An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KYAUTA. HALITTAR ZUCIYA (1) Shimfid'a Jajare garin jajaye in kaga bak'i to bak'o ne ya ka zo,wannan inkiya ce ta garin Jajere.Jajere gari ne na fulanin damaturu,Malam Madu yana d'aya daga cikin mutanen garin,haifaffan garinne shi tun iyaye da kakanni,mahaifansa ne suka wanke Mariya suka bashi,Mariya kamar 'ya take a gurinsu saboda su sukayi rik'onta tun tana yarinya,sun tsinceta ne a wani kango da ake gini suka rik'eta ba tare da k'yamata ba,suka kuma d'auketa suka bawa d'ansu duk saboda soyayya,anman Madu sam ba ya k'aunar Mariya,ya karb'i auranta ne saboda biyayya ga iyayansa,suna zaune,lafiya ba mai jin kansu duk da Mariya tana matuk'ar hak'uri da wasu halayen na Madu dan baza ta iya fitowa ta fad'a ba ne ana haka ta samu ciki inda ta haifi 'ya mace,zo kuga ruwan tijara gurin Madu shi ba ya son mace,mace ai k'arin wahala ce babu abinda za ta tsinana maka yak'i yin komai na haihuwa sai iyayansa ne suka yi mata,sunama babansa ne ya rad'a mata Halima,(Sunan mahaifiyar Madun kenan)a haka rayuwa ta gangara Mariya na matuk'ar hak'uri da halayen Madu duk saboda darajar iyayansa wanda su take kallo a matsayin nata iyayan da Allah ya bata sama ta ka,gashi yanzu k'asa ta rufewa Inna Halima idanu wacce ta kasance tana tausayinta da taimaka mata da wasu abubuwan,a haka rayuwa take ta juyawa Madu ya sake auran Hajara, haihuwar fari ta haifo masa namiji zo kuga murna gurin Madu sai a wannan haihuwar Mariya ta san mijin nata ba k'aramin arzik'i ne da shi ba dan sosai ya saki bakin aljihu yana wa Hajara da d'anta hidima har zuwa ranar suna inda yaro yaci sunan mahaifin Madu Idris. Tun daga haihuwar Halima,Mariya ba ta sake haihuwa ba har sai da Hajara tayi haihuwa uku a jere duk maza wanda suke ganin so da k'auna da gata gurin Madu,Halima kuwa ko kallo ba ta isheshi ba a cewarsa bazai wahalta mata ba,dan su mata sai dai ka wahalta musu a banza ba tare da kaci moriyarsu ba,inda Allah ya taimaki Halima sai ya yota mai sanyin hali,ko kad'an ba ta dosar mahaifin nasu saboda ta san halinsa,abu kad'an za tayi ya mangareta har yanzu kuwa da take da shekaru takwas a duniya. Hajara da Mariya a lokaci guda suka haihu inda Mariya macen dai ta kuma haifa,inda Hajara ta dinga yadar mata da maganganu shi kwa Madu ba ta isheshi kallo ba daga ita har jinjirar da ta haifa,inda Allah ya taimaketa ta tanadi komai na haihuwarta saboda tana sana'arta ta kayan miya bushashe da kuma wainar gero da k'uli da safe,tunda mai taimakon nata babu ita yanzu a doron k'asa,kamar haihuwar Halima wannan ma mahaifin Madu shi ya nad'awa jaririya suna RAHEENA. Akwai bam-bamcin halaye k'ara k'ara tsakanin Halima da Raheena,Halima mai shiru shiru ce da sanyin hali,duk inda aka nuna ba'a sonta ba ta dosar gurin,yayin da Raheena ta kasance mai kwaraf niya ga tsokanar tsiya a cikinta kamar me,inda kuma Allah ya d'ora mata k'aunar mahaifinsu Madu duk da kasancewar shi yafi tsanarta ma akan Halima,dan dukan da take sha gurinsa bai daki Halima haka ba ga kyararta da yake anman ba shi zai hana ta koma gurinsa ba,zasu had'u ita da Mubarak tsarar haihuwarta d'an wajan Hajara suyi k'iriniya anman idan Madu ya tashi ko dunguri ba zaiwa Mubarak ba anman in ya kama Raheena da duka kamar Allah ya aikoshi. Halayen Raheena suna mugun ciwa Mariya tuwo a k'warya anman babu yadda za tayi sai addu'a ta san k'uruciya ce ko wani yaro da kalar k'uruciyarsa nan gaba idan ta san ciwon kanta ba za tayi ba,gashi yanzu ta aurar da Halima tana cikin shekarunta na sha hud'u kenan Raheena kuma shida,komai na auran Halima Baffa Idris mahaifin Malam Madu shi yayi,har yau yana nisar da d'an nasa anma ya kasa ganewa shiyasa ya d'au ido ya zuba masa ya tabbata akwai ranar da zai gane kad'an daga cikin ni'imar da Allah ya yi maka idan ya azurtaka da samun 'ya mace. Wannan kenan …… Da gudu ta yanko layin gidansu k'afafuwanta fututu hakama kayan jikinta,kafin fitarta sai da Innarta tayi mata wanka tas anman yanzu wani ya ganta zaiyi zaton tafi sati rabonta da wanka,tana gab da shiga soron gidansu suka ci karo da Babansu wanda ya doso kai zai fita,k'afafuwanta ya tad'e ta zube a gurin had'e da sakin k'arar dake nuni da ba k'aramin buguwa tayi ba,kuma taji zafin fad'uwar ainun,ko sauraranta baiyi ba yasa kai ya fice daga soron gidan,yayin da kuma Innarta ta yo soron gidan dan jin ihunta da ya karad'e cikin gidan gaba d'aya,da sassarfa ta isa gareta ta d'agota tana kallon yadda bakinta ya fashe,ba ta kai ga tambayarta abinda ya faru ba sai ga Ramatu ta shigo zauran rik'e da hannun k'aninta jikinsa kwata ce gaba d'aya. ‘’Lafiya?‘’ Inna ta tambayi Ramatu,bayan ta mik'ar da Rahina tsaye har lokacin tana kuka sai dai kuma ta rage sautin kukan nata. ‘’ Rahin ce ta jefashi cikin kwatar gidan Ade,shine Innarmu tace na kawoshi ki wanke masa,ita baza ta iya saka hannunta cikin kwatar ba.‘’ Ba tace komai ba bayan ta gama saurarar Ramatu sai hanun k'anin nata da ta kama bayan ta saki na Rahin tayi ciki da shi,k'ilama sakayyar yaron ce ta saka Rahin d'in fad'uwa har ta fasa bakinta,ba manaki kuma kwatar da ta jefashin ce ta sakata nufo gida da gudu har ta fad'in ta fasa baki . Kowa yasan kwatar gidan Ade da tsinannan d'oyi,k'azamai ne na k'in k'arawa,wani zubin a rariya suke kashi su koroshi waje,shiyasa kowa yake k'ank'yamin kwatar,anman haka Inna ta wankewa yaron kwatar tas,tayi masa wanka had'e da wanke kayan tas,to ya za tayi?D'an kuka ai shi ke janyowa uwarsa jifa. Bayan ta gama wanke kayan ne ta nufi d'aki zata d'an zauna ta huta,dan Rahin ta faki idonta ta kuma ficewa,addu'ar shiriya kawai take nemawa Rahin d'in cikin ranta,har ta tsuguna zata zauna aka rafka sallama daga soron gidan,d'an dakatawa tayi da zaman gabanta na fad'uwa kafin ta amsa sallamar. "Ina magana da Innar Rahin" Cewar Muhammadai mai kanti dake tsaye a soran gidan,fuskarsa a murtuke babu sassauci a cikinta karma ayi tunanin zai d'aga k'afa,dan wallahi bazai d'auki asara ba. Jin abinda akace ya sanyata sanyo hijabi ta nufo soron jikinta a matuk'ar sanyaye da tunanin wata maganar kuma ta innarta ta kuma d'auko mata? [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA. HALITTAR ZUCIYA (2) Idonta akan Ta innarta ya fara sauka wacce ke rik'e da hannun Muhammadai,d'aya hannun nasa kuma rik'e yake da wata yarinya wacce kayan jikinta duk ya b'aci da wani abu mai yauk'i wanda baza ta tantance meye shi ba,sanyi jikinta ya kuma yi don ta tabbatar wata maga Ta innarta ta kuma d'auko mata,don a rana in ba'a kawo k'ararta sau goma ba za'a kawo sau biyar. "Na ajiye k'waina a bakin shago,kafin na bud'e shagon na shiga da shi ciki,shine ta hankad'o wannan yarinyar kai,gaba d'aya sun fashe." Cewar Muhammadai yana kuma d'aure fuskarsa karma tayi tunanin zai yafe. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,yanzu Mhumadai k'wan har na nawa ne?" "Kiret biyar ne" "Nawa kenan ya kama?" Inna ta kuma tambaya. "8000 a ma yadda na saro"Muhammadai ya fad'a yana k'ara tamke fuska,karma tayi tunananin zai iya ragin ko ficika" Jinjina kai Inna tayi,tana shiga tunanin yadda zata lalibo wannan kud'i,don ko jarin wainarta bai kai haka ba,bare kuma d'an kud'in kayan miyan da sai lokaci zuwa lokaci ake cinikinsa."Dan Allah Muhammadai kayi hak'uri zuwa k'arshen watan nan idan na d'au dashina zan baka." "A'a wallahi,ni yanzu nake son kud'ina don wani zan koma na saro kinsan d'an jarin nawa ba wani taka kara ya karya yayi ba." "Yanzu yanzu kuwa ai sai Allah,don ni ko zuwa gobe ma kace ban san inda zan samo maka kud'innan ba,idan baza ka jirayi zuwa k'arshen watan ba,bansan kuma ya zan maka ba." "Zaki san yadda zaki mini idan naje na d'ebo miki 'yan sanda,dan wallahi yau duk masifar da za'ayi sai an biyani kid'ina." Yakai k'arshen maganar yana hankad'a Rahin d'in gaban Inna,saurin tareta Innar tayi bacin haka da sai tayi muguwar fad'uwa. "Hankalinki ya kwanta ko Rahina,kin fi son ki ganni cikin tashin hankali ko yaushe?." "Innarmu wallahi ita ta fara tsokanata,ni kuma ban san ya ajiye k'wai ba da bazan turata gurin ba." Innar ba tace komai ba sai hannunta da ta jaa suka shiga ciki,suna shiga ciki sai ga Halima tayi sallama da gudu Rahin taje ta tarota,duk da a rana takan je mata sau kusan uku,anman idan taga Haliman a cikin gidansu ba k'aramin dad'i take ji ba,ko don ba ta fiya ganinta cikin gidan nasu ba ne oho?tunda ba kasafai takan zo ba,saboda Baba ba ya barinta,da tazo yake korarta indai yana cikin gidan. Rungume k'anwarta Halima tayi cike da so da k'auna,anman da sun zauna guri d'aya sai sun raba gari saboda k'iriniyar Rahin d'in. "Inna ina yini?" "Lafiya lau Mamana,ya kuke ya Abdullahin?" "Lfy lau wallahi yana gaisheki,lafiya naganki wani iri?" "Ina amsawa "Kafin ta numfasa ta kuma cewa. "Ta Innarta ce ta tura wata yarinya kan k'wan Muhammadai suka fashe,yanzun nan yabar k'ofar gidannan yace sai na biyashi kud'inshi ko ya kira mini 'yan sanda." "Innalillahi,kud'in har nawa ne?" "8000 yace,wai akan ma yadda ya saro" Duka ta kaiwa Rahin d'in da ke kusa da ita tana danna wayar Haliman,duk da ba ta san inda take shiga ba,wani wawan ihu ta saki saboda yadda dukan ya shigeta ba zato ba tsammani,aikwa ba shiri tayi jifa da wayar Haliman inda tayi gefe tai fisis fisis. A fusace Haliman tayi kanta ita kuma tayi bayan Inna tana zunduma ihu. "Yi hak'uri Mamana,kinji,sau nawa zan gaya miki ki dinga hak'uri da k'anwar nan taki,idan kowa ya kasa hak'uri da ita ke ya zamar miki dolen doliya ki hak'uri da ita,wata rana idan ba na raye ke zata rab'a taji sanyi domin ke zaki zame mata gurbina." Cike da takaicin Innar ta hanata dukan Rahin d'in take had'a wayar tata,dama wayar ba wata wayar kirki ba,sam ba ma ta saurari me Innar ke fad'i ba saboda ranta da yayi mugub b'aci." "Amman Inna har da d'aurin bayanki Rahin ke samu tana wani iskancin wallahi" "Haba Mamana,yau ke kike gaya mini wannan maganar,maganar da in an jefeni da ita kin fini jin d'acinta?Nonon da kika sha shi Rahina ta sha,tarbiyar da na baki ita na bata ba kuma hakanne zai hana halayyarku bam bamta ba,ba zab'ina bane ba kuma son raina ba ne Rahina ta zamo a haka,duka zagi hantara ba shi zai sauyata ba illa addu'a ina kuma fatan Allah ya tsayar mata iya k'uruciya." "Ba ina nufin ba ki bata tarbiya ba,ba kuma ina nufin ke kike sakata yi ba,ina ganin kamar soyayyar da kike mata ce ta saka hakan saboda tasan baza ki tab'a iya dukanta ba." "Ke kanki shaida ce,da duka yana gyara mutum da ko dukan da Babanku kewa Rahina yasa ta gyaru,so kike Babanku ya daka yayyanta su daka 'yan waje su daka,nima na daka,babu inda zata rab'a taji sanyi kenan?Itama ba zab'inta bane Allah ne yayi ta haka,kuma ko wani yaro da kalar k'uruciyarsa duk me kallon ni na sangarta Rahina Allah ne zai mana sakayya." "Allah ya huci zuciyarki Innarmu" Halima ta fad'a cike da dana sanin furucinta.Sallama aka rafka daga k'war gida,Inna na jin sallamar tace. "Ina to Muhammadai ne ya dawo." "Inna ke a gurinki nawa za'a samu? mu had'a mu bashi kud'insa,ni bana son harka da 'yan sanda" "Ai ina jin kud'in hannuna idan na had'esu gaba d'aya baza su huce dubu hud'u ba." "Kawo na bashi,anjima idan na koma na fasa bankina na cikasa masa sauran." "Yaa Halima zaki bani biyar in kin fasa bankin?" Wata shegiyar harara ta zabga mata kana ta anshi kud'in gurin Inna ta fita kai masa,anci sa'a ya karb'a,da sharad'in anjima tana komawa zai biyo bayanta ya ansa. "Inna sati mai zuwa Abdullahi zai tafi habuja cirani." "Ke dan Allah." "Wallahi kuwa,nima yace idan yaje yaga yanayin garin zai turowa D'ahiru k'aninsa kud'i na bi bayansa,dan yace in ya tafi zai jima bai zo ba,zai dai dingawa su Innarsa aike,saboda matsa masan da suke sai ya k'ara aure wai tunda ni nak'i haihuwa,shiyasa ma ya tsiri tafiyar." "Hmmmm,Allah ya kyautawa wasu mutanen wallahi,da yake ke zaki bawa kanki shiyasa kika k'i haihuwa kenan,in banda jahilci na mutane sun san Allah ke bada haihuwar nan anman da mutum ya kwana biyu bai samu ba za'a jingina masa laifi,dudu auran naku da ko shekara biyu bai rufa ba har an sanya muku idanu,banda ma haihuwar ta zama ta zamani yanzu wata tara cif zaki ji mace ta haihu,da kwa da sai a 'yebi shekaru kafin kiji ance wance ta haihu." "Wallahi kuwa Inna,shiyasa ma bana damuwa,saboda ban isa na bawa kaina abinda Allah bai bani ba,shima kuma bai damu ba,ko nayi zancen sai dai kiji yace"To ke zaki bawa kanki,ba sai sanda Allah yaso ba" Dai dai k'arshen maganarta Hajara tayi sallama ta shigo,taje yinin biki a can mak'otan gidansu,sai yanzun ta dawo,sallamarta kawai suka amsa suka cigaba da hirarsu dama Halima ba kulata take ba,tun wani fad'a da akai tun kafin bikin Haliman,babu yadda Inna ba tai da ita ba akan taci gaba da gaisheta anman fir tak'i,tace gaisuwa kam tsakaninsu da ita har abada,Halima akwai zuciya ban bancinta da Rahina kenan,ita Rahina yanzu zaki mata abu kuma anjima ta komo gurinki. Bayan sallar magariba Inna na cikin zubowa Halima d'anwaken da tayi dominta sai ga sallamar Baba ya shigo cikin gidan,idansa akan Haliman ya fara sauka ya wani had'e fuska,ko gaisuwar da take mik'o masa bai amsa ba yace tazo ta shige ta koma inda ta fito,tsam ta mik'e tana saka hijabinta a ranta fad'i take."Banda arzik'in mahaifiyarta dake cikin gidan da ko fuskarta baza su k'ara gani ba,har sai sun manta ya kalar fuskar tata take.A kwano mai murfi Inna ta juye mata d'an waken ta k'ulle a leda ta bata."To Inna na gode,idan da sauran canji zan bayar a kawo miki sai ki sayi sauran abinda babu a kayan wainar." "To na gode Mamana,Allah ya yiwa rayuwa albarka,ki gaishe da mutan gidan." "Amin Innarmu,zasu ji in sha Allah" "Yauwa Babansu ga Mubarak can a kwance mashashshara ta kwantar da shi sakamakon dukan da Rahin tayi masa." Cewar Hajara,bud'ar bakin Inna sai cewa tayi. "Ke Hajara kiji tsoron Allah,yanzu Mubarak d'in da ke sa'an Rahina,shi za tayiwa dukan da har zai sakashi zazzab'i,bayan ke kanki kinsan k'arfin mace da namiji ba d'aya ba ne,idan har bai saka mata zazzab'i ba ai ba ta saka masa ba." "To zan mata k'arya,sai an magana ba ke ke daure mata baya ba ki kawowa mutum k'auli da ba'adi." Baba kuwa inda Rahin ke kwance na sharar bacci ya nufa,tun bayan gama cin abincinta ta b'ingire a gurin,saboda anyi fitina har an gaji... [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA. Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. HALITTAR ZUCIYA (3) Sa k'amshi sa dad'i,hana gafi k'arni no,spices da curry kenan gangariya gurin k'awata girki. 09037093702 Ina macen da girkinta ke k'arni idan tayi amfani da nama,ina macen da ke son amfani karafish tana tsoron k'arni,ina kuma macen da rashin albasa ke hanata soya k'wai,ina macen da take son girkinta ya k'ara dad'i da d'and'ano da kuma k'amshi?maza hanzarta ki nemi spices d'in Rashuna domin kuwa nata ba irin nasu ba ne.09037093702 Mata da dama idan suka soya kifi zubar da man suke saboda gudun k'arni,abinda kuma ba ku sani ba kun zubar da sinadarin ki kelaya abinki Hajiyata,ki kawo curry da spices d'in Rashuna ki zuba,Hmmm na rantse miki da Allah mityarki ba za tayi k'arni ba. K'afa yasa yakai mata wani irin dukan da ya sanyata farkawar ba shiri had'e da tsanyara wani uban ihu,dukanta ya shiga yi ko ta ina tana ihu tana kwararato shikwa yana fad'in. "Ai yadda kika saka shi yau zai kwana da zazzab'i wallahi yau kema sai kin kwana da shi,shegiya me siffar aljanu,in baki wasa ba wata rana sai na nakasta ki wallahi." Ko kallon inda yake dukanta Inna ba tayi ba tai shigewarta d'aki,duk da zuciyarta dake mata suya bama akan dukan nata da yake ba,a'a irin furucin da yake jifanta da shi,duk wanda ya zauna da su na wuni d'aya sai ya fuskanci irin tsanar da yayiwa Rahina wacce ba ya iya b'oyeta ko a gaban waye,ita kuma zuciyarsa na matuk'ar sonsa da k'aunarsa,abu d'aya take jiye masa shine ranar da ZUCIYAR RAHINAN zata fara tsanarsa wacce kuma ta tabbata wannan tsanar mai iya cireta daga zuciyarta sai Allah kuma. Sai da ya tabbatar ta daku kana ya k'yaleta,band'aki ya shiga ya fito ya d'aura alwala ya fice saboda kiraye kirayen sallar isha da aka fara.Tana zaune tana rusa kuka Sale ya shigo,irin kukan da take ya fara kwaikwaya,aikwa da ta d'auki farantin silbar dake kusa da ita ta lailaya shi ta jefa masa sai kuwa akan goshinsa,wata gigitacciyar k'ara ya saki da ta sanya Hajara saurin fitowa,nufo inda take a zaune yayi yana."Wallahi bazan yadda ba sai na rama." Mik'ewa tayi tana huci tana jiran yazo ayi duk wacce za'ayi,janyeta Inna tayi had'e da fad'in. "Shige kiyi alwala kibar nan gun." Hajara ce a k'ufule tace."Wannan wani irin zalinci ne?Kibar yaro mana ya rama abinda ta masa zaki wani janyeta tsabar rashin gaskiya." Ci kanki Inna ba tace da ita sai tsaiwarta ta gyara tana jiran Rahin d'in ta fito daga band'akin,tana fitowa kuwa Hajara ta hankad'a Sale had'e da fad'in jeka ka rama dukanka,in kuwa ba haka ba wallahi Babanku ya dawo sai na gaya masa tunda ita aljana ce duka ba ya shiga jikinta,ko kuma nace jaka" Inda Rahin d'in ke tsugune na alwala Sale ya nufa Inna ta dakatar da shi da fad'in. "Kada ka sake hannunka ya sauka a jikinta,in ba haka ba wallahi sai ranka yayi mugun b'aci,uban waye yace ka tsokaneta?da kaja girmanka zata bi ta taka shine?" Jaa da baya yayi saboda yana shakkar Innar Rahin d'in,sam bata musu wasa shiyasa suka fi tsoranta ma akan Innarsu,k'wafa kawai yayi,had'e da cewa Rahin d'in. "Shegiya mummuna,duk fad'in garin nan kowa ya shaida Baba baya sonki,kuma wallahi zan kamaki a waje ne inda babu Innar taki sai naga me tare miki." "Ka nad'a mata na jaki wallahi ni nan na tsaya maka,kuma mahaifinka ma ya tsaya maka,yarinya sai kace iblishiya kuma ana dad'a d'aure mata baya,kai nidai Allah na gode maka da ba ka bani 'ya mace ba,ashe ta bakin baban nasu 'ya mace tarin wahala ce." "Shige d'aki,kiyi sallar magariba sannan ki isha." Inna tacewa Rahin,sai da taga shigewarta d'akin kana ta juyo kan Hajara dan mayar da martani. "A gurin kune 'ya mace tarin wahala,anman a gurina ni'ima ce kuma sanyin idaniya,da ace zan k'ara haihuwa dubu,kuma Allah du ya bani 'ya'ya mata da zanyi matuk'ar farin ciki,abinda Rahin kuwa keyi k'utuciya ce kuma kowa da kalar tasa k'uruciyar,wata rana baza kice tayi haka ba,kuma ina ji a jikina wata rana sai kin shiga inuwarta 'ya'ya mazan da kike ganin mafaka ne a gareki sai tawa macen ta zane miiki mafaka kafin su,da kina da hankali da tunani ko akan Halima zaki fahimci falala da ni'imar da yayi mini da ya azurta ni da samunta." Tana kawowa nan tayi shigewarta d'aki ba ta tsaya saurarar kunfar bakin da Inna Hajara ke yi ba ta dai jiyota tana Allah ya sawak'e ta shiga inuwar Rahin d'in ba taga abinda zata tsinana mata ba ita da Allah ya azurtata da samun mazaje har guda biyar ba taga wani abu da wannan iblishiyar za tayi mata ba. A k'udun dine ta samu Rahin d'in tana ta rawar d'ari,alamun zazzab'i ne yake shigarta,paracetamol ta d'auko ta bata tasha,kana tace ta shige cikin gidan sauro ta kwanta ita kuma ta tayar da sallar isha'i. Rantsuwar Baba taci Rahin,dan kwa kwana tayi da azababban zazzab'i,gashi in tana zazzab'i sai tai ta firgita,washe gari da safe kuwa ko makaranta ba taje ba su Fad'ime da suka,biyo mata suka tarar bata da lafiya sai kwa bulki cewa tayi. "Alqur'anin Allah yau nima kwa baza ni ba,komawa zanyi nacewa Innata ba'a yi." cikin marai raita Fad'ime tace. "Kekwa dan Allah Bulki kizo muje,yau ni kad'ai kuke so ku bari,makarantar baza tamini dad'i ba,gashi in naje na yiwa Innata k'arya baza ta yadda ba." "Ai yau ko me zaki Fad'ime ba zanje makarantar nan ba,kin manta jiya na tsokano kin manta jiya na tsokano Abun gidan Bawa me jakai,tace sai mun had'u a makaranta zata ci ubana,kuma me tare mini ba lafiya in ba so kike tayi k'uli k'ulin Kubra da ni ba." Ba yadda Fad'ime ta iya haka ta bar Bulki ta juya gida ita kuma ta nufi makarantar bokon nasu da ke da d'an tazara sosai da su,ajinsu uku a yanzu,kuma ajinsu d'aya duka su ukun,k'awaye ne tun daga yarinta,Bulki tsinanniyar tsokana ce da ita wacce ta dame ta Rahin ta shanye ga tsoro fal ciki,idan tayo tsokanar Rahin ke uwa ke makarb'iya,ita Rahin fitina tafi yawa a cikinta,Fad'ime ce me sanyin hali kawai a cikinsu anman itama idan ana fad'a da d'aya a cikinsu haka zata zage ayi da ita duk da ba ta kasance me son fad'a ba. Bayan sallar la'asar Baba Malam(Mahaifin Madu,Rahina ce ta rad'a masa Baba Malam,dama Malam d'in ake kiransa,Innarta ce me ce masa Baba ita kuma sai ta had'e duka biyun take cewa Baba Malam)yayi sallama cikin gidan,Inna na jin sallamarsa ta fito da hanzari rik'e da tabarma ta shimfid'a masa a gurin da yakan zama a duk sailin da ya kawo musu ziyara,sannu take ta jera mishi har ya cire takalmansa ya nemi guri ya zauna da bismillah a bakinsa,yayin da Inna ta juya ta d'ebo masa ruwan randarta me sanyi a kofin silba ta kawo ta ajiye a gabansa kana ta durk'usa har k'asa ta gaisheshi ya amsa cike da kulawa da soyayya kana yace. "Hala uwata ba ta gidan nan?" "Taje nan gidan Hari ta anso awara,jiya da zazzab'i ta kwana ta kasa cin abinci,shine na bata hansin ta anso awara da kunu ko zata iya ci." "Haba ko da naji,tun da naga ba azo tarb'ata ba nasan ba ta nan,Ayya ashe ba taji dad'i ba?shiyasa Gwaggo (Matarsa da ya aura bayan rasuwar Inna Halima)tace mini yau ba ta biyo daga makaranta ba." "Wallahi kuwa,anman dai da d'an sauk'i." A dai dai nan Inna Hajara ta fito suka gaisa da Malam,ya amsa mata cikin kulawa had'e da tambayarta yara,sai ga Rahin ta shigo da hanzari ta k'araso gurin Malam ta kwanta a jikinsa had'e da fad'in. "Baba Malam" "Uhmmm,Uwata,ya jikin naki?" Ya fad'a yana shafa wuyanta yaji babu zafi. "Naji sauk'i Baba Malam." "To maza gyara zamanki ga gurasa da nama na kawo miki,har da fura." Baki ta washe cike da farin ciki ta gyara zamanta Inna ta d'auko kofi ta juye mata furar a ciki bisa Umarnin Malam,shi kuma ya bud'e mata ledar nama da gurasar ta hau danna lauma kamar ba mara lafiya ba,ta ma manta da ledar awara da kunun da ta ajiye a gefenta saboda taga masoyinta nama,Sale da Mubrak da Kabiru ne suka shigo,suka tisa Rahin d'in a gaba da kallo,Mallam ya d'ad'd'auka ya basu kafin Inna Hajara ta fito ta korasu d'aki tana zaginsu,ko d'aga kai Malam baiyi ya kalleta ba sai hirar su da suke ta yi da Inna Rahin na kora furarta bayan ta gama cin naman. "Ina sonka Baba Malam,ina jin sonka sama da na Baba,ni dama kaine ka haifeni wallahi." Ta fad'i hakan bil hak'k'i da gaskiya har cikin ZUCIYARTA "Nima ina sonki Uwata sosai da sosai,Allah Ubangiji ya nuna mini auranki anan za'a ga soyayya." Rufe idanuwanta tayi alamun jin kunya kafin tace. "Ai Inna tace ba za tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba sai nayi karatu sosai." Tana kai k'arshen maganarta Baba da Idi da Kabiru suka shigo,sun dawo daga gona,jin muryar Baban yana sallama su sale suka fito suna masa oyoyo yayin da Rahin ma ta shiga ayarin 'yan masa oyo yo anman haka ya tureta daga jikinsa alamun ba ya so tazo kusa da shi,gurin Malam ya nufa ya durk'usa yana gaisheshi,yayin da ya amsa masa a sake,kafin suka d'an tattauna game da aikin gona. "Malam, 'yan bindiga fa sun kuma kawo hari k'auyen dake kusa da mu,kuma ana rad'e rad'en k'auyen nan zasu kawowa hari na gaba shiyasa nake k'ara rok'anka dan Allah mu tattara mu koma birni." "Tun tuni na gaya maka,babu abinda zai saka na bar mahaifata,kuma kaima ban aminta ka bar garin nan ba sai dai idan har bana numfashi,ka saka a ranka duk wanda kaga ya mutu lokacinsa ne yayi." Jinjina kai kawai Baba yayi,anman Allah na gani k'auyen gaba d'aya ya fita a kansa kawai dai dan ba yadda zaiyi da mahaifin nasa ne. "Hajara kuje d'aki ke da yara zamui magana." Cewar Malam kafin ya kalli Rahina ma yace. "Uwata kema jeki d'aki kici gaba da shan furarki." Ran Inna Hajara babu dad'i ta shige d'aki yaran suka bi bayanta,dama dawowar Baba ce ta saka ta fitowa bacin haka tasan Mallam d'in ba ya maraba da ita ko kad'an. (A cewarta ba) "Ahmadu .... 09037093702 [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA. Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. HALITTAR ZUCIYA (4) Malam ya kira sunansa,ya amsa yana me bawa Malam d'in dukkanin nutsiwarsa,dan da dukkan alamu magana ce zai masa mai muhimmanci,baiyi mamakin ganin bai cewa Inna ta bashi guri ba dan yasan akwai sirrikan Malan d'in da Innar ta sani wanda ko shi da ya haifa bai sansu ba. "Wanene ni a gurinka." Malam ya jefo masa tambayar nan sai da ya numfasa kafin yace. "Mahaifina ne kai." "To a mtsayina na mahaifinka yau ina k'ara jaddada maka akan abinda muka sanar da kai ni da mahaifiyarka,ko bayan raina ka rabu da Mariya ko ka wulak'anta ta ban yafe maka ba,ina sane da har yau akwai nauyikan da baka sauke mata wannan kuma Allah ne zai tambayeka dalili,dan wallahi dalilinka ba dalili ba ne jahilci ne da jayayya da Ubangin,domin kuwa shine ya halicci ko wani jinsi,kuma shine nan ya bawa Mariya kyautar 'ya'ya matan da kake gudu ya kuma bawa Hajara mazan da kake so saboda haka yaso kuma haka yaga dama dukkaninsu ba zab'insu ba ne ba kuma son ransu ya zab'aba,sai dai dan hakan yayi niya kuma kyautar da yaga damar basu kenan.Bari na sanar da kai abinda baka sani ba,sanda Allah ya bamu cikinka fata muka dinga yi Allah yasa mace ce,anman da aka haifeka kazo a namiji haka muka nuna maka so da gata duk kwa tsanani da son da mukai na mace bai hana mun nuna maka k'auna ba,kuma daga kanka Innarka ba ta sake haihuwa ba har Allah ya bamu kyautar Mariya. Dan haka abinda kake a tak'aice sunanshi jahilci,idan zaka gyara ka gyara dan wallahi abu d'aya nake jiye maka ranar da ZUCIYAR RAHEENA zata fara tsanarka,in bakai wasa ba kuwa sai kazo kana zub da hawayen ta soka wata rana a lokacin kuma bata da ikon yin hakan.Banga abin tsana a mace ba.Mahaifiyarka mace ce,kowa da ka gani a duniya silar zuwansa macece,idan ba macen za'a haifa ma mazan da kake so ne? Mace na nufin k'warin guiwa. Idan ba mace ba hayayyafa. Idan ba mace ba rayuwar halitta. Idan ba mace ba Zubin halitta. Idan ba mace ba d'orewar gobe. Idan ba mace babu ahali. Idan ba mace babu gudanar da rayuwa. Idan ba mace babu samun nutsuwar rayuwa. idan ba mace ba ni'imar rayuwa. Mace abar a tausayawa ce ba abar tsangwama da kyara ba. Idan maganganuna sun hankaltar da kai ruwanka,duk da ba yau na fara ba,idan kaci gaba da nunawa Raheena tsangwama da kyara ruwanka Allah yana gani." Daga haka ya mik'e sukai sallama da Inna ya fice yabar Baba a durk'ushe ko karatun Malam ya shige shi? (To wa ya sani sai mun bishi munji tukunna. ) Washe gari RAHENA ragas ta tashi,dan haka da su Bulki suka biyo mata makaranta a shirye suka tarar da ita,suna zuwa suka rankaya suka tafi Bulki rik'e da jakar Rahin d'in dan ita ke d'aukar mata ba kuma ta isa tace ta gaji baza ta d'auka ba. "Rahin nima jiya fa banje makarantar ba Abun gidan Bawa me jakai na tsokana a burtsatse shekaran jiya shine na gudu tace sai a makaranta zata kama ni taci ubana." "Me yasa ba ki gaya mata ubanki yayi mata kad'an ba sai dai taci Bawa me jakai dan shine dai dai da ita." "Bari nayi sai yau ma gaya mata." A dai dai nan suka shiga cikin ajinsu,Salima ce dake mugun son k'awance da Rahin ta taso ta tareta had'e da fad'in. "Allah yasa kin tahon da wainar Inna ?" "Na dai tawo da ita,idan an fita break in zamu ci sai na kirawoki ." "Me yasa jiya ba kizo ba?na tambayi Fad'ime ba ta kulani ba ." Dan haushinta suke ji yadda take likewa Rahinan ta k'arfin tsiya,yanzun ma tsaki sukai suka wucesu. "Ban ji dad'i ba ne,nayi fama da zazzab'i." "Ayya,Allah ya sawak'e,idan an fita break d'in sai mu fita tare yai d'ari Innata ta bani " Washe baki Rahin tayi had'e da farin ciki,a ranta tana b'uyarwa su Bulki zasui wainar ma yau baza taci tare da su ba. Bayan tashinsu daga makaranta ansha dambe tsakanin Abur wacce Bulki ta tsokano da Rahin,har sai da Rahin tayi mata k'ululu a goshi aikwa tayi rantsuwar baza ta yadda ba washe gari sai takai k'ara gurin Headmastee d'insu dan ba ma za ta kaiwa Innarsu k'arar ba da iyakacinta tace tayi hak'uri. A k'aida kullum aka tashesu daga makaranta sai ta biya ta gidan Ya Halima,a k'ofar gidan suke rabuwa da su Bulki,su huce ita ta shiga ciki,to yauma hakance ta kasance,da gudu ta manna tayi cikin gidan kawa wacce aka biyo a guje,da ta daki wata buta dake babban tsakar gidan ba ta sauka a ko ina ba sai a gadon bayan Innar Audu (Surukar Halima)da ta tsuguna tana hura hutar iccen da ke ta bata wuya,a fusace ta d'ago dan ganin wanda ya jefo mata butar sukai ido hud'u da Rahin tana shishshigar da ido ciki sai kuma tayi murmushi ta bagarar kafin tace. "Innar Audu me kike dafa mana ne." Dan haushi da takaici ba ta san sanda bakinta ya bata amsa da "Innarki Mariya nake dafa muku,dan tsabar rashin kunya ki jefon buta,sannan ki tsareni da k'ananun idanuwanki kina tambayata me nake dafa muku,to uwarki Mariya na had'a da yayarki Halima nake dafawa." Turo baki gaba tayi kafin k'asa k'asa tace."Wannan mitsitsiyar tukunyar taki ai tawa Innata kad'an sai dai wannan tsililin mijin naki me kama da sandar rake,dan shi kam cif tukunyar zata amsheshi har da sarari" "Me kike cewa?" Innar Audu ta tambaya dan ganni bakinta yana motsi,sai kwa Rahin cewa tayi. "Ca nayi da kwa kin samu tsoka ba kamar k'yamushashen mijinki ba da motsatstsiyar Zuwairarki "(Itace Autar Innar daga Audu sai ita) A harzuk'e Innar Audu ta d'auki muciya tayi kanta,da ta manna a guje tayi sashen Halima. Halima kuwa tana can da d'an Audunta,fad'a suka yi da faccalarta ta mata gorin haihuwa shine take ta kuka shi kwa ya saka kayarsa a d'aki yace yau ba inda zashi sai sunyi cikin a yau yau d'innan.(To Malam Audu zafin nema ai baya kawo samu da yana kawo wa da mutane da yawa ba su jiggata ba,samu da rashi duka na Allah,Allah ka bamu zuri'a tsarkakakkiya.) Jin yadda aka banko k'ofarsu aka shigo da mugun gudu yasa Audu hantsilawa gefen gadon yana k'ok'arin shigewa k'ark'ashin gadon,Halima kuwa cikin sif take k'ok'arin shigewa tsabar razana da kad'uwar da sukai babu wanda ya tsaya suturta jikinsa,duk a tunaninsu 'yan bindigar da aka ce suna harin k'auyansu ne suka shigo,a tsakar gidan ta tsaya tana rarraba idanu ,dan Inna ta hana ta afkawa mutane d'aki kai tsaye. "Yaya Halima" Ta shiga rattaba mata kira,jin muryar Rahina yasa Halima sauke ajiyar zuciya da fasa shiga cikin sif din da take ta k'ok'arin yi,zani ta janyo ta d'aura,tana kallo Audu ma ya ja rigarsa yana maidawa,kallon Rahinan take cike da takaici kafin ta hauta da fad'an shigowa a gujen da tayi,sai cewa tayi." To ba Innar Audu ce ta biyoni da muciya ba" "Hala b'arnar da kika saba yi mata kikai mata?" "To ba ita bace daga tambayarta me take dafa mana tace Inna da ke take dafawa ba shine nace..." Saurin katseta Halima tayi,sanin cewar Audu yana jinsu,kuma tasan ba abu me dad'i Rahinan zata fad'a ba. Fitowa Audun yayi yana. "Kaga k'anwar matas,tafi matas kyau,duk da ba haka naso ba,amman haka dai nake maleji,dama can rufa ido aka mini" Wani dad'i ne ya kasheta dan daga Baba Malam sai Innarta sai Audun ne kawai suke cewa tafi Halima kyahu,kowa sai dai kiji yace Halima ta fita kyau, Inna kwa cewa take a jira aga girman Rahinan tata musamman idan ta nutsu guri d'aya. "Allah ya bar mini Yaya Auduna,anman da ni zaka tafi Habujar ko?" "Ai k'afata k'afarki matas,dole naje da ke na sanya ki a makaranta mai kyau da inganci,Allah dai yasa Inna ta bamu ke." Wani ihu da tsalle ta daka tana murna kafin tace. "Zata baku mana,ai Inna tana so nayi karatu sosai,tace baza tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba." "To ya zaki da saurayinki Tanimu?" Ya fad'a cike da tsokana. " Cif wa zai auri wannan k'azamin gaja da shi? Nidai na tafi gayawa Inna da ni za'a Habuja." Ba ta jirayi cewarsu ba ta manna a guje,tayi ball da tukunyar Innar Audu ta kife akan murhun ta kashe hutar da ta bata huya kafin ta kama anman ko waiwaye Rahin ba tayi ba ta fice,Innar Audu ta shiga sababi da masifa har sai da Halima ta kuma hura mata wutar ta mai da mata da tukunyar a ranta tana ta adduar Allah ya shirya musu RAHEENAH. 09037093702 Sa k'amshi sa dad'i,hana gafi k'arni no,spices da curry kenan gangariya gurin k'awata girki. 09037093702 Ina macen da girkinta ke k'arni idan tayi amfani da nama,ina macen da ke son amfani karafish tana tsoron k'arni,ina kuma macen da rashin albasa ke hanata soya k'wai,ina macen da take son girkinta ya k'ara dad'i da d'and'ano da kuma k'amshi?maza hanzarta ki nemi spices d'in Rashuna domin kuwa nata ba irin nasu ba ne.09037093702 Mata da dama idan suka soya kifi zubar da man suke saboda gudun k'arni,abinda kuma ba ku sani ba kun zubar da sinadarin ki kelaya abinki Hajiyata,ki kawo curry da spices d'in Rashuna ki zuba,Hmmm na rantse miki da Allah mityarki ba za tayi k'arni ba. [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH HALITTAR ZUCIYA..... Watpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar Soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar Suruka K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar Zuciya500 Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. (5) Da gudu ta shigo cikin gidan nasu,wanda ba ta kula da redion Baba da ke tsakar gida ba tayi gaba da ita ta ragargaje a gurin dama redion ba ta kirki ba,gefe ta ja cike da tsoro tana shishshigar da idanuwanta ciki,kafin hantar cikinta ta kuma kad'awa jin muryar Baban daga d'akinsa yana. "Kai waye nan ya tab'an radio?" Inna Hajara ce da ke durk'ushe gaban murhu tace. "Wa ka sani banda mahaukaciyar 'yarka" A harzik'e ya fito ya kalli radion dake yashe a k'asa a ragargaje ya d'ago ya kalleta tana ta raba idanuwa,kwalfa yayi ya koma d'aki ya zaro wayar radion ya fito,wayam ya tarar babu ita ba alamunta kallon Inna Hajara yayi had'e da tambayarta. "Ina Rahin d'in take?" "Ta fice" Ta bashi amsa,k'wafa yayi had'e da fad'in. "Zata dawo ta same ni ne" "Idan ta dawo ta sameka dan Allah kada ka barta da ranta,ina ba Sale ne ya lalata radion ka zauna ka gyarata ba ko dunguri ba kai masa ba sai ita da yake tsintarta akayi ba haihuwarta akai ba?" Cewar Inna da fitowarta kenan daga band'aki takaici yasa ta yin magana ta yadda ko yaushe yake nuna yafi son 'ya'yansa maza a kan Rahin d'in. "Ke ni kike gayawa maganar banza,idanma na kasheta ai na kashe banza da ita da babu duk d'aya suke a gurina wallahi,ki bar tunk'aho da Malam,dan wallahi ba shi zai hana na ci miki mutumci ba." D'aki Inna tayi shigewarta ba ta saurareshi ba tana jinsa yana ta sababi a tsakar gidan,dama bata tanka mishi yau dinma kuskure aka,samu. Har yamma Inna na zaman jiran shigowar Rahin shiru kike ji,ga babar Salima ta kaho k'arar Rahin d'in wai tana saka Salimar sato mata kud'i tazo makaranta su kashe,hak'uri ta bata anman da cewar ba musu tayi mata ba tunda ba'a shaidar 'ya'yan yanzu,in Rahin d'in ta dawo zata tisota suzo nan gidan duk inda matsalar take za'ai maganinta,to anman gashi har yamma Rahin d'in shiru ba ta dawo ba,duk inda take tsammaninta taje ba ta nan,gidan Halima ne hop dinta na karshe anman kuma ta rasa wani yaro zata aika. Itakwa Rahin tana can gidan Halima,kamar yadda Innar take tsammani,tsoron dukan Baba take tunda har yau ba ta manta dukan da yayi mata shekaran jiya ba,shiyasa tayi zamanta gidan Haliman,idan taje gurin Innar Audu ta isheta da fitina ta koreta sai ta koma gurin matar wan Audun can ma in ta korota sai ta dawo gurin Haliman,to itama Haliman ba tsira tayi ba kawai itama dan ba yadda za tayi da ita ne,daga k'arshe dai cewa tayi ta tashi ta rakata gida,ita kuma ta botsare ba inda zata sai da ta bata naira ashirin kana ta yadda suka taho,uniform d'innan nata yaci k'aniyarsa ya fita daga hayyacinsa. Halima gaisawa sukayi da Inna kawai ta juyo,dan ba ta k'aunar su had'u da Baba ya koreta ranta yana matuk'ar k'una da suya,sai da Inna taiwa Rahin wanka ta shiryata kana ta sakata gaba da tuhumar ita ke saka Salima na sato kud'in Innarta suna kashewa? Sai da tayi rau rau da ido kafin tace. "Wallahi cewa take Innarta ce ta bata,ni kuma idan naje da waina sai muci tare mu kashe kudin tare." "Ta Innarta ki gayan gaskiya,fain lam takun tarahu." "Fa innahu yaraka" Tayi saurin k'arasa mata,haka Innar ke mata indai tana son gane gaskiyarta,a gaba ta sakata sukaje gidansu Salima,sai gashi da aka titseye Saliman ta fad'i gaskiyar Rahin din ba ta san sato kudin take ba,Innar Saliman kunya duk ta isheta ta bawa Innar Rahin din hak'uri.Kashedi sosai Inna taiwa Rahin akan babu ita babu Salimar,tace ai dama su Bulki basa son ta kulata,Salimar ce ta nane mata anman tawa Innar alkawarin ba ita ba ita. A haka kwanaki ke shud'ewa a hankali su koma watanni,watanni su rikide su koma shekaru cikin hikimomi da iyawar Ubangiji.Su Rahinah har an zana common entrance,ana ta tsalle da murnar jiran zuwan su Halima su tafi da ita Habujar.Audun ne ya fara yin gaba sai da yayi wata shida a can kana ya turowa wansa Magaji kud'i ya yiwa Halima shirin komai na tafiya ta bi bayanshi da alk'awarin idan Rahin ta kare primary Halima zata zo ta taho da ita,sai dai kuma murna da farin cikin Rahin ya koma ciki sabili da Baba da yace babu inda zata je makarantar ma ta gama aure zai mata,a can gidan mijin tayi hankali,Inna babu yadda ta iya tunda maganar aure ake anman ta so Rahin d'in tata tayi karatu sosai sai gashi ita tun tana shekara goma ma Baban zai mata aure ko shekarun Haliman ba ta cika ba sanda aka mata auran.Ihu kuka tumami Rahin baza ta auri Tanimu ba,anman Baba ya kafe sai ta aureshi dan ya karb'i komai na aladarsu yinin biki ya rage,kuma ya samu goyan baya gurin Baba Malam d'in nata tunda shima bai fiya son karatun bokon ba,kuma auran shi ya dace da Rahin d'in sai tayi hankali da nutsuwa.Rahin kuwa tayi rantsuwar baza ta auri Tanimu ba dan haka ta shiga neman hanyar kaucewa wannan aure. Gidansu Tanimu sukaje da ita da su Bulki suka dinga yi musu ruwan duwatsu ko ta ina suna yi suna cusa musu zagi kala kala har da ambato sunan Innar Tanimu da cewa."Zulai idan har kin haifu cikin iyayanki kisa Tanimu ya fasa aurena,dan kwa in na shigo cikin gidianna sai na zame muku masifa da bala'i." Daga nan kuma sai sukai gonar Malam Buba(Mahaifin Tanimu)sukai b'arnarsu san ransu suka sha mangoro sukai nak kana kowa yayi gida. Aikwa a ranar Malam Buba yayi sallama da Baba ya anshi komai da suka kawo na aure,dan ya samu labarin su Rahin ne sukai masa b'arna a gona,ga ruwan duwatsun da sukai a gidansa har goshin Shafa(kanwar Tanimu)suka fasa shiyasa ma suka yanke shawarar fasa aurota dan in ta shigo ba su san wata illa zata yi musu ba,Tanimu dai yasha kuka dan yana mugun son Rahin dan ba yadda zai da mahaifansa ne,ya gaya musu k'uruciya ce nan gaba sai sunsha mamakinta anma sunk'i fahimtarsa bama su tsaya sun saurareshi ba. To dai fad'a k'arshe sai da ya kaure tsakanin Malam Buba da Baba,dan yace sai an biyashi b'arnar da su Rahin suka shiga gonarsa sukai,shikwa Baba yace bazai biya ba sai dai yaje ko wacce tsohuwarta ta biya shi,shikwa Malam Buba yace hukuma ce zata raba su,ai dama yasan 'yarsa bata da hankali da yake neman lik'awa d'ansa,shikwa Baba yace dad'in abin d'an nasa ne ya kawo kansa ba janyoshi yayi ba. A harzuk'e Baba ya shiga cikj ya dank'i Rahin yana jibgarta kamar Allah ya aiko shi yana fad'in. " 'Yar iskar yarinya mara mutumci mara hankali,haka kawai kin janyo mini masifa ina zaman zamana wallahi in baki wasa ba sai na nakasta ki,kuma aure dole ne ki rubuta ki ajiyeshi wallahi sadaka zan bada ke tunda ke annoba ce ga duk wanda ya rab'e ki ." Wani mari da yakai mata ta hantsila ta kifa kan dan damalin k'ofar d'akin Innarta goshinta ya dakin gurin da ta saki wata shegiyar k'ara ta azabar da takai mata ziyara har tsakiyar k'wak'walwarta. "Waiyo Inna Baba zai kasheni,Innata kaina,innata goshina ,innata idona zafi,Innata jini,shi kenan Innata zan mutu ban cika miki burinki ba.... [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH HALITTAR ZUCIYA..... Watpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar Soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar Suruka K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar Zuciya500 Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. (Oum Samha) (DATA SERVICES) (MTN) >500 =150 >1Gb =250 >2Gb =580 >3Gb =900 >4Gb =1200 >5Gb =1500 >10Gb=3000 ( AIRTEL) >500mb =150 >1Gb. =300 >2Gb. =600 >3Gb. =900 >4Gb. =1,200 >5Gb. =1,500 >10Gb. =2,850 (GLO) >1Gb. =350 >2Gb. =700 >3Gb. =1,050 >4Gb. =1,400 >5Gb. =1,750 >10Gb. =3,000 ( 9MOBILE) >1Gb. =450 >2Gb. =1,000 >3Gb. =1,400 >4Gb. =1,700 >5Gb. =2,150 >10Gb. =3,500 >11Gb. =3,800 ✓All data plan valid for 30days. Always available and reliable. Account Details: 8167316776 Ummi Saidu 08167316776 .Thanks as u patronize🤝 (6) Ganin yadda jini ke wanke mata fuska yasa jikin Baba yin sanyi,Inna kuwa ta rasa wani taimako zata bawa Rahin d'in,ga tsohon ciki ne jikinta haihuwa ko yau ko gobe,ga kuma Rahin d'in ta runtse ido tana zunduma uban ihu sai Baba ne jiki a sanyaye ya d'auketa ya nufi camise da ita,treatment in goshin nata akai tana zunduma ihu tana kaiwa Baba duka ko ta ina sai da ya had'e hannuwan nata guri guda kana aka samu aka gama mata har d'inkin goshin nata da ya tsage a tsaye,sai kuma me? Tana bud'e idanuwanta taga babu abinda take gani banda duhu dumd'in ai da ta zunduma wani uban ihu sai da ta firgita mai camise d'in da Baba. "Na shiga uku na lalace Inna Baba ya makanta ni,kizo kice ya maida mini da idanuwana." Hantar cikin Baba ce ta kad'a ya kalli mai camise d'in cike da tsoro. "Ke Rahin nutsu ki gaya mini me kike ji?" Cewar Baba k'irjinsa na dakan lugude. "Wallahi bana ganin komai,ka taimaka mini ka dawo mini da idanuwana wallhi na maka alk'awarin zan auri ko mahaukaci ne ba ma Tanimu ba dan Allah Baba." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Cewar Baba yana kallon mai camise ko da wani taimako da zai musu. "Ai abinda yafi kamata kawai ku bari zuwa gobe da safe ka tafi da ita asibiti anan ne za'a binciki ko wata matsala ce." "Tom shikenan na gode" Cewar Baba ya kamo hannun Rahin d'in suka taho yana ta zabga salati,wata iriyar nadama ce ta shige shi (NADAMA MARA AMFANI)itakwa Rahin kuka take bil hakki tana tausayawa rayuwarta tana fad'in shi kenan rayuwarta ta durkushe ta lalace tunda ta makance zata fara bara a titi,da ta sani da ba tayi jayayya da auran Tanimu ba,gashinan Baba ya makantata a banza makantar da bata jin akwai wanda zai iya auranta a haka,burin rayuwarta(karatu)ya ruguje raga raga. A tsaye suka tarar da Inna ta kasa zaune ta kasa tsaye,k'irjinta sai wani irin bugu yake. "Har d'inki akai a goshin?" Tana jin muryar Inna ta k'ara k'arfin kukanta. "Inna bana ganin komai sai duhu,shi kenan na daina ganinki Innata sai dai naji muryarki,na daina ganin komai,ji nake kamar zan mutu Inna,dan Allah kicewa Baba ya dawon da idona bazan k'ara masa musu ba,bazan k'ara rashin ji ba,zanje duk inda zan samo HANKALI DA NUTSUWAr da kuke so kuga nayi." Innalillahi Inna ke ta ambata a zuciyarta kafin ta kalli Baba tace. "Yau dai hankalinka ya kwanta ka aikata abinda ka dade kana furtawa (furuci)ka nakasta Rahina,sai ka zuba ruwa dan Allah a k'asa kasha tsabar farin ciki." Tana kawowa nan,ta share hawayen da ya biyo kuncinta,ta kamo hannun Rahin d'in suka nufi d'aki tana rarrashinta da cewar zaa gyara mata idanuwanta zata dawo tana gani kamar daa. Baba baisan da wani baki zai wanke kansa gurin Inna da Malam ba,komai zaice komai zai dad'e yana gaya musu baza su yarda ba da niyya yai mata ba duba da furucinsa a kullum a kanta,anman zai nema mata magani matuk'ar zata warke dan goge laifinsa daga idanuwansu harma da na Rahin d'in. Fad'a da sababi babu wanda bai sha a gurin Malam ba,ya tabbata da zai iya dukanshi babu abinda zai hana ya dakeshidon ransa yayi mugun b'aci aunun. "Muddun kana son ganin farin ciki cikin rayuwarka yadda ka zamo silar nakasta Uwata ka zamo silar warkewarta,in ba haka ba ni kaina bazan yafe maka ba." Kalamin mahaifinshi ya k'ara masa k'aimi gurin ganin ya nemawa Rahin lafiya,asibitoci biyu suka je suka bashi shawarar ya kaita asibitin Makka da ke garin kano. Da Inna Hajara ya so su tafi kanon tunda Innar Rahin d'in babu dama anman tace ba inda zata je dan haka suka tafi daga shi sai Rahin d'in. Kasantuwar mota da ta dinga lalace musu ana sallar isha suka shiga garin kano,dan haka ya bari su kwana a tasha washe gari sai sui tambaya su isa asibitin Makan,cikin dare 'yan fashi suka yiwa tashar haure a lokacin Baba yana can ya zaga cikinsa ya rud'e,ya bar Rarhin tana barci,aikwa aka shiga gudun ceton rai kowa ta kansa yake Baba kuwa hankalinsa yana kan Rahin har zuwa lafawar komai ya koma inda take kwance wayam ba ta nan,hankalinsa yayi mugun tashi yadda alk'alami bazai iya rubutawa ba.Kwanansa biyu cikin tashar yana fita bilayin neman Rahin bai ganta ba,har police d'in da suka zo bayan barin 'yan fashin gurin ya sanarwa amman har yau babu wani information haka ya hak'ura ya koma cikin taraddadi da tashin hankali anman da niyar zai dawo yaci gaba da nemanta ko Allah zaisa a dace,fatanshi d'aya Allah yasa ba 'yan fashin ne suka saceta ba.Bai iya gayawa Malam da Inna gaskiyar Rahin d'in ta b'ata ba,musamman da yaga Innar ba dad'i take ji ba sai kawai yace da su anyi aikin,basa bukatar masu jiyya ne shiyasa ya taho anman kwana biyu kawai zai ya koma,a daren washe garin da ya dawo kuma 'yan bindiga suka dira a k'auyan,sun kashe na kashewa sun tafi da na tafiya wanda suka tsira Allah ya tseratar da su,a cikin wanda aka kashe harda Baba Malam da matarsa da Idi suka tafi da Bashir (Da yake Idi da Bashir d'in acan gidan Baba Malam d'in suke kwana)su kuma Baba da Inna,Inna Hajara,Sale,Kabiru,Mubarak suka b'uya a d'akin da Baba ke ajiyar dukiyarsa,kunsan mutumin k'auye ba kowa ya yadda da accaunt ba,k'ofa ya sakawa d'akin me kyau wacce duk dukan da za'a mata kuma datse kanta take ta nan Allah ya kub'utar da su wanda a cikin gumurzun Inna ta haihu ta haifi jaririyarta MACE,rungume 'yarta tayi ta fashe da kuka, ba ta sani ba ashe kukan rashin Malam take,ta rasa mahaifi,ta rasa mai sanyawa jaririyarta suna,ta kuma rasa mai tayata son jaririyarta a wannan karan. Zata iya rantsuwa mutuwar Mallam tafi gigitata akan yadda ta gigita Baba,mutuwar ta kad'ata yadda ba kwa zato,addu'a zata yi ta bin bayansu da ita da itace take jin zata iya cike wani guri na soyayya da d'awainiyar da sukai da ita dan ba tace zata biyasu ba Allah ne kawai zai iya biyansu. An yiwa wa'yanda suka rasu sallah an binbinnesu,a ranar Baba ya harhad'a komai nasa suka bar garin dan da yuyuwar 'yan bindigan suka k'ara waiwayar garin nasu,wasu da dama ma sun bar garin,wanda kwa zaman garin ya zame musu dole haka suka zauna da kuma masu halin rik'au irin na Baba Malam. Halima da d'an Audunta kamar wa'yanda aka sanarwa da abinda ya faru a k'auyansu gaba d'aya hankalinsu yayo gida,dama kuma Haliman na ta shirin zuwa d'aukar Rahin,sai kwa Audun yace tare kawai zasu huce shima hankalinsa ya yo gida,dan yana ta kiran wayar Magaji baya samu,kwana biyu da barin Baba garin su kuma suka dura anan ne suka tarar da bak'in labari dan shi Audu gaba d'aya gidansu babu wanda ya tsira sun kashe na kashewa sun tafi da na tafiya,Halima kuwa tashin hankalinta ba ta san ina su Innarta suka nufa ba,ga cikinsu babu wani mai waya,dama Kabiru ne me wayar kuma sun kasheshi,taji mutuwarsu shi da su Baba Malam ta kuma bi bayansu da addu'a ga kuma mutuwar ajalin mijinta,ta tayashi kukan fili da na zuciya sun taho da daddad'an labari a bakunansu (Halima na dauke da cikin watanni hudu)ashe babu wanda zasu fesawa cikin ahalin nasu,gara ita in da rabo zata ga nata iyayan shi kuwa sun tafi inda babu dawowa har abada,kwana sukayi cikin alhini da k'unar zuciya washe gari suka koma inda suka fito rayuka babu dad'i,kuzari ya tafi sai zuciya ke azabta... [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH HALITTAR ZUCIYA..... Watpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar Soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar Suruka K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar Zuciya500 Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. (Oum Samha) (DATA SERVICES) (MTN) >500 =150 >1Gb =250 >2Gb =580 >3Gb =900 >4Gb =1200 >5Gb =1500 >10Gb=3000 ( AIRTEL) >500mb =150 >1Gb. =300 >2Gb. =600 >3Gb. =900 >4Gb. =1,200 >5Gb. =1,500 >10Gb. =2,850 (GLO) >1Gb. =350 >2Gb. =700 >3Gb. =1,050 >4Gb. =1,400 >5Gb. =1,750 >10Gb. =3,000 ( 9MOBILE) >1Gb. =450 >2Gb. =1,000 >3Gb. =1,400 >4Gb. =1,700 >5Gb. =2,150 >10Gb. =3,500 >11Gb. =3,800 ✓All data plan valid for 30days. Always available and reliable. Account Details: 8167316776 Ummi Saidu 08167316776 .Thanks as u patronize🤝 (7) Baba bai bari sunyi kwanan tasha ba,duk da kasancewar sai dare suka sauka cikin garin kano,gudin kar 'yan fashin su kuma yi musu haure,gashi tare da dukiyarshi yake tafe,duk da ba wanda zaiyi zatan kud'i ne don sun fi kama da tsummokara. Kwatancan gidan hamsin wani bawan Allah yayi musu,musamman da yake babu nisa gidan daga nan tashar sai suka nufi can d'in kai tsaye,suna zuwa ya biya kud'in kwanan da zasu yi kowa hamsin-hamsin. Innar Rahin tafi kowa jigata musamman da yake gata da d'anyen jego,daga ita har jaririyar wanka suke buk'ata shine zasu samu yin bacci cikin nutsuwa,don jaririyar ma sai 'yan koke koke take mata,anan cikin gidan ta samu ta sayi ruwan zafi ta hayi bawo ta fara yiwa jaririyarta wanka ta shiryata kana taje ta yo nata wankan,sai da ta fara wanke band'akin tas kafin ta iya shigarsa don ya mugun k'azancewa babu kyahun gani,ga mamakinta shayi ta tarar me mugun kauri da gurasa a Baba ya ajiye mata,ba tace komai ba anman cikin ranta cike da mamaki har tasha shayin ta ci gurasar ta kwanta. Washe gari ma ruwan zafin ta siya sukai wanka ita da jaririyarta,wainar shinkafa Baba ya siya musu a nan cikin gidan dan yadda ta fuskanta babu abinda ba'a sayarwa a gidan,anman ita har da shayi mai kauri ya siya mata yayin da lamarin nasa ke k'ara d'aure mata kai anman dai ta ja bakinta tayi shiru,ko sallama bai musu ba yasa kai ya fice dan tsoron kar Inna ta sako masa zancen Rahin. Tashar ya fara zuwa don jin ko an samu wani information na b'atan Rahinan,anman bai samu labarin komi ba don haka ya fara bulum biton neman gida tare da wani Malam Habu da Allah ya had'a su a cikin tashar jininsu kuma ya had'u,ba su samu gidan ba duk inda suka je sai dai haya shi kuma yafi son ya siya gidan saboda,idan kana da muhalli komai da zai biyo baya mai sauk'i ne,ganin magariba tayi dole suka hak'ura sai zuwa gobe sa cigaba da bulumbiton neman gidan,haka ya nufo gida k'irjinsa na dukan tara tara da tunanin amsar da zai bawa Inna akan Rahin,ya ya zata d'auki lamarin,zata yadda da duk abinda zai gaya mata ko kuma zata zargeshi da saka hannunsa a b'atan Rahinan?Wannan tunanin kad'ai na dugunzuma zuciyarsa yana kuma sanyashin nadamar tsanar da ya nunawa Rahinan a sarari. RAHINAH hayaniya da iho ihon mutane yasa ta farkawa a firgice tana kiran Baba,jin babu alamun Baban kusa da ita sai ihun mutane da take ji yasa ta fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi,kukanta ne yasa Hadi da ya lab'e daga bayan katangar da take lek'owa idonsa ya sauka a kanta,wani irin sanyi yaji a ransa,yana ganin kamar wahalarsa ce tazo k'arshe idan ya samu damar k'wamushe wannan yarinyar,da azama ya fito ya ja hannunta ya koma inda ya lab'e,ganin yadda take a firgice tana kiran Baba yasa shi janyo wani hankici daga aljihunsa ya shek'a mata,ba tayi baccin da yake so ba anman jikinta ya saki gaba d'aya ta zube a jikinsa,bayan komai ya lafa ya faki idanuwan mutane ya sakata a bayan motarsa,Allah Allah yake gari ya waye ya fice daga cikin tashar dan ko lodi bazai yi ba tunda ga babban lodi ya samu. K'arfe bakwai ya fice daga cikin tashar ya fara sharara gudu akan titi Allah Allah yake yaga ya d'auki hanyar barin gari dan yana hango yawan kud'in da zai samu idan ya kaiwa oga wannan yarinyar sai dai kuma kana naka ne Allah yana na shi,nashi kuma shine gaskiya domin kuwa wani k'aton ice da bai kula da shi ba motarshi ta daka a take sitiyarin motar ya kubfce mishi motar ta kife akan titi,mai ya fara zuba a take ta fara hayak'i alamun tana gab da kamawa da huta,mutum biyu Allah ya jeho zasu huce,su suka taimaka suka ciro Rahina daga cikin motar ba su kai ga fito da Hadi ba motar ta kama da huta. Ko k'warzane babu jikin Rahina,anman a mugun tsorace take,rashin gani babbar illa ce a rayuwa tana jin komai anman bata ganin abinda ke faruwa,kuka take sosai tana kiran sunan Innarta ba ta san ina Baba ya kawota ya ajiye ba ko kuma da had'in bakinsa wannan mutumin yake k'ok'arin sayar da ita,dan taji wayar da yakeyi abinda ya shek'a mata baiyi nasarar sakata bacci ba jininta yana da mugun k'arfi,hankulan mutane na can kan motar da ta kama da huta da kuma k'ok'arin kiran police ta d'auki wata hanya da ban tana tik'ar gudu a ganinta Allah ne ya kub'utar da ita daga hannun azzalumin can dake k'ok'arin sayar da ita,bata da tabbas d'in wanda suka cirota daga motar suma ba azzaluman ba ne,gudu take sosai akan titi wanda ita ba ta san titin bane tunda ba gani take ba,aikam wata mota da ta yanko a guje tai sama da ita ta watsar babu alamun rai a tattare da ita,kifa kai mamallakiyar motar tayi jikin siyiyarin cike da takaici da bak'in cikin wannan mahaukaciyar yarinyar,ba komai take tsoro ba sai azumin da zata janyo mata ba taji ba ba ta gani ba,na Ramadan ma da yaya take sauke shi bare kuma wannan da ya ninka shi,tsaki ta ja kafin ta fito daga motar a ranta tana addu'ar Allah yasa ba ta mutu ba,ko k'warzane babu a jikinta anman da alamun wuya ta saka numfashinta d'aukewa. D'aukarta tayi ta sanya cikin motarta ta juya zuwa asibitin da ta fito,tana jan tsaki akai akai da addu'ar Allah sa ba ta mutu ba,tsabar zafin da kanta ya d'auka baccin da ke cikin idanuwanta ji tayi ya wartsake gaba d'aya. Sai da aka tabbatar mata yarinyar na da rai ta samu karaya a k'afa da hannu kana ta samu nutsuwar tafiya gida bayan ta bar sallahun a yiwa yarinyar duk abinda ya dace idan taje gida zata turo wanda zai kula da ita. Sai takwas da rabi ta baro asibitin zuwa gida,tana parking d'in motarta ta hango Fadwa ta nufi sashen FASIHUL LISAN a ranta tace "Wahalalliya." Tana shiga falon,Fadwan ta shigo da tray a hannunta fuskarta d'auke da damuwa,dining ta nufa kai tsaye ta ajiye tray d'in hannunta tana fad'in. "Ammi sai yanzu?" "Hmm wata yarinya ta jamin musifa wallahi,ta hau kan tsakiyar titi tana gudu ban aune ba na kad'eta,inda Allah ya tak'aita ba ta mutu ba,kicema Talatu ta shirya Bala ya kaita asibitin ta kula da yarinyar kafin a samu kanta." "Ayya Allah ya kiyaye gaba,nima zan bisu na duba yarinyar." Kamar yadda ta tsammata Ammin baza ta tanka ba,ba kwa ta tanka d'in ba sai shigewarta part d'inta tayi dan wanka take buk'ata kafin ta kwanta bacci,kwana tayi ba ta rintsa ba saboda yawaitar marasa lafiya duk rashin kirkinta tsakaninta da Allah take aikinta. Murmushi Fadwa ta saki,ta d'auko kwaandon saka abinci ta jere break fast d'in da ta hana idonta bacci ta tashi ta tsantsarawa Yaa Fasee duk don ta burgeshi ta kuma karkato da hankalinsa kanta a bisa shawarar aminiyarta Siyama,sai dai kuma da yake Namijin duniya ne haka ya tsallake break d'in ko tab'awa bai yi ba ya fice ya bar mata,yanzu kuwa dole ya ci tunda ta samu hanyar zuwa asibitin sai ta bishi da shi har office d'insa wahalarta baza ta zama a banza ba in sha Allah. Sai da ta gama jera abincin kana taje ta sanarwa da Talatu sak'on Ammi,ta d'auki d'an abinda zata d'auka suka fito Bala ya jasu zuwa asibitin... Zan iya cewa a nan free page ya k'are masu buk'atar cigabansa zasu iya samuna kai tsaye a wannan layin 09037093702 na gode. BEBEE'ARTH RASHUNA[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KYAUTA. HALITTAR ZUCIYA (1) Shimfid'a Jajare garin jajaye in kaga bak'i to bak'o ne ya ka zo,wannan inkiya ce ta garin Jajere.Jajere gari ne na fulanin damaturu,Malam Madu yana d'aya daga cikin mutanen garin,haifaffan garinne shi tun iyaye da kakanni,mahaifansa ne suka wanke Mariya suka bashi,Mariya kamar 'ya take a gurinsu saboda su sukayi rik'onta tun tana yarinya,sun tsinceta ne a wani kango da ake gini suka rik'eta ba tare da k'yamata ba,suka kuma d'auketa suka bawa d'ansu duk saboda soyayya,anman Madu sam ba ya k'aunar Mariya,ya karb'i auranta ne saboda biyayya ga iyayansa,suna zaune,lafiya ba mai jin kansu duk da Mariya tana matuk'ar hak'uri da wasu halayen na Madu dan baza ta iya fitowa ta fad'a ba ne ana haka ta samu ciki inda ta haifi 'ya mace,zo kuga ruwan tijara gurin Madu shi ba ya son mace,mace ai k'arin wahala ce babu abinda za ta tsinana maka yak'i yin komai na haihuwa sai iyayansa ne suka yi mata,sunama babansa ne ya rad'a mata Halima,(Sunan mahaifiyar Madun kenan)a haka rayuwa ta gangara Mariya na matuk'ar hak'uri da halayen Madu duk saboda darajar iyayansa wanda su take kallo a matsayin nata iyayan da Allah ya bata sama ta ka,gashi yanzu k'asa ta rufewa Inna Halima idanu wacce ta kasance tana tausayinta da taimaka mata da wasu abubuwan,a haka rayuwa take ta juyawa Madu ya sake auran Hajara, haihuwar fari ta haifo masa namiji zo kuga murna gurin Madu sai a wannan haihuwar Mariya ta san mijin nata ba k'aramin arzik'i ne da shi ba dan sosai ya saki bakin aljihu yana wa Hajara da d'anta hidima har zuwa ranar suna inda yaro yaci sunan mahaifin Madu Idris. Tun daga haihuwar Halima,Mariya ba ta sake haihuwa ba har sai da Hajara tayi haihuwa uku a jere duk maza wanda suke ganin so da k'auna da gata gurin Madu,Halima kuwa ko kallo ba ta isheshi ba a cewarsa bazai wahalta mata ba,dan su mata sai dai ka wahalta musu a banza ba tare da kaci moriyarsu ba,inda Allah ya taimaki Halima sai ya yota mai sanyin hali,ko kad'an ba ta dosar mahaifin nasu saboda ta san halinsa,abu kad'an za tayi ya mangareta har yanzu kuwa da take da shekaru takwas a duniya. Hajara da Mariya a lokaci guda suka haihu inda Mariya macen dai ta kuma haifa,inda Hajara ta dinga yadar mata da maganganu shi kwa Madu ba ta isheshi kallo ba daga ita har jinjirar da ta haifa,inda Allah ya taimaketa ta tanadi komai na haihuwarta saboda tana sana'arta ta kayan miya bushashe da kuma wainar gero da k'uli da safe,tunda mai taimakon nata babu ita yanzu a doron k'asa,kamar haihuwar Halima wannan ma mahaifin Madu shi ya nad'awa jaririya suna RAHEENA. Akwai bam-bamcin halaye k'ara k'ara tsakanin Halima da Raheena,Halima mai shiru shiru ce da sanyin hali,duk inda aka nuna ba'a sonta ba ta dosar gurin,yayin da Raheena ta kasance mai kwaraf niya ga tsokanar tsiya a cikinta kamar me,inda kuma Allah ya d'ora mata k'aunar mahaifinsu Madu duk da kasancewar shi yafi tsanarta ma akan Halima,dan dukan da take sha gurinsa bai daki Halima haka ba ga kyararta da yake anman ba shi zai hana ta koma gurinsa ba,zasu had'u ita da Mubarak tsarar haihuwarta d'an wajan Hajara suyi k'iriniya anman idan Madu ya tashi ko dunguri ba zaiwa Mubarak ba anman in ya kama Raheena da duka kamar Allah ya aikoshi. Halayen Raheena suna mugun ciwa Mariya tuwo a k'warya anman babu yadda za tayi sai addu'a ta san k'uruciya ce ko wani yaro da kalar k'uruciyarsa nan gaba idan ta san ciwon kanta ba za tayi ba,gashi yanzu ta aurar da Halima tana cikin shekarunta na sha hud'u kenan Raheena kuma shida,komai na auran Halima Baffa Idris mahaifin Malam Madu shi yayi,har yau yana nisar da d'an nasa anma ya kasa ganewa shiyasa ya d'au ido ya zuba masa ya tabbata akwai ranar da zai gane kad'an daga cikin ni'imar da Allah ya yi maka idan ya azurtaka da samun 'ya mace. Wannan kenan …… Da gudu ta yanko layin gidansu k'afafuwanta fututu hakama kayan jikinta,kafin fitarta sai da Innarta tayi mata wanka tas anman yanzu wani ya ganta zaiyi zaton tafi sati rabonta da wanka,tana gab da shiga soron gidansu suka ci karo da Babansu wanda ya doso kai zai fita,k'afafuwanta ya tad'e ta zube a gurin had'e da sakin k'arar dake nuni da ba k'aramin buguwa tayi ba,kuma taji zafin fad'uwar ainun,ko sauraranta baiyi ba yasa kai ya fice daga soron gidan,yayin da kuma Innarta ta yo soron gidan dan jin ihunta da ya karad'e cikin gidan gaba d'aya,da sassarfa ta isa gareta ta d'agota tana kallon yadda bakinta ya fashe,ba ta kai ga tambayarta abinda ya faru ba sai ga Ramatu ta shigo zauran rik'e da hannun k'aninta jikinsa kwata ce gaba d'aya. ‘’Lafiya?‘’ Inna ta tambayi Ramatu,bayan ta mik'ar da Rahina tsaye har lokacin tana kuka sai dai kuma ta rage sautin kukan nata. ‘’ Rahin ce ta jefashi cikin kwatar gidan Ade,shine Innarmu tace na kawoshi ki wanke masa,ita baza ta iya saka hannunta cikin kwatar ba.‘’ Ba tace komai ba bayan ta gama saurarar Ramatu sai hanun k'anin nata da ta kama bayan ta saki na Rahin tayi ciki da shi,k'ilama sakayyar yaron ce ta saka Rahin d'in fad'uwa har ta fasa bakinta,ba manaki kuma kwatar da ta jefashin ce ta sakata nufo gida da gudu har ta fad'in ta fasa baki . Kowa yasan kwatar gidan Ade da tsinannan d'oyi,k'azamai ne na k'in k'arawa,wani zubin a rariya suke kashi su koroshi waje,shiyasa kowa yake k'ank'yamin kwatar,anman haka Inna ta wankewa yaron kwatar tas,tayi masa wanka had'e da wanke kayan tas,to ya za tayi?D'an kuka ai shi ke janyowa uwarsa jifa. Bayan ta gama wanke kayan ne ta nufi d'aki zata d'an zauna ta huta,dan Rahin ta faki idonta ta kuma ficewa,addu'ar shiriya kawai take nemawa Rahin d'in cikin ranta,har ta tsuguna zata zauna aka rafka sallama daga soron gidan,d'an dakatawa tayi da zaman gabanta na fad'uwa kafin ta amsa sallamar. "Ina magana da Innar Rahin" Cewar Muhammadai mai kanti dake tsaye a soran gidan,fuskarsa a murtuke babu sassauci a cikinta karma ayi tunanin zai d'aga k'afa,dan wallahi bazai d'auki asara ba. Jin abinda akace ya sanyata sanyo hijabi ta nufo soron jikinta a matuk'ar sanyaye da tunanin wata maganar kuma ta innarta ta kuma d'auko mata? [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA. HALITTAR ZUCIYA (2) Idonta akan Ta innarta ya fara sauka wacce ke rik'e da hannun Muhammadai,d'aya hannun nasa kuma rik'e yake da wata yarinya wacce kayan jikinta duk ya b'aci da wani abu mai yauk'i wanda baza ta tantance meye shi ba,sanyi jikinta ya kuma yi don ta tabbatar wata maga Ta innarta ta kuma d'auko mata,don a rana in ba'a kawo k'ararta sau goma ba za'a kawo sau biyar. "Na ajiye k'waina a bakin shago,kafin na bud'e shagon na shiga da shi ciki,shine ta hankad'o wannan yarinyar kai,gaba d'aya sun fashe." Cewar Muhammadai yana kuma d'aure fuskarsa karma tayi tunanin zai yafe. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,yanzu Mhumadai k'wan har na nawa ne?" "Kiret biyar ne" "Nawa kenan ya kama?" Inna ta kuma tambaya. "8000 a ma yadda na saro"Muhammadai ya fad'a yana k'ara tamke fuska,karma tayi tunananin zai iya ragin ko ficika" Jinjina kai Inna tayi,tana shiga tunanin yadda zata lalibo wannan kud'i,don ko jarin wainarta bai kai haka ba,bare kuma d'an kud'in kayan miyan da sai lokaci zuwa lokaci ake cinikinsa."Dan Allah Muhammadai kayi hak'uri zuwa k'arshen watan nan idan na d'au dashina zan baka." "A'a wallahi,ni yanzu nake son kud'ina don wani zan koma na saro kinsan d'an jarin nawa ba wani taka kara ya karya yayi ba." "Yanzu yanzu kuwa ai sai Allah,don ni ko zuwa gobe ma kace ban san inda zan samo maka kud'innan ba,idan baza ka jirayi zuwa k'arshen watan ba,bansan kuma ya zan maka ba." "Zaki san yadda zaki mini idan naje na d'ebo miki 'yan sanda,dan wallahi yau duk masifar da za'ayi sai an biyani kid'ina." Yakai k'arshen maganar yana hankad'a Rahin d'in gaban Inna,saurin tareta Innar tayi bacin haka da sai tayi muguwar fad'uwa. "Hankalinki ya kwanta ko Rahina,kin fi son ki ganni cikin tashin hankali ko yaushe?." "Innarmu wallahi ita ta fara tsokanata,ni kuma ban san ya ajiye k'wai ba da bazan turata gurin ba." Innar ba tace komai ba sai hannunta da ta jaa suka shiga ciki,suna shiga ciki sai ga Halima tayi sallama da gudu Rahin taje ta tarota,duk da a rana takan je mata sau kusan uku,anman idan taga Haliman a cikin gidansu ba k'aramin dad'i take ji ba,ko don ba ta fiya ganinta cikin gidan nasu ba ne oho?tunda ba kasafai takan zo ba,saboda Baba ba ya barinta,da tazo yake korarta indai yana cikin gidan. Rungume k'anwarta Halima tayi cike da so da k'auna,anman da sun zauna guri d'aya sai sun raba gari saboda k'iriniyar Rahin d'in. "Inna ina yini?" "Lafiya lau Mamana,ya kuke ya Abdullahin?" "Lfy lau wallahi yana gaisheki,lafiya naganki wani iri?" "Ina amsawa "Kafin ta numfasa ta kuma cewa. "Ta Innarta ce ta tura wata yarinya kan k'wan Muhammadai suka fashe,yanzun nan yabar k'ofar gidannan yace sai na biyashi kud'inshi ko ya kira mini 'yan sanda." "Innalillahi,kud'in har nawa ne?" "8000 yace,wai akan ma yadda ya saro" Duka ta kaiwa Rahin d'in da ke kusa da ita tana danna wayar Haliman,duk da ba ta san inda take shiga ba,wani wawan ihu ta saki saboda yadda dukan ya shigeta ba zato ba tsammani,aikwa ba shiri tayi jifa da wayar Haliman inda tayi gefe tai fisis fisis. A fusace Haliman tayi kanta ita kuma tayi bayan Inna tana zunduma ihu. "Yi hak'uri Mamana,kinji,sau nawa zan gaya miki ki dinga hak'uri da k'anwar nan taki,idan kowa ya kasa hak'uri da ita ke ya zamar miki dolen doliya ki hak'uri da ita,wata rana idan ba na raye ke zata rab'a taji sanyi domin ke zaki zame mata gurbina." Cike da takaicin Innar ta hanata dukan Rahin d'in take had'a wayar tata,dama wayar ba wata wayar kirki ba,sam ba ma ta saurari me Innar ke fad'i ba saboda ranta da yayi mugub b'aci." "Amman Inna har da d'aurin bayanki Rahin ke samu tana wani iskancin wallahi" "Haba Mamana,yau ke kike gaya mini wannan maganar,maganar da in an jefeni da ita kin fini jin d'acinta?Nonon da kika sha shi Rahina ta sha,tarbiyar da na baki ita na bata ba kuma hakanne zai hana halayyarku bam bamta ba,ba zab'ina bane ba kuma son raina ba ne Rahina ta zamo a haka,duka zagi hantara ba shi zai sauyata ba illa addu'a ina kuma fatan Allah ya tsayar mata iya k'uruciya." "Ba ina nufin ba ki bata tarbiya ba,ba kuma ina nufin ke kike sakata yi ba,ina ganin kamar soyayyar da kike mata ce ta saka hakan saboda tasan baza ki tab'a iya dukanta ba." "Ke kanki shaida ce,da duka yana gyara mutum da ko dukan da Babanku kewa Rahina yasa ta gyaru,so kike Babanku ya daka yayyanta su daka 'yan waje su daka,nima na daka,babu inda zata rab'a taji sanyi kenan?Itama ba zab'inta bane Allah ne yayi ta haka,kuma ko wani yaro da kalar k'uruciyarsa duk me kallon ni na sangarta Rahina Allah ne zai mana sakayya." "Allah ya huci zuciyarki Innarmu" Halima ta fad'a cike da dana sanin furucinta.Sallama aka rafka daga k'war gida,Inna na jin sallamar tace. "Ina to Muhammadai ne ya dawo." "Inna ke a gurinki nawa za'a samu? mu had'a mu bashi kud'insa,ni bana son harka da 'yan sanda" "Ai ina jin kud'in hannuna idan na had'esu gaba d'aya baza su huce dubu hud'u ba." "Kawo na bashi,anjima idan na koma na fasa bankina na cikasa masa sauran." "Yaa Halima zaki bani biyar in kin fasa bankin?" Wata shegiyar harara ta zabga mata kana ta anshi kud'in gurin Inna ta fita kai masa,anci sa'a ya karb'a,da sharad'in anjima tana komawa zai biyo bayanta ya ansa. "Inna sati mai zuwa Abdullahi zai tafi habuja cirani." "Ke dan Allah." "Wallahi kuwa,nima yace idan yaje yaga yanayin garin zai turowa D'ahiru k'aninsa kud'i na bi bayansa,dan yace in ya tafi zai jima bai zo ba,zai dai dingawa su Innarsa aike,saboda matsa masan da suke sai ya k'ara aure wai tunda ni nak'i haihuwa,shiyasa ma ya tsiri tafiyar." "Hmmmm,Allah ya kyautawa wasu mutanen wallahi,da yake ke zaki bawa kanki shiyasa kika k'i haihuwa kenan,in banda jahilci na mutane sun san Allah ke bada haihuwar nan anman da mutum ya kwana biyu bai samu ba za'a jingina masa laifi,dudu auran naku da ko shekara biyu bai rufa ba har an sanya muku idanu,banda ma haihuwar ta zama ta zamani yanzu wata tara cif zaki ji mace ta haihu,da kwa da sai a 'yebi shekaru kafin kiji ance wance ta haihu." "Wallahi kuwa Inna,shiyasa ma bana damuwa,saboda ban isa na bawa kaina abinda Allah bai bani ba,shima kuma bai damu ba,ko nayi zancen sai dai kiji yace"To ke zaki bawa kanki,ba sai sanda Allah yaso ba" Dai dai k'arshen maganarta Hajara tayi sallama ta shigo,taje yinin biki a can mak'otan gidansu,sai yanzun ta dawo,sallamarta kawai suka amsa suka cigaba da hirarsu dama Halima ba kulata take ba,tun wani fad'a da akai tun kafin bikin Haliman,babu yadda Inna ba tai da ita ba akan taci gaba da gaisheta anman fir tak'i,tace gaisuwa kam tsakaninsu da ita har abada,Halima akwai zuciya ban bancinta da Rahina kenan,ita Rahina yanzu zaki mata abu kuma anjima ta komo gurinki. Bayan sallar magariba Inna na cikin zubowa Halima d'anwaken da tayi dominta sai ga sallamar Baba ya shigo cikin gidan,idansa akan Haliman ya fara sauka ya wani had'e fuska,ko gaisuwar da take mik'o masa bai amsa ba yace tazo ta shige ta koma inda ta fito,tsam ta mik'e tana saka hijabinta a ranta fad'i take."Banda arzik'in mahaifiyarta dake cikin gidan da ko fuskarta baza su k'ara gani ba,har sai sun manta ya kalar fuskar tata take.A kwano mai murfi Inna ta juye mata d'an waken ta k'ulle a leda ta bata."To Inna na gode,idan da sauran canji zan bayar a kawo miki sai ki sayi sauran abinda babu a kayan wainar." "To na gode Mamana,Allah ya yiwa rayuwa albarka,ki gaishe da mutan gidan." "Amin Innarmu,zasu ji in sha Allah" "Yauwa Babansu ga Mubarak can a kwance mashashshara ta kwantar da shi sakamakon dukan da Rahin tayi masa." Cewar Hajara,bud'ar bakin Inna sai cewa tayi. "Ke Hajara kiji tsoron Allah,yanzu Mubarak d'in da ke sa'an Rahina,shi za tayiwa dukan da har zai sakashi zazzab'i,bayan ke kanki kinsan k'arfin mace da namiji ba d'aya ba ne,idan har bai saka mata zazzab'i ba ai ba ta saka masa ba." "To zan mata k'arya,sai an magana ba ke ke daure mata baya ba ki kawowa mutum k'auli da ba'adi." Baba kuwa inda Rahin ke kwance na sharar bacci ya nufa,tun bayan gama cin abincinta ta b'ingire a gurin,saboda anyi fitina har an gaji... [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA. Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. HALITTAR ZUCIYA (3) Sa k'amshi sa dad'i,hana gafi k'arni no,spices da curry kenan gangariya gurin k'awata girki. 09037093702 Ina macen da girkinta ke k'arni idan tayi amfani da nama,ina macen da ke son amfani karafish tana tsoron k'arni,ina kuma macen da rashin albasa ke hanata soya k'wai,ina macen da take son girkinta ya k'ara dad'i da d'and'ano da kuma k'amshi?maza hanzarta ki nemi spices d'in Rashuna domin kuwa nata ba irin nasu ba ne.09037093702 Mata da dama idan suka soya kifi zubar da man suke saboda gudun k'arni,abinda kuma ba ku sani ba kun zubar da sinadarin ki kelaya abinki Hajiyata,ki kawo curry da spices d'in Rashuna ki zuba,Hmmm na rantse miki da Allah mityarki ba za tayi k'arni ba. K'afa yasa yakai mata wani irin dukan da ya sanyata farkawar ba shiri had'e da tsanyara wani uban ihu,dukanta ya shiga yi ko ta ina tana ihu tana kwararato shikwa yana fad'in. "Ai yadda kika saka shi yau zai kwana da zazzab'i wallahi yau kema sai kin kwana da shi,shegiya me siffar aljanu,in baki wasa ba wata rana sai na nakasta ki wallahi." Ko kallon inda yake dukanta Inna ba tayi ba tai shigewarta d'aki,duk da zuciyarta dake mata suya bama akan dukan nata da yake ba,a'a irin furucin da yake jifanta da shi,duk wanda ya zauna da su na wuni d'aya sai ya fuskanci irin tsanar da yayiwa Rahina wacce ba ya iya b'oyeta ko a gaban waye,ita kuma zuciyarsa na matuk'ar sonsa da k'aunarsa,abu d'aya take jiye masa shine ranar da ZUCIYAR RAHINAN zata fara tsanarsa wacce kuma ta tabbata wannan tsanar mai iya cireta daga zuciyarta sai Allah kuma. Sai da ya tabbatar ta daku kana ya k'yaleta,band'aki ya shiga ya fito ya d'aura alwala ya fice saboda kiraye kirayen sallar isha da aka fara.Tana zaune tana rusa kuka Sale ya shigo,irin kukan da take ya fara kwaikwaya,aikwa da ta d'auki farantin silbar dake kusa da ita ta lailaya shi ta jefa masa sai kuwa akan goshinsa,wata gigitacciyar k'ara ya saki da ta sanya Hajara saurin fitowa,nufo inda take a zaune yayi yana."Wallahi bazan yadda ba sai na rama." Mik'ewa tayi tana huci tana jiran yazo ayi duk wacce za'ayi,janyeta Inna tayi had'e da fad'in. "Shige kiyi alwala kibar nan gun." Hajara ce a k'ufule tace."Wannan wani irin zalinci ne?Kibar yaro mana ya rama abinda ta masa zaki wani janyeta tsabar rashin gaskiya." Ci kanki Inna ba tace da ita sai tsaiwarta ta gyara tana jiran Rahin d'in ta fito daga band'akin,tana fitowa kuwa Hajara ta hankad'a Sale had'e da fad'in jeka ka rama dukanka,in kuwa ba haka ba wallahi Babanku ya dawo sai na gaya masa tunda ita aljana ce duka ba ya shiga jikinta,ko kuma nace jaka" Inda Rahin d'in ke tsugune na alwala Sale ya nufa Inna ta dakatar da shi da fad'in. "Kada ka sake hannunka ya sauka a jikinta,in ba haka ba wallahi sai ranka yayi mugun b'aci,uban waye yace ka tsokaneta?da kaja girmanka zata bi ta taka shine?" Jaa da baya yayi saboda yana shakkar Innar Rahin d'in,sam bata musu wasa shiyasa suka fi tsoranta ma akan Innarsu,k'wafa kawai yayi,had'e da cewa Rahin d'in. "Shegiya mummuna,duk fad'in garin nan kowa ya shaida Baba baya sonki,kuma wallahi zan kamaki a waje ne inda babu Innar taki sai naga me tare miki." "Ka nad'a mata na jaki wallahi ni nan na tsaya maka,kuma mahaifinka ma ya tsaya maka,yarinya sai kace iblishiya kuma ana dad'a d'aure mata baya,kai nidai Allah na gode maka da ba ka bani 'ya mace ba,ashe ta bakin baban nasu 'ya mace tarin wahala ce." "Shige d'aki,kiyi sallar magariba sannan ki isha." Inna tacewa Rahin,sai da taga shigewarta d'akin kana ta juyo kan Hajara dan mayar da martani. "A gurin kune 'ya mace tarin wahala,anman a gurina ni'ima ce kuma sanyin idaniya,da ace zan k'ara haihuwa dubu,kuma Allah du ya bani 'ya'ya mata da zanyi matuk'ar farin ciki,abinda Rahin kuwa keyi k'utuciya ce kuma kowa da kalar tasa k'uruciyar,wata rana baza kice tayi haka ba,kuma ina ji a jikina wata rana sai kin shiga inuwarta 'ya'ya mazan da kike ganin mafaka ne a gareki sai tawa macen ta zane miiki mafaka kafin su,da kina da hankali da tunani ko akan Halima zaki fahimci falala da ni'imar da yayi mini da ya azurta ni da samunta." Tana kawowa nan tayi shigewarta d'aki ba ta tsaya saurarar kunfar bakin da Inna Hajara ke yi ba ta dai jiyota tana Allah ya sawak'e ta shiga inuwar Rahin d'in ba taga abinda zata tsinana mata ba ita da Allah ya azurtata da samun mazaje har guda biyar ba taga wani abu da wannan iblishiyar za tayi mata ba. A k'udun dine ta samu Rahin d'in tana ta rawar d'ari,alamun zazzab'i ne yake shigarta,paracetamol ta d'auko ta bata tasha,kana tace ta shige cikin gidan sauro ta kwanta ita kuma ta tayar da sallar isha'i. Rantsuwar Baba taci Rahin,dan kwa kwana tayi da azababban zazzab'i,gashi in tana zazzab'i sai tai ta firgita,washe gari da safe kuwa ko makaranta ba taje ba su Fad'ime da suka,biyo mata suka tarar bata da lafiya sai kwa bulki cewa tayi. "Alqur'anin Allah yau nima kwa baza ni ba,komawa zanyi nacewa Innata ba'a yi." cikin marai raita Fad'ime tace. "Kekwa dan Allah Bulki kizo muje,yau ni kad'ai kuke so ku bari,makarantar baza tamini dad'i ba,gashi in naje na yiwa Innata k'arya baza ta yadda ba." "Ai yau ko me zaki Fad'ime ba zanje makarantar nan ba,kin manta jiya na tsokano kin manta jiya na tsokano Abun gidan Bawa me jakai,tace sai mun had'u a makaranta zata ci ubana,kuma me tare mini ba lafiya in ba so kike tayi k'uli k'ulin Kubra da ni ba." Ba yadda Fad'ime ta iya haka ta bar Bulki ta juya gida ita kuma ta nufi makarantar bokon nasu da ke da d'an tazara sosai da su,ajinsu uku a yanzu,kuma ajinsu d'aya duka su ukun,k'awaye ne tun daga yarinta,Bulki tsinanniyar tsokana ce da ita wacce ta dame ta Rahin ta shanye ga tsoro fal ciki,idan tayo tsokanar Rahin ke uwa ke makarb'iya,ita Rahin fitina tafi yawa a cikinta,Fad'ime ce me sanyin hali kawai a cikinsu anman itama idan ana fad'a da d'aya a cikinsu haka zata zage ayi da ita duk da ba ta kasance me son fad'a ba. Bayan sallar la'asar Baba Malam(Mahaifin Madu,Rahina ce ta rad'a masa Baba Malam,dama Malam d'in ake kiransa,Innarta ce me ce masa Baba ita kuma sai ta had'e duka biyun take cewa Baba Malam)yayi sallama cikin gidan,Inna na jin sallamarsa ta fito da hanzari rik'e da tabarma ta shimfid'a masa a gurin da yakan zama a duk sailin da ya kawo musu ziyara,sannu take ta jera mishi har ya cire takalmansa ya nemi guri ya zauna da bismillah a bakinsa,yayin da Inna ta juya ta d'ebo masa ruwan randarta me sanyi a kofin silba ta kawo ta ajiye a gabansa kana ta durk'usa har k'asa ta gaisheshi ya amsa cike da kulawa da soyayya kana yace. "Hala uwata ba ta gidan nan?" "Taje nan gidan Hari ta anso awara,jiya da zazzab'i ta kwana ta kasa cin abinci,shine na bata hansin ta anso awara da kunu ko zata iya ci." "Haba ko da naji,tun da naga ba azo tarb'ata ba nasan ba ta nan,Ayya ashe ba taji dad'i ba?shiyasa Gwaggo (Matarsa da ya aura bayan rasuwar Inna Halima)tace mini yau ba ta biyo daga makaranta ba." "Wallahi kuwa,anman dai da d'an sauk'i." A dai dai nan Inna Hajara ta fito suka gaisa da Malam,ya amsa mata cikin kulawa had'e da tambayarta yara,sai ga Rahin ta shigo da hanzari ta k'araso gurin Malam ta kwanta a jikinsa had'e da fad'in. "Baba Malam" "Uhmmm,Uwata,ya jikin naki?" Ya fad'a yana shafa wuyanta yaji babu zafi. "Naji sauk'i Baba Malam." "To maza gyara zamanki ga gurasa da nama na kawo miki,har da fura." Baki ta washe cike da farin ciki ta gyara zamanta Inna ta d'auko kofi ta juye mata furar a ciki bisa Umarnin Malam,shi kuma ya bud'e mata ledar nama da gurasar ta hau danna lauma kamar ba mara lafiya ba,ta ma manta da ledar awara da kunun da ta ajiye a gefenta saboda taga masoyinta nama,Sale da Mubrak da Kabiru ne suka shigo,suka tisa Rahin d'in a gaba da kallo,Mallam ya d'ad'd'auka ya basu kafin Inna Hajara ta fito ta korasu d'aki tana zaginsu,ko d'aga kai Malam baiyi ya kalleta ba sai hirar su da suke ta yi da Inna Rahin na kora furarta bayan ta gama cin naman. "Ina sonka Baba Malam,ina jin sonka sama da na Baba,ni dama kaine ka haifeni wallahi." Ta fad'i hakan bil hak'k'i da gaskiya har cikin ZUCIYARTA "Nima ina sonki Uwata sosai da sosai,Allah Ubangiji ya nuna mini auranki anan za'a ga soyayya." Rufe idanuwanta tayi alamun jin kunya kafin tace. "Ai Inna tace ba za tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba sai nayi karatu sosai." Tana kai k'arshen maganarta Baba da Idi da Kabiru suka shigo,sun dawo daga gona,jin muryar Baban yana sallama su sale suka fito suna masa oyoyo yayin da Rahin ma ta shiga ayarin 'yan masa oyo yo anman haka ya tureta daga jikinsa alamun ba ya so tazo kusa da shi,gurin Malam ya nufa ya durk'usa yana gaisheshi,yayin da ya amsa masa a sake,kafin suka d'an tattauna game da aikin gona. "Malam, 'yan bindiga fa sun kuma kawo hari k'auyen dake kusa da mu,kuma ana rad'e rad'en k'auyen nan zasu kawowa hari na gaba shiyasa nake k'ara rok'anka dan Allah mu tattara mu koma birni." "Tun tuni na gaya maka,babu abinda zai saka na bar mahaifata,kuma kaima ban aminta ka bar garin nan ba sai dai idan har bana numfashi,ka saka a ranka duk wanda kaga ya mutu lokacinsa ne yayi." Jinjina kai kawai Baba yayi,anman Allah na gani k'auyen gaba d'aya ya fita a kansa kawai dai dan ba yadda zaiyi da mahaifin nasa ne. "Hajara kuje d'aki ke da yara zamui magana." Cewar Malam kafin ya kalli Rahina ma yace. "Uwata kema jeki d'aki kici gaba da shan furarki." Ran Inna Hajara babu dad'i ta shige d'aki yaran suka bi bayanta,dama dawowar Baba ce ta saka ta fitowa bacin haka tasan Mallam d'in ba ya maraba da ita ko kad'an. (A cewarta ba) "Ahmadu .... 09037093702 [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH 2023 Wattpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar surika K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar ZUciya500 Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA. Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. HALITTAR ZUCIYA (4) Malam ya kira sunansa,ya amsa yana me bawa Malam d'in dukkanin nutsiwarsa,dan da dukkan alamu magana ce zai masa mai muhimmanci,baiyi mamakin ganin bai cewa Inna ta bashi guri ba dan yasan akwai sirrikan Malan d'in da Innar ta sani wanda ko shi da ya haifa bai sansu ba. "Wanene ni a gurinka." Malam ya jefo masa tambayar nan sai da ya numfasa kafin yace. "Mahaifina ne kai." "To a mtsayina na mahaifinka yau ina k'ara jaddada maka akan abinda muka sanar da kai ni da mahaifiyarka,ko bayan raina ka rabu da Mariya ko ka wulak'anta ta ban yafe maka ba,ina sane da har yau akwai nauyikan da baka sauke mata wannan kuma Allah ne zai tambayeka dalili,dan wallahi dalilinka ba dalili ba ne jahilci ne da jayayya da Ubangin,domin kuwa shine ya halicci ko wani jinsi,kuma shine nan ya bawa Mariya kyautar 'ya'ya matan da kake gudu ya kuma bawa Hajara mazan da kake so saboda haka yaso kuma haka yaga dama dukkaninsu ba zab'insu ba ne ba kuma son ransu ya zab'aba,sai dai dan hakan yayi niya kuma kyautar da yaga damar basu kenan.Bari na sanar da kai abinda baka sani ba,sanda Allah ya bamu cikinka fata muka dinga yi Allah yasa mace ce,anman da aka haifeka kazo a namiji haka muka nuna maka so da gata duk kwa tsanani da son da mukai na mace bai hana mun nuna maka k'auna ba,kuma daga kanka Innarka ba ta sake haihuwa ba har Allah ya bamu kyautar Mariya. Dan haka abinda kake a tak'aice sunanshi jahilci,idan zaka gyara ka gyara dan wallahi abu d'aya nake jiye maka ranar da ZUCIYAR RAHEENA zata fara tsanarka,in bakai wasa ba kuwa sai kazo kana zub da hawayen ta soka wata rana a lokacin kuma bata da ikon yin hakan.Banga abin tsana a mace ba.Mahaifiyarka mace ce,kowa da ka gani a duniya silar zuwansa macece,idan ba macen za'a haifa ma mazan da kake so ne? Mace na nufin k'warin guiwa. Idan ba mace ba hayayyafa. Idan ba mace ba rayuwar halitta. Idan ba mace ba Zubin halitta. Idan ba mace ba d'orewar gobe. Idan ba mace babu ahali. Idan ba mace babu gudanar da rayuwa. Idan ba mace babu samun nutsuwar rayuwa. idan ba mace ba ni'imar rayuwa. Mace abar a tausayawa ce ba abar tsangwama da kyara ba. Idan maganganuna sun hankaltar da kai ruwanka,duk da ba yau na fara ba,idan kaci gaba da nunawa Raheena tsangwama da kyara ruwanka Allah yana gani." Daga haka ya mik'e sukai sallama da Inna ya fice yabar Baba a durk'ushe ko karatun Malam ya shige shi? (To wa ya sani sai mun bishi munji tukunna. ) Washe gari RAHENA ragas ta tashi,dan haka da su Bulki suka biyo mata makaranta a shirye suka tarar da ita,suna zuwa suka rankaya suka tafi Bulki rik'e da jakar Rahin d'in dan ita ke d'aukar mata ba kuma ta isa tace ta gaji baza ta d'auka ba. "Rahin nima jiya fa banje makarantar ba Abun gidan Bawa me jakai na tsokana a burtsatse shekaran jiya shine na gudu tace sai a makaranta zata kama ni taci ubana." "Me yasa ba ki gaya mata ubanki yayi mata kad'an ba sai dai taci Bawa me jakai dan shine dai dai da ita." "Bari nayi sai yau ma gaya mata." A dai dai nan suka shiga cikin ajinsu,Salima ce dake mugun son k'awance da Rahin ta taso ta tareta had'e da fad'in. "Allah yasa kin tahon da wainar Inna ?" "Na dai tawo da ita,idan an fita break in zamu ci sai na kirawoki ." "Me yasa jiya ba kizo ba?na tambayi Fad'ime ba ta kulani ba ." Dan haushinta suke ji yadda take likewa Rahinan ta k'arfin tsiya,yanzun ma tsaki sukai suka wucesu. "Ban ji dad'i ba ne,nayi fama da zazzab'i." "Ayya,Allah ya sawak'e,idan an fita break d'in sai mu fita tare yai d'ari Innata ta bani " Washe baki Rahin tayi had'e da farin ciki,a ranta tana b'uyarwa su Bulki zasui wainar ma yau baza taci tare da su ba. Bayan tashinsu daga makaranta ansha dambe tsakanin Abur wacce Bulki ta tsokano da Rahin,har sai da Rahin tayi mata k'ululu a goshi aikwa tayi rantsuwar baza ta yadda ba washe gari sai takai k'ara gurin Headmastee d'insu dan ba ma za ta kaiwa Innarsu k'arar ba da iyakacinta tace tayi hak'uri. A k'aida kullum aka tashesu daga makaranta sai ta biya ta gidan Ya Halima,a k'ofar gidan suke rabuwa da su Bulki,su huce ita ta shiga ciki,to yauma hakance ta kasance,da gudu ta manna tayi cikin gidan kawa wacce aka biyo a guje,da ta daki wata buta dake babban tsakar gidan ba ta sauka a ko ina ba sai a gadon bayan Innar Audu (Surukar Halima)da ta tsuguna tana hura hutar iccen da ke ta bata wuya,a fusace ta d'ago dan ganin wanda ya jefo mata butar sukai ido hud'u da Rahin tana shishshigar da ido ciki sai kuma tayi murmushi ta bagarar kafin tace. "Innar Audu me kike dafa mana ne." Dan haushi da takaici ba ta san sanda bakinta ya bata amsa da "Innarki Mariya nake dafa muku,dan tsabar rashin kunya ki jefon buta,sannan ki tsareni da k'ananun idanuwanki kina tambayata me nake dafa muku,to uwarki Mariya na had'a da yayarki Halima nake dafawa." Turo baki gaba tayi kafin k'asa k'asa tace."Wannan mitsitsiyar tukunyar taki ai tawa Innata kad'an sai dai wannan tsililin mijin naki me kama da sandar rake,dan shi kam cif tukunyar zata amsheshi har da sarari" "Me kike cewa?" Innar Audu ta tambaya dan ganni bakinta yana motsi,sai kwa Rahin cewa tayi. "Ca nayi da kwa kin samu tsoka ba kamar k'yamushashen mijinki ba da motsatstsiyar Zuwairarki "(Itace Autar Innar daga Audu sai ita) A harzuk'e Innar Audu ta d'auki muciya tayi kanta,da ta manna a guje tayi sashen Halima. Halima kuwa tana can da d'an Audunta,fad'a suka yi da faccalarta ta mata gorin haihuwa shine take ta kuka shi kwa ya saka kayarsa a d'aki yace yau ba inda zashi sai sunyi cikin a yau yau d'innan.(To Malam Audu zafin nema ai baya kawo samu da yana kawo wa da mutane da yawa ba su jiggata ba,samu da rashi duka na Allah,Allah ka bamu zuri'a tsarkakakkiya.) Jin yadda aka banko k'ofarsu aka shigo da mugun gudu yasa Audu hantsilawa gefen gadon yana k'ok'arin shigewa k'ark'ashin gadon,Halima kuwa cikin sif take k'ok'arin shigewa tsabar razana da kad'uwar da sukai babu wanda ya tsaya suturta jikinsa,duk a tunaninsu 'yan bindigar da aka ce suna harin k'auyansu ne suka shigo,a tsakar gidan ta tsaya tana rarraba idanu ,dan Inna ta hana ta afkawa mutane d'aki kai tsaye. "Yaya Halima" Ta shiga rattaba mata kira,jin muryar Rahina yasa Halima sauke ajiyar zuciya da fasa shiga cikin sif din da take ta k'ok'arin yi,zani ta janyo ta d'aura,tana kallo Audu ma ya ja rigarsa yana maidawa,kallon Rahinan take cike da takaici kafin ta hauta da fad'an shigowa a gujen da tayi,sai cewa tayi." To ba Innar Audu ce ta biyoni da muciya ba" "Hala b'arnar da kika saba yi mata kikai mata?" "To ba ita bace daga tambayarta me take dafa mana tace Inna da ke take dafawa ba shine nace..." Saurin katseta Halima tayi,sanin cewar Audu yana jinsu,kuma tasan ba abu me dad'i Rahinan zata fad'a ba. Fitowa Audun yayi yana. "Kaga k'anwar matas,tafi matas kyau,duk da ba haka naso ba,amman haka dai nake maleji,dama can rufa ido aka mini" Wani dad'i ne ya kasheta dan daga Baba Malam sai Innarta sai Audun ne kawai suke cewa tafi Halima kyahu,kowa sai dai kiji yace Halima ta fita kyau, Inna kwa cewa take a jira aga girman Rahinan tata musamman idan ta nutsu guri d'aya. "Allah ya bar mini Yaya Auduna,anman da ni zaka tafi Habujar ko?" "Ai k'afata k'afarki matas,dole naje da ke na sanya ki a makaranta mai kyau da inganci,Allah dai yasa Inna ta bamu ke." Wani ihu da tsalle ta daka tana murna kafin tace. "Zata baku mana,ai Inna tana so nayi karatu sosai,tace baza tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba." "To ya zaki da saurayinki Tanimu?" Ya fad'a cike da tsokana. " Cif wa zai auri wannan k'azamin gaja da shi? Nidai na tafi gayawa Inna da ni za'a Habuja." Ba ta jirayi cewarsu ba ta manna a guje,tayi ball da tukunyar Innar Audu ta kife akan murhun ta kashe hutar da ta bata huya kafin ta kama anman ko waiwaye Rahin ba tayi ba ta fice,Innar Audu ta shiga sababi da masifa har sai da Halima ta kuma hura mata wutar ta mai da mata da tukunyar a ranta tana ta adduar Allah ya shirya musu RAHEENAH. 09037093702 Sa k'amshi sa dad'i,hana gafi k'arni no,spices da curry kenan gangariya gurin k'awata girki. 09037093702 Ina macen da girkinta ke k'arni idan tayi amfani da nama,ina macen da ke son amfani karafish tana tsoron k'arni,ina kuma macen da rashin albasa ke hanata soya k'wai,ina macen da take son girkinta ya k'ara dad'i da d'and'ano da kuma k'amshi?maza hanzarta ki nemi spices d'in Rashuna domin kuwa nata ba irin nasu ba ne.09037093702 Mata da dama idan suka soya kifi zubar da man suke saboda gudun k'arni,abinda kuma ba ku sani ba kun zubar da sinadarin ki kelaya abinki Hajiyata,ki kawo curry da spices d'in Rashuna ki zuba,Hmmm na rantse miki da Allah mityarki ba za tayi k'arni ba. [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH HALITTAR ZUCIYA..... Watpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar Soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar Suruka K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar Zuciya500 Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. (5) Da gudu ta shigo cikin gidan nasu,wanda ba ta kula da redion Baba da ke tsakar gida ba tayi gaba da ita ta ragargaje a gurin dama redion ba ta kirki ba,gefe ta ja cike da tsoro tana shishshigar da idanuwanta ciki,kafin hantar cikinta ta kuma kad'awa jin muryar Baban daga d'akinsa yana. "Kai waye nan ya tab'an radio?" Inna Hajara ce da ke durk'ushe gaban murhu tace. "Wa ka sani banda mahaukaciyar 'yarka" A harzik'e ya fito ya kalli radion dake yashe a k'asa a ragargaje ya d'ago ya kalleta tana ta raba idanuwa,kwalfa yayi ya koma d'aki ya zaro wayar radion ya fito,wayam ya tarar babu ita ba alamunta kallon Inna Hajara yayi had'e da tambayarta. "Ina Rahin d'in take?" "Ta fice" Ta bashi amsa,k'wafa yayi had'e da fad'in. "Zata dawo ta same ni ne" "Idan ta dawo ta sameka dan Allah kada ka barta da ranta,ina ba Sale ne ya lalata radion ka zauna ka gyarata ba ko dunguri ba kai masa ba sai ita da yake tsintarta akayi ba haihuwarta akai ba?" Cewar Inna da fitowarta kenan daga band'aki takaici yasa ta yin magana ta yadda ko yaushe yake nuna yafi son 'ya'yansa maza a kan Rahin d'in. "Ke ni kike gayawa maganar banza,idanma na kasheta ai na kashe banza da ita da babu duk d'aya suke a gurina wallahi,ki bar tunk'aho da Malam,dan wallahi ba shi zai hana na ci miki mutumci ba." D'aki Inna tayi shigewarta ba ta saurareshi ba tana jinsa yana ta sababi a tsakar gidan,dama bata tanka mishi yau dinma kuskure aka,samu. Har yamma Inna na zaman jiran shigowar Rahin shiru kike ji,ga babar Salima ta kaho k'arar Rahin d'in wai tana saka Salimar sato mata kud'i tazo makaranta su kashe,hak'uri ta bata anman da cewar ba musu tayi mata ba tunda ba'a shaidar 'ya'yan yanzu,in Rahin d'in ta dawo zata tisota suzo nan gidan duk inda matsalar take za'ai maganinta,to anman gashi har yamma Rahin d'in shiru ba ta dawo ba,duk inda take tsammaninta taje ba ta nan,gidan Halima ne hop dinta na karshe anman kuma ta rasa wani yaro zata aika. Itakwa Rahin tana can gidan Halima,kamar yadda Innar take tsammani,tsoron dukan Baba take tunda har yau ba ta manta dukan da yayi mata shekaran jiya ba,shiyasa tayi zamanta gidan Haliman,idan taje gurin Innar Audu ta isheta da fitina ta koreta sai ta koma gurin matar wan Audun can ma in ta korota sai ta dawo gurin Haliman,to itama Haliman ba tsira tayi ba kawai itama dan ba yadda za tayi da ita ne,daga k'arshe dai cewa tayi ta tashi ta rakata gida,ita kuma ta botsare ba inda zata sai da ta bata naira ashirin kana ta yadda suka taho,uniform d'innan nata yaci k'aniyarsa ya fita daga hayyacinsa. Halima gaisawa sukayi da Inna kawai ta juyo,dan ba ta k'aunar su had'u da Baba ya koreta ranta yana matuk'ar k'una da suya,sai da Inna taiwa Rahin wanka ta shiryata kana ta sakata gaba da tuhumar ita ke saka Salima na sato kud'in Innarta suna kashewa? Sai da tayi rau rau da ido kafin tace. "Wallahi cewa take Innarta ce ta bata,ni kuma idan naje da waina sai muci tare mu kashe kudin tare." "Ta Innarta ki gayan gaskiya,fain lam takun tarahu." "Fa innahu yaraka" Tayi saurin k'arasa mata,haka Innar ke mata indai tana son gane gaskiyarta,a gaba ta sakata sukaje gidansu Salima,sai gashi da aka titseye Saliman ta fad'i gaskiyar Rahin din ba ta san sato kudin take ba,Innar Saliman kunya duk ta isheta ta bawa Innar Rahin din hak'uri.Kashedi sosai Inna taiwa Rahin akan babu ita babu Salimar,tace ai dama su Bulki basa son ta kulata,Salimar ce ta nane mata anman tawa Innar alkawarin ba ita ba ita. A haka kwanaki ke shud'ewa a hankali su koma watanni,watanni su rikide su koma shekaru cikin hikimomi da iyawar Ubangiji.Su Rahinah har an zana common entrance,ana ta tsalle da murnar jiran zuwan su Halima su tafi da ita Habujar.Audun ne ya fara yin gaba sai da yayi wata shida a can kana ya turowa wansa Magaji kud'i ya yiwa Halima shirin komai na tafiya ta bi bayanshi da alk'awarin idan Rahin ta kare primary Halima zata zo ta taho da ita,sai dai kuma murna da farin cikin Rahin ya koma ciki sabili da Baba da yace babu inda zata je makarantar ma ta gama aure zai mata,a can gidan mijin tayi hankali,Inna babu yadda ta iya tunda maganar aure ake anman ta so Rahin d'in tata tayi karatu sosai sai gashi ita tun tana shekara goma ma Baban zai mata aure ko shekarun Haliman ba ta cika ba sanda aka mata auran.Ihu kuka tumami Rahin baza ta auri Tanimu ba,anman Baba ya kafe sai ta aureshi dan ya karb'i komai na aladarsu yinin biki ya rage,kuma ya samu goyan baya gurin Baba Malam d'in nata tunda shima bai fiya son karatun bokon ba,kuma auran shi ya dace da Rahin d'in sai tayi hankali da nutsuwa.Rahin kuwa tayi rantsuwar baza ta auri Tanimu ba dan haka ta shiga neman hanyar kaucewa wannan aure. Gidansu Tanimu sukaje da ita da su Bulki suka dinga yi musu ruwan duwatsu ko ta ina suna yi suna cusa musu zagi kala kala har da ambato sunan Innar Tanimu da cewa."Zulai idan har kin haifu cikin iyayanki kisa Tanimu ya fasa aurena,dan kwa in na shigo cikin gidianna sai na zame muku masifa da bala'i." Daga nan kuma sai sukai gonar Malam Buba(Mahaifin Tanimu)sukai b'arnarsu san ransu suka sha mangoro sukai nak kana kowa yayi gida. Aikwa a ranar Malam Buba yayi sallama da Baba ya anshi komai da suka kawo na aure,dan ya samu labarin su Rahin ne sukai masa b'arna a gona,ga ruwan duwatsun da sukai a gidansa har goshin Shafa(kanwar Tanimu)suka fasa shiyasa ma suka yanke shawarar fasa aurota dan in ta shigo ba su san wata illa zata yi musu ba,Tanimu dai yasha kuka dan yana mugun son Rahin dan ba yadda zai da mahaifansa ne,ya gaya musu k'uruciya ce nan gaba sai sunsha mamakinta anma sunk'i fahimtarsa bama su tsaya sun saurareshi ba. To dai fad'a k'arshe sai da ya kaure tsakanin Malam Buba da Baba,dan yace sai an biyashi b'arnar da su Rahin suka shiga gonarsa sukai,shikwa Baba yace bazai biya ba sai dai yaje ko wacce tsohuwarta ta biya shi,shikwa Malam Buba yace hukuma ce zata raba su,ai dama yasan 'yarsa bata da hankali da yake neman lik'awa d'ansa,shikwa Baba yace dad'in abin d'an nasa ne ya kawo kansa ba janyoshi yayi ba. A harzuk'e Baba ya shiga cikj ya dank'i Rahin yana jibgarta kamar Allah ya aiko shi yana fad'in. " 'Yar iskar yarinya mara mutumci mara hankali,haka kawai kin janyo mini masifa ina zaman zamana wallahi in baki wasa ba sai na nakasta ki,kuma aure dole ne ki rubuta ki ajiyeshi wallahi sadaka zan bada ke tunda ke annoba ce ga duk wanda ya rab'e ki ." Wani mari da yakai mata ta hantsila ta kifa kan dan damalin k'ofar d'akin Innarta goshinta ya dakin gurin da ta saki wata shegiyar k'ara ta azabar da takai mata ziyara har tsakiyar k'wak'walwarta. "Waiyo Inna Baba zai kasheni,Innata kaina,innata goshina ,innata idona zafi,Innata jini,shi kenan Innata zan mutu ban cika miki burinki ba.... [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH HALITTAR ZUCIYA..... Watpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar Soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar Suruka K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar Zuciya500 Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. (Oum Samha) (DATA SERVICES) (MTN) >500 =150 >1Gb =250 >2Gb =580 >3Gb =900 >4Gb =1200 >5Gb =1500 >10Gb=3000 ( AIRTEL) >500mb =150 >1Gb. =300 >2Gb. =600 >3Gb. =900 >4Gb. =1,200 >5Gb. =1,500 >10Gb. =2,850 (GLO) >1Gb. =350 >2Gb. =700 >3Gb. =1,050 >4Gb. =1,400 >5Gb. =1,750 >10Gb. =3,000 ( 9MOBILE) >1Gb. =450 >2Gb. =1,000 >3Gb. =1,400 >4Gb. =1,700 >5Gb. =2,150 >10Gb. =3,500 >11Gb. =3,800 ✓All data plan valid for 30days. Always available and reliable. Account Details: 8167316776 Ummi Saidu 08167316776 .Thanks as u patronize🤝 (6) Ganin yadda jini ke wanke mata fuska yasa jikin Baba yin sanyi,Inna kuwa ta rasa wani taimako zata bawa Rahin d'in,ga tsohon ciki ne jikinta haihuwa ko yau ko gobe,ga kuma Rahin d'in ta runtse ido tana zunduma uban ihu sai Baba ne jiki a sanyaye ya d'auketa ya nufi camise da ita,treatment in goshin nata akai tana zunduma ihu tana kaiwa Baba duka ko ta ina sai da ya had'e hannuwan nata guri guda kana aka samu aka gama mata har d'inkin goshin nata da ya tsage a tsaye,sai kuma me? Tana bud'e idanuwanta taga babu abinda take gani banda duhu dumd'in ai da ta zunduma wani uban ihu sai da ta firgita mai camise d'in da Baba. "Na shiga uku na lalace Inna Baba ya makanta ni,kizo kice ya maida mini da idanuwana." Hantar cikin Baba ce ta kad'a ya kalli mai camise d'in cike da tsoro. "Ke Rahin nutsu ki gaya mini me kike ji?" Cewar Baba k'irjinsa na dakan lugude. "Wallahi bana ganin komai,ka taimaka mini ka dawo mini da idanuwana wallhi na maka alk'awarin zan auri ko mahaukaci ne ba ma Tanimu ba dan Allah Baba." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Cewar Baba yana kallon mai camise ko da wani taimako da zai musu. "Ai abinda yafi kamata kawai ku bari zuwa gobe da safe ka tafi da ita asibiti anan ne za'a binciki ko wata matsala ce." "Tom shikenan na gode" Cewar Baba ya kamo hannun Rahin d'in suka taho yana ta zabga salati,wata iriyar nadama ce ta shige shi (NADAMA MARA AMFANI)itakwa Rahin kuka take bil hakki tana tausayawa rayuwarta tana fad'in shi kenan rayuwarta ta durkushe ta lalace tunda ta makance zata fara bara a titi,da ta sani da ba tayi jayayya da auran Tanimu ba,gashinan Baba ya makantata a banza makantar da bata jin akwai wanda zai iya auranta a haka,burin rayuwarta(karatu)ya ruguje raga raga. A tsaye suka tarar da Inna ta kasa zaune ta kasa tsaye,k'irjinta sai wani irin bugu yake. "Har d'inki akai a goshin?" Tana jin muryar Inna ta k'ara k'arfin kukanta. "Inna bana ganin komai sai duhu,shi kenan na daina ganinki Innata sai dai naji muryarki,na daina ganin komai,ji nake kamar zan mutu Inna,dan Allah kicewa Baba ya dawon da idona bazan k'ara masa musu ba,bazan k'ara rashin ji ba,zanje duk inda zan samo HANKALI DA NUTSUWAr da kuke so kuga nayi." Innalillahi Inna ke ta ambata a zuciyarta kafin ta kalli Baba tace. "Yau dai hankalinka ya kwanta ka aikata abinda ka dade kana furtawa (furuci)ka nakasta Rahina,sai ka zuba ruwa dan Allah a k'asa kasha tsabar farin ciki." Tana kawowa nan,ta share hawayen da ya biyo kuncinta,ta kamo hannun Rahin d'in suka nufi d'aki tana rarrashinta da cewar zaa gyara mata idanuwanta zata dawo tana gani kamar daa. Baba baisan da wani baki zai wanke kansa gurin Inna da Malam ba,komai zaice komai zai dad'e yana gaya musu baza su yarda ba da niyya yai mata ba duba da furucinsa a kullum a kanta,anman zai nema mata magani matuk'ar zata warke dan goge laifinsa daga idanuwansu harma da na Rahin d'in. Fad'a da sababi babu wanda bai sha a gurin Malam ba,ya tabbata da zai iya dukanshi babu abinda zai hana ya dakeshidon ransa yayi mugun b'aci aunun. "Muddun kana son ganin farin ciki cikin rayuwarka yadda ka zamo silar nakasta Uwata ka zamo silar warkewarta,in ba haka ba ni kaina bazan yafe maka ba." Kalamin mahaifinshi ya k'ara masa k'aimi gurin ganin ya nemawa Rahin lafiya,asibitoci biyu suka je suka bashi shawarar ya kaita asibitin Makka da ke garin kano. Da Inna Hajara ya so su tafi kanon tunda Innar Rahin d'in babu dama anman tace ba inda zata je dan haka suka tafi daga shi sai Rahin d'in. Kasantuwar mota da ta dinga lalace musu ana sallar isha suka shiga garin kano,dan haka ya bari su kwana a tasha washe gari sai sui tambaya su isa asibitin Makan,cikin dare 'yan fashi suka yiwa tashar haure a lokacin Baba yana can ya zaga cikinsa ya rud'e,ya bar Rarhin tana barci,aikwa aka shiga gudun ceton rai kowa ta kansa yake Baba kuwa hankalinsa yana kan Rahin har zuwa lafawar komai ya koma inda take kwance wayam ba ta nan,hankalinsa yayi mugun tashi yadda alk'alami bazai iya rubutawa ba.Kwanansa biyu cikin tashar yana fita bilayin neman Rahin bai ganta ba,har police d'in da suka zo bayan barin 'yan fashin gurin ya sanarwa amman har yau babu wani information haka ya hak'ura ya koma cikin taraddadi da tashin hankali anman da niyar zai dawo yaci gaba da nemanta ko Allah zaisa a dace,fatanshi d'aya Allah yasa ba 'yan fashin ne suka saceta ba.Bai iya gayawa Malam da Inna gaskiyar Rahin d'in ta b'ata ba,musamman da yaga Innar ba dad'i take ji ba sai kawai yace da su anyi aikin,basa bukatar masu jiyya ne shiyasa ya taho anman kwana biyu kawai zai ya koma,a daren washe garin da ya dawo kuma 'yan bindiga suka dira a k'auyan,sun kashe na kashewa sun tafi da na tafiya wanda suka tsira Allah ya tseratar da su,a cikin wanda aka kashe harda Baba Malam da matarsa da Idi suka tafi da Bashir (Da yake Idi da Bashir d'in acan gidan Baba Malam d'in suke kwana)su kuma Baba da Inna,Inna Hajara,Sale,Kabiru,Mubarak suka b'uya a d'akin da Baba ke ajiyar dukiyarsa,kunsan mutumin k'auye ba kowa ya yadda da accaunt ba,k'ofa ya sakawa d'akin me kyau wacce duk dukan da za'a mata kuma datse kanta take ta nan Allah ya kub'utar da su wanda a cikin gumurzun Inna ta haihu ta haifi jaririyarta MACE,rungume 'yarta tayi ta fashe da kuka, ba ta sani ba ashe kukan rashin Malam take,ta rasa mahaifi,ta rasa mai sanyawa jaririyarta suna,ta kuma rasa mai tayata son jaririyarta a wannan karan. Zata iya rantsuwa mutuwar Mallam tafi gigitata akan yadda ta gigita Baba,mutuwar ta kad'ata yadda ba kwa zato,addu'a zata yi ta bin bayansu da ita da itace take jin zata iya cike wani guri na soyayya da d'awainiyar da sukai da ita dan ba tace zata biyasu ba Allah ne kawai zai iya biyansu. An yiwa wa'yanda suka rasu sallah an binbinnesu,a ranar Baba ya harhad'a komai nasa suka bar garin dan da yuyuwar 'yan bindigan suka k'ara waiwayar garin nasu,wasu da dama ma sun bar garin,wanda kwa zaman garin ya zame musu dole haka suka zauna da kuma masu halin rik'au irin na Baba Malam. Halima da d'an Audunta kamar wa'yanda aka sanarwa da abinda ya faru a k'auyansu gaba d'aya hankalinsu yayo gida,dama kuma Haliman na ta shirin zuwa d'aukar Rahin,sai kwa Audun yace tare kawai zasu huce shima hankalinsa ya yo gida,dan yana ta kiran wayar Magaji baya samu,kwana biyu da barin Baba garin su kuma suka dura anan ne suka tarar da bak'in labari dan shi Audu gaba d'aya gidansu babu wanda ya tsira sun kashe na kashewa sun tafi da na tafiya,Halima kuwa tashin hankalinta ba ta san ina su Innarta suka nufa ba,ga cikinsu babu wani mai waya,dama Kabiru ne me wayar kuma sun kasheshi,taji mutuwarsu shi da su Baba Malam ta kuma bi bayansu da addu'a ga kuma mutuwar ajalin mijinta,ta tayashi kukan fili da na zuciya sun taho da daddad'an labari a bakunansu (Halima na dauke da cikin watanni hudu)ashe babu wanda zasu fesawa cikin ahalin nasu,gara ita in da rabo zata ga nata iyayan shi kuwa sun tafi inda babu dawowa har abada,kwana sukayi cikin alhini da k'unar zuciya washe gari suka koma inda suka fito rayuka babu dad'i,kuzari ya tafi sai zuciya ke azabta... [9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH HALITTAR ZUCIYA..... Watpad@Rashuna Mama Jiddah Heenah Silar Soyayya Masoya Rabee'ah Babbar Cuta Muguwar Suruka K'addarar Rayuwarmu Cikin Duniyarmu500 Katanga500 Cin Amana500 Wadjda500 Halittar Zuciya500 Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani. (Oum Samha) (DATA SERVICES) (MTN) >500 =150 >1Gb =250 >2Gb =580 >3Gb =900 >4Gb =1200 >5Gb =1500 >10Gb=3000 ( AIRTEL) >500mb =150 >1Gb. =300 >2Gb. =600 >3Gb. =900 >4Gb. =1,200 >5Gb. =1,500 >10Gb. =2,850 (GLO) >1Gb. =350 >2Gb. =700 >3Gb. =1,050 >4Gb. =1,400 >5Gb. =1,750 >10Gb. =3,000 ( 9MOBILE) >1Gb. =450 >2Gb. =1,000 >3Gb. =1,400 >4Gb. =1,700 >5Gb. =2,150 >10Gb. =3,500 >11Gb. =3,800 ✓All data plan valid for 30days. Always available and reliable. Account Details: 8167316776 Ummi Saidu 08167316776 .Thanks as u patronize🤝 (7) Baba bai bari sunyi kwanan tasha ba,duk da kasancewar sai dare suka sauka cikin garin kano,gudin kar 'yan fashin su kuma yi musu haure,gashi tare da dukiyarshi yake tafe,duk da ba wanda zaiyi zatan kud'i ne don sun fi kama da tsummokara. Kwatancan gidan hamsin wani bawan Allah yayi musu,musamman da yake babu nisa gidan daga nan tashar sai suka nufi can d'in kai tsaye,suna zuwa ya biya kud'in kwanan da zasu yi kowa hamsin-hamsin. Innar Rahin tafi kowa jigata musamman da yake gata da d'anyen jego,daga ita har jaririyar wanka suke buk'ata shine zasu samu yin bacci cikin nutsuwa,don jaririyar ma sai 'yan koke koke take mata,anan cikin gidan ta samu ta sayi ruwan zafi ta hayi bawo ta fara yiwa jaririyarta wanka ta shiryata kana taje ta yo nata wankan,sai da ta fara wanke band'akin tas kafin ta iya shigarsa don ya mugun k'azancewa babu kyahun gani,ga mamakinta shayi ta tarar me mugun kauri da gurasa a Baba ya ajiye mata,ba tace komai ba anman cikin ranta cike da mamaki har tasha shayin ta ci gurasar ta kwanta. Washe gari ma ruwan zafin ta siya sukai wanka ita da jaririyarta,wainar shinkafa Baba ya siya musu a nan cikin gidan dan yadda ta fuskanta babu abinda ba'a sayarwa a gidan,anman ita har da shayi mai kauri ya siya mata yayin da lamarin nasa ke k'ara d'aure mata kai anman dai ta ja bakinta tayi shiru,ko sallama bai musu ba yasa kai ya fice dan tsoron kar Inna ta sako masa zancen Rahin. Tashar ya fara zuwa don jin ko an samu wani information na b'atan Rahinan,anman bai samu labarin komi ba don haka ya fara bulum biton neman gida tare da wani Malam Habu da Allah ya had'a su a cikin tashar jininsu kuma ya had'u,ba su samu gidan ba duk inda suka je sai dai haya shi kuma yafi son ya siya gidan saboda,idan kana da muhalli komai da zai biyo baya mai sauk'i ne,ganin magariba tayi dole suka hak'ura sai zuwa gobe sa cigaba da bulumbiton neman gidan,haka ya nufo gida k'irjinsa na dukan tara tara da tunanin amsar da zai bawa Inna akan Rahin,ya ya zata d'auki lamarin,zata yadda da duk abinda zai gaya mata ko kuma zata zargeshi da saka hannunsa a b'atan Rahinan?Wannan tunanin kad'ai na dugunzuma zuciyarsa yana kuma sanyashin nadamar tsanar da ya nunawa Rahinan a sarari. RAHINAH hayaniya da iho ihon mutane yasa ta farkawa a firgice tana kiran Baba,jin babu alamun Baban kusa da ita sai ihun mutane da take ji yasa ta fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi,kukanta ne yasa Hadi da ya lab'e daga bayan katangar da take lek'owa idonsa ya sauka a kanta,wani irin sanyi yaji a ransa,yana ganin kamar wahalarsa ce tazo k'arshe idan ya samu damar k'wamushe wannan yarinyar,da azama ya fito ya ja hannunta ya koma inda ya lab'e,ganin yadda take a firgice tana kiran Baba yasa shi janyo wani hankici daga aljihunsa ya shek'a mata,ba tayi baccin da yake so ba anman jikinta ya saki gaba d'aya ta zube a jikinsa,bayan komai ya lafa ya faki idanuwan mutane ya sakata a bayan motarsa,Allah Allah yake gari ya waye ya fice daga cikin tashar dan ko lodi bazai yi ba tunda ga babban lodi ya samu. K'arfe bakwai ya fice daga cikin tashar ya fara sharara gudu akan titi Allah Allah yake yaga ya d'auki hanyar barin gari dan yana hango yawan kud'in da zai samu idan ya kaiwa oga wannan yarinyar sai dai kuma kana naka ne Allah yana na shi,nashi kuma shine gaskiya domin kuwa wani k'aton ice da bai kula da shi ba motarshi ta daka a take sitiyarin motar ya kubfce mishi motar ta kife akan titi,mai ya fara zuba a take ta fara hayak'i alamun tana gab da kamawa da huta,mutum biyu Allah ya jeho zasu huce,su suka taimaka suka ciro Rahina daga cikin motar ba su kai ga fito da Hadi ba motar ta kama da huta. Ko k'warzane babu jikin Rahina,anman a mugun tsorace take,rashin gani babbar illa ce a rayuwa tana jin komai anman bata ganin abinda ke faruwa,kuka take sosai tana kiran sunan Innarta ba ta san ina Baba ya kawota ya ajiye ba ko kuma da had'in bakinsa wannan mutumin yake k'ok'arin sayar da ita,dan taji wayar da yakeyi abinda ya shek'a mata baiyi nasarar sakata bacci ba jininta yana da mugun k'arfi,hankulan mutane na can kan motar da ta kama da huta da kuma k'ok'arin kiran police ta d'auki wata hanya da ban tana tik'ar gudu a ganinta Allah ne ya kub'utar da ita daga hannun azzalumin can dake k'ok'arin sayar da ita,bata da tabbas d'in wanda suka cirota daga motar suma ba azzaluman ba ne,gudu take sosai akan titi wanda ita ba ta san titin bane tunda ba gani take ba,aikam wata mota da ta yanko a guje tai sama da ita ta watsar babu alamun rai a tattare da ita,kifa kai mamallakiyar motar tayi jikin siyiyarin cike da takaici da bak'in cikin wannan mahaukaciyar yarinyar,ba komai take tsoro ba sai azumin da zata janyo mata ba taji ba ba ta gani ba,na Ramadan ma da yaya take sauke shi bare kuma wannan da ya ninka shi,tsaki ta ja kafin ta fito daga motar a ranta tana addu'ar Allah yasa ba ta mutu ba,ko k'warzane babu a jikinta anman da alamun wuya ta saka numfashinta d'aukewa. D'aukarta tayi ta sanya cikin motarta ta juya zuwa asibitin da ta fito,tana jan tsaki akai akai da addu'ar Allah sa ba ta mutu ba,tsabar zafin da kanta ya d'auka baccin da ke cikin idanuwanta ji tayi ya wartsake gaba d'aya. Sai da aka tabbatar mata yarinyar na da rai ta samu karaya a k'afa da hannu kana ta samu nutsuwar tafiya gida bayan ta bar sallahun a yiwa yarinyar duk abinda ya dace idan taje gida zata turo wanda zai kula da ita. Sai takwas da rabi ta baro asibitin zuwa gida,tana parking d'in motarta ta hango Fadwa ta nufi sashen FASIHUL LISAN a ranta tace "Wahalalliya." Tana shiga falon,Fadwan ta shigo da tray a hannunta fuskarta d'auke da damuwa,dining ta nufa kai tsaye ta ajiye tray d'in hannunta tana fad'in. "Ammi sai yanzu?" "Hmm wata yarinya ta jamin musifa wallahi,ta hau kan tsakiyar titi tana gudu ban aune ba na kad'eta,inda Allah ya tak'aita ba ta mutu ba,kicema Talatu ta shirya Bala ya kaita asibitin ta kula da yarinyar kafin a samu kanta." "Ayya Allah ya kiyaye gaba,nima zan bisu na duba yarinyar." Kamar yadda ta tsammata Ammin baza ta tanka ba,ba kwa ta tanka d'in ba sai shigewarta part d'inta tayi dan wanka take buk'ata kafin ta kwanta bacci,kwana tayi ba ta rintsa ba saboda yawaitar marasa lafiya duk rashin kirkinta tsakaninta da Allah take aikinta. Murmushi Fadwa ta saki,ta d'auko kwaandon saka abinci ta jere break fast d'in da ta hana idonta bacci ta tashi ta tsantsarawa Yaa Fasee duk don ta burgeshi ta kuma karkato da hankalinsa kanta a bisa shawarar aminiyarta Siyama,sai dai kuma da yake Namijin duniya ne haka ya tsallake break d'in ko tab'awa bai yi ba ya fice ya bar mata,yanzu kuwa dole ya ci tunda ta samu hanyar zuwa asibitin sai ta bishi da shi har office d'insa wahalarta baza ta zama a banza ba in sha Allah. Sai da ta gama jera abincin kana taje ta sanarwa da Talatu sak'on Ammi,ta d'auki d'an abinda zata d'auka suka fito Bala ya jasu zuwa asibitin... Zan iya cewa a nan free page ya k'are masu buk'atar cigabansa zasu iya samuna kai tsaye a wannan layin 09037093702 na gode. BEBEE'ARTH RASHUNA An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels