An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ๏ปฟ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. BAN HAK'URI. Inaba masoyana hak'uri najina shiru da suka yi. GARGAD'I. Meenalyn daddy banyar da wani/wata ba ya yi min amfani da littafi ba ta ko wata sibgaba sai da izinin marubuciyar . KADA KU MANTA ,FADILA SANI BAKORI CE, MARUBUCIYAR. IN DA RAI... OGA HABIB RAYUWAR HAIDAR SO NE SILA ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI AND NOW MEENALYN DADDY. SADAUKARWA: Na sadaukar da page d'in nan baki d'ayan shi gareki shugubar Jarumai writer's association, Basira Musa,Wato (Mommyn shukura) Ki dad'e ki yi k'arko ki shekaru irin na dabino๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป. Page 1 & 2 Garin Kaduna Saban kawo layin 'yan majalissu.Wanda za'a iya cewa duk Wanda ke layin 'yan majalisu yaci ya tada kai.koda na shiga Unguwar ban tsaya ko Ina ba sai gidan Doctor Alhaji Abba Sani. Alhaji Abba Sani kwance yake a faffa d'an gadon shi,sai juyi ya ke bisa ga alamu dai kamar da akwai abinda ke damun shi . Hajiya Mariya matar Doctor Abba, ta yi sallama ta shiga bedroom d'in,hajiya Mariya jin shiru maigidannata bai amsa mata sallamar da tayi ba ne yasa ta shiga kai tsaye. ta dad'e tsaye kan maigidannata tana tunanin, tunanin me ya ke yi haka ,ita dai a iya saninta bata san wata damuwa da ke damun maigidannata ba. Hajiya Mariya zama tayi gefan gadon,ta na hura ma Alhaji Abba iskar bakinta,sannan cikin dadda d'an lafazi ta ce. "Daddyn Meenal lafiya kuwa,tun d'azu nake tsaye kanka amma bisaga alamama bakasan da tsayuwata ba". Wanda aka Kira da Abban Meenal , kallo d'aya za kai Mai kasan tattijon arzik'i ne.Duk da baza akira shi da tsoho ba , ya dai manyanta Masha Allah, k'ila kuma wadata ce da kwanciyar hankali ta hana tsufan bayyana. D'ago fararan idon shi yayi ya kalli hajiya Mariya batare da ya motsa ba ko alamun zaiyi magana ba. Hakan da yayi sai ya sa Hajiya Mariya cikin damuwa ,hakan yasa ta sa hannuta d'aya tana tab'a wuyan maigidan nata taji ko zazzab'i ne,amma jin babu alamun zazzab'i yasa cikin alamun damuwa ta ce. "Abban Meenal bakajin dad'i ne?". Wanda aka Kira da Abban Meenal tashi yayi ya zauna ,sannan ya kalli matar tashi Mahaifiyar tilan 'yar shi ya ce,yana mai sakin murmushi afuskar shi ,dan ya kauda da mata tunanin da take na yanada damuwa,ya ce. "Mommyn Meenal me kika gani ne?". "Abban Meenal dan Allah ka fad'imin damuwarka kawai,alamunka sunnuna kanada damuwa,me ke damunka please?". Hajiya Mariya tayi maganar cikin nuna sansanin damuwar maigidannata" Alhaji Abba tashi yayi Yana rik'o hannun matar tashi,ya ce. "Tashi muje muyi breakfast babu abinda ke damuna,kawai dai kinsan watarana hakanan mutum sai ya tashi yaji shi baya jin dad'in garin,shine kawai,amma me zai daman, Meenalyn daddy da mommynta na kusa dani". Magana hajiya Mariya za ta kuma yi Alhaji Abba yayi saurin ri gata da cewa. "Mu je inyi breakfast inada pertient a asibiti da zan duba ga lokaci ya ja muje". Alhaji Abba na zaune Yana breakfast ya kalli Hajiya Mariya ya ce. "Ina Meenalyn daddy fa?". Murmushi Hajiya Mariya tayi ta ce. "Meenalyn daddy yau da fushi ta tafi School bataga daddynta ba,dan na san badan suna da Exam ba da cewa za tai ba zata ba" Murmushi Alhaji Abba yayi ya ce. "Bari idan na fita zan biya ta school d'in tasu". "Ai wallahi daddyn Meenal duk kai ke k'ara shagwab'a Meenal shi yasa kullum take ganin kanta kamar k'aramar yarinya,ta girma har yanzu kai da ita baku san ta girmaba". Alhaji Abba aje cup d'in d'in hannun shi yayi Yana kallan Uwar gidan shi ,ya ce. "Wai Meenal d'in ce ta girma ?" " 21 years fa,aiko akowace duniya ta girma ,sai dai awajanka ne bata girma ba".cewar hajiya Mariya. Murmushi Alhaji Abba yayi,ya ce. "Ni dai kallan Baby har yau nakema Meenalyn daddy". Haka Alhaji Abba ya gama breakfast d'in shi ya yi shirinsa ya fita aiki. kamar yadda Alhaji Abba yace sai da ya biya ta University d'in da Meenal ke karatu.Yana shiga ya Kira number ta,aiko da hanzarinta ta naimi excuse ta fito. Alhaji Abba na jingine jikin motar shi Yana murmushin shi da ya saba dan shi mutum ne mai fara'a,bakamar da ya hango Meenal ta tahoba cikin na tsuwarta da take bashi mamaki,dan yana yaba natsuwar Meenal sosai awaje,agida ne dai sai addu'a. Meenal na zuwa ta rungume daddynta cikin fara'arta tana cewa . "Oyoyo my sweet Daddy ,yau nayita jiranka baka tashi ba sai dai Bilya driver ya kawoni". Meenal ta idasa maganar tana turo baki,kamar wata k'aramar yarinya. Bayanta Alhaji Abba ya fara bubbugawa alamun lallashi,ya ce. "Yi hak'uri Meenaln daddy nima da na tashi banganki ba sai naji duk ba dad'i,shi yasa Breakfast kad'an nayi ,yafi min dad'i idan naci da Meenalyn daddy". Meenal tana murmushi irin na daddyn ta, duk da ita nata mai tsada ne kusan daddynta kad'ai takema irin shi,ta ce. "Sweet daddy nikam yau banci komai ba ". Cikin hanzari Alhaji Abba ya kamo hannun Meenal Yana k'ok'arin sata amota ya ce. "Meenalyn daddy muje restaurant kici abinci,bana hanaki tafiya biki breakfast ba?". "A'a Sweet daddy nikam bazan ci ba ,kasan bana son abinci waje" D'aurewa Alhaji Abba yayi,ya ce. "Meenalyn daddy Allah indai biki biyoni ba kikaci abincin nan,yau ba zanyi dinner da ke ba". Meenal jin haka turo baki tayi ta shiga motar tana cewa. "Amma dai sweet daddy kasan bana cin abinci waje ko?". "Eh nasani ,me yasa biki breakfast agida ba?". Turo baki Meenal tayi daga nan bata kuma cewa komai ba taja bakinta tayi shiru. Alhaji Abba da kan shi ya bud'e ma Meenal motar ta shiga,Shima ya shiga yaja motar yabar harabar makarantar" Restaurant tsadadde Alhaji Abba ya kai meenal taci abinci.Sai dai me bayan ankawo mata white rice da soup ,ko kallan abincin k'i tayi ,Alhaji Abba cikin lallama da lallashi ya ce. "Meenalyn daddy kici Mana ,ko restaurant d'in ne bai miki ba,mu canza wani,koko abincin ne baiyi ba?". "Sweet daddy kasan nifa bana iyacin abinci sai da kai". Meenal ta idasa maganar tana mai kauda kai ga abincin. Murmushi Alhaji Abba ya yi,sannan ya d'auki spoon d'in yaci gaba da cin abinci. Meenal ma ganin haka itama ta d'auka ta faraci. Alhaji Abba ya k'oshi kasan cewar sai da yayi lafiyayyan breakfast sannan ya fito gida,amma kasan cewar yasan daga ya cire hannun shi meenalynshi ma zata cire yasa ya d'aure yayita tusawa . Masha Allah,Meenal an samu taci abinci ba laifi,sannan ta aje spoon d'in tana mai tashi tsaye alamun su tafi. Alhaji Abba ma tsam ya tashi kasan cewar ya biya kud'in yasa ya kama hannun Meenal kamar wata Baby ya sata mota Shima ya shiga. Sai da Alhaji Abba ya Maida Meenal school sannan ya kama hanyar zuwa wajan aiki" Kamar yadda Meenal ta saba da wowa daga school yauma haka ta dawo,tana zuwa ta fad'a kan caution d'in falon tana cewa. "Wayyo Allahna!". Hajiya Mariya Mahaifiyar Meenal,kallan Meenal tayi tana mai cewa. "Meenalyn daddy dan Allah sai yau she zaki koyi yin sallama ne in kika shiga waje?,kefa ba jahila bace,kinada saninki d'ai-d'ai gwargwado ,kuma ke bak'aramar yarinya bace,amma sai ki shiga waje babu sallama.Tom kin san Allah daga yau indai kika kuskura kika k'ara shigo min falo bikimin sallama ba Allah sai ranki ya b'ace!". Meenal turo baki tayi kamar za tai kuka dan idan da akwai abinda tak'ijini bai wuce ai mata fad'aba.Hakan yasa ta turo bakin nan,kamar za tai kuka. Hajiya Mariya tashi tayi taba Meenal waje dama ita da wiya kaji firarta ita da Meenal sai dai da daddynta". Hajiya Mariya tana ciki har ta gama abinda take ta dawo Falon,amma abin mamaki Meenal na nan yadda ta barta,har yanzu kuma fuskarta babu walwala alamun har yanzu bata huce da fad'an da Mommynta tayi mata ba,na rashin sallama da batayi ba. Hajiya Mariya zama tayi kusa da Meenal ta na mai dafata dan duk sai taji ta shiga damuwa ganin tilo d'in 'yartata cikin damuw.Hakan yasa ta ce. "Haba Meenalyn daddy dan namiki fad'ane akan sallama kika yi fushi haka?,amma dai kin san ni Mommyn ki ce da bazan so inga yarinya ta tayi ba dai_dai ba.Sannan duk cikakkan musulmi baya shiga gu sai yayi sallama,dan amusulinci idan mutum yazo waje baiyi sallama ba idan baka tanka Mai ba bakayi laifi ba.Indai dan fad'an da nai miki ne ki saki ranki,bana so ne mutane su zagi tarbiyar daughterna shi yasa" Haka Hajiya Mariya ta zauna sai nasiha takema Meenal cikin lallab'awa da lalla shi,kamar wata 'yar 2 years. Meenal dai bata tankama Hajiya Mariya ba,kuma har yanzu bakinta a ture yake,daga k'arshema cewa tayi. "Tom mommy ai mantawa fa nayi, ai tunamin ya kamata kiyi bawai kimin fad'a ba". Murmushi Hajiya Mariya tayi ta ce. "Tom naji Meenalyn daddy amma fa kullum sai na tuna miki". "Tom ai ahaka-ahaka watarana zan rik'e". Cewar Meenal. Hajiya Mariya dai shiru tayi,sai zuwa can ta kalli Meenal ta ce. "Abinci fa?". Yatsine fuska Meenal tayi sannan ta ce. "Kema kinsan sai daddyna ya dawo zamuci tare" . Hajiya Mariya bata Kuna cewa komai ba ta tashi ta shiga ciki,dan yin abinda ba'arasa ba,har zata wuce ta kalli Meenal ta ce. "Zoki tayani aikin mana?". Meenal tab'e baki tayi tana mai cewa cikin sanyin muryarta da alamun rashin sonyi magana. "Ai wallahi tunda kika hana daddyna kawo mai aiki gidan nan sai dai ke duk ki rik'ayin aikinki". Hajiya Mariya harta zo zata tafi,komai ta tuno ta dawo tana mai kallan Meenal ta ce. "Bari daddyn naki yadawo ,yau zai Mana shara'a dake agidan nan,wallahi daga yau dole ki fara ko da sharane ". Meenal dai bata ce komai ba,ta juya ta tafi abinta". Misalin k'arfe takwai na dare(8:00PM) Alhaji Abba ya shigo gida kamar yadda ya saba da wowa kusan kulkum. Meenal zau ne ta ke kan caution ,ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ,ta yi kwalliyar tar bar daddynta kamar yadda ta saba kullum,haka zata zo falon ta zauna tana jiran shigowar daddynta.Aiko tana jin sallamar shi ta ta shi da gudu ta rungume daddynnata,tana mai amsar jakar hannun shi,sannan cikin sanyin muryarta ta ce. "Welcome daddy". Alhaji Abba cikin k'aunar 'yar tashi ya ce. "Ina ta sauri kar inyi ma Meenalyn daddy laifi". "Ai daddy yau da ka k'ara lokaci da bazan kulaka ba".cewar Meenal tana mai yima daddyn nata jagoranci izuwa bedroom d'in shi. Mahaifiyar Meenal ko da fitowarta daga kitchen kenan, ta k'araso da fara'arta irin ta tarbar mai gida d'in nan ta ce. "Oyoyo daddyn Meenal barka da dawowa" Alhaji Abba Yana mai ci gaba da tafiya ya ce. "Yauwa Mommyn Meenalyn daddy". Meenal ko na rik'e da jakar daddynta da ta amsa har i'zuwa bedroom d'in shi.Sai da ta aje jakar sannan ta fita tana mai cewa . "Tom Daddy ka fito yanzu fa kar Ulcer ta kamain kai". Murmushi Alhaji Abba yayi ,batare da ya tankaba ya shi ge toilet" Meenal ko na fita darning space ta nufa ,ta zauna tana danna wayarta tana jiran fitowar daddyn ta. Meenal na nan zaune Alhaji Abba ya fito shida Mommyn Meenal. Bayan Alhaji Abba ya zauna ne,Meenal ta ja plate d'in daddyn ta ta mik'a mai itama taci gaba tacin nata. Hajiya Mariya Mahaifiyar Meenal kallan Meenal tayi ta ce. "Wato Meenal ke kullum bakimin ta ido ko?,sai ki zuba ma daddynki kema ki zuba ni ina kallanku ni da nai girk...". Alhaji Abba wuf yayi ya ce. "Aikin ai sai yayi mata yawa,ni bari in zuba miki". Meenala dai tanaji bata tankaba, Daddynta ya zuba Mommynta abincin. Bayan Alhaji Abba ya gama cin abincin ne,Mahaifiyar Meenal ta kalle shi ta ce. "Daddy Meenal na kawoma k'arar Meenal?". Alhaji Abba kallan Mahaifiyar Meenal ya yi ya ce. "To me kuma Meenalyn daddy tayi?". Mahaifiyar Meenal d'aure fuska tayi,alamun maganar da za tai babu wasa,dan ta san Daddyn Meenal zai iya d'aukar maganar da wasa.Mahaifiyar Meenal kallan Alhaji Abba ta kuma yi sannan ta ce. "Daddyn Meenal,dama akan maganar rashin yin aikin Meenal ne,nifa abinda nake nuna maka Meenal macece ba zai yuwu ba,ace kamar Meenal batasan ta d'auki d'auki tsintsiya ba tayi shara,bare kuma ayi maganar mopping, tom gaskiya nikam nagaji daga yau ga Meenal nan a gabanka koda falo ne ta rik'a gyarawa ,ahankali-ahankali watarana zata iya". Alhaji Abba tunda Mahaifiyar Meenal ta fara magana yake kallanta,har ta kai k'arshe, ajiyar zuciya ya sauke sannan,ya kalli Meenal da ta turo baki, murmushi Alhaji Abba yayi sannan ya ce. "Meenalyn daddy kinji abinda mommynki ta ce ko?" . Meenal turo bakinta ta kuma yi,kamar ba za tai magana ba sannan ta ce. "Tom Daddy waya ce ta k'i samun mai tayata aiki idan aiki ne yayi mata yawa". Meenal ta idasa maganar tana mai ci gaba ga game d'in da take yi a wayarta" Alhaji Abba kallan Mommyn Meenal yayi ya ce. "Tom kinji". Mahaifiyar Meenal cikin kwantar da kai dan daddyn Meenal ya fahinceta dan tasan idai tace da tsiya za tai tom ba zai fa yuwu ba,hakan yasa cikin kwantar da kai ta ce. "Daddyn Meenal kafa duba lamarin nan ina teaching ,kullum sai sha biyu nake da wowa gidan nan,kuma ace kamar Meenal ba zata iya kamamin komai ba,duk bama haka ba,ni aikin gidan nan bawai ya gagaran bane,kawai dai ina duba rashin dacewar ace mukai Meenal gidan miji mata iya komai b....". Kukan da Meenal ta fara ne tana buga k'afa abin gunin mamaki,kamar wata 'yar 4 years, tana cewa. "Daddy kaji ko ta fara ko" . Alhaji Abba tashi yayi Yana kamo hannun Meenal ya ce. "Tashi mu bar mata wajan dama abinda take so kenan taga tasaki kuka". mommyn Meenal kuwa da ranta ya b'aci ,duk da indai rashin isa da Meenal ne dama saba,sai dai aduk lokacin da hakan ta faru ranta kan b'ac.Mommyn Meenal sai dai ta bisu da ido" Alhaji Abba ko har bedroom d'in Meenal ya kaita ,ya zaunar da ita bakin gadonta,sannan yasa hannu yana goge mata hawayanta ya ce. "Meenalyn daddy ki yi shiru kinji ki goge hawayanki,babu bai saki aiki,wa yace ta kori masu ta yata aiki saboda wata hujjatata ta banza da wofi.ki yi shiru kinji meenalyn daddy kar ki yi ciwan kai". Meenal da har yanzu kuka ta ke,kallan Alhaji Abba tayi ta ce. "Daddy nifa badan ta ce inyi aiki bane nake kuka,kanaji cewa tayi wai akaini d'akin miji,bacin nace ta bar cemin haka". "Yi hak'uri Meenalina batzata K'ara ba,d'akin miji kuma naga mai kaiki har sai ranar da kikai ra'ayin kanki sannan ko?". Kai Meenal ta d'aga ta ce , "Tom ka kirata kace mata karta k'ara cemin haka" Alhaji Abba wayar shi ya ciro ya Kira Mommyn Meenal.Tana d'agawa ya ce. "Ki sameni a bedroom d'in Meenal". Yana kaiwa haka ya kashe wayar" Mahaifiyar Meenal ko da tana zaune inda sukabarta tashi tayi tana mai addu'ar Allah yasa Meenal ta amince zata rik'a yin aikin ne". Da sallama Mommyn Meenal ta shiga bedroom d'in. Alhaji Abba ne ya amsa mata Amma Meenal ko kallanta batayi ba dan fushi take da mahaifiyartata. Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi alamun inajinka. Alhaji Abba gyara zama yayi yana Kara rik'e hanun Meenal ya ce. "Mommyn Meenal wai me yasa ne idan muka fara magana d'aya dake mun dinka nanatata kenan bazamu barta ba?,Me yasa bazaki guji duk abinda kika san Meenal bataso ba?,So nawa ina ce miki duk wata magana da ta shafi aure ki bar furtata akan Meenal ?,inda yarinyar nan ta nuna miki bataso,tom wannan shine magana ta k'arshe kar ki Kuma dan ganta min yarinya da duk wani abu da kika san bataso" . Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba kawai tayi bata iya tankamai ba,dan idan ma tace zata tanka tasan kanta zata jawoma b'acin rai gara tayi shiru" Alhaji Abba kuma hannun Meenal dake cikin hannun shi ya murza ya ce. "Ki yi hak'uri kinji meenalyn daddy kinji na fad'a mata bazata Kuma ba". Meenal gurza ido ta fara alamun za tai kuka ta ce. "Daddy ai banji ta ce bazata Kuma ba". Alhaji Abba kallan Hajiya Mariya ya yi ya ce. "Hajiya Mariya wai me yasa kike haka ne,shikenan ke kinfiso kita ganin yarinyar nan tana zubba hawayanta, dan Allah ki yi mata maganar bazaki k'araba dan hankalinta ya kwanta ". Mahaifiyar Meenal da ta fara gajiya da lamarin Meenal kallan Alhaji Abba tayi,ta ce. "Daddy Meenal taya Meenal tana mace baliga ace bazan mata maganar aure b...". Tsawar da mahaifin Meenal yayi ma hajiya Mariya ce yasa tayi shiru". Meenal ko ci gaba da bubbuga k'afa tayi tana cewa. "Ka ji ko daddy bazata bari ba ko!". Alhaji Abba cikin b'acin rai ya huna ma hajiya mariya hanya alamun ta fita. Hajiya Mariya tashi tayi itama cikin alamun ranta ya b'ace ta fita,tana mai jan k'ofar d'akin Meenal d'in da k'arfi" Bayan fitar hajiya Mariya ne,Alhaji Abba cikin lallashi ya ce. "Ki yi shiru kinji meenalyn daddy,aure ai ba farillah ba ne,bare ace dole sai kinyi shi,idan ma bakisan yi ba bu komai ki yi shiru, da take maganar aure-aure waye mahaifinki?". Meenal nuna Alhaji Abba tayi tana goge hawayanta . Alhaji Abba kuma yaci gaba da cewa. "Tom kin gani nine me yi miki auran dan haka kima kwantar da hankalinki ,ita kuma kibarni da ita zata san ta sa Meenalyn daddy kuka". Haka Alhaji Abba yi ta allashin Meenal yana nan zaune har sai da yaga tayi bacci sannan ya tashi ya fita..........โœ๏ธ Meenalyn daddy karki gaggawa Sister ki bini ahankali har in kaiki inda nake son kaiki,salon shi da ban ne daga cikin litattafan marubuciyar. idan kin karanta sister ki, daure ki comment dan ki kasance d'aya daga cikin wa'inda zasu samu banus d'in da zan saki a littafin nan,alk'awari ne insha Allah kuma zan cika. Share & comment pls ๐Ÿ“šMEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 3&4 Haka Alhaji Abba ya yi ta lallashin meenal yana nan zaune har sai da yaga tayi bacci sannan ya tashi ya fita. bedroom d'in hajiya Mariya ya shiga.lokacin hajiya Mariya har ta kwanta,jin sallamar Alhaji Abba ce duk da ahankali yayi sallamar ya sa ta tashi. Alhaji Abba ya dad'e zaune bai tanka ba,dan hajiya Mariya har shirun ya isheta,jin shirun yayi yawa ne yasa ta ce. "Daddyn Meenal lafiya kuwa?". Alhaji Abba kallan hajiya Mariya ya yi ,nan ma kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce. "Mommyn Meenal inaso zanmiki magana ta farko da k'arshe daga yau karki kuma yadda ki zama sanadin kukan Meenal,idan bahaka ba zamu samu sab'ani tsakanina da ke!". Hajiya Mariya tashi tayi ta zauna tana kallan Alhaji Abba,sannan cikin nuna fushinta ta ce. "Daddyn Meenal naji insha Allah daga yau bazan sake yi ma Meeenal maganar da ta danganci aure ba kamar yadda kace insha Allah,amma maganar Meenal ta tayani aiki agidan nan bazan tab'a janyewa ba,dole Meenal tayi aiki agidan nan".Hajiya Mariya ta'idasa maganar cikin b'acin rai. Alhaji Abba tashi yayi zai fita,har ya kai bakin k'ofar da zata sata shi da falo ya juyo yana kallan hajiya Mariya ya ce. "Wallahi kinji na rantse indai tai makon aiki kike so sai dai ki samu 'yar aiki,amma ba dai Meenal ba".Alhaji Abba na kai haka ya ja k'ofar hajiya Mariya da k'arfi ya fita" Hajiya Mariya ta dad'e konce tana juyi tana tunanin ta yadda zata b'ulloma lamarin nasu,dan awannan karan ta d'auki aniyar yak'i da Meenal da daddynta.Washe gari mahaifiyar meenal haka ta tashi da wuri kamar yadda ta saba tashi ta shirya musu abin breakfast,tana nan zaune Alhaji Abba ya fito dan yau k'in shiga part d'in shi tayi dan ya san fushin da gaske take yi da shi.Alhaji Abba ko da fara'ar shi ya k'araso inda hajiya Mariya take,yana cewa"Wato yau dan ana fushi dani shine aka k'i tadani ko?".Murmushi Mommy Meenal tayi tana mai cewa"A'a daddyn meenal nikam bana fushi dake makara nayi nima". Alhaji Abba zama yayi yana mai cewa"Ina meenalyn daddy fa?". "Kasan indai ba Exam gareta ba sai an tadata ". Alhaji Abba tashi yayi ya nufi bedroom d'in Meenal,lokacin da Alhaji Abba ya shiga kwance ya sameta sai sharar baccinta take.Ahankali Alhaji Abba ya fara bubbuga Meenal yana kiran sunanta. meenal bud'e idonta tayi tana mai sakin murmushi wa daddyn nata. Alhaji Abba kallan Meenal yayi ya ce"Meenalyn daddy tashi ki yi wanka ki yi breakfast ".meenal tashi tayi batare da ta tanka ba tana mai shigewa toilet . Alhaji Abba ganin meenal ta tashi ,shima fita yayi" Meenal cikin sauri ta shirya ta fita dan ta kusa late.Zaune ta iske daddynta na jiranta,tana zuwa sauri-sauri suka yi breakfast d'in ,dan dukkan su sunyi late" Alhaji Abba kamar yadda ya saba sai da ya kai meenal cikin makarantar su sannan ya tafi private hospital d'in da yake aiki . Hajiya Mariya ko ita ma kusan tare suka fita,dan tana son ta fara biyawa gidan kakannin meenal kafin ta shiga school d'in da take teaching" Hajiya Mariya zaune gaban Alhaji Abdullahi ,wato kakan meenal kenan,mahaifin Alhaji Abba . kakan Meenal da kallo d'aya za kai mai kasan datijon ya kwana biyu dan kanshi gaba d'aya farin gashi ne,sai dai da k'arfin shi sosai. Alhaji Abdullahi ,wansa yawancin mutane da kuma sukansu suke Kira da Alhaji,da fara'arshi ya tari hajiya Mariya wato mahaifiyar meenal ,yana cewa" Mariya tunda naganki da wuri haka nasan ba gaidani akazo yi ba "Hajiya Mariya dariya tayi,ta ce"Ina kwana Alhaji,ya k'arfin jikin" "Jiki alhamdulillah"cewar kakan meenal. Hajiya Mariya k'ara gyara zama tayi sannan ta ce"Alhaji dama wallahi akan meenal ne,kamar yadda dai kasani bani da iko akan meenal,ban'isa insata ba ban'isa in hanata ba,tom har yanzu ahaka muke.Wato abinda kedamuna meenal banda cin abinci da wankanta babu abinda ta'iya,akoda yau she ina nuna ma mahaifinta ita macece gidan wani zata,amma wallahi ita da daddynta duk ranar da na furta haka ma sai munyi ba dad'i,shine nazo nasan kai in kayi mai magana zaiji kace mai dole meenal ta rik'a tayani aikin gida ko asamu ta iya wani abun daga cikin aikin gida"Shiru hajiya Mariya ta yi ta d'an numfasa sannan ta ce"Tom Alhaji wannan ita ce buk'atata dan Allah". Kakan meenal tashi ya yi daga shingid'an da yake ya ce"Wai Mariya kina nufin Amina bata iya komai ba na aikin ku mata?"."Wallahi Alhaji bata iya komai ba,shara wanan, Allah tunda meenal ta isa hankakinta banta b'a ganin tayita ba da idona ba,tun abin baya damuna nikam yanzu har yafara damuna". "To shi Sani in banda abin shi haka zai d'auki "'yar ya kaita gidan aure bata iya komai ba,tom ki barshi dani ,bari Sule yazo zansa ya kiramin shi". Hajiya Mariya godiya ta yi ma sirikinnata sosai sannan ta tashi ta tafi" Sule mai kula da Alhaji wato kakan Meenal yana zuwa Alhaji ya sashi ya kira mai Alhaji Abba awaya ya ce daga ya tashi aiki ya biyo Alhaji nason ganin shi". Aiko haka akayi Alhaji Abba na tashi aiki ya je Kiran Mahaifinnasa, dama kuma dai kullum sai ya laik'a Mahaifinasa.Bayan sungaisa ne Mahaifin Meenal ya ce"Alhaji gani ance kana son ganina" "Eh Sani ina son ganinka,d'azu Mariya tazo nan ta kawomin k'ararka kai da Meenal,taya zaka ce Meenal bazata rik'ataya Mahaifiyarta aiki ba,bakasan tana da hak'i akanta ba ne?,dan haka karka kuskura kajama yarinyarka fushin Allah,karik'a barinta tanayin aiki,kamar yadda mahaifiyarta tace ita macece nan gaba gidan wani zata,dan haka daga yau duk wani aiki su rik'ayi tare,idan ma ta kama ta hak'ura da makaratun ne tom ta hakura ta zauna ta taya Mahaifiyarta aiki, itama ta iya". Mahaifin Meenal wato Alhaji Abba kallan Mahaifin nasa yayi ya ce"Alhaji meenal fa yarinya ce ,taya za'ace ta had'a karatu da aiki,bazata juri aiki irin wannan ba,inda ba sabawa tayiba.Sannan tunda Mariya tayi min maganar zata takatar da masuyi mata aiki nahanata,gudin haka,amma saboda wata hujja tata ta banza da ta tsiro da ita tak'iji ,shine yanzu aiki yayi mata yawa zata d'orama Meenal". kakan Meenal da tunda Abban meenal ya fara magana yake kallan shi,har ya kai k'arshe,cikin sanyin shi,dan shi ko fad'a zaiyi cikin sanyi yake abinsa,ya ce"Sani dole meenal ta yi aikin gida kamar yadda mahaifiyarta ta buk'ata ,zaka iya tafiya". Alhaji Abba ya dad'e bai iya k'ara cewa komai ba sannan yayi k'arfin halin cewa"Shikenan Alhaji zatayi,zan tafi babu abinda kake buk'ata?"."Babu Allah yayi maka albarka "cewar Alhaji wato kakan Meenal" "Ameen"Mahaifin Meenal ya ce ya tafi. Sosai ran alhaji Abba ya b'ace da abinda hajiya Mariya ta yi mai,yana shiga gida hajiya Mariya ta lura da yanayin shi tasan Alhaji ya fad'a mishi,dama kuma tunda taji shi shiru ta yi tunanin hakan. Meenal ko da ke zaune tana aikin buga game awayarta ,aje wayar tayi tana mai yin welcoming din daddynta.Alhaji Abba hannun meenal ya kama suka zauna. Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce"Barka da dawowa daddyn meenal""Uhm"Alhaji Abba ya iya ce mata kawai. Meenal ma ganin haka tasan yau an tab'a daddynta hakan yasa cikin sanyi ta ce." Daddyna waya b'atama rai?".Meenal tayi maganar tana kamo fuskar shi abin gunnin mamaki. Alhaji Abba Mahaifiyar meenal ya nuna ma meenal ya ce"Kin ganta meenalyn daddy bata son farincikina".Meenal cikin sanyi ta ce"Daddy mai tayi ma?".Alhaji Abba murmushin takaici yayi sannan ya ce"Meenal ta had'ani da Alhaji wai sai dai ki rik'a tayata aiki"."Wallahi daddy bazanyi b...".Alhaji Abba saurin rufe bakin meenal yayi dan karta idasa fad'in abinda take cewa,ya ce" Yi hak'uri Meenalyn daddy karki rantse kinji,ki yi hakuri kina kallon yadda take aikin,ahakama zaki iya,basai kin amsa kinyi ba ".Meenal kuka tasa tana cewa"Daddy inje school in dawo inyi aiki Allah bazan iya ba ni kam bazanyi ba". Alhaji Abba hannun meenal ya kamo ya shigar da ita side d'in sa ,cikin falonsa suka zauna ,cikin lalla shi ya ce"Meenalyn daddy tausayin daddynki zakiji ki yi badan Mommynki ba,kinga Alhaji zai iya fushi dani".Bud'ar bakin meenal sai cewa ta yi"Yo daddy ya dad'e bai yi ba,ba shi ya sani b..." .Alhaji Abba rufe bakin meenal ya yi ya ce"Meenalyn daddy Mahaifina ne fa,ni dai dan Allah ki tai maka kirik'a ganin yadda ake girkin zanma rik'a biyanki ba kyauta ba zaki yi".meenal dai turo baki ta yi bata ce komai ba,haka Alhaji Abba ya yi ta rok'on meenal daga k'arshe dai sai da ya yi kamar zaiyi kuka ta yadda,amma fa ta d'auki matakan yak'i da Mommynta dan acewarta bata sonta .Niko abin ta kaicima ya ke ban dan tab'arar tayi yawa" . Ranar dai abincin da Hajiya Mariya ta yi daga Alhaji Abba har meenal babu wanda ya kallai dan dukkan su fushi suke da ita.Tsaddan restaurant Daddyn Meenal ya kaisu sukaci abinci" Washe gari takama Weekend ,hajiya Mariya da wuri taje ta tada Meenal,Meenal da ke kan duniyar bacci kallan Hajiya Mariya ta yi tana turo baki ta ce"Lafiya".",Tashi zakiyi muje kifara gani inda kice bazaki ba,naji ki kallama ya wadatar "cewar Mahaifiyar meenal. Meenal turo baki tayi tana k'unk'u nai ta ce" Tom kije ganinan zuwa"."Tashi zakiyi muje ". Meenal sakkowa tayi tana mai bin bayan hajiya Mariya tana mai goge hawayan da ya fara zubar mata. Hajiya Mariya cigaba tayi da gyaran falon da tafara ta tuna bata tada Meenal ba.Hajiya Mariya tanayi tana surutu ,kinga idan kika fara share duster d'in sanna sai ki share ki goge,duk abinda hajiya Mariya za ta yi tanayi tana magana,irin dai na masu koyama mutum abu.Meenal ko kallanta kawai take da na goge hawayan da ke zubar mata akai-akai. suna gamawa hajiya Mariya ta kalli meenal da yanzu tabar kukan sai dai baki da ta turo ta ce"Yauwa Meenalyn daddy ba gashi har mun gamaba,yanzu saura mana mu had'a breakfast". Nan ma dai haka meenal ta bi Mommynta tana turo baki,ahaka dai suka dama kunun gyad'ar da suka dama ,ana cikin dama kunun ne Alhaji Abba ya shigo kitchen d'in,cikin fad'ad'a murmushin shi ya ce"Sannu da k'ok'ari meenalyn daddy".meenal turo baki tayi bata tanka ba. Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi ta ce"Barka da safiya daddyn meenal". maimakon alhaji Abba ya amsa hannun meenal ya kamo ya ce"Tom aikin ya isa haka muje ki huta". Meenal hannun daddynta ta rik'e suka tafi suka bar Hajiya Mariya nan ,hajiya Mariya da kallo kawai da bisu taci gaba da aikinta.Alhaji Abba kallan Meenal yayi ya ce"Jeki shirya meenalyna mu je muyi breakfast bama k'aracin abincinta sai dai taci ita kad'ai ki rabu da ita karma ki k'ara b'ata ranki ko kiyi kuka ".Meenal kallan daddynta ta yi tana goge hawayan jin dad'in son da daddynnata ke mata ta ce"Daddy me yasa mommy da tafi sona yanzu ta ke min haka ne?".Alhaji Abba goge ma meenal hawayan da ke zubar mata ya yi ya ce"Ki yi hak'uri kinji meenalyna ni bagani ba kuma ina sonki,kibarni da ita zanyi maganinta kwanannan,maza kije ki shirya muje muyi breakfast". Meenal cikin jin dad'in daddynta yace zaiyi maganin takurawar da Mommynta ke mata ta shirya da wuri.Haka suka zo suka wuce hajiya Mariya da ke zaune daga gani jiran fitowar su take suyi break tare,amma sai ta ga sun fita. Alhaji Abba restaurant d'in jiya da ya kai Meenal su kai breakfast,can ya kaita yau ma,sai da suka yi breakfast d'insu sannan suka koma gida " BAYAN SATI D'AYA. Gaba d'aya satin nan haka hajiya Mariya ta yi shi duk ba dad'i dan tagaji da fushin da Meenal da daddynta su ke yi da ita,gashi aikin ma Meenal ba wai yi take ba sai dai tai mata tsaye akai dan ita bata ce tanama fahimtar abinda take koya mata ba. Fushin da Daddyn meenal ya ke yi da hajiya Mariya sosai abin ya fara damunta hakan yasa yau da daddare bayan meenal sun rabu da daddynta ta kwanta ,hajiya Mariya ta turo d'akin Meenal d'in ta shiga,kamar ko yadda ta zata zaune ta iske Meenal d'in tana game awayarta. Meenal najin sallamar hajiya Mariya ,kamar bazata amsa ba ,sai kuma ta amsa ciki-ciki,amma ko tad'aga kai ta kalleta. Hajiya Mariya amshe wayar hannun Meenal ta yi.meenal turo baki tayi sannan ta juya zata kwanta,hajiya Mariya da sauri ta rik'o Meenal tana cewa"Haba meenaly daddy da mommynki kike fushi?,dan nace ki koyi aikin gida ne kike fushi dani keda Abbanki ko,tom indai hakane kisha zamanki daga yau ni kad'ai zan rik'a aikina shikenan ko ?". Meenal turo baki tayi ta ce"Tom ba ke bace yanzu kin canza".Murmushi hajiya Mariya tayi ta ce"Meenal ba canzawa nayi ba bakudai fahimtan bane keda daddynki shi yasa"."Ni kam Mommy indai kina son mushirya sai dai ki dawo kamar da ".Shiru hajiya Mariya ta yi sannan ta ce"Tom meenalyna na daina ,mun shirya ko?".Meenal rungume hajiya Mariya ta yi ta ce"Yauwa mommyna har naji dad'i". Murmushi hajiya Mariya ta yi ,ta ce"Meenal kenan,ke kikasa daddynki ya yi fushi dani ko?"."A'a mommy Allah babu ruwana ". Murmushi hajiya Mariya ta yi ta ce" Tom ki aje game d'in ki kwanta ki yi bacci".Hajiya Mariya nakaiwa haka ta tashi tajama ma Meenal k'ofa,ta nufi bedroom d'in Alhaji Abba,koda taje ya rufe k'ofar shi hakan yasa sai da ta bubbuga Alhaji Abba da har bacci ya fara d'aukar shi ya ce"Waye"yana sane yace haka dan yasan ba meenal ba ce. Hajiya Mariya kamar karta tanka dan tasan yana sane da ita ce,amma sai ta daure ta ce"Daddyn Meenal ka bud'e ni ce" Alhaji Abba tashi yayi ya bud'e ,yana kallan hajiya Mariya kallan har yanzu fa ina fushi dake.Hajiya Mariya kutsawa tayi ta shiga .Alhaji Abba kallanta yayi ya ce"Zan kwanta ne lafiya?".Shiru Hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Ka zauna mana,magana zamuyi"Alhaji Abba zama yayi ya ce"Inajinki?". Hajiya Mariya cikin siririyar muryarta ta fara magana kamar haka"Yanzu daddyn meenal fushi kake dani dan nasa meenal aiki?,Shikenan insha Allah daga yau bazan kuma sata ba".Alhaji Abba cikin d'aga murya alamun yaji zafin abinda mommyn meenal ta yi ya ce"Eh Mommyn meenal fushi nake da ke kamar yadda kika ce,akan me na d'aukar miki masu aiki ki koresu kice ke sai dai meenal ce zata ta ya ki,tom da me zataji da karatun da takeyi koko da aikin gida zataji!?".Numfasawa mommyn Meenal tayi sannan ta ce"Shikenan daddyn meenal ai ya wuce dan Allah kayi hak'uri insha Allah hakama ba zai sake faruwa ba duk yadda kace haka za'ai".Murmushi Alhaji Abba yayi ya ce"Yauwa,bawai bana son Meenal ta tayaki aiki bane,a'a nafi son sai ta gama karatunta kar abin yayi mata yawa".Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Tace tom ai shikena,ni kunsa duk na rame kai fushi meenal fushi.Memakon ko kaine kaji tausaina,amma kaziga 'yarka kuka had'emin kai kuka sani gaba,tom nadai janye". Dariya sosai Alhaji Abba yayi ya ce "Yauwa mommyn meenalyna koke fa,amma nima fa naga kamar kinrane da gaske ,kamarma hadda k'ashin wuya mugani" Alhaji Abba ya idasa maganar yana jawo mommyn meenal.Hajiya Mariya buge mai hannu tayi ta ce"Ni rabu dani tashi zanyi in tafi "Hajiya Mariya ta fad'i maganar tana tashi zata tafi.Alhaji Abba jawota yayi ta fad'o kanshi ya ce"Ai inkinga kin fita nan tom kin ba Abban meenal gamsassan hak'uri dan Wanda kikaban yayi kad'an "Alhaji Abba na fad'in haka ya had'e bakin shi da na Hajiya Mariya..............โœ๏ธ Yadda kike tunanin labarin ba haka yake ba sister bini ahankali๐Ÿ˜‡๐Ÿ˜‡๐Ÿ˜‡ kada ku manta da akwai banous da zan saki , masu Comment ne kad'ai zasu samai Shere & Comment please ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* NA Fadila Sani Bakori. Page 5&6. Washe gari ,hajiya Mariya da wuri ta tashi kamar yadda ta saba tashi ta shirya komai ta d'ora musu abin breakfast.Lokacin da Meenal da daddynta suka tashi hajiya Mariya ta kammala komai kamar yadda ta saba. Yau cikin fira da tsokana Meenal suka yi breakfast da daddynta da mommynta.Sosai hajiya Mariya taji dad'in hakan,amma satin nan gaba d'aya da suka daina cin abincinta firama suka bar zama suy da ita'dan hatta kallo Meenal a Falon daddynta take zuwa tayi.Bayan sun gama karyawa Alhaji Abba ya d'auki Meenal ya direta a school d'in da take karatu sannan shima ya tafi wajan aiki" ASALIN LABARIN. Alhaji Abba shine d'aya d'aya tilo wajan mahaifin shi,hakan yasa mahaifin alhaji Baba wato kakan meenal,ya ba Alhaji Abba gata sosai,alhaji Abba na matakin k'arshe na karatu Allah yayi ma mahaifiyar shi rasuwa. Tunda Mahaifiyar Alhaji Abba ta rasu hankalin Alhaji wato kakan Meenal ya koma akan Alhaji Abba yayi aure, dan dama tun da ran mahaifiyar shi taso haka Allah bai yi ba. Babu maganar da Alhaji wato kakan meenal bayi ma Alhaji Abba ba akan aure amma yak'i,hakan yasa sai ya fara bincikin abokan shi ko sun sa budurwar shi amma abin mamaki sai suka sanar da shi bashi da budurwa,dan shi alakacin babu abinda yakeso kamar karatun shi,gani yake yin budurwa kamar b'ata lokaci ne,hakan yasa ya maida hankalin shi sosai akaratu,har ya kammala ya samu aiki,amma babu maganar aure aran shi. Atak'aice dai Alhaji wato kakan meenal ya sha fama sosai kafin mahaifin meenal yazo mai da maganar auran mahaifiyar meenal itama lokacin ansha karatu.Cikin k'ank'anin lokaci aka tsaidar auran su akayi,za'a'iya Kiran auran da auran tazurai.Mahaifin meenal ana d'aura auran shi da hajiya Mariya bai yadda ya kusanceta ba sai da ya kaita asibitin da ya ke aiki akai mata tsarin family planing,acewar shi sai sun mori k'uruciyarsu sannan ko zasu haihu. Atak'aice dai ,sai da sukai shekara tara babu haihu,daga nan suka fara bin asibitoci ,amma za'a'iya cewa ba adace ba.Nan fa abin ya fara damun su. Suna shekara ta goma da aure Allah ya ba hajiya Mariya ciki.kalar munar da sukai da cikin nan ba'acewa komai.Nan da suka fara tarairayar cikin . Wayyo Allah ranar da hajiya Mariya ta haihu sai da alhaji Abba yayi kukan dad'i ,tun daga nan fa ya d'auki son duniya ya d'orama babyn ,ranar suna taci sunan mahaifiyar shi wato Amina,sukarik'a mata lak'abi da Meenal ,alhaji Abba kuma yana kiranta da meenalyn daddy kamar wasa sunan ya bita. Tsabar son da alhaji Abba da hajiya Mariya suke nuna ma meenal yasa duk abinda tayi basa ganin laifinta,gashi tun daga kanta hajiya mariya bata kara koda b'atan wata ba.Hakan yasa meenal ta taso a sangarce, babu mai kwab'amata,tom garama hajiya Mariya dake shiga cikin mutane tana ganin yadda iyaye ke iko da yaransu takanji dama ita,dan ita kome zatai ma Meenal bata isaba tasa ta daina abinda takeyi,hakan sai ya fara damunta,tom shine fa yanzu ta fara k'ok'arin gyarawa amma ina abin ya ci tura. Wannan shine dalikin da Mahaifin Meenal ya d'auki son duniya ya d'aura ma Meenal ganin ita kad'ai gareshi,gashi yasha wuya sosai kafin susameta .Wannan kenan" Tunda hajiya Mariya tabar sa Meenal aiki suka dawo kamar yadda suke da Meenal da daddynta,suka dawo kamar da. Yau ta kama Weekend Alhaji Abba zaune suke shida iyalinshi suna fira Kira ya shigo wayar shi,Alhaji Abba shiru yayi yana sauraran Kiran da aka ce mahaifin shi na mai,cikin fargamar zarkin Kiran nashi da ya yi ya ce"Okey,gani nan zuwa yanzu". Dama Alhaji Abba da shirinsa na fita,hakan yasa ya tashi ya nufi gidan Mahaifinsa da baida nisa da gidan shi. Alhaji Abba zaune gaban Mahaifin shi,bayan sun gaisa ne,Alhaji Abba ya kalli Mahaifin shi ya ce"Alhaji gani".Shiru Alhaji yayi,wato kakan Meenal,sannan ya ce" Sani akan maganar da mukayi da kaine,yau kwana goma sha hud'u kenan"Numfasawa dattijon yayi sannan yaci gaba da cewa"Nagaji da zuwa nai man auran Meenal da akeyi wajena,nayi maka magana akan Yaron gidan Alhaji Musa,amma shiru Sani ba kaimin maganar ba har yau ,tom yau ya sake dawomin ".Alhaji wato kakan Meenal ya idasa maganar cikin damuwa. Numfasawa Alhaji Abba yayi,sannaya ce"Alhaji yaron ne ban yadda da tarbiyar shi ba shi yasa kajini shiru ". Alhaji kallan Alhaji Abba yayi kawai ya girgiza kai sannan ya ce"Sani fad'amin kai ne baka son aurar da Amina koko Aminar ce bata son yin auran inji,ina fa sane, rashin kula masu nai man auranta da bakayi ne yasa aka fara zuwa wajena naiman auran Amina".Alhaji Abba shiru yayi dan bai son abinda zai ce ba,shiko kakan Meenal jin haka sai cewa yayi,"Sani yau zan fad'a maka abinda baka sani ba,kuma itama Amina ina tunanin kai tayi gado inma ciwone ko kuma ra'ayi,wato Sani sai da nasa akai ta maka addu'a ana baka kana sha sannan nasamu hankalinka ya juyo akan maganar aure,sanin kankane abokanka babu Wanda baiyi aure ba sannan kayi,nasha surutun muta ne akanka,tom kadubafa kai namiji ne akaimaka shurutu ina ga Amina Amina fa mace, Allah ya yi Amina da farinjini amma kai da ita kunk'i,tom koma dai menene insha Allah abinda nayi maka shi zan mata,dan haka ka shirya kai da iyalanka zuwa gobe zamu je Katsina wajan Malam Abdullahi Wanda mukai karatu tare shine dama alokacin ya yi ta tofamaka addu'a aruwa ina kawoma kana nasha tom amma kai alokacin faka fashinci komai ba,kuma cikin yaddar Ubangiji Allah yasa hankalinka ya dawo akan maganar auran,tom inajin itama Amina hakan za ai mata tun wuri,kuma mu tafi gaba d'aya tare mu gaida shi zaiji dad'i kaga nima nayi tsohon zuminci,dan rabona da shi tun lokacin naje mai da albishir d'in auranka,Sai kuma gobe insha Allah zamu tafi dan haka ka tashi kaje kasanar da su" Alhaji Abba da gaba d'aya zifa yakeyi kota ina dan shi kanshi bai shirya zuwa Katsina ba yanzu,hakan saya cikin sanyi da naiman alfarma ya ce"Alhaji Katsina fa yanzu bata shiguwa,dan Allah idan ma hakane tom ka bada sak'omana akai mai,sannan inada meeting gobe,dan Allah Alhaji kabar magan...".Hannu Alhaji ya d'agama Alhaji Abba ya ce"Wallahi koda na samu Wanda yasan gidan Malam Abdullahi tom bazan ai ka mai ba,ai da kunya shekaru kusan talatin ace in akamai da sak'o,ko bama haka ba zuwa da kai yafi sak'o.Sannan Katsina da kake maganar babu lafiya yanzu ,ai ba cikin Katsina bane kyauyan Katsina ne,dan in ba yanzu ba garin ko network basu da shi" Alhaji Abba cikin damuwa ya ce "Alhaji ai kyauyukan ne abun gudu,saboda anan ake ta'addancin ai,alhaji dan Allah ka yi hak'uri da tafiyar nan sai n...""Sani babu abinda zai hana tafiyar nan gobe insha Allah,tashi ka tafi".Alhaji Abba da yarasa abin cewa tashi yayi ya yi ma Mahaifinna shi sallama ya tafi" Koda Alhaji Abba ya koma gida ,Allah yasa bai iske kowa afalo ba hakan yasa yayi part d'in shi,yana shiga ya Kira hajiya Mariya awaya yace tasamai part d'in shi" Hajiya Mariya bayan ta zauna ne ta kalli Alhaji Abba ganin yayi shiru da'ido kawai yake binta ta ce"Daddyn Meenal lafiya kuwa?" Numfasawa Alhaji Abba yayi ya ce"Mommyn Meenal Wallahi abinne yasha min kai ban san yadda zanyi da Meenal ba ta yadda da wannan tafiyar.Alhaji wai dole sai munje Katsina gobe kuma harda Meenal,kuma kyauye ".Shiru hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Lafiya meza ayi a Katsinar?"."Wai Meenal za'aima addu'a kinsan tsofaffin nan da k'irk'irar abu,idan ba hakaba yarinya lafiyarta lau babu abinda ke damunta amma wai sai anyi tattaki anyo mata addu'a sai kace mai wata lallurar" Ita kanta hajiya Mariya shiru tayi dan ta jinjina tafiyar ,dan Meenal takan fad'i da bakinta haushin d'an kyauyan mutum takeji shi yasa tama gode da basu da 'yan'uwa akyauye.Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi da yayi tagwumi sai kace wadda aka aikoma da wani bala'in ta ce"Tom Daddyn Meenal ni kaina abin nama rasa abinda zance dan Wallahi bansan wayan da za'ai ma Meenal ba ta yadda aje kyauye da ita,dan har fariya take basu da "Yan'uwa akyauye,duk da tace koda suna dasu Wallahi bazataje ba,kuma bazatayi zuminci da suba,ba adad'e ba ina nan ina kallan wani film da arewa tasa ,ashe itama tana kallo tashi tayi ta kashe tibin ,wai da me zan k'aru zan zauna intasa tibi gaba ina kallan abin ta kaici.Gaskiya ganinake in dai dole sai antafi da ita, tom karka fad'amata inda za'a ,dan indai ta sani bazata ba" Shiru Alhaji Abba yayi na d'an wani lokaci sannan ya ce"Kina nufin inyi ma Meenal k'arya?".Ikon Allah sai kace Uwarka. Alhaji Abba yacigaba da cewa"Bazai yuwuba in b'oyemata gara in fad'amata gaskiya in samu in lallasheta,yanzu ki sameta ki fara mata maganar tafiyar kiji me zatacemiki,amma karfa ki mata maganar dalilin tafiyar"Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Nida nasan halin 'yan kayana akan me zan fad'amata,so kake in ruguza tafiyar kenan".hajiya Mariya na fad'in haka ta tashi ta ce"Bari inje inyima ta maganar tun yanzu" Meenal kwance kan caution tana game awayarta,hajiya Mariya tazo ta sameta.Hajiya Mariya kallanta tayi ta ce"Sarkin buga game,daddynki ya ce ki tashi ki shirya gobe zamu Katsina"Meenal aje wayar tayi tana kallan Mommynta ta ce"Mommy katsina kuma ,wannan wata irin tafiya ce babu shiri,kuma daddy yana da dangine a Katsina?".Hajiya Mariya zama tayi ta ce"A'a abokin Alhaji ne zamu mu gaid..."Hajiya Mariya mata gama maganarta ba Meenal ta amshe maganar da cewa"Mommy nikam gasjiya bazani ba,sai kun dawo,haka kawai Katsinar da bazaman lafiya ake ba".Hajiya Mariya rufe bakin Meenal tayi ta ce"Kul!Karki k'ara cewa bazaki ba,wannan tafiyar dolece ,dan haka karma in k'arajin maganar bazaki ba.Maganar Katsina kuma ba lafiya ai ba cikin gari zamu ba,kyauyan Katsina zamu".Meenal tashi tayi ta zauna tana ajewayarta ta ce"Mommy dan Allah inma daddy ne ya aikoki ki cemai bazani ba,kema dai kinsan bazanje ba,ni me zai wani kai ni kyauye,koma lafiya bare kuma kyauyan Katsina,gaskiya mommy bazani ba"Meenal na kaiwa haka ta tashi ta nufi part d'in daddynta tana turo baki,tana zuwa ko sallama babu ta ce"Daddy kaji kuma abinda Mommy ta k'ara tsiro da shi kyauyan Katsina zamu tafi gobe wai?"Daddyn Meenal hannun Meenal ya kamo ya ce"Zokiji Meenalyn daddy,ba Mommynki bace ta ce nina ce"Meenal kamar za tai kuka ta ce"Amma dai daddy ai kaima kasan ni bazanje ba,kuma wai akanmema sai dani dole za'a?"."Haba Meenalyn daddy tunda nina ce dan Allah ki shiya mu tafi,idan mun'isa da wuri tom ba zamu kwana ba,muna zuwa zamu dawo"Meenal juya baya tayi tana turo baki,babu dai alamar ta amince.Alhaji Abba ko cigaba yayi da lallashin Meenal daga k'arshe yayi mata alk'awarin daga sun dawo zai kaita Mina wajan yarinyar k'anwar Hajiya Mariya da Allah ya had'a jinin Meenal da ita.Meenal jin haka yasa ta amince da sharad'in bazasu kwana ba. Dole alhaji Abba ya bitada "Eh".Saboda ta yadda amma ya san dole sai sun kwana bazai yuwuba suje su dawo ranar kodan tsoran hanya". Alhaji Abba sosai yaji dad'in amincewar Meenal,dan bai tab'a tunanin zata amince ba. Da daddare Alhaji Abba na kallo Meenal kuma na chart da yarinyar k'anwar mamarta ta Mina wato Hafsat tana sanar da ita tafiyar da zasuyi gobe.Hafsat jin Meenal zata kyauye yasa taita mata dariya daga k'arshe ta ce"Kar dai kije wani d'an kyauyan ya mak'alemiki ,kuma wallahi bashi zamuyi"bak'in cikin maganar yasa Meenal ta aje wayar batare da ta rufe ko datarta ba.Alhaji Abba da hajiya Mariya da hankakinsu ya koma kan kallo sai ji sukai Meenal ta d'ad'e da kuka.Alhaji Abba da Hajiya Mariya kusan atare suka iso wajan Meenal ,bakamar alhaji Abba ba ,cikin damuwa ya ke cewa"Meenalyn daddy lafiya,yi shiru ki fad'amin karkanki yayi ciwo?". Meenal cikin kuka ta ce"Ba Hafsat bace wai kar in samomusu d'an kyauye" .Alhaji Abba lallashin Meenal ya fara yana cewa"Kiyi shiru dan Allah karma kanki yayi ciwo akan shirman maganar nan"Haka alhaji Abba ya dage sai lallashi yake dakyar ya samu Meenal tayi shiru. Washe gari da wuri suka gama shirinsu suka kama hanyar gidan Alhaji,Meenal dai yau bata magana da kowa,dan daddynta ma ganin Meenal kad'an take jira tasa mai kuka yasa shima yaja bakin shi yayi shiru.Koda suka je gidan Alhaji,wato kakan Meenal sun samu ya shirya su yakejira. Hajiya Mariya da alhaji Abba haka suka gaisa da kakan meenal cikin girmama,inda Meenal ko kallan shi tak'iyi. Alhaji kallan Meenal yayi ya ce"Amina har yanzu kinanan da halinki na miskilanci ko?".Meenal turo baki tayi ta ce"Karabu dani dan bagaidaka zanyi ba,kawani jawoma mutane zuwa kyauye muna zamanzamanmu lafiya"."Uwaki nace kice bazakiba mana dan'ubanki tafiyar duk danwa za'ayita badan keb....".Daddyn Meenal jin Mahaifinshi zai janyomai rigimar meenal yayi saurin katse shi da cewa"Alhaji rabu da Meenal kazo mutafi kar lokaci ya k'ure" Alhaji Abba shiga yayi inda Meenal da Mommynta suka zauna a baya.Alhaji Abba yaja motar suka tafi..................โœ๏ธ Shere & Comment please๐Ÿ™๐Ÿป ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 7&8. Kasan cewar tsakanin Kaduna da funtua tafiyar two hours ce,hakan yasa cikin lokaci suka iso funtua,suna shiga funtua Alhaji Abba ya kalli mahaifinshi wato alhaji ya ce"Alhaji kace kyauyan Funtua ne,tom gamu cikin Funtua ta ina zamubi?"Alhaji shiru yayi sannan ya ce " Ikon Allah shekaru aruru kaga hanyar ta b'acemin sai dai muyi tambaya asamu ahanya,ka fita kasamu wani ka tambaye shi layin kad'anya" Daddyn Meenal fita yayi daga cikin motar ya tambayi wasu nan dake zaune bakin titi.Nan fa suka nuna mai hanya suka ce kafin kakai d'andume anan zaka dauke hanyar ,sai karik'ayi kana tambaya"Godiya daddyn meenal yayi ya koma cikin motar,sai da ya koma baya sosai sannan yabi kwatancan da sukai mai.Alhaji Abba yana tafiya yana tambaya ahaka har suka kama hanyar kyauyan layin kad'anya.Nanfa suna tafiya mota na sama tana k'asa kasan cewar hanya babu kyau,ahaka suka shiga cikin garin layin kad'anya ,suna shiga daddyn Meenal ya kalli Mahaifinsa ya ce"Alhaji gamu a cikin garin,zaka'iya gane gidan?"."Ina Sani bazan ganeba,amma ka sauka katambayi gidan Malam Haruna mai allo".Daddyn meenal fita yayi ya tambayi wasu matasa da ke zaune.Aiko yana tambaya suka bashi amsa da basu San shi ba, juyawa daddyn meenal yayi ya koma cikin motar,gaba suka k'ara nan ma dai amsar iri d'aya basusan gidan ba,ak'alla sun tambayi mutane da dama amma amsar kenan basu san gidan ba.Alhaji Abba kallan Mahaifin shi yayi ya ce"Alhaji ko dai kamanta sunan shine,kaga kowa muka tambaya sai suce basu San shiba,in da ko sunan shi kenan inma ya mutune zasu ce ya rasu,shi yasa nace ko dai ka manta sunan ne?"." Mudai matsa gaba,amma taya zan manta sunan Haruna ,haka ake mai lak'abi da mai allo,mu matsa gaba mu tambaya".Daddyn Meenal shiga yayi suka matsa ,wani d'an dattijo suka gani suka tsaya ,Alhaji da kan shi ya bud'e ya fita,bayan Alhaji ya mik'amai hannu sun gaisane ya ce"Malam dan Allah gidan malam Haruna mai allo nake tambaya?".Shiru tsohonnan yayi yana tunanin inama yasan sunan nan,can bayan dogon nazarin da yayi ya ce"Wayyo haba nifa nasan nasan sunan nan da dad'ewa,amma sai na shafa'a,ai malam idan ka fad'i sunan sai ka b'ata sai dai irin mu da muka kwana biyu,amma kafi shekara talatin rabanka da kyauyan nan?". Meenal da ke jin su daga cikin mota tsaki tayi ta ce"Kaji daddy wallahi d'an kyauyan mutum nada wuyar sha'ani,daga tambaya ya dage sai zuba ma tutane surutu yake idan yasani ba sai ya fad'amana ba muwuce idanma bai sani ba ne shima musani amma ya wani turke shi da fira".Daddyn meenal murnushi yayi ya komo hannun Meenal ya ce"Meenalyn daddy kenan ai yanzu zai fad'imai mu tafi". Daga can kuma,shohon nan ya ce"Ai malam Haruna mai allo yanzu ai shine sarkin nomar garin nan,tun da aka bashi sarkin noma sunan shi ya b'ata da Haruna mai allo ya koma Sarki,yanzu ai indai ba Sarki kace ba mutane da dama bazasu gane ba,dan ko mu da muka kwana biyu wani ya manta sunan .kaga wata kuka can ko?,tom daga nan duk yaran da ka samu kace mai gidan sarki za'akaika". Godiya sosai alhaji yayi mai ya ciro canjin ajjihun shi ya bashi,sannan ya koma motar suka tafi. Suna zuwa dai_dai kukar suka tambayi matasan gun gidan Sarki daga nan aka nuna musu gidan suka k'arasa.Yaran da ya nuna musu gidan ne ya shiga yayi musu sallama da Sarki . Sarki fitowa yayi yana musu sannu da zuwa, ya yi musu iso izuwa "yar ma dai_dai ciyar fadar shi.Bayan sun gaisane,Alhaji ya kalli Sarki ya ce"Malam Haruna bakaganeni ba ko?"."Wallahi Alhaji kabani sani?".Dariya kakan Meenal yayi ya ce"Tom Malam Haruna Abdullahi ne na Kaduna".Ai Sarki naji hanka ya zabura yazo ya rik'e kakan Meenal ya ce"Malam Abdullahi kaine ,Masha Allah barka da zuwa ,sannu_sannun ku" Nanfa akafara sabuwar gaisuwa.Bayan an k'ara gaggaisawa ne ,Sarki ya ce"Gaskiya naji dad'in zumincin nan,dama bakamantani ba Malan Abdullahi ,kaddai kacemin wannan Sani ne ?"."Aiko shine banmantakaba duk da kai kamanta ni"."Wallahi banmanta da kaiba lokacin da kazomin da maganar auran sani tom nima alokacin na samu Sarkin noma na kyauyan nan har dama k'ananun kyauyukan da ke kusa damu,tom ince yau zanzo ince gobe da haka da haka dai na shafa'a,gashi kasan bantab'a zuwa ba bazan gane kwatancan da kaban ba,gashi lokacin ba lokacin waya ba kamar yanzu".Nan dai fira ta b'arke tsakanin su.Sarki wayar shi ya ciro ya mik'ama Alhaji wayar ya ce" Lalibomin number D'an juma ya kawo muku abin sanyi sana'ar shi kenan". Dariya kakan Meenal yayi ya ce"Yo idon namu ai duk d'ayane nima baganin nake ba sosai".Kakan meenal mik'ama Alhaji Abba yayi wayar ya ce"Lalibomai number".Amsa alhaji Abba ya yi ya ce"Me ye sunan?"."D'an juma zaka gani".Cewar sarki" Aiko Alhaji Abba na dubawa ya ga number,Kira d'aya d'an juma ya d'aga,yana d'agawa ,alhaji Abba ya mik'ama sarki wayar ya ce"Gashi an d'aga". Sarki amsa yayi ya ce"Assalamu aikum,d'an juma kananan ne koko ka shiga Funtuar ne?".Banji mai akace ba sai ji nayi ya ce"Tom dan Allah ka aikoshi yanzu ya kawo nayi bak'ine".yana kaiwa haka ya kashe wayar yana cewa"Dama nayi tunani bayanan, ka ganshi nan kullum yana Funtua kome yake zuwa Funtua yi kullum oho mai".Murmushi kakan meenal yayi ya ce"Wai ina Yahaya ne?"."Malam ,da yake haka yake kiran shi,ya ce"Ai yaran nan da na kira d'an wajan shi ne,kasan shima Allah bai bashi haihu da wuri ba,sai da yayi wani auran ma,tom shine kad'ai yaron shi Namiji,sauran duk mata ne,nima dai shikenan jikan namiji".Sunanan suna hira wani matashin yaro ya shigo ya kawo musu laimummuka,bayan yaron ya aje zai fita ne, kakan Meenal ya ce" Shine d'an juman "."A'a shine dai Yaron da d'an juma yake barma tsaran shagon shi".Yaron zai tafi ne sarki ya kirashi ya ce"Isihu maza kaje wajan Maryama kace nace nayi bak'i daga Kaduna ai musu girki". Sarki mik'amusu ledar da yaron ya kawo yayi ya ce"Malam Abdullahi ga laimu fa kusha dan Allah kafin ai muku girki,babu dai sanyi kasan Nepar tamu sai ahankali,dan ma d'an juma da daddare yana tada inji dan kayan suyi sanyi".Alhai mik'ama Mommyn Meenal yayi ya ce"Mariya kusha ko".Mommyn Meenal bud'ewa tayi taba kowa,sannan ta mik'ama Meenal da ke can gefe rakub'e tace Meenalyn daddy zoki amsa".Meenal cikin ya tsune fuska ta ce"Bazan shaba mommy".Sarki da sai yanzu ya lura da Meenal ,kallan Alhaji yayi ya ce"Ko ba afad'i ba nasan itace tawajan Sani,dan ga kama nan, a Kadunar take aure?".Alhaji wato kaka Meenal kai ya jinjina ya ce"Kaganta nan ko saurayi bata da shi bata da ranar aure ga mahaifinta nan ya d'aure mata gindi".Sarki kai ya jinjina ya ce"Wallahi Malam Abdullahi abinda ke damuna kenan ga d'an juma nan shima zaune babu ranar auran dan ko a wajan ku sai an mai surutu". Sarki maida hankalin shi yayi ga Meenal yana al'ajabi dan shi gani yake ko abirni sai amma wannan surutun rashin aure,suko anan ai ba'ama magana. Sarki kallan Meenal yayi ya ce"Zoki sha kinji irin nakune na binni".Alhai wato kakan Meenal kallan sarki yayi ya ce"karka biyema wannan miskilar banzar ,rabu da ita karta sha d'in kanta tayimawa".Kakan Meenal tashi yayi ya ce"Malam Haruna zamuyi sallah ga la'asarnan ana kira bamuyi azahar ba"."Tom bari in kira d'an juma ya turomin yaron da ya turo d'azu ya kawo lemu,sai ya rakasu can suyi sallar suhuta,mu kuma sai muyi zaman mu nan". Sarki number d'an juma yasa aka k'ara kiramai ,ya ce ya turomai da isihu ya raka bak'in da yayi gidan su". Aiko suna gama wayar ba dad'ewa yaron ya iso.Sarki sashi yayi ya ce" Karaka su gidan su d'an juma shashin Maryama" Meenal dai na zunb'ure_zunb'ure ta tashi,sukabi bayan yaron.suna tafiya Mommyn Meenal na ma meenal na siha,tana cewa"Meenalyn daddy dan Allah kisaki ranki insha Allah gobe zamu bargarin nan,kinsan mutanan kyauye da tsegumu,karmu tafi anayi dake,dan Allah kiyi hak'uri karkiyi abinda zaki jawoma kanki magana". Meenal dai bata tankama Mommynta ba,ahaka suka isa gidan. Babban gidane Wanda akekira gidan gandu,dan gidan cike yake da yara da manya.Su meenal na shiga kallo ya dawo kan su ,nan fa mutane suka rik'a mamakin daga ina suke.wata daga cikin matan gidan ta ce"Bukuga shashin Maryama sukai ba,kunsan d'an juma ne zai kawo su". Mommyn Meenal dai haka suka ri'kabin shashi_shashi suna tafiya,dan wadda aka Kira da Maryama wato surikar sarki ita ce Uwar gida agidan,hakan yasa sashinta ne acan k'arshe.Hajiya Mariya koda taga shashin da yaron ya shiga dasu sosai taji dad'i dan ita kanta tana tunanin yadda zasu kwana agidan suci abinci ,ganin sauran shashinan da suka baro kaca-kaca ,ga kwanonin cin abinci nan ko ina anbaza atsakar gidan.Hakan yasa mommyn meenal taji dad'in ganin inda aka saukesu saboda can fes yake babu alamun katsanta,daga gani dai matar shashin mai tsabta ce. Zuk'unne suka sameta tana alwallah.Cikin fara'a ta tari mommyn Meenal ta ce"Barkan ku da zuwa hajiya".Ta fad'i maganar tana mai amsar jakar hannun hajiya Mariya,tayi musu iso izuwa cikin d'akinta". d'akine guda d'aya kamar yadda dai kukasan d'akin kyauye,sai gadaje guda biyu na k'arfe ,angyaresu tsab,d'akin irin babban d'akin nan ne watacce.Maryama tabarma ta d'akko ta shimfid'amusu tana mai cewa"Barkan ku da zuwa hajiya ku zauna".Mommyn Meenal zama tayi tana mai cewa"Yauwa sanninku ,mun sameku lafiya".Nan dai suka gaisa sosai kamar sunsan juna,inda Meenal ko kallo mata bata isheta ba,ita kuma da fara'arta ta ce"Sanninku da zuwa"."Yauwa ".Meenal tace can cikin mok'oshi.Ruwa mai sanyi na randa ta kawo musu .Dama koda Sarki ya aikomata da tayi abinci yayi bak'i da take tana saida taliya 'yar murza ita ta d'ora musu tai musu jaloup d'inta.Bayan ta aje ruwan taliyar ta kawomusu sannan ta basu waje ta tafi d'akin yara ta tada sallar acan".Hajiya Mariya da ke son taliyar hausa cigaba da cin abinta tayi ta kalli Meenal ta ce"Meenalyn daddy kinga ni ko'ina fes matar na da tsabta sosai kici kinji".Meenal fuska ta ya mutsa ta ce"Mommy nifa bazan iya cin abincin nan ba,kika sani kodan an aikomata ne anyi bak'i ta gyara gidan,sannan duk "yan kyauye k'azamai ne,masu girki da ruwan kogi,nikam bazan iya ciba, keda za ki'iya kici".Mommyn meenal kallan Meenal tayi ta ce"Meenal kenan,nan ai bawani shahararran kyauye bane,bikiga sunada da tuk'atuk'a ba da wutar Nepa?"."Uhm".Meenal ta ce. Hajiya Mariya haka taci taliyarta ta k'oshi Meenal ko tak'i'ci.Hajiya Mariya na gamaci ta d'auki buta tayi alwallah tayi sallah,Meenal ma tashi tayi tayi alwallar ta tada sallar itama.Bayan duk sun idar ne Maryama wato mai shashin tazo ta zauna ,tana mai kara musu sannu da zuwa,ganin abincin da takawo musu sunci kad'an ta ce"Hajiya abincin beyi dad'i ba ko naga kunci kad'an".Murmushi Hajiya Mariya tayi ta ce"A'a wallahi da yake ni inama son taliyar hausa naci sosai,Meenal ce bataci ba"."Ayyah tom ko fura za'a samo mata ne?".Hajiya Mariya tasan Meenal na son fura sosai,amma ganin sunan taraina musu wayau hakan yasa ta ce"A'a batajin yunwa ne aniima zataci". Haka dai su kaita fira sama_sama ,har almuru ya gabato ,Maryama tashi tayi ta d'ora tuwan dare,tanayi suna hira da Hajiya Mariya.Kub'ewa Maryama ta d'akko zata yanka hajiya Mariya ta amsa ta yanka mata duk da tak'i hajiya Mariya ta nuna dole sai ta yanka hakan yasa ta bata.Ana sallar magriba ta tuk'a tuwan dawarta ta d'ora miyar, dama sarki ya aiko da zakaru biyu da yasa aka yanka yace ajuye su duka amiyar,da yake Maryama akwai iya girki da sarrafa girki hakan yasa ta raba uku tasa Kashi d'aya amiyar, Kashi biyu kuma ta yi musu farfesu da shi,aiko take b'angaran yahau k'amshi ,Meenal da bajuriyar yunwa gareta ba,take yunwa ta sata baccin dole.Hajiya Mariya bayan ta'idar da sallar magriba ne ta tadata akan tayi sallah,Meenal sosai tayi mamakin k'amshin da takeji azuciyarta sosai ta yaba da k'amshin dake tashi agidan,haka dai tayi sallah ta idar ta tashi ta tada sallar issha'i da ake kira.Itama hajiya Mariya sallar ta tashi tayi,dama maryama ta kawo musu tuwan ta aje musu harma da ruwan sha ,suna idar da sallah aka kawo Nepa ta haske wajan .Hajiya Mariya tana idarwa ta fara cin tuwanta dan tana marmarin tuwan dawa sosai,kallan Meenal tayi dake zaune tana kallanta, dagani kuma yunwa takeji,hajiya Mariya dai banza tayi da ita taci gaba da cin tuwanta dan sosai tuwan yayi mata dad'i.Meenal kallan hajiya Mariya tayi ta ce"Mommy kamar tuwan honey Well ko?"Hajiya Mariya Dan Meenal taci dan tasan indai tace mata irin tuwan da in sukaje Kano wajan Yayarta takeyine bazataci ba yasa ta ce"Eh Meenal shine". Meenal kallan Mahaifiyarta tayi ta ce"Mommy Allah yana kama da tuwan da kike cewa Mommyn Aisha taimiki in munje Kano".Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Tom kici kiji mana". Meenal hannu tasa tana turo baki kamar anmata dole taci.Loma d'aya taci tayaba da dad'in girkin kuma dama gaskiya ta yaba da tsabtar matar sosai.Sosai tuwan yayi ma Meenal dad'i dan har da cewa"Mommy da kad'an kika fita iya tuwo".Hajiya Mariya dai batace komai ba,murmushi tayi ta ce"Kin ma fad'i gaskiya. .Haka su hajiya Mariya da Meenal suka ci tuwansu sosai dan sun yaba da dad'in tuwan.Bayan sun gama ci ne nan Maryama ta dawo ta nuna musu inda zasu kwanta ,itama tai musu sai da safe taja musu k'ofar ta fita" B'angaran su Alhaji ko suma bayan sun gamacin tuwan sun dad'e suna santin shi.Sarki d'akin d'an juma ya kai Alhaji Abba ya ce ya kwanta su kuma zasu kwanta shi da Alhaji tare . Da daddare Alhaji wato kakan Meenal ya ce"Malam Haruna wato zan iya cewa tafiyar nan tamu gaisuwa ce da rok'on iri mu kai,wato Amina yarinyar wajan Sani,jikata kenan wadda kagani d'azu, Wallahi malam yarinyar nan in ra'ayine in ma ciwo ne dai tom ta gado wajan mahaifinta,in bazaka manta ba na dad'e ina amsar addu'a awajanka ina ba Sani dan hankalin shi ya juyo akan maganar aure,tom itama yarinyar nan da kagani Amina haka take kaganta dai babu maganar aure akanta,tom duk da mu acan Amina ba wata babba bace wadda za'aima surutu dan ba tai aure ba,amma ni gaskiya awajena tuni ta isa aure inda bamu manta al'adar iyayan mu ba,da kuma koyarwa ta addinin musulinci,tom shine fa na had'o abin biyu mu sada ziminci kuma aima Amina addu'a itama kamar yadda akaima Mahaifinta kafin ya auri mahaifiyarta".Shiru sarki yayi ,ya ce"Tom Malam garama ku can sai ace birnine babu mai maka surutu,amma bari kaga zuwa gobe zaka Abdurrahaman ,wato d'an juma kenan,Wallahi Alhaji kaikanka zaka fad'a ko acan birni yaci afara mai surutun rashin aure bare kuma munan kyauye ,da sa'annin shi sun manta da sunyi aure dan da akwai wanda ya aurar da 'Ya ma,amma shifa har yanzu babu maganar auran akan shi,nayi addu'ar nayi na kuma,tom har yanzu dai Allah bai kawo lokacin ba,Yanzu haka maganar da nakema mahaifin shi sama_sama yake mai magana saboda rashin aure".Shiru sarki yayi sannan ya ce"Yau she zaku kuma ne?,sai mu fara addu'ar zuwa gobe".Eh tom gobe gaskiya mukasa zamu koma,amma idan ba zai yuwuba sai mu k'ara kwana ai".Shiru sarki yayi sannan ya ce"Gaskiya idan sansamu ne ita Aminar abarta anan koda kwana goma ne mugani ".Tom shikenan ai ba damuwa,nima ina nan inda hakane shi Sanin sai su tafi shida Mariya,mu kuma mu zauna nida Aminar" Haka dai su kaita firar su ta yaushe gamo har bacci ya kwashe su". Washe gari,Alhaji Abba bayan sun gaisa da Alhaji ne yake sanar da shi sai dai shida hajiya Mariya su tafi,shida Meenal kuma sunanan har agama ma Meenal addu'ar nan da kwana goma".Alhaji Abba rasa abinda zai ce yayi dan yasan da akwai daru wajan Meenal sosai,amma babu damar yayi ma mahaifin shi gaddama hakan yasa ya ce"Tom shikenan,Alhaji idan hakane ni yanzu zan wuce dama ina da meeting yau".Alhaji Abba na fad'in haka ya tashi yayi musu sallama ya ce"Tom ni zan wuce idan munyi waya naji ranar da zaku dawo".Alhaji Abba na kaiwa haka yayi musu sallama ya tafi,dan Sarki na cewa ya tsaya ko karyawa mana yayi ,ya ce"Wallahi yanzu haka ana jirana ne". Alhaji Abba haka ya tafi baima Meenal da Mommynta Sallama ba ,dan yasan indai Meenal taji zata zauna za'asha daru ,bazata yadda ya tafi yabarta ba,hakan yasa ya tafi bai musu sallama ba......โœ๏ธ Meenalyn daddy yanzu zamu shiga cikin labarin Sister,bini ahankali๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ. Share & Comment plz ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 9 & 10 Alhaji Abba sai da ya shiga cikin garin Kaduna sannan ya Kira Airtel d'in Mommyn Meenal dan yaji ance basu da network d'in M.T.N,Hajiya Mariya zaune take tana karyawa da kunu da k'osan da Maryama ta kawo musu .Meenal ko da ma ko agida ba shan kunu take ba.Hajiya Mariya na cikin shan kununta Kiran Alhaji Abba ya shigo wayarta,d'auka tayi tana mai kangawa a kunnanta .Bayan hajiya Mariya sun gaisa da daddyn Meenal ne yake sanar da ita ya tafi.Hajiya Mariya cikin mamaki ta ce"Daddyn Meenal ka tafi kuma kamar ya,mu fa?".Meenal da mamaki take kallan mommynta.Amsar wayar tayi daga hannun mommynta ta kanga akunnanta ta ce"Daddy kana ina?".Alhaji Abba cikin lallami ya fara magana,kamar haka"Meenalyn daddy meeting gareni 8:00 AM ,shi yasa banzo mu kayi sallama ba ina saur..."Meenal katse daddynta ta yi da cewa"Daddy wai kamar ya bangane ba,mu fa sai yaushe zamu tafi?".Alhaji Abba cikin lallami ya ce "Meenalyna ki yi hak'uri kinji ,Alhaji ya ce dole keda mommynki zaku zauna ku dawo tare,nan da sati mai zuw....".Ai Meenal bata gamajiba,ta yi wurgi da wayar ta fasa kuka.Maryama dake waje da saurinta har tana tuntub'e ta shigo d'akin tana tambayar lafiya. Meenal kuka take tsakaninta da Allah ita tafiya za tai.Maryama cikin damuwa ta kalli hajiya Mariya da bata tankama Meenal ba tsabar haushi ta ce"Hajiya lafiya bata da lafiya ne?"."Wai daddynta ya tafi bai mata sallama ba,sai kace wata k'aramar yarinya". Mariyama dai mamaki ya kamata ,amma sai ta aje mamakinta ta kalli meenal ta ce"Ki yi hak'uri kinji kar kanki yayi ciwo ".Haka dai Maryama tai ta ba Meenal baki har sai da taga tayi shiru sannan ta rabu da ita. Hajiya Mariya kallan Maryama tayi ta ce"Dan Allah ko akwai yaro kusa in bashi ya amso ma ta kayan tea,da yake ita bata shan kunu ko agida". Sallamar d'an juma da Maryama wato mahaifiyar shi taji ne yasa ta ce"Yauwa bari ga yayansu nan ya amso mata". D'an juma cikin na tsuwar shi yayi sallama ya shiga,wani irin yarrrr yaji lokacin da idanun shi su kai mai tozali da Meenal da ke zaune ana bata hak'uri har yanzu dai tana shasshek'ar kukan.D'an juma cikin zuciyar shi ya ce"Ko sune bak'in da jiya sarki yace min anyi,amma kuwa wa In can kamar maza ne inda shi ya kirani yace min in samu d'akin kwana bak'i zasu kwana a d'akina". Maryama wato Mahaifiyar d'an juma kallan d'an juma tayi ta ce"Yauwa dan Allah kawomana kayan tea".D'an juma kai ya siddar cikin sanyin muryar shi ya gaida hajiya Mariya sannan ya fita.Dai-dai k'ofar da zata sadashi da wajene yasake wai gowa,aiko take idon shi ya fad'a ana Meenal.Meenal da dama ta tsani kallo ta gallamai harara,aiko sai a idon Momnynta. Hajiya Mariya kallan Maryama tayi ta ce"Shine babban d'anki ko?".Kai Marayama ta duk'ar tana murmushi irin kunyar d'an farin nan.Meenal ko azuciyarta hattace kai wannan bai kama da d'an kyauyan nan ba,amma jin alamun d'an matar ne ma,sai ta ce"Koda yake ko yadda yake kallan muta ne ma yasa ka shaida d'an kyauye ne". Mahaifiyar d'an juma kuma fita tayi ta ce"Bari a'a za ruwan shayin".Bayan mahaifiyar d'an juma ta fitane ,Mommyn Meenal ta kalli Meenal ta ce"Meenal ina miki magana amma bakyaji ko,ke ala dole sai kinyi abinda za'asan baki da tarbiya ko,yanzu wannan da kika harara tsaranki ne?".Meenal turo baki tayi ta ce"Mommy bikiga yadda yake kallona ba,nifa na tsani kallo Wallahi".mommyn meenal dai na siha irin wadda ta sabayi ma meenal ce tayi mata. Abin mamaki d'an juma sai fara jin shi wani iri ga wata irin fad'uwar gaba da kasalar zuciya ta samai , tunda yayi tozali da bak'uwar nan tasu.Abu kamar wasa koda yaje shagon manta abinda zai d'auka yayi sai da ya Kira Mahaifiyar shi awaya sannan ta tuna mai,ya aiki yaro ya kai.Shi kuma ya zauna yayi shiru,daga ya rufe ido sai yaga fuskar yarinyar yake gani,bai kawo komai aran shi ba sai cewa yayi tsabar kyan yarinyar ne yasa take min gizo a Ido. Can cikin gidan kuma lokacin da Yaron ya kai kayan tea d'in lokacin ruwan zafin da Mahaifiyar d'an juma tasa har yayi zafi.D'iba tayi a kofi mai kyau ta kaima Meenal.Hajiya Mariya amsa tayi ta had'ama Meenal tea d'in ta bata.Meenal tana turo baki kamar yadda ta saba in ranta na ab'ace ta ce"Mommy na k'oshi".Hajiya Mariya babu yadda batayi da itaba tak'i.Hajiya Mariya d'aukar tea d'in tayi ta kaima mahaifiyar d'an juma da ke waje tana wanke kwanonin da ta b'ata. Hajiya Mariya zama tayi gefan Maryama ,ta ce"Kin ga 'yar gidan na ki tak'i sha".Mahaifiyar d'an juma amsa tayi ta ce"Tom ko wani abun take so ta fad'a kafin yayansu ya tafi insa shi ya kawo mata"."Ki rabu da Meenal in taji yunwa da kanta zata naima bata da juriyar yunw..."Sallamar d'an juma ce tasa Mommyn meenal yin shiru. D'an juma kallan Mahaifiyar shi yayi ya ce"Inna zan tafi ko akwai abinda kike buk'ata".Mahaifiyar d'an juma banza tayi da shi kamar bata ji abinda ya ce ba,ta ci gaba da wanke-wankenta.Shiru d'an juma yayi sannaya juya ya ce"Inna na tafi".yana fad'in haka ya tafi dan yasan ba amsa mai za tai ba. Bayan d'an juma ya fita ne,Hajiya Mariya ta kalli Mahaifiyar d'an juma,ta ce"Auntyna idan laifi yayi ayi hak'uri dan Allah d'a zuma ina gani yana gaidaki baki amsa mai ba".Maihaifiyar d'an juma aje wanke-wanken da takeyi ta yi ,ta ce"Hajiya dole in fushi da shi ink'i amsa gaisuwar shi,na san ke kanki kallan mai mata kike mai,amma kin gan shi nan bashi da ranar auran ma,ke budurwar ma baida ita,an bashi yara da dama agarin nan yace baiso,tom ya yake so muyi,nan fa kyauye ne ba binni ba bare yace ,na tabbata ko a binni Namiji d'an shekara talatin da bakwai ya isa afara mai surutu bare kuma anan.Mahaifin shi yanzu haka fushi yake dani yace nina d'aure mai gindi,tom kwanannan k'anwar baban shi ta bashi 'ya itama yace bai so,tom taya bazanyi fushi da shi ba".Mahaifiyar d'an juma ta idasa maganar cikin alamun damuwa" Hajiya Mariya kallan mahaifiyar d'an juma tayi ta ce"Eh gaskiya kam kallan mai mata nayi mai,duk da da darkoma banyi tunanin anan ya ke ba,amma abinda zaku duba aure lokaci ne,idan lokacin yazo zaiyi,duk kalar fushin da za ku yi da shi dole sai ranar da Allah ya nufa zaiyi auran zaiyi.Dan haka shawarar da zan baki nisiha zaki tayi mai ".Haka dai Mommyn meenal tai ta yima mahaifiyar d'an juma nasiha,da ankarar da ita komai lokaci ne" D'an juma ko na fita gidan Sarki ya biya wato kakan shi kenan,zaune ya iske tsofaffin biyu sai hirar su suke.D'an juma zama yayi sannan ya gaida sarki da kuma kakan Meenal.Alhaji cikin fara'ar shi ya ce"Tun da na iso nakejin ana cewa d'an juma-d'an juma amma kuma d'an juma yayi wahalar gani".D'an juma dai murmushi yayi ,kuma dama shi mutum ne ba mai yawan magana ba .Sarki amshe zan can yayi da cewa"Ka gan shi nan girman banza ne babu mata,tom ko dai Kadunar zaka tafi da shi ka zab'ar mai matar aure acan inda yak'i na mahaifar shi".Dariya Alhaji yayi ya ce"Abdurrahaman zaka Kaduna ko in baka mata".Shi dai d'an juma murmushi kawai yayi.Sannan ya yi musu sallama ya tashi ya tafi,yana mai son sanin su waye su,dan shi dai bai tab'a jin ance suna da 'yan'uwa a Kaduna ba,amma kuma abisa ga dukkan alamu wannan sun saba da Sarki . Sarki Kiran d'an juma yayi ya ce"Yauwa d'an juma zoka kaima Yarinyar nan addu'ar nan ta fara sha tun yau".Alhji wato kakan meenal ya ce"A'a indai Amina ce bazata shaba,yaje dai su taho tare in tsareta ta sha agabana" . D'an juma fita yayi ya d'auki mashin d'in shi roba-roba ya nufi gidan su,yana zuwa ko ya iske Mahaifi yar shi ce kad'ai atsakar gidan .kusa da ita ya k'arasa ya ce"Inna Sarki ya aikoni inzo in tafi da yarinyar nan bak'in da akayi". Mahaifiyar d'an juma ba tare da ta amsa mai ba ta shiga d'akinta inda Meenal take da Mommynta, Meenal na kwance dan yunwa ta fara matsa mata.Mahaifiyar d'an juma kallan Mommyn Meenal tayi ta ce"Hajiya wai sarki ne ya aiko kiran Amina"."Tom shikenan d'an ai kyan na nan ai sai su tafi tare".Mommyn Meenal na fad'in haka ta fara bubbuga Meenal dake jin su ,ta ce"Meenalyn daddy ki tashi kije ana kiranki".Bud'ar bakin Meenal sai cewa tayi "Mommy ni bazani ba".Hajiya Mariya d'aure fuska tayi tana mai jin kunyar maganar da Meenal tayi,ta ce"Meenal ki tashi nace ko?".Meenal turo baki ta yi ta ce"Tom mommy ni mai zanyi dan Allah ni bazani ba" .Hajiya Mariya sosai taji kunya,haka yasa k'asa-k'asa yadda Mahaifiyar d'an juma bazataji ba ta ce"Wallahi kinji na rantse idan har biki tashi ba zan kira daddynki in ce mai ba yanzu zamu koma ba,idan kina ganin wasa ne kar ki tashi ki tafi" . Meenal tashi tayi tana zun b'uro baki tayi hanyar waje,dan ita bama ganin Wanda zai kaita tayi ba .Hajiya Mariya gyalan Meenal d'in ta wurga mata ta ce"Ga gyalanki nan".Meenal amsa tayi ta fita ba tare da ta yafa ba ,bak'ar abaya ce jikinta taji adon stone tayi mata kyau sosai dama kuma ita Meenal tafi ra'ayin dogayan riguna. Tsaye yake da key d'in mashin d'in shi a hannu ,yayi adon shi ciki wani yadi mai kyau Masha Allah,Wanda ya dai wuce araina,dan d'an juma mutum ne mai son gayu gashi kuma shi dama hurd'ar shi tafi yawa a funtua. Sosai ya k'osa tafito ya k'ara kallan kyakkyawar fuskarta.Meenal tsaye tayi tana kallan shi bisa ga alama shine zai kaita.D'an juma ko dama tun kafin ta k'araso ya k'ureta da ido dan ko kyaftawa ba yayi,tana zuwa kusa da shi yayi saurin kauda idon shi,Meenal tsaki tayi dan ta tsani kallo,ja tai ta tsaya ,batare da ta tanka mishi ba,shima kuma sai ya kasa mata magana.Mahaifiyar d'an juma ce ta ce"Yayan su kuje mana gata nan ta fito" .Meenal tsaki tayi tai gaba yana binta abaya.Aiko suna fitowa 'yan gidan kowa idan shi akan Meenal .Meenal na zuwa taja ta tsaya kusa da mashin d'in.D'an juma ta gefan ido ya k'ara satar kallan Meenal d'in dan ya lura bata San kallo shi kuma baya son raini hakan yasa ya kalleta asace. D'an juma ya hau mashin d'in ,yaji bata hauba taja ta tsaya,cikin ko in kula dan shima miskilin ne ya ce"Ki hau muje ".Meenal sai da ta kallai jin yadda yayi mata magana,agadarance,ita dariyama yaso ya bata ,azuciyarta ta ce"Dan kyauye ko da me zai gadara har da zai min magana ahaka,ta ce koda yake ance d'an kyauyan mutum akwai iyayi" . Meenal zata iya rantsewa bata tab'a hawa mashin ba,inda ita dai duk inda zata daddynta ke kaita amota ko a motar Mommynta.Meenal rasa yadda zata hau mashin d'in tayi sannan ta dafa d'an juma tana mai jan tsaki ta hau. Kasan cewar hanyar bawani kyau gareta ba,hakan yasa Meenal kejin kamar zata fad'i.Wani rami suka fad'a Meenal ta rungumo bayan d'an juma cikin gigita tana mai cewa"Da Allah malam kayi ahankali karka kadani ".D'an juma sai da yaja burki ,ya tsaya ,sakkowa yayi daga kan mashin d'in ya ce" Sau biyu kenan kina min tsaki kar ki yi na uku". Meenal da ke cikin haushi ,gashi ya k'ara mata wani haushin maganar shi ,cikin b'acin rai ta ce"Idan na k'ara mai zaka iyayi!?".Ki k'ara kiga abinda zan iyayi".Meenal da takaici da haushi suka cikata wai ita d'an kyauyan nan yake cema haka.Cikin d'aga murya Meenal ta ce"An maka tsakin,an kuma an maka tsakin me zakayi!".D'an juma d'aga mashin d'in yayi Meenal ta tafi zata fad'i.k'ara ta saki na rik'o d'an juma cikin tsoran fad'uwar da zatai, ta kwanta kan bayan shi tana rik'e shi katakam tana zaro ido irin na mutum in yaji tsoro sosai.D'an juma abin dariya ya bashi yadda ta furgita,kuma dama shi ba kadata zai ba,hasalima abinda taimai duka baiji haushi ba,kawai dai dan ya samu hanyar da zasuyi magana ne ko mara dad'i ce yasa ya biye mata.D'an juma rik'e mashin d'in yayi da k'arfi dan yadda ta rik'e shi din yasa ya kusa sakin mashin d'in ta fad'i. Meenal jin ta zauna bata fad'iba ,ajiyar zuciya ta sauke.Ran meenal sosai ya b'ace ga bak'inci ya isheta ga yunwa ta isheta ka wai sai ta fashe da kuka. Sosai abin yaba d'an juma mamaki,yadda take kuka sosai,ci gaba da tafiya yayi bai tsayaba inda sun kusa gidan.Dai-dai k'ofar gidan D'an juma ya tsaya ,yana kallanta alamun ta sauka.Meenal sakko wa ta yi tana mai ci gaba da kukanta.D'an juma rashin sanin abinda zai ce mata yasa suka shiga gidan haka tana kukan,dan bai san me zai ce mata ba,duk da sai yaji zuciyarci cikin k'uncin kukan da takeyi.Ahaka Meenal da d'an juma suka shiga gidan. Sarki da alhaji da mamaki suke kallan Meenal ganin yadda take kuka.Sarki cikin damuwa ya kalli d'an juma ya ce" Abdurrahma,da yake so dadama yafi Kiran shi da sunan shi,ya ce"Abdurrahman lafiya ,me akai mata?".D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Nima bansani ba,muna tafiya naji tana kuka".Sarki hannun Meenal ya kamo yana cewa"Yi hak'uri Amina me akai miki yi shiru dan Allah kar kanki yayi ciwo".Babu maganar da sarki baima Meenal ba amma ko d'ago kai ta kalle shi tak'i.Alhaji ne da abin ya fara ba haushi ya ce"Amina wai bazaki fad'i abinda akai miki bane zakibzo ki tasamu kina mana kuka?".Alhaji ma wato kaka Meenal babu irin maganar da baima Meenal ba ,amma tak'i sauraran shi,ganin haka yasa ya ce"Malam Haruna rabu da ja'idar yarinyar nan da iyayanta suka sangartata d'akko mata addu'ar tasha taba mutane waje".Sarki d'akko addu'ar da yayi ma Meenal yayi ya bata ya ce"Gashi ko kisha da bisimillah".Meenal bata d'agoba daga kukan da take bare kuma sarki yasa ran zata kula shi.Alhaji wato kakan Meenal sosai ran shi ya b'ace hakan yasa ya kalli D'an juma ya ce"Abdurrahaman idan mu tarainamu tana ganin bama iya mata dan Allah in dai bata shaba ka d'ura mata shi nina saka ja'idar yarinya mara kunya".Alhaji na fad'in haka ya kamo hannun sarki ya ce" Dan Allah mu fita in barjin kukan ja'idar yarinyar nan" .Sarki bin shi yayi aka bar Meenal da D'an juma. D'an juma ruwan addu'ar ya d'auka ya matsa kusa da Meenal ya ce"Ba'ama tsofaffi gaddana ,amsa ki sha".Meenal amsa tayi babu zato babu tsammani d'an juma sai dai yaji ta watsa mai ruwan addu'ar a fuska,dai_dai nan Alhaji da Sarki suka dawo d'akin.Aiko Alhaji wato kakan Meenal hannu yasa ya yarfama Meenal mari zai k'ara na biyu Sarki ya rik'e hannun shi da sauri,yana cewa"Haba Alhaji me yasa zaka mareta ai abin dama sai da lallab'awa ,idan bazata shaba shikenan sai arabu da ita".Alhaji cikin jin haushi ya ce"Wallahi Malam Haruna Amina bazata bar garin nan ba sai ta sha maganin nan adadin yadda ya kamata,idan kuma ba hakaba sai dai mu shekara anan".Alhaji wayar shi ya ciro ya mik'ama d'an juma ya ce"Lalibomin numbar Ubanta in sanar da shi............โœ๏ธ Meenalyn daddy group Comment d'in ku yayi k'aranci . idan kin karanta ki daure ki Comment sister. Share & Comment please๐Ÿ™๐Ÿป. ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 11 & 12 Sarki kallan d'an juma yayi ya c"Abdurraman jeka mai data gida,inda bazata gane ba". D'an juma fita yayi yana mai jin duk ba dad'i abinda Alhaji yayi ma Meenal,ko ba komai ita d'in bak'uwar su ce. Meenal ko na fita hanya ta mik'e taci gaba da tafiya tana kuka babu ruwanta da kowa,dan tunda take ba'atab'a b'ata mata rai irin na yau ba.Hanyar da tabi ko kwatakwata ba hanyar komawa inda tafito bace,hasalima hanyar fita cikin garin tabi" D'an juma da sauri ya bita yana mai cewa" Hanyar da kikabi ba hanyar komawa gida ba ce,kizo ki hau mashin d'in in mai da ki". Meenal babu alamunma taji abinda d'an juma yace tafiyarta taci gaba dayi babu alamun zata tsaya.D'an juma ma binta yarika yi ya nama mai cewa"Dan Allah kizo in kaiki da akwai inda zani". Meenal still tafi yarta taci gaba dayi tana mai goge hawayan da ke zubar mata,dan acewarta Alhaji ya tozartata,ga Meenal ba dai iya fushi ba. D'an juma ganin babu alamun zata tsaya hakan yasa sha gabanta.Meenal cikin masifa dan gwanace a iya fad'a ta ce"Ni ba sa'arka ba ce Malam da zaka taremin gaba ina tafiya,dole ne sai na bika?,Koko dole ne sai na koma gidanku,nace bazani ba ,shin ana dole ne!!?".Meenal ta idasa maganar cikin tsantsar masifa har tana Kumfar baki. D'an juma cikin kwanciyar hankali ya ce"A'a ba dole bane,amma kuma ni dole ne in cika umarnin sarki".Meenal mamaki,Al'ajabi suka cikata wai ita d'an kyauyan nan kema magana haka,ko da yake babu komai alhaji yaja mata,in bahakaba inama zai ganta bare har yasamu damar fad'a mata magana. Meenal goge hawayanta ta yi ta ce"D'an asabe ka ke ko d'an me ye,dan Allah jani ka kaini".Murmushi d'an juma yayi yana girgiza kai ya ce" Bazan jaki ba,da k'afarki zaki hau mu tafi". Meenal ja tai ta tsaya batare da tak'ara tanka ma d'an juma ba.D'an juma kuma ganin haka zuwa yayi ya d'akko mashin d'in shi ya matso da shi kusa da ita ya ce"Beauty dan Allah hau muje mana".Sunan da d'an juma ya ga ya cancanci da Meenal kenan acewar shi,dan ita kyakkyawa ce ya ce". Meenal kuma jin sunan da d'an juma ya kirata yasa ta kallai batace komai ba ta hau mashin d'in tana mai k'ara goge hawayanta." Suna gaf da shiga Gida,Meenal taga mai nono da fura,gashi dama yunwa takeji,hakan yasa ta ce"Tsaya" . D'an juma tsayawa yayi yana mai sauraran abinda zata ce,sai ji yayi ta ce"Me nono".Mai nono da saurinta ta k'arasa,Meenal sai da tagama kallanta sama da k'asa wai ko zataga inda take da alamun k'azanta.D'an juma jin shiru yasa ya waiga yana kallan Meenal jin ta tsaida mai nono batace komai ba,ya ce"Kina so ne". Meeenal banza tayi da shi ta ce"Me nono ki ban ta yadda zan iya shanyewa".Me nonon kallan Meenal tayi ta ce"Tom aini bansan cikinka ba,na nawa dai zan baka". Meenal tsaki tayi ta ce"Ban ta d'ari biyu"."Tom za'adama maka ne koko abaka kadama"."Bani in dama".cewar Meenal. Me nonon zubama Meenal tayi aleda ta bata.Meenal ko bata fito da kud'i ba hakan yasa ta ce"Ki biyo bayana ki amshi kud'in".da me nono da d'an juma mamaki ne ya kama su, taya zata iya bin mashin ita dake ak'asa. D'an juma ciro kud'in yayi ya bata,yaja mashin d'in shi ya tafi,yana mai cewa"Na ranta miki idan mukaje sai ki ban kud'ina".Meenal banza tayi da shi bata tanka mai ba.D'an juma ko sai da ya kai Meenal har cikin d'akin Mahaifiyar shi sannan ya juya zai tafi.Meenal ta ce"Dakata!". D'an juma tsayawa yayi,inda Mommyn Meenal da Mahaifiyar d'an juma suka tsaya suna sauraran ikon Allah. Meenal kallan Mahaifiyar d'an juma ta yi ta ce"Ki ja mai kunne ya fita daga har kata saboda ni ba sa'ar sa'insar shi ba ce,idan kuma ba haka ba...." .Tsawar da Mommyn Meenal ce tayi ma Meenal yasa tayi shiru,hajiya Mariya cikin b'acin rai ta ce"Meenal sa'anki ne,koko ita d'in sa'arki ce da kike kawo mata k'ara haka?". Meenal turo baki tayo.Mahaifiyar d'an juma kuma ta ce" Yi hak'uri kinji Amina,kuma zan ja mai kunne ba zai k'ara ba kinji" . Abin mamaki kawai sai meenal ta fashe da kuka kamar wadda aka buga tana nuna ma Mommynta fuskarta ta ce" Kalli fa kigani yadda Alhaji ya maran saboda shi,du ba fa ku gani" .Meenal ta fad'i maganar tana k'ara fashewa da kuka" .Daga d'an juma har Mahaifiyar shi da mamaki suke kallanta. Mahaifiyar d'an juma ce taita lallan shi Meenal tana bata hak'uri ahaka dai aka samu tayi shiru.Mommyn Meenal kuma ta kaici yasa bata tanka ba" Mahaifiyar d'an juma furar hannun Meenal ta amsa ta damamata. D'an juma kuma bayan ya fitane ya ba yaro peak milk ta ruwa ya ce a kaima Maman shi ace tadama furar da ita. Mahaifiyar d'an juma bayan ta gama dama furar ne ta kaima Meenal tare da bata hak'uri.Meenal ko kasan cewar yunwa takeji yasa bata wani tsaya sanabeba ta d'aga furarta ta shanye tass.Tana gama shan furar takwanta takama bacci. B'angaran d'an juma ko yauma kamar kullum yana zaune acikin saif plaza dake garin funtua.D'an juma kallan Kamal yayi ya ce" Kamal kana yawan fad'amin wata magana,da sai yau nake son insan gaskiyarta,ka ce duk yarinyar da nace ina so da wuya tak'ini,shin a cikin kyauyan mu kake nufi koko har acikin gari,ma'ana cikin birni?".Murmushi Kamal yayi ya ce"Abdurrahaman a ko ina nake nufi ba wai a kyauyanku kad'ai nake nufi ba".Shiru d'an juma yayi ya ce"Kana ganin yarinyar da ta fito cikin garin kaduna tayi karatu agarin kaduna,ta tashi cikin gata ,Kamal dan Allah karka yau dareni kana ganin yarinyar nan ko zata iya soni?". Murmushi Kamal yayi ya kamo hannun d'an juma,dan ya kula abokin nashi ya rufta da yawa ya ce"Abdurrahman,koda cikin garin Abuja ta tashi,tayi karatu acan ,sai dai son zuciya da girman kai irin na mata amma tsab zata soka". Shiru d'an juma yayi sannan zuwa can ya ce"Kamal kallo d'aya nayi mata ,yadda naji akanta na tabbatar shi akekira so,tabbas yadda naji da kuma yadda nakeji yanzu tambari ne na soyayya,dan Allah ka ce inyi hak'uri Wallahi tafi k'arfina". Shiru Kamal yayi ,na d'an wani lokaci sannan ya ce"Wacece ita Abdurrahman?"."Nima kaina bansan wacece ita ba,na gansu ne da Sarki,bisaga'alama dai kakanta abokin sarki ne"."Kai tom ai in hakane Abdurrahman kanada dahir,nasan sarki na sonka da yawa zai iya maka k'ok'ari ganin ka sameta".Cewar Kamal" Shiru d'an juma yayi,sai kuma ya ce,"Ga sunanta mai dad'i ,Amina suna kiranta da Meenal,tana da fad'a da masifa,amma kasan me Kamal?".Kamal kai ya girgiza.D'an juma kuma ya ce"Tsiwarta kyau take mata,ta kasa b'acemin a ido lokacin da takemin fad'a zan kadata" Kamal kai ya girgiza,dan yaga abin banawasa ba ne ,k'arshema sai cewa yayi"Amma idan haka ne Abdurrahman yana da kyau ka samu soyayyarta kafin ta tafi".Kai d'an juma ya girgiza ya ce"Kamal bazata soni b ,kawai dai nina san tamin shigar sauri,tabbas na kamu da sonta lokaci guda,kuma so mai wahalar fita". Kamal da sosai ya gaskata maganar d'an juma dan ko dan yanayin yadda yake magana kamar wani maraya yasan tabbas so yayi mai shigar sauri.Kamal kallan d'an juma yayi ya ce"Kuna magana da ita ne?".Kai d'an juma ya girgiya ya ce magana da ita bazata yuwuba,yarinyar miskilar gaske ce,kuma kamar tana da jida kai bisa ga alamunta". "Tom duk da haka dai ni shawarar da zan baka ,karik'a musu alheri ita da 'yan'uwanta kafin su tafi,sannan bahaushe yace da rashin tayi akan bar arha,lokuta da dama muna ma mututa ne kallan halinda ba d'abiyar su bace sai ka zauna dasu zaka San haka,dan haka ina mai baka shawara ka gwada sa'arka k'ila kadace" . D'an juma kallan Kamal yayi ya ce"Kana ganin zan iya da cewa?"."Sosai ma kuwa".Cewar Kamal.Ranar dai haka d'an juma ya wuni yana mai jin wata irin fargaba akanta,dan ko ajikin shi bayajin za ta so shi ,hasalima zuciyar shi gargad'in shi take karya sake ya furta kalmar so ga Meenal.Wata zuciyar kuma ta ce "Koma biki gargad'an ba nima bazan iya furtawa". Haka dai d'an juma ya yi ta sak'arshi yana warware abin shi,kamar yadda ya saba tafiya gida gaf magriba yauma haka ya tafi,sai da ya biya ya sai mata fura,inda yaga d'azu ta siya ,sannan ya hau mashin d'in shi ya tafi". WAYE D'AN JUMA?: Mahaifin d'an juma mahaifiyar d'an juma ce uwar gidan shi,sai dai Allah yasa bata samu haihuwa da wuri ba,hakan yasa Sarki wato kakan d'an juma kasan cewar yana son ganin jikan shi yasa Mahaifin d'an juma k'ara aure,inda Mahaifin d'an juma ya k'ara auran badan yana soba,sai dai bayan auran su da Lami da wata goma ta haifi d'iya mace wato Rabi suna ce mata Yaya Rabi.Lami wato kishiyar Mahaifiyar d'an juma sai da ta haifi mata uku babu namiji aciki,hakan yasa Sarki yasa Mahaifin d'an juma k'ara aure ko za ahaifar musu Namiji.Cikin ikon Allah Maryama wato Mahaifiyar d'an juma da amaryar da Mahaifin d'an juma ya aura kusan atare su kai laulayin ciki,dan sati d'aya ne tsakanin su a haihuwa,inda ranar wata juma mahaifiyar d'an juma ta haifi d'a namiji,amaryar su kuma ta haifi mace.lokacin mahaifin d'an juma na da Yara biyar duk mata,hakan yasa Sarki da Mahaifin d'an juma suka rasa inda zasu sa Maryama wato Mahaifiyar d'an juma,tsabar murnar haihuwar Namiji da akai musu.Ranar sunan d'an juma yaci sunan Abdurrahman.Tom kunsan mutanan kyauye da rad'ama mutum sunan ranar da aka haife shi,dalilin ranar juma'a aka haifi d'an juma shine fa suka b'atar da da sunan shi suka rik'a Kiran shi da d'an juma. Tun ranar sunan d'an juma aka fara cin karo da ban-banci,dan ko sarki ya kashe kud'in da bai tab'a kashe rabin su ba sauran jikokin da aka haifar mai .Haka Sarki da Mahaifin d'an juma suka d'auki son duniya suka d'orama d'an juma.D'an juma na yaro sosai akazo layin kad'anya akai gina musu primary School,tun ana ginin makarantar d'an juma ya kwallafa rai dan gani yake wani abunne,hakan yasa ana gama ginin Sarki da kan shi ya d'auki d'an juma ya kai shi.Allah kuma yasa d'an juma nada k'okari ,ahaka dai ya kammala aji shida,kasan cewar babu secondary agarin hakan yasa Sarki ya samar mai gurbin karatu a d'an dume dan babu nisa sosai tsakanin su,ahaka-ahaka dai d'an juma ya kammala secondary d'in shi,daga nan ne fa Sarki yace ba zai shigema kafuran nan da yawa ba dan haka ya isa hakanan karatun,dole d'an juma ya hak'ura badan yaso ba.Tom daga nan fa sai kuma ya fara zaman gida babu sana'a,gashi shi saboda Makaranta da yayi bai iya aikin gona ba.Sosai rashin sana'ar d'an juma ta fara damun Maryama,ana hakane Allah yayi ma Mahaifinta rasuwa,tom da aka rabamusu gado ne Maryama ta ba d'an juma ya bud'e provision, kusan babu abinda bai sai dawa .A funtua yake zuwa Sarin kaya,hakan yasa ya fara abokai,ahaka-ahaka dai suka saba da ogan nashi,ahankali-ahankali ya fara jawoshi jikin shi yana tsare mai kayan shi,shi kuma d'an juma shima can sai yayi yaro shima yana bashi tsaron nashi,tom inda d'an juna ke tsarewa plaza ce babba ba laifi.Abinda yasa yake b'oyema sarki gani yake kamar zai hana shi,shi yasa sarki bai San abinda d'an juma ke zuwa funtua yi ba kullum. Layin kad'an ya Yaro d'an shekara goma sha bakwai,Shatakwa,ashirin suke aure, hakan yasa d'an juma ma tun yana matakin secondary suke bashi aure amma yak'i,atakaice dai har izuwa girman shi na cikakkan namiji .Wanna yasa akema d'an juma surutu sosai,dan wasu cewama suke k'ila aljana ce ta aurai.Shiko d'an juma tunda ya taso Allah yasa baida ra'ayin irin auran garin su,macan yarinya shima angon yaro. Tunda d'an juma ya fara mallakar hankalin shi yafi buk'atar budurwa wadda tasan abinda takeyi ba kwaila ba irin na garin su.Wannan kenan" D'an juma haka ya hawo mashin d'in shi ya dawo gida . Meenal ko tun da ta farka daga bacin da tayi take neman wayar da zata Kira Daddaynta ta kai k'arar alhaji wato kakanta ,akan maganar shan addu'ar da ya ce sai ta sha, idan bata sha ba baza ta tafi ba.Wayar mommyonta ko tun jiya da tayi wurgi da ita ta d'auke, wayar mahaifiyar d'an juma kuma babu caji,hakan yasa ta rasa wayar da zatai kiran. Meenal sosai take jinta atakure zaman kyauyan,dan ko abinci rana da Mahaifiyar d'an juma ta kawo musu k'in ci tayi. Meenal kallan Mommynta ta yi, ta ce"Yanzu mommy da ban gama Exams ba haka mutunin nan zauzo nan kawai ya kama zaunar da muta ne,Allah ni dai kije ki mai magana,idan ba haka ba zaki nai man kirasa,dan ni daga gobe bazan k'ara kwana kyauyan nan ba,tun da nazo wayana baya aiki,inda ni M.T.N garan ,dan Alllahi nidai ki san yadda zaki Mommy Allah duka mutanan garin haushin su nakeji".Meenal dai har ta gama maganarta Mommynta bata tankamata ba,hakan yasa tayi shiru. Meenal har dare tak'i cin komai kuma dama da daddaran tuwan gari akayi,ita kuma dama ba son shi take ba,nan fa yunwa ta fara damunta,dan ko sallar magriba da kyar tayi ,tana cikin sallar ne d'an juma ya shigo gidan,bai shiga d'akin ba daga waje ya gaida Mahaifiyar meenal sannan ya mik'ama mahaifiyar shi hurar da ya siyo ya ce"Inna gashi adamama mu su". Hajiya Mariya cikin fad'ad'a fara'arta ta ce"Tom mun gode Allah yasaka da alkairi" D'an juma fita yayi dan yin sallah Isha'i da ake kira,saboda ya k'osa yaje gidan Sarki yaji dangartakar dake tsakanin su da su Alhaji. D'an juma masallacin k'ofar gidan su ya fara zuwa yayi sallar Isha'i sannan ya nufi gidan Sarki.Sai dai koda yaje badamar samun sanin abinda ya kawo shi dan Sarki fira suke da Alhaji sosai,bayan sun gaisa ne Alhaji wato kakan Meenal ya ce"Yauwa Abdurrahman dama yanzu zansa Malam Haruna ya kiraka,amma inda gaka kazo ai shikenan,maza kaje gidanku ka tafomin da Amina"."D'an juma tashi yayi ya fita yana mai jin dad'i zai kuma ganinta,yana tafiya zuciyar shi na ingiza shi da cewa" Ka gwada furta mata kallamar so mana ko zaka dace".Wata zuciyar ta ce"Gaskiya yaudarar kanka kawai kake,amma kaima kasan bazata amin ce ba".Can kuma sai ya ba kan shi amsa da "Darashin tayi akan bar arha,sosai d'an juma ya yadda da wanna kalma da hausawa ke cewa,hakan yasa cikin full Confidence ya idasa gidan su". Meenal ko ta gama Shan furar da d'an juma ya kawo mata har tayi shirin bacci ta kwanta d'an juma ya yi sallama ya shiga d'akin.............โœ๏ธ Idan kin karanta ki Comment sister๐Ÿ˜—๐Ÿ˜— ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. page 12 & 13. Meenal ko ta gama shan furar da d'an juma ya kawo mata har tayi Shirin bacci ta kwanta d'an juma ya yi Sallama ya shiga d'akin. Mommyn meenal zaune ita da mahaifiyar d'an juma sai fira suke,d'an juma ya shiga. D'an juma gaida hajiya Mariya yayi sannan ya ce"Dama alhaji ne ya ce in kira Meenal,kuma naga tama kwanta"."A'a ai ba bacci tayi bari in mata magana"cewar hajiya Mariya" Hajiya Mariya sunan Meenal ta Kira,dan ta san ba bacci take ba.Meenal na jin haka ta ce"Mommy wai lafiya?"."Tashi za ki yi ku je alhaji na kiranki".Meenal ba tare da tayi wani alamu da ya nuna zata tashi ba ta ce"Mommy nikam gaskiya babu inda zani". Hajiya Mariya kallan d'an juma tayi da ke sauraran su ta ce"Meenal ki tashi,idan kuma kink'i babu ruwana tsakaninki ne da alhaji,kinji dai abinda yace bazaki bar garin nan ba har sai kin sha addu'ar nan dan haka ki tashi kije ki sha tun wuri kinga dai kin kusa fara practical asibiti tom".Meenal wurgar da abinda ta rufa tayi ta ce" Wayyo wai me nayi ma alhaji ne da ya tsanan haka,mutum duk yabi ya ta kura rayuwata".Meenal ta idasa maganar tana sakkowa daga kan gadon batare da ta kuma cewa komai ba tayi hanyar waje da wani zin bulelan hijab blue black na Mommynta. D'an juma fita ya yi ya bi bayanta. Tsaye ya sameta ak'ofar gidan tana wani cin magani,d'an juma kallanta yayi ya ce"Mu je ko?". Meenal kallan sama da k'asa tayi ma d'an juma sannan ta ce"Ba dai ak'asa ba ko ?"."Beauty mashin d'in na gidan sarki ". Meenal kallan d'an juma ta kuma yayi sama da k'asa sannan ta ce"Kar in k'ara jin ka kirani da wannan sunan,dan kaga rannan ka kirani ban tanka maka ba shine yauma ka sake kirana da shi,karka sake !". Kai d'an juma ya jinjina ya ce"Tom ranki shi dad'e bazan kuma ba".Meenal tsaki tayi tana wani yatsine fuska ,ta wuce. D'an juma cikin wani irin sauk'i ya tsinci kan shi ganin yadda suka jera suna tafiya da Meenal,duk da ba magana suke ba,d'an juma so yake ya sanar da ita sak'on zuciyar shi amma kuma yana jin tsoro.Kallan Meenal yayi ta gefan ido ya ce" Hijab d'in nan yayi miki kyau".Meenal da katawa da tafiya tayi tana ma d'an juma wani irin kallo da ya kasa fassara mai kallan ke nufi. Meenal ta dad'e tana tsaye tana kallan d'an juma tama rasa abinda zatace mai dan ita gani take rainine kamarta d'an kyauye na yaba kwalliyarta.Meenal da ta rasa abinda zata cema d'an juma sai cewa tayi"Malam yi gaba muje".Wato ma'ana subar jerawa tare" D'an juma kallanta yayi ya ce"Don me tafiyar mu d'aya kuma zanyi gaba?".Meenal cikin d'aga murya kamar tana magana da wani sa'anta ko kuma k'aninta ta ce"Malam kaga ba wai so nake ina sa'insa da kai ba,kayi gaba nace bana son doguwar magana na shiga tsakanina da kai". D'an juma murmushi yayi ya ce"Saboda me?,ko kina tsoran afkawa ne?". Meenal ja tai ta tsaya tana kallan d'an juma dan gaba d'aya tama rasa abinda zatace mai,sai zuwa can ta ce cikin alamun b'acin rai"D'an asabe ka ke ko d'an me?,Ka tsarkake har shanka,kasan da wadda ka ke magana, ana cewa d'an kyauyan mutum dabba ne ban tab'a sanin haka ba sai yau,in banda tsabar dabbanci kai ni zaka cema ko ina tsoran zan abka ka ne". Sosai kalaman Meenal zuka b'atama d'an juma rai,amma sai ya danne yaci gaba da tafiya ba tare da ya k'ara cewa komai ba.Ahaka suka shiga gidan sarki d'an juma najin zuciyar shi duk babu dad'in kalaman da Meenal ta yi mai" D'an juma cikin sanyi yayi sallama da alamun 'yar damuwa a fuskar shi.Meenal zama tayi tana mai gaida sarki,alhaji ko kakanta ko kallo bai isheta ba. Alhaji murmushi yayi ya ce"Ja'irar yarinya wato ni kad'ai ne bazaki gaida ba ko?,Ohoo addu'a ce dai sai kin shata ". Meenal ba takanma alhaji ba bakin nan dai ta turo.Shi kuma alhaji ya ce"Sarki bata ta sha". Sarki tashi yayi ya d'akko addu'ar ya mik'ama Meenal,ya ce"Yauwa Amina amsa ki sha da bismillah kin ji". Meenal amsa tayi tana turo baki ta ce" Ni alhaji sai naje gida zan sha". D'an juma da ke neman hanyar rama abinda Meenal tai mai yayi carab ya ce"Alhaji ban yarda ba ko taje ba sha za tai ba,tasha agabanka ka gani". Meenal cikin d'aga murya ta ce"Waye kai!? Wa ke neman yaddarka?, kada Allah yasa ka yarda d'in,Shane kuma bazan sha anan ba d'in sai naje gida". Alhaji kai kawai ya girgiza Ya ce"Amina amsa ki sha".Meenal baki ta turo ta ce"Alhaji nifa lafiyata lau da zaka ce aban addu'a,cama nayi ban da lafiya ne?"."Amina koma ma lafiyarki lau ki amsa kisha,dan ko ubanki yazo gunnan sai kin sha addu'ar nan yau". Meenal kallan d'an k'ok'on da akai addu'ar aciki tayi,ita bawai bazata sha bane, taji ta hak'ura zata sha,tom amma kyankyamin abinda akai addu'ar take dama ita kanta addu'ar,hakan yasa bata son sha,amma gudin kar alhaji yaja su k'ara kwana ,dan ita gobe take tunanin zasu wuce.Meenal runtse ido tayi sannan ta d'aga addu'ar ta shanye. Meenal da gudu ta fita saboda aman da yazo mata,hakan yasa ta ruga da gudu waje taci gaba da kwara amai,kamar zata amaye hanjin cikinta,dan hatta furar da tasha sai da ta amayeta tass" D'an juma ko ganin Meenal ta fita da gudu tana rufe baki,yayi saurin mara mata baya,ganin yadda take aman yasa duk ya damu. Zuk'unnawa yayi kusa ita kamar zai rik'eta yana jera mata sannu. Meenal ko tsabar aman da tayi ne yasa cikinta ya murd'e,zuk'unnawa tayi awajan kamar zata kwanta awajan,tana rik'e cikinta. D'an juma cikin damuwa ya ce"Sannu tashi muje chamise abaki magani". Meenal da maganar ma ta gagareta saboda yadda cikinta ya murd'e ,banza tai da d'an juma taci gaba da murk'usanta . D'an juma ganin haka sai yaga kamar cikin wani hali take,hakan yasa cikin rud'ewa yasa hannu zai d'agota shi da niyyar shi ya taimakamata. Meenal da ta ga abinda d'an juma ke son ai katawa da sauri ta matsa tana d'aga mishi hannu ta ce"Karka kuskura ka tab'ani Malam,cema akai ban iya ta shine da zaka wani bud'e hannu kai gaka mai taimako mai tausai,Wallahi da ka yi gangancin tab'ani ,da ka yi da nasani". Alhaji da Sarki da duk suna kallan abinda ya faru,da yadda d'an juma ya nuna kulawar shi akanta na son taimakonta amma k'arshe ta b'age da mai maganganu marasa dad'i. Alhaji wato kakan Meenal cikin nuna rashin jin dad'in abinda ya faru ya kamo hannun d'an juma ya ce"Sannu ko Abdurrahman,Allah ya baka ladar niyar taimakon da kayi,rabu da ja'ira naga uban da zai taimakamata ta tashi". Meenal jin abinda alhaji ya ce yasa ta tashi tana cewa"Ko da ban iya tashi da ya tadani gara in shekara agun kwance". Sarki dai murmushi yayi ya ce" Abdurrahman jeka maidata gida,ku biya ka sai mata magani ". D'an juma dai bai ce komai ba.Ya dad'e tsaye yana kallan Meenal yana yana jiran ta tashi su tafi. Meenal sai da ta mila ta milmile sannan ta tashi,daga zuk'unnan da take,tayi hanyar waje batare da ta tankama kowa ba. D'an juma kallan Sarki yayi ya ce" Bari in rakata indawo". D'an juma bin Meenal yayi da tabi hanyar gida,alamun ta gane hanyar.Sunyi tafiya har sun kusa gida d'an juma ya kalli meenal ya ce" Mu biya chamise mana abaki magani". Meenal ko kallan d'an juma ba tayi ba taci gaba da tafiyarta,ahaka suka isa gidan.Suna zuwa Meenal ta zube kan Mommynta tana sakin kuka sosai.Mahaifiyar d'an juma cikin damuwa ta ce"Yayan su lafiya me akai mata?". "Inna ba ai mata komai ba". Meenal tashi tayi tana harara d'an juma jin abinda ya ce ba ai mata komai ba,ta ce ma Mahaifiyar d'an juma "Dan Allah kima sarkin nan magana haka kawai zai tasani da dole sai nasha wata addu'a ni ce mai akai Banda lafiya ne,ni dai dan Allah ki mai magana".Mahaifiyar d'an juma cikin lalla shi ta ce"Ki yi hak'uri kinji Amina ki daure ki sha kinji ,ba'ama tsofaffi musu".Haka mahaifiyar d'an juma tai ta ba meenal baki.Mommyn Meenal dai bata tanka musu ba. D'an juma ko tun tuni ya fice daga d'akin.Ba dad'ewa sai gashi ya dawo da kayan tea a hannun shi,Mahaifiyar shi ya mik'amawa ya ce"Inna gashi a had'a mata tea ta yi amai a gidan sarki".Hajiya Mariya kallan d'an juma ta yi,ta ce"Sannu da k'ok'ari Abdurrahman" . D'an juma murmushi yayi ya fice daga gidan" Washe gari,d'an juma yana d'akin shi da ke gidan Sarki,bayan ya kai ma su sarki abin Karin kumallo bayan sun karya ne,yaga shigar alhaji woto kakan Meenal ban d'aki.D'an juma d'akin sarki kakan shi ya shiga,zama yayi kusa da sarki ya ce"Sarki wai ya kake da alhajin nan ne?". Sarki murmushi yayi ya ce"Abdurrahman Malam Abdullahi,a nan garin mahaifin shi ya kawo shi karatun allo,tun da aka kawo sai tamu tazo d'aya muka k'ula abota mai k'arfi dan so dadama nike biyamai alllan shi saboda na wuce shi akaratu.Abdullahi ya yi nisa akaratu sosai ya tafi kaduna ganin gida,tom dama muna karatu da shi yana yawan sanar da ni ba da son mahaifiyar shi yake karatun allon nan ba,ita fati son yayi agabanta,tom tun daga zuwannan ne dai bai koma ba.Sai dai duk da haka alak'armu na nan dan duk lokacin da ya samu dama yana zuwa nan,kaji alak'armu da shi abota ce,kuma sai shi yama fi ni rik'e amanar abotar,inda ni ban tab'a zuwa wajan shi ba shike zuwa wajena.Kaji alak'ata da shi".Shiru d'an juma yayi sannan ya ce"Tom naga kana ma yarinyar nan addu'a me ke damunta?"."Irin lallurarka ke damunta,yarinya kamar wannan ace bata son aure ,batama son ai mata maganar auran,kamar kai agari".Cewar Sarki. Dan juma murmushi yayi ya ce" Sarki ni kam daga yau kafara lissafi dan na samu matar aure".Allah sarki sarki da babu abinda yake son gani kamar auran d'an juma cikin tsantsar farin ciki ya ce"Alhamdulilah,Allah ya amshi rok'on mu,Abdurrahman ina yarinyar take?" D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Ni ka d'ai ke sonta sarki ita bata sona,ni kuma ita kad'ai na tab'ajin sonta araina,har nakanji idan tak'ini bazan yi aure b..." .Sarki da sauri ya rufe bakin d'an juma ya ce"Haba Abdurrahman wannan wata irin magana ce,in dai ba sokake kasani adamuwa ba,karka sake furta kallmar baza kai aure ba dan Allah,yarinyar kuma insha Alllah zata soka,ko ko ita tace bata sonka da bakinta?". Kai d'an juma ya girgiza ya ce"Ina fargabar sanar da ita ina sonta,dan bana tunanin zata amince min"."Shurman banza kenan,waya fad'ama namiji na karaya wajan furta so,ai wanna mace aka sani ba namiji ba,ka cire fargabar komai ka tun kareta kai tsaye, insha Allah zata soka,ka cire fargaba ,da rashin tayi akan bar arha" . D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Ka yi min addu'a ta soni Allah idan tak'ini haka zan ci gaba da zamana bazanyi aure b...".Sarki da sauri ya k'ara rufe bakin d'an juma ya ce"Abdurrahman kabar furta kallamar nan, dan wata tak'ika sai ka ce baza kai aure ba,idan fa Allah bai tsara aure tsakanin ku da ita ba fa?,shikenan ba za kai aure ba,dan Allah kabar furtawa ,ganin auranka shine burina .Ayanzu haka babu abinda nake fatan Allah ya k'aramin tsawan rai in gani kamar matarka, Abdurrahman dan Allah kabar furta kallamar nan mai fad'ar min daga ba". D'an juma ganin yadda sarki ya shiga damuwa,yasa ya kamo hannun shi yana murmushi ya ce"Kwantar da hankalinka bazaka mutu ba sai ka ga d'ana insha Allah,daga yau sai ka fara k'irga ranar aure na nan da watani kad'an musu zuwa".Sarki cikin jin dad'i ya ce"Allah yasa Abdurrahman ,dan baka tab'amin maganar aure ba sai yau,ko ba komai insha Allah nasan ko mai ya kusa zama tarihi". D'an juma har ya fita alhaji bai shigo ba yana ban d'aki ". B'angaran Meenal kuma ta hura ma mommynta wuta ita fa bazata kuma kwana garin nan ba daga gobe ba. Meenal sai nai man wayar da zata Kira daddynta take babu,gashi wayar mommynta tunda ta bugata da k'asa ta d'auke,wayarta kuma M.T.N gareta batayi hausar cire Sim d'in mommynta ba tasa awayarta ba.Mommyn Meenal kuma ta hana mahaifiyar d'an juma taba Meenal wayarta ta ce ta ce mata bata da caji.Sosai Meenal ta shiga damuwa dan so take tai waya da daddynta ruwa ajallo.Tana nan tana tunanin ya za tai d'an juma yayi sallama ya shigo" D'an juma da ledar kayan tea d'in Meenal hannun shi,ya mik'ama mahaifiyar shi,sannan ya gaida su,ya kalli Meenal ya ce"Sarki na kiranki".Meenal har zatace bazata ba,amma da ta tuno d'an juma na da waya zata ara ta kira daddynta batare da mommynta bama taji abinda zatace ba,hakan yasa ta tashi ta yafa d'an kwalin abayarta ta fita,d'an juma yabi bayanta shima. Suna fita daga gidan Meenal ta kalli d'an juma ta ce"D'an aramin wayarka". "Ayyah nabadata caji amma idan na amso zan baki idan kuma kin matsu da yin kira idan mukaje sai ki amshi ta sarki kiyi amfani da ita". Meenal shiru tayi sannan ta ce"Badamuwa idan ka amso nayi kiran".Meenal na fad'in haka ta juya zata tafi.D'an juma yayi saurin cewa "Sarki na kiranki fa nace"."Bazan je ba".Meenal na fad'in haka ta juya tayi ta fiyarta.D'an juma d'aga murya yayi ya ce"Bari inzo in cema Mommy kince bazaki ba". Meenal da dowa tayi taja ta tsaya gaban d'an juma tana kallan shi,shima ita yake kallo.Meenal tsaki ta yi ta ce"Uhm dan Allah ka d'an taimakeni magana,Wallahi bazan iya shaba,kuma alhaji ya sa daddyana indai ban sha ba sai dai in ci gaba da zama kyauyan nan,ni koma gaskiya bazan iya shaba,dan Allah ka san abinda zaka ce mai ya baka ka kawomin".Shiru d'an juma yayi sannan ya ce"Tom Mommynki fa ai zataga biki shaba".Meenal ta ce"Ai idan ka amso zuwa zan rik'ayi da sunan zanje amsowa idan nagama zamana in koma".Murmushi d'an juma yayi ya ce"Shikenan sai anjima,bari inje in amso". Meenal juyawa tayi ta shige gida tana jan tsakin takurata d'in da duk akayi". D'an juma gidan Sarki ya koma yace ya bashi ya kai ma Meenal ,yaje ya isketa batajin dad'i.Sarki ba d'an juma yayi ya ce ya tabbatar ta sha.D'an juma na fitowa ya kurb'e addu'ar acewar shi ayar Allah ce,inda yasan ko ya kaima Meenal ba sha za taiba,zubarwa za tai" Yau d'an juma da wuri ya dawo daga funtua,yayi wankan shi cikin wani brown d'in yadi,masha Allah sosai d'an juma yayi kyau ya shafe kayan shi da aribian oud. D'an juma ya fito zai tafi gidansu,suka ci karo da sarki ya fito ban d'aki. Sarki murmushi yayi dan indai kaga sauri ya d'au wanka da daddare tom ba sai ya fad'aba kasan inda za shi.Sarki da fara'ar shi najin dad'in d'an juma ya fara nai man aure ya ce" Abdurrahman daga ganin kwalliyar nan nasan gimbiyarka zaka gani".Murmushi d'an juma yayi yana mai jin wata irin fargaba ya ce"Sarki yau ne zan fad'ama yarinyar da nace maka ina so,tom ina fargaba ka tayani addu'a Allah yasa ta amince".Sarki hannun d'an'juma ya kamo ya ce"Bacin kayi addu'ar fita gida,ka karanta izaja'a,insha Allah zaka samu nasara".D'an juma cikin jin dad'i ya ce"Nagode ,bari in tafi" . Sarki Kiran shi yayi ya ce"Bari in d'akkoma addu'ar Amina idan ka dawo wajan gimbiyartaka ka biya ka kai mata". Sarki d'akin shi ya shiga ya d'akko addu'ar yaba d'an juma. D'an juma amsa yayi ya tafi ,azuciyar shi yana cewa"Sarki wadda zan ba addu'ar nan ita ce gimbiyar tau,amma kai kanka fargabar sanar maka nake yi". Haka d'an juma ya kama hanyar gidan su ,zuciyar shi na cike da fargaba" B'angaran Meenal kuwa ta k'osa d'an juma ya shigo ya bata wayar shi ta Kira daddynta,dan jin shirun yayi yawa,yasa ta ce ma mahaifiyar d'an juma "Wai yau ba zai zo bane?".Mahaifiyar d'an juma da bata gane abinda take nufi ba,ta ce"Waye ba zai zo ba?" ."Wanda ke ....".Sallamar d'an juma ce tasa Meenal ta yi shiru............โœ๏ธ Idan kin karanta ki daure ki Comment Sister. Share & Comment please๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 17 & 18. Daddyn Meenal tashi yayi yazo inda Mahaifinshi yake ya rik'e k'afar alhaji ya ce" Alhaji dan Allah ka canza wani abun ba wannan ba,na yi ma Meenal alk'awarin ba zan mata auran dole ba,dan Allah ka barni in cika alk'awarin da na d'aukar mata". "Kwantar da hankalinka Sani,babu wanda zai ma Amina auran dole".Cewar Sarki.Alhaji kallan sarki yayi ya ce"Alk'awarin da na d'aukarma Abdurrahman fa?,Sannan Amina bawai Abdurrahman bane bata so kuwa ma baso take ba". Shiru sarki yayi sannan ya ce"Duk da haka alhaji baza ai ma Amina auran dole ba". alhaji da ran shi sosai ya b'ace ganin yadda Sani ya fito k'iri-k'iri ya nuna baya son d'an'juma,hakan yasa alhaji cikin tsantsar b'acin rai irin Wanda daddyn meenal bai tab'a gani ba ya ce"Sani tashi ka tattara kaida iyalinka kubar garin nan yanzu-yanzun nan!". Daddyn meenal ganin yadda ran mahaifinshi ya b'ace sai kuma hankalinshi ya tashi ,kallan maihaifinsa yayi ya ce"Alhaji dan Allah kayi hak'uri".Alhaji cikin d'aga murya ya ce"Sani ka d'auki iyalanka nace ku koma Kaduna ka cikama 'yarka alk'awarin da kai mata ". Daddyn Meenal cikin sanyi ya ce"Alhaji kai fa?".Bazan tafi da kai ba,gobe Sule yazo ya d'aukeni ". Daddyn meenal shiru yayi,k'arshe ya gama zamanshi ya tashi ya tafi cikin sanyin jiki". Alhaji Abba ko da ya fita rasa inda zaiyi ya yi , dan baisan gidan da su meenal sukeba.Tunanin number da meenal ta kirashi ta fad'omai,hakan yasa ya ciro wayar shi ya Kira number d'an'juma. D'an'juma ko dama yayi serving number daddyn meenal,hakan yasa daddyn Meenal nakiranshi ya gane mai Kiran ya d'aga yana mai yin sallama. Alhaji Abba amsawa yayi sannan ya ce"Meenal ce ta kirani da number nan,dan Allah ko tana kusa"."A'a bata kusa, ina Funtua ne ,sai dai in nadawo".Cewar d'an'juma" Shiru alhaji Abba yayi sannan ya ce"Ina son inje wajan su ne,babu yadda za ai?".D'an'juma cikin girmamawa kamar daddyn meenal na kusa da shi ya ce"Kana ina ne sai in turo yaro ya tafi da kai?"."Ina k'ofar gidan sarki"."Tom bari in turo yaro sai ya k'arasa da kai gidan". D'an'juma na fad'in haka ya kashe wayar ya kira yaran shi sule mai tsaran shagon shi ". Daddyn Meenal na jikin motar shi tsaye cikin damuwa sosai,sai ga Sule da d'an'juma ya turo.Sule gaida daddyn meenal yayi sannan yayi mai bayanin shine Wanda d'an'juma ya turo yaraka shi gidan su. Alhaji Abba motar shi ya bud'ema sule ya shiga suka tafi. B'angaran Meenal ko tana zaune tana shafa mai ,Sule ya shiga gidan .Bayan ya gaida su ne ya ce"Daddyn Meenal ya ce su Meenal su fito su tafi" . Meenal cikin jin dad'i ta ce"Wayyyo sweet daddy ya iso".Mommyn meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Jiki gani meenal".Aiko meenal da sauri ta zira doguwar rigarta ta yafa ma yafinta ta fita da murnarta" Meenal da gudu ta fad'akan jikin daddynta tana cewa"Oyoyoyo sweet daddy naji dad'in zuwanka Wallahi dama duk atakure nake". Alhaji Abba bai tankama Meenal ba dan cikin damuwa yake sai dai kanta da yashafa ya ce"Kira mommynki mu tafi".Meenal jin amsar da daddynta ya bata yasa ta d'ago tana kallan shi ta ce"Sweet daddy naganka so silent".Murnushi alhaji Abba ya kuma yi ya ce"Kira mommynki mu tafi yamma tayi". Meenal kallan daddynta tayi ta juya ta tafi, tana mamakin yadda taga daddyn nata.Meenal na zuwa ta ce"Mommy ki tashi tafiya zamuyi ".Hajiya mariya da babu abinda za tai jakar ta ta d'auka ta rataya ta kalli Mahaifiyar d'an'juma da itama ita take kallo ta ce"Tom Auntyna zamu tafi sai watarana in mun dawo ko kuma ku in kunzo". Meenal kallan Mommynta ta yi ta ce"Mommy har kina fatar ki k'arazuwa kyauyan nan,tom sai dai kinzo amma ni kam bani ba"."Suma basa gyayyatarki".Cewar mommyn meenal. Mahaifiyar d'an'juma dai murmushi ta yi ta ce"Tom hajiya Allah ya k'addara saduwar mu". Mommyn Meenal tun yadda ta hangi daddyn meenal atsaye yayi shiru ta san da akwai matsala.Mommyn meenal cikin fad'ad'a fara'arta ta k'arasa wajan daddyn Meenal ta ce"Barka da zuwa daddyn meenal".Alhaji Abba cikin kasa danne yadda yakeji ya ce cikin sanyi"Yauwa mommyn meenal,na sameku lafiya?". Daddyn meenal ya fad'i maganar yana mai bud'e musu motar su shiga. Bayan sun shiga ne daddyn meenal har yaja k'ofar ya tafi ,hajiya Mariya ta kallai ta ce"Daddyn Meenal alhaji fa?". Shiru daddyn meenal ya yi. Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba ta yi da kyau ,tabbas dagani mai gidannata yanada damuwa,hajiya mariya cikin sanyi ta ce "Daddyn Meenal alhaji fa ?"."Wai ba zai tafi damuba ". Hajiya mariya cikin mamaki ta ce "Daddyn meenal lafiya,ko munyi mai laifi ne?".Shiru alhaji Abba yayi dan bai san mai zai ce ma hajiya Mariya ba. Haka su Alhaji Abba sukaci gaba da tafiya shiru kakeji,dan Meenal ma tayi ma daddynta magana ,ganin daddyn nata kamar yana cikin damuwa yasa Meenal ma taja bakinta tayi shiru. Daddyn meenal basu suka shiga gida ba sai k'arfe tara na dare(9:00PM).Suna shiga Meenal ta baje afalo.Alhaj Abba ko ciki ya shiga yayi alwallah ya tada salloli biyu da aka biyosu, magriba da isha'i. B'angaran hajiya Mariya ma haka,itama ciki ta shiga ta gabatar da sallolinta,tana idarwa ta shiga kitchen tayi musu jolop d'in taliya.Hajiya Mariya da ta fito kwance ta iske Meenal kan caution tana bacci .Hajiya Mariya bubbugata ta farayi da k'arfi tana cewa"Meenal bacci kika fara bacin kinsan biki sallah ba,babu irin tashin da hajiya mariya ba taima Meenal ba amma tak'i tashi dole ta k'aleta.Bedrom d'in daddyn Meenal hajiya Mariya ta nufa kwance ta iske shi kanshi asama daga gani dai yayi nisa sosai a tunani,hajiya Mariya zama tayi gefan kadon ,sannan cikin alamun damuwa ta ce "Daddyn Meenal dan allah mai ke damunka,tun da kaje d'akko mu na lura kanada damuwa amma kayi shiru,ita fa damuwa idan mutum ya furtata yana samun sauk'i daga yadda yakeji". Daddyn Meenal tashi yayi ya zauna yana kallan mommyn meenal,ya ce"Wa ye Abdurrahman a kyauyan da ku kaje?".Hakanan hajiya Mariya sai taji gabanta ya fad'i batare da tayi tunanin komai ba,ta ce"D'an'juma kenan,jikan sarki,gaskiya yaron nada hankali sosai da natsuwa".Hajiya Mariya ta idasa maganar tana kallan daddyn Meenal. Numfasawa alhaji Abba yayi ya ce"Yaron ya nuna yana son Meenal ne?" Gaban Mommyn meenal fad'uwa yayi jin abinda daddyn meenal ya ce,kallan shi ta yi ta ce"Eh tom,gaskiya ni banga wata alama ba,amma Meenal yau kwana biyu kenan ta shigo tana kuka wai yaron da kake magana ya ce yana sonta,dan ta dad'e tana kuka,nan ma dai mahaifiyar yaron ita taita lalla shinta".Shiru mommyn meenal tayi sannan ta ce "Wani abu ya faru daddyn meenal?" .Alhaji Abba shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce "Jiya alhaji ya kirani akan inzo yau ,tom shine bacin naje yake sanar dani wai yayima yaron alk'awarin auran Meenal".Alhaji Abba ya idasa maganar cikin damuwa sosai. Hajiya Mariya ko ai rud'ewa tayi ta ce"Daddyn Meenal alhaji ya bada auran meenal kace fa?,A kyauyan nan ya bada auran nata?".Kai daddyn meenal ya jinjina ya ce "Haka alhaji ya ce min,da nanuna banyadda ba shine ya nuna min b'acin ranshi sosai,har ya nuna bazai biyomu ba ,tom Wallahi tunda alhaji ya furta maganar nan narasa natsuwata,nama rasa yadda zan b'ulloma al'amarin". Wai Allah,hankalin hajiya Mariya ai sosai ya tashi,dan yafi na alhaji Abba tashi ma. Cikin Sanyi hajiya Mariya ta ce "Kabari zamuyi maganar da alhaji nasan insha Allah zai fahimceni"Tom Allah yasa".Cewar alhaji Abba". "Tom ka tashi muje kaci abinci".Alhaji Abba da ya d'anji sauki daga yadda yakeji tashi yayi yabi hajiya Mariya .Kwance ya iske meenal tana bacci,zuwa yayi dan ya tadata taci abinci tak'i tashi ,dama yasan haka dan Meenal akwai wuyar tashi idan tayi bacci.Alhaji Abba bayan ya gama cin taliyar ziboma meenal yayi a plate ,da kyar ya samu ta tashi,ka d'an taci ta tafi zata kwanta hajiya Mariya ta kalla mata harara ta ce "Sallah fa?".Meenal turo baki tayi ta ce "Ai tunda kikaga banyi ba sai ki rubu dani ko ,kinsan bayi zanyi ba".Meenal na fad'in haka ta d'agama daddynta hannu ta ce"Sweet daddy good night"."Good night too meenalyn daddy ". B'angaran alhaji ko bayan daddyn meenal ya tafi sarki hannu alhaji ya kamo ya ce "Alhaji mubi komai ahankali dan Allah,idan Allah yasa Amina rabon Abdurrahman ce tom babu abinda zaihana ya aureta inda wani bai auran matar wani".Hakane malam Haruna,nima bawai zantsauwala abin bane,dama ina tuna alk'awarin da naima yaron nan ne,sannan kai abinda baka fahimta ba Sani baya son Amina tai aure yafi son yayita ganinta agabanshi.Wallahi malam Haruna idan ba wani ikon Allah ba Sani bazai bar Amina tai aure ba,inda itama bason auran take ba,ita kuma 'uwar ba isa tayi ba,lokacin da ita kuma zataso auran in ba sa'aba babu samarin kuma".Cewar Alhaji . Shiru sarki yayi,dan shi harga Allah cikin zuciyar shi bama son d'an'juma da yarinyar yake ba. B'angaran d'an'juma ko bai San da tafiyar su Meenal ba.Dan koda yaje gidan bai gansuba kasa tambayar mahaifiyar shi yayi bakamar yadda yaga tana ta d'aure mai fuska ba ,hakan yasa ya koma gidan Sarki,nanma ba damar tambaya yanajin kunyar kakan meenal hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru. D'an'juma da daddare yana kwance ad'akin shi kan shi sama yana ta tunanin sahibar shi Meenal, ahaka bacci ya kwasheshi. Washe gari d'anj'uma yaje kaima tsofaffin abin Kari ya iske alhaji wato kakan Meenal ya zagaya bayi,d'an'juma cikin jin dad'in rashin ganin alhaji ya kalli sarki ya ce "Sarki ina bak'in mu ne?".Aiko kamar d'an'juma ya tunama sarki ya ce "Yauwa Abdurrahman dan Allah abinda nake so da mai kasamu alhaji kace mai kajanye maganar son yarinyar nan da kace,saboda kaga yanzu haka alhaji ya d'au fushi da mahaifin yarinyar nan ,dan Allah Abdurrahman ka naimi mata akyauyan nan kayi auranka". Shiru d'an'juma yayi sannan ya ce"Sarki kamar yadda na fad'ama ban tab'a jin ina sha'awar inyi aure ba Wallahi sai akan yarinyar nan,sannan ni kaina nayi yak'i da zuciyata ganin na cire sonta araina tun kafin kaikankama in furtama amma abin yak'i yuwuwa,dan Allah Sarki katayni addu'a kawai". "Abdurahman ka kwantar da hankalinka insha Allah zaka auri Amina kamar yadda nace maka da farko,kai dai kawai abinda nake so da kai kayi addu'a".Cewar alhaji da shigowar shi kenan d'akin ya riski maganar. D'an'juma cikin jin sanyi ya ce"Nagode sosai da karramawarka gareni alhaji"."Babu komai Abdurrahman ".Cewar alhaji . Sarki dai bai ce komai ba.Bayan sungama shan tea d'in da d'an'juma ya kawomusu babu dad'ewa ishuhu yazo d'aukar alhaji.Sosai sarki yaji babu dad'i .Haka dai su kai sallama alhaji ya tafi" Da yamma daddyn meenal ya je gaida mahaifin shi yayi mai sannu da zuwa,amma haka daddyn meenal ya gama zaman shi alhaji bai tankamai ba,k'arshe ya gaji ya tashi ya tafi,haka yaje gida duk ba dad'i. BAYAN SATI D'AYA:Haka kullum daddyn meenal idan yaje gaida mahaifin shi sai dai ya gama zaman shi ya tashi amma ko gaisuwar shi baya amsawa.Dan yau da yajema Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce " Sani nikam daga yau na yafema wannan gaisuwar da kake zuwa yimin,daga yau ba sai kazo ba kayi zamanka a inda kake nagode". Daddyn meenal kallan mahaifinshi yayi zaiyi magana ,alhaji ya d'aga mai hannu ya ce "Sani dan Allah bana son doguwar magana sai anjima". Alhaji Abba tashi ya yi ya tafi .Yana zuwa yayi part d'in shi yana mai dafe kan shi.Hajiya Mariya ganin yadda Alhaji Abba ya shigo ne yasa tabi shi da sauri,sai dai yadda ta ganshi rik'e dakaine yasa ta rud'e ta ce "Daddyn Meenal lafiya?".Alhaji Abba ba magana ,k'arshema kawai sai ya fashe da kuka".Hajiya Mariya cikin tashin hankali ta fita ta kira Meenal.Meenal da ita kanta yanzu kusan cikin damuwa take ganin yadda take ganin daddynta dan ya daina fira da ita sosai,magana ma yabar yin mai tsawo.Meenal cikin kuka take girgiza daddynta tana cewa"Daddy Lafiya wayasa kuka daddy,dan Allah kayi shiru".Daddyn meenal ko rik'o hannun Meenal yayi ya ce "Meenal gara in mutu da inga wannan rana,Meenaln daddy zuciyata bazata iya zurewa ba in ganki cikin damuwa,bazan iya jurewa ba Gara Allah ya d'auki rayuwata zaifi min dad'...."."Haba daddyn Meenal akan abin nan ne har zaka rik'a kirarin mutuwa?". Meenal ko fad'awa tayi kan daddynta tana cewa "Wayyo daddyna bazaka futu kabarni ba,dan Allah kar ka mutu daddy,Mommy dan Allah kice ma daddy karya mutu"."Tom ki yi shiru ga docter nan na Kira zai zo yanzu ya duba shi". Su mommyn Meenal sunanan zaune sun tasa daddy Meenal da ke ta faman juye-juye saboda yadda kanshi ke mai . Su hajiya Mariya na nan zaune abokin alhaji Abba ya shigo,yana zuwa ya yima alhaji Abba aune-aunan da yakamata yayi mai,ya kalli hajiya Mariya ya ce "Hajiya gaskiya jinin Alhaji Abba ya hau,amma babu damuwa da akwai magani da zan kawo mai yanzu,kuma gaskiya ayi k'ok'arin ganin yabar shiga damuwa,Dan shi yayi sanadin halinda yakeciki yanzu haka". Hajiya Mariya dai godiya taimai.Shi kuma fita yayi samoma alhaji Abba magungunan da suka kamata. Hajiya Mariya ko kama hannun Meenal da keta kuka tayi suka koma Falo suka zauna.Hajiya Mariya kallan Meenal tayi ta ce "Meenal daddynki na cikin wata damuwa wadda ita ce tayi sanadiyar da jininshi ya hau.Alhaji yau kusan kwana goma kenan baya amsa gaisuwar daddynki Meenal,k'arshema yau yace mai baya son ya k'ara zuwa inda yake,Wanda inada tabbacin shine yayi sanadiyar da jinin daddynki ya hau.Meenal daddynki na sonki da yawa baya son kwatakwata yaganki cikin damuwa ko matsala,duk wannan yana daga cikin abinda yasa jinin shi ya hawa". Shiru mommyn meenal tayi tana kallan Meenal kamar mai nazartarta,sannan taci gaba da cewa "Meenal ko kinsan babu abinda ke saurin kisa kamar irin damuwar da daddynki yake ciki yanzu?,ina tsoran karmu rasa shi ,ya zamu idan ya mut...". Kukan da Meenal ta fasa ne yasa mommyn meenal yin shiru.Hajiya Mariya ganin yadda meenal ta rud'e jin daddynta zai mutu,rungume Meenal tayi tana lallashinta ta ce"Ki yi shiru,insha Allah daddynki zai samu sauk'i,amma sauk'in nada gareki ne Meenal,duk da nima ban amince ba amma sai naga da murasa daddynki gara inyi hak'uri..". Meenal katse momynta tayi da cewa "Mommy ki min bayani mekesa sweet daddy adamuwa?". Hajiya Mariya kallan Meenal tayi yadda duk ta rud'e ta k'osa taji aninda zatace.Hajiya Mariya ta ce"Meenal alhaji ne wai dole sai kinyi aure ,tom kinsan daddynki nason abinda kikeso,shine yak'i yadda dan yasan baki son aure,tom shine alhaji yake fushi dashi,tom kinsan hukuncin Wanda iyayanshi ke fushi da shi, idan ya mutu wuta zashi,shi yasa daddynki duk ya tada hankalin shi har jininshi ya hau,kuma kinajin likita yace ayi k'ok'ari abarbari yana shiga damuwa.Meenal dan Allah kije ki samu daddynki kice mai kin yadda zaki auri wanda alhaji ke so dan hankalinshi ya kwanta". Meenal da gudu tana mai k'ara tsananta kukanta ta ruga bedroom d'in daddynta,tana zuwa ta fara buga daddynta tana janye mai hannun shi dake rik'e da kanshi, ta ce "Daddy ka tashi karka mutu na yadda alhaji yayi min auran ..............โœ๏ธ Meenalyn daddy group, Comment d'inku yayi k'aranci.Amma......๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค. ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 19 & 20. Meenal da gudu tana mai k'ara tsananta kukanta ta ruga bedroom d'in daddynta ,tana zuwa ta fara bubbuga daddynta tana janye mai hannu shi dake rik'e da kanshi ta ce,"Daddy dan Allah katashi karka mutu ,na yadda alhaji ya yi min auran..."Meenal ta idasa maganar tana kuka. Daddyn meenal jin abinda Meenal ta ce,lallab'awa yayi ya tashi yana kamo hannun Meenal d'in yana bubbuga baayanta,alamun lallashi tayi shiru daga kukan da take,sannan cikin dauriya dan sosai kanshi kemai ciwo,ya ce,"Yi shiru Meenalyna,ya isa haka kibar kukan".Meenal cikin kuka ta ce,"Tom daddy dan Allah karka mutu,Allah inka mutu nima mutuwa zanyi". Alhaji Abba lallan shi meenal yayi ya ce,"Ki yi shiru tom ai bazan mutu ba sai kwanana sun k'are". Hajiya Mariya da shigowarta kenan,zuwa tayi ta janye meenal ta ce,"Meenalyn daddy mai nake gani haka,tom ai sai kik'aramai wani ciwan".Meenal jin haka da sauri ta goge hawayanta,tana cewa"Sweet daddy sannu".Alhaji Abba kai ya jinjina ma Meenal ,dan bayason magana,kanshi saramai yake sosai. Hajiya Mariya lallab'a Meenal ta yi ta janyeta suka fita,dan alhaji Abba ya samu ko zaiyi bacci,dan doctor ya had'a mai da maganin bacci. Allah yasa suna fita ko bacci ya d'auke alhaji Abba. Hajiya Mariya shiryawa tayi ta ta tafi gidan kakan Meenal. Bayan hajiya Mariya sun gaisa da alhaji ne ta ce"Alhaji tun safe da daddyn meenal yazo gaidaka da kyar ya koma gida yanzu haka bashi da lafiya,likita yazo ya duba shi yace jinin shi ne ya hau,alhaji dan Allah ka yi hak'uri ki rik'a amsa gaisuwar daddyn meenal,Wallahi cikin damuwa yake sosai,shine ma abinda yayi sanadin ciwan shi".Shiru alhaji yayi,sannan zuwa can ya ce,"Mariya nazaci ba Sani ba na isa da abinda Sani ya haifa,ashe bahaka bane,ni Sani zai kunyata saboda karya b'ata ma 'yar shi rai,a abinda Nina san alheri ne da Amina,soboda Wallahi yadda kuka lallata Amina ba kowana yaro zai iya zama da ita ba,amma Yaran nan ina tabbacin zaiyi hak'uri da duk shurman Amina,amma Sani agaban kakan yaran nan ya nuna shi ba zaiba wannan yaran Amina ba, harda wata k'aryar banza da wofi,wai yayi ma Amina alk'awarin ba zai mata auran dole ba".Shiru alhaji yayi kamar mai tunani sannan ya ci gaba da cewa,"Wallahi Mariya indai ni ban isa da Sani ba,tom banga amfanin gaiduwar da yakemin ba,shi yasa nace bana so,sannan shi yaron fa ba a kyauyan zai ajeta ba,shi kan shi kuna gani ba'anan yake har kokinshi ba.Mariya matuk'ar Sani ba zai aminta da maganata ba ke kanki ina dab da daina amsa gaisuwarki "Hajiya Mariya numfasawa ta yi ta ce,"Alhaji yanzu haka nazo nai in sanar da kai Meenal ta amince da auran".Hajiya Mariya ta fad'i maganar kamar zatasa kuka,dan tabbas tafi daddyn Meenal tsanar auran nan dan dai bata da yadda za tai ne ,sannan bata san daddyn meenal ya sab'a da Mahaifinsa. Alhaji jin abinda mommyn meenal ta ce wani k'ayataccan murmushi yayi ya ce,"Nagode Mariya da wannan kunyar da kika fitar dani,duk hankalina ya tashi ina tunanin yadda zanyi da alk'awarin da na d'aukar ma yaran nan,nagode yadda kika fiddani kunyar nan kema Allah ya fidda ke kunyar duniya da lahira"Mommyn meenal cikin sanyi ta ce,"Ameen alhaji"Yanzu kije gida ,anjima zansa Issuhu ya kawoni inga jikin nashi,gobe kuma insha Allah zani garin su yaran nan in mai albishir shima".Hajiya Mariya dai jikinta duk a mace yake ,haka ta tashi tayi ma alhaji Sallama ta tafi". Alhaji ko kamar yadda yace issu na zuwa yasa ya kawo shi gidan su Meenal.Suna zuwa Meenal kad'ai suka gani zaune a Falo da waya hannunta,alhaji kallan Meenal yayi ganin yadda ta d'auke kai kamar bata san shi ba,ya ce,"Ja'ira idan biki gaidani ba,Uwarki da Ubanki za su gaidani su".Meenal dai ko kallan alhaji ba taiba taci gaba da abinda takeyi,da akwai wata sanda hannun alhaji da yake dogarawa da ita,ita ya d'auka ya kwala ma Meenal,ya ce,"Ja'ira wato ina magana kinyi banza dani"Meenal tashi tayi tana hararar alhaji ta ce"Wai kai dan Allah alhaji mai na tare maka ne da kake naiman takurama rayuwata"."Uwaki da Ubanki kika taremin kinji ko?"Cewar alhaji. Hajiya Mariya da tajiyo muryar alhaji da sauri ta fito dan tasan yadda meenal take cike da haushin alhaji tsab za tai mai rashin kunya.Hajiya Mariya na zuwa da fara'arta ta ce," Barka da zuwa alhaji,rabu da Meenal karta sama Cowan's kai". Yajiya Mariya jagora tai ma alhaji izuwa bedroom d'in alhaji Abba. Alhaji Abba na kwance har yanzu,alhamdulilah ya samu sauk'i bakamar d'azu ba.Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce,"Sannin ko Sani,ya jikinnaka?"Alhamdulilah naji sauk'i"Cewar daddyn meenal. Nan dai alhaji ya gama zaman shi ya tashi ya tafi" Washe gari alhaji suka yi sammakon tafiya layin kad'anya garinsu d'an'juma.Kasan cewar sun tafi da wuri hakan yasa sukayi isar wuri sosai.Sarki sosai yayi mamakin ganin alhaji dan alisafinsu bazasuwuce wata d'aya da tafiya ba.Sarki cikin fara'a ya tari alhaji. Alhaji bayan ya huta sosai ya sha ruwa ya kalli Sarki ya ce," Sarki wannan tafiyar ta Abdurrahman ce ,gashi naga kamar baya kusa"."Eh aikam yau yayi sammakon shiga Funtua saro kayan shago,yanzu ba dad'ewa zakagan shi".Cewar Sarki. Nan fa alhaji da Sarki suka cigaba da fira,suna cikin firane d'an'juma ya yi sallama ya shigo.D'an'juma da fara'ar shi ya k'arasa cikin d'akin yana mai cewa"Barka da zuwa alhaji,kai ne da sammako haka,sai kace ba daga Kaduna kake ba".Murmushi alhaji yayi ya ce,"Ni ne Abdurrahman,wannan tafiyar takace baki d'ayanta"D'an'juma jin haka k'ara gyara zama yayi sosai,alamun inajinka. Alhaji kallan d'an'juma yayi ya ce,"Abdurrahman fad'amin yau shene kake ganin kanada damar aure?".Shiru d'an'juma yayi,dan ya zaci maganar meenal alhaji zai mai.Cikin sanyi d'an'juma ya ce," Eh,idan nasamu wadda nake so zan fidda lokacin".Murmushi alhaji yayi ya ce"Abdurrahman na amso maka auran Amina shi yasa nace wannan tafiyar takace,dan haka yanzu ina son atsaida komai in tafi ma iyayanta da albishir,yanzu dai ka turomin mahaifinka muyi magana da shi shima". D'an'juma sumar zaune yayi dan ya kasa cewa komai ma,yarasa wane hali yake ciki,dan take sai yaji fargaba ta rufe shi.D'an'juma matsowa yayi ya kama hannun alhaji ya ce"Alhaji nagode da k'ok'ari ,Allah ya sakamaka da mafificin alkairi"."Babu komai Abdurrahman maza kai min magana da mahaifinka,dan gobe zan yi saammakon tafiya".D'an'juma tashi yayi ya tafi,cikin sanyi dan sosai kuma yakejin fargaba,wata zuciyar take cewa,"Anya kuwa bakayi kasada ba?" D'an'juma ya dad'e a tsaye yana tunanin yadda zai sanar da mahaifin shi,sannan ya ce kai gaskiya bazan iya ba,gara idan yazo yaji.D'an'juma wayar shi ya ciro ya Kira mahaifinshi ya sanar da shi Sarki na son ganin shi.Mahaifin d'an'juma sosai yayi mamaki dan babu dad'ewa yaje sun gaisa,amma kuma sai ya kauda mamkin shi ya ce"D'an'juma yanzu yake son ganina d'in"."Eh yanzu ya ce". Mahaifin d'an'juma da yana can gona yana aiki,aje aikin yayi ya hawo keken shi ya kamo hanyar gida. Can wajan su Sarki ko,bayan d'an'juma ya fita Sarki ya kalli alhaji ya ce"Alhaji auran nan fa da kake son had'awa gaskiya za ashiga hak'in Amina,ni sai inga yanada kyau dan aji dad'in abinnan sosai ace da amincewar Amina za'ayi" Alhaji dan yayi maganin Sarki sai cewa ya yi "Malam Haruna indai ba wai kafi son Abdurrahman ya auri 'yar nan bane,dan Allah ka sama abin nan albarka kawai,Amina kuma muna fatan tabamu mamaki".Sarki jin haka sai yayi shiru ya ce"Tom inda kayima maganata wata fassarar nayi shiru alhaji,Allah yasa duk muce gara da akayi" "Yauwa tom haka zaka ce". Su alhaji su na nan suna tattaunawa akan maganar ,Mahaifin d'an'juma yayi sallama ya shigo.Mahaifin d'an'juma da fara'arshi suka gaisa da alhaji .Nan dai yayi musu anzo lafiya,sannan ya kalli Sarki ya ce"D'an'juma ya jirani inakan aiki da yake yau naje sharar gona yace kana kirana?".Alhaji ne ya amshe zan can da cewa"Eh ,ni nace ya kiramin kai.Wato zuwan yarinyar ta wajan Sani wato Amina Abdurrahman ya nuna yana sonta,ni kuma nayi mai alk'awarin samo mai auran Amina,tom atak'aice dai yanzu haka na samoma Abdurrahman auran Amina,shine nazo yanzu mu tsaida lokacin biki". Mahaifin d'an'juma rasa abin da zaice yayi, dan sai yaji maganar wata iri,da kyar dai ya samu ya bud'e baki ya ce"Tom amma alhaji ina d'an'juma ina Yarinyar nan,ai tafi k'arfin shi,sai dai kankanba irin ta yaran yanzu,amma ni gani nake ai ba biyema d'an'juma za'ai ba,taya yarinyar da ta tashi cikin kankara yace zai zo ya aje ta a nan ai abinnan ma ba zaiyuwu ba" Sarki gudin kar alhaji yaga kamar basu San abinne ya ce"A'a ya ce wai a Funtua zai ajeta" Mahaifin d'an'juma shiru yayi dan bai san abin da zai ce ba kuma.Sarki ganin Mahaifin d'an'juma ya kasa magana tashi yayi ya je inda yake ajiyar kud'i ya k'irgo dubu goma ya kawo ya ce"To dama dai ni zan biyama Abdurrahman komai na aure,dan haka ga kud'in sarana inda kace gobe da wuri zaka shige sai ayi komai yau,shi kuma Abdurrahman d'in zansa ya kawo alawa da biski(biscuit) da kan shi" Alhaji sosai yaji dad'in abinda Sarki yayi hakan yasa ya ce"Ai wannan kud'in sun isa,daga su ma ba sai ankawo komai ba,yanzu bari Abdurrahman yazo sai muji yaushe za'a tsaida auran" "Eh tom bari in kira shi awaya ai yana kusa". Sarki Kiran d'an'juma yayi awaya.Suna nan zaune d'an'juma ya shigo,bayan d'an'juma ya zauna ne Sarki ya kallai ya ce"Abdurrahman nan da wata nawa kake ganin zaka iya gabatar da hidamar auran nan da muke son tsaidawa yau insha Allah?" D'an'juma rasa abinda zaice yayi dan sai yaji maganar kamar wasa.Sarki murmushi yayi dan ya fahimci d'an'juma al'ajabi ne yasa ya kasa magana,hakan yasa ya ce" Abdurrahman wata nawa kake ganin idan munsa ka shirya?" D'an'juma d'agowa yayi ya kalli mahaifin shi,ganin ba shi ya ke kallo ba sai ya maida kallan shi ga Sarki ya ce "Duk yadda kukayi yayi" "A'a Abdurrahman ai kaine mai hidima kai zaka fad'i lokacin da kake ganin ka shirya sai mu kuma muduba mu gani" Cewar alhaji.Shiru d'an'juma yayi dan baima san abinda zai ce ba,kallan Sarki yayi ya ce"Duk lokacin da kukasa yayi alhaji"Magana Sarki zai kuma yi,alhaji ya rigashi da cewa"A'a Malam Haruna inda yace duk lokacinda akasa yayi,ma'ana kenan yanada shiri,dan haka ina ganin mubar abin wata uku ai yayi ko?" "Eh yayi ,Allah ya kaimu lokacin"Sarki ya fad'i hakane kawai amma shi bai tab'ajin sarana wata uku ba,su da duk saranar su shekara guda wasu shekara biyuma,akasarima wata yarinyar kusan tun kan ta idasa auran ake badata asa rana,daga lokaci yayi sai dai asha biki. Alhaji kallan Sarki yayi ya ce"Tom Masha Allah na cika alk'awarin da na d'aukar ma Abdurrahman,yanzu Abdurrahman sai ka samu lokaci ka je Kadunar ku gaisa da Aminar" D'an'juma dai kai ya jinjina.Mahaifin d'an'juma ko kasa cewa komai yayi . Ahaka dai suka gama zantawar su suka tashi " Mahaifin d'an'juma na zuwa gida ya kalli mahaifiyar d'an'juma ya ce"Ashe d'anki aure zaiyi amma Banda labari?" Mahaifiyar d'an'juma da alamun mamaki ta ce"Wana d'annawa?"Mahaifin d'an'juma ,d'an'juma ya nunama mahaifiyar d'an'juma da zuwanshi kenan. Mahaifiyar d'an'juma da mamaki da kuma alamun farincikin d'annata zai aure ta ce" Kai Alhamdulilah,Allah mungode maka,tom ni inama nasani,har'an bashi auran yarinyar ne?" "Har'ansa rana ma wata uku masu zuwa". "To fa amma dai yarinyar banan garin take ba?" "Yarinyar da tazo nan ta zauna 'yar Kaduna ita"Mahaifiyar d'an'juma cikin zaro ido ta ce"Amma dai bata amincewar yarinyar ba ko?,dan ko ranar da zasu bar garin nan ta ce ma mahaifiyarta bata fatan abinda zai k'ara kawota garin nan,dan haka idan ma maganar nan wasace tom banason k'ara jinta,idan kuma da gaske ce in dai nina haifeka tom wallahi kayi gaggawar janye maganar nan ,dan bazaka auri Yarinyar nan ba,yarinyar da bata kallan kowa da mutunci ,mu nan duk ba kallan mutane takemana ba,taya zakaji dad'in zama da yarinyar nan,daga kai harmu babu Wanda zai ji dad'in auran nan,dan haka kai maza-maza kafin Sarki ya fitar da maganar nan kowa ya sani ka tafi ka sanar dashi ka fasa " D'an'juma shiru yayi dan yana ganin halaccin da alhaji yayi mai amma kuma sai ya ce mai ya fasa.D'an'juma kallan mahaifiyar shi yayi ya ce"Innna alhaji yayi Mana halacci sosai,mu ya kamata muje wajansu naiman aure amma shine yazo,yanzu kuma angama magana sai ince mai na fasa?" Mahaifiyar d'an'juma zata k'ara magana mahaifin d'an'juma ya d'aga mata hannu ya ce" Maryama inda dai anriga an tsaida magana shikenan,duk Wanda ya d'akko da zafi bakin shi,ban mai baki ba,amma dai nasan ba zai tab'ajin dad'in zama da yarinyar nan ba.Allah ya sanya alkairi sai ka k'ara hak'uri akan wanda kake da shi tun yanzu.......โœ๏ธ ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Inama 'yan'uwa da abokan arzik'i barka da sallah,musamman masoya littafin meenalyn daddy. Page 21 & 22. D'anjuma shiru yayi dan yana ganin halaccin da alhaji yayi mai Amma kuma sai ya ce mai ya fasa auran da bakinsa ya amsa yana so.D'anjuma numfasawa yayi sannan ya kalli mahaifiyarshi ya ce"Inna alhaji yayi mana halacci sosai ,mu ya kamata muje wajansu naiman aure amma shine yazo wajan mu yanzu kuma angama magana sai ince mai na fasa?" Mahaifiyar d'anjuma zata k'ara magana mahaifin d'anjuma ya d'aga mata hannu ya ce"Maryama indadai anriga an tsaida magana shikenan duk Wanda ya d'akko da zafi bakinsa,ban mai baki ba amma nasan ba zai tab'a jin dad'in zama da yarinyar nan ba.Allah ya sanya alkairi ,sai ka k'ara hak'uri akan Wanda kake dashi tun yanzu" D'anjuma shiru yayi kanshi ak'asa,dan tabbas shi kanshi yarasa acikin halin da yake ciki,shin murna yake ko fargaba.Mahaifiyar d'anjuma kuwa cewa tayi"Malam bamu tab'a jayayyaba ,amma gasjiya yau zamuyi,dan ban yadda da wai inda anriga anyake magana shikenan ba,gasjiya banyadda ba,ya koma yasanar da sarki idan kunyar kakan yarinyar yakeji alabashi sarki sai ya sanar dashi ya ce anriga anbashi yarinya"daga mahaifin d'anjuma har d'anjuma shiru su kai dan shi kanshi mahaifin d'anjuma bawai son auran yake ba,mafitace kawai da yarasa.Mahaifin d'anjuma ya dad'e bai iya cewa komai ba,sannan ya kalli mahaifiyar d'anjuma da kallo d'aya za kai mata kasan ranta ab'ace yake .Maihaifin d'anjuma kallan d'anjuma yayi da kanshi ke duk'e ya ce"Tashi kaje abinka Abdurrahman"D'anjuma tashi yayi ya fita.Bayan d'anjuma ya fitane,mahaifin d'anjuma ya kalli mahaifiyar d'anjuma ya ce"Maryama naji abinda kikace,amma da zaki bud'e zuciyata ki gani wallahi nafiki k'in wannan auran da akaba Abdurrahaman,saboda tunda yarinyar nan tazo gidannan har suka tafi bata tab'a min kallan arzik'iba,amma tabbas mahaifiyarta mutuniyar kirkice,tom amma tafi k'arfinta ,ni aganina mutaya Abdurrahman da addu'ua Allah tabbatar da abinda yafi alkairi,saboda abinda kikeso ba zai tab'a yuwuwaba,maganace sun riga sun yanketa,dan haka saidai fatan alkairi kuma". Har mahaifin d'anjuma ya gama magana mahaifiyar d'anjuma bata iya kuma cewa komai ba. B'angaran alhaji ko sa sarki haka suka raba dare suna hira akan auran jikokinnasu. Washe gari da wuri alhaji ya tasa Isuhu suka kama hanyar Kaduna. B'angaran daddyn meenal ko alhandulillah jikinshi da sauk'i sosai ,sai dai tunda hajiya Mariya ta sanar dashi alhaji ya tafi garinsu d'anjuma ya shiga cikin farkagaba ,kuma tun daga lokacin yanayinshi gaba d'aya sai ya canza. Yauma haka daddyn meenal ya wayi gari da fargabar nan,haka dai ya daure yayi breakfast. Misakin k'arfe sha d'aya na safe alhaji wato kakan meenal suka shiga garin Kaduna,suna isa alhaji yacema Isuhu yayi gidan Sani da shi.Daddyn meenal na zaune meenal na mai hirar tak'osa ta ga ta fara aiki alhaji sukayi sallama suka shigo.Bayan alhaji ya zaunane daddyn meenal ya gaidashi yayi mai ya hanya.Alhaji cikin fad'ad'a fara'arshi ya ce"Ina Mariya ne,tafe nake da albishir mai kyau so nake sai agabanta zan fad'a?"Daddyn meenal da gabanshi ke dukan uku-uku kallan meenal yayi ya ce"Kira mommynki idan kinkirata ki je Falona ki zauna nan zamuyi magana ne".Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce"A'a ta dawo dan maganar tatace ai"Daddyn meenal shiru yayi meenal kuma ta shiga kitchen ta kira mahaifiyarta da ke aikin girki. Hajiya mariya waje ta samu ta zauna sannan ta gaida alhaji. Alhaji K'ara gyara zama yayi sannan ya ce"Alhamdulillah dama ance komai yayi farko zaiyi k'arshe,kuma matar mutum kabarinsa wani baya auran matar wani,sannan tunda yaran nan ya furta yana son yarinyar nan sai da nayi kwana bakwai ina addu'a indai ba alkairi acikin lamarin Allah ya kaudamin son abun,amma naji son abin k'ara k'aruwanmin yake,hakan yasa na tabbatar da akwai alkairi alamarin,shi yasa kukagananace,jiya da na koma munyi magana da Sarki dan antsaida komai ansa rana wata uku masu zuwa,dan yaron ma da yake akwai himma har yaba da biskit (biscuit)an taho da shi nasa ranar da akai"Alhaji har ya gama maganar shi babu Wanda ya tankamai daga daddyn meenal har hajiya mariya,itako meenal bama fahimtar abinda alhaji yace tayi ba,dan tuhda ya fara magana ta d'auki wayarta ta fara buga game.Alhaji ko jin babu Wanda ya tanka mai ,kallan daddyn meenal yayi Wanda kallo d'aya ya hango tsantsar damuwar da yashiga najin abinda yace,alhaji share daddyn meenal yayi ,dan ya hango damuwar da ya shiga najin abinda yace,alhaji yana sane yace"Sani ko bukuji abinda nace bane nayi magana kunajina kun shareni?"Daddyn meenal da gaba d'aya yarasa abinda ke mai dad'i da kyar ya bude baki ya ce"Alhaji munji abinda kace"Alhaji cikin jin dad'i ya ce"Yauwa isuhu dan Allah shigo da biskit d'in da suka bada nasa ranar". Wanda aka kira da Isuhu tashi yayi yaje ya shigo da kwalayan biskitin da d'anjuma ya bada amatsayin kayan sa ranarshi da Meenal. Bayan isuhu ya aje kwalayan biskit d'inne ,Alhaji ya kalli Meenal dake ta famar danna waya wadda hankalinta gaba d'aya ba akansu yake ba,da alamama batagane abinda ake magana akai ba,hakan yasa alhaji ya kalli meenal ya ce"Amina bani hankalinkinan,wannan kwalayan biskit d'in da kike gani nasa ranarki da Abdurrahman ne,yaron nan d'anjum......".Yadda meenal ta mik'e azaburene har wayar hannunta na fad'uwa yasa alhaji yayi shiru.Meenal cikin zazzare ido na alamun furgicin abinda alhaji yace ta ce"Alhaji banganeba,kana nufin ni wai akasama rana da d'an kyauyan nan kome?"Alhaji da k'uwa yayima meenal yace"Amina k'aniyarki nace,dan garinku ni zaki rik'a zaroma ido kina tambayata,tom ki k'ara bud'e kunnanki da kyau inma jine biki ba,d'anjuma dai yaro mai hankaki na garinda kikaje shi aka samiki ranar aure da shi wata uku masu zuwa.....".Meenal wurgi tayi da wayarta tana mai fasa kuka iya k'arfinta tana mai kallan daddynta tana cewa"Daddy wai kaji abinda alhaji yakecewa ko daddy?".Meenal ta idasa maganar tana mai k'ara tsandarewa da kuka. Alhaji Abba tashi yayi yazo ya kama Meenal cikin damuwa ya zaunar da ita kusa da shi yana mai cewa"Ki yi shiru Meenalyn daddy alhaji wasa yake mik....."Kaine dai kake mata wasa ,ga biskit nan dan haka duk ku rabama mutanan arziki,idanma bazaku rababa Mariya gashi nan ke duk kiba mutanan da kuke tare da su,ki shaida musu wata uku masu zuwa insha Allah biki"Alhaji na kaiwa nan ya tashi yayi ficewar shi,ya iske isuhu acikin mota yaja suka tafi. Meenal ko kukanta taci gaba dayi tana mai cewa"Wallahi daddy tunda wuri kajema ka tsaida maganar nan dan Wallahi kajima na rantse bazan auri d'an kyauye ba".Aifa nan hankakin alhaji Abba ya kuma tashi sosai,dan yama rasa abinda zai cema meenal ya samu tayi shiru ta saurareshi,kallan hajiya Mariya yayi dake zaune tayi tagwumi tana kallansu ya ce"Haba Mommyn meenal kizo ki tayani ba yarinyarnan hak'uri mana kinyi shiru kina ganin ahalinda take"Tom daddyn meenal mai zance?,aikin gama yariga ya gama meenal sai dai tayi hak'uri". Meenal tashi tayi da gudu ta tura bedroom d'inta ta shige tana mai k'ara tsananta kukanta.Alhaji Abba ma tashi yayi ya bita da gudu amma kafin yaje ta sama d'akin key dole ya tsaya yana buga k'ofar yana mai rok'on Meenal da cewa"Dan Allah meenalyn daddy ki bud'e ki saurareni kiji abinda zance miki,Wallahi meenal hankalina yafi naki tashi bana son auran nan,kuma insha Allah baza ayishi ba,dan Allahi ki bud'e k'ofar"Babu yadda alhaji Abba baiyi da meenal ta bud'e k'ofar ba amma tayi banza dashi taci gaba da kukanta.Alhaji Abba jingina yayi da k'ofar yayi ta gwumi dan sosai kukan meenal d'in ke k'ara d'aga mai hankali. Hajiya mariya da ita kanta cikin damuwa take najin abinda alhaji yace, fitowarta kitchen kenan jin abincinta na kyauri tazo ta iske daddyn meenal ya rafka uban tagwumi yana jingine da k'ofar d'akin meenal.Yajiya Mariya k'arasawa tayi ta zuk'unna kusa da daddyn meenal ta ce"Daddyn meenal kayi hak'uri dole muyi hak'uri mujure ire-iran halinda zamuga Meenal ciki,idan ko ba hakaba tom sai dai mu bujirema maganar alhaji,wadda hakan kuma ba abu bane mai yuwuwa,yanzu ga abinci nan na sauke dan Allah kazo muje kaci..." .Wata irin tsawa alhaji Abba yayima hajiya Mariya ya ce" Wata irin banzar magana kike fad'amin ko sokike mutaru makashe meenal ne ko me?,Yarinya tana cikin wannan halin zaki cemin wai inzo inci abinci,wato in rabu da ita ta mutu,ba zanci abincin ba ,ki b'acemin da gani Mariya kafin ranki ya b'ace!!". Hajiya Mariya da mamaki ta kalli alhaji Abba dan ita bataga abin da ta fad'a na fad'a ba sai dai in zai hucekanta ne.Hajiya Mariya tashi tayi taba alhaji Abba waje kamar yadda ya naima. Alhaji Abba kukan meenal ba k'aramin d'aga hankalinshi yake ba,alhaji Abba kamar zai yi kuka ya tashi yana mai bubbuga k'ofar d'akin meenal ya ce"Meenalyna dan Allah ki yi shiru tom kibar kukan,dan Allah ki bud'e muyi magana kinji Meenalyn daddy"Mennal ko ai babu alamunma taji abinda alhaji Abba yace bare har ta wani saurarai .Alhaji Abba jin Meenal bata tanka mai ba kamarma bataji abinda yaceba hakan sosai ya k'ara d'aga hankalin shi,hakan yasa kamar wani zautacce yaci gaba da buga k'ofar yana cewa"Meenalyna dan Allah ki bud'ema daddynki ki saurareni muyi magana dan Allah". Hajiya Mariya da takasa fushi duk da abinda alhaji Abba yayi mata,zuwa tayi takamo hannun Alhaji Abba ganin yadda ya dage yanata bubbuga k'ofar ko zafin hannun shi bayaji.Yajiya Mariya cikin lallami ta ce"Daddyn meenal dan Allah ka saurareni nimafa kaina adamuwa nake,kuma kasan ni kaina bazanso in aurar da Meenal ga Wanda bataso ba,bare kuma ace za ad'auketa kaita kyauye bazanso ba,sai dai in ba yadda zanyi shine zanyi hakuri ,yanzu kamata yayi mu zauna mu sami mafitar abinnan,itacan ta rufe kanta tana kuka tak'i saurararka ,kai kuma kazo nan sai famar bubbuga k'ofa kakeyi kak'i natsuwa ka samo mafita,yanzu zaunawa zamuyi muyi magana muji ta ina zamu b'ulloma al'amarinnan,dan Allah kazo muje ka zauna muyi magana,saninkankane Meenal bazata sauraremu ba yanzu,dan haka sai mu tafi mu samo mafita"Mariya banda wata natsuwa inajin kukan Meenalyn daddy ,dan Allah ki gwada mata magana ke ko zata bud'e sai ayi shawarar baki d'aya da ita" Shiru Hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Tom mu zagaya baya muyi mata magana ta window" Ta baya hajiya Mariya da daddyn meenal suka je ,Allah ko yasa suka samu window abud'e.Daddyn meenal da saurinsa ya k'arasa jikin window inda ya hangi meenal d'insa ta tusa kanta k'ark'ashin cinyoyinta sai kuka take,babu alamun za tai shiru.Alhaji Abba cikin damuwa ya ce"Meenalyn daddy ki yi shiru dan Allah karkanki yayi ciwo ,ki bud'emin k'ofar muyi magana dan Allah"Meenal d'agowa tayi tana kallan daddynta kamar bazatayi magana ba,sai can ta ce"Daddy Allah bazan bud'eba gara in mutu ma kawai in huta inda kaima kadaina Sona,agabanka akecewa za aimin aure kakasa hanawa,kuma auranma d'an kyauye,ai wallahi sai alhaji yazo gidan nan da bakinsa yace anfasa sannan zan bud'e ,idan ko ba hakaba zamana zanyi babuci babu sha har mutuwa tazo in mutu"Alhaji Abba kamar zaiyi kuka ya ce"Ayyah meenalyn daddy dan Allah ki bud'e kin manta kince bazaki mutu kibar daddynki ba tare zamu mutu?"Alhaji Abba babu kalar allashin da baiyima Meenal ba dan ta bud'e amma tak'i,gashi ta dage sai kuka take kamar wadda ranta zai fita,hajiya Mariya ko babu yadda batai da daddyn meenal ba akan yazo yaci abinci ya barta zata gaji tai shiru,amma k'arshema fad'a yarufeta dashi dole tayi shiru ta tafi tabasu waje. Abu kamar wasa har akai sallar la'asar amma meenal batabar kuka ba kuma bata bud'e k'ofar ba,nan fa hankalin alhaji Abba ya gama tashi.Wayarshi ya ciro ya kira alhaji,alhaji na d'agawa daddyn meenal cikin alamun tsantsar damuwar da yake ciki ya ce"Alhaji Wallahi tunda kabar gidannan Meenal tarufe kanta ad'aki take kuka ,anyi-anyi tak'i bud'ewa wai sai kazo kace mata anfasa auran nan sansan zata bud'e, dan Allah alhaji kayi wani abu idan bahaka ba yarinyar nan zata iya shiga wani halin,Wallahi yanzu haka bakaga yadda ta fita hayyacinta ba"Alhaji shiru yayi dan shi kanshi saiyaji badad'i jin gudaliyar jikarshi tana cikin wani hali,hakan yasa ya ce"Shikenan bari inzo gidan"alhaji Abba na cewa haka ya kashe wayar. Daddyn meenal har bakinsa narawa wajan lek'awa ta window yana cema meenal,"Meenalyna kinji munyi waya da alhaji yanzu zaizo dan Allah ki bud'e min kinji "Meenal ka fad'a ta mak'ale alamun bazata bud'eba,alhaji Abba zamewa yayi ya zauna bayan window yana mai sauraran zuwan alhaji. Alhaji Abba nanan zaune alhaji ya shigo shida hajiya Mariya,alhaji k'arasawa yayi jikin window yana ma meenal kallan mamakin yadda take kuka kamar wadda iyayanta suka mutu,daddyn meenal ko yana ganin alhaji ya tashi da sauri yana cewa"Yauwa Meenalyn daddy kinga alhaji yazo ko tashi ki bud'e min dan Allah" Meenal cikin kuka ta ce"Bazan bud'e ba har sai alhaji ya ce ya fasa min wannan auran sannan ,idan kuma ba hakaba Wallahi anan zanta zama babu ci babu sha har in mutu..........โœ๏ธ ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 23 & 24 Meenal cikin kuka ta ce"Bazan bud'e ba har sai alhaji ya ce ya fasa min wannan auran sannan,idan kuma ba haka ba Wallahi anan zanta zama babu ci babu sha har in mutu kowama ya huta inda abin hakane" Daddyn meenal cikin rud'ewa ya ce"Alhaji kaji ko abinda tace,dan Allah kataimakamin afasa wannan auran." Alhaji Abba ya idasa maganar yana rik'e da hannun mahaifinsa kamar zaiyi kuka. Alhaji shiru yayi baice komai ba sai zuwa can ya ce"Sani ka yi hak'uri inajin kunyar sarki,bazan iya zuwa insanar da shi abinda kakeso ba,muyi ta addu'a Allah ya karkato da hankalinta kafin lokacin bikin." Daddyn meenal cikin marairaicewa ya ce"Alhaji ni zanje zansanar da sarki da kaina"Bazai yuwu ba Sani,addu'ar dai ita zamuyi Allah ya juyomana da hankalin Amina kafin bikin" Meenal da tayi tunanin abinda tace zaisa alhaji ya janye maganar fasa auran,amma sai taji kuma yana cewa wai suyi addu'a Allah ya juyo da hankalinta,meenal rugawa tayi da gudu ta d'akko wata k'aramar wuk'a tasa dai-dai wuyanta tana cewa"Daddy shikenan kashe kaina zanyi yanzu nan ,dan wallahi bazan zauna da ranar d'an kyauye akaina ba,gara in kashe kaina kowama ya huta kafin inga wannan bak'ar ranar"Meenal ta fad'i maganar tana d'ora wuk'ar awuyanta alamun zata yanka. Daddyn meenal fasa kuka yayi jikinshi ko ina yana rawa yana cewa"Alhaji dan Allah kataimake ni dan Allah! dan Allah!!" Alhaji ganin yadda jikin Alhaji Abba ke rawa abin sai ya bashi tsoro,hakan yasa bawai dan yaji tsoran abinda Meenal zatayi ba dan yasan k'arya take baban take godawa.Alhaji ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"Shikenan gobe zanje in yima sarki magana abashi wata yarinyar"Alhaji na fad'in haka ya juya ya tafi. Daddyn meenal cikin k'osawa ya ce"Yauwa meenaln daddy kinji dai alhaji ya fad'a da bakinsa aje wuk'ar dan Allah ki bud'emin kinji".Meenal turo baki tayi sannan ta aje wuk'ar ta bud'e d'akin.Meenal na bud'e d'akin daddyn meenal ya shiga da sauri ya rungune Meenal yana mai sauke ajiyar zuciya yana mai bubbuga bayan meenal d'in.Sun dad'e ahaka sannan Alhaji Abba ya kamo hannunta ya ce" mu je kici abinci" Alhaji Abba a caution d'in falonshi ya zaunar da Meenal ya shiga kitchen da kanshi ya d'ebo mata taliya ya kawo mata. Kasan cewar Meenal yunwa takeji hakan yasa ta amsa taci,tana gama ci baccin wahalar kukan da tayi ya kwasheta,sanna Alhaji Abba shima ya tashi yaje ya gabatar da sallolonshi " B'angaran alhaji ko,hajiya Mariya ganin yadda ya fito jikinshi asanyaye yasa cikin sanyi tabi bayan shi tana cewa"Alhaji lafiya kuwa?" Alhaji kamar ba zai yi magana ba ,sai kuma ya tsaya yana kallan Mommyn meenal ya ce"Mariya ke ma baki son auran Amina ko?" Shiru hajiya mariya tayi tana tunanin abinda zatacema alhaji,sannan ta ce"A'a alhaji bawai bana so bane,kawai ina tunanin yadda Meenal ta saba rayuwar nan kuma ace ta koma rayuwar kyauye,sannan kuma mahaifin Meenal yariga ya shagwab'a Meenal da yawa bazata iya bibiyayya wa mijinta ba,garama idan ta auri Wanda ta ke so k'ila tayi biyayya tabishi,amma wannan kamma ina hangyan zamanda za ai" Shiru Alhaji yayi sannan ya ce"Eh tom Mariya maganarki hakane,amma yaran nan yace ba'a kyauyansu zai ajeta ba,magabar so kuma ke kina ganin da akwai Wanda Amina zata so,yarinyar da kullum kallan kanta take kamar wata jinjira"Shiru Alhaji yayi kamar mai tunani,sannan zuwa can ya ce"Mariya ki sanar da Sani maganar auran Amina na nan,dan bazan iya tunkarar sarki ba da maganar warware auran nan gaskiya,ita kuma Aminar ina tunanin aci gaba da b'oye mata har izuwa ranar bakin,ni kuma zanci gaba da addu'a kuma sai ku tayani Allah ya karkato mana da hankalinta akan al'amarin" Mommyn meenal cikin sanyi ta ce "Tom insha Allah za'ayi." Meenal na tashi bacci ruwa ta watsa ,sannan ta koma wani baccin inda dama hutun sallah take" Da daddare alhaji Abba na zaune falonshi yana kallo Hajiya Mariya ta yi sallama ta shiga.Bayan hajiya Mariya ta zauna da d'an jimawa sannan ta kalli daddyn meenal ta ce"Daddyn Meenal alhaji ya bani sak'o in baka" Alhaji Abba maida hankalinshi yayi ga Hajiya Mariya alamun inajinki.Hajiya Mariya cikin sanyi ta fara magana kamar haka"Daddyn Meenal sai dai muyi hak'uri kuma muyita addu'a Allah ya sa haka shi yafi alkairi,d'azu Alhaji yacemin maganar auran meenal da yaran nan tananan,amma wai mu b'oyema meenal har sai ranar bikin ta sani" Shiru Alhaji Abba yayi dan yama rasa abinda zai ce,sai zuwa can ya ce"Amma baki tunanin halinda Meenal zata shiga tana mai sa ran anfasa auran nan gaba kuma sai dai taji an d'aura mata aure da yaran nan?" "Tom daddyn meenal maganar halinda Meenal zata shiga ni sai inga sai dai muyita addu'ar Allah ya tabbatar mana da abinda yafi alkairi amm...."Alhaji Abba cikin jin zafi ya katse mommyn meenal ya ce"Mariya wata kalar magana kikeyi haka,Allah ya tabbatar mana da alkairi kinsan dai yaran nan bazai tab'a zama alkairi ga meenal ba, dan haka idan zaki addu'a kice Allah yasa afasa kawai bawai Allah ya tabbatar da alkairi ba,alkairin me?,wana alkairi wannan yaran yake dashi?,nifa dama kallo d'aya na yi ma yaran naji bai min ba." "A'a daddyn meenal dan dai baima meenal bane,amma gaskiya Abdurrahman nada hankali da natsuwa,danni Wallahi lokacin da naga yaron banzaci a kyauyan yake ba ma,amma da meenal zata kwantar da hankalinta inda ba a kyauyan zai ajetaba sai inga da...."Tsawar da daddyn meenal yayi ma mommyn meenal ce tasa tayi shiru bata k'arasa fad'in abinda take fad'a ba. Alhaji Abba cikin alamun jin zafn Hajiya Mariya ganin bata goyan bayan meenal ya ce "Mariya Wallahi na fara tunanin da had'in bakinki za ai ma Meenal auran nan,dan haka indai kinsan dasa hannunki akan maganar nan tun wuri kafin in ganoki ki cire hannunki,kuma yadda ki kai aka had'a kiyi yadda zaki a raba,Meenal nawa take da ake k'ok'arin sata cikin wannan tashin hankalin."Alhaji Abba kamar wani zararre yazo ya kama hannun mommyn meenal yana cewa"Mariya na rok'eki idan kina da sa hannu a maganar nan dan Allah ku janye,kuji tausaina nida meenal,meenal shekarunta sunyi kad'an da zata fara fuskantar tashin hankali irin wannan." Hajiya Mariya shiru tayi tana kallan daddyn meenal dan tsakanin shi da Allah yake magana,hajiya Mariya cikin sanyi ta ce"Daddyn meenal Wallahi Allah d'aya bana farinciki da auran nan na Meenal,hasalima hankalina atashe yake, amma da alhaji yayi min bayani shine hankalina ya kwanta har ma ke ganin kamar koda had'in hannuna za ai hakan,karfa ka manta nina haifi meenal taya zan so abinda nasan meenal bazata so shi ba.Abinda na ke tunani shine inda har yace ba akyauyansu zai ajeta ba babu wani makusa alamarin inda....."Alhaji Abba hannu ya d'aga ma mommyn Meenal ya ce"Je ki kawai ." Dan sosai ranshi ki b'aci idan tana yabon d'anjuma. Hajiya Mariya fita ta yi batare da tak'ara magana ba. Haka Rayuwa taci gaba da tafiya batare da meenal tasan ba awarware auranta ba,inda alhaji Abba ko kullin cikin fargaba yake da tsoran halinda meenal zata shiga aduk lokacin da taji za'a d'aura auranta da d'anjuma" B'angaran d'anjuma ko shi da sarki suke shirye-shiryansu inda shima iyayanshi bason auran nashi suke ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiya dan yanzu haka saura wata d'aya auran,sosai d'anjuma ke cikin damuwa da fargaba, saboda tun lokacinda akai maganar saranar shi da meenal har yau daga mahaifiyarshi har mahaifinshi babu Wanda ya kuma mai maganar auran,sai dai shi da sarki kawai suke shawarwarinsu,yanzu haka d'anjuma yazo gaida sarki ne bayan sun gaisa har d'anjuma zai fita sarki ya kirashi ya ce "Abdurrahman yaufa saura kwana ashirin da bakwai bikinka ,ya maganar lefan ,ka gama had'awa inda kace saura kad'an?." "Eh sarki nagama ."maganar wajan zama fa inda dai ka amsa ma alhaji zaka ajeta a Funtua."Cewar Sarki. Shiru d'anjuma yayi sannan ya ce "Eh dama da akwai wani gida da nakeso in kama haya sai in ajeta nan,tom amma Baba nake tunanin ba zai yadda ba." Sarki gyara zama ya yi ya ce " Kaje ka kama hayar zanma mahaifinka maganar anjima idan yazo duk da banso na kuma yi mai maganar ba har izuwa ranar d'aurin auran,saboda tunda akasa ranar nan bai kuma zuwa yayimin maganar ba,amma ni zanmai anjima idan yazo." D'anjuma cikin jin dad'i ya ce"Yauwa idan kaine nasan bazai musaba." Kamar yadda sarki yace haka ko akai,da daddare mahaifin d'anjuma da yaje gaida sarki ,sarki ke sanar da shi maganar kama hayar da d'anjuma zaiyi a Funtua.mahaifin d'anjuma "To"kawai ya iya cewa,dan bazai iya yima mahaifinshi gaddama ba,yana komawa gida yasanar da mahaifiyar d'anjuma abinda sarki yace mai,aiko nan mahaifiyar d'anjuma tanuna bazata yadda ba,suna cikin maganar ko Allah ya kawo d'anjuma. Mahaifiyar d'anjuma kallan d'anjuma tayi ta ce"Nasan kai ka sa sarki ya sanar da mahaifinka a Funtua zaka zauna,saboda ita yarinyar bazata iya zama a mahaifarka ba,tom ka bud'e kunnanka da kyau kaji idan har bazaka ajeta garin nan ba,sai dai ka fasa auranta,ka naimi wadda zata iya zama damu,dan bazaka jamana surutun jama'a acikin garin nan ba,tunda ka ke garin nan ka tab'ajin wanda yayi aure bai fara aje matarshi gidansu ba,koda zai ajezata agidansa saninkanka ne sai ya barta agidansu tayi kamar shekara ko k'asa da haka sannan ko zai fidda ta gidansu,amma kai gaba d'ayama garin zaka bar da ita,tom Wallahi banyarda ba , sarki kuma zanje in sa mai muyi magana wata k'ila ya manta al'adar garin nan ne." D'anjuma dai baice komai ba,dan yadda mahaifiyarshi ta d'auka da zafi haka yasan saukarta sai Allah,gashi duk yadda takejin kunyar sarki ko magana akan abinda ya shafai kasan cewar shi d'an fari amma tana maganar zataje tayi magana da sarki,gashi tabbas sarki na kunyar mahaifiyarshi sosai yadda take darajashi yasan babu yadda za ai yak'i buk'atarta,tom amma indai hakane sai dai in tayi hakane dan afasa auran inda itama tasan meenal bazata tab'a iya zama a kyauyan nan ba,mahaifintama yasan bazai bari ba. Mahaifin d'anjuma tsawa ya dakama d'anjuma ya ce "Bamu waje ka tsayama mutane akai!" D'anjuma da yashiga duniyar tunani da sauri ya d'ago yana kallan iyayannashi da yake hango tsantsar k'iyayar auranshi da su ke.Fita ya yi ba tare da yace komai ba. B'angatan daddyn meenal ko yau alhaji ya aiko yana son ganinshi shida hajiya Mariya. Da daddare alhaji Abba ya d'auki hajiya Mariya suka je Kiran alhaji,bayan sun gaisane alhaji ya ce "Sani dama nakirakune in tunasar da ku yau saura kwana goma sha shida d'aurin auran Amina,kuma naga har yanzu baku sanar da kowa ba kamar ma baku da niyyar yin hakan?" Daddyn meenal shiru yayi dan tashin hankalin da yake jin shi ciki ba'a magana. B'angaran hajiya Mariya ma haka take,shiru tayi dan batasan mai zata ce ba,yan'uwanta ko daddyn meenal ya hana ta sanar da mutane dan yace hakan zaisa meenal taji,tom gudun rigimar alhaji Abba yasa hajiya Mariya taja bakinta tayi shiru,amma tasanar da yayarta da k'anwarta suma kuma sai da ta gargad'esu su yi shiru.Alhaji ko jin sun mai shiru ya ce"Mariya bakujina ne,nace yau saura kwana goma sha shida d'aurin auran Amina,amma buku cemin komai ba,sannan zuwa yanzu ya kamata ace kun sanar da Amina dan banga amfanin b'oye-b'oyan ba." Sai anan daddyn meenal ya d'ago ya kalli alhaji ya ce"Alhaji dan Allah ina rok'onka alfarma naji na yadda ka aurama meenal yarannan,amma dan Allah dan annabi inaso ab'oyema meenal maganar nan har sai an d'aura aure ni zansan yadda zanyi in sanar da ita,sannan bana buk'atar aimin taro agida saboda yin taron zaisa meenal ta fahimci abinda akeyi dan Allah ataimakamin aimin haka." Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce "Sani ko mutuwa anatara mutane bare kuma taron biki taron farinciki,amma saboda b'acin ran Amina kace baza ai ba,tom ba zaiyuwu ba." Daddyn meenal ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Alhaji bawai bana son tara mutane bane saboda b'acin ran meenal a'a,bana son tara mutane ne saboda sanin halin meenal da nayi zatayi abubuwan da mutane zasu tashi da ita,sai inga gara duk abinda za tai da haukar da za tai ace muka d'ai mukaji muka gani ,shine kawai dalilina." Shiru Alhaji yayi yana tunanin maganar daddyn meenal,sannan ya ce "Eh nagamsu da maganarka,bayan biki sai aba mutane hak'uri"Shiru alhaji yayi sannan yaci gaba da cewa"Dama maganar da nakiraku muyi kenan,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka."Daddyn meenal cikin sanyi ya ce "Ameen" Daddyn meenal bayan sun dawo gidane ya kalli Hajiya Mariya ya ce "Mommyn meenal nama rasa abinyi game da lamarin nan,wallahi ji nake kamar in gudu kafin bkin ayi komai ba'agabana ba,dan bana son ganin halinda yarinyar nan zata shiga" Hajiya Mariya kallan alhaji Abba tayi ta ce "Daddyn meenal nifa bana ganin auran nan na Meenal zaije ko ina saboda meenal dai batasan wani abuba waishi biyayya ,garashin kunya daga yaron har iyayan yaron bazasu laminci halin meenal ba,hakan yasa nake ganin abun babu inda zaije ,dan haka ka kwantar da hankalinka mu zubama abin ido muga yadda Allah zaiyi da ikonshi,amma tabbas nikam zanso meenal tayi biyayya ta amshi auranta hannu biyu,amma nasan hakan ba zai yuwu ba.........โœ๏ธ Zan rik'a fashin kwana d'aya a posting,mana idan nayi posting yau ba zanyi gobe ba. ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. page 25 & 26. Hajiya Mariya kallan alhaji Abba tayi ta ce "Daddyn meenal nifa bana ganin auran nan na meenal zaije ko ina,saboda meenal dai batasan wani abuba wai shi biyayya ,ga rashin kunya,hakan yasa nake ganin daga yaron har Iyayan yaron bazasu laminci halin meenal ba,hakan yasa nake ganin auran babu inda zaije ,dan haka ka kwantar da hankalinka mu zubama abin ido muga yadda Allah zaiyi.Amma tabbas nikam zanso meenal tayi biyayya ta amshi auranta hannu biyu,amma nasan hakan ba zai yuwu ba." Alhaji Abba dai bai tankaba dan tuni ya lula duniyar tunani bajin abinda mahaifiyar meenal tace yayi ba ma. Haka rayuwa taci gaba da tafiya meenal batasan da maganar auranta nanan ba. sauran sati biyu bikin meenal ta fara practical a asibitin da daddynta ke aiki.Yau ya kama saura kwana goma d'aurin auran kamar yadda suka tsayar,yau ne kuma sarki yayima alhaji maganar suna nan zuwa,sosai alhaji yayi mamakin jin zasuzo amma sai bai ce komai ba yayi musu fatan zuwa lafiya .Alhaji daddyn meenal ya Kira awaya ce yasa mommyn meenal tayi girki da yawa masu auran Amina ne zasu zo.Daddyn meenal to ya ce sanan ya Kira hajiya mariya awaya ya sanar da ita. Sarki su uku sukazo shida k'annan mahaifin d'anjuma.Alhajima kafin su iso ya kira aminin mahaifin meenal ,wato alhaji Kabiru dama alhaji ya sanar da shi maganar auran meenal.Bak'i ko tun kafin su iso alhaji yasa aka kawo musu abincin da akai musu . Bayan sun gamacin abincin ne an gaggaisa Sarki ya ce tom dama dai akan maganar bikin nan ne naga lokaci ya k'arato nace bari inzo muyi magana,Abdurrahman ya gama kammala kayan lefe,gidama ya kama haya acikin Funtua kamar yadda yayi alk'awari kafin Allah yasa yayi nasa,tom amma dai dalilin zuwana shine tom kasan mu mutanan kyauye da al'adu kala-kala,wato yau kwana bakwai kenan da Abdurrahman yake sanar dani wai mahaifiyarshi tace bata yadda ya aje Amina Funtua ba sai yayi kamar yadda akeyi,wato mu acan yaro ko da ya gina gida tom ba zai aje matar can ba sai ya fara ajeta gidan iyayanshi sannan koda zai ajeta gidan shi,tom shine kar kukaga abu ba yadda mu kaiba da yake ni namamanta da wannan al'adar tamu shine nazo in sanar da ku,Amina zata fara zama agidan su Abdurrahman koda na sati biyu ne dole abisa al'adar wajanmu kafin ta tare gidanta da mijinta." Murmushi alhaji yayi yace mata kenan masu rik'o da al'ada,ai inda wannan ne bakomai ,ni Wallahi al'adar sai ta burgenima ankoyama yaro abinda bai iyaba ai,kuma yaro ya saba da surikanshi sosai,gaskiya hakan yayi kuma babu komai,ai ni da kasanar da ni aida bakazo ba,yanzu dan wannan maganarce kawai ka kwaso jiki kazo?." Dariya sarki yayi yace wallahi Abdurrahman ne ya matsamin wai sai dai inzo in sanar da kai."Abdurrahman kenan ya kwantar da hankalinshi babu komai zai auri Amina insha Allah,wannan ai ba komai bane,ni hakanma yayimin dai-dai ta saba da surikannata da sauran mutane ai kafin su tashi."Cewar alhaji. Sarki sosai yaji dad'in hakan,godiya sosai yayima alhaji ya ce "Alhaji mungode da wannan k'yauna da kake nunamana,kuma insha Allah nayi maka alk'awari kamar yadda kayima Abdurrahman hallacin wannan auran baka duba matsayishi ba,tom insha Allah shi kuma zai saka maka na rik'e Amina tsakani da Allah." Alhaji ma sosai yaji dad'in furucin sarki,ya ce "Nagode da wannan albishir d'in,yanzu idan kun koma ana gobe d'aurin aure ko jibi dan Allah ku sanar da Abdurrahman ina son ganin shi kafin bikin." Haka Sarki suka koma gida,duk da alhaji yayi-yayi su kwana sunk'i. Yau saura kwana bakwai d'aurin auran d'anjuma da meenal, yau ne kuma alhaji yayi Kiran hajiya Mariya da alhaji Abba. Alhaji Abba kuwa zuwa yanzu ba k'aramin rama yayi ba,dan har meenal takan tasashi da tambaya tana cewa daddy yanzu kabar fira dani, kabar yawan magana,kabar yawan dariya.Alhaji Abba sai dai yayima meenal dariya yace aikine sukai mai yawa,meenal tun tana tanbayar mahaifinnata har ta bar tan bayarshi tayi shiru,idan kuma ta tambayi mommynta sai ta ce mata meenal duk halinda kikaga daddynki ciki akanki ne,ni dai abinda nikeso da ke duk radda mahaifinki ya naimi kemai wani abu tom komai wahalarshi ki mai meenal,dan mahaifinki bak'aramin so yake miki ba,baki da hanyar da zaki sakamai sai ta hanyar bin umar nin shi,da kuma aminta akan duk abinda kikaga shima ya aminta dashi meenal." Meenal ko sai dai tayi murmushi ta ce "Mommy kenan,nima ina son sweet daddy kamar yadda yake sona." Da daddare kamar yadda alhaji ya kira iyayan meenal haka suka shirya sukaje.Bayan sun gaisa ne,Alhaji ya kalli mahaifin meenal ya ce " Sani yau dai saura kwana bakwai d'aurin auran Amina, dama wata shawara ce na kawo nace mai zai hana aje Funtua asaima Amina kayan d'aki acan an huta wahalar d'aukarsu akai su can,amma ku ya kuka gani?" Daddyn meenal kasa cewa komai yayi sai mahaifiyar meenal ce ta ce "Eh alhaji shawarar tayi,yanzu tom ya za ai?". Alhaji murmushi yayi ya ce "Tom auran Amina dai inda nina k'ullashi tom ni zanma Amina kayan d'aki,dan haka gobe zanyi magana da Abdurrahman d'in inda shi yasan mutane sosai a Funtua ina ganin basai munjeba sai yayi mana hanyar inda zamu saya sai in baku kud'in ku tura musu ,ala bashi sai su jeramata kayanta.Sai dai wani hanzari ba gudu ba,kasan 'yan kyauye da al'adu kala-kala,tom wai su a al'adarsu sai amarya ta zauna gidan iyayan yaro na satittika koda zata zauna gidanta,tom ni hakan ma sai yayimin dad'i ta saba da su kafin,wai sai Amina ta fara zama gidan su Abdurrahman kafin ta zauna gidansu." Daddyn meenal dai ya rasa bakin magana sai zufa kawai da yake aikin gogewa ta tsantsar tashin hankakin da ya k'ara shiga,ita kanta hajiya Mariya hankakinta ya tashi da jin wai Meenal zata zauna gidan su d'anjuma kafin su tare anasu gidan. Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce "Alhaji bank'i tatakaba,amma wallahi gara cikin rufin asiri meenal ta zauna gidanta in sansamu ne ita kad'ai, amma Allah meenal bazata zauna gidansu d'anjuma ba,idan kuma anyi mata ta k'arfin tsiya ta zauna tom abubuwanda da zataima masu gidan wallahi kai kanka ina tunanin sai kayi da kasanin had'a auran baki d'aya,amma idan gidanta ne komai zai dai-daita ahankali kuma kaga duk abinda zatai basujiba basu gani ba,kasan dai surutu irin na mutanan kankara,kuma idan can Funtua ne inda tana gani ba kyauye bane zatafi hak'uri." Shiru Sarki yayi ya d'auki dogon lokaci yana tunanin maganar ,sannan ya ce "Aiko maganarki Mariya hakane,indai hakane tom tafiya gobe ta kamani dole inje in naimi alfarma awajan iyayan Abdurrahman." Alhaji har ya gama maganarshi daddyn meenal bai tankaba,sai dai hajiya Mariya ke magana.Daga k'arshe su ka tashi suka tafi.Alhaji Abba har suka isa gida bai iya cewa komai ba,hajiya Mariya ma jan bakinta tayi ta yi shiru. Washe gari kamar yadda Alhaji yace da wuri yayi shirinsa Isuhu ya jashi suka nufi garinsu d'anjuma. Sarki da fara'arshi ya tari alhaji.Bayan an gaggaisa ne alhaji ya ce "Sarki wanna tafiyar ta mahaifan Abdurrahman ce,idan sansamune ina son magana da mahaifiyar Abdurrahman d'in". Sarki wayar shi ya lalibo yaba isuhu ya kiramai d'anjuma,bayan d'anjuma ya d'aga ne sarki ya ce "Abdurrahman kaje gida yanzu nan ka kiramin mahaifiyarka." D'anjuma ko dama yana nan bai riga ya shiga Funtua ba,dama kuma yana k'ofar gidan nasu,shiga yayi ya sanar da mahaifiyarshi kiran sarki. Alhaji da sarki na nan zaune suna hirarsu d'anjuma suka shigo shida mahaifiyarshi,d'anjuma bayan sun gaisa da alhaji fita yayi. Alhaiji ko bayan sun gaisa da mahaifiyar d'anjuma ne ya ce "Tom wannan tafiyar dai baki d'ayanta taku ce,nazo naiman alfarma ne,kinsan yaranmu na birni sai suyita abubuwan da su aganinsu wayewa ne ,wanda anan ko abin magana ne babba ,nasan dai kin zauna da yar gidan taki kinga yadda take,shine nake naiman alfarma kinsan yaran yanzu sai addu'a dan Allah abar d'anjuma ya yi zaman shi da matar shi a Funtua gudun abin magana ,kin san dai halin 'yar gidan taki."Mahaifiyar d'anjuma da bazata iya musama alhaji ba,cikin sakin fuska ta ce "Haba alhaji indan wannan ne ai da bakazo ba,shikenan babu komai wallahi,tayi zamanta d'akinta." Alhaji sosai yaji dad'in yadda mahaifiyar d'anjuma ta nuna mai bakomai ,godiya yayi mata sosai,sannan tayi musu sallama ta tafi. Bayan mahaifiyar d'anjuma ta tafine,alhaji ya kalli sarki ya ce "tom zamu tafi amma ana jibi biki zamu aiko asiyi kayan d'aki anan Funtua kaga shikenan anhuta wahalar d'akko su daga can."Eh kuma hakan yayi ."Cewar Sarki. Nan dai su alhaji suka k'ara tattaunawa game da bikin,sannan sarki yayima alhaji sallama suka kama hanyar Kaduna suka tafi." Haka kwana kai sukaci gaba da tafiya inda yake dai-dai da yau saura kwana uku d'aurin auran d'anjuma da meenal,Wanda har yau meenal batasan da maganar bikin ba,alhaji tun safe ya aiko da yana son ganin hajiya mariya,haka hajiya mariya ta shirya ta nufi gidan alhaji.Bayan sun gaisane,alhaji ya kalli hajiya mariya ya ce "Mariya na kirakine cikin 'yan'uwanki gobe zaki tura guda biyu Funtua su saima Amina kayan d'aki ala bashi sai su shirya komai,koya kiga gani?". Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce "Eh alhaji hakan yayi Allah ya kaimu goban." "Ameen Mariya,Allah yayi miki albarka". Hajiya Mariya da ameen ta amsa ta yima alhaji sallama ta tafi gida,tana zuwa ta kira yayarta da k'anwarta ta sanar da su maganar zuwa Funtua gobe. Washe gari da wuri 'yan'uwan hajiya Mariya sukayi sammakon tafiya Funtua,inda alhaji ya d'auki kud'i masu yawa ya basu yace duk abinda ya dace su siya su jera mata,ya had'asu da numbar d'anjuma. Hajiya Jamila yayar hajiya Mariya suna isa Funtua,inda ake saida furnitures suka nema,nan fa suka saima meenal kujesu masu kyau sosai,suka biya kud'in sannan sukaje b'angaran kayan d'aki nan ma dai haka suka sai duk wani abu da ake amfani da shi na kayan aiki,sannan sukaje b'angaran labulaye da zanin kado da katifa suka siya.Suna gama siyayyar suka Kira d'anjuma awaya,dama ya San da zuwan su shida abokinshi suka zo da mota tar d'aukar kayan,nan cikin k'ank'anin lokaci aka sa kayan cikin mota,cikin mutunci d'anjuma suka gaisa da iyayan meenal,sannan d'anjuma ya samar musu adaidaita suka hau suka nufi gidan da za akai meenal. Hajiya Jamila kallan k'anwarta tayi ta ce "Aisha gaskiya na yaba da yaran nan da zai auri meenal,ni wallahi jin ancemin d'an kyauye ne nazaci d'an kyauyan ne na gaske,yanzu wannan idan ba anfad'amaba wa zai kallai ya ce d'an kyauye ne,gaskiya da yarinyar nan zatayi hak'uri da ta amshi auran nan hannu biyu yaron nan baida wani aibu wallahi dan meenal ma sai dai ta nuna mai haske,amma Allah yama fita kyau". Aisha dai hmmm ta ce,ta ce "Aunty Jamlila nifa idan meenal ta nuna bazata zauna ba tom Allah laifin iyayanta ne,kina ganifa kamar tsoranta sukeji b'oyemata auran akeyi fa,har yanzu fa batasan da maganar auran ba,yo wani abunma da takeyi ai ni gani nake suke sata,inba daurema k'arya gindi ba,kina ganin wai ko taro ba za ai ba wai karta sani,nikam na zuba ido inga yadda abin zai kaya." Dariya Jamila tayi ta ce "Ke dai bari Aisha tunda nake ban tab'a ganin tab'ara irin ta yarinyar nan ba,garama Allah da kakan yayi mata haka dan inajin inda ba hakaba da baza tai auran ba,dan gani tak'e tafi k'arfin kowa,kuma fa in ba hasken fatar ba ba wani kyau gareta ba,yarinya kamar wata sanda."Isowarsu gidan yasa sukayi shiru. Gidane d'an ma dai-daici na zaman mutum d'aya , ciki da falo sai kitchen da toilet. D'anjuma abokanshi uku ya Kira suka jajjera kujerun su kuma suka jera kayan kitchen d'in,su nayi Aisha na dariya tana cewa "Aunty Jamila niko zanso inzo inga yadda zaman meenal zai kaya acikin gidan nan,anya ko kina ganin zaman nan zaiyuwu?."Jamila dai itama dariyar tayi ta ce "Tom Aisha wannan abin sai dai kazuba ido kayi kallo ,amma abin kam sai dai shiru,amma wallahi gidan baida wata makusa sai dai su yaranmu na yanzu suna duba inda suka tasone ,bakamar kuma meenal ba maiji da isa da k'asaita." Haka dai suka gama shirya kayan, sukace zasu tafi, d'anjuma babu yadda baiyi dasu su kwana ba amma sukak'i,da yake isuhu da alhaji yasa ya kawosu yana nan hakan yasa suka kama hanyar kaduna gab da magriba. Su hajiya Jamila ba su suka isa Kaduna ba sai tara da rabi na dare(9:30PM).Suna isa sukaci abinci suka wanta kasan cewar sungaji. Washe gari bayan sun gama karyawa ne,Hajiya Jamila yayar hajiya Mariya kallan hajiya Mariya tayi ta ce "Mariya banga meenal tana shirin komai ba na biki,kardai kicemin har yanzu kuna b'oye mata buku sanar da ita ba?" Ajiyar zuciya Mommyn meenal ta sauke ta ce "Tom mahaifinta ya hana afad'amata ,tom nima da da farko dai na goyi bayan hakan,amma zuwa yanzy kam ya kamata ace ansanar da ita,amma yak'i ." "Aiko ya zama dole asanar da ita yau d'in nan,taya jibi za'a d'aurama yarinya aure ace har yau bata sani ba,ko dan d'an k'unshi da kitso ai ansanar da ita,koko haka za a d'auketa akaita gidan mijin babu kitso babu k'unshi?". Shiru mommyn Meenal tayi sannan ta ce "Tom Aunty Jamila ko zaki sanar da ita ki bari sai kinsata tayi kitson da k'unshi sannan,dan wallahi meenal indai ta san da maganar auran nan tom bazata yadda tayi k'unshi da kitson ba." Tsaki Jamila ta yi ta ce "Wallahi Mariya kunji haushi tarbiyar da ku kai ma meenal,gashi nan tsoranta kukeji baku isa da ita ba,har fargabar ku b'ata mata kukeyi,kiramin meenal d'in." Hajiya Mariya Kiran meenal tayi awaya,tasanar da ita tazo falo yanzu ta sameta. Meenal da ke zaune tana game awayarta tashi tayi taje. Tana zuwa Jamila da yake babu wasa ta ce "Ungo taki".tayi mata da k'uwa,ta ce "Dan uwarki kinsan mun kwana anan shine bazakizo ki gaidamu ba ko?". Meenal sosa kai tafara ta ce "Mommy Allah na manta anan kuka kwana,ina kwanan ku."lafiya klau,maza kije ki tsafe kanki kizo". Meenal kallan Jamila tayi ta ce "Mommy aini kaina atsafe yake."Yauwa tom ina kikeyin kitso,kije aimiki kitso da k'unshi mai kyau mai tsada ni zan biya kud'in gobe zaki rakani Kano." Meenal wani tsallan dad'i tayi ta ce"Wayyo mommy wannan surprise haka,aikam yanzu ma kuwa".Meenal dama tayi wankanta hakan yasa ciki ta shiga ta d'akko mayafinta. Hajiya Jamila dubu goma taba meenal tace gashi nan ayi mai kyau,amma karki kitson attachment idan kuma ba hakaba kinsan halina".Meenal baki ta turo ta ce "Mommy indai hakane na fasayin kitson,banfa da wani gashi taya kitson zaiyi kyau ,nikam nafasa zan tafi da kaina haka inda hakane." Jamila da yake duk yaran dangi tsoranta sukeji hakan yasa kallan meenal kawai tayi ta yi shiru ta yafa mayafinta ta tafi kitson.Meenal na fita alhaji ya kira wayar hajiya Mariya,bayan sun gaisane ya ce"Mariya yau d'in nan ba sai gobe ina son kusanar da Amina jibi za'a d'aura mata aure,idan kuma kunk'i kunajin tsoranta tom ni zanzo da kaina in sanar da ita...........โœ๏ธ ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori. Page 27 & 28 Meenal na fita alhaji ya Kira wayar hajiya Mariya ,bayan sun gaisane ya ce "Mariya yau d'innan ba sai gobe ba inason kusanar da Amina jibi za'a d'aura mata aure ,idan kuma baku fad'a mataba kunajin tsoranta tom ni zan zo da kaina in sanar da ita." Hajiya Mariya numfasawa tayi sannan ta ce "Alhaji yanzu muma mukagama maganar sanar da Meenal,tom munyi shawarar turata k'unshin da kitso ne kafin musanar da ita ,saboda indai ta san da maganar bazatai kitson ba,daga ta dawo zamu sanar da ita" Alhaji kashe wayar yayi . Meenal ko ba ita da dawo ba sai gaf magriba,tana da wowa taita b'oye kitson kanta batason hajiya Jamila ta gani dan kitson k'ari tayi (attachment) Bayan meenal ta ci abincine tayi sallah ta kalli mommynta ta ce "Mommy daddy fa?."Bai shigoba" Meenal wayarta ta ciro ta kira daddynta awaya Kira d'aya ko ya d'aga ,meenal cikin shagwab'arta ta ce "Sweet daddy banganka ba fa tun safe?"Alhaji Abba cikin lallashi ya fara magana kamar haka "Meenalyn daddy ki yi hak'uri kinji tafiya ce takamani zuwa Abuja ko mommynki ma ban fad'amawa ba"Meenal kamar zatai kuka ta ce "Daddy gashi gobe zamu Kano da mommy Jamila"Alhaji Abba da yasan babu wata maganar zuwa Kano k'ila dai amma ta wata dubararne ya ce "Babu damuwa meenalyna ki yi tafiyarki idan nazo sai inzo kano d'in kiganni ai haka yayi miki ko?" Meenal cikin jin dad'i ta ce "Tom sai ka dawo"Tana fad'in haka ta kashe wayarta. Hajiya Mariya ko sosai ta yi mamakin tafiyar daddyn meenal baisanar da ita ba,amma da ta tuna gobe zai dawo sai ta share. Bayan hajiya Mariya da 'yan'uwanta sun gama duk abinda zasuyi misalin k'arfe tara suka Kira meenal falon,hajiya Jamila ce ta kalli meenal ta fara magana kamar haka "Meenal nasan kinsan kwanakin baya da ya wuce daddynki ya sanar dake maganar samiki rana ko?" Meenal kai ta d'agama hajiya Jamila.Hajiya Jamila kuma taci gaba da cewa " Tom kamar yadda ya sanar da ke anfasa awancan lokacin ya fad'amiki hakane dan baya son ganinki cikin damuwa amma ahak'ik'anin gaskiya magana na nan yanzu haka jibi juma'a idan Allah ya kaimu za'a d'aura auranki ina fatan zakiyima mahaifinki biyayya ki amshi auranki batare da tada hankalinki ba ,dan kinsan ba zai zab'a miki abinda yasan zai cutar da ke ba." Meenal cikin kuka ta ce "Mommy Jamila Wallahi bana sonshi,ni na yadda daddy ya auramin koma waye amma banda d'an kyauye dan Allah ." Hajiya Jamila da yake bawasa zarema meenal ido tayi ta ce "Ke banason shashanci kina son ki maida mahaifinki k'aramin mutum ne bayan anriga angama magana yanzu kuma sai ya koma yace anfasa ,tom kinsan dai halina wallahi ban iya lallashi ba yanzu sai in miki dukan da zaki kai kanki kafin jibi dan haka tun kafin kowama yaji ki shiga hankalinki ." Sosai Meenal kejin tsoran hajiya Jamila hakan yasa ta tashi ta ruga da gudu ta shiga d'akinta tana mai ci gaba da kukanta,waya ta d'akko ta kira number daddynta ya fi ak'irga amma bata shiga ya kashe wayar ,dole ta hak'ura taci gaba da kukanta kafin daddynta yazo afasa acewarta ,haka dai bacci b'arawo ya saceta. Bayan meenal ta shiga d'aki ne hajiya Jamila ta kalli mommyn meenal ta ce "Mariya wallahi karki nunama meenal wasa amaganar auran nan duk abinda zatace kice mata tayi hak'uri tayi biyayya ga Mahaifinta,idan taga babu goyan bata ta ko'ina zata hak'ura ta zauna"Hajiya Mariya dai saboda bata son yi ma yayarta gaddama shiru tayi,amma ita tasan meenal kome za'ai mata bazata tab'a hak'uri ta zauna ba dan tasanta da kafiya sosai. Haka dai suka k'araci tattaunawarsu game da bikin kafin suka kwanta" Washe gari daga mommyn meenal har 'yan'uwanta babu wanda yabi takan meenal haka sukaci gaba da harkokinsu Aisha ce k'anwar Mommyn meenal ta kalli hajiya Jamila ta ce "Aunty Jamila kinga fa har k'arfe sha biyu har yanzu meenal bata fito ba ta naimi abin kari (breakfast) ko in dubata dan Allah?"Jamila tsaki tayi dan bata son naci ta ce "Aisha bikijiba akace maganin biri karan maguzawa tom meenal indai muna son tayi biyayya da zab'inmu tom dole sai mun rintse ido mun nuna mata k'arfin ikonmu akanta,mun nuna bamu damu da wata shirman damuwarta ba,ana barin yaro ya tab'a wuta bawai dan ba'a sanshi ba ne ,a'a sai dan gaba ya kiyaye ". Dole Aisha taja bakinta tayi shiru amma tana lure da mommyn meenal duk ta shiga damuwa ta rashin fifowar meenal d'in. Mommyn meenal jin daddyn meenal shiru waya ta d'auka ta kirashi amma wayar shi kashe tana aje wayar tana tunanin lafiya saiga kira da bak'uwar number tana d'auka ta ji muryar daddyn meenal .Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce "Daddyn meenal lafiya inata Kiran numberka bata shiga?"Daddyn meenal cikin kwantar da hankali ya ce " Mommyn meenal ki yi hak'uri aikine yayimin yawa,naso na dowa yau amma sai gobe zanyi sammakon dawowa aiki yayimin yaw..."Mommyn meenal cikin katse daddyn meenal ta ce "Daddyn meenal gobane fa d'aurin auran meenal,kuma kace sai gobe zaka dawo?"Tom mommyn meenal nima naso ace yau na dawo kodan meenal amma abin bai yuwu ba,gobe insha Allah zanyi sammako."Tom shikenan Allah ya kaimu goban".Tana fad'in haka ta kashe wayar ,mommyn meenal yayarta ta kallah ta ce " Aunty Jamila kinga daddyn meenl ya tsira tafiyar nan ne saboda gudun rigimar meenal ne fa, dama tunda nakira wayarshi najita akashe nayi zargin haka"Hajiya Jamila cikin kwantar ma mommyn meenal da hankali ta ce "Ai garama da yatafin kinga munyi taranmu hankali kwance, inda indai daddyn meenal nanan meenal sai tafi yima mutane iskanci,kuma ni dama nagayyaci 'yan'uwanmu dan yanzu haka 'yan Kano na hanya,inko yana nan ba bari zai ba inda kince yace bai son agayyaci kowa kinga yanzu sai muyi taran mu cikin kwanciyar hankali" B'angaran meenal ko tana can kwance sai aikin kuka take bunubuni ta Kira wayar daddynta amma kashe ,tanan kwance ga yunwa ga damuwar rashin samun daddynta awaya ga kuma babbar damuwar da takeciki ta auran da za ai mata.Tananan kwance Aisha k'anwar Mommyn meenal ta lallab'a ta shigo,kusa da meenal ta zauna tana mai k'are mata kallo sannan ta ce "Meenal ki tashi ga abin breakfast na kawomiki,sanan shi kukan nan da kike babufa maganin da zaimiki,ni indai zakiji maganata kiyi hak'uri Meenal ki ma mahaifinki biyayya kina ganin shima bason auran nan naki yake ba,amma ya yi hak'uri ya yi biyayya ga mahaifinshi tom kema ki yi biyayya ga mahaifinki mana "Meenal dai bata saurari Aisha ba haka taci gaba da kukanta Aisha kuma ta tashi ta fita. Meenal ganin yunwa zata ka sheta tashi tayi ta d'auki abincin taci kad'an. Zuwa dare 'yan'uwan Hajiya Mariya suka iso inda akazo harda Hafsat yarinyar hajiya Jamila wadda suke sa'a da meenal.Tana zuwa d'akin meenal ta shiga ,kwance ta isketa idon nan yayi jajir alamun tasha kuka tagaji,Hafsat cikin sanyi ta dafa meenal dan taji komai game da rashin son auran da meenal batayi,ta ce "Meenal wai meye haka sai kace akanki aka fara aure ,tun jiyafa mommy tace min kike kukan nan." Meenal tashi tayi tana kallan Hafsat ta ce "Hafsat kinsan wa daddy zai auramin kuwa?, d'an kyauye fa Hafsat!"Hafsat da mamaki ta kalli meenal ta ce wai dan Allah da gaske ki ke d'an kyauye daddy zai aura miki?"Kai meenal ta d'agama Hafsat .Hafsat kuma tacigaba da cewa "Amma shine mommy ta ke cewa in lallasheki ai ko wallahi bazan goyi bayan ki auri d'an kyauye b....."Ubanki nace Hafsat ubanki dama kinzo ne ki zigata ?".Hafsat cikin turo baki tace "Mommy Allah ni bansan d'an kyauye zaku aurama sister ba,gaskiya mommy ba ai mata adalcib..."Marinda hajiya Jamila taima Hafsat ne yasa tayi shiru,sannan ta nuna meenal da hannu ta ce "Ke kuma sakarya idanma kin d'auki zugarta ke ki ka sani dan babu abinda zai hana auran nan sai wani ikon Allah!"Meenal kuma fashewa da kuka tayi hajiya Jamila kuma juyawa tayi tayi tafiyarta. Bayan Hafsat taje ta lek'a ta tabbatar da mahaifiyarta ta tafine ta dawo inda meenal take ta ce "Meenal share hawayanki kibar asararsu akan wani banza can,kiyi hak'uri kamar yadda suka nuna sai anyi anyi d'in akaiki da kanshi zai gaji ya sakeki,wulak'anci yau da ban nagobe da ban,da kanshi sai fahimci ke ba tsararshi bace ya baki ta kaddarki,yanzu abinda nakeso dake kiyi hak'uri kada kanki yayi ciwo dan Allah, nikaina wallahi ban goyi bayan ad'aukeki aba d'an kyauye ba."Haka dai Hafsat taita zuga meenal da nuna mata irin abubuwan da zata rik'amai nacin mutunci wanda abinma kwatakwata ba zaiyi k'arko ba. B'angaran daddyn meenal ko waya yakira alhaji yasanar dashi sai gobe zayi sammakon zuwa kafin d'aurin auran . Washe gari haka gidan su Meenal ya cika da mutane dan hajiya Jamila da kanta ta shiga mak'otan gidansu Meenal ta sanar da d'aurin auran meenal d'in yau.Aiko haka gidan yacika da mutane,inda mutane da dama sun k'osa suga waye angon. B'angaran meenal ko hayaniyar mutane da takeji wai anzo bikinta hakan sosai ya kuma d'agamata hankali lokaci guda zazzab'i mai zafin gaske ya rufeta. Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya.'Yan'uwan d'anjuma gaba d'aya sun hallara da 'yan'uwan meenal .Ababbban masallacin kawo wato shak Zafar,inda har yanzu babu daddyn meenal balabarinshi .Babban abokin daddyn meenal shi ya bada auran meenal ga k'anin mahaifin d'anjuma. Bayan an d'aura auran ne da d'an jimawa Alhaji wato kakan meenal ya naimi d'anjuma dan yanason keb'ewa da shi. D'anjuma zaune afalon alhaji,alhaji ya kalli d'anjuma dakanshi ke ak'asa ya ce "Abdurrahman naso ace tun jiya kazo dan maganganun da nakeso da kai suna da yawa,inda kaga yau ba lokaci inda yanzu zaku juya da amarya,wato d'anjuma da farko dai kafin in fad'i abinda nakeson fad'a maka ina naiman alfarma awajanka?"D'anjuma kanshi k'asa ya ce "Alhaji babu abinda zaka naima awajena banma shi ba,dan bacin kai nasan da bazan samu meenal ba dan haka karkaji komai kome kakeso awajena ni kuma zan maka shi insha Allah ." Alhaji cikin jin dad'in bayanin d'anjuma ya fara magana kamar haka"Abdurrahman Amina dai ta zauna agidanku nasan ka fahimsu wasu halayyarta ko kad'anne duk da ba zama mai tsawo ta yi ba,Abdurrahman nasan zakasha wuyar Amina sosai kafin kagane kanta ,abinda nakeso da kai dan Allah kayi hak'uri aduk yadda kasamu Amina watarana sai labari kuma mahak'urci mawadaci watarana zaka girbi ribar hak'urin insha Allah, sannan Amina bata san lallashi ba sai ammata jan ido take abu.Babu lokaci katashi kuje Allah yayi muku albarka Allah ya baka hak'urin zama da Amina."Insha Allah alhaji zanyi hak'urin zama da Amina kodan halaccinka agareni,nagode sosai" D'anjuma na kaiwa haka ya tashi ya tafi dan abokanshi dama sai kiranshi suke awaya suna k'ofar gidansu meenal suna jiran abasu amarya su wuce. Acan gidansu Meenal ko da kyar Hafsat ta lallab'a meenal tayi wanka tasa gayan da mahaifiyarta ta d'inka mata dan su basuga lefeba.Hafsat na shirya meenal tana cewa "Meenal bana son kina nuna musu wani abu aranki ki saki ranki akaiki d'in ,adai zaman aure bai yuwuwa saida soyayya ko ,da akwai wata shawara ma da zan kuma baki amma kinga yanzu ba lokaci ki bari sai munje can sai muyi magana" Ita dai meenal cigaba da kukanta tayi ,Hafsat nacikin shiryata ne hajiya Jamila tazo takamo hanunta tace "Muje wajan mommynki kuyi sallama. Meenal na kuka akakaita gaban mommynta,Allah sarki mommyn meenal d'inma kasa cema meenal komai tayi saboda kuka da yaci k'arfinta,da kyar dai ta iya cewa "Meenal kiji tsoran Allah kiyi biyayya ga mijinji shine abinda zakiyi ki samu ceto ranar gobe k'iyama"Meenal da kuka yaci k'arfinta cikin kuka ta ce "Mommy daddy dan Allah ina son ganin daddyna "Mahaifiyar meenal gogema meenal hawayanta tayi ta ce "Meenal ki yi tak'uri ki tashi ki tafi mutane najira daddynki zaizo har d'akinki ya ganki" Haka aka tafi da meenal tana kuka tana ciccijewa akasata amota aka tafi da ita .Hafsat ko babu yadda batayiba dan taraka Meenal amma hajiya Jamila lurada Hafsat kamar tana zuga meenal yasa tahana tafiyar da ita. Mutum biyu suka raka meenal d'akinta daga hajiya Jamila yayar mommyn meenal sai Aisha autarsu Mommyn meenal.Sai gaf magriba suka shiga garin Funtua inda aka kai amarya d'akin mijinta acikin unguwar wanzamai .Meenal haka ta kwana kuka babu yadda su hajiya Jamila basuyi da itaba amma tak'iyin shiru. Washe gari da wuri abokan d'anjuma suka kawomusu tea da bread suka karya,suna gama karyawa sukayi wanka suka kuma yima meenal fad'a sosai sannan mota tazo ta d'aukesu,aifa da zasu tafi meenal rik'esu tayi tana kuka sosai dan har hajiya Jamila sai da ta tausayama meenal halin da tashiga ,haka dai suka janye suka tafi suka barta suna mai tausayamata dan yadda take nuna k'iyayyar d'anjuma abin yayi yawa. D'anjuma ko da su hajiya Jamila zasu tafi sai da suka k'ara ankarar da shi akan hak'uri komai mai wucewa ne.Motarsu zata tafi hajiya Jamila takalli d'anjuma ta ce "Abdurrahman kashiga gida kayi lallashi dan mun baro ta tana kuka kuma bataci komai ba". Bayan motarsu hajiya Jamila ta tashine d'anjuma ja yayi ya tsaya ya kasa shiga gidan yana mai fargabar yadda Amaryar tashi zata karb'ai,dan tunda aka tsaida auranshi da ita magana bata kuma shiga tsakaninsu ba,hasalima shi tunda tabar garinsu bai kuma ganinta ba.D'anjuma cikin shahada da fargaba ya yi Sallama ya shiga gidan jin shiru ya k'arasa cikin d'akin ,can ya hango meenal bakin kadon sai kuka take iya k'arfinta ,d'anjuma ta kawa yayi ya isa inda take ,cikin sanyin ya kalli meenal ya ce.............โœ๏ธ ๐Ÿ“š Meenalyn daddy ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ* Na Fadila Sani Bakori Page 29& 30. D'anjuma cikin shahada da fargaba ya yi sallama ya shiga gidan,jin shiru ya k'arasa cikin d'akin, can ya hango Meenal bakin gadon sai kuka ta ke iya k'arfinta .D'anjuma takawa ya yi ya isa inda Meenal take,cikin sanyi ya kalli Meenal ya ce" Meenal ki yi shiru dan Allah ki fad'amin damuwarki, kukan ki yana shiga cancikin tsakiyar zuciyata yana min ciwo,sai inga kamar nagazane ina gabanki ace ban magance miki abin da ki ke ma kuka ba,dan Allah ki fad'amin damuwarki kin ji Meenalyn daddy?"Meenal da jajayan idonta ta d'ago tana ma D'anjuma wani irin kallo na raini da tsana,sannan ta tashi daga zaunan da take tana kallan D'anjuma ta ce "Ka ta shi akaina malam zaka wani tsaya kana tanbayata damuwata! Gazawa kuma da kake magana kana tunanin kanada abin da zaka burgenine?Bacin na tsaneka na tsani duk wani abu da ya danganceka ka tashi agabana malam!"Meenal ta fad'i magana cikin tsantsar d'aga murya. D'anjuma ko shiru ya yi bai matsa ba kamar yadda ta umarceshi , zuciyarshi namishi zafin maganar ta tsaneshi da tayi.D'anjuma da kyar ya iya bud'e baki ya ce "Meenal na sanni mai laifine agareki saboda nayi miki k'utsu cikin rayuwarki sai dai inason kisan komai yana faruwane abisa ga abin da Allah ya k'addara, hakan ya farune saboda k'addarar had'uwar aure tsakanina da ke da Allah ya k' ....." Wata tsawa Meenal ta bugama D'anjuma ta ce"Ka fita nace bana son ganinka gabana ,bana son jin muryarka!, bana son jin komai da ya shafeka ka fita na ce!"Meenal ta fad'i maganar da k'arfin tsiya Wanda yake nuna ranta amatuk'ar b'ace yake. D'anjuna ko cikin danne zafin maganganun Meenal ya ce "Naji zan fita amma ki fad'amin me zakici in kawomiki dan ance min bikici komai ba?" Meenal cikin sanyi kamar za tai kuka ta ce "Bazan iyacin duk wani abu da yafito daga hannunka ba , kai ba wai hannunka kad'ai ba ba zanci duk abin da yafito daga garin nan ba,saboda na tsaneka! Natsani komai dake garin nan saboda kai" D'anjuma cikin damuwa ya ce "Nasan baki sona Meenal amma dan Allah karki hora kanki da yunwa ki yi hak'uri ki fad'amin kome kike so ni kuma nayi miki alk'awarin zan kawo miki shi?" Meenal tsaki tayi ta taja bakinta tayi shiru dan ta gaji da magana acewarta.D'anjuma kuma ganin tayi shiru fita yayi yaje wajan mai tea da bread d'in kusa da su ya sa aka soya mata indomie da kwai , ya koma gidan tare da addu'ar Allah yasa ta yadda taci. Meenal ko na ganin D'anjuma ya fita ta tashi tafara naiman wayarta dan tun jiya da suka iso bata ganta ba,saidai abin da Meenal bata sani ba,mommynta tasa aka d'auke mata wayar su Hajiya Jamila suka tafi mata da ita. Babu irin naiman da Meenal bataima wayar ba amma bata ganta ba,zama tayi tai tagumi tana mai share hawayan dake zubar mata.Meenal na awannan halin ne D'anjuma ya yi sallama ya shigo da plate d'in indomie d'in da yasa asoyo mata.D'anjuma gefan Meenal yanufa zai zauna Meenal ta d'aga mai hannu da sauri tare da cewa "Malam karka kuskura ka zauna kusa dani wallahi!"D'anjuma fasa zama yayi ya mik'ama Meenal indomie da ya soyo mata . Meenal ko kallan plate d'in indomie bataiba sai cewa tayi "Ina zansamu waya ina son yin waya yanzun nan?." Shiru D'anjuma ya yi dan basu dad'e da gama waya da mahaifiyar Meenal ba akan ko tatanbayai waya karya bata,hakan yasa D'anjuma ya kalli Meenal ya ce "Wayata babu caji ki bari sai na samu caji"Waya na ke son yi yanzun nan,dan haka kota aro ka aro min ina buk'ata da sauri". Shiru D'anjuma ya yi sannan ya ce "Sai dai ki yi hak'uri gaskiya har lokacin da zan anso tawa Wayar dan ban iya aro ba". Meenal tashi tayi da saurinta ta jawo gyalanta ta yafa ta kama hanyar fita,D'anjuma da sauri ya tareta tare da cewa "Haba Meenal ina zaki keda bikisan kowa ba,kuma ko bama hakaba kefa Amarya ce bai kamata ki fita yau ba." Meenal jatai ta tsaya dan har sunajin saukar numfashin juna ita da D'anjuma ,dan sun yi kusa da juna sosai,Meenal cikin isarta da gadararta ta ce "Malam karka kuskura ka yi yin k'urin tab'ani fita kuma dole in fita alokacin da naso in dawo alokacin da naso ,kai baka isa kahanani yin abin da nayi niyya ba wallahi!". Meenal na fad'in haka ta bangaje D'anjuma da sunan ta wuce,sai dai D'anjuma ko gezau bai yi ba.Ganin haka cikin sanyi alamun lallashi D'anjuma ya ce "Dan Allah kiyi hak'uri ki zauna daga wayata tayi caji zan kawomiki kiyi amfanin da zaki ." Meenal da kema D'anjuma kallan tsananin raini dan dama ita mutum ce mai rana mutane ,hakan yasa cikin tsantsar rashin kunya irin tata da rashin ganin girman nagaba da ita ta ce "Kai D'anjuma kake ko D'anjummai yanzu nake son amfani da Waya dan haka bani hanya in wuce". D'anjuma da arayuwarshi ya tsani raini daurewa kawai yake da kuma nasihar kakan meenal Alhaji kenan da yake tunawa,shi yasa yakasa cema Meenal komai,amma wannan Karan yadda ta kira sunanshi atsananin raina sai ranshi yab'ace hakan yasa ya ce "Bari in kawo miki yanzu" D'anjuma na fad'in haka yafita,yana fita ya ciro wayarshi ya Kira mahaifiyar Meenal,bayan sun gaisane D'anjuma ya ce cikin sanyi "Mama dama Meenal fa ta amtsa akan saidai in bata Waya zata yi anfani da ita,dan harma ta d'auki mayafinta wai zata fita ta aro,yanzu haka dai sai cemata nayi bari in anso mata". Shiru Mahaifiyar Meenal ta yi sannan ta ce "Abdurrahman karka bata Waya kuma karka bari tafita,sannan duk rashin kunyar meenal da kake gani tana da tsoro sosai dole sai kana mata jan ido gaskiya kila zata rik'abin umarninka,amma indai kabari Meenal ta rainaka gaskiya bazakaji dad'inta ba,sannan dan Allah ka k'ara hak'uri dan nasan zaka yi fama ba kad'an ba."Mahaifiyar meenal na kaiwa haka ta kashe wayarta. D'anjuma ko gudin rigimar meenal bai koma gidan ba.Yana nan zaune ak'ofar gidan 'yan garinsu suka ciko mota guda wai sunzo ganin gidan Amarya.D'anjuma da fara'arshi ya tarbesu ya yi musu jagoranci izuwa cikin gidan ,amma a b'arin zuciyarshi cike yake da fargaba,dan yasan meenal bazataima 'yan'uwanshi tarba mai kyau ba. A tare suka jera suka shiga gidan.Zaune suka samu Meenal,saidai ko sallamarsu bata amsa ba bare kuma susa ran zata gaida su.Yayar mahaifiyar D'anjuma ce ta kalli Meenal da fara'arta ta ce"Saninu Amarya,ya kwanan b'ak'unta?"Meenal batare da ta kalleta ba ta ce"Lafiya"Tom da yake dama tun kafin dangin D'anjuma su je gidan mahaifiyar D'anjuma ta sanar da su halin matar D'anjuma d'in ,hakan yasa basu wani ji haushi cancan ba,a cewar su "D'anjuma ya d'ebo ruwan dafa kanshi". Haka suka gama kalle-kallan su dan sosai suka yaba da kayan d'akin da Iyayan Meenal duka zuba mata,duk da dama sun san 'yar mai kud'i ce D'anjuma ya aura.Iyayan D'amjuma da abokan arzik'i da aka zo ganin gidan Amarya sallama su kaima D'anjuma dake tsaye kunya duk ta damai ganin yadda amaryar tashi ta amshi 'yan'uwanshi .Haka dai cikin kunya ya yi musu sallama da godiya suka tafi. Bayan sun tafine Meenal ta kalli D'anjuma ta ce"Malam kace zaka aromin Waya amma kuma naji shiru"D'anjuma cikin damuwa ya kalli Meenal ya ce"Yanzu dan Allah abin da kikai ma 'yan'uwana kin kyauta!"Meenal kamar bata ji abin da D'anjuma ya ce ba ta ce"Baka ji abin da nace bane? Nace ina Wayar da kace zaka aro min?"Amina ba maganar Waya nai miki ba,maganar abin da ki kai ma 'yan'uwana nake miki, banji dad'in haka ba!"Meenal tashi tayi ranta b'ace tana kallan D'anjuma ta ce"Maganar da ta dameka kayi ,nima kuma maganar da tadaman nayi,sannan abu na k'arshe karka kuma kirana da Amina idan zaka kirani da sunan da kaji iyayena na kirana ka ki rani da shi,sannan zaka samar min Wayar ne koko inje in samar ma kaina?"D'anjuma da ranshi ya fara b'acewa da kuma tuna maganar mahaifuyar Meenal da y yi ya ce"Amina wai biki ji abin da nake miki magana akai bane?"Meenal batare da ta saurari D'anjuma ba ta buga tsaki ta juya ta yi hanyar fita.D'anjuma cikin jin zafi ya fusgo hanun Meenal ta dawo baya da sauri dan tama kusa fad'uwa,cikin jin haushin yadda D'anjuman ya fusgota ta ce"Kai wana irin bagidaj ..."Marin da D'anjuma ya yi ma Meenal ne yasa takasa k'arasa abin da tayi niyya, ta dafe gun dan har ganinta sai da ya d'auke.Meenal cikin azabar jin yadda taji Marin ta fashe da kuka,dan tunda take ba'atab'a mata mari irin wannan ba.Meenal cikin kuka ta kalli D'anjuma ta ce"Dan anta kurama mahaifina ya had'ani aure da kai shine kake ganin har ka isa ka d'aga hannu ka maran?Tom Wallahi Allah sai kasan ni ka mara ,kai ka yi kad'an ka maran mu had'u a kutu da ka ............. ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ Na Fadila Sani Bakori Page 31 "Dan an takura ma mahaifina ya had'ani aure da kai shi ne kake ganin har ka isa ka d'aga hannu ka maran? Tom Wallahi Allah sai ka san ni ka mara,mu had'u a kutu da kai!"Meenal na gama fad'in haka ta jawo mayafinta ta yafa tayi hanyar waje zata fita. D'anjuma da sauri ya sha gaban Meenal ya tare mata hanya.Meenal kallan D'anjuma tayi da jajayan idanuta ta ce"Ka bani hanya in wuce!" Ina za ki?"D'anjuma ya tambaye ta. "Ka ba ni hanya in wuce Malam!"D'anjuma cikin sanyi da kuma nadamar Marin Meenal d'in da ya yi ya ce"Ki yi hak'uri meenal raina ne ya b'ace yasa har nad'aga hannu na mare ki ,insha Allah haka ba zai k'ara faruwa ba"Wallahi sai na fita ,indai kaga na fasa fita a gidannan ,tom saidai in waya ka ban nayi waya da daddyna"D'anjuma dan asamu zaman lafiya yasa ya ciro wayarshi yaba Meenal.Meenal na amsar wayar ta bar gun ta Kira daddynta. Mahaifin Meenal na kwance kusa da mahaifiyar Meenal kira ya shigo wayarshi,saidai mahaifin Meenal yana d'agawa yaci karo da kukan Meenal.Dan Meenal najin daddynta ya d'aga Kiran ta fashe da kuka.Daddyn Meenal jin kukan Meenal a firgice ya tashi daga kwancan da yake,cikin rud'ewa yake cewa"Meenalyn daddy yi shiru kimin bayani me ya yi miki?"Meenal k'in magana tayi taci gaba da kuka .Mahaifin Meenal cikin rud'ewa ya tashi daga kishingid'an da yake yana cewa"Meenal lafiya?Ko wani abun ya yi miki?"Still dai Meenal ba tai magana ba tana mai ci gaba da kuka .Aifa nan take hankalin Mahaifin Meenal ya yi k'ololuwar tashi,cikin rawar hanun ya mik'a ma Mahaifiyar Meenal wayar ,alamun tayi magana da ita. Mahaifiyar Meenal itama cikin damuwa ta fara magana kamar haka"Haba Meenalyn daddy kinga kin tadama daddynki hankali nima kin tadamin,ki natsu dan Allah ki min bayani me ya faru da ke?" Meenal cikin kuka ta fara magana kamar haka"Mommy ki ba daddyna wayar!"Daddyn Meenal cikin k'osawa ya amshi wayar dan wayar a speaker take yaji abin da Meenal ta ce ,ya ce"Meenalyna inajinki fad'amin ya a kai?"Meenal cikin kuka ta fara magana kamar haka"Daddy dukana ya yi"Duka!?"Mahaifin Meenal ya mai-maita. D'anjuma ko na zaune yana kallan Meenal yana jin sherin da tayi mai.Mahaifin Meenal kuma cikin tsantsar b'acin rai ya kashe wayar batare da ya iya cewa komai ba.Idonshi jajir ya kalli mahaifiyar Meenal ya ce"Kinga abin da nake gudu tun farko ko? Amma Alhaji yak'i fahimtata,ace yarinya kwananta d'aya har ya farasa hanu yana bugunta!"Tom daddyn Meenal kadai yi bincike sannan,ni gaskiya bana tunanin yarannan zai iya sa hannu ya bigi...."Cikin tsawa daddyn Meenal ya ce"Ya isa haka! Kina son kice sheri tayi mai ko? Yanzu ko kukan da Meenal keyi bai isa yasa ki gane gaskiyar abin da ta fad'a ba,tom Wallahi yarinya d'aya bazan d'auka ba!"Daddyn Meenal nagama fad'in haka ya kashe wayar ya d'auki key d'in motarshi ya yi hanyar fita,da sauri Mommyn Meenal ta sha gabanshi ta ce"Haba daddyn Meenal da wowarka kenan fa! Ina zaka kuma?"Da yake da wowar daddyn Meenal kenan daga gudun auran Meenal da ya yi."Funtua zani"Ya bata amsa."Funtua kuma daddyn Meenal ? Me za kai a Funtua kuma?"Daddyn Meenal ba tare da yaba Mommyn Meenal amsa ba ya yi tafiyarshi. Daddyn Meenal misalin k'arfe 2:00Pm ya shiga cikin garin Funtua. Meenal ko dama tanajin daddynta ya kashe wayar tasan wajanta zaizo,dan tasan wannan kukan da tayi ba zai lamince shi ba,gashi rashin cin abincin da bataiba yasa ta kuma zama wata iri idan ka ganta sai ka yadda da abin da tace. Daddyn Meenal number D'anjuma ya kira. D'anjuma ko lokacin ya fita gidansu kenan ya hau mota zuwa Funtua.yana gaf shiga gida Kiran daddyn Meenal ya shigo mai .D'anjuma na d'aga Kiran daddyn Meenal ya ce"Gani a Jabiri ina ne gidanka?"D'anjuma shiru ya yi ,sannan ya ce"Daddy gani nima kusa da Jabirin bari in k'araso"D'anjuma na sauka a mota ya hango motar daddyn Meenal,k'arasawa ya yi kusa da motar .Cikin girmamawa D'anjuma ya gaida daddyn Meenal, amma ciki-ciki daddyn Meenal ya amsa mai ya ce"Muje gidan".D'anjuma shiga cikin motar ya yi yana nuna ma daddyn Meenal hanya har suka isa k'ofar gidan.Tare suka shiga gidan,Meenal ko najin sallamar daddynta ta fashe da kuka tana rik'e ci dan dama yunwa take ji kuma har yanzu bataci komai ba. Daddyn Meenal da saurinshi jin kukan Meenal ya idasa shiga d'an madai-daicin falon nasu.Yana zuwa cikin tashin hankali ya tarbo Meenal yana cewa"Meenalyna meke damunki?"Meenal cikin kuka ta ce"Daddy yunwa nake ji mutu zanyi daddy!"Daddyn Meenal kamar zai yi kuka ya ce"Ba za ki mutu ba Meenalyn daddy"Meenal cikin kuka ta ce"Daddy gida ka kaini gida "Daddyn Meenal tada Meenal yayi ya ce"Tom ki yi shiru tashi mu tafi"Meenal tashi tayi daddynta na rik'e da ta suka fita daga gidan D'anjuma na kallansu ya kasa cewa komai har suka b'ud'e mota suka shiga suka tafi ........ ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ Na Fadila Sani Bakori Page 33 & 34 "Sani in dai ni na haifeka,kuma na isa in fad'ima kaji,tom Amina ta tashi tabi mijinta su tafi"Daddyn Meenal kafin ya yi magana Meenal ta fashe da kuka ta ce"Daddy Wallahi ni bazan bishi ba!"Daddyn Meenal cikin sanyi ya fara lallashin Meenal ya ce"Meenalyna ki yi hak'uri ku tafi dan Allah"Meenal tashi tayi tayi shigewarta ciki ta barsu Daddaynta a nan. Alhaji cikin fushi ya kuma cewa"Sani kaima Amina magana yamma fa tana yi!"Daddyn Meenal tashi ya yi ya shiga d'akin Meenal d'in ,kwance ya sameta tana kuka.Daddyn Meenal k'arasawa ya yi ya kamo hannun Meenal d'in cikin lallashi ya ce"Meenalyn Daddy ki yi hak'uri ki koma kinji nan da lokaci kad'an ni zansa yadda za ai auran ya mutu ma gaba d'aya dan nima ba san auran naki nake ba, fad'amin yanzu meye damuwarki a komawar?" Meenal tashi tayi tana kallan Daddynta ta ce"Daddy ni fa bana iya cin abincinsu"Tom Meenalyna ba sai ki taida shi daga nan ba"Meenal tashi tai tana goge hawayanta ta ce"Daddy Allah indai ka matsamin na bishi tom Allah bana k'ara cin komai har yunwa ta kasheni in huta!"Daddyn Meenal cikin damuwa da jin abin da Meenal ta ce ya ce"A'a haka ma ba zai faru ba,yanzu inda har kin furta haka bari in je in ma Alhaji magana muji ya za ai" Daddyn Meenal falon ya koma ya kalli Alhaji ya ce"Alhaji kasan rigimar Meenal nayi-nayi tak'i Wallahi,k'arshe abin tashin hankali cewa tayi "In dai na matsa mata ta tafi tom bata k'ara cin abinci yunwa ta kasheta ta huta,tom Alhaji kasan Meenal ba hankaki gareta ba zata iya aikata haka,dan Allah inda abin yazo da haka yayi hak'uri ya tafi ni zan san yadda zan yi in kaita da kaina dan Allah Alhaji"Daddyn Meenal ya idasa maganar kamar zai yi kuka. Alhaji magana zai yi D'anjuma ya rigashi da cewa"A'a Alhaji babu komai ta zauna d'in kamar yadda Daddy ya ce idan ta yadda sai ya kawota nan gaba"Alhaji kai ya girgiza ya ce"A'a Abdurrahman baza ai haka ba,ni na san wacece Amina dan haka ta fito su tafi bana son shashansci kafin ranka ya b'ace kai da ita yanzun nan!"Abin mamaki kawai sai ga Daddyn Meenal ya zube ak'asa ya yana rok'on Alhaji yana cewa"Alhaji dan Allah kaimin wani taimaka inda Meenal ta riga ta tsani zaman garinnan nina san bazata tab'a kwantar da hankalinta ba,ni indai babu damuwa zan ba shi gidana da ke nan su zauna, kamar za tafi kwantar da hankalinta anan"Alhaji shiru ya yi sannan ya ce" Tom Abdurrahman kaji abin da Sani ya ce? Zaka iya aje Aminar anan Allah bashi shi da ya tsara hakan sai ya rik'a baka kud'in mota duk lokacin da ka buk'aci zuwan"Shiru D'anjuma ya yi sannan zuwa can ya ce"Shikenan Alhaji indai zamanta nan d'in zata kwantar da hankalinta ai ba komai bane"Masha Allah ,Allah ya yi maka albarka ,tom yanzu shi can gidan an gyara shi ne?"Alhaji ya tambayi Daddyn Meenal. "Eh Alhaji a gyare yake dan kusan wata biyu kenan ma nasa komai a gidan ,dan tun lokacin da akai maganar nasa komai da niyyar hakan tom amma kuma sai Mariya ta hanani sai da Meenal ta b'ullo da haka na tuna da gidan" Tom ai shikenan yanzu saika d'aukesu ka kaisu gidan" Daddyn Meenal bedroom d'in Meenal ya shiga,kwance ya sameta kamar yadda ya barta, kallan Meenal d'in yayi ya fara magana cikin lallami ya ce"Meenalyna kinga Alhaji ya matsa sai kinbi d'an'iskan yarannan dan haka kiyi hak'uri yanzu naima Alhaji magana zaku zauna a gidana da ke nan Tudunwada"Meenal tura baki tayi ta ce"Daddy nifa ko inane bazan zauna da shi ba "Daddyn Meenal zama ya yi yana kamo hanun Meenal d'in ya ce"Haba Meenalyn Daddy yanzu idan na koma nace ma Alhaji haka ai bazai yadda ba, cewa ma zai sai kin koma can Funtuwan ma,amma kinga idan ki kai hak'uri ki ka zauna can Tudunwadan ahankali-ahankali sai in kashe auran ma baki d'aya"Haka Daddyn Meenal ya yi ta lallab'a Meenal da kyar ya samu ta yadda ta tashi suka tafi. Driver Alhaji mai dashi gida ya yi inda shi kuma Daddyn Meenal d'in ya d'auki Meenal da D'anjuma a mota suka nufi Tudunwada,ko a mota Daddyn Meenal kallan D'anjuma yayi ya ce"Kai D'anjuma ka gane ko Meenal yarinya ce dan haka indai kana son zama da ita dole za kai hak'uri da ita,dan muma hak'uri muke da ita ,in banda abin ka ma Meenal nawa take da har zaka wani d'aga hannu ka mareta,in ban da kai ba lallab'ata za kai ba ku zauna lafiya inda kaga dai yadda akai auran nan ba sonka take ba matsawar Alhaji ce,ai duk abin da tace bi za kai asamu ta hak'ura ta zauna,amma dan shashanci irin naka shine zaka mareta,waya cema irinsu Meenal haka ake musu ai lallab'ata zakai ku zauna lafiya"Haka Daddyn Meenal yayi ta yima D'anjuma nasiha akan ya lallab'a Meenal su zauna lafiya har suka isa gidan nasihar kenan. Gida ne mai kyau dan dai bai kai wanda su Meenal suke ciki ba.Daddyn Meenal har falon ya kaisu sannan ya kalli Meenal ya ce"Tom Meenalyna zan tafi?"Meenal turo baki ta yi ta ce"Daddy Kayan sawana fa? Banda kaya fa?"Tom ki yi hak'uri gobe zan siya miki in kawo miki"Haka dai Daddyn Meenal ya tafi yana mai lallab'a Meenal kamar wata 'yar jinjira. D'anjuma ko zama ya yi yana mai tunanin yadda zai b'illo masu Meenal ,tabbas yana son Meenal tom amma a yanzu ya fara tunanin hak'ura da ita,amma kuma yana tunanin in ya ce zai saki Meenal tom bai kyauta ma Alhaji ba.D'anjuma na nan zaune sai tunane-tunane yake har aka kira Sallar La'asar sannan ya fita yaje ya yi sallah ya dawo. Meenal ko dama tun da suka shigo tai shigewarta ciki tabar D'anjuma a nan falon shi kad'ai.D'anjuma na nan har akai sallar Magriba,fita ya yi bashi ya dawo ba saida yayi sallar Isha'i a can, sannan ya je wani restaurant da ke kusa da masallacin yaci abinci. Har zai sema Meenal sai kuma ya tino mutuniyar tashi zata iya cewa wani abun take so,hakan yasa ya fasa ya dawo.D'anjuma bedroom d'in Meenal ya shiga,kwance ya sameta tana danna wayarta da Daddynta ya amsa ya bata.D'anjuma da sallamarshi ya shiga,amma Meenal ko sallamarshi bata amsa ba bare kuma yasa ran zata d'ago ta kallai.D'anjuma zama ya yi gefan gadon,sannan ya ce"Kin yi sallah ko?"Meenal banza ta yi da D'anjuma,shi kuma bai gaji ba ya kuma cewa"Amina na ce kin yi sallah ko?"Meenal cin jin zafin ya dameta ta tashi a fad'ace ta ce"Ban yi ba,kasanni Kristen ce bana sallah!"D'anjuma fisge wayar hannun Meenal ya yi ya ce"Tom ki tashi kiyi sallah sannan kici gaba da danna-dannan wayar taki"Ka ban wayata Malam!"Ba zan baki ba sai kin yi sallah"Meenal cikin tsiwarta da tashan rashin kunya da take yi ta ce"D'anjuma ka ke ko D'an'asabe kaban wayata Wallahi kafin raina ya b'ace!" D'anjuma da sosai yake jin zafin duk lokacin da Meenal ta kirashi da D'anjuma yake ko D'an'asabe,duk da itama Meenal lura da yana jin zafin hakan ne yasa take kiranshi da sunan.D'anjuma juyawa ya yi ya fita ya ce"Idan kin yi sallah ki zo ki amsa,sannan me zaki ce in siyo miki?" Har'abada ni Meenal bazanci abin da yafito daga hannunka ba, sannan kaban wayata wannan ma ai salan sata n...."Jawowar da D'anjuma ya yi ma Meenal ce tasa ta yi shiru,D'anjuma kuma cikin d'aurewa da nuna tsantsar b'acin ranshi ya ce"Wallahi koda wasa kika kirani b'arawo saina fasa bakinki!" Sannan ya saketa ta fad'i.Shi kuma ya fita d'akin ranshi b'ace sosai. Meenal gyalanta ta d'auka zata fita.D'anjuma na zaune yana kallanta ya ce"Amina karki fita daga falon nan!"Meenal wani mugun kallo taima D'anjuma sannan ta ce"Ko a gidamu abin da nake so nake yi dan haka kai baka isa kahanani yin abin da nai niyya ba"Meenal na fad'in haka tasa kai tayi tafiyarta ita ala dole gida zata koma saboda ya yi mata tsawa ya amshe wayarta ya ce sai tayi sallah. Meenal ta kama k'ofar gidan zata fita D'anjuma da gaba d'aya yake jin Meenal d'in ta na naiman fice mai arai dan shi mutum ne mai fushi.D'anjuma fusgo Meenal yayi ya jata ya maida ta falon ya wurgata kan coution d'in ya ce"Haba Amina ke wata irin yarinya ce ,ace tun da na aureki na rasa sukuni,shin so haukane?Koko dan nace ina sonki shine kike ganin kinsamu damar da zaki wulak'antani! Taya zaki rik'a zuyani kamar d'anki! Kin taho nan Kaduna bada izinina ba ko sanina,na kwaso jiki na biyoki ,kince bazaki koma garinmu da zama ba na yadda zan zauna inda kike so ko hakan zaisa asamu zaman lafiya amma duk da haka haka bai miki ba yanzu kuma kin kuma tada wata rigimar tom ya ki ke so in miki?"Meenal kallan banza taima D'anjuma sannan ta ce"So nake kasakan shikenan sai ka samu sukunin zuciya "Amina tabbas ina sonki amma bacin halaccin Alhaji agareni da nake dubawa da Wallahi tun tahowarki zan sake ki tom Amma Alhaji ya yi min halacci sosai a auranki"Meenal tsak'i tayi ta ce"Ni bana son ina doguwar magana da kai, matsamin in wuce dan tunda nasa ran fita agidan nan Wallahi bazan kwana ashi ba!"Meenal na kuma fad'ar haka ta kuma tunkarar k'ofar zata fita . D'anjuma hannu yasa ya d'auki Meenal ya yi cikin gidan da ita.Meenal ko haka ta dake tana zaginshi tana cewa"Allah ya isa tunda ka sa k'azamin hanunka ka d'aukeni ".D'anjuma ko bai dire Meenal a ko ina ba sai bedroom d'inta, yana direta ya ce"Ni kike ma Allah ya isa !Kina kirana k'azami ko?"Meenal cikin tsantsar ranshin kunyarta ta ce"Eh d'in ,ance Allah ya isan k'azami kawai" D'anjuma fisgo Meenal ya yi sannan ya had'e bakin shi da nata yana tsoso yana k'ara d'ura mata miyan bikinshi abakinta saboda k'azamin da ta kirashi.D'anjuma sai da ya gaji dan kanshi sannan ya saki Meenal da ta fashe da kuka tana mai goge bakinta tana cewa"Allah ya isa banza d'an k'yauye ! Mai tabi'ar dabbobi!"D'anjuma da duk yadda yaso ya danni zuciyarshi ya yi hak'uri kasawa ya yi ,rasa hukuncin da zaima Meenal ya yi.Jawota ya yi yana cewa"Zan nuna miki tabi'ar dabbobi" D'anjuma na fad'in haka ya fincike d'an kwakin kan Meenal sannan ya fara k'ok'arin cire kayan jikinta.Sai da D'anjuma ya cire komai na jikin Meenal .Da farko tana zaginshi da taga abin ya yi nisa ta fara bashi hak'uri.Amma D'anjuma bai saurareta ba,sai da ya gama ya cire na jikinshi sannan ya ya d'auketa tana ihu ya d'orata kan kadon ya na ce mata cikin kunnanta "Zannuna miki t'abi'ar abbobi yanzun nan"Meenal ganin D'anjuma da gaske yake ta ce"Wallahi idan har kayi kuskuran min wani abu zaka had'u da fushin Daddyna dan Wallahi ba zai k'yaleka ba"Meenal ta fad'i maganar cikin kuka da tashin hankali ."Ni da kayana ,zan yi yadda nake so dake babu abin da Daddynmu zai min"D'anjuma na fad'in haka bai k'ara ba Meenal wata damar yin Magana ba sakamakon had'e bakinsu da ya yi.Meenal naji nagani haka D'anjuma ya amshi hak'inshi ta k'arfin tsiya......... Idan kin shirya siye kiyi hanzari free pages ya kusa k'arewa sister. Number marubuciyar 08063830828 ๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ Na Fadila Sani Bakori Page 35 Asubar fari kukan Meenal ya farkar da D'anjuma daga bacci.D'anjuma cikin kulawa ya kamo Meenal yana cewa"Ayyah yi hak'uri Meenalyna ki bar kuka haka dan Allah kar kanki ya yi ciwo"Meenal hanun D'anjuma ta bige da ke rik'e da ita ta samu ta yunk'ura ta tashi ta shiga toilet d'in t ta yi wanka.Meenal har tayi wanka ta gama tana kuka. B'angaran D'anjuma kuma bai kuma komawa ta kan Meenal ba sai da ya kimtsa jikinshi shima ya yi wanka ya yi sallah sannan ya dawo inda Meenal take har yanzu tana mai ci gaba da kukanta.D'anjuma cikin sanyi ya kamo hannun Meenal d'in ya ce"Amina dan Allah kiyi hak'uri da kukan nan ni na yadda ki yanke min duk hukuncin da ya yi miki indai zaki bar kukan kar kanki ya yi ciwo"Ina wayata?"D'anjuma sanin ko ya ba Meenal wayan Daddynta zata kira ta tona mai asiri yasa ya k'i bata wayar ya ce"Amina idan na baki wayar me za ki da ita? Idan wani abun kike buk'ata ki fad'amin zan kawo miki yanzu?"Meenal cikin goge hawayanta ta kuma tsantsar tsanar D'anjuman da take ji ta ce"Wallahi Allah sai ka yi da kasanin abin da kaimin! waya kuma kaje ka rik'e ,bazan d'an gidan talakawa wanda bai gaji arzik'i ba,indai ka cika kai D'an halak ne ka sakan yanzun nan!"D'anjuma murmushi ya yi mai ciwo dan Meenal ta kaishi bango.Jajayan idonshi ya d'ago yana kallan ta ya ce"Amina tabbas ni d'an halak ne,saki kuma da kike magana ba wai sai na sake ki bane ya tabbata ni d'an halak ne,abin da zan yi in nuna ni d'an halak ne shine duk da kika kasance ke d'in ba mai tarbiya bace in daure in zauna da ke d'an in nuna ma Alhaji ni d'an halak ne kar in watsa mai k'asa a ido,amma bacin haka ke baki da abin da ni zan so ki har in nace miki, saboda ko ta ina baki da tarbiyar !Sai yanzu nake danasanin bijere ma shawarar iyayena da nayi na auranki ,sakarya kawai shashasha!"Meenal cikin tsiwa irin ta cikakkun marasa kunya ta ce"Ashe kaima baka da tarbiyar inda har b'akar matar nan mai kama da kai ta hanaka aurena amm...."Maganar Meenal mak'alema ta yi saboda dukan da D'anjuma ya kai mata ko ta ina.Meenal tun tana zagin D'anjuma har ta fara bashi hak'uri da taji wayi.D'anjuma ko saida ya yi ma Meenal dukan da ko magana ta gagareta sannan ya rabu da ita,ya zuk'unna kusa da ita yana kallanta ya ce"Saboda ki tabbatarmin baki da kunya shine zaki kalli cikin idona ki kira mahaifiyata da sunan banza ko?"Meenal da gaba d'aya take tsoran D'anjuma ya kamata kaita ta girgiza mai.D'anjuma kuma cikin fushi ya kuma cewa"Saki kuma ba zan sake ki ba! duk inda zaki ki je!Amma fa ba wai dan ina sonki ba,kawai dan in baki abin da kika rasa agidanku ne wato tarbiya,sai na koya miki yadda ake magana da manya sakarya kawai shashasha!". D'anjuma nagama fad'in haka ya juya ya fita ranshi b'ace . Meenal ko da jikinta ko ina ke rawa dan sosai ta bugu.Tana ganin D'anjuma ya fita ta tashi ta lallab'a ta sa ma yafinta ta fita gidan da sauri tana fita ko taci karo da mai Napep ta tare ta hau. Meenal na sauka kud'in da ke hannunta taba mai Napep d'in.Haka ta fara takawa kad'an-kad'an ta shiga gidansu ,lokacin Daddynta da Mommynta na breakfast.Dukkansu da sauri duka d'ago jin kukan Meenal da sasafe haka............. Meenalyn Daddy a nan free page ya k'are sister , idan kina buk'ata zaki magana da marubuciyar ta 08063830828 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels