tsawon bala'i. Zaune saman sofa mai laushi ga kyau Tga ya isko Romeo zaune yana latsa wayar sa, kusa da shi Tga yaje ya zauna, cikin girmamawa yace "Good morning Lion" shiru Romeo ya ɗan yi na yan mintoci, kafin ya ɗago kan sa daga kan wayar sa, ya sanya kyakkyawan farin hannun sa gently ya zame face mask ɗin face na shi zuwa gemun sa, Subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangiji da yayi wan nan hallitar, kyakkyawa ne ajin farko, yana da face mai design mai kyau, ga dogon hanci har baka mai matikar kyau, soft skin na shi ba'a magana, kwance yake luf yaji hutu, bakin sa ɗan karami mai ɗauke da lips red color kamar ya sanya lipstick ja saboda kyau, idon sa kuwa kamar ya kara musu girma ne da ya cire first mask ɗin, dan har wani kyalli suka kara yi, gashin gerar san nan kamar an zana masa Calvin san nan suna cike dan kamar zasu haɗe saboda cikan kyakkyawar dark black gashin dake wajen, gefe da gefe kumatun sa dukka kyakkyawar dark black gashi ne kwan ce a wajen sai sheƙi da kyalli yake, kyau iya kyau kamar shi yayi kan sa Masha Allah. Slowly ya lumshe dara daran blue eyes ɗin nasa ya sake buɗe, tare da ɗagawa Tga kai ba tare da yayi magana ba, dai dai lokacin su Michael suka shigo wajen, slowly ya dawo da kallon sa kan su, sai sambatu John ke yi kamar zararre, A gaban su Tga James yazo ya durkusar da John, ya wuce ya zauna saman sofa, suma su Micheal wuce wa sukayi suka zauna saman sofa, John na kokarin miƙewa sai sambatu yake, slowly Romeo ya juyo da dara daran blue eyes na shi ya kalli Tga ba tare da yayi magana ba Da sauri Tga ya miƙe ya damko wuyar John tare da ware yatsun hannun sa kamar mai zagi, ya ɗaga hannun sama da karfi ya cakawa John yatsun nasa a cikin sa kusa da cibiyar sa, nan take John ya fara kwara amai, yana tari, kara caka masa yatsun nasa Tga yayi a karo na biyu, sosai John ke tari yana sheƙa amai, ganin yana amayar da wine ɗin ne yasa Tga ya sake sa ya koma kusa da Romeo ya zauna, yana kallon John ɗin , yayin da shi kuma Romeo ya miƙe gently ya taka stair ɗin ya sauƙo kasa ya nufi wata yar siririyar hanya dake cikin fillin. Sai da John ya amayar da gaba ɗaya wine ɗin da ya sha san nan ya kwanta a wajen na yan mintoci yana mai da numfashi, kafin ya ɗago kai yana kallon jama'ar dake wajen, while Tga ya sunkuyar da kan sa kasa yana latsa wayar Romeo da ya tashi ya bari a wajen, ihu John ya fasa lokacin da idon sa suka sauka kan Tga dan a tunanin sa Romeo ne, kasan cewar Tga ya sunkuyar da kai kasa, baka ganin kwayar idon sa jin ihun John yasa Tga ɗago kai, yana kallon sa, miƙewa zaune John yayi ya fara kuka, dan da Tga da Romeo duk mugun tar su kusan ɗaya, dan mafiyawanci lokaci ma Tga ke hukun ta masu laifi, shi Romeo sai idan abun yayi yawa yake sa bakin sa, bai cika shiga har kan su ba, amma dai idan ka kuskura ya damke ka tofa in ba kayi Sa'a ba sai na lahira ya fika jin daɗi, haka shima James ya kware wajen iya hora mutane ya iya mugun ta kamar Tga. Jibga jibgan Bodyguard biyu ne suka zo suka fara gyara wajen da John yayi amai, sai bayan sun gyare wajen tsab har da perfume suka sa, nan take wajen ya ɗau kamshi sosai, sai da suka gama san nan Romeo ya dawo wajen. In da ya tashi ya koma ya zauna tare da mai da face mask na face na shi, Tga na kokarin yin magana, bodyguard huɗu suka fito da manya manyan dawaki guda uku masu lafiya da ji da karfi, sun ci sun koshi sun samu kiwo mai kyau, sai daka sukuwa suke, daga farkon in da a ka sanya grass carpet ɗin nan bodyguard ɗin suka tsai da dawakin ba tare da sun saki linzamin su ba, kallon John Tga yayi a ta kai ce yace "Get ready" in da sabo John ya saba dan wan nan ɗaya ne daga cikin salon hukuncin Tga da Romeo, basu cika bugun mutun ba sai ta kama dole amma horo kala kala na mugunta sun iya kallon John ɗin James yayi kafin yace "Ko dai wine ɗin bata sake ka bane? Na ga ka kasa tashi kamar ba da kai a ke magana ba, ko dai sai nazo nayi nawa ne?!!" A hankali John ya miƙe dan wine ɗin ta sake sa tsab kamar ma bai sha ba, kasa ya sauko ya tsaya wajen da a ka sanya tiles while su kuma dawakin suna ɗan gefe wajen grass carpet counting from one to three Tga yayi, yana kai wa three bodyguard ɗin suka saki linzamin dawakin, yayin da shi kuma John ya kwasa a guje, suma dawakin sukuwa sukayi kafin su fara gudu, dam, dam, dam, kallo ɗaya zaka yiwa dawakin kasan a kan hakan a ka horasu, ka ida shi ne idan ka bari dawakin nan ɗaya ya wuce ka sai ka karɓi hukunci mai tsanani, wan nan ɗaya ne daga cikin punishment da Romeo ke musu. Sosai John ke gudu kamar zai tashi sama, ga tsantsin tiles kamar zai faɗi kasa, gashi ba halin cire ta kalma, dan yana ɗan tsayawa dawakin nan dazu wuce sa, duk da yasan daman dole zasu wuce sa dan ba wanda ya taɓa cin wan nan jarabawar ta Romeo amma duk da haka zagewa suke suta sharara gudu kamar zasu tashi sama, haka suma dawakin suke sharara gudu dan sun san gasa ce, John dai yana gudu yana kuka, sai dariya Jay ke masa yana masa mugun addu'a dan daman rashin kunyar John da Michael ya ishe sa a gidan "Where is your exam card Michael?" Cewar Tga, kallon Romeo Michael yayi kafin yace "I already discussed this issue with lion" kallon Romeo Tga yayi, yana faɗin "is that so?" Jinjina masa kai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, yana latsar wayar sa "Okey what about James, it's better for him to start work?"Jay ne ya ansa zancen da cewa "Gaskiya is better, dan ya kammala karatu ba shi da aiki sai zuwa clubs da partys" girgiza kai Romeo yayi gently ya miƙe ya nufi hanyar sauka daga wajen cikin nitsuwa da sexy voice na shin nan yace "I will think about it" yana kai karshen maganar ya fice daga wajen, Romeo ko mai na shi a nitse yake yin sa, san nan komai daki daki yake bin sa ɗaya bayan ɗaya, baya son hargagi da rashin nitsuwa a lamuran sa, bai taɓa damuwa da yan uwan sa sai sun yi aiki ba, shi a ganin sa dukiyar sa ya ishe su da suji daɗin duniyar su, shi yasa yake sake musu kuɗi baya damuwa da lallai sai ya san abun da suke saboda ya yarda da su, a baya kafin yanzu baya basu kuɗi sosai lokacin da James ke School wan nan dalilin yasa James ya shiga wan nan har kan, daga baya bayan ya kammala school Romeo ya fara sake musu kuɗi over dan a cewar sa yanzu sun yi hankali, bai taɓa bibiyar su ko bincikan su dan yaga me suke ba, dan ya basu yarda 100, yana bala'i son su fiye da tunanin mai tunani, amma duk da wan nan son da yake musu baya hanawa ya basu horo idan suka masa ba dai dai ba, duk cikin yan uwan sa yafi son Michael hakan yasa ko Michael yayi laifi baya iya hukun ta shi dan yana kaunar sa over, bai taɓa hora Michael ba, idan Michael yayi laifi a gaban kowa, kowa yaga yayi laifin kuma sun san yayi laifin, sai Romeo ya fiske yace Tga ya hukun tashi ko kuma James, gaba ɗayan su daga James ɗin har Tga ɗin basa iya hukun ta Michael ɗin saboda son da suke masa, shi yasa Michael ke zuba tsiyar sa iya son ran sa, yanzu haka jiya da daddare yaje ya samu Romeo ya rinƙa zuba masa kukan shagwaɓa yana rokan sa da yayi hakuri a kan bai rubuta Exam ba amma next time yayi alƙawarin zai rubuta, sosai Romeo ya masa faɗa a kan ya tsaya yayi karatu, amma ya kasa hukun ta shi, su uncle Herry duk sun fi kaunar Michael fiye da kowa, sosai Romeo ke sakar masa kuɗi yana abun da ya ga dama, sai dai yana da kyau ta over da mutun ya roke sa zai bada, abokan sa su dest duk ya sai musu motocin hawa, a School na su kowa ya san shi da kyauta idan ka cire tsoro kazo ka tambaye sa tofa zai baka abun da ma baka taɓa zato ba, haka zalika duk kuɗin nan da Romeo ke bashi hakan bai sa ya nemi matan ban za ba, shi mace ma bata gaban sa, saboda gani yake halin su ɗaya da mum ɗin sa, a baya yana shaye shaye daga baya yazo ya dai na saboda wani friend na shi dake hana shi, kuma yana kaunar abokin nasa over, duk sati yana zuwa gidan gajiyayyu da marayu ya ta raba musu abubuwa kamar dai yadda yaga Romeo na yi, sai dai shi Romeo har da church ɗin su yake bawa taimako shi kuma Michael saboda tsanar da yayi wa Pasto church ɗin ma sai an yi da gaske yake zuwa kuma baya bawa Pasto ko biyar, idan yaje church ɗin ma baya sauraron komai da suke faɗe, saboda gani yake ba amfani, dan bai da ilimi ba karatu yayi ba shi gani yake ɓata masa lokaci kawai suke da surutun banza, kan sa emty yake duk mate na shi a School wasu sun zama lectures wasu kuma sun kama aikin yi amma shi yana nan sai jagaliyanci ya sa a gaba, wan nan dalilin ne yasa ba abun da ya sani sai kashe kuɗi da zuwa party clubs da abokan sa, hakan yasa yake kallon Pasto a matsayin mahaukaci mara aikin yi, shi kwanta kwata bai yarda da wasu addinai ba a cewar sa duk adinin nan ɓata lokaci ne. Bari mu leƙa Nigeria mu dawo *KADUNA* Har bakin hanya Rufaidat ta rako Aafia sai murna take tana zuba mata godiya, ita kuma Aafia sai fatan alkhari take wa Rufaidat da fatan ta tsaya tayi karatu da kyau, dan karatu shi ne mutun, anguwar nasu shiru ba hayani sosai, shi kan shi bakin hanyar ba jama'a sosai, kafa ta ɗauke saboda ba babban hanya bane, irin kana nan titin nan ne dake ratsawa ta cikin layi suna tsaye a bakin hanya suna jiran taxi yazo Aafia ta hau ta koma gida, wata dankareriyar mota kirar *Mercedes-Benz* tazo tayi parking a gaban su, a hankali mamallakin motar ya sauke glass ɗin motar sa, babban Alajine mai ɗan yawan shekaru, dan a kalla zai kai, 45 to 47 years, sanye yake cikin manyan kayan hausawa da hula, yayi shiga irin ta kamala da cikar bahaushe, nan take Aafia ta ɗaure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ita kuma Rufaidat sai washe baki take an ga mai kuɗi. "Sannun ku yan mata" Alhajin ya faɗa yana washe baki, cikin sauri Rufee tace "Yauwa Alhaji Sannun ka" ita kuwa Aafia ko kallon in da yake ba tayi ba dan a koi ta da jiji da kai over "Yan mata idan ba damuwa ku shigo na kai ku in da zaku je mana, dan baku yi kalar tsayuwa cikin ranar nan ba" yana magana yana kallon Aafia, kara washe baki Rufee tayi tace "Kawata ce kaɗai zata tafi ita zaka ragewa hanya ni kuma ga gidan mu a nan idan ka dawo" a sukwane Aafia ta juyo tana kallon Rufee da mamaki, wato ita rufe har tallan kan ta take, shi kuwa Alhaji washe baki yayi tare da shafa gemun sa yana faɗin "Daman ai kawar taki ita ta tsai dani" hannu Aafia ta miƙawa Rufee suka gaisa, san nan tace "Sai kin zo gida ko sai mun haɗu ga taxi nan zuwa na wuce" "Wow gaskiya izzar ki ya kara burgeni ba kaɗan ba, hakan ya sa naji na kara son ki" cewar Alhaji, ita kuwa Aafia wucewa tayi abun ta, ta tari taxi ɗin da yazo ta shiga, cikin sauri Alhaji ya buɗe motar ya fito waje ya nufi wajen taxi ɗin yana faɗin "Dakata malam, haba yan mata, dan Allah ki tsaya mana, minti biyu kawai nake bukata daga gareki" a kule Aafia tace "Kai malam ko in ce baba, kai baka ji kunyar tare yarinya sa'ar yar cikin ka kace kana so ba, to idan kai baka san kunya ba ni na san shi, kai mai taxi muje!!!" Ta kai karshen maganar cikin faɗa, kunna taxi ɗin mai taxin yayi suka bar wajen sai magana Alhaji yake amma Aafia taki kula shi Sai da taxi ɗin ya kurewa ganin sa san nan ya juya cikin sauri ya koma cikin motar sa, cikin rangwaɗa Rufee tace "Alhaji ai daman ni nasan ba zata saurare ka ba, saboda bata da mutunci ga girman kai da izzar banza, ga rashin kunya da rashin girmama manya, amma ni ba ruwana ina girmama manya musamman irin ka mai kima da daraja" kakalo murmushi dole Alhajin yayi kafin yace "Nagode" tana kokarin sake magana sai ga yayan ta Yusuf, a sukwane ta wuce ta nufi gida ba dan taso ba, dan tana bala'i tsoron Yusuf, bashi da wasa ko kaɗan shi kuwa Yusuf cikin fushi ya nufo Alhaji, yayin da Alhajin ke kokarin kunna motar sa yabi bayan Aafia. "Kai malam wanene kai?" Cewar Yusuf, shiru Alhajin yayiwa Yusuf bai yi magana ba, kasan cewar Yusuf mutun ne mafaɗa ci hakan yasa ya fara faɗa "Wato kune irin Alhazawan dake ɓata yaran talakawan ko? To wlh ƙanwata tafi karfin ka idan ka kuskura na sake ganin kafar ka a layin nan wlh sai ran ka ya ɓaci bar ganin kana da kuɗi, maganin ka zan yi, a kan kanena bani da mutunci" ba karamin ɓatawa Alhajin nan rai Yusuf yayi ba, gashi ya dakatar da shi daga bin Aafia, cikin fushi ya juyo da idon sa kan Yusuf, nan take idon nasa suka sauya launi suka koma light purple mai bala'i haske kamar torchlight, hasken na haska face ɗin Yusuf, Yusuf ya zube kasa a wajen sai gawa, a guje Alhaji ya ja motar sa ya bar layin. sai da ya ɗan yi nisa san nan ya dakatar da motar tasa tare da canza kalar idon sa ya koma irin na mutane, fari da baki, haɗe da canza kalar face nashi da jikin sa dukka ya zama matashi mai jini a jika wadda ba zai wuci 25 years ba kyakkyawa fari tas da shi kamar balarabe, san nan ya ja motar yabi hanyar da su Aafia suka bi, ko zai gan ta. *KANO* Daddyn Jelly ya shiga damuwar da har ta jawo masa rashin lafiya mai tsanani dan shi a gaskiya ba zai iya cin amana ba, gashi yana tsoron video sa ta fita wa duniya, tun jelly bata iya gane daddyn ta na cikin damuwa har tazo ta fara ganewa, duk in ta tambaye sa sai yace mata ba komai, haka ta ci-gaba da hakuri, gashi su biyu suke rayuwar su sai Nana da Zuwaira masu aikin su, yan uwan maman Jelly suna zuwa time to time, iyayen Mahaifiyar Jelly sunyi sunyi a kan daddyn Jelly ya auri kanwar Hajiya Umaima wato mum ɗin Jelly amma yaki yadda yace shi baya so, ba zai iya rayuwa da kowa ce mace ce ba, dan shi gani yake ko kan kanwar Hajiya Umaima ɗin ma ba zata iya kula masa da Jelly ba, yafi son ya kula da kayan sa shi da kan sa, shi yasa ya zaɓi suyi rayuwar su su buyu, ko hutu baya barin Jelly taje wajen family maman ta baya son komai ya raba ta da gida in ba school ba. *Washington DC* Tun John na iya gudu har ya kasa dan already dawakan ma sun riga sun jima da wuce sa, shi kuma Romeo ya wuce ya bar wajen tun tuni, yau Tga ne ya hukun ta John, ya hora John iya horar wa, kafin ya kyale sa tare da yi masa kashe di a kan kar ya sake sha wine ya shigo cikin gida a buge, idan zai sha ya nitsu waje guda ya sha kuma ya kwanta a wajen yayi barci har sai ta sake sa, gidan su gidan mutun ci ne a kasar dan haka ya kiyaye shan wine yana yawo a sakar gari kamar mahaukaci kar ya ja musu zagi da zub da mutunci, sosai John ya niku tillis da kyar ma yake magana, sai murna Jay yake an masa magani John yau, da haka suka watse kowa ya nufi part na shi. *12:30 am* Duniya duk suna barci shi kuma Romeo a lokacin bodyguard ɗin sa ke serving nasa abinci, kamar wani aljani, while shi kuma James yana kwance saman katafaren gadon sa yana aiki a system na sa, yana shirya ta yadda zai sa mai gidan sa ya janye daga aikin kashe GAR. Zaune Romeo yake saman table chair na palon kasa ga jibga jibgan Bodyguard guda 24 a kan sa 12 ta gefen nan 12 ta gefen nan, kamar dai yadda suka saba, palon gaba ɗaya gauraye yake da hasken kwayayen lantarki dake manne a saman POP palon, har wutan jikin staircase a kunnen suke, shi yasa palon yayi haske over, hakan ba karamin kara kawata palon yayi ba gwanin kyau da ɗaukan hankali, ga sanyin Ac da kamshi air freshener da ya haɗu da kamshin perfume ɗin Romeo hakan ya bada wata irinyar fitinanniyar kamshin mai kwatar da hankali mai shaƙa sanye Romeo yake da kayan barci, riga fara kal mai jikin bargo zuwa gwiwar sa mai ma ɗauki a tsakiyar rigar, while gaban rigar a buɗe, ga wani kwantatciyar dark black gashi mai tsantsi da sheki kwance a saman faffaɗar kirjin nasa, soft skin na shin nan sai sheki yake kamar bai taɓa fita waje ba, sai faman lumshe dara daran blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan lips na shin nan sun kara zama red sosai saboda ya ɗan cizasu kamar wadda wani abun ya ɓata wa rai, hakan yasa suka kara ja sosai, lips na shin sun kasan ce kamar audiga saboda laushi shi yasa da ya ɗan ciza su kaɗan sai su kara ja. Duk wani abun da zai buƙata bodyguard ɗin sun zuba masa a plate kasan cewar sun san koda sun tambaye sa ba amsa musu zai yi ba, hakan yasa daddy ya faɗa musu abubuwan da yafi buƙa ta da yazo dining table su zuba masa, shi yasa da yazo suke serving na shi kawai. Almost 20 mins yana zaune yana latsa waya sai faman lumshe dara daran ido sa yake yana ɗan cije lallausan lips na shi, ga abinci kuma bodyguard sun zuba masa. A ɓangaren James kuma bayan ya kammala shirye shiryen sa sai ya kira mum ɗin su a waya, dan su gaisa, duk da ba wani son ta yake ba kuma yana jin haushin ta hakan baya hana shi, duk bayan 1 year ya kirata su gaisa, ba ƙaramin daɗin hakan take ji ba, saboda son da take musu amma shi Romeo da Michael da Tga, da dad, uncle Herry, ko da wasa basu taɓa kiran ta a waya ba ba kuma su taɓa kusan tar in da take ba, Mahaifiyar su baturiyar cikin New York ce, a halin yanzu ma tana zaune a can New York ɗin, tsakanin Washington DC da New York babu wani nisa sosai amma ko da wasa basu taɓa tunanin ma su kai mata ziyara ba, sun tsani ganin ta basa son ta ko kaɗan ta sanadiyar haka ne Michael da Romeo suka tsani dukka mata, dan su sunfi tsanar ta. Sai daɗi mum take ji da James ya kirata, suna gaisawa ya tambaye ta ko tana buƙatar kuɗi, cikin murna tace masa a'a kiran da ya mata ma yafi mata komai a duniya, yana jin bata bukatar komai ya katse kiran sa, tayi kokarin kiran sa amma ina bata same sa ba, dan in ya kira ta suna gama waya yake sata a blacklist dan ma kar ta sake kiran sa, dan ba wani son ta yake ba kawai tana ɗan bashi tausayi ne shi yasa yake kira yaji ko tana bukatar wani abun ko kuɗi Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 20 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 EPISODE 20 Sai daɗi mum take ji da James ya kirata, suna gaisawa ya tambaye ta ko tana buƙatar kuɗi, cikin murna tace masa a'a kiran da ya mata ma yafi mata komai a duniya, yana jin bata bukatar komai ya katse kiran sa, tayi kokarin kiran sa amma ina bata same sa ba, dan in ya kira ta suna gama waya yake sata a blacklist dan ma kar ta sake kiran sa, dan ba wani son ta yake ba kawai tana ɗan bashi tausayi ne shi yasa yake kira yaji ko tana bukatar wani abun ko kuɗi Ajiye wayar yayi saman bedside drawer ya ɗauki remote ya kashe wutar ɗakin gaba ɗaya, san nan ya kunna lamp na saman bedside drawer, tare da jan bargo zuwa saman kirjin sa ya lumshe ido, amma ya kasa barci sai tunani yake a kan yadda zai ɓullowa ramarin aikin da a ka sa shi na kisan GAR, dan gaskiya zai iya kashe kowa idan suka bashi aikin hakan amma ban da GAR, ba zai iya wan nan aikin ba, ko wani ya gani zai cutar masa da ɗan uwan sa na jini sai in sa karfin sa ya kare bare kuma a ce shi da kan sa kai ina hakan ba zai yiwu ba, gashi kuma baya jin kamar zai iya fita daga kungiyar nan nasu, dan yana son aikin sosai da sosai, Yasan cewa shi ne yake da hanya mafi sauki da zai iya kashe GAR cikin ruwan sanyi ba tare da shan wahala ba, amma ko a mafarki yayi mafarkin hakan to idan ya tashi sai ya hukun ta kan shi, yanzu shi babban damuwar sa a nan shi ne idan shi yaki yarda ya kashe GAR to fa zasu bawa wani aikin, gashi kuma GAR bai damu ya yawo da sojoji ko bodyguard sosai ba kasan yana ganin kamar ba wata damuwa, amma time to time yana fita da sojoji sosai. Haka dai ya rinƙa tunane tunanen sa na neman mafita har barci yayi awon gaba da shi. A ɓangaren Romeo kuwa, hankali sa kwance yake ɗaukan fruit da bodyguard suka yayyan ka masa suka shake masa plate da su, hankalin kwance cikin nutsuwa yake ɗauka yake kaiwa ɗan ƙaramin bakin sa, a hankali yake motsa laɓɓan sa kamar bai son tauna abu haka yake cin fruits ɗin, da yaci kaɗan bodyguard ɗin jikin su na kerma zasu muƙo masa tissue paper, wani lokaci ya ansa ya goge bakin sa wani zubin kuma yayi kamar bai gan su ba, haka zasu mai da, suna tsai tsaye kamar wasu saƙaguna ko alamar barci babu a idon su, shi kuma yana zaune sai latsa waya yake yana cin fruits a hankali cike da class da izza. Sai 01:00 am, san nan Romeo ya miƙe cikin nitsuwa ya nufi bedroom na shi, yana tafiya suma bodyguard ɗin suka nufi waje dan suje su kwanta su hutu, kasan cewar dama Romeo shi ne mutun na karshe dake cin abinci kullun, dan wani lokaci ma sai 2 na dare yake cin abinci kamar wani aljani sai dai ba wani abun kirki yake ci da daddaren ba baya wuce fruits ko kuma salmon, to da zarar yaci abincin daren sa ya wuce bedroom suma bodyguard ɗin zasu wuce nasu bedroom ɗin sai kuma da safe idan za'ayi breakfast sai suzo wajen table ɗin dan suyi serving masu cin abinci, sojoji uku ne ke girka musu abincin a gidan, idan sun gama kirkin su Romeo sai su fara girkin nasu bodyguard da sauran sojojin dake gidan, mai shara da mopping a gidan dukka sojiji ne, duk wani aiki na gidan jibga jibgan sojoji masu razanar da zuciyar maza ke yin sa. Romeo na shiga bedroom na shi ya haye katafaren lallausan gadon sa mai kama da audiga, daman sai lumshe dara daran idon nasa yake alamar yana jin barci, bedroom ɗin gauraye yake da gasken wuta lantarki launin sky blue, hakan ba karamin karawa bedroom ɗin kyau yayi ba, kashe wutar ɗakin gaba ɗaya yayi har da na jikin furniture ɗin da lamp na saman bedside drawer duk ya kashe su dan shi bai son haske idan zai yi barci, nan take ɗakin ya gauraye da duhu, remote ya ɗauka ya kara gudun Ac san nan ya ja lallausan bargon sa mai kama da audiga zuwa saman faffaɗar kirjin sa, ba jimawa barci yayi awon gaba da shi. *NIGERIA* *KADUNA* Matasan unguwa ne suka fito yuka samu Yusuf yashe a kasa ya rasu, sosai suka sha mamaki da jimami abun da ya faru, wasu daga cikin abokan sa sai cewa suke yanzu fa suka rabu da Yusuf lafiyar shi kalau, wasu kuwa cewa suke an ya ba wani abun ne ya samu Yusuf ba, haka dai jama'a sukayi ta ceceku ce. Sai washegari a kai masa sutura a ka kaishi makwancin sa wato gabarin sa, sosai mahaifiyar su Rufee tashiga damuwa da tashin hankali dan Yusuf shi ne karfin gidan, ita kam Rufee bata wani damu sosai ba kuka iya na yan mintoci tayi daga nan ta dasa daga in da ta tsaya, ba wanda ya iya gane me yayi sanadiyar mutuwar Yusuf, kowa ya bar abun a matsayin karar kwana, alokacin da abun ya faru a koi matasa guda biyu dake zaune kofar gidan su, a kan idon su komai ya faru amma sun manta komai sun kasa tunawa, abun ya wuce musu kamar basu gani ba. A ɓangaren ita kuwa Aafia kai tsaye unguwar su ta wuce Allah ya taimake ta wan nan Alhaji bai samu damar ganin taba har ta shige gida, shima mai taxi ɗin da ya tashi dawowa sai bai bi hanyar da suka bi suka zo ba, sai ya canza hanya, hakan yasa bai haɗu da Alhajin ba. Ko da Aafia ta shiga gida Umaisha na sharara barcin ta cikin kwanciyar hankali, tsaki Aafia taja ta wuce toilet dan tayi wan ka. *ABUJA* Kwance tashi babu wuya a wajen Allah a yau a ka ɗauki azumi, tun karfe 10 Jehan ke zubawa Gwaggo da mum kukan shagwaɓa wai ba zata iya kai azumin ba, while ita ma Rimsha tasha kukan ta koshi ne ta hakura mum tace wa Rimsha ta karya azumin amma taki tace ita kam bazata karya ba zata kai, sai kukan yinwa take amma taki yarda ta karya azumin, ita kuma Jehan sai cewa take zata karya mum ta hana ta saboda a lokacin ta fara kirgan dangi ta kirma tana da 13 to 14 years azumi ya haukan ta dan duk alamomin balaga sun bayyana a jikin ta, amma ta dage ita sai ta karya azumin dan ba zata iya ba, ga Rimsha bai war Allah ita da azumi bai hau kan ta bama ta zage sai ta kai bazata karya ba, sai kukan yinwa take, yayin da shi kuma daddy ya tafi wajen meeting bai dawo ba sai 2 pm. Ko da ya dawo zama sukayi a palo shi da gwaggo da mum suka fara lissafin abubuwan sadaka da zai sayawa bayin Allah, while lokacin Jehan da Rimsha sunyi barci wahala da yinwa, daddy yaso a tasan masa su dan yaji su kuma ra'ayin me suke da shi a kan abubuwan sadaka da zai saya, amma mum tace ya kyale su dan ba barcin daɗi sukayi ba, hakan yasa ya hakura ya kyale su ba dan yaso ba. Mum tace ya sai atampopi manyan bundir kamar guda ɗari da shadduji, hijabai, takalma, ya kai wa gajiyayyu da marasa karfi tare da marayu, ita kuma Gwaggo tace ya haɗa da kayan abinci, kama daga shinkafa, taliya, mai, manja, maggi, macaronic, indomie, sugar, madara, da dai sauran kayan abinci suje su rabawa gidajen marayu da kauyukan dake cikin wahala duk kan su daddy ya karɓi shawarar su, ya kira Uncle Shitu a waya ya sanar masa abubuwan da zasu saya, sukayi lissafi ya tura masa kuɗi, a kan ya saya ya rabawa talakawa da mabukara, sai fatan alkhari Mum da gwaggo ke masa, tare da fatan sumun nasara a siyasar sa, sai murmushi yake yana amsawa da amin, yana mai jin matikar kaunar family sa a ran sa, da haka suka zauna suka rinƙa hiran duniya da abun dake faruwa a cikin ta. *KANO* Sosai shima daddyn Jelly ya sai kayan sadaka irin su kayan abinci, da kayan sawa ya rinƙa rabar wa marasa karfi masu buƙata, da niyar Allah ya fitar da shi daga kuncin da yake ciki. Yana zaune a palo yayi shiru yana tunani, damuwa ta masa yawa ya rasa ina zai sa ransa ya rasa mafita duk ta in da ya tuna sai yaji ba gwara, ya buga uban takumi ga yinwar azumi na damun sa Da gudu Jelly ta fito daga bedroom nasu hannun ta riƙe da wayar sa tana faɗin "Daddy yaya Imran want to talk to you" ta kai karshen maganar tare da faɗa wa jikin sa tana kokarin miƙa masa wayar, hannu yasa ya ansa wayar tare da karawa a kunnen sa yana faɗin "Assalamu alaikum Imran ya kake?" Daga ɗayan ɓangaren Imran yace "Amin Waalaikumussalam bappa ina wuni" murya a dashe daddyn Jelly ya amsa da "Lafiya lou Alhadulillah ya School" ba tare da Imran ya amsa tambayar ba yace "Bappa Jelly ta faɗa min wani abun da ya tayar min da hankali yanzun nan shin da gaske ne?" Waro ido waje daddy yayi yana faɗin "Me tace maka?" "yanzu kiran da ta min ɗin nan tace min a koi wanda ya kiraka a waya ta ɗauka taji yana faɗin wai ka tura masa 100 millon ko kuma ya saki video ka wa duniya, to ina son sanin wanene wan nan bappa ni ban damu dana san a kan wani video a ke magana ba, kawai ina son in san me matsalar sa da kai" kara waro ido waje daddy yayi lokacin guda yaji jikin sa ya warware tsananin tashin hankali da firgici ne suka bayyana a kan face ɗin sa, kirjin sa sai dukan uku uku yake, nan take zufa ta fara karyo masa faɗi yake ina zan sa kai na ni Maik, a zuciyar sa, yayi shiru ya kasa magana dan yaji gaba ɗaya harshen sa ya masa nauyi, jin daddy yayi shiru sai wani irin numfashi yake fitar wane yasa Imran ya gane eh gaskiyan Jelly bappan sa na cikin damuwa. A nitsa yace "Bappa dan Allah ka kafaɗa min kaji ko dai sai nazo ne zaka faɗa min ɗin?" Da kyar daddy ya iya cewa "Aa Imran ba sai kazo ba" yayi maganar kamar zai sa ihu saboda damuwa da suka cunkushe masa waje guda, zuchiyar sa kamar zata fashe saboda zafin raɗaɗin azaban ciwon da take masa. "Bappa to meke faruwa? Dan girman Allah ka faɗa min ko zan samu sauƙi a rai na" shiru daddy ya ɗanyi kafin ya fara bawa Imran labarin duk abun da yake faruwa na takarar da suke da baban Muneer sai dai ya ɓoye masa batun video, da kuma abun da ya shiga tsakanin su da P.A ya dai cewa Imran baban Muneer na masa baraza na da wani abu wadda ya zama wani sashe na rugujewar rayuwar sa, amma kada Imran ɗin ya tambaye sa menene wan nan dan Allah shiru Imran yayi na ɗan wani lokaci kafin yace "Bappa nayi nisa amma duk time da na dawo sai na sa anyi maganin mutumin nan, yanzu dai shawarar da zamu yi a nan shi ne ka fito kace ka sayar min da company kawai kaga ba wanda ya sanni a Kano ba wanda ya san ni ɗan yayan kane, san nan yadda zumuncin mu yake nan ba wanda ya san ma kana da yaya, to ina son kafito ka ce masa kasayar min da company idan ta kama ma muyi cinikin boge a gaban sa sai muyi, ka sauya tsare tsaren company ta yadda zai gamsu ka sai da min ɗin, zaka iya mai da takardun ma da sunana na wani ɗan lokacin, in yaso daga baya sai mu gyara komai, yanzu ka zauna a matsayin aiki na baka a company, shikenan dole ya kyale ka ta fannin company kam, tun da ba company ka bane a idon sa, kaga zaka samu ka gudanar da aikin ka yadda ya dace kenan" cool murmushi daddy yasaki wadda rabon sa da yayi ta harya manta, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Kai amma naji daɗi sosai Imran" "Ba komai bappa all the best, yauwa san nan nasan zai na tambayar ka kuɗi tun da yanzu ma kuɗi ya kira ya tambaya Allah yasa wayar na hanun Jelly ta ɗauka taji, to idan ya tambaye ka karka rinƙa bashi kaje ka buɗe wani account ka kwashe kuɗin ka dukka ka zuba a sabon account ɗin sai ka rinƙa nuna masa balance na tsohon account ɗin, kace masa wanda ya saya company ma bai biya kuɗin ba kaɗan ya baka yace sai gaba yanzu baka da kuɗi dan aiki kake a karkashin wani, na lura bashi da ilimi ko kaɗan jahiline, dan mai yiwuwa result ɗin ma ta karfi ya ansa, dan abun da yayin nan mai ilimi ba zai yi shi ba, to dan haka sai mu rai na masa hankali tun da jahiline, kasam dai yadda zakayi kana kauce masa har na dawo, ina dawowa zanyi maganin sa" sosai daddy yaji daɗin maganganu Imran harma ya rinƙa zubawa Imran ɗin godiya da Addua'o'i fatan Alkhari, daga haka suka yi sallama da fara'a ya miƙe ya ɗauki Jelly cak suka nufi bedroom, yau da kan sa ya mata wanka, sabanin a baya tun da abun nan ya faru su Zuwaira ke mata wanka dan shi lokaci kwata kwata baya tare da mutane yana can duniyar tunanin mafita. Sosai itama Jelly taji daɗin yau daddy ya mata wanka, har da wanke mata gashi ya kawota gaban mirror ya mata kwalli tare da busar mata da gashin kan ta da hand dryer, ya tara mata gashin ya ɗaure mata, ya sanya mata kana nan kaya na shan iska san nan ya feshe ta da perfume masu kamshi, shima yaje yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya shadda milk color mai kyau da tsada, ya riko hannun ta suka fice daga gidan, kai tsaye suka nufi wajen sai da puppy dog, sai farinciki yake yau ji yake kamar an masa albashr da gidan aljanna, a nan ya saiwa jelly puppy dog kyakkyawa fara kal mai yalwar gashi a jiki, tun a lokacin da a ka sai mata karen ta sa masa suna dolly tun a wajen, tana bala'i kaunar puppy ɗin, haka suka wuce super market yai musu shopping sosai san nan suka dawo gida cike da murna, ita kam Jelly murnan ta yafi na daddy dan ta samu dolly. Da daddare ba yadda daddy bai yi da ita ba a kan ta kawo dolly a sanya ta cikin keji da a ka sawota da shi, amma Jelly taki yarda ta kafe ita dole da dollyn ta zasu kwana a gadon ta, haka daddy ya hakura ba dan yaso ba. Washegari haka ta tashi rungume da dolly ɗin ta, dan ko sallama asuba ma dolly na gefen ta tayi, ba yadda daddy bai yi da ita ba a kan ta ajiye dollyn saman gado tayi Sallah amma taki yarda, ba yadda ya iya haka ya kyaleta. Wunin ranar dai Jellyn rungume da dolly ta wuni har dare, suka sake kwana gado guda, yanzu daddy ya hakura ya dai na shiga zancen ta ita da dolly ɗin ta ya zuba musu ido. Lokaci ya ja haka James ya rinƙa wasa da tunanin ogan su a kan kashe GAR, yayin da shi kuma daddyn Jelly ya samu saukin takura daga wajen baban Muneer haka zalika shi kuma Abbi dukiya sai haɓaka take yana kara samun kuɗi, Allah ya sawa abun albarka, yayin da shi kuma, daddyn su Rimsha siyasa ta gaba to ko ina sunan sa ke yawo jama'a na son shi sosai, ta ko ina masoya ne, Nawazudden, Nawazudden, ta ko ina, sosai daddy ke murna da farinciki a kan haka, tun wan nan tafiya da su Imran sukayi basu sake samun dama sun zo Nigeria ba, saboda abubuwa da suka sha musu kai, yayin da ita kuma Umaisha ta biyewa Aafia ta dai na sanya hijabi, duk wani abun da Akil yace mata sai da ta watsar ta dai na yi, kasan cewar abubuwa sun sha kan sa sosai baya samun damar bibiyar me take, sai dai bata sanya attachment da eyelashes, sune abun da ya rage a cikin dokan da Akil ya kafa mata bata karya ba, ita kuwa Aafia komai sanya wa take hankalin kwance, shima Irfan tun wan nan tafiya da yayi sau ɗaya yazo hutu, ko da yazo ya tsawatar wa Aafia sosai a kan sanya hijabi da ta daina sanya attachment da eyelashes da sauran su, amma yana komawa ta watsar da duk wani nasiha da tsawatar wan da ya mata ta koma gidan jiya shi kuwa wan nan mutumin da suka haɗu a kofar gidan su Rufaidat yasha neman ta har ya gaji basu sake haɗuwa ba amma bashi da burin da ya wuce sake ganin ta, Abbi bai cika zama a gida ba shi yasa su Aafia ke yin abun da suka ga dama, sai dai duk wan nan abun da suke sun san ba dai dai suke ba dan Abbi bai barsu haka nan ba sai da ya tabbatar ya basu ilimin addini, so sun san komai sun san ba dai dai suke ba, amma suka take sani. A ɓangaren su Abba kuwa duk karshen shekara wayan nan dodannin suna zuwa musu, kuma sai sunyi sati suna zane su kafin su tafi, in sun tafi kuma sai bayan shekara suke sake dawuwa, babban damuwar shine da dodannin sun tafi shikenan suma zasu manta komai hakan yasa basu samu dama sun iya sawa a musu saukan Al Qur'ani mai girma ba kasan cewar sun manta komai basa iya tuna komai. *ABUJA* Kamar kullun yau ma daddy na gida bai fita ba missalin karfe 3 na yamma, yau suna tare da uncle Shitu, sai hira suke a palo, uncle Shitu na ta hira da Rimsha ita kam Jehan daman ba shiri take da kowa ba, dan Uncle Shitu bai isshe ta kallo ba, a cewar ta duk wanda ke karkashin daddyn ta to a karkashin ta yake dole ya girmama ta, Jehan yar sanda sosai take bawa kan ta horo tayi ta azabtar da kan ta ta fannin gudu da ɗaga karfe, iya bin kwakkwafi a kan abu, bata da yawan surutu kamar dai ita ma Rimsha ɗin basu da yawan surutu, sai dai Jehan a koi ta da zafin kai, rai na mutane, rashin kunya, tsaurin ido, shagwaɓa, izza da kuma girman kai, amma duk da haka tana da ilimin addini sosai sai dai bata kai Rimsha ba amma tafi Rimsha ilimin boko, dan ita ta ɗauki boko da muhimmanci, ita ma Rimsha tana da ilimin bokon sai dai ko a School daman Jehan tafi Rimsha da class, ita ma Rimsha bata son rai ni amma tana da fara'a ga son mutane ba ruwan ta shiru shiru bata son hayaniya. Sai hira suke zubawa daddy na cike da farinciki ita kuwa Jehan ta lafe a cinyar Gwaggo sai shagwaɓa take zuba mata, gwaggo na biye mata, mum dad suna hira Uncle shitu na hiran da Rimsha a kan wani hadisi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama in da yake cewa ka kyautatawa Mumini kyakyawan zato, ka zauna da kowa zuciya ɗaya, idan kayi hakan ko da wani yayi niyar cutar da kai Allah ba zai bashi dama ba dan kai baka kullace sa a ranka ba. Suna tsaka da hirar su mai gadi yayi sallama, da fara'a daddy ya amsa masa, har kasa mai gadi ya duƙa yace "Alhaji kayi baki a waje" kasan cewar daddy ya saba da ansan baki kala kala ko yaushe musamman ma da siyasa ta gaba to hakan yasa bai damu ba ya miƙe ya nufi waje yana faɗin "Ina zuwa baby Jehan" jikin sa sanye da jallabiya baka. Fitan daddy ba'a da 5mins ba uncle Shitu ya miƙe yana faɗin "Bari na bi bayan Alhaji sai mu dawo tare" da fara'a mum ta amsa masa da to, san nan yayi waje. Yana fita harabar gidan sai bai ga kowa ba, cikin sauri ya nufi waje, dai dai lokacin wasu jibga jibgan sojoji ke kokarin tura daddy cikin motar su, jibga jibga ne sosai da sosai gashi dukkan su face nasu da face mask zasu kai su takwas, cikin sauri Uncle Shitu yace "Meke faruwa lafiya?" Ɗaya daga cikin sojojin ne ya nunawa uncle Shitu ID card nashi na aiki ba tare da yayi magana ba, kallon daddy uncle Shitu yayi kafin yace "Meke faruwa Alhaji" girgiza kai daddy yayi kamar zai yi kuka yace "Wai wani ɗan kidnaping suka kama yace musu nine mai gidan shi nike basu makamai suke sace mutane, nayi kokarin su barni na kira lawyer amma sun ki yarda, ni ina jin akoi abun da a ka shirya min ne, please Shitu ga amanar family na ka kulamin da su kafin na dawo karka sanar musu abun da ke karuwa san nan ka kira min lawyer mu haɗu da kai a office ɗin na su" innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine kawai abun da uncle Shitu ke iya furtawa, muryan sa har kerma yake wajen cewa "bari na fito da mota sai muje tare" basu jira uncle Shitu ya gama magana ba suka ja motar su a guje suka tafi da daddy kamar zai yi kuka cikin sauri Uncle ya koma cikin gida ya ɗauko mota, duk abun da ke faruwa mai gadi na kallon su sai salati kawai yake, uncle Shitu na kokarin jan motar mum ta fito, tana faɗin "Lafiya Shitu fita kuma zaku yi ne ba sallama" in brief uncle Shitu ya sanar da ita sojoji sun kama da daddy da kuma abun da ke faruwa amma yanzu zai bi bayan su, su taya su da addu'a komai zai dai dai ta In Sha Allah, sosai mum ta shiga tashin hankali mara misaltuwa har jiri jiri take gani saboda tashin hankali nan take taji kan ta ya mata yauyi ta kasa motsawa daga wajen, har uncle Shitu ya ja motar mai gadi ya buɗe masa gate ya fita da gudun gaske yabi bayan su daddy. Slowly mum ta juyo da nufin ta koma cikin gida sai ganin Jehan tayi tsaye a bayan ta tana hawaye, da kyar ta iya ɗaga kafafun ta da suka mata nauyi kamar dutse ta karisa wajen Jehan ɗin, ta rungumeta tana goge mata hawaye tare da bata baki, a haka suka koma cikin Palo. Da gudu Jehan ta faɗa jikin gwaggo tana kuka tana faɗin "Gwaggo uncle yace an kama daddy wai ɗan kidnaping ne" zubur gwaggo ta miƙe tare da dafe girjin ta tana ambaton sunan Allah, ita ma Rimsha miƙewa tayi cike da shin hankali nan take hawaye suka fara wanke mata fuska, mum na kokarin yin magana sukaji sallama daga bayan su, a bakin kofar shigowa palon, a sukwane suka juya, wasu yan sanda ne sanye cikin kayan aikin su hannun su riƙe da wasu mai ɗauke da wasu rubutu, kai tsaye suka shigo cikin palon basu jira wani izini ba kuma Kai tsaye wajen mum suka nufa suka miƙa mata takardun da bairo a kan ta sanya hannu, ko kaɗan bata damu ba a tunanin ta tun da har suka iya wuce asalin babban gate na estate ɗin suka zo nan to manyan yan sanda ne, kuma kila a kan case ɗin daddy suka zo, dan haka bata tsaya duba takardun ba kawai ta sanya hannu jikin ta sai kerma yake gwaggo ce tayi ta maza wajen cewa takardun me wan nan, already lokacin mum ta sanya hannun sun miƙawa Rimsha a kan itama ta sanya hannu, ko kallon in da Gwaggo take basu yi ba cikin kiɗi ma da tashin hankali Rimsha ta sanya hannu jikin ta sai kerma yake, ansan takardun daga hannun Rimsha sukayi suka miƙa wa Jehan ita ma ta sanya hannu, kallon tsab Jehan ta musu kafin tace "Wace dokace ta baku damar shigowa gidan matan aure kuma har cikin palo ba tare da izinin masu gidan ba kuna kartin maza da ku? San nan wan nan takardun me, ba zan sanya hannu ba sai na san takardun menene" tayi maganar babu alamar tsoro ko kaɗan a face nata, sai lokacin mum tayi nadamar sanya hannu da tayi a takardun, taruɗe sosai shi yasa tayi saurin sanya hannun dan bata kawo komai a ran taba. Ba tare da sun yi magana ba babban cikin su mai riƙe da takardan ya ciro ID card ya nuna mata, kallon sama da kasa ta masa ko tsoro babu a face nata tana ganin kartin maza har huɗu amma bata ji shakkan su ba tace "ID card ba shine na tambaye ka ba, abun da na tambaye ka wace dokace ta baku damar shigowa cikin gidan matar aure ba tare da izinin su ba, kuna kartin maza da ku, san nan kuma takar dan me kuka kawo mu sanya hannu, ba zan sanya hannu a komai ba sai naji na menene ko kuma ku bani takardan na karanta" tsare ta da sheggun idon sa wanda ya riƙe takardun yayi, a zuciyar sa yana faɗin "Wan nan idan muka ce zamu bita ta karfi zata iya tona mana asiri amma in ta san wata ai bata san wata ba" ya kai karshen zancen zucin na sa tare da shammatar ta ya zaro takarda guda ɗaya daga cikin takardun ya miƙa mata, amma sai ya zaro takarda na kasa ba na sama da su mum suka sanya hannu ba, kwata kwata Jehan bata lura da hakan ba, ansan kawai tayi ta fara larantawa, ganin an sanya takardan neman bellin daddyn sune yasa cikin sauri tace "Ku bani pen na sanya hannu" ansan paper yayi sai yayi kamar ya ɗaura mata a saman sauran takardun al halin kasan sauran na hannun sa ta tura ya miƙo mata takardun dukka tare da bairo, cikin zumuɗi ta sanya hannu a kan wadda su mum suka sanya hannu ba tare da ta lura ba, tana sanya hannu suka ansa suka juya suka fice daga palon, rungume mum Jehan tayi tana dariya tana faɗin "Mum daddy zai dawo, yanzu ba zai daɗe ba" nan take dukkan su suka fara murmushi suna jin daɗi, sai godiya ga Ubangiji talikai suke, suka koma suka zazzauna suna tayiwa daddy addu'a. Misalin karfe 9 na dare duk suna zaune a palo sun yi jugum jugum kamar masu zaman makoki, kowan nan su da abin da yake sakawa a ransa, duk sai tambayar kan su suke ya akayi daddy bai dawo ba bayan kuma sun sanya hannun a kan takardun beli, sai addu'a suke ta masa, ita kam Jehan ta tada kai da cinyar Gwaggo tana aikin hawaye ita kuma Rimsha tana kan dadduma ta buga uban ta gumi tana tunanin wani hali daddyn ta ke ciki. Sun yi nisa cikin tunanin da suke Uncle Shitu ya faɗo cikin palon babu ko sallama goshin sa a fashe ga jini duk ya wanke masa kayan jikin sa sai nishi yake sama sama ya dafe goshin nasa in da ya fashen ga jinin sai bin hannun sa yake, jiri yake gani sosai amma saboda karfin hali irin nasa sai ya danne yana kame kan sa. Jehan ta riga kowa miƙewa tsaye, cike da tashin hankali Mum tace "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Shitu lafiya? Accident kayi ne? Girgiza kai uncle Shitu yayi ciki firgici da kyar ya iya buɗe baki murya na rawa sai haɗe kalmomin yake saboda azaban da yake ji "Hajiya ku wuce muje da wuri karku ɓata lokaci" gwaggo ce tace masa "Ina zamu je" juyowa yayi ya kalle ta yana faɗin "Aunty A'isha in mun fita zan faɗa muku ni dai burina mu bar gidan nan, ku ɗauki ɗan abun da zaku buƙata muje baku da lokaci fa" tun da mum taji haka sai ta fahinci a koi babban matsala dan haka sai ta haura sama da gudu ta ɗauki trolley ɗaya babba ta zuba kayan ta da gwala-gwalai ɗin ta, da duk wani abu ta mai tsada ta haɗo da wayar ta da ATM nata, ta sauko kasa ta ajiye trolley ta wuce ta koma ɗakin su Rimsha cikin sauri suma ta ɗauko musu kayan su trolley ɗaya tare da wayoyin su da ATM na Jehan, ko da ta dawo palon gwaggo ta ɗauko nata trolley, a tare suka fice uncle duk da jirin da yake ji hakan bai hana shi ya ɗauka wa mum trolley ɗin ta ba. Mum ta kara tsorata sosai lokacin da suka fito waje taga motar uncle Shitu duk taɓo da datti yayi caɓa caɓa da alama yayi gudun cetan rai ne dukkan su gidan baya na motar suka shiga, ko sallama basu yiwa mai gadi ba, kasan cewar daman uncle a waje ya bar motar bai shigo da ita cikin gida ba, haka suka wuce cikin motar. Da wani mahaukacin gudu uncle ya ja motar, baya ganin gaban sa sosai saboda jirin da yake ji, jinin sa ya zuba sosai abun ya fara affecting na shi, amma haka ya daure yana ambato sunan Allah yana gudu da motar. Uncle na tafita ba'a fi da minti 20 ba sai ga wasu jibga jibgan sojiji sanye da kaki sun diro gidan, kai tsaye suka wuce cikin gida, ganin babu kowa ne yasa suka dawo bakin gate dan su tambayi mai gadi, nan suka tarar da ba mai gadi shima ya gudu, hakan ba karamin fusata su yayi ba, haka suka kulle gidan ko ina suka sanya kwaɗo da key suka rufe gidan suka fito suka shiga Hilux car ɗin su suka bar estate ɗin da gudun gaske cike da bakin ciki. Shi kuwa uncle kai tsaye park ya kai su mum, yayi Sa'a motar zuwa Katsina ya samu saura mutun uku a ke buƙata motar ta tashi, haka ya ciro kuɗi daga aljihun sa ya bawa mum ta biya musu kuɗin mota, san nan ya sanar da su a kan su ɓoye kan su karsu kuskura su bari wani wadda ya sansu ya gane face na su, suje Allah na tare da mai gaskiya kuma Allah zai tsare su, mum ta tambaye sa ina daddy, amma sai ce mata yayi suyiwa daddy addu'ar Allah yasa can ta fi masa nan, mum taso sake tambayar sa amma kasan cewar babu lokacin, hakan yasa suka fita suka shiga motar Katsina, shi uncle yaki fita daga motar sa saboda jinin dake jikin sa idan jama'a suka gani zasu iya kin ɗaukan su mum a tashan ko kuma suyi wani abun da zai tonawa su mum asiri, Allah ma yasa dare ne ba'a ganin sosai a koi duhu. Haka uncle yaja motar sa ciki fitar hayyyaci dan ya fara fita hayyacin sa sosai, haka ya bar park ɗin ya hau titi, duhu yake gani sosai baya ganin komai bai san ina ya nufa ba kawai gudu yake shararawa a kan titi gashi ya kasa dakatar da motar saboda ya galabaita over. Tafiyar 10mins yayi tsakanin sa da park ɗin ya samu haɗari, yayi karo da wata motar, juyi uku motar sa tayi a saman titi kafin ta kama da wuta, anyi Sa'a a komai mutane a wajen suka fara kawo ɗauki, shi wan can motar da sukayi accident ɗin ma da alama driver shima ya mutu. Su mum kuwa sai kuka kasa kasa suke a cikin mota Rimsha na zaune saman cinyar mum, ba abun da take sai ambato sunan Allah, yayin da ita kuma Jehan ta fita kanta da jikin kujerar motar tana tunani a kan takardan da ta sa hannu tana yi tana hawaye, while ita ma gwaggo hawayen take sosai da sosai, mum kam ba'a magana nata tashin hankali na daban ne, yafi nasu dukkan su. 01:30 am suka shiga Katsina, kasan cewar dare yayi sosai a tasha suka kwana cikin sauro da zafi, abun da basu taɓa ba, hakan yasa suka kasa barci, Jehan sai kuka take yayin da ita kuma Rimsha tayi shiru tana yiwa daddy addu'a, har wayewan gari. Tun gari bai yi haske sosai ba suka sayi face mask suka sanya a face nasu, mum tayi kokarin kiran layin daddy, amma a rufe haka tayi kokarin kiran layin uncle Shitu shi ma a kashe, sun rasa ina zasu je dan basu san kowa ba, gwaggo ce tayi ta maza taje ta tambayi wasu maza dake zaune a runfar mai sai da shayin cikin tashan, ta musu sallama bayan sun amsa ta musu sannu san nan tace hotel take so su nuna mata su baƙi ne basu san kowa ba, wani bawan Allah ne ya tashi yace da gwaggo "Mama muje na numiki in da zaki hau abin hawa zuwa hotel ɗin" ba musu gwaggo tayi gaba yabi bayan ta har zuwa wajen su mum, gwaggo ce ta sanar da mum abun da ke faru wan nan mutumin zai nuna musu in da hotel yake su kama ɗaki su zauna, kallo gwaggo da kyau mum tayi sai taga gwaggo fa bata cikin hayyacin ta, hakan yasa mum ta kalli mutunmin cikin sanyin murya tace "Bawan Allah ba hotel muke da buƙata ba karamin gida ɗan dai dai muke so dai dai talaka" washe baki mutumin yayi yana faɗin "Nima ai dillaline, daman a koi gidan na da zan sayar muje ku gani in ya muku sai ku saya" ba musu su mum suka bi shi, ya tari abun hawa suka ɗauki trolleys ɗin su suka hau. Nan ya kai su wani gida ya nuna musu wai gidan shi ne zai sayar, kasan cewar a kiɗi me suke ba su wani duba gidan sosai ba suka ce ya musu, sukayi ciniki 5 million, haka mum tace ya nuna musu bank, ya nuna musu, ga baɗaya basa cikin hayyacin sosai sun rikice ga tashin hankali ita kam Jehan ko magana ta kasa, Rimsha ce ma mai kuzarin bakin magana itama gwaggo ta kasa magana, haka mum ta ciro kuɗin nan ta bawa mutumin nan ko takardun gidan basu tambaya ba, su dai kawai sun samu gida, suka fara sanya kayan cikin ɗakin suka zauna shiru, shi kuwa mutumi yayi gaba abun sa A wan nan halin asalin masu gidan ya dawo ya same su, da mamaki ya tambaye su mum wanene su, nan mum ke shaida masa ai sun saya gidan ne, ba karamin mamaki mai gidan ya sha ba, cike da mamaki ya tambayi su mum a wajen wa suka sayi gidan nan da kyar mum ta iya masa bayanin yadda komai ya gudana, a fusace mutumin yace "Wlh dan faran ku murtala yayi wan nan ba gidan shi bane gida nane, tare muke kwana da shi a ɗakin kawai amma ba gidan shi bane" lokacin guda mum taji duniya na juya mata dafe kan ta tayi ta zauna tana mai da numfashi kwata kwata daman 9 millon ne a account nata sai gwala-gwalai ɗin ta, dukkan su sun kasa magana, waya mutumin ya ciro ya fara kiran layin Murtala amma a kashe, tuni Murtala ya bar garin Katsina abun sa ya samu kuɗi, sai lokacin gwaggo ta lura da gidan ma da suka saya, ashe gidan ma irin gidan mazan nan ne ɗaki biyu ne a cikin gidan, sosai su mum suka shiga damuwa, gashi ba halin zuwa police station basu da zaɓi dole su hakura, wan nan abokin Murtala ne ya taimaka musu ya nema musu gida a Unguwar farin yaro da kan sa ya musu jagora suka sayi gidan 3 millon suka biya kuɗi, san nan suka ɗauki 500k suka sayi kado da kayan abinci da sauran kayan amfani na talakawa, sauran 500k suka bari a account ɗin mum while ita gwaggo daman bata da account sai account na Jehan mai ɗauke da 1 million a ciki. Tun da sukazo Unguwar Jehan bata cin abincin da su mum ke girkawa, kuɗin account nata kawai take kashe musu ita da Rimsha, dan ita Rimsha bata da account ita ma Jehan ɗin da kyar bank suka yarda suka buɗe mata account tana da 15 years sai da daddy ya nemi alfarma san nan suka bata account, kullun Jehan ke fita ta sawo musu abinci ita da Rimsha da su mum, ita kuma Rimsha tana gida bata fita, dan ita unguwar ma tsoro yake bata shi yasa bata fita take zaune a gida. Tun da suka zo sau biyu Rimsha ta fita ranar da ta raka Jehan restaurant, sai ranar da ta fita a ka sace ta shi kenan. *KADUNA* A wan nan satin Abbi ya auri amaryan sa Halima wadda wani abokin sa ya haɗa su kasan cewar Halima yarinya ce mai hankali ga addini sai dai yar gidan talakawa ne sosai da sosai, shi kuma Abbi yanzu arziki ba'a magana su Aafia an kara goge wa dama ba daga nan ba. Wan nan shine takaitacen labarin a kan abun da ya raba su Jehan da daddyn su da kuma abun da ya sanya daddyn Jelly zai aurawa Jelly Muneer, da kuma yadda Abbi ya auri Aunty har su Aafia ke mata rashin mutunci. Yanzu sai mukoma cikin asalin Story. STORY.....✍️🤪 MUCH KAUNA MASU MIN COMMENTS ALLAH YA BAR ZUMUNCI ALLAH YA BAR KAUNA ❤️💖 KUMA MASU MIN LIKE MUCH KAUNA ❤️ MASU MIN SHARE ALLAH YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNATUL FIRDAUS INA GODIYA BA ZAN MANTA DA KU BA MUCH KAUNA ❤️ Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪🤪 B 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 21 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 Mai neman karin bayani yamin magana ta wan nan number 09162620621 EPISODE 21 ```*💞BACK TO THE STORY💞*``` ______Da iya karfin su wayan nan magicians (Matsafa) suka sanya hannu suka fara tsigewa yaran nan gashin kan su, koda ɗaya daga cikin su ya damko gashin Rimsha ya ja yana kokarin shigewa, ihu ta fasa tare da furta kalmar shahada da karfi, hakan yayi sanadiyar magicians ɗin suka ja da baya da sauri, gudun kar su kone, jin sunan Allah yasa Santilago ɗago kai da sauri yana kallon su, yayin da sauran magicians suka ja baya suna zaro ido gwanin ban tsoro, ita kuwa Rimsha sai sauke ajiyar zuciya take tana ambato sunan Allah ta runtse ido gam. Gigitatchiyar tsawa Santilago ya daka, tare da fara Yaren tsafin su, da karfi ya ɗaga hannu tsama nan take idon sa suka sauya launi, kan kace me gidan ya turnuke da duhu da hayaki kamar guguwa mai karfi, Rimsha bata cikin hayyacin ta sosai ba zata iya ja da su ba, dan bata san meke faruwa ba, salatin Annabi ka ɗai take iya furtawa sai kalmar shahada dake fita daga bakin ta, shima kuma ba'a dai dai take karan tasu ba saboda ruɗu da tashin hankali, yayin da shi kuma Santilago ke faman kiran abubun tsafin su, kusa da shi Barbushi ya zo ya tsaya, suka haɗa hannu da murya sama suka ci-gaba da ambato sunayen manya manyan jiga jigan magicians ɗin na su, gidan gaba ɗaya sai kara duhu yake kamar dare, ga wani iska mai karfin gaske dake tasowa daga ta saman gidan mai birkita tunanin ɗan adam. Nan take Rimsha taji an ɗaure mata maƙogwaro da karfi kamar za'a tsinke mata shi, ta kasa magana shiru tayi tare da waro sleeping eyes nata waje, wadda yanzu suka sauya sukayi ja sosai kamar garwashin wuta, Saboda kuka da wahala ga yinwa da barci duk sun haɗe mata waje guda. Kamar a mafarki taji an ɗaga ta sama ta rabu da kasa haka zalika ta fita daga cikin igiyar da suka ɗaure ta, sama sosai sukayi da ita, sai da ta kusa kurewa tsayin gidan, a hankali ta kalli kasa, ba karamin tsorata tayi ba lokacin da taga babu wanda ya ɗaga ta haka nan ta tashi sama, runtse ido tayi a ranta tana ambato sunan Allah, dan afilin kam ta kasa faɗa sun shake mata maƙogwaro. Almost 5mins tana tsaye a saman iska kafin su fara bujijjigata suna wainata kamar fanka, ga wan nan iskar guguwa mai karfi mai haɗe da yashi wato kasa sai shiga mata hanci yake dan ta runtse idon ta kam sosai, da kyar take samu tayi mumfashi nan ma sai ta buɗe bakin ta take samun damar yin numfashin da karfi suka ja ta da tsafin su suka bugata da jikin wani bango sai da ta fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa, a cikin ihun nata ne take kiran "wayyo daddy na mummy gwaggo Jehan ina kuke zan mutu kuzo ku taimake ni, wayyo na shiga uku mutuwa zanyi wayyo Jehan kizo ki taimake ni" ba shiri ta sake fasa wani ihun sakamakon buga mata kai da sukayi da jikin wani karfe dake tsakar gidan, jijjigata da karfi suka sake yi kafin su juyo da ita kan ta na kallon kasa kafafun ta a sama, da karfi sukayo kasa da ita, kamar zasu makata da kasa, sai kuma suka da katar da ita, dark black curly hair tan nan ya curkuɗe saboda wahala yana ja a kasa, yayin da kafafun ta ke saman iska, tana lilo tsakanin kasa da sama, a nan ma kara jujjuya ta sukayi kamar fanka, sai da suka tabbatar ta jijjigu a ganin su tafita hayyacin ta sannan suka juyo da ita suka sauke ta kasa Suna sauke ta kasa su kuma su barbushi suka dakata da ambaton sunan suwagabannin tsafin na su, suna dakatawa gidan ya washe duhun ya tafi haske ya gauraye ko ina, haka shima kuran ya ɓace ɓat kamar ba'ayi ba. Shiru Rimsha tayi ta kasa buɗe idon ta saboda wahala, ta kuma kasa zama waje guda sai juyawa take saboda jijjigata da sukayi suka ta juyata kamar fanka, amma dai har lokacin Allah da ikon sa bata fita hayyacin taba su barbushi sun sha ruwan mamakin ganin bata fita hayyacin taba, basu taɓa yiwa wani ɗan adam irin abun nan da suka mata kuma a ce mutumin bai fita hayyacin sa ba sai ita sun yi mamaki sosai, sun kuma kara jin haushin ta da tsanar ta. Ita kuwa ta kasa buɗe idon ta sai jin duniya na juya mata take, ban da sunan Allah da sunan daddy da mum ba abun da take kira a ranta. Haka su Barbushi ba dan sun so ba suka bada umarni a kai ta next room wato Part 2, su kuma sauran yaran sanadiyyar abun da a kayiwa Rimsha yasa wasu daga cikin su suka fargaɗo wasu kuma suka dawo cikin hayyacin su, Santilago ne yasa sauran magicians suka tsince yara masu hankali a ka haɗa su da Rimsha a ka wuce dasu wani ɗakin, su kuma sauran yaran da basu dawo hayyacin su ba, Barbushi ya yankasu, kamar yadda suka saba suka kaiwa dodannin tsafin su jinin, kai da kafa kuma a ka kaiwa dodannin su masu cin kai da kafa, su kuma suka wuce da naman dan suje suyi ferfesun su. Wani part dake cikin gidan suka wuce da su Rimsha, sai a lokacin Rimsha ta samu damar bude dara daran sleeping eyes nata sunyi ja sun kan kance saboda wahala, a hankali ta fara bin wajen da kallo, ba karamin tsorata tayi ba ganin wajen, waje ne mai cike da gumakan dodannin tsafin su, abun gwanin ban tsoro da rikitarwa, bata kara tsinke wa ba ma sai da suka buɗe wani kofa suka jefasu suka rufesu sukayi tafiyar su, su uku ne rayar da su ka rage masu hankali sai Rimsha ta huɗu. Wani irin ɗaki ne idan ka ganshi zakayi tunanin gidan prison ne, gefe da gefen dukka an sanya burglaries daga sama har kasa an tare wajen kamar keji, shi kuma tsakiyar an barshi kamar hanyar wucewa, gaba ɗaya wajen sai wani irin fitinanniyar wari mai tada hankalin mai shaƙa ke tashi. Wayan nan magicians ɗin suna jefa su Rimsha ciki, wasu jibga jibgan dodanni ne suka taso ta cikin burglaries ɗin suka fara miƙo hannun su ta cikin burglaries ɗin suna son kama su Rimsha jibga jibga ne sosai masu siffar spider (gizo gizo) sai dai girman jikin su ya kai kusan giwa, gashi ido ɗaya gare su a tsakar goshin su, gasu da bala'i muni, fuskar su kawai ya isa ya sanya mai rai suma saboda muni, hannun su da kafafun sun nan babu kyan gani ko kaɗan, bakin su kuwa kamar mutun yayi ta kwarara amai idan ya gani, haka suka bufo su Rimsha suna gurnani mai razana kwakkwal mai rai. Gudun cetan rai su Rimsha suka fara yi a wajen gashi wajen ba wani faɗi ne gare sa ba, sai zuro hannu dodan nin nan suke suna son kama su, da gani a matsanancin yinwace dodannin suke, abin ci kawai suke buƙata ihu sosai Rimsha take kamar makogwaron ta zai fashe, gwanin ban tausayi, duk in da ta gudu a wajen sai dodanin sun je gashi an ɗaure mata makogwaron ta bata iya kiran sunan Allah, hakan ba karamin cutar da ita yayi ba, sai ihu take tana gudu ta rasa ina zata sanya ranta, sukam sauran, yara biyu daga ciki sun sume a wajen, saura yarin ya ɗaya dake ta faman gudu tare da Rimsha, su kuwa dodannin sai musu barazana suke, dan hannun su ba zai kai su iya kama su Rimsha ɗin ba, su Rimsha ke ganin kamar dodannin zasu kama su. *KADUNA* Aafia In da ta bar Aunty a nan ta fito ta same ta, kallon sama da kasa ta mata kafin ta ɗauki remote ta can za channel na Tv, shiru Aunty tayi bata yi magana ba, amma tana son kallon film ɗin da take kallo a arewa 24 sai dai ba yadda ta iya dole ta hakura ta zauna shiru ta zubawa Tv ido kawai tana kallon wakar da Aafia ta sa, ba dan taso ba. A wannan halin Abbi ya dawo ya same su, da sauri Aafia ta miƙe ta faɗa jikin sa tana dariya, rungumeta yayi yana faɗin "My daughter ana hira da Aunty ne?" Shiri Aafia tayi masa kamar bata ji me yace ba, dai dai lokacin idon ta ya sauka a kan yarinyar dake biye da Abbi a baya, cikin sauri ta ɗago daga jikim Abbi tana faɗin "Abbi wace ce wan na kuma?" Juyowa Abbi yayi ya kalli Aunty dake zaune tana son yi masa oyoyo amma ta kasa saboda Aafia, wucewa yayi ya zauna kusa da Aunty yana faɗin "Mai aiki na samo muku hajiya zuwaira ce ta kawo min ita, sai ku riƙe ta da amana kun dai ga yarinyace" a kule Aafia tace "Abbi to ita kuma wan nan fa me zata rinƙa yi" tayi maganar tana nuna Aunty da hannun ta, ba tare da ya kalle ta ba yace "Ke zoki zauna ina Umaisha take? Kuzo na muku wani albishir" cikin zumuɗi ta dawo kusa da shi ta zauna tana faɗin "Albishir ɗin me Abbi?" "ina Umaisha take?" Cikin sauri Aafia ta miƙe har tana haɗawa da yar gudu ta nufi bedroom nasu, Aafia na tafiya Aunty ta kira mai aikin da Abbi yazo da ita a kan tazo ta zauna, yarinya ce karama wadda ba zata wuci sa'ar Umaisha ba wato 18 years kenan, ba musu Yarinyar tazo ta zauna a kasa kusa da kafar Aunty, gaba ɗaya a tsorace yarinyar take taki sakin jikin ta da su, Tare Umaisha da Aafia suka sauko sai murna suke suna jin daɗi, har rige rigen zama kusa da Abbi suke, ganin haka yasa Aunty ta miƙe ta bar musu sofar ta koma mai zaman mutun 1, Abbi bai wani damu da hakan ba shi a ganin sa su Aafia yarane basu girma sosai ba shi yasa bai cika tsawatar musu a kan faɗa da suke wajen zama kusa da shi ba har su sanya Aunty ta tashi ta basu waje, Allah sarki Aunty baiwar Allah bata taɓa damuwa ba da sun fara zata basu waje ita ta koma gefe. Cike da farinciki Abbi ya ciro takardun daga jakar sa tare da key ɗin motoncin guda uku, Aafia na kokarin ansan key ɗin ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu yana faɗin "Ki bari auntun ku ta fara ɗauka tukun nan" kallon sama da kasa Aafia tayiwa aunty tare da turo bakin nan nata kamar biro tana jin kamar taje ta tsake Aunty ta kashe ta kawai kowa ya huta, shi kuwa Abbi sai murmushi yake yana kallon Aunty bai lura da abun da Aafia ke yi ba. Ganin Aafia ta ɓata rai ne yasa Aunty tace "A'a Abbi ka bawa Aafia ta fara ɗauka ni ku bani ko wane ma ina godiya" Aunty tayi wannan maganar ne ba dan komai ba sai dan ta samun zaman lafiya da Aafia, ko kaɗan bata son irin zaman da suke da Aafia bata jin daɗi shi yasa take kokarin duk yadda zasu yi su sami zaman lafiya, amma duk a banza saboda Aafia da zancen su Rufee take aiki ba da nata tunanin ba. Girgiza kai Abbi yayi kafin yace "Ke nace ki fara ɗauka ai, ba kece babba ba?" Haka ba dan taso ba ta sanya hannu ta ɗauki key ɗaya, sannan Abbi ya miƙa wa Aafia, kamar ba zata ɗauka ba amma sai ta ɗauki ɗaya dan tasan halin Abbi yana da wasa da dariya amma bai son a kawo masa shirme a lamuran sa yanzu zai harzuƙa ya fara faɗa Key na karshen ya miƙa wa Umaisha yana faɗin "Key ɗin sabbin motocin da na sai muku ne" a sukwane Aafia miƙe tana faɗin "Abbi ina motar take? Tana waje ne?" Sai murmushi yake yace "Motar na sabon gidan mu da zamu koma ga takardun gidan nan ma, shine albirushir da zan muku daman" Aafia da Umaisha har suna rige rigen rungumar Abbi dan murna da farinci, sai murmushi ita ma Aunty take bakin ta yaki rufuwa, sai godiya ga Allah take a ranta "Ina key ɗin tsofaffin motoncin ku?" Abbi ya tambaya yana kallon su, har suna haɗa baki wajen cewa "yana bedroom" "je ku kawo min" da sauri Umaisha ta miƙe ta haye sama. Jim kaɗan ta dawo hannun ta riƙe da keys ɗin tazo ta miƙa wa Abbi, ansa yayi ya miƙa wa aunty yana faɗin "Ki bawa yayan ki da kanin nan naki yama sunan su? To ki basu su rinƙa hawa" Aunty ta ansa tana kokarin yin magana kenan Aafia ta katse ta cikin jin haushi tace "Haba Abbi ni gaskiya a'a zan bawa Rufee nawa motar gaskiya Sai dai a bata na Umaisha" tsare ta da ido Abbi yayi kafin yace "da Auntyn ku da Rufee ɗin wace ta fi muku?" Har suna haɗe baki wajen cewa "Rufee tafi mana Abbi" tashin sense "What?" Abbi ya furta da mamaki a face nashi, kukan shagwaɓa Aafia ta sa masa tana bubbuga kafa a kasa jiki na rawa Aunty tace "A'a Aafia ga key ɗin naki kiyi hakuri" kallon ta Abbi yayi kafin yace "Ita ta baki key ɗin ne?" Cike da ladabi Aunty ta girgiza kai tana faɗin "A'a kayi hakuri" kallon Aafia yayi kafin yace "Ba dai Rufee kike son bawa mota ba?" Da sauri Aafia ta gyaɗa masa kai alamar eh "Je ki bedroom na yayan ku ki ɗauki key ɗin motar sa ki bata dan shi ma ya sayi sabbi guda biyu" nan take murmushi ya kubcewa Aafia cike da murna ta miƙe ta bar palon, shima Abbi miƙewa yayi rike da takardan sabon gidan da ya sai musu da jakar sa ya wuce bedroom na shi, cike da murna Umaisha ta miƙe ita ma takoma bedroom nasu kallon yarinyar da Abbi yazo da ita Aunty tayi kafin tace "Muje na nuna miki ɗakin ki ko?" Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tayi gaba yarinyar ta bita zuwa ɗakin masu aikin dake kusa da kitchen, nan Aunty ta kai ta san nan ta fito ta wuce bedroom nasu dan taje ta tayiwa Abbi godiya, sai murna take yayan ta da kanin ta sun samu mota. **💞WASHINGTON DC💞** *HARVARD UNIVERSITY🎉* Gudu Test yake shatarawa kamar zai tashi sama a chikin katafaren fillin *Harvard football place* kallo ɗaya zaka masa ka gane gudun cetan rai yake, da wani mahaukacin gudu Michael ya biyo bayan sa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana chikin matsanancin bachin rai. Sosai Test ke gudun cetan rai, yazo dai dai tsakiyar wajen *Harvard basket ball Place* kenan Michael ya kai masa wani wawan bugu a bayan wuya wadda ya sanya shi ya faɗi kasa, gadan gadan Michael ya nufeshi kamar wani mayinwacin zaki sai huci yake ran maza ya ɓaci, gadan gadan ya nufe sa da niyar dukan shi, wani dattijo ne ya kariso wajen da gudu ya tsugunna ya kama kafar Michael ya fara magana chikin harshen turanci "Sorry Michael, kayi hakuri ka kyalesa" babu ko tausayi Michael yasa kafa ya hambare dattijon har sai da dattijon ya faɗi kasa, a fusace rai amatukar ɓace ya nufi kan Tast gadan gadan, hannu ya dunkule zai kai wa Test naushi a fiska, wani kyakkyawan Bature matashi ya riƙe hannun nashi ta baya, A fusache Michael ya juyo chike da ɓacin rai yace "Robertson ka sake ni" "No Michael ba zan sake kaba me yasa zaka bugeshi wai ba friend naka bane?" "Please Rob ka kyaleni na kashe wannan jakin" ya karisa maganar tare da kwachewa daga rikon da Robertson ya masa yana kokarin kai wa Tast duka a cikin, cike da izza Rob yace "Allah Michael idan ka sake ka buge sa sai na kira Romeo yanzun nan" a sukwane Michael ya juyo, chike da ɓacin rai ya fara magana "Rob kasani awannan karon Romeo ba zai che komai ba sai dai ma ya kashe Test (Tase) da hannun sa, kasan me Test yamin ne da har yasa nace sai na illatashi!? "Aa Michael ban san me ya maka ba amma ko ma me ya maka kamata yayi ka masa afuwa tun da friend ɗin kane, tukun nan ma me ya maka?" Shiru Michael yayi na ɗan lokachin kafin yace "dazun na sai musu kyautan mota, dan na canza musu tson da suke hawa da murna na kawo musu key ɗin shi da Dest, wai ina miƙa musu keys ɗin buɗar bakin Tese wai God bless your mum har da wani cewa Allah yasa ta dawo gare mu" iya ɓacin rai Rob ranshi ya baci, dan bai son abun da Michael ke yi wa mahaifiyar sa ko kaɗan, duk da chewa da gaske mum nasu ta musu laifi amma bai kamata suna yin abin da suke yin nan ba, cikin sigar rarrashi yace "Michael please stop saying this i knew mum did something wrong to... Rob bai kai karshen maganar ba Michael ya daga masa tsawa yana faɗin "Rob please live this place, for now i don't want to see you" "what!? Micheal are you heard what you said ? Ni kake chewa na tafi? Good, to ba zan tafi ba Please ka kyale tese kazo muje" "Rob idan kaga ban illata Test ba yau to sai dai in nine na mutu" ya kai karshen maganar ya juya, a fusache ya rufe Test da duka, girgiza kai kawai Robertson yayi yana mamakin zuciya irin na Michael, san nan yana tausayawa su Test dake friends nashi. dukan shi yake ba ji ba gani kamar an aiko sa, ta ko ina yake sauke masa hannu a jikin, Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, a sukwane ya juyo dan ganin wanene, karaf idon sa ya sauka kan face ɗin James dake tsaye fuskar nan tashi babu alamar annuri ko kaɗan kallo ɗaya zaka masa kasan yau yana cikin ɓacin rai over. Sakin Test Micheal yayi ya taho ya rungume James yana huci yana jin zuciyar sa na masa zafi kamar zata fashe ta fito waje, ajiyar zuciya James ya sauke kafin yasa hannu yana ɗan bubbuga bayan Michael alamar rarrashi "What happened between you and your friend Tese" James ya tambaya yana tsare Test da ido, cike da tsoro da tashin hankali Test yace "I'm sorry Michael it was a mistake" "I did not ask you whether it's mistake or not, I say what happened" cewar James a tsorace Test yace "we warmly received a car gift early morning from him, mistakenly I say to him, God bless your mum because I'm really happy, I forgot he hate his mum" Dawo da kallon sa James yayi kan face ɗin Michael da ya kwantar a saman kafaɗar James ɗin, sai wani huci yake yana lumshe brown eyes na shi, girgiza kai James yayi a ransa yana faɗin Michael ɗan rigima, a zahiri kuma shafa kumatun Michael ɗin yayi kasa kasa yace "It's okey, let's go home" shiru Michael ya masa kamar bai ji me yace ba, dawo da kallon sa kan Test yayi cike da bada umarni da izza yace "be careful Test, don't repeat this mistake again" cikin sauri Test yace "Okey sir thank you very much" sake kallon Michael James yayi "Are you okey Michael? Where is Lucky and copper?" "They are at home" Michael ya bashi amsa tare da wucewa ya nufi hanyar parking space, girgiza kai James yayi kafin ya bi bayan Michael ɗin suka jera tare, suka bar su Robertson da Test tsaye a wajen, suka shiga motocin su suka nufi gida. Lokacin da suka dawo gida babu kowa a palon kasa sai daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac da ke tashi, ko ina a gyare tsab kamar sabbin abubuwa a ka zuba a wajen. Kai tsaye saman bene suka wuce, a tare suka shige part ɗin Romeo babu ko excuse, Suna shiga Michael ya faɗa saman katafaren bed ɗin Romeo yayin da shi kuma James ya zauna gefen gadon yana sanya hannun sa ya ɗauko wayar Romeo dake saman bedside drawer kusa da system, Dai dai lokacin Romeo ya fito daga toilet ɗaure da towel a kugun sa, wow asalin kyansa ta sake bayyana, soft skin nan nashi a kwance luf kamar ka latsa jini ya fita, asalin surar murɗanɗan jikin sa ta bayyana, hannun nan nasa kamar zasu fashe saboda horo, kasan cewar jikin sa a koi ɗan ruwa ruwa hakan yasa kyakkyawan dark black gashin kirjin sa suka kara kwnciya luf, gashin kan sa a jiƙe alamar ya wanke, zubo masa gashin yayi har bayan sa yayin da shi kuma guntu na gaban goshin sa ya zubo masa a face na shi, sai faman tattare wa yace lallausan laɓɓan nan nasa kamar ya sanya musu lipstick ja dan sun kara ja sosai, lallausan gashin dake kwace a cinyoyin sa da hannayen sannan sun kara kwanciya sosai gwanin ban sha'awa, ya kware wajen iya lumshe ido, a yanzu ma sai fama lumshe dara daran blue eyes na san yake kamar mai jin barci, ga wasu guraye a flat tummyn sa irin na jaruman maza. Wucewa yayi ya shiga wani wajen da aka keɓe da glass ba tare da ya lura da su Michael ba. Good 40mins ya ɗauka a cikin wajen kafin ya fito, nan take bedroom ɗin ya gauraye da wannan fitinanniyar kamshin perfume ɗin nasa, shirye yake cikin wandon jeans baki mai bala'i kyau da tsada sai Turtle high blue daya sanya a jikin sa ya ɗaura puffer Jacket baki a sama, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hair sa da ya sha gyara a bayan sa, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa ya zubo masa a saman kyakkyawar face ɗin sa, sai kyalli gashin ke yi yasha gyara ga kamshi mai bala'i daɗi da yake zubawa, ba karamin kyau yayi ba, still wannan diamond watch ɗin nasu na manne a hannun sa, sai kyalli yake yana ɗaukan ido, yayin da wuyar sa ke sanye da gold chain necklace masu bala'i kyau da tsada, sai kyalli suke suna ɗaukan ido, hakan ba karamin kyau ta kara masa ba, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin wata laullausan bedroom slippers fari tas mai bala'i kyau da laushi kamar jikin mage, sai fitinanniyar kamshin wannan perfume ɗin nasa ke tashi daga jikin sa. Wannan fitinanniyar kamshin ita ta kai wa su James sakon Romeo ya fito, a tare su ɗago kai suka kalle sa, wucewa yayi ya zauna gefen gadon kusa da Micheal tare da jawo system na shi dake saman bedside drawer ya kunna ta cikin sauri har suna haɗe baki wajen cewa "Good morning lion" shiru ya ɗan yi na yan mintoci, ba tare da ya kalli in da suke ba, kasa kasa da wannan sexy voice ɗin nashi mai kwantar da hankalin mai sauraro yace "How are you doing this morning?" A tare suka amsa da "we are doing well what of you" shiru ya musu ba tare da ya sake magana ba. Matsowa kusa da shi Micheal yayi tare da kwantar da kan sa saman cinyar James cikin murya kamar mai yin shagwaɓa yace "lion please I need money I'm broke" "same here" James ya faɗa, yana matsewa Michael kumatu da hannun sa, shiru Romeo ya musu bai yi magana ba, shiru suma suka zauna basu sake magana ba sun zuba masa ido suna kallon sa. Almost 30mins suna zaune shiru in da sabo sun saba, gently yasa hannu ya ansa wayar sa dake hannun James tare da juyowa ya kalli Michael dake ta faman turɓune fuska irin na shagwaɓa, "i need hot coffee" ya faɗa in a cool voice, kallon time James yayi a jikin diamond watch na shi 11:00am dai dai yana kokarin niƙewa dan yaje ya kawo wa Romeo breakfast na shi, dan lokaci yin breakfast na shin tayi, bai kai ga miƙewa ba Michael ya rigasa miƙewa, da sauri ya diro daga gadon ya nufi waje Michael na fita James ya juyo ya dubi Romeo "a nan zaka yi breakfast ne?" Gyaɗa masa kai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, daman can shi Romeo bai cika zuwa table cin abinci ba dan time ɗin cin abincin sa daban dana kowa a gidan 11 na safe yake breakfast, yayin da su kuma su Michael suke breakfast 8, sai 4 na yamma yake cin abincin rana yayin da su kuma su Michael suke cin na su 2, da daddaren kam bashi da takamaimen time na cin abinci wani lokaci yaci da wuri wani lokaci har 2 na dare yake kaiwa wani lokaci ma baya cin abincin daren maltina kawai yake sha, bai damu da cin abinci sosai ba, musamman abinci mai nauyi bai damu sosai da ci ba da daddare. "Bro I want go somewhere" cewar James shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba yayin da hannun sa ke kan wayar sa ga system nasa a saman lallausan cinyar sa. A haka Michael ya dawo ya same su, hannun sa ɗauke da katuwar tray mai shake da kayan abincin su na turawa, saman Chinese carpets dake kusa da gadon ya ajiye tray ɗin sannan ya faɗa saman gado yana faɗin "I'm tired" miƙewa James yayi ya fara serving na Romeo tun kafin ya sauko, daman idan har a bedroom na shi zai yi breakfast to su suke serving na shi dan bai yarda wani bodyguard ya shigo masa ɗaki ba, ko gyaran bedroom ɗin ma TGA ke masa, idan kuma TGA baya nan to sai dai uncle Herry ko daddy, dan James da Michael kam basu iya gyaran bedroom ba, suma gyara musu a ke, mu samman ma Michael da yafi kowa lalaci da son jiki bai san aikin wahala, shi yasa baya karatu dan yana ganin karatun ma wahala ce caza masa kai zata yi, ba abun da ya iya sai ya ɗauki wanka yaci gayu ya zuba chain a wuya ya kwashi kuɗi da mota ya tafi yawo da abokai, idan kuma ya dawo sai cin abinci da barci, baya neman faɗa sai ka neme sa, idan kuma ka nemesa faɗa in ya fara yi baya bari, har sai in anyi Sa'a James ko Romeo suna kusa, su kaɗai ke iya dakatar da shi, ban da su ko daddy bai isa ya dakatar da shi ba, ban da wannan ba wani abun da Michael ya iya, shi kuma James ga kwakwalwa da kaifin basira sai dai kashe ya jefa kan sa cikin haɗari, ya kammala karatun sa, a School da Michael ke karatu a nan suka yi karatu dukkan su. Gently Romeo ya ajiye system na sa saman bedside drawer ya miƙe ya nufi saman Chinese carpets ɗin ya zauna tare da lanƙwashe kyawawan kafafun sa, James ya tura masa abincin a gaban sa, cup ɗin coffee ya fara ɗauka slowly ya kai ɗan karamin bakin sa ya ɗan kurɓa ya cire. Baki ɗauke da excuse TGA ya shigo bedroom ɗin, jikin sa sanye da pajama launin sky blue, yayi kyau sosai, in the first place idan kaga face na shi sai ka rantse da Allah face ɗin Romeo kake gani sai ka zuba masa ido sosai sannan zaka iya ganin ban ban cin su, idan ka gansa da kyau zaka ga basu wani kama sosai irin wannan kamman ne da a ke cewa kaman jini, Kusa da Romeo yazo ya zauna yana faɗin "Good morning My lion" shiru Romeo ya ɗan yi na yan sakanni kafin yace "Morning uncle how are doing this morning?" Fuska a ɗaure TGA yace "I'm fine what of you?" Shiru Romeo ya masa bai sake magana ba, cikin girmamawa Jame da Michael suka haɗa baki wajen cewa "Good morning Uncle" murmushi TGA yayi kafin yace "My Tiger, your eyes is shiny like Tiger eyes" kara lafewa a gado Michael yayi yau da alama yan shagwaɓan nasa suna gaban goshin sane, sai wani narkewa yake yana wani yauƙi hannu uncle TGA yasa suka fara breakfast tare da Romeo, yayin da shi kuma James ke zaune yana ta aikin serving na su, duk abun da suka nuna sai ya zuba musu cikin nitsuwa Romeo ke cin abincin sa hankali kwance, kamar bai son taunar abincin haka yake ɗan tauna, shi kuma uncle TGA sarkin sauri komai nasa sauri sauri yake ayi kawai a wuce wajen, ya riga Romeo ma gama cin abin cin, james ya miƙo masa tissue paper ya ansa ya goge bakin sa sannan ya miƙe ya nufi dressing room na Romeo, yayin da shi kuma Romeo yake taunan abincin cikin class da kwanciyar hankali kamar bai son tauna haka yake ɗan motsa lausasan laɓaɓɓan sa. Jim kaɗan Tga ya fito sanye da face mask a face ɗin sa, sai dai ya gangaro da face mask ɗin zuwa gemun sa bai sanya dukka ba, kai tsaye gadon Romeo ya nufa, cike da so da kauna ya mannawa Michael kiss a goshi yana faɗin "Ilove you my Tiger, take good care of yourself" kamar Tga yace ya kara lafewa a gado haka ya kara rungume pillow yana ɗan turo baki yana kwaɓe fuska, sai hararar wasa James yake masa. Har Tga ya kai bakin kofar fita bedroom ɗin ya jiyo voice ɗin Micheal can kasa kasa yana faɗin "uncle I'm not feeling fine" "what?" Tga ya faɗa tare da juyowa da sauri, shi kam Romeo ko a jikin sa dan ya san rashin lafiyan me Michael keyi, ya kwashe kuɗin account nashi ne kap ya saiwa friends nasa motoci da wasu abubuwan shine yanzu ya zo ya kwanta ya dawo shagwaɓaɓɓe wai bai da lafiya. Da sauri Tga ya juyo ya dawo wajen bed ɗin tare da sanya hannun sa saman lallausan kumatun Michael ɗin yana faɗin "What is wrong with you?" "My head" yayi maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka ɗaura hannun sa Tga yayi saman goshin Michael ɗin yana waro ash eyes nasa waje, James ji yake kamar ya kwashe su da mari dukkan su daga Michael ɗin har uncle T ɗin, dan haushi ma suka bashi, wai duk iskancin da Michael yazo da shi sai su biye masa suna wani lallaɓa sa yanzu uncle ya sani sarai ba wani ciwo dake damun Michael fa ce iskanci irin nasa kawai, amma sai uncle ya biye masa. Dawo da kallon sa Tga yayi kan Romeo a nitse yace "please my lion ka duba min Tiger kaji?" Cikin sauri Michael yace "No uncle I'm okey now" James bai san lokacin da murmushi ta kubce masa ba, shi kan shi Tga abun yaso sashi murmushi amma sai ya danne, shi dai Romeo ko kallon in da suke ma bai yi ba kamar bai san da mutane a bedroom ɗin ba, Waya Tga ya ciro daga aljihun sa, ya ɗan latsa kamar na 2mins sannan ya mai da aljihun na sa ya juya ya nufi hanyar fita, a sukwane Michael ya miƙe zaune yana kallon wayar sa da ya fito da ita daga aljihun sa saboda yar kara da tayi, da sauri ya diro kasa daga saman gadon ya tafi da yar gudun sa ya haye bayan Tga yana faɗin "Thank you uncle" tangal tangal Tga yayi kamar zai faɗi kasa dan bai yi expecting Michael zai haye masa baya ba A hankali ya sauke Michael ɗin daga bayan sa yana faɗin "My Tiger now your okey kenan?" Turo baki Michael yayi ya wuce ya fice daga bedroom ɗin daman kuɗi yazo nema wajen Romeo tun da ya samu wajen uncle Tga shikenan ai bukatar sa ta biya wucewa shima Tga yayi ya nufi waje yana faɗin "I'm waiting for you at the garden My lion" jinjina kai kawai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, dai dai lokacin ya kammala cin abincin na sa ya miƙe ya zauna a bakin gadon sa, yayin da shi kuma Tga ya fice daga bedroom, James kuma ya tattare kayan abincin yayi waje da su. **💞NIGERIA💞** _👹DAULAR MUTUWA👹_ Cikin wannan ɗakin Rimsha ta kwana, kwanan zaune sukayi, tun tana kuka hawaye na fita har ya dai na fita, yanzu kukan ma ta kasa yi ga bala'i yinwa da kishin ruwa da take ji, sukam sauran yaran sun sume saura yarinya ɗaya, tare sukayi kwanan zaune da Rimsha, gashi Rimsha ta kasa iya ambato sunan Allah sun rufe mata baki, ji take an shaƙe mata maƙogwaran ta, haka ta hakura ta takure waje guda tana jin wayan nan dodannin suna ta gurnani suna ihu a dab kunen ta amma ba yadda ta iya haka ta zauna a kasa cikin dotti, da daskararren jini busasshe, bata da zaɓi dole ta zauna a wajen. Allah sarki Rimsha renon madara da chocolate dasu ice cream, kwanciyar gadon lausi da Ac a rufu da bargo nai laushi, yau ta kare da kwanan zaune cikin daskararren jini ga wari sannan ga wayan nan dodannin masu razanar wa da ɗan Adam kwakwalwan sa. Washegari sai da rana ya ɗaga sannan magicians ɗin suka zo suka buɗe su, ba ƙaramar razana sukayi ba ganin still Rimsha na cikin hayyacin ta, ita da ɗayar yarinyar, sun sha mamaki sosai, haka suka fito da su suka kai su wani keɓaɓen waje mai kama da gida, yana da girma sosai, a nan suka turasu cikin wani ɗaki suka juya suka koma, suka ɗauki wayan can sauran yaran da suka suman kuma suka tafi da su in da suke yanka mutane. A hankali Rimsha ta fara rarrafawa a cikin ɗakin ɗan ba zata iya miƙewa ba, saboda yinwan da take ji, kamar a mafarki ta ga kamar halittar mutun zaune an kifa kai da gwiwa, ta kasa gane mace ce ko namiji Saboda idon ta baya gani sosai saboda yinwa da take ji, Dan ma ɗakin nada haske sosai ba kamar ɗakin da a ka fito da su daga cikin shi ba, hakan yasa Rimsha ta iya karewa wan nan halitta kallo, da kyar ta iya rarrafawa a kan gwiwowin ta, ta ƙarisa wajen wan nan halitta wadda ta kasa gane wace halitta ce, babu ko tsoro a rattare da ita ta sanya hannu ta taɓa wannan halitta, a razane wannan halittar ta ɗago kan ta wadda ta kasan ce....✍️✍️ Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 B 💞Star Lady💞 TRIPLET'S https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞*STAR LADY*💞 Mai neman karin bayani yamin magana ta wan nan number 09162620621 Masu tambaya ta ma'anar sunayen danake using dasu a book ɗin gasu nan Names and their meaning 1Ayla Moonlight. 2Aafia Confident . 3Umaisha soft hearted 4 Ayla Moonlight 5 Rimsha means Beautiful or face like moon 6 Jehan meana the world EPISODE 22 a razane wannan halittar ta ɗago kan ta wadda ta kasan ce mutun ce mace ce yarinyar yar karama, wadda wahala ta mai da ta kamar kashi da rai, duk ta rame ta bushe gaba ɗaya face nata ya rama ga idon ta sun yi manya manyan kamar zasu faɗo waje saboda raman da tayi, a tsorace Rimsha ta ja da baya tana kallon yarinyar nan wadda a shekaru ba zata wuci 14 years ba, baya baya Rimsha ta ja ta koma ta zauna ɗan nesa da yarinyar, a hankali ita ma wan can yarinyar ta rarrafo ta kariso wajen Rimsha ɗin suka haɗu suka zauna shiru, dukkan su sai ƙugi cikin su ke musu saboda yin wa. Kamar da ga sama sukaji wan nan yarinyar tana faɗin "Sannun ku da zuwa Daukar mutuwa, daular da ba wani mai rai da yake shiga ya fita, na jinjina muku da ku ka iya tsallake level 1 da 2 ku ka iso nan na taya ku murna sosai, amma sai dai daga nan babu in da zaku sake zuwa kai tsaye lahira zaku wuce" duk da ba wani Hausa kirki Rimsha ke ji ba ta fahimci abun da yarinyar take faɗi, sosai murmushi ya bayyana a face ɗin Rimsha jin yarinyar tayi magana da da farko ta ɗauka kawai ba mutun bane idon tane ke nuna mata kamar mutun ne a wajen. Cikin zumuɗi ta rarrafo ta matso kusa da yarinyar ta sanya hannu ta dafa kafaɗar yarinyar tana faɗin "zamu fita In...ta kasa fitar da In Sha Allah ɗin maganar ta tsaya kamar wadda a ka shaƙe, hannu tasa a wuyar ta tariƙe da karfi tana jin yadda wuyar nata ke mata raɗaɗi kamar ana zare jijiyoyin wajen, nan take ta fara hawaye sirara masu ɗumin gaske, ganin haka yasa yarinyar ta riƙo ta tana faɗin "Ki dai na wahalar da kan ki, babu wanda ya taɓa shiga ɗaular mutuwa kuma ya fita, rayuka sun fi a kirga suka zo nan kuma suka tafi lahira kamar ba'ayi su ba, abun da nake so dake kawai yanzu ki shirya daga yanzu kowani lokaci za'a iya samun mai son wani abu daga jikin ki" ita dai Rimsha gaba ɗaya ta kasa magana sai hawaye take masu zafi saboda raɗaɗin da wuyar ta ke mata. Rarrafowa ɗayar yarinyar ma tayi ta kariso wajen su, suka zubawa Rimsha ido, yayin da ita kuma Rimsha take kokarin ceto muryan ta dan ta samu ta musu magana. Almost 30mins suna haka, sannan Rimsha ta samu sauki daga shakan da a kayiwa wuyar ta, a hankali murya ciki ciki tace "Wayyo na shiga uku na" da sauri suka rirriƙeta suna mata sannu, shiru ta ɗan yi kafin ta iya furta "Zan sha ruwa" a takaice yarinyar da suka samu a ɗakin tace "kullun sau ɗaya suke kawo min abinci da ruwa, kuma already sun riga sun kawo na yau na cinye sai kuma gobe dan haka kiyi hakuri kawai" shiru Rimsha tayi tana mamakin me ya hana ta iya kiran sunan Allah kuma gashi tana iya faɗi a ranta amma a fili ta kasa faɗe. Kallon yarinyar da a ka kawo ta tare da Rimsha yarinyar da suka samu a ɗakin tayi tace "Ya sunan ki?" Da sauri yariyar da aka kawosu tare da Rimsha tace sunana Kausar" yanayin yadda tayi maganar ne yasa yarinyar tace "amma ke ba bahaushiya bace ko?" Gyaɗa mata kai kausar tayi kafin tace "Eh ni bayarbiya ce" jinjina kai yarinyar tayi kafin tace "Ni kuma sunana Alia amma mamana tana kirana da Ayla so kawai ku ma ku kirani da Ayla ɗin koba komai zan iya samun damar in rinƙa tuna mamana" sai lokacin Rimsha ta sanya musu baki a cikin maganar da suke tace "how many days have you being here" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "Good 3 years" zaro ido waje Rimsha tayi ta ma kasa magana tayi shiru ta koma ta jingunu da jikin bangon ɗakin tana jin matsanancin ciwon ciki saboda yinwa, haka ta dafe cikin ta da hannun ta dukka biyu tare da runtse idon ta gam tana matsar kwallan dole, zuba mata ido kawai su Ayla sukayi basu da wani hanya da zasu iya taimaka mata fa ce su zuba mata ido kawai, dan suma taimakon suke nema ba abun da Rimsha ke tunawa sai mum dad gwaggo da Jehan sune duniyar ta, yayin da time to time tunanin GAR yana ratsa tunanin su Jehan a cikin ƙwaƙwalwar nata, haka suka zauna jugum jugum, sai matsar kwalla take wadda a halin yanzu sai tayi da gaske ma kwallan ke fitowa daga idon ta. _KANO_ Time ɗin ɗaukan Jelly a school yayi daddy ya ajiye duk wani aikin sa ya nufi School nasu dan ɗaukan ta, nan ya ji tashin hankali da bai taɓa jin makamancin sa, uncle's ɗin su Jelly sun shaida masa Jelly bata zo school ba yau, lokaci guda yaga duniya na juya masa dafe kan sa yayi ya fara neman layin su Zuwaira dan yaji ko dai ta koma gida. Bugu ɗaya Zuwaira ta ɗauka murya sa har rawa yake sai haɗe words yake wajen tambayar ko Jelly ta dawo gida, cikin girmamawa Zuwaira tace masa "A'a bata dawo ba" sake wayar yayi ta faɗi kasa ta tarwatse a wajen, dafe kan sa yayi yana tuna irin rabuwar da suka yi da safe tabbas akoi matsala, kasan cewar shi daddyn Jelly ƙaramin abu yake iya birki tashi hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya zube kasa, kafin ya kai kasa uncle's ɗin su Jelly suka riƙe sa suna faɗin innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Da sauri suka yayyafa masa ruwa, dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali, ba tare da ya buɗe ido ba ya fara sambatu kamar zararre "why Jelly? Why zaki wa daddyn ki haka, daman tun da naga irin yadda muka rabu da safe na tafi gaba na na faɗuwa naje office ina ta tunanin anya lafiya kuwa ashe dai ba lafiya ba, dan Allah Jelly ki dawo nayi alkawarin sai dai komai ya faru da ni amma ba zan taɓa aura miki wanda baki so ba, dan Allah ki dawo tabbas na miki alkawari Imran zan aura miki" haka daddy yayi ta sambatu, sosai uncle's ɗin su Jelly suka tausaya masa tare da lallaɓashi da bashi baki. Da kyar suka samu yayi shiru amma ya kasa miƙewa ma bare kuma a je ga tukin mota, wani uncle ɗin su Jelly ne ya jasa a mota suka wuce gida, dan ko magana daddy ya kasa yi, yana bala'i son jelly fiye da tunanin duk wani mai tunani, ita kaɗai garesa saboda ita yaki raɓar kowa, kuma yaki yin wani aure Ita ce duniyar sa ita kaɗai yake ɗaga ido ya kalla yaji daɗi a rayuwar sa itace farincikin sa komai nasa, baya jin zai iya rayuwa a duniyar nan idan har bai gan taba, sai fita da sauri sauri numfashin sa ke masa har suka isa gida. Fita motar ma ya kasa sai uncle ɗin ya taimaka masa har zuwa bedroom na sa, ya kwantar da shi a saman gado, uncle ɗin na kokarin gyara masa pillow kenan suka ci karo da farar wasika da Jelly ta ajiyewa daddy, cikin sauri Uncle ya ɗauko takardan ya buɗe tare da miƙa wa daddy, daddy jiki har kerma yake wajen ansan takardan ya fara karantawa kamar haka "i love You my dad I love You my world" dogon numfashi daddy yaja da kyar ya iya cewa "ina wayata" da sauri uncle ɗin yace "wayar ta fashe ai tana cikin mota" shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "yanzu na tabbatar da zargina, da gaske guduwa Jelly tayi ba sace ta akayi ba, tun da har wasiƙa ta ajiye min" shiru uncle yayi yana mugun jin tausayin daddy, dan tun Jelly na da 5 years uncle yake karantar wa a School ɗin nasu yasan irin soyayyan dake tsakanin daddy da Jelly, yasan irin son da daddy ke wa Jelly. Sunyi shiri dukkan su Uncle yana son ya koma amma ya kasa faɗa wa daddy zai koma saboda tausayin da daddy ya bashi, suna cikin wannan halin kenan dolly ta shigo ɗakin tana yar kuka saboda ita ma tasan lokacin dawowar Jelly daga school yayi shiyasa tazo mata oyoyo, ba karamin karawa daddy tashin hankali dolly tayi ba, lokaci guda yaji karfi yazo masa cikin hanzari da kuzari ya miƙa ya nufi waje, ba karamin mamaki uncle yasha ba ganin yadda daddy ya miƙe da kuzarin sa kamar ba shi ba. Da sauri uncle ya miƙe yabi bayan daddy, daddy da kan sa yaja motar kai tsaye sai police station, yaje ya shigar da report a kan batar Jelly ɗin san nan ya wuce ya sauke uncle a school, ya zarce gidan Radio suma ya sanar da su, daga nan ya fara neman ta da kan sa a cikin garin Kano, gashi wayar sa ta fashe bare ya nunawa jama'a hoton ta, wani zuciya nace masa ya sanar da Imran wani zuciya kuma yace masa a'a ya kyale sa tun da Exam suke kada ya hana shi rubuta Exam nashi, gashi kuma Exam na karshe suke karya samu matsala gwara kawai ya kyale sa tun da sun kusa dawowa sai sun dawo kawai, haka yarinƙa sake sake a ransa yana yawon neman Jelly a cikin Kano bai taɓa kawowa a ran sa ta fita garin Kano ba shi yasa bai yi wani yunkurin neman ta a wajen Kano ɗin ba. *KADUNA* A kawo driver ya sauke su Jelly, nan fa Jelly taga duniya dan ko da ta fito daga motar ta kasa gaba ta kasa baya ta tsaya shiru a bakin hanya, ita daman a nata tunanin idan tazo Kaduna kawai gidan su Imran zata gani sai ta shiga amma sai taga a kashin hakan, Tana tsaye tana ta kallon jama'a dake ta harkan gaban su har rana ya iso in da take, ganin rana ya iso in da take ne yasa ta tsallaka titi ta fara tafiya da kafar ta wadda bata san ina ta nufa ba, tana rungume da School bag ɗin tana tafiya. Sosai tayi tafiya tsakanin ta da kawo har ta fita daga cikin jama'a ba tare da ta ankara ba, tafiya kawai take bata san in da ta dosa ba, bata fargaba sai jin tayi an damki jakar dake hannun ta ta baya, da sauri ta juyo tana kallon su, natasane su biyu, cikin tsawa wanda ya riƙe jakar yace "kawo ta nan" yan waige waige tayi sai lokacin ta lura da tabar cikin mutane, rai a ɓace ga yinwa na damun ta tace "bag ɗin kane da zaka ce na kawo" matasa ne biyu tsaye kai da ganin su kaga yan buguwa dan bakin nan nasu bakin kirin kamar gawayi sabida shaye shaye, san nan ga wani askin yan iska dake kan su sun bar dada a tsakiyar kai. Wanke ta da wani wawan mari ɗaya daga cikin su yayi, ɗayan kuma ya fisge jakar suka hankaɗe ta ta faɗi kasa suka kwasa a guje suka bar wajen, kuka ta sa mai sauti tana faɗin "wayyo Allah daddy na" da kyar ta iya miƙewa zaune tana kuka tana kiran daddyn ta, yayin da shi kuma daddy ke can Kano yana haukan neman ta lungu da sako. A wannan halin wani babban mutun mai ɗan yawan shekaru yazo wajen ya sameta, irin mazan tashan nan ne marasa mutuncin nan dan kallo ɗaya zaka wa face nashi ka gane hakan kallon tsab yayiwa Jelly nan take ya fara washe baki, kusa da ita yazo ya tsaya yana faɗin "Yan mata me kike yi a nan kuma?" Cikin kuka da muryan shagwaɓa tace "wasu ne suka kwace min School bag ɗina" murmushi mugun ta yayi yana faɗin "ayya sannu ko? Yanzu dai to tashi muje gidana na baki wani jakar" jin yace zai bata wani jaka yasa ta yunkura tana kokarin muƙewa, cikin sauri yasa hannu yana kokarin ɗaga ta, a sukwane ta ja baya cikin tsiwa tace "Don't touch me" ko a jikin sa bai damu ba yace "Okey to tashi da kan ki" ba musu ta miƙe sai shagwaɓe fuska take tana turo baki, shi kuwa mutumin sai murmushi irin na yan bariki yake, ya nuna mata hanya wani yar lungu yace suje, ba musu ta wuce yabi bayan ta sai washe baki yake, yana murmushi irin na yan bariki. Yayin da shi kuma daddy bai dawo gida ba sai 2 na dare, da kyar yake iya jan kafar sa ya shiga bedroom na shi, nan ya samu dolly saman gado sai kuka take, ba karamin tayar masa da hankali dolly keyi ba, dan in ya ganta sai yaga kamar Jelly na zaune a gefen ta, yau daddy ya kasa cin abinci ma bare wani zancen wanka, yana shigowa bedroom ɗin dolly ta taho da gudu ta haye jikin sa tana yar kara, runtse ido yayi ya wuce yaje ya sanyata cikin kejin ta sai kuka take amma ya share ta kamar bai jiba ya wuce ya dawo ya zauna saman gado ya haɗe kai da gwiwa yana tunanin mafita, ta ina zai fara neman Jelly gobe. A wajen zaune ya kwana kamar yadda yaga rana haka yaga dare, babu alamar barci ko kaɗan a idon sa ana kiran sallan asuba ya fice daga gidan ko wanka bai samu daman yi ba, yana yin Sallah ya wuce police station dan yaji ko ansamu wani information akan ta kwata kwata yama manta da wayar sa bai kaita gyara ba. Ko da yaje police station ba wani information haka ya wuce neman ta lungu da sako ko abinci bai ciba dan baya jin yinwa ko kaɗan, bazama yayi cikin gari kawai yana neman ta. 💞KADUNA💞 💞Aafia💞 Zaune Aafia take a cikin department nasu department of law, tayi shiru tana latse latse a wayar ta, jikin ta sanye da atamfa riga da skit ɗinki ya kamata sosai, ya bi shape ɗin jikin ta ya zauna, yayin da tayi ɗaurin ture kaga tsiya a kan ta, ga uban attachment da ta zubo har baya kamat gashin ta, sai faman turɓune fuska take. Baki ɗauke da sallama Rufee ta kariso wajen tana wani murmushi kamar ba na lafiya ba, hannu ta miƙa wa Aafia suka gaisa, Aafia na faɗin "Ina su Amal" "Amal tana tare da Mansur, ita kuma Anisa taje sayan drinks" Rufee ta bata amsa, shiru Aafia tayi bata sake magana ba. "Aafia a koi wani Alhajin dake son magana dake ya takuramin, dan Allah a wannan karon kam kiyi hakuri ki bashi dama shi kam, na san halin ki yanzu zaki iya cewa ba haka ba shi yasa tun kan kice nake nema masa alfarma" ɗaure fuska Aafia tayi kafin tace "Rufee kin dai san bana son irin hakan ko? Karatun nazo yi school ɗinnan ba kula samari ba, bani da lokacin ɗa namiji a rayuwa ta ta yanzu, idan kuma na gama School kin san zaɓi na mutun ɗaya ne Prince Nawid duk da ban san shi ba, ban san ina zan ganshi ba, ban san wanene shi ba, amma dai shi nake so, tun ranar da na fara ganin taimakon da yayiwa wata mara lafiya a Tv daga ranar ya shiga raina bana ganin kowa sai shi, shiyasa ma bana kula maza kin san hakan, dan haka kada ki sake kawomin zancen wasu mazan bana so" yar dariya Rufee tayi kafin tace "To shi kuma TGA ɗin fa? Ko kin dai na son shi ne?" Guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Ina mutuwar son shi mana, amma tun da na san ba samun sa zan yi ba ai dole na kama dahir, mutumin da Bature ne bai san Nigeria a ido ba sai dai a suna, kuma chiristen ne fa waya sani ma ko baya son bakaken fada, ko ya tsani Musulmai kin san fa turawan nan haka suke basa son Musulmai da kuma bakaken fata" dariya Rufee tayi kafin tace "Wallahi kuwa muna wahalar da kan mu wajen son turawan nan, gashi mafiyawancin su ba son bakaken fata suke ba, sannan dayawa daga cikin su basa son musulmai da addini musulunci baki ɗaya" Aafia na kokarin yin magana Umaisha ta kariso wajen bakin ta ɗauke da sallama Aafia da Rufee har suna haɗa baki wajen amsa mata sallamar, kusa da Aafia ta tsaya sai faman kwaɓe fuska take tana turo baki kamar biro "lafiya Umaisha kike kwaɓe fuska haka?" Cewar Rufee uwar son jin gulma, kara turɓune fuska Umaisha tayi kafin tace "Wannan yaya Akil ɗin ne mana ya wani dami mutun da kira, nifa Aunty Aafia yanzu bana son shi, da ɗin ma soyayyar yarin tane, yanzu kuma ina big girl kama ta me zanyi da Small boy, ni gaskiya sai babban mutun irin mai 35 years ɗin nan zan aura" shekewa da dariya Rufee tayi tana tafa hannu tana faɗin "Gaskiya Umaisha yanzu ai ke ba matan yara bace sai manyan alhazawa dama kuma gashi suna ta bibiyar Aafia taki kulasu, ke tun da irin sune zaɓin ki wlh sai na haɗa ku kawai" Umaisha na kokarin yin magana Aafia ta rigata da cewa "Ke Umaisha wallahi ki kiyayi kanki ina rabaki tam, karki kuskura ki bari yaya Akil ya damkeki kin san dai halin sa, wallahi ina faɗa miki yanzu in da ya jima rabon sa da Nigeria nan ina da tabbacin ya kusa zuwa" dogon tsaki Umaisha taja kafin tace "Nifa a dane ya min wannan iko da iskancin nasa kuma na hakura na biye masa, yanzu ko wlh bai isa ba, ina da yancin nayi abun da nake so, kuma babu wanda ya isa ya aura min wanda bana so yanzu nasan me nake" Aafia zatayi magana wayar Umaisha ya fara kara, ansan wayar Aafia tayi, da mamaki ta ɗago ta kalli Umaisha "Ke Umaisha waye kuma Basir ɗan damuwa?" "Yaya Akil mana shi na sawa basir kuma ɗan damuwa" Umaisha ta faɗa tana jan tsaki, waro ido waje Aafia tayi tana salati, Umaisha tafi karfin ta, ita kam Rufee hannun Umaisha taja suka wuce tana faɗin "Ke dai Aafia ki zauna kan ki ya kulle ga kanwar ki nan ta gane gaskiya, muje Umaisha ke ba matar yara bace" baki galala Aafia ke kallon Rufee da Umaisha har suka kurewa ganin ta, sannan ta dawo da kallon ta kan wayar Umaisha dake ta faman ringing. Bayan kiran Akil ɗin ya katse ne ta shiga binciken wayar da kyau dan taga me Umaisha ke yi, ko ta ina Aafia ta shiga a wayar sai ta samu massage ɗin Akil, kama da ga WhatsApp, facebook, Instagram, Twitter, dukka massage ɗin Akil take cin karo da shi, in da yake wa Umaisha zazzafar warning a kan kar ta kuskura ya dawo ya samu tayi wani abun da ba dai dai ba, sai kuma massage na tambayar ta lafiya bata ɗaukan call ɗin sa tun last week. Sosai Aafia ta binciki wayar dan taga ko dai Umaisha ta samu wani saurayi ne yasa tace bata son Akil, amma ina ba wani hiran ta da wani namiji da ta gani, Akil ɗin dai shi kaɗai ne, sosai Aafia ta sanya ƙwaƙwalwar ta cikin tunanin me yasa Umaisha zata ce bata son Akil yanzu, bayan tun tana da 15 years a duniya take dakon son sa bata taɓa cewa bata son shi ba sai cikin yan kwanakin nan, haka Aafia ta rinƙa tunani amma bata samu wani solution ba, gashi sai kira Akil yake ta kasa ɗauka dan bata da amsan da zata bashi in ya tambaye ta ina Umaisha kuma tasan halin sa yanzu tana ɗauka zai iya fara mata ruwan bala'i shi yasa ma bazata ɗauka ba, ranta cike da tunani ta tura wayar Umaisha cikin jakar ta ta ci-gaba da latsa nata wayar tana mamakin sauyawan Umaisha. *💞WASHINGTON DC💞* Zaune suke a palon kasa da daddy, uncle Herry, James, Tga, John, Jay, sai Michael da ya tada kai da cinyar Tga yana latsar wayan sa, Romeo ne kaɗai baya wajen kasan cewar shi daman bai cika zama a palon kasa ba, sai hira su uncle Herry suke cikin kwanciyar hankali, ga sanyin Ac da daddaɗar kamshin air freshener dake tashi a palon, gwanin ban sha'awa. Baki ɗauke da excuse wata kyakkyawar maturiya ta shigo palon wadda idan ka ganta zakaga kamannin Micheal a face ɗin ta, jikin ta na sanye da wandon jeans baki sai t-shirt ta ɗaura fleece jacket a saman kayan nata wadda yazo mata har gwiwar ta, babbar mace ce ba yarinya bace. Jin voice ɗin ta yasa Michael miƙewa a sukwane, yayin da gaba ɗaya palon suma suka miƙe suna kallon ta da mamaki. Kallo ɗaya Michael ya mata ya kawar da kan sa, nan take face ɗin sa ya sauya kamar ba shi ba brown eyes nashi suka sauya launi zuwa ja jijiyon wuyar sa dana kan sa duk sun tashi cikin tsawa da ɓacin rai yace "get out before I open my eyes!!!" cikin sanyin Murya James yace "Please Michael stop saying h....Bai kai karshen maganar ba Michael ya daka masa tsawa mai firgitar da kwakwalwar mai sauraro "shut up James!!" Tashin sense a fusace James yace "are you mad Michael? are you heard what you are said" damko wuyar rigar James Michael yayi tare da haɗe wa da wuyar tasa ya shaƙe sa da karfi yana kallon cikin idon sa, ga jijiyon kan nan nasa duk sun tashi sai zufa yake haɗawa duk da sanyin Ac dake palon, sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, ran maza ta ɓaci, rai a matukar ɓace yace "I hate her, I don't want to see close to me, tell her to leave this house, if not i will kill her with my hand" ya kai karshen maganar tare da kara shaƙe wuyar James ɗin da karfin gaske, cikin fushi James yasa hannu ya damki hannun Michael dake wuyar sa yana kokarin ɓanɓaren hannun Michael ɗin daga wuyar nasa yana faɗin "Oya go an kill her!!" Yayi maganar cikin ɓacin rai, tashin hankali su Jay basu taɓa ganin James yayiwa Michael magana cikin tsawa haka ba sai yau, basu taɓa ganin in da suka samu saɓani ba sai yau, daddy na kokarin yin magana cike ta tashin hankali a face nashi, bai kai ga buɗe baki ba yaga Michael ya ya kara shaƙe James da karfi kamar zai kashe shi, yayin da shi kuma James ke kokarin ɓanɓare hannun Michael daga wuyar sa, ita kuwa mum ɗin nasu ta kasa gaba ta kasa baya ta tsaya kawai tana hawaye tana kallon su, da sauri uncle Tga ya nufo su da niyar ya rabasu, sai ganin yayi Michael ya hankaɗe James ya nufi mum ɗin su da sauri a fusace James ya miƙe ya riƙe Michael ɗin, a sukwane Michael ya juyo ya kaiwa James mugun bugu a wuya, wani irin azaban zafi James yaji ya ziyarce sa a wuyan nasa, cikin fitar hayyaci da ɓacin rai ya haɗe hannun Michael dukka biyu ya ɗaga shi sama yayi wurgi da shi gefe guda, lokacin guda shi ma James ɗin kamannin sa suka sauya, sai huci yake, ba karamin mamaki su uncle Herry suka sha ba dan basu taɓa kallon James ya ɗauki zafi haka ba, duk gidan yafi kowa hakuri shiru shiru yake yana da hakuri sosai sannan yana bala'i son Michael bai son ɓacin ran Michael ko kaɗan, amma yau da hannun sa ya bugi Michael abun da bai taɓa yi ba. Ihu azaba Michael ya fasa, gadan gadan James ya nufe sa da niyar dukan sa, da sauri Tga ya rike sa yana faɗin "Please James control your anger?" Kokarin fisge kansa James yake dan yaje ya daki Michael, yau Michael ya kai shi makura bai taɓa tunanin tsanar da Michael yayiwa mahaifiyar su ta kai ya iya yunkurin dukan ta ba Cikin zafin nama ya kwace daga rikon da Tga ya masa tare da hankaɗe Tga ɗin har sai da ya faɗi saman sofa, ba karamin tsorata Tga yayi ba, tambayar kan sa yake daman James na da karfin da zai iya tureni? Kasa miƙewa yayi ya zubawa James ido kawai yana kallon sa da mamaki Damko wuyar rigar Michael James yayi ya mikar da shi tsaye, sai numfashi sama sama Micheal keyi saboda wahala, dan ya bugu sosai wurgi da shi da James yayi, ya kasa yin wani yunkuri idon James ya rufe baya ji baya gani bai lura da halin da Michael ke ciki ba ya dunƙule hannu zai kai masa naushi kenan, fitinanniyar kamshin perfume ɗin Romeo ya daki hancin duk wata halitta mai rai dake palon A tare suka kai kallon su saman benen, yana tsaye saman bene ya goya hannu a kirjin sa ya zuba musu wannan dara daran kyawawan blue eyes ɗin nasa yana kallon su, jikin sa sanye yake da Ripped Jeans da Round neck polo shirt fara kal kamar yanzu ya fito da ita daga kwallin ta, yau dai ya saki dark black curly hair sa bai ɗaure ba ta kwata masa har bayan sa sai sheki take tasha gyara ga wani fitinanniyar kamshin da take zubawa, kyau iya kyau kamar shi yayi kan sa, soft red lips na san nan sai wani sheki suke kamar ya sanya musu lip balm Ganin sa yasa James ya saki Michael, James na sakin sa ya wuce sai numfashi yake fitarwa da sauri sauri har wani tangal tangal yake, ya taho ya faɗa jikin Romeo yana sauke huci a hankali kyakkyawan fararen hannun sa Romeo ya ɗago gentle yana ɗan bubbuga bayan Michael ɗin, slowly ya dawo da kallon sa saman face ɗin Michael ɗin, ya ɗan kalle sa sannan ya mai da kallon sa kan su mum, gently in a cool voice yace "What brought this woman in this house?" Shiru suka masa suna zare ido jikin su sai kerma yake, ita ma mum ganin Romeo yasa ta shan jinin jikin ta, duk da ita ta haifesa amma ganin sa ba karamin razana ta yake ba, ganin sa firgitata yake, in da tasan yana gida da bazata zo ba, yanzu ma tsautsayi ya kawota tana burin ganin sune shi yasa ta ansa wayar kawar ta tayi wa James massage ta roki sa a kan ya sanya security su buɗe mata tazo ta gansu kawai ta koma, da kyar ya yarda ya sanya security suka buɗe mata gate amma yace mata komai ya faru da ita shi baruwan sa, saboda son da take musu yasa tace ta yarda. Jin sunyi shiru yasa Romeo yace in a cool voice "James, TGA who gave the security authority to open the gate for her? I knew one of you most have given the security permission to do that!!!" still shiru suka masa suna zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko, dukkan su har shi TGA ɗin kirjin su sai dukan uku uku yake saboda tsoro jikin su sai kerma yake, sun sha ruwan mamaki ma da suka ga Romeo bai ɗau zafi sosai ba yau duk da mum tazo. "Dad tell her I don't want to see her in this house henceforth, if I sees her footh here again she should fine herself to be blame!!!" Ya kai karshen maganar yana kokarin juyawa kenan, muryan mum ta katse shi, har in ina take wajen furta "I love you my pleasure" tayi maganar cikin tsoro, a fusace ya juyo, har suna haɗa baki da Michael wajen cewa "I hate you!!" Tashin sense shi dai James abun nasu yafi karfin sa, shi dai yasan yana jin haushin mum amma ba irin wannan haushin ba, yana ɗan son ta kaɗan rai a matukar ɓace Romeo yace in a strong voice "tell her dad i hate her and i don't want to see her close to me, if not I will shoot her with my hand!!!" ya kai karshen maganar tare da sakin Michael yana wani sauke huci kamar mayin wacin zaki sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, Michael kuwa kamar jira yake, Romeo na sakin sa yayi bedroom ɗin Romeo da sauri, Jim kaɗan ya dawo hannun sa rike da pistol gun, yana zuwa ya sai ta mum yana faɗin "get out" a sukwane daddy yace "Michael what is this?" Harɗe hannu a kirji Romeo yayi ya zubawa Michael dara daran blue eyes na sa, murya na rawa dad yace da Romeo "Please lion stop him" shiru Romeo yayi kamar bai ji me daddy yace ba, ita kuwa mum tana tsaye ta zuba musu ido yayin da shi kuwa Michael ke kokarin harbin ta, tabbas daddy yasan Michael zai aikata sarai zai iya harbin nata kamar yadda ya faɗa dan Michael yana da zuciya kamar Romeo ba a ban za yake kiran su da Lion and Tiger ba, suna da zafin zuciya over, barin ma Romeo shi na sa zafin zuciyar na daban ne idan ya fusata ba mai iya dakatar da shi jikin daddy har kerma yake, sai faman rokan Romeo yake da ya dakatar da Michael "Please My lion stop him" wata gigitatchiyar tsawa Romeo ya dakawa daddy wadda ya sanya gaba ɗaya jama'ar palon razana da kiɗi ma "I can't stop him dad, Michael shoot her!!" Mum na jin abun da Romeo yace ta juya a guje ta fice daga palon, dan tasan halin su sarai tsab zasu iya aikata abun da sukayi niyya, dan tun suna yara ba wadda ya isa ya sanya Romeo yayi abu kuma ba wadda ya isa ya hana shi, ganin Romeo da idon ta a lokacin da yake cikin farinciki ma razana ta yake bare kuma ransa ya ɗan ɓaci, dan yau bai ɗau zafi bama, da ya ɗau zafi da ya jima da harɓe ta. Mum na fita Michael ya faɗa jikin Romeo tare da sakin kuka mai ɗan sauti yana faɗin "she is wicked, she has wrong us, please lion tell me the reason why has she done that to us why?" Ya kai karshen maganar tare da kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Rungume sa Romeo yayi suma wuce bedroom ɗin Romeo. A tare su dad suka koma suka zauna, dad ya tsorata sosai, duk da cewa baya son mum bai son a kashe ta, ya fi son dai tayi nisa dasu ne ta bar su su samu peace of mind, shi kuma James a fusace ya haura sama yabi bayan Romeo da Michael...✍️ Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 B 💞Star Lady💞 *ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TAALA WA BARKATUHU JAMA'A INA MUKU FATAN ALKHARI DA FATAN CIN MA BURI NA ALKHARI, MASU MIN MAGANA A KAN CEWA BAI KAMATA ROMEO YA RINƘA YIWA IYAYEN SA TSAWA HAKAN NAN BA, BAI KAMATA YA RINƘA YIWA MUM ƊIN SA HAKAN NAN BA, INA SON KU SANI FAƊAKARWA NAKE BA KARA ƁATA TARBIYA BA, IDAN KUKA YI HAKURI A HANKALI ZAKU JI MENENE YASA YAKE MUSU HAKAN, KOMAI NADA DALILIN SA A RAYUWAR NAN, SO PLEASE KU KYALENI HAKA NAN, BUGU DA KARI KUMA KARKU MANTA FA SHI ROMEO BATURE NE, KUN SAN TURAWA YADDA SUKE WANI LOKACIN MA ƳAƳA SUKE KOMAWA MASU MULKI A GIDA, IYAYE SU KOMA KARKASHIN SU, SAN NAN KUMA KARKU MANTA SHIFA ROMEO KIRISTAR NE BA MUSULMI BANE, MU MUSULMAI MUNE MUKA SAN DARAJA IYAYE DA GIRMAMA SU, AMMA YAWANCIN KIRISTOCI BASU SAN WANNAN BA FATAN KUN FAHIMTER, KU CI-GABA DA BIBIYA A HANKALI KOMAI ZAI WARWARE MUKU, NAGODE* 💞TRIPLET'S💞 https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo *THE BEGINNING* 💞STAR LADY💞 WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 23 A tare su dad suka koma suka zauna, dad ya tsorata sosai, duk da cewa baya son mum, amma bai son a kashe ta, ya fi son dai tayi nisa dasu ne ta bar su su samu peace of mind, shi kuma James a fusace ya haura sama yabi bayan Romeo da Michael. Zaune bakin lallausan katafaren gadon Romeo ya isko Michael, sai faman turɓune fuska yake, while shi kuma Romeo yana tsaye gaban mirror, karasawa cikin bedroom ɗin James yayi, tare da zama kusa da Michael ɗin yana faɗin "Sorry My tiger, how are you feeling now?" Yayi maganar cike da kauna da kuma tausayin ɗan uwan nasa, kasan cewar shi Micheal a baya an taɓa masa aiki a ƙwaƙwalwar sa saboda wata matsala da ta taɓa faruwa da shi a baya, shi yasa sometimes idan ya birkice ba mai iya shi sai Romeo, kuma wannan dalili yasa gaba ɗaya gidan sukafi son shi saboda tausaya masa da suke, ko shi James ya bugi Michael ɗin ne cikin fitar hayyaci, baya hayyacin sa lokacin, badan haka ba da ba zai bugesa ɗin ba, karisa hayewa saman gadon Michael yayi ya gyara kwanciyar sa yana faɗin "Please James i need hot coffee" yayi maganar a shagwaɓe, dukan wasa James ya kai masa a kirji yana faɗin "You make me thinking" lumshe ido Michael yayi ya buɗe tare da kara shagwaɓe murya yace "Thinking for what?" Hararar wasa James ya masa kafin ya miƙe yace "I'm coming let me bring the coffee for you first" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga room ɗin, duk abun da suke Romeo na jin su amma kamar bashi a ɗakin, yana tsaye gaban mirror yana faman latsa waya da alama sako yake turawa mai muhimmanci, Jim kaɗan James ya dawo hannun sa riƙe da kyakkyawar cup mai ɗauke da hot coffe sai tiriri yake, yana fitar da hayaki, gefen gadon ya zauna yana faɗin "stand up please" kara turɓune fuska irin na shagwaɓa Michael yayi kafin yace "I don't need a coffee again" zaro ido waje James yayi lallai Michael ya raina masa wayyo yaje ya kawo coffee ɗin ne dan iskanci kuma zai ce bai so, shi kuwa Michael lumshe brown eyes ɗin sa yayi abun sa kamar mai barci, hannu James ya kai kamar zai kai masa duka, sai kuma ya tuna da ya bugesa ɗazun kuma yasan wannan bugun da ya masa ma Romeo ba zai kyale sa ba, sai ya tuhumesa a kan me yasa zai bugi Michael, amma sai in Michael ɗin baya nan, dan Romeo baya yiwa ɗaya daga cikin su faɗa a gaban kowa, duk wanda yayi laifi a cikin *TRIPLET'S* ajiye sa yake shi kaɗai ya masa faɗa, tuna hakan yasa James ya miƙe ya fice da coffee ɗin a hannun sa ya mai da in da ya ɗauko. Shi kuwa Michael daga lumshe ido yayiwa James barcin wasa sai abun ya zama da gaske barci ya ɗauke sa, ko da Jame ya dawo room ɗin Michael ya riga da yayi barci, kwanciya yayi shima a gefen Michael ɗin yana jiran yaji Romeo yace me yasa zai bugi Michael, shima daga kwanciya ba jimawa barci tayi awon gaba da shi, basu san time da Romeo ya fice daga bedroom ɗin ba sun yi barci, Michael yana barcin ma sai sauke ajiyar zuciya yake cikin barci saboda zafin zuciya irin nasa. NIGERIA KADUNA Kai tsaye gidan sa mutumin nan ya wuce da Jelly, irin gidan nan ne na matasa yan ci rani masu cike da ɗakuna, kamar matar sa haka yaje ya sanya key ya buɗe bedroom nasa yana faɗin "Shiga mana" make masa kafaɗa tayi a shagwaɓe tace "No daddy na ya hana ni shiga room ɗin kowa, kawai ka ɗauko min bag ɗin ka bani in tafi gidan su yaya Imran" da dai yaga taki shiga ɗakin ta lalama sai ya zare mata ido yace "Ki shiga ko na yanka ki da wuƙa" dariya Jelly tayi kafin tace "Ni rago ne da zaka yanka ni?" Ƙasa yayi da murya baya son yi mata da karfin sauran matasan da suka rage basu fita ba wato yan zaman banzan nan su jisa shi yasa ma bai shigar da ita ta karfin tsiya ba yake bin ta a hankali ya sami ta shiga, tana shiga shikenan sai ya ɗaure ta ya toshe mata baki yayi raping ɗin ta niyar sa kenan, amma ina Jelly taki shiga ta kafe a kan lallai daddyn ta ya hana ta kuma bazata ki bin maganar daddyn taba Ganin da gaske taki shiga ne yasa ya kara kasa da murya yace "Muje ciki kici abinci" turo baki tayi kafin tace "A'a ka kawo min abincin waje" "Ke ni sa'an kine? Zaki shiga ne ko dai sai na ɗaga ki na shigar da ke" kallon sama da kasa ta masa kafin tace "Tun da ka dage na shiga room nan nasan ba alkhari bane a ciki dan daddy na duk ya koya min irin wannan haka Aunty Zuwaira mai aikin mu ma ta koya min karna yarda da maza, kuma ni ba jahila bace babu in da zanje, I'm 14 years now duk irin wannan abun na sansu ɗan iska kawai katon banza kazami" ta kare maganar tana murguɗa masa baki, duk shagwaɓa irin na Jelly tana da wayyo da kuma ilimi sosai duk abun da take tana sane gata bata barin ko ta kwana ba'a mata ta kyale, kana mata abu tun da zafin sa zata rama. Damko yar hijabin school nasu dake jikin ta yayi yana kokarin turata ɗakin, ihu ta fasa tare da cire masa hijabin ta kwasa a guje tayi waje ta barsa rike da hijabin a hannu. gudu take sosai dan a tunamin ta ya biyo bayan ta, bata san lokacin da ta hau saman titi ba saboda tsoro, bata ankaraba wata dankareriyar mota kirar *falcon Supernova* ya kwashe ta, nan take ta baje kasa bata suraba, kan ta ya fashe sai jini ya fara malala kamar kogi, bata numfashi kamar ta mutu, a sukwane ma tukun motar ya taka birki tare da fitowa da sauri, ya buɗe gidan baya na motar, wata babbar mace ce ta fito daga cikin motar, irin hamshaƙan Hajiyoyin nan ne wadda nera ta zauna musu sosai, sanye take da dankareriyar swiss lace pink color mai bala'i kyau da tsada, ɗinki riga da zani kasan cewar ba yarin ya bace ta manyan ta sosai, wuyan ta da hannun ta ta musu kwalliya da gold masu tsada, yayin da idon ta ke manne da farin glass (medicated glass) Cikin sauri Hajiyar nan ta kariso wajen da Jelly ke kwance cikin jini, kan kace me jama'a sun taru a wajen, kowa sai salati yake, cikin sauri Hajiyar tace "Dan Allah ku taimaka ku samin ita a mota mu wuce asibiti da ita" tayi maganar a ruɗe, da sauri jama'ar wajen suka taimaka a ka sanya Jelly a mota, Hajiya ta koma cikin motar, da gudu driver ma ya koma cikin motar, ya kunna motar ya figeta da wata mahaukaciyar gudu suka nufi hospital. 💞Aafia💞 Zaune suke saman gadon su bayan sun dawo daga school, sai faman latsa wayoyin su suke, yayin da ita Aafia a zuciyar ta take shirya yadda zata ɓullo wa yar aikin da Abbi ya kawo da wuri ta koreta a gidan, Aunty ta fara aiki dan ita ya dace da tayi aiki a cewar su, suyita ɓata mata aikin har Abbi ya gaji ya koreta ya sake ta, sai ayyana hakan Aafia take a ranta tana latsar wayar ta da sallama mai aikin ta shigo bedroom ɗin nasu hannun ta rike da plate mai shake da fruits, duk cikin su ba wanda ta amsa mata sallamar, Baiwar Allah bata damu ba ta wuce ta ɗaura musu plate ɗin saman table ɗin dake bedroom ɗin san nan ta dawo gaban gadon ta duƙa cikin sanyin murya tace "Aunty ina wuni" kamar ba dasu take ba sun yi banza da ita kamar basu san da zaman ta a wajen ba, shiru ta ɗan yi, a tunanin ta basu ji ba ne sai ta sake cewa "Aunty ina wuni" tsawa Umaisha ta daka mata "ke mahaukaciyar ina ce? Ki fice mana daga bedroom dan Allah, bamu buƙatar gaisuwar!!!" baiwar Allah jikin ta har kerma yake ta mike ta fice daga bedroom ɗin cikin sauri. Dogon tsaki Aafia taja kafin tace "I hate that girl kuma dole ta bar gidan nan, Halima ita zata ci-gaba da aiki dan ita ce yar aiki da ta dace da yi mana aiki " "same here" Umaisha ta faɗa tana kwaɓe fuska tana turo baki, dai dai lokacin kiran Akil ya shigo wayar ta Dogon tsaki taja kafin ta ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Ina kika yasar da wayar kin tun safe nake kira?" Hararar wayar tayi kamar tana gaban sa, san nan tace "In school ne shiyasa" "A School ba'a picking call ne?" "Kayi hakuri to" shiru ya ɗan yi kafin yace "Umaisha ni sa'an wasan kine? Har zaki ga call na kiki ɗauka" shiru ta masa batayi magana ba sai faman hararar wayar take kamar yana gaban ta "Okey ba zaki yi magana ba kenan?" Turo baki tayi a kule tace "Kayi hakuri" "Good ya miki kyau next month ina dawowa ki shirya ina zuwa zanzo na ɗauke ki na kawo sadaki" kamar zata yi wata magana kuma sai ta fasa tace "Ok sai kazo ɗin" yasha ruwan mamakin amsar da ta bashi, ita da a baya kullun ita ke tambayar sa yau she zai dawo, idan yace mata ba rana har kuka take masa amma yau yace mata ga ranar da zai dawo ko ajikin ta sai dai tace masa wani ok kawai, tun daga nan ya fahimci a koi matsala amma bai bari hakan yayi affecting na tunanin saba kasan cewar yana da Exam a gaban sa, sai ya tattara komai ya ajiye a kan sai ya dawo kawai ya ɗauki mataki da ya dace, da haka sukayi sallama yana cike da mamakin ta, yayin da ita kuma take ta faman jan tsaki tana faɗin "ɗan damuwa kawai ni zaka cewa zakazo ka ɗauka, hmmm yaro mankaza kazo ka ɗauke ni ɗin mu gani tun da uban ka ya haifa maka ni" sai suruntan ta take yayin da ita kuma Aafia ta sanya Bluetooth a kunnen ta tana jin waka, hankalin ta baya kan Umaisha ɗin ma kwata kwata, bata jin me Umaisha ke faɗe ba. 💞KANO💞 A ɓangaren daddyn Jelly kuwa duk ya rame ya fita hayyacin sa ya sauya kamar ba shi ba, gashi ba wani information da ya samu a kan Jelly, da kyar ya iya samu ya ci abinci, shima yaci ne saboda yinwa dake kokarin yi masa illa, kullun tun safe idan ya fita baya dawowa sai 1 na dare, ya daina zuwa office ban da yawon neman Jelly cikin garin Kano ba abun da yake, sai neman layin sa Imran keyi amma a kashe kasan cewar wayar tasa ta fashe bai kuma kai ta gyara ba, haka zalika baban Muneer sai neman layin sa yake a kan batun auren Jelly da Muneer dan Muneer na takura masa a kan batun auren, amma ina layin daddy baya tafiya, yazo gida yafi a kirga amma baya samun daddy kasan cewar daddy na can wajen yawon neman Jelly, duk in da baban Muneer yasan zai samu daddy yaje amma shiru ba labari, haka ya hakura ya fara bincike ko dai daddy ya gudune yabar Kano, daddy kuwa yana can cikin wahalar gararin neman Jelly, tun kayan da ya sanya ranar da Jelly ta ɓace bai samu damar wanka ba bare ya canza wasu, dan kwata kwata baya tuna komai sai Jellyn sa. 💞KATSINA💞 ga idon nashi jawur kamar jini manya manyan, kai da gani kasan wan nan yana shaye shaye over, ganin shi ba karamin tsorata mum tayi ba nan take numfashi ta ya ɗauke ta zuɓe kasa sumammiya, su kuwa ko a jikin su, suka danno hasken torchlight na su mai kashe karfin ganin idon ɗan Adam saboda haske, kai tsaye saman gadon suka haska da mamaki sai basu gane Jehan ba kasan cewar tasa fake face, tsawa Nasir ya dakawa gwaggo tare da sanya kafar sa yana taka ta "Ke tashi ki faɗa mana ina Jehan Nawazudden" a firgice gwaggo ta miƙe zaune tana zaro ido ganin kartin maza a ɗakin su ne yasa ta fara salati tana ambato sunan Allah "ke ina Jehan Nawazudden?!!!" Nasir ya sake tambayar gwaggo, hannu gwaggo tasa tana mutsuke idon ta dan ta samu damar ganin su wanene da kyau, hakan yayi dai dai da farkawan Jehan daga barci saboda hayaniyar da tajine ya farkar da ita, miƙewa tayi zaune tana goge idon ta, kallo ɗaya Nasir ya mata ya gane ita ce Jehan saboda yanayin jikin ta, sai dai yayi mamankin ganin face ɗin ta ya sauya kamar ba ita ba Ɗaya daga cikin abokan Nasir ɗin ne yace "Ba zaku faɗa mana in da Jehan ɗin take bane sai mun muku yan kan rago" sai lokacin Jehan ta fahimci meke faruwa babu ko tsoro a idon ta tace "Ni ce Jehan sai a kayi yaya, uban me kuka zo nema waje na? Ko kun ban ajiya ne?" Tashin sense da mamaki dukkan su suka zuba mata ido yar karama da ita da irin wannan karfin hali haka, to ko dai akoi abun da ta takane, sai yiwa kansu tambayar da basu da amsan shi suke, shi kan shi Nasir yasha jinin jikin sa ya tsorata, gani yake anya ba wani abun da Jehan ta taka kuwa, su kan su su Fadil dake ɓoye a bayi sun tsorata sosai gani irin karfin hali irin na Jehan ko tsoron wayan nan kartin maza bata jiba Ita kuwa ganin sun mata shiru suna mamaki ne yasa tace "Idan kun tashi faɗa min uban da kukazo yi gidan nan sai ku tashe ni dan barci nake ji" ta kai karshen maganar tana komawa ta kwanta, tashin sense ba'a sa maka date a fusace ɗaya daga cikin su yace "Tafiya dake mukazo yi ma'ana kidnaping naki mukazo yi" kwashewa da dariya gwaggo tayi kafin tace "Amma dai ku mahaukatane ko? Jehan ɗin kukazo kamawa to gata ku ɗauke ta" miƙewa tsaye Jehan tayi tana faɗin "Haba dai dirty Boyz ni zaku yi kidnaping? To muje mana gani nan ai" ta kai karshen maganar tare da dirowa kasa daga saman gadon, sosai Nasir ya kara tsorata, yanzu ya kara tabbatar wa kan sa akoi abun da Jehan ta taka, dan haka kawai ba zata ce su kama ta ba, in kaji makaho yace muyi wasan jifa to dutse ya taka, hakan yasa ya fara ja da baya da baya, yayin da Jehan ke tin karosa tana faɗin "Muje ko" ba shiri suma abokan Nasir ɗin suka fara ja baya baya suna bin Nasir "Gwaggo ɗauko waya kicewa DPO su kariso yanzu" cewar Jehan ɗin jin haka yasa Nasir ya kwasa a kuje yayi waje, wandon sa na faɗuwa ya haye saman katanga kamar biri ya dira waje, yayin da suma abokan nasa suka rufa masa baya Fadil na ganin su Nasir sun yi waje shima ya fito a guje dan kar DPO yazo ya kama shi, a ɗari suma suka haye katanga suka dira waje. Suna fita Jehan ta kwaso a guje ta haye saman gadon ta rungume gwaggo tana faɗin "wayyo na shiga uku ni Jehan" ita kan ta gwaggo kirjin ta sai dukan uku uku yake, yau taga abun da yafi karfin ta, ashe duk wannan cika baki da suke kirjin su sai dukan uku uku yake a tsorace suke, kawai karfin haline ,irin na Jehan da gwaggo kamar wasu wayan da suka taki wata tsiya ashe duk bogene tsoro cike fal ransu Kuka Jehan tasa tana faɗin "gwaggo dan Allah mu bar gidan nan kar su sake dawowa wlh tsoro nake ji" rungume ta gwaggo tayi tana faɗin "Ni kai na saura kaɗan nayi fitsari a wando saboda tsoro kawai karfin haline innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun gode maka da ka kuɓutar damu daga wannan masifa" jin gwaggo tayi zancen fitsari yasa Jehan ta taɓa jikin ta da sauri dan lokaci da su Nasir ke magana ita ma ji tayi kamar zatayi fitsari a wando saboda tsoro, ashe ta yi fitsarin ma bata sani ba ga kayan barcin ta a jike, kara rungume gwaggo tayi jikin ta sai kerma yake tana haɗa zufan wahala, while ita ma gwaggo sai zufan take haɗawa gashi tana jin fitsari amma tsoron fita take, an kasa samun wanda zai iya miƙewa cikin su ya rufe musu kofar ɗakin saboda tsoro, ga mum kuma kwance a bakin kofa a sume basu sani ba. Haka a zaune rungume da juna suka kwana, sun kasa rintsawa saboda tsoro gani suke kamar su Nasir zasu dawo, yau sunga bone, ko sallar asuba sun kasa tashi suyi a lokacin da ake kiran Sallah, dan suna ganin kamar su Nasir na waje, har sai da gari yayi haske sannan Jehan ta iya samun dama ta saki gwaggo jikin su sai kerma yake suka fito waje, ba karamin tsorata sukayi ba ganin mum kwance a kasa, ga hannun ta nan da zanen shatin kafar mutun, da alama a garin gudune ɗaya daga cikin abokan Nasir ko shi da kan sa Nasir ɗin suka takata a hannu ta. Jiki na kerma gwaggo ta ɗebo ruwa ta yayyafa mata, dogon numfashi taja tare da tashi a birkice tana faɗin "Ina Jehan dan Allah karku mata wani abun, duk abun da zaku mata ni ku min, dan Allah marainiyar Allah ce" turus gwaggo ta tsaya murya na rawa tace "Me kika ce Maryam? Marainiya kuma Jehan ɗin ce marainiya?" Sai lokacin mum ta dawo cikin hayyacin ta jin muryan gwaggo, a hankali ta gyaɗawa gwaggo kai kafin tace "Eh marainiya" a ruɗe gwaggo tace "ban gane marainiya ba kimin bayani" dogon numfashi mum taja tare da saukewa a hankali, cike da tashin hankali ta fara magana "Eh Aunty A'isha, tun ranar da yan sanda suka ɗauki daddyn Jehan, bai jima da tafiya ba yamin massage a kan cewa ba yan sandan gaske bane suka ɗauke sa haɗin bakine, abokan hamayya ne suka shirya masa hakan, kuma kashe shi zasuyi dan haka mu gudu, mu tseratar da rayuwar mu dan a halin yanzu ma, sun ɗauki hanyar Niger da shi kuma tabbas kashe shi zasu yi dan hakan suka shirya addu'ar mu kawai yake buƙata san nan kamar yadda ya faɗa min mu gudu dan muma ba zasu barmu ba saboda ba iya takarar sa suke so ba har da dukiyar sa, shi yasa da Shitu yazo yace mu tafi ban musa ba naje na ɗauko mana kayan mu dan mu gudu, tun da already daddyn Jehan ya sanar da ni, shi yasa ban takura Shitu a kan ya faɗa min ina daddyn Jehan yake ba, dan banson jin yadda suka kashe shi" murya na sarkewa sai haɗe words gwaggo keyi tace "To waya ce miki sun kashe shi? Da zaki fara kiran Jehan marainiya" "Sun kashe shi Aunty A'isha, sun kashe shi, dan in kika lura da yanayin da Shitu ya shigo gida a ranar, duka da gindin bindiga ce fa a goshin sa, shi da yabi daddyn Jehan daga baya ma kenan, kin ga kenan shima Shitu kashe sa suka so yi Allah yasa ya kubce musu yazo ya kubtar da mu, ba dan haka ba da dukkan mu mun mutu" jin mum tace an kashe daddy yasa Jehan fasa ihu ta sulale kasa sumammiya. Mum da gwaggo har suna haɗa hannu waje rungumo Jehan ɗin suna kiran sunan ta a rikice, shiru Jehan bata motsa ba, zaro ido mum tayi ta fara hawaye tana faɗin "Shi yasa naki faɗa muku tun da jimawa Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dan Allah Jehan ki tashi" ita kam gwaggo ta kasa magana abubuwan sun haɗu sun cushe mata waje guda, ta rasa ina zata sanya rayuwar ta taji sanyi a ranta, kan ta sai sara mata yake duniya na juya mata wani irin duhu take gani yana gelmawa ta cikin idon ta wannan wace irinyar masiface, ita kuwa mum kokarin danne abun take dan bata son abubuwan su mata yawa ta samu matsala ko dan saboda Jehan zata yi kokari ta danne da ta kula da ita, sai dai abubuwan sun mata yawa ga rasuwar daddy ya dawo mata sabo ga ɓatan Rimsha yanzu kuma ga Jehan, ta yanke jiki ta faɗin. Duk yadda mum ta kai ga son ta danne abun ta kasa nan take taji zuciyar ta na harbawa da karfi karfi kamar zai fasa kirjin ta ya fito waje, lokacin guda taji kan ta ya mata nauyi, wani irin duhun ta gani ya kilma mata a cikin idon ta, kamar fanka haka taga duniya na juya mata, idon ta ya fara ganin mata daddy na kiran ta, kan tayi wani yunkuri ta zube kasa rungume da Jehan a kirjin ta, ihu gwaggo tasa kamar zararriya haka ta bazama Kitchen ta ɗebo ruwa a kofi tazo ta zuba musu a kan su. Dogon numfashi Jehan taja tare da sauke wa a hankali kafin ta fara kuka, yayin da ita kuma mum ko motsi bata yi ba, kara ɗebo ruwa gwaggo tayi ta zuba mata nan ma shiru ba ta motsa ba, jijjigata gwaggo ta fara yi tana kiran sunan ta, amma ina ko motsi bata yi ba, sosai Jehan ke kuka tana kiran mum yanzu ta bar ta batun daddy ta koma kiran mum dake gaban ta. Sadiq yazo zai shiga gidan su Jehan dan yaje ya ɗebawa su mum ruwa kenan Yusuf ya kwala masa kira ta bayan sa, da sauri ya juya yana kallon Yusuf ɗin "Yaya Sadiq ina zaka je? Kazo muje mu gaishe da Fadil yanzu kanin sa ke faɗa min wai ya samu karaya a kafa jiya da daddare a wajen hanyar sa ta dawowa gida" zaro ido Sadiq yayi yana faɗin "Allah sarki to kaje ina zuwa bari na ɗebawa su mum ruwa" to Yusuf yace tare da wucewa ya nufi hanyar gidan su Fadil, shi kuma Sadiq ya shige cikin gidan su Jehan. Ganin gwaggo da Jehan na ta kuka suna kiran sunan Mum dake kwance a kasa bata ko motsi ne yasa Sadiq karisawa wajen da gudun gaske yana faɗin "Lafiya me ya same ta" tsabar ruɗu da tashin hankali Jehan bata san lokacin da ta riƙo Sadiq ba, cikin fitar hayyaci take faɗin "Dan Allah dirty boy ka taimaki mum ɗina karka bari ta mutu please" kasa motsawa Sadiq yayi saboda irin riƙon da Jehan ta masa gaba ɗaya yaji sa wani iri ta kashe masa jiki, ita kuwa sai jijjiga shi take tana kiran "dirty boy ka taimaki mum ɗina" sai da gwaggo ta janye Jehan ɗin daga jikin Sadiq ta rungume ta sannan Sadiq ya samu dama ya iya juyawa ya fice daga gidan, yaje ya kira ɗan sahu. Har kofar gida mai a daidaita sahu yazo, Sadiq ya kira maman shi tazo ta taya gwaggo suka ɗauki mum suka sata cikin a daidaita sahun, gwaggo da maman Sadiq suka shiga a daidaita sahu suka riƙe mum ɗin, shi kuma Sadiq ya riƙe hannun Jehan dake ta faman kuka yace mata suje bakin hanya su tari wani a daidaita sahun subi bayan su tun da wannan ba fili, ba musu Jehan ta bishi sai kuka take kamar ranta zai fita, Wani a daidaita sahu Sadiq ya tara musu suka shiga gidan baya, sai kuka Jehan keyi suka bi bayan su mum. Ko da suka isa Hospital ɗin an rasa wa zai biya mai a daidaita sahu kuɗin sa sakamakon babu wanda yake da kuɗi a jikin sa, ganin haka mai a daidaita sahu da ya ɗauko su mum yace ya yafe musu, shi kuma wanda ya ɗauko Jehan da Sadiq yace a'a shi da ba zai yafe ba kawai a biya sa hakkin sa san nema ya fito ba taimako ba, a wannan marra da wahalar rayuwa da jama'a ke ciki ko biyar ba zai iya yafewa wani ba saboda shi family man ne, sai zare ido Sadiq yake dan bashi da ko biyar, while su kuma su gwaggo sun shige da mum ciki Jehan ma tabi bayan su, sun bar Sadiq tare da yan sahu, sai faman sosa kai yake yana zare ido, ganin haka yasa ɗan sahun da ya ɗauko su mum ya biya wancan ɗin, sai godiya Sadiq ke masa, yace "Kar ka damu abokina Allah dai ya bawa mara lafiyar ku lafiya, ai talauci bata hana ka taimaki wanda yafika bukata idan kana da hali, talauci ba hauka bane Allah dai yasa mu dace Allah ya mana karshe mai kyau" Amin Sadiq ya amsa dashi, sai zuba godiya yake har ɗan sahun ya tafi. Sai bayan ɗan sahun ya tafine Sadiq ya tuna basu rufe gidan su Jehan ba sun bar ko ina a buɗe, sosai tashin hankali ya bayyana a kan face ɗin sa kar a shiga a musu sata, da yar gudun sa ya shiga cikin hospital ɗin dan yaje yaga halin da mum take ciki sai yazo ya koma ya rufe musu gidan. Zaune a saman benci ya isko su gwaggo sun zaunar da mum suna zazzaune suma, cike da mamaki yace da manan sa "mama ina likitocin kuma? Ya baku shiga ciki ba" kamar maman Sadiq zatayi kuka tace "wai sai mun yanki kati, Jehan taje yanko mana" shiru Sadiq ya ɗan yi kafin yace "To mama bari naje na rufe musu gidan dan mun ruɗe mun tafi munbar gidan ko ina a buɗe" zaro ido waje maman sa tayi tana faɗin "Kayi sauri babana innalillahi kash munyi ganganci Allah dai yasa ba baun da zai faru, Allah ya kau da idon masu dogon hannu kayi sauri kaje ka rufe musu" dai dai lokacin Jehan ta dawo tana faɗin "Wai katin sai da kuɗi" gwaggo ce tace "Ina ATM naki ki basu su cire mana" da sauri Jehan ta wuce face nata sanye da fake face tana faɗin "ATM ɗin yana gida bari naje na ɗauko" da sauri Sadiq yabi bayan ta dan yasan ba sanin hanya tayi ba, yayin da ita kuwa mum take ko mutuwa tayi ne oho ba wanda ya sani, gashi likitoci sunki kulata wai sai an yanki kati sannan su bi layi wajen ganin dr kafin ma a yanke musu hukuncin ko gado za'a basu ne ko magani. A ɓangaren su Jehan kuwa a daidaita sahu Sadiq ya sake tara musu suka shiga suka koma gidan su Jehan ɗin. Kai tsaye ɗakin Jehan ta nufa, ba shiri taja birki tana ganin yadda a ka watsa musu ɗaki an zubar mata da kayan ta dake cikin trolley dukka, har kayan dake cikin bayi ba'a bari ba an watsar, kasan cewar tana sauri ne yasa ta zura hannun ta cikin aljihun trolley ɗin ta dake yashe a tsakar ɗakin, ta ɗauko ATM card nata, haka ta bar ɗakin a watse ta nufi hanyar fita Har ta kai bakin kofa sai ta juyo wai bari ta ɗauki wayar ta, da mamaki sai bata ga wayoyin ba dukka biyu, daga nata har na Rimsha, kasan cewar sauri take yasa bata wani tsaya neman wayoyin ba ta wuce ta nufi bedroom na mum dan ta ɗauko ATM card na mum ta haɗa da nata ko da kuɗin account nata ba zai isa ba, dan ba wani kuɗin kirki ya rage a account ɗin nata ba. Nan taga ikon Allah dan watsa ɗakin mum da a kayi yafi yadda a ka watsa nasu, haka ta tsallake kayan ta wuce ta duba ATM card na mum ta ɗauko ta fice daga ɗakin cikin sauri. Sadiq na tsaye a harabar gidan yana jiran ta bai san meke faruwa ba kuma itama bata sanar da shi ba, tana fitowa suka fice daga gidan tare da rufe ko ina na gidan, suka nufi bakin hanya Suna tafiya ne Sadiq yace mata "da kika sanya face ɗin nan kin canza ba wanda zai ce kece" bata gane me ya faɗa ba sai dai kawai tace masa "Okey" shiru ya mata har sukaje wajen mai POS ta miƙa ATM nata tace ya bata 20k cikin sauri mai POS ya ciro mata kuɗi kasan cewar yaga kamar suna sauri, ansan kuɗin tayi tare da ATM nata suka wuce suka hau a daidaita sahu suka koma asibiti. Kamar yadda suka bar su mum haka suka dawo suka same su, sauri sauri Jehan taje wajen sai da kati ta miƙa 1k nan suka haɗa mata kati Sadiq na tsaye a gefen ta, suka miƙo mata kati da canji, kati kawai ta ansa bata ansa canji ba tace bata buƙata, hannu Sadiq yasa ya ansa mata canjin 800, ya miƙa mata a wulakance tace bata buƙata ta bashi, bai damu ba ya zura kuɗin cikin aljihun sa suka wuce suka koma wajen su mum dan su samu damar ganin likita. A takaice dai sun ga nurse sannan an basu gado a kan mum ta kwanta likita zai zo ya dubata, Jehan ce ta biya kuɗin gadon suka shiga da mum ciki, kwalla Jehan ta fara yi ta zauna kusa da mum ta riƙo hannun ta tana karan to mata duk addu'ar da yazo bakin ta, while su kuma maman Sadiq da gwaggo suna zaune daga ɗan gefen gadon ta kafan mum sunyi tagumi jugum jugum gwaggo na hawaye ta sunkuyar da kan ta kasa, shi kam Sadiq bakin window ɗakin yaje ya tsaya ya dafe kan sa suna jiran dr yazo ya duba mum suji meke damun ta gashi dai ko motsi bata yi kamar ta mutu. To bari mu leƙa Rimsha kafin dr yazo muji meke damun mum 👹DAULAR MUTUWA👹 Zaune a wajen Rimsha ta kwana, ko motsi bata iyayi saboda matsanancin yinwa da kishin ruwa da take ji, yau kwanan ta na huɗu kenan ba abinci ba ruwan sha, duk da cewa kwana biyu daga ciki a sume tayi su, sosai Ayla ta tausayawa Rimsha duk da cewa bata san labarin taba bata san daga ina Rimsha ɗin ta fito ba, amma dai tana ji a jikin ta tabbas Rimsha bata saba da rayuwar wahala ba, ba yar gidan malam Shehu bace, daga ganin fatar jikin ta da yar gidan hamshakin mai arziki tayi kama ko dai yar gidan sarauta ko yar gidan wani shugaba, haka Ayla ta rinƙa ayyana Rimsha yar gidan wanene a ranta, har rana ya ɗaga, kwata kwata Rimsha bata iya magana ko motsa bakin ta bata iya yi. Sai da rana ya ɗago sosai ne sannan magicians ɗin suka zo suka buɗe wa su Rimsha kofar ɗakin nasu suka turo musu abinci, sannan suka fice suka bar kofar a buɗe, da sauri Ayla ta jawo kayan abincin ta ɗauki jug ɗin ruwan da suka kawo masu da sauri ta kafawa Rimsha a bakin ta, da kyar Rimsha take iya haɗiyar ruwan saboda wahala da ta sha Ka ɗan ta sha ruwan ta fara kwarara amai tana tari, da sauri Ayla ta riƙe ta tana ɗan bubbuga mata baya, sosai Rimsha tayi aman ruwan da tasha kafin ta koma ta jingunu da jikin bangon, sakin ta Ayla tayi ta matso kusa da Kausar dake kwance rai a hannun Allah itama saboda yinwa, haka Ayla ta ɗago kan ta ta fara bata ruwan, itama Kausar kamar Rimsha kaɗan ta sha ruwan ta fara amai. Sai bayan sun ɗan huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaɗan kaɗan, a wannan karon basu yi amai ba.. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 B 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 *THE BEGINNING* 💞STAR LADY💞 WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 24 Sai bayan sun ɗan huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaɗan kaɗan, a wannan karon basu yi amai ba, yau dai Ayla bata ci abincin ba ta kyale musu a kan su suci tun da ita taci jiya kasan cewar abincin ba yawa, kallon abincin da kyau Rimsha tayi kafin ta ɗago ta kalli Ayla cikin raunanniyar murya tace "Ayla wannan miyar ai kamar naman mutun ne a ciki" gyaɗa mata kai Ayla tayi kafin tace "Eh naman mutun ne a ciki, nima kullun iya shinkafar kawai nake ci bana sa miyar, sai kuma fruits ɗin nan shima ina cinyewa" shiru Rimsha tayi tana mamakin a ran ta tana faɗin "Wa ina zubillah ya Allah ka kawo mana ɗauki, ya Allah dan karfin mulkin ka, dan karfin izzan ka da girman ka ya Allah ka tarkatsa wannan gida na azzalumai cikin gaggawa, ya Allah ka kawawo bayin ka musulmi ɗauki, Allah kayiwa wa'yannan azzaluman hukunci mai tsanani tun a duniya, ya Allah kai ka ɗai kasan adadin rayukan bayin ka da ya salwanta a nan" zuba mata ido Ayla da Kausar sukayi suna kallon yadda ta zubawa abincin dara daran sleeping eyes tana tana zancen zuci. Ganin ta ki dai na kallon abuncin ne yasa Ayla ta ɗan taɓa ta, ɗago dara daran sleeping eyes nata tayi ta kalli Ayla ɗin "Kuci shinkafar mana, baiwar Allah ni gashi baki faɗa mana sunan ki ba ma" cewar Ayla, lunshe ido Rimsha tayi tare da mayar da kan ta ta jingina da jikin bangon ɗakin tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Cikin sanyin murya tace "Sunana Rimsha kuma ni ba zan iya cin wannan shikafar ba, dana ci namar mutun gara yinwa ta kashe ni" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "A'a ni bance kici namar ba miyar ma gaba ɗaya bance ku ciba iya shikafar kawai nace kuci sai kuci fruits ɗin, shi kuma miyar ku kyale musu abunsu zasu zo su ɗauka anjima, kuci da wuri mu fita waje mu sha iska, muyi hira da sauran yan gidan zuwa yamma za'a rufemu" kanta na jingine da jikin bangon ba tare da ta ɗago ba ta waro dara daran sleeping eyes nata a kan face ɗin Ayla kasa kasa tace "Ni ba zanci shinƙafar bama, dan ko nace zan ci amai kawai zanyi dan haka kawai kuci" tayi maganar cikin harshen turanci, kallon kausar Ayla tayi kafin tace "Matso kici kinji?" ba musu Kausar ta matso ta fara cin gayan shinkafa babu miya Ɗaukan Apple Ayla tayi ta sanyawa Rimsha a hannu tana faɗin "kiyi hakuri kici wannan kinji?" rike apple ɗin Rimsha tayi tana matsar kwalla haka ta kai apple ɗin ɗan bakin ta, ta ɗan ciza tana matsalar kwalla. Haka Rimsha wannan apple ɗin kawai taci yayin da ita kuma Kausar taci shikafa fari ba miya sannan suka haɗa da fruits ɗin ita da Ayla su kaci. Bayan sun gama ne Ayla tace suzo su fita waje, make kafaɗa Rimsha tayi tana faɗin "No i can't go anywhere" "Kiyi hakuri muje mu ɗan kalli hasken waje kinji ko" Ayla tayi maganar a raunane Da kyar Rimsha ta iya dafa bango ta miƙe suka nufi waje sai dafa bango take suka fito tsakar gidan, nan fa Rimsha taga duniya ga yara nan har da manya mafiyawancin su suna zaune ne a bakin kofar ɗakin su, dukkan su suna bushe kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin yinwa da wahala. Saman wata yar benci Ayla ta wuce taje ta zauna ta zubawa yan gidan ido wadda ko wace ke zaune a kofar ɗakin ta, duk yinwa ya cinye su, sun rame sun bushe sun zama kamar kashi da rai, ko maganar kirki basa iyayi, saboda yinwa mafi yawancin su basa cin abincin gidan kasan cewar da naman mutun ake miyar sai dai suci fruits wasu suci da gayar shinkafa wasu kuma suci fruits zalla amma basa taɓa shan miyar, kusa da Ayla Rimsha ta zauna tana bin gidan da kallo tana mamaki a ranta. Can idon ta ya hango mata wani mutun dake zaune ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru, zuba masa ido Rimsha tayi na yan mintoci kafin ta miƙe da kyar ta nufesa a tsorace Ayla tace "Meesha karkije wajen mutumin nan fa zai iya marinki dan bai da mutunci ko kaɗan" a ta kai ce Rimsha tace "Sunana Rimsha ba Meesha ba" da sauri Ayla tace "Irin sunan wata friend na a islamiyar mu ne gare ki kuma ita Meesha muke ce mata shiyasa na kiraki hakan amma kiyi hakuri yanzu dai ki dawo karki je wajen sa" shiru Rimsha tayi kamar bata ji me Ayla ke faɗe ba ta wuce abun ta ta nufi mutumin tana jan kafa da kyar. A gaban sa ta tsugunna cikin sanyin murya tace "sannu" shiru yayi bai mata magana ba kuma bai ɗago ba, sake mai mai ta maganar nata tayi nan ma bai ɗago ba, sai a karo na uku ne ya ɗago a zafafe yana zaro ido ya ɗaga hannu zai mareta kenan, a sukwane ta rimtse idon ta a hankali ta furta Wayyo Allah na, zaro ido sukayi dukkan su lokaci guda jin Rimsha ta iya furta sunan Allah, cikin sauri shi ma mutunmin ya kwatanta ko zai iya kiran sunan Allah amma ina ya kasa, ita ma Rimsha tayi kokarin sake kira amma ina sunan yaki fitowa, haka ta hakura ba dan taso ba Zuba mata ido mutumin yayi kafin yace "Ya sunan ki" cikin nitsuwa tace masa "Rimsha" a hankali ya mai mai ta sunan, ba karamin mamaki su Ayla suka shaba ganin Rimsha na hira da mutumin nan, "Kai fa ya sunan ka?" Ta tambaya tana tsare sa da dara daran sleeping eyes nata, kasa kasa yace "Mustapha" shiru suka ɗan yi na yan mintoci kafin yace "Ya akayi kika zo daular mutuwa gidan da ba'a shiga a fita, duk wanda ya shiga to kai tsaye zai tafi in da ba'a dawowa?" Hawaye Rimsha ta fara yi ta fara bashi labarin yadda a kayi ta tsinci kan ta a daular mutuwa, sosai ya tausaya mata, sai dai abun mamaki shi da ta tambaye sa ya akayi yazo nan, ya kasa faɗa mata dan ya kasa tuna komai, yayi mamaki sosai ma jin ita ta iya tuna yadda a kayi ta shigo gidan, shiru yayi ya zuba mata ido yayin da ita kuma take ta kokarin tuna wani abu mai muhimmanci daga cikin rayuwar ta, amma ina ta kasa tunawa, haka suka yita hira da Mustapha har rana ya ɗago sakiyar duniya, ma'ana azahar tayi kenan, lokacin azahar na cika Rimsha ta fara jin gaban ta na faɗuwa, dan har da Sallah sun mantar da ita sai dai da yake abun na jikin ta da time yayi zata ji jikin ta har kerma yake sai dai ta kasa gane hakan. Bayan sun yi sallama da Mustapha ta koma wajen su Ayla ta zauna saman bencin in da ta tashi, cike da mamaki Ayla ta tambaye ta a kan hirar me sukayi da mutumin nan, nan ta basu labari sama sama, sun sha mamaki sosai dan Mustapha ba ya yiwa kowa magana a gidan kullun yana zaune shiru kamar kurma. Suna zaune a wajen har mamallakin bencin yazo wato mai gadi su mai kula da su a part ɗin nasu, gidan Part by part ne kowani Part su barbushi suna ajiye mutun ɗaya mai kula da yan wannan part ɗin kallo ɗaya Rimsha ta masa taji ta tsani mutumin nan, bata son kallon sa, wani mummuna da shi mai kiran samudawa sai dai da alama cikakken mutun ne ba aljani bane, matsa masa gefe Ayla tayi a kan ya zauna, washe baki yayi yana faɗin "Kiyi zaman ki bari na zauna a kasa dan naga yau da baki kika zo da alama munyi sabbin baki kenan" dariya Ayla tayi ka san cewar sun saba da mutumin tace "Kai dai duna bari yau na haɗu da yan uwana ne" kara washe baki yayi kafin yace "Suma musulmai ne kenan?" Jin ya ambaci sunan musulunci yasa Rimsha ta ɗago a sukwane tana kallon sa yayin da ita kuma Ayla tace "Me kuma musulmai" kallon tsab yayiwa Ayla kafin yace "Kema an juya miki tunani kenan?" Shiru Ayla ta yi dan kwata kwata ta dai na fahimtar abun da yake faɗa, ita kuwa Rimsha da Allah yasa tunanin nata bai gama tafiya dukka ba abun yana mata kamar gizo ne yazo ya koma, wani lokaci har sunan Allah tana iya kira wani lokaci kuma tayi kokarin kira amma sai ta kasa, hakan ku ya samo asali ne saboda addua'o'i da mum ta biya kuɗi a ke ta mata ga saukan Al Qur'ani mai girma da ake ta mata hakan yasa ita kaɗai ta saura a gidan mai iya kiran sunan Allah time to time, kuma time to time tana iya tuna wasu abubuwa masu muhimmanci da ko wani musulmi ya kamata ya kasance yana aikata su wato askar. Jin mai gadin nasu ya ambaci sunan musulunci ne yasa Rimsha ta miƙe ta karisa gaban sa ta tsugunna tana faɗin "Kai kasan musulci ne?" Gyaɗa mata kai yayi kafin ya fara mata bayani "Lokacin da a ka kawo Ayla gidan nan tana yawan faɗa min ita musulmace daga baya suka juya mata tunanin kasan cewar basa son wannan addinin ko kaɗan shiyasa duk mai irin addini in suka kawo shi sai sun mantar da shi komai" cikin sauri Rimsha tace "Amma to kai me yasa baka manta komai ba" zaro mata idon sa kamar na mujiya yayi har sai da ta tsorata ganin idon nasa sun sauya sun koma green color, yar dariya yayi kafin yace "Kin ji tsoro ne?" Gyaɗa masa kai tayi ta kasa magana "To karkiji tsoro, kawai na ɗan nuna miki dalilin da yasa ni basu juyamin tunani na bane" "Ban gane ba" ta faɗa a tsorace, kara kwashe baki yayi kafin yace "To ina nufin da ni da su duk ɗaya ne, nima magicians ne sai dai ni ban cika cin namar mutane sosai ba, kaɗan kaɗan nake ci time to time kuma ban na shan jini sosai sai in naji kewa" mamaki ne ya kamata ta kasa magana ta yi jugum ta zauna shiru tana tunanin to me yasa shi yake dariya har da wasa da Ayla su barbushi kuma basa yin hakan. Kyasta mata munanan yatsu hannun sa yayi a kan face ɗin ta kafin yace "Kin tsoratane?" Gyaɗa masa kai tayi "To karkiji tsoro ke ba zan cinye ki ba, because you look so beautiful, your face look like moon, ba zai yi kyau ba a ce ancin ye yarinya mai kyau kamar ke" sai lokacin ta tuna tambayar da take son yi masa, cikin sauri tace "Kai musulmi ne?" Zaro mata wannan idon nasa mai kama dana mujiya waje yayi nan take idon nasa suka sauya color zuwa purple color, kan kace me kamannin sa sun sauya ya fara huci da gurnani mai razana kwakwalwa ɗan adam, ihu ta fasa tana kokarin niƙewa yayi saurin riƙo rigar ta, cikin fishi tace "Karka sake taɓa ni dan ba haka aka koya min a gida ba" janyota yayi yayi wurgi da ita ta faɗi kasa tare da sakin ihun azaba, gaba ɗaya wayan da suke wajen sai da suka miƙe tsaye har da Mustapha ka san cewar sun san halin mai gadin yana da dariya da mutane, dan duk gidan ma shi kaɗai ke dariya amma kuma yana da fushi sosai, kuma duk yadda kuka saba da shi idan ka masa ba dai dai ba nan take yake kashe mutun, yana da wasa da dariya amma bai da mutunci idan ka taɓo sa, a fusace yace "Yau dole amin fefesunki a gidan nan idan ba haka ba ba zaman lafiya" da sauri Ayla ta zube kasa tana masa kirari tana rokan sa a kan yayi hakuri Rimsha bakuwa ce bata san komai ba, sai wani huci yake yana gurnani kamar wani basamude Ban da kuka ba abun da Rimsha keyi dan wurgi da ita da yayi ta bugu da kasa sosai taji zafi. Sosai gaba ɗaya wayan dake wajen suka duƙa suna rokan duna a kan yayi hakuri ya kyale Rimsha, da kyar ya yarda zai hakura amma sai Rimsha ta taso da kan ta, ta dafa kafafun sa ta bashi hakuri, cikin sauri Ayla taje ta taimakawa Rimsha ta miƙe suka dawo gaban shi suka duƙa, cikin kuka Rimsha ta bashi hakuri, lokaci guda taji tsanar mutumin ya kara ninkuwa a ranta, mummunar katon kafar sa yasa ya hanɓare ta sai da tayi baya ta faɗin ta buga kan ta a kasa, sannan yayi wucewar sa yabi ta wata kofa ya bar wajen, sai kuka Rimsha take da kyar Ayla da Kausar suka ɗaga ta, ganin duna ya tafi yasa Mustapha ya kariso wajen su dan ya ja wa Rimsha kunne a kan tabi a hankali karta kuskura ta sake bari tayi wani gangancin, sosai Rimsha ta ji shawarar Mustapha dan ta ji wahala wurgi da ita da duna yayi, kuma tayi danasanin shiga sabgar sa da tayi, da haka Rimsha tace ita ɗaki zata koma ba zata sake fitowa waje ba har ta mutu, Ayla da Kausar ne suka taimaka mata zuwa ɗakin su suna mata sannu. Cikin dattin ɗakin nasu suka koma suka zauna suka buga uban tagumi sukayi jugum jugum kai daga ganin su kasan suna cikin tashin hankali da ba zai misaltu ba. 💞RUFEE💞 cikin kungurmin daji ne mai yelwan bishiyoyi da ciyayi dogaye, waje ne mai bantsoro, haka Rufee ta keta wayan nan grasses ɗin ta wuce ta nufi bayan wata katuwar dutse mai ɗauke da yar karamar kogo a wajen, kan saman dutsen taje ta hau, da kyar ta iya hawa, ta zauna zaman dirshan saman dutsen tana haki kamar wadda tayi gudu. Tana zama ba jimawa wani tsohon mutumi ya ɓullo a saman wata yar dutse dake wajen, tsohone sosai yana da dogon jenu fari kal, sai dai da alama gemun sawa yayi ba nasa bane, mummuna da shi bashi da kayan gani yana da ido jajawur kamar jini gasu manya manyan kamar ball abun tsoro, ga hancin nan nasa a ɗage kamar irin nasu Barbushi abuɗe kamar kofa, mutumin nan abun tsoro ne, face na sa ba kyan gani ko kaɗan babu ko tsoro a idon Rufee ta fara masa bayani a kan abun da ya kawo ta "Baba daman na zone ne yau ma a kan wacan Aafia" da muryan mara daɗin ji kamar an tada injin niƙa baban yace "Me kuma ya faru? Bata baki kuɗin ne?" Girgiza kai Rufee tayi tana faɗin "A'a tana bani kuɗi ina so ne yanzu a juyamin tunanin ta tadawo sai abun da nace mata shi zatayi dan gaskiya tana kawo min cikas a lamurana, akoi wani Alhajin da yace zai bani 10 millon idan har na kawo masa ita amma ba yadda ban yi da ita ba taki yarda ta masa magana ma bare kuma har ta bishi ta biya masa bukatar sa, ni kuma na samu abun da nake so" shekewa da dariya baba yayi kafin yace "Karki damu kin san aiki na ai yanzu dai ki zube kuɗin ni kuma zan dawo miki da Aafia cikin tafin hannun ki" washe baki Rufee tayi kafin tace "Yauwa baba kuɗi kam yanzu ma kuwa zan zube maka su dan jiya 100k Aafia ta bani" washe baki shima baban yayi, buɗe jaka Rufee tayi ta ciro masa kuɗi ta ajiye masa a gaban sa, tana ajiye kuɗin baban ya ɓace da shi da kuɗin, dariya tayi ta miƙe ta sauƙo kasa daga saman dutsen ta nufi hanyar da tabi tazo sai dariya take tana jin daɗi tana faɗin "Aafia kenan idan kin san wata ai baki san wata ba haka kawai zaki hana manya masu kuɗi su bani kuɗi ga dama na samu amma kina neman hana ni, shegiya gaki da farinjini kamar me, ko wani Alhaji sai yace sai ke yake so, ke kuma kina wulakan tasu to Wlh baki isa ba sai na mai daki tantiriyar yar duniya ki bi maza a guje sannan ki bi kayan maye a guje, kafin na shigo gidan uban ki a matsayin mata kin riga da kin bi duniya kin lalace" kamar wata zararriya haka ta kutsa cikin grasses nan ta wuce sai surutu take ita kaɗai. *KADUNA* Kwance saman gadon majinyata Jelly take jikin ta na sanye da kayan majinyata, an mata ɗin ki a kan ta duk in da taji ciwo an ɗinke mata an sanya mata bandeji, a takaice dai ta samu kulawa sosai sai dai bata motsi, har yanzu tana sume, ita kuma Hajiyar da ta bugeta tana zaune a gefen ta ta buga uban tagumi da alama ta shiga damuwa sosai da sosai, dan sai haɗa zufa ma take duk da Ac dake ɗakin hospital ɗin. *KATSINA* Tun jiya sai yau su Jehan suka samu likita ya zo ya duba mum, nan ya gaya musu tashin hankali da yafi karfin tunanin gwaggo, dan da farko ma likitan yaki yarda ya faɗa musu yace su turo masa namiji, sai da gwaggo ta kafe tace basu da kowa dan haka ya faɗa musu kawai, shine ya kira gwaggo office na sa nan yake faɗa mata abun da kan ta ya kasa ɗauka, mum na ɗauke da wani babban ciwo a zuciyar ta wadda dole a mata aiki cikin gaggawa idan ba haka ba zata iya mutuwa, duk ba shine damuwar ba, babban damuwar a nan shi ne dole waje za'a fitar da ita dan wannan asibitin basu da kayan aikin da zasu mata aikin, wannan kwararrun doctors ake buƙata, har wani duhu duhu gwaggo take gani a idon ta, ita damuwar ta ɗaya shine samun lafiyar mum kuɗin ba damuwa bane dan mum tana da manya manyan gwala-gwalai da idan a ka haɗa a ka sayar a kalla zasu kai 10 millon so kuɗi bai dame taɓa, lafiyar mum shi ne a gaban ta. Da sauri ta fito daga office ɗin dr Jehan na tambayar ta amma ina bata bi ta kam kowa ba ta nufi hanyar fita hospital ɗin dan taje gida, har ta kai bakin gate ɗin hospital ɗin sai kuma ta juyo tayiwa Sadiq da yazo tun safe dan duba jikin mum, alama da hannu gwaggo ta masa a kan yazo su tafi dan bata san hanya ba, a tare Sadiq da Jehan suka miƙe sukabi gwaggo, idon Jehan ya kunbura sosai saboda kukan da ta sha duk ta sauya kamar ba ita ba. Tare suka wuce gida da mai a daidaita sahu, suna shigowa gida kai tsaye ɗakin mum gwaggo ta nufa dan ta ɗauko gwala-gwalan mum suje su sayar su san yadda zasu yi su fitar da mum kasar waje a mata aiki da wuri. Gwaggo na shiga ɗakin mum taga ikon Allah nan taga ba komai duk wani abu mai amfani an kwashe har da wayan mum, ba abun da aka barmusu sai kayan sawan su, kamar mahaukaciya haka gwaggo ta fito waje tana ihu, da sauri Jehan da ta tsaya ta jingunu da bango ta taho ta tare gwaggo tana faɗin "Gwaggo me ya faru menene?" shima dai Sadiq abun da yake tambaya kenan, me ya faru kamar karamar yarinya haka gwaggo ke kuka tana faɗin "Shikenan nan komai ya kare sun kwashe komai sun kashe mu Jehan babu komai innalillahi wa inna ilaihir shikenan yanzu muna ji muna gani zamu rasa Maryam bayan mum rasa Nawazudden ga Rimsha babu ita ya Allah ka ɗauki rayuwa ta kafin ka ɗauki na Maryam" tashin hankali kalma ɗaya Jehan ta kasa furtawa dan ta rasa ta ina zata fara kuka kawai take, shi ma Sadiq kuka yake musu sosai yana addu'ar Allah ya kawo musu mafita. Da kyar ya iya saita kukan sa yace "Gwaggo meke faruwa ne? Me mum take bukata yasa kuke neman kuɗi?" Cikin kuka Gwaggo tace "Ya zama dole na faɗa muku dan ina ji a jikina zan riga Maryam mutuwa, to ko na mutu kuyi kokarin wajen ganin kun taimaki Maryam idan kuma Allah yasa itama kwanan ta ya kare to Sadiq ga amanar Jehan ka riƙe ta kamar kanwar ka" nan gwaggo ta basu labarin abun da ke damun mum san nan da kuɗin da suke bukata almost 5 million dan su fita kasar waje ai wa mum aiki, ta kai karshen maganar da kyar saboda kuka da ya ci karfin ta, sosai Sadiq ke hawaye yayin da ita kuwa Jehan hawayen idon ta suka tsaya cak idon ta ya bushe gaba ɗaya taji bata bukatar ci-gaba da kuka kuma dan komai ya kare mata me zata yiwa kuka kuma, komawa tayi duk tsabta irin nata haka yau tayi zaman yan bori a kasa ta jingina kan ta da bayan gwaggo ta ɗaga kai sama kamar mai tunani, while ita kuwa gwaggo sai hawaye take haka shi ma Sadiq. 💞WASHINGTON DC💞 Yana yin garin gwanin ban sha'awa a hankali iska ke kaɗawa mai nishaɗan tar da zukatan masoya, sanyi Ac ne ya ratsa shi kasan cewar Romeo ya kara gudun Ac dan su tashi daga barcin, ya san cewa dukkan su basa son sanyi idan sanyi yayi musu yawa basa iya barci shi yasa ya kara gudun Ac. A hankali Michael ya waro brown eyes nashi masu ɗauke da barci, kai tsaye kan kyakkyawar face ɗin Romeo suka sauka, yana zaune a saman bedside drawer jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya cirota daga letar ta saboda tsabtar ta, bai ɗaure kyakkyawan dark black curly hair sa ba ya bar shi ya kwanta masa har baya while wannan guntu na gaban yana nan a gaban goshin sa, soft skin na sa nan sai kyalli take a kwance luf taji hutu, sai wani fitinanniyar kamshin dake tashi a jikin sa, lallausan red lips na san nan idan ka gani kace ya sanya lips balm saboda kyalli da yake kuma yayi red sosai, kyawawan hannun sa na sanye cikin hand gloves masu kyau yana riƙe da allura yana kokarin haɗawa. Zubawa Michael wayan nan dara daran blue eyes ɗin nasa yayi yana kallon sa, ganin abun dake hannun sa yasa Michael miƙewa zaune yana kwaɓe fuska yana turo ɗan karamin bakin nan nasa, da ya kalla alluran sa Romeo ke haɗawa, sai yayi sauri ya diro kasa daga saman gadon yana kokarin guduwa, gently Romeo yasa hannu ya riƙo hannun sa, turo baki Michael yayi kafin yace "I want to go and ease my self" lumshe ido Romeo yayi kafin ya buɗe su a kan face ɗin James dake ɗan motsi yana son farkawa "No, do it here" ya furta in a cool voice kara turo baki Michael yayi har ga Allah baya son alluran nan amma duk lokacin da aka ɓata masa rai ko wani abun da badaɗi ya faru sai Romeo ya masa wannan alluran, kamar zai yi kuka ya koma ya zauna yana jin haushi dan dai ba yadda zai yi ne bai isa yace wa Romeo baya so ba, da James ne da ba abun da zai sa shi ya tsaya ya masa. Shi kuwa Romeo ko a jikin sa ya ya ɗaure hannun ya nemi jijiya ya masa alluran san nan ya miƙe ya nufi dressing room na shi ya bar Michael rike da wajen da a ka masa alluran yana turo ɗan karamin bakin sa kamar biro. Dai dai lokacin James ya farka saboda sanyin Ac da ya masa yawa, kallo ɗaya yayiwa Michael ya gane me ya faru dama kuma yasan da kwanan zancen alluran, dan haka sai ya miƙe yana tsokanar Michael ya fice daga bedroom ɗin ya nufi palon kasa. Nan ya isko daddy da Tga suna gardama a kan daddy ya dage sai yaje hospital dan an kirasa a waya yar abokin sa tasha poison tana bukatar taimakon gaggawa, gashi kuma shi daddy Romeo ya hana shi zuwa aiki, yanzu ma ya rikice ne yana tsoron kar yarinyar ta mutu sannan kuma bai san Romeo ya dawo ba, dan fitan Romeo kawai ya gani bai ga dawowan sa ba lokacin yayi barci shi yasa yace zai je wajen aikin. Ganin abun dake faruwa yasa James karisawa wajen da sauri yana faɗin "Uncle what is happening" a fusace Uncle Tga yace "where is lion?" "He's inside his room" James ya bashi amsa yana kallon daddy, wucewa Tga yayi ya haura sama, daddy kuma ya wuce ya nufi waje abun sa dan a tunanin Romeo bai dawo ba, da sauri James ya riƙe sa yana faɗin "Please dad don't..bai kai karshen maganar ba daddy ya dakatar da shi ta hanyar marairaice murya yace "Haba James my friend daughter fa tayi poison na kan ta, please ku bari naje na ceto rayuwar ta" girgiza kai James yayi kafin yace "Daddy you already know that lion baya magana biyu so just kawai ka hakura wasu likitoci su dubata" daddy na kokarin yin magana idon sa ya sauka kan face ɗin Romeo dake tsaye a sama bakin kofar shiga part ɗin sa furkar nan tasa a ɗaure tamau kamar hadari babu alamar wasa a tattare da shi ko kaɗan, tsabar yadda ya ɗaure fuskar har sai da gashin gerar sa suka haɗu daman kaɗan ya hana basu haɗe ba, shiyasa daya ɗaure fuska suka haɗe, nan take jikin daddy ya fara kerma ba shiri ya yasar da jakar hannun sa Gently Romeo ya fara magana da wannan sexy voice ɗin nasa sannan ya tsare daddy da sexy eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali "where are you going?" Cikin sauri Tga dake gefen sa ya buɗe baki ya fara magana, hannu Romeo ya ɗaga masa alamar ba shi ya tambaya ba, daddy ya tambaya, shiru Tga yayi ya kama bakin sa yana kallon daddy, a tsorace daddy ya yiwa Romeo bayani a ta kaice, yar abokin sane tasha poison saboda son da takewa Romeo shi kuma daddyn ta da daddy suna tsoron ma Romeo yaji maganar dan zai iya harbe ta da kan shi, gashi yarinyar bata samun ganin Romeo a zahiri sai dai a Tv dan ko daddyn ta zai zo gidan su Romeo baya taɓa yarda yazo da ita saboda ya san halinsu Michael ma kawai in ya ganta tsab zai iya harbe ta da bindiga, dama dai James tace to shi yana da ɗan saukin kai, hakan yasa daddyn ta kullun yake ce mata zai faɗa wa Romeo idan sun haɗu, amma kuma bala'i tsoron Romeo yake kamar me, ko gaishe da Romeo baya iya yi saboda tsoron sa da yake ji, ita kuma yarinyar ta gaji da jira shi ne tace wa daddyn ta in dai bai faɗa wa Romeo ba zata sha poison, da a ka kwana biyu taga daddyn ta bai faɗa wa Romeo tana son shi ba shi ne tasha poison ɗin a ka kai ta hospital ɗin daddy, to shi daddy Romeo ya hana shi zuwa aiki kwata kwata, saboda ya hana daddyn shan wine, domin daddy idan yaje hospital baya iya yin aiki sai yasha wine wannan dalili yasa Romeo ya hana shi zuwa aiki gaba ɗaya yace ya zauna a gida dama ai ya tsufa, gashi kuma kwararen likitane mumber ɗaya a garin nasu, ana ji dashi sosai, doctor William jacop, sai dai baya iya aiki sai yasha wine yayi tatul ya bugu sosai. Da hannu Romeo ya yiwa daddy nuni da hanyar bedroom na sa ba tare da yayi magana ba kasan cewar bai son yawan magana, jiki ba kwari daddy ya wuce bedroom na sa, zuciyar sa sai dukan uku uku yake yana addu'ar Allah yasa kar yar abokin sa ta mutu, yasani kab asibitin nasa ba wani likitan da zai iya yiwa yarinyar nan aiki cikin ƙan ƙanin lokacin ya cito rayuwar ta sai shi amma sai dai gashi yau yana ji yana gani shan giya ta ja masa ba zai taimaki yar abokin sa ba, ba zai iya tinkarar Romeo yace masa ba zai sha wine ba yayi hakuri ya barshi yaje ya mata aiki ba, yana jin tsoro dan ya san ma Romeo baya magana biyu ko mai zai faru idan yayi magana yayi ne. Wucewa James yayi ya nufi hanyar fita daga palon dan suna da meeting da abokan harkallan sa karfe 6 dai dai, shi yasa zai yi sauri yaje saboda Romeo ya hana su wuce 9pm a waje shi yasa yanzu ya lallaɓa ogannin na sa akan a dai na meeting ko wani harkalla da daddare sai da safe, kasan cewar James shine babban yaron su da sukafi ji dashi yasa suka hakura suka dai na meeting na dare, dan James yana da girma a idon su suna son sa sosai, shine babban yaron su da idan suka bashi aiki cikin kankanin lokaci yake wannan aiki ya gama, har mamaki suke domin ko shugaban kasa suka ce James ya kashe zai iya kashe shi tsab ya samu horo daga wajen su sosai kama daga harbi da bindiga faɗa da hannu da sauran su, sai dai shi James ɗin yana ɓoye ya iya duk wayan nan abubuwan a gida saboda kar Romeo ya fahimci a koi wani abu, hakan yasa yake zama kaman wawa a cikin su ya nuna musu baya son tashin hankali kuma yana da hakuri, dan karsu kawo wani zargi a ransu amma ba abun da bai iya ba kuma shima ba wai saukin kai gare sa ba kawai basajane amma yana da zafi. "Where are going James" Romeo ya tambaya in a cool voice yana tsare James ɗin da sexy eyes ɗin nan nasa masu firgitar da marasa gaskiya su kwantar da hankalin yan mata su razana zukatan jaruman maza, cikin sauri James yace "I just want to go out and chill" wucewa Romeo yayi ya koma bedroom na sa ba tare da ya sake magana ba, shi kuma James ya fice waje da sauri, Tga ya kuma ya sauko kasa ya zauna saman sofa, while shi Micheal daman bai fitoba yana lafe a saman katafaren bed ɗin Romeo, su kuma Jay da John basa nan uncle Herry na barci. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 *THE BEGINNING* 💞STAR LADY💞 WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 25 Kai tsaye *Florida avenue* James ya nufa sai sharara gudu yake da motar sa a saman shinfiɗaɗiyar titin da zata sada shi da*Florida avenue* ya sanya kiɗa na tashi yana tuƙi yana tunanin yadda zai yi da ogan su, dan yanzu sun dawo masa da zancen kashe GAR sabo, kuma sun matsa masa a kan maganar sosai, saboda sun san duk cikin yaran su shi kaɗai ne zai iya yi musu wannan aikin cikin sauri, kan sa ya kulle sosai ya shiga damuwa neman mafita. Bai ankaraba ya buge wani mutumi da yazo tsallaka titin, a sukwane ya ja wata mahaukaciyar birki har sai da kansa ta bugu da jikin glass ɗin motar, wani irin jiri ya gani lokacin guda, da sauri ya fito daga cikin motar, duk da kan sa sai faman sara masa yake haka ya karisa wajen mutumin da ya buge ɗin, kwance yake saman titi, sai dai da alama bai wani bugu sosai ba, bai ji ciwo sosai ba amma da alama ya samu karaya a kafa, da sauri James ya duƙa duk girman mutumin haka ya ɗauke shi cak, ya sanya shi cikin mota, kasan cewar unguwar na masu kuɗi ne hakan yasa ba hayani ya ba mutane kowa na cikin gida, tunani ya fara yi ina ya kamata ya kai mutumin nan. Daga karshe dai ya yanke shawara ya wuce da shi gida duk da ya san zai fiskanci matsala daga Michael da Romeo amma bashi da zaɓi dole ya kai shi gida, haka ya ja motar sa da gudu ya juya motar ya koma gida. Yana yin parking a parking space na gida ya fito ya ɗauki mutumin ya nufi hanyar shiga cikin gida, a guje jinga jingan sojojin dake tsakar gidan suna gadi, suka nufo shi, har suna rige rigen ansan wannan mutumin daga hannun sa dan su taimaka ma shi, ba musu ya miƙa musu dan dama bai son su Romeo su gan shi ya ɗauko mutumin zasuyi mamaki kasam cewar sun san shi da lalaci. Haka suka shiga palon, a sukwame TGA ya miƙe tsaye yana mamaki, wucewa sojan da ya ɗauko mutumin yayi, yaje ya kwantar da mutumin saman sofa 3 seater sannan ya fice daga palon. "James who is this man? What happened to him?" Tga ne ya jerowa James wannan tambayar, a takaice James ya faɗa masa abun da ya faru na buge mutumin da yayi, nan take Tga ya ɗaure fuska sosai, a fusace yace "carry him out from this house!!!" zaro ido James yayi yana kallon ikon god, yana jinjinawa karfin hali irin na Tga, sai kace gidan sa to ko Romeo mai gidan ma ai ba zai ce a fita da mutumin nan lokaci guda ba tun da ni na bugesa da mota, sai ya bari mun masa jinya. James yayi nisa cikin tunanin da zancen zuci da yake, sai ji yayi Tga ya daga masa tsawa "James I'm I not talking to you?" Yar firgigit James yayi kafin yace "I can't uncle" zaro ash eyes ɗin sa Tga yayi kafin ya wuce ya nufi waje, James na tsaye yana mamaki hali irin na yan uwansa su kwata kwata basa son baki a rayuwar su, inma mace ko namiji duk su basa so, basa son kowa ya raɓe su, sun fi son suyi rayuwar su su kaɗai, gaba ɗaya gidan haka suke ba mai son wani yazo cikin su, basa son mutane musamman Romeo yafi kowa tsanar wasu suzo kusa da su, daga shi sai Michael da Tga sun tsani baki. Sai tunanin ta yadda zai kare da Romeo a kan mutumin nan yake, gashi mutumin yana sume baya cikin hayyacin sa, zuba masa idon James yayi yana kallon sa. A fusace Tga ya dawo cikin palon tare da sojoji biyu jibga jibga masu jini a jika, kai tsaye mutumin Tga ya nuna musu yana faɗin "carry this man out from this house" kallon sojojin James yayi suna kokarin ɗaukan mutumin cikin tsawa James yace "Are you mad, get out from here!!!" Cikin fushi Tga yace da sojojin "i said take this dirty man out" kafe su da ido James yayi kafin yace "Okey carry him let me see" shiru sojojin suka tsaya sun rasa maganar wa za su bi, dan duk wanda suka karyawa doka to zasu rasa aikin su, Tga ogan sune a wajen aiki, while shi kuma James sanyin idanniyar ogan kowa a gidan ne wato Romeo, sun gwammaci suki bin umarnin ogan su wato tga a kan su ɓatawa James rai dan gwara musu hukuncin Tga a kan na Romeo, dan haka sai suka juya suka fice daga palon dan sun san halin Romeo a kan yan uwansa sam baya adalci kuma zai iya yin komai a kan Triplets ɗin sa. Ganin sojojin sun juya sun fice ne yasa Tga ya nufo mutumin da kan sa da nufi ya ɗauke sa ya fitar da shi, yana kai hannun sa zai ɗauki mutumin, a fusace James ya damki hannun nasa tare da turesa gefe guda, rai a matukar ɓace Tga yayi kan James da nufin dukan sa, nan fa James yace bai isa ba, kamar wasu zakuna haka suka fara faɗa. Da karfi Tga ya kaiwa James duka a gefen ciki wadda hakan ya masa mugun zafi sosai, lokacin guda James ya sauya idon sa sukayi jawur nan fa ya riƙiɗe ya zama tamkar mayinwa cin zaki wadda yayi shekara biyu babu abinci ya fito farauta, nan yafara farauta Tga, a fusace ya sanya dukkan karfin sa ya ɗaga Tga yayi wurgi da shi gefe saman glass table na tsakiyar sofa milk color, nan take table ɗin ta tarwatse, gadan gadan James ya haye kan Tga ya fara kai masa bugu ta ko ina yana gurnanin ɓacin rai, ran maza ya ɓaci gaba ɗaya jijiyoyin kan sa dana wuyar sa sun miƙe sai dukan Tga yake sosai, da dai yaga duka da hannun ma bata masa ba sai ya ɗamko wuyar rigar Tga ɗin ya miƙar da shi tsaye, yana kokarin kai masa naushi a ciki, Tga ya riƙe hannun sa tare da kwashe kafafun James ɗin ya zube kasa, nan fa Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka shima Kasan cewar James ya samu horon faɗa sosai wajen ogannin sa, hakan yasa ya san dabarun faɗa sosai, cikin dabara ya juyar da Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka. kamar wasu mayinwatan zakuna haka suka rinƙa farautar junan su, sai dai Tga yaci karfin James, dan shi horon soja ya samu daga wajen Romeo, hakan yasa yayiwa James duka duk ya farfashe masa jiki da fuska, da kyar James ke mumfashi, amma Tga idon sa ya rufe duka kawai yake kai masa ta ko ina. Zuciya ta jasa yana neman kashe James ba tare da ya sani ba. Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, yana kokarin juyowa, a fusace Romeo ya murɗe masa hannun da karfi ta baya tare da ɗaga sa sama daga kan James ɗin yayi wurgi da shi gefe, idon Tga ya rufe baya ji baya gani, bai san waye yayi wurgi da shi ba, a fusace ya taso ya nufi Romeo dan idon sa James yake gane masa, Romeo na tsaye, fuskar nan a ɗaure tamau kamar bai san menene dariya ba, dara daran blue eyes na san nan sun sauya zuwa ja saboda dukan James da Tga yayi, har wani tsuma jikin sa keyi, yau da Tga ba kanin daddy bane da ba abun da zai hana ya kashe shi, amma duk da haka dole ya basa hukunci mai tsanani, shi kuwa Tga idon sa ya rufe gadan gadan ya iso wajen Rome yana kokarin kaiwa Romeo duka a ciki, cak Romeo ya riƙe hannun sa tare da kai masa wawan bugu a ciki wadda ta sanya sai da ya fasa ihu mai sauti, bai kai ga gama ihun ba, Romeo ya sake ɗaga sa sama yayi wurgi da shi saman sofa, wadda sai da ya sanya ya fara dawo cikin hayyacin sa, karisawa wajen sa Romeo yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗamko wuyar sa ya miƙar da shi tsaye, ya tsake masa wuyar tasa, nan fa Tga yaji kamshin mutuwa, cikin fitar hayyaci yasa hannu yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar sa amma ina ya kasa koda motsa hannun Romeo ɗin, sai faman zaro ido waje yake, Yana kokarin tantance wa idon sa ke gane masa, shin abun da ya gani da gaske ne, shin Romeo ne ko gizo ne, bai kai ga iya tantance wa ba Romeo yasa kyakkyawar kafar sa ya taka shi da karfi a kirjin sa wadda sai da ya saki ihu mai ranaza kwakwalwa, tamko wuyar sa Romeo ya sake yi ya kai masa duka a ciki wadda sai da tasa shi dawowa cikin hayyacin sa da kyau, dan yasan ba mai karfin yi masa irin wannan damka da dukan duk gidan sai Romeo. Kwashe kafafun sa Romeo yayi nan take Tga ya zube kasa kan gwiwowin sa, rai a ɓace Romeo ya sanya kyakkyawar farin hannu sa ya ɗamko gashin kansa Tga ɗin ya ɗago kan nasa sama suna fiskantar juna, zuba masa dara daran blue eyes nasa nan Romeo yayi yana kallon face nashi kamar mai tunanin wani abu. Sai galabaitaciyar kukan wahala Tga yake, murya na sarkewa da kyar ya iya faɗin "I'm sorry lion" shiru Romeo yayi kamar bai ji saba, yayin da shi kuma James ke kwance kasa yana numfashin da kyar da kyar, ga fuskar sa nan duk Tga ya fashe masa sai jini yake, abun ku da fatar turawa ba quality sosai ba kamar bakar fata ba, fatar su bata jure wuya ko kaɗan. Jin hayaniya yasa su daddy saukowa kasa, ganin abun dake faruwa yasa suka kariso cikin palon da yar gudun su, cike da tashin hankali a fuskokin su, kuka Michael yasa ya duka kasa yana bawa Romeo hakuri, dan yasan halin Romeo sarai duk yadda yake son sunnan idan suka ɓata masa rai ya zuciya to dukan mutuwa yake musu, gashi kuma da alama yaji haushin abun da Tga ɗin yayiwa James sosai, dan da alama ya ɗan ɓata rai ka ɗan, shiyasa ma ya murɗe wa Tga ɗin hannu kuma ya dake sa har sai da ya zube kan gwiwowin sa, kwata kwata Michael baya son yaga suna samun matsala da juna. Su kuwa su daddy sai godiya suke dan yau Romeo bai ɗauki zafi sosai ba, da ya ɗau zafi yadda Tga ya bugi James ai da yanzu wani zance ake. Ganin yadda Romeo ya ɗagawa Tga wuya sama sosai ne, gashi kuma Tga na shan wahala wajen jan numfashi, hakan yasa murya na rawa daddy ya kariso wajen ya ɗan tsaya daga ɗan baya, cike da kaunar ƴaƴan nasa yace "Please my lion leave him" shiru Romeo ya musu yana ta kallon face ɗin Tga kamar mai karantar wani abu daddy zai sake magana, Romeo ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu alamar bai son jin wata magana kuma, shiru daddy yayi ya koma gefe ya tsaya jin kukan Michael ya fara yin yawa ne kuma gashi Michael yana da matsala yasa Romeo ya juyo da dara daran blue eyes nasa kan fiskar Michael ɗin, a hankali ya saki gashin kan Tga ɗin tare da nunawa Michael hanyar bedroom nasa da hannu ba tare da yayi magana ba, dan bai son Michael ya shiga damuwa, kuma yasan halin sa sarai yanzu zai sa kan sa cikin damuwa, matsowa Michael yayi da rarrafe ya kariso gaban Romeo yana faɗin "Please lion for giv....bai kai karshen maganar ba, Romeo ya daka masa wata gigitatchiyar tsawa wadda ya razana duk wata halitta mai rai dake cikin palon "I said get in!!!" Saboda tsorata Michael bai san lokacin da ya tashi da gudu ya haye sama ba ya razana sosai, yasan halin Romeo idan ya ɗau zafi ba wanda ya isa ya tinkaresa shi yasa su daddy duk suka tsaya a baya, shima Michael ɗin dan yafi su sanin halin Romeo ne, ya san bai ɗauki zafi sosai ba shi yasa ya tinkaresa. Goya hannu a saman kirjin Romeo yayi gently ya fara magana "what is happened?" Yayi maganar yana tsare Tga da dara daran blue eyes nasa nan, da kyar Tga ya iya buɗe baki saboda wahalar yadda Romeo ya muɗe masa wuya ya sanya shi kallon sama, ba dan Romeo ne ya masa tambayar nan ba da ba zai iya magana ba, amma tun da Romeo ne ba yadda zai yi dole ya amsa Maganar ko ma tayaya ne, a hankali yace "please help me with water, i need water!!" kallon Romeo daddy da Uncle Herry sukayi suna jiran Romeo ya bada izinin su kawo wa Tga ɗin ruwan, amma sai sukaga Romeo yayi shiru alamar ba za'a kawo ruwan ba kenan, dan shi Romeo shirun sa ma magana ne, wani lokaci da shiru yake magana da Mutane, gaba ɗaya jama'ar gidan sun san ma'anonin shirun Romeo, idan anana magana da shi yayi shiru to akoi abun da yake nufi baya shiru haka kawai, sannan baya magana sai da kwakkwaran dalili, shima kafin yayi maganar sai ya ɗauki lokaci kuma ba wai dan bai ji me kace ba, yana ji, wani lokaci ka masa magana kana sauri sai yafi 5mins bai baka amsa ba, wata zubin ma har sai ka cire rai da zai yi magana sai kuma gaji ya baka amsa a nitse da sassayan murya, idan kuma bai game sa ba da wannan shirun zai baka amsa in ka gane to ruwan ka, idan ma baka gane ba nan ma kai ta shafa shi dai ya gama nasa. Komawa yayi saman sofa ya zauna yayi shiru yana kallon Tga yana jiran amsar tambayar sa, dan shi baya mai mai ta magana idan yayi, idan baka ji bama dole dai ka bashi amsa, already Tga ya san da wannan dan haka sai ya rarrafa ya koma kusa da kafafun Romeo cikin nitsuwa da shakakiyar murya yace "I'm sorry lion it's was a mistake" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me Tga ɗin yace ba, ganin haka yasa Tga ya gane, bayani abun da ya haɗasu faɗa da James kawai Romeo yake buƙatar ji, cike da tsoron, murya na rawa ya fara bawa Romeo labarin abun da yafaru tum daga farko har kashe. Slowly Romeo ya kai kallon sa kan mutumin, sannan ya kalli James dake ta faman juyi a wajen yana numfashi da kyar da kyar, dawo da kallon sa kan Tga yayi yana mamakin, wai ace James ya samu accident dan bai ji ciwo ba ya dawo gida kuma Tga ya masa irin wannan dukan, nan take yaji wani ɓacin rai ya rufe masa zuciya, a fusace ya miƙe rai a ɓace ya fara dukan Tga, daddy na bashi hakuri ya kyale Tga haka ai ya daku amma ina ba wanda ya saurara dan Tga ya bashi haushi, ace James yayi accident Allah ya tsare bai ji ciwo ba ya dawo sannan Tga ya kama sa ya masa irin wannan duka dan yazo da wanda ya buge da mota gida. Sosai Romeo ya bugi Tga har sai da yaji ya ishe sa, yayin da shi kuma Tga ya sume baya ko motsi, yayi lilis a hannun Romeo, dan ma yayi Sa'a Romeo bai ɗau zafi sosai ba Cike da jin haushin Tga Romeo ya wuce ya nufi in da James ke kwance yana mai da namfashi da kyar da kyar, ko kallon in da su daddy suke bai yi ba, ya ɗauki James ya saɓa sa a kafa ɗan sa ya haye saman bene ya koma bedroom na sa. Yana tafiya su daddy sukayo kan Tga, dan bashi taimakon gaggawa kasan cewar daddy likitane. Shi kuwa Romeo saman katafaren gadon sa ya kwatar da James kusa da Michael dake kwance yana kuka. Ko kallon in da Michael ɗin yake Romeo bai yi ba, ya wuce ya ɗauko kayan aiki ya fara duba James. Sai bayan James ya dawo hayyacin sane yace "Please lion ka taimaki mutumin nan da na buge da mota" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, shi kuma Michael wai yayi fushi da shu shi yasa ya kwanta shiru yana hawaye. After 40mins Sai bayan Romeo ya gama duk abun da ya dace yayiwa James ne sannan yace su kira likita ya duba mutumin, amma shi ba zai duba kowa ba, da sauri James ya miƙe, jikin sa ba kwari ya fito ya nufi wajen daddy, dan ya rokesa ya duba mutumin, abun mamaki ko da ya fito palon sai bai ga mutumin ba, yaji tsoron ko dai sunje sun jefar da mutumin ne kamar yadda suka faɗa, da sauri ya nufi hanyar fita daga palon dan yaje ya tambayo security waya fita da mutumin nan Yana kokarin fita muryan dad ta dakatar da shi "James where are you going" a sukwane ya juyo ya kalli daddy cikin sauri yace "Please dad where is the man I brought" murmushi daddy yayi kafin ya sanar da James mutumin yana ɗakin duba marasa lafiyar su, da sauri James ya nufi wajen dan alhakin kula da mutumin na rataye ne a wuyar sa. Yaji daɗi sosai ganin yadda daddy ya bawa mutumin nan kulawa, har da karin ruwa daddy ya masa, sannan mutumin ya farka, kafar sa da ya karye kuma daddy ya sanya kafar cikin wata na ura na aikin su likitocin. Karisawa cikin ɗakin James yayi, ya zauna a gefen mutumin yana faɗin "Sorry" kallon sa mutumin yayi kafin ya ɗan ɗaga masa kai kawai, "What is your name?" James ya tambayi sunan mutumin, a hankali mutumin yace masa "Musharraf" jinjina kai James yayi kafin yace "are you an Arab from saudia?" Gyaɗa masa kai mutumin yayi kafin yace "Yes" shiru James yayi kafin ya sake cewa "Are you a Muslim?" Nan ma eh mutumin yace masa "Okey how is your body now" James ya faɗa yana kokarin mikewa ya nufar hanyar fita "Alhadulillah" Musharraf ya faɗa yana bin James da ido kawai amma shi kaɗai yasan azaban da yake ji. Ficewa James yayi daga room ɗin yana jin daɗi da mutumin bai mutu ba, a palo ya isko daddy, da fara'a ya yiwa daddy godiya, shima daddy ba karamin daɗi yaji ba, dama kuma ya kula da mutumin ne dan James yaji daɗi, yana son yaga yaran sa suna nuna masa soyayya kamar yadda yake son su amma basa hakan sai dai tsawa da faɗa, shi yasa yanzu yake kokarin yin duk abun da suke so dan ya jawo su jikin sa. Wannan kenan ku koma Nigeria muga meke faruwa 💞NIGERIA💞 💞KATSINA💞 kallon Sadiq tayi idon ta a bushe, dan yanzu gaba ɗaya ta dai na jin kuka zuciyar ta ya bushe, cikin sauri tace "Sadiq ka nemomin masu sayan gidan nan" sannan ta dawo da kallon ta kan gwaggo dake ta faman kuka tace "Gwaggo bamu bukatar mu fitar da Mum waje kuɗin aiki kawai zamu nema mu wuce babban asibiti, na san dai kuɗin gidan nan zai isa ai mata aiki, daman kuɗin jirgin fita wajen shi ne mai tsada, dan haka a sayar da gidan nan a mata magani daga baya zamu san abun yi bayan ta samu lafiya" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi cikin ɗaki. Jim kaɗan ta fito sanye da abaya a jikin ta tana faɗin "Gwaggo ki koma hospital ni da Sadiq zamu nemo mai sayan gidan" kasa magana gwaggo tayi dan ta jinjinawa Jehan wannan shine dalilin da yasa a kace ilimi na da amfani yau gashi ilimin Jehan ya taimaka musu, dan kwata kwata bata kawo zancen sai da gida ko kuma karsu fita waje da mum ba sai gashi Jehan ta kawo musu mafita. Jiki ba kwari gwaggo ta miƙe ta wuce hospital wajen mum, su kuma Jehan da Sadiq suka wuce nemam dillalai. Babban tashin hankali shine duk wanda su Jehan suka kira dan ya sayi gidan idan ya fahimci kuɗi suke buƙata ruwa a jallo, sai yayiwa gidan kuɗin wulakanci, a wannan karon ba karamin tashin hankali Jehan ta shiga ba, dan abun da take tunani shine mafitar su shima yana neman ya gagara, ga mum kuma kwance rai a hannun Allah kowani lokaci daga yanzu tana iya mutuwa, dan da gaggawa ake buƙatar a mata aiki saboda ciwon yaci jikin ta sosai, dan likitan yace ciwon ya jima a zuciyar ta tun bata kai haka ba, cikin watan nan ne kuma ciwon ya kara tsanan ta saboda tashin hankali da ta shiga na rasuwar daddy da kuma ɓatan Rimsha. Kamar zararriya haka Jehan ta dawo lokaci guda ta fita hayyacin ta rasa mada fa. Da kyar suka samu wani ya sai gidan 2 million haka suka sallama masa ya zuba musu kuɗin a account ɗin mum, haka Jehan taje ta ciro 1.5m misalin karfe 5 na yamma, duk wannan yawon da suke tare da Sadiq suke, haka suka shiga a daidaita sahu suka kama hanyar asibiti dan taje ta ɗauki mum su wuce babban hospital, tana rungume da jakar kuɗin tana tunanin halin da suke ciki. A kan hanyar su ta zuwa asibitin ne suka samu accident da wata mota, cikin kwata Jehan ta faɗa yayin da shi kuma Sadiq ya faɗi can gefen titi, saboda juyin da a daidaita sahun tayi da su, shi ne ta watsar da su, kan kace me jama'a sun taru sai salati suke yayin da shima mai motar da sukayi accident ɗin da shi ya sume sakamakon buga kan sa da glass ɗin marfin motar da yayi. Allah ya kiyaye Jehan da Sadiq basu ji ciwo sosai ba, a sukwane Jehan ta miƙe bata damu da kwatar dake jikin taba, ita dai kawai burin ta mum ɗin ta tafita daga haɗari ta samu lafiya. Kai tsaye bakin hanya ta koma tana neman wani mai a daidaita sahu dan su wuce asibiti, ta ruɗe ta manta da jakar kuɗin ma, haka Sadiq yazo ya same ta, suka ɗan kara gaba da in da sukayi accident ɗin suka samu wani abun hawan, zasu hau kenan Sadiq yace mata "Jehan ina kuɗin kuma" a sukwane ta juyo, tana faɗin "Yana cikin wannan abun da muka hau ɗin" a guje Sadiq ya juya ya koma, da sauri ta bi bayan sa. Ko da suka zo wajen babu jakar, tsab suka duba cikin mashin ɗin duk da cewa mashin ɗin ma ya faɗi dan sai da sukayi juyi biyu kafin mashin ɗin ya faɗi. Tsab suka duba cikim mashin ɗin babu komai, a razane Sadiq ya ɗago yana tambayar jama'ar dake wajen, kowa yace masa bai gani ba, mutuwar tsaye Jehan tayi ta kasa motsawa, ta rasa me zatayi, daman ta ciro kuɗin ne a nata tunani dan tana zuwa kawai su wuce babban asibiti ta biya kuɗi kawai a yiwa mum aiki ba sai sun kai gobe ba, a yau zaayiwa mum komai shi yasa tayi sauri ta ciro kuɗin dan kar banki su rufe, gashi a daren nan take son ayiwa mum aiki kuma banki basa aiki da daddare bare tace zata bar kuɗin a bank har sai an buƙata, a takaice dai bata son ɓata lokacin shi yasa ta ciro kuɗin, yanzu gashi wanda ya fisu iya ajiyar kuɗin ya ɗauke,ko in ce mara imani. Shi ma Sadiq kasa magana yayi dan yasan ba karamin wahala suka shaba, wajen neman kuɗin nan, jiki ba kwari ya kariso wajen da Jehan ɗin ke tsaye, a hankali yace "Ya Zamuyi" shiru Jehan ta masa dan bata da bakin magana, ganin haka yasa ya riko hannun ta suka hau abin hawan da suka tare suka nufi asibiti, cike da tashin hankali da fargaban abun da zasu gayawa gwaggo. wannan shi ne ba ɗaya kanin biyu, ba gida kuma ba kuɗi sannan ba yiwa mum aiki, tashin sense, muje zuwa yanzu wasan zai fara, karki bari a baki labari. 👹Daular mutuwa👹 Rimsha bata sake fita ba tun ranar da abun nan ya faru tsakanin ta da duna, yau kwana biyu kenan. Yauma kamar kullun suna zaune cikin ɗakin su, sunyi jugum jugum, ita Rimsha sai faman kokarin ɗaure dark black curly hair ta take, gashin nata na da tsantsi sosai yaki ɗauruwa, ita kuma bata son barin sa a sake haka saboda ƙuran dake ɗakin nasu. Cikin sauri Ayla tace "La Meesha muje mu gaishe da baba, kwana biyu ban je ba" juyo da dara daran sleeping eyes nata Rimsha tayi kan Ayla kafin tace "waye kuma baba?" Miƙe wa Ayla tayi tana faɗin "Zo muje ki gan shi" miƙa wa Ayla hannu Rimsha tayi, Ayla tajata ta miƙe tana faɗin "Meesha kin fini quality fa" shiru Rimsha ta mata ba tayi magana ba, mukowa Ayla hannu itama kausar tayi, Ayla ta kama, ta miƙar da ita. A tare suka jera suka fita a ɗakin, suna fita suka hango Mustapha a bakin kofar ɗakin sa yana ɗaure takalmin sa da igiya, da yar fara'ar su suka karisa wajen sa, suka gaida shi, shima da fara'a ya amsa musu tare da tambayar ina zasu je, Ayla ce ta sanar da shi wajen baba zasu je "to kuje nima ina zuwa bari na ɗan gama aiki na" to suka amsa masa da shi kafin su wuce su shiga ɗaya daga cikin ɗakunan dake wajen, yanzu sosai Mustapha ke sake musu fuska suyi hira, tun ranar da Rimsha ta masa magana, shi kenan sai suka zama ɗaya. Kusa da wani tsohon mutumi suka je suka zauna, tsoho ne sosai, ya manyan ta, gashi fari tas kamar bature ga dogon hanci da dara daran ido, duk da tsufa da wahala da yake ciki, hakan ba zai hana kaga kyan saba, ga gashin kan nan nasa da ya zama farin saboda tsufa kwance luf mai tsantsi har goshin sa, Rimsha ta sha mamakin ganin mutumin nan, ji take kamar ta san shi, lokaci guda taji kaunar tsohon ya shiga ranta. Ayla ce ta fara gaishe sa, ya amsa cike da kulawa yana tambayar ta kwana biyu ina ta shiga ta dai na zuwa wajen sa suyi hira, nan take bashi labarin su Rimsha, sosai ya jajan ta musu, kafin suma su gaishe shi ya amsa, sai kallon shi Rimsha keyi tana tunanin ina ta san wannan fuskar, amma ina ta kasa tunawa, amma dai koma me tabbas tasan wannan fuskar. Suna zaune suna hira har Mustapha shima yazo nan suka ci-gaba da hiran su, baba na basu labarai suna dariya, a nan wata yarinya tazo ta same su, suka ci-gaba da hira.. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 *THE BEGINNING* 💞STAR LADY💞 WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 25 Kai tsaye *Florida avenue* James ya nufa sai sharara gudu yake da motar sa a saman shinfiɗaɗiyar titin da zata sada shi da*Florida avenue* ya sanya kiɗa na tashi yana tuƙi yana tunanin yadda zai yi da ogan su, dan yanzu sun dawo masa da zancen kashe GAR sabo, kuma sun matsa masa a kan maganar sosai, saboda sun san duk cikin yaran su shi kaɗai ne zai iya yi musu wannan aikin cikin sauri, kan sa ya kulle sosai ya shiga damuwa neman mafita. Bai ankaraba ya buge wani mutumi da yazo tsallaka titin, a sukwane ya ja wata mahaukaciyar birki har sai da kansa ta bugu da jikin glass ɗin motar, wani irin jiri ya gani lokacin guda, da sauri ya fito daga cikin motar, duk da kan sa sai faman sara masa yake haka ya karisa wajen mutumin da ya buge ɗin, kwance yake saman titi, sai dai da alama bai wani bugu sosai ba, bai ji ciwo sosai ba amma da alama ya samu karaya a kafa, da sauri James ya duƙa duk girman mutumin haka ya ɗauke shi cak, ya sanya shi cikin mota, kasan cewar unguwar na masu kuɗi ne hakan yasa ba hayani ya ba mutane kowa na cikin gida, tunani ya fara yi ina ya kamata ya kai mutumin nan. Daga karshe dai ya yanke shawara ya wuce da shi gida duk da ya san zai fiskanci matsala daga Michael da Romeo amma bashi da zaɓi dole ya kai shi gida, haka ya ja motar sa da gudu ya juya motar ya koma gida. Yana yin parking a parking space na gida ya fito ya ɗauki mutumin ya nufi hanyar shiga cikin gida, a guje jinga jingan sojojin dake tsakar gidan suna gadi, suka nufo shi, har suna rige rigen ansan wannan mutumin daga hannun sa dan su taimaka ma shi, ba musu ya miƙa musu dan dama bai son su Romeo su gan shi ya ɗauko mutumin zasuyi mamaki kasam cewar sun san shi da lalaci. Haka suka shiga palon, a sukwame TGA ya miƙe tsaye yana mamaki, wucewa sojan da ya ɗauko mutumin yayi, yaje ya kwantar da mutumin saman sofa 3 seater sannan ya fice daga palon. "James who is this man? What happened to him?" Tga ne ya jerowa James wannan tambayar, a takaice James ya faɗa masa abun da ya faru na buge mutumin da yayi, nan take Tga ya ɗaure fuska sosai, a fusace yace "carry him out from this house!!!" zaro ido James yayi yana kallon ikon god, yana jinjinawa karfin hali irin na Tga, sai kace gidan sa to ko Romeo mai gidan ma ai ba zai ce a fita da mutumin nan lokaci guda ba tun da ni na bugesa da mota, sai ya bari mun masa jinya. James yayi nisa cikin tunanin da zancen zuci da yake, sai ji yayi Tga ya daga masa tsawa "James I'm I not talking to you?" Yar firgigit James yayi kafin yace "I can't uncle" zaro ash eyes ɗin sa Tga yayi kafin ya wuce ya nufi waje, James na tsaye yana mamaki hali irin na yan uwansa su kwata kwata basa son baki a rayuwar su, inma mace ko namiji duk su basa so, basa son kowa ya raɓe su, sun fi son suyi rayuwar su su kaɗai, gaba ɗaya gidan haka suke ba mai son wani yazo cikin su, basa son mutane musamman Romeo yafi kowa tsanar wasu suzo kusa da su, daga shi sai Michael da Tga sun tsani baki. Sai tunanin ta yadda zai kare da Romeo a kan mutumin nan yake, gashi mutumin yana sume baya cikin hayyacin sa, zuba masa idon James yayi yana kallon sa. A fusace Tga ya dawo cikin palon tare da sojoji biyu jibga jibga masu jini a jika, kai tsaye mutumin Tga ya nuna musu yana faɗin "carry this man out from this house" kallon sojojin James yayi suna kokarin ɗaukan mutumin cikin tsawa James yace "Are you mad, get out from here!!!" Cikin fushi Tga yace da sojojin "i said take this dirty man out" kafe su da ido James yayi kafin yace "Okey carry him let me see" shiru sojojin suka tsaya sun rasa maganar wa za su bi, dan duk wanda suka karyawa doka to zasu rasa aikin su, Tga ogan sune a wajen aiki, while shi kuma James sanyin idanniyar ogan kowa a gidan ne wato Romeo, sun gwammaci suki bin umarnin ogan su wato tga a kan su ɓatawa James rai dan gwara musu hukuncin Tga a kan na Romeo, dan haka sai suka juya suka fice daga palon dan sun san halin Romeo a kan yan uwansa sam baya adalci kuma zai iya yin komai a kan Triplets ɗin sa. Ganin sojojin sun juya sun fice ne yasa Tga ya nufo mutumin da kan sa da nufi ya ɗauke sa ya fitar da shi, yana kai hannun sa zai ɗauki mutumin, a fusace James ya damki hannun nasa tare da turesa gefe guda, rai a matukar ɓace Tga yayi kan James da nufin dukan sa, nan fa James yace bai isa ba, kamar wasu zakuna haka suka fara faɗa. Da karfi Tga ya kaiwa James duka a gefen ciki wadda hakan ya masa mugun zafi sosai, lokacin guda James ya sauya idon sa sukayi jawur nan fa ya riƙiɗe ya zama tamkar mayinwa cin zaki wadda yayi shekara biyu babu abinci ya fito farauta, nan yafara farauta Tga, a fusace ya sanya dukkan karfin sa ya ɗaga Tga yayi wurgi da shi gefe saman glass table na tsakiyar sofa milk color, nan take table ɗin ta tarwatse, gadan gadan James ya haye kan Tga ya fara kai masa bugu ta ko ina yana gurnanin ɓacin rai, ran maza ya ɓaci gaba ɗaya jijiyoyin kan sa dana wuyar sa sun miƙe sai dukan Tga yake sosai, da dai yaga duka da hannun ma bata masa ba sai ya ɗamko wuyar rigar Tga ɗin ya miƙar da shi tsaye, yana kokarin kai masa naushi a ciki, Tga ya riƙe hannun sa tare da kwashe kafafun James ɗin ya zube kasa, nan fa Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka shima Kasan cewar James ya samu horon faɗa sosai wajen ogannin sa, hakan yasa ya san dabarun faɗa sosai, cikin dabara ya juyar da Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka. kamar wasu mayinwatan zakuna haka suka rinƙa farautar junan su, sai dai Tga yaci karfin James, dan shi horon soja ya samu daga wajen Romeo, hakan yasa yayiwa James duka duk ya farfashe masa jiki da fuska, da kyar James ke mumfashi, amma Tga idon sa ya rufe duka kawai yake kai masa ta ko ina. Zuciya ta jasa yana neman kashe James ba tare da ya sani ba. Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, yana kokarin juyowa, a fusace Romeo ya murɗe masa hannun da karfi ta baya tare da ɗaga sa sama daga kan James ɗin yayi wurgi da shi gefe, idon Tga ya rufe baya ji baya gani, bai san waye yayi wurgi da shi ba, a fusace ya taso ya nufi Romeo dan idon sa James yake gane masa, Romeo na tsaye, fuskar nan a ɗaure tamau kamar bai san menene dariya ba, dara daran blue eyes na san nan sun sauya zuwa ja saboda dukan James da Tga yayi, har wani tsuma jikin sa keyi, yau da Tga ba kanin daddy bane da ba abun da zai hana ya kashe shi, amma duk da haka dole ya basa hukunci mai tsanani, shi kuwa Tga idon sa ya rufe gadan gadan ya iso wajen Rome yana kokarin kaiwa Romeo duka a ciki, cak Romeo ya riƙe hannun sa tare da kai masa wawan bugu a ciki wadda ta sanya sai da ya fasa ihu mai sauti, bai kai ga gama ihun ba, Romeo ya sake ɗaga sa sama yayi wurgi da shi saman sofa, wadda sai da ya sanya ya fara dawo cikin hayyacin sa, karisawa wajen sa Romeo yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗamko wuyar sa ya miƙar da shi tsaye, ya tsake masa wuyar tasa, nan fa Tga yaji kamshin mutuwa, cikin fitar hayyaci yasa hannu yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar sa amma ina ya kasa koda motsa hannun Romeo ɗin, sai faman zaro ido waje yake, Yana kokarin tantance wa idon sa ke gane masa, shin abun da ya gani da gaske ne, shin Romeo ne ko gizo ne, bai kai ga iya tantance wa ba Romeo yasa kyakkyawar kafar sa ya taka shi da karfi a kirjin sa wadda sai da ya saki ihu mai ranaza kwakwalwa, tamko wuyar sa Romeo ya sake yi ya kai masa duka a ciki wadda sai da tasa shi dawowa cikin hayyacin sa da kyau, dan yasan ba mai karfin yi masa irin wannan damka da dukan duk gidan sai Romeo. Kwashe kafafun sa Romeo yayi nan take Tga ya zube kasa kan gwiwowin sa, rai a ɓace Romeo ya sanya kyakkyawar farin hannu sa ya ɗamko gashin kansa Tga ɗin ya ɗago kan nasa sama suna fiskantar juna, zuba masa dara daran blue eyes nasa nan Romeo yayi yana kallon face nashi kamar mai tunanin wani abu. Sai galabaitaciyar kukan wahala Tga yake, murya na sarkewa da kyar ya iya faɗin "I'm sorry lion" shiru Romeo yayi kamar bai ji saba, yayin da shi kuma James ke kwance kasa yana numfashin da kyar da kyar, ga fuskar sa nan duk Tga ya fashe masa sai jini yake, abun ku da fatar turawa ba quality sosai ba kamar bakar fata ba, fatar su bata jure wuya ko kaɗan. Jin hayaniya yasa su daddy saukowa kasa, ganin abun dake faruwa yasa suka kariso cikin palon da yar gudun su, cike da tashin hankali a fuskokin su, kuka Michael yasa ya duka kasa yana bawa Romeo hakuri, dan yasan halin Romeo sarai duk yadda yake son sunnan idan suka ɓata masa rai ya zuciya to dukan mutuwa yake musu, gashi kuma da alama yaji haushin abun da Tga ɗin yayiwa James sosai, dan da alama ya ɗan ɓata rai ka ɗan, shiyasa ma ya murɗe wa Tga ɗin hannu kuma ya dake sa har sai da ya zube kan gwiwowin sa, kwata kwata Michael baya son yaga suna samun matsala da juna. Su kuwa su daddy sai godiya suke dan yau Romeo bai ɗauki zafi sosai ba, da ya ɗau zafi yadda Tga ya bugi James ai da yanzu wani zance ake. Ganin yadda Romeo ya ɗagawa Tga wuya sama sosai ne, gashi kuma Tga na shan wahala wajen jan numfashi, hakan yasa murya na rawa daddy ya kariso wajen ya ɗan tsaya daga ɗan baya, cike da kaunar ƴaƴan nasa yace "Please my lion leave him" shiru Romeo ya musu yana ta kallon face ɗin Tga kamar mai karantar wani abu daddy zai sake magana, Romeo ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu alamar bai son jin wata magana kuma, shiru daddy yayi ya koma gefe ya tsaya jin kukan Michael ya fara yin yawa ne kuma gashi Michael yana da matsala yasa Romeo ya juyo da dara daran blue eyes nasa kan fiskar Michael ɗin, a hankali ya saki gashin kan Tga ɗin tare da nunawa Michael hanyar bedroom nasa da hannu ba tare da yayi magana ba, dan bai son Michael ya shiga damuwa, kuma yasan halin sa sarai yanzu zai sa kan sa cikin damuwa, matsowa Michael yayi da rarrafe ya kariso gaban Romeo yana faɗin "Please lion for giv....bai kai karshen maganar ba, Romeo ya daka masa wata gigitatchiyar tsawa wadda ya razana duk wata halitta mai rai dake cikin palon "I said get in!!!" Saboda tsorata Michael bai san lokacin da ya tashi da gudu ya haye sama ba ya razana sosai, yasan halin Romeo idan ya ɗau zafi ba wanda ya isa ya tinkaresa shi yasa su daddy duk suka tsaya a baya, shima Michael ɗin dan yafi su sanin halin Romeo ne, ya san bai ɗauki zafi sosai ba shi yasa ya tinkaresa. Goya hannu a saman kirjin Romeo yayi gently ya fara magana "what is happened?" Yayi maganar yana tsare Tga da dara daran blue eyes nasa nan, da kyar Tga ya iya buɗe baki saboda wahalar yadda Romeo ya muɗe masa wuya ya sanya shi kallon sama, ba dan Romeo ne ya masa tambayar nan ba da ba zai iya magana ba, amma tun da Romeo ne ba yadda zai yi dole ya amsa Maganar ko ma tayaya ne, a hankali yace "please help me with water, i need water!!" kallon Romeo daddy da Uncle Herry sukayi suna jiran Romeo ya bada izinin su kawo wa Tga ɗin ruwan, amma sai sukaga Romeo yayi shiru alamar ba za'a kawo ruwan ba kenan, dan shi Romeo shirun sa ma magana ne, wani lokaci da shiru yake magana da Mutane, gaba ɗaya jama'ar gidan sun san ma'anonin shirun Romeo, idan anana magana da shi yayi shiru to akoi abun da yake nufi baya shiru haka kawai, sannan baya magana sai da kwakkwaran dalili, shima kafin yayi maganar sai ya ɗauki lokaci kuma ba wai dan bai ji me kace ba, yana ji, wani lokaci ka masa magana kana sauri sai yafi 5mins bai baka amsa ba, wata zubin ma har sai ka cire rai da zai yi magana sai kuma gaji ya baka amsa a nitse da sassayan murya, idan kuma bai game sa ba da wannan shirun zai baka amsa in ka gane to ruwan ka, idan ma baka gane ba nan ma kai ta shafa shi dai ya gama nasa. Komawa yayi saman sofa ya zauna yayi shiru yana kallon Tga yana jiran amsar tambayar sa, dan shi baya mai mai ta magana idan yayi, idan baka ji bama dole dai ka bashi amsa, already Tga ya san da wannan dan haka sai ya rarrafa ya koma kusa da kafafun Romeo cikin nitsuwa da shakakiyar murya yace "I'm sorry lion it's was a mistake" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me Tga ɗin yace ba, ganin haka yasa Tga ya gane, bayani abun da ya haɗasu faɗa da James kawai Romeo yake buƙatar ji, cike da tsoron, murya na rawa ya fara bawa Romeo labarin abun da yafaru tum daga farko har kashe. Slowly Romeo ya kai kallon sa kan mutumin, sannan ya kalli James dake ta faman juyi a wajen yana numfashi da kyar da kyar, dawo da kallon sa kan Tga yayi yana mamakin, wai ace James ya samu accident dan bai ji ciwo ba ya dawo gida kuma Tga ya masa irin wannan dukan, nan take yaji wani ɓacin rai ya rufe masa zuciya, a fusace ya miƙe rai a ɓace ya fara dukan Tga, daddy na bashi hakuri ya kyale Tga haka ai ya daku amma ina ba wanda ya saurara dan Tga ya bashi haushi, ace James yayi accident Allah ya tsare bai ji ciwo ba ya dawo sannan Tga ya kama sa ya masa irin wannan duka dan yazo da wanda ya buge da mota gida. Sosai Romeo ya bugi Tga har sai da yaji ya ishe sa, yayin da shi kuma Tga ya sume baya ko motsi, yayi lilis a hannun Romeo, dan ma yayi Sa'a Romeo bai ɗau zafi sosai ba Cike da jin haushin Tga Romeo ya wuce ya nufi in da James ke kwance yana mai da namfashi da kyar da kyar, ko kallon in da su daddy suke bai yi ba, ya ɗauki James ya saɓa sa a kafa ɗan sa ya haye saman bene ya koma bedroom na sa. Yana tafiya su daddy sukayo kan Tga, dan bashi taimakon gaggawa kasan cewar daddy likitane. Shi kuwa Romeo saman katafaren gadon sa ya kwatar da James kusa da Michael dake kwance yana kuka. Ko kallon in da Michael ɗin yake Romeo bai yi ba, ya wuce ya ɗauko kayan aiki ya fara duba James. Sai bayan James ya dawo hayyacin sane yace "Please lion ka taimaki mutumin nan da na buge da mota" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, shi kuma Michael wai yayi fushi da shu shi yasa ya kwanta shiru yana hawaye. After 40mins Sai bayan Romeo ya gama duk abun da ya dace yayiwa James ne sannan yace su kira likita ya duba mutumin, amma shi ba zai duba kowa ba, da sauri James ya miƙe, jikin sa ba kwari ya fito ya nufi wajen daddy, dan ya rokesa ya duba mutumin, abun mamaki ko da ya fito palon sai bai ga mutumin ba, yaji tsoron ko dai sunje sun jefar da mutumin ne kamar yadda suka faɗa, da sauri ya nufi hanyar fita daga palon dan yaje ya tambayo security waya fita da mutumin nan Yana kokarin fita muryan dad ta dakatar da shi "James where are you going" a sukwane ya juyo ya kalli daddy cikin sauri yace "Please dad where is the man I brought" murmushi daddy yayi kafin ya sanar da James mutumin yana ɗakin duba marasa lafiyar su, da sauri James ya nufi wajen dan alhakin kula da mutumin na rataye ne a wuyar sa. Yaji daɗi sosai ganin yadda daddy ya bawa mutumin nan kulawa, har da karin ruwa daddy ya masa, sannan mutumin ya farka, kafar sa da ya karye kuma daddy ya sanya kafar cikin wata na ura na aikin su likitocin. Karisawa cikin ɗakin James yayi, ya zauna a gefen mutumin yana faɗin "Sorry" kallon sa mutumin yayi kafin ya ɗan ɗaga masa kai kawai, "What is your name?" James ya tambayi sunan mutumin, a hankali mutumin yace masa "Musharraf" jinjina kai James yayi kafin yace "are you an Arab from saudia?" Gyaɗa masa kai mutumin yayi kafin yace "Yes" shiru James yayi kafin ya sake cewa "Are you a Muslim?" Nan ma eh mutumin yace masa "Okey how is your body now" James ya faɗa yana kokarin mikewa ya nufar hanyar fita "Alhadulillah" Musharraf ya faɗa yana bin James da ido kawai amma shi kaɗai yasan azaban da yake ji. Ficewa James yayi daga room ɗin yana jin daɗi da mutumin bai mutu ba, a palo ya isko daddy, da fara'a ya yiwa daddy godiya, shima daddy ba karamin daɗi yaji ba, dama kuma ya kula da mutumin ne dan James yaji daɗi, yana son yaga yaran sa suna nuna masa soyayya kamar yadda yake son su amma basa hakan sai dai tsawa da faɗa, shi yasa yanzu yake kokarin yin duk abun da suke so dan ya jawo su jikin sa. Wannan kenan ku koma Nigeria muga meke faruwa 💞NIGERIA💞 💞KATSINA💞 kallon Sadiq tayi idon ta a bushe, dan yanzu gaba ɗaya ta dai na jin kuka zuciyar ta ya bushe, cikin sauri tace "Sadiq ka nemomin masu sayan gidan nan" sannan ta dawo da kallon ta kan gwaggo dake ta faman kuka tace "Gwaggo bamu bukatar mu fitar da Mum waje kuɗin aiki kawai zamu nema mu wuce babban asibiti, na san dai kuɗin gidan nan zai isa ai mata aiki, daman kuɗin jirgin fita wajen shi ne mai tsada, dan haka a sayar da gidan nan a mata magani daga baya zamu san abun yi bayan ta samu lafiya" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi cikin ɗaki. Jim kaɗan ta fito sanye da abaya a jikin ta tana faɗin "Gwaggo ki koma hospital ni da Sadiq zamu nemo mai sayan gidan" kasa magana gwaggo tayi dan ta jinjinawa Jehan wannan shine dalilin da yasa a kace ilimi na da amfani yau gashi ilimin Jehan ya taimaka musu, dan kwata kwata bata kawo zancen sai da gida ko kuma karsu fita waje da mum ba sai gashi Jehan ta kawo musu mafita. Jiki ba kwari gwaggo ta miƙe ta wuce hospital wajen mum, su kuma Jehan da Sadiq suka wuce nemam dillalai. Babban tashin hankali shine duk wanda su Jehan suka kira dan ya sayi gidan idan ya fahimci kuɗi suke buƙata ruwa a jallo, sai yayiwa gidan kuɗin wulakanci, a wannan karon ba karamin tashin hankali Jehan ta shiga ba, dan abun da take tunani shine mafitar su shima yana neman ya gagara, ga mum kuma kwance rai a hannun Allah kowani lokaci daga yanzu tana iya mutuwa, dan da gaggawa ake buƙatar a mata aiki saboda ciwon yaci jikin ta sosai, dan likitan yace ciwon ya jima a zuciyar ta tun bata kai haka ba, cikin watan nan ne kuma ciwon ya kara tsanan ta saboda tashin hankali da ta shiga na rasuwar daddy da kuma ɓatan Rimsha. Kamar zararriya haka Jehan ta dawo lokaci guda ta fita hayyacin ta rasa mada fa. Da kyar suka samu wani ya sai gidan 2 million haka suka sallama masa ya zuba musu kuɗin a account ɗin mum, haka Jehan taje ta ciro 1.5m misalin karfe 5 na yamma, duk wannan yawon da suke tare da Sadiq suke, haka suka shiga a daidaita sahu suka kama hanyar asibiti dan taje ta ɗauki mum su wuce babban hospital, tana rungume da jakar kuɗin tana tunanin halin da suke ciki. A kan hanyar su ta zuwa asibitin ne suka samu accident da wata mota, cikin kwata Jehan ta faɗa yayin da shi kuma Sadiq ya faɗi can gefen titi, saboda juyin da a daidaita sahun tayi da su, shi ne ta watsar da su, kan kace me jama'a sun taru sai salati suke yayin da shima mai motar da sukayi accident ɗin da shi ya sume sakamakon buga kan sa da glass ɗin marfin motar da yayi. Allah ya kiyaye Jehan da Sadiq basu ji ciwo sosai ba, a sukwane Jehan ta miƙe bata damu da kwatar dake jikin taba, ita dai kawai burin ta mum ɗin ta tafita daga haɗari ta samu lafiya. Kai tsaye bakin hanya ta koma tana neman wani mai a daidaita sahu dan su wuce asibiti, ta ruɗe ta manta da jakar kuɗin ma, haka Sadiq yazo ya same ta, suka ɗan kara gaba da in da sukayi accident ɗin suka samu wani abun hawan, zasu hau kenan Sadiq yace mata "Jehan ina kuɗin kuma" a sukwane ta juyo, tana faɗin "Yana cikin wannan abun da muka hau ɗin" a guje Sadiq ya juya ya koma, da sauri ta bi bayan sa. Ko da suka zo wajen babu jakar, tsab suka duba cikin mashin ɗin duk da cewa mashin ɗin ma ya faɗi dan sai da sukayi juyi biyu kafin mashin ɗin ya faɗi. Tsab suka duba cikim mashin ɗin babu komai, a razane Sadiq ya ɗago yana tambayar jama'ar dake wajen, kowa yace masa bai gani ba, mutuwar tsaye Jehan tayi ta kasa motsawa, ta rasa me zatayi, daman ta ciro kuɗin ne a nata tunani dan tana zuwa kawai su wuce babban asibiti ta biya kuɗi kawai a yiwa mum aiki ba sai sun kai gobe ba, a yau zaayiwa mum komai shi yasa tayi sauri ta ciro kuɗin dan kar banki su rufe, gashi a daren nan take son ayiwa mum aiki kuma banki basa aiki da daddare bare tace zata bar kuɗin a bank har sai an buƙata, a takaice dai bata son ɓata lokacin shi yasa ta ciro kuɗin, yanzu gashi wanda ya fisu iya ajiyar kuɗin ya ɗauke,ko in ce mara imani. Shi ma Sadiq kasa magana yayi dan yasan ba karamin wahala suka shaba, wajen neman kuɗin nan, jiki ba kwari ya kariso wajen da Jehan ɗin ke tsaye, a hankali yace "Ya Zamuyi" shiru Jehan ta masa dan bata da bakin magana, ganin haka yasa ya riko hannun ta suka hau abin hawan da suka tare suka nufi asibiti, cike da tashin hankali da fargaban abun da zasu gayawa gwaggo. wannan shi ne ba ɗaya kanin biyu, ba gida kuma ba kuɗi sannan ba yiwa mum aiki, tashin sense, muje zuwa yanzu wasan zai fara, karki bari a baki labari. 👹Daular mutuwa👹 Rimsha bata sake fita ba tun ranar da abun nan ya faru tsakanin ta da duna, yau kwana biyu kenan. Yauma kamar kullun suna zaune cikin ɗakin su, sunyi jugum jugum, ita Rimsha sai faman kokarin ɗaure dark black curly hair ta take, gashin nata na da tsantsi sosai yaki ɗauruwa, ita kuma bata son barin sa a sake haka saboda ƙuran dake ɗakin nasu. Cikin sauri Ayla tace "La Meesha muje mu gaishe da baba, kwana biyu ban je ba" juyo da dara daran sleeping eyes nata Rimsha tayi kan Ayla kafin tace "waye kuma baba?" Miƙe wa Ayla tayi tana faɗin "Zo muje ki gan shi" miƙa wa Ayla hannu Rimsha tayi, Ayla tajata ta miƙe tana faɗin "Meesha kin fini quality fa" shiru Rimsha ta mata ba tayi magana ba, mukowa Ayla hannu itama kausar tayi, Ayla ta kama, ta miƙar da ita. A tare suka jera suka fita a ɗakin, suna fita suka hango Mustapha a bakin kofar ɗakin sa yana ɗaure takalmin sa da igiya, da yar fara'ar su suka karisa wajen sa, suka gaida shi, shima da fara'a ya amsa musu tare da tambayar ina zasu je, Ayla ce ta sanar da shi wajen baba zasu je "to kuje nima ina zuwa bari na ɗan gama aiki na" to suka amsa masa da shi kafin su wuce su shiga ɗaya daga cikin ɗakunan dake wajen, yanzu sosai Mustapha ke sake musu fuska suyi hira, tun ranar da Rimsha ta masa magana, shi kenan sai suka zama ɗaya. Kusa da wani tsohon mutumi suka je suka zauna, tsoho ne sosai, ya manyan ta, gashi fari tas kamar bature ga dogon hanci da dara daran ido, duk da tsufa da wahala da yake ciki, hakan ba zai hana kaga kyan saba, ga gashin kan nan nasa da ya zama farin saboda tsufa kwance luf mai tsantsi har goshin sa, Rimsha ta sha mamakin ganin mutumin nan, ji take kamar ta san shi, lokaci guda taji kaunar tsohon ya shiga ranta. Ayla ce ta fara gaishe sa, ya amsa cike da kulawa yana tambayar ta kwana biyu ina ta shiga ta dai na zuwa wajen sa suyi hira, nan take bashi labarin su Rimsha, sosai ya jajan ta musu, kafin suma su gaishe shi ya amsa, sai kallon shi Rimsha keyi tana tunanin ina ta san wannan fuskar, amma ina ta kasa tunawa, amma dai koma me tabbas tasan wannan fuskar. Suna zaune suna hira har Mustapha shima yazo nan suka ci-gaba da hiran su, baba na basu labarai suna dariya, a nan wata yarinya tazo ta same su, suka ci-gaba da hira.. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 💞TRIPLET'S💞 💞STAR LADY💞 *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 26 Suna zaune suna hira har Mustapha shima yazo nan suka ci-gaba da hiran su, baba na basu labarai suna dariya, a nan wata yarinya tazo ta same su, suka ci-gaba da hira, nan baba ke basu labarin mutanen da a ha rinƙa kashe wa a gidan, sosai Rimsha ta sha mamaki kuma tafi kowa kuka a cikin su, sai lokacin baba ya ɗago ido yana kallon ta, sosai shima yayi shock da ganin ta, abun ya bashi mamaki sai yaji kamar ya santa kamar ya taɓa rayuwa da ita a wani wajen, ya zuba mata ido, ya ɗan jima yama kallon ta kafin ya fara share mata hawaye da hannun sa, yana mamakin ina yasan wannan fuskar, da kyar Rimsha ta yi shiru tare da sah hannun Mustapha dasu Ayla suka samu tayi shiru. "Ya sunan ki?" Baba ya tambaya yana tsare ta da ido, da sauri tace masa "Rimsha" a hankali ya mai mai ta sunan kafin yace "daga wani gari a ka kawo ki nan" nan ma da sauri ta bashi amsa, shiru ya ɗan yi kamar mai nazari, can kuma sai yace "Da farko naji kamar na san ki, amma yanzu danaji daga in da kike sai na fahimci kawai kamace da yanayi yasa naji kamar na san ki, kuma ba zai yiwu ma a ce na san ki ba, dan tun kan a haife ki nake gidan nan, ni bani da wani ɗan uwa a Abuja da Katsina" cikin sauri Rimsha tace "To baba zan iya tambayar ka" gyaɗa mata kai yayi yana murmushi "Baba ya akayi kazo nan?" Shiru ya ɗan yi kafin yace dogon labari ne, zan faɗa miki daga baya, to kawai Rimsha tace masa tare da kara matsowa kusa da shi ta zauna tana tunanin ina ta san face ɗin wannan baban, dan tabbas ta san shi ko kuma mai kama da shi, to ai na kuma wanene, haka ta rinƙa jerowa kan ta tambayoyi, suna zaune shiru. Babu ko excuse duna ya faɗo ɗakin, gaba ɗayan su sai da suka ɗan tsorata, kusa da Rimsha yazo ya tsugunna, sai washe baki yake yace "Two days beautiful girl why are you not coming out?" Rimsha ji take kamar ta kwasa masa mari dan haushi ɗan iskan banza haka take ta faɗi a ranta, tayi shiru tayi banza da shi kamar bata ji me yace ba. Kokarin riko hannun ta yayi dan ya bata hakuri, cikin sauri ta ja baya tana faɗin "don't touch me" mai da hannun sa yayi yana faɗin "because of what?" A kule Rimsha tace "Because I'm a Muslim" zaro ido gaba ɗayan su sukayi, dan gaba ɗayan su ji sukayi kamar sabon abu ta faɗa, baba ne kawai bai ji komai ba kasan cewar shi bai manta komai ba, game da addinin sa, sai dai sun hana shi, sun zaunar da shi baya iya tashi, amma sun kasa mantar da kwakwalwan sa komai, shi kuwa Duna, washe wannan bakin nasa kamar kofar gari yayi kafin yace "Okey Musulmai ba sa son a taɓa jikin sune?" Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Yes of cause" "alright, anyway dama I came to ash you lafiya baki fitowa two days, but please may I know the reason why Muslim people the don't want someone to touch them?" Gyara zaman ta tayi, ta fara masa bayani a kan addinin musulunci "No ba wai bamu son ko babu kyau a taɓa mu bane, a koi wayan da ya halakta ka taɓa akoi kuma wayan da basu halakta ba" tsare ta yayi ya wayan nan jajayen idon nasa yana kallon ta, ci-gaba da magana tayi "idan mutun ɗan uwan kane na jini, ma'ana kanin ka ko kanwar ka ko yayan ka, wannan ya halakta ka taɓa shi, maman ka da baban ka suma sun halakta su taɓaka, sannan idan mutun matar kace ko mijin ki wannan ma ya halakta" zata cigaba da magana yayi saurin ce mata "What is mata ko miji and mama da baba? I knew brother an sister" baba ne ya amsa zancen da cewa "wanan kam ni zan baka amsa" shiru Rimsha tayi suka fara sauraron jawabin baba a kan menene mata da miji, sosai Rimsha ta kara samun ilimi a kan hakan, kallon baba duna yayi kafin yace "Amma dai naji daɗin addnin musuluncin nan kaɗan dan na lura yana da tsab ta, to kenan mu da muke kwanciya da duk matan da muke so babu wannan aure da kuka ce me laifi?" Nan ma baba ne ya kara yi masa bayani a kan hukuncin zina, "duk wanda yayi zina bai tuba ba yakoma ga Allah a ranar tashin alkiyama, zai shiga wuta, bayan ya shiga wuta za'a ɗaure sa da wasu manya manyan sarka a cikin wutar jahannama Allah ya turo wasu halittu masu kama da ɓeraye suzo suna cin gaban sa suna cakwaɗa yana ihu, ga azabar wuta babu mai kawo masa ɗauki, kafin aje ga wutar ma sai ya fiskanci ukuba acikin kabari" shiru duna yayi da alama jikin sa yayi la'asar ganin hakan yasa baba ya kara zafafa masa abun ta hanyar cewa "ba zai taɓa fita wutar nan ba, koda wutar ta kone masa jikin sa dukka to za'a sake halittar sa sabo, wuta ta ci-gaba da cin jikin sa har illa masha Allah" sai dai a wannan gaɓar da kyar baba ya iya ambatar sunan wadda zai sake halittar wato Allah, shima ciki ciki ya ambato, duna dai duk jikin sa ya mutu, a sanyaye yace "to yanzu zan iya auren wannan kenan" yayi maganar yana nuna Rimsha, a zabure Rimsha ta kara ja baya da shi, tana kallon sa wani mummuna da shi, ɗan datti sai wari yake, dariya yayi dan yasan munin sa Rimsha ke gudu, cikin yan sakan ni ya juya kamannin sa ya riƙiɗe zuwa kyakkyawan mutun, kyakkyawar gaske kamar shi yayi halittar kan sa, ba karamin tsorata Rimsha tayi ba, ita kam Ayla dama ta saba ganin suna sauya kamanni, kan kame baba Rimsha tayi tana kuka kasa kasa, "Kin ga yadda muke komawa sai mu kwanta da duk macen da muke so, kuma dole ta yarda ko dan kyan mu" cewar duna yana kokarin ci-gaba da magana, baba ya rigasa da cewa "Musulmai mata basa auren namiji krista, amma musulmi maza suna iya auren mace Kirista" "menene Kirista?" Duna ya tambaya yana kokarin gyara kyakkyawan zobe dake hannun sa, har da zobe ya fitar, yayi kyau da shi sosai kamar shi yayi kan sa, kamar wani balarabe, ya zama matashi mai jini a jika nan dai baba ya fara yi masa bayanin menene krista da kuma yadda aka yi suka zama Kirista, tare da haɗa masa har da yahudawa, sai dai duk lokacin da yazo kiran sunan Allah a bayanin nasa sai yasha wahala "Kiristoci sune wadda suka ce Allah na da ɗa wato annabi isa, sune wadda suka raunata Allah domin wannan babban rauni ne suce Allah na da ɗa, hakan kuma ya samo asaline ta dalilin su guda biyu, na farko wanda suke kira da ɗan Allah, wato annabi Isa, an haifesa ne babu uba, wannan ba shi ne babban matsalar ba, dan ana haifan ƴaƴa dayawa ta cikin shege wadda suma kiristoci da farko irin kallon da suka yiwa annabi isa kenan, suka ce shegene, cikin shege mahaifiyar sa tayi, babban abun da yasa suka ce shi ɗan Allah ne, saboda yayi magana yana jariri, wadda yayi maganar ne ya wanke kan sa da mahaifiyar sa daga ɗan shege da kuma mahaifiyar sa tayi zina kamar yadda suke faɗa, sannan ya faɗa musu shi bawan Allah ne, tun a lokacin suka suma, bayan sun farfaɗo ne suka dage a kan lallai ɗan Allah ne saboda an haifesa babu uba kuma gashi yana jariri yayi magana" cikin sauri duna ya katse baba da cewa "kaji wani tatsuniya ya za'ayi jariri yaro yayi magana" girgiza kai baba yayi, ko kaɗan bai damu ba, dan yasan jahilcine cike da kan duna, banda shan jini da cin namar mutane ba abun da suka iya, dan haka sai bai damu ba ya ci-gaba da yi musa bayani ta yadda zai gamsu, "Ba annabi Isa bane kawai yayi magana yana jariri akoi wani ma wadda lokacin da ake kashe musulmai yayi magana yana jariri, lokacin da kafurai suka tona rami suka hura wuta sosai a ciki, su kace duk wani musulmi in dai ya yarda da shi musulmi ne yazo ya faɗa wutan nan da kan sa tun kafin a jefasa, sau uku wata mata tana zuwa zata faɗa, sai kuma ta fasa saboda yaron ta jariri dake bayan ta a goye, a wannan lokacin ne Allah ya buɗe wa yaron baki yayi magana in da yake sanar da ita ta faɗa shi ne mafita a gare su, to wannan ba abun mamaki bane, kaɗan ne daga cikin ikon Allah" "su waye kuma Yahudawa?" Duna ya sake jefowa baba tambaya, kuma duk wannan tambayoyin da yake wa baba yana yin sune dan yaji ta yadda zai samu Rimsha dan shi gaskiya yarinyar ta burge sa yana son ta, nan fa baba ya shiga yi masa bayani a kan yahudawa, wadda kusan sunfi kowa ilimi a duniyar nan, sai dai kashe ilimin su duk a banza ne saboda basu yarda da Annabi Muhammad (SAW) ba kasan cewar sun karanta a littafin su annabin karshen, wato Muhammad (SAW) zai bayyana ne a cikin su, sai kuma annabi ya bayyana a cikin Larabawa kuraishawa hakan yasa suka kafurce masa suka ki binsa sukaki yarda da shi, kuma suka nemi kashe sa, wannan shi ne sukuma dakilin su na kin yarda da addini musulunci, shiru duna yayi shi dai duk wannan bayani da baba ya masa bai fahimci komai ba, bayan cewa ba'a auren mata sai dai in mutun musulmi ne. Tabbas baba ya fahimci babu abun da duna ya fahimter dan gane da bayanan sa dama kuma yasan mawuyacin abune dunan ya fahimter kasan cewar sa jahili sosai wadda bai taɓa sanin wani abu ba face shan jini, hakan yasa baba yayi shiru kawai yana addu'a a ransa Allah yasa duna ya gane gaskiya, Allah yasa yana da rabon shiriya, ita kuwa Rimsha ta kan kame baba saboda tsoron ganin yadda duna ya rikiɗe ya dawo kyakkyawan saurayi, faritas da shi ga dogon hanci har baka, har da wani curly hair kwance masa a kai har zuwa gaban goshin sa, kyau iya kyau duna ya haɗu, sai satar kallon sa Kausar take tana tsoro su haɗa ido. Kallon ta duna yayi kafin yace "Fine girl why kika cika tsoro ne haka?" Kara matsawa jikin baba tayi dan tsoro, saboda har muryan duna sai da ya sauya, ya dawo mai cool voice, ita ma Kausar ta tsorata sosai, ita kuwa Ayla ko a jikin ta, dan ta saba ganin abun da yafi wannan ma, sai dai tasha mamaki yau saboda son da duna kewa Rimsha ya biyota har nan yazo tambayar kwana biyu lafiya bata fito waje ba, tab lallai akoi kura, aure tsakanin mutun da aljani, aljanin ma magician tab lallai Rimsha kin cire tuta, shi kuwa duna ba abun da yake tunawa sai kyan fuskar Rimsha da kuma dimple nata idan tana magana. Ganin duna yayi shiru ne, yasa baba yace "lafiya duna" miƙewa yayi yana faɗin "zan dawo anjima sai ka faɗa min me ya kama ta nayi kafin wannan yarinya ta dawo nawa" to kawai baba yace masa, sannan ya fice daga room ɗin. Dawo da kallon sa baba yayi kan face ɗin Rimsha dake ta zazzaro sleeping eyes nata, cikin nitsuwa ya fara magana "kina jina Rimsha, na san baki son shi kuma bana miki fatan ma ko hannun ki ya taɓa, amma karki nuna masa hakan, dai basu da imani ko ɗigo a ransu, idan yazo ki biye masa kuyi hira, a hankali har mu ja shi ya shiga cikin addinin mu, idan ya shiga addinin Musulunci, imani ta ratsa shi to komai zai yi sauki, amma yanzu idan kika yi avoiding na shi to tsab zai iya kashe ki, kuma kafin ya kashe ki, zai iya biyan bukatar sa a kan ki tun da kinga ra'ayin hakan ya nuna, zai biya bukatar sa sannan kuma ya kashe ki da kan sa, kuma zai dafa namar jikin ki ya cinye" kara tsorata Rimsha tayi nan take taji hanjin cikin ta ya kaɗa shi ru tayi tana tunanin yadda zata kaya tsakanin ta da wannan bakin aljanin. 💞KADUNA💞 Aafia Yau tun safe Aafia ke ta surfa uban bala'i a gida wai an sace mata waya, hayaniyar ta ya tashi Abbi da Aunty daga barci, suka sauko Palon kasa nan suka same ta, ta tasa mai aikin da Abbi ya kawo a gaba wai ita ta sace mata waya, sai kuka yarinyar take tana ta rantsuwa a kan wlh ba ita bace, abun gwanin ban tausayi, sai wani girgiza Aafia keyi da kugu, tana surfawa yarinyar masifa, while ita kuma Umaisha tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya, sai faman latsa nata wayar take taba turɓune fuska, "Meke faruwa Aafia" Abbi ya tambaya yana kallon ta, kukan makirci ta sawa Abbi tare da tafiya ta rungume sa tana faɗin "Abbi jiya da daddare ina barci naji motsi dana ɗago kai na, sai naga wannan mai aikin ne, to ban kawo komai a rai na ba kasan cewar nasan wani lokaci tana kawo mana tea da daddare, yau da safe na tashi banga waya taba, kuma wlh Abbi ita kaɗai ta shiga bedroom na mu, kuma kafin nayi barci nayi amfani da wayar, dana gama na ɗaura saman bedside drawer nayi barci" already ita kam Aunty tasan sharri Aafia keyiwa mai aikin, dan wlh ba wani tea ɗin da yarinyar nan ke kai musu da daddare, mawai makircine dan sun ga ba mai iya ce wa karya suke, ita kuwa yarinya sai kuka take tana faɗin "wlh ban ɗauki wayar taɓa" shiru Abbi ya ɗan yi kafin yace "to muje ki sai wata wayar mana" turo baki Aafia tayi tana faɗin "Ni Abbi wancan wayar nake so, saboda ina da abubuwa da dama masu amfani a cikin ta" kasan cewar shi Abbi namiji ne kuma babba mai hankali, sai ya gane karya Aafia keyi, hakan yasa yace "to jeki ni zan ansa miki wayar" turo baki Aafia ta kara yi cikin shagwaɓa tace "Abbi muje room nata mu duba mana, nasan ba zata wuce ɓoye wayar a room ɗin ba, kuma wlh idan yana wajen Abbi barin gidan nan zatayi dan ba zamu zauna da ɓarauniya ba" "ke dai jeki kiyi shirin zuwa school zan ansa miki wayar da kai na na ce ko, batun zaman ta a gidan nan kuma ni zan yanke hukunci" ba dan haka taso ba, ta wuce rai a ɓace ta haye sama, Dawo da kallon sa kan Umaisha yayi kafin yace "Ke ba zaki tashi bane, kin zauna kin tasa mu a gaba" tun bai gama rufe baki ba Umaisha ta miƙe ta wuce tabi bayan Aafia, dawo da kallon sa kan Aunty dake tsaye a bayan sa tana mamaki yayi, a nitse yace "Je ki duba ɗakin yarinyar ki ɗauko min wayar" ba musu Aunty ta wuce dan ita ma tasan can Aafia ta kai wayar ta ajiye, dan tayiwa yarinyar sharri Dawo da kallon sa kan yarinyar Abbi yayi a nitse yace "Kiyi shiru" cikin kuka tace "Wlh baba bani na ɗauka ba, ni bana sata kuma ban taɓa yi ba, ka tambayi mamana kaji, dan Allah kada ku koreni daga gidan ku, wlh babana ya rasu bamu da mai bamu abinci, da kuɗin aikin nan nake saya mana abinci" tsugunnawa Abbi yayi ya goge mata hawaye yana faɗin "Ya isa tashi kije kiyi kwanciyar ki, ni ba yaro bane kinji ko? Kuma babu wanda ya isa ya koreki daga gidan nan, dan ba su suka kawo ki ba, ko bana nan wata tace ki bar gidan nan kice ba in da zaki je sai wanda ya kawo ki ya dawo ya mai dake" Gyaɗa masa kai tayi tana ta zuba masa godiya, ta wuce ta koma ɗakin ta. Abbi na wajen har Aunty ta dawo hannun ta riƙe da wayar Aafia, amsar wayar Abbi yayi ya nufi bedroom na su Aafia, ita kuma Aunty ta wuce nasu bedroom ɗin. Tsaye gaban mirror ya isko Aafia, tana tsaye tana faman feshe jikin ta da perfume, cikin nitsuwa ya fara magana ta hanyar amfani da matsayin sa na babba kuma mahaifi a gare su "ina son ku sani duk abun da mutun yayi a duniyar nan kan sa yayiwa, in ma mai kyau ko mara kyau, kuma kullun ina mai tsawatar muku a kan ku rinƙa jin kan nakasa da ku, sannan ku tausaya masa amma bakwa ji, ku dai na ɗaukan duniya da zafi, dan ba wata tsiya a duniyar nan, kun san da haka, tun da duk da wayon ku Mahaifiyar ku ta bar gidan nan, sannan kuna sane da dalilin da yasa ta bar gidan nan, ta guje mu ne saboda bani da kuɗi na shiga jarabawar Ubangiji, amma hakan da tayi yasa na samu nakaso ko wani abu, gashi kwance tashi ba wuya a wajen Allah, Allah ya azurta ni da arzikin da ban mallaka a baya kafin na aure taɓa, kuma kuna sane 3 years back, mun sake shiga jarabawar Ubangiji, Allah ya aiko Husain ya taimake ni, ba dan haka ba ai da yanzu kuma sai dai ku tafi aikatau gidan wasu, wannan bai ishe ku ishara ba? To ina mai kara jan kunnen ku, kubi duniya a sannu, dan ko wani lokaci duniya na iya juyawa daku" ya kai karshen maganar tare da miƙa mata wayar ya fice da bedroom ɗin. A tunanin sa maganar sa ya shiga kunnen su, sai dai abun da bai sani ba, maganar Rufee ta riga nasa zama a kunnen su, sun riga sun yi nisa, Abbi yayi kuskure wajen rashin binciken da waye suke kawance, idan su fita ina suke zuwa, me da me suke aikatawa a School, duk wannan bai sani ba kuma bai damu da ya sani ba, ka san cewar ba wani zama yake a gida ba, wannan shi ne ɗaya daga cikin babban illar rashin uwan a kusa da mutun. Abbi na fita Aafia ta ja guntun tsaki tare da turo baki tana faɗin "wlh Abbi bashi da wani aiki sai yiwa mutane wa'azi kamar wani malami, sai kace mu bamu yi karatu ba" Umaisha ce ta ansa zancen da cewa "Ki godewa Allah Ummi da Yaya Irfan basa nan, ai sun fi Abbi masifa musamman ma Ummi, ni gwara ma da ta tafi, da yanzu tana nan tan faman takura mana, a kan abubuwa da dama, ni bari na kira yaya Irfan ɗin ma na lafaza shi ya bani kuɗi koda 200k ne dan na ɗan yi broke" cikin sauri Aafia tace "Ai kuwa kin tunamin zan biya ta bank na cirowa Rufee 100k ɗazun ta kirani tace tana son 100k kuma kashe take bukata" turɓune fuska Umaisha tayi kafin tace "Kuma sai ki bata? Sai kace wata uwar ki, nifa wlh Rufee nan bata burgeni kawai dai ban son nuna mata hakan ne yasa nake biye mata, amma dai natsane ta wlh" "wlh Umaisha idan kika sake shiga tsakani na da Rufee sai ranki ya ɓaci, ba ruwan ki da ni" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki, ta wuce wajen drawer kayan su, ta ɗauko wasu riga da wando ta sanya kayan sun matse ta sosai, sannan ta ɗauko suwaga bag ɗin ta ta sanya Booth a kafar ta, wani ɗan handkerchief fari ta ɗaura a kan ta, sannan ta ɗauki key ɗin motar ta, a fusace ta fice daga ɗakin, ko breakfast ba ta tsaya ta yi ba bare kuma yiwa su Abbi sallama, haka ta wuce ta fice daga gidan, dan tana da class 8 dai dai. Miƙewa Umaisha tayi ta kwanta dan bata da class ita sai 11 dan haka sai tayi kwanciyar ta sai 10 zata shiga school. Bari mu leƙa Washington DC mu dawo. 💞WASHINGTON DC💞 12:20am Zaune James yake a gefen Musharraf yana kallon ruwan da daddy ya sake kara masa, bayan na jiya ya kare, a hankali Musharraf yace cikin harshen turanci "Amma gaskiya mahaifiyar ku tayi Sa'ar aihuwa, kuna da kirki sosai, gaskiya naji daɗi taimakon da kuka min kuma ina godiya" ɗaure fuska James yayi kafin yace "Mmm ya ma kake da suna? This Your name is seems to be difficult for me, I will just call you uncle kawai, kar ka sake maganar mum a gidan nan, idan ba haka ba zaka mutu lokacin ka bai yi ba" zaro ido Musharraf yayi yana mamaki, cike da tsoro yace "Please may I know what happened to your mum, why did you say kar na sake maganar ta?" Kara ɗaure fuska James yayi kafin yace "Because we hated her, bamu son maganar ta, kai ma i don't know they reason why ka shiga rai na har nake iya baka amsa a kan ta, kuma nayi mamaki yadda a kayi daddy da lion duk suka yarda a kan ka zauna a gidan nan sai ka samu lafiya ka tafi, shawarar da zan baka shine karkayi mistake kayi zancen mum a gaban lion and tiger, dan zasu iya kashe ka" shiru Musharraf ya ɗan yi kafin yace "okey ina godiya, amma dai ban ji daɗi ba domin uwa ita ce jigon ko wani ɗan adam" da sauri James ya ansan da cewa "except our mother, my mother she's a wicked, ba mutuniyar kirki bace that's why we hated her, ta mana abubuwa na mugun ta dayawa" Shiru Musharraf yayi a ran sa yana son sanin me Mahaifiyar su ta musu haka suka tsane ta. Miƙewa James yayi ya nufi hanyar fita daga room ɗin yana faɗin "Good night, daman i came to see your body ne" shi dai Musharraf ya shiga duniyar tunanin me mum ɗin su James ta musu suka tsane ta haka. James na fitowa ya nufi part na sa, zai wuce ya hango hasken wuta a palon kasa wadda ko bai tambaya ba yasan lion ke cin abinci, dan wani time ma har 1 na dare yake kaiwa kafin yaci abinci. Fasa shiga part nasa yayi, ya sauko kasa, ya nufi wajen Romeo dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun table yana latsa system, jikin sa na sanye da kayan barci, farare kal masu laushi marasa nauyi, riga ne da dogon wando, ya kulle dark black curly hair sa nan a baya, while wannan guntu na gaban goshin sa yana nan bai ɗaure shi ba, yana kwance masa a face ɗin sa, hakan ba karamin kyau ke karawa face ɗin sa ba, sai wani fitinanniyar kamshin perfume dake tashi a jikin sa, ya kafe system ɗin dake gaban sa saman table da dara daram blue eyes ɗin nan nasa, kasan cewar dare ne kuma wutar da ya kunna a palon sky blue ne ya kashe farin wutar dan yana son hasken light sky blue, shiyasa wutar part nasa dukka sky blue ne, hakan tasa kwayar idon sa suka kara haske sosai, har wani kyalli suke, yana aiki a system yana ciza red lips na sannan da kyawawan fararen hasoran masu kama da farin auduga, sai kyalli suke suna ɗaukan ido, while lips na sa kuma, duk in ya ciza su sai sun kara ja, kamar lipstick yake sanya musu, gashi sai faman ciza su yake alamar aikin da yake yana ɗan caza masa kai. Ga jibga jibgan bodyguard ɗin sa nan a tsaye a kan sa, sun zuba masa duk wani abincin da zai buƙata a plate sun jere masa, suna jiran kawai yaci. Kujerar kusa da shi James yazo ya zauna yana faɗin "How are you lion?" Shiru Romeo ya masa kamar bai san da zaman sa a wajen ba, aikin sa kawai yake, hannu James ya sa ya fara ɗaukan fruits yana kai wa ɗan bakin sa, shi kuma Romeo sai faman aiki yake. Kai James yasa ya ɗan leko system ɗin Romeo yana faɗin "What are you going ne" kara waro ido James yayi ganin hoton manya manyan shuwa gaban nin su a cikin gaban screen ɗin system ɗin, da alama aiki Romeo yake a kan su, lokacin guda hankalin James yayi mugun tashi, tsoro ya bayyana karara a kan face nashi, wata irinyar zufar wahala ne ta fara karyo masa daga gefe da gefen kunnen sa, ji yayi kan sa na sara masa, har wani duhu duhu yake gani, tunani ya fara yi, me ya kawo hotonan manya manyan jiga jigan ogan nin su kuma a system ɗin Romeo, wadda ko shi kan sa bai taɓa haɗuwa da su fiska da fiska ba, sai dai suyi videos call idan za'ayi wata harkallah, lokaci guda wani tunani ya faɗo masa, to ko dai taron da zasu yi na shakaran nan ne Romeo ya samu information a kai, tun da ogan sa yace masa a wannan taron gaba ɗaya manya manyan jiga jigan ogan nin su zasu halarci taron, dan za'a karrama wasu daga cikin su, tab lallai a koi matsala, in dai Romeo yasan da taron dole zai sa yaran sa su wa taron dirar mikiya su kashe kowa, gashi ni kuma ban isa in ce ba zan halakci taron ba, dan ina ɗaya daga cikin wayan da za'a karawa girma a karramani, wannan taro na shekaran nan ni za'ayiwa. Sosai James ya shiga damuwa yana ta zancen zuci bai san lokacin da Romeo ya kammala aikin ba, sai dai yaji sanyayyar murya Romeo yana faɗin "What are you going here?" Yar firgita irin na marasa gaskiya James yayi, har sai da yasa Romeo kara zaro blue eyes nasa yana kallon shi Zubawa kumin dake gangarowa daga gefe da gefen kunnen James ɗin Romeo yayi, slowly ya mai da blue eyes na sa saman manya manyan Ac dake palon, dukka Ac a kunne suke ga palon da sai yi, amma ya akayi James ke zufa haka, kwata kwata Romeo bai kawo komai a ran sa ba, calmly ya bawa bodyguard ɗin dake tsai tsai ye a kan su, umarnin a kan su kara gudun Ac dake palon dukka, jikin su har kerma yake wajen aikata abun da ya sanya su Kai kallon sa yayi kan abin cin da suka zuba masa, hot coffee kawai ya ɗauka, cikin nitsuwa ya fara kai cup ɗin ɗan bakin sa yana kurɓa yana cirewa cikin class da nitsuwa. Da kyar James ya iya sai ta voice na sa ya fara magana "Please lion i want to know something about this pics that I saw on your system now" shiru Romeo yayi na yan mintoci, da kamar ba zai yi magana ba, sai kuma yace "What did you want to know about them?" "Everything" James ya faɗa cike da tsoro, Ansan tissue da bodyguard ke miƙa masa Romeo yayi, ya ɗan goge kyawawan lausasan red laɓaɓɓan sa, kafin ya juyo da dara daran blue eyes nasa kan James ɗin, calmly ya fara magana "they are the most notorious criminals in the world, I'm investing about them, I want to know where they are residing and I want 2 know who and who theyre working with, and which organisation is funding them" kara tsorata James yayi dan yasan halin Romeo sarai idan har ya sa aiki a gaba tofa tsab yake kammala aikin cikin kankanin lokaci, sai dai daɗin abun ba shi yake fita aikin ba, yana zaune a gida yana fama da system yake bada command yaran sa suna aikatawa, sai dai kuma wani lokaci Tga ke jan ragamar tawagar, abu ɗaya James ya tuna wadda ya sanya shi sakin murmushi lokacin guda, tunawa yayi da cewa, da fake face yake amfani a wajen aikin nasu, dan haka ko Romeo ya binciko hotonan sauran criminals ɗin ba zai gane sa ba, saboda fake face, kuma daman yayi tunanin wannan rana zata iya zuwa shi yasa tun farko yayi dabarar using fake face, a wajen dan gudun kar Romeo ya iya gane sa. Shi kuwa Romeo juyawa yayi ya ci-gaba da shan coffee ɗin sa yana tunanin wa ya kamata ya naɗa wadda zai ja ragamar aikin nan, dan yanzu gaba ɗaya tun da Tga ya bugi James yaji baya son sa, duk da kanin daddyn su ne. Sun yi shiru dukkan su kowa da abun da yake tunawa a ransa. Wayar James ne ta katse musu shirun ta hanyar fara ringing, a sukwane ya ɗago ya kalli Romeo dan yasan abokan harkallan sa ne kawai ke kiran sa cikin daren nan, to ya zai yi idan Romeo ya ansa wayar yayi picking call ɗin, ko ya tambaye sa wanene ke kiran sa, sai dai kuma shi Romeo ko a jikin sa kamar ma bai ji ringing na wayar ba, sai dai ya ɗago kyakkyawar farin hannun sa, ya duba time a diamond watch nasu na Triplets, 01:05am ci-gaba yayi da shan coffee ɗin sa, hakan ba karamin jefa James yayi cikin ruɗani ba, dan yasan shirun Romeo ba karamin abu bane, kuma gashi ya duba time, abun ku da mara gaskiya duk sai ya tsargu, tun Romeo bai tambaye sa ba sai yace abokan sa ke kiran sa dan bai je party su ba, shiru Romeo ya masa kamar bai ji me ya faɗa ba, ya ci-gaba da shan coffee ɗin sa. Shi kuwa James duk a tsarge yake, yabi ya takura kan sai aikin zufa yake ya sanya wa kan sa tunani da damuwa, while shi kuma Romeo ko a jikin sa, kuma bai kawo komai a ran sa ba, saboda ya yarda da su. Sai bayan ya kammala shan coffee ɗin sane ya miƙe, cikin sauri bodyguard suka bashi tissue paper ya goge bakin sa, ya wuce ya nufi sama yana faɗin "Stop telling me what I did not ask you" yayi maganar in a cool voice, ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi part nasa, yana taku irin na jaruman maza, masu izza da nitse. Sosai James ya sake shiga damuwa, ɗan wannan cewa da Romeo yayi ya daina faɗa masa abun da bai tambaye shi ba, hakan ya kara sa shi cikin damuwa, to kenan me Romeo yake nufi, while shi kuma Romeo ko kaɗan ba da wata manufa ya faɗi hakan ba, kawai shi baya son a rinƙa masa maganar abubuwan da ba shi ya tambayi mutun ba ne, shi kuma James tsabar rashin gaskiya ya sashi faɗin abokan sa ke kiran sa kamar an tambaye sa. Jiki ba kwari ya miƙe ya nufi bedroom na sa ransa cike fal da tunanin ko dai Romeo ya fara zargin sane. Yana tafiya suma bodyguard ɗin suka wuce nasu bedroom ɗin dan suje suyi barci su huta aikin su na yau ya kare sai kuma gobe. Washegari gari ta kama Sunday, tun 8 na safe daddy yayi shirin zuwa church shi da Uncle Herry, da Tga, da James, da John da Jay, sai dai me shi dai Michael yana zaune a palo yana latsa wayar Romeo ko alamar shirin zuwa bai yi ba, while shi kuma Romeo yana lafe saman lallausan katafaren gadon sa yana sharara barci, ya ja lallausan bargon ya rufe kan sa, su daddy sun gama shiri suna jiran su. Da dai Jay yaga Michael fa bashi da niyar tashi yaje ya shirya sai yace "Michael we are waiting for you to ga to church" shiru Michael ya musu kamar bai ji me suka ce ba, ya ci-gaba da latsa wayar Romeo yana ɗaure fuska, cikin muryan rarrashe cike da so da kauna dad yace "My tiger we are waiting for you" cikin tsawa Micheal yace "Dad I can't go anywhere, I dnt want to waste my time going there, I have a lot of important thing to do, so please leave me!!!" tashin sense, zaro ido daddy yayi jikin sa har kerma yake yace "Michael are you heard what you said, I you our of sense?" Karo na farko Michael yaja dogon tsaki, dan shi ba mai jan tsaki bane. Kallon James dad yayi jikin sa sai kerma yake, dan tsoron kar pasto ya tsinewa Michael su shiga uku, daman ga Michael ba wani isasshen lafiya gare sa ba, idan Pasto ya tsine masa ina zasu sa ran su, "James go and call lion for me" zama James yayi kusa da Michael yana cire suit ɗin jikin sa yana faɗin "I remember nima ina da abun da zan yi mai muhimmanci, lion kuma yana barci zaka iya zuwa da kan ka, ka tashe sa, kuma daga yau ni ina ga canza church za muyi, dan wannan Pasto he doesn't know anything, makaryaci ne kawai, duk abun da ya faɗa maka last week a kan mu karya yake, zai wani ce maka wai muna rayuwar farinciki da murna, kuma bamu wani aikata abun da ba dai dai ba, tun daga lokacin nasan karya yake saboda ni jiya da kyar nayi barci saboda damuwa" juyowa Michael yayi ya bawa James hannu suka tafa, kamar muna fukai, Michael yace "Well said my blood, nima saboda karyan sa yasa na dai na yarda da shi, kuma naji na tsani duk wata addni ma, dan makaryata na ɗauke su" daddy ya tsorata sosai, shi tsoron sa ɗaya kar pasto ya tsine wa Triplets ɗin sa, ya shiga uku, dan su kaɗai gare sa, sune jin daɗin sa sanyin idanniyar sa, duk da tsufar da ya fara yi hakan bai hana ya haura sama da gudun sa saboda damuwa ba. Kai tsaye part na Romeo ya nufa, kallon Michael James yayi kafin yace "What are we going to do now, dan daddy yaje report na mu ne wajen Romeo kuma ni gaskiya a hate this pasto canza church zan yi" kashewa James ido Michael yayi kamar wasu muna fukai abun ka da Triplets, nan take Michael ya sakewa daddy wasu shegun kwari masu cizon bala'i, duk in da suka cize ka, tofa sai wajen yayi sati yana kumbura yana maka azaban raɗaɗi, gashi basu da magani, wajen yayi ta maka raɗaɗin zafi kamar cizon kunama ka rasa ina zaka sa ranka kaji sanyi. Dad yana kokarin shiga part ɗin Romeo kwarin suka isa gare sa, kai tsaye cikin suit ɗin jikin sa suka shige gasu da yawa, haka suka fara ɗalla masa cizo, ihu ya fara yi, ya fara cire kayan jikin sa, dariya Michael ya fara yi, abun da bai taɓa yi ba a rayuwar sa dariya, saboda mamakin ganin dariyar Michael ya hana su Uncle Herry jiyo ihun daddy, while shi kuma James tausayin daddy yake, amma basu da zaɓi dole su rufewa daddy baki, ko ya dai na takura musu a kan zuwa Church ɗin nan dan basa son ganin Pasto. Tun daga saman staircase daddy ya fara birgima a kasa, har izuwa kasan stair ɗin cikin palon, sai ihu yake yana kiran sunan Jesus, a guje su Uncle Herry sukayo kan sa suna tambayar lafiya, nan suma James ya sake musu nashi kwarin, zo kaga yadda ake rige rigen cire kaya, tuni sunyi wurgi da Bibles dake hannayen su, sun fara birgima suna ihu, shi kam Tga ma nashi yafi yawa dan haushin sa James ke ji, sai dariya Michael ke ɓaɓagawa kamar zararre. Daddy gwanin ban tausayi tsohon nan, duk wayan nan kwari sun cize masa fuska, fuskar ta kunbura sumtum kamar ruɓaɓɓiyar alale, abun ku da fatar Bature ba quality sosai, gashi sai cizon sa suke, shi kam John bayan ihu har da zagi yake zubawa kwarin, shi kuma uncle Herry tsinuwa yake ta aikawa kwarin ba iya ka da turanci, duk kwarin sun kunbura musu jiki. Yau har da yaren mahaukata su kayi, ba iya turancin kawai ba Uncle Tga bai ankara ba kawai sai yaji kwarin sun shige cikin Short ɗin sa, dai dai sai ti suka samu suka fara kai masa harbi da cizo, kuma James ya tura su saboda mugunta. Wani mahaukacin ihu Tga ya fasa tare da miƙe wa kamar mahaukaci haka ya bazama, bai san in da ya nufa ba, saboda azaba, Allah sarki bawan Allah, sai gudu yake yana tsalle kamar doki, ya kan kame wajen, kai tsaye ya haye saman bene, ai ko awannan gaɓar na Tga sai da ya sanya James ma dariya mugunta, daman shi kam Michael kamar zararre ya dawo saboda dariya, uncle tga kuma ya kara haukata sa da dariyar, har da sulalowa kasa daga saman sofar saboda dariya. Michael akoi iya dariyar mugunta Kai tsaye bedroom na Romeo Tga ya nufa cikin fitar hayyaci da azabar raɗaɗi, ya manta in da ya nufa, yafi abun da yake gudun wa bala'i, dan in ya kuskura ya tashi Romeo daga barci, hmmm.....✍️ Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 27 Kai tsaye bedroom na Romeo Tga ya nufa cikin fitar hayyaci da azabar raɗaɗi, ya manta in da ya nufa, yafi abun da yake gudun wa bala'i, dan in ya kuskura ya tashi Romeo daga barci baya ji da daɗi ba. Yana shiga a guje ya haye saman bed ɗin Romeo, sai faman mammatse short na shi yake yana ihu kamar ƙaramin yaro. A nitse Romeo ya waro dara daran blue eyes na sa masu ɗauke da barci a kan face ɗin Tga dake kankame da short ɗin sa yana ihu, lumshe ido Romeo yayi ya sake buɗe wa, fuskar nan tasa a ɗaure kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, tamkar bai san menene dariya ba, already daman shi Romeo haka face ɗin sa take kullun a ɗaure tamau kamar hadari, tsabar kyan sa yasa ɗaure fuskar ke kara masa kyau kuma yasa hakan tafi dacewa da shi. A hankali ya miƙe zaune tare da sanya kyawawan fararen hannun sa ya tara dark black curly hair sa da suka bazo masa a face, tara su yayi ya mai da su ta bayan sa, calmly da wannan sexy voice na shin, gashi yanzu ya tashi daga barci, voice ɗin kasa kasa mai ɗauke da barci gwanin daɗin sauraro, a nitse yace "What happened? What brought you here?" Kasa magana Tga yayi saboda ihun azaba da yake yana kallon kofar shigowa, slowly Romeo ya juya dara daran blue eyes nasa kan kofar, ganin babu kowa ne yasa in a cool voice yace "get out" yayi maganar yana kara ɗaure fuska kamar hadari, sai lokacin Tga ya kalli face ɗin Romeo da kyau, sai lokacin ya gane in da ya shigo Ganin ɗaurariyar face ɗin Romeo kamar wani lion ɗin gaske ne yasa Tga sake fasa razananiyar ihu tare da dirowa kasa daga saman gadon yayi waje da gudu, shiru Romeo ya ɗan yi yana tunanin, me ya samu Tga, yake wannan ihun, tabbas yaji a jikin sa Triplets nasa sun yi wani abun, amma bai kawo a ransa abun da suka aikata ba kenan, guntun tsaki yaja tare da komawa ya kwanta. Can kasa kasa yake jiyo ihun su daddy, kamar a mafarki, shiru yayi kamar ba zai miƙe ba, can kuma da yaji ihun yaki tsayawa, kuma ba voice ɗin mutun ɗaya bane, hakan yasa, ya miƙe zaune, a hankali ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasa tare da miƙewa kamar bai son taka kasa saboda barci dake idon sa, haka ya sanya kyakkyawan bedroom slippers na sa white color masu bala'i kyau da laushi da tsada, sannan ya nufi waje. Yana fitowa palon sa, sai yaji ihun nasu ya kara yawa, kasan cewar part nasa yayi nisa da palon kasan ne yasa baya jin hayani sosai idan a nayi a palon kasa, Part na sa a hawa na biyu yake. A farkon saukowa benen shigowa palon kasan ya tsaya tare da goya hannu a kirji ya zubawa su daddy dake birgima a kasa, dara daran blue eyes nasa yana kallon yadda suke ihu suna birgima suna neman taimako. Slowly ya dawo da kallon sa kan su Michael dake ta faman ɓaɓɓaga dariya kamar wayan da suka zare, yar gyaran murya yayi wadda tasa duk wata halitta mai rai a palon ɗagowa yana kallon sa, har su daddy masu ihun, jin voice ɗin Romeo yasa sun mance da meke cizon su, sun mance da bala'i da suke ciki, dan gwara musu kwarin nan a kan hukuncin Romeo. A ɗari James da Michael suka miƙe, kamar zasu tashi sama saboda gudu suka fice daga palon suka yi wajen harabar gidan, jinjina kai Romeo yayi yana tunanin ya zai yi da yaran nan wani hukunci zai musu, ihun uncle Herry ya dawo da shi daga duniyar tunanin me ya kamata yayiwa su James. Guntun tsaki yaja tare da dakatar da kwarin, ya kalli Jinga jibgan sojojin dake cikin Kitchen suna Aikin girki "go and bring them for me" ya faɗa tare da fara taka staircase ɗin a hankali, ya sauko zuwa cikin Palon, ya zauna saman sofa yana kallon yadda su daddy ke fama da sosa jikin su suna kuka. A saman ka faɗar su Sojojin nan suka ɗauko Michael da James suka kawo su gaban Romeo, still har lokacin guntse dariya suke kallon fuskokin su Romeo yayi, a maimakon yaji haushi ko ya musu wani hukunci, sai ya tsinci kan sa da jin zuciyar sa tayi sanyi ganin dariyar dake kan fuskokin su, yau first time yaga sun yi dariya a rayuwar su, dukkan su Triplets ɗin ba masu dariya bane, dan basu taso a yanayin dariya ba, tun suna yara renon sojoji uncle Herry da dad suka musu, sannan kuma sun taso da tsantsar tsanar mum ɗin su, hakan yana ɗaya daga cikin abun da yasa basa dariya kuma basu da yawan magana, basa shiga harkan kowa kuma basa son a shiga nasu, basa son baki, su kaɗai suke rayuwar su, dan basa yarda da kowa, sunce tun da mum ɗin su ta iya cin amanar su, to kowa ma zai iya, shiyasa ko daddyn su ba su yarda da shi ba, su ukun nan su kaɗai suka yarda da kan su, bayan su basu yarda da kowa ba, sai dai gara James da Michael su kana iya yi musu magana har su tsaya su saurare ka, shi kam Romeo ai duk gidan ba wanda ya ga fuskar da zai iya yi masa magana, bala'i tsoron sa suke, ba mai iya tinkarar sa ya masa wata maga, har daddy mutuwar tsoron sa yake, ɗan gara Michael da yake suna shiri sosai, kuma saboda matsalar Michael yasa ya jasa a jiki, ban da haka ba mai kwarim gwiwar iya tinkarar sa, a baya kafin yanzu ma idan daddy na son yi masa magana a kan wani abu to fa sai dai in ya sha giya, baya taɓa iya tinkarar Romeo ko da a waya ne baya taɓa iyawa sai ya sha giya ya bugu, saboda tsoron Romeo, ganin wannan ɗaurariyar face ɗin na Romeo ba karamin razana mutane yake ba, yana sanya hantan manyan maza ta kaɗa, shi yasa mum take cewa ganin Romeo yana cikin farinciki ma razana ta yake, dan shi koyana cikin farinciki fuska a ɗaure take, baga taɓa gane masa, yanzu kuma da yake bawa daddy dama ya faɗa masa duk wani abun da ke damun sa, idan daddy yaje daga can baya yake tsayawa, saboda tsoro, kuma ba duka ba zagi, ba ɗaya da Romeo ke masa, kawai dai Allah ya zubawa daddy tsoron wanan face ɗin na Romeo ne mai sanya hantan manyan maza kaɗawa. Shiru Romeo yayi ya zuba musu wayan nan kyawawan dara daran blue eyes na sa nan yana kallon su, sai faman guntse dariya suke, shi kan shi abun ya ɗan nishaɗan tar da shi ganin yan uwan sa haka ya kayatar da shi, da yake ba'a gane farin cikin sa yasa ba wanda ya gane hakan, lumshe idon nasa yayi, hakan yasa long eyelashes nasa suka kara bayyana, kamar wadda ya kara dana kanti, sake waro idon nasa yayi sosai har sai da suka kara kyalli, saboda ya zaro su sosai. "Go and apologize to them" ya faɗa a sanyaye, ba musu suka miƙe still har lokacin guntse dariya suke, jikin daddy suka fara shafa masa dan ya samu saukin yaraɗaɗin, dan daman idan ba su suka shafa wannan cizon kwarin ba, babu wani magani da zai kashe kai fin dafin cizon ta dai na raɗaɗi, tsab suka shafe jikin daddy, hakan yasa daddy ya samu sassauci daga raɗaɗin azaban zafin cizon kwarin. Romeo yana zaune yana kallon su, sai da suka bi kowa suka shafe su, sannan suka dawo gaban sa suka tsuguna suna sunnar da kai kasa, irin na marasa gaskiya, wayan da suka yi laifi jingina kai Romeo yayi da jikin sofa tare da lumshe dara daran blue eyes nasa yana mai jin kaunar yan uwan nan nasa a ransa. Almost 30mins kafin ya miƙe ba tare da ya musu magana ba, ya haura sama abun sa, kallon juna sukayi kamar wasu munafukai, a tare suka kwashe da dariya, kamar wayan da suka sha suka bugu, har da faɗuwa kasa suna ɓaɓɓaga dariya kamar ba lafiya ba, kasan cewar su daddy sun samu saukin raɗaɗin, hakan yasa suka samu damar dawowa cikin hayyacin su, suka zubawa su James ɗin ido sai faman dikar dariya suke, shi dai daddy addu'a kawai yake Allah ya shirya masa wayan nan yara, dan tun suna yara suke azabtar da shi da wayan nan kwari idan ya musu laifi, da suka girma ne suka dai na, har ya manta da kwarin nasu, a tunanin sa ma yanzu babu kwarin ashe ashe a koi su kawai basa fitar wa ne. A tare suka miƙe har lokacin dariyar ya ki sakin su, haka suka wuce sama suka nufi part na James, binsu da ido daddy yayi har suka ɓace sannan ya lallaɓa ya miƙe yana bawa su Uncle Herry hakuri, nan fa daddy yaga Tga har lokacin sai murkusoso yake, kusa da shi daddy ya matso ya taɓa shi yana faɗin "General what's wrong with you? Are you okey?" Kasa magana Tga yayi kasan cewar su James ba su shafa masa wajen da ya samu harbi cikin Short na sa ba, to wajen ya kunbura sai azaban zafi yake masa. Daddy da ya fahimci haka ta hanyar wajen da Tga ɗin ya riƙe da hannun sa, hakan yasa daddy yace da Bodyguard ɗin dake gadin wajen table ɗin cin abinci suzo su ɗauka masa Tga su kai shi ɗakin duba mara lafiya, dan ya bashi taimakon gaggawa, ko ya ɗan samu sauki, duk abun dake faruwa a palon tun daga farko har karshe bodyguard da sojojin suna gani amma ba halin yin magana dan ba shine aikin su ba. Cikin sauri suka ɗauki Tga suka wuce da shi word room na su, da kyar daddy ya iya takawa zuwa room ɗin dan ya ceto kanin sa kuma ɗan autan su, daga haɗari. Ba karamin dirama daddy ya shaba wajen dubawa Tga wajen, dan Tga yaki tsayawa saboda azaban zafin, har sai da dad yace zai kira Romeo sannan Tga ya yarda, daddy ya taimaka masa, duk da ba wani maganin da zai sa ya dai na zafin, amma ba laifi ya ɗan rage. Haka daddy ya bawa sauran ma kulawa kafin yayi treating na kan sa. A takaice dai a wannan rana ba'aje wannan church ɗin ba saboda aika aikan da Triplets sukayi, ko in ce James da Michael. 💞NIGERIA💞 💞KADUNA💞 Kai tsaye bank Aafia ta wuce, taje ta cirowa Rufee kuɗi sannan ta wuce school, kamar wasu wadda a ka gaji da su a gida, kullun sassafe suke zuwa school Rufee da Amal ko da basu da class sai sun zo, suyi ta zaman banza, kamar wayan da basu da mafaɗi, kai tsaye department na su Aafia ta wuce, nan ta isko su Rufee Suna ganin ta suka fara rungumar juna Amal tana faɗin "I missed you two days?" Zama Aafia tayi saman kujerar dake wajen ta ciro kuɗi ta miƙa wa Rufee 100k tana faɗin "Missed you too my girls" amsan kuɗin Rufee tayi tana wash baki, ba ko na gode bare Allah ya yi albarka haka ta tura kuɗi cikin jakar ta kamar bashi ta bawa Aafia ɗin. Sai bayan ta sanya kuɗin a jaka ne sannan ta zauna kusa da Aafia tana faɗin "Please Aafi ya maganar Alhajin nan ne? A matse fa yake yana son ganin ki dan Allah" shiru Aafia ta ɗan yi kafin tace "Idan muka gama exam kice masa yazo mu haɗu a nan" washe baki Rufee tayi aikin bokan ta yayi kyau, ita kuma Aafia haka kawai taji bata ji daɗin amsa wa Rufee da tayi ba, dan tana jin kamar ba zata iya haɗuwa da Alhajin ba, amma ba zata iya yiwa Rufee musu ba. 💞Gidan Abba💞 09:00pm Zaune Akila baiwar Allah take saman sofa a palon su, sai faman kiran layin daddyn Jelly take amma layin baya shiga, yau wajen week ɗaya kenan Akila na neman layin daddy dan suyi hira da Jelly, amma a kashe, yau sosai Akila ta shiga damuwar ko lafiya, tunani ta fara yi yadda zata ɓullo wa lamarin, "ko dai na je kanon na duba meke faruwa ne" ta jefowa kan ta tambaya da bata da amsa "To idan zanje Kano me zan cewa Abba da Ammie ina zance musu zanje" shiru tayi ta rasa mafita ta shiga damuwa, gashi in ta tambayi yaya Imran ma sai yace mata shi ma baya samun daddy a waya, amma sun kusa kammala exam zai dawo cikin Month mai kamawan nan zai ɗauke ta suje kanon tare, ta dai na damuwa In Sha Allah komai yana nan normal. Ita dai amsa masa da to kawai tayi amma ba wai dan haji daɗin hakan ba, tayi shiru tana tunanin ko dai ta kira su Aafia ne, duk ta shiga damuwa tana kewar yan uwan ta, sai dai idan ta kira su Aafia ba wani jin daɗin su take ba, saboda basa mata magana mai daɗi. Haka tayi shiru tana tunani, kamar a mafarki ta fara ganin wutar palon su na kawowa yana ɗauke wa, da farko ta ɗauka rikicin yan nepa ne dan haka bata wani damu ba, sai kuma taga abun gaba yake yaki tsayawa, har wani shekin wutar yake, yana abu kamar shocking na nepa, tsoro ta fara ji, jikin ta ya fara kerma, sai zare ido take, a hankali ta miƙe tana takawa kamar wadda koi ya fashewa a ciki, kai tsaye saman bene ta nufa, tana tafiya tana jin motsi kamar ana bin ta a baya, ji tayi kamar ta fasa ihu, sai dai kuma ta kasa yin ihun, sosai ta tsorata, ganin ta kusa haurawa sama ne yasa ta kwasa da gudu, ta nufi betroom ɗin Ammie. Ko da tazo zata shiga bedroom ɗin sai kofar bedroom ɗin ya rufe kan sa da kansa, ihu ta saki tare da juyawa da gudun gaske ta nufi bedroom na Abba, nan ma ko da tazo zata shiga, sai kofar bedroom ɗin ya rufe kan sa, nan fa tsoro ya kara dira mata a ran ta, jikin ta har wani kerma yake, sai zaro ido waje take, ta rasa ina zata sa ranta, tana tsaye a kofar bedroom na Abba kamar a mafarki gaba ɗaya wutan gidan ya ɗauke, wani bala'i duhu ya gauraye ko ina, a guje ta nufi bedroom nata tare da yin wurgi da wayar ta, da karfi ta fara kiran Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, tana furta hakan kan kace me, wutar gidan ya dawo, haske ya gauraye ko ina, hayewa saman gadon ta tayi, a ɗari ta shige cikin bargo tana kuka kasa kasa, tana ambato sunan Allah, da karfi ta runtse idon ta yau taga tashin hankali da kyar barci yayi awon gaba da ita, har tayi barci jikin ta bai dena kerman tsoroba. 💞KATSINA💞 Ko da Jehan suka isa Hospital ta sanar da gwaggo abun da ke faruwa, sosai gwaggo ta shiga damuwa, ga mum kuma har yanzu bata ko motsi, bata san in da kan ta yake ba, sun zauna jugum jugum a harabar hospital ɗin sun rasa madafa, ban da sunan Allah ba abun da suke ambata a ransu, kamar daga sama sukaji sallama a ta bayan su, gwaggo Jehan Sadiq har suna rige rigen juyawa Sadiq ne kawai ya iya amsa sallamar, tare da miƙa wa matashin hannun sa suka gaisa, "idan ba damuwa zan iya zama, dan ina son magana da mama ce" matashin yayi magana yana kallon gwaggo, kallon gwaggo shima Sadiq ɗin yayi yana jiran suji me zata ce Da hannu gwaggo ta yiwa saurayin nuni da wajen zama ba tare da tayi magana ba, kasan cewar matashin ba zai fi sa'an Sadiq ba a haihuwa, shi yasa gwaggo bata damu ba. "Mama sunana Ibrahim, ni ma'aikacine a super restaurant, wadda aka buɗe kwannan nan, nasan kun san restaurant ɗin, to a takaice dai, daman an baki aikin samo yara yan mata wayan da zasu dace da aiki a wajen, to tun jiya da na shigo hospital nan, naga wannan yar taki a fiska ta dace da irin wadda muke buƙata, sai dai ta fannin karatu kuma zamu mata jarabawa, idan ba damuwa ina muku tayin aikin" cewar Ibrahim, yayi maganar yana karewa Jehan kallo, murya a dashe gwaggo tace "Muna cikin damuwar da ba zamu iya yin wani abun ba yanzu, ita kan ta yarinyar ba zata iya yi muku abun da kuke buƙata ba, duk da ma bamu san a kan wani restaurant kuke magana ba" Sadiq ne ya ansa zancen da cewa "Gwaggo ni nasan restaurant ɗin yana da kyau sosai kuma sabo ne, babban restaurant ne, wlh da Jehan zata ansa tayin su zai taimaka muku sosai" da sauri Ibrahim ya ansa zancen da cewa "Sosai mama wlh mai gidan mu yana da kirki sosai, kuma kinga sabon restaurant ne zata ji daɗi aiki damu sosai" kallon Ibrahim da kyau gwaggo tayi kafin tace "ba wai munki aiki bane, a'a muna cikin damuwar da ba zata iya yi muku abun da kuke bukata ba" "Mama menene damuwar taku?" Cewar Ibrahim, Sadiq ne ya bashi labarin halin da Mum ke ciki, yana magana Jehan na kuka gwaggo na rarrashin ta. Shiru Ibrahim yayi kafin yace "To nawa ne yanzu ya rage kuɗin" da sauri Jehan ta bashi amsa, tana sharan kwallai "500k saura kuɗin gida da muka sayar, sai kuma 200k da daman already yana cikin account ɗin" "idan aka haɗa ya zama 700k kenan ko?" Cewar Ibrahim, da sauri Jehan ta gyaɗa masa kai, "to nawa daman ake buƙata wajen aikin nata?" Gwaggo ce tace "Dr yace mu tana ji kuɗin aiki kawai 1.5 sai kuɗin jirgin fita waje" jinjina kai Ibrahim yayi kafin yace "Zan iya cika muku amma aro bashi, idan ta fara aiki a restaurant ɗin mu, 40k za'a na biyanta ko wani wata, to idan an biyata ni zan rinƙa cire 20k a ciki ina barin mata 20k tana taimaka muku a gida, har Allah yasa ta gama biyana kuɗi na" da murna su gwaggo suka rinƙa zuba masa godiya, a tunanin su dan Allah ya musu hakan, sai dai basu sani ba idan ya kai Jehan kuɗin da za'a bashi sai ya fi haka, dan mai restaurant ɗin ne yace masa ya samo masa yan mata kyawawa masu jini a jika, wayan da kyan su zai rinƙa jawo masa costumers, shi yasa Ibrahim tun da ya kwalla ido yaga Jehan shikenan, har da hoto ya ɗauke ta bata sani ba, ya turawa mai gidan nasa, aikuwa mai gidan nasu na gani yace Jehan tayi ya kawo ta zasu bashi 500k, dan kyan Jehan dole jama'a suyita tururuwan zuwa cin abinci, mu sammanma matasa da manyan masu kuɗi, sai dai abun da mai gidan nasu bai sani ba, Jehan ba kamar yadda suke tunani bace, dan bata da fara'ar da zata ja musu costumers kamar yadda suke tunani, sannan bata daukan raini bata ɗaukan wulakanci haka zalika tana da raini da kirman kai ga izza, sannan tana kallon kowa kamar a karkashin ta yake, saboda yadda ta taso a gida lokaci daddyn su naman. hmmm akoi cakwakiya a wannan restaurant ɗin yasin, muje zuwa. Ibrahim da kan yaje ya muɗe musu motar sa kirar *Corolla* suka sanya mum gidan baya, suka shiga suka wuce babban Hospital sai daɗi Jehan take ji, shima Ibrahim sai daɗi yake ji, zai samu kyautar 500k daga ogan sa. A takaice dai sun yi Sa'a za'a iya yiwa mum aikin a kan 1.2 Ibrahim ya cika musu 500k a ka sanya rana, nan da 1 week za'a mata aiki, sai murna Jehan take, ta mance da duk wani bakin ciki da kuncin da take ciki, ita dai burin ta ya cika mum zata samu lafiya. 💞KADUNA💞 Su Aafia suna zaune suna hiran su na kawaye kamar yadda suka saba kafin lokaci class nasu ya cika, da sallama wani kyakkyawan mata shi ya kariso wajen su, fari tas da shi kamar balaraɓe, da fara'a Rufee da Amal suka amsa ma shi sallamar, while ita Anisa daman bata damu da yawan magana ba, kuma bata cika shiga harkan mutane ba, kusan halin ta ɗaya da Aafia. Kusa da Amal matashin ya zauna yana faɗin "Ina babban yarinya ne" yayi maganar yana kallon Aafia, guntun tsaki Aafia taja tana turɓune fuska tace "Tana gida, amma anjima kaɗan zata shigo" murmushi yayi kafin yace "Allah Aafia Umaisha babban yarin ya tana matukar burgeni" dogon tsaki Amal taja tare da miƙewa tsaye tana faɗin "Yanzu Man a gaba na kake cewa wata tana burgeka? Ko kunya ta baka ji ba, wannan ai cin fuska ce" ita dai Aafia shiru ta musu kamar bata a wajen, Anisa ce tace "Kai Amal amma baki da kunya, yanzu dan Mansoor yace Umaisha na burge shi ne zaki ɓata rai? To Umaisha ɗin ba kanwar ki bace? Ai ko dan ganin idon Aafia kya mata kara, kuma ai man ba cewa yayi yana son Umaisha ɗin ba, kawai cewa yayi tana burge sa" Rufee ce ta dakawa Anisa tsawa da cewa "Ke Anisa kiyiwa mutane shiru, ke me kika sani game da kishi? Amal na da gaskiya wannan cin fuska ya mata, akan me zai ce wata mace na burgesa a gaban matar sa In Sha Sha" shiru Anisa tayi taba tanka Rufee ba, ita kuwa Aafia ka san cewar bata cika son hayaniya ba, sai ta miƙe kawai ta bar musu wajen, da sauri Anisa ta miƙe tabi bayan ta, dogon tsaki Rufee taja kafin tace "Wlh Amal karki yarda son Umaisha yake tun da ya faɗi hakan" ta kai karshen maganar tare da miƙewa tabi bayan su Aafia. Matsowa gaban sa Amal tayi suna fuskantar juna ta fara surfa masa uwar masifa, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, cikin masifar nata har da cewa karya sake yi mata magana sun rabu kenan, shi dai man shiru ya mata yana kallon ta, har ta gama ruwan bala'i nata, ta wuce ta bashi waje, tana tafiya ya ɗaure fuska tare da zaro idon sa, nan take idon suka sauya zuwa purple color, jikin sa har kerma yake, ɗan jujjuyawa yayi dan yaga ko a koi mutane, ganin babu mutane sosai a wajen ne, yasa ya faki idon yan kalilan student dake wajen ya buɗe bakin sa, wasu dankara dankaran macizai guda biyu suka fito daga cikin bakin nasa, bakake kirin masu kan faranti, kai tsaye bayan su Aafia macizan nan suka bi, cikin sauri kamar munafiki ya miƙe ya bar wajen tare da mai da asalin kalar idon sa wato fari da baki. Su Aafia kuwa, suna barin wajen kai tsaye wajen wani ɗan karamin wajen hutawa dake cikin school ɗin suka nufa, waje ne mai ɗauke da kujeru wadda aka gina su da siminti, kasan wajen grass ne kanana masu kyau green color. Saman kujerun su Aafia suka je suka zauna, Anisa na bawa Aafia hakuri Yar dariya Aafia tayi kafin tace "Ba komai kuma idan kika duba ai Amal na da gaskiya, taya za'ayi Man yace wata tana burgesa kuma a gaban budurwar sa wadda yake ikirarin zai aura, duk da cewa basu wani jima da haɗuwa ba, ai hakan bai dace ba" Anisa zata yi magana sai ga Rufee, kasan cewar tasan halin Rufee da masifa, sai tayi shiru kawai suka basar da maganar, zama kusa da su Rufee tayi ba tare da tayi musu magana ba, sai wani kwaɓe fuska take kamar wadda taga kashi. Shiru suka zauna har Amal ta kariso wajen, Amal na zama wayan nan mayun macizan suka iso, masu karfin dafin bala'i ga idon su nan kamar na mutane, gasu da kattin kai kamar faranti, idan ka gansu kai kace mutane ne saboda ison su, sulalewa sukayi ta cikin grass dake wajen, kai tsaye suka kaiwa Amal sara a kafa, suna saran ta kuma suka ɓace ɓat, ihu Amal ta fasa tare da sulalowa ta zube kasa, kamar an ɗauke wutar nepa tayi tsit, daga wannan ihu ɗayan shikenan bata kara wani ba, ta zama gawa. A razane su Aafia suka miƙe sukayo kan ta, yayin da shi ma, man ɗin ya kariso wajen a lokacin wai yazo bawa Amal hakuri kamar bai san komai ba. Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa... Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 💞TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 28 Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa, cikin sauri ya kariso wajen ya sanya hannun sa ya ɗaba Amal ɗin, shiru bata ko motsi, su Aafia basu sani ba, sanya hannun sannan da yayi, ya kwashe dafin da ke jikin tane, ba dan haka ba suka taɓa ta mutuwa zasu yi suma. Munafiki nan fa ya sanya musu kukan munafurci yana faɗin "Amal bata numfashi, Amal bata tare da mu, Shikenan munshiga uku" Aafia ta kasa magana ganin abun take kamar mafarki, ita kuwa Rufee ihu ta sa ta duƙa tana girgiza Amal ɗin tana kiran sunan ta, baya baya Anisa ta fara yi tana hawaye, ganin abun ita ma take tamkar a mafarki. Shikuwa Man yana tsugunne sai kuka suke shi da Rufee, kan kace me jama'a sun taru a wajen, nan fa a ka ɗauki Amal a ka wuce da ita Hospital, a in da likita ke tabbatar musu da cizon maciji ne ya kashe ta. Haka a ka ɗauke ta zuwa gida, dan aje a sallace ta a kai ta gidan ta na gaskiya, Aafia tsabar tsorata ta kasa driving na motar ta da kan ta, ta kai kan ta gida, sai dai Anisa ce ta jata zuwa gidan nasu. Ko da ta shigo palo, a zaune ta samu Aunty tana kallo a Tv, taci kwalliyar ta kamar yadda ta sama tana zaune ta aza kafa ɗaya kan ɗaya. Ganin Aafia wata zololo da ita jiki ba kwari ko sallama bata yi ba ta shigo palon, ba karamin ɗagawa Aunty hankali tayi ba, cikin sauri Aunty ta miƙe tsaye tana faɗin "Aafia lafiya meke damun ki" kuka Aafia tasa tare da zama saman sofa, dai dai lokacin Umaisha ta sauko kasa cikin shirin ta zata wuce school, jikin ta na sanye da atamfa ɗinkin doguwar riga A shape ta sanya karamin gyale a kan ta sai kamshi take zubawa. Da yar gudun ta, ta kariso cikin palon ganin Aafia na kuka, ita kan ta Aunty sai da taji jikin ta ya mutu, yau dai Aafia ke kuka to me ya faru da ita, ita kuwa Aafia kuka take tsakanin ta da Allah kamar yarinya karama, dan ta tsorata sosai shi yasa ma ta kasa zuwa gidan su Rufee ɗin, ba zata iya ganin sallar jana'izar Amal ba, hakan yasa ta nemi dawowa gida kawai. Rungumeta Umaisha tayi tana faɗin "Aunty Afi lafiya meke faruwa?" Cikin kuka da kyar Aafia tace "Umaisha Amal ta mutu, Amal ta mutu Umaisha" zaro ido waje Umaisha tayi cike da tsoro tace "Ban gane Amal ta mutuba, ai na ta mutu ɗin? Ko dai mafarki kike ne?" Kara sautin kuka Aafia tayi tana faɗin "Umaisha da gaske nake wlh Amal ta mutu yanzu nan muna zaune da ita kawai tayi ihu ta faɗi kasa, sai gawa, an kai ta asibiti, dr yace saran maciji ne ya kashe ta, kuma su guyson sun duba ko ina a wajen basu ga snake ɗin ba" salati Aunty tasa tana faɗin "Kiyi hakuri ki mata addu'a ne kinji Aafia" cikin kuka Aafia taje dogon tsaki kasan cewar already Rufee ta shiga tsakanin su da Aunty ɗin kome zata musu ba zasu taɓa ganin farin taɓa. Miƙewa Aafia tayi ta haye sama ta ci-gaba da kukan ta, ita ma Umaisha saman ta koma dan ta fasa zuwa school ɗin, dan lokaci guda itama tsoro ya kama ta, sai dai gani take kamar Amal bata mutu ba, tana raye, ita dai Aunty addu'ar nemawa Amal Rahma wajen Ubangiji tayi sannan ta koma ta zauna taci gaba da kallon ta, tana mamakin hali irin na su Aafia. 💞JELLY💞 Ba laifi jikin nata ya samu sauki sosai dan har ta farfaɗo, sai dai kuma me ta mance komai she lost her memory, saboda buguwar kai da ta samu, amma likita yace idan ta haɗu da abun da ya taɓa faruwa da ita a baya ko kuma wani da ta sani zata komawa dai dai, yanzu duk wani abun da wannan Hajiya ta tambaye ta sai tace bata sani ba, sai dai kuma still wannan shagwaɓa da bakin surutun nata yana nan bai mutu ba. Haka dr ya sallame su, suka wuce gidan Hajiyar da Jelly, gida ne babban gida irin na manya manyan atrajirai masu faɗa a ji a kasar, mata huɗu ne a cikin gidan, gaba ɗayan su suna haɗe waje guda, ma'ana ba amusu part part ba, part ɗaya a kayi, mai ɗauke da katafaren palon kasa, to daga palon kasan ne zaka iya wucewa Part ɗin duk wanda kake so, amma duk a cikin palo guda. Kai tsaye ɓangaren ta Hajiyar nan ta nufa da Jelly, sai kallon gidan Jelly ke yi kamar bata taɓa kallon wani abu makamancin hakan ba, suna shiga ta kai ta wani haɗaɗɗiyar bedroom mai bala'i kyau, yaji komai da ake buƙata. Sai da ko da ta kai ta zata fita sai Jelly tace bata san wannan ba, ita dai Hajiya bazata fita ta barta ba, sai dai su zauna tare, sosai Hajiya ta lallaɓata tace taje tayi wanka tazo taci abinci, nan fa Hajiya taga ikon Allah dan kuwa Jelly dai ba abun da ta iya ga bala'i shagwaɓar tsiya ,ga bakin surutu kamar reza. Kuka ta sawa Hajiya kamar yar karamar baby, dama yaya lafiyar kura bare tayi zawo, daman ita Jelly da lafiyar ta ma ya a ka kare da ita bare kuma an samu matsala ta manta komai tayi losing memory ai sai dai abun da hali yayi, sai hakuri kawai. Haka Hajiya ba dan taso ba ta shiga toilet tayiwa Jelly zan kaɗeɗiyar budurwa wanka, ita a tunanin ta saboda matsalar da Jelly ta samu ne yasa ta zama haka, bata san cewa dama already jelly kam haka take ba. Kayan da Nawid ya sai mata lokacin da suke hospital Hajiya ta sanya mata ɗaya daga ciki, sannan ta riƙo hannun ta suka fito palo dan ta zuba mata abinci sai taje itama tayi wanka ta ɗan miƙe. Koda sukazo palo ta zubawa Jelly abinci tace taci, kafin ta dawo bari tayi wanka, kuka Jelly ta sanya mata tana faɗin "A'a ni karki tafi ki barni" Hajiya dai taga abun da yafi karfin ta, tunani ta fara yi karfa Jelly tace da ita zata kwana a ɗaki, in ko haka ne shi kuma Abbon Nawid ta kai shi ina kenan, tab lallai a koi babban matsala. Haka Hajiya ta hakura ta zauna ta fara bawa Jelly abincin a baki, dan Jelly taki yarda taci abincin da hannun ta, wai sai dai a bata a baki, hakako Hajiya ta hakura ta rinƙa bata abaki, jelly na ci tana wasa, dan da alama abincin bashi a kan ta, ba yinwa take ji ba. 💞WASHINGTON DC💞 Zaune Romeo yake kusa da daddy saman bed ɗin dad, hannun sa riƙe da cup da kuma drugs, ya tsare dad da wayan nan dara daran idon nasa, yana jiran dad ya shanye drugs da ya bashi, sai faman kwaɓe fuska dad yake alamar baya son drugs ɗin, daman Romeo yasan halin sa shiyasa yake tasa shi a gaba har sai ya sha a gaban sa sannan yake kyalesa, da kyar da kyar dad ke tura drugs ɗin a bakin sa Romeo na bin masa da ruwa mai sanyi dake cikin kyakkyawan cup ɗin hannun sa. Babu ko excuse Michael ya faɗo cikin bedroom ɗin yana kwaɓe fuska, ko kallon in da yake Romeo bai yiba, kusa da dad yazo ya zauna yana turo Dark brown curly hair sa dad ya shafa yana faɗin "How far My Tiger?" Kara turo baki Michael yayi yana wani turɓune fuska, jawosa jikin sa daddy yayi yana ɗan bubbuga bayan sa alaman rarrashi, kamar wadda akayi wa wani abun, shiko Romeo a jikin sa ya ci-gaba da buɗe wa dad drugs yana bashi, idan dad yasa drug ɗin a baki, sai Romeo ya sanya masa cup na ruwa a ban nasa dan ya haɗiye maganin. Calmly yace "Where is James?" Yayi maganar ba tare da ya ɗago ya kalli Michael ɗin ba, cikin sauri Michael yace "he is in the word room" miƙewa Romeo yayi bayan dad ya kammala shan maganin, ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin hannun sa rike da sauran drugs ɗin yana faɗin "you and James meet me in my room" ya kai karshen maganar tare da ficewa, shiru Michael yayi kamar mai tunanin wani abun, zuba masa ido dad yayi yana kallon sa, ba tare da wani yace da ɗan uwan sa uppan ba. A ɓangaren James kuma. Zaune yake kusa da Musharraf yana kallon sa, wani irin yana yi yake ji duk lokacin da ya kalli kwayar idon Musharraf, ji yake kamar ɗan uwan sa na jini, haka kawai yake jin kaunar Musharraf sosai. Kallon sa Musharraf yayi kasa kasa yace "I want to pray, it's time for prayer" kallon diamond watch ɗin hannun sa James yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Musharraf yace "Okey now what do you want?" "I want to perform ablution" miƙewa James yayi ya ɗauko ruwan roba a fridge, ya dawo ya ɗauko wani kwano na silver mai faɗi irin wadda marasa lafiya ke amfani da shi idan zasu yi alwala ko wani abun, saman gadon ya haye, da yake gadon yana da girma. Hannu yasa ya ɗago Musharraf ya ɗan zaunar da shi tare da sanya masa pillow a bayan sa, abun da ya bawa Musharraf mamaki shine alwalar da James ya masa babu tangarɗa ko wani kuskure, kasa hakuri Musharraf yayi har sai da ya tambayi James, ya akayi yana Kristen ya iya yin alwala dai dai haka, yar murmushi James yayi yana faɗin "I knew it through my friend, i have a Muslim friend, he is of good character, i like him more than your expectations, I understood a lot of Islam perspective from him" sosai Musharraf yayi mamaki tare da ɗaukan kudirin in dai ko hakane suna da masani a kan addinin musulunci kuma sun san wasu daga cikin littafan musulunci to ba zai bargidan ba har sai ya tabbatar ya musuluntar da su, bai gama tunanin da yake ba ya jiyo muryan James yana faɗin "Don't allow uncle, dad, and the rest to know you are a Muslim, because All of these people that your seeing in this house they don't like Muslim, they hate Islam, especially dad, uncle Herry, but lion has a Muslim friend" sosai Musharraf yaji daɗin bayanan James dan ya kara samun makama da zai musuluntar da su, a iya ɗan zaman sa a gidan ya fahimci kowa na gidan yana tsoron lion da suke kira kuma suna shakkan sa, duk da bai taɓa ganin wannan lion ɗin ba, yasan dai yadda suke maganar sannan shine mai power a gidan, da alama shike juya kowa, amma Alhamdulila tun da shima lion ɗin yana da aboki musulmi hakan yazo masa da sauki, dan yana da tabbacin shima lion ɗin ba zai rasa sanin wasu abubuwa dangane da addinin musulunci ba, through wannan abokin nasa. Ganin Musharraf yayi shiru ne yasa James yayi tunanin ko dai yaji tsoron dan nace masa yan gidan nan basa son musulmai ne, karfa ya shiga damuwa gashi kuma bashi da lafiya, tuna haka yasa James yace bari ya masa wata dabara dan karya sa kansa cikin damuwa yazo ya kara ciwo kan ciwo "No uncle don't worry, me a really like Muslim people, I'm thinking about there religion, sometime they are doing something good, I read some Muslim books, most of the things that I saw in the books are true, that's means they are not laying, which is why I believed in the books, I'm thinking about the religion, this is the reason why i hate our pasto, he is lying to us everyday, he is always talking about something that is not coming to pass" jin hakan ma ya sanya Musharraf ya kara jin daɗi, da tunanin James ba zai yi wuyar shiga musulunci ba, saboda shi ya fara gane gaskiya, zai yi saurin amsan kalmar shahada, shi kuwa James sai kokarin tattaro kalaman da zai kwantar wa da Musharraf hankali yake, dan bai son ganin Musharraf ya shiga damuwa saboda rashin lafiya da yake ciki. "I want to see this lion" cewar Musharraf, girgiza kai James yayi kafin yace "give thank to god da a baya baka taɓa kallon lion ba, kuma ka roki Allah yasa kada kayi ido biyu da shi" "why?" Musharraf ya tambaya yana tsare James da ido, jinjina kai James yayi yana faɗin "kawai" "No James ni gaskiya ina son ganin sa" shiru James ya ɗan yi kafin yace "Anywhere yanzu dai i think yana wajen dad, yau ɗaya ga wata lokaci shan drugs na dad yayi, yana can yana bashi magani" cikin sauri Musharraf yace "meke da mun dad ɗin?" "Wine da yake shane before yayi affecting nasa over, yayi spoil na wasu abubuwa daga halittar sa, shiyasa something zakaga yana da saurin rikicewa, yana abu kamar like bashi da sense, kuma zakaga idan abu kaɗan ya faru zai birkice jikin sa ya fara kerma, baka ganin ko magana mukayi sometimes zaka ga jikin sa ya fara kerma kamar mai tsoron mu?" Shiru Musharraf ya ɗan yi kafin yace "to me yasa baku hana shi shan wine ɗin ba?" "We already stop him since before now, kuma yana shan drugs, by the God grace ya kusa samun lafiya ya koma kamar da" addu'a sosai Musharraf ya masa, James yana amsawa da Amin, sannan James ya sauƙo da kwanon ya je toilet ya zubar da ruwan ya dawo ya gyarawa Musharraf zama ta yadda zai ji daɗin yin sallar sa. A wanna yanayin Micheal ya shigo ya same su, ɗaure fuska yayi kafin yace "who is this James?" Yayi maganar yana kallon Musharraf, "is my uncle my friend also" James ya bashi amsa, yayin da Musharraf kuma ya tada kabbara ya fara sallah a rigingine, juyawa Michael yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "Lion want to see us, in his room now" kallon Musharraf James yayi yace "Uncle I'm coming" kasan cewar Musharraf yana sallah sai bai amsa wa James ɗin ba, shima James bai damu Musharraf ya amsa masa ba saboda ya san idan ana sallah ba'a magana, ya san haka a wajen friend nasa. A tare suka jera shi da Michael zuwa part ɗin Romeo. Bakin su ɗauke da excuse suka shiga bedroom ɗin Romeo, yana tsaye ya bawa kofar shigowa baya, ya goya hannun sa a saman kirjin sa, tun da sukaga haka suka gane ba lafiya ba, dan haka jiki ba kwari suka zauna a bakin katafaren bed ɗin Romeo. Shiru Romeo ya musu, suma shiru suka zauna almost 30mins kafin Romeo ya juyo a hankali, fuskar nan tasa kamar hadari, dara daran blue eyes nasan nan, sun sauya launi zuwa ja, lausasan laɓaɓɓan san nan har wani kwalli suke kamar yasa lips balm saboda ya ɗan ciza su kafin ya juyo, ganin shi a haka ba karamin razana su James yayi ba, nan take suka sha jinin jikin su. Rai a matukar ɓace, first time da Romeo ya fara ɗaga murya yayi magana, cikin zafin rai yace "I was thinking you are responsible, but you people are not, your misbehaves has jump from our uncle now to our daddy!! I most give you specifies punishment, daddy didn't deserve that miscresant from you, have you forgotten wen he was up and down for us, it's time to repay him, to provide happiness for him and draw him close to us, met me at my place!!!" yana kai karshen maganar ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, dukkan su sun fahimci kuskuren su na haɗawa da dad da suka yi tun ma Romeo bai fara basu horo ba, tabbas suna son daddyn su, amma basu san me yasa suke ɗaukan dad ɗin kamar su Uncle Herry ba. Ganin Romeo ya fice ne, kuma baya son African time yasa suka miƙe da sauri suka bi bayan sa. Kai tsaye wajen wannan filli na dawakan suka nufa, Romeo yasan babban kuskure ne ya bawa Michael wannan hukunci saboda ciwon sa, to amma bashi da zaɓi dole ya hukun tasu, saboda gobe kada su kara yiwa daddy abun da suka masa, sunyi babban kuskure, kuma sun san dad bai da lafiya amma haka suka rufe ido suka haɗe sa da su Uncle suka masa wannan tsiya, ya zama dole su karɓu hukunci dan gaba. Zama saman ɗaya daga cikin manya manyan kujeru masu numfashi dake wajen Romeo yayi, sannan ya bada Umarni da a fito masa da dawakan sa, dan suyi tsre da Michael da James, abun da basu taɓa kwatantawa ba, yau zasu yi. Haka kuwa akayi, suka fara tsare da wayan nan manya manyan dawakan masu jini a jika da ji da lafiya da karfi. Sai dai abun mamaki, dawakan sun kasa wuce James, shi kam Michael tun ba'ayi nisa ba suka wuce sa, James ne ya sha fama da su har zuwa karshen wajen, kuma suka dawo dawakan basu wuce saba, ko kaɗan Romeo bai yi mamaki ba, ya danganta hakan da cewa dan jinin sane yasa dawakan basu wuce James ba, shi kuma Michael saboda laluran sa yasa suka wuce sa, so bai wani damu ba. Ɗaukan su yayi suka tafi mataki na biyu, shi dai Michael har kuka ya fara yiwa Romeo dan ba zai iya jurewa ba, bashi da lafiya bashi da kwarin jure hakan, amma haka dole ya jure suka shiga mataki na biyu Manya manyan karafuna Romeo ya sanya su ɗagawa masu bala'i nauyi, haka ya sanya jibga jibgan sojojin sa suka ɗaura musu wayan nan mayun karafuna a kan su da kuma hannayen su, sannan Romeo ya sanya su suyi tsayuwar sojoji, idan sukayi kuskuren sakin karfe ɗaya, to fa a kafar su zai faɗa musu, sai ya musu daga daga da kafa, saboda nauyin sa da girman sa, sai ya fashe musu kafa tsab, haka suka hakura suka riƙe karfen nan da iya karfin su na karshe, gashi Romeo yace tsayuwar 1h zasuyi a wajen, tuni Michael ya fara kuka, wi, wai, wi, kamar ƙaramin yaro, har da majina, ya saki ɗan karamin bakin nan nasa yana zubar da yawu ga majina ga hawaye, gwanin ban tausayi, shi kuwa James sai haɗa zufa yake amma bai yi kuka ba, kasan cewar ya samu ire iren wannan horo daga wajen ogannin sa. Romeo ganin kukan Michael na neman ɗaga masa yankali ne yasa ya ɗauko Bluetooth ya sanya a kunnen sa, ya mai da kan sa kan screen ɗin wayar sa, ya daina kallon su, shi kuwa Michael sai kuka yake ya kasa shiru. Gaba ɗaya tausayin Michael ya hana James samun nitsuwa, ji yake kamar ya sanya sojojin dake kewaye da su suna gadin sun nan, su ansa karafunan Michael su kara masa, su bar Michael ya koma ya zauna ya huta, sai dai kuma bai isa yayi hakan ba kasan cewar Romeo ne ke basu horon da kan sa. Masu fi 30mins da fara tsayuwar ba, jikin Michael ya fara kerma, ya kasa tsayawa waje guda, kan kace me ya fara tangal tangal, gashi kuma idan ya faɗi kasa karafunan nan suka danne sa, sai dai wani ba shi ba dan mutuwa zai yi, Romeo kuwa ya sanya Bluetooth a kunnen sa hankalin sa na kan waya, bai san meke faruwa ba, su kuwa sojojin basu isa suyi wani abuba idan ba Romeo ne ya basu izini ba, koda kuwa faɗuwa Michael zai yi ba su isa su tare sa ba sai dai in Romeo ya basu izini. Tafiya gaba ɗaya Michael yayi zai zube kasa, kamar wani walkiya haka Romeo ya miƙe ya tarosa yayin da wayan nan jibga jibgan sojojin suka ansa karafunan hannun sa a sukwane, rungume Micheal Romeo yayi, da kyar da kyar Michael ke mumfashi, nan take jikin sa yayi ya ɗau zafi over kamar wuta, sai kerma jikin sa keyi kamar ba lafiya ba, da hannu Romeo yayiwa sojojin nuni da su karɓi karafunan hannun James karya faɗi shi ma, a sukwane suka karɓawa James ɗin, da Romeo yayi niyar idan suka gama part two zasu wuce part three, dan yana son ya horasu da kyau, sai dai kuma ina hakan ba zai yiwu ba saboda Michael. Cak ya ɗauki Michael saman kafaɗar sa suka wuce cikin gida, da kyar James ke jan kafa yabi bayan su, sai faman haɗa zufa yake yaji wuya sosai. Saman katafaren bed nasa ya kwantar da Michael ya fara duba sa, yana mai jin ba daɗi a ran sa, James kuma bedroom nasa ya wuce dan yaje yayi wanka ya huta. Mu leƙo Nigeria mu dawo 💞NIGERIA💞 A ɓangaren Hajiya da Jelly kuwa, Hajiya dai taga ikon Allah iya ganin idon ta, dan kuwa duk in da taje sai Jelly ta bita, taki yarda ta zauna ita kaɗai, har toilet idan Hajiya ta shiga sai Jelly ta bita, Hajiya na son tayi wanka amma ba hali dan kuwa Jelly dai taki yarda ta zauna ita kaɗai, ko abinci Jelly bata ci da hannun ta sai dai a bata a baki, daga karshe dai Hajiya da taga ba zata iya da Jelly ba sai ta kira ɗan ta Nawid da kuma Mijin ta a waya dan suzo ko zasu san yadda zasu yi da Jelly. Ko da Nawid yazo sai cewa yayi, zai zane ta da bulala, nan fa Jelly tace ba'a haifesa ba ,dan kuwa tsayawa tayi ta riƙe kugu tace wlh in dai ya daketa sai ta rama, har ya zaro belt zai fara zaneta Hajiya ta dakatar da shi ta hanyar ce masa "Haba Nawid bakaga bata da lafiya bane? Dan Allah ka bita a hankali, kasan yadda nake son yarinyar nan kuwa, kasan yadda nake son ya mace kuwa, kai ka ɗai gare ni, ina burin samun ƴa mace Allah bai yi ba sai yanzu Allah ya bani kace kuma zaka takura mata, a'a ni na kira kane kawai dan kazo ka tayani lallaɓata ta zauna nayi wanka" zaro ido Nawid yayi yace "Haba Ummi ni da nake cewa idan ta samu sauki, miƙata wa hukuma za muyi dan su nemo iyayen ta" girgiza kai Hajiya tayi tana faɗin "Tab lallai Nawid, ai wannan yarinyar marainiya ce dan kuwa kaga a kan titi take yawo na bugeta, kuma wlh ko da ma ba marainiya bace dole iyayen ta su bani ita, dan ina son ta ba zan iya rabuwa da ita ba, kana ga yarinya kamar yar india tab, ni ai har na hango auren ka da ita" kasan cewar Nawid ya san halin Ummin sa, da bala'i son ƴaƴa mata hakan yasa yayi shiru kawai ya zuba mata ido tana ta fama lallaɓa Jelly, kamar wata yar Baby har da ce mata "my baby ki zauna ko idan na fito wanka zan goyaki muje muyi wasa" mamaki Nawid yake Jelly ta haukata masa uwa lokacin guda, girgiza kai kawai yayi ya fice daga ɗaki haushi kamar ya shaƙe Jelly. Haka Hajiya ta rinƙa lallaɓa Jelly har Abbon Nawid ya dawo, suka haɗu sai lallaɓa Jelly suke, dan shima Abbo Jelly ta tafi da shi, lokaci guda yaji kaunar yarin yar a ransa, sai dai shi kauna na daban yake mata. Da kyar Jelly ta yarda ta aminci suka zauna tare da Abbo a cikin bedroom ɗin, Hajiya ta wuce toilet da sauri dan taje tayi wanka. Sai kallon Jelly Abbo yake, ya kasa cire idon sa daga kallon ta, ita kuwa sai faman turo baki take, ita kaɗai tana kunkuni, sai wani cool murmushi Abbo ke sakewa yana kallon face ɗin ta, dan turo wannan ɗan bakin nata da take ba karamin tafiya da shi take ba, ji yake kamar ya jawota jikin sa. Haka Hajiya ta fito ta same su, Hajiya na fitowa Jelly ta miƙe ta rungume ta tana faɗin "Ke bakin ga wannan mutumin ba sai kallo na yake yana min dariya" ko kaɗan Hajiya bata damu ba, dan tasan shi ma Abbo yana bala'i kaunar ƴaƴan mata, dan haka sai tace "Sunana Ummi ba ke ba, shi kuma sunan sa Abbo baban ki ne, kin ji ko? Idan ya kalle ki ya miki dariya kema ki masa, zai ji daɗi, dan yanason farincikin yarsa" yar dariya Jelly tayi tace to, sannan ta saki Hajiya ta koma kusa da Abbo ta zauna tana murmushi a ɓangaren shi kuma Abbo, gaban sa sai dukan uku uku yake lokacin da Jelly ke faɗa wa Hajiya yana kallon ta, ya san halin Hajiya da bala'i Kishi zata iya fara ruwan bala'i, sai dai kaunar da take wa ƴaƴa mata yasa bata kawo komai a ranta ba, kuma a tunanin ta Jelly bata da lafiya duk wani abun da zata faɗa kawai shirmene. Tab akoi fa cakwakiya gidan su Nawid, dan da alama shi dai Abbo ya faɗa muje dai zuwa Ɗaukan kayan ta Hajiya tayi ta koma cikin toilet dan shiryawa, saboda su Jelly suna ɗakin, shiryawa tayi tsab cikin wata dankareriyar shadda milk color ɗinkin doguwar riga, tasha aiki daga sama har kasa. Bayan ta gana shiri ne ta fito ta riƙo hannun Jelly suka wuce Palo, miƙewa Abbo yayi ya biyo bayan su. Saman sofa suka zauna Hajiya ta fara ƙoƙarin koyawa Jelly wasu abubuwan, irin su yadda ake gaida mutun da kuma matsayin su a wajen ta, na iyayen, sai kuma yadda zata rinƙa zama da mutane da yadda zata yi wanka da kan ta da sauransu, ba wani abun da Jelly ke ɗauka, Hajiya ke zancen ta kawai, shi dai Abbo da yaga abun nasu bana karewa bane sai ya miƙe ya musu sallama ya wuce office na sa, daman Hajiya ta kira shi ta sashi ya dawo. Sai faman surutu Hajiya take wai tana yiwa Jelly bayani a kan yadda zata zauna a gidan, ko word ɗaya bai shiga kunnen Jelly ba, bare kuma kanta, a wanna hali wata budurwa ta fito daga ɗaya daga cikin part dake cikin palon, kallo ɗaya zaka wa yarinyar kasan yar duniya ce ta bugawa a jarida, dan wasu shegun riga da wando ne a jikin ta sun matseta, duk wani halitta dake jikin ta ya bayyana, ta zuba attachment a kai kamar wata dodanniya, ga wani uban glass da ta maka a ido kamar wata roka da glass, abun ba kyan gani wai an yi kwalliya Kai tsaye hanyar fita daga palon yarinyar ta nufa, ko sannu bata cewa Hajiya ba kamar ma bata san da zaman ta a wajen ba Kwatsam idon ta ya sauka kan, Jelly dake zaune sai faman turo baki take, a hankali matashiyar budurwan ta sauke glass ɗin fuskar ta ta ɗan kalli Jelly from head to toe na yan wasu mintoci kafin nan ta mai da glass ɗin ta fice daga palon, tana tafiya tana juyowa ta kalli Jelly tana wani lashe baki kamar tsohuwar mayya. Ganin yarinyar yasa Hajiya ta kara zawa Jelly kunne a kan babu ruwan ta da yan gidan nan, dan basu da mutunci a cewar Hajiya, sai dai abun da Hajiya bata sani ba shi ne, Jelly fa bata jin ma me take faɗe hankalin ta na kan Tv dake kunne sai faman turo baki take. Kai jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Hajiya baban Nawid, hmmm muje zuwa amma dai akoi show Mu leƙo Rimsha mu dawo 👹DAULAR MUTUWA👹 Sanyin safiya ne ya ratsa ta, kasan cewar lokacin hunturu ya fara shiga, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci, a razane ta miƙe zaune ganin kyakkyawar face ɗin matashin nan wato duna da ya canza halittar sa zuwa kyakkyawa, da sauri ta miƙe zaune tare da taja baya tana zaro ido, murmushi yayi kafin yace "Fine girl kin cika tsoro" yar wawwaigawa tayi kamar mai neman wani abu, a hankali tace "Ayla ina kuke?" Ɗan matsowa kusa da ita yayi yana faɗin "Suna ɗakin baba, ya kamata yanzu ki dai na jin tsorona" ja da baya Rimsha ta fara yi tana ambato sunan Allah a zuciyar ta a fili kuma ta kasa, dan yau ma gaba ɗaya ta tashi cikin wani yanayi, ta mance da komai na rayuwar ta na baya, yau ji take kamar ba ita ba jikin ta duk a sake. A hankali ta miƙe jikin ta sai kerma yake tazo ta raɓa ta gefen sa ta wuce da sauri tayi waje, shi burge sa ma take idan tana irin wannan tsoron nata, son ta kuma karuwa yake a ransa. Tab wannan shi ne soyayya tsakanin mutun da aljani. Miƙewa yayi yabi bayan ta, kai tsaye ɗakin baba ta nufa, sai toshe hanci take, ita da kan ta bata son shakan warin dattin dake jikin ta, saboda yau kwana biyar kenan ba wanka. Nan ta isko su Ayla sai hira da baba suke, kusa da Ayla ta zauna tana faɗin "Ayla wai ku bakwa wanka ne a gidan nan?" Cikin sauri Ayla tace muna wanka amma ga wanda yake so" "ai na ake yin wankan?" Ayla za tayi magana baba ya rigata da cewa "Meesha da yake shima yabi bakin Ayla, gaba ɗaya gidan sai suka mai da mata da suna meesha, "Meesha idan kina magana kina min yanayi da ɗana Nawazudden, sai dai shi farine sosai kuma baku kama, amma dai kina min yanayi da shi sosai, musamman idan kikayi murmushi dimple naki ta lotsa sai naga kamar Nawazudden ɗi na, ko yana ina yanzu oho, rabona da shi tun yana level 1 a Ahmadu Bello university Zaria" shiru Rimsha ta ɗan yi tana jin kamar tasan wanna suna da baba ya kira Nawazudden, a hankali tace "Ayya baba kila shima yana can yana kewar ka" murmushi kawai baba yayi, har sai da dimple nasa irin nata ya lotsa, shiru yayi bai sake magana ba, dawo da dara daran sleeping eyes nata tayi kan Ayla tace "ai na zan yi wankan Ayla? Ko dai a wajen da muke fitsarin nan ne?" duna dake tsaye a bakin kofa ne yace "Muje na nuna miki" make kafaɗa tayi cike da tsoro tace "A'a ni na fasa wankan ma" yar dariya yayi yana faɗin "My wife sarkin tsoro, ba wani abun da zai faru, raka ki kawai zan yi na nuna miki na dawo" zatayi magana baba yace "Tashi kije Meesha" Ba dan taso ba ta miƙe cike da jin haushi ta wuce tayi gaba, duna yabi bayan ta, sai turo ɗan karamin bakin nan nata take, dai dai tsakiyar gidan suka hango su Barbushi daga ɗan nesa sun zo ɗaukan wasu yara wayan da aka samu mai yasan private part na su da idon da kodar su, shine za'a je a yanka su Rimsha zatayi ihu ganin munin su Barbushi ya razanata, da sauri duna ya rufe mata baki, dan su Barbushi ba lura da su ba, kuma sun ɗan wuce su shi yasa basu lura da su ɗin ba, girgiza mata kai duna yayi kasa kasa yace "Kiyi shiru idan ba haka ba zaki bi layi" shiru tayi jikin ta sai kerma yake, dan ita bata taɓa kallon su Barbushi tana cikin hayyacin taba, wancan karon data gansu ba'a hayyacin ta take ba, kuma ga bala'i yinwa da take ji lokacin, shi yasa bata iya ganin su da kyau, bibbiyu take gani a wancan lokaci. Su Barbushi na barin wajen Duna ya kamo hannun ta suka nufi hanyar bayi, cikin sauri ta fisge hannun ta tana faɗin "Bana so karka sake taɓa ni" hakuri ta bata dan ya manta da cewa ba'a taɓa matan Musulmai da ba muharramar kaba shiyasa ya riƙe mata hannu. Kai tsaye wajen toilet ɗin suka wuce yaje ya nuna mata sannan ya tsaya a bakin kofa ta waje wai yana gadin ta, ita kuwa tace wlh ba zatayi wanka ba sai ya bar wajen, shi kuma yace ba zai tafi ba sai yayi gadin matar sa. Da dai taga da gaske yake ba zai tafin ba kuma ai ba ganin ta yake ba, tun da yana ta waje, hakan yasa ta hakura ta kunna fanfo ruwa ya fara zuba, gashi ba wajen tara ruwan sai dai kayi wanka daga fanfon kawai, haka ta cire kayan ta, babu sabulu bare soso ruwa kawai ta rinƙa sheƙawa jikin ta da sunan wanka, Tana gama sheƙa ruwan ta mai da kayan ta da sauri, ta ɗan leko kanta dan taga ko yana kallon ta, sai taga akasin haka, domin kuwa baya ya bawa toilet ɗin yana kallon cikin harabar gidan. Da sauri ta fito ko sannu bata ce masa ba ta nufi hanyar komawa ɗakin baba Kamar daga sama taji muryan sa yana faɗin "Me yasa kuke son zuba ruwa a jikin ku? Dan naga Ayla ma tana yawan zuwa ta zuba ruwa a jikin ta" ba tare da ta kalle saba tace "Saboda tsabtar jiki da kuma kiyaye lafiya" "manene tsabta?" Cewar duna, a nitse ta fara yi masa bayani a kan tsabta "Tsabta yana ɗaya daga cikin manyan abubuwa da addinin mu ya koya mana, ko ibada zakayi sai da tsabta, sai ka tsabtace jikin ka, domin da kyar ta iya kiran sunan Allah, domin Ubangiji mu mai tsabta ne, so aiki ma mai tsabta yake karɓa" "manene Ubangiji" ya faɗa yana kallon ta, kasa magana tayi saboda sun shaƙe mata wuya ji tayi kamar zata mutu, nan take ta riƙe wuyar nata da hannun ta ɗaya ta fara hawaye ganin haka yasa duna ya fahimci meke faruwa, dan haka sai ya riƙo hannun ta guda ɗaya, yana riƙe ta taji kamar anyi ruwa an ɗauke wuyar nata ya sake, da sauri ta kwace hannun ta daga nashi, ta wuce ɗakin baba, zuba mata ido yayi tana tafiya yana kallon ta cike da so, sai mamaki yake a kan kullun idan tazo bashi labari a kan addinin su sai Queen ta shaƙe ta, hakan na nuni da addinin ta addini ne mai kyau kenan, me yasa su Queen basa son wayan da ke da irin addinin su my wife, dole na binciko dalili, sai jerowa kan sa tambayoyi yake a cikin zuciyar sa, yana tsaye ta kasa tafiya. Ita kuwa tana shiga ɗakin baba ta zauna kusa da baba suka ci-gaba da hira kamar yadda suka saba. 💞KATSINA💞 A tare Jehan da Sadiq suka je gidan su Jehan da suka sayar, suka kwanshe musu kayan su dukka suka kai gidan su Sadiq, a ɗakin maman Sadiq suka zuba, Allah sarki maman Sadiq baiwar Allah ita tace su dawo gidan, su rinƙa kwana a ɗakin ta kafin suga me Allah zai yi, nan fa baban Sadiq yace bai san wannan ba sai dai su kama hayar ɗayan ɗakin dake kusa da na maman Sadiq, maman Sadiq tace masa yayi hakuri dan ɗakin can bashi da kyau idan ana ruwa yana zuba, kwanon sa duk ya huhhuje kuma ɗakin kiwon awakin sane a baya, nan fa ya taso zai ci mutumcin maman Sadiq, da kyar Sadiq ya bashi hakuri tare da ce masa sun yarda su Jehan zasu kama ɗakin su biya, nan ya musu kuɗin ɗaki shekara 20k, Sadiq yace zai sanar da su gwaggo zasu biya, Jehan na tsaye aketa wannan dirama kasan cewar bata wani jin hausa yasa bata gane komai da suke faɗe ba. Sadiq da Yusuf suka haɗu suka gyarawa su Jehan ɗakin, ɗan canjin da Sadiq ya samu daga wajen Jehan, dasu yayi amfani ya sawo siminti yar awo sukazo suka kwaɓa suka toshe musu ramukan ɓeraye dake ɗakin, duk wannan dirama da ake ita dai Jehan tana tsaye ne kawai bata san ina a ka dosa ko me ake ciki ba. Sai bayan su Sadiq sun gama gyara komai ne, ya samu ya yiwa Jehan yar gwari gwari yadda zata fahimter, bata nuna wani damuwa ba, taje ta ciro kuɗi daga account nata, kasan cewar ita a account nata akoi sauran 100k sai taje ta ciro 20k a wajen masu POS ta bawa Sadiq dan ya bawa baban sa kuɗin hayan ɗakin, ta bar ragowar 80k ɗin, sai lokacin ta tuna da cewa, Ibrahim fa fake face nata ya gani har ya dage tayi aiki a restaurant ɗin su, tuna hakan yasa ta samu Sadiq ta faɗa masa fake face nata Ibraheem ya gani A nitse Sadiq yace mata "Ki godewa Allah ma da yasa ba asalin fuskar ki suna gani ba, kuma hakan ma yayi dai dai, dan ba wanda zai wani takura miki da zancen soyayya, duk da cewa shima fake face ɗin yana da kyau, amma ki sani asalin face naki yafi wannan kyau nesa ba kusa ba, to garama da basu ga na asalin ba, ko dan ki zauna lafiya kiyi aiki cikin kwanciyar hankali ba tare da takuran samari ba, yanzu ma sai kin shiryawa takurawar maza, dan na faɗa miki shima fake face ɗin yana da kyau. Shiru Jehan tayi ba wani abun da ta gane bayan cewa face ɗin yayi. To masu karatu me kuke tunani zai faru, a gidan su Sadiq da kuma restaurant? sannan ga gidan Hajiya baban Nawid, ga kuma soyayya tsakanin mutun da aljani wato, Rimsha da duna, ga kuma Aafia ta amsa zata haɗu da alhaji, shin ma wani Alhaji ne? Sannan ga kuma man a jefe, shin Musharraf zai yi nasara a kan burin sa na musuluntar da dad da familyn sa kuwa? Yaya Michael zai kare, yaya Umaisha za tayi idan Akil ya dawo? Sannan ga Man na son ta, yaya su Hajiya Umaiya za suyi da dodannin nan? Waye baba? Ku dai muje zuwa yanzu wasan yanzu zai fara sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai amma dai akoi show 💃💃💃🤪 Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 💞TRIPLET'S💞 https://chat.whatsapp.com/BuWeogC8lCiKW1AK808Nde 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 29 💞WASHINGTON DC💞 Da kyar da kyar Michael ke fitar da numfashi, ga jikin nan nasa kamar wuta, sai nishi yake kamar wadda ya tiki uban gudu, cire masa rigan jikin sa Romeo yayi, sannan ya ɗauko A box ya fara duba shi, dan cito rayuwar sa. Kasan cewar already sun san da matsalar sun saba da matsalar, sai Romeo bai sha wata wahala ba wajen sai ta komai Michael ya dawo dai dai, kan kace me Michael ya ɓige da barcin wahala, miƙewa Romeo yayi ya mufi toilet dan yin wanka, mai da A box ɗin yayi first kafin ya wuce toilet ɗin. A ɓangaren James kuwa shima wanka yayi, ya haye saman lafiyayyiyar bed nasa, yana sauke ajiyar zuciya, ba jimawa barci tayi awon gaba da shi. 💞NIGERIA💞 💞GIDAN ABBA💞 Tsaye Hajiya Umaiya take gaban dining table, taci kwalliya sosai kamar ba ita ba, sai kamshi take zubawa kamar anyi ɓarin turare a jikin ta, sai wani taunar chewing gum take kamar yan mata. Da sallama Abba ya shigo palon ya sauko daga samma, ya sha mamakin ganin Hajiya Umaiya tayi kwalliya yau, kuma bata amsa masa sallamar da yayi ba, bai wani damu ba, ya wuce yaje ya zauna saman kujeran table ɗin yana faɗin "Ina Akila?" Bai kai karshen maganar ba ya dakata, sakamakon ganin yau Hajiya Umaiya girki ta musu da kan ta, ba abincin restaurant bane. Daɗi ya sanya shi ya miƙe ya rungume ta yana faɗin "Yau da kan ki kika mana girki, gaskiya naji daɗi sosai, dole naci abinci na koshi" shiru ta masa ba tayi magana ba, kara matse ya yayi a jikin sa yana faɗin "Yau fa da alama Umaiya suna gaban goshi, dan naga anki min magana, ko dai nayi wani laifin ne ban sani ba? To idan nayi laifi a faɗa min na bada hakuri dan yau kin gamamin komai tun da kika mun gir... Bai kai karshen maganar ba yaga wata Hajiya Umaiya ɗin zaune a saman sofa ta zaro masa ido tana kallon sa, a sukwane ya saki Hajiya Umaiya da ya rungume yana kallon face ɗin ta, kwas kwas kwas ya jiyo ta bayan sa, tsoro ya hana shi juyawa, ji yake Kamar ya fasa ihu amma ba hali, gashi tsoro ya kamasa har fitsari yake ji, kamar zata zubo masa a wandon sa. Bai ankaraba kawai sai ganin wata Hajiya Umaiya ɗin yayi tazo ta zauna saman kujerar table ɗin tana faɗin "Abban Akil wani abinci zan zubama?" Still dai tsoro ya hana shi juyawa yaga wacece, gashi kuma muryan Hajiya Umaiya yaji, sannan ga wata Hajiya Umaiya a gaban sa, ga wata saman sofa a zaune. Kan kace me wasu Hajiya Umaiya ɗin su biyar sun bayyana saman kujerun table ɗin, ɗaya na daka a wata yar turmi irin na daka karunfari, ɗaya kuma tana tsosan ƙashi, ɗaya na shan tea, ɗayan kuma tana cin abinci, na karshen kuma ta zuba masa idon dara dara kamar zasu faɗo kasa, idon nata ba kyan gani gwanin ban tsoro. A sukwane ya juya da nufin guduwa zuwa sama, kwatsam idon sa ya sauƙa kan face ɗin Hajiya Zainab matar Alhaji Mustapha, suna zaune saman sofa suna hira da wata Hajiya Umaiya, sai dariya suke suna tafawa, amma ba ka iya jiyo sautin komai, sai dai kaga bakin su na motsawa. A guje Abba ya haye sama, da karfi ya banko kofar ɗakin sa ya shiga, ya mai da ya rufe, a tunanin sa bedroom nasa ya shiga ashe na Hajiya Umaiya ya shiga tsabar ruɗu, yana murza key ya juyo sai ganin asalin Hajiya Umaiya yayi tsaye gaban gado tana latsa wayar ta. Saita nutsuwar sa yayi ya karisa cikin ɗakin, turɓune fuska Hajiya Umaiya tayi tana faɗin "Ina kuma ka fito?" Bata gama rufe baki ba sai ganin wani Abba tayi ya buɗe kofar bedroom ɗin ya shigo, kallon face ɗin Abban asali tayi, ta sake juyawa ta kallin face ɗin wanda ya shigo yanzu, komai nasa iri ɗaya da Abba, kai Abba ne ma, sai dai sun zama biyu baka iya rabewa, tana kokarin yin ihu wani Abban ya buɗe kofar toilet ya fito yana faɗin "Hajiya ki shirya muje restaurant muyi breakfast ko?" ihu tasa ta haye saman gadon ta runtse idon ta tana jiran taji sun kashe ta kawai ihun ta yasa Abba juyawa, aikuwa yana ganin masu kama da shi, ya fasa wani mahaukacin ihu ya watsa a guje, yana baza babban riga ya haye saman gado suka dukunkune shi da Hajiya suna jiran suji me zai faru gaba. Tsawon lokaci suna hakan ba wani abun da ya faru, karjin su sai dukan uku uku yake gaba ɗaya sun rasa ina zasu sanya ransu, Hajiya sai kuka take ta rasa meke mata daɗi a duniyar nan, Allah sarki baiwar Allah duk ta rasa ina zata sanya rayuwar ta, sai numfashi sama sama suke fitarwa, gashi sun dukunkune kan su cikin bargo basa samun iska sai haɗa zufa suke, sun yi shiru suna jiran saukan bulala. A hankali Akila ta turo kofar ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ganin iyayen ta a dukunkune a cikin bargo ne yasa ta juya da wuri zata fita Abba yayi saurin miƙewa dan yaji voice ɗin ta, waige waige ya fara yi a ɗakin babu kowa, shiru duk masu kama da shi ɗin sun tafi, a hankali ya kira sunan ta "Akila" juyowa tayi ta ɗan ricinar da kai tace "Abba ina kwana?" Sai lokacin Hajiya Umaiya ta taso tana faɗin "Akila baki ga kowa ba da kika shigo?" Girgiza kai Akila tayi tana faɗin "Ban gani ba" dirowa kasa daga saman gadon Hajiya Umaiya tayi sauri sauri ta fice daga ɗakin, dan kar abubuwan su dawo, shima Abba da sauri ya diro kasa tare da zuwa ya riƙo hannun Akila suka fice waje, yana tafiya yana waigo ɗakin, dan shi har yanzu bai yarda da wayan nan masu kama da shi ɗin sun tafi ba. A palo suka tsaya Abba yace da Akila ta ɗauko mayafin ta suje restaurant suci abinci, to kawai Akila tace sannan ta koma sama taje ta ɗauko mayafin ta, dan daman yinwa ne yasa taje kiran su Abba. Abba da kan sa yayi driving na motar suka fice daga gidan suka nufi restaurant kamar yadda suka saba. To mu leƙo su Jehan mu dawo 💞KATSINA💞 Yau dai a ɗakin maman Sadiq Jehan ta kwana kasan cewar gwaggo na asibiti da mum, ita kaɗai a ɗaki kuma bai yi ba, shine maman Sadiq tace, tazo su rinƙa kwana har sai an sallamo su mum. Kamar kullun maman Sadiq na tsakar gida tana shara, while Jehan na zaune saman kujera tana son taya maman Sadiq aiki amma bata iya ba, shine kawai ta zauna ta zuba mata ido tana kallon ta, yayin da shi kuma Sadiq yana yiwa maman sa wanke wanke, ita kuma amarya tana tsaye a bakin kofar ɗakin ta tana latsa waya, da alama kira take son yi, mama Hanan kuma tana kitchen tana kokarin hura wutar itacen su mai bala'i hayaki, dan ta musu ɗumamen towon jiya, abun gwanin ban sha'awa yadda suke a tsakar gidan. By mistake kawai maman Sadiq irin ta ɗan sharo dattin da ɗan karfi, dattin ya watsu kaɗan ya haura saman barandar bakin kofar ɗakin amarya har wasu dattin suka taɓa mata kafa, a sukwane Amarya tayo kan maman Sadiq, ba kunya ba tsoron Allah ta ɗaga hannu zata mari maman Sadiq, da sauri Jehan ta miƙe ta riƙe hannun nata tare da wanke ta da wani mahaukacin mari ta tureta gefe, tana mata kallon sama da kasa Kukan kura amarya tayi tayi kan Jehan da nufi duka, Jehan na tsaye ko motsi bata yi ba, amarya na zuwa zata kama ta da faɗa wani marin Jehan ta kara sauƙe mata tare da hankaɗe ta cikin faɗa tace "Wannan bata haifeki bane? Stupid wani dirty girl dake, wlh in dai ina gidan nan sai na gyara miki zama" duk wanna masifa da Jehan take cikin harshen turanci take yin sa Da sauri Sadiq ya kariso wajen yana faɗin "Dan Allah Jehan ku bari ya isa haka" ita ma maman Sadiq abun da take faɗe kenan, dan suna gudun bala'i baban sadiq, ita kuwa maman Hanan daɗi taji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, dan daman kullun addu'ar da take kenan Allah ya kawo mai ci musu uban amarya koda sau ɗaya ne, wata kila zata rage rashin kunya da fitsari da take musu a cikin gidan nan Faɗuwa kasa Amarya tayi tare da dafe cikin ta tasa ihu makircin tana birgima, har sai da baban Sadiq mijin hajiya ya fito daga ɗakin amarya, da sauri yayo gunsu yana faɗin "Wani ɗan tsinanniyar ya taɓa ki" duk da Jehan bata san me ya faɗa ba ta fahimci kamar zagi yayi dan haka sai tace "hy Old man be careful don't angry me" da yake baban Sadiq kai ɗin fanko ne babu komai a cikin ta sai mugun ta da jahilci da bala'i, sai bai san ma me Jehan ta faɗa ba, kawai wajen amarya ya nufa abun sa, yana ta surfa ruwan bala'i. Nan amarya ta kwashi karya da gaskiya ta faɗa masa, har da ce masa Jehan da Sadiq sun ce zasu kashe ta da daddare, dan haka ya kore su daga gidan nan, Allah sarki maman Sadiq baiwar Allah nan take idon ta ya cika da hawaye dan tasan tsab baban Sadiq zai iya korin Sadiq daga gidan, itama dai maman Hanan idon nata da hawaye, dama kuma ita hawayen tun ɗazun yake idon ta saboda hayakin itacen da take kokarin hurawa ya kama yaki, saboda itacen ɗanyune. Shi kan shi Sadiq sai da yaji wani iri dan bai son nisa da maman sa, kuma idan baban sa ya kori su Jehan yanzu ina zasu je, basu da kowa basu da komai. Shi kuwa baban Sadiq sai wani cika yake yana batsewa yana lallaɓa amaryar sa yar gold yana bata hakuri, shegiya Naira, kuɗi sun haukata baban Sadiq Allah ka rabamu da iyaye masu son duniya. Cikin kukan makirci amarya tace "Wlh ba zan zauna a gidan nan da wayan nan yaran ba, dole su bar gidan nan, marina fa wannan mayyar yarinyar tayi, kuma wanna shegen yaron Sadiq har da ce mata, wai ta ƙaramin wani marin dan bani da kunya ya tsaneni kuma sai ya kashe Ni, ni shegiya ce, ba dai irin zagin da basu min ba" Allah sarki Sadiq bawan Allah zaro ido waje yayi, yana mamakin kalaman amarya na sharrin da take musu, ita kuwa Jehan tana tsaye ne kawai ta zuba musu ido amma ba wani abun da take ganewa a maganganun nasu. A fusace baban Sadiq yace "Yanzu kuwa zasu bar gidan nan, yan iskan yara, ai daman ba ƴaƴan albarka bane, wlh ba wanda ya isa ya taɓa ki ya zauna lafiya, ku fice min daga gida, daga ku har iyayen naku ban son ganin kowa" wayyo Allah kuɗi ta rufewa baban Sadiq ido baya ji baya gani sai zancen amarya ne kaɗai ke shiga masa kunne. Nan fa Sadiq da maman sa suka shiga bawa amarya hakuri, ita kam Jehan tana tsaye. Ganin maman Sadiq ta tara hawaye a ido ne yasa Jehan ta fahimci a koi matsala, dan haka sai ta matso tana tambayar maman Sadiq meke faruwa suke kuka. Maman Hanan dake cikin Kitchen ita ce ta fito, kasan cewar ta ɗan yi karatu zuwa Jss 2 sai ta yiwa Jehan bayani cikin kwaɓaɓɓiyar turancin ta Ba laifin duk da turancin na maman Hanan sai a hankali, amma Jehan ta fahimtar, dan haka sai ta ɗago kai ta kalli Sadiq kafin ta mai da kallon ta kan baban Sadiq dake ta surfa uban bala'i, karo na farko a rayuwar ta da taji ba daɗi dan zatayiwa baban Sadiq rashin kunya, amma bata da zaɓi dole ta koya masa hankali dan ta lura bashi da hankali. Duk wani Hausar da ta iya ranar sai da ta tattaro shi dan tayiwa baban Sadiq magana yadda zai gane, cikin fushi ta fara magana "Babu in da Sadiq da maman sa zasu je, idan ma baka son ganin su a gidan ne, tofa sai dai kai ka fice daga gidan, dan sune da gidan yanzu, ke kuma stupid wlh ina nan gidan babu in da zanje sai na baki tarbiya tun da iyayen ki basu baki ba, da kake cewa mu fita maka a gida, haya muka biya ka, kuma munyi da kai sai after 1 year dan haka sai 1 year ta cika zamu bar gidan nan, da bana son gidan ka amma yanzu dan na baku tarbiya kai da wanna stupid ɗin dole zan zauna a nan, islamikali baka isa ka kori Sadiq daga gidan nan ba, maman Sadiq dai kana da damar ka koreta, amma ban da shi, islamikali sai dai kai ka fita ka barmusu gidan ba dai Sadiq ya fita ba, kuma idan kayi wasa wlh sai fushin Allah ya hau kan ka, a kan cewa da kake zaka kori ƴaƴan cikin ka daga gidan ka, mu kuma da muka kama haya, zaka iya kai mu court, a nan ne zakaga asalin yadda ake duniyan ci, amma fita gida bazamu fita ba, ina binka ta lalama ne because of your son, Sadiq is a nice person, if not wlh dana sanya ka kayi regretting abubuwan da kake wa bayin Allah nan, ke kuma stupid daga yau a gidan nan idan kika sake shiga harkan wani ko wata a cikin gidan nan wlh I will make you regret" ta kai karshen maganar tare da jan tsaki, ta juya zata wuce ɗakin maman Sadiq, a fusace Amarya ta jawota har sai da tayi baya zata faɗi, cikin fushi ta juya ta damko wuyar amarya ta shaƙe ta da karfi, rai a matukar ɓace tace "Ke na lura baki san magana ta hankali ba, bari ma miƙi da yaren ku na marasa kunya ta hakan zaki fi gane wa" hannu baban Sadiq ya kai zai mari Jehan ɗin, da sauri Jehan ta kauce tare da sakin wuyar amarya, ta juyo a fusace za tayiwa baban Sadiq tsawa, idon ta ya sauka kan face ɗin Sadiq, dogon tsaki taja kawai tasa kai ta wuce ɗakin maman Sadiq. Amarya anji shaƙa sai zaro ido take ta kankame wuyar ta, bin bayan Jehan Sadiq da maman sa sukayi suka bar baban Sadiq da amarya a wajen, itama maman Hanan wuce wa tayi abun ta ta kyalesu nan wajen. Kuka amarya tasa tana faɗin "Wlh gidan mu zan tafi ba zan zauna da kai ba, kuma karka kuskura naga kafarka a gidan mu, in dai ba ka kori wayan nan yaran ba" baban Sadiq anji kunya yarinya karama ta tsaya tana tsara masa magana har da gargaɗi da sharaɗi, yarinyar da Sadiq ma ya fita a shekaru, amma saboda son abun duniya, jikin sa har kerma yake yace "Yanzu kuwa zan kore su dan Allah kiyi hakuri ki dai na zancen komawa gidan kun nan, idan kika tafi ina zan sanya kai na" ya kai karshen maganar tare da nufan kitchen ya ɗauko itace daga cikin murhun maman Hanan, kai tsaye ya nufi ɗakin maman Sadiq, Jehan na zaune kusa sa yar katifar maman Sadiq shi kuma Sadiq yana zaune ta bakin kofa saman wata yar kujera, ita kuma maman Sadiq tana zaune saman katifar. Kamar wani mahaukaci haka baban Sadiq ya faɗo ɗakin yana faɗin "Kuzo ku fice min daga gida ko yanzun nan na kashe ku ɗaya bayan ɗaya, yan iskan banza marasa albarka, yarinya uban ta ya sai muku gidan da zaku tsugunna saboda rashin albarka ku sata a gaba kuyi ta duka kamar an kawo muku jaka, to wlh baku isa ba, ko kuzo ku wuce ku fita ko kuma in make ku da icen nan. Miƙewa sukayi dukkan su jikin maman Sadiq har kerma yake, Jehan kuwa shiru tayi tana tunanin yadda zata ɓullo wa baban Sadiq, can kome ta tuna, tace "Baban Sadiq we are so sorry zuwa gobe zamu barmaka gidan gaji, kuma kuɗin hayan ma da muka baka mun barmaka kyauta gobe da safe zan kara maka wani kuɗin ma" nan fa baban Sadiq ya fara dariya yaji an basa kuɗin hayan kyauta, kuma za'a kara masa wani, a tunanin sa abun da Jehan ta faɗa masa haka ne, bai san halin Jehan ba ne. Sai washe baki yake ya fito daga ɗakin tare da yin wurgi da itacen hannun sa, ya karisa gaban amarya, yaje ya lallaɓa ta itama ya bata baki, da kyar ta yarda a kan gobe su Jehan zasu bar gidan, ta wuce suka koma bedroom nasu. Kallon Jehan Sadiq yayi yace "Me yasa kika cewa baba haka?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "I'm sorry to say baban ka yana bukatar a gyara masa zama da kyau, kuma dole muyi hakan, yanzu dai ka kira Yusuf da Sha'aban, cikin dare irin 1 na dare kuyi dressing irin na manyan aljanu, ku shiga ɗakin baban naku, sai kuyi kamar ɓarayi ne ku, kada ku bari ya ganku, koda kun boye fuska kada ku yarda ku haska jikin ku da torchlight ya ganku zai iya gane ku idan ya ga jikin ku, ku tabbatar kun zane fuskokin ku ya zama irin na Magicians, sai ku shiga room ɗin, ku shaƙe murya ya zama irin na aljanu, ku masa barazana a kan idan ya sake shiga harkan wani daga cikin gidan nan sai kun dawo kun kashe shi, haka zaku masa zaku samu zaman lafiya da shi, ko bai zauna da ku dan Allah ba, ya zauna da ku dan tsoron aljanu karsu kashe sa" tayi maganar duk a kwaɓe sai haɗe words take, amma ba laifi Sadiq ya fahimci hausar nata. Jinjina kai yayi kafin yace "Anya kuwa hakan zai yiwu? Baba fa wlh bayi da tsoro" "try it, zai yiwu" Jehan ta bashi amsa tana komawa ta zauna, to kawai Sadiq yace mata amma cikin zuciyar sa yana ɗar ɗar yadda abun zai kasance. Kamar yadda Jehan ta basu shawara haka suka yi, ta saman cilip ɗin palon amarya ta baya suka shiga, sunyi dressing kamar wasu bokaye duk sun shafe fuska da toka da gawayi kamar ba lafiya ba, haka suka cire cilip ɗaya suka shige. Kai tsaye wajen baban suka nufa, sai sharan barci yake saman gado amarya mai laushi, ya buɗe bakin nan kamar ka tsula masa fitsari a ciki, sai minshari yake Yusuf ne ya fara taɓa su yana kokarin tashin su daga barci, shi kam Sadiq saboda tausayi ya kasa, kawar da kan sa ma gefe guda yayi yana hawaye, shi kuwa Sha'aban daman bai shigo ɗakin ba ya tsaya a Palo, dan kar baban Sadiq ya gansu, su uku ya fara zargin ko dai sune ba aljanu ba. A firgice baban Sadiq da amarya suka tashi suna salati, dan a tunanin su ma ɓarayi ne, Sabon torchlight da Jehan ta bawa Sadiq kuɗi suka sawo, shi su ka dannawa baban su da amarya hasken a fuska, ga torchlight ɗin da bala'i haske kasan cewar saboda ne. Sadiq ya kasa magana Yusuf ne ya shaƙe murya kamar aljanin gaske ya fara magana "Kai dattijo wajen ka mukazo" nan fa baban Sadiq ya fara salati yana kiran sunan Allah, ita ma amarya sai salati take tana zazzare ido, dan tsoro kamar zata saki fitsari a wando, har wani zufan hawala suke fitarwa, Sadiq ji yake kamar zai yi musu kuka, shi kam Yusuf dama ogane a zafin rai da rashin kunya dan haka ko a jikin sa, ya fara jerowa baban sa kashedi kala kala, sai amsa masa baban sa yake cike da girmamawa jikin su sai kerma yake, daga karshe Yusuf ya rufe da cewa yu aljanun Jehan ne wlh idan basu fita har kan Jehan ba sai sun dawo sun kashe su, daman Jehan ne tace musu suce haka idan sun zo tafiya, ai kuwa dai baba da amarya suka rinƙa basu hakuri, Yusuf yace musu su kwanta su rufe ido kar su kuskura su motsa sai da safe zasu tashi idan ba haka ba zasu shanye musu jini ko kuma su shanye musu kafafu su dai na tafiya, duk wanna zancen da Yusuf keyi Jehan ta bashi kalaman ta daura sa kan hanya. Babu musu Baban Sadiq da amarya suka yi abun da Yusuf yace, gashi Sadiq ya dalle musu fuska da hasken torchlight basa iya ganin komai. Sadiq ne ya tsaya yana haske musu ido har sai da su Yusuf suka haye saman celin suka sauka ta waje, sanan shima ya kashe hasken torchlight ɗin ya salallaɓa a cikin duhu yaje ya haye suka sauka ta baya. Bayan sun sauka ne suka mai da cilin ɗin suka ɗan chogana shi suka wuce ɗakin su kirjin su sai dukan uku uku yake suna addu'ar Allah yasa kar baban su ya gane su ne ba aljanu ba, ita kuwa Jehan ta ɗaura su a kan hanya tana can tana sharara barci ta cikin kwanciyar hankali, dan yanzu ta samu peace of mind tun da za'ayi wa mum aiki, damuwa ya ragun mata sosai ta fara farinciki, amma ba kamar abaya ba. Washegari bayan sun fito, Jehan ta shirya tsab cikin doguwar riga Abaya pink color za su wuce asibiti da Sadiq, daga nan Sadiq ya kai ta taga restaurant ɗin da zatayi aiki dan gobe Monday zata fara aiki a can, amma still fake face ne a fuskarta, dan tun da ta sawo fake face ɗin nan take yawo da shi ko ina bata taɓa cirewa, mutanen anguwa sunyi magana har sun gaji, sai tambayar ina rayinyar nan Jehan take suke yi, ko dai ta koma garin sune sai dai ba mai basu amsa. A tsakar gida za su fita Sadiq da Jehan suka isko amarya, ko sannu basu ce mata zasu wuce amarya tayi saurin cewa "Sannun ku da fitowa" a sukwane Sadiq ya kalli Jehan, kashe ma shi ido ɗaya Jehan tayi suka wuce basu tanka amarya ba, sai da suka fita wajen Jehan tace "Karamar mara kunya, da Jehan yar sanda mai zaman kanta kike, wlh tsab zan gyara miki zama a gidan nan" cike da mamaki Sadiq yace "Jehan dan Allah shekarun ki nawa" "I'm close to 16 years" ta bashi amsa, mai mai ta wa yayi a ransa yarinya 16 years da wanna irin kwakwalwa da confidence haka abun da mamaki wlh, duk wani makirci da iya shege Jehan ta san shi, sai dai alhadulillah tana da ilimin addini kuma duk abun da zata yi bata saɓa dokan Allah, tana kokarin kiyaye wa. Kai tsaye Hospital suka wuce, mum dai tana nan jiya iyau kullun sai dai a sanya mata ruwa, amma bata fargaɗo ba. Zaune suka isko gwaggo saman kujerar da mai jinya ke zama, gaishe da gwaggo Sadiq yayi tare da tambayar ya jikin mum, "jiki da sauki" gwaggo ta bashi amsa, wucewa yayi ya nufi waje yana wa mum addu'ar Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗun ta, a tare gwaggo da Jehan suka amsa da ameen, Jehan ta dubi gwaggo tace "My gwaggo what do you want to eat?" Shiru gwaggo ta ɗan yi kafin tace "duk abun da ya samu" sallama Jehan ta musu sanna ta fito ta samu Sadiq a waje tace suje restaurant ɗin da zata fara aikin sai ta saiwa gwaggo abinci a can, ba musu Sadiq ya miƙe suka tafi zuwa wajen asibitin bakin hanya su samu abun hawa. Taxi suka tara suka shiga, suka tafi restaurant ɗin, Tun daga bakin bakin gate ɗin tampatsetsen restaurant ɗin Jehan ta fara, yiwa wajen kallon sama da kasa, Sadiq ya lura da hakan sai yace "Jehan lafiya kike kallon wajen haka" guntu tsaki taja kafin tace "Dirty place" tayi maganar dai dai lokacin da suka karasa cikin restaurant ɗin, nan fa Jehan ta fara yiwa ma'aikatan dake wajen kallon raini kallon yan datti, da fara'a Ibraheem ya tarbe su yana washe baki, kara ɗaure fuska sosai Jehan tayi wai dan kar su raina ta, shi dai Sadiq idan da sabo ya saba da halin Jehan ɗin sa. Jagora Ibraheem ya musu zuwa ya nunnuna musu abubuwan da ya dace Jehan ta sani, duk in da ta wuce sai ma'aikatan wajen sun mata sannu da zuwa, amma babu wanda tayiwa kallon mutunci ma bare ta amsa masa gaisuwar sa. Abun da ya bata mamaki shi ne wasu ɗakuna da Ibraheem ya nufa da su, ashe restaurant ɗin haɗe yake da hotel ta ciki ita bata sani ba, tab lallai a koi cakwakiya. Bata damu ba suka shiga ko ina Ibraheem ya nuna musu sannan suka dawo wajen reception, Jehan ta saiwa gwaggo shinkafa da miya steew aka mata takeaway. Zasu tafi Ibraheem ya kawo mata rigar da wando nasu na aiki, kallon kayan tayi a wulakance, riga blue da wando baki, a takaice tace "For what?" Sai faman murmushi Ibraheem yake yace "uniform work, shi zaki rinƙa sawa idan zaki zo aiki" ɗaure fuska tayi sosai tace "Kayan da zan sa nazo ma kune zaku zaɓa min?" Ba tare da nuna damuwa ba Ibraheem yace "A'a Hajiya Jehan haka tsarin yake, abun da oga yace shi a keyi a nan" tirkashi kallon sama da kasa tayiwa Ibraheem kafin tace "Au sayata kukayi gaba ɗaya kenan?" Shiru Ibraheem yayi dan bashi da amsan tambayar nan nata ganin Jehan zata jiƙa musu aiki yasa Sadiq ya ansa kayan daga hannun Ibraheem yana faɗin "Ba komai malam Ibraheem, karka damu zata sanya, sai goben idan tazo" ya kai karshen maganar tare da juyowa ya kalli Jehan yace "Jehan muje ko, zanje gareji kin ga kuma rana nayi" ba musu ta wuce gaba yabi bayan ta, Ibraheem dai zuba musu ido yayi yana kallon Jehan kamar ya make ta yaji dan haushi, yar karama da ita sai iya shege. A wanna karon abun hawa daban daban suka hau, dan Sadiq zai wuce gareji ita kuma hospital, ba yadda Sadiq bai yi da Jehan ba a kan ta amsa kayan uniform nata amma taki, ta kafe tace sam ita ba zata ansa ba, dan babu wanda ya isa ya zaɓa mata kayan da zata sanya in zata fita, haka Sadiq ya wuce da kayan garejin su ita kuma ta wuce hospital, daman haka suke kullun, idan Sadiq yazo ya gai da su gwaggo sai ya wuce gareji sai yamma idan zai koma gida sai yazo ya ɗauke ta su koma tare. Tirgashi akoi fa cakwakiya Jehan dai tace bazata sanya uniform ba, wanna shine wasa farin girki, mu leƙo Washington DC mu dawo. 💞WASHINGTON DC💞 12:30Am kamar kullum duniya dukka sun yi barci, shi kuwa yana zaune saman table chair na dining table na kasa yana latsa system, jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya fito da ita a ledar ta, gata da laushi tilis kamar audiga, kasan cewar gaban rigar a buɗe hakan ya bayyanar da kyakkyawar lallausan dark black gashin mai tsantsi kwance a saman faffaɗar kirjin, gwanin ban sha'awa dan sai kwalli gashin yake kamar ya shafa mata baby oil, gashin hannayen sa da na kafafun sannan duk suna kwance lup a jikin sa, kasan cewar gashin dark black ne shi kuma fatar sa farane kal hakan yasa gashin bayyana sosai, ya tara dark black curly hair sa ya ɗaure a baya, ya bar wannan na gaban goshin nasa ta karawa face nasa kyau over, yau ma kamar kullun sky blue light ne kunne a palon, hasken wutar ba karamin kyau tayi ba a kan face nasa, ya zubawa system nasa dake saman table wanyan nan dara daran blue eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali, kasan cewar ya sauke idon nasa kasa kaɗan yana kallon system ɗin, hakan yasa, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana dan idon nasa yayi kamar a rufe, yayi shiru yana ɗan cizan red lips nasa nan, kamar mai tunanin wani abu, ya kafe system da ido, ga jibga jibgan bodyguard na su a tsai tsaiye suna jiran yace abinci su bashi tissue ya goge bakin sa, already kamar kullun sun zuba masa duk wani abun da zai buƙata. A hankali James ya fito daga bedroom nasa sai hamma yake alamar barci, wuce wa yayi ya nufi word room wajen Musharraf zai je yayi masa alwala, dan Musharraf yana sallar dare kullun, shi yasa ya roki James dan Allah karfe 1 dai dai ya rinka zuwa yana tashin sa dan ya samu yayi nafila, kasan cewar James Allah ya ɗaura masa kaunar Musharraf yasa baya wani damuwa kuma ya sanya abun a ransa, tun 12:30 yake zuwa wajen Musharraf su zauna suyi ta hira, sai 1 dai dai yake wa Musharraf alwala, kuma ya zauna yayi ta kallon sa har sai yayi nafila raka'a 8 sannan ya rufe da shafa'i da witiri, sai bayan ya gama dukka, James ke kwantar da shi ya wuce nasa bedroom yaje ya kwanta, kuma haka da asuba zai dawo yayiwa Musharraf alwalan sallar asuba, duk sojojin da bodyguard ɗin dake gidan basu iya yadda ake alwala ba shi yasa yake zuwa da kan sa yayiwa Musharraf ɗin, kuma yana laakari da shiya buge Musharraf ɗin da mota, dan haka alhakin kula da shi ya rataye ne a wuyar sa. Zai wuce wajen Musharraf ya hango blue light na palo kasa a kunne, ko ba'a faɗa masa ba, yasan Romeo ne, dan shi kaɗai ne mai cin abinci da tsakar dare kamar wani aljani, wani lokaci kuma ba abinci yake ci ba haka kawai zai fito palon kasa ya zauna yana latsa system ko kuma wayar sa, da wuya ka gansa a palon kasa idan ba tsakar dare ba. Fasa nufa wajen Musharraf yayi, ya sauƙo kasa wajen Romeo, saman chair ɗin kusa da Romeo ya zauna yana faɗin "well done lion" kamar dai kullun shiru Romeo ya masa kamar bai san da zaman sa a wajen ba, ɗaukan fruit yayi ya fara ci, a hankali ya matso da kan sa yana kallon cikin screen ɗin system da Romeo ke aiki a ciki, zaro ash eyes nasa waje yayi, har sai da fruits da yake ci suka kwaresa, nan take ya fara tari da karfi karfi, bodyguard ɗin dake tsai tsaye har suna rige rigen miƙa masa glass cup mai ɗauke da ruwa mai sanyi, da sauri ya ansa ya kafa a bakin sa yasha Shi kuwa Romeo kamar bai san James na tari ba, aikin sa kawai yake, yana cizan lausasan laɓaɓɓan sa, sai bayan tarin James ya tsaya ne, ya ajiye fruit na hannun sa, ya miƙe zai bar wajen, gently in a cool Romeo yace "Come here" ba musu ya koma ya zauna, yana faɗin "here I am"....✍️✍️ Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 30-31 💞WASHINGTON DC💞 Shi kuwa Romeo kamar bai san James na tari ba, aikin sa kawai yake, yana cizan laullausan laɓaɓɓan sa sai bayan tarin nasa ya tsaya ne, ya ajiye fruit ɗin hannun sa, ya miƙe zai bar wajen, gently in a cool Romeo yace "Come here" ba musu ya je ya zauna, yana faɗin "here I am" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me James ɗin yace ba, shima James shiru ya zauna yana tunanin me yasa Romeo ya kiransa. After 45mims A hankali Romeo ya ɗan ture system ɗin gefe, yana ture system ɗin bodyguard sukayi sauri matso masa da plates ɗin abinci gaban sa, tsalleke abincin yayi ya ɗauko fruits ya fara ci a nutse kamar bai son tauna, hannu James yasa suka fara ci a tare, sai satar kallon Romeo yake dan ya fahimci ko akoi wani sauyi a face ɗin Romeo. "Why are you looking at me like this?" Kamar saukar aradu haka James yaji wanna tambaya ta Romeo, ko taya akayi Romeo yasan yana kallon shi oho, sai ta nitsuwar sa yayi yace "Because your my blood, I like to watch my blood face like film" shiru Romeo ya masa bai sake magana ba. Yau dai fruits kawai Romeo ya ci, gently ya miƙe ya nufi hanyar haurawa sama, binshi da ido James yayi yana mamakin, to akan me Romeo zai kirasa kuma bai yi masa wata magana ba, a ransa yace "Lion murɗaɗen mutun baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ina ya dosa kwata kwata, Allah ya kawo masa sauki, yanzu kawai ya wani kirani kuma ya tashi ya barni zaune, ni ya ɗaga min hankali ma" ta kai karshen zancen zucin na sa tare da miƙa wa ya wuce word room. Ido biyu ya isko Musharraf, bawan Allah ya jima da tashi babu mai masa alwala shiyasa ya kwanta shiru kamar wani maraya, hakuri James ya bashi sanna ya ɗauko ruwa da niyar yi masa alwala. "No James just leave it, yau bana jin daɗin jikina, sai zuwa gobe zan yi sallar daren" kamar James zai yi magana sai kuma ya fasa, ya ajiye ruwar ya dawo gefen Musharraf ɗin ya zauna yana faɗin "Okey let's chatting" murmushi Musharraf yayi, zai yi magana wayar James ta fara kara, cikin sauri ya fito da wayar daga aljihun wandon barcin jikin sa. Josephine shine sunan da ya bayyana a saman screen ɗin, guntun tsaki yaja kafin yace "Not know" yana kai karshen maganar ya katse kiran tare da sanya number a blacklist ya mai da wayar aljihun sa Cike da karanbani Musharraf yace "who called at this time 1:20am?" (Waye ya kira ka a wanna lokacin) Ɗaure fuska James yayi kafin yace Josephine, "Who is Josephine?" Musharraf ya sake tambaya, a kule James yace "Our mum" ya bashi amsa a takaice, zaro ido waje Musharraf yayi kafin yace "gaskiya ina son sanin me mum ɗin nan taku ta muku, da har kuka mata wanna tsana haka" shiru James ya ɗanyi kamar mai tunani, kasan cewar su turawa ba ruwan su, kusan yaruwar su rabi dukka a faranti suke basu san kunya ba, bare rufawa wani asiri, sai James ya fara bawa Musharraf labarin abun da ya haɗa su da mum nasu, abubuwan da ta musu a baya in short dai ya bashi labarin "daddy tell us, lokacin da muke jaririrai, mum ɗin mu ta haɗu da wata friend ɗin ta yar kasar India kuma musulma ce, sun zama friend sosai, shi ne wan can ɗin tace wa mum ta kai mu wajen magicians, ta bada jinin mu su mata kuɗi da shi, lokacin dad bai da kuɗi, mum kuma sai ta biyewa wan can musulman ta kai mu wajen Magicians, thank God, muna da sauran kwana dad yaje ya karɓo mu ba'a riga an yanka mu ba, shine fa mum tace ba zatayi feeding namu breast nata ba, kuma ba zata zauna da dad ba dan bai da kuɗi, ta tafi ta bar daddy, haka ya rinƙa shan wahalar renon mu har muka girma, that is why bamu son ta, shiyasa su dad basa son Musulmai wai Musulmai mugaye ne, sannan yana ɗaya daga cikin abun da yasa bama son girl a area da muke, dan mata duk haka suke basu da gaskiya, shi yasa nace kada ka faɗa wa su daddy you are a Muslim, ba zasu yarda ka zauna a nan ba" girgiza kai Musharraf yayi kafin yace "Amma kana ganin gaskiya dad ya faɗa muku a kan mum ta kai ku wajen Magicians?" Da sauri James ya gyaɗa kai yana faɗin "Yes ita da bakin ta ma ta faɗa, she accepted her mistake, before now har kasa ta duƙa ta bawa dad da lion hakuri tana kuka, dad da lion sun ce ba zasu yafe mata ba because haka mata suke in sun yi abu zasu ce Sorry later kuma zasu sake repeating na the same wannan mistake ɗin, kuma this is the reason why kawai ba su yafe mata ba, dan ko sun yafe mata zata sake wani mistake ɗin, kuma ai kaga muna da gaskiya, tun muna yara bata son mu sai yanzu da muka girma, she saw we have plenty money now, shine kuma zata dawo tace tana som mu no we can't except her" jinjina kai Musharraf yayi yana faɗin "Eh haka ne kuna da gaskiya, kuma kunyi dai dai, amma in dai ita da kan ta ta yarda da kuskuren ta kuma ta baku hakuri, to please ku yafe mata mana" miƙewa James yayi yace "Good light uncle, and please don't talk about mum to me again" zuba masa ido Musharraf yayi a ransa yana faɗin "Tabbas sheɗan ya ruɗi Mahaifiyar ku tayi kuskure to amma bata cancanci hukuci mai tsauri haka ba, tun da har ta baku hakuri, kamata yayi ku hakura, domin uwa da ƴaƴan ta sai Allah, yanzu Allah ne kaɗai yasan irin raɗaɗin da take ji a zuciyar ta na rashin amincewa da ita da kuka yi, amma ina da tabbacin In Sha Allah kuka musulta, imani ya ratsa ku, kuka san darajan iyaye da amfanin su, da izinin Allah zaku nemeta da kan ku" shi kuwa James tuni ya wuce bedroom nasa ya bar Musharraf da zancen zuci, gyara kwanciya shima Musharraf yayi tare da tuntse idon sa yana son yin bacci. James dai ko da ya kwanta sai yaji ya shiga damuwa kala biyu, bacci yaki zuwa masa, abu na farko, yana jin like bai kyautatawa Musharraf ba, na biyu kuma damuwa a kan gobe zasu yi taron su na yan ta'adda, kuma tabbas yaga Romeo ya shirya yadda za'a farmaki taron a system na sa, amma ba yadda zai yi dole yaje taron nan in ma ya mutu ko yayi rai, abun da ya fi sawa ran sa shi ne mutuwa zai yi, dan mawuyacin abu ne yaran Romeo su farmaki waje kuma basu yi nasara a kan aikin ba da kamar wuya, yasan tsab sai sun kashe kowa da kowa, a ransa yake jin shike nan zai rabu da yan uwan sa kenan. Ya kasa bacci sai tunani yake, kamar yadda yaga rana haka yaga dare, sai kusan karfe 6 na safe sannan ya samu bacci wahala ta ɗauke sa. A fannin shima Romeo bai yi baccin ba, ya kwanta yana ta tunanin yadda aikin zai kasan ce, sai yiwa yaran sa fatan nasara yake, duk da yana da kwarin gwiwa a kan su, Yasan sun samu horo, bai taɓa turasu aiki basu yi nasara ba, sai dai babban damuwar sa ɗaya ba tare da Tga zasu tafi ba, kasan cewar Tga na kwance a gadon masu jinya, daddy na dubasa, wajen da kwarin nan suka harbesa ya kumbura sosai, abun dai sai addu'a dan kuwa ko wando baya iya sawa, yana kwance yana baje yana shan iska, gashi yaki tsayawa a wani duba shi ma saboda raɗaɗin azaba, duk wannan Romeo bai sani ba, bai san cewa Tga yaki tsayawa a bashi kulawar da ya dace ba, da tuni yaje da kan sa ya danne sa ya bashi kulawa da kan sa, sai dai bai sani ba, kuma duk suna tsoron faɗa masa shi yasa, shi kuma bai cika shiga harkan yan gidan ba kullun yana ɗaki, in dai ba kai ka nemo sa ba, to shi baya neman kowa, ɗan gara Triplets na sa da kuma daddy, idan ya wuni bai ji motsin su ba yana kiran su a waya yaji lafiya. Haka dai shi ma ya kwana ido biyu ba bacci, yana ta tunanin yadda tafiyan yaran nasa zai kasan ce ba Tga ,wannan ne dalilin da yasa jiya da daddare ya kira James dan ya duba masa jikin Tga ɗin sai kuma ya mance da me yasa ma ya kira James ɗin, shiyasa ya miƙe ya bar james zaune a wajen. Asuba ta gari Wannan kenan bari mu leƙo su Jelly mu dawo muga cakwakiyar familyn William jacop. 💞NIGERIA💞 JELLY Yanzu ta ɗan fara sakewa da gidan tana iya zama ita kaɗai, inma a bedroom ko a palo, sai dai fa har yanzu bata wanka da kan ta kuma bata cin abinci da kan ta, sai dai Hajiya ta mata wanna dukka. Yauma kamar kullun tana zaune a palo ita kaɗai tayi shiru tana kallon Tv ana labarai, duk da ba gane abun da ake faɗe take ba, ta zuba musu ido kamar ta san me ake cewa, yayin da news ɗin ke magana a kan ɓatar ta, dan daddyn ta ya shiga damuwa over, shiyasa har gidan Tv a ka kai zancen, ana cab da sanya hoton daddyn ta, wannan tantiriyar budurwan ta shigo palon babu ko sallama, hakan yasa hankalin Jelly ya kau daga kan Tv ta koma kallon yarinyar, while a Tv kuma an sako hoton ta dana daddyn ta zubawa attachment ɗin kan yarinyar ido Jelly tayi tana mamaki, ganin babu kowa a palon yasa yarinyar tace da Jelly "Ke zonan" turo baki Jelly tayin kafin ta make kafaɗa tace "A'a ni ba zam zo ba" shiru yarinyar ta ɗan yi tana tunanin yadda zata yi da Jelly ta fara bin ta ɗaki, can wata dabara ta faɗo mata, hannu tasa cikin Jakarta ta fito da chewing gum da take yawan ci, ta miƙawa Jelly, ba musu Jelly ta miƙe ta karisa wajen ta, ta sanya hannu ta karɓa chewing gum ɗin tana dariya, dariya irin na yan duniya yarinyar tayi kafin tace "Yauwa ki saki jikin ki dani ko? Ni auntyn kice, daga yau in nace kiyi abu, ki rinƙa yi zan saya miki sweet kala kala kinyi?" Tayi maganar tana shafa kan Jelly zuwa wuyar ta, Gyaɗa mata kai kawai Jelly tayi tana faman tura chewing gum a baki, murmushi shakiyanci yarikyar tayi kafin ta ɗan duƙo da kan ta, dai dai saitin goshin Jelly kasan cewar ta fi Jelly tsawo, ta mannawa Jelly kiss a goshi tana shafa wuyar ta, ta wuce part nasu, wucewa itama Jelly tayi ta koma cikin bedroom na Hajiya. Hajiya na kwance Jelly ta faɗo mata ɗakin babu ko sallama, Hajiya bata damu ba dan ta ɗauki hakan a matsayin dan Jelly bata da lafiya ne, bata san Jellyn daddy ba already haka take daman. Hayewa saman gadon Hajiya tayi ta fara gaya mata yadda suka yi da wancan yarinyar, zubur Hajiya ta miƙe zaune tana kallon ta dan tasan halin afnan sarai, ta santa yar lesbian ce dan kuwa har ita kan ta Hajiya sai da afnan tayi mata tayin lesbian a baya, Hajiya batayi kasa a gwiwa ba taci mata mutunci fes shi ne yasa yanzu Afnan bata mata magana a gidan. Miƙewa tsaye Hajiya tayi, ta diro kasa daga saman gadon rai a matukar ɓace ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin su Afnan, da sauri Jelly ta sauko kasa ita ma tabi bayan Hajiya. A palon part na su Afnan Hajiya ta tsaya, ta fara kwalawa Afnan kira, da sauri mahaifiyar Afnan da yaya ta da ita kan ta Afnan ɗin suka fito suna tambayar ko lafiya Hajiya ta shigo tana ihu hakan, rai a matukar ɓace Hajiya tace "Ke Afnan wlh summa wlh ki fita harkan baby, babu ruwan ki da ita, na rantse miki da Allah idan kikayi gigin taɓa hannun yarinyar nan zan nuna miki yadda ake bariki, karkiga kina yin duk abun da kikaga dama a gidan nan muna zuba kiki ido, wlh ba wai kinfi karfi na bane, dan dai kawai bani da lokacin kine, amma a kan baby ina da lokacin ki daga nan har illah masha Allah, ke in takaice miki zance wlh zan iya komai a kan baby" kallon sama da kasa Afnan tayiwa Hajiya zatayi magana mahaifiyar ta ta rigata da cewa "Ke Hajiya Turai bafa tsoron ki muke ji ba zaki zo ki wani tayar mana da hankali a kan wancan shegiya tsintaciyar magen, daman ina cike dake a kan yarinyar, dan Alhaji yazo jiya yana wani ce mana kin kawo yarinya dan Allah kar yan gidan nan su takura mata, to yarinyar yar kanwar uwar ki ce? Ko ma yar kanwar uwar ki ce idan bata mana ba sai munci uban ta a gidan nan bare kuma naji Alhaji yace wai tsintar ta kikayi, to wlh tsintaciyar mage bata isa ta zo tace zata takurawa yan gida ta hana su jin daɗi ba kinji na faɗa miƙi, Afnan kuma koma me tayiwa yarinyar dedene, Afnan ki ci uban ta dan ba gidan uban ta bane, na uban kine" ita maman Afnan a tunanin ta rigima ake dan Afnan ta daki Jelly bata san kan magana ba Aliyu yayan Afnan ne yace "Ummi kiyi hakuri kije, dan Allah komai ta wuce haka kinji?" Ita kuwa Hajiya jin abun da maman Afnan tace yasa tayi tunanin kenan da sanin maman Afnan, Afnan ke yin lesbian? Ta tambayi kan ta tambayar da babu amsa, amma a zahirin gaskiya maman Afnan bata san Afnan na wanna aika aikan ba, shikan shi yayan nata bai sani ba, su suna tunanin duk wannan masifar da Hajiya keyi tanayi ne dan Afnan ta daki Jelly, basu san dawar garin ba, shi yasa maman Afnan ta zage dantse dan tarewa yarta faɗa, shi kuma yaya Afnan kasan cewar baya son hayani sai yayi ta basu hakuri. Da kyar ya samu Hajiya ta hakura ta wuce ta koma part nata, tana shiga palon ta ta samu Jelly zaune tana kallon Tv, da Jelly ta fito ne zata bi Hajiya, sai taga ana nuna cartoon a Tv sai ta zauna kallo. Hannun ta Hajiya ta ja suka bar palon zuwa nasu part ɗin. A palon part nasu Hajiya ta zauna ta zaunar da Jelly gefen ta, cikin nitsuwa tace "Baby daga yau karki sake fita babban palo bana so, kiyi zaman ki a nan, ga Tv nan zan rinƙa kunna miki, kuma idan wani ya sake cewa ki zo a gidan nan karki yarda ki je, ba ruwan ki da kowa karki sake yiwa kowa magana daga ni sai Abbo sai yaya Nawid, mu kaɗai zaki rinƙa yiwa magana, kuma mu kaɗai ne idan munce kiyi abu zaki yi kin ji ko?" Kai Jelly ta gyaɗawa Hajiya alamar taji. Cab lalai Hajiya kin kashe maciji baki sare kai ba, dake da Abbo da Nawid ne kawai zaku mata magana tayi abun hmmm, muje zuwa. Wunin ranar dai Jelly bata sake leƙa babban palon ba tun safe da abun ya faru, a nan tayi zaman ta har dare, idan ta gaji da zama ta kwanta, idan ta gaji da kwanciya ta shiga bedroom ɗin Hajiya su ɗan yi hira, Hajiya na koya mata karatu, amma fa ba abun da take gane wa. Da daddare suna cin abinci ne Nawid ke sanar da Ummi zai yi tafiya zuwa Katsina next week, kasan cewar Hajiya Turai ya ce ga sarkin matsina, Nawid jikane ka sarkin, hakan yasa yake yawan kaiwa kakan nin sa ziyara Da fara'a Hajiya ta amsa masa da to dan tana son daman zumuncin ta da yan uwan ta maza da ƴaƴan su ya kara karfi sosai yafi haka, Yanzu Nawid na daina hantarar Jelly dan ya fahimci haka take, kuma abun ya haɗu mata da ciwo, shi yasa baya damuwa idan tana wani shagwaɓar nata, yanzu in tace masa yaya yana amsawa har ya biye mata, dan Hajiya ta masa kanwar dole, kuma haka ya karɓa ba yadda zai yi, wani lokaci ma idan Jelly ta tayar da ballin ba zata ci abinci da hannun ta ba, shi yake bata a baki da kan sa, ko Abbo. Bayan sun kammala cin abin ne kowa ya miƙe ya nufi bedroom nasa, ita kuma Hajiya ta riƙo hannun Jelly suka tafi bedroom nata, dan sun saba sai Jelly tayi barci Ummi ke mai data bedroom nata, dan bata yarda tayi barci ita ka ɗai, wani lokaci kuma a bedroom ɗin nata suke zuwa su kwanta har sai tayi barci, sai su salallaɓa su fice su koma nasu bedroom ɗin. Yau Hajiya ta gaji sosai, suna kwanciya ba jimawa barci ya ɗauke ta, saura Abbo da Jelly, daman Jelly na ta gefen Hajiya, ma'ana Hajiya ce a tsakiyar su. Miƙewa Abbo yayi, yayi kwanciyar rigingine yana fiskantar Jelly, ya zuba mata ido yana ta kallon ta daga sama har kasa, yana son taɓa ta yana kuma tsoron kada ta masa ihu ko ta tashi Hajiya daga bacci, dan yasan halin Jelly sarai ba'a mata abu tayi shiru, kana mata abu da ɗumi ɗumin sa zata faɗa wa Hajiya ba ɓata lokaci, tunani ya fara yi ya zai yi, dan shi gaskiya yana matikar son Jelly, sai kallon ta yake ita kuma tana kwance ta rintse ido amma ba tayi barci ba, dan ga idon nata nan sai motsi suke, wutar ɗakin a kunne yake dan Jelly bata zama a ɗaki sai da wuta a kunne, tana tsoron duhu, wani lokaci sai tayi barci hajiya ke zuwa ta kashe mata wutar, amma fa idan ta tashi cikin dare, to akoi dirama dan ihu take kamar zatai hauka, da kyar ake lallaɓa ta ta mai da barci, ta hanyar kunna mata wutar ɗakin. Ahankali ya kai hannun sa zai taɓa ta, sai kerma hannun nasa keyi kamar mazari, ya kasa taɓa ta, yana son taɓa kuma yana tsoron tsiwarta, sai dai abun da bai sani ba, yanzu Hajiya tace duk abun da Abbo da Nawid suka ce mata tayi to tayi shi, kuma ita Jelly duk abun da Hajiya tace tana yin sa ba ɓata lokaci, sannan in dai Hajiya tace tayiwa wani biyayya tofa kome zai mata ba lallai ta faɗa wa Hajiya ba, tun da Hajiyar ce tace tayi. Haka Abbo yayi ta kokarin taɓa Jelly yana tsoro, har barci ya ɗauke Jelly, haka ya zauna ya zuba mata ido yana ta kallon ta, yana kara jin haunar ta a ransa. Sai wajen 1 na dare sannan barci ya ɗauke sa, yau kasan cewar Hajiya ta rigasu yin barci, sai Abbo bai ce ta tashi ta kai Jelly bedroom nata ba, dan shima hakan yake so Jelly ta rinƙa kwanciya kusa da su, shi yasa ma baya wani damuwa wajen sa Hajiya ta koya mata kwana ita kaɗai a ɗaki, shine ma mai kara injiza abun, da Jelly ta fara cewa bata so, sai ya wani ce a'a a barta tun da bata so kar a wani takura mata, shi ya fara kawo shawarar tun da tana tsoron kwanciya ita kaɗai to su rinƙa kwanciya da ita sai tayi barci su ɗauke ta su mai da ta bedroom nata, insert of ya sanya Hajiya ta koya mata kwana ita ɗaya, sai ya kara dagula komai dan shima yana ra'ayin hakan. A ranar dai a ɗakin su Jelly ta kwana. Mu leƙo Rimsha mu dawo 👹DAULAR MUTUWA👹 Yanzu dai ba laifi shakuwa ta shiga tsakanin Rimsha da duna, sai dai ita Rimsha tana biye masa ne kawai bisa umarnin baba na cewa ta biye masa har Allah yasa ya musulunta imani ya ratsa shi ya daina shan jini da sauran su, wannan dalilin yasa take biye masa, yanzu har zama take suyi ta hira, yana mata tambayoyi a kan addinin Musulunci tana bashi amma with her confidence, dan ita ma tana burin ya shiryu ya musulunta ya dai na duk wani abun da yake ya koma ga Allah, sai dai kullun in zata bashi amsa a kan addini, sai Queen ta shaƙe ta, tayi ta fama har sai duna ya taimaka mata, kasan cewar shi ma irin sune, da jikin sa ya haɗu da nata kaɗan, tofa dole su sake ta. Yauma kamar kullun suna zaune saman bencin duna suna hira, shi kuma yana zaune daga ɗan gefe da su, saman wata kujera da ya bayyanar da ita da tsafin sa, yanzu baya zama kusa da su sosai a ɗan gefe yake zama, saboda sun faɗa masa a addinin musulunci ba'a yin haka, saboda son da yake wa Rimsha yasa yake girmama addinin ta da kuma dokokin addinin nata. Sai hira suke ita da su Ayla cikin nishaɗi, yau basu je wajen baba ba, sun zauna wajen, zuba musu ido kawai duna yayi yana kallon yadda Rimsha ke ta murmushi kyakkyawan dimple nata yana lotsawa gwanin ban sha'awa hakan ba karamin kyau yake karawa face nata ba, daman abu huɗu zuwa biyar ne a face ɗin Rimsha da yafi ɗaukan hankali duk wanda yayi ido huɗu da ita, na farko wayan nan kyawawan dara daran sleeping eyes ɗin nata farare kal kamar audiga, ba karamin tafiya da imanin ɗan adam suke ba, kasan cewar idon nata yayi daban, sai ka tara mutane sama da dubu baka samu biyu masu irin wanna idon ba, shine babban abun da yafi jan hankali mutane a face nata, na biyu kyakkyawan dimple nata, idan tana murmushi ko tana magana, ko baka son ta sai ka tsaya ka kalleta, saboda dimple ɗin nan, ba karamin kyau yake kara mata ba, ɗan siririn open teeth, dake tsakanin hakwaran ta da suke farare kal a baya amma yanzu saboda da hannu take brush babu brush hakan yasa hakwaran nata suka rage haske, amma still suna da hasken sai dai ba kamar lokacin da suke tare da daddyn su ba, abu na huɗu ɗan bakin ta, wow idan tana magana abun sai wanda ya gani, laɓɓan ta na sama design of heart ne ga bakin nata ɗan karamin dashi launin pink color kamar wadda ta sanya lipstick, hancin nan nata har baka ɗan siriri kamar karas Masha Allah, ga bakin saje kwance a gefen kumatun ta. Sai hiran su suke duna ya tsare su da ido, can kome ya tunan ya miƙe yazo ya tsugunna a gaban ta, tare da zuba mata ido a hankali yace "Me yasa idan kuna magana kuke yawan sanya Annabi Muhammad? Waye shi?" Dawo da kallon ta kan face nashi tayi cikin nitsuwa tace "Shi ne Babban abun soyuwa a gare mu, kuma shine annabin karshen da baba ya faɗa maka ranar, duk wani cikakken musulmi yana son Annabi Muhammad" "eh nasan kuna son shi kam dan baku magana ɗaya biyu baku kira shi ba" yar murmushi Rimsha tayi kafin tace "Saboda son da muke masa ne yasa har a zamanin baya kafin yazo duniya ya samu takwara dayawa, sosai jama'ar zamanin da kafin yazo suka masa takwara" zaro ido duna yayi kafin yace "To bai zo ba kuma ya akayi suka san shi har suka masa ta kwara? Waye ya faɗa musu sunan shi da har zasu masa takwara? Bayan ni nasan sai an haifi yaro ake sanin sunan da za'a sa masa" ɗan kawar da idon ta tayi daga kallon sa kafin tace "Annabi Muhammad (SAW) an san shi ne tun kafin a ganshi, kuma an sanshi ne tun kafin a haife sa, domin yazo a littafai da dama, sunan sa ya bayyana a littafai irin su attaura, injila, zabura, so already wayan nan littafai sun bayyana zuwan sa da sunan sa da yanayin da zai zo, da kuma in da zai bayyana, waye shi da sauran su, shi yasa jama'a suka rinƙa masa takwara saboda son da suke masa, muma yan zamanin yanzu muna kaunar sa fiye da rayuwar mu, ni kullun cewa ma nake da azamanin sa a ka haifeni dana more" shiru duna ya ɗan yi kafin yace "Kwarai kuwa na san kuna son shi, nima shaidane dan kuwa akoi wata mata dana taɓa shanyewa jini a kasuwa, lokacin na riƙeɗe na dawo kamar yadda kika ganni yanzun nan, na shiga cikin mutane, a kasuwa na ga matar tana sai da kaya, kawai naji ina son shanye jinin ta, to lokacin akoi wata waƙa da ta kunna suna faɗin annabi kwarai kasan gaibu, na kasa manta wannan wakar ita kan ta matar na kasa mantawa da ita, ban san ya akayi ba ita ce mutun na farko dana taɓa shan jinin ta dana kasa mantawa, bayan na sha jinin nata sai naji ban ji daɗi ba, har yanzu na kasa mance ta" jinjina kai Rimsha tayi har idon ta ya kawo ruwa saboda tausayin matar a hankali tace "Baka kyau ta ba, amma dai karka ɗauka abun da suke faɗe a wakar gaskiya ce, domin Annabi bai san gaibu ba, dalili kuwa shi da bakin sa yace bai san gaibu ba, a lokacin da sayyidina Abubakar ya tambaye sa yaushe za'a tashi kiyama, sai yace wa sayyidina Abubakar sanin gaibu sai lillahi shi bai sani ba, Allah ne kaɗai ya san ranar tashin Al kiyama, kaga kenan idan da annabi yasan gaibu da muma mun san lokacin da za'a tashi kiyama dan da zai faɗa wa sayyidina Abubakar, shi kuma zai ruwaito mana hadisai, abu ɗaya ne yasa mutane ke ganin kamar annabi yasan gaibu, shine mafi yawancin lokaci Allah yana masa wahayi mala'ika Jibril yazo ya faɗa masa Allah ya bawa wanna sahabi aljanna, ko kuma Allah ya saukarwa wannan sahabi wata ni'imar, to idan mala'ika ya isar masa da wanna wahayi, shi kuma sai ya sanar da Sahabban sa, hakan yasa mutanen mu na yanzu suke ganin kamar annabi yasan gaibu tun da yana faɗin abubuwan da basu kai ga faruwa ba, kamar dai yadda ya bayyana Allah ya baiwa su sayyidina Abubakar aljannan tun suna raye, shi yasa rashin fahimter ce kawai da mutane ke samu, mafi yawancin mutane suna kan dai dai bisa nasu fahimter, basu kauce hanya ba kawai basu fahinci abun dai dai bane" hannu ya kai zai shafi kumatun ta, sai kuma ya fasa, cike da kaunar ta yace "To ni dai gaskiya addinin ku yana burgeni, ta in da kuma yake burgeni in da akace matar ka kai kaɗai zaka taɓa ta ba wanda zai taɓa maka ita, wannan abun yamin daɗi sosai, addinin akoi tsabta sosai, kinga a baya zamu kwanta da duk macen da muke so, kuma ina da tabbacin kafin mu wasu sun kwanta da ita, hakan tsam ba tsari, ace mace ɗaya maza dayawa suyi ta kwanciya da ita abun ba ɗaɗi, amma addinin ku yayi hani da wanna gaskiya naji daɗi kuma na jinjinawa addnin nan naku" cool murmushi ta saki taji daɗi duna ya fara yaba addinin musulunci, da alama ya fara hawa kan hanya ma dai'dai ciya hakan ba karamin farinciki ya sanya su ba, dukkan su har da su Ayla. A wanna yanayi Mustapha yazo ya same su, dan yanzu yana zuwa suyi ta hira da duna sun zama kamar friend, yana zama Rimsha ta miƙe tana faɗin "Ina zuwa Ayla bari na je ɗaki na ɗauko apple na najiya" to kawai suka amsa mata da shi, sannan ta wuce ta bar wajen, su kuma suka ci-gaba da hiran su. Tazo zata shiga ɗakin nasu, sai taga yar siririyar hanya daga ɗan gefen ɗakin nasu, Rimsha da karambani tace bari ta leƙo taga menene a wajen, ɗan karamin hanya ne, ga wani fitinanniyar wari bala'i dake fitowa daga wajen, haka ta kutsa ta wajen tare da toshe hanci ta tana lallaɓawa saɗaf saɗaf kamar wata ɓarauniya har ta kai karshen hanyar, ba tare da su duna sun ankara da ita ba, suna ta hiran su ko da taje karshen hanyar sai taga ba wani abu a wajen sai wani katanga mai ɗan tsawo daya musu katanga, ma'ana ya raba su da wan can part ɗin. Kamar a kafarki taji kafar ta ya tsunduma cikin wani abun, cikin tsoro a hankali ta kai kallonta kasa, nan taga wani irin jini mai bala'i kauri da yauki, cikin jinin duk guda gudan naman jikin mutun, ta wani gefen ma har da kashi ɗan adam, ɗago idon ta tayi a razane ta kalli gefe gefen wajen da kyau, gaba ɗaya kashin kwarangal na mutane ne, ga kuma naman jikin mutun wadda bai gama murmushe wa ba, kasan wajen wani daskararren jini ne mai balai wari, ga kuma wani sabon jini na malala a saman wannan daskararren, da alama yanzu ake zubar da wannan jinin, wani mugun tsoro ne ya dira mata a ranta lokaci guda, nan take jikin ta ya fara ɓari, wani irin wahalallan yawu ta haɗiye da kyar, nan take idon ta ya rena fata, wani gumin wahala ya fara karyo mata. Amma saboda fitina irin na Rimsha sai da ta kama katangar nan har da yar tsallen ta, ta leƙo, dan ta dage sai taga daga ina jinin nan ke fitowa. Nan fa idon ta suka gane mata abun da kwakwalwa ba zai ɗauka ba, wani mahaukacin ihu ta fasa tare da sakin katangar, kamar zararriya haka ta bazama ta fito daga wajen, a guje su duna sokayo kan ta, saboda ihun ta da sukaji Tun da yaga ta in da ta fito yace shikenan kuma mawuyacin abune yau Rimsha ta rayu a gidan nan, ita kuwa sai ihu take kamar wata zararriya, tunani duna ya shigayi ya zai yi ya kuɓutar da Rimsha daga sharrin su Gujungu, dan yasan definitely wayan nan magicians dake wajen zasu biyo bayan ta dan sun jiyo ihun ta, kuma tabbas bazasu barta da rai ba, dan ba'a ganin sirrin su a rayu. Sai ihu Rimsha take da alama ta fita hayyacin ta, dan ta razana sosai da abun da ta gani, jin takun sahun jiga jigan magicians ɗin ne yasa duna kara tsorata dan yana ji a ransa sai dai yau ya mutu amma ba zai iya bari su ɗauki Rimsha ba, takun magicians ɗin sai kara kusan tosu yake, duk in sukayi taku ɗaya, sai kasa da katanga sun girgiza saboda girman su da larfin bala'i irin nasu. Sai zaro ido duna yake, kasan cewar yasan duk bala'i sa su Gujungu wato masu gadin fadar Queen sun fisa bala'i, ko su Barbushi basu isa su tinkare su ba bare kuma shi, banda Queen ba mai iya ja da su Gujungu a gidan, manya manyan jiga jigan magicians ne masu ji da larfin ɗaga mota kamar yar baby da hannu ɗaya, tsabar girman jikin su da karfin su, idan suka taka kasa, sai katangar dake wajen ta girgiza, hakan yasa mafiyawancin ɗakunan gidan da dafaffun karafuna a kayi su katanga ɗai ɗai ne a gidan, dan katanga ba zai iya ɗaukan karfin takun su Gujungu ba rushewa yake. Jin sun kusa isowa in da suke ne, dan ga alamar sautin takun kafar su da kuma amshin kasa nan ya kara karuwa, tsabar tsorata duna bai san lokacin daya batar da Rimsha da tsafin saba, a baya yayi alƙawarin ba zai sake amfani da tsafin ba, saboda Rimsha ta nuna masa tana tsoro kuma bata son hakan, idan har zai ci-gaba da amfani da tsafin to gaskiya ba zata ci-gaba da yi masa magana ba, shiyasa yace mata ya dai na ba zai sake ba, amma yau bashi da zaɓi dan Rimsha ta taɓo gidan rina ta tsokalo gindin dodo bala'i da yafi karfin su, shiyasa ya ɓatar da ita gaba ɗaya daga wajen Bayyanar su Gujungu a wajen ba karamin haukata kwakwalwan yan gidan gaba ɗaya yayi ba, banda duna da ya saba ganin su, ba wanda kwakwalwan sa bai haukace ba a gidan sai Mustapha, saboda su Gujungu sun fi su Barbushi a muni uban ni su Barbushi ne, sanna a girman jiki sunyi biyun su Barbushi, sai dai basu da tsawo, gajeru ne, sai bala'i faɗi shiyasa kofar shiga wanna wajen nasu ma faɗin sa ya kai 2 miter dan su iya shiga da fita, amma duk da haka a takure suke, saboda girman jikin su, hancin su kawai ya kai girman kan bil adama, idon nan nasu bazai ganun wa ɗan Adam ba, ka fafun sunan ya kusa faɗin fridge, munin su kawai zai iya sanya ɗan adam zuciyar sa ta buga ya mutu, babu ko ɗigon imani a tattare da fuskokin su bare tausayi, basu fitowa kullun suna wanna part din nasu suna aikin sarrafa wa Queen ganganjikkin ɗan Adam da sauran ayyuka. Tun kafin su iso daman duna ya koma asalin halittar sa na Magicians, Ayla da kausar tuni sun sume a wajen, shikuwa Mustapha, kamar mahaukaci haka ya bazama yayi ɗakin da ya samu a buɗe ya shege, haka sauran yan gidan da basu suma ba, suma duk ɗakin da suka samu kawai shiga sukayi dan cetan ransu, kuma basa hayyacin su. Duna na tsaye har suka ƙariso wajen, Gujungu ne ya fara tambayar ina wadda ta leƙa su take, cikin yaren su na matsafa, da muryan sa mai doɗe kunnen ɗan adam ya daina ji gaba ɗaya, nan fa duna ya fara musu kame kame na cewar bai ganta ba, wani mahaukacin kururuwa Gujungu ya sa wadda yayi sanadiyar tada guguwa mai karfi gaske bakin kirin kamar bakin hayaki na itacen damuna, jijjiga jikin sa yayi tare da ɗaga kofatan kafa ɗaya zai sauƙe a kan Ayla, duna yayi saurin kwanciya kasa ya shiga tsakanin su, kafar Gujungu ya sauka ma shi a cinyoyin sa ta baya razanannen ihu mai bala'i sauti duna ya sake mai razana kwakwalwar duk wani halitta mai rai, kan kace me cinyoyin duna sun rugurguje har kashin sa sai da suka rugurguje saboda takun kafar Gujungu fa ba wasa ba. Wucewa su Gujungu sukayi suka nufi cikin gidan dan neman Rimsha, shi kuwa duna sai ihu azaba yake na cinyar sa da ta daddage, haka suka wuce zuwa tsakar gidan dukkan wadda suka samu a kan hanya ya suma bi ta kan sa suke su wuce, duk kuma wanda suka sauƙewa wanna gofaton kafar nan tasu, tofa namar sa daga'daga yake ya daddage, wasu ma har lumewa cikin kasa suke idan suka take shi, banda jini ba wani abun dake malala a tsakar gidan, sai fantsala musu a fuska da jikin jinin yake, amma da yake yan datti ne ko ajikin su basu damu ba. Bayan sun tsaya a tsakiyar gidan ne suka fara jawo duk wata halitta dake cikin gidan suna fito da su, da tsafin su, sai dai kagan su fiw sun jawo mutun waje ya fito, haka suka jawo Mustapha ma fiw ya fito kamar iska, har da baba suka fito da shi, duk a tsakar gidan suka tara kowa, kafin su juya idon su ya koma kalar na tsafin su, wato light green, da tsafin nasu suka fara neman in da Rimsha take a cikin gidan, domin kuwa madubin Queen ya nuna musu babu Rimsha cikin wayan da suka tara a wajen, sai zazzaro ido suke suna jujjuya idon nasu gwanin ban tsoro da tashin hankali Bayan Mustapha da duna da baba ba wata halitta mai rai da ta rage tana cikin hayyacin ta a gidan, har ita Rimsha ɗin da duna ya ɓoyeta bata cikin hayyacin ta, mai iya kallon su Gujungu ido huɗu kuma ya iya rayu bai mutu ba, tofa sai mai tsawon kwana kuma mai karfin imani, irin dai mutanen part ɗin su Rimsha, dan sune masu imanin gidan, tun da har suka iya wace part 1 suka wuce part 2 suka zo nan to tabbas sune jiga jigan masu imani, dan mai raunin imani baya iya tsallake wa su Barbushi. Can cikin duhu ɗakin duna idon tsafin su ya hango musu Rimsha tana kwance tana ihu, da karfi, Gujungu ya fisgota, da tsafin sa zuwa tsakar gidan Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita.... Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 32-33 Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita. Haka suka wuce da ita, duna yana ji yana gani dan kuwa babu abun da zai iya shima neman a kawo masa ɗauki yake. A wanna yanayi su Barbushi suka shigo part ɗin suka same sa, kasan cewar mutumin sune kuma dole su taimaka masa saboda aikin da yake musu, cikin sauri suka ɗauke sa suka wuce da shi, dan suje su nema masa ruwan tsafi wajen Queen ko kafafun nasa zasu gyaru. Su Ayla kuwa bayan tafiyar su Barbushi Mustapha ne ya taso yazo ya taimaka musu ya jasu zuwa ɗakin su, sanna ya mai da baba ma ɗakin sa, ya dawo ya zauna shiru ya buga uban tagumi sai haɗa zufar wahala yake, yau yaga abun daya kwance masa notikan kansa, duk sai yaji duniya ta isshe sa, ban da addu'a a ransa babu abun da yakewa Rimsha, shi kan shi baba addu'a kawai yake mata tare da tausaya mata da kuma su Ayla idan suka tashi ya zasu ji a ransu ace musu an kashe Rimsha. Haka baba da Mustapha suka zauna jugum jugum suka buga uban tagumi kamar wasu marayu, suna yiwa Rimsha addu'a. Wanna kenan mu leƙo Washington DC mu dawo 💞WASHINGTON DC💞 9:20am Sai sauri James yake ya sauko kasa daga saman bene, kamar wani mara gaskiya yana tafiya yana waigen bayan sa yana waya kasa kasa, jikin sa na sanye da suit ashe colar mai shegen kyau da tsada, kayan sun kara masa kyau sosai. Dai dai tsakiyar palon yana waigen bayan sa bai ankara ba sukayi karo da wani bodyguard wadda ya ɗauko tray mai ɗauke da kyawawan glass cup wadda a ka cike su da drinks. Gaba ɗaya drinks dake cikin cups ɗin nan suka kware a jikin James, zaro ido bodyguard nan yayi Allah sarki nan take jikin sa ya fara kerma, ya kasa magana saboda tsoro, James kuwa ransa ya ɓaci iya ɓaci, a fusace ya wanke wa bodyguard nan fuskar sa da wata mahaukaciyar mari, ji kake tass, dai dai lokacin Romeo ya sako kafar sa saman benen yana kokarin saukowa Cikin jin haushi abun da James ɗin yayi rai a ɓace ya dakawa James tsawa "Are you mad James!!? Tsabar tsorata da bodyguard nan yayi na tsawar da Romeo ya daka sai da zuciyar sa ta buga a wajen ya yanke jiki ya faɗi kasa gawa, Allah sarki ya ɗauka shi Romeo ya dakawa wanna tsawar shiyasa ya tsorata haka har zuciyar sa ta buga ya mutu, dan dukka gidan idan Romeo yayi magana a hankali ma firgita su yake jikin su yayi ta kerma bare kuma tsawa ai sai mutuwa, criminals da dama tsawa Romeo ke daka musu zuciyar su ke bugawa saboda tsoro su mutu, dan duk wanda ya kwana ya tashi a Washington DC tofa yasan hukuncin GAR babu kyau, yasan GAR baya hukunci mai daɗi, mutuwar tsoron sa jama'a keyi, ganin face nashi yana cikin farinciki ma razanar da hantar manyan maza yake bare kuma in ya ɓata rai, Subhanallah ba sai ya kai ga hukunta mutun ba tsawa kawai ya wada wa mutun zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu, sai dai in mai sauran tsawon kwana. Ganin bodyguard ɗin ya faɗi kasa yasa James yayi saurin tsugunnawa yana taɓa shi, ina rai yayi halin sa, ɗago ido James yayi a tsorace ya kalli Romeo dake tinkaro su "He died" ya faɗa a razane, har cikin ransa Romeo bai ji daɗin mutuwar bodyguard ɗin ba, yasan dai jama'a da yawa a wajen suna tsoron tsawan sa, a wajen aikin su ma, wasu idan ya waro musu dara daran blue eyes na sa ya kalle su ma kawai suma suke, wasu criminals ɗin ma da ance musu GAR ne zan yanke musu irin hukuncin da ya dace da su, a wajen suke murɗe wuyar su su kashe kan su, dan a cewar su, da hukuncin GAR gwara mutuwa, da GAR ya kalleka da fusatacciyar fuskar sa kamar wani lion ɗin nan gara su mutu, bai taɓa tunanin bodyguard nasu na gida suna tsoron tsawar sa har haka ba, kasan cewar su bodyguard ɗin wajen dining table ba sojoji bane, su kawai an ajiye sune dan miƙa musu tissue paper da kuma ruwa da drinks sai serving nasu abinci. Abun bai ma Romeo daɗi ba, wuce wa kawai yayi ya nufi hanyar fita daga palon ba tare da ya kara tanka James ɗin ba, yana fita ya turo jibga jibgan sojojin sa a kan suzo su ɗauki bodyguard ɗin su fitar da shi, aje a shirya sa zuwa mutuware, Wanna ma ba cikin ɓacin rai Lion yayi wanna tsawar ba, da ransa a ɓace yayi ta ina ga da har shi kan shi James ɗin sai zuciyar sa ta buga. Haka sojojin suka zo suka ɗauki gawar bodyguard ɗin suka fice da shi Gaba ɗaya James yaji ba daɗi kuma ya ɗaura alhakin mutuwar bodyguard ɗin a kan sa, a cewar sa komai ya faru shine sila, da yayi hakuri bai mari bodyguard ɗin ba da Romeo ba zai yi wanna tsawar ba, zai zo ne kawai ya wuce su ya fice daga palon, amma gashi yanzu saboda nuna masa kuskuren sa da Romeo ke kokarin yi yasa zuciyar bodyguard ya buga. Jiki ba kwari James ya wuce ya koma bedroom na sa dan sake wanka ya canza kayan jikin nasa. After some hours Shirye cikin wando jeans baki three quarter James ya fito da riga Turtle high blue, kai tsaye wannan fili na Romeo ya nufa, dan yana da tabbacin suna can. Da excuse ɗauke a bakin sa, ya iso wajen, Romeo na zaune saman sofa daya saba zama yana latsa waya, while shi kuma Michael yana tsaye ya ɗaure wasu kwalaɓe wadda Romeo ke ɗaurewa sojojin sa idan suka masa laifi, sai ya ɗaure musu wayan nan kwalabe suna lilo ya ce su ja baya sosai su saita kwalaben da bindiga su harbe su dukka su fashe su, kuma kwalaben ba tsaye suke waje guda ba kaɗawa suke sosai suna lilo idan kayi missing na bullet ɗaya baka fasa kwalbar nan ba, to horo mai tsanani Romeo zai baka, a koi wani ruwa mai kankara, gaba ɗaya ruwan waje ice ne haka Romeo zai jefa ka ciki, ta kofar da yasa aka yiwa ice ɗin, ka zauna cikin ice nan tsawon 3 hours kafin ya sa a fitar da kai ya sanya wasu sojojin su zane ka, kana rawan sanyi suna zane ka, idan suka maka kamar bulala hamsin sai a sake mai daka cikin ice ɗin na 3 hours again, duk wanna hukuncin na missing bullet ɗaya da kayi ne ba'a kai ga na laifin da kayi a ka kawo ka wajen harbin kwalaben bama tukun nan, wanna dalili yasa criminal da dama suke kashe kan su in dai suka san lion ne zai yanke musu irin hukuncin da za a musu, wanna ma idan yana farincikin kenan, duk wata kalar hukuncin mugun ta Romeo ya iya shi, gashi da zuciyar bala'i, ga kafiyar masifa idan yayi magana yayi ne ba wanda ya isa ya sanya shi ya sauya, baya mai mai ta magana idan yayi yayi ne, koda bakaji me yace ba to yazama dole kayi abun da yace dan ba zai mai mai ta maka ba idan kuma ba ka aikata abun da yace ɗin ba hukun taka zai yi, ga bala'i zafin rai kamar wuta, ga zafin kai, ba mai iya tankwara shi ya canza masa abun da yayi niyar yi, babu wanna mahalukin dan shi kaifi ɗaya ne, sannan miskiline na karshe, dan baya son magana, magana wahalan yi take masa, ga izzan bala'i idan ka masa magana sai ya dauki mintoci kafin ya amsa maka, bai son hayani, baya shiga tsabgar kowa, sannan bai yarda da kowa ba, sai Triplets na sa, da dad, su Uncle Herry, bayan su bai yarda da kowa ba, imma mace ko namiji. Ɗaure kwalaben Michael yayi, sai famar harbin su yake da irin silent pistol gun ɗin nan, wayan nan kananan bindigun marasa karan nan. Michael ya karan da bullet sau uku, yana kare wa yana kara wani amma ko kwalba ɗaya bai samu ya iya harba ba, saboda harbin wayan nan kwalabe ba wasa ba, sai wanda yaji training ya koshi, sai manyan jiga jigan sojoji masu saiti da kyau, Romeo na zaune yana ganin sa ta wutsiyar ido. Wucewa James yayi har zai zauna kusa da Romeo, sai kuma ya fasa, ya nufi Michael tare da amsan gun ɗin, kwata kwata ya manta sai abun ya masa kamar wajen ta'addancin su yake, sai ta kwalaben yayi ya fara harɓi, tsabar iya saiti irin na James, kan kace me, ya fashe kwalaben nan dukkan, ba tare da yayi missing na bullet ko ɗaya ba, ba wani bullet da ya faɗi kasa ba tare da ya fasa kwalbar ba, sosai abun ya bawa Romeo mamaki, dan kuwa wanna abun da James yayi kananan sojoji basu iya yin sa, horo ne mai wahala, dan ko Tga bai jima sosai da gama iya ire-iren wayan nan horon ba, abun ya ɗan bawa Romeo mamaki, kallon tsab yayiwa James yana tunanin, a iya sanin sa dai James ko yadda ake riƙe bindiga bai iya ba, dan bai koya musu ba, gara Michael ma daman shine mai karanbanin ɗaukan kananan bindiga yace zai koyi harɓi, amma James bai taɓa ɗaukan gun ba ko da sunan wasa to tayaya ya iya harbin wayan abubuwan, kuma yayi harbin ne cike da kwarewa da kwarin gwiwa, kamar wadda ya ɗauki 10 years yana karɓan horo. Shi kuwa Michael rungume James yayi yana turo baki a shagwaɓe yace "Why to ni na kasa harbin ko ɗaya" raba jikin su James yayi yana faɗin "Baka mai da hankali ka sanya kan ka bane amma da zaka iya ai dan ba wahala" ya kai karshen maganar tare da wucewa zai zauna kusa da Romeo, sai lokacin idon sa ya sauka kan Romeo da ya tsare sa da dara daran blue eyes nasa yana kallon su da mamaki Nan take James ya sha jinin jikin sa, dan kuwa yasan me Romeo ke wa mamaki, kwata kwata ya macen da ina yake shiyasa ya harbe kwalaben, kuma yasan wanna horo ne mai wahala, dan sai da yayi wata biyu yana koya kafin ya iya, dan ma yana da ƙwaƙwalwa da basira shiyasa yayi saurin iyawa. Cikin sauri ya kawar da kan sa daga kallon Romeo ya fasa zaman da zai yi ma, dan dama yazo ne ya sanar da Romeo zai je party a New York kuma ba zai dawo ba sai gobe karsu neme sa, a zahirin gaskiya kuwa Meeting na su na criminals zai je. A nitse ya sanar da Romeo zai je party, shiru Romeo ya masa har lokacin bai ɗauke blue eyes nasa daga kan James ɗin ba, ganin haka yasa James ya sauka daga wajen ya nufi hanyar fita daga wajen yana faɗin sai ya dawo, cikin sauri Michael yace "wait for me I want to go to White House so mu fita tare kawai" shi dai Romeo ido kawai ya zuba wa James yana kokarin fahimter wani abu, tunani yake ai na James ya iya wanan harbi haka Kasan cewar baya yi musu tambayoyi a kan abun da ya shafe su, sai yayi shiru bai tambayi James ɗin ai na ya koyi har bi ba, idan ya ga wani abun da bai masa ba a tattare dasu bincike kawai yake da kan sa gani, baya tambayar su, har suka fice daga wajen bai dai na kallon suba. Sai bayan sun tafi da jimawa sannan ya miƙe ya bar wajen shi ma, ya koma cikin gida. Michael kuwa, suna fita kai tsaye white house ya wuce, dan yau yace bari ya kaiwa president ziyara, tun daga bakin gate bodyguard da sojojin dake tsaron white house suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, da wata Winter Sports Hat nasa da yansa a kan sa, saboda yawan gashin kan sa, sai hat ɗin tayi masa katuwa a kai. Kai tsaye cikin ya wuce bai bi ta kan kowa ba, da fara'a President ya tare sa, sai turɓune fuska Micheal keyi kamar wadda aka sa shi zuwa dole, shiko president sai daɗi yake ji, saboda murna ya rasa ina zai sa Michael, saboda kaunar da yakewa GAR ne ya shafi su Michael, yana son family William jacop sosai, kasan cewar kakan su Romeo jacop Roshan babban ɗan siyasa ne kafin ya mutu, shiyasa suke da damar shiga ko ina a kasar ba wata shamaki sai ma girmamawa da suke samu daga manya manyan yan siyasa masu tasowa yanzu. Wata dankareriyar diamond watch mai bala'i kyau da tsada president ya ɗauko ya bawa Michael kyauta, first time da Michael ya cire diamond watch na su na Triplets ba barci zai yi ko wanka ba, kuma ya cire ne dan ya sanya wanda president ya bashi, saboda ya nunawa president yaji daɗi. Sosai president yaji daɗin abun da Michael ɗin ya masa, na cire diamond watch na su na Triplets da yayi ya sanya wadda ya ba shi, sosai agogon tayiwa Michael kyau kamar dan hannun sa a kayi ta, sanya diamond watch nasu na Triplets yayi a aljihun jacket nasa ya bar na president ɗaure a hannun sa, suka ci-gaba da hira kamar wasu friend, bayan kuma president ya kusa jika da Michael, amma saboda son da yake musu, sai ya zama kaman friend nasu idan suka zo wajen sa. Shi kuwa James kai tsaye wajen taron su ya nufa, a in da zasu gudanar da taro cikin dajin palace, a nan zasuyi taron, manya manyan criminals uban nin gidan su James sun hallara, sun zauna sai hira suke suna jiran saukowar sauran jiga jigan ogannin nasu, sai a fara taron. Shi kuwa Romeo yana kwance saman lallausan katafaren gadon sa, yayi kwanciyar rigingine ya tasa system a gaba yana bawa yaran sa dake shirin tafiya yaki umarni, sai faman lumshe dara daran blue eyes nasa yake kamar mai jin barci, ga daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac dake ta faman tashi a bedroom ɗin nasa, gaba ɗaya wutar ɗakin nasa ya kashe farin wutar ya kunna sky blue, sky blue light ɗin ba karamin karawa ɗakin nasa kyau yayi ba, abun gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali. A ɓangaren TGA kuwa, sosai wayan nan kwari suka masa illa, dan kuwa a kan gaban sa suka matsa wanna tsiyar, wajen ya kunbura sosai yayi jawur kamar jini ne a ciki, duk jarunta irin na soja sai da TGA yayi kuka, saboda ciwo a irin wanna waje ba karamin abu bane, yana da zafi sosai over, Allah sarki bawan Allah ko wando baya iya sawa saboda azaba, ga sanyi Ac amma duk da haka sai daddy ya kunna rechargeable fan ya kawo masa sai tin gaban nasa yana shan iska saboda azaba, shi kaɗai kwarin suka yiwa irin wanna lahani mai muni sosai haka, duk wannan hali da TGA ke ciki Romeo bashi da matsani dan yana can ya nitsa cikin aikin da yake. Mu leƙa Jehan mu dawo 💞KATSINA💞 Yau ya kama Monday, tun 8 na safe a ka shiga da mum ɗakin da za'a mata aiki, while ita kuma Jehan ta shirya tsab cikin wata dakakkiyar atamfan ta super wax mai bala'i kyau ɗinkin riga da skit, kayan sun zauna a jikin ta sosai, sunbi shape ɗin coca colan ta sun mata ɗas, kasan cewar bata son ɗankwali ma bare hijabi hakan yasa ta ɗauki ɗan karamin Malaysian hijab ɗin ta pink color tare da takalmi pink color, ta ɗauko jakar ta suwaga shi ma pink color ta fito tsakar gida, ba karya duk da cewa fake face ne a fuskarta ba ƙaramin kyau tayi ba sai kamshin sauran perfume da ya rage mata take. Kai tsaye kitchen ta nufa wajen maman Sadiq, suka gaisa sanna maman Sadiq ta mata addu'ar fatan fara aiki a Sa'a, yar murmushi tayi ta amsa da amin sanna ta fito daga kitchen ɗin da sauri saboda hayaki. Tana fitowa sukayi karo da Sadiq yana kokarin shiga kitchen ɗin, ɗan baya kaɗan tayi tana faɗin "Good morning" zuba mata ido yayi yana kallon ta yana mai kara jin kaunar ta a ransa, tab lallai ita kuwa Jehan babu wani abu wai shi soyayya a ranta, bata san shi ba, kuma bata da wani ra'ayi a kan soyayya, ita da namiji da mace duk kallon abu guda take musu, namiji baya gaban ta, maza basu isshe ta kallo ba, kai har matan ma ita a wajen ta basu isshe ta kallo ba, bata taɓa kawo wani abu wai shi tunanin aure ma a rayuwar ta ba, a nata wautan har ta mutu dasu mum ɗin ta kawai zata yi rayuwa. Ganin Sadiq ya zuba mata ido ne yasa ta raɓa gefen sa zata wuce, cikin sauri yace "Jehan dan Allah ki koma ki cire kayan nan ki sanya uniform da suka baki karki ja su hana ki aikin nan, kuma kinga dai akoi bashin kuɗin aikin mum a kanki ta wanna aikin ne kawai zaki iya biyan bashin da ake binku, to dan Allah karkiyi sanadin rabuwar ki da aikin nan kar kiyi wani kuskuren da zasu kore ki daga wanna aiki" ba tare da ta kalle sa ba, a takaice tace "I can't wear this uniform" girgiza kai Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri ki sanya jehan" cike da izza tace "Babu wanda ya isa ya zaɓa min abun da zan yi a rayuwa ta, ba zan sanya wani banza uniform nasu ba, ai ba sayata sukayi ba da zasu ce abun da suke so zanyi, ni Jehan babu wani da ya isa ya min iko da rayuwa ta bayan dad and mum, ko gwaggo lallaɓani take in tana son nayi abu, so kayan nan nayi niyar sawa babu kuma wadda ya isa ya sanya na canza" ta kai karshen maganar tare da sa kai ta nufi hanyar fita daga gidan. Dawo da kallon sa Sadiq yayi kan maman sa dake tsaye a cikin kitchen ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah "Ina kwana mama?" Ya faɗa yana sunkuyar da kai, dan yaji kunya ashe mama na tsaye tana kallon sa yadda ya zubawa Jehan ido, da fara'a maman sa ta amsa masa. Bayan sun gaisa ne ya mata sallama ya wuce yabi bayan Jehan, sai addu'a mama ke musu da fatan alkhari, yana amsawa da amin amin ya wuce. A ɓangaren Jehan kuwa tana fitowa wajen gidan tayi karo da baban Sadiq yana shigowa, ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce, zata wuce shi ne yace "Sannun ki yarinya" yauwa kawai tace masa ta wuce tana ɗaure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, dan haka kawai taji ta tsani baban Sadiq ɗin nan bata son shi, kawai tana masa karane saboda Sadiq. Jehan uwar dirama ta koyawa baban Sadiq da amarya hankali, yanzu amarya har gaishe da su Maman Sadiq take da safe, kuma yanzu sun ɗan samu zaman lafiya da fitinar amarya, ta daina takurawa kowa dake gidan, ta shiga hankalin ta da kyau saboda tsoron aljanu, wanna shine idan baka yi sharan masallaci ba kayi na kasuwa, duk iskancin ka akoi baban ka. Jehan zata wuce ta nufi bakin hanya ne, sai taga Hanan zaune gaban murhun gawayin ta na tuyar awara ta kifa kai da gwiwa tana kuka, da kamar ba zata kula taba zata wuce dan ita ba mai shiga harkan mutane bane, idan kuma ka kuskuren shiga nata harkan sunan ka sorry, dan Jehan ba sauki. Kasan cewar Hanan yarinya ce so silent bata da hayaniya kuma bata neman magana hakan yasa Jehan ta matso kusa da ita tare da dafa kafaɗar ta tana faɗin "Ke lafiya kike kuka haka?" Yar firgigit Hanan tayi tare da ɗago kan ta idon ta sunyi jawur kamar jini saboda kukan da tasha, "Subhanallah lafiya kikayi irin wannan kuka haka?" Cewar Jehan tayi maganar tana tsugunnawa kusa da Hanan ɗin, dai dai lokacin Sadiq ya fito. Da sauri ya kariso wajen su yana faɗin "Lafiya Hanan me ya same ki?" Cikin kuka Hanan ta fara yi musu bayani "Wani Alhaji ne dake yawan zuwa wajen nan sayan awara, yaya Sadiq ba ka san shi ba? Wannan mai farar ƙatuwar motar nan?" Gyaɗa mata kai Sadiq yayi yana faɗin "Eh na san shi me ya faru? Wani abun ya miƙi ne?" Ci-gaba da magana tayi tana kuka "To daman yace yana sona kuma ni bana son shi, kullun idan yazo nan ba sayan awara yake ba, kune kuke ganin kamar awara yake saya, hira kawai yake zuwa sai in ya tashi tafiya ya bani kuɗi, to ni bana karɓan kuɗin sa, ce masa nake bana so, yayi ta haɗani da Allah naki karɓa dan ni tsoron masu kuɗin nan nake, watarana baba yazo wucewa sai yaga Alhajin yana bani kuɗi naki karɓa yana roƙana na karɓa, shine da baba ya ga haka sai yayi sauri yazo shi ya karɓe kuɗi daga hannun Alhajin ba tare da an bashi ba, ya fara washe baki yana zubawa Alhajin godiya, Alhajin ya fito zai masa faɗa akan me yana bani kuɗi shi kuma zai wani sanya hannu ya karɓa, sai nayi saurin cewa Alhajin baba nane, shine Alhajin ya kyale sa ya kara masa wani kuɗin ma har da wani cewa baban ki kam ai baban nane, tun daga lokacin da baba yaga motar Alhajin yazo zai zo ya zauna a zaure yana jiran Alhajin ya bani kuɗi ya tafi shi kuma yazo ya karɓe kuɗin, ni wanna dukka bashi ne damuwa ta ba, damuwata shine kullun idan Alhajin yazo sai ya rinƙa yimin maganar banza, wai in munyi aure a ranar farko zai bani ciki, idan na nuna masa bana son maganar sai yace ai yana son ya koyamin yadda akayi ne tun yanzu dan na iya kar sai munyi aure naje na kasa yi masa abun da yake so, kuma sai ya rinƙa cemin ya kamata na rinƙa binshi muna fita zuwa hotel, ko gidan sa, bashi da wata magana sai na banza, idan nace bana so sai yace zai faɗa wa babana ina zagin sa, kuma kasan halin baba tun da Alhaji na basa kuɗi duk abun da Alhajin ya faɗa masa yarda zai yi ya haukai ya zauna ya kamani ya min duka, saboda tsoron hakan yasa kawai nayi shiru ina sauraron maganganun banzan da Alhajin yake faɗamin, jiya da daddare Alhajin yazo lokacin kuna cikin ɗakin mama kuna hira, baba yasa na fito dan muyi hira da Alhajin, dana fito Alhajin yace na shiga motar sa muyi hira naki, yace dole na shiga ai shi mijina ne tun da baba ya bashi aure na, kuma idan ban shiga ba sai ya faɗawa baba, ina tsoron ya faɗa wa baba shine na shiga na zauna, haka ya rinƙa taɓa min kirjina yana wasa da su har da gaba na ya rinƙa sa hannun sa yana wasa da shi, har yanzu sai zafi suke min, da kyar ya barni na dawo cikin gida bayan ya gama wasa dani, na rasa wazan faɗa wa, tunjiya da daddare nake kuka yau da zazzaɓi na tashi, babban abun da ya sake sani kuka yanzu, shine ina fitar da wanna murhun zan fara tuya, sai ga Alhajin yazo, wai jiya yaji daɗi kuma ya kasa barci na tayar masa da hankali dan haka na shirya anjima zaizo ya ɗauke ni, muje gidan sa mu ɗan huta, ina cikin faɗa masa ba zanje ba sai ga baba yazo zai shiga gida, da yaga Alhajin shine yazo suka gaisa, nan fa Alhajin yace masa wai yace zaizo ya ɗauke ni muje shopping ya sai min kayan arziki nace bana so, shine baba ya mare ni, ya rinƙa faɗa wai dole nabi Alhajin ko kwana ma yace zamuyi ba sai maje mayi ba, bare kuma kaya kawai zai saya min mu dawo, dan munafurci irin na Alhajin nan sai bawa baba hakuri yake wai baba ya dai na yimin faɗa baya so ana yiwa matar sa haka, sanna ya ciro kuɗi dayawa ya bawa baba ya shiga Motar sa ya tafi yana faɗin karfe ɗaya na rana zaizo ya ɗauke ni, baba kuma kuɗin ne kawai damuwar sa, yana karɓan kuɗi ya wuce cikin gida yana faɗin dole ma ta bika ai shegiya mai kashin tsiya arziki na bin ta tana gudu, abun yamin ciwo shiyasa nake kuka dan nasan idan nabi Alhajin nan wlh shikenan zai rabani da mutunci na" ta kai karshen maganar tare sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ba laifi Jehan ta fahimci abun da ta fahimta a zancen Hanan ɗin, ta gane in da zancen nata ya dosa, duk da cewa wasu abubuwan bata gane su ba, ɗago ido Jehan tayi ta kalli Sadiq. Kara zaro ido tayi tana kallon Sadiq ɗin, lokaci guda kamannin sa sun sauya, idon nan nasa sunyi jawur zuciyar sa na tafasa ji yake kamar yaje ya shaƙe baban sa ya kashe sa dan haushi, tunani yake a ransa yanzu yana cikin gidan nan jiya wani katon banza yazo yana matse masa kanwa, wani ihu yayi kamar mahaukaci cikin fushi yace "Aina Alhajin yake?" Ita ma Hanan ba karamin tsorata da ganin Sadiq a haka tayi ba, dan tasan Sadiq mutun ne mai hakuri ga murmushi ba zaka taɓa ganin fuskar sa a ɗaure ba, duk damuwa da matsalar da gidan su ke ciki, kullun cikin murmushi yake. Murya a dashe saboda kuka da tayi Hanan tace "Nima ban san in da Alhajin yake ba" a fusace Sadiq yace "Jehan tun da kin san hanya kije wajen aikin kawai, idan kin taso ki wuce asibiti, ni zan tsaya a nan ba yace karfe ɗaya zaizo ya ɗauke taba, to zan jirashi, idan kinje hospital ki gaishe min da gwaggo da jikin mum sai da yamma zan zo in ɗauke ki mu dawo" miƙewa tsaye Jehan tayi kafin tace "Yaushe ake tashi daga restaurant ɗin?" Shiru ya ɗan yi kafin yace "Inaga ku yan safe karfe ɗaya zaku tashi, sai yan yamma su karɓe ku, amma dai in kinje ki kara tambayar Ibraheem" jinjina kai Jehan tayi kafin tace "Okey koma karfe nawa ake sallamar mu, ni dai by 1 dole zan dawo, dan inason in bawa Alhajin nan capital warning" tsabar bakin ciki da ɓaci rai sun hana Sadiq bawa Jehan amsa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata buga saboda haushin abun da Alhajin nan yayiwa Hanan. Komawa Jehan tayi ta tsuguna ta gogewa Hanan hawaye, tana bata hakuri tare da mata alkawarin ba zasu bar Alhajin ya ɗauke taba. Sai da ta tabbatar Hanan tayi shiru sanna ta yiwa Sadiq sallama ta wuce bakin hanya dan tarar abun hawa ta wuce restaurant, yau asibiti ma sai ta taso daga restaurant zata biya ta can, gashi sai tunanin mum take, dan an shiga da ita ɗakin da za'a mata aiki. 💞SUPER RESTAURANT💞 Tana shigowa kai tsaye reception wajen Ibraheem ta nufa, tun daga nesa Ibraheem ɗin ya hangota, ganin bata sanya uniform nasu ba yasa ya ɗaure fuska ya ɓata rai sosai, dan yasan ogan su ba zai yarda da rashin sanya uniform ɗin ba. Tana karisowa wajen sa tun bata yi masa magana ba yace "Ina uniform naki? Me yasa baki saka ba?" Ɗaure fuska sosai ita ma tayi kafin tace "Ai tun jiya na faɗa maka ba zan sanka uniform ɗin ba, au kai daman ka ɗauka wasa nake maka, to idan ma baka sani ba ka sani ni Jehan bana faɗan abun da nasan ba zan aikata ba, garama kasani tun yanzu idan nace ba zanyi abuba tofa da gaske nake ba zan yi shi bane" tsabar haushi Ibraheem bai san lokacin da ya ɗaga hannu kamar zai mare ta, sai kuma ya dakata yana wani huci, yariya yar karama kamar wanna ta tsaya tana faɗa masa magana, gently tace "Ya ka dakata? Ai da ka marenin ina ga zai fi" shiru Ibraheem yayi yana mai dana sanin taimaka mata da yayi. Ganin yayi shiru ne yasa tace "Menene aiki na? Ka faɗa min naje na fara yi dan ina son tafiya gida karfe ɗaya dai dai" zaro ido yayi yana kallon ta da mamaki, wato ita ma zata yanke wa kan ta hukunci ga lokacin da zata tafi cab lallai aiko aiki dole na koyawa yarinyar nan hankali. A fusace ya buɗe baki zai yi magana, wayan dake gaban sa saman table ta fara kara, dogon tsaki yaja tare da sa hannu ya ɗauki wayar, irin wayar nan ne da ake ajiyewa saman table wadda costumers ke kira dan bukatar abu. Picking na call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnen sa. Jim kaɗan ya ajiye wayar ya ɗago ya kalli Jehan yace "Kije room 22 akoi wani costumer da yake bukatar ma aikaci ɗaya" rai a ɓace tace "to me zan masa" mai da wayar yayi ya ajiye yana faɗin "Idan kinje ai koma menene zakiji" guntun tsaki taja ta wuce ta tafi ta bar Ibraheem da binta da ido yana mamaki. Ko da taje bakin kofar Room 22 ɗin sai da taja dogon tsaki kafin tayi knocking na kofar, bugu ɗaya tayi aka buɗe kamar daman jira ake. Wani Alhaji ne kato bakin kirin da shi gashi da katon ciki, yana sanye da gajeren wando, kaya ya miƙo mata yana faɗin "Wanki ne zaki min" zaro ido tayi ta kalle sa kafin ta kalli kayan dake hannun sa yake miko mata, singlet and boxers ne, dawo da kallon ta kan face nasa tayi a kule tace "Yanzu saboda baka da hankali nice zan wanke maka shot naka? Ko kunya baka ji ba kato da kai, hauka nake zan wanke wandon kato kamar ka, tab lalai to Jehan dai ba za tayi wanna kazantar ba sai dai wata, daman wanna aikin shine aka kawo ni nayi, to wlh ba zata saku ba, ba zan iya ba" Tashin hankali zaro idon mutumin yayi kafin ma yayi magana, Jehan ta sa kai ta wuce ta bar wajen, da sauri mutumin ya leƙo da kan sa waje yana kallon ta, mamaki ya sa ya kasa komawa cikin ɗaki, a ransa yana faɗin "wannan yar yarinyar dai a shekaru da wuya ta wuce sha bakwai tsawo ne kawai gare ta, shine zata cemin katon banza, anya wannan a gaban iyayen ta ta taso kuwa, anya ta samu tarbiya, to wlh ba zan zauna a hotel ɗin nan ba, basu san darajar costumer ba, har ma'aikaciya tana da bakin cewa costumer ba zata yi masa abun da yake so ba, tab lalai da sake" da wannan tunani ya koma cikin ɗaki ya ɗauki waya ya sake kiran Ibraheem, Ita kuwa Jehan kai tsaye wajan sauran ma'aikatan tan restaurant ɗin ta nufa dan ta tambaye su ko shine aikin da suka zo yi kenan wato wankin kayan costumers. Da sallama ɗauke a bakin ta ta karisa wajen da sauran ma'aikatan ke zaune, har suna rige rigen amsa mata sallamar nata, sunga kyakyawa, dan Jehan akoi farinjini na fitar hankali, duk in da taje sai an so ta, haka itama Rimsha Sai wani washe baki ma'aikatan suke suna ɗaga mata gaisuwa, ita kuwa kara ɗaure fuska tayi kafin tace "dan Allah zaku iya faɗa min aikin me muka zo yi a nan?" Kallon kallo suka fara yiwa junan su, lallai wato wanna ma bata san aikin da ya kawo ta nan ba tab akoi cakwakiya. Ɗaya daga cikin sune ta miƙe ta dafa kafaɗar Jehan ta fara yi mata bayanin irin aikin da ya kawo su nan "Wanke wanke, shara, mopping, kai wa mutane abinci idan suka zo ci, sanna kaiwa yan ɓangaren hotel abinci room nasu idan suka buƙata, wasu costumers ɗin zasu buƙaci mu musu wanki su biya mu, wanna ma yana daga cikin aikin mu, sanna dole ki san ta yadda zakiyi wajen kontarwa da costumers hankali har suji daɗin wanna restaurant ɗin gobema su dawo cin abinci, dole ki koyi sakin fuska da murmushi dan jawo ra'ayin costumers su sake dawowa cin abinci, danna dol.... Bata kai karshen maganar ba Jehan ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ya isa haka, da yake sayata sukayi ba ai dole su ce nayi kaza nayi kaza, to wlh ni idan ba kaiwa costumers abinci ba, ba wani aiki da zanyi a nan, dan ni Ibraheem bai cemin da Hotel ba iya restaurant yace min, kuma a restaurant ɗin ma iya serving abinci kawai ya cewa iyaye na, dan haka iya shi kawai zan yi" ta kai karshen maganar tare da juyawa ta bar wajen ta nufi wajen girkin restaurant ɗin. Mamaki ya hana sauran ma'aikatan magana, yau sun haɗu da abun da yafi karfin su. A hanyar ta na zuwa wajen girkin restaurant ɗin ne suka haɗu da Ibraheem, rai sa a matuƙar ɓace, cikin tsawa yace "Ke zonan!!" Ba musu taje "Ke dan uban ki baki da mutunci ko? Baki da albarka ko? Mu rufa miki asiri mu ɗauko ki mu kawo ki nan dan ki samu abun da zaki rufawa kan ki da iyayen ki asiri, shine bai miki bako? Yanzu dan baki da kirki baki da albarka costumer kikaje kikayiwa ɗiban albarka haka eh? Keda muka kawoki dan ki jawo mana costumers shi ne zaki kora mana wayan da muke dasu ko? To wlh baki isa ba dan uban ki, tun wuri kije ki bawa mutumin nan hakuri ki karɓo kayan sa kizo ki wanke idan kina son zaman lafiya kinji na faɗa miƙi!!!" Tsare sa da wayan nan dara daran idon nata tayi babu ko kyap tawa, har sai da ya kai aya a maganar tasa, sannan gently tace "Ba zan yiwa wani katon banza wanki ba, dan ba wanna aikin mukayi da kai ba, masu sayan abinci kawai zan kaiwa abinci idan sun zo saya, bayan su ba wani aikin da zanyi, sai kuma maganar uniform karka sake min maganar sa dan ba zan saka ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi in da take da niyar zuwa wato wajen girkin su. A fusace Ibraheem ya bi ta ya je ya sha gaban ta, dan yana takamar ya ranta mata 500k ne yasa ya ɗaga hannu a fusace zai mare ta, cak ta rike hannun sa, cikin fushi ta ɗaga hannu zata mare sa, sai kuma ta fasa saboda ta tuna da cewa ko ba komai ya taimaka musu ya basu aron kuɗi gashi yau ana yiwa mum aiki saboda shi, dan haka bai kamata ta masa irin wannan rashin kunya ba. A hankali ta sake masa hannu sa tare da sauke nata hannun cike da ɓacin rai tace "Ina ganin mutuncin ka amma kana neman ka kaini bango, ka kiramin ogan naka zanyi magana da shi, domin kuwa bashi da iko dani, daga yanzu ba zan sake yin magana da kai ba, da ogan ka zanyi magana, dan na lura duk wanna hargagan da kake kana yin sane dan tsoron kar ogan ka ya maka faɗa a kan ban sanya uniform ba dan sauran su, to ni ka kiramin shi bari na masa bayani da baki na, a kan cewa ba zan saka uniform ɗin ba, kuma iya kai abinci zanyi, sanna shawara da zan baka shine, ka daina jin tsoron wani ɗan adam kamar kai, kaji tsoron Allah kaɗai, idan kana jin tsoron Allah tofa babu wani ɗan adam da zai baka tsoro ko ya maka wani abun da Allah bai kaddara maka ba, bana son hayaniya amma kana son sani cikin ta, bana son yawan magana shima kana sani yi, please ina ganin girman saboda taimakon da ka mana, dan Allah ka fita harka ta!!!" Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya ɗauko wadda ta fi karfin sa Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 34-35 Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya ɗauko wadda ta fi karfin sa. Nima dai Jehan tafi karfi na dan haka mu leƙo su Jelly mu dawo. 💞KADUNA💞 Yau dai Hajiya Turai tace ba zatayiwa Jelly wanka ba, dan Jelly ta girma, yanzu ta doshi 15 years amma ba abun da ta iya, saboda daddyn ta bai koya mata ba, komai shi yake mata da kan sa, bata iya komai ba sai shagwaɓa, sai dai daddy bai barta haka ba ya koya mata karatun Alqur'ani mai girma dana boko, Hajiya Turai tayi tunanin kodan saboda ciwon da take ciki ne yasa ta manta har da yadda ake wanka da sauran su, sai dai bata san dama already Jelly kam haka take ba, ciwon ne ya kara haukatata, ta zama asalin shagwaɓaɓiya haka, gashi tun da tazo gidan Hajiya Turai ke kokarin koya mata yadda ake wanka da sauran abubuwa, amma duk a banza domin kuwa ba wani abun da ta mai da hankali wajen koyan sa sai shirme, shi kuwa Abbo shi yake kara ɓata abun, dan kuwa idan Hajiya Turai tace ta koyi abu da kan ta, sai Abbo yace a'a dan Allah a kyale ta, taji da ciwo ne ko kuma taji da takura dan haka su kyale ta ta sha iska, hakan yasa Hajiya Turai wato Ummi bata takura mata da lallai sai tayi abu. Yauma kamar kullun suna zaune saman dining table suna breakfast suna hira sama sama. "Abbon Nawid ina son asamin baby a school dan ta ɗan koyi wasu abubuwa" cewar Ummi, Nawid ne ya karɓi zancen da cewa "Eh Ummi haka ne, in ta shiga school zai taimaka mata wajen kara tunatar da ita abubuwan da ta manta a baya, dan ina da tabbacin a baya kafin wannan accident ɗin ya faru yarinyar nan tayi karatu, idan kika lura da yanayin jikin ta, ni wlh ina ganin ba yar gidan talakawa yar malam Shehu wadda aka gaji da ita saboda rashin abinci kamar yadda kuke faɗe bane, da ganin ta Allah kin san wanna renon madara da su Ice cream ce" shiru Ummi ta ɗan yi kafin tace "Haka ne kuma, amma fa ni ina ganin kamar ba yar nan Kd ba ce" Nawid zai yi magana Abbo ya riga sa da cewa "A'a ba za'a sata school ba, kuma ku dai na wani maganganu a kan ta, mu dai Allah ya bamu ƴa kuma mun gode, dan haka ya isa haka, makaranta kuma ba zata je ba, saboda laluran ta ko taje school ba wani abun da zata fahimter kawai ku kyale ta a nan ɗin" shiru Ummi tayi tana tunanin zancen Abbo gaskiya ne, karsuje a garin hira da tone tone har su tono wace ce Jelly suyi sanadiyyar barin ta wajen su, dan haka garama kawai su kyale ta kar ma su sata a School taje ta haɗu da wanda ya santa yaje ya faɗa wa iyayen ta suzo su ɗauke ta kawai a banza gara suyi shiru. A ɓangaren Nawid kuma tunani yake akan me ya sanya Abbon sa yake yawan damuwa da Jelly haka ne, why kullun baya son a takura mata, baya son gaskiya a kan ta, abun ya fara yawa, amma da yake Ummi soyayyar da take wa Jelly ya rufe mata ido bata fahimci illar abun da Abbo ɗin keyi ba. A ɓangaren shi kuma Abbo yayi saurin cewa kar a kai ta school ne dan baya son a kai ta makaranta wani wadda ya santa ya ganta ya gane ta har yaje ya faɗa wa iyayen ta, suzo su ɗauke ta ba tare da ya bayyana mata soyayyan sa ba, dan yasan in dai iyayen ta suka ɗauke ta tofa ko zai mutu ba zasu bashi auren taba, shiyasa yake son su barta a nan har lokacin da zai bayyana mata soyayyar sa. Duk kan su dai kowa da abun da yake tunani, ita kuwa Jelly sai faman cin nama kaza take bata ma jin abun da suke faɗa, zancen su baya shiga kunnen ta. Har su Abbo suka gama cin abincin su Jelly bata sani ba, tana can duniyar naman kaza, ta mance da su ma zaune a wajen. Lokacin da ta gama cin naman ta, ta ɗago kai sai taga table ɗin wayam babu kowa, turo baki tayi ta miƙe ta wuce bedroom nata, dan yanzu ta ɗan kara sakin jiki tana iya zama a bedroom ɗin nata ita kaɗai. Shi kuwa Nawid tunani fal ransa game da Jelly, haka ya shirya ya tafi office, Abbo kuwa ko ajikin sa sai wani daɗin ma yake ji, Hajiya Turai baiwar Allah da zuciya ɗaya ta riƙe Jelly har cikin ranta tana mutuwar kaunar Jelly, bata wani tunanin mugunta ko wani abu wa Jelly, haka zalika a nata tunanin Abbo ma a ƴar cikin sa ya ɗauki Jelly bata kawo komai a ranta ba, shiyasa idan yana yiwa Jelly wasu abubuwan bata damuwa, kuma duk hukunci da ya yanke a kan jelly bata taɓa damuwa, sai tace ai yar sace yana da damar yanke mata duk hukuncin da ya ga dama. A ɓangaren daddyn Jelly kuwa, bawan Allah duk ya fita hayyacin sa, duk wanna murmushi kullun dake kan fuskar nan tasa ta kau, ya sauya kamar ba shi ba, ya zama so silent ko magana bai cika yi ba, sai in zai sayi wani abun, tun ranar da Jelly ta ɓata bai sake zuwa company ba har yau, Engineer Muhammad Imam ke kula da company yanzu, daddyn Jelly yana gida, yace ba zai sake zuwa ko ina ba har sai Jelly ta bayyana, saboda ɓatan Jelly har jini sai da aka kara masa, yayi baki ya rame sosai, sai manya manyan idon sa irin nata zaka gani a face nashi, saboda ramar da yayi har kasusuwan wuyar sa sun bayyana sosai, ya sanar da su Zuwaira duk wanda yazo neman sa suce baya nan, hakan yasa baban Muneer yazo neman sa yafi sau a kirga baya samun sa, dan kuwa su Zuwaira ce masa suke daddyn Jelly baya nan kuma basu san in da yake ba, idan ya kira wayar sa a kashe kasan cewar daddyn Jelly yaki gyara wayar tasa da ta fashe, kuma yaki gyarawa ne saboda Imran, baya son ya hana Imran rubuta Exam da zai yi da kyau, baya son jefa shi cikin damuwa, sai dai kuma abun da daddy bai sani ba, rashin samun su a waya da Imran bai yi ba yafi jefasa cikin tashin hankali fiye da komai, Imran ya shiga damuwa sosai a kan ko lafiya number bappan sa bata shiga, damuwar har tana nema tayi affecting nasa, baya wani karatu sosai, bai da aiki sai tunanin Jelly da daddy, yau saura 2 weeks dai dai su gama komai su dawo gida Nigeria, sosai shima Imran ɗin yayi rama saboda tunanin wani hali bappan sa da matar sa Jelly suke ciki. Ba Imran kawai ba har Irfan da Akila sun shiga damuwar lafiya number bappan su bata shiga, shikam Akil daman ko number bappan nasa bai da shi bare ma yasan tana shiga ko bata shiga, ko number bappan sa kuma sirikin sa wato Abbin su Umaisha shima bai da shi, number Umaisha kawai gare sa. Yau ne Abbi ya shirya tsab zai je Kano ya duba lafiya number daddy bata shiga, dan Irfan da Imran sun dame shi a kan yaje ya duba musu meke faruwa dasu Jelly, tun karfe 10 na safe ya fice yayiwa Aunty sallama yace ta sanar da su Aafia idan sun tashi barci. Abbi na tafiya tamkar ya tafi ne da lafiyar Aunty, nan fa ta fara laulayin ciki wadda bata san tana da shi ba, tun fitan Abbi take ta faman amai a tsakiyar palon kasa, dan kuwa ta raka Abbi kofar palo ta masa Addu'a ya tafi ne ta juyo zata dawo, nan fa amai yace bata isa ba, tana kokarin gudu ta haura sama amma ina yaci karfin ta shi ne ta zauna a tsakiyar palon kawai tana tikar amai ɗin, kamar zata amayar da kayan cikin ta dukka, shi kuwa Abbi bai ji lokacin da ta fara amai ɗin ba, ya shiga motar sa ya tafi. Sautin kakarin amai ɗin da take ne ya tashi su Aafia daga barci, daga su sai kayan barci suka sauko palon kasa, sai faman tura baki suke Tun basu karisa sauko wa ba Aafia tace "Kutumar uban can, ke Halima dan jahila ce ke sai ki zauna a tsakar palo kinawa mutane amai dan ki samu amai ɗin muma ko? To wlh baki isa ba" Umaisha kuwa wucewa tayi ta kwata saman sofa tana faɗin "Amma gaskiya Aunty baki kyauta min ba, ina barci na kawai zaki tashe ni, gaskiya wanna zalunci ne, idan ma amai ɗin ne kije toilet naki kiyi mana amma sai kizo tsakiyar Palo, dan rashin hankali" tsawa Aafia ta dakawa Umaisha "Ke dallah ki mana shiru!! ba wani zancen adalci a nan yar iska dai iskanci ne yasa ta fito palo ta fara amai ɗin nan, kuma ni nasan da biyu tayi shi, kin san wanna amai ɗin da take wlh da alaman ciki gareta, shine ta fito ta nuna mana idan zamu mutu mu mutu to ba zamu mutu ba, zaki yabawa aya zakin ta" ta kai karshen maganar tare da wucewa fuuu ta haye sama ta koma ɗakin su, aunty kuwa ji take kamar ran ta zai fita, cikin ta sai murɗa mata yake, duk abun da su Aafia ke faɗe ko kaɗan baya shiga mata kunne dan ta fara fita a hayyacin ta Umaisha na zaune tana kallon ta, sai da taga da gaske Aunty na kokarin sume wa a wajen sanna ta miƙe da gudu ta haura sama tana kiran Aafia a kan tazo ta taimaka mata su kai Aunty asibiti, nan fa Aafia ta murje idon ta tace bata san wanna zance ba, ita ba ruwan ta da wata aunty, Auntyn ta mutu ma idan ta ga dama. Sosai Umaisha taji babu daɗi abun da Aafia tayi, da sauri ta dawo palo, tazo ta riƙo aunty da kyar suka nufi waje, taje ta buɗe kofar motar ta gidan baya ta sanya aunty, ta shiga gidan gaba, babu ko ɗankwali a kanta daga ita sai kayan barci haka taja motar suka nufi hospital Ita kuma sarauniya Aafia tana ɗaki tana faman neman layin Rufee dan ta sanar mata Aunty na da ciki ya zasu yi. Tayi Sa'a kuwa ta samu number Rufee a buɗe, kira ɗaya Rufee ta ɗauka, cike da kunan rai Aafia ta sanar mata da abun da ke faruwa na Aunty na da ciki, tun bata tabbatar da gaskiyar cikin ne ko ba shi ba, kai tsaye tacewa Rufee ciki ne, Duk da rasuwar amal da akawa Rufee bai sa ta saduda ta koma ga Allah ba, haka ta ɗaura Aafia kan mummum shawara "Kina jina Aafia idan muka haɗu gobe a School zan baki wani magani sai ki zuba mata a abinci, cikin nata zai zube Shikenan" ita kuwa Aafia Allah sarki Rufee ta juya mata kwakwalwa, da murnan ta ta amsawa Rufee da to, tana kokarin katse kiran ne Rufee tace "Aafia ya batun Alhajin nan fa, kin ga next week zamu kammala Exam" shiru Aafia ta ɗan yi kafin tace "Okey idan mun fito class na karshe ranar da zamu gama Exam kenan, irin karfe biyun nan sai mu haɗu da shi, amma fa ba zan wuce 1 hour ba dan a ranar yaya Irfan zai yi diran dare kasar nan, kinga kuwa idan yaya Irfan ya dawo babu zancen fita ko kuwa hira a School, dan bincike yake wani lokaci muke da class yaushe kuma zamu fito class, kuma kinga ma next week zamu gama Exam idan muka gama ba zai taɓa barin mu mu fita zuwa wani waje ba tun da ba school, ko shopping sai dai ya kai mu da kan sa, haka yake ya cika takura shiyasa bana son ya dawo" yar tsaki Rufee tayi kafin tace "To shikenan zan faɗa wa Alhajin ba komai hour ɗayan ma yayi ai" daga haka sukayi sallama Aafia ta haye saman gadon tayi kwanciyar hankali kwance tana tunanin yadda cikin Aunty zai zube Yayin da ita kuma Umaisha ke ta fama da Aunty a asibiti, dan an karawa Aunty ruwa da kuma alluran zazzaɓi, dan sunce akoi zazzaɓi a jikin ta, yar aikin da Abbi ya kawo itace tazo ta goge wajen da Aunty tayi amai ta gyare wajen tsab. Wanan kenan abun dake faruwa a gidan Abbi bari mu leƙa Daular mutuwa mu gani meke faruwa a can. 👹DAULAR MUTUWA👹 Lokacin da su Ayla suka tashi daga sumar da suka yi, sun sha kukan ɗaukan Rimsha da akayi kamar ransu zai fita, baba da Mustapha ne suka yi ta basu hakuri, da kyar sukayi shiru, yayin da shi kuwa duna da kyar Queen ta yarda ta bashi ruwan tsafi su Barbushi suka bashi yasha kafafun sa suka koma kamar da, da farko Queen taki bashi ruwan tsafin nasu a cewar ta bata ga amfanin duna a gidan ba, sai da su Barbushi suka ta rokan ta sannan ta yarda ta ba shi, yana sha kuwa kafafun sa suka dawo dai dai, ya dawo bakin aikin sa wajen su Ayla kenan. Yana shigowa part ɗin nasu, da sauri ya wuce ɗakin baba, a nan ya isko su Ayla sai faman shasshekar kuka suke, kusa da su ya musu sannan ya dubi baba yace "Baba ku dai na damuwa dan basu kashe Rismha ba, sun rufe tane a ɗakin duhu na Queen dan ba zai yiwu su yanka ta yanzu ba, saboda Queen zata yi tafiya zuwa kasar Israel tace ranar da zata dawo ranar take bukatar a mata ferfesun naman Rimsha, yanzu abun da nake so da kai baba, ni dai kaga ba cikakken mutun ne kamar ku ba, rabi mutun rabi aljani nake, shiyasa tsafin su baya kamani, yanzu zan musulunta saboda Rimaha dan mu cetota, ba kunce duk abun da kuka roki Allah ku zai muku ba?" Gyaɗa masa kai baba yayi "To na san dai su Queen ba zasu bari kuyi wani abun addini a nan ba, zasu rufe muku baki, ku rinƙa roka mana Allah a ranku nasan zai ji kukan mu, amma akoi wani abu ɗaya da nake so ka sani, zan gwada karfin tsafi na na tsinke sarakunan da aka ɗaure Rimsha da su, daga nan zan fitar da ita daga ɗakin zuwa nan, to ina son ka sani dole da tsafi zan yi wannan kuma ina son ka roka mana Allah da ya kawar wa da Queen tunanin cin naman Rimsha, su kyale ta su manta da ita" sosai baba yaji daɗin zancen duna, farinciki fal ransu baba da Mustapha suka rinƙa sawa duna albarka suna masa fatan alkhari da fatan nasara Har ya miƙe zai fita, sai kuma ya dawo yace "Baba kafin muyi duk wanna aiki fa sai mun fara mantar da su wace ce Rimsha idan ba haka ba, muka ɗauko ta muka dawo da ita ma mun kira mutuwar mune gaba ɗayan mu dan dukkan mu zasu zo su kashe mu, yanzu zanje mayi aikin mantar da su komai shiyasa nace kuyi mana addu'a, sanna ba lallai na iya kai labari ba, dan tsafin su yafi nawa karfi, kuma idan nayi kuskure suka kama ni to wlh nasan kashe ni kawai zasu yi, dan haka tun yanzu muyi bankwana, zan iya mutuwa a kowani lokaci, amma ba zan mutu ban fitar da Rimsha daga fadar Queen ba" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, sai daɗi su Ayla suke ji Rimsha zata dawo, sai addu'a suke mata a ransu. A ɓangaren Rimsha kuwa, wani ɗaki ne mai bala'i duhun gaske suka kai ta, baka iya ganin komai a ɗakin saboda tsananin duhun dake ɗakin, ga wani fitinannen wari da karnin bala'i dake tashi a ɗakin, ga shi ɗakin ba'a zama sai dai tsayuwa kasan cewar kasan wajen wasu kifiyoyi ne masu bala'i kaifi da tsini a suke a wajen, iya in da suka tsayar da ita, iya wajen ne babu wayan nan kifiyoyi masu tsinin bala'i wadda suke iya fasa nama har kashi, sanna sun ɗaure ta da sarkoƙi masu bala'i karfi, sarka ne wadda aka yi shi da dafaffiyar karfe wadda babu wani abun da ya isa ya tsinƙa sa, da gani kasan wanna sarka na tsafin sune, farko da suka ɗaure ta da ta gaji da tsayuwa ta matso da kafar ta tana son zama Tana sako kafar ta kasan wajen wayan nan kifiyoyin suka cake mata tafin kafar ta har ciki kusa da kashin kafar ta, kan kace me jinin ta ya fara malala a wajen, Allah ma yasa bata ida sauke kafar ta a wajen ba shiyasa wayan nan mayun kifiyoyi basu mata illaba sosai ba, ta gaji da tsayuwa ga yinwa da kishin ruwa, ga bala'i duhu gaske, gashi yanayin ɗaurin da suka mata dole ta gaji dan sun buɗe mata hannu ne suka mata ɗaurin cros ɗayan hannun ta yayi gabas ɗayan kuma yayi yamma, kafafun ta kuma sun haɗe su waje guda saboda wayan nan kifiyoyin, ba halin tayi wani motsin kirki, tayi kuka har ta godewa Allah, ga bala'i zufa da ke damun ta, saboda ɗakin babu hanyar da iska zata shiga sosai, Tun tana iya kukan gajiya da yinwa da kishin ruwa har ta hakura ta fawwalawa Allah lamuran ta, dara daran sleeping eyes nata sunyi luhu luhu saboda kuka, duk sun kunbura sunyi jawaur da su, babban tashin hankali na biyu bata iya kiran sunan Allah, da zarar tayi yunkurin kiran sunan Allah sai Queen ta shaƙe mata maƙogwaran ta tayi ta fama tana shan azaba tana kuka, sai bayan wani ɗan lokacin sanna Queen ta sake ta, saboda wahalar da take sha wajen furta sunan Allah yasa ta dai na yunkurin furtawa ma kwata kwata, tayi shiru ta hakura tana kiran Allah'n a ranta, Allah sarki baiwar Allah, duna kuwa yana can yana kokarin fitar da ita da tsafin sa, dan shima abun ya sha kan sa yafi karfin tunanin sa, domin shu'umancin Queen ya wuci tunanin mai tunani. Wannan kenan mu leƙo Washington DC mu dawo 💞 WASHINGTON DC💞 4:00am Tsaye Romeo yake a balcony bedroom nasa ya goya hannun sa a saman kirjin sa ya zubawa garin nasu ido, yayin da iska dake kaɗawa yana ta watsa masa dark black curly hair sa kasan cewar bai ɗaure gashin nasa ba, jikin sa sanye da Ripped Jeans blue da Round neck polo shirt fara kal kamar yanzu ya ciro ta daga kwali, kasan cewar rigar nasa mai ƙaramin hannu ne hakan ya bada damar bayyanar murɗaɗun damatsan hannun sa, wayan dake cike kamar zasu fashe saboda ɗaga barfe da yake sosai, fuskar nan tasa kamar an aiko masa da sakon mutuwa a ɗaure take tamau babu alamar ya san menene dariya, hannun sa na ɗaure da diamond watch na su na Triplets, sai faman cizan lallausan lips nasa yake, alamar wani tunani yake yana yin yadda iskan nan ke kaɗa masa wanna dark black curly hair nasa abun gwanin ban sha'awa, domin har fuskar sa gashin ke bazo masa, Brady na kwance daga ɗan nesa da shi kusa da wata yar karamar pool dake wajen, sai kallon cikin ruwan Brady yake, yanayin nasu dai gwanin burgewa da ban sha'awa tare da ɗaukan hankali mai kallo. Almost 30mins yana tsaye a wajen shiru kamar ba shi a wajen, wayar sa dake ɗaure saman wata haɗaɗiyar karamar bed na kwanciya ka huta dake kusa da pool ɗin ne ta fara kara, tamkar bai ji ringing ɗin wayar ba yayi shiru, bai yi wani motsi da zata nuna yaji ringing ɗin ba, wayar ta katse kira na biyu ya shigo, haka kawai ya tsinci kan sa da jin yanayi mara daɗi a jikin sa, slowly ya juyo ya nufi in da wayar take, yana taku irin na jaruman maza, gently ya ɗauki wayar yana bin screen ɗin da kallo, heartbeat wato Michael shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ganin sunan Michael yasa yaji wani irin yanayi mara daɗi ya karu a jikin sa, a nitse yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru yana sauraron Michael ɗin. "Hello lion" shiru Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, ci-gaba da magana Michael yayi dan idan da sabo sun saba, kuma yasan Romeo ɗin yana jin sa "Lion I'm feel like I'm not feeling fine, tun ɗazun ina jin jiki na yana min zafi zuciya na yana bugawa da sauri sauri gaba na yana faɗuwa kamar ba lafiya ba, na rasa meke min daɗi yanzu zan bar white house in dawo gida kawai" shiru Romeo yayi na ɗan lokaci kafin yace "okey come back now" to Michael ya amsa da shi, a tsanake Romeo ya katse kiran tare da mai da wayar ya ajiye saman wannan bed ɗin, ya koma in da yake tsaye ya tsaya tare da zura hannayen sa a aljihun wandon sa, yayi shiru yana tunanin meke damun Michael. Tsayuwar 20mins yayi a wajen wayar sa ta sake fara rururi, shiru yayi yana jin yana yi mara daɗi a jikin sa, har wayar ta katse bai ɗaga ba, kira na biyu ya shigo, haka kawai ya tsinci kan sa da baya son ɗaukan kiran, shikuwa mai kiran nasa ya nace kamar dama yasan halin Romeo baya ɗaukan kira da wuri idan a ka masa, musamman idan yana wani abun sai ayi ta kiran sa ba zai ɗauka ba har sai ya gama abun da yake yi, baya haɗa abubuwa biyu lokaci guda a nitse yake yin komai nasa, ko tunanin wani abu yake aka kirasa tofa koma wanene mai kiran dole ya hakura har sai ya gama tunanin sa sannan. Ganin mai kiran nasa yaki dai na kiran ne yasa ya juyo gently ya nufi wajen wayar, dan ya kai 10 miss call mai kiran ya masa. Tyrone Shine sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar, lumshe dara daran ido sa yayi nan take zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana gwanin burgewa, a hankali ya sake buɗewa idon a kan screen ɗin wayar, gently ya kai hannun sa kamar bai son taɓa screen ɗin yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru bai yi magana ba Daga ɗayan ɓangaren Tyrone yace "Oga we are done the mission kuma munyi waning, mun kashe kowa dake wajen, sai dai akoi wani abu ɗaya da yake ɗaure mana kai" shiru Romeo ya ɗan yi kafin yace "What is this?" Cikin sauri Tyrone yace "Your watch sir, bayan mun kashe kowa, muna kokarin tattara bayanai da wasu evidence mun samu wani watch a wajen irin na hannun ka sak kamar shi ne ma" zaro blue eyes nasa waje yayi har sai da suka kara kwalli saboda zaro su da yayi Da ɗan karfi yace "What?!!" Sorry sir kawai Tyrone yake faɗi "Ku kawo min watch ɗin gida yanzun nan" ya faɗa tare da sauke wayar daga kunnen sa ya nufi hanyar komawa cikin bedroom nasa, daga nan ya fice daga bedroom ɗin gaba ɗaya ya sauka palon kasa. Palon babu kowa sai fitinannen kamshi air freshener da sanyin Ac dake tashi a palon, ko ina tsab tsab, ga haske ya karaɗe ko ina a cikin palon, dan har wutar jikin staircase a kunnen suke, shiyasa palon yayi haske sosai kuma hakan ba karamin kara kawata palon yayi ba. Saman Sofa set milk color ya nufa ya zauna a saman three-seater tare da jingina kan sa da jikin kujerar ya lumshe dara daran idon sa kamar mai jin barci. Zaman sa a wajen bai fi minti ashirin ba sai ga wasu jibga jibgan sojoji guda 6 masu jini a jika, jibga jibgan gaske ne masu ji da karfi da lafiya sun ƙoshi da training dan kowannen su ka gani kasan ya karɓi horo yadda ya dace, fuska nan tasu babu alaman imani bare tausayi a ɗaure take tamau, sai wani taku suke a jire, suka kariso gaban sa, sai da suka sara masa sanna suka tsugunna kasa, kasan cewar already yasan da zuwan su sai yayi shiru bai ɗago ya kalli su wanene bane. Sai da ya ɗauki 10mins a haka yana lumshe da ido sa, su kuma suna tsugunne a gaban sa, sannan ya ɗago kan sa tare da waro dara daran idon sa har sai da sojojin suka ɗan tsorata Gently yace "Tyrone where is the watch?" Cikin sauri Tyrone ya zura hannun sa cikin aljihun kakin jikin sa ya fito da watch ɗin ya miƙa wa Romeo, gently Romeo yasa hannu sa zai karɓa, sai kuma ya fasa ya zuwa ba Tyrone dara daran idon nan nasa, masu raza jaruman maza, kasan san cewar su Tyrone sun saba da shi, dan Tyrone ne baban yaron sa na biyu daga Tga ne na farko kenan, hakan yasa Tyrone ya dukar da kan sa kasa dan yasan me ya hana Romeo karɓan watch ɗin Murya na rawa cikin girmamawa yace "Sorry sir I thought is your watch, that is the reason why ban sanya handkerchief wajen ɗauka watch ɗin ba kuma ban damu ba nasa cikin aljihuna ina.... Bai kai karshen maganar ba Romeo ya ɗauke sa da wata mahaukacin gigitatchen mari mai sanya mutun dai ma jin motsin komai na ɗan lokaci, har wasu taurari Tyrone ya gani a face na sa, sai da idon sa suka yi jawur kamar jini saboda marin, abun ka da farar fata nan take shatin yatsun Romeo suka bayyana kwance a kumatun Tyrone raɗau, wajen yayi jawur kamar jini, kan kace me sai hawaye masu bala'i zafi suka fara bin kumatun Tyrone ɗin, an san soja da jarunta, amma fa duk jaruntar su idan Romeo ya mare su sai sunyi hawaye. A fusace Romeo ya miƙe ya damko wuyar kakin jikin Tyrone tare da haɗawa da wuyar sa ya shaƙe shi ya ɗaga shi sama, da karfi yayi wurgi da shi gefe, yau Tyrone ya ɓata masa rai, a kan me zai ce watch ɗin sa ne me yake nufi da hakan kenan , shima criminal ne kenan? Kan kace me yana yin Romeo ya sauya, idanun sa sun rikiɗe sunyi jawaur kamar wuta, gaba ɗaya jijiyoyin saman idon sa sun tashi, gashin jikin sa har wani miƙewa suke saboda ɓacin rai, jijiyoyin kan sa duk sun miƙe zara zara dasu, lokaci guda ya riƙeɗe ya zama asalin lion da daddy ke kiran sa da shi, har wata irin huci mai bala'i zafi yake fitar wa tamkar zakin da yayi shekara biyu babu abinci yanzu kuma ya samu abinci an hana shi ci, haka Romeo ya zama. Gadan gadan ya tinkari Tyrone, da hannu ɗaya ya damko wuyar sa tare da miƙer da shi tsaye, wani mahaukacin shaƙa yayiwa wuyar Tyrone ɗin har sai da idon Tyrone suka firfito waje kamar zasu faɗi kasa, wani irin zufar ɓacin rai ne ta fara gangarowa lion daga gefe da gefen kunnen sa, nan take wasu zara zaran jijiyoyi suka bayyana a wuyar sa yau ran maza ya ɓaci, Tyrone ya dangan tashi da manya manyan criminals na duniya, idan ya tuna hakan sai yaji zuciyar sa na tafasa kamar zata fasa kirjin sa ta fito waje A fusace yayi wurgi da Tyrone saman centre table glass dake tsakiyar sofa set Milk color, Watsa watsa tables ɗin yayi glass ɗin suka tarwatse pieces a wajen, wani razanannen ihu azaba Tyrone ya saki domin glass ɗin ya soke masa fuska, kan kace me jini ya fara fita daga face nasa, yana son bawa Romeo hakuri amma ya kasa, saboda wahalar da ya sha, sanna kuma ya san halin Lion idan yana hukunta ka kace masa sorry kara fusata shi zakayi har ya maka abun da baka taɓa tunani ba. Lion wato Romeo baya son kalmar sorry kwata kwata a rayuwar sa, hakan kara arzuƙa sa da fusata sa yake, idan yana hukunta ka kayi kuskuren ce masa yayi hakuri, to kashiga uku, kara masa ɓacin rai zakayi har ya kashe ka ba tare da ya sani ba, ya tsani kalmar sorry ne saboda mum ɗin sa, tun ranar da ta tsugunna a gaban su tace musu sorry yaji ya tsani wannan kalmar. Ko kaɗan lion bai damu da glass dake wajen ba tsabar ran maza ya ɓaci, ta kan fasassun glass ɗin yabi ya wuce ya damko wuyar Tyrone, sai faman nishi Tyrone yake kamar zai mutu, su kuwa sauran sojojin da suka zo tare da Tyrone tun Romeo bai biyo ta kan su ba sukayi neel down suka kama kunne suna jiran nasu hukuncin. Riƙo Tyrone da lion yayi ashe akoi glass a jikin rigar Tyrone ɗin, kasan cewar fatar Romeo soft skin ne sosai hakan yasa glass ɗin tayi masa wani wawan yankan a hannun ga kuma wanda ya bi ta kan su ya wuce duk sun suke masa kafa kasan cewar ɓacin rai yasa ya cire takalman kafan sa, wajen duk ya fara ɓaci da jini, amma lion ko ajikin sa, kamar ba jikin sa glass ɗin ta yanka ba, ɓacin rai yasa bai ma ji wani abu wai yanka a jikin sa ba, banda huci ba abun da yake fitar wa. Wani mahaukacin naushi ya kai wa Tyrone a gefen ciki, kasa kasa Tyrone ya saki ihun azaba, dan ya galabai ta sosai ko mumfashi baya iya yi da kyau bare ihu, da karfi lion ya shaƙe masa wuya, sai hucin yake sauke wa yana furzar da isaka mai bala'i zafi daga bakin sa, yana ji a ran sa ko kashe Tyrone yayi ba zai huce ba. A wannan hali su daddy suka fito da yar gudun su suka same su, dan sun ji hayaniyar fashewar glass a palon Ganin yadda Romeo ya shaƙe Tyrone kamar zai kashe shi ne, ga kuma Tyrone ɗin yana ta zaro ido waje alamar rai ya kusa yin hakin sa, hakan yasa Jay yayi shahada ya nufi Romeo da sauri yana faɗin "Please lion please and please let him go" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya kariso wajen, cikin sadaukar da rayuwar sa ya sanya hannun sa yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar Tyrone, amma ina ko motsa hannun Romeo Jay ya kasa yi, sai fama yake. A fusa ce Romeo yasa ɗayan hannun sa ya damko wuyar Jay ɗin ya haɗa su da Tyrone ya gwara kan su ji kake gwaram, wani gigitatchiyar ihu Jay ya fasa, kafin ya rufe baki, lion yayi wurgi da shi gefe guda saman dining table, shi kuwa Tyrone har lokacin yana shaƙe masa da wuya yaki sakin sa, dan ji yake ko kashe sa yayi ba zai huce ba, a kan me zai ce watch nasa ne a wajen wayan nan jiga jigan criminals ɗin, dan me zai dangan tasu, yanzu idan a gaban wasu ko yan jarida ya faɗa hakan ba shikenan sai suyi ta yaɗawa suce ashe The general of the army babban criminal ne na duniya ba shi ma Su daddy kuwa tun da sukaga yau Romeo wato lion ya daki wani soja da kaki a jikin sojan suka san lallai yau ran maza ya ɓaci, domin kuwa lion baya hora sojijin sa da kaki a hijin su dan kamar yadda suke girmama tutan kasar su haka suke girmama kakin sojojin su, amma yau ya daki Tyrone da kaki a jikin sa bai cire masa ba ya fara dukan sa tab yau ran Lion ya ɓaci. Sai da su daddy sukaga da gaske lion zai kashe Tyrone sanna sukayi kan sa da sauri suna faɗin "Please and please lion... Basu kari sa ba ya daka musu wani mahaukacin tsawa, wadda ya sanya dad da John sume wa a wajen, shi kuma uncle Herry ya kwasa da gudu yayi sama abun sa, shi kam Jay tun da Romeo yayi wurgi da shi daman ya sume a wajen Gaba ɗaya bodyguard dake wajen table sun fice daga palon tun farko da lion ya fara dukan Tyrone dan suna mutuwar tsoron lion fiye da tunanin mai tunani. A hankali Tga yake saukowa daga benen saboda har yanzu wajen na masa ciwo, sai dai yanzu yana iya sanya wando kuma ba laifi ya ɗan samu sauki, saboda Michael yaje ya shafa masa wajen yau da safe, yanzu ma hayaniyan da yaji a palon ne yasa ya lallaɓo ya sauƙo kasa dan yaga menene. Ganin abun dake faruwa na lion na shirin kashe Tyrone ne yasa Tga karisowa wajen da sauri, already Tyrone ya sume, hannun Tga yasa yana ɗan bubbuga bayan lion alamar rarrashi a fusace lion yayi wurgi da Tyrone tare da juyowa ya damki wuyar Tga, idon sa ya rufe ransa ya ɓaci, baya ji baya gani, bai san suwaye ke gaban sa ba, haka ya ɗaga Tga sama yayi wurgi da shi, gefe guda, Tankar zakin gaske Romeo ya zama yau Cikin fushi da ɓacin rai ya sanya hannun sa ya ɓanɓaro Makeken Tv su dake kunne yana magana ya dame sa da kara, da karfi ya ɗaga Tv sama yayi wurgi da shi a jikin bango, ji kake tarrsss Tv ya tarwatse kaca kaca, wani irin ihu yayi, har yanzu idan ya tuna maganar Tyrone sai yaji kamar ya sanya gun ya harbe kan sa dan haushi, gashi duk gidan ba wani wanda ya isa ya tinkari sa idan yana cikin farinciki ma bare kuma idan ransa ya ɓaci Da karfin gaske ya buga kan sa a jikin bango yana mai sauke wani irin numfashin wadda jin ta kawai ya isa yasa mutun suman tsaye, yau ina James ina Michael sune kaɗai ke iya sanyayawa lion rai idan ya shiga ɓacin rai gashi dukkan su basu nan. Kaca kaca lion yayi da palon nan, sai da ya fashe komai, har kujerun palon ɗaya bayan ɗaya ya rinƙa ɗaukan kujerun yana wurgi da su jikin bango, duk ya watsa komai ya fashe komai, duk da haka bai huce ba lokacin ne ma zuciyar sa ke kara tafarfasa tana masa zogin zafi, har Sojojin da suka zo da Tyrone sai da ya sumar da su gaba ɗayan su, ga hannun sa da kafafun sa sai zubar da jini suke, amma ina kamar ba jikin sa ba sam bai ji ba, yau ran maza ya ɓaci, sai faman fashe komai na palon yake, dan ya gama sumar da kowa dake palon, har goshin sa sai da ya fasa saboda buga kansa da jikin bango da yayi tayi, dan ɓaci rai. A hankali Tga ya miƙe dan shi bai suma ba, lallaɓawa yayi kar lion ya gansa, ya wuce ya haura saman bene da sauri ya wuce word room na su, Musharraf yana kwance yana barci bai san meke faruwa ba Sauri sauri Tga ya haɗa allura ya fito, a hankali ya lallaɓo ta baya ba tare da lion ya ankare ba, cikin sauri Tga ya caka masa alluran a wuya, nan take lion ya sulale kasa sumamme, nauyayyar ajiyar zuciya Tga ya sauƙe tare da ɗago ido yana bin palon da kallo, duk girman palon nan babu wani abu ɗaya da ya rage a mazaunin sa, duk Romeo ya watsa komai, yayi kaca kaca da ko'ina, duk wasu kayan fashe wa ya fashe su. Girgiza kai Tga yayi a filli yace "Lallai da alama yau muna da sauran kwana a duniya, haka shima palon nan yana da sauran kwana a duniya, badan haka ba da ba wani abun da zai saura wanda zaka iya gane wa kace wanna kaza ne a palon nan, to wai ma me ya haɗa lion sa da su Tyrone ne har ransa ya ɓaci?" Ya tambayi kan sa tambayar da bashi da amsa, a hankali ya dawo da kallon sa kan su daddy girgiza kai ya kuma yi kafin yace "daddy kai ma kana da problem kasan baka da lafiya kuma kasan halin lion idan aka ɓata masa rai baya ji baya gani riƙiɗewa yake ya zama lion ɗin da gaske, amma sai ka rinƙa zuwa wajen sa yana cikin ɓacin rai, kai kake ja ma kan ka ai" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi waje harabar gidan. Jim kaɗan ya dawo tare da jibga jibgan sojojin su masu jini a jika, manyan sojoji biyu suka ɗauki Romeo Tga ya musu jagora zuwa bedroom ɗin Romeo, dan ba wani sojan da ya san in da bedroom ɗin lion yake a cikin gidan, dan bai yarda dasu san in da bedroom ɗin nasa yake ba. Saman katafaren gadon sa suka kwatar da shi, sanna suka fito sukaje suka ɗauki su dad ko wanne suka kai shi ɗakin sa, sannan suka dawo suka kwashi su Tyrone suka wuce da su hospital A&E Accident and emergency, dan a basu taimakon gaggawa, dan dukkan su suna gaɓar mutuwa, sun ji bugun namiji, ai lion ba wasa ba, Ko da sukaje hospital ɗin ma sai da doctors ɗin suka tambayi sojojin shin da mota su Tyrone sukayi accident ne? Nan fa sojojin ke sanarwa doctors ɗin a kan cewa GAR ne ya dake su wato The general of the army, jin sunan Romeo yasa doctors ɗin su ka ja bakin su suka yi shiru suka fara aikin duba su, a ran kowannen su suna tunain ai in dai GAR ne ma ka ɗan ya musu, dan hukucin sa yafi haɗarin mota muni, idan ya zuciya ran sa ya ɓaci duk wani halitta mai rai dake wajen sai hantar cikin sa ta kaɗa, sai yaji kamshin lahira, domin Romeo fa yaci sunan sa da dad yace lion Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 36-37 Ko da sukaje hospital ɗin ma sai da doctors ɗin suka tambayi sojojin shin da mota su Tyrone sukayi accident ne? Nan fa sojojin ke sanarwa doctors ɗin a kan cewa GAR ne ya dake su wato The general of the army, jin sunan Romeo yasa doctors ɗin su ka ja bakin su suka yi shiru suka fara aikin duba su, a ran kowannen su suna tunain ai in dai GAR ne ma ka ɗan ya musu, dan hukucin sa yafi haɗarin mota muni, idan ya zuciya ran sa ya ɓaci duk wani halitta mai rai dake wajen sai hantar cikin sa ta kaɗa, sai yaji kamshin lahira, domin Romeo fa yaci sunan sa da dad yace lion A ɓangaren Tga kuwa, waya yayi a kan masu decoration na gida suzo su cire komai na palon nan su zuba sabbi, dan wayan nan duk sun tashi a aiki, duk Romeo ya fashe su. ba afi 10mins da kiran su da Tga yayi ba sai gasu da jibga jibgan motoncin masu ɗauke da manya manyan sofa masu numfashi wayan da suka amsa sunan su sofa, da kuma sauran kayan decorations, Tga ne ya lallaɓa kafar sa yaje ya tarbo su zuwa cikin palon ya nuna musu sanna ya wuce zai haura sama kenan idon sa ya sauka kan watch da Tyrone ya bawa Romeo A tunanin Tga watch ɗin Romeo ne dan yaga jikin watch ɗin duk jini, kuma ya san Romeo yaji ciwo a hannu, hakan yasa ya ɗauki watch ɗin ya wuce part ɗin Romeo. A saman bedside drawer ya ɗaurawa Romeo watch ɗin sanna ya fito ba tare da ya lura da watch dake hannun Romeo ɗin ba. Yana fita ya wuce bedroom nasa, dan yaje ya kwanta ya hutawa ran sa, saboda gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, wurgi da shi da Romeo yayi ba karamin zafi yaji ba, hakan yasa gaɓoɓin jikin sa duk suke masa ciwo. After some hours. Gaba ɗaya komai na palon kasa an sauya harta labulayen palo duk an zuba zabbi kal kal, sanna an kara sofa set, set ɗaya yanzu sun zama set biyar ne a cikin palon, ko ina yayi tsab gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali ga wani fitinanniyar kamshin air freshener da sanyin Ac dake tashi, an kunna sky blue light a cikin palon gaba ɗaya, hakan ba karamin karawa palon kyau yayi ba, ba zaka taɓa cewa palon da Romeo ya tarwatsa ɗazun bane, komai yayi need yanzu. Su daddy kuwa duk sun farfaɗo daga suman da suka yi Tga ne ya bawa dad maganin sa yasha dan jikin nasa kamar yana son tashi, A hankali lion ya sauko daga saman benen, yana tafiya kamar baya son taka kasa hannun sa na riƙe da watch da Tyrone ya kawo masa, ga kuma na sa watch ɗin a ɗaure a hannun sa, jikin sa na sanye da wando jeans guntu zuwa gwiwar sa, da yar riga mai ƙaramar hannun, hakan ya bawa damatsan hannun sa damar bayyana, suna cike tam kamar zasu fashe, fiskar nan tasa tayi fayau kamar wanda yayi rashin lafiya, a ɗauren fuskar tasa kamar kullun, bai ɗaure wanna kyakkyawan dark black curly sa ba, ya sake ta sai wani kyalli yake kamar ya shafa mata baby oil, sai tashin fitinanniyar kamshin perfume na sa yake perfume nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa da nitsar da zuciya, har yar rama yayi saboda abun da ya faru ɗazun, soft skin na san nan sai wani sheki yake, still hannun sa na ɗan zubar da jini, dan yaki duba hannun nasa, kafar sa kuma yana sanye cikin bedroom slippers masu kyau da tsada ga laushi. Saman sofa mai zaman mutun 2 yazo ya zauna ya jingina kan sa da sofar tare da ɗaga kan nasa sama yana tunain watch ɗin wanene wannan, yasan dai dole watch ɗin ɗaya daga cikin sune dan su uku kawai ke da irin watch ɗin, shi da kan sa yayi tattaki zuwa company nin apple ya basu design da yake so suka masa sanna kuma ya ja kusu kunne a kan karsu kuskura su yi wa wani design mai kama da nasu, dan baya son anko da wasu bayan Triplets nasa, shiyasa duk wani abu in dai nasa ne to ko kaje sayan irin sa ba zaka samu ba, dan shi baya sayan kaya kamar yadda kowa yake saye, aa shi sawa yake a buga masa design da yake so, kuma shi da Triplets nasa kaɗai akewa. Yayi nisa cikin tunanin sa na neman gano ya akayi watch ɗin ɗaya daga cikin su yaje wajen, dan shi bai yarda a cikin su ako criminal ba, ko da sunan wasa baya kawo wannan tunanin a ransa. Babu ko excuse Micheal ya shigo palon ya dawo daga white house, ganin an sauya komai na palon bai wani bashi mamaki ba dan yasan dama duk bayan 6 month suna canza komai na palo da ɗakunan su. Bai lura da Romeo a zaune a palon ba, ya wuce zai hau bene, kamar daga sama yaji zazzakar voice ɗin lion yace "Come here" da sauri ya juyo dan bai yi zaton ganin Romeo a palon kasa by this time around ba, cikin sauri ya juya ya koma kusa da Romeo ɗin ya zauna yana kallon face ɗin Romeo. Shiru Romeo ya ɗan yi na yan mintoci kafin ya ɗago ya kalle sa yace "Where is your watch?" Da sauri Michael ya duba hannun sa, babu watch na sa, ɗago ido yayi ya kalli Romeo, a nitse yace "Ban san in da watch ɗin yake ba" kwata kwata Michael ya mance da ya cire watch ɗin ya sanya a aljihun sa lokacin da president ya basa wata watch ɗin Kwata kwata Romeo bai kawo zargin su a ransa ba saboda yana musu kallon har yanzu basu mallaki wasu abubuwan da zasu iya shiga wannan harkan ba, bugu da kari kuma kullun yana tare da su, basu fita sai dai in zasu je wajen president a white house da kuma wajen partyn abokan su, shike fitar da su daga gidan kawai, bai damu ba kuma bai kawo wani tunani mara kyau nasu a ransa ba, shi tunanin ma da yake tun da Michael ya yasar da watch ɗin sa bai san in da yake ba, kila ɗaya daga cikin yaran criminals ɗin can su suka ɗauki watch ɗin tun da agogo ne mai bala'i tsada, sannan kuma criminals ɗin suna shiga mutane sosai kila da Michael ya yasar da agogon bai sani bane suka tsinta suka tafi da shi wajen. Miƙa wa Michael watch ɗin yayi yana faɗin "Gashi ka rinƙa kulawa" miƙo hannu Michael yayi zai karɓi agogon, lokacin idon Romeo ya sauka kan agogon da president ya bashi Kallo ɗaya Romeo yayiwa agogon yasan cewa daga wajen president agogon ya fito, dan akoi wani tambari a jiki, bai kawo wani abu a ransa ba, dan yana ganin kila Micheal da ya yasar da watch na sa ne yaje wajen president babu watch shine president ya basa wannna kyauta, dan haka sai bai ce komai ba, Karɓan watch ɗin Michael yayi yana turo ɗan karamin bakin nan nasa, yana son tashi ya tafi yaje ya kwata dan jiri yake ji, amma ba halin tashi domin kuwa bai isa Romeo ya kirasa sannan kuma ya tashi ya bar wajen ba, dole ya jira sai Romeo ya sallame sa. Miƙewa Romeo yayi ya nufi saman bene, zaro brown eyes nasa waje yayi a ɗan tsorace yace "Lion what happened to your hands naga jini na zuba ne" tamkar Romeo bai ji me Michael ya faɗa ba, ya wuce ya nufi part nasa ba tare da ya sake cewa Michael uppan ba. Ganin ya tafi bai masa magana ba yasa Michael kara turo baki ya miƙe da sauri yabi bayan sa. Dai dai zai shiga part ɗin Romeo, shi kuma Romeo har ya shiga yana fitowa, ɗan ja baya Michael yayi ya ba shi hanya, wucewa Romeo yayi jikin sa na sanye da puffer Jacket ya sanya hular jacket ɗin a kan sa, sannan ya sanya face mask, binsa da ido Michael yayi har ya fice daga palon kasa, shiru Michael yayi yana tunanin anya yau lafiya kuwa, me ya faru? Ina kuma lion zai je da irin wannan shiga haka? Ina James? Me ya samu lion a hannun sa yake jini? Sai jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su yake, daya ga tambayoyin suna neman su tarwatsa masa tunanin sa, sai ya hakura ya nufi hanyar part nasu, riƙe da agogon da Romeo ya bashi a hannun sa. Ko da yaje wajen shiga part nasu, kasan cewar part ɗin sa dana James a gere suke waje guda, gajiya tasa ya shige part ɗin James a mai maikon nasa part ɗin Yana zuwa yasa ruwa ya wanke jinin dake jikin watch ɗin ya kwance wanda president ya bashi, ya ɗaura wanda Romeo ya bashi yanzu, Yana ɗaurawa ya haye saman gadon James ya kwanta, dan jikin sa duk a mace ji yake kamar bashi da lafiya, ba zai iya yin komai ba, sai ya kwanta kawai yana mai da numfashi, yana kwanciya watch nasa dake aljihun jacket ɗin jikin sa ta faɗo saman gadon, shi kuwa ya lumshe ido alamar barci yazo, ba jimawa barci yayi awon gaba da shi, ga watch ɗin dukka biyu suna jere waje guda, dan hannun sa dake ɗaure da watch ɗin yana kusa da asalin watch nasa da ya faɗo daga aljihun sa, shi kuwa yayi barci bai gani ba. 🏞️Dajin Colorado🏞️ Cikin karkashin kasa, wani ɗaki ne mai girma gaske a karkashin kasan, matasa ne masu jini a jika wadda a kalla zasu kai su 10 a cikin ɗakin, ga wasu manya manyan disturb computers dake cikin ɗakin, gaba ɗaya ginin ɗakin ba da block akayi shi ba, da dutse a kayi shi, komai na cikin wannan ɗakin da dutse akayi su hatta tables ɗin da wayan nan disturb computers ɗin suke kai, da dutse akayi tables ɗin, kowani matashin aikin dake gaban sa kawai yake, sun dukufa suna aiki tukuru, kallo ɗaya zaka musu kasan sun samu horarwa mai kyau, dukkan su fuskar su babu alamar annuri a ɗaure take tamau. Daga wani keɓaɓen waje a cikin wannan ɗakin wutane yake ci awajen a gefe guda, gaba ɗaya cikin ɗakin ya kaure da ɗumi mai daɗin gaske Kyawawan matasan turawa ne wadda ba za su wuci saanin James da Michael ba, su uku ne tsaye kan James dake kwance saman wata lafiyayyiyar bed mai kyau da tsada, kallo ɗaya zaka yiwa matasannan kasan sun samu horo damin kowanne su jikin sa a murɗe yake kamar dai na James, sai aiki suke cikin kwarewa suna kokarin yiwa James dressing in da bullet ya ɗan kuskure sa, ba wani babban waje bane, kasan cewar bullet ɗin kuskuran sa tayi ta wuce. 10mins suka ɗauka suna wanke masa wajen da hydrogen, kafin nan su sanya masa bandeji su ɗaure wajen, duk da cewa sun sanya chemical da ya tsotse jinin wajen gaba ɗaya amma dai sun kara masa da bandeji saboda tsaro Kamar jira yake su kammala, suna gamawa ya miƙe tare da ɗaukan wani yar gora kusa da shi ya nufi wata yar hanya dake ɗan gefen su. Har ya ɗan yi nisa, sai kuma yaji karan wayar sa, da gudu ɗaya daga cikin matasan nan ya biyo bayan sa da wayar a hannun sa yazo ya miƙa masa. Karɓan wayar yayi tare da bin screen ɗin wayar da kallo, guntun tsaki yaja tare da mai da wayar aljihun sa ya ci-gaba da tafiyar sa, har cikin ransa yake jin raɗaɗin azaban zafin wajen da bullet nan ta kuskure sa, daurewa kawai yake yana tafiya. Wani waje ya shiga mai kamar ɗaki, wajen wani dutse mai kama da table ya nufa, yana zuwa ya cire wayar sa daga aljihun sa ya ajiye a gefen sa, sannan ya fara haɗa wasu chemicals masu bala'i karfi Wani gari ya ɗebo ya zuba cikin goran da ya ɗauko, sannan ya ɗauko wani kwalba dake ɗauke da wani ruwa kamar ruwan acid, cikin wannan garin ya zuba wannan ruwan kwalbar, shi da kan sa sai da ya ja baya lokacin da ya zuba wannna ruwan cikin garin, saboda karfin chemicals ɗin Yana zuba ruwan wani kara garin yayi kamar an zubawa tafasasshen mai ruwan sanyi, Zubawa chemicals ɗin ido yayi yana kallon yadda suke canza kamanni, After some minutes ya kara matsowa ya jawo wata yar akwati dake wajen ya buɗe ya ɗan yi dube duben sa dan ya tabbatar komai na ciki Ganin komai na ciki ne yasa ya rufe akwatin ya ɗauka tare da wannan chemical da ya haɗa ya juya ya nufi wasu maza guda biyu da suke sanye da kakin soja daya ɗaure su ɗaurin goro a wajen. Tun bai kariso wajen su ba, suke girgiza masa kai alamar suna son yin magana domin ya rufe musu baki, ko kallon arziki basu samu daga wajen saba bare kuma su sa ran zai iya tausaya musu. Wata yar kujera ya jawo ya zauna a gaban su tare da ajiye akwatin dake hannun sa da kuma chemical ɗin, Akwatin ya fara buɗe wa, ya ciro wasu manya manyan almakashi guda biyu, a hankali ya fara datsewa sojojin nan yatsun kafar su da wannan almakashi, ga azaba amma babu halin yin ihu dan ya rufe musu baki, sai mutsu mutsu suke alamar suna jin azaba. Yayin da James ke azabtar da wayan nan sojoji shi kuma Romeo yana can ɗakin hora masu laifi dake cikin gidan su, ya ɗaure manya maza su biyu, kana ganin su kaga marasa gaskiya, da alama yana son yi musu tambayoyi ne. Ɗakin horar war nasu ɗaki ne mai cike da manya manyan makamai da injuna na azabtar da ɗan Adam mai laifi, ga masuna kala kala na hukunta mutun, sannan akoi chemicals iri daban daban har da su acid da sauran mugayen abubuwa, kamar ɗakin yaki, sannan ɗakin yana da girma sosai ga jibga jibgan sojoji masu jini a jika kewaye da ɗakin ta waje saboda tsaro Gidan William jacop kenan gida ce hukumance mai zaman kanta, babu abun da ba zaka samu a cikin gidan ba, sai kotu, lawyer ma akoi alkalin ma suna da shi kotun ne kawai basu gina a cikin gidan, amma suna da asibitin su, suna da ɗakin horo, ɗakin doka, ɗakin karatu, duk wani abu mai mahimmanci suna da shi. Gaban wayan nan mazan Romeo ya zauna saman kujera suna fiskantar juna, yayin da ya ɗaure su saman a nasu kujeran, shima ya rufe musu baki ba damar suyi magana. Zubawa tattoo jikin su ido yayi yana kallon abun da suka zana A,N,D,L,R,C shine abun da suka rubuta ta ko'ina a jikin nasu, shiru yayi yana tunanin aina ya taɓa kallon wannan tambari, sosai ƙwaƙwalwar sa ke faɗa masa kamar a bedroom ɗin James ya taɓa gani, amma sai ƙaryata ƙwaƙwalwar nasa yake, dan baya son zargin yan uwan sa. Amma da yaga duk wani tunani da zai yi sunan James tunanin yake bashi sai ya fara wasu tunani, ya akayi James ya iya harbi da bindiga ranan? Ya akayi ya iya tsere da doki? Ina James yake yawan zuwa? Idan suka tambaye sa sai yace party yaje, yanzu ma gashi yace musu ya tafi party a New York, anya gaskiyane New York ya tafi kuwa? Wayan nan abubuwa suna kamanceceniya da juna, wani tunani ne ya sake faɗo masa, anya wannan watch ɗin na Michael ne kuwa? Nan take zuciyar sa ta fara bugawa da sauri sauri, cikin sauri ya ciro wayar sa ya fara bin hotonan wayan nan criminals ɗin yana kallo. Daga farko har karshe ya kalli hotonan, amma babu na James a ciki, da karfi da yaji ya tilasta wa zuciyar sa a kan James ba criminal bane dan haka ta dai na zargin sa, har wani yar firgice wa yayi lokaci guda dan zuciyar sa ta fara zargin James, kwakwalwan sa ba zata iya ɗaukan James a matsayin criminal ba, cikin sauri yayi kokarin ya kawar da wannan zargi da tunain banzan. Gently ya dawo da kallon sa kan wayan nan maza daya ɗaure, hannun sa ya sanya ya zame musu short ɗin jikin su gaba ɗaya, suka zauna tsirara ba komai ajikin su, dan dama already ya cire musu rigan jikin su kam, buɗe a kwatin dake gefen sa yayi ya ciro wani katon almakashi irin wanda James ya fitar yana yanke yatsun kafan sojijin can. Ajiye almakashi yayi a gefen sa, ya sanya hannu ya cire musu abun da ya rufe musu baki da shi, kamar jira suke ya cire musu suka fara magana, hannu ya ɗaga musu alamar baya son wani magana, shiru sukayi suna zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko. Gently cikin harshen Chinese ya fara tambayar su, abun da yake bukatan sani daga gare su. Sai faman zare ido suke cike da tsoro suka fara bashi amsa, muryan su sai kerman tsoro yake, har wani haɗiyar wahalallen yawo suke, suna ta haɗa zufa, kai da gani kasan sun gama tsorata over. Almost 20 mins suna yiwa lion bayani, nan take face na shi ta sauya idon sa sukayi jawur, a hankali ya furta "Josephine why?" A fusace ya ɗago hannun sa ya mai da musu bakin nasu ya rufe ya ɗauko wanna almakashin da ya ajiye a gefe. Babu alamar tausayi ko kaɗan a face nashi dan ya fusata, da karfi ya sanya almakashin ya datsewa ɗayan gaban sa, saboda azaban zafi wanda aka datsewa gaban nasa bai san lokacin da yayi baya baya da kujeran ya faɗi kasa ba, sai Allah kaɗai yasan me ye sukayi wa lion, babu ko tausayi ya datsewa ɗayan ma gaban sa, gashi ya rufe musu baki babu ta yadda zasu yi ihu sai mutsu mutsu suke kamar zusu mutu, ga hawaye wani na bin wani. Shi kuwa lion zuciyar sa sai tafasa yake masa kamar zata fasa kirjin sa ta fito waje, rai a ɓace ya ɗauko wani mashin ɗan karami mai tsini kamar kifiya ya saita saitin cinyar ɗaya daga cikin su, ya kunna mashin ɗin Yana kunnawa wannan tsinin jikin mashin ɗin ya fara fasa namar jikin mutumin yana ratsa cikin gashin sa A takaice wanna mashin ɗin har kashin cinyar wannan mutumin ta fasa ya fito ta kasa, gashi babu damar yin ihu ya rufe musu baki sai zafafan hawaye kawai suke fitar wa, gwanin ban tausayi, amma shi lion ko kaɗan babu alamar tausayi a fiskar sa Haka yayiwa ɗayan ma, ya fashe masu cinyoyin su har kashi, gashi ya yanke musu gaban su wato bananan su Sai da ya musu raga raga da cinyoyin su sannan ya miƙe rai a matukar ɓace ya fice daga wajen ya nufi cikin gida, ya bar su awajen suna zubar da jini, suna hawayen azaba. A ɓangaren James kuwa, tas ya datsewa sojojin nan yatsun kafafun su dana hannayen su, sannan ya ɗauko wannan chemical daya haɗa ya fara bin wajen da ya cire yatsun nasu yana zuba musu, ga kuma jinin dake zuba daga wajen, sai mutsu mutsu suke bala'i azaba suke ji, sun rasa ina zasu sanya ran su su ji sauki. Face ɗin James ta sauya tamkar ba shi ba, idon nan nasa sun yi jawur kamar jini asalin kamannin sa ya bayyana sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, alamar yana cikin matsanancin ɓacin rai. Bayan ya gama zuba musu chemical ɗin ne ya miƙe ya je ya ɗauki wayar sa ya fice ya barsu a wajen, nan take namar wajen da aka cire musu yatsun nasu ya fara dagargajewa saboda karfin chemical ɗin, sai zaro ido waje suke ga idon nasu yayi jawur Allah sarki bayin Allah abun tausayi, ko wai'wayan su James bai yi ba, ya wuce ya bar wajen. Sai da ya fito gaba ɗaya daga wajen ne ya ɗago hannun sa da niyar bari ya duba time a watch nasa, sai yaga babu watch ɗin, zaro idon sa waje yayi cike da tashin hankali ya fara taɓa aljihun sa, walam babu komai, da sauri ya juya ya koma cikin wajen nasu, ya koma in da ya kwanta aka masa treatment na hannun sa. A hargitse ya fara duba ko ina a wajen amma wayam babu, duk matasan dake wajen ya tambaye su, cikin girmamawa suka ce masa basu gani ba, sosai ya shiga damuwan ya zai yi da rayuwar sa, wannan watch ɗin tamkar rayuwar sa take, dan duk in da zai je idan yana tare da watch ɗin ji yake tamkar yana tare da Triplets nasa, babban damuwar sa ma idan Romeo ya tambaye sa ina watch ɗin me zai ce masa, tunani cike fal ransa, jikin sa ba kwari ya bar wajen ya nufi hotel ɗin da ya kama dan yace wa Romeo ya tafi party a New York sai gobe zai dawo shiyasa ya kama hotel. Yana shiga hotel ɗin wayar sa ta fara ringing, ko da ya ciro wayar sai yaga My lion ne ke kiran sa, cikin sauri ya saita nitsuwar tare da yin picking call ɗin, a nitse yace "Hello lion" daga ɗayan ɓangaren Romeo yace "Duk abun da kake ka bari ka dawo gida ina son ganin ka yanzu" kara zaro idon sa waje yayi ya ɗan juyo ya kalli ciwon hannun sa, a hankali yace "Okey give me 30mins" ɗiff Romeo ya katse kiran ba tare da ya sake magana ba. Wurgi da wayar James yayi a saman bed ɗin dakin hotel ɗin ya nufi toilet da sauri, Allah ma yasa ba wani ciwo sosai yaji ba, sauri sauri ya sakarwa kan sa shawa, ya fara wanka. Yana wanka yana tunanin yadda akayi watch na sa ya fita hannun sa, ya san dai lokacin da sojoji suka zo wajen taron nasu suka fara harbin bindiga yayi kokarin guduwa ya bar wajen, kasan cewar daman yasan da zuwan sojojin shiyasa ya shirya ta yadda zai gudu idan suka zo, sai dai an samu akasi dayayi yunkurin gudu wasu sojoji uku sunbi bayan sa, sai da ya tsaya yayi faɗa da su, ya kashe ɗaya ya kama biyu ya ɗaure su ya tafi da su, sune yaje yana azabtar dasu a wa can ɗakin, To abun da ya faru shine a wajen faɗan da yayi da sojojin ne watch nasa ta fita daga hannun sa ba tare da ya sani ba, kasan cewar ya jiwa sojan da ya kashe ciwo hakan yasa jikin watch nasa ta ɓaci da jini, wannan shine ta yadda akayi ya rabu da agogon kuma ta yadda aka samu jini a jikin agogon. Sosai James ya rinƙa tunanin ai na ya yasar da watch nasa, da kuma amsar da zai bawa Romeo idan ya tambaye sa ina agogon sa. Har ya gama wanka ya shirya abun da yake tunani kenan, High neck sleeve shirt ya sanya a jikin sa tare da Ripped Jeans sai ya ɗaura jacket ɗin su ta sukafi kauna wato puffer Jacket, sannan yasa Booth a kafar sa, ya canza kamar ba shi ba, ya fito sauri sauri ya shiga motar sa, da gudun gaske ya bar hotel ɗin ya nufi gida. A ɓangaren Romeo kuwa yana fita daga wannan ɗakin nasu na hora masu laifi kai tsaye bedroom na dad ya nufa ransa a matukar ɓace. Dad na kwance jikin sa duk yayi weak saboda maganin sa da Tga ya bashi, gefen sa Romeo yazo ya zauna, cike da ɓacin rai yace "Dad I want to talk to you" miƙewa zaune dad yayi har lokacin jikin sa na kerma dama haka ciwon nasa ke masa. Cikin harshen turanci sukayi magana mai ɗan tsawo da dad sannan ya kira James a waya yace yazo gida yana son ganin sa, daga haka sukayi sallma da dad ya fito ya wuce part nasa. After some minutes. Kamar wani mara gaskiya haka James ya shigo gidan, ko da yake dama ba gaskiyan gare shi ba, yasha mamakin ganin an canza komai na palon, ran sa cike da tunani kala kala ya haura sama. Kamar zai wuce part ɗin Romeo sai kuma yace bari ya shiga part ɗin sa ya sanya hulan sanyi a kan sa, dan kar Romeo ya masa faɗa, akan ya fita cikin sanyin nan babu hula a kan sa, da sauri ya shiga part ɗin sa, nan ya isko Michael yana ta zuba barcin sa hankali kwance Kai tsaye dressing room nasa ya nufa ya ɗauko hula ya fito ya tsaya gaban mirror dan ya duba jikin sa ko akoi wani abun da zai sa a gano sa, sai ya gyara Ganin babu wani abun da ya bayyana a jikin sa na rashin gaskiya ne yasa ya sanya hulan a kan sa yana kallon face ɗin sa, kamar a mafarki ta cikin mirror ya hango watch guda biyu a gere saman bed nasa, dana hannun Michael da kuma wadda ya faɗo daga aljihun Micheal ɗin. A sukwane ya juyo dan ya tabbatar wa idon sa abun da yake gani, ganin da gaske ne yasa ya karisa wajen da sauri ya sanya hannu ya ɗauki asalin na Michael wadda ta faɗo daga aljihun sa yana mamakin ya akayi watch ɗin sa ya dawo gida, to ko dai daman bai tafi da shi bane? Ya jefawa kan sa tambayar da bashi da amsar ta, tuna cewa Romeo na kiran sane yasa yayi saurin ɗaukan watch ɗin ya fice zuwa part ɗin Romeo. Yana tafiya a hanya ya ɗaura watch ɗin a hannun sa. A nitse yayiwa Romeo excuse sannan yashiga ɗakin, Romeo yana tsaye yana fiskantar balcony bedroom ɗin ya bawa kofar shigowa baya, James ɗan basaja nan fa ya fara basajan nasa ya murje kamar ba shi ba, har da murmushi yana faɗin "My blood how are you" Shiru Romeo yayi na yan mintoci Ba tare da ya juyo ya kalli James ɗin ba yace "where did Josephine live" Wato mum ɗin su kenan, James yayi shock da jin tambayar da Romeo ya masa, dan Romeo kwata kwata bai taɓa yin wani magana da ta shafi mum ɗin su ba, yau kawai ya tambayi ai nane location ɗin ta lallai akoi matsala kenan Cike da tsoro yace "Me ya faru? Me kuma tayi?" A takaice Romeo yace "zan je nayi warning ɗin tane" zaro ido James yayi dan yasan warning ɗin Romeo babu kyau a tsorace yace "Daman gobe zan yi tafiya zan biya ta wajen nayi warning ɗin nata please lion karkaje wajen ta ka bari naje" shiru Romeo yayi bai sake magana ba, James kuwa yayi amfani da kwarewar sa a fannin basaja ya rinƙa lallaɓa Romeo har ya hakura da zuwa New York wajen mum ɗin nasu, ba karamin daɗi James yaji ba, sallama ya yiwa Romeo ya fito ya nufi wajen Musharraf, ta cikin glass ɗin show glass dake gefen sa ta nan ta bi James da kallo yana son fahimtar wani abu, sosai ya zubawa watch ɗin hannun James dara daran idon nan nasa, har James ya fice, a ransa yana tunanin dole yayi bincike a kan James dan zuciyar sa ta dage da zargin James sosai, a hankali ya juyo ya koma saman bed nasa ya kwanta tare da lumshe dara daran idon sa yana tunani a kan James, yana jin babu daɗin a ransa har barci ta ɗauke sa. Mu leƙo Nigeria mu dawo 💞KATSINA💞 💞SUPER RESTAURANT💞 Shabiyu da minti arba'in Jehan ta fito daga wajen girkin restaurant ɗin hannun ta rike da tray mai ɗauke da plate dake shake da jolof rice yaji kayan haɗi sai kamshi yake, ga soyayyen ayaba wato plantain a gefe plate ɗin, sai coca colar ɗaya da ruwan faro, wani table ta nufa wadda wani matashin ke zaune a wajen yana latsa wayar sa, kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan karya ne, dan yadda yake wani bubbuɗe hanci yana kallon mutane kallon banza. Gaban sa tazo ta ɗaura masa abincin saman table ɗin ta juya zata tafi, a wulakance yace "Ke wace iriyar dakikiya ce? Wannan shine abun da nayi oder?" Shiru tayi ma shi kamar bata ji shi ba ta ci-gaba da tafiyar ta Tsawa ya daka mata "Ke ba dake nake bane?!!" Ci-gaba da tafiyar ta tayi dan ita bata cika kula ire iren wayan nan mutanen ba, a cewar ta basu da hankali, ita kuma bata kula mahaukata, ta san wannan hargagin duk me yake wa, dan yaga wasu yanmata sun shigo restaurant ɗin ne yake wannan hargagin banzan dan su ɗauka shi wani shegene yazo sayan abinci mai tsada, alhalin shinkafa yar 2k yazo ci. Ganin Jehan taki kula shine ga kuma yanmatan suna kallon sa hakan yasa yaji idan ya bar su Jehan haka yaji kunya wajen yanmatan nan, dan haka sai ya miƙe a fusace ya nufi wajen Ibraheem tun da shine mai controlling na restaurant ɗin, sai wani cika yake yana batsewa kamar wani shegen mai kuɗi, duk kuma yana yi ne kar yaji kunya a idon ƴanmatan nan. Ibraheem bawan Allah tun da Jehan tazo yake aikin kashe wuta, daga ta jajumo masa wannan sai ta jajumo masa wancan, yanzu ma yana zaune shiru yana latsa wayar sa cikin nishaɗi yana murmushi da alama abun da yake gani a cikin wayar tasa tana sashi nishaɗi, Kamar daga sama ya fara jin ruwan bala'i wannan mutumin da Jehan ta kaiwa abinci "Wannan wani irin iskanci ne? Nayi odar gasassun kaji da chip ma'aikaciyar ku ta kawomin yar gidan malam Shehu wato shinkafa, me za'ayi da wata yar gado itace gidan uban kowa, ni na wuce cin shinkafa wlh sai dai kaji, kuma abun haushi ina mata magana tayi banza dani, har kamar ni zaku yiwa wannan cin mutuncin, to wlh baku isa ba sai na sa an rufe wannan restaurant ɗin, kun san waye ni kuwa? To na ma fasa cin abinci a wannan kazamin restaurant ɗin, kun ɓata min rai!!!" Duk bala'i da yake Jehan na jin sa amma ko ajikin ta dan bai ishe ta kallo ba. Sai hakuri Ibraheem yake ba wa mutumin nan, amma yaki hakura ya dage shi ba zai ci abincin ba ya fasa Daga jin wannan zancen nasa kasan dama bai da kuɗin sayan abincin. Ba yadda Ibraheem bai bashi hakuri ba amma yaki yace ba zai ci ba kuma ba zai sake zuwa restaurant ɗin ba, sannan sai yasa an rufe restaurant ɗin yaga uban da zai buɗe Daga karshe dai shiru Ibraheem yayi yana jin sa, har ya kammala surfa ruwan masifar nasa ya juya zai bar wajen, karaf sukayi ido huɗu da Jehan dake tsaye a bayan sa Dogon tsaki yaja kafin yace "Ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar abun da kika min" daga kasa Jehan ta fara kallon sa zuwa sama, wani kazami da shi ta faɗa a ranta A takaice cikin kwanciyar hankali tace "Kuɗin abinci" zaro ido yayi yace "Ban gane kuɗin abinci ba, ai ga abincin ku can ban ci ba kuje ku ɗauki kayan ku" shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "Kai kasan baka ci ba, ni dai kuɗi zaka bani, domin in dai Jehan ce ta kawo maka abinci to ko kaci ko baka ci ba dole zaka biya kuɗi" Shi dai Ibraheem ido kawai ya zubawa wannan dirama na Jehan da mutumin, Rai a ɓace mutumin yace "Wannan ne kuma baki isa ba, bazan biya abun da ban ci ba" shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "Zaka bani kuɗi nane ko dai sai rai na ya ɓaci?!!" A wannan karon tayi maganar cikin harshen turanci, nan take yaji tsoro ya kama shi yadda Jehan ke magana da confidence yana sanya mutane da yawa tsorata suyi zaton ko yar wani ne ko kuma akoi abun da ta taka, amma kuma basu sani ba ita ma tsoron nata na ciki, kawai dannewa take tayi magana da confidence dan ta kwatar wa kan ta yanci, a tunanin ta idan ka nuna kana tsoro abune sai ya baka tsoron da gaske, amma idan kace baka san tsoro ba a filli sai abun yazo maka da sauki. Mutumin dai yaji kunya domin ya tsorata da Jehan dan ta tsaya with her full confidence tayi masa magana kamar wata yar uban wani ko ta taki wani tsiya. Ƙasa ya farayi da murya yana faɗin "Ni ba zan biya abun da ban ci ba" tsare sa da ido tayi bata sake masa magana ba, hakan ba karamin tsorata shi ya sake yi ba, dan gani yake kamar ko dai wannan kanwar maza ne, ma'ana irin kannen yan daban layin nan ne shi yasa take haka, ko kuma dai yar wani hamshakin ɗan daban ne, wadda idan ka taɓa ƴaƴan su suke kashe mutun Allah sarki bawan Allah shi kuma ta nan ya kai Jehan, ita kuwa ta tsaya kyam a fili babu alamar tsoro a fiskar ta amma a ciki sai dukan uku uku zuciyar ta keyi kamar zatayi fitsari a wando. Ibraheem na kokarin dannan Jehan a kan ta hakura mutumin ya tafi tun da bai ci abincin ba su su ɗauki asaran kawai, afili Ibraheem yayi magana kamar da gaske amma ba haka bane, yana tsoron kalaman mutumin ne da yake cewa zai iya sawa a rufe restaurant ɗin wadda idan hakan ta faru ogan su sai ya rufe shi a police station zai ce shi ya hadda sa komai, shine baya kula da costumers, sai dai ya manta wace ce Jehan dan in tayi magana ba wanda ya isa ya sata ta janye. Hannu ta ɗagawa Ibraheem kafin tace "Malam ka manta nace kada ka sake min magana ne? Ogan ka shine dai'dai nayi magana da shi ba kai ba, please karka sake shiga harka ta" shiru Ibraheem yayi dan shi kan shi Jehan na bashi tsoro wani lokaci, shi ɗaukan mai aljanu ma yake mata. Jehan kenan duk wanda ya zauna da ita tofa ɗaukan da zai mata daban. Ɗago dara daran idon ta tayi ta kalli agogon dake manne a bangon wajen 12:50pm ɗaure fuska tayi sosai cikin tsawa tace "Ka bani kuɗin abinci lokacin tafiya ta gida yayi!!!" Zaro ido Ibraheem yayi "Lokacin tafiyan ta gida yayi kuma?" Ibraheem ya mai'mai ta a zuciyar sa yana mamaki. Mutumin kuwa da yaga Jehan fa ba wasa take ba, sai ya hakura ya ciro 2k daga aljihun sa ya miƙa mata yana faɗin "kuje Allah ya isa na" karɓan kuɗin tayi abun ta ta wuce ta koma wajen girkin nasu, shi kuma mutumin haka ya wuce ya fice daga restaurant ɗin yana son cin abinci amma yana jin kunyar yaje yace zai ci yanmatan da yayi burga dan su su mashi dariya gashi kuma yinwa yake ji sosai haka ya hakura ya fice daga restaurant ɗin, Yana fita waje yace "Allah ya isa na munafukai yar 2k na ya tafi ni ban ci abinci ba, kuma bala'i yinwa nake ji wlh, gashi 500 ya ragemin a aljihuna, wayyo Allah rayuwar tiktok bakiyi ba nazo nayi video mai kyau ina cin lafiyayyen abinci, yanzu gashi na kare ni ba ga video ba, ban kuma ci abinci ba ba kuɗi ba ga kuma yinwa, kai kwata kwata rayuwar karya dai baiyi ba, dole na tuba na koma ga Allah, in godewa Allah da arzikin da yamin, daga yau a gidan ubana zan rinƙa video sai dai followas na su zaje ni ko su daina following nawa ina dalili in wuni ina fama da buga katako duk ƙusa tayi ta fasa mana hannun da kyar muke samu da wuya mu haɗa kujera, oga ya sallame mu naje na karar da kuɗin a yawon restaurant da hotel dan yin video fake life" kamar zararre haka ya tsaya yayi ta suruntan sa a bakin gate ɗin restaurant ɗin, har ya gaji ya kama kan sa ya wuce yana jan tsaki. A ɓangaren Ibraheem kuwa ba karamin daɗin yaji ba karɓan musu kuɗin da Jehan tayi wajen mutumin nan, sai dai kuma ta wani ɓangaren yana tsorace karfa da gaske mutumin nan zai iya sawa a rufe musu restaurant ɗin su, dan ɗan Adam ba abun renawa bane ta iya yiwu wa yana da hanyar da zai iya yin hakan. Sai tunai Ibraheem yake bai ankara ba sai yaga Jehan ta nufi hanyar fita daga restaurant ɗin, cikin sauri yace "Ke ina zakije?" Ko kallon in da yake ba tayi ba bare ya sa ran zata amsa masa ta wuce abun ta ta fice daga restaurant ɗin, baki sake Ibraheem ya bita da kallo yana tunanin yadda zai yi da ita. Jehan kenan mai abun ban mamaki ita da kan ta ta tsarawa kan ta lokacin zuwa aiki da lokacin tashi kamar restaurant ɗin nata ne ko na daddyn ta. Tana fita ta tari abun hawa ta hau zuwa anguwar su, dan tace sai taje gidan su taci uban Alhajin nan sannan ta dawo asibiti ta duba jikin mum, ba karamin haushin taji ba abun da Alhajin nan yayiwa Hanan ji take kamar idan ta ganshi ta shaƙe ɗan banza sai ya mutu, yau ta ɗaura niyar duk wanda ya dakatar da ita wajen ciwa wannan Alhajin mutunci tofa bazata ɗaga masa kafa ba, sai ta haɗe da shi duk taci uban su. Tun daga nesa take hango jama'a sun ɗan taru a kofar gidan su Sadiq wato gidan su na yanzu Tsabar sauri irin nata gani take mai mashin ɗin baya sauri dan haka sai tace ya sauke ta a wajen ta karisa da kafar ta zata fi sauri, yana sauke ta ta miƙa masa 500 bata tsaya ta karɓi chanji ba ta wuce, yana ce mata ga canjin ki amma ina bata ji ba, hankalin ta yayi wajen jama'ar nan dan tana zaton su Sadiq ke rikici da Alhajin. Ai kuwa zaton ta gaskiya ne hakan ne, Sadiq ne yake rikici da Alhajin da kuma baban sa, ga Hanan zaune saman dakali kofar gid tana kuka, jama'a suna ta bawa baban Sadiq hakuri, sai zuba ruwan bala'i baban Sadiq ɗin yake wai bai isa ya yiwa ƴaƴan sa magana ba, wannan mijin Hanan ne ya bashi auren ta zai ɗauke ta suje duba kaya a shopping Sadiq yace zai hana wlh ba zata saku ba, haka baban Sadiq ke ta surfa uban bala'i, shi kuma Sadiq ya kasa faɗin abun da Alhajin ke nufi da Hanan dan ya rufa wa kanwar sa asiri baya son kowa yasan abun da Alhajin ya mata jiya da daddare. Shikuwa Alhajin babu kunya ba tsoron Allah ya tsaya ya kafe ya tsare zai tafi da Hanan suje sayayyar kayan auren su, a yadda yake faɗawa jama'a kenan Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 38-39 Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa, cike da damuwa da tashin hankali ya ɗago kai ya fara bata labarin abun da yake faru, baban sa ya tara musu jama'a wai basa jin maganar sa mijin Hanan zai fita da ita suje sayayya shi Sadiq ɗin ya hana, ɗagowa Jehan tayi ta kalli Alhajin. Kara zaro ido tayi tana kallon sa tabbas tasan wannan fuskar amma ai na ta mance, shiru tayi tana tunanin ai na ta san wannan fuskar Ganin ta zubawa Alhajin ido tana kallon sa tayi shiru ne yasa Sadiq yace "Jehan lafiya" dago da kallon ta kan Sadiq ɗin tayi tana girgiza kai alamar babu komai, shesshekar kukan hakan yasa ta juyo ta kalle ta A takaice tace "Hanan tashi ki shiga gida" ƙin tashi Hanan tayi dan tana tsoron baban ta, Jehan ta fahinci abun da Hanan ɗin ke nufi, dan haka sai ta dawo da kallon ta kan baban Sadiq wadda yayi shiru saboda zuwan Jehan, yana tsoron aljanun Jehan na dare shiyasa yayi shiru "Kace mata ta shiga gida" Jehan ta faɗa tana kallon baban Sadiq ɗin, ba musu baban Sadiq yace "Tashi ki shiga cikin gida Hanan" da gudu Hanan ta tashi ta shige cikin gida, dan dama kamar a kan kaya take zaune. "Baba ya zaka ce ta shiga gida ban gane ba" cewar Alhajin, shiru Jehan tayi tana kallon su tana son taga ya zasu kare Cikin girmamawa baban Sadiq yace "Kayi hakuri Alhajin wani lokaci zaku je yanzu dai ka kyale ta" da sauri Alhajin yace "A'a baba ni yau nake son muje, yau nayi niyya" satar kallon Jehan baban Sadiq yayi kafin yace "Dan Allah kayi hakuri Alhaji" girgiza kai Alhajin yayi yana faɗin "Ina ba zai yiwa ba gaskiya kawai ta fito mu tafi" sai hakuri baban Sadiq ke bashi amma Alhajin nan ya murje ido yace sam bai yarda ba dole Hanan ta fito su tafi. Da dai Alhajin yaga da gaske baban Sadiq ba zai kira Hanan tazo su tafi ba, sai ya fara masifa yana faɗin baban Sadiq ya karɓe masa kuɗin sa akan ya bashi Auren Hanan, to wlh ba zai yarda ba dole yau Hanan ta fito su tafi, Yadda zaka gane da wata manufa a ran sa game da Hanan ɗin shiyasa ya dage a kan tazo su tafi. "Hanan ba zata fito ba kuma daga yau ma karka sake zuwa wajen Hanan idan ba haka ba duk abun da muka maka kai ka ja ma kan ka" cewar DPO wato Jehan, tayi maganar cikin kwanciyar hankali, kallon tsab Alhajin ya mata kafin yace "Idan Hanan ba zata zo ba ke zaki zo kenan? Dan naga kin fi Hanan ɗin hankali zaki fita iya zaɓen kayan sai mu tafi dake kawai a bar hanan ɗin" karo na farko da Jehan ta saki murmushi a rayuwar ta na yanzu, dan ita ko lokacin da suke tare da daddy ba ta murmushi bare dariya haka face nata yake a ɗaure tamau. Matsowa ta ɗan yi gaba kaɗan kasa kasa tace "Anya zaka iya fita da Jehan kuwa?" Tayi maganar tana murmushi, shiru Alhajin ya ɗan yi kafin yace "Amma ke kin san me kika faɗa kuwa" kashe masa ido ɗaya tayi kafin tace "Eh niko na san me nake faɗe cewa nayi mu tafi, idan zaka iya fita da ni, Jehan a shirye take" Tashin sense, shiru Alhajin yayi Jehan ta jefa sa cikin tunani, "anya wannan yarinya lafiyar ta kuwa, kai ina ga bata san me na shirya a tafiyar bane shiyasa amma bari na gwada ɗaukan ta muje in gani, idan bata san me na shirya ba, na samu ɓagas daman tafi Hanan komai da komai zan more tsuntsu daga sama gasashen" duk Wannan zancen a zuciyar sa yake sakawa. Yana cikin zancen zucin nasa ne muryan Jehan ta katse shi da cewa "Ko dai ka manta baka kama hotel ɗin bane? Au sorry na manta fa ashe gidan ka zamu je ba hotel ba, amma ina son sani wani abu ɗaya kafin mu tafi, a gidan naka babu kowa ko, ma'ana iyayen ka ba a nan suke ba ko? Dan ban cika son hayani ya ba" tashin hankali, wani irin dukan uku uku gaban Alhajin nan yayi, tunani ya kara shiga "Anya wannan yarinyar mutunce kuwa? Ita da kan ta ta kawo kan ta, to gaskiya ba lafiya take ba, kila tana da wani ciwon dai, dan mace mai lafiya kuma cikakkiyar mace kamar wannan ba zata miƙa kan ta haka ba, gata da ka ganta kaga cikakkiyar mace mai addini to meke shirin faruwa ne" Su Sadiq dai yau suna ganin ikon Allah Ganin yayi shiru yasa Jehan ta kara matsowa kusa da shi, kasa kasa tace "Farooq Salahuddeen Abubakar, right?" Zaro ido waje yayi yana kallon ta da mamaki ai ina ta san shi Bai gama tunanin sa ba muryan ta ta katse shi da cewa "Me yasa kayi shiru? Ka tsorata ne? To karkaji komai, amma dai ya kamata kasan wani abu guda, duk abubuwan da kayiwa Hanan jiya da daddare munyi audio recorded na voice naka, sannan duk wasu maganganu da kake mata a nan duk munyi recorded, dan kullun idan ka zo tana kunna karamar wayar ta tayi ta recording, so ina son ka sani idan ka sake dawowa cikin garin Katsina wlh sai na baza wannan recorded ɗin wa duniya kowa yaji, kasan dai ba wanda bai san muryan ka ba ko? Dan kullun kuna hawa kaban mike kuyi ta shirgawa mutane karya, kowa ya sheda wannan ɗan iskan muryan naka kamar na karuwar akuya, ka baro Abuja kana bin kauyuka kana lalata ƴaƴan mutane, dan bakin iyaye na bin ka ko? To mu nan munfi karfin yaro sai dai baban yaro wato Salahuddeen Abubakar ina ga shine dai dai mu, wato yanzu kun dai na neman mata a manyan birane saboda gudun cututtuka, sai ku shiga kauye ku yau dari ƴaƴan talakawa da sunan aure ku lalata musu rayuwa ku gudu ku barsu, wasu ma da ciki zaku gudu ku barsu, ayi ta haifan ƴaƴan da basu da uba suna tashi cikin wahala da kuncin rayuwa, ba ilimin boko bare Arabic, da sun girma su zama yan shaye shaye dan ba ilimi, saboda ire iren ku zan zama yar sanda, duk sai naci Kutumar uban ku, na tarwatsa muku tunani yan iska banza" duk wannan magana tayi shine cikin harshen turanci Tun da ta fara magana Farooq ya tsare ta da ido yake ta faman haɗiyar wahalallen yawu, sai zazzaro ido waje yake kamar wani ƙasurgumin munafuki, tunani yake wace ce Jehan, ai na kuma ta san shi farin sani haka, wayan nan tambayoyin duk ita ya dace yayiwa sai dai ba dama, dan cikin sa ya ɗuri ruwa, musamman da yaji sun yi recorded abubuwan da yayi ta faɗe a matsayin sa na kanin babban ɗan siyasa, idan wannan abun ya fita yake nan, gashi kuma ba wanda bai san voice na saba, wasu ma a media har tsokanar muryan nasa suke, saboda yana magana da sauri sauri kuma muryan tasa kamar na yar baby, irin munafukan muryoyin nan gare sa. A ɓangaren su Sadiq da sauran yan anguwa kuwa, sun zubawa Jehan da Farooq ido, sun kasa kunne suna son jin me Jehan take faɗawa Farooq, sai dai basu samu damar ji ba, dan ƙasa ƙasa Jehan tayi maganar saboda ita da kan ta bata son fitina, bata son kowa ya gane wace ce ita, kuma da turanci tayi maganar. A ruɗe Farooq ya shiga motar sa ya kunna, har lokacin yana kallon cikin idon Jehan yayin da itama take kallon cikin idon sa, sai dai Farooq ya kasa gane wace ce saboda fake face dake fiskar ta yasa bai gane wace ce ba, amma bashi da wani burin da ya wuce ya gane wace ce Jehan ai na kuma ta san shi, dan shi bai cika wani fitowa gidan Tv ba, sai dai ya taya yayan sa kanfen da muryan sa kawa, amma dai dayawan mutane sun san shi, sai dai ba kowa ya damu da fuskar tasa ba dan ba shi ne mai neman takarar ba yayan sane, tunani ɗaya yake, ko ma wace ce Jehan makusanciya ce a gare shi dan wannan sanin da ta masa ba sanin wasa bane farin sani ta mi shi. Ko uppan ya kasa cewa Jehan ya ja motar sa ya bar wajen yana tunanin ko dai kashe Jehan zai sa ayine, dan in wanna voice ɗin nasa ta fita shikenan ya gama yawo yayan sa ma ba zai bar shi ba, da tuni fal ransa na ya zai yi da Jehan, ya zai yi ya kwace Audio sa dake hannun ta haka ya bar layin gaba ɗaya tunani cike da ran sa, sai dai abun da bai sani ba ba wani recording da Jehan ta masa, kawai ta shirga masa karya ne dan ta ceci Hanan. Bayan ya tafi ne Sadiq ya matso wajen Jehan, dan tana tsaye tana bin motar Alhajin da kallo har ya bar layin nasu. "Jehan me kika ce masa haka, naga ya tafi da sauri kuma yana cikin tashin hankali har haka?" Cewar Sadiq, kamar jira Jehan take a mata magana ta juya da sauri ta wuce cikin gidan. A zaure ta wuce su maman Sadiq sunyi cirko cirko suna leƙo abun dake faruwa, kai tsaye ɗakin maman Sadiq ta wuce, ta faɗa saman yar katifar maman Sadiq ta hau kuka kamar karamar yarinya. Tashin hankali yau ga DPO Jehan tana kuka meke faruwa muje zuwa. A tare Sadiq da maman sa suka biyo bayan ta, kusa da ita maman Sadiq ta zauna yayin da shi kuma Sadiq ya zauna ta bakin kofa, in da ya saba zama. A hankali maman Sadiq ta shafa kan ta tana faɗin "Lafiya Jehan meke faruwa? Me ya saki kuka" ɗago wa tayi cikin kuka tace "Daddy na na tuna, Farooq ya tunamin da daddy na" ka san cewar su maman Sadiq sun san wace ce ita sai bata ɓoye musu waye Farooq ba da kuma abun da yake tsakanin su. "Yayan Farooq yana ɗaya daga cikin abokan takarar daddy na, ya taɓa zuwa har gidan mu, sannan kuma akoi hotunan su a wayar daddy na sosai, na san Farooq nasan halin sa, duk yan gidan su na san su, da Farooq da yayan sa sun taɓa zuwa har gidan mu wajen daddy na" ta kai karshen maganar tare da sake fashe wa da kuka, sosai maman Sadiq da Sadiq suka shiga bata baki suna rarrashin ta, da kyar suka samu tayi shiru ta hakura. Da sallama Hanan ta faɗo ɗakin da sauri taje ta rungumi Jehan, duk da zata girmi Jehan a shekaru amma sai tace "Aunty Nagode" shafa kan ta Jehan tayi murya a dashe tace "Ba komai Hanan" maman Sadiq ce ta tambaye su wai meke faruwa ne tsakanin Hanan da Alhajin nan, basu ɓoyewa maman Sadiq komai ba suka sanar da ita, sosai ta musu addu'ar kariya daga sharrin zina sai amsawa da amin suke. Sannan Jehan da Sadiq suka fito suka nufi asibiti, dan maman Sadiq tace musu anyiwa mum aiki cikin nasara, amma har yanzu bata farfaɗo ba likitoci sunce zuwa gobe da safe zata farfaɗo, tun safe maman Sadiq na asibitin sai shabiyun rana ta dawo gida. A tsakar gida suka wuce baban Sadiq da amarya, baban Sadiq yana zaune saman kujera yana tsinkewa amarya ganyen alayyaho zatayi musu miya, sosai Jehan ke jin haushin baban Sadiq kamar ta shake sa ya mutu kowa ya huta, wani kato da shi sai ya rinƙa biyewa yar amaryan nan tana sashi abubuwa kamar ƙaramin yaro. Amarya da baban Sadiq ɗin har suna haɗa baki wajen cewa "Sannun ku" ko kallon su Jehan bata yi ba ta wuce, shi kam Sadiq mamaki ne yake hana shi amsa sannun nasu, Allah sarki Sadiq bawan Allah bai saba ba, sai yaga abun kamar a mafarki. Sunyi Sa'a suna fita suka sami taxin suka hau zuwa asibiti. Mu koma muje mu leƙa su Umaisha wato gidan Abbi mu dawo sai muga ya jikin mum. 💞KADUNA💞 Sai karfe 4 na yamma sannan su Umaisha suka dawo gidan, ba laifi Aunty ta samu sauki sosai da sosai, taji kwarin jikin ta saboda ruwan da aka kara mata suna shiga Palo Umaisha ta wuce bedroom nasu, ita ma Aunty nata bedroom ɗin ta wuce, tana mai godiya ga Allah sanan tana yiwa Umaisha addu'ar fatan alkhari da fatan Allah ya tsare ta da tsarewar sa. Umaisha na shiga bedroom nasu wayar ta ya fara kara, dogon tsaki taja kafin ta kalli Aafia dake baje saman gado tayi ɗai ɗai tana barci, a ƙule ta ɗauki wayar kamar zata sa ihu dan haushi. Shiru tayi bata yi magana ba, shima Akil ɗin shiru yayi bai yi magana ba, almost 5mins suna manne da waya a kunne ba wanda yace da ɗan uwan sa uppan, da dai taga bashi da niyar yin magana sai tace "Hello" shiru yayi kamar ba zai amasa ba "Hello ina jin ka, kayi maganar da zakayi pls" ta sake faɗa tana hararar ɗakin nasu kamar Akil ɗin take gani a zahiri Cike da wannan izzar nasa yace "Lallai dole na koya miki hankali har ni zaki cewa kina jina nayi magana na ba, tom ki shirya gobe zan yiwa Nigeria diran mikiya, da safiya ina garin Kaduna, kuma ina sauka ki sani gidan mijin ki zaki wuce" shiru tayi kamar bata ji me yace ba, yana sane tana jin sa sarai amma taki yin magana, katse kiran yayi zuchiyar sa na tafasa ji yake tamkar ya ganshi a gaban ta yanzu, ya karya ta ya zauna kuma yayi jinyar kayan sa, yana bala'i kaunar ta sosai, sai dai baya ɗaukan raini ko kaɗan, shiyasa duk wani maganar da zai mata da umarni yake maganar. Ita kuwa yana katse kiran tayi wurgi da wayar saman gado tana faɗin "Dan wahala kawai, Allah ya kai mu goben in ga karshen rashin kunyar taka, yaro man kaza, gobe zan diro Nigeria ina zuwa zan ɗauke ki, eyee to sannu Sulman dan ba zance Abbi ba sai dai ince sannu baban Abbi" ta kai karshen surutan rashin kunyar nata tare da wucewa toilet dan tayi wanka, tun safe bata yi wanka ba, tana fama da Aunty a asibiti ti. A ɓangaren Abbi da daddyn Jelly kuwa, ko da Abbi yaje yaji abun dake faruwa, sosai hankalin sa yayi mugun tashi, ya shiga damuwa fiye da tunanin mai tunanin, bai yi kasa a gwiwa ba, ya ɗauko daddy dan su dawo Kaduna tare har sai angane in da Jelly take, idan ba haka ba barin daddy shi kaɗai babban haɗari, sannan Abbi ya sake hurawa jami'an tsaron Kano wuta akan su kara kokari wajen neman Jelly, shiyasa ma basu baro Kano da wuri ba sai karfe 4 na yamma, dan sunyi ta zarya tsakanin police station da gida, duk da daddy bai da lafiya amma sai da ya dage yayi ta bin Abbi, tare sukayi ta zarya, daga karshe suka kama hanyar Kd, Abbi yana jin kamar zai yi kuka, yaso faɗa wa su Imran amma daddy ya hana shi, yace ya bar su su rubuta Exam nasu cikin kwanciyar hankali da nitsuwa, to Abbi yace sannan ya hakura da zancen faɗa wa su Imran ɗin har sai sun dawo. A ɓangaren Jelly kuwa, yau dai anyi Sa'a da kan ta tayi jika jikan ta wato wanka bata fita ba sam, duk jikin ta sabulu da kumpa, Hajiya Turai tana palon bata ma san Jelly ta shiga wanka ba, yau ra'ayin kanta kawai tayi, da kan ta tayi wankan. Tana fitowa daga toilet ɗaure da towel ta nufi gaban mirror kamar yadda taga hajiya na mata, ita da kan ta sai sosa jikin ta wajen bayan wuyar ta take, saboda ta lapka sabulu a wajen kuma bata wanke ba, sai sosa wajen tare. Tana zuwa gaban mirror ta hau labta mai a kan sabulu da kumfa, gashi mai ɗin ma har da na gashi ta tabka dayawa dayawa, a takaice dai duk wani mai dake Wajen mirror sai da ta labka a fiskar ta zuwa jikin ta, sai kwailin take, har wani kyalli fatar ta keyi, fuskar ta taji mai har yana ɗiga Akan mai ɗin ta ɗauko Foundation da beauty blending ta fara labkawa shima, bayan ta gama ta ɗauki kwalli ta saka a kasan idon ta, kamar wata dodo haka ta zama, bata sa lipstick ba dan yau taji bata ra'ayi, fiskar nan nata yayi wani faw kamar jan kosai ko in ce kamar an ɗaye fatar biri, ga wajen idon ta yayi bakin kirin da kwalli, baka ganin komai a fiskar ta sai idon ta farare tas, idan ka haɗu da ita da daddare sai ka suma saboda tsoro, ta labka mai a saman labkakken sabulu da kumfa ga Foundation abun ba'a cewa komai. Bayan ta gama lafke lafken kwalliyar ta sai ta wuce wajen drawer kayan sawar Hajiya, dan duk wannan tsiya a bedroom ɗin Hajiya akayi shi, sai faman haɗa zufa take saboda uban mai da ta labka wa jikin ta. Tun bata karisa wajen drawer ba ta cire towel ɗin jikin ta tayi wurgi da shi saman bed, taje ta buɗe drawer kayan Hajiya, abuna farko da ta fara cin karo da su shine breziya da pant, ɗauko pant ɗin Hajiya tayi, ta ɗago shi sama tana kallo, kara zaro ido tayi, a sukwane ta kalli waist nata wato kugun ta, taga pant ɗin Hajiya wargajeje gari guda, irin ta biyar sai su shige cikin pant ɗin, sai jujjuya pant ɗin take wai ko zata samu wajen rage masa girma Da dai taga ba wajen rage masa girma, sai ta dura shi haka nan, dukka kafofin ta a site ɗaya ta haɗe su, wato a kafan pant ɗaya, sauran jikin pant ɗin da ya mata yawa kuma sai ta tattara ta ɗaure kamar mai ɗaure alale, ta cusa cikin ta saman kugun ta, sannan ta ɗauko breast, tayi shiru tana tunanin ya ake sawa, dan tabbas tana ganin shi a jikin Hajiya, sai dai koko ɗaya na breziyar Hajiya dai'dai yake da ya ɗauke breast nata dukka biyu, tashin sense, haka ta saka abun ta, koko ɗaya a breast nata ɗayan kuma a cikin ta, abun gwanin ban dariya, ga fuskar kamar an ɗaye fatar biri sai turo baki take. Sake sanya hannun ta tayi cikin drawer ta ɗauko wani shaddan Hajiya fari tas, yaji aiki sosai ɗinkin half gown da zani, rigar kawai ta sanya wadda yazo mata har idon sahu na kafar ta, dan Hajiya Turai irin hamshaƙan matan nan ne, ga tsawo ga kiɓa, ta ko ina masha Allah, a gefen faɗi kuwa, Jelly kamar tsinke ta zama cikin rigar Hajiya, abun gwanin ban dariya, kayi dariya har cikin ka yayi ciwo. Bayan ta gama duk wannan shirye shiryen nata, ta fito ta nufi palo da zumuɗin ta zata je ta nunawa Hajiya yau tayi abun arziki da kan ta. Hajiya na zaune a palo tana shan black tea ɗin ta, Kamar daga sama Jelly ta faɗo mata babu ko sallama, duk kiba irin na Hajiya ganin Jelly bai hana ta tashi a ɗari kamar siririyar mace ba, idan ana zancen cetan rai wake ta wani zancen kiba, to wannan ma hakane domin a tunanin Hajiya aljana ce, sai faɗin innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahirrahamanin rahim, a guje Hajiya fa ta zura tayi babban palon kasa tana ihu yau ga aljana a palon ta, Ganin Hajiya ta zura a guje tayi waje ne yasa Jelly tayi tunanin kila wani abun tsoro Hajiya ta gani, ita ma ai sai ta kwasa a kuje tabi bayan Hajiya tana ihu dan kar abun tsoron da Hajiya ta gani ya kama ta, bata san itace abun tsoron ba Hajiya kuma ganin Jelly na bin ta da gudu sai tayi tunanin Aljanar ke binta, dan haka sai ta kara karfin ihun ta dan jama'ar gidan su kawo mata ɗauki, ga firskar Jelly yasha daɓa daɓa da kayan make up sannan gashi ta sanya farar shadda, kuma burgujeje ya mata yawa, tana yawo a cikin kayan, ya kuke ganin abun zai kasance?. Da gudun gaske Hajiya Turai ta faɗa ɓangaren su Afnan, tana gudu tana ihu, a palon part ɗin su ta isko Afnan da Maman ta suna zaune, ganin Hajiya Turai a guje yasa suka miƙe suna faɗin "Ke Hajiya Turai me hakan, zaki shigo mana ba sallama, bamu san... Basu kai ga karisa maganar ba Jelly ta faɗo cikin palon da gudu, Subhanallah zokaga yadda ake gudun cetar rai, Afnan uwar rashin kunya, tuni ta watsa a guje tayi cikin ɗakin ta ta banko kofa, karo na farko a rayuwar Afnan da ta fara kiran sunan Allah data ga bone, ita kuwa maman Afnan ɗin, tsabar tsorata rungume Hajiya Turai tayi tana faɗin "Na shiga uku na lalace ki taimake ni Hajiya Turai, karki bari Aljanar nan ta kama ni" ita kan ta Hajiya Turai neman tsira take maman Afnan zata wani ce ta taimake ta, ture maman Afnan tayi ta bi bayan Afnan da dugu ta shige ɗaki, aiko itama maman Afnan bata yi kasa a gwiwa ba ta rufa musu baya, ita ma Jelly bin su da gudu tayi dan a tunanin ta wani abun tsoron suke gudun wa. Jelly na shiga ɗakin Afnan, suka fasa ihu a guje suka sake bazama waje, still itama Jelly tabi bayan su tana kuka. A takaice dai yau Jelly tasa gaba ɗaya familyn Abbo sun haɗu waje guda, wayan da basa shiri basa ko ga maciji yau sun haɗe waje guda saboda Jelly, dan ba wani part a cikin gidan dasu Hajiya turai basu faɗa da gudu suna ihu ba, duk kuma in da suka shiga sai yan part ɗin sun rufa musu baya suyi ta gudun cetan rai tare. Daga karshe dai tsakar gida suka koma suna yar tsere da Jelly, suna gudun ta, ita kuma tana gudun abun da suke gudu, domin a ɗaukan ta wani abun suke gudu, Allah sarki Hajiya Turai gata da ƙiba sosai haka Jelly tasa baiwar Allah nan ta rinƙa tikan gudu kamar mahauniya sai haki take tana mumfashi sama sama. A wannan yanayin na yar tsere da suke da Jelly Nawid ya shigo cikin gidan same su, dan yana ta horn ba wanda ya buɗe masa gate, dan mai gadin ma dayake mara hankali ne irin kauyawan nane wai sai ya ɗauko sanda yana bin Jelly zai make ta, idan kuma ta juyo ta kalle sa, sai ya fasa ihu ya shige bayan flowers. Nawid dai yaga tashin hankali dan kuwa ya rasa me ma zai yi, tsayuwa kawai yayi yana kallon yadda iyayen nasa da kannen sa har ma da yayyun sa mata ke gudu suna ihu, tun shigowar sa kallo ɗaya yayiwa Jelly ya gane ita ɗin ce, abun da bai ganeba shine gudun me iyayen nasa keyi, dan shi bai ga abun da suke wa gudun ba, saboda yaga Jelly ɗin na binsu ita ma tana gudun, gashi dukkan su sai ihu suke har da ita Jelly, shine abun ya kulle masa kai ya rasa me suke wa wannan gudu da ihun Afnan uwar rashin kunya yau tayi gudu ne har ta godewa Allah, gashi kuma sai addu'a suke aljananan wato Jelly taki ɓace wa, sai gudu suke daga masu kiran, ya Allah ka kawo mana ɗauki sai masu faɗin, Ya Rahman bayin ka suna cikin halin a ula'e, addu'a kala kala yau sun zuba shi, wasu ma basu san me suke faɗe ba kwata kwata saboda tashin hankali, duk abun da yazo bakin su suke faɗe. Shiru Nawid ya tsaya, sai da ya ga Hajiyar sa na kokarin zubewa kasa saboda gajiya sannan ya karisa wajen da sauri, cikin tsawa yace "Wai me hakan ne? Meke faruwa ne?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo Hajiya Turai, sai faman nuna masa Jelly Hajiya Turai take da hannun ta ta kasa magana, kallo Jelly yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Hajiya "Ummi me babyn kuma tayi yau kike gudun ta? Ko dan tayi wannan kwalliyar ne" sai lokacin Hajiya Turai ta waro idon ta da kyau ta kalli Jelly da kyau, daman su sauran yan gidan basu san Jelly ba bare su gane ta, dan bata taɓa zuwa part ɗin kowa ba, kullu tana tare da Hajiya Ganin Jelly ce da gaske yasa Hajiya Turai ta sake jikin ta tana faɗin "Ruwa a taimaka min da Ruwa" ba ita ka ɗai ba masu bukatar ruwan suna dayawa a wajen, mafi yawancin su sun baje a kasa suna a basu ruwa, girgiza kai Nawid yayi ya riƙo hannun Hajiya, da kyar da kyar take ɗaga kafar ta, suka wuce ciki, har sun ɗan yi nisa, ya juyo ya kalli Jelly dake tsaye, da hannu ya mata alama da tazo su tafi, da yar gudun ta ta kariso wajen sa suka shige cikin palo tare, su kuwa sauran sun baje a kasa suna ta neman agajin ruwa, mai gadi ma ya fito daga maɓoyar sa wato bayan flowers ya koma bakin gate yana faɗin "Amma wannan abu bai min daɗi ba, naso na make shagiya ta mutu, amma ba komai akoi gobe ma ai sai na make ta ta mutu ɗin" sai surutan sa yake shi kaɗai kamar wani zararre. Hajiya Turai suna shiga palon su, ta haye saman sofa mai zaman mutun 3 ta kwanta tana mai da numfashi, ruwa Nawid ya ɗauko mata mai sanyi a fridge ya bata tasha sannan ya wuce bedroom nasa, kusa da ita Jelly ta zauna tana kallo a Tv ko a jikin ta, Hajiya kuwa ta lumshe ido tana sauke mumfashi wahala, dan yau ta wahala fiye da tunain mai tunani, kun dai san yadda gudun mai ƙiba yake to hakane. Kun dai ji halin da Jelly ke ciki na saka mutanen gida motsa jiki, yanzu dai muje mu leƙo Washington DC mu dawo kafin nan kila Hajiya tayi barci ta huta, sai ta tashi tayiwa Jelly ɗin ku wanka... 💞WASHINGTON DC💞 James yana fita wajen Romeo kai tsaye word room ya nufa, zaune ya isko Musharraf, abun ku da na'urori na zamani sha yanzu magani yanzu, idan kana da kuɗi ba abubuwan da ba za'a maka ba, saboda kayan aiki na zamani da Dr William jacop yake da shi hakan yasa kafar Musharraf yayi saurin samun sauki, sai dai baya iya tafiya sosai kaɗan kaɗan yake ɗingisa kafar, amma yana iya tashi da kan sa ya zauna, kuma yana samu kulawa sosai a wajen dad da James, su kaɗai ke kula shi a gidan, shima dad dan bai san Musharraf Musulmi bane da ba zai kula shi ba. Gefen Musharraf ɗin James yazo ya zauna yana faɗin "Uncle are you feeling?" Murmushi Musharraf yayi kafin yace "My son I'm getting better" "what do you want to eat today uncle?" Sosai Musharraf yaji daɗi cike da matikar kaunar James yace "Gaskiya ina son cin miyar steew da akayi da kifi, da kuma shinkafa" okey James yace lafin ya miƙe ya ɗauko wa Musharraf kujeran tura mara sa lafiya wayan da ke da matsalar kafa Kamar baby haka James ya ɗaga Musharraf ya ɗaura sa saman kujerar yana faɗin "Muje ka ga gida, yau dai ka ɗan fita waje" sai murmushi Musharraf yake yaji daɗi sosai dan dama ya gaji da zama a ɗakin. James da kan sa ya turo Musharraf suka fito, kai tsaye palon kasa ya nufa, su dad gaba ɗayan su suna palon kasa suna zaune suna hira har da Michael mai barci ma ya taso yayi joined nasu. Suna ganin Musharraf suka ɗaure fuska, musamman uncle Herry da Tga da John, Jay ne yace "Kai James who is this man?" Dan su Jay kwata kwata basu san da zaman Musharraf a gidan ba, atakaice James ya faɗa musu waye Musharraf da kuma zaman me yake a gidan, nan fa suka ce basu yarda ba dole Musharraf ya bar gidan nan yau, a kai shi hospital ayi jinyar sa a can ba dai a gidan nan ba, kallo Michael James yayi kafin yace "Kana tare da su Michael? Kana son uncle ya bar gidan na?" James ya tambayi Michael ne dan yasan idan Michael yace baya son Musharraf ya zauna a gidan tofa ko zai mutu sai Musharraf ya bar gidan, dan lion ba zai yarda da zaman Musharraf ba muddin Michael baya so, amma idan Michael yana so to ya samu daman da zai tinkari Romeo ya neman wa Musharraf takardan izinin zama a gidan. Romeo yana da wata ka ida, ko wani irin mutun ne yazo gidan zai zana to fa ba zai yiwu ya zauna ba sai da takarda izinin zama gidan, misali yanzu idan daddy ya kawo abokin sa yace to ga abokin sa zai ɗan zauna da su a gidan, tofa sai ya sa hannu a takarda dan gidan su tana da takardan zama a cikin ta, ma'anar takardan nan kuwa, shine, misali bari ayi gwari gwari, idan bako yazo zai zauna dasu, Romeo zai tambaye sa zaman shekara nawa zai yi, idan yace shekara ɗaya, to Romeo zai rubuta a takardan sa, shekara ɗaya mutunmin zai yi, sai ya baka ka sa hannu, kana sanya hannu to ka dawo karkashin kulawar Romeo ko fita zakayi sai da izinin sa, dan shi baya yarda da mutane shiyasa, ba zai bari ka rinƙa fita da shiga gidan ba, sannan kuma baka isa kace zaka tafi wannan shekara ɗayan bata cika ba, baka isa ba, kome zai faru sai wannan shekaran ta cika, amma babban abun daɗin shine in dai ka samu takardan zama a gidan tofa kana cikin tsaro, dan Romeo zai kula da rayuwar ka duk in da zaka je zai iya sanya sojiji su raka, dan ka sanya hannu a takarda kamar ka zama ɗan gida ne, sai dai fa samun takardan izinin zama a gidan nasu ne, babban tashin hankali dan basu ma son bako, bare har ya samu wannan takarda, amma in ka samu lafiya Lou. Shiru palon yayi suna jiran amsar Michael, ya amince Musharraf ya zauna ne ko kuma bai amin ce ba, hannu Michael ya miƙa wa Musharraf yana faɗin "James is my blood, i love him more than everything in my life, duk abun da James yake so ina son shi dan haka uncle ɗin James kayi zaman ka tare da James ɗin ka" nan fa Tga ya bugi kirji yace uban kuturu yayi kaɗan bare na makawo, ba zai taɓa yarda ba dole Musharraf ya bar gidan. Miƙa hannu Musharraf yayi sukayi shaking hand da Michael, shi kuma James ya wuce ya haura sama ya bar Michael da Musharraf suna hira, su kuma su Tga suna surfa bala'i dole Musharraf ya bar gidan, kamar gidan su. Part ɗin Romeo James ya nufa dan yaje ya nemawa Musharraf takardan izinin zama a gidan, ko da ya shiga bedroom ɗin Romeo sai yaga kamar Romeo na barci, ganin haka yasa sai ya juya a hankali zai fita, kamar daga sama yaji sexy voice ɗin Romeo yace "James" da sauri ya juyo still idon Romeo a lumshe sai dai ba barci take ba Da sauri James ya koma kusa da shi ya zauna yana faɗin "Please my lion wata alfarma nazo nema" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, ci-gaba da magana James yayi dan yasan Romeo na jin sa sarai "Ina son ka bawa uncle na wadda na buge da mota takardan izinin zama a gidan nan dan su Uncle T da uncle Herry sun takura masa wai sai ya bargidan nan, ni kuma bana so ya tafi yanzu dan ya faɗa min bai da kowa" sai lokacin Romeo ya waro dara daran fararen idon sa tal kamar audiga masu ɗauke da kwayar ido blue, shiru ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma gently yace "Ba dai kai da Michael kuna son zaman shi a tare da ku ba?" Da sauri ya gyaɗa kai yana faɗin "Of course numa so" da hannu yayiwa James nuni da cikin drawer mirror sa, akan ya ɗauko takardan, cike da zumuɗi James yaje ya ɗauko takardun ya dawo ya miƙa masa, karɓa yayi ya ciri guda ɗaya ya miƙawa James ɗin yana faɗin "Ka kai masa ya karanta doka idan yayi agree fine ya sa hannu ka kawo min nima na sa hannu" da sauri James ya karɓa ya nufi waje. Har lokacin sai surutu su Tga suke a kan lallai Musharraf ba zai zauna a gidan ba, ganin James ya dawo riƙe da takardan izinin zama a gida ne yasa sukayi tsit kamar babu kowa a palon, dan sun san lion ya amince kenan basu da wani bakin magana kuma, James kan ko a jikin sa yazo ya miƙawa Musharraf takardan yana faɗin "include we need your signature here" karɓan yar takardan Musharraf yayi ya fara karanta dokokin kamar haka, shekara nawa zaka zauna, hannu Musharraf ya miƙawa James a kan ya bashi bairo, ba musu James ya ciro bairo daga gaban rigan Tga ya miƙa masa, haushi kamar Tga ya shaƙe su daga James ɗin har Musharraf ɗin duk su mutu. Wajen da aka rubuta shekara kawa zakayi, haka kawai Musharraf ya tsinci kan sa da rubuta 4 years bai yi tunain me zai je yazo ba, kawai ya damɓara shekara huɗu, doka ta biyu, idan ka sa hannun rayuwar ka ta zama a karkashin kulawar lion kuma sai abun da yace zakayi, Musharraf ya damɓara yes ba wani tunani, na uku, babu fita daga gidan nan babu zuwa ko ina sai da izinin lion, nan ma ya damɓara yes ya yarda kenan, na huɗu, baka isa kace zaka bar cikkin familyn William jacop ba har sai wannan shekaru da kace zakayi sun cika, nan ma ya damɓara yes, daga karshe ya sanya signature wato sa hannun sa, ya miƙa wa James, sai daɗi James yake ji ya wuce ya mayarwa Romeo takardan ya karɓa ya sa hannu sannan ya bawa James ɗin ya mayar in da ya ɗauko, Su uncle ba karamin haushi sukaji ba wannan ma basu san cewa Musharraf musulmi bane wata kila idan sun sani sai kisa kawai zasu masa, dan haushi. James na dawowa Palon ya wuce kitchen yaje ya sanar da sojojin dake musu girki a kan suyi miya da kifi yau, sun sha mamakin jin abun da James yace, amma basu da wani zaɓi abun da yan gida keso shi suke girka musu. Sosai James yayi yawo da Musharraf a cikin gidan, nan yake sanar masa anjuma da daddare zai yi tafiya, amma baya son kowa ya sani, har lion shiyasa ma zai yi tafiyar dare, shima Musharraf ɗin ya faɗa masa ne dan yasan ba zai faɗawa kowa ba, sosai Musharraf ya masa fatan alkhari da fatan nasara, haka suka ci-gaba da yawata cikin gidan suna hira. After some hours Gaba ɗaya family'n daddy sun haɗu a table dan cin abinci amma banda oga lion, sai kuma James da ya tafi kai wa Musharraf abincin sa, daga kaiwa Musharraf ɗin abinci sai ya zauna suka ɓige da hira, haka kawai yake bala'i kaunar Musharraf har cikin ran sa. Bodyguards dake serving nasu abinci ne suka fara zuba musu abincin Jin kalan kamshin da abincin keyi yasa gaba ɗayan su suka ɗago idon su a sukwane suna kallon kallo wa junan su, mamaki ya hana su magana, yau shinkafa da miyar steew kuma har da kifi da basa ci a gidan su, nan take ran kowannen su ya ɓaci, Michael yafi kowa shiga ɓacin rai dan saboda shine ma ba'a girka kifi a gidan, kwata kwata baya son kifi bai son ganin kifi, saboda shi Romeo ya kafa dokar kada a kuskura a girka kifi a gidan, ba'a taɓa girki da kifi ba, shiyasa sauran ma basu saba cin kifin ba, kuma suke kyamar kifin sosai, dan suna ganin kamar wani kazanta ne tun da lion ya hana girkawa, shi kuma James lokacin da yaje ya sanar da masu girkin su dafa miya da kifi, bawan Allah ya manta bai cewa sojojin iya abincin Musharraf kawai zasu girka da kifi ba, shi dai kawai yace suyi girki da kifi bai rabe musu ya zasu yi ba, shiyasa sukuma suka labta kifin wa gaba ɗaya jama'ar gidan. Jin warin kifin yasa Michael miƙewa da gudu ya haura sama, ya shiga part nasa, yaje toilet ya rinƙa kwara amai kamar zai amayar da hanjin cikin sa, gaba ɗaya bodyguards dake wajen sai da hantar cikin su ya kaɗa, saboda tsoron hukuncin da zasu fiskanta duk da basu sukayi girkin ba. A tare gaba ɗaya family dake saman table ɗin suka tashi da gudu sukabi bayan Michael dan sun san bawan Allah amai yake, tun yana yaro baya son ko kallon kifi da ido Shi kuwa James yana can yana zuba hirar sa da Musharraf, Musharraf na ba shi labarin tarihin rayuwar sa, sai dariya James yake kamar ba shi ba, can kuma ga Michael na tikar amai kamar zai amayar da ƴaƴan hanjin sa. Sosai family suka tausayawa Michael dan yayi amai ne har ya galabaita kamar zai amayar da kayan cikin sa duka, da kyar da ma kyarkyata ya samu amai ɗin ya dakata, rai a matukar ɓace ya fito ba tare da yayiwa su daddy magana ba, kai tsaye ɗakin ajiye makaman su ya wuce, babu kalan makamin da babu a ɗakin sai na kare dangi Wata iriyar wuƙa mai bala'i kaifin gaske wadda ke aiki da wata yar inji a jikin ta wadda akewa charji, idan aka kunna injin wannan wuka zata iya zaba ɗan adam gida biyu saboda kaifin balai da take da shi, wannan wukar Michael ya ɗauko ya nufi waje. Kai tsaye palon kasa ya koma su daddy suna biye da shi, cikin tsawa ya kira sojojin dake musu girki, sai wani huci yake kamar ɗan zaki, cikin sauri sojojin suka fito daga cikin Kitchen ɗin, kallon sa dad yayi kafin yace "Michael what are you going to do with this AK" sunan wukar kenan AK, "that I want to cut their hand" Tashin hankali kasa sojojin suka zube sunji Michael zai yanke musu hannu, ɗaya daga cikin su kam ma kuka ya fara yi dan yasan yaran William jacop basa maganan da ba zasu aikata ba, hakuri dad ya shiga bawa Michael yana lallaɓa sa akan ya kyale sojojin yayi hakuri ya tsaya suji dalilin da ya sa suka saka musu kifi a abinci, ina Michael yayi nisa baya jin kira ya dage sai ya yanke musu hannayen su, da sauri daddy yace da su jay su rike Michael kar su bari ya yanke wa sojojin nan hannu, Kin rike Michael ɗin su Jay sukayi dan mugunta sai ma kara ingiza shi suke, jikokin mugaye, su Jay akoi su da mugun ta zuciyar kafurci babu ɗigon imani, shi kuwa James da ya haddasa wannan bala'i yana can suna hira da Musharraf hankali kwance sai dariya yake bai san meke fatuwa ba, sai dai shima yaki cin abinci ko da Musharraf yace yaci, sai yace a'a basa cin kifi, basu saba ba, shi a tunanin sa iya Musharraf kawai akayiwa girki da kifi. Sojojin dake girkin kuwa sai kuka suke bayin Allah basu jiba basu gani ba za'a yanke musu hannun suna ji suna gani, ɗayan kam har da majina ya haɗe hawaye sharɓa sharɓa a fuskokin su, Tga har da cewa idan Michael ba zai yanke musu hannu ba ya bashi wukar bari shi ya yanke musu, mugun kafuri zuciya ba imani ba tawakkali, shekara wajen 8 sojojin nan suna yi musu girki ba'a taɓa samun matsala ba sai yau, yau ɗin ma matsalar daga wajen James aka samu shine bai musu bayani yadda ya kamata ba, amma su Tga sun murje ido sunce dole su yankewa sojojin nan hannun su, daga saman wajen hammatan su zasu yanke gaba ɗaya. A ɓangaren Romeo kuwa, tsaye yake gaban mirror ɗaure da towel mai laushi fari tas a kugun sa, soft skin na sa kaɗai abun kallo ne, yaji hutu sosai yana kwance lif sai sheki yake ga tsantsi kamar fatar jariri, kasan cewar babu riga a jikin sa, hakan ya bayyanar da kakkarfar suran jikin sa, Romeo yana da tsawo sosai, dan ya fi su James tsawo dukkan su, daga shi sai James Michael ne ya ɗauko tsawon mum ɗin su ɗan dai'dai da shi, James kuma tsawon uncle Tga ya ɗauko, Romeo kuma tsawon daddyn su, har ma yafi daddyn su tsawo kaɗan, amma shima daddy ba baya ba a tsawo. Romeo yana da buɗaɗen kirji sosai sannan gashi yana ɗaga karfe sosai wato gym kenan, hakan yasa kirjin nasa ya kara buɗe wa sosai kamar wani irin manya manyan zakunnan nan, wayan da suka riƙa, damtsen hannun sa kawai idan ka gani ya isa ya sa ka razana har kaji kamshin suma, breast nasa kuwa ba'a magana a cike suke bul bul gwanin burgewa, yana da korjinin bala'i wadda ganin sa yana cikin farinciki ma kawai yana sanya hantar manyan jaruman maza ta kaɗa, shiyasa mum nasu take cewa ganin lion yana cikin farinciki ma razana ta yake, ## Korjinin sa ya sanya idan yayiwa mutane tsawa suke iya mutuwa, gashi da bala'i farinjini kamar me, ba iya mace ka ɗai ba har maza idan suka ganshi kyasawa suke, maza ma bala'i san shi suke ina ga mata kuma ai ba'a magana, ko wani jinsi son shi suke kamar me, gashi kuma ko full face nasa basu sani ba, haka suke son shi, wasu da dama masoyan kyakkyawan kiran jikin sane, wasu kuma masoyan tarin dukiyar da Allah ya bashi, wasu masoyan matsayin sa a wajen aiki wato THE GENERAL OF THE ARMY, wasu kuma masoyan kuruciyar sa ne, da wuya a samu mai san shi dan Allah bacin iyayen sa da Triplets nasa, kullun fiskar sa a ɗaure take tamau kamar hadari bai san menene dariya ba. Sai faman shafawa kan sa tsadaddun hair cream nasa masu bala'i kamshi da kyau da tsada yake, ga gashin nasa sai kyalli yake yana wani curly gwanin ban sha'awa Mai kala uku ya shafa a kan nasa, duk wannan fitinannen kamshi mayu kan dake tashi daga gashin nasa hakan bai hana shi ɗaukan turaren gashin mai bala'i kamshi, ya sake fesawa curly hair na saba, dan shi ma'abocin kaunar kamshi ne sosai, kullun yana cikin zuba kamshi har kamshin turaren nasa ya kama jikin sa, ko bai sa turare ba kamshi yake zubawa, amma a haka sai ya saka. Bayan ya gama ne ya ɗauko almakashi ya rage tsawon wannan guntun gashin gaban goshin nasa, dan yanzu gashin ya ɗan yi tsawo ya zo masa har wajen gemu shi kuma bai san haka ya fison na gaban goshin ɗan guntu zuwa kyakkyawan dogon hancin sa, shiyasa duk bayan 1 week yake rage tsawon gashin gaban goshin ya bar na bayan da yake har tsakiyar bayan sa. Dressing room nasa ya nufa bayan ya gama shafe jikin sa da gashin kan sa da tsadaddun mayukan sa, 10mins ya ɗauka a dressing room ɗin sannan ya fito, jikin sa na sanye da pajama launin sky blue mai kyau da tsada, ya ɗaure gashin kan sa a baya, ya saki wannan ɗan guntu na gaban goshin da ya datsen ya kara rage mata tsawo yanzu, sai tashin fitinannen kamshi perfume nasa yake. Saman katafaren lallausan gadon sa ya haye tare da jawo laptop nasa dake saman bedside drawer ya kunna wutar gaban screen ɗin tare da cire password ya shiga bincike a kan James Kasan cewar ya saukar da idon sa kasa yana kallon screen na laptop ɗin hakan yasa idon nasa tayi kamar a rufe, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana, dan shi da Michael irin eyelashes ɗin daddy gare su dogaye sosai kamar sun kara dana kanti, ga gashin geran su kiris ya rage su haɗe da juna dan cikan gashi dake wajen, sai dai duk cikan gashin gerar nasu a kwance yake lif yana ta shaƙi kamar wayan da akayiwa make up, duk cikin su lips na Romeo ne yayi red sosai kamar ya sanya jan baki, shi Micheal lips nasa dark purple ne, shi kuma James red ne irin na Romeo sai dai bai kai na Romeo yin red sosai ba. Duk wannan badaƙala na yankewa sojoji masu yi musu girki hannaye da Michael ke shirin yi Romeo da James basu sani ba, suna nan suna aikin gaban su, Micheal na tsula tsiyar sa a palon kasa son ran sa... Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 40-41 Duk wannan badaƙala na yankewa sojoji masu yi musu girki hannaye da Michael ke shirin yi Romeo da James basu sani ba, suna nan suna aikin gaban su, Micheal na tsula tsiyar sa a palon kasa son ran sa. Da gaske Michael ya nufe su zai yanke musu hannu, nan fa suka fasa ihu mai karfin gaske, wadda ya sanya James fitowa da gudu dan yaga meke faruwa, shi kuwa Romeo daman kome za'ayi a cikin gidan baya tankawa in dai ba yaji muryan James da Michael ko daddy a cikin hayaniyar ba baya fitowa, ba ruwan sa baya shiga harkan kowa. Ganin abun dake faruwa yasa James saukowa kasa da yar gudun sa yana faɗin "Stop Michael" turo baki Michael yayi yana faɗin "Kifi fa suka saka a abinci" ɗan shafa kan sa James yayi dan yasan shi yasa su saka kifin, da murya irin na mai rarrashi yace "Sorry our heartbeat ni nace su saka kifi a abincin Musharraf, to nayi kuskure ban faɗa musu a nashi kawai zasu saka ba" miƙa wa John wukar AK Michael yayi yana faɗin "To suje su kwashe duk wani abun da ya taɓa kifin nan su zubar da shi, ko spoon karsu rage min bana so gani, kuma shima uncle ɗin naka ka faɗa masa ba'a cin kifi a gidan nan, ba dan ma ya sa hannu a takarda ba da ya bar gidan nan yanzu" ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun dad suka haura sama yana faɗin "My dad I'm so sorry kaji?" Gyaɗa masa kai daddy yayi yana shafa kan sa yana faɗin "Kun cika zuciya over kamar mum ɗin ku" ɗaure fuska Michael yayi kafin yace "Dad ka dai na maganar ta, I don't want" shiru dad yayi yana jin kaunar yaran nasa har cikin ransa Part ɗin Michael suka shiga sai shagwaɓa da sangarta Michael ke zubawa daddy, daddy kuma yana biye masa, dan yasan ba laifin sa bane matsalar daga kwakwalwan sane, Allah sarki Michael shi bashi da zafin zuciya sosai kamar na James da oga kwata kwata wato lion, ciwon sa yasa wani lokaci idan ya binkice sai ya zama kamar mahaukaci kamar mai tsananin zuciya, amma a zahirin gaskiya duk cikin triplets Michael yafi su saukin kai, dan shi bai yi karatu ba, cikin sauki zaka masa wayo kasa shi yayi maka abu koda baya so, kuma yana da saurin yarda da magana idan aka masa, shiyasa ko yayi fushi yake saurin sauka, shi James ba saukin kai gare shi ba kawai basaja yake, shi kuma oga lion ma ai ba'a magana karshe ne shi a zafin kai da zafin zuciya. A ɓangaren su James kuwa, umarni James ya bawa sojojin a kan su sake yin wani girkin wannan duk su kwasa su zubar da shi, sannan kamar yadda Michael yace duk wani kwanon da pots da suka san kifin nan ya taɓa to su zubar da kwanikan dukka har da tukanen, sai murna suke James ya cecesu Michael bai yanke musu hannu ba, har wani yar sakin fiska sukayi yau, sosai suka zubawa James godiya da fatan alkhari sannan suka amsa umarnin da ya basu, suka tashi suka koma bakin aikin su, dan su sake yiwa family'n daddy abinci, dan duka yaran daddy ba wanda ya iya cin abinci a waje, sai dai idan tafiya sukayi, shima tafiya idan suka san zasu fi kwana ɗaya a waje tofa ɗaukan mai aiki suke, duk wuya a gida suke cin abinci, su wasu irin mutane nen da suke da kyamar bala'i dukkan su karku cire kowa, suna da kyama sosai, ba kuma iya abinci suke kyama ba har da ɗan adam, haka suke, mu samman Romeo yafi kowa wannan ɗabiar yana da kyama over, sannan baya son wani ya raɓe sa, ammafa yana da kyauta sosai, ga sadaka duk wasu gidan marayu dake cikin birnin Washington DC kullun ranar Sunday yana kai musu ziyara na kyaututtuka masu yawan gaske, haka duk wani wajen bauta yana kai sada bai ware ko ɗaya ba, har masallaci, dan akoi wani babban masallacin ma wadda shi ya gina da kuɗin sa, haka akoi wani babban church da ya gina da kuɗin sa, time to time yana kai ziyara gidan tsofaffi da ga jiyayyu haɗe da makarantun gomnati, sannan a ɓangaren wasanni ma, irin su kwallon kafa da sauran su yana basu kyauta sosai, amma pannin wasanni yana bada kyautar ne saboda Michael, shi baya kallon kwallo da sauran su Michael ne mai kallon kwallo, to da Michael yaga Team nasu taci zai zo ya sanar da Romeo a kan ya musu kyauta, akoi islamiyoyi da dama da yake kai musu ziyara tare da kyaututtuka da dama, baya ware wani addini guda ɗaya yace ba zai musu kyautaba a'a idan ya tashi dukka addinan yake haɗawa ya basu kyauta, duk wasu manya manyan masallatai da church's dake birnin Washington DC ya sai musu manya manyan motocin na zuwa da'awa, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya ya kasan ce mai bala'i farinjini ta ko'ina, yana ɗaya daga cikin abun da ya sanya ya sawa ransa babu wani ɗan adam da zai soshi domin Allah sai dai dan kuɗin sa ko kyan sa ko mukamin sa a wajen aiki, hakan yasa ma baya yarda da kowa. Wucewa James yayi ya bar palon ya koma wajen Musharraf dan su ci-gaba da hiran su, Tga da John kwata kwata basu ji daɗi ba sun so Michael ya yankewa sojojin nan hannu da mugunta irin na zuciyar kafurci, cike da jin haushi suka wuce kowa ya koma bedroom na sa. Misalin karfe 8 Na dare Romeo na tsaye a balcony bedroom nasa ya goya hannayen sa a saman faffaɗar kirjin sa, saboda sanyin da ake sosai yasa ya sanya puffer Jacket nasa mai ɗan girma wadda yazo masa har gwiwar sa duk tsawon nan nasa, ya sanya hulan jacket ɗin a kan sa, ga wannan kyakkyawan guntun gashin gaban goshin nasa ba karamin kyau yake karawa fuskar sa ba, sai dai fuskar kamar kullun a ɗaure take tamau kamar hadari, sai tashin fitinannen kamshi yake, yayi shiru yana tunani a kan James Kamar a mafarki ya hango James a kasa harabar gidan, yana kokarin fita ta kofar sirrin su dake ta bayan wajen lambun daddy, zuba masa dara daran ido sa Romeo yayi yana kallon yadda yake lallaɓawa alamar mara gaskiya Ganin zai fice ne yasa Romeo yayi sauri Juyawa ya komo cikin ɗaki, ya shige dressing room nasa yana tunanin ina James zai je a daren nan da zai fita ta kofar sirri sannan kuma ba tare da motar sa zai fita ba, satar hanya zai yi kenan ko me. Jim kaɗan Romeo ya fito sanye da takalmi Booth baki mai shegen kyau a kafar sa, sannan ya sanya face mask a fiskar sa tare da hand gloves a hannun sa, ya sa bakin glass a idon sa, a takaice baka iya ganin komai nasa kuma ba zaka gane wanene ba, wayar sa ya ɗauka da sauri ya nufi waje dan yabi bayan James. Yana fitowa Palon sa sukayo ya karo da Michael yana kokarin shigowa, baya kaɗan Michael yayi ya bashi hanya, da sauri Romeo ya fice ba tare da ya kallin in da Michael ɗin yake ba, bin sa da ido Michael yayi yana mamakin ina zai je yake wannan saurin. Sai da Romeo ya kurewa ganin Michael sannan ya wuce ya karisa cikin bedroom ɗin, yana shiga ya faɗa saman lallausan katafaren bed ɗin Romeo yana wani sauke ajiyar zuciya. A hankali ya kai hannun sa ya kwance diamond watch nasu na Triplets dake hannun sa yana kokarin ɗaurawa saman bedside drawer kwatsam idon sa ya sauka a bayan watch ɗin, ganin wajen yayi tamkar anyi ajiya a wajen. Matso da agogon yayi sai tin fiskarsa ya zubawa agogon ido na yan mintoci kafin ya kai hannun sa ya zaro abun da idon sa ke gane masa, memory card ne guda biyu wadda James ya ajiye cikin agogon, sosai Michael ya sha ruwan mamaki tare da shiga ruɗun waye ya sa masa wannan memory's ɗin a cikin agogon sa, sai dai abun da bai sani ba wannan ɗin agogon James ne ba na shi ba Ɗayan hannun sa ya kai ya jawo laptop ɗin Romeo dake saman bedside drawer ya kawo gaban sa, kunna wutar screen ɗin yayi tare da cire password, kasan cewar already ya san password ɗin, nan fa idon sa yayi masa arba da abun da ya kara jefa kwakwalwan sa a cikin ruɗani, da sauri ya kara waro brown eyes nasa waje dan ganin abun da yake gani gaskiya ne tabbas idon sa gaskiya yake gane masa, kofar gidan mum ɗin sune Romeo ya sanyawa camera dan yaga masu shiga da masu fita, Michael yayi mamaki over, kenan duk wannan kiyayya da tsana da Romeo ke nunawa mahaifiyar su yana bata kulawa da kariya to yaushe ya fara yin hakan, da sauri Michael ya fara tariye camera'n baya dan yaga yaushe hakan ta fara faruwa bai sani ba, sai yaga ashe ɗazun ba jimawa aka sa camera'n bata ɗauki abubuwa da yawa ba, yasha mamaki sosai, fita wajen gaba ɗaya yayi ya ɗauko card reader a cikin bedside drawer ya sanya memory card guda ɗaya daga cikin biyun da ya fitar, ɗayan kuma ya ajiye saman laptop ɗin Sanya card reader yayi a laptop ɗin ya fara duba memory dan yaga menene a ciki ko zai gane waye ya sa masa memory's ɗin a jikin agogon sa. Bayanai ne na duk wani abubuwan har kallan su James, bayanai ne na daga in da suke sayo makamai har in da suke sayarwa, duk wani sheɗanci da suke yana cikin wannan memory, ga kuma hotonan manya manyan jiga jigan yan ta'addan na duniya, wasu ma ba wanda ya taɓa ganin hoton su, sai sunan su na ta'addanci kawai aka sani, sunyi kaurin suna wajen ta'addancin amma James yana da hotonan su duka, kasan cewar shi Micheal ba wani karatu ya tsaya yayi ba, sai bai gane komai da ke rubuce a wajen ba, kawai kallon rubutun yake, sai dai ya shiga folder nan ya fita ya shiga wannan amma ba wani abu da ya fahimtar, ga bayanan da gomnati da kuma Romeo suke nema ruwa a jallo Michael ya same su a ɓagas amma ba abun da ya fahimtar, kallon shirme ma yakewa bayanai dan rashin karatu, ba abun da ya iya karantawa aciki. Da yaga sai gayyan rubutu ne a wajen sai ya cire memory card ɗin, kamar zai sanya ɗayan memory ma ya gani, sai ya fasa ya kwashe su ya mai dasu cikin watch ɗin yana faɗin "Bari lion ya dawo na bashi na tambaye shi ko dai nashi ne shiya ajiye a wajen" da wannan tunanin ya mai da laptop ɗin saman drawer ya kwata yana kallon sama, kamar mai tunani. Abun da Michael bai sani ba shine ɗayan memory card ɗin videos ne makare a ciki na yadda suke shirya ta'addancin su har yadda James ke canza fiska ya shiga cikin yan ta'addan yayiwa kan sa video yana cikin ɗayan memory da Michael ɗin ya fasa sawa cikin laptop ɗin A ɓangaren su Romeo kuwa, shima ta kofar sirrin yabi ba tare da ya bari wani soja ya lura da fitar sa ba, dan bai son kowa yasan meke faruwa, idan ma wani abu James ke aikatawa to bai son kowa ya sani sai shi kaɗai, dan in wani yasan James na aika ta ba dai'dai ba maganar ba zata tsaya iya nan ba shiyasa yayi fitar sirri shima ko mota bai ɗauka ba. Sai sauri James yake Romeo na biye da shi a baya ba tare da ya sani ba, dan akoi tazara mai ɗan nisa a tsakanin su, saboda James ya riga Romeo fitowa. Sai da James ya fita daga anguwar su gaba ɗaya sannan ya nemi motar haya ya hau, shima Romeo karo na farko daya fara hawa motar haya, kaɗan kaɗan yacewa mai motar hayan nasa ya tafi a hankali kar James ya gansu. Suna cikin tafiya ne wata babban mota irin mai kwantena a bayan nan, irin na ɗaukan kaya tazo a guje saura kaɗan tabi ba kan motar su Romeo, kasan cewar hanyar akoi fitullun kan hanya masu bala'i haske, sun haske ko ina hakan ya bawa Romeo damar ganin motar da kyau, kasa kasa yace da driver motar hayan ya dakatar da mota, dan bai yarda da wancan motar da ta wuce su ba dan yadda take wannan uban gudu alamar rashin gaskiya ne, gashi kuma yana son bin bayan James, amma yafi son bin wancan motar saboda yasan ko ba komai dole James zai dawo gida kuma in ya dawo dole ya faɗa masa in da yaje, ita kuma motar idan ya barta ta tafi ba lallai ya sake ganin taba, dan haka sai yace da driver motar hayan daya juya subi wancan motar. Ba musu driver ya juya duk da bai san waye ya ɗauko a cikin taxi ɗin nasa ba, sosai wancan motar ke tsala gudu a kan hanya duk da girman ta, hakan yasa Romeo ya kara zargin motar sosai da sosai. Dai dai wani check point na kan hanya wasu yan sanda dake tsayawa a wajen suka dakatar da motar, shima Romeo dakatar da mai taxi ɗin sa yayi ya fito yace wa mai taxi ɗin "I'm coming" ya nufi wajen motar can, dai dai lokacin driver motar ya bawa ɗan sandan cin hanci, ba tare da yan sandan sun binciki motar ba sukace motar ta wuce dan sun karɓi cin hanci. Driver ya koma cikin motar yana kokarin tada motar Romeo bai yi wata wata ba ya fisgo driver motar yayi wurgi da shi waje, cikin sauri sauran dake cikin gaban motar suka fito, su biyu ne, da ka gansu kaga rikakkun yan daba, ga jikin sunan duk tabon shatin yan kan wuka, Saboda jacket da ya sa ya kuma saka hular a hansa ga face mask da glass a fiskar sa gashi dare ne hakan yasa har yan sandan dake wajen basu gane shi ba. A guje wayan nan yan daba biyun sukayi kan sa da nufin dukan sa, duk kan su duka ɗai'ɗai ya musu suka zube kasa kamar wasu kayan wanki Abun ku da rashin gaskiya irin na duniyar yanzu, sai yan sandan dake wajen suka ciro bindigu suka saita Romeo da shi wai ya ɗaga hannu sama ko su harbesa a kan me zai daki wayan nan mutane, saboda sun basu cin hanci yasa suke wannan hargagin, hakan da yan sandan sukawa Romeo yasa ya kara zargin su ya kara sawa a ransa kenan kullun motar tana wuce suna bata hanya kenan. Bai ɗaga hannun sa ba sai ya juyo yana kallon yan sandan, sun dage zasu harbe sa idan bai ɗaga hannu ba, a hankali ya ɗago kafar sa ya fara tinkarar su, sai kokarin harbin sa suke amma bindigar taki harbi saboda tsorata da sukayi jikin su nata kerma sun kasa danna kunamar bindigar da kyau, ɗaya daga cikin sune ya kira wayar over over akan a karo musu yan sanda ga ɗan ta'adda sun kama yana kokarin yi musu illah. Wannan danganta Romeo da ɗan ta'adda da sukayi hakan ya ɓata masa rai a fusace ya kwace bindugun hannun su, ya musu dukan tsiya, wadda ya sasu sumewa a wajen, da farko bai yi niyar dukan su ba, a matsayin su na jami'an tsaron yaso ya sa a cire musu kakin sune ma'ana a kore su daga aiki sannan a basu hukunci dan sune ɓata garin tun da su suke karɓan cin hanci su bar masu laifi su gudu, amma danganta shi da ɗan ta'adda da sukayi yasa ransa ya ɓaci ya musu dukan kawo wuka duk ya fashe musu fuska, shi kuwa driver taxi daya kawo Romeo tuni ya juya kan motar sa ya gudu, yaga Romeo na dukan yan daban nan kar ya shafesa dan shima bai san wa ya ɗauko a taxi ɗin nasa ba, shima cewa yake ko dai ɗan ta'adda ya ɗauko ne. Daman yan sanda uku ne a wajen lilis Romeo ya musu da duka, sannan ya ɗauki bindigar ɗaya daga cikin su yana kokarin har bin kwaɗon da aka rufe kwantenan bayan motar dan yaga me suka ɗauko suke wannan gudu haka bai kai ga harbin kwantenan ba sai yaji diran motoncin yan sanda, wanda wancan ɗan sandan ya kira office nasu a kan a turo yan sanda ga ɗan ta'adda sun kama. Zubawa motoncin yan sandan ido yayi ta cikin black glass nasa yana kallon su, motoci uku ne, suna iso wajen sukayi parking suka diro kasa suka kewaye sa da bindigun su, suna faɗin "you are under arrest keep this gun and raise up your hand" ka ajiye bindigar nan ka ɗaga hannun ka sama" shiru ya musu kamar bai ji me suka ce ba, abun ma haushi ya bashi, hannu yasa a aljihun sa, a sukwane yan sandan suka ja baya a tunanin su boom ko wani makamin zai ciro, haushi ma yaji kamar ya harbe yan sandan duka su mut dan a cewar sa basu da ammafa suna yan sanda suna da wannan tsoro haka, daga sa hannu a aljihun sa sun ja baya Wayar sa ya ciro suna ta ce masa ya ajiye wayar nan amma kamar ba da shi suke ba, latsa wayar nasa yayi na ɗan lokaci kafin ya mai da aljihun sa ya juya ya saita kwaɗon dake jikin kwantenan zai harba kenan ɗaya daga cikin yan sandan ya harbe bindigar hannun sa, bindigar ta faɗi kasa shi kuma bullet ɗin ta ɗan kuskure hannun sa, a fusace ya juyo yana kallon wanda yayi harbin Kwata kwata baya jin duka mutane yau kuma baya jin yin kisa, amma suna kure sa, tsawa yan sandan suka daga masa wai ya zube a kan gwiwowin sa, ran sa ya fara ɓaci yanzu, yana kokarin takawa ya tinkare su dan ya musu dukan mutuwa kenan sai wajen gaba ɗaya ya karaɗe da jiniyan jiga jigan motoncin sojoji masu numfashi kai daga jin jiniyar ma kasan ba sojojin wasa ne ke tunkarar wajen ba, dakata wa yayi dan shi ya kirasu a kan suzo su tafi da gaba ɗaya yan sandan nan, dan yana da aiki a kan James sosai so baya son ransa ya ɓaci yau, yana son cikin nitsuwa idan James ya dawo suyi magana shiyasa ya kira sojojin. A ɓangaren yan sandan kuwa sai murna suke wai an turo musu sojoji kila manyan su sun samu labarin babban ɗan ta'adda ne suka kama shiyasa suka haɗa musu da sojoji, sai dai abun da ya ɗaure musu kai, wannan jiniyar na motar jiga jigan sojojin kasan ne, kenan manya manyan sojoji kamar wayan nan zasu iya kawo wa kananan yan sanda kamar su ɗauki, abun ya basu mamaki amma dai sun zuba ido suna jiran suga me ke shirin faruwa. Jibga jibgan motoncin masu numfashi shabiyu ne suka iso wajen, wasu jibga jibgan sojojin masu jini a jika, fararen American tas da su, gasu da kirar karfi sun samu horo mai kyau, fuskokin nan nasu kamar hadari babu wasa a ɗaure take tamau ba su san menene dariya ba, ganin wayan nan sojojin kawai ya isa ya sa rundunar mutane zuciyar su ya buga su mutu saboda tsoro. Ji kake dip dip, suna dirowa kasa daga bayan motocin su, da gudu wasu suka kewaye Romeo dake tsaye, wasu kuma suka kewaye wannan motar yan ta'addan wasu kuma suka kewaye gaba ɗaya kan titi daga ta in da suke, hannun su na rike da jiga jigan bindigogi wayan da suka amsa sunan su bindiga, wadda baya saɓa saiti in da ka aikashi nan zan wuce kai tsaye, ba irin makaman kananan yan sanda da sojoji bane. Ɗaya daga cikin yan sandan ne yace da sojojin "Yauwa wannan shine ɗan ta'addan ku kama shi, ɗan tada kayan baya ne, yazo ya fara dukan jami'an tsaron mu ya.... Bai kai karshen maganar ba sojan ɗaya ya daka masa wani gigitacen tsawa wadda ya sanya gaba ɗaya yan sandan dake wajen zubewa kasa a kan gwiwowin su, tsabar tsoro jikin su sai kerma yake A hankali Romeo ya zame hular kan sa tare da karɓan bindigar ɗaya daga cikin sojojin sa, ya sai ta kwaɗon jikin kwantenan motar yan ta'addan can, ya harbe kwaɗo, kofar ta buɗe Ji kake dip dip da gudu sojoji biyu suka zo suka buɗe masa kofar contenan, yan mata ne cike a ciki duk basa cikin hayyacin su an musu allura fita daga hayyacin su, kallo ɗaya Romeo ya musu ya kawar da kan sa gefe ya juya tare da cire hand gloves dake hannun sa ya nufi mota ɗaya daga cikin motocin da sojojin sa sukazo yanzu. Lokacin da Romeo ya cire hulan kan sa kamannin sa suka bayyana tsoro yasa yan sandan dake wajen sume saboda babu wani ɗan adam dake cikin birnin Washington DC da baya tsoron Romeo bare kuma su da suka masa laifi har da harbin bindigar hannun sa tab, sun gama sadaukarwa yau mutuwa zasu yi, shiyasa suka fara da suma tun ma basu ji hukuncin da zai yanke musu ba. Shi kuwa bai bi ta kan su ba ma dan yana da abun yi, motar sojojin sa ya nufa, da gudu jibga jibgan sojoji biyu suka nufe sa, suka buɗe masa kofar motar gidan gaba, shiga yayi ya zauna sannan gently yace su kai masa wayan nan yan ta'addan gida zai yi aiki a kan su da kan shi, motar yan ta'addan kuma su kai headquarter su ajiye zuwa da safe yan sandan nan kuma su kira president su sanar da shi ya soke aikin su, dan dukkan su basu san aikin da suke ba. Ɗaya daga cikin sojojin sane ya shiga motar ya mata key yaja sa zuwa gida, har cikin gida ya shiga da Romeo, yana yin parking ya fito ya buɗe masa kofar motar, gently Romeo ya sako kafar sa waje kafin ya fito gaba ɗaya ya nufi cikin gida, shikuma sojan ya juya kan motar ya koma wajen sauran sojojin can dan suyi aikin da lion ya saka su. Lokacin da Romeo ya shiga bedroom nasa, Micheal na kwance masa saman katafaren gadon sa idon sa a lumshe da alama barci yake, wuce sa Romeo yayi yaje ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kayan barci masu kyau da tsada launin sky blue riga da dogon wando mara sa nauyi. Sai tashin fitinannen kamshi yake ya saki dark black curly hair sa har baya, ya haye saman bed nasa kusa da Michael ya jawo laptop nasa ya fara aikin bincike a kan James. Number wayar James ya shigar cikin laptop ɗin nasa ya fara kokarin bin diddigin in da James ɗin yake, yasha mamaki ganin number James yana shararin sama niya, kenan jirgi James ya hau zuwa ina to? Shiru Romeo yayi yana mamakin ina James zai je bai sanar da shi ba, kuma dole yasan tafiya zata fita cikin Washington DC, har James zai iya fita cikin garin nan ba tare da sani na ba? Sai jerowa kan sa tambayoyi wadda bashi da amsar su yake, "gaskiya nayi sake na biye musu ina musu abun da suke so, daman dan suje suyi ta tsula tsiyar su a waje ne yasa sukace basa son bodyguards ko sojoji surinƙa binsu idan zasu fita, nayi kuskuren yarda da hakan da nayi" sosai Romeo yake tunani a zuciyar, daga karshe dai sai ya fara binciken wace jirgi James ya hau kuma ina zai je, me ya fitar da shi cikin Washington DC da daddaren nan kuma da jirgin kasuwa abun da basu taɓa yi ba, koda yawon shakatawa su James zasu je wata kasa jet ɗin sa yake badawa a kai su duk in da zasu je dan tsaro, amma yau James ya saci hanya ya hau jirgin kasuwa why. Duk wani binciken da yayi a wannan daren dan gane ina James ya dosa bai samu damar gane wa ba, dole dai sai da safe yasa sojojin sa su bincika masa a wani airport James ya hau girji dan suji ina zai je, daga nan ya ajiye bincike a kan James ya shiga bincike cikin sauran criminals da basu samu damar halactar taron su James ba dan ya gano ina suke, Bayan ya kammala wannan binciken ne kuma ya shigar da number motar da ya kama ɗazun mai ɗauke da yanmata nan, nan ma yayi bincike a kan motar, daga ina motar ta fito ina kuma ta nufa, dan ya san dai ba iya wayan nan yanmatan ne kawai ba, tun da motar ta kwaso wayan nan tofa tabbas ta saba kwasan yanmata ne dole ya san ina ake wannan badakala a cikin garin sa, Da binciken nasa yayi bincike a wajen bibiyar ɗaya daga cikin driver masu safaran yanmata da suka kama, nan yaci karo da driver'n yana yiwa wani babban likita aiki, ganin yana aiki da likitan yasa Romeo ya fara bincike a kan likitan da kuma asibitin, nan yaga abun da ya tayar masa da hankali, domin kuwa a wannan asibitin ana kawo maza da dama ana cire musu kodar su, da wasu sassa jikin su irin su ido gaban su da dai sauran, ana sanyawa manyan masu kuɗi na duniya, yasha mamakin ganin duk wannan badaƙala da sheɗan ci ace a cikin garin da yake ake yin su, abun ya ɓata masa rai sosai, ji yake kamar ya tashi ya tafi wannan asibitin yanzu, sai dai dare yayi, kashe laptop ɗin yayi ya ajiye saman bedside drawer ya ɗan yi shiru na yan mintoci kamar mai tunanin wani abu, sannan ya kwanta ya ja musu bargo shida Michael yau ko abinci ma bai jin ci saboda tunanin da ya masa yawa meke shirin faruwa da su ne, ina James ya tafi wayan nan abubuwa sun dame sa, hakan yasa yaji baya jin yinwa kwata kwata. Ko da ya kwata ya kasa barci tunanin James kawai yake, ya rasa dalilin da yasa yake ji a ransa tamkar zai rabu da James, slowly ya waro dara daran idon sa, ya zubawa Michael kallo, sai barcin sa yake bawan Allah hankalin sa kwance bashi da wata matsala, shafa kan sa Romeo yayi sannan ya mai da idon sa ya lumshe yana tunanin ya zasu yi idan akace yau babu James a tare da su, dan tabbas idan abun da yake zargi a kan James ya tabbata shi da kan sa zai harbe James ɗin da bindiga, dan ya kamanta adalci, to ya zasu yi yau idan akace ya harbe James da bindiga ya mutu, tare suka taso kullun suna tare, duk da baya shiga har kan su, yana matuƙar kaunar su fiye da tunanin mai tunani A wannan dare dai da kyar barci ya ɗauki Romeo zuciyar sa cike da tunanin ɗan uwan sa. Asuba ta gari Mu leƙo Nigeria mu dawo jama'a # 💞NIGERIA💞 💞KADUNA - GIDAN ABBO💞 Almost 30mins Hajiya ta ɗauka kwance tana mai da numfashi kafin ta ɗago ta kalli Jelly, a hankali ta zuro kafafun ta kasa sannan ta miƙe ta riƙo hannun Jellyn suka nufi bedroom nata tana faɗin "Me yasa kikayi wannan kwaɓen a fuskar ki?" Toro baki Jelly tayi kafin tace "Nifa wanka da kwalliya nayi" shiru Hajiya tayi dan tasan halin Jelly yanzu idan tace zata mata wani magana ko ta mata faɗa idan ta fara kuka sai ta kai dare bata yi shiru ba, gashi bata jin rarrashi ko kaɗan, dan haka Hajiya sai ta rufa wa kan ta asiri tayi shiru taja hannun ta kawai suka wuce toilet Suna shiga toilet a sukwane Hajiya ta zaro ido ganin lalatan da jelly tayi da sabulai dake cikin toilet ɗin Bokitin dake cikin toilet ɗin Jelly ta ɗauka ta ɗaura shi saman baf ɗin wanka ya ɗebo duk wani shower gel da su toothpaste da su sabulai su man kamshin baki shaving powder duk ta haɗe su cikin bokitin nan ta gauraye su waje guda, da farko Hajiya ta kasa gane menene ma a cikin bokitin sai daga baya data kalli robobin su shower gel ɗin a gefe ne yasa ta gane menene a cikin bokitin, salati tayi ta sanar da Ubangiji yau ga abun da ya fi karfin tunanin ta, tana tsoron yiwa Jelly wata magana, dan in ta kuskura tawa Jelly maganar da bai mata daɗi ba, idan ta fara yi mata ihu har dare bazata yi shiru ba, sai Abbo ya dawo ya rarrashe ta yayi ta yiwa Hajiya faɗa a kan me zata ɓata mata rai. Ɗaukan bokitin Hajiya tayi ta fitar waje, dan wayan abubuwa da Jelly ta haɗa sai zubarwa, dan har da su makilin na goge baki ta musu asarar makudan kaya masu tsada. Jelly na tsaye a cikin toilet ɗin har hajiya taje ta zubar da kwaɓen da tayi ta dawo hannun ta riƙe da wani carton na sabulu mai kyau da tsada, ajiye bokitin tayi ta haɗa ruwan wanka sannan ta cirewa Jelly kaya ta fara yi mata wanka Ba karamin wahala ta shaba wajen wanke fuskar Jelly, dan mai data damɓara kan sabulu ga foundation da kwalli abun ba'a magana, ita kan ta Jellyn sai da tayi kuka wajen wanke mata fuskar nata. Bayan Hajiya ta gama mata wanka tsab ne ta ɗaura mata towel suka fito suka nufi bedroom ɗin Jelly ɗin, sosai Hajiya baiwar Allah ta mata kwalliya mai kyau ta sanya mata kaya dogon riga abaya wanda yaya Nawid ɗin ta ya sayo mata, sannan ta feshe ta da turare mai kamshi, tsab ta koma kamar ba ita ba, ta dawo asalin Jellyn daddy, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka fito palo. Saman sofa ta zaunar da ita tace "Ki zauna kiyi kallo bari nayiwa Abbon ku girki kinga yau a part namu yake kuma yamma yayi" make kafaɗa Jelly tayi ta turo baki tana faɗin "Ni a'a zan biki kitchen na taya ki aikin nima" Hajiya zatayi magana Nawid da ya fito yanzu yace "Ai gara duk wani aiki da zaki nayi Ummi ki rinƙa yi tare da ita ko zata koyi wani abun arziki tun da kinga mace ce kuma ba yarinya bace nan gaba kaɗan sai aure" jin abun da Nawid yace yasa Hajiya tace eh yana da gaskiya dan haka sai ta kama hannun Jelly suka wuce kitchen tare Aiki Hajiya ta fara yi, tana yi tana nunawa Jelly komai dalla dalla, sai gyaɗa mata kai Jelly keyi kamar mai gane duk abun da Hajiya ke faɗe, alhalin ba abun da ke shiga kan ta, miyar steew sukayi ko in ce Hajiya tayi dan Jelly kam tana tsaye a gefe tana ganin duk abun da Hajiya ke sakawa a cikin miyar, ta zuba ido tana kallon yadda Hajiya ke saka su carry kaɗan kaɗan a cikin miyar, ji take kamar taje ta karɓa robar carry ɗin ta bulbula dukka cikin miyar dan ita bata son harka da karanta so take taga ana bulbula komai yaji sosai Bayan Hajiya ta tabbatar miyan yayi ne sai ta sauke dai'dai lokacin kuma ruwan shinkafa data ɗaura a gefe ɗayan gas ɗin ya fara tafasa, store ta nufa tana faɗin "Bari na ɗebo shinkafa" shiru Jelly tayi bata amsa ba Hajiya na shiga store Jelly ta ɗauko goran plate wash wani omo ne na wanke wanke, dan taga Hajiya ta saka su curry black pepper da sauran su, kuma taga kaɗan kaɗan Hajiya ta saka, ita kuma bata son harkan abu kaɗan tafi son dayawa shiyasa Hajiya na shiga cikin store ta ɗauko goran plate wash dake kusa da pots da Hajiya ta wanke yanzu, dan a tunanin ta shima kayan haɗin miyane Buɗe miyar tayi ta zuba mai ɗan yawa sannan ta gauraya miyar, ta mayar da plate wash ɗin ta ajiye a in da ta dauko, ta ɗauko ledan gishiri shima ta zuba ta ɗan kara su carry da duk wani abu da Hajiya ta sa a miyar, jin Hajiya na zuwa yasa tayi saurin gauraya miyar ta mayar ta rufe tana jin daɗi ta zuba abubuwa dayawa dan ita bata son har abu kaɗan tafi son taga komai yaji sosai zam zam. Koda Hajiya ta dawo bata wani lura da Jelly ba kawai ta ci-gaba da aikin ta, har suka kammala, da Hajiya tazo zuba abincin a cikin warmers data buɗe miyar taga ya ɗan canza kala amma da yake hankalin ta baya wajen tana sauri mangariba yayi zataje tayi wanka dan Abbo ya kusa dawowa hakan yasa ta zuba abincin kawai ta kwasa suka wuce palo A saman table ta jere komai sannan tace Jelly ta zauna bari taje tayi wanka, ba musu Jelly ta koma ta zauna saman sofa tana tunanin ko dai ta ɗauko su curry ɗin nan ne ta kara dan kamar wadda ita ma tasa yayi kaɗan, sai sake sake take a zuciyar ta ita kaɗai, har Hajiya tayi wanka ta fito tace taje tayi alwaya suyi Sallah Ba musu ta tashi ta nufi toilet nata ta ɗauro alwalar ta kamar yadda Hajiya ta koya mata sannan ta fito ta zo sukayi Sallah tare da Hajiya a palo. Sai bayan sallar issha sannan Abbo da Nawid suka shigo, wanka sukaje suka fara yi first kafin su zo saman table su zauna, Hajiya ita tayi serving nasu dan tace bata son masu aiki ita take komai da kan ta. Abbo shi ya fara kai abincin bakin sa, a ɗari ya tofoshi waje har yana kakarin amai, zaro ido Hajiya tayi tana tambayar menene a ruɗe da hannu ya mata nuni da ta ɗanɗana abincin taji dan ya kasa magana abincin har ɗaye fatar baki yake saboda gishiri da plates wash da kuma su carry da Jelly ta banka a ciki yayi yawa over yana ɗaye harshe Nawid kam tun da yaga haka sai ya fasa kai abincin bakin sa ya mai da ya ajiye, Hajiya kuma ɗaukan spoon tayi ta ɗeba abincin ta kai bakin ta, a sukwane ta fito da shi waje tana salati, ita kam Jelly dama tun da suka zauna ta fara cin naman kasa hankalin ta baya kan su kwata kwata, sai bayan ta cinye cinyar kazar ne ta ɗauki spoon ta ɗebo shinkafar da labcecen miya ta kai bakin ta Wani ihu ta fasa wadda yasa Hajiya da Nawid miƙewa suna kokarin gudu, shi ma Abbo ya tsorata da ihun sai dai bai miƙe ba. Rai a ɓace Nawid yace "Ke baby me haka?" Abbo ne ya daka masa tsawa "Haba Nawid me ta maka zaka mata wannan tsawa haka?!!" Zaro ido waje Nawid yayi yana mamakin abun da Abbon yayi, Abbo bai taɓa yi masa tsawa ba ko da wasa, hakan da yayi yanzu ya kara ɗarsa zargin sa a zuciyar Nawid ɗin, ita kan ta Hajiya sai da tayi mamaki a wannan karon Abbo bai taɓa yiwa Nawid tsawa ba sai yau Abbo kuwa ganin Hajiya da Nawid sunyi mamaki ne yasa yayi saurin basar da maganar da cewa "Ku tashi muje restaurant kawai muci abincin tunda wannan kam dai ya tashi aiki, sannan Nawid kai kuma ka dai na yiwa baby tsawa baka ganin tana cikin ciwo ne?" Shiru Nawid yayi yana tunanin yadda zan binciko me Abbo'n sa ke nufi da Jelly, dan yasan ba haka kawai zai rinƙa yin wayen nan abubuwa a kan taba, Nawid ba yaro bane a kalla zai kai 26 years a duniya gashi da saurin fahimtar abubuwa Ganin sunyi shiru basu da niyar tafiya ne yasa Abbo ya miƙe yana faɗin "Muje ko?" Jiki ba kwari Hajiya ta wuce bedroom nata tana faɗin "Bari na ɗauko mayafi" to kawai Abbo yace suka wuce waje shi da Nawid ita kuma Jelly tana zaune tana cin namar gazan ta, dan tun da ta saka shinƙafar a bakin ta tayi wannan ihu daya razana su Hajiya sai ta ci-gaba da cin namar ta kawai bata ma san da su Hajiya sun tsorata ba. Jim kaɗan Hajiya ta fito sanye da mayafin hannun ta riƙe da mayafin Jelly, zuwa tayi ta sanyawa Jelly mayafin sai faman figar nama Jelly keyi, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka bi bayan su Abbo, motar Nawid suka shiga shi yaja su suka tafi zuwa restaurant ɗan cin abinci, sai mamaki Hajiya take, me ya samu abincin da ta girka. To masu karatu mu leƙo Daular mutuwa mu dawo 👹DAULAR MUTUWA👹 Sosai duna yake aiki a kan yadda zai samu ya kuɓutar da Rimsha daga ɗakin duhu na Queen, baba da Mustapha kuwa sun dukufa sai addu'ar fatan nasara suke masa, Ayla da Kausar ma ba'a bar su a baya ba, sosai sukewa Rimsha addu'a a zuciyar su dan ba daman kiran sunan Allah a baki, amma fa sosai Ayla ke kuka duk lokacin da ta keɓe ita kaɗai sai tayi kukan rashin Rimsha, yan kwanakin kalilan da sukayi da Rimsha sunyi sabo sosai wadda rabuwar su abune mai matukar wuya wadda zai yiwa ko wannen su balai ciwo, Ayla akoi ta da hakuri ga kirki da son mutane shiru shiru bata da hayani ta. Allah sarki Ayla baiwar Allah ko ya akayi tazo daular mutuwa ita kuma oho, sai dai ku kasance da alkalamin princess Teema dan ita kaɗai ce zata warware muku komai sannu a hankali, ammafa akoi cakwakiya, yanzu wasan zai fara. To masu karatu kuma sai ku taya Rimsha'n ku da Addu'a kuyiwa duna addu'ar fatan nasara na barku lafiya, gobe idan Allah ya kai mu The beginning zai kare sai ku shirya, yanzu wasan zai fara bye sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu.. Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 TRIPLET'S💞 💞 FATEEMA MUSA💞 (💞STAR LADY💞) *Gargarɗi* _Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_ WhatsApp me for more information 09162620621 Episode 42-43 💞KADUNA GIDAN ABBI💞 Tun da Abbi ya ɗauko daddyn Jelly Aafia ta ɓata rai alamar bata ji daɗin zuwan sa gidan ba, dan shi ba fita zai yi ba yana gida ko da yaushe, idan kuma yana gida basu isa su fita da shigar da suke soba, zai takura musu lallai su saka hijabi idan kuma suka ki zai sanar da Abbi in suka masa rashin kunya kuma sun san Abbi uban su zai ci a kan ɗan uwan sa sai faman hararar dad Aafia take, ji take kamar taje ta shaƙe sa dan haushi, shikuwa dad sai faman jan su a jiki yake da wasa da dariya wai ko zai samu raɗaɗin ciwon rashin Jelly ya ragu masa a zuciyar sa, sai dai bai samu haɗin kan Aafia ba domin ko magana ya mata ciki ciki take amsawa ɗan gara Umaisha ma tana amsa masa da gimamawa a matsayin sa na bappan ta kuma a matsayin baba ta ɗauke sa. Abbi da kan sa ya kira Akila a waya ya haɗa ta da daddyn Jelly, sai murna Akila baiwar Allah mai kaunar yan uwan ta, sosai ta rinƙa dariya har da hawaye jin daɗi, ko da ta tambayi daddy ina Jelly sai yace mata tana barci, Akila bata ji daɗi ba taso yin magana da jelly amma haka ta hakura tace wa dad zata kira gobe da safe dan su gaisa da jelly, to kawai dad yace mata zuciyar sa na kuka, a pannin su Imran ma Abbi ya haɗa su da dad, da suka tambayi Jelly dad yace tana barci, Imran kamar zai yi kuka yace wa dad shikenan sai da safe zai kira, shima ya kusa dawowa saura masa kwana biyar, sosai daddy ya masa Addu'a da fatan alkhari, daga haka sukayi sallama, kowa ya kwanta, asuba ta gari. Washegari kuwa tun karfe 7 su Umaisha suka shirya dan su bar gidan da wuri kar dad ya tashi barci ya hana su fita da kalar kayan da suke son sawa, Umaisha bata cika saka riga da wando taje school ba, sai dai tasa atamfa ko lace amma yau da gangan ta saka riga da wando wadda suka kama ta sosai duk dan tasa Akil yaji ya tsane ta yaji haushi tun da yace mata yana shigowa Kaduna gidan su zai fara zuwa gashi kuma da bala'i kishi, ita kuma Aafia yau doguwar riga na kanti tasa, kasan cewar rigar jikin ta kamar roba yake hakan yasa ya kamata sosai, duk wani sura na jikin ta ya bayyana, haka suka fito sauri sauri kamar marasa gaskiya suka fice, sukaje kowacce ta shiga motar ta suka bar gidan suka nufi school. A ɓangaren Aunty kuwa lokacin da Abbi ya samu labarin juna biyun ta ba karamin murna bawan Allah nan yayi ba, sai dai abun da basu sani ba, su suna nan suna murna Aafia da Rufee suna can suna shirya yadda za'a zubar da ciki , wannan shine cakwakiya muje dai zuwa dan ganin yadda wannan rikici zai kare. Daddy kuwa kwata kwata bai ji daɗin zaman gidan Abbi ba, dan yadda Aafia ke masa baya jin daɗi, ji yake kamar ya koma Kano ko kuma ya tafi gidan su Imran wato gidan babban ya'yan su dan ko ba komai Imran da Akila suna kaunar sa, amma kuma idan ya tuna yadda yayan sa wato Abbi yayi tattaki daga nan Kd har Kano yaje ya ɗauko shi, sai yaji kamar idan yace zai bar gidan bai yiwa Abbi adalci ba, hakan yasa ya hakura ya danne zuciyar sa ya ci-gaba da zaman hakuri, dan zama da su Aafia sai ka dangana da hakuri in ba haka ba zuciyar ka zata fashe. Mu leƙo Jehan mu dawo 💞KATSINA💞 Ba karamin daɗi Jehan taji ba ganin yadda jikin mum ya fara kyau har wani cool murmushi take sake wa, shima Sadiq yaji daɗi sosai sai addu'a yake ta zubawa mum gwaggo na amsawa da Amin, yau sai karfe 9 na dare sannan su Jehan suka baro asibiti saɓa nin kullun da suke dawowa da yamma, yau saboda murnan anyiwa mum aiki jikin ta ya fara kyau yasa basu kamo hanyan dawowa da wuri ba. Bayan sun baro asibiti, suna tafiya suna yar hira suka nufi bakin hanya dan taran abun hawa, basu kai ga isa bakin hanya ba, wasu mata sa irin ɓata garin nan suka tare su hannun su rike da sanduna irin goran nan, sai warin sigari wato taba suke da alama wasu daga cikin suma a buge suke Tsawa suka dakawa su Jehan a kan su kawo wayoyin su da kuɗin dake jikin su, ba karamin tsorata Jehan da Sadiq sukayi ba, har wani fitsari Jehan take ji yana kokarin zubo mata, Amma saboda karfin hali irin na Jehan sai ta ɗaure fuska tace "Kai nima fa yar daban nan ne ta bugawa a jarida kuma idan baku sani ba ku sani yaya na ƙasurgumin ɗan daba ne na gaske, shine kamar ni kan war sa zaku tare kuce na baku waya ta to wlh sai na faɗawa yayana kuma duk in da kuke sai ya nemeku ya muku yan kan rago" kasan cewar dukan su basa cikin hayyacin sosai, zokaga yadda ake shiga tashin hankali, har kasa wayan nan yan iskan gayun suka duka suka fara bawa Jehan hakuri dan tsoron kar ta faɗawa ya'yan ta dan yanzu ma bala'i dake cikin garin Katsina kawai ma ya ishe su inaga kuma ta sake faɗawa yayan nata abun ai ba zai yi kyan gani ba, su daman irin yan iskan nannen masu neman kuɗin sayan sigari da wiwi kawai ba dan wani abu suke tare mutane su musu kwace ba. Jehan manya Jehan DPO an samu dama har da ja musu kunne da yi musu last warning a kan idan ta sake jin sun sake yin wani abu makamancin haka tofa kamar a kunnen yayan tane ne, sosai suka mata alkawari a kan bazasu sake ba, shidai Sadiq bawan Allah yanzu Jehan ta dai na bashi mamaki ma ya fawwalawa Allah lamuran sa yana bin Jehan a duk yadda ta bi da shi, sai dai ɗan zaman sa da ita yasa shima ya fara cire tsoro a ransa, yanzu yana jin jarunta har cikin jinin jikin sa. Niko nace tab aiko baka san itama duk burga bace a fili amma daga ta ciki har fitsari take, gara maka ma ka ci-gaba da jin tsoron ka dan ba ilimi gare kaba karka je ka taɓo abun da ya fi karfin ka kasha dukan mutuwa a banza, ita Jehan akoi ilimi sai ta karanci yana yin mutun take yanke masa irin hukuncin da zata masa, kai kuma ba ilimi kawai zaka afkawa abu hmm akoi matsala!!!. Sallamar guys ɗin Jehan tayi sannan tace "Muje Sadiq" sai godiya guys ɗin ke mata tare da fatan alkhari na dole, wannan shine idan ba kayi sharan masallaci ba kayi na kasuwa. Suna tafiya a hanyane kafin su kai bakin titi Sadiq yace "Jehan me yasa zaki yi karya? Meyasa zaki danganta kan ki da yan daba?" ba tare da ta kalle saba tace "Akoi wuraren da yin karya ya halatta wadda idan kayi su baka da laifi har gaban Allah, ciki kuma har da wanda nayi yanzu, kayi karya domin ka kare rayuwar ka, zaka iya karya dan ku zauna lafiya a gidan ka, zaka iya karya dan ka sulhun ta mutane biyu da suke faɗa ko gaba, to a nan in da suka far mana nan kaga ai bumu da mafita dole mu musu abun da hankalin su zai kama, a yadda suke yan iskan garin nan, ba Allah da annabi zaka faɗa musu ba, domin bazasu saurare ka ba, dan ba hanyar Allah suke ba, amma idan ka faɗa musu kana da wanda ya fisu zama ɗan kwalta zasu nitsu ga misali dai ka gani, ko wani ɗan adam akoi direction ɗin da yake tafiya a kan sa, to kai ma dan ku zauna lafiya kasa ya yarda da abun da kazo masa da shi sai ka ɗauki direction ɗin da yake kai kaima ɗin, ba wai zakayi hakan dan kazama irin sa ba ko dan ka saɓawa Allah no a'a zakayi hakan ne dan kasa ya fahimci abun da kake nufi koda bai yi niya ba, yanzu yadda suka tare mun nan kana tunani idan shekara zamuyi muna ce musu dan Allah zasu hakura su kyale mune?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a, kasan cewar yanzu Jehan Hausa ya ɗan fara zama zam zam a bakin ta tana ɗan yi magana da Hausa sosai tana ɗan kwaɓawa da English nata Ci-gaba da magana tayi "Yauwa ashe ka gane ko kwana zamuyi muna haɗa su da Allah baza su kyale muba, dan ba aikin Allah suka fito yi ba, saboda babu in da Allah yace ɓarawo yaje yayi sata, hasalima sai dai in da yake sanar da mu hukuncin da za'a wa ɓarawo mai cin hakkin bayin Allah, ajiye wannan zancen muje in da nake so ka fahimtar ko dan ɓacin rana wata rana, aduk lokacin da wasu yan iska suka tare ka, ka nitsu sosai ka duba yanayin su a kan wani tsari suke, misali kaga wayan nan yadda suka tare mu ai sun nuna mana su yan daba ne, shiyasa na musu amfani da sunan ɗan ta'adda wato baban yan daba, amma idan ka duba kaga cikakkun yan iska ne masu son iskanci kamar ni mace ai nuna musu zan yi iskancin nima nake so kamar yadda mukayi da Farooq sai ka rabu da su lafiya ba tare da sun maka illaba, koda sun karɓa maka wani abun ba zasu maka illaba" shi dai Sadiq bin ta kawai yake da to domin wani Hausar a kwaɓe take wani kuma tana saka turanci Shiru ya ɗan yi kafin yace "Jehan aina kika san yan daba ne ma? Ke da lokacin da kuke tare da daddy kullun kuna gida baku san wahala ba baku fita waje" guntun tsaki taja kafin tace "Na san shi mana a media before ai ina da waya kuma ina hawa net" shi dai Sadiq tun da ba sanin net ɗin yayi ba sai yayi shiru bawan Allah bai taɓa riƙe karamar waya bama bare babba, sun tsaya suna ta hira sai wucewa taxi suke saboda dare, da kyar suka samu wani suka tara zuwa gida. Koda sukaje gida basu ci abinci ba dan sunci a asibiti da gwaggo wadda Jehan ta sayo musu, karatu kawai Jehan ta koyawa Sadiq da Hanan har da Yusuf kamar yadda suka saba, Sadiq yana son karatun sosai shiyasa ya mai da hankalin sa sosai yana ɗaukan abun da take koya masa musamman fannin addini yana kokari sosai yana mayar da hankali. Sai karfe 11 na dare sannan su Sadiq suka yiwa maman su da Jehan sallama suka fito, har bakin kofar ɗakin maman Hanan suka raka Hanan sannan suka wuce ɗakin su shida Yusuf Sha'aban kuma baya nan yaje garin maman sa duba ta Su Sadiq suna fita Jehan ta tashi taje tayi wanka Allah sarki yanzu har ta saba da wanka da ruwan sanyi, bayan tayi wanka ta fito ta dawo ɗakin maman Sadiq, already maman Sadiq ta jima da yin barci abun ta, kayan barcin ta ta ɗauko riga mai laushi da dogon wando ta saka a jikin ta ta ɗauki mayafin lulluɓa da maman Sadiq ta bata ta kwanta ta lulluɓe jikin ta, sai bayan ta kwanta sai ta tuna kamar basu yi Sallah ba, tana kokarin miƙewa sai kuma ta tuna ashe sunyi a asibiti, addu'ar barci kawai tayi ta kwanta, ta lumshe ido tana tunanin Rimsha tana hawaye kamar kullun har barci yayi awon gaba da ita. Asuba ta gari. Mu leƙo Washington DC mu dawo # 💞WASHINGTON DC💞 80:00am Slowly ya waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci, kasan cewar idon nasa akoi alamar barci bai isshe shi ba, sai idon nasa ya kara kyau dan yayi yanayi da sleeping eyes, wani azaban duka kirjin sa tayi lokaci guda wadda yasa yaji barcin ta watsake ta sake sa, miƙewa yayi zaune a tsakiyar gadon ya dafe saitin faffaɗar kirjin sa, da sanyayyar murya mai bala'i daɗi da kwatar da hankali mai sauraro yace "Meke shirin faruwa da nine" dan bai taɓa jin makaman cin wannan bugun zuciya ba a tattare da shi, shiru ya ɗan yi na ɗan lokacin kafin ya yaye bargon jikin sa a hankali ya zuro zara zaran kyawawan fararen kafafunsa kasan bed ɗin sannan ya miƙe ya nufi toilet. Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani haɗaɗen jeans mai bala'i kyau da tsada launin baki da High neck sleeve shirt launin blue kasan cewar rigar ta kama jikin sa sosai, hakan ya bayyanar da kakkafar suran kirjin sa, faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe take sosai cikan damatsan hannun sa yasa faffaɗar kirjin nasa ta kara buɗe wa sosai, har wannan bul bul ɗin breast nasa kana iya hangowa saboda kama shi da rigan tayi, ba karamin kyau kayan suka masa ba, kamar dan shi akayi su, Winter Sports Hat ya sanya a kan sa, bayan ya ɗaure dark black curly hair sa, ya fito yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai, sai dai ya bar wannan ɗan guntun gashin gaban goshin nasa a waje bai shigar da ita cikin hulan ba, fuskar nan nasa a ɗaure take kamau kamar kullun sai dai na yau ma tafi na kullun, dan ina ga yau idan sukayi ido huɗu da mai karamain zuciya nan take zuciyar zata buga ya mutu awajen saboda tsoron yadda fuskar lion tayi yau abun ba'a magana ya wuci tunanin duk wani mai tunani, sai tashin fitinannen kamshi yake, hannun sa na ɗaure da diamond watch nasu na Triplets, kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $76000, kasan cewar takalmin launin baki ne sai yayiwa farar kafar sa bala'i kyau, wayar sa da kuma laptop na sa ya ɗauka ya nufo waje, yana taku irin na manyan jarumai, ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkafa ne ke tinkaro ka. Lokacin da ya fara sako kafar sa a benen sauƙowa palon kasa, ji kake tsit duk wani halitta mai rai dake cikin palon ya nitsu tsit sun sha jinin jikin su, wasu daga cikin bodyguards kam jikin su har kerma yake saboda tsoron sa, John, Jay, uncle Herry, Tga, gaba ɗaya suna palon kasan, sun zauna kamar masu jiran wani abun kowannen su yana ta faman latsawa waya cikin kwanciyar hankali, lokacin da kamshin perfume na lion ya kai musu karo a hancine yasa sukayi saurin ajiye wayoyin nasu suka nitsu suna satar kallon sa ta kasan ido dan shi baya son yawan kallo, sai yaga kamar wani abu kake kallo a jikin sa hakan yasa idan ya kama ka kana kallon sa sai ya maka hukunci mai tsanani. wucewa yayi ko kallon in da su John suke bai yi ba ya nufi hanyar ficewa daga palon, har suna haɗa baki wajen rige rigen ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar ko ɗaya daga cikin suba dan dama ba amsawa yake ba sai dai ya ɗaga musu hannu dan magana na masa wuya, to yau kam ma ko hannun basu samu arzin ya ɗaga musu ba dan hankalin sa kusan baya tare da shi. Dai dai zai fita palon yajiyo muryan dad da Michael har suna haɗa baki wajen tambayar sa ina zai je, juyowa yayi yazo ya rungumi daddy tare da mannawa daddy kiss a kumatu kasa kasa yace "I need your prayer my dad" daddy sarki saurin razana ya ɗauka yaki Romeo zai tafi nan take jikin sa ya fara kerma cike ta tsoro yace "Where are you going my lion?" Kasan cewar sun san halin dad sai bai faɗa masa abun dake faruwa ba ya basar da maganar ta hanyar cewa zai je wajen friend na sa ne dad karya damu kawai ya yi musu addu'a, ajiyar zuciya dad ya sauke kafin yace zai faɗawa pastor ya musu addu'a, wucewa Romeo yayi zai tafi, sai kuma ya sake juyowa ya shafa kan Micheal dake tsaye yana kallon su, shi dai Michael duk da ba ilimi gare saba yasan ba lafiya ba, dan yana ji hakan a jikin sa, daman kuma ko ciwon kai ɗaya daga cikin triplets yake tofa sauran sai sunji a jikin su, hakan yasa yau tun da suka tashi barci zuciyar Romeo ke bugawa da karfi karfi, shi kuma Michael yana fama da faɗuwar gaba da kasala wadda ta haifar masa da ciwon kai, sai Allah kaɗai ya san shi kuma James me yake ji. Wucewa Romeo yayi cikin sauri ya fice daga palon, yana fita rundunar jinga jibgan sojojin sa suka fara sara masa, sunyi layi a bakin kofar palon da alama jiran fitowar sa suke. Wuce su yayi ba tare da yayi wani alama ma da zata nuna ya gansu a wajen ba, kai tsaye wajen shirga shirgan motoncin da aka jera musu ya nufa, motoncin manya manyan masu numfashi, na sojoji guda 8 sai wata dan kareriyar motar fara tas har wani kyalli take kirar Bugatti La voiture wadda a kalla kuɗin ta ya kai $18.7 million, jikin motar kawai abun kallo ne dan ta tsaru iya tsaruwa, idan ka shiga cikin motar nan sai ka rantse da Allah a cikin manya manyan haɗaɗun palo irin na manyan shuwagabannin kasa kake, saboda haɗuwa irin na cikin ta, kujerun motar irin manya manyan kujerun nan ne masu mumfashi wadda suka amsa sunan su kujeru, har wani lotsawa ciki suke idan ka zauna a kan su, sai wani fitinannen kamshi mai bala'i daɗi ke tashi daga cikin motar nan, saboda ansan mamalakin motar ma'abocin son tsabta da kamshi ne shiyasa komai nasa yake kasan cewa mai kamshi da tsabta. Da taku irin na jarumai sadaukan yaki ya nufi motar, yayin da jibga jibgan sojojin sa ke take masa baya Wani jibgegen katon Baturen soja fari tas da shine yayi gudu ya sha gaban lion ya buɗe masa gidan baya na wannan farar Bugatti La voiture noira, gently lion ya shiga cikin motar ya zauna, dan shi komai nasa a nitse yake yin sa, daki daki yake bin komai Sai da wannan sojan ya ɗaga hannu ya sara masa sannan ya rufe kofar motar Ji kake dip dip sojojin sa suka nufi motoncin su da gudu suka haye saman bayan motoncin nasu, wannan sojan daya buɗe wa lion kofar mota ya shiga, shi ya ja motar lion ɗin. A tare motoncin suka tashi suka nufi gate ɗin fita gidan, duk in da suka wuce sara musu sojojin dake tsakar gidan suke. Suna fita wajen gidan suka saki jiniya kamar yaki zasu tafi, abun da ya sa basu saki jini tun a cikin gida ba, saboda daddy, yana jin jiniya zai ruɗe yace yaki Romeo zai je ko wani wajen, shiyasa suka bari sai da suka fita waje sannan suka saki jiniyar. Duk wata mota ko abun hawa dake hanya kaucewa suke su bawa tawagar jerin kwanon motocin The general of the army hanya, wasu ma jiniyar kawai suke ji tun daga nesa, tun bai iso su ba suke sauka daga kan titi da abun hawan su su bada hanya Ko da tawagar motocin suka zo wajen fitillar bada hannu, a sukwane mai kula da fitillar wajen ya basu hanya dan su wuce dan yasan ma ko bai basu hanya ba ba tsayuwa zasu yi ba, dan in tawagar motocin The general of the army suka tinkaro waje tofa sai dai ku ku hakura sai sun wuce. Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin Ac na ratsa shi, sai faman cizan lallausan laɓɓan sa yake, ga lips ɗin nasa ya kara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza su da yake, duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar tunani ina James yaje, dan shi har yanzu yaki yardan wa zuciyar James criminal ne, duk lokacin kuma daya tuna James sai yaji zuciyar sa ta bada dum dum ya rasa me matsalar, kokarin sake bin diddigin layin James yayi abun mamaki sai yaga layin a kashe bayan a kashe ma an soketa daga hanyar sadarwa gaba ɗaya, cike da tashin hankali ya ciro wayar sa ya fara kiran layin, kwata kwata layin an suke ta, zaro idon sa waje yayi yana tunanin meke shirin faruwa ne, taya za'ayi ace an soke layin James gaba ɗaya bayan jiya da daddare lafiya lou layin take, to me ya faru da James ɗin?. Yana cikin tunani bai san lokacin da suka isa *Dulles International airport* ba sai da yaga jibga jibgan sojojin sa sun kewaye motar sa da manyan bindigun su, sannan ya farga, sojan daya tuƙo sane ya fita ya buɗe masa kofar motar suka tsaya cirko cirko suna jiran fitowar sa Ko da aka buɗe masa kofar motar ya ɗauki tsawon good 30mins zaune acikin motar kafin ya zuro kafafun sa waje a nitse ya fito ya wuce gaba, jiga jigan sojoji masu ji da lafiya wadda da ka haɗu da irin su gara ka haɗu da zaki koba komai shi zaki cinyewar lokaci ɗaya zai maka, sukuma fargana da faɗuwar gaban ganin sune zai yi ta sumar da kai kana farfaɗowa har ka mutu, wayan nan jiga jigan sojoji su 8 suka take wa lion baya zuwa ciki, Abun mamaki duk wayan nan sojojin mutuwar tsoron lion suke, suna razana jama'a a gari sukuma fuskar lion na razanar dasu yana sanya hantan cikin su kaɗawa. Bincike lion yaje yayi a kan wani jirgi James ya hau, ba karamin mamaki lion yayi ba jin cewa jirgin Europeans country ya hau, a Europeans ɗin ma jirgin kasar Spain ya hau, Spain lion ya mai maita a ransa Shiru yayi yana tunani abubuwan sun haɗu sun cakushe masa yanzu ba binciken a kan James criminal ne ko ba criminal bane ya kama shi, bincike a kan ina James yake me yasa aka soke layin sa daga hanyar sadarwa wani hali yake ciki, shine abun da yake gaban lion yanzu, abun da ya sawa ran sa dai tabbas James yana cikin tashin hankali da damuwa a duk in da yake, kuma yana bukatar taimakon gaggawa, dan baya cikin koshin lafiya ba abanza kirjin lion ke yawan dukan uku uku time to time ba, sannan ga Michael can a gida yana cikin faɗuwar gaba hakan har ta hadda sa masa ciwon kai da kasala. Juyowa lion yayi suka koma cikin motocin su suka musu key suka bar airport ɗin zuwa gida, yanzu babban damuwar ma shine ya rasa ta ina zai fara bincike a kan James domin bashi da wata maka ko guda ɗaya da zai ce ga wannan zai riƙe ya zama masa makami da zai yi bincike ya gano in da James yake. Kamar yadda jerin gwanon motocin suka fita gida haka suka koma sukayi parking a in da suka taso, sojan daya tuka shi, shiya fito ya buɗe masa kofar mota, a wannan karon da sauri lion ya fita zuwa cikin Palo, kai tsaye part nasa ya nufa Yazo zai hau bene dai dai lokacin Tga zai sauko, a guje Tga ya koma baya ya bashi hanya, dan dama already sun sani idan lion na saman staircase ba mai hawa har sai ya sauka ya tafi Yana shiga bedroom nasa ya fara aiki gadan gadan dan sanin ina ɗan uwan sa jinin jikin sa yake wani hali kuma yake ciki, ya manta ma da batun zuciyar sa na zargin James ya dukufa aikin neman sa kawai. Misalin karfe sha ɗaya na rana zaune suke a palon kasa gaba ɗayan su ban da lion dan shi ba'a sa shi ma a lissafin su saboda kwata kwata baya shiga cikin su, idan yazo waje ma saboda tsoron sa lallaɓawa suke su gudu, kuma ba dukan su yake ba ba zagin su yake ba, wannan fusataccen fuskar nasa suke mutuwar tsoro da kuma kwarjinin da Allah ya masa, Wani sojane ya shigo cikin palon pastor na biye da shi a baya, ma'ana sojan yayiwa pastor jagora zuwa cikin palon kenan Da murna dad ya miƙe yaje ya taro pastor sai dariya yake, ɗaure fuska Michael yayi yana hararar pastor kamar yaje ya shaƙe sa yake ji, shikuwa pastor sai washe baki yake, wai ya biyo sahu yaji ko lafiya two weeks basu zo church ba, daddy ya yi imani da wannan pastor nasu sosai jikin sa sai kerma yake ya shiga bawa pastor hakuri, cike da isa pastor yace to ba damuwa yanzu dai su shirya su wuce church ɗin tare da shi tun da yau Friday akoi Church, nan fa Michael yace pastor bai isa ba shi babu in da zai je kuma daga yau ma ba zai sake zuwa church ba har ya mutu, nan fa rigima ta kauri, pastor yace zai tsinewa Michael daddy jikin sa sai kerma yake yana hawaye yana rokan pastor yayi hakuri karya tsinewa Michael, shi kuwa Romeo yana part nasa ya dukufa wajen neman ina ɗan uwan sa ya shiga. Ganin pastor ya saka daddy kuka hawaye sharɓa sharɓa ne yasa Michael ransa ya ɓaci ya sakarwa pastor wayan nan mayun kwarin nasu na Triplets, ihu pastor ya fara yi yana birgima a kasa, saboda tsanar da Michael yayiwa pastor har da kara masa da ƙudan zuma yayi, Tga, John, Jay suna ganin Michael ya sako kwarin nan sukayi ta kan su dan sun ɗanɗana a baya basu ji ta daɗi ba, uncle Herry ma ba'a barshi a baya ba wajen gudu, kafa me naci ban baka ba, ai a miliyan kowa yayi part nasa, bayan sun shiga part nasu ma sai da suka kara da danna wa kofofin key dan karma kwarin su biyo su. Iya pastor kawai kwarin suka farma, daddy ya tsorata sosai Allah sarki shi damuwan sa kada pastor ya tsinewa Michael rayuwar sa ta lalace shi yake wa kuka, amma dan iskanci irin na Michael ana neman masa sauki wajen pastor ya kara laifi kan laifi ya sakar wa Pastor wannan bala'i mai kama da tashin duniya. Daddy na kuka gwanin ban tausayi ɗan tsohon nan, haka ya haura sama da gudun ya nufi part ɗin Romeo dan ya kira shi yazo ya dakatar da kwarin nan karsu kashe pastor, dan yayi ta rokan Michael, Michael yace ba zai dakatar da su ba sai dai su kashe pastor ɗin. Ganin daddy na kuka ba karamin ɗagawa lion hankali yayi ba, a sukawane ya miƙe ya taro daddy yana tambayar sa lafiya, cikin kuka daddy ya sanar da shi abun da Michael ya aikata, rai a matukar ɓace ya zaunar da dad saman bed nasa sannan ya nufi Palo, daman ga damuwa sun masa yawa ga batun James ga bincike a kan asibiti masu sai da koda da sassan jikin maza, ga bincike a kan kontenan mai ɗauke da mata daya kama jiya, abun ya haɗe masa lokaci guda Yana sauƙa palo rai a matukar ɓace ya ɗauke Michael da wani gigitacen mari wadda yasa Michael zubewa kasa a kan gwiwowin sa yana ganin wasu taurari masu hasken gaske suna gilmawa ta cikin idon sa, saboda azaban zafin marin ma ya kasa kuka, daman hausawa na cewa duk ciwon da akewa kuka bai kai ciwo bane, idan ya kai ciwo neman kukan ake a rasa, to wannan ma hakane Michael dai ya nemi kukan sa ya rasa Romeo kuwa bai kara bi ta kan ba dan sauri yake aiki na gaban sa, dakatar da kwarin yayi sannan ya koma sama da sauri, dad kuma yana zaune in da Romeo ya zaunar da shi. Allah sarki pastor ya jama kan sa bala'i duk fuskar nan tasa ta sunduma luhu luhu kamar an hura palo palo, abun ka da fatar Bature jikin sa yayi jajir kamar jini da kyar da kyar yake fitar da numfashi. A ɓangaren Michael kuwa good 40mins ya ɗauka a wajen zube a kan gwiwowin sa kafin ya samu marin Romeo ya sake sa, sai lokacin da marin ya sake sa ne ya samu damar fitar da zafafan hawaye daga idon sa, da kyar ya miƙe ya fice daga palon, bai ɗauki mota ba ya fice daga gidan da kafar sa, yana tafiya yana hawaye yana tunanin yau shi Romeo yayiwa wannan marin gaskiya dole ya bar musu duniyar baki ɗaya tun da basa son shi, da wannan tunani ya hau babban hanya wadda manya manyan motocin ke wucewa wai shi zai mutu, yana tafiya yana hawaye, duk motar da tazo da kyar take iya kauce masa, sai zagin sa wasu drivers ɗin suke idan suka kauce masa da kyar, shi kuma ko ajikin sa dan yace mutuwa zai yi kawai tun da ba mai son shi, Allah sarki bawan Allah matsalar daga kwakwalwan sane ba daga shi bane Wata mota kirar Mercedes-Benz ne ta taho a guje ba tare da ta lura da shi ba ta kwashe sa, ji kake kiiiii gam, sai jinin Michael ya wanke glass ɗin gaba na motar, da kyar driver motar ya iya taka birki, nan take jama'a suka cika wajen, motocin dake wucewa duk suka dakata saboda haɗarin da akayi, driver da ya buge Michael ɗin ne ya fito da gudu duk da shima yaji ciwo da jikin glass ɗin motar dan glass ɗin ya tarwatse kaca kaca, sai dai shi bai mutuba a iya goshi yaji ciwon. Duk da cewa gaba ɗaya jikin Michael yayi caɓa caɓa da jini hakan bai hana jama'ar dake wajen su gane daga family William jacop yake ba, duk wani halitta mai rai dake wajen babu wanda bai tsorata ba lokacin da sukaga diamond watch na Triplets a hannun Michael, dan duk wanda ya kwana ya tashi a Washington DC to dole zai san da wannan agogon a hannun The general of the army Romeo, sun tsorata sosai, an rasa mai karfin zuciyar kiran Family William jacop a waya a ranar da su an buge ɗaya daga cikin yan gidan da mota kuma ya mutu, dan ko ina jini ke zuba daga jikin sa. Daga karshe dai motar asibiti suka kira ya zo ya ɗauki gawar Michael dan kowa na tsoron a fara jin maganar daga bakin sa, gara suji zancen daga asibiti zaifi Yau saboda tsoron da jama'a kewa Romeo an rasa mai karfin zuciya da dauriyan kiran over over'n cikin gidan William kai abun dai babu daɗi ko kaɗan. Allah sarki Michael ba zan iya ganin tashin hankali da dad da lion zasu shiga ba idan suka samu labarin mutuwar ka, dan haka mu koma Nigeria mu leƙo wata kila kafin mu dawo anyi jana'izar Michael. 💞KADUNA STATE NIGERIA💞 Zaune Su Umaisha suke wajen gaban department nasu Aafia suna hira sama sama ita da Aafia Babu ko sallama Rufee ta kariso wajen, da sauri Aafia ta miƙe ta rungumo ta tana faɗin "Rufee ya mukaji da hakurin rashin Amal" hawayen munafurci Rufee ta fara yi tana faɗin "Wlh ji nake kamar na mutu nabi Amal yanzu ma saboda ke nazo school nan, nazo na baki maganin nan ne sai na koma ana can ana zaman makoki" Allah sarki Aafia da yake ba yin kan ta bane sai ta karɓa maganin da Rufee ta kawo na zubar da cikin Aunty, kuma daga nan Abbi zai tsane ta, sai murna Aafia take Abbi zai tsani Aunty ya koreta daga gidan, ita kuwa Umaisha yar ba runa ko ajikin ta dan da zaman Aunty a gidan da babu duk ɗaya ne a wajen ta bata da matsala da hakan, sai kitsawa Aafia mugun abu Rufee take, nan Aafia ke sanar da Rufee'n zuwan daddyn Jelly gidan su, ko kaɗan Rufee bata ji daɗi ba musamman ma da Aafia tace mata daddyn Jelly zai hana su fita da ko wani kaya sai atamfa da kuma hijabi, ba haka Rufee take so ba, ita tana son ne ta koyawa Aafia bin maza dan haka sai ta fara shirya yadda zasu yi da daddyn Jelly. Suna tsaka da wannan zancen nasu ne kamar daga sama, sukaga wani handsome guy ya diro wajen ya danki hannun Umaisha, ita kan ta Umaisha bata gane Akil ɗin ba dan ya canza sosai ya kara girma ya kara tsawo da cika yayi bul'bul gwanin ban sha'awa, daman Akil ba baya ba wajen kyau, duk da ita ma Umaisha ɗin ta canza dan shakara uku ba wasa ba hakan bai hana Akil gane taba, dan Imran na tura masa hotunan ta, shi kuma Imran wajen Irfan yake samun hotunan nata. Kokarin kwace hannun ta tayi dan bata gane saba kwata kwata musamman dayayi shigar kananan kaya abun ba'a magana, wani mahaukacin mari ya sakar mata wadda yasa ta game ko wanene, cikin fushi yace "Kina matata ne zaki fita da wannan ɗan iskan shiga ko? To yau zan koya miki hankali sai kin yi nadama wlh" sai da yayi magana sannan Aafia ta gane wanene, da farko ta ɗauka wani saurayi ne daban har ta fara kamuwa da son shi dayake basu da aiki sai faɗawa soyayya da kyawawan maza, ita kuwa Rufee baki ta sake tana kallon Akil taga kyau nan take taji ta kyatsa da shi kuma tana son shi amma ba da aure ba da iskanci kawai dan ta sawa ran ta Abbin su Aafia kawai zata aura bayan ta gama barbaɗancin ta da tambaɗancin ta a titi. Cak Akil ya ɗauki Umaisha kamar yar baby ya saɓata a kafaɗar sa tana ta bubbuga masa bayan sa tana faɗin "Ka sauke ni bana so" bai saurare taba ya wuce wajen motar sa, yana zuwa yayi wurgata gidan baya na motar ya shiga gidan gaba ya datse marfin motar tare da tada motar da gudun gaske ya figeta suka bar cikin school ɗin, sai wani hucin ɓacin rai yake, kamar shi ace matar sa ta fita da wannan kaya kai ina dole yayi maganin ta yau, makarantar ma daga yau anyi cancel na shi ba zata sake zuwa ba, sai saka zancen zuci yake a zuciyar sa yana zuba uban gudu da mota. Ganin Akil ya tafi da Umaisha ne yasa Aafia ta nufi motar ta da sauri dan tabi su taga ina zasu je, sai tambayar ta Rufee take waye Akil? Aina yake? Shima a School ɗin nan yake ne Amma ina Aafia bata bata amsa ba dan hankalin ta a tashe yake burin ta kawai ta isa wajen su Akil, da gudu itama ta ja motar ta tabi bayan su ta bar Rufee tsaye a wajen, Juyawa Rufee tayi tana faɗin "Tun da kin saka maganin a jakar ki ai bukata ta tabiya shi kuma guy ɗin can ko ki faɗamin wanene ko karki faɗa sai na nemo ɗan gidan uban waye ne dan na ji shawarar sosai ya kamani gaskiya" sai surutu take har ta isa wajen tsohon motar Irfan da Abbi ya bata ta shiga itama ta bar school ɗin. Akil kuwa kai tsaye gidan su ya wuce da Umaisha sai ihun rashin kunya take masa tana maganganu marasa kan gado, hakan ba karamin fusata shi yake ba, yana parking a parking space na gidan su ya fito ya ɗauke ta kamar yar baby sai zagin sa take, bai kula taba ya wuce cikin gida, a palo yaci karo da Ammie su tana zaune, da sauri Ammie ta miƙe tana tambayar sa wace ce wannan ya ɗauko Ina hankalin sa baya jikin sa part nasa ya wuce kawai, da sauri Ammie tabi bayan sa cike da tashin hankali, ita da take zaune take jiran anje ɗauko shi a airport ko ina kuma ya samo yar mutane oho masa, tana tafiya tana zancen zuci kafin ta isa bakin part nasa, tuni ya shige ya murzawa kofar key, tsayuwa Hajiya Umaiya ko in ce Ammie tayi tana ɗan bubbuga kofar tana kiran sunan sa, amma ina ya shige can cikin bedroom nasa Yana zuwa yayi wurgi da Umaisha saman gado tana kokarin tashi ta gudu ya sake mai data, yasa kafa ɗaya ya take mata hannaye dan kar ta tashi, a fusace ya cire kayan jikin sa duka yayi wurgi da su gefe, ya rage daga shi sai Short, hayewa saman gadon yayi ya damkota, Ammie na tsaye a bakin kofa tana buga mashi kofa, amma ina baya jin ta. Jin Umaisha na kuka ne yasa Ammie ta tsorata dan tasan halin Akil sarai baya son reni tun yana yaro, idan ka rena shi to ba abun da ba zai iya aikatawa ba, son girman bala'i gare shi cikin sauri ta koma palo ta ɗauko wayar ta, takira Abba ta sanar dashi abun da yake faruwa, shima Abba ya tsorata sosai yace yayi nisa amma ba zai wuce 1h ba yana zuwa, amma kafin nan Hajiya ta dakatar da Akil dan basu ma san ko yar waye yaje ya sankamo ba, sai zare ido Hajiya take. To jama'a ta ko ina ba sauki Washington DC Triplets suna can cikin tashin hankali gashi shima Akil yana neman ɓata komai, bari dai mu leƙa daular mutuwa mu dawo kila a can mu dace mu ɗan samu sassauci, amma idan ba haka ba akoi matsala, wannan tashin hankali dame yayi kama🥺 👹DAULAR MUTUWA👹 Wani irin turnukin bakin turɓayan kasa ne ke tashi kamar guguwa, gaba ɗaya girman Daular mutuwa sai da ko ina ya karaɗe da wani masifaffen duhun bala'i, ga wani iska mai karfin gaske mai karfin ɗaukan ɗan adam sama abun gwanin ban tsoro, wasu muryoyi mara sa daɗin ji masu bata amo mai sauti ne ke tashi daga fadan Queen, sai juyawa gaba ɗaya gidan yake yadda kasan ba daga kasa a ka yi ginin ba sai ka rantse da Allah a saman iska gidan yake saboda yadda yake juyawa, wannan guguwa mai bala'i karfin gaske ne yasa gaba ɗaya wayan dake cikin gidan kowa ya shige cikin ɗakin sa Ihun wasu halittu masu kama da zakuna ne ya fara tashi a cikin gidan mai bala'i sautin doɗe kunnen ɗan adam Duk wannan duhun da iska da guguwa duna na tsaye a tsakiyar part nasu, yadda kasan an dasa shi ko motsi bayayi ya tsaya kekam kamar daga sama Rimsha ta faɗo gaban sa, tana faɗowa yayi saurin sake tsafin nasa ya duka gaban ta yana kiran sunan ta Yana sakin tsafin nasa kuma cikin kankanin lokaci gidan ya fara washe wa, sai dai kuma me, nan fa jiga jigan matsafan Queen suka biyo sahu dan basu barin bashi Ganin yana yin gidan ya fara canzawa alamar jiga jigan mutanen Queen suna zuwane yasa duna miƙewa da sauri ya riƙo hannun Rimsha ya miƙar da ita sai nishi take da kyar da kyar, dai dai lokacin Ayla da Kausar suka fito dan sunga gidan ya ɗan wastsake Ganin Rimsha yasa suka kwasa da gudu sukaje suka rungume ta, itama ganin su ya kara mata karfin jikin ta, gidan nasu kuwa sai kara riƙiɗewa yake zuwa jawur kalan jini dan dama ita Queen kalar jini ce shiyasa komai nata yake ja kamar jini Wasu irin halittu ne suka bayyana a tsakiyar wajen masu bala'i girman gaske wadda zasu iya haɗiye dan adam kamar paracetamol, wayan nan halittu su shidda ne suna da kafofin guda huɗu kamar damisa, sai dai kafofin nasu kanana ne jikin su yafi kamar basu girma, munin wayan nan halittu kawak ya isa ya kashe mutun idan ya gansu, gadan gadan wayan nan halittu suka nufi su Rismha yayin da su Barbushi suke biye da wayan nan halittu a baya Ganin haka yasa duna yaja hannun Rimsha da gudu ita kuma tana riƙe da hannun Ayla yayin da Ayla ke riƙe da hannun Kausar, da gudu wayan nan halittu suka rufa musu baya, suma su Barbushi suka rufawa halittun baya Duna ya ɗan yi gudu a cikin gidan mai nisa dasu Rimsha kafin ya tsaya dai'dai wajen wani katon gunkin Queen tare da sakin hannun Rismha ya caka hannun sa cikin kasa da iya karfin sa yana ihu ya ɗago wata kofa ya buɗe wajen, cikin sauri yace da su Rimsha ku fi ta wannan hanyar idan kuka fara gudu karku tsaya kuma karku juyo baya, kuyi gudu ku ceci ranku, ni nasan kashe ni zasu yi ba zan rayuwa ba, amma dai ki sani ina son ki ba zan iya bari su kashe ki ba dan haka ki gudu, ya kai karshen maganar tare da fitar da wani ɗan gora mai ɗauke da ruwan tsafi yace "Idan kuna da rabon tsira in kuka kai kofar karshe na hanyar nan, ki buɗe wannan ruwan ki zubawa kofar kaɗan zata buɗe sai ku fita, ragowar ruwan kuma ki ajiye wata rana zai miki amfani ku gudu" sosai su Rimsha suke hawayen rabuwa da duna musamman ma da sukaji yace yasan kashe shi zasu yi sai Rimsha taji wani irin duk babu daɗi a jikin ta Ganin ta tsaya shiru taki tafiya ne ga kuma wayan nan munanan halittu sun kusa cin musu hakan yasa duna ya turata ta cikin ramin mai kama da rijiya A tare Rimsha suka faɗa da Ayla da Kausar dan suna riƙe da hannu juna Yana turasu wayan nan Halittu na isowa wajen, riƙiɗewa shima yayi ya koma irin su suka fara gwabza faɗa a tsakanin su, sai dai daya ke suna daya sai suka fara dukan sa suna ji masa rauni abun tausayi, su kuwa su Barbushi bayan su Rimsha sukabi dan su kamo su su cinye su ɗanye, dan ba zasu barsu su karya musu tarihin gidan Daular mutuwa ba, a tarihin Daular mutuwa duk wanda ya shiga baya fita ya shiga kenan sai a lahira. Su Rimsha kuwa gudun cetan rai suke, tsabar gudun da suke basu san lokacin da suka saki hannun juna ba, kasan cikin ramin duk kasusuwan jikin ɗan adam, sai suke musu kafofin su kashin yake jini na zuba, duk da haka basu damu ba, sun daure suna ta gudu. Kamar ance Rimsha ta juya, ta manta duna yace karsu kuskura su juya kome zai faru da su, tana juyawa sai taga babu Ayla iya Kausar ce kawai, ihu Rimsha ta saki wadda ya sa Kausar dakatawa da gudun da take tare da juyawa, a guje Rimsha ta nufi hanyar komawa Daular mutuwa dan ba zata iya tafi ba tare da Ayla ba, itama Kausar bata da zaɓi dole tabi bayan Rimsha dan su gudu tare su tsira tare. Tashin hankali Abun da ya faru shine lokacin da suke cinkin gudu Ayla ta taka wani kashin mutun mai bala'i tsini ya fasa mata kafa, hakan yasa ta faɗi kasa, taki yin ihu tayi shiru dan bata son ta dakatar da su Rimsha har azo a kama su dukan su, tafi son ko ba ita ba wani daga cikin su ya tsira, kashin ya fasa mata kafa sosai ta yadda ba zata iya gudu ba har su Barbushi suka cin mata a wajen, shine suka kama ta, Barbushi ya goyata a bayan sa ya ci-gaba da bin su Rismha, ga kuma su Rimsha sun juyo suna tinkarar su. Wayyo ni jikan mutun huɗu gaba ɗaya ta ko ina ba sauki, zuciyata ba zata iya jure ganin wannan azaba da my Rimsha take ciki ba. Masu karatu nan na kawo karshen Book 1 wato The beginning kuma shine free, yanzu zamu shiga The struggle masu son ci-gaba da karanta Book nan ku hanzarta kuyi payment naku dan wasan yanzu zai fara, ya kuke ganin wannan cakwakiya, ya kuke tunanin rayuwar lion zai kasan ce bayan mutuwar Michael da ɓatar James?!!, Ya kuke ganin anya Rimsha zata tsira kuwa? Dan ita da kan ta ta juya ta koma Daular mutuwa ga kuma su barbushi ɗauke da Ayla a kan hanya suma suna tinkaro ta!! Yaya Akil zai kare da Umaisha? Meke shirin faruwa tsakanin su?! Anya Abbi zai bawa Akil auren Umaisha kenan? Ya makomar cikin Aunty? Shi zai sube kuwa? Yaya rayuwar Jehan zai kasan ce? Yaya makoman Jelly da Abbo? Yaya makoman Musharraf a gidan Dr William jacop? Gashi dai ya sa hannu a takarda zai yi zaman 4 years, gashi mai tausaya masa wato James baya nan ya ɓace!! Wanene Alhajin dake bibbiyar Aafia?!! Yaya bakoman baba da Mustapha a Daular mutuwa?!! Anya lion zai yafewa mum ɗin sa kuwa?! Anya akoi wanda zai iya rusa Daular mutuwa kuwa?!!!! Shine wace ce ma Queen?!!! Waye ya kafa Daular mutuwa?!!! Menene kama sudin kafa shi?!! Anya kuna ganin Jehan zata iya aikin restaurant har ta biya Ibraheem kuɗin sa?!!! Ina James ya tafi?!! Shine sace sa akayi ko menene?!! Abbo zai auri Jelly kuwa?!!! Idan ta kasan ce ya Imran zai yi?!!! Cakwakiya ziryan domin samun amsoshin ku dole ku kasance da alkalamin *PRINCESS TEEMA* Domin ci-gaba da karanta book ɗin *TRIPLETS* ki hanzar ta kiyi payment naki 500 Naira ne only 👌3167987863 Musa Fatima Zahra first bank, masu Opay bank kuma 9162620621 Musa Fatima Zahra opay bank, sai ku turo shaidar biya ta wannan number 09162620621, kada ki bari a baki labari dan yazu wasan zai fara, na barku lafiya Much kauna 🥰 Share fisabilillah 👏 To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪 💞Star Lady💞 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels