An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: *♡ YA ABIN YAKE? ♡* Na Nazeefah Sabo Nashe 08033748387 Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e E.O.W _Yauma tafe nake da wani sabon rubutun wanda salonsa ya bambanta da waɗancan kamar yarda dai kuka sani. Fatana na nishaɗantar daku na kuma wasa muku ƙwaƙwalwa Sabon littafi kenan Mai Sabon Salo..._ _Daga jin sunansa kun san akwai rikita-rikita ku dai ku biyo.. ina masoya *ME ZAN YI DA ITA?.*_ Page 1 Kamar yarda ta saba tashin y’arta ta kullum, yau ma ranta a b’ace take shurinta da k’afa tana dukanta wai duk so take ta tashi. Da kyar Hamda ta bud’e idonta ta zuba su akan mahaifiyarta. Zazzafan zazzab’ine a jikinta amma hakan bai sa ta d’aga mata k’afa ba. Ta bud’e idonta da kyar da duk sun canja launi na azabar da take ciki, ba yau bane mafari haka dama can Ammin take tashinta daga barcin a kowace asubar fari, tamkar ba mahaifiyar da ta tsuguna ta haifota duniya ba. Duk da a kullum tana tantamar kasancewarta tsatson Ammin,saboda tsana muraran da take nuna mata, wanda ko ƴar tsintuwa sai haka a yarda Ammin take ɗaukar lamarinta. Hawayen idonta ya zuba akan fuskarta, da gaske tana jin ƙunar lamarin sau tari Mahmah da ta ksance kishiyar uwarta tafi lura da lamarinta fiye da Ammin koda kuwa a ɓoye ne don idan ta fuskanci ka na tausaya mata ma tsanarka take sosai ta kuma ja maka kashedi game da shiga shirgin yarinyarta. Da kyar ta miƙe zaune bayan ta dafa yaloluwar katifar ta irin ta ƴan boarding da take kwana akai ita ɗin ma tatace ta makaranta take kwana akai bayan gama karatunta. Hannayenta dafe da goshinta alamar kanta yana matuƙar sara mata ta ce "please Ammi wallahi yau da ciwon kai na tashi ba zan iya komai ba." haɗe rai tayi idanunta cikin nata tace "ƙwarai tunda yau kika saba aikin da ciwo a jikinki kin tashi ko sai mangareki?ai tunda kika sake kika zo duniya duk da ba ke naso haifa ba wallahi kin yi ta shan baƙar wahala kenan, ko kaɗan bana son na buɗe ido na ganki na tsaneki tsana mafi muni da ban taɓa yiwa wani ita ba, ki miƙe bakinki alaikum kije ki fara aikin da kika saba." Da kyar ta miƙe zuciyarta na wani irin hanƙaron ɓacin rai ta zuba idonta akan gadon da yake bedroom ɗin yayyenta ne zube su uku suna shan barcinsu akan gadajen da suke zube reras a cikin faffaɗan bedroom ɗin.. kuma duk babu wanda bai bata shekaru ba a Cikinsu babbar ta bata ak’alla shekara goma mabiyarta Ta bata shekara takwas yayinda wacce take bi ta bata shekaru shidda cif. Kuma duk ba suyi aureba. Yayarsu Najwa ce kawai mai aure a d’akin su. Hawayenta Ya sake ninkuwa fiye da nada, ta rasa me tayiwa Ammi da tayi mata wannan muguwar tsanar ga yayyenta nan zube bata saka su aikin ba sai ita da take ƙaramarsu, madadin auta da aka sani da riritawa ita mahaifiyarta wulaƙantata take tana kuma nuna mata tsana muraran da gaske bata sonta. Ta faɗa a gaban idonta ta faɗa a bayan idonta. Hasashe kala-kala tayi tana son gano dalilin tsanar sai dai sam bata ci ribar gane gaskiya ba. Bata Sani ba Ko don kasancewarta baƙa saɓanin su da suka kasance farare tas dasu don kalar Ammin suka ɗauko gaba ɗaya kasancewarta balarabiyar jordan, Gashinta yalolo suka ɗauko saɓanin ita da ta zamo kalar mutanen Habasha, Gashinta kuwa.cunkus yake ga taurin tsiya don ko kitsashi ba a iya yi, sau tari haka take ƙudunduneshi ta cusashi a tsakiyar kai yayi mata kamar gammo. Ba ta yiyo kyan Ammi ba ko kaɗan bata sani ba ko wannan shine silar tsanar, duk da ta sha ji mutane da Dama suna faɗin tafi ƴan uwanta kyau don dai ita ƙananan kyau ne da ita ta kuma fi ƴan uwanta dirin jiki sosai da sosai. Bata san dalilin tsanar ba duk da tana kyautata zaton wannan ne dalilin saɓanin hasashenta taji kuma mutane da dama suna faɗin don taso ta haifi mace ne a haihuwarta kamar yarda kishiyarta tayi mata fintinƙau a haihuwar yara maza to rashin zuwanta a namiji tun bayan da aka yi mata scanning aka tabbatar mata namiji ne ta 'kwallafa rai Lamarin Allah kuma ranar haihuwar sai taga mace itama macen Gata kalar mutanen Habasha bata da Haske kamar larabawan da ta saba haifa ba. Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi bayan Ammin ta hankaɗa ƙeyarta cikin ƙaraji ta ce"wuce kafin naci ubanki, so kike ki tona min asiri ya dawo daga masallachi ya tarar kina aiki ya hau min banbamin masifa." Tana hawayen ta shige kitchen. Ga wani mukumukun sanyi da ake zubawa mai shiga jiki. Don haka ruwan famfon ya zama tamkar ƙanƙara. Taɓashi kuma da tayin shi ya sake haddasa mata rawar ɗari take kuma zazzafan zazzaɓin ya sake sabunta a jikinta. Tana hawaye ta shiga wanke kwanukan sannan ta gyare kitchen ɗin tsaf bayan ta kunna karatun Alƙur'ani kamar kullum kafin kiran sallah na shigar lokaci ta gama da kitchen tsaf sannan ta shige bedroom don gabatar da sallah, bayan ta ɗaga katalalliyar katifarta ta ɗau panadol ta ɓalla ta sha saboda dama duk ciwon da zata yi shine dai maganinta ba wanda ya damu ya kaita asibiti taga likita itama tuni ta saba. Panadol ɗin ma Munirah yayartace take siya mata ta ce ta ɓoye saboda in dai Ammi ta gani ita kanta ranar kashinta ya bushe. Toilet ta shige tayi alwala sannan ta fito ta fara tashin ‘kartin yayyanta don duk sun gama degree suna zaune ba aure Muneerah ce kawai a level 2 ita kuwa wannan shekarar ta gama secondary school d’inta.suna zaman jiran ministoci ko sanatoci ko ma shugaban k’asar gaba d’ayansa. Kuma Ammin ce ta da’ure musu k’ugu. Ganin rawar d’arin da take yasa Muneerah ta kalleta cikin muryar tausayi ta dafa kanta kafin tace “Sorry Little jikinne?” Lumshe idanunta tayi zara-zaran gashin idon suka yiwa idanunta rumfa sai ga tarin ‘kwalla sun zubo mata. Ta tada Sallah kawai da sauri jin Ƙafafunta sun fara shirin gaza ɗaukarta, yasa ta zauna tayi sallahr a zaune. Suna idarwa zazzafan zazzaɓin ya sake mata rufdugu amma tsoron masifar Ammi yasa ta dole ta miƙe ta fita don gyaran gidan. Muneerah ce tabi bayanta da sauri don dama kullum ita take tayata aikin gidan a ɓoye don idan har Ammi ta gani to ta tabbata ranar kashinta ya bushe. Wajen zuwa zubar da sharar da take dustbin ɗin kitchen ɗin, sanyi ya kaɗata sosai take ta yanke jiki ta faɗi haƙoranta na kafkaf saboda kakkarwa ga idanunta da suke shirin ƙafewa. Mahmah kishiyar Ammi da take tsaye a window ta saka salati da sauri ta fito daga sashenta ta ɗaga Hamda ɗin tana kiran Sunanta amma ina tuni numfashinta yayi sama, hakan yayi daidai da shigowar Abbu daga masallachi da sauri ya ƙaraso yana tambayar lafiya? Cikin muryar ruɗewa. Mahmah ta nuna masa Hamda da take yashe a cinyarta, bai gama jin bayaninta ba ya sunkuceta da sauri yayi parking space da ita Mahmah tabi bayansa kasancewar da dogon Hijab a jikinta. ____________________________ Likitan yayi gwaje-gwaje da yawa kafin ya tura su ayi mata test ɗin typhoid da malaria. Suna dawowa ya buɗe takardar cikin ɓacin rai ya ɗago yana kallonsu ya ce "Me yasa jama'a basu da tausayine? Yanzu haka wannan yarinyar mai aiki ce ko marainiya ko kuma wacce uwarta bata gidan aka bari ciwo yayi mata mummunan kamu haka? Typhoid malaria ga pneumonia tayi mata mummunan kamu wanda idan ba'a kiyaye ba nan gaba kaɗan zata iya zana asthmatic." kunya da takaici ne suka yiwa Abbu rufdugu lokaci guda ya rintse hannunsa da kyau Yana jin zuciyarsa kamar zata hudo don Ɓacin rai. Tabbas Sakinat ta cuce shi bai tabbatar ita jahila bace har sai da ta haifi yarinyar nan, yau kuwa zai nuna mata zahirinsa idan da baɗininsa ta sani. "Admitting ɗinta zan yi" likitan ya faɗa ransa a ɓace don sosai yaji tausayinta ya kamashi. Abbu ya jinjina masa kai kawai don baya jin yarda yake jin zuciyarsa zai iya furucin ko da kalma ɗaya ne. Sai da suka shiga ɗakin ya kalli Mahmah ya ce." ki daure ki zauna min da ita don na san ko na ce tazo ma ba zuwa xa tayi ba wallahi, na gaji da halayen Sakina a dole nake zaune da ita." Mahmah murmushi tayi tana gyarawa Hamda hular da take kanta ta ce"Ni wallahi Abbu na rasa silar wannan tsana ni fa bana jin ko ɗan kishiya aka bar min zan yi masa wannan abin da Sakina take yiwa yarinyar nan da tunda tazo duniya bata barta ta huta ba. kuma tun ranar da ta haifeta da ta’ki Shayar da ita nace ta bar min ita amma ta’ki sannan kuma ita bata yi mata ri’ko mai kyau ba bata tunanin Allah ya kamata da ha’k’kinta?” Abbu ya girgiza kai “Tsabar jahilcine da jayayya da hukuncin ubangiji, Idan banda haka kace kai lallai ga abinda kake so ka haifa da baka samu ba kuma sai ka d’aura tsana akan wanda Allah ya baka Allah dai ya kyauta amma yau kam zan shayar da Sakina ruwan mamaki.” Daga Haka ya fice ya bar Mahmah rik’e da hannun Hamda da ake ‘karawa ruwa. Daga yanayin parking d’in da yayi duka ma’aikatan gidan suka tabbatar ba lafiya ba, ko amsa gaisuwar da suke masa bai yi ba ya danna kansa sashen Ammi, a masife ya shiga k’wala mata kira. Da sauri ta fito k’irjinta yana dukan uku-uku don ta tabbatar ba lafiya ba. turus tayi a gabansa tana kallon yarda yake nuna ta da yatsa cikin tashin hankali ya ke fad’in “Ban tabbatar jahila na aura ba Sakinah sai bayan da kika haifi Hamda to ina tabbatar miki ko ki canja takunki ko kuma wallahi Na guntule igiyar aurena da take kan ki wacce irin masifa ce wannan? Saboda son zuciya kin tattara tsanar duniya kin zuba akan ‘diyata don tazo a mace ita ta halicci kanta? kuma Sadiya tana son rik’eta kin hanata saboda kin fi son ta zauna a wajenki ki cigaba da gallaza mata, ga shi nan mummunan ciwo yayi mata dirar mikiya to wallahi ki tabbata idan kika yi sanadiyyar rasa ranta wallahil azim sai na makaki kotu da sunan makashiyar ‘yar da ta haifa ta cikinta. Na gaya miki na sake jaddada miki, ko su wa’dancan kitika kitikan ‘yan matan da kika ajiye a ‘daki kika hanasu aure kuna jiran mai ku’di mai suke yi da ba zasu yi aikin ba sai ita ‘yar shila Na sake jaddada miki ki fita sabgar yarinyata kuma daga yau ta koma hannun Sadiya tsakaninki da ita kallo daga nesa idan kuma kin k’i ina tabbatar miki a bakin aurenki shashashar banza da bata yarda da k’addara ba.” Ammi ta bi bayansa da kallo tana sakin tsaki a fili tace “Aikin banza ni na zata ma wani abin tashin hankalinne ya faru yake samba’do min kira ashe akan waccar banzar ‘yar ce da ban k’i ko yanzu naji ance ta mutu ba da ina ji don murna har taka rawa zanyi.” Muneerah da take gefe tasa hannunta ta d’auke hawayen da yake bulbula a idonta a zuciyarta ta dinga nemawa ‘yar uwarta sau’ki da addu’ar shiriya ga mahaifiyarta, da take tunanin kamar Aljannu sun shafeta lamarin Ammin yana bata tsoro mutum ‘daya ne yake iya tan’kwarata in dai yana gari Yaya Hammad to shi kuma rabonsa da Nigeria ma an doshi shekara shekara Goma sha biyu kullum sai dai matarsa tazo amma ko y’ay’ansa baya bari su zo. tun wani mummunan duka da tayiwa Hamdan ransa ya ‘baci ya shiga gaya mata magana har da kusan marin Ammin yayi kuma a gaban kowa ya kirata jahila, shikkenan bayan kwana bakwai ya tattara ya tafi Birmingham dake k’asar England inda a can zai nemi Aiki. yafi sati ma a abuja kafin lokacin da visar sa ta fito shikkenan bai sake waiwayar Nigeria ba idan bata manta ba lokacin Hamda bata fi shekara Hud’u ba.Ta saki ajiyar zuciya a hankali ta furta Allah ya dawo da kai lafiya Ya Hammad don tabbas Ammi shi kad’ai ne yake tan’kwarata akan Hamda. Tana gama break fast wanka kawai tayi ta zuba na asibitin a cikin basket ta fito da sauri don nufar asibitin da aka kwantar da ‘yar uwarta. Murd’a ‘kofar yayi daidai da fitowar Ammi daga corridor d’in bedroom d’inta ta zubawa Muneerah wani banzan kallo kafin ta ce “Gidan Uwar wa zaki kai abincin nan?” Muneerah ‘kirjinta ya buga sosai tana kallon k’asa tace “Asibiti zan kai...” “Da izinin uban wa?”........ [1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on ArewaBooks @nazeefah ELEGANT ONLINE WRITERS (Haɗin kai shine takenmu.) _2 ⭐️⭐️ Tuni hawaye ya b’alle daga idanun muneerah jin Abbu ya ce cikin zafin rai "Da izinin ubanta, kin ga sakina ki kiyayeni wallahi, ke Muneerah zo ki wuce kije kinji Allah yayi miki albarka.” Fuskar Ammi a ɗaure take jifa masa kallo mai cike da bala’i. Ai kuwa Muneerah na fita ta sauke kwandon masifarta a kansa. “Na fa gaji da wannan rainin hankalin naka ba zaka dinga juyani kamar wata Ƴarka ba, ban maka dole ka zauna dani ba, haba ina dalili kayi ta sakin nawa mana sai me? Daɗin abin ba cusa maka ni aka yi ba, har ƙasar mu kaje ka yaudaro iyayena ka auro ni." tsaki yaja kawai ya fice yana jinta tana sake faɗar aikin banza, kuma wallahi ba wata shegiya da zan bari ta riƙe min ƴa, a barni idan ma kasheta zan yi na kasheta ai ta wace." Abbu girgiza kai kawai yayi, yana mamakin Sakina da ko kaɗan bata jin nauyin furta masa duk maganar da tazo bakinta. A kullum kuma sai tayi wannan zancen na ba cusa masa ita aka yi ba, wanda yasan gori ne kawai take wa Sadiya tunda itace aka yi musu auren haɗi. A zahiri ya ce "Ai fa, ko baki faɗa ba da zan iya nima da na sahhale miki, saboda na gaji da matsalolinki matsalar ɗaya ba zan iya ba, duk wannan hargagin a baki ya tsaya Allah ya riga ya jarrabeni da tarin ƙaunarki da ya riga ya zama jinin jikina, bana jin ma zan iya rayuwa babu ke, amma shi kaɗai ya san wahalar dashi da take amma a haka yake rufe idonsa daga aikata adalci tsakaninta da kishiyarta duk da tarin haƙuri da biyayyar da Sadiya take masa amma sam baya mata so koda kashi ɗaya cikin goman da yake yiwa Sakina, ya rasa irin wannan masifa ko fushi tayi dashi yana rasa sukuni har sai ta sauko yaga murmushinta sannan ya ke sakin ransa da samun kwanciyar hankali. Bai sani ba ko don kasancewarta daga jinsin larabawa,shi yasa ya ke mata kallon tafi sauran mata? _________________________________ Da sauƙi sosai a yanayin da ta samu jikin ƴar uwartata. Muneerah ta sakar mata cute smile kafin cikin tsananin ladabi ta durƙusa ta gaida Mahmah, ita dai tana ganin mutuncin matar nan duk da ƙoƙarin cusa musu tsanarta da Ammi take. Sadiya ta shafa kan Muneerah kafin ta furta "ƴar albarka yau ba'a tafi Islamiyyar ba?" murmushi ta saki tana ajiye basket ɗin hannunta ta ce "Zuwa nayi na zauna kije gida ki huta kada su Humaid su buƙaceki don na jiyo rigimarsa ma da zan fito da na tambayi Saliha mai aiki sai ta ce wai Islamiyya ce ba zai je ba." Riƙe haɓa Mahmah tayi tace "Kiji min ja'irin yaro amma Humaid akwai ɗan kirki shikkenan bari naje na dawo bayan la'-sar sai na kwana da ita, kinga ai ba za'a barki ke kaɗai ba naga ma jikinnata da sauƙi ƴar nema ta sha allurai." Ta faɗa tana shafa gefen kumatun Hamda da haka kawai take mata wata irin ƙauna ji take kamar jininta kamar kuma daga tsatsonta ta fito. Hamda ma rintse ido tayi tana ayyana da ana shawara da mutum kafin yazo duniya da tace ita tafi son zuwa a tsatson Mahmah mace saliha mai kyautayi jin ƙai da bata ɗau duniya a bakin komai ba. Banda tata uwar da ta tattara duk saɓanin halayen Mahmah a hankali ta ce "Nagode Mahmah sai kin dawo." Haɗe rai Mahmah tayi tace "Kul na sake ji, ba godiya tsakaninmu yarda na ɗauki ƴaƴan cikina haka na ɗaukeku, zan iya yi muku duk wata hidima da ta kama uwa zata yi ga ƴaƴanta Ubangiji Allah yayi muku albarka gaba ɗaya." suka amsa da ameen gaba ɗaya suna bin bayanta da kallo har ta fice daga bigiren da suke. Muneerah ta saki ajiyar zuciya a fili ta furta Mahmah Uwace ta nunawa ayi alfahari da ita ubangiji ka shiryi Ammi itama. Hamda runtse ido tayi kafin ta ce ameen cikin rawar murya da gaske tana jin raɗaɗin da ya ninka na Muneerah a ranta. Da yamman kuwa Sadiya ta yakice duk wasu tarin ayyukanta duk da yawan da suka yi mata, kasancewar Didi mahaifiyar mai gidansu a gobe ake saka ran zuwanta daga ƙauyen Gwarzo kamar yarda ta saba duk shekara a watan azimin tsofaffi take zuwa sai kuma ta tafi bayan sallah babba bayan ta dawo daga aikin Hajji. Idan kuka lissafa zaku ga wata shidda take a kano tayi watanni shidda a gwarzo. Macece mafaɗaciyar gaske kuma idan tazo duk wani iya shegen Ammi sai dai tayi shi a bayan idonta kasancewar ta san ba ita bace ƴar gaban goshinta asali ma tun sanda ta bayyana muraran a matsayin matar ɗanta ta nuna mata tsana ba tayi farin ciki ba sam da auren nasu. Duk da dai bata nuna mata baƙin hali amma fa kaifi ɗaya ce kana yi zata kiraka ta gaya maka gaskiya ko mai zaka yi kuwa. Ga shi Allah ya zuba mata kwarjini da duk tsaurin idonka baka isa ka kalleta ka gaya mata magana ba sai dai a bayan idonta. Ba kuma ta son ƙazanta kuma duk sanda tazo dama janye Hamda take ta mayar sashenta. Ƙyale Sakina kawai tayi ba don tafi ƙarfinta ba sai don tana son taga ƙarshen rashin mutuncinta, tana so kuma ubangiji ya shayar da ita ruwan mamaki shi yasa ma bata ɗauketa ba don idan ta ɗauketa tabbas Sakina taci riba a wajensu tunda ta bayyana ƙarara kenan ita take juya su. Shirye-shirye da gyaran ɗakin ya hana Mahmah zuwa asibitin sai bayan ƙarfe biyar, sannan ta tafi bayan ta tura Humaid gidan yayansu na biyu Hamidan ya kwana, don idan ta barshi da Saliha wahala zai sha, da Hamood yana nan ne ma da sauƙi to ya tafi karatu can ƙasar Egypt. Da Abbu suka tafi asibitin, suka bar Ammi a jikin window sai cizon yatsa take ganin yarda suke tafe cikin nishaɗi sai tuntsira dariya suke, wato ita ya mayar ƴar banza bai damu da ɓacin ranta ba tana sane taƙi fita gyaran ɗakin Didi, duk don ta samu ya kulata amma kamar ya san manufarta ya tattara ya watsar da ita da kansa ya zage aka yi aikin dashi da Mahmah don a dokarsa bai yarda ƴan aiki suyi masa aikin uwarsa ba don ƙarara ta nuna masa bata son hakan kasancewarta mai tsafta da tsantseni. Kamar ya san tana lafe a window tana kallonsu ta taga ya buɗewa Sadiya ƙofar motar yana jifanta da wani irin murmushi da ya tunzira zuciyar Ammi taji wani kishi yana katantawa da ita, har yau ta kasa iya danne kishinta akan Sadiya duk da ta fita da komai amma haushinta take ji sosai tana tunanin duk duniya ba wanda ta tsana sama da Sadiya musamman da tayi mata zarra wajen haihuwar ƴaƴa maza don ita kaf ƴaƴanta biyar maza ne ba mace ko ɗaya abinda yake sake baƙanta ran Ammi kenan musamman idan kalmar ‘ Sadiya taci gida’. Ta faɗo dodon kunneta da mafi yawan akasarin mutane suke faɗa musamman a wajen taron biki ko suna na dangin mijinta, kai har da ma na mutuwa ta sha ji ana mata gori ko don mutanen sunyi la'akari da yarda maitarta ta fito a fili na son haihuwar ƴaƴa maza ne shi yasa ake jifanta da zancen? Da sauri ta saki labilan tana runtse ido tuno da maganar da likita yayi bayan haihuwar Hamda ya tabbatar mata da ba zata sake haihuwa ba saboda mahaifarta ta taɓu dole aka juyata haka dole tana ji tana gani burikan ta suka bi iska, tayi burin haihuwar ƴaƴa maza ita ba don gado bama don son taje gidajensu ta shimfiɗa mulki kamar yarda Didi take shimfiɗa mulkinta a gidajen nata yaran. Tana jin tashin motarsu ta saki tsaki haɗe da furta zaka biyo dare ka nemeni ne wallahi kayiwa kanka sai nayi sati ban baka haƙƙinka ba, ta tabbata kuma sai ya kusa suma don idan tayi masa yaji ko na kwana ɗaya ne ranar girkinta zama yake yayi mata kuka yana roƙonta, don da gaske shi kaɗai yasan ruwan zallar daɗin da yake kwankwaɗa a jikinta balle sati! ta saki murmushi da ta tuna haɗaɗɗiyar zumar da ta siya da zata kusa zautar dashi a zahiri tace gidan ka tarar. _____________________________ Da sauƙi sosai suka sameta don likita ya tabbatar musu zuwa safiya ma idan drip ɗin da ake saka mata ya ƙare za'a iya sallamarta. Mahmah da kanta ta zauna tana bata kunun gyaɗar da ta damo mata ta sha kuma sosai har sai da tayi gyatsa. Abbu murmushi kawai yake yana sake jaddada kimar Sadiya a zuciyarsa, da gaske ɗin ita ta dabance zuciyarta mai kyauce,Mai halin mutanen farko shi yasa kullum yake mata kirari da Hali dubu. Kashegari kuwa aka sallamesu, ko kafin suje gida tuni Mahmah tayiwa Saliha waya ta ce ta gyara mata ɗakin da yake kusa dana Humaid nan zata saka Hamda a ciki, duk da bata da tabbacin uwarta zata yarda sai dai wannan karan Abbu ya tsaya kai da fata ya ce dole nema ta yarda tunda ita bata sonta bata isa ta hana wani riƙeta ba. Suna shigewa sashenta Ammi ta fito a sukwane cikin bala'i ta shiga ɓangaren Sadiyar tana zuwa ta shiga surfa bala'in sai an fito mata da ƴarta ai ba uban wanine ya haifa mata ita ba matar shige kawai borar gida" Sadiya murmushi ta saki kafin ta girgiza kai ta ce"Wallahi ba zata fito ba sai dai idan Ubanta ne yazo ya fitar da ita da kansa, kuma alhamdulillah borar gida ita ta zama uwar mazan gida mowa kuma ta haifi mata...... Wani kukan kura Ammi tayi, tayi kanta yasa na runtse ido don na tabbata ba za'a kwashe da daɗi ba. [1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e ELEGANT ONLINE WRITERS (Haɗin kai shine takenmu.) _3 Ya abin yake? Daban yake da sauran. Da sauri Sadiya ta fincike wuyanta haɗe rai sosai tayi ta ce "kada ki fara kada kiyi wannan kuskuren, ko ina yarinya ban yarda da dambe da kishiya ba, balle yanzu da nake da ƴaƴa da jikoki har da surikai." A zafafe Ammi ta ingijeta tare da ɗaga hannu zata zabga mata mari dai-dai lokacin da drivern Didi ya danno hancin motarsa cikin gidan tare da sakin gigitaccen horn, bisa bin umarnin Didi don sanar da masu gidan zuwanta, wanda hakan shine tambarinta. Cak Ammi tayi da hannunta cikin matuƙar ɓacin rai da haushin bayyanar jarababbar tsohuwar, tayi tsaki ta fice daga sashen Mahmahn da sauri don ta san tabbas Didi tazo ta tarar da wannan tashin hankalin ranar na lahira ma sai yafi ta jin daɗi. Mahmah tayi murmushi kafin ta furta “Gaba da gabanta”da ki tsaya mana. Sannan tayi azamar fita don tarar Didin. Fuskar Didin a washe take kallonta, da duk jama'ar gidan tana amsa gaisuwarsu cike da murnar samunsu lafiya, ahalin Sakina ne kawai bata gani ba. Bata damu kanta ba ta san dalilinsu na ƙin zuwa bai wuce ba sa son tayi musu gorin rashin aure ba, alhali ba mijin suka rasa ba suna dai jiran wanda ya ci ya tada kai. Murya a cunkushe ta kalli Sadiya ta ce"Ita hakimar kishiyar taki tana ina?" Mahmah ta ɗan yi jim kafin ta ce "Ina ji sallah take tunda baki ganta ba." ta samu kanta da gillara ƙarya duk don ta gyara lamarin. Didi ta kalli agogon hannunta kafin ta ce "Sallahr walaha take Kenan da sha biyun rana? Sadiya kenan kishiya kike karewa don kada nayi mata sababi? ai ba tun yau na san Sakina bata ƙaunar taga nazo gidannan ba, saboda bata son na sawa yaranta ido to wannan karan a shirye nazo tsaf wallahi ba zan bar gidannan ba sai na aurar da iyayen matan da ta girke a ɗakinta, su ba zawarawa ba su ba ƴan mata ba, shi kuma soloɓiyin mijinku ya saka mata ido sabida baya son laifin balarabiya." Sunkuyar da kai Sadiya tayi kafin ta ce "Kiyi haƙuri Didi ai aure lokacine da zarar lokacinsu yazo ko suna so ko basa so sai sun yi." Dai-dai lokacin da Ammin ta shigo kuma duk wani sababin Didin akan kunnenta take yi ranta ya sake ɓaci shikkenan wannan matar zata zo ta ɗaga mata hankali. Fuskarta ba yabo ba fallasa tayi sallama haɗe da faɗawa cikin parlourn. Didi ta zuba mata ido tana jijjiga kai ganin yarda Sakinan ta cono ɗankwali har gaban goshi,alamar dake nuni da cewa a shirye take da amsar duk wani rashin mutunci na Didin. Murya a cunkushe ta fara gaisheta Didin ta yamutsa fuska kafin ta ce "Ai Sakina da kin bar gaisuwarki tunda ba dole nace sai kinzo kin gaisheni ba, ba buƙatar ta nake ba gaisuwar da za'a yiwa mutum ana faman ɗaga hanci dai-dai nake dake wallahi, ki bini a hankali kafin ki kaini bango." Sakina dai ɗan murmusawa tayi wanda direct zan iya kiransa dana rainin hankali ta miƙe cike da izza tace "A huta lafiya Didi" daga haka ta kaɗa zaninta ta wuce ta bar Hajja Didi da hangamemmen baki don kuwa ta hango raini tsagwaronsa a fuskar Sakina, girgiza kai tayi kawai tana kallon Sadiya tace "Shahara iyye! Cabd’i jam" girgiza kai itama Sadiyar tayi ita kanta tana mamakin yarda Sakinah ta fetsare har haka? Didin da ko ido mutane basa iya haɗawa da ita idan tana magana. Ita dai murya a sarƙafe ta hau bata haƙuri sannan ta miƙe don ta bawa Didin waje ta huta har ta kai bakin ƙofa Didin tace "Ina Hamda ne ban ganta ba ko bata gama gallafirin makarantar kwanar bane?" Sadiya ta girgiza kai ta ce tana ɓangarena bata da lafiya ne yau ma aka yi discharging ɗinmu daga hospital ai da tuni kin ganta ta fito." "Subhanallahi me ya sameta haka? Yanzu haka shaiɗaniyar uwarta har yau bata san annabi ya faku ba ko? Wannan mata sai kace wacce tazo a zamanin jahiliyya ƙiri-ƙiri ka ƙi ƴarka ba laifin tsaye ba na zaune, muje in ganta ai gwara da aka mayar da ita ɓangaren naki, naga uban da zai ce sai ta koma gurin wulaƙantacciyar matar can da ta zamewa mijinki matar jaraba." Ita dai Sadiya murmushi kawai ta saki ta bi bayan Didin tana tafe tana riƙe zaninta da yake shirin faɗuwa. A kwance suka sameta idanunta a lumshe lokaci guda ta sake zabgewa dama ita ba jikin arziki ba kyalan-kyalan take tamkar ta faɗi ko don bata da kwanciyar hankali ne Allahu ya alamu. Didin da sauri ta ƙarasa gefen gadon ta zauna tana dafa goshin Hamdan, da kyar Hamdan ta buɗe idanunta da suka zama tamkar garwashi ta zuba su akan Didi tana sakin wani malalacin murmushi, tana shirin miƙewa Mahmah ta ce "Koma ki Kwanta Ke da ba kya jin daɗi." Wani kallo Didi ta zabga mata kafin ta ce "Ta zauna a ina? Bayan Allah ya kawo ni, ke tashi dahalla mu wuce idan banda kafirin iyayi na Sadiya me ye haɗinki da ita da har zaki rabamu? Sadiya ta gumtse dariyarta ta ce "Ayi haƙuri Didi bari na taimaka mata ta koma ɓangarennaki" "Ya dai fi, in banda shegantaka ba ita take taya ni hira ba, sai kuma a barni can a zaune ni kaɗai kamar wata mayya dama ku gidannan ba wani yawan arziki ba kowacce ta tsaya ragwanta daga haihuwa biyar kawai ni sai da na haihu sau goma sha huɗu ke da kanki kin sani zama ne kawai Allah baiyi zasu yi ba, Huɗu kacal Allah ya raya min na kuma gode masa a hakan ma, muje dahalla kin tsaya min wani iyayin banza." Ammi da take tsaye a jikin window ta hango fitowarsu ana rirriƙe da Hamda wani abu mai kama da tausayi yaso shiga ranta amma sai tayi tsaki kawai ta saki labilan zuciyarta na sake ɓacin ran ƙin barinta ta cigaba da wahalar da Hamda da aka yi, yarinyar da ko sunanta bata son ji bare karo da baƙar fuskarta. Didi suna shiga ɗakin ta hau damawa Hamda fura da nononta mai kyau da tazo da shi, sai garin fura mai ƙanshi da aka yi mata dakan hannu sai zabga ƙamshi yake. Sosai damun yayi kyau sai ƙamshi take bata saka mata sugar ba sai zuma farar saƙa. Da kyar Hamda ta miƙe ta karɓi furar ta fara sha dama Allah ya zuba mata son fura don dai bata samu ne sai Didi tazo, don wani lokacin da gangan Ammi take dama furar kuma ta hanata ta bawa masu aiki saboda ta san tana tsananin son furar. Ta lumshe ido tana jin daɗin zuwan kakartata da ta tabbatar soyayyar da take mata babu algus. Sosai ta samu ƙwarin jikinta har ta miƙe da kanta ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada sallah a gefen Didin da take sallahr itama. Suna idarwa suka jiyo sallamar su Muneerah Najma da Nasma fuskar Muneerah ce kawai a washe banda ta su Najma da suka yi kamar an aiko musu da saƙon mutuwa. Muneerah da sauri ta isa wajen Didin tana gaisheta, itama cike da kulawa take amsawa tana son Muneerah musamman da yake ita sunanta taci "Ina kika shiga tun ɗazu ban ganki ba?" Muneerah tana ɗibar fura ta ce "Wallahi Didi Islamiyya naje da na gaji da tsimayin zuwanki.".Didi ta ce "Masha Allah ubangiji ya bada nasarar karatu. Ku kuma asararru ina kuka shige ana nan dai ana haɗa kafaɗa da iyaye an ƙi aure ko? To ku kwana da saninku wannan karan da shirina nazo inma ku fitar da miji ko ni na fitar muku acan Gwarzo cikin dangi ko abokan arziki, na baku wata ɗaya kacal wallahi wannan karan ba zan karɓi uzirinku ba ko kun wuce azimi ba zaku wuce sallah ƙarama ba insha Allah ku haƙura ku zaɓi ko waye tunda govenor da shugaban ƙasar har yau ba su ganoku ba, sai ku rungumi haƙuri kafin furfura ta fara bayyanar muku a gida, don kyan da kuke taƙama da shi zagwanyewa zai yi matuƙar babu aure shashashai kawai." suna gama gaisheta suka miƙe ransu a. ɓace da tijarar da take musu suka ƙarasa wajen Ammi Suna shiga taga alamun Didi ta kunnosu tsaki tayi kawai tayi kafin ta tambayesu mai ya faru? Najma ta zauna tana zuba tagumi ta ce "Jarrabar tazo yaushe zamu ga dai-dai daga zuwanta har ta fara zancen aure wai mu zata haɗa da ƴan gwarzo kurt da kuwa sai ta gwammaci kiɗa da karatu wallahi don ba mai saka ni auren mutumin ƙauye." Tsaki Ammi tayi kafin ta ce "Ya zama kuwa dole na tashi tsaye wajen samo muku mazaje na kece raini ko da kuwa zanyi yawo tsirara burina naga kun auri mazan kece raini da zanyi tunƙaho dasu a matsayin surukai tunda dai Allah bai bani yara mazan da nake burin naje gidansu na baje mulkina ba, kamar yarda waccan tsohuwar take baje nata, tun ina yarinya ban fi shekara sha shidda ba nasa wa raina son haihuwar ƴaƴa maza ganin yarda yayar Mamma na take baza mulki a gidajen ƴaƴanta maza Ita kuwa Ummi mu kawai ta haifa mata bata da inda take zuwa tayi tunƙaho sai daga baya ta haifi ƙaninmu shikkenan na sawa zuciyata burin haihuwar maza amma Allah bai cika min burina ba, duk da ƙoƙarin da nayi tayi akan haka." Tana faɗar haka hawaye ya shiga gangaro mata akan fuskarta wanda hakan yake nuni ƙarara da zallar ɓacin ran da yake zuciyarta. Ko da Abbu ya dawo zancen dai ɗaya ne Didi ta tareshi da shi ta kuma tabbatar masa wannan karan da gaske take dole ne ta aurar dasu da son su ko ba son su, su suka kawo mijin ko akasin haka ta sake jaddada masa "Idan har kaga hakan bai faru ba tabbacine na rashin rayuwata, amma ko sharafa nake a gadon asibiti sai na aurar dasu banda tsiya ko Munirah da Hamda sun kai munzalin aure. Shima kuma Hammad ka sanar dashi ya tattara ya dawo gida Yaro shekara sha uku yana can zube a ƙasashen masu jajayen kunnuwa yayi sammakal ko matarsa yana can aka Kai masa ita, ai barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. To wannan karan da shirina nazo ƙwal uban kowa zan ci har shi Hammad ɗin da ku iyayensa." Abbu dai sunkuyar da kai yayi yana jaddada mata za'a yi yarda take so. Haka nake so Didi, ki soyawa kowa gyad’arsa a hannu y’an k’wal uba.. [1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e ELEGANT ONLINE WRITERS (Haɗin kai shine takenmu.) _4 ******************************* Da asubar fari, da tayi sallah bata koma ba, tana zaune gefen Didi suka yi azkar kafin ta karanta abinda ya sawwaƙa daga Alƙur'ani mai girma. Bata koma barcin ba, kasancewar ta ɗan ji sauƙin jikinta gyara sashen Didin tayi tas. ta wanke toilets uku da suke sashen ɗaya a Parlour biyu a sauran bedroom ɗin da suke sashen Didin inda ta mayar da ɗayan bedroom ɗinnata duk da dai Didin bata yarda su raba ɗaki ba tare suke kwana. Tas gurin ya fito sai zabga ƙamshi yake farin ciki ya lulluɓe Didi yana daga dalilin da yasa take son Hamda, sam bata da ƙiwa ko kaɗan. Wanka Didi ta shiga tana faɗin kema sai ki shiga kiyi wanka ga sabbin kaya nan da na ɗinko miki don na san waccan gallafirin uwar taki ko kayan ubanku yayi muku ba bari take ki saka ba, ta gwammaci ta haɗaki da gwanjo ina nan Ina jiran ranar da zata zo tana neman gafarar ki, to ko cikin shegen Ki tayi ai iya ɗiban albarkar da zata yi kenan, balle laifinki ɗaya wai kinzo a mace, shikkenan tun ranar da aka haifeki ake gumurzu da ita bari muyi walaha mu karya na baki labarin da kika daɗe kina son ji na san yanzu shekarunki sun kai sha bakwai tsab kwanyarki zata ɗauki labarin takaicin uwarki mai hali kwatankwacin na jahiliyya, na tabbata ita da kanta banda an saka mata ido tsaf zata iya hallakaki a lokacin, kai mun ga tashin hankali Ƙiris fa ya rage ta zauce sabida masifa. Daga haka ta shige wanka wannan damar Hamda ta samu tayi saurin ficewa tana mamakin surutun Didin. Sashen mahaifiyarta ta shiga, dama da spare key a hannunta ta buɗe a hankali, shiru ta tarar da parlourn da alama barci suke tabi gurin da kallo duk datti ɗan kwana biyun da tayi bata yi shara ba. Dama ita Ammi sam taƙi yarda ta ɗau mai aiki don tace gata bata buƙatar wata mai aiki. Ta ɗaure Hijabinta a ƙugunta ta shiga wanke kwanukan kitchen ɗin ta gyarashi tsaf burinta ta faranta mata ko ta samu ta goge tabon ƙiyayyarta a zuciyar Ammin. Kan kace me? Ta gyare gidan tsaf banda ɗakunan barcinsu ta wanke har toilet ɗin parlourn sannan ta saka turarukan wuta a burner da humidifier tuni gidan ya ɗau wani irin Ƙamshi daga haka tayi sauri ta fice ta koma sashen Didi. A saman sallaya ta tarar da Didin da alama sallahr walaha tayi, ita kanta Didin ita Ta koyar da ita sallahr walahar, tana sake jaddada mata ɗimbun ladan da yake cikin Sallahr walahan da tarin nutsuwa da mai yinta yake samu a zuciyarsa, ga shi Allah yana amsa addu’arsa ba da jinkiri ba. Wankan itama ta shiga ta yiyo sannan ta ɗauro alwalarta ta saka tsaleliyer atamfarta da Didin ta ɗinko mata kaya ne kala goma dama ta saba duk sanda zata zo sai tayi mata don ta san kafin tazo nata sun mutu tunda ba wata sutturar arziki uwar take barinta ta saka ba. Idan ka shigo gidan ma zata zaka yi ƴar aiki ce, Saboda tsabar yarda zaka ga kayan sun ƙojale don tsufa ga kanta da baya samun cikakken gyata fatarta ma don dai Allah yayi ta cikin jinsin mutane masu taushin fata ne, da duk wahala bata jemewa tabbas da ba ta kai haka kyauba. Tayi kyau sosai ɗinkin kuma ya zauna a jikinta tamkar ba daga ƙauye aka ɗinko mata su ba. Ta cukuikuye gashinta ta danna cikin ɗankwali don rabon da ta tajeshi har ta manta balle ta saka man kitso, ko wanke shi tayi haka take barinsa. A gefen Didi da take lazimi da jug ɗin furarta a gefe ita ma ta tada sallahrta cikin nutsuwa. Sai da ta idar tayi addu’ointa Didin Ta tura mata cup cike da fura tace “Maza kwankwaɗeshi tas ki bani cup don na san waɗannan mashiriritan kafin su kawo abin karyawa sai goma ta gifta shi yasa wannan karan zan saka ya kawo min kayan abincina kaf da kaina zan dinga girki ba zan iya zaman jira ba, girkin da sai an ga dama sannan ake yin mai daɗi ko a zabga mai da maggi to bana ba dani ba kowa ta riƙe banzan abincinta." Ita dai Hamda murmushi ta saki kawai tana kai cup ɗin furar bakinta. Ta shanye tas zuciyarta cike da farin ciki. Har zata kishingiɗa ta kwanta sai kuma ta miƙe ta ce "Didi baki ba ni labarin ba." "Ƴar nema ashe kina so bari mu ɗan runtsa tunda yau ba islamiyya sai na baki anjima yanzu kam idanuna har yaji yake.” Duk da ba haka ta so ba haka ta hakura don ta san idan ta matsa Didin zata iya cewa ta fasa. ________________________________ Ammi na fitowa ta ga parlournta tsaf sai baza kamshi yake da sauri Ta isa bedroom ɗin ƴan matanta don a tunaninta su suka yi sharar tunda Ta san Hamda na can ɓangaren Didi turus tayi ganinsu sheme suna barci har Muneerahn da take zaton ita tayi. Jikinta a sanyaye ta juya don ta tabbatar Hamdan ce dai tayi, wani abu ya Tsirga a ranta mai kama da tausayin uwa ga yaranta, sau tari tana tunanin sassautawa Hamdan sai dai tuni shaiɗan yake rinjayar zuciyarta wajen tunanin Hamdan a matsayin wata tashin hankali ce wanzuwarta a rayuwarta, mutuwarta a zahiri ita tafiye Mata alheri shi yasa take takura mata ko don wataƙil zuciyarta ta buga ta rasu ta huta da baƙin cikinta, don tabbas idan Hamda bata mutu ba nan gaba kaɗan akwai tashin hankalin da bata so ya afku tana da rai wanda zai zamo tamkar tozarci ne mai girma a gareta da zuri’ar D’an Borno gaba d’aya. Ta sha auna kashe Hamdan a ranta sai dai tana fasawa gudun fallasuwar asirinta da kuma tonuwar sirrin da ta riga ta bisne a cikin ƙasa. Ta ja ajiyar zuciya bayan ta zauna ta nutse a cikin kujerar three seater ɗinta samfurin royal da take girke a babban parlourn, idanunta akan tv tamkar mai kallon labaran da ake yi sai dai gaba ɗaya zuciyarta ta Lula can tunanin wani zamani da ya shuɗe. _____________________________ Barci sosai su kayi bayan idar da sallahr walahar akan faffaɗar daddumar Didin mai laushin tsiya da take ambula mata turare kullu yaumin don son tsaftace wajen ibadartata da yake can kusurwar ɗakinta. Bugun ƙofar da ake yi ne ya farkar da su daga barcin Hamda ta miƙe don taga waye itama Didin miƙewa tayi tabi bayanta da hanzari don bata da jiki ko kaɗan shi yasa bata jin nauyin jikinta. Saliha ce mai aikin Mahmah ta shigo hannayenta ɗauke da manyan warmers bayanta kuma Humaid ne yake biye da ita da flask ɗin tea. Didi ta dinga amsa gaisuwarrsu tana girgiza kai haɗe da duba agogo "Ba shakka, wannan abincin da mai za'a kirashi kenan na safe ko na rana? Kai jama'a ayi mata da shegen lalacin tsiya, to ni ba zan yarda da wannan tujarar ba bari wanda ya ajiye su yazo na faɗa masa ya jawa matansa kunne dama kada wacce ta sake ɗora sanwarta dani, su riƙe abincinsu can, zan dinga yi da kaina naga acan gwarzon ma da kaina nake yi to name za’a dinga wahalashsheni Allah na tuba abincin ma da ba ɗanɗanon arziki." Ta faɗa tana buɗe coolerr abincin faten dankali ne da ya sha busashshen kifi da alayyahu sai ɗaya coolerr farfesun cow-tail ne ɗayar kuma gurasar larabawa. Baki ta taɓe,dan ta tabbatar dai abincin ba makusa sannan ta ce Hamda ta kwaso plates ta zuba musu. "Ku tashi kuje ku ke kallona kamar kun samu akwatin kallo, kai kuma me ya hanaka zuwa makaranta." Humaid da yake duk a tsorace da faɗan tsohuwar ya ce "Hutun independent day muke." kallo ta watsa masa kafin ta ce "Wani abu ne kuma indafadan?" Ba Humaid kaɗai ba har ta Hamda sai da ta tuntsire da dariya Didi Ta ce “Kaji min aikin banza faɗar tawa kuke wa dariya? Aikin kawai to turancin faɗar annabi ce da sai na iya? ka tashi kaje kace ina son ganin ubanka tunda gaisuwar ma sai na roƙa." Humaid ya fice yana dariya Ƙasa-ƙasa a zuciyarsa ya ce "Drammer Queen" Abincin suka ci sosai kafin Hamda ta kai kwanukan kitchen ta ɗaurayesu sannan ta dawo. Man zafi ta ɗauko tana shafawa Didin a ƙafarta. Didin ta ce Alhamdulillah tunda ciki ya ɗauka bari na baki labarin asalinmu ciki da bai, da yarda aka yi auren uwarki da ubanki ba bisa son raina ba.....” _____________________________ Asalin kakanku haifaffen garin maiduguri ne kasuwanci ya kawoshi kano Ƙauyen Gwarzo, inda anan Allah yayi arzikinsa yake kuma anan ya had’u dani ya aureni har muka hayayyafa duk a Ƙauyen Gwarzo. Haihuwata sha huɗu sai dai a ciki huɗu ne suka rayu mahaifinki Umar ne babba sai Aliyu kafin na haifi Aliyu kuwa yara uku na haifa tsakaninsa da mahaifinki sai dai basu zo da rai ba. Daga Ali gadanga ƙusar yaƙi sai Gwaggonku Asma'u da take zaune a can ƙasar dubai da mijinta daga ita kuwa haihuwa biyar nayi ba rai kafin na haifi autata lauratu wato Ammanku Ta Janbulo daga nan ne fa haihuwar Ta tsaya min bayan nayi biyu ba rai. Ni kad’ai ce wajen kakanku Usmanu dan Borno bai sake aure ba duk da baloƙoƙon da danginsa suke masa wajen son ya ƙara auren acan gida borno har mata aka bashi amma yace ya yafe ni kad’ai na isheshi tunda ina yi masa duk abinda yake so baya son yazo ya had’a tashin hankali a gidansa yana zaune lafiya. Haka suka gaji suka zuba masa ido duk da surutun da suke masa yasa auduga ya toshe kunnensa ya ce ba zai ƙara aure ba. Ni nan da kike gani na macece mafaɗaciyar gaske da ba na barin ta kwana in dai ka takaleni ka taɓo masifa bana shiga shirgin kowa amma fa bana yarda a taka ni. Hadizatu nake mutane da dama suna kirana wargi kike dai-dai Ƙugun kowane ɗan iska. Shi yasa duk garin Gwarzo in dai kika je kika ce kina neman Didi matar D’an Borno to kin gama samu na saboda shaharar da nayi a masifa, wanda bakomai bane sai zallar fad’ar gaskiya da mutanenku basa so yanzu. Ko iyayenki Shakkata suke, saboda bana sakar musu fuska kamar yarda Kakanku yake sakar musu. Ba yabon kai ba dole Kakanku ya kasa aure sabida na riga na siye zuciyarsa da girki tunda shi in dai cikinsa zai d’auka to kin gama masa komai, idan kinga masifarsa to ya dawo gida ban gama abinci ba. Sannan ba yabon kai ba ina da tsafta dai-dai gwargwado, ga kwalliya kamar me don idan na cab’a kwalliya irin Ta mutanen da baki ga yarda yake zama yayi ta kallo na ba, na tabbata da yanzu zan yi wannan kwalliyar wasu ma mahaukata za su d’aukeni. Idan kuwa kika shigo gidana ba abinda zaki fara jiyowa sai k’amshin turaren wuta da na tsinke d’an Borno, don sana’ata kenan duk da ba wani ciniki nake ba kasancewar jama’ar garin mu basu damu da k’amshi ba. Ke na fa zabga iyayi ina yarinya Wani suna suke kira na da shi Delu iyayi har na haihu Umaru ya cigaba da kira na wai Delu, bisa tilas na koya masa cewa Didi shikkenan sai sunan ya bini. Idan kakanku yayi fushi wuyartana shafe baki na da jan jambaki nayi d’igo-d’igo a gefen k’uncina na ja siririyar jagirata, na bad’e fuskata da hoda pankeke shikkenan zaki ga ya daina fushin yana bina da ido yana fad’in Indiyana ni kuma kaina yana kumbura duk da ko a layin bak’ak’en India ba za’a saka ni ba, gashinta k’ak’k’arfa ne irin na hausawa, haka nan ba wani idon arziki gareni ba ga ni bak’a kamar yarda kika ganni d’in nan, amma don son ran kakanki yake kira na Indiyana ni kuma ina amsawa Cike da izzar nafi sauran mata, duk da wani ko a k’afa aka k’ulle masa ni ina tabbatar miki sai ya kunce ya arce ni da y’ar dab’as... wata dariya ce ta kufcewa Hamda, ganin duk suffofin da ta zayyana Haka zubinta da fasalinta yake, sam bata da tsaho ko kad’an... Hajiya Didi tamu.... [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽 ELEGANT ONLINE WRITERS (Haɗin kai shine takenmu.) Page 5 Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861 Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd **************************** _Mu d’in ba wasu masu wadata bane sai dai muna cikin ni’imar ubangiji, don bamu rasa ci ba, bamu rasa sha ba, Kakanku a tsaye yake sosai akan iyalinsa ta yarda duk abinka baka isa ka hango gazawarsa ba, ya tsaya sosai musamman ga karatun iyayenku, burinsa a kullum bai wuce yaga sun samu nagartaccen ilimi ba, na boko da na muhammadiyya, Musamman Babanki Umar. Sanda ya gama secondary School Allah ya taimake shi har jami’a yaje can zaria inda yayi karatunsa a ‘bangaren Zane-Zane kasancewarsa mai hazaƙa wata rana kawai yazo min da labari mai dad’i wai Gwamnati ta d’au nauyin karatunsu ‘kasar waje can ‘bangaren larabawa ‘kasar Jordan zasu je su yi babban degree a can. Mun yi murna sosai sai dai Kakanku ya ce bai isa ba, ba zai tafi ba sai da aurensa, amma mahaifinku ya turje ya kuma kawo uzurin gwamnati tace ba zata d’au masu mata ba saboda ba zasu d’au nauyin mutum sannan su d’au nauyin iyalinsa ba, har da ce mana sunce sai dai ya hak’ura Haka dai dole muka k’yaleshi ya tafi ashe tafiyar zata zame mana jangwamgwam domin dai a can ya had’u da alak’ak’an uwarki ya aura. Tafiyarsa da wata uku yayi mana aike akan ya samu mata zai yi aure a can. Ai kuwa na rufe idona na ce bai isaba, hakan ya tashi hankalinsa sai gashi ya dawo k’asar ba shiri lokacin watansa shidda da tafiya. Da Allah da annabi da saka malamai suyi mana wa’azi muka amince da yayi auren amma da sharad’in ni da kakanku zamu je muga tushe da asalin yarinyar. Bai wani damu ba ya ce mana ya yarda. Nan muka fara cuku-cukun tafiya kakanku ya siyar da gonarsa d’aya muka tafi har da k’aninsa da suke ciki d’aya wanda kuke kira Baffa Mamman. Mun samu tarba Ta mutunci daga iyayenta,babu aibu sam a tattare da su dattawa ne sosai, don shi kansa Umarun a gidansu yake zaune kuma yana d’an aiki a kamfanin mahaifinsu mutumin kirki shima daga Nigeria yaje karatu sai ya had’u da uwarta mutuniyar Jordan d’in ta nuna bu’katar aurensa shikkenan zamansa ya koma can don haka da yaga Umar bahaushe ne ya ja shi a jikinsa, ya shiga farin ciki, ko da yarinyarsa ta nuna tana sonsa take ya amince ya bashi aurenta. Hankalina ya kwanta da naga ubanta bahaushe ne, kuma har kwatancen gidan su yayi mana a garin Niger (Minna) cikin unguwar limawa nan ce mahaifar Kakanku na wajen uwa, ta daina muku fankamar wai asalinta balarabiya ce, asalin uwarta dai.Kakanku ya ce zai bincika ya gani, ai Niger ba bak’on waje bane a wajensa. Ba mu dawo ba sai da aka d’aura auren, amma jikina ya yi sanyi da na lura da uwar Sakina ce take kula da al’amuran gidan shi uban nasu ba shi da ta cewa sai abinda Ta d’aurashi a kai, kuma yarinyar da naji suna kira Sakna ni ce nan na mayar mata da sunanta Sakina har yanzu a garinsu Sakna ake kiranta, kaf halayen uwarta ne a tare da ita bata ganin mutane da gashi. Gaisuwa kanta sai taga dama take min gashi iyayen suna ji da ita tamkar masifa ko don itace babba. Satinmu biyu muka baro garin daga nan umara muka wuce, na kuwa dad’e a d’akin Allah ina kaiwa Rabbil Izzati kukana akan aurennan na ubanki don sam zuciyata ba wai ta gama yarda da auren d’ari bisa d’ari bane, na yarda ne dai don Malam yafi ‘karfina. Dawowarmu Nigeria muka dinga zuba idon ganinsu sai dai kamar mun shuka dusa ba amo ba labarinsu. Hankalina ya tashi matuk’a da gaske ga gari ba kusa ba kuma lokacin wayar hannu bata zo ba iyakaci ta landline ce shima ba waje mai nisa ake kira ba. Ganin tashin hankalin nawa ya yawaita hakan yasa Malam ya shiga addu’a da a lokacin ake kiranta addu’ar kiranye. A lokacin har aka yi bikin k’anwarsa amma bai dawo ba. Na haifi autata lauratu shima bai dawo ba. Kwatsam wata rana muna zaune da hantsi sai ga sallamarsu ina d’aga Kai suna shigowa da hakimar uwarku tana wani cin magani tana yatsina kamar ta shigo gidan da ake tsubire himulin kashi, ba mu bi ta kanta ba muka shiga murnar ganin Umaru da duk yayi ‘kiba ya zame min babban mutum kuma duk da a lokacin ko shekaru talatin bai rufa ba. Na shige rumfa ina musu lale marhabin ku shigo mana. D’aki na tsaf yake duk da dai ba kujeru amma malale yake da sabuwar leda sabuwa dal don mun fara shirin azimi daga gefe kuwa fanka ce Ta tsaye sai dadduma da tum-tum irin na gidan sarauta. kuma bana mantawa a lokacin k’amshin turaren tsinke yake da na kukkunna a duk wata kusurwa da take d’akin, ya kuma sha Fenti da farar k’asa kamar yarda malam yake k’o’kari duk shekara a watan sallahr tsofi yake shafe gidan da farar k’asa. Duk da wannan abin amma Sakina yamutsa fuska kawai take, ta d’ofana d’uwawunta akan tum-tum d’in da yake gefe sai sannan Umar ya kalleta ya ce “Ki gaisheta mana.” Fuskarta kamar ta zunduma ihu cikin gwarin hausarta da ko fita bata yi a lokacin ta ce “Ina kwana?” Ina murmushi na ce mata “Lafiya k’alau Sakina.” Ji nayi tana masa magana da turanci ban dai fahimci abinda tace masa ba amma tabbas naji ta ce Sakna da Sakina a cikin zancen nata. Sai naga yayi murmushi ya ce “Didi sunanta ba Sakina ba Sakna sunanta.” Na kuwa daddage na jefe shi da umbola na ce nak’i nace Saknan ka gaya mata ba zance ba Sakina zance Au nan k’arata Ta kawo don rashin Ta ido? gaisuwar ma ina ce sai da kace ta gaisheni, kai Umaru!ni dai ka tak’aitan da ba ka auro mai jin hausa ba balle ta fahimci masifar da nake mata ja’ira fuska kamar jan k’osai.” Kallona kawai take tana ta’be baki ni kuwa na mik’e ina kallon Ummaru da yake ta guntse dariyarsa nace “Sai ka kawo mana bak’uwa ba sanarwa yanzu mai kakeso mu bata? Ga d’akin naku ma ba a gyare yake ba.” Na k’walawa Ali kira yana zuwa nace “Gadanga sai ka tattara kayanka ka dawo d’akin nan na tsakargida sai a gyara musu can d’in tunda d’aki ne da rumfa har da makewayi a ciki.” Ali cikin farin ciki ya shiga aiki ma’kota kuwa tuni aka fara shigowa ganin Amaryar Ummaru ana mamakin yarda ya auro balarabiya sai da nayi musu jan ido sannan suka fice na saka sakata a Zauren gidan ina sake tsinewa k’auyanci banda haka meye na dandazon zuwa ganinta abinda gobe zan saka ta zaga gida-gida su gaisa dasu. Abincin da muka yi na rana shinkafa da miya da salak na juye musu kaf na bawa gadanga ya siyo kifi sukunbiya na saka musu, har da dafaffen k’wai wai duk don na karramata. Na zuba musu zo’bo mai sanyi har da fura da yake ina siyarwa k’aton firiza ne dani a tsakrgida, nake sararwa da mutane zo’bo da fura mai sanyi kuma cinikin ya kar’beni sosai. Reras na jere musu langunan abincin har da cokula na sababbi gal dasu. Umaru yayi saurin jan tray d’in abincin ya fara k’o’karin zuba musu, gani nayi tayi wuf Ta ri’ke hannunsa tana girgiza masa kai sai kuma naji tana ambaton hotel da nuna masa lokaci ta hanyar kallon agogo. Sai naga ya mayar da abincin ya rufe yana sakar min murmushi ya ce “Didi ai wucewa ma masauki za muyi mun riga mun kama d’aki a hotel.” Ban san sanda bakina ya zunduma masa zagi ba nace “Ba Otel ba Otalo kai har kayi kud’in da ba zaka iya ajiye iyalinka anan ba? to wallahi baka isa ba nan d’in da take ‘kyama anan zata zauna ba gidan uwar da zata je, ina kallo da ma tun d’azu kallon rainin da take wa gidannan to ka gaya mata nan kwana nan yini don uwarta ba inda zata je ga d’aki can na saka gadanga yana gyara muku, kuma ko dawowa kayi gaba d’aya ga ‘bangarenka can malam yasa ana gina maka anan d’in zaka zauna. Ni za’a kawowa fi’ili da zancen banza.” Ina kallo tana tambayar me nake cewa naji ya ja ajiyar zuciya yana mayar mata da harshen da tafi wayo a kansa kawai sai naga yarinya ta saka kuka ta mi’ke tana d’aukar jakarta tayi hanyar waje da sauri Umaru ya bita dai-dai lokacin da malam yayi sallama ya shigo.. kamar zata bangaje Malam, Umar d’in yayi sauri ya rik’ota ai kuwa munyi kallo don fad’awa jikinsa tayi tana kuka sosai kamar yarinya cikin kukan babu abinda nake ji sai furucin Back da kuma Jordan sai kuwa wata kalma da take yawan maimaita Ta wai now now. Malam ya saka salati tare da furta “Umaru saukar yaushe naji kuma amaryar taka tana ita Jordan zata koma? Ku muje ciki naji me yake faruwa a tsanake.” Umaru ya ja hannunta ko kunyarmu bai ji ba ya saka ta a gefen hammatarsa yana goge mata k’wallar idonta. Sosai takaici ya kumeni nama kasa magana zuwa lokacin da suka shigo Malam ya sake tambayata na bashi labarin kaf abinda ya faru. Take shima na ga fuskarsa ta sauya da yanayin ‘bacin rai amma da yake namiji ne sai bai nuna ba kalmar Ashsha kawai yake fad’i sai kuma ya girgiza kansa ya kalli Umaru ya ce “Kai kuma don sakarci sai ka biyewa matarka ka ‘batawa uwarka rai? Meye da gidannan d’in da ba zaku sauka ba? ka gwammace Ku kama Hotel ina ce kaima a gidan ka rayu?” Kasa cewa komai yayi ganin ran mu ya ‘baci ina kallo yana ta fama da hakimar tasa kan ta ha’kura amma taja ta turje akan sai ta tafi abincin da na kawo musu ma ko ci ba suyi ba. Bama ta kalleshi ba ran Malam a ‘bace ya ce masa su wuce su tafi sa dinga lek’omu kafin su tafi. Abin mamaki Umaru kuwa ko ja da lamarin baiyi ba yaja matarsa suka wuce ba abinda ya dameshi balle ya gane Malam gatse yayi masa. Bayan fitarsu Mun dad’e muna ta’ajibin abin, mamaki kuwa kamar ya kashe mu haka yasa Malam yanke shawarar aura masa yarinyar mak’ocinmu Sadiya, Yarinyar da kowa ya shaida da nagartar halayenta ga son ibada kamar me. Ubanta Aminin Malam ne. Murna na shiga yi da shawarar Malam na karb’eta d'ari bisa d’ari muka kuma ce ba za mu sanar dashi ba sai dai yaji an aura masa aure da ita dole kuma ya amsheta matsayin mata. Malam bai bari sai kashegari ba a daren ranar yaje wa da Talle amininsa zancen, Talle yayi farin ciki sosai don babu wanda zai k’i had’a zuri’a da Malam sai marar rabo, take suka saka lokacin aure Sati biyu masu zuwa. Malam ya cigaba da ginin da yakewa Umaru a gefe guda a gidanmu. D’aki biyu ne da babbar rumfa sai makewayi ‘d’aya da yake dangar rumfar daga can gefe. Kashegari Umaru shi kad’ai ya zo don hakimar ta ce ba zata Biyoshi ba, ban ko tambayeshi ba shi yake rattabo min bayani, na ta’be baki na ce ta sha zamanta ai ni ba na nemanta, don na gane k’yank’yamun mu take kuma tayi Ta banza don kwanannan zata gane kurenta.” Bai wani da’de sosai ba ya tafi. Da ku’dina da na Malam har da na gadanga da Y’ar uwarsu da tayi aure muka ha’da aka yi lefen kishiyar Uwarki Sadiya. Da yazo yaga ana had’a lefen bai kawo komai a ransa ba ranar ma bai dad’e ba kuma nan ma bata biyoshi ba sai wasu dogayen riguna na k’asar da Ta aiko min dasu da na k’annensa ni kuwa duk na tattara na zuba a lefen Sadiya.... To fa! Ko me Ummaru zai ce idan ya Samu labarin aurensa da Sadiya? Shi da yake da tsaleliyar Balarabiya [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on wattpad Nazeefah381 ELEGANT ONLINE WRITERS (Haɗin kai shine takenmu.) Ya Abin Yake? Daban yake da sauran. ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽 6 Duk tunaninsa lefen Gadanga ake haɗawa, shi yasa bai damu ya tambayeni ba. Sai ana gobe ɗaurin aure kamar an jefo su sai ga su sun zo da yamma. Fuskata babu wani alamun damuwa na tareta da murnata da komai, na malala mata tabarma a rumfa, ta kuwa zauna ranar kamar abin arziki har tana gaisheni cikin gwarancin hausarta. Lauratu da ta dawo daga islamiyya ganin ta yasa ta faɗawa jikinta a guje sai naga ta tureta a fusace tana kaɗe jikinta, mamaki ya hanani cewa komai sai janye Lauratu da ta fara kuka nayi. Lokacin bata wuce shekara goma ba, cikin lallashi nace mata yi haƙuri daɗin abin burinmu daf yake da cika.” Sai naga ya kalleni da alamar neman ƙarin bayani, ni kuwa na galla masa harara. Muna zaune Malam ya dawo fuskarsa fal ɗauke da murmushi da katinan aure a hannunsa. Shi kansa Malam ɗin ba fara'a ba girmamawa ta shiga gaisheshi, shi kuwa ya amsa ba tare da komai a ransa ba. Ya miƙe ya shige turakarsa yana faɗin “Idan ka tashi tafiya ka sameni.” Ƙasa yayi da kansa kafin ya ce "Malam ai tafiya zamuyi jirgin dare yau zamu bi." Daga ni har Malam ba wanda bai firgita da jin zancen ba muka ji tamkar saukar aradu a ka. Ni dai har razana nayi. Malam ya dawo da baya yana masa kallon tuhuma kafin ya ce “Da kazo mai kace min? Ca nake cewa kayi wata guda zaku yi?” Ya ɗaga kai kawai, idanunsa sun nuna yana cikin wani yanayi na ƙaƙa ni kayi. Malam ransa a ɓace ya ce "To menene dalilin canjin zancen?” Daburcewa yayi sosai kafin ya ce “Kawai dai zafin garin ta ce ya isheta.” “Shine kai kuma kabi abinda tace wajen ruguza shirinka kuka ɗaura aniyar tafiya yau?" Na faɗa raina a ɓace da tunanin sun canja min ainahin Ummaruna wannan ba nawa bane wani ne can daban. Zufa ya goge kafin ya ce “Duk ba haka bane,jarrabawa zata je ta zana.” Malam Yaja ajiyar numfashi a kufule ya ce “Jarrabawo ba jarrabawa ba, ta bakin uwarka ne duk an canja maka halaye, to albishirinka ungo nan.” Ya faɗa yana manna masa katin auren a tafin hannun da ya miƙo "Ɗaurin aurenka gobe da Sadiya, sai ka sanar mata idan taga zata tafi sai tayi gaba ita kaɗai." Sam bamu san zufa bace take karyo masa, sai da na kai idona kansa sannan na ankare. Na kuwa saka salati ganin yarda ya durƙushe a gaban Malam yana faɗin "Kayi min rai wallahi ba zan iya haɗa Sakna da kowacce mace ba." A zafafe Malam ya ce idan an ɗaura ka saketa, amma ka tabbatar in dai ni na haifeka to babu shakka aure ya ɗauru." Yasa kai ya fice Lauratu da take gefe sai dariya take zuciyarta fal farin ciki, duk da umbolar da nake mata bata fasa ba. A zuciye Ummaru ya jawota zai fara jibga. Na kuwa saka Hannu na janyeta ina cewa kada ma ka fara, don wallahi ba zan ɗauka ba. Ina kallo tana tambayarsa daga yanayin fuskarta na gane tambayarsa take masifar mai muke? Sai naga ya saki murmushin dole ya girgiza mata Kai. A daddafe ta bari suka cika awa guda cur, naga ta miƙe hannunta ɗauke da Jakarta ta kalleni a banzace naji ta ce "Good bayi." tana ɗaga min hannu shima ya mara mata baya bayan ya ajiye min wata leda yasa kai ya fice da sauri. Shikkenan daga ranar bamu sake ganinsa ba, amma haka Malam yasa aka d’aura auren kuma Sadiya ta tare a shiyyarsu da aka gina mata ita da Umarun da Ya wuce ya koma Ƙasarsu ko salaam babu. Bai kuma dawo k’asar ba sai bayan shekara Guda, Ba ni kad’ai ba wannan karan hatta Malam sai da ya nuna masa ‘bacin ransa. Don muna zaune a tsakargida wannan karan ma muka ji sallamarsu. Nayi turus ina kallonsu, Allah yaso ranar juma’a ce dama Sadiya ta saba duk sati a juma’ar take kitso idan kuma k’unshinta ya goge ta sake mayar da wani. Ranar ma haka ta kasance tsaf da ita tayi adonta cikin atamfa Diamond ta kada d’auri had’e da zubo himulin gashinta da ko balarabiyar ba zata nuna mata komai ba a gashi ko dirin jiki sai dai ta nuna mata hasken fata da santsin Gashi. Sadiya na da sirrin kyau da baya bayyana sai idan ta haske idanunka da murmushi anan zaka hangi zallar madarar kyau, Sai dai bak’ace kamar yarda kika sani kuma bak’innata sam bai dameta ba balle tayi shafe-shafe kullum cewa take haka Allah yaso ya ganni. Tayi karatu sosai duk da karatun nata yafi k’arfi ana addini na bokon kam ka’dan ta samu a k’aramar sakandire ta tsaya. Murmushin dai ta haske shi da shi da ya sakashi ya tsaya cak yana kallonta da alama addu’ar da muka duk’ufa yi ni da sadiya taci don kullum addu’armu Allah yasa ha’duwar farko ubangiji ya jefa k’auna mai girman dutsen dala a Zuciyarsa, ba ta kowa ba sai ta Sadiya baiwar Allah da Sam Duniya da abinda yake cikinta ba su dameta ba. Da fara’a ta na mik’e ina aukin fa’dar Ta’al Ta’al Ta’al! Wata irin dariya naji Sakina ta shek’e da ita har da dafa ciki. Raina a b’ace nake kallonta ganin kamar ta mayar dani mahaukaciya, Lauratu tayi kanta a zafafe tana fad’in Uwarki kike wa dariya?” “Uwar ki wannan nake wa.” Ta fad’a cikin gwarin hausarta ina kallon Ummaru ya dafe kai cikin takaici ya “Zagi fa kika yi!” Sai naga ta bud’e hannu tana girgiza kai, shi ma kansa a k’asa ya ce “Didi ba zaginki tayi ba, ba mamaki jin kina yarensu ne abin ya burgeta kika ga tana dariya.” Na girgiza kai ina faɗin Yo ko da naji. Ku zauna” Sai naga wannan karan ta saki jikinta ta zauna har da d’an murmushinta tana kallon Laurat da ko kallonta ba tayi ba da alama bata manta abinda tayi mata wancan zuwan da ta zo ba. Hannu ta miƙawa Lauratu amma Laurat tayi shigewarta d’aki bata fito ba. Shi kuwa Gogan idanunsa akan Sadiya, sai da na gaji da kallon da yake jifanta da shi baka ganeta bane? Sai naga matarsa tayi saurin kallon Sadiya da alama wannan karan ta fara Jin yaren Hausa don haka don kar nayi ɓaranɓarama nace masa ta fata jin yaran Hausa ne? Ya girgiza kai ya ce "Ta fara ji Didi kawai dai ba sosai ta iya mayarwa ba" nace "Hakan yayi kyau, kada kace mịn baka gane Sadiya ba?” Girgiza kai yayi “Wallahi Inna ban Wanye da ita ba.” raina a bace nace Ai kuwa naga alama to tashi muje waje zan yi magana da Kai.” Ya kuwa bini muka shiga madafa. Idanuna cikin nashi na rik’e kunne nace “Ka jini da kyau Sadiya ‘yar gidan Baba mak’oci CE, ba zaka santa ba tunda ba anan tayi wayo ba daga yaye yar uwarta ta tafi da ita can Zariya sai da ta girma baka ma k’asar aka dawo da ita, itace matar da muka aura maka kashegarin ranar da ka gujemu.” Ji nayi kawai yana jan Innalillahi kamar na watsa masa wuta a jiki. Cikin wata iriyar murya ya ce “Yanzu Didi sai da aka yi aurennan?” Tab’e baki nayi ina kallonsa nace “Aure kam an yi shi yau shekarata uku kenan da aurenta akan ka, baka kuma isa ka saketa ba wallahi ka saketa sai na d’aga maka Nono, ko Bayan raina ban amince ka saki Sadiya ba. Ga can shiyyarku an gama d’aki biyu ne da parlour sai bayan gida a rumfa ta d’au d’aki ciki d’aya Sadiya dama an Zuba mata kayan a d’ayan ita kuma ta d’au d’ayan kuyi maleji kafin ku tattara ku koma.” Hawaye sosai ya zubo masa takaici yasa na fice daga madafar Na shige Rumfa. Idanuna a kanta tana ta faman yatsina tana kurb’ar zob’on da na kawo musu, nace “Kinyi ta banza ke Sadiya zo kije ga shi can ki kai musu abincin su k’arata a can yasan yarda zaiyi ya sanar da ita ke a matsayin kishiyarta, na san dai yau akwai dambarwar tsiya, da kinji taga-taga ki gudo suje can su k’arata ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka. Sadiya murmushi tayi tana yafa mayafinta idanunta akan matar tana fatan bata ji abinda na fad’a ba. Tsaki nayi nace “Duk iya hausarta ai bata isa ta kamo nan a Hausaba.” ********************************* Kai ranar mun ga abinda ake kira tashin hankali, ashe hausawa duk haukan da suke idan an musu kishiya na su Lami ne akan na Balarabiya Sakina, k’iri-k’iri ta fito daga ita sai d’an tofi da vest tana cilli da duk abinda ta samu a tsakar gidan tana sai ta tafi, idan kuma ya k’i barinta ta tafi sai ta kasheshi ta kashe Sadiya sannan ta kashe kanta. Duk ta jijjiwa kanta ciwo da kyar ya turata a d’aki ya gark’ame da d’an mukulli yana sakin ajiyar zuciya, murya a raunane ya ce “Didi kinga abinda na gaya miki ko? Su k’asar su wallahi basu san kishiya ba, kuma duk abinda ta fad’a zata iya aikata shi ba burga bace irin ta Malama Bahaushiya, don Allah a raba aurennan.” Na ce “Wallahi ba za’a raba ba sai dai ita ka saketa ta tattara ta koma k’asarsu don ni yanzu ba zan ma amince ka bita ba, balle su kashe min kai a can.” Da kyar da sid’in goshi Malam ya rarrasheta, yayi da guntun larabcin sa ya haɗa da guntun turancinsa sai ga shi tayi luf wallahi ta yarda ta amince zata zauna zuwa lokacin da zasu tafi. Tunda ta tabbata idan sun tafi da kyar zata barshi ya dawo nan kusa. Ni kuwa gefe guda, na dinga tsuma Sadiya da kayan magunguna kala-kala da na tanada saboda irin wannan ranar, har gyaran jiki nake mata a b’oye. Sai gashi kafin suyi shirin komawa Sadiya ta fara kwarara amai a bakin rariya da alama dai ta k’unso. Itama Sakina sai gashi ta fara nata laulayin. Hakan yasa ta uzzira masa sai sun koma can inda suka fi wayo. Ya lallab’a Malam aka siyar da wata Babbar gonar Malam d’in, ya bashi kud’in da niyyar zai je can ya kafa bisiness d’insa. Wannan kud’in shine silar arzikinsa. Basu tafi da Sadiya ba amma yayi mata alk’awarin ba zai kai shekara ba zai dawo da zarar ta haihu. Don kam ya karb’i Sadiya hannu bibbiyu ya tabbatar da zancen da nake gaya masa na kasancewarta yarinya mai hak’uri mai kuma ibada. Duk wani abin buk’ata na haihuwa sai da ya dire mata shi. Tun farkon cikin matarsa ta k’wallafawa ranta haihuwar namiji don kullum sai ta fad’a idan muna hira cikin gwarancin Hausarta zata ce “Insha Allah Sadiya na mata zata haifa ni kuma na maza.” Dariya muke mata Sadiya ta ce Allah dai ya kawo mai albarka. Ita ta fara haihuwa ta haifi Mace, suna yin arba’in da kwana biyu suka zo Nigeria Sadiya ta dinga murna da ganin y’ar nan ita da Lauratu, yarinya jajir kamar Balarabiya Ta d’auko uwarta Sak. Zuwansu da kwana goma Sadiya ta zankad’o namiji sak mahaifinsa tun a ranar Sakina ta fara bak’in ciki kuma ta kasa dannewa har sai da ya fito fili. D’an shirin da aka fara yi da ita duk ta watsar, ta janye y’arta ba ta barin kowa ya d’auketa. Kullum rayuwarsu suke yi a d’aki. Ko Na aika nace ta bani yayarku Najwa sai ta hana, Har na hak’ura na tattara ta na zubar. Ranar suna yaro yaci sunan kakanku muna kiransa Hammad shine a can k’asar waje sanda ya tafi baki fi shekara hud’u ba har yau kuma baiyi sha’awar dawowa ba. Ko shekara ba suyi da komawa ba suka dawo Nigeria gaba d’aya, don lokacin ubanku arziki ya zauna masa har ya siyi gida Anan cutar da Malam yake yi ya buk’aci ya dawo ya fara kula da k’annensa don ya tabbatat ciwon ajali yakeyi. Kamar yarda Sadiya take da tsohon ciki, wannan karan ma Sakina cikin ne da ita sai dai nata karami ne. Ranar da Sadiya take nak’uda na lura Sakina a k’age take taga abinda Sadiyar zata haifa, don dama kaf nice nake karb’ar haihuwarsu. Abin ikon Allah sai ga Sadiya ta haifi santalelen yaro wannan karan ma namiji. Sakina kuma da ta tashi haihuwa itama ni na karb’i haihuwarta sai ga shi ta haifi mace._ [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on wattpad Nazeefah381 ELEGANT ONLINE WRITERS (Haɗin kai shine takenmu.) ******************************** Hankalinta a tashe take duban yarinyar kafin ta ce “Wannan karan ma Mace ce?” Ina murmushi na amsa mata Macece kyakykyawa kuwa har tafi Najwa kyau.” Wani tsaki tayi, kafin k’wallar da ta taru a idonta ta zubo mata cikin muryar kukan ta ce “Ya Allah yaushe Zaka cika min burin da na dad’e ina fata.” Da sauri na janyo ista’aza raina a b’ace na ce “Sakina me kenan? Shin ba zaki godewa Allah ba da ya baki kyautar yara matan? ki kuma yi addu’a Allah yasa su zame miki sanyin Idaniya.” Hawayen fuskarta ta d’auke kafin Ta ce “Ni ban ta’ba son haihuwar mace ba, kullum burina da tunanina a haihuwar yara maza yake, sai gashi Sadiya tana samu ni ban samu ba.” A zafafe nace Allah ne yaso ya jarrabeki, sai kiyi ta istigfari, da kika samuma kike haihuwar wasu suna can suna rok’on Allah ya basu yaran ma kowane jinsi ne amma bai basu ba, Sai ke da kika samu har kike k’ok’arin tantance jinsin da kike so, ki tuba ga Allah kafin yayi fushi dake.” Na mik’a mata yarinyar ta karb’eta cikin halin ko in kula sai kuma ta saki d’an murmushi ba mamaki na ganin yarinyar kyakykywar gaske ce. ____________________________________ Bayan sunan yarinyarta ta biyu da sati biyu Najma Allah ya karb’i ran Malam bayan ya sha doguwar jinya, tabbas mun shiga alhini da tashin hankali kuma mutuwar ta shiga jikin mu sosai bare ni da nake ganin mutuwar tasa ni aka yiwa. Haka Rabbi yake baya barin wani don wani yaji dad’i. A tsukun lokacin bayan na fita daga takaba mahaifinki ya kammala wannan ginin da muke ciki Muka tattara muka dawo, cikin birnin Kano. Anan aka yi bikin Lauratu da Gadanga da ya auri k’anwar Sadiya Murjanatu. Anan kuma iyayenki suka ta hayayyafa har zuwa sanda aka zo kan cikinki, Sakina ta dinga murna da fallasuwar cikin, mu dai bamu san dalili ba. Wata rana taje asibiti ta dawo sai gata ta shigo d’akina da sauri ta zauna a saman kujera takarda a hannunta tana ta jifan Yayanku Hammad da murmushi, wanda bamu san dalilin da yasa ya tsaneta ba, duk da a lokacin bai zarce shekaru sha tara ba, yaro ne shi mai Kazar-kazar da fara’a ga son mutane amma tashi d’aya gaba d’aya halayensa suka canja ya zama mafad’aci, miskili da son kad’aicewa shi kad’ai ba kuma ya san ganin matar Babanku, Ko me yake da zarar ya ganta yake barin wajen. Kamar a tsorace yake da ita. Kuma tambayar duniya an masa ya ce “Bakomai” Ganin lamarin nasa kamar ya fara girmama Babanku ya tasa shi a gaba akan lallai sai ya fad’i dalilinsa, take ya sanar dashi son fita waje karatu aka ce ya zab’i k’asar da yake so ya ce “Birmingham” dake can a k’asar England. Nan kuwa aka fara yi masa shirye-shiryen tafiya wajen. Da murmushin ta mik’o min takarda tana cewa “Didi Burina zai cika, wannan karan cikin namiji nake d’auke da shi, bayan na k’i haihuwa har shekaru biyar saboda ina tsoron sake haihuwar mace sai gashi Allah ya cika min burina a wannan karan namiji zan haifa.” Ta fad’a idanunta cikin na Hammad, gani kawai nayi ya mik’e da sauri ya fice daga sashen nawa. Nima cikin murna nace mata “Masha Allah, abin Allah kenan da har kina cewa kin daina haihuwar?” Da murna ta mik’e ta fice ni kuma na bi bayanta ina taajjibin lamarinta. Duk cikun-cikun da akayi na son Hammad ya tafi karatu Allah bai yi ba, sai da aka ja lokaci. A tsukun wannan lokacin ina hankalce da shi tsana mai tsanani ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarki sam baya son ganinta. Sau tari na sha kama shi yana kuka amma tambayr duniya sai ya ce “Bakomai.” Har raina ya b’aci na tattara lamarinsa na watsar. Cikin Sakina ya isa haihuwa, ta fara d’igimi da shirye-shirye, d’aki guda ta ware a b’angarenta aka zuba kayan yara maza, komai fari da kalar shud’i, kalar maza kenan a lokacin naji suna fad’a. Duk wani tattalin arzikin Sakina akan cikin nan ta k’arar dashi, har shirin Suna duk tayi. Wannan karan ma, cikin dare ta fara nak’uda aka kira likita, da ni da likitar muka karb’i haihuwarta. Tun da tayi nishi ko zafin nak’udar bata ji ba ta zuba ido tana son ganin mai ta haifa. Nice Na zaro ki, gabana ya fad’i ganin dai wannan karan ma an kuma macece ta haifi mace, tun kafin a yanke cibiya Sakina ta cire kunyarta, cikin gwarancin hausarta take cewa na mik’o mata shi ta ganshi, gaba na ya dinga luguden daka ganin mace ce ban san kalar haukan da zata yi ba idan ta ganki, ban da kasancewarki mace duk a yaran da take haifa ke kika zo da duhun kala. Murmushin yak’e Na saki. “Bari ki shirya a tsanake sai ki ga babyn, ki shiga ki gasa jikinki tukunna, Ai ba gudu ake ba.” Bata min musu ba, ta mik’e ta shige toilet, ni kuma na fice da jaririyar nayi mata wanka tas a falo. Na sink’eta cikin kayan sanyi burina ta bata Nono a karan farko kafin ta san abinda ta haifa. Zai ma yi wuya na gaya mata yau. A bakin gado na tarar da ita, tayi kyau sosai cikin shigar atamfarta England y’ar Ghana. Na mik’a mata Babyn bata kawo komai a ranta ba ta fidda wankakken Mamanta ta bata ta sha sosai ba tare da sanin me ta haifa ba. Likitar naja gefe nace ta ja bakinta tayi shiru kada ta sanar da ita. Amma me? Cikin talatainin dare na dinga jin wani irin bugu kamar za’a jijjige min k’ofa a razane na farka ina fad’in wanene?” Muryarta a shak’e ta ce “Ni ce” Na bud’e k’ofar gabana na fad’uwa ina fad’in Sakina Lafiya?” Duk da Na San dawar garin. Mik’o min jaririyar tayi fuskarta a had’e ta ce “Wallahi, ba zan shayar da ita ba, wallahi asiri aka yi min kuma bani da haufi Sadiya ce tasa matsafa suka canja min yaro na, namiji aka nuna min har a scanning a mafarkina kuma namiji na gani.” Tsananin mamaki yasa na kasa ce mata komai sai karb’ar yarinyar da take shirin yar da ita nayi, ko pampers babu a jikin yarinyar sai tsala ihu take. Raina a b’ace nace “Yanzu Sakina wannan wani shirme ne? A darennnan zaki kawo min yarinya ya kike so nayi da ita? Ina da abin bata ne? Kina ganin tana Kuka.” “Wallahi sai dai ta mutu, in dai da Nono na zata rayu wanda na bata ma don ban san mace bace.” Daga haka ta juya a fusace ta shige sashenta, duk da kiran da nake k’wala mata amma tayi burus dani. Tilas na juya da ke cikin d’akina, Na jik’a dabinon ajwa a ruwan zamzam shi na dinga baki har aka wayi gari. Da Asuba Babanku ya shigo b’angarena kamar yarda ya saba shigowa duk asuba. Mamakine ya kamashi gani na da yarinya a zaune na zuba uban tagumi. Hankalinsa a tashe ya dinga tambayata “Lafiya?” Na ja ajiyar numfashi idanu na cike da kwalla Na fara gyara zama ina Bahijja labarin abinda ake ciki, Salati ya saka. Dai-dai lokacin da Hammad ya shigo, Babanku ya mik’a masa yarinyar ya ce “Karb’eta kaje falo ina fitowa.” Wata irin zabura yayi yaja baya yana girgiza Kai, kamar yaga abin tsoro sai kuma ya fice da sauri cikin tsananin b’acin rai. Mamaki ya kama mu ni da Babanku, sai dai ya girgiza kai ya fice da yarinyar a hannunsa. Dambarwar tsiya aka kwasa, tsakaninta da shi akan sai ta shayar dake amma ta k’ek’asa k’asa ta ce sam ba zata yarda ba sai dai ya saketa. Ganin lamarin ya ta’azzara yasa naje nace ya fice na karb’i yarinyar da zummar na bawa Sadiya da ta nuna tana sha’awar rik’eki, amma nan ma ta k’ek’asa k’asa Ta ce bata amince a bawa Sadiya ke ba, ta karb’eki a hannuna sai dai sam ta k’i yarda Ta shayar dake sai dai madara haka kika tashi a gantale wajen y’an aiki, wani lokacin na karb’oki wani lokacin ta bani haushi na k’yaleki. A tsukun lokaci abin Hammad ya ta’azzara dole aka sadashi da asibiti nan ya fara ganin likita, aka d’ora shi kan magani muka samu ya samu lafiya ya tattara ya tafi karatu. Bai sake waiwayar garin ba sai bayan shekara hud’u lokacin da ya dawo sai kuma yazo da sabon salo ya dinga janki a jiki, yana nuna miki Soyayya da kulawa, kuma ko Uwar da ta kawo ki duniya ma bata isa ta dokeki ba matuk’ar yana wajen, sai muka lura a lokacin ma kamar wani shakkarsa da tsoronsa take ji. Bana manta wata rana kin dawo daga Islamiyya baki fi shekara biyar ba shi kuwa a lokacin shekararsa ashirin da hud’u,kika yiwa Amminku laifi ko sugar kika zubar mata ta dinga jibgarki sai ga shi Allah ya kawo shi, ya dawo daga companyn mahaifinku da yake tab’a aiki a can, yana ganinki kina kuka yaja hannunki, kuka nufi wajen da take ya shiga surfa mata masifa abin har mamaki ya dinga bamu ganin yarda yake surfeta da masifa amma tayi shiru har ya gaji ya tafi. Shine fa bayan kwana biyu ya gama shirinsa, sai gashi yaje Gwarzo yake gaya min zai koma Birmingham, hankalina ya tashi nace bai isa ba ya bari a masa aure. Girgiza kai yayi ya ce “Ba zan iya k’ara ko kwana guda ba akan jibin da zan tafi idan kun shirya auren ku samo min matar a d’aura auren zan mata visa aka kawo min ita ina maraba da zab’inku ko wacece. Shine fa muka sama masa Nanna y’ar yar Babarsa, aka yi auren aka tura masa ita. shi kam bai sake dawowa ba amma ita Nanna tana zuwa hutu duk K’arshen shekara yaranne dai baya bari tazo dasu saboda makaranta. Wannan shine abinda na sani na dangane da labarinki da dalilin tsanar mahaifiyarki gareki, a zahiri dai wannan shine bamu san bad’ininta ba, sai ki cigaba da hak’uri har Allah ya nuna mata ikonsa a kanki ba mamaki kece wacce zata zo tayi alfahari da ita nan gaba kad’an ki zame mata Sanyin idaniya.” Tuni hawaye ya gama b’ata mata fuska, a yau ta tabbatar ba laifin da tayiwa mahaifiyarta laifinta d’aya da tazo a jinsin Mace, menene laifinta anan? Me yasa kuma bata tsani sauran y’ay’anta ba sai ita? Ko don ita bak’a ce? Tabbas hakane aka amsa mata daga can k’asan zuciyarta, ya zama lallai ta nemawa kanta mafita kafin ciwon damuwa (Depression) ya kamata. [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE ? LIttafin Nazeefah Nashe. 08033748387 Follow me on wattpad Nazeefah381 ELEGANT ONLINE WRITERS ********************************** BIRMINGHAM Dake k’asar England. Unguwar padstow Road Birmingham B24. A cikin d’aya daga cikin gidajen rent d’in masu bala’in kyau. Gida ne mai d’auke da 3 bedrooms da 1 parlour sai kitchen da dinning area. Kamar yarda aka san gine-ginen turawa wannan ma gini ne da yake d’auke da tsari, da zarar ka kalleshi tun a waje zai birgeka balle idan ka shiga cikin ainahin building d’in. Nanna ce zaune gefe guda da waya a hannunta tana kuka sosai bayan samun sak’on mutuwar Babanta. Ta sake kallon Hammad mijinta a karo na biyu kafin ta ce “Kayi wa darajar girman Allah ka bini mu tafi tare har yarannan, yanzu fa Khairi shekararta Sha d’aya amma bata san danginka ba balle nawa, sannan yanzu ma Baba na ya mutu kace ba zaka ba, wannan wace irin masifa ce wai me aka yi maka a Nigeria?” Ta fad’i furicin hawayen na sake kwarara a fuskarta na zallar b’acin ran mijin nata wanda wani lokacin idan ya rikid’e mata sai ya zama kamar bak’in kumurci don fad’a da b’acin rai, wani lokacin kuma suyi zamansu gwanin sha’awa. Wannan karan ma ya rikid’e d’in, don runannun idanunsa ya d’ago ya zuba su a kanta, wanda ya sata had’iye kukan babu shiri. Tayi saurin mik’ewa zata shige d’aki da azama ya fincikota, rintse idanunta tayi tana jiran taji saukar mari kamar yarda ya saba a duk sanda ta kawo masa zancen zuwan Sa Nigeria. Madadin marin wannan karan hankad’ata kawai ya yi ya mik’e da sauri ya shige bedroom d’insa ya kulle k’ofar har da murza key. Nanna ta runtse idanunta, don ta San tabbas abinnasa yazo, idan abin ya tashi zame mata yake kamar mahaukaci, sai kace mai aljannu. A hankali furucin Ya Allah ya fito daga bakinta. Ba zata bishi ba don ta san ko zata shekara tana bugu ba zai bud’e ba a wannan bad condition d’in da yake. Allah ma ya taimaka yau baya zuwa aiki da bata san yarda zata yi da shi ba. Wayarta ta shiga lalube ta fara danna kiran Mahmah, gwara ta gaya mata tayi iya yinta ya ce Ba zai zo ba. Bugu biyu Mahmah ta d’au wayar, dafatan Allah yasa surukartata taci nasarar shawo mata kan d’annata. Madadin daddad’an labarin sab’anin haka ta samu. Mahmah ta runtse ido zuciyarta na karyewa bata san dalilin yaronta Na rashin son zuwa inda suke ba, ko su suke son ganinsa sai dai yayi Musu Visa suyi tattaki su je. Gashi wannan karan Didi ta takura ta gaya musu dole su saka Hammad d’in yazo gida musamman da surikinsa ya mutu. Ta ja aijyar zuciya kafin ta ce “Shikkenan, ki kyaleshi zuwa anjima zan kira shi, dama har yanzu yana shiga wannan condition d’in?” Nanna ta ja ajiyar zuciya kafin ta saki kuka na nuna alamun zallar damuwa ta ce “In dai zan masa zancen da ya shafi Nigeria sai yayi.” Mahmah tayi jim kafin ta ce “Kin ga kuwa dole yazo ko dan na nema masa Magani, zuwa yanzu kam na tabbata ba k’alau tabbas akwai wani k’ulli da Allah ne kad’ai ya barwa kansa sani.” Daga haka suka yi sallama, Mahmah ta lalubi numberr Hammad ta tura masa text. Slm. Ya zama dole ka taho Nigeria a wannan gab’ar idan ba so kake na bayyana maka b’acin rai na ba ta hanyar sallamaka a cikin zuri’ata. Daga haka ta ajiye wayar, ta jingina kanta jikin kujera wannan karan zuciyarta ta kasa sukuni har sai da ta zubar da wasu tarin ruwan hawaye. Rashin gane takamaimai matsalar d’annata abin yana ci mata tuwo a k’warya kullu yaumin da abin take kwana ta tashi kuma, don dai ta kasance mace mai juriya ba kasafai take bari b’acin rai ya bayyana k’uru-k’uru a fuskarta ba. Ta haddaci k’unshe b’acin rai tun farkon aurenta da mijinta, da ta tabbatar ba sonta yake ba yana zaune da ita ne kawai don itace zab’in Didi mahaifiyarsa, amma soyayyarsa kam tana ga Sakinah Balarabiya da soyayarta yake kwana yake tashi sau tari ya sha kiran sunan Sakina a cikin barcinsa ko a yayin da suke saduwar aure. Duk ta danne take zaune da shi da zuciya d’aya, ta kowane hali kuma burinta yi masa biyayya ko ta samu rahmar ubangiji tunda dai shi yayi umarni abi su. Ta share hawayen da ya zubo mata a fili ya furta YA ALLAH ka kawo mana d’auki akan bawannan naka ka sanyaya zuciyarsa ka dawo min da hankalinsa gida. ____________________________________ Farkawarsa daga nauyayyen barcin da ya sureshi yaci karo da sak’on mahaifiyarsa. Zuciyarsa ce ta buga ya tabbata yau Mahmah fushinta ya kai mak’ura, don bata tab’a nuna masa b’acin ran wanzuwarsa a Birmingham ba sai yau. Shi kuwa ya tabbata idan yaje Nigeria ya sake ganin yarinyar nan ba abin mamaki bane zuciyarsa ta buga. Shi a nasa tsarin yayi sallama da k’asar sa ta haihuwa babu abinda zai sake mayar da shi. Me yasa Mahmah zata yi masa wannan furucin bata san zamansa anan shine kwanciyar hankalin kowa a zuri’arsu ba. Cikin wani irin yanayi ya murza goshinsa tare da furta Oh Allah. Ya sake duba agogonsa sai yaga har lokacin dawowar yara tuni ya shige ya tabbata zuwa lokacin Nanna ta d’aukosu. Wanka yayi kafin ya fita parlourn. duk da zuciyarsa a tunzire take bai hanashi shafa kan yaran nasa ba da suke zaune suna buga ps game a tv. Idanunsa akan Yarinyarsa ta biyu Kamla, yana mamakin sake bayyanar kamatarta da waccan yarinyar Hamda da gaske suna kama sosai yarda take black beauty haka Kamla take da eye shape da mouth d’insu duk d’aya. Cikin k’udirar Ubangiji sam ba banbanci a zubin a halittarsu, ba zai mance kamannin k’anwar tasa ba a idanunsa. Da sauri ya rik’e kansa yana tuhumar kansa da zamantowarta k’anwar tasa a zahiri take k’anwarsa amma a bad’ini shi da uwarta sun san sai dai su kira ta........ Ya runtse idanunsa baya son tuna matsayin yarinyar, abu ne da zai iya kiransa direct ABIN KUNYA da Allah Wadai. Murmushi ya sakarwa Nanna da take tsaye da cup d’in coffee tea a hannunta tana mik’a masa, duk da ranta a b’ace yake kuma idanunta sun nuna ta sha kuka bata fasa kyautata masa a kowanne yanayi yake. Da gaske Nanna ta cancanci kansa tsaye ya kira ta da suna MACE TA GARI. Ta kowanne fanni ta cika ta tumbatsa bata da makusa ko kad’an. Hannunta ya ja ya zaunar a gefensa bayan ya lura hankalin yaran su yana kan t.v game, don duk kasancewar suna rayuwar turai suna matuk’ar jajircewa wajen tarbiyyar yaransu. Ya rungumota jikinsa sosai, kafin a kunne ya rad’a mata “Am very much sorry, zamu wuce Nigeria within this week Allah yaji k’an Baba.” Wani irin tsalle tayi tare da rugumeshi, wanda har sai da yaja hankalin yaransu. Abul khair ya ware ido yana furta What?” Nanna ta jashi jikinta had’e da cewa “Uban masu gida zamu je Nigeria k’asar da kuke son zuwa gashi har Babana ya mutu bai sanku ba.” Da Hausa tayi masa maganar kasancewar sosai suke musu Hausa shi yasa yaran suka iya yaren Hausa tunda nan ne asalinsu da tushensu. Yaran ma sosai suka shiga murna Musamman Khairi da burinta dama taje Nigeria. A ranar ya fara nema musu booking flight kafin kashegari yaje ma’aikatarsu ta Miller Hughes construction Building contractor ya sanar musu yana buk’atar d’aukan hutu. Bai sha wahala ba wajen amincewarsu musamman sani ba tab’a nema yayi ba. Daga nan ya tafi makarantar yaransa Junior league of Birmingham sunshine school suma ya fad’a musu, suma suka nuna masa bakomai zasu bawa yaran kayan karatun da zasu dinga yi kafin su dawo. Shikkenan suka fara shirye-shirye yayi waya ya sanar da Mahmah da Abbu zuwansu in the next four days. Gaba d’aya gidan murna aka d’auka na zuwan Babban Yaya. _____________________________ Gefe guda kuwa Sakina hankalinta a tashe yake da zuwan nasa, a zuciyarta ba sak’e-sak’en da ba tayi ba, wato bai ji abinda tace masa ba akan sake dawowarsa Nigeria shine zai sake dawowa, sam bata san wanzuwarsa a gidan gudun bankad’uwar sirrinsu. Shi yasa ma take ta bankawa Malamai kud’i akan a cire masa son gida gaba d’aya a ransa. Hanakalinta ba k’aramin tashi yayi ba ta shiga suntiri cikin bedroom dinta cikin mummunan b’acin rai tabbas lokaci yayi da zata san mataki na k’arshe da zata d’auka akan Hammad, duk da dai ta san ba zai tab’a fitowa ya gayawa duniya wannan sirrin ba tunda shina kamar ya d’au wuk’a ya dab’awa kansa ne. _____________________________ Gidan a hargitse yake sosai da shirin dawowar Hammad d’in. Abbu yasa an fitar da kayan da yake sashensa tun yana saurayi gaba d’aya, akayi fenti tare da canja komai Na toilet da furnitures d’in ciki. D’aki biyu ne da parlour kawai a ciki sai wani k’aramin kitchen. Guri ya d’au harami sosai sai jiran dawowar Babban Yaya. Y’ayan su Gadanga k’annen Abbu duk Didi tayi musu waya akan su zo. Musamman kasancewar lokacin hutun second term ne anan k’asar mu ta gado Nigeria. Yaran Gadanga Ali k’usar yak’i hud’u: Salima Salima Salman sai Salma. Ita kuwa Asma’u yaranta uku Sajeed, Sajida sai Sajjad. Lauratu tana da hud’u: Sa’ad,Sa’adatu sai Sadik da Saddik’a. Nan kuwa gidan Umaru Usman Dan Borno da aka fi sani da UU D’an Borno kamar yarda kuka sani Sadiya Na da yara biyar Hammad Humaid Sai Hamidan da Abdul Hameed da Humaid. Ita kuma Sakina (Ammi Na da Biyar) Najwa ce babba sai Nasma da Ahlam sai Muneerat da Hamda. Wad’anna sune jikokin Didi tsohuwa mai ran k’arfe, mai tsage gaskiya duk d’acinta. Manyan duk an aurar dasu idan ka cire d’akin Ammi da mace d’aya jal ta aurar. Inda ta auri wani hamshak’in d’an kasuwa suke zaune a can k’asar ibadan yanki yarbawa duk da bahaushe ne ya zab’i zaman ibadan a can ya ke duk wasu kamfaninnikansa saboda rashin kishin arewa. _____________________________ Da k’arfe hud’u na yammacin ranar ta juma’a suka Sanka a airport d’in Malam Aminu Kano international airport da ke birnin kano. Kaf k’annensa maza da cousins brothers d’insa ne suka zo tararsa. Suka fara saukowa daga jirgin, ransa ya b’aci lokacin da ya fara shak’ar iskar Nigeria. Sanye yake cikin black jeans na companyn Gucci, Sai casual T.shirt Na companyn Tommy Hilfiger dake U.S da rigar sanyin Tomford Bumber a jikinsa sai zabga k’amshin turarensa na kullum yake Emporio armani oud. K’afafunsa sanye da takalman Dolce and Gabbana logo embossed leather slippers, bak’ake Wanda suka haskaka kyakkyawar tausashshiyar fatar k’afarsa. Idanunsa kuwa cikin black glass suke Na companyn Gucci. Hannunsa da yake d’aure da agogo k’irar Gucci bracelet watch ya kalla. Yana sauka daga matattakalar jirgin fuskarsa a d’an d’aure yana sakin tsaki akai-akai musamman ganin arnen zafin da ake kwararawa a k’asar Nigeria mai barazanar dafa fatar mutum, musamman Su da suka dad’e basa k’asar. Ya ilahil Alameeen’ ya fad’a murya a cunkushe. Daga kallon farko idan kayi masa zata zaka yi saurayi ne da ba zai haure matakin shekaru takatin ba ba zaka Ta’ba bashi shekaru har talatin da takwas ba. Da gudu k’annesa suka rungume y’an cutest yaransa. Idanun Hamood cikin na Kamla da sauri ya bud’e baki yace “Masha Allah Hamda’s carbon copy.” Da sauri sauran ma suka kai dubansu kanta suna ta’ajjabi da mamaki a zahirance suka ce “Wannan dai Hamda ka haifo y’a.” Gabansa ne yake fad’uwa a duk sa’ilin da suka had’a Hamda da y’arsa, duk da zahiran shima ya san suna kama irin kamar nan da dole idan Na gansu ka san JININ SU D’AYA. [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin JIKAR NASHE Ya Abin Yake? Page 9. 08033748387 Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861 Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd _________________ Haka suka d’unguma zuwa ainahin main House d’in su da ke unguwar Hotoro G.R.A. Mutanen gidan suna jin shigowar motocinsu suka fita a guje domin tararsa. Sakina ce kawai bata fito ba, da yaranta masu bak’in hali Najma da Nasma. Amma hatta da Muneerat sai da ta fito a guje duk da kiran da Ammin take zabga mata. Tunda ya fito ya zubawa k’annensa ido yana mamakin yarda suka girma lokaci guda. Har zai shiga sashen mahaifiyarsa Hamood ya kama hannunsa had’e da fad’in “Big Bro rufa mana asiri idan ba so kake Didi tasa ayi yak’in duniya na biyu ba.” Ya d’an bud’e ido yana kallon k’aninnasa, saboda sam ya manta a irin wannan lokacin Didin tana kasancewa ne a gidansu. Ya juya direct ya nufa sashenta, yaransa da matarsa suna bin sa da sauri. Mahmah da take tsaye a window Ta saki Hamdala don farin cikin ganin yaronta, duk da kawaici da Alkunya ya hanata fita ta ganshi. Didi da azama ta mik’e tana janye k’afarta da Hamda take shafawa Man zafi. Cikin fara’a kamar bakinta zai yage take fad’in Maraba lale, Oyoyo da mutanen Birmingham Masha Allah tubarakallah. Ta rungumeshi cikin tsananin farin ciki. Hamda kuwa idanunta cikin na Kamla tana mamakin tsananin kamarsu. Su kansu su Khairi kallonta suke musamman Nanna da ta kasa janye idanunta daga kallon yarinyar mai kama da tata d’iyar Kwabo da Kwabo. Saboda duk zuwan da take Hamda lokacin tana makaranta shi yasa basu tab’a had’uwa da ita ba. Hamda cikin ladabi ta durk’usa ta gaida Nanna, ita kuwa ta jata a jiki tana kallon Didi da Hammad da ya rintse idanunsa yana mamakin yarda yarinyar ta sake girma, da gaske kuma tsananin kamanninsu ya sake bayyana da Kamla musamman yanzu da suke zaune waje d’aya. Cikin Masifa Didi ta dinga korar mutanen da suka yi dandazo a falonta. “Haba yau naji masifa, a bar mutum ma ya huta da jikokinsa ba za’a bari an zo an zuba musu ido kamar me? Ni jaraba ta yaran gidannan ta fara isata, mutane ga ido k’wala-k’wala, duk sun bi sun gado manyan idona na masifa.” Ta dinga mita bayan sun tafi sun barta da jikokinnata sai kace su ba jikokinta bane, ko da yake su kansu sun san soyayyar da takewa Hammad daban ce, ko kuma don kasancewarsa shine Jikanta Babba a maza tunda Najwa da suke kira Yana ta girme masa. Sai da suka tafin sannan ta zuba idonta akan Hamda ta saki baki tana kallon kamanninsu da Kamla. Gaza shiru tayi har sai da ta magantu “Ikon Allah, ikon gaske kai kuma Hammadu sai ka haifo mai kama da Hamda kwabo da kwabo, ko wa suka yo a dangi don mu dai kaf danginmu ba masu kama da mutanen itofiya (Ethiopian). Idanunsa ya zuba yana kallonsu, a duk sanda kuma ya kallesu sai gabansa ya buga fad’uwar gaba ta sameshi, baya son ana yawan ambaton kamanninsu haka ne yake sawa yaji k’irjinsa kamar ya tarwatse. Nanna ta ce “Ai haka lamarin ubangiji yake, ba abin mamaki bane musamman kasancewarsu Jini d’aya, ai k’arfin jini ya zarce haka.” Hammad ya sake jin dukan da k’irjinsa yake ya tsananta musamman da ake ta nanata kalmar Jini d’aya. Anya kuwa wannan sirrin da suke k’ok’arin k’udindunewa nan gaba kad’an kuwa ba zai fallasu ba. A sama ya jiyo muryar Didi tana tsaki “Ayi mace lusara, kina girma kina cin kashi abincin ma jira kike nace ki d’ebo ki kawo musu? Bayan tun safe muke tsaye akan digadiginmu muna aikinnan amma ba zaki tashi ki kwaso su ba.” Ita dai Hamda bata bari ta k’arasa mitar ba, sai tsintar ta suka yi a k’ofar kitchen, Nanna Ta sake binta da kallo tana yaba kyau da tsarin halittar zubin jikin yarinyar, farin ciki ya cikata da ta tuna itama Kamlanta haka zata dawo mai kyau idan ta girma. Shi kuwa Hammad tunaninsa daban yake ta yarda yake mamakin girmanta, duk da ba wata k’iba bace da ita amma duk wasu halittu na y’an matancinta a cike taf da albarkatun ubangiji. Yayi ta’awwizu da tunanin hakan da yayi don ya San sarai ba shi da hurumi anan. K’ememe Didi ta hanasu tafiya wajen Mahmah da ta kasa zuwa ta gansu, anan suka zube akan daddumar Didi mai taushin gaske suka ci abincin mai dad’I don Didi gwana ce wajen girki shi yasa Hamda ita ma ta koya. Ta iya girkuna kala-kala. Shigowa U U D’an Borno ya yi yana fara’a, da farin cikin ganin yaronsa da familynsa. Da sauri Hammad da Nanna suka durk’usa don gaisheshi haka nan su Khairi da Abul khair ma suka gaisheshi. Idanunsa akan Kamla yana dafe da kan Abul khair ya ce “Didi kin ga ikon Allah ko? Tunda naje barkar yarinyar nan na ce miki kamar su d’aya da Hamda, don har hotonta Na d’auko a waya Na had’a da Na Hamda wallahi ba banbanci ko kad’an banbancin d’aya ne wannan lotsawar da Hamda take da shi a k’asan hab’a ita Kamla a gefen Hanci take da shi. Tabbas kun haifawa Hamda y’a don nan gaba ko guduwa tayi da ita ba wanda Zai ce ba y’arta bace.” Gani suka yi kawai Hammad ya rik’e kansa ya mik’e, had’e da cewa “Godiya nake Didi, bari naje na gaida iyalan Abbu” daga haka yasa kai ya fice da sauri bai saurari surutun Didi ba. Su Nanna ma suka bi shi suna dariya. B’angaren Ammi ya fara shiga direct, yana fatan ya iya danne b’acin ransa idan yayi arba da fuskarta da kai tsaye yake kira bak’ar Fuska. Addu’oi ya fara yi a zuciyarsa kafin ya saka kai cikin sashen nata. A zaune ya sameta saman kujera, gaba d’aya yanayinta zaka kalla ka tabbatarwa kanka da gaske yau bata cikin nutsuwar zuciya, don dai ko kallabin kanta bata d’aura ba balle akai tajallin gyaran gashi. Idanunta k’ozai-k’ozai babu kwalli. Guri d’aya ta zubawa ido, da alama tayi nisa cikin zuzzurfan tunanin da ya ke mata kaikawo a zuciya. Bata ji sallamarsu ba sam, sai k’amshin turarensa da ya riga ya zauna rad’am a hancinta ba tun yau ba tun yana saurayi shine dai ainahin turaren da yake amfani da shi. K’amshin ne ya farkar da ita cikin razani, idanunsa kuwa suka gauraya cikin nata. Y’ar fara’ar da take fuskarsa ya d’inke tsaf, tare da amsa gaisuwar su Najma da suke gaisheshi cikin mutuntawa, kasancewar sun san shi mutum ne da baya wasa da su tun suna yara balle yanzu da ya mallaki hankalin kansa. Shigowar Kamla ne yasa Ammi wani irin mik’ewa da sauri cikin razana tana dubanta. Ganin yarda idanu suka yi yawa a kanta sai kuma ta sunkuyar da kai ta waske tana jan hannun Abulkhairi. Abin mamaki madadin shi da yake matsayin d’a wajenta ya gaisheta, itace take gaisheshi cikin basarwa da sunkuyar da kai tamkar dai surikinta. Mintuna uku cikakku bai k’ara a d’akin ba, ya mik’e da sauri ya fice, yana jin zcuciyarsa kamar ana hura masa wuta. Suma su Nanna suka d’unguma suka bishi. Hakanne ya bawa Ammi damar shigewa d’aki a sukwane tana sake lalubar numberr wayar babbar aminiyarta da tun safe take nema bata shiga. Wannan karan ma dai still wayar a rufe take kamar yarda ake ta sake jaddada mata a waya. A kujerar parlourn Mahmah ya zube idanunsa a runtse kafin ya bud’e ya zube su cikin na mahaifiyrsa da take ta kallonsa cike da murmushi. Rabin hankalinta kuma yana kan Nanna da y’an jikokinta da sam babu shakuwa a tsakaninsu. Taja hannun Abul khairi tare da fad’in “Maigidan da ba awo ba cefane.” Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya samu damar gaishe da Mahmahn cikin k’arfin hali da dauriyar zuciya. Mahmah ta amsa masa zuciyarta cike da farin cikin zuwansa Nigeria. Sun dad’e suna hira duk da shi rabin hankalinsa ba akan hirar yake ba, sau tari sai Nanna ta sako shi a zancen sannan yake ankarewa da nisan tunanin da ya lula. Ganin da ya yi ya rasa samun nutsuwa ya mik’e ya nufi sashensa, don ya sake nazari sosai akan lamarin da kansa tsaye zai iya cewa ALMARA. _____________________________ Cikin sa’a k’arfe sha biyun dare ta samu numberr aminiyarta ta ta shiga ta saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya, duk wani abu da ya tokare mata na b’acin rai ya sauka daga k’irjinta. Gani take tamkar ta samu mafita ta gama. Murya a cunkushe ta ce “Ke kuwa Kady ina kika shiga tun safe nake nemanki?” Kady daga can taja ajiyar zuciya “Ke dai bari, ya aka yi? Akwai matsala ne?” Tsaki Nanna taja ta ce “Idan kin ji matsala d’aya kenan matsaloli dai yaronnan Hammad fa ya dawo k’asar nan.” “Innalillahi!” Daga can Kady ta zabga kafin ta ce “Yanzu meye abin yi?” Ammi taja tsaki “Ke zan tambaya kady, wallahi kaina ya k’ulle kin jefa ni a matsala da na sani tun farko ban karb’i shawararki ba, takaicina d’aya ranar fallasuwar sirrina, ranar da za’a tono b’aragurbin k’wan da na burne, ranar da jama’a da dama za su......” kuka ne ya kufce mata. Kady tayi tsaki “Yanzu na barki kiyi kukan kenan? Idan kin gama kukan sai na kiraki, tunda kuka ne zai mana maganin matsalarmu.” Had’iye kukan tayi da kyar ta ce “To yanzu ya kike so ayi?” “Ki bud’e kunne da kyau ki jini, idan zai yiwu a salwantar da ran Hammad kawai idan ba haka ba komai na iya faruwa.” Ammi ta saki ajiyar zuciya a karo na biyu kafin Ta ce “Kina ganin haka ne mafita?” Tsaki kawai Kady ta ja tare da latse madannin wayar ta mutu ta san sarai Ammin yanzu zata waske zancen kisan, duk da ita dai bata hango wata mafita bayan wannanba. ___________ Sai da ya yi wanka sannan ya samu nutsuwa, duk da har a lokacin yana jin yanayin yarda k’irjinsa yake duka, Kansa yana matuk’ar sarawa, a zahirin gaskiya ji yake ya Kamata ya sanar da mahaifiyarsa zancen nan, duk da muninsa ya kai muni amma bai kamata ya b’oye mata ba ba yanzu ake ji ba gaba ake ji, tunda ya tabbatar Hamda bata da gadon mahaifinsa, Bai kamata kuma ta cigaba da amsa sunan Mahaifin nasa alhali shi yasa ba ubanta bane....... To fa! Wannan shine Ya Abin Yake? [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe. Ya Abin Yake? 08033748387 Follow me on Wattpad @Nazeefah381 ArewaBooks @Nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e Da safiyar ranar ta shirya tsaf, da azama ta ja motarta sai gidan Kady don sam kasa barci tayi jiya tambayar duniya kuma Abbu yayi mata sai ta ce Bata jin dad’i ne, shi yasa yau tana cewa zata Asibiti bai yi nawar hanata ba, don yanayin da ta kwana shi kansa abin ya yi matuk’ar rikitashi, sai ya ce tun bayan haihuwar Hamda bai tab’a riskarta a yanayi kwatankwacin na jiya ba. Daga jin yanayin horn d’in motar Kady Ta tabbatar mutuniyartace ita kanta sam bata cikin nutsuwa don haka yau da wuri ta sallami mai gidan, tana shirin kiranta a waya sai gata ta bayyana. Da sauri ta bud’e k’ofar hasashenta kuwa ya yi dai-dai don Sakina ce cikin wani irin yanayi ta shigo parlourn, wullar da jakarta kawai tayi ta ce “Kina ganin kashe Hammad shi zai rufe b’aragurbin sirrina? “K’warai kuwa.” Kady ta masa mata cike da k’warin gwiwa “Rashin salwantar da rayuwar Hammad shi yake nuni da fallasuwar b’aragurbin k’wan da zai girgiza ahalin D’an Borno.” Sakina tayi tsai da ranta, kafin ta saki gwauran ajiyar zuciya, ta ce “Bana son salwantar rai, zan saka dai a sake masa gargad’i had’e da tabbatar masa da k’udirina na k’arshe idan har ya sake ya bayyanawa mutane gaskiyar lamari.” Kady tsaki ta ja, kafin ta ce “Ni ban ga dalilinki na rashin son kashe shi ba, mutumin da rayuwarsa kamar wata bala’i ce ga taki rayuwar, ke da kanki kince baya miki kallon mutunci balle ya girmamaki, kina tunanin idan ya cigaba da yi miki haka uwarsa ba zata so sanin dalili ba? Kina tunanin idan ya b’oyewa kowa zai iya b’oyewa mahaifiyarsa?” Sakina ta share zufar da ta game goshinta. Hankalinta a tashe ta ce “Tabbas zancenki na kan hanya, saboda yarinyarsa Kamla yarda kika san kaki yarinyar nan Hamda tayi saboda tsananin kamarsu, ni kaina har mamakin bayyanuwar kamar nayi, wallahi abin ya bani tsoro kamar dai wata ishara ce Allah yake so ya nuna....” “Shi nake so ki gane, ki cire duk wani shakku a kawar dashi daga doron k’asa, ina dalili? Tun ranar da abin ya afku na sanar da ke a kawar da shi kika wani ce a gargad’eshi, alhali kwalliya bata biya kud’in sabulu ba namijin dai da kike so baki haifeshi ba, kika tsaya cewa wai yaro ne zai ji tsoron tona hakan ga kowa, to ga dai yaro nan ya girma kuma yana shirin bankad’a duk wani sirri idan ba kiyi wasa ba, haba idan da nice ai da tuni an wuce wajen.” Sakina ta ja ajiyar zuciya “Shikkenan, ki bari zan shigo yanke shawara anjima insha Allah.” Daga haka suka yi sallama, Sakina kam ta samu salama a zuciyarta ta kuma amince da shawarar Kady tana ganin hakan kawai shine mafita a gareta, da ahalin D’an Borno family gaba d’aya. _____________________________ Tun asuba da ta farka bata koma ba gyara sashen Didi tayi kafin ta tafi sashen Amminta nan ma ta gyara. Wanka kawai tayi ta dawo parlourn Didin ta zauna had’e da d’aukar Alk’ur’ani tana karatu, Didi kuwa lazimi take, da radio a gefenta tana saurarar labaran BBC Hausa. Sai da Takwas ta cika sannan ta shiga kitchen don d’ora abin karyawa kasancewar juma’a ce Didin bata azimin tsofaffi don idan watan azimin tsoffin ya shiga sau hud’u take yinsa duk sati litinin,talata,laraba da Alhamis. Kunun tsamiya da ta saka wadataccen lemon tsami tayi musu, sannan ta soya musu k’osai da dankali da k’wai. Kafin kace me? Har ta gama, ta kawo Daddumar Didin ta jeresu. Didin shi mata albarka kawai take tana fad’in Uwarki tayi farar haihuwa sai dai ita bata san haka ba shashasha, a zamanin nan samun yarinya mai hali irin naki ai sai an tona.” Murmushi kawai Hamda tayi. Dai-dai lokacin da aka yi knocking k’ofar sashen Didin. Tsaki Didi tayi kafin ta ce “Jaraba, ko waye kuma da safiyar nan? Allah yasa dai lafiya.” Hamda ta kalli agogon parlourn ta ce “Didi k’arfe 9:30, yanzu ai ba sassafe bane.” “Gurinki ne ba sassafe ba wajen mutanen gidan nan kam ai ba mamaki yanzu suka yi juyin farko.” Hamda dariya ta guntse kafin ta k’arasa bakin k’ofar. Cikin sanyin muryarta ta ce “Wanene?” “Bud’e” kawai ya ce cikin dakewar tasa muryar. Gabanta ne ya fad’i sanin cewa shine tun jiya ta haddaci muryar tasa, da zarar taji take riskar kanta cikin wata irin razananniyar fad’uwar gaba. Hannunta na rawa ta murd’a handle d’in k’ofar bayan ta murza mukullin da yake jikin k’ofar. K’amshin turarensa ne ya fara dokar hancinta kafin ya shigo idanunsa a kanta, yarda ta mak’ale jikin bangon ya tabbatar masa da yanayinta na rashin sabo da jama’a. Kamar a tsorace take da mutane bata sakewa da su, kullum yanayinta na nuna kamar ace kyat ta zura da gudu. Idanunta a k’asa cikin rawar murya ta ce “Ina kwana?” D’auke idanunsa ya yi daga kanta kafin ya amsa da “Lafiya” ya shige ya barta a tsaye ta bi bayansa da kallo sanye yake da jallabiya mai gajeren hannu, wanda ta bayyana damtsen hannunsa da gashi ya kwanta luf a jikinsa. A gefen Didi ya zauna yana gaisheta cike da Kamala, idanunsa akan coolers d’in da suke zube bisa daddumar, dama ji yake kamar an wawashe masa kayan cikin sa kaf, ko don daga training wanka kawai yayi ya taho nan wajen Didi, kamar yarda ya saba tun a da, in dai Didin tana nan da safe nan wajenta yake karyawa. Cup kawai suka ga ya d’auka ya fara tsiyayyar kunun da yake cikin flask d’in sai zabga k’amshi yake na lemon tsami da kayan k’amshi. Da turirin da komai ya kai bakinsa, har hakan ya ba Hamda mamaki ganin yarda yake cin k’osan da zafinsa cikin hanzari ko ta kan Irish d’in bai bi ba. Haka dama shi yake cin abincinsa a hanzarce musamman idan yana jin yunwa, shi yasa yake da k’akk’arfan jiki kuma ginanne mai d’auke da murjajjiyar fata. Tsaki Didi tayi tana harararsa “Ni fa Hammadu bana son iya shege, waye ya gayyato ka nan kake shirin cinye mana abinci? Shi yasa ga kanan a tsaye k’ik’am da kai.” Fuskarsa ya d’aure sosai kafin ya ture kwanan k’osan cikin fad’in “Alhamdulillah” Didi ta saka salati bayan ganin ya wawashe k’osan tas guda biyar kacal ya bari. Murmushi ya sauke a fuskarta ya ce “Kin san rabona da irin abincin nan kuwa?” “Ina zan sani tunda ni ba Allahn musuru bace, kawai ka zo ka wawashe k’osan nan yarinyar nan ko ci ba tayi ba, tun safe take aiki akan digadiginta, ina ruwana y’ar uwarka ka cuta don wannan biyar d’in dai ba bata zan ba wallahi.” Ta fad’a tana dangwalar yaji ta cinyeshi tas. Hamda mik’ewa tayi ta shige d’aki don dama ita ba gwanar karya wa bace da wuri. Yabi bayanta da kallo cike da tausayinta sai ji Didi tayi ya saki ajiyar zuciya ya ce “Har yanzu uwarta bata karb’eta a matsayin y’a ba tamkar sauran y’ay’anta?” Tsaki Didi tayi ta ce “Yaushe zata karb’eta ai Umaru ya cuceku da ya auro muku jahila, wannan zuwan ma da nayi haka na zo na tarar da ita a galabaice ciwon sanyi ya kwantar da ita, saboda tsabar aikin azaba da take bata. Allah wadaran dai Halin Sakina mai farar fuska bak’ar zuciya.” Shiru Hammad yayi duk da fuskarsa ta nuna zallar b’acin rai bai ce komai ba, ya had’iye abinsa had’e da mik’ewa, ganin Didin na hamma alamar barcin hantsi take buk’ata. Ko da ya koma sashensa, tararwa yayi su Nanna har sun shirya, gidansu zata je kuma ta rok’eshi kwana biyu zata yi da yaran gaba d’aya. Mahaifiyarta Yayar Sadiya ce (Mahmah) uwa d’aya amma uba kowa da nasa. Ita dangin nata mahaifin a gwarzo suke ita kuma na Mahaifiyar Nanna anan Kano suke. __________________________ Yana kwance a parlourn da yake b’angarensa yaji ana buga k’ofar da k’arfi tamkar za’a cireta. Rintse ido yayi sam baya son tashi daga kwanciyar da yake, amma ya lura koma waye a uzurce yake daga yanayin bugun na rashin nutsuwa. “Waye?” Ya fad’a cikin cunkusashshiyar muryarsa daga can b’arin aka ce bud’e ka gani” Ba zai manta muryar ta ba, muryar shaid’aniyar matar nan ce k’awar Sakina wato Kady, ba zai manta wancan lokacin ba, da tare suka aikata abinda har yau yak’i barin zuciyarsa ta huta , bisa son zuciyarsu suka kuma buk’aci tilas ya rufa musu asiri. Fuskarsa ya tamke sosai kafin ya bud’e mata k’ofar, don a shirye yake wannan karan ko da mai suka zo ya shirya karb’arsa. Kallon-kallo suka shiga wurgawa juna bayan ya bud’e k’ofar, Mamaki ne ya kama Kady ganin yarda Hammad d’in ya zama wani ingarman namiji, kamar ba yaronnan da shekarun baya suka..... Tayi saurin katse tunaninta ta hanyar sake kallon fuskarsa, sai taji tana shakkar zancen da tazo masa dashi, da alama bata tsammaci ganin sa haka ba, cikakken namiji da yake tashe da k’arfi da lafiya, daga yanayin fuskarsa ta san wannan karan ba zai d’au rainin hankali ba. Da baya da baya ya juya cikin parlourn, wannan damar suka samu suka rufa masa baya. Tuni har ya zauna kan kujera yana murza goshinsa da d’an yatsa, hakan ce take kasancewa a duk sanda ya kai matuk’a a b’acin rai ko tashin hankali. Tsawon lokaci parlourn ya samu bak’uncin shiru, su sun kasa magana saboda yarda yayi musu kwarjini a parlourn, shi kuma ya runtse idonsa saboda sam baya son yayi ido da ido da su, ji yake tamkar ya shak’esu ya kashe su ya huta. Idanun nasa a runtse ya ce “Me ke tafe da ku? Ko kuma kun zo kuyi abinda kuka saba ne?” Da sauri Ammi tace “Subhanallah, ko d’aya wallahi, wancan karanma kamar yarda na gaya maka wallahi sharrin shaid’an ne. Don Allah ka manta ka d’auka ma kamar ba a yi ba wallahi rud’in zuciya ne da son haihuwar d’a namiji ta kowane hali.” Idanun nasa a runtse yake sakin wani murmushi da kai tsaye zaka kira shi na takaici murya a kaurare ya ce “In manta da abinda ya faru fa kika ce? To idan na manta ita kuma yarinyar a wani mizani kuka ajiyeta? Ya zaku yi ku fahimtar da mutane cewa bata da gadon Abbu, a lokacin da ya rasu? Ko kuwa kuna son nayi shiru Allah ya kamani da laifi? Dole ne ko ba yau ba in sanar da duniya wannan bak’in labarin.” Har zuwa lokacin da ya kai aya, idanunsa still a lumshe suke amon muryarsa ne kawai yake tashi a parlourn cikin isa da ginshira. Ammi ta kalli Kady kafin tayi mata alamun kinga taurin kansa ko? Jin shiru basu ce komai ba, ya bud’e idanunsa ya sauke su akan Ammi. “Yanzu yarinyar nan kina so kai tsaye na b’oye gaskiyar lamari a dinga kiranta y’ar Abbu alhali ni da ke mun san ba haka bane. Wannan karan a shirye nazo zan fallasa sirrinki, in huta da abinda ya tokare min k’irji shekaru da shekaru ko da kuwa Abbu ba zai yafe min ba........ Da sauri Ammi ta katseshi ta hanyar durk’ushewa a gabansa gwiwa bibbiyu “Don Allah kada kayi min haka Hammad, kamar yarda kace yarinyar zaka duba, zaka shafa mata bak’in paint mai wuyar gogewa.” “Kina son kice min kina son yarinyar da tun farkon haihuwarta kika nuna mata tsana muraran, yarinyar da kika so hallakarwa banda da kwananta a gaba, yarinyar da kike gallazawa tamkar ba jininki ba? Yaushe kika fara Sonta? Yaushe kika daina cutar da ita? Yarinyar da tun tana jaririya kika so mutuwarta akan wanzuwarta a duniya, yarinyar da ba kya son farin cikinta, ko ba ke na kama da shinkafar b’era zaki bata a tea ta mutu ki huta ba, saboda nayi shirin fallasa sirrinki kika min asirin da na gwammace nayi rayuwa a birmingham fiye da k’asata Nigeria Am sorry to say wannan karan ba gudu ba ja da baya wajen bankad’uwar sirrinki ko da hakan yana nufin kaf zuri’ar D’an Borno zasu d’ora min laifin akan rashin sanar da su da wuri, na kuma shirya karb’arwa yarinyar nan y’ancinta ta kowane hali.” Ya fad’a yana bud’e idanunsa da suka kad’a suka yi jajir, ya zuba su akan fuskar Sakina da take durk’ushe a gabansa, idanunta ta sauke k’asa ruwan hawaye na ambaliya a saman k’uncinta. Kady ce ta ja wani wawan tsaki ta mik’e had’e da janyeta. “Mik’e yaje ya gayawa duk uban da zai gayawa, sai me? Idan kika tubure ubansa ne yayi cikin akwai yarda za’ayi dake ne? Idan ma ya fad’a dole shima Za’a tuhumeshi....” haka tayi ta masifa kafin su bar parlourn da sauri, kana ganinsu ka san a hassale suke. Allah yaso gidan ba kowa Mahmah tabi su Nanna gidan iyayenta, ita Didi sun tafi asibiti ita da Hamda. Don haka suka samu wannan damar suka shiga wajen nasa. Ya dad’e yana cizar leb’ensa na K’asa kafin ya furzar da wani hucin numfashi ya mik’e. Wanka ya shiga yana fitowa kuma yayi shirin zuwa gaida surikansa, Gidan su Nanna. _______________ Kady a zafafe ta sake duban Sakina kafin ta ce “Wallahi kina so ko ba kya so sai an kawar da wancan banzan a doron k’asa, don na lura da shirin tozartaki yazo, kina ganin yarda yake cika yake batsewa idan ya san wata ai bai san wata ba shashashan banza, ba dai kince yarinyarsa da ita take kama ba?” Sakina ta runtse hannayenta kawai kafin ta ce “Ban so zata kaimu ga jallin kisan kai ba, amma idan haka ne mafita ba yarda zamu yi, sai dai zamu aikata hakan ta hanyar da ba za’a saka mana zargi ba, wacce hanya kike ga zamu bi.” “Kunce burkin motarsa da k’usoshin tayar motar ta hanyar had’a baki da ma’aikatan gidan nan ko mak’udan kud’i sai mu shak’a musu......... [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe. YA ABIN YAKE? 08033748387 Wattpad muna page 13 Follow me on Wattpad @Nazeefah381 ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽 11 ******************************* Idanunta jajir ta sake zubesu a fuskar kady “Wallahi har ga Allah bana son kalmar kisan nan ba yarda zan yi ne tunda ya riga ya kafe ne, tun yana shekarun yarinta dama yaron nan kafiya ce da shi da d’an banzan taurin Kai.” Kady ta ja tsaki kafin itama cikin takaici ta ce “D’an banza kina kallon yarda ya rufe ido yana magana a gadarance alamar ko son magana da mu baya yi, ni fa da zaki bar ni da kaina zan aika da shi lahira amma tunda kina tsoron kisan bari mu bi ta yarda kike so, zan Aiko masa da fataken dare su ja masa kunne na k’arshe idan ya k’i yarda kuwa wallahi zai gane kurensa.” Sakina ta d’an ja fasali kafin ta ce “Shikkenan, Allah yasa mu samu nasarar hakan, matsaloli sun yi min rufdugu a kaina, ga matsalar yarinyar nan da matar can ta saka musu ido akan lallai sai sun fitarda miji, ga matsalar nan da muke ciki. Kady ta dafa kanta murya a raunane cike da tausayinta ta ce "Komai zai daidaita Insha Allah, su yaran ki bar lamarinsu a hannuna zan samo musu mazaje na kece raini, tunda kyawawa ne ba zasu yi wuyar shigaba, nayi mamaki ma da har yau ba wani k'usan Gwamnati da yazo ya kawo musu hari, sai kace wad'anda aka yiwa asirin bak'in jini." Ajiyar zuciya Sakina taja kafin ta ce Allah ya shige mana gaba, zan saka su tura hotunansu sai ki watsasu a status k'ila ta wajenki a dace tunda kina huld'a da manyan k'asar nan, da kuwa ranar nayi rawa da tsalle idan senator ko minister suka taya." Kady murmushi ta saki kafin ta ce "Ai ba abin mamaki bane, kyawun da suke da shi kad'ai ya isa yaja hankalin maza kansu, ki saka dai suje ayi musu makeup na kece raini, sai a kira FARISH yayi musu hoto, don naga ya iya fidda hotuna masu kyau." Ammi cike da murna ta ce "Haka ma za'ayi wallahi kin kawo idea" __________________________________ Daga ita sai Didi a parlourn, Didin tana taje mata dank’ararren gashin kanta da bata son gyarawa sai dai ta wanke, mita take tayi mata “Ke sai kace ba mace ba a haka zaki samu mijin aure, naga ko y’ar powderr nan ta y’an mata ba shafawa kike Ba kullum idanuwa a kod’e kamar nama, ai gwara ki dinga gyara jikinki ko kya samu saurayi kiyi aurenki ki huta da masifar Uwarki. Gobe zan baki kud’i dama ki siyo kayan kwalliya har da gazal da jam baki, don ance ko kana da kyau ka k’ara da wanka, amma lamarin tsoro yake bani ace har yanzu ba wanda yazo yace yana sonki, ko kuma don ana ganin y’an uwanki masu kalar larabawa, kema ai ba mummuna bace kawai da duhun fata ne da ke na kuma tabbata da rashin gyara.” Shiru Hamda tayi mata, zuciyarta ta lula can tunani, sai yanzu da Didin tayi mata maganar sannan ta ankarar da ita, da sam ta manta a irin shekarunta ya kamata ace tana da saurayi ko da kuwa ace na wasa ne, ko me yasa ita bata da saurayin a tsayin rayuwarta ba wanda ya tab’a cewa yana sonta, ba mamaki rashin kwalliyar ne kamar yarda Didi tace idan kuwa hakane ya zama wajibi ta fara kwalliya, don da gaske itama tana son tayi aure ta bar gidannan fatanta da burinta ma bai wuce ta auri d’an wani garin ma, ta yarda zata dad’e bata zo gida ba. Dai-dai lokacin da Didin take kame mata k’ak’k’arfan gashin nata ya turo k’ofa ya shigo, idanunsa a kanta, da tayi saurin sunkuyar da kai. Ya d’an tab’e baki had’e da zama gefen Didin. Ta kuwa washe masa baki ganin ya turo mata leda shak’e da kaya gabanta. Kaya ne fal na ciye-ciye a ciki sai kayan tea da k’unshin ledar gasassun kaji a ciki, ga yoghurt masu sanyi. Fara’ar Didi ta yawaita cewa take “Yanzu na san Hammadu ya dawo k’asar nan, wallahi da a zuciyata har na fara tunanin ko ka zama zumbuli ne kakan marowata, har na fara tsinewa Ingila gaba d’ayanta don na tabbatar su suka koya maka rowa, kai da kake kyauta kamar baka so, Ina matar taka ta dawo kuwa?” Ya d’an girgiza kai yana sakin murmushi ganin yarda take cin naman kamar wacce a shekara sau d’aya take ci. Tsaki taja kafin tace “Zancen banza zancen wofi, to zaman me take a gidan nasu? Ta barka anan wa zai kula da kai, idan kazo nan kaci abinci, cikin dare kuma wa zai gyara maka shimfid’arka, fisabilillahi A’a nifa bana son shegantaka daga kwana biyu shine za’a tafi har hud’u, ina ce tuni aka yi sadakar bakwan uban nata, wanda ya mutu ba ya mutu ba fisabilillahi na meye kuma zata rashe waje ta zauna kai kuma ta barka da rungumar filo cikin dare da mafarkai barkatai” Tsaf ya had’e fuskarsa ganin zata yi masa b’aranb’arama a gaban Hamda, itama Hamdan kunya ce ta d’an kamata don sarai ta san inda zancen Didin ya dosa, ta mik’e ta shige kitchen gwara ta tsiri wanke-wanke akan ta zauna jin hirar Didi marar kan gado. Tana jiyoshi yana yiwa Didin sababi, da sanar da ita shi ya amince matar tasa taje a zafafe yace “Kuma ni nace miki idan bana tare da matata ina rungumar pillow da mafarkai cikin dare?da zaki bani kunya gurin k’aramar yarinya.” Tsaki Didi tayi ta ce “Zancen banza Zancen wofi Hamdan ce yarinya? Allah na tuba itama tun yaushe na gama gane aure take so, ai Ina lura da mafarkan da take yi da matse filo a k’irji, don haka ma zan sanar da ubanku ayi mata aure.” Hamda da take kitchen ji tayi kamar ta nutse cikin k’asa saboda bala’in kunya da gaske yau Didi ta shammace ta ko a ina ta tab’a kamata tana rungumar pillow? ita ina ruwanta ma da wata soyayya, don takaici har wata y’ar k’walla ce ta zubo mata, yanzu wani kallo Didi take so Yaya Hammad yayi mata? Shi kuwa don takaici kasa ce mata komai yayi, a fusace ya mik’e ya fice daga d’akin yana mamakin tsofaffi yarda ba ruwansu suke sakar zantukan da suke so son ransu ba tare da sun tauna abinda zasu fad’a d’in ba. Ya tabbata Hamda tana can tana jin takaicin furucin Didin. Shi kad’ai kuma sai ya saki murmushi ya girgiza kai kawai ya fad’a sashen mahaifiyarsa. _____________________________ Hamda kuwa cikin takaici ta amsa kiran Didin da take ta k’walla mata. Ta fito daga kitchen d’in fuskarta a had’e tana cono baki, ji take kamar ta rufe Didin da duka. Didin data lura da b’acin ran kan fuskarta taje Tsuka ta ce “Kamar kumbo kamar katanta, shima haka ya fita yana muzurai dad’in abin dai a dake ba zan daku ba, a zage ba zan zagu ba sai dai a zageni a zuciya, wannan kuma mutum shi ya jiyo, k’arya aka yi miki ba auren kike so ba ranar fa ina kallonki kina barci kina faman matse k’afa.” Hamda ta d’ago ta watsa mata wani kallon takaici kafin ta ce “Wallahi Didi ba kyau, Allah fa yana kallonki, ki ji tsoron Allah yanzu me kike so Yaya Hammad ya d’aukeni?” Dariya Didin tayi ta ce “D’an nema, yazo da k’warin gwiwarsa da alama yunwa yake ji, anzo cinye min abinci,daga maganar gaskiya kuma ya fice, ba don halinsa ba d’auki abincinsa ki kai masa ko don himulin siyayyar nan da yayi mana.” Hamda ta waro ido kafin ta ce “Ni zan kai masa abincin? Cabd’i ai kam ba dani ba. Da wani idon Zan kalleshi bayan kin gama kwaye min zani a wajensa.” Didi ta zabga mata harara “Ni kike so in tashi in kai masa kenan ko? Da yake ni marainiyar wayonki ce, idan da Uwarki ce ai da ba ki fad’a mata haka ba, sai ni da kika ga na sakar miki ko? To ko ki d’auka ki kai ko nayiwa Gadanga waya yazo shi ya kai masa. Hammadun bai fi min uban kowa ba, duk cikinku wa ke kula da ni yarda shi yake yi, to wallahi ko ubanki sai na kira na saka shi ya kai masa abicin nan, tunda ke ban isa dake ba.” Jin haka da sauri Hamda ta sunkuci tray d’in ranta fal da takaicin Didin. Tana fita kuwa Didin ta saka dariya ta ce “Ja’ira y’ar nema banda nayi mata haka, ba zata je ba.” Dai-dai zata shiga k’ofar sashensa shima ya sawo kai, ya dawo daga b’angaren Mahmah. Da sauri taja gefe kanta a k’asa murya na rawa tace “Didi ce tace a kawo maka abinci.” Banza yayi mata yana bud’e k’ofar. Ganin bai kulata ba ya sanya kanta cikin parlourn, da ba abinda kake ji sai k’arar Ac da sautin karatun alk’ur’ani daga bakin Sudais cikin suratul wak’ia, sai kuma sanyayyen K’amshin turarukan wuta, da suka gauraya da nasa turaren. A dininig ta ajiye, cikin sauri har ta murza handle d’in k’ofar “Hamda” ya kira sunanta cikin ginshira wanda direct zata iya cewa shine karo na farko da taji sunan nata akan harshensa a dai yanzu da ta manyanta. Kamar ba zata jiyo ba sai kuma ta juyo a hankali ta k’arasa inda yake zaune, tsawon seconds yana danna waya bai ce mata komai ba har ta ji ta gaji da tsayuwar sai taji yace “Aure kike so kamar yarda Didi tace?” Da wani irin shock take kallonsa kafin ta russunar da k’wayar idonta, duk da Cewa idanunsa ba akanta yake ba Ta k’asan ido yake kallon duk halin da ta shiga, yana cigaba da danna wayarsa ya ce “Ina jin ki, ke nake saurare, kina da tsayayyen saurayin da ya shirya maganar aure ne?” Wannan karan ba jikinta kad’ai ba har k’afafunta rawa suke mata ta rasa me yasa yake mata kwarjini ta fi jin shakkarsa fiye da Abbu mutumin da ta kwana da sanin cewa shine mahaifinta. “Ba fa na son rashin hankali, na miki magana kin mini banza, nace kina da tsayayyen saurayin da zuciyarki ta amince zaki iya aurensa ko Babu.” Maganar ce ba zata iya ba, ta tabbata idan ta bud’e baki tayi magana muryarta rawa zata yi bai zama lallai ma ya fahimci me ta ce ba. da dai ace zai kalleta ne to da sai ta girgiza masa Kai, amma magana yake yi hankalinsa baya kanta, kamar yarda take hasashe, sab’anin haka tar yake kallonta ta yanayin da bai zama lallai ta fahimci ita yake kallo ba. “Kurma ce ke?” Wannan karon a zafafe yayi maganar da alamun b’acin rai cikin maganar tasa ji yake tamkar ya kai mata mangari. Idanu ya tsatstsareta da su. Hakan yasa ta shiga wasa da yatsun hannunta kafin cikin dakiya ta ce “Bani da saurayi, kuma ma ni ba’a tab’a cewa ana so na ba, sannan ni ba ni na gayawa Didi ina son aure ba.” A rarrabe tayi maganar kamar mai in’ina amma tsaf ya had’e kalaman nata ya fahimcesu don haka ya saki wata ajiyar zuciya kafin ya ce “Auren naki kuma shi zai sama miki kwanciyar hankali ba, ya fitar dake daga k’angin bautar ba gaira ba sabar da kike ciki ba, don haka ki saka a ranki kin kusa aure, na baki sati guda jal ki fidda gwaninki kafin Na bar k’asar nan zan miki aure Na gaji da ganinki a wannan bak’ar rayuwar, da ba abinda zai samar miki y’anci sai aure. Kije kiyi k’ok’arin kawo min miji nan da sati guda, 3 months kawai zan yi a garinnan hakan yana nuni da cewa ana sallah cewa zan tafi, kafin nan insha Allah zan aurar dake.” Wani irin bugun k’irji ne ya Sameta, kafin ta runtse ido cikin wani yanayi da kai tsaye ba zata bashi suna ba, abu d’aya Ta sani kamar yarda ya ce Aure ne mafitar ta, Abin tambayar wa zata kawo nan da sati guda kacal? Ita da ba’a tab’a cewa ana sonta ba. “B’ace min da gani” Taji muryarsa daga sama, hakan yayi saurin dawo da ita cikin hankalinta, duk da ba kallonta yake ba ta tabbata da ita yake, don haka da sauri ta juya har ta na yi kamar zata kifa. _____________________________ Ko da tazo barci, kasa barcin tayi tana kallon Didi da take sallolin Nafilfilunta hakan yasa itama ta mik’e a fili ta furta Barci ba nawa bane gwara na kaiwa Rabbi Kuka ne yayi min maganin damuwata sannan ya kawo min Mijin Aure Kwana kusa. ⭐️Sanye take da Hijabin Islamiyyarsu da yazo mata har k’asa, fuskarta d’auke da nik’af sai dai ta d’age shi sama. Yau kam har da y’ar powderrta da jambakinta light pink ta goga. Dai-dai bakin gate zata shiga taji ance “Y’an mata salamu Alaikum.” Da sauri ta juyo tana amsa sallamar duk da ta d’an firgita a karon farko sai dai bata bayyana hakan ba.Matashin da zai kai shekaru Arba’in ko kusa da haka ya jefeta da wani murmushi da yasa ta saurin d’auke ido daga kansa “Kiyi hak’uri na tsayar dake a hanya, sunana Zunnurain idan ba damuwa numberr wayarki zaki bani, nafi awa biyu anan ina jiranki tunda zaki shiga islamiyyarku Na ganki,kwarjininki ne ya hanani yi miki magana....” Hamda da kyar ta d’ago kanta tana masa kallo na biyu, kafin ta daure ta nuna masa wajen zama da yake gefe kad’an a kuma daidai lokacin Motar Hammad ta danno Kai, har ya yi parking ya fito idanunsa ya na kansu, kana ganinsa kaga matashin Dattijo da ya kusa cika shekaru Arba’in cif, wannan karan sanye yake cikin farar shadda fara tas sai zabga k’yalli take, kansa sanye da zanna bukar da tayi masa kyau sosai cikin takunsa na isa da ginshira ya isa wajen da suke zaune, cikin wata k’aramar bukka. Tunda ya nufosu gaban Hamda ya ke dukan Tara-tara, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana gani ya mik’awa mutumin hannu da a shekaru zasu iya kai d’aya. Suna gama gaisawa ya shige gida sai sannan Hamda ta samu salama ta d’ago idanunta cikin na Usman tana murmushi shima murmushin ya sakar mata, a hankali ya furta “Yayanmu ko?” Ta d’aga kai tana wasa da zoben hannunta. Shikkenan tashi ki shiga gida, sai na dawo insha Allah don naga ba ki sake da ni ba sosai, kuma ma ya kamata na fara neman iso kafin na zo wajenki..." [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Follow me on ArewaBooks https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e Follow me on Wattpad @Nazeefah381 12 ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽 Tunda ya fara maganar tayi k’asa da kanta sai da taji yayi maganar neman iso wajen Iyayenta sannan ta d’ago tana masa wani irin duba A tsorace take kallonsa, kasantuwar ba’a tab’a tareta da magana kwatankwacin wannan ba. Taji zuciyarta na wani irin bugu kamar yarda dai hakan take faruwa ga tarin y’an mata, a karo na farko da saurayi ya taresu da kalmar Na gani Ina so. “Kin amince min?” Ta jiyo maganarsa daga sama tamkar dirar mikiya. Da sauri ta d’aga kai, don bata da zab’in da ya zarta hakan, Wa take da shi bayan shi? Da zata ce bata amince masa ba? Ta tabbata Allah ne ya kawo mata mafita a lokacin da ta kai kukanta garesa cikin sakankancewa da cewa Jallan ya amsa mata. Sai ga shi a cikin lokacin da bai gaza kwana biyu ba kacal Allah ya aiko mata da Zunnurain ya aureta, ashe dai ba zata bawa Yaya Hammad kunya ba, kamar yarda yace ya bata kwana bakwai, zata je masa da labari mai dad’i Samun Miji a gab’ar data dace. “Kisa min digit d’inki” Ta sake jiyo maganarsa wannan karan ma a bazata. Da sauri ta kalli wayar hannunsa tana girgiza kai tare da cewa “Bani da waya.” Ya kuwa dad’e da ido a bud’e bisa ga dukkan alamu tarin mamakinta ne yake nema ya karshi, a zamanin nan da waya ta zama ruwan dare ace zabgegegiyar budurwa kamarta da ta fito daga zabgegen gida bata da waya? Abin a jinjinawa lamarinta ne don kuwa yayi girman da ya kamata ya girgiza zuk’ata. “Wasa kike amma?” Ya sake jefo mata tambayar, ta girgiza kai tana turo baki kafin tace “Da gaske bani da ita, bata yarda za’a yi had’uwar farko na jaka da wasa alhali ba ban san ko kai waye ba.” Ya jinjina kai had’e da sakin murmushi, “Shikkenan, na yarda dama kamila kamarki bai kamata aji zance akasin gaskiya a bakinta ba, zan dawo jibi da misalin takwas na dare, insha Allah zan taho miki da waya.” Tamkar tace masa Ya barshi, sai dai ita kanta tana buk’atar rik’e wayar, kamar yarda taga k’awayenta na rik’ewa, Abbu ya tab’a siyo mata amma Ammi na kyalla ido ta k’wace ta, taji ciwon hakan a ranta, sai dai bata damu sosai ba, saboda ta san hakan ce take faruwa a duk sa’ilin da Ammin taga abu mai mahimmanci da zai sata nishad’i a rayuwa, sai ta san hanyar da tayi ta k’wace. “Ki shiga gida beauty, naga a gajiye kike sai Allah ya dawo dani.” Murmushi ta d’an sakar masa kafin ta tura wangamemen gate d’in gidan nasu, ta d’aga masa hannu kamar yarda shima yayi waving d’inta. Da shigarta Kamla da suke wasa a harabar gidan ta taho ta d’aneta da gudu, haka kawai jininsu yazo d’aya da yarinyar, kai gaba d’aya d’iyoyin Hammad ma suna sonta tamkar yarda take sonsu cikin tata zuciyar. Peck ta bata a kumatu, a kunne kuma ta rad’a mata “My Kamlulu, dirar yaushe? Yaushe kuka dawo daga gidan Granny?” Kamla ta d’an cono baki had’e da cewa “Ni nafi son nan gidan, can ba dad’i shine Mom tace a dawo damu ita sai jibi zata dawo.” Hamda taja hancinta had’e da cewa to Parrot wa ya tambayeki, ina Khairi? Da Abul khair? Tayi mata pointing b’angaren Didi da hannu, “Suna can suna cin wani abu wai zogale, nifa na kasa ci amma Sis Khairi tana taci wai dad’i ita da Dad nifa idan naci am sure I will vomit it.” Ta fad’a tana kakarin amai “Please Anty Hamda will you cook noodles for me?” Hamda ta gyad’a mata kai, dai-dai lokacin da take tura k’ofar parlourn Didi. A baje ta gansu duka akan carpet sun yi Baja-baja da tarkacen b’awon gyad’a ga kwanon da suka ci zogale, shi kuma yana saman three seater yana danna waya. Sallamar da tayi cikin sanyin murya yasa shi d’ago kai, idanunsa akansu ita da Kamla, sai ya sake ganin zahirin kamanninsa ashe da ba abinda ya gani. Bayan ta gaida Didi ta gaisheshi, suma su Khairi suka gaisheta, ta amsa musu cike da kulawa, ta fara harhad’a plates d’in wajen, Khairi ta sa hannu tana tayata. Didi sai mita take “Baiwar Allah daga zuwanki zaki fara gyara waje, ai wallahi wanda ya aureki ya more mace, ba dai tsafta ba abinci kuwa idan aka ci naki kamar kunne zai tsinke, to ba dole na soki a Cikin jikokina ba, mai kula da kai ai Shine abin martabawa, ba wanda ya mayar da kai d’an iska ba, yanzu tunda nayiwa Hammad magana akan matarsa da taje ta rashe gindi ta zauna gidan iyayenta yake zaune nan yake ta cin magani ina ji ma har zagina yayi a zuciyarsa..” Hamda ta ware ido tana kallonta kafin a hankali ta ce “Yaushe kika shiga zuciyar tasa kika gani? Ba fa kyau shaidar zur Didi?” Sarai yaji abinda ta ce kafin Didin cikin kwararato ta fara masifa “Ubanki Damanga shine mak’aryacin, ban ga zuciyar tasa bane zance yace? Haka kawai mace don taga y’ar uwace ita sai ta zauna tayi ta abinda taga dama, ita kuma Sadiya da yake shashashace ko kuma kwad’ayin abin duniya oho mata? Taga uwarta tana auren maikud’i dad’in abin mun san komai ai ba shi ya haifi Nannan ba, nata uban da ya mutu matalauci ne sai bayan mutuwarsa sannan ta auri wannan Alhajin, Allah na tuba mu za’a yiwa k’aryar arziki, kai Sadiya ba dai son abin duniya ba.” Wani kallo Hammad ya wurga mata kafin yayi k’wafa ya mik’e, murya a cunkushe ya ce “Kada ki sake jefa min mahaifiya cikin maganganunki balle ki jingina mata sunan banza.” Salati Didi tasa cikin k’ank’ance ido tace “Kiji min Annamimanci, yaushe na zagi Sadiya, Sadiyar ba don ni ba ai ubanka ba zai zauna da ita ba, balle har a d’au cikinka A haifeka kazo kana min rashin kunya, kaje ka tambayi Sadiyar idan bani na dinga banka mata magungunan mata ba, har ya mak’ale mata ya d’ura mata cikinka, ke bana baki labari ba?” Hamda rintse idonta tayi, da sauri ta shige kitchen a zuciyarta ta ce “Kai lamarin Didi sai a addu’a kuma.” Cikin cunkushewar bak’in ciki Hammad ya zabga tsaki yasa kai zai fice sai ji yayi Didin ta ce “K’aton banza kawai dama kada na sake ganin k’afafunka anan balle kazo ka cinye mana abinci kamar da ubanka aka siya min, dad’in abin wannan karan ba Ummaru bane ya siya min, Ali k’usar yak’i ne ya siya min, balle kayi fankama kace abincin ubanka nake ci.” Shi dai Hammad girgiza kai yayi ya fice a ransa yana cewa zan koya miki hankali wallah, kafin na bar k’asar nan, mata sai zaro zance tamkar ba a gasa miki baki ba. *********************** Sai da ta gama gyaran gidan, sannan tayiwa Kamla da Abul khairi wanka ta dafa musu Noodles, Jallop tayi musu a abincin dare da taji alayyahu da Naman rago da busassan Kifi, sannan ta yiwa Didi kunun zak’in da ta saba sha duk dare. Tsaf ta sake gyara gidan sai fitar da sihirtaccen k’amshi yake. Wannan daren dai Hammad yayiwa Didi yajin cin abinci, duk da Dai ya san duk inda yaje yaci dole sai ya tuna abincin Didi ko yace abincin Hamda. Tun Didi na basarwa har ta fara damuwa da rashin bayyanar jikannata, mafi soyuwa kuma a cikin jikokinta idan ka d’auke Hamda da ta biyo bayansa, bata jin ko y’ay’anta na cikinta tana yi musu soyayyar da takewa su Hammd d’in. Gajiya tayi da jiransa ta sab’i gyalenta tana fad’in da kaina zanje bikonsa yanzu haka yana can Sadiya ta tasa shi a gaba, jarababbiyar yarinya ko kunyar d’an fari bata ji.” (Kuji Didi da K’arfin hali, ita da d’anta.) Har ta isa b’angaren Sadiyar mita take kamar taci babu, hannunta damk’e da Na Khairi take cigaba da fad’ar “Wallahi Idan naje na ganshi wajen Sadiya ko abincin yake ci sai Na kifar, Allah Na tuba Matar da bata iya girki ba ma, ai kudai Ummal Khairi ba kiyi sa’ar Kaka ba, kamar yarda Hamda tayi sa’ata a matsayin kakarta ga shi babu ce kawai idan an bata ba zata girka ba.” Khairi dai murmushi kawai take wani zubin kuma ta tuntsire da dariya. Danna k’ofar kawai tayi ba tare da sallama ba, a fusace ta shige d’akin idanunta cikin na Sadiya da suke zaune gaba d’aya da yaranta hud’u Hamid ne kawai baya nan, Girgiza kawai Didi ta shiga yi ta zauna a kujera tana kad’a k’afa. A tsorace Sadiya ta fara shirin gaisheta, da sauri ta saka hannu alamar dakatarwa, “Yau kam na gane dalilin Sakina na son haihuwar maza ashe wannan take gudu, ke yanzu Sadiya ba kijidon kunya ba, ki tasa yara a gaba kina gayaa musu k’arya da gaskiya wai ke mai y’ay’a, Ashe shi yasa naga Hammadu yau ya taho nan ya tare kin koya musu su raina mutane, Allah na tuba Banda na kasa na tsare ta ina zaki samu cikin Hammd d’in, kin san dai lokacin ko kallon arziki Ummaru ba yi miki yake ba, wato yanzu yara sun girma zaki fara iko da su, to wallahi ahir ki fita ido na akan Hammad sai na ci uban kowa a gidannan, su dama wad’annan ai tuni na sallama miki su, don daga gaisuwa ba abinda yake had’a mu da su, kin riga kin koya musu tsanata. Kai Hammadu tashi mu tafi.” Fuskarsa ya d’aure tamau, alamar ba inda za shi har sai da Sadiyar ta dinga had’a shi da Allah sannan ya mik’e fuskarsa a had’e ya fice. Sai da Mahmah tagais fitarsu sannan ta saki ajiyar zuciya Humaid kuwa sai dariya yake don shi ya mayar da itabin comedian. Mahmah ta kai masa duka da pillow ganin yarda yake kwaikwayar Didin. _____________ K’ememe ya k’i cin abincin har sai da Didin ta bashi hak’uri sannan yaci, don dama duk burga ce shi kansa yana son cin abincin ya kuwa ci da yawa, musamman kunun zak’in da ya dinga shansa kamar ba gobe, ta kowanne fanni zai iya dakar k’irji yace matarsa Nanna tayi hundred percent, inda take da matsala kawai a b’angaren girki ne, sam bata iya girki sosai ba, duk da tana k’ok’ari matuk’a da gaske wajen ganin ta iya d’in. _____________________________ Cikin dare, don zai iya kiran lokacin talatinin dare, idan ya dinga jiyo motsin mutane kasancewar ba barci yake ba, yana ta duba ayyukan companyn su ta internet. Motsin da yaji ya yawaita ne ya saka shi fitowa da d’an hanzari, duk da matarsa batanan shi kad’ai ne a part d’in nasa, yaransa na can Wajen Hamda da Sam suka k’i rabuwa da ita, musamman Kamla. A hankali yake taku kafin ya k’araso parlourn. Gabansa ne ya buga sosai, ganin mutanen zube a parlourn nasa, sanye cikin bak’ak’en kaya, hatta da fuskarsu sun k’unsheta ba zaka tab’a shaidasu ba, idanunsu sanye da Glass. Duk da ya tsorata da ganinsu, Sam jarumtarsa bata bayyana hakan ba, sai ma b’ata fuska da yayi, ya kuma isa wajensu cikin takun sa na gadara. Da ginshira da komai tamkar jinin sarauta ya ce “Lafiya?” Mai suffar samudawan daga cikin su ya mi’ke tsam da niyyar kai masa duka, da sauri d’aya daga cikin su ya tare shi “Kada ka fara ka san ba abinda muka zo yi ba kenan, aiko mu aka yi mu gusar masa da tunaninnasa na shekara da shekaru, ta hanyar wannan maganin da tabbas idan ya sha shi ko kalar uwar da ta haifeshi ba zai sake tunawa ba, balle ubansa sunansa ma sai an masa Tarjama...” yana jin su suka shek’e da dariya had’e da Kai masa shak’a........ [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe YA ABIN YAKE? https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e Follow me on ArewaBooks @nazeefah On Wattpad @Nazeefah381 13 ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽 Kamar an farkar da Abbu cikin daren, akan idonsa Samudawan suka shiga sashen Hammad d’in bayan sun sumar da masu gadi har biyu da suke bakin gate d’in. Hankalinsa a tashe ya kira y’an sanda kafin cikin sand’a ya nufi part d’in su Hammad d’in yana bin bango, akan kuma kunnensa suka yi wannan furucin, da yayi barazanar hargitsa kayan cikinsa. Addu’a ya shiga yi akan Allah ya kawo police d’in da wuri. Cikin hukuncin Ubangiji duk da dukan da suka yiwa Hammad d’in bai yarda ya sha k’wayar da suke tura masa a baki yana furzarwa ba. Ance Sarkin yawa yafi sarkin k’arfi, don haka kafin kace me tuni sun wahalar da shi, duk da ya kafe akan k’in shan maganin. A lokacin ne kuma y’an sandan suka bayyana cike da k’warin gwiwa suka danna kai sashen bisa jagorancin Abbu. K’ok’arin gudun da suke ne yasa police d’in danna musu harbi a k’afafunsu, sun yi nasarar kama mutum biyu, yayinda uku suka tsere. Ba wani b’ata lokaci suka gark’ame su da ankwa, a kuma lokacin ne mutanen gidan k’arar harbin bindiga ya farkar da su, Dama Didi da Hamda ba barci suke ba, a razane suka fito duka d’aukacin jama’ar gidan suka nufi inda suke jiyo harbin. Cikin tashin hankali Didi take kiran sunan Hammad “Ubangiji Allah kasa ba su kashe min jika na ba” Ta fad’a idanunta akan Hammad d’in da yake kwance magashiyyan Abbu yana k’ok’arin d’aukansa don su kaishi asibiti amma ya kasa, ga shi gidan ba maza duk suna gidajensu shi kuma Hamood yana makaranta. Mahmah kuwa kuka kawai take ta kasa katab’us, sai Ammi ce cike da kissa ta kama k’afafun Hammad d’in suka kinkimeshi da Abbu don zuwa asibiti, hankalinta a tashe don bata san mai zai je ya dawo ba idan Hammad d’in ya farfad’o, ba mamaki a take a wajen ya tona mata asiri, da ta sani bata bi gurguwar shawarar kady ba gashi ta kaita ta baro. Dole ta nemi mafita a gaggauce kuwa kafin wankin hula ya kaita dare. Bugun da suka yi masa a baya da gefen muk’amik’insa shine yake masa ciwo sosai sai kuma dukan da suka yi masa a kai da yayi sanadiyyar sumansa. Haka likitan yayi musu bayani kafin suyi masa allurai aka kuma jona masa drip barci mai nauyi ya d’aukeshi. Dole Abbu da Didi ne suka kwana a asibitin don Sadiya bata zo ba bata son surutun Didi, shi yasa tayi zamanta a gida, Ammi ta so zama amma Didi ta ce a sabida me? Don kalan dangi, to ki fita idona wannan ba huruminki bane me kika had’a dashi? Banda auren ubansa da kika yi, maza-maza ki tattara komatsanki kiyi can wajen samudawan y’an matanki da Kika ajiye kina adon d’aki da su.” Ranta a tunzire ta tafi, dama taso zama ne ko ta samu mafita, wannan karan yarda take jin zuciyarta da tsoron tonuwar sirrinta, tana tunanin da kanta ma zata iya kawar da Hammad idan ta samu faraga sai gashi tsohuwa Didi tayi mata kanda garki, ta hanata sakat don haka jikinta a salub’e ta tafi, had’e da aniyar sake wani shirin ko da na zuba masa guba a abinci ne, sai dai tana tsoron a kamata, don haka zuciyarta ta amince da shawara d’aya da zata zartar da ita da zarar ya warke ya koma gida. ____________________________________ Da sassafe Hamda ta gama duk wasu aiyakunta, har peppe soup da sinasir tayiwa su Didi da zummar idan tayiwa yaran wanka su tafi gaba d’aya su duba Babansu. Tana cikin shafawa Kamla mai Mahmah ta aiko idan ta gama shiryasu suje gaba d’aya. Tsaf ta shirya su cikin kayansu na yau da kullum English wears kasancewar har lokacin basu saba da kayan hausawa ba. A zaune suka sameta a parlour da coolers a gabanta, ta zabga uban tagumi so take taje duba yaronta amma tana tsoron tijarar Didi, gashi wad’annan mutane na jiya sun tsaya mata a rai, ya kamata tabbas ta bincika wajen sanin ko su waye, dole akwai wanda ya saka su ba zuwan kai bane. Sallamarsu ce ta sata sauke wani dogon numfashi, idanunta akan Kamla da Hamda, da suka yi tamkar ya da k’anwa. Har k’asa Hamda ta durk’usa ta gaisheta kafin su Kamla suma suyi koyi da ita. Mahmah ta saki murmushi zuciyarta tana jin dad’in yarda Hamdan take kula da y’ay’an d’an uwanta ta ce “Masha Allah, inye yaran Anty Hamda har an shirya, to maza kuzo mu karya sai akaiku asibiti ku gano jikin Babanku ko.” Khairi ta zaro ido “Me ya samu Dad?” Kafin Mahmah ta bada amsa Hamda tayi saurin cewa “Fad’uwa yayi yaji ciwo kad’an, ai tafiya ma za muyi Mahmah saboda mun karya.” Mahmah ta jinjina kai, “Duk dai baki gaji ba, ga d’awainiya da su ga girki to ubangiji yayi miki albarka.” Murmushi ta saki tana amsawa cikin jin dad’i da gaske tana son jin wad’annan addu’ar abinda bata tab’a samu ba daga bakin mahaifiyarta, sai dai Mahmah Abbu da Didi sai kuwa Malaman islamiyyarsu da kullum suke sambad’a mata albarka kwando-kwando. “Ku tashi maza ku shirya kuje, ga driver can ya kaiku ga abinci ku kai musu.” Da sauri Hamda ta ce “Ai nayi musu sinasir, kunun gyad’a da k’osai naga Ya Hammad yana masifar son su.” Mahmah cikin sake Soyuwar yarinyar a ranta ta ce “Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari, ya fahimtar da mahaifiyarki tarin ni’imomin da Allah yayi mata da Ya bata ke a matsayin y’arta, ba’a ja da lamarin ubangiji amma da nace dama nice.” Murmushi Hamda tayi hawayen idanunta na barazanar zubo mata, duk da k’ok’arin togacesu da tayi. Mahmah jikinta yayi sanyi matuk’a tana tsaye har suka shiga mota suka fita daga gidan. Ta ja ajiyar numfashi tana sake jin tausayi da k’aunar Hamda a zuciyarta a zahirance jinta take tamkar jininta. __________________________ Da sauk’i sosai jikinsa, ganinsu yasa Abbu tafiya gida, Didi kuwa ta zubawa Hammad abincin a baki tana bashi kamar k’aramin yaro. Sai da yaci ya k’oshi sannan ta gyara zama tana rik’e hab’a ta ce “Sadiya dai ta tabbata Asararriya, wallahi bana haufi Rashin ilimin nasara ke d’awainiya da Sadiya take yin wani abu tamkar zubin mutanen farko, to ko ni da nake y’ar zamnin da ai ba zank’i zuwa duba Ummaru idan lalura ta sameshi ba, balle har ta kai ga kwanciya asibiti, amma kuji min lusarar mace yarda ta bursune idanunta da toka tak’i zuwa dubata, Yanzu ai ka tabbatar daga ni sai ubanka Ummaru ne muke sonka, Sadiya kuwa da kai da Babu duk d’aya ne a wajenka, shashashar uwa kenan lamba d’aya Sadiya kenan, har yanzu ruwan Gwarzo bai bar jikinta ba, ai zamu koma gidan da ni take zance.” Hammad ya d’an bud’e idonsa kad’an yana harararta k’asa-k’asa, shi surutunta ya fara isarsa, ta daddage sai magana take, ta barshi ma yaji da matsalarsa. Ya Zama dole ya sanar da duniya wacece matar ubansa da ta...... Bugun k’ofa ne yasa Didi shiru, shima kuma tunaninsa ya yanke a wajen, Nanna ce ta shigo da Sauri ba tare da la’akari da Didi da take zaune ba ta rungumeshi a jikinta tana sakin kuka. “Tafiya zamu yi England Dear ba zan yarda su salwantar min da rayuwarka ba, dama ni na tilastaka sai kazo, ban san lamarin k’asar nan ya tab’arb’are haka ba.” Ta fad’a tana shafa gefen fuskarsa da sakar masa peck a kumatu, sai ji tayi Didi ta ce “Auzubillahi, Kice Nanna duk harkar nasara kin d’abeta tsaf a kanki, yanzu baki ji kunya ba da ranar Allah kike dak’umarsa da manna masa sumba a kumatu, sabida ki nuna Mana ke jarababbiyace.” Tsit Nanna tayi tana wasa da zoben hannunta, hankalinta ne a tashe sam bata lura da Didi da take d’akin ba balle su Hamda, duk da ita a wajenta hakan ba wani abu bane, musamman dubi da can yarda suke rayuwa. Nanna tsit tayi tana jin Didin na sababi kamar ta ari baki, kafin ta mik’e tsama tana kallon Hamda Ta ce “Ai sai mu tattara mu tafi tunda jarababbiyar matarsa tazo, kada kuma tayi abinda idanunmu zasu makance, ah to don kinibibi kina son mijin kika tsallake kika tafi kika barshi, kin tafi agolanci gidan uwarki.” Nanna dai ko tanka mata bata yi ba, don da zarar zata tanka mata sai Hammad ya k’ifta mata ido alamar tayi shiru. Tana kallo Didi ta tasa y’ay’anta a gaba tafi da su duk da Abulkhairi yaso zama amma ta ce “Sam, ba zan barka ba, haka kawai suje su bud’e maka ido a banza a wofi, don ina kallon almurin ubanka yarda yake narke idon nan shima jaraba ce take ci sa, sai azo ana abinda ba shikkenan ba, sahunka a likkafa ka wuce mu tafi, har kwad’on zogale zan maka.” Abul Khair tilas ya bita, suna fita Hammad ya saki murmushi kawai yana mamakin yarda tsohuwar bata jin kunyar furta duk abinda yazo bakinta. Ita kuwa Nanna b’ata fuska tayi sosai don abin na Didi ya bata haushi, haka kawai ta hau mata sababi akan abinda ba shikkenan ba har da wani cewa Agolanci taje gidan mijin Uwarta, kullum sai tayi mata wannan gorin. Hammad ya ja hannunta yana murzawa a hankali da sauri ta janye hannunta, “Rufa min asiri, kada tayi mantuwa ta dawo kaga da gaske sai ta sake manna mana sunan Jarababbu. Hancinta ya ja cikin wata irin murya ya ce “Kamar fa Didi ta shiga zuciyata, jarabarce take ci na, kin san ta riga ta gama sanina tun ina yaro.” Ya fad’a yana kashe mata ido da ya sata sakin murmushi tana sunne kai a jikin sa, da gaske ita ma tayi kewarsa. A cikin kunne ya rad’a mata “Close the door.” Sosai jikinta ya amsa yanayin yarda yayi mata magana har bata san sanda ta sake shigewa jikinsa ba. _____________________________ Kwanansa biyu aka sallameshi, ya samu sauk’i sosai duk wasu rauni na jikinsa sun warke illa kafad’unsa da suke d’an masa ciwo kad’an. Sai sannan Mahmah Ta ganshi duk da gorin da Didin tayi mata bai sata taje ba, don ta san da zarar taje d’in itace dai mutum ta farko da zata fara yi mata gori. Ya fara yamad’id’i da ita taje duba d’an fari duk da sunyi mata kara, shi yasa tayi burus da zancen Didin bata je ba. Hamda ce ta gyare musu b’angarensu tas, sai zabga k’amshi yake, sannan su kayi musu sakwara da miyar egusi, aka had’awa Hammad zob’o mai abarba. _____________________________ Da Yamma Ammi ta shiga dubashi, fuskarta d’auke da murmushi, ta sauke idanu a kansa, shi kuwa yana ganinta yayi kicin-kicin da fuska, baya buk’atar ganinta sam. Ta kuwa ci sa’a Nanna ta shige d’aki can ciki ta bar Ammin daga shi sai ita. Cikin wani salon murya ta ce “To ya jikin naka? Dafatan yanzu ka san ba wasa nake ba da nace maka zan iya aikata kisan kai, ko don waccan maganar ta mutu, ina so na sake jaddada maka matuk’ar ka cigaba da k’ok’arin fallasa sirrina tabbas rayuwarku kai da y’ar uwarka ko nace y’ar.........hmmn tana cikin had’ari don wallahi daga kai har ita zan iya b’atar da ku daga Doran k’asa, don haka ina k’ara jan kunnenka be careful.” Ta fad’a tana shafa gefen wuyansa inda raunin yake had’e da sakar masa wani kafirin murmushi ta ce “Mu huta lafiya, Kayi kuma gaggawar had’a ya naka ya naka ka bar k’asar nan shine kwanciyar hankalinka kai da waccan yarinyar.....” ta sa kai ta fice tana sake sakin murmushi, Turus tayi a bakin k’ofa, cikin fad’uwar gaba bayan sun yi ido biyu da.......... [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Al’kalamin Jikar Nashe.. YA ABIN YAKE? Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e 08033748387 On Wattpad @Nazeefah381 14 ____________________________________ ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 Ido biyu suka yi da Mahmah da take shirin shiga duba Hammad d’in, suka shiga kallon-kallo kowa da abinda yake rayawa a ransa, musamman Mahmah da haka kawai gabanta ya yanke ya fad’i. Ammi ta d’an saki yak’en murmushi don bata son Mahmahn ta zargi komai a ranta, duk da hakan ma bata tsira ba, don Sadiya Ta san tabbas ba wani dalili Sakina ba zata sakar mata murmushi ba, yarda ta tsaneta har kowa ya fuskanci hakan. Ga mamakinta sai ji tayi Sakinan ta ce “Ya kuma mai jiki? To Allah ya tsare ya sake kiyaye gaba, ai ma an auna arziki.” Mahmah ta d’an yi murmushi kawai had’e da furta Ameen tana shigewa cikin sashennasa, haka kawai zuciyarta ta k’i yarda da lamarin Sakinan. Tana shigewa Sakina ta saki tsaki murya can k’asa ta ce “Algunguma, da ni kike zancen, shegiya bak’a kawai kin zo kin mamaye gida.” Wayarta da ta shigo ne yasa ta saurin shigewa b’angarenta, ganin Kady ke kiranta. “Sakna mu godewa Allah yara dai sun yi kasuwa, Senator Aruwa na son Najma Shi kuma D’an majalissar birni da kewaye yana son Nasma Wata irin shewa Sakna ta saka, don tsananin farin ciki bata san sanda ta dinga k’wala musu kira ba. Su d’inma a sukwane suka fito samun labarin ya saka su rungumar juna suna shewa da gaske abin ya zo musu tamkar almara a lokacin da suka cire rai. Ammi ta gargad’esu da jan bakinsu su tsuke gudun y’an hana ruwa gudu, ko zancen za suyi, sai dai suje gidan Kady, ta kalli Muneerah kafin ta ce “Saura kuma don ubanki na ji labarin ya fita, yanzu ke kika rage min na samo miki wani gwaskan d’an kasuwan ko b’arawon gwamnati, don ta waccan banzar bana tata kowa ma ya aureta ba matsala ta bace.” Turus y’an uwan suka yi, zuk’atansu cike da tambayoyi game da dalilin da yasa Ammin ta tsani y’ar uwarsu, kullum abin yana damunsu ganin dai Ammin bata son yawan zancen yasa suka tattara suka watsar da lamarin. Wannan karan dai kam sai da Munira tayi k’uru ta ce “Wai Ammi me Hamda tayi miki kika tsaneta har haka? Alhali Ko mu da kike nunawa k’auna ba ma yi miki biyayyar da Hamda take yi miki.” Wani kallo Ammin ta jefeta da shi kafin ta ce “To uwata naji duka tukunna kafin na sanar miki, wallahi duk ranar da kika kuskura kika sake yi min makamanciyar wannan tambayar ranar na lahira ma sai ya fiki jin dad’i kinibabba kawai.” Sunkuyar da kai Kawai Muneerat tayi kafin ta mik’e ta shige bedroom d’insu da sauri. Tayi alk’awarin sai ta binciko dalilin da yasa ake yiwa y’ar uwarta wannan tsana ta ba gaira ba sabar, sam bata yarda da dalilin wai don an haifeta a mace bane, akwai dai wani b’oyayyen lamarin da dole zata bincikoshi. Ammi ta bita da banzan kallo sai taji ma duk farin cikin da take ciki ya b’ace b’at, saboda wannan zancen da Munira ta tsillo mata na waccan bak’ar yarinyar mai kalar mutanen Habasha. Ta ja tsaki kawai had’e da mik’ewa. ____________________________________ Zunnuraini, bayan kwana hud’u da had’uwarsu ya zo, cikin shigarsa ta alfarma sai zabga k’amshin turaren Miyaki yake yana asalin. Suna zaune gaba d’aya a parlourn Didi har da Nanna da Hammad da yaransu sai Hamda da take gefe take tsakurar tuwon kamar bata so, haka kawai yau ta tashi da yanayi na fad’uwar gaba da b’acin rai shi yasa take zaune a gefe, duk da surutun da Kamla take damunta da shi bai sa ta cire damuwar da take ranta ba. Sallamar yaron da yake musu sharar harabar waje ne ya dawo da ita cikin duniyar tunanin da ya zurfafa jin yace “Wai ana sallama da Hamda.” Da sauri ta kai idonta wajen da Hammad yake, sai dai ko alamar yaji zancen bai yi ba, gaba d’aya hankalinsa yana kan Abulkhairi da suke buga TV game, a gark’amemiyar t.v d’in da take parlourn. Didi tsaki ta ja tana zabga mata harara ta ce “Ji min y’ar banza, shin baki ji ana sallama da ke bane?” Jikinta a salub’e ta mik’e ra shige d’aki, Kamla na binta a baya, sai yanzu ta gane dalilin b’acin ranta, da fad’uwar gaba, duk sabida a karo na farko saurayi yazo zance wajenta. Ba abinda ta saka a fuskarta sai ma zumbulelen Hijabin da ta saka da ya kai mata har idon sawu, sannan ta rik’e hannun Kamla suka fice, ta k’asan Ido Hammad yake kallonta, ya saki ajiyar zuciya, a ransa yana mata fatan dacewa da abokin zama Na gari don shine kad’ai abinda Zai saka ta samu peace of mind Ta huta da gallababbiyar Uwarta. A can bakin gate ta tarar da shi saman bonnet d’in motarsa yana danna waya hasken farin wata ya haske kyakkyawar madaidaiciyar fuskarsa, har a zuciyarta take jin Zunnuraini ya kwanta mata kuma zata iya zaman aure da shi. Don ita dai bata hango makusa tattare da zubin halittarsa ba. Cikin nutsuwa take takun, hannunta rik’e dana Kamla har suka isa inda yake. Ya d’ago fuskarsa cikin murmushi yana tsareta da idanunsa gaba d’aya yarinyat ta gama tafiya da imaninsa tun ranar da yayi tozali da ita duk da bai ga zubin halittarta ba ta fuska kam tayi masa hundred percent irin matar da yake so, mai matsakaicin kyau ba mai manyan kyau ba. Tsawon lokaci suka d’auka suna hira kafin ya sake sanar da ita ainahin wanene shi da sunan mahaifinsa da komai, sai dai gabanta ya fad’i jin cewa yana da mata har da yara biyu. Ganin ta firgita ya saki murmushi kafin ya ce “Kada fa ki damu, matata bata da matsala kuma ba gida d’aya zan had’aku ba.” Murmushi ta d’anyi lokaci guda kuma yana sake burgeta ganin ba halinsu d’aya da sauran maza ba masu kushe matansu na gida a yayin da suke neman aure madadin haka ma shi yabon tashi matar yake, nan take zuciyarta ta sake amincewa da shi hundred percent. Da zai tafi ya mik’a mata sabuwar waya dal a hannunta, ganin ta k’i karb’a sai ya mik’awa Kamla had’e da fad’in ya sunan k’anwar tamu don da gani babu tambaya k’anwarmu ce ga kama nan b’aro-b’aro. Hamda murmushi ta saki kafin tace Baka canka daidai ba, Niece d’ina ce ba k’anwa ba.” cikin mamaki ya ce “Ai kuwa wannan ko y’ar waye tabbas mu ya haifawa y’a don kamar babu banbanci. Masha Allah, Idan kin gama shawarar please ki fad’a a gida Zan turo magabatana so samu ne ma ki azimi a gida na, amma na san yayi wuri don haka zan barshi Immediately after Sallah Insha Allah.” Da sauri ta shige Gida cikin matsananciyar kunya. Da murna Didi ta karb’i kwalin wayar tana cewa “Masha Allah, haka muke so kab’akin arziki, kice saurayin naki mai d’an maik’o ne? Har da dalleliyar waya haka, gaya min waye ubansa anan garin? Burina ki auri wanda uwarki zuciyarta zata kusa bugawa ta mutu kowa ma ya huta, Allah yasa dai Ubansa yafi d’angote kud’i.” Wani tsaki Hammad ya ja kafin ya ce “Ai duk halinku d’aya da Ammin shegen son abin duniya, madadin kiyi mata fatan samun mutumin k’warai sai ki wani ce Allah yasa Ubansa yafi d’angote kud’i, mhmn don dai baki san arzikin d’angoten bane, ke kuma shashasha ki tsaya daka tatata kada ki samo mutumin arziki ki tsaya neman mai dukiya Ba mai zuciya ba.” Sak’ek’e Didi tayi tana kallonsa baki a mele kafin tace “Kaji min mutum banda kai d’in wanta ne da sai nace bak’in ciki da hassada kake mata, waye yak’i dad’i a duniya inace ko kai yanzu d’iyar d’angote Ta ce zata aureka murna zaka yi.” Bai bi ta kanta ba ya fice don ma ya cusa mata takaici har da jan hannun Nanna kamar zai mayar da ita ciki, duk da Nannan na turjewa Didi ta ce “Jarababbe, jarabar ta motsa ai ni yanzu lamarinku tsoro yake bani, mata ki bi ki nanik’ewa miji, Allah dai ya kyauta.” Dariya kawai suka fita suna yi. Hamda ma dariyar take kafin ta shige d’aki tana dafe da k’irjinta saboda tsananin bugun da yake mata. __________________________ Ciwon cikin da ya murd’awa Muneerah cikin dare da misalin Sha biyun dare ne ya sata fitowa daga bedroom d’insu don ta samo magani a first aid box da yake d’akin Amminsu. Kasancewar dare ne kafin ta murd’a k’ofar d’akin ta ji sautin muryar Ammin da alama waya take jin tana kiran sunan Hamda yasa ta dakata da bud’e k’ofar ta kara kanta sosai a jikin k’ofar sai taji Ammin ta cigaba da cewa “Kin san sarai ta yarda aka samar da yarinyar nan? Ta yaya kike tunanin hankalina zai kwanta idan ban kawar da ita ba, duk ranar da Umar ya san maganar nan na ha’intarsa da nayi ha’inci mai muni ina tabbatar miki Mami ba zan kwana da igiyar aurensa ba, don Allah Mami ki nemar min mafita wallahi kaina ya k’ulle, na rasa yarda zan yi, don na lura yaron nan bai k’i ya fallasa sirrin nan ba ko da shi zai kwana a ciki, na tabbata akwai abinda Hammad ya taka shirunsa ba yana nufin ya hak’ura bane musamman da na san ya kwana da sanin cewa ni na turo mutanennan suka yi masa duka cikin dare....... Wata irin hajijiyace ta fara d’iban Munirat ji da ganinta duk suka d’auke na wuncin gadi, a take ta kurma wani uban ihu........✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 Jikar Nashe// [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE (Mai tak’ama da ikon Subhana) YA ABIN YAKE? 08033748387 Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e On Wattpad @Nazeefah381 Last free pages. 15 ✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽 __________________________________ Da sauri Sakina ta fito daga bedroom d’inta, hankalinta a tashe dafatan Munira bata ji abinda take cewa mahaifiyarta a waya ba. Turus tayi ganin Muniran a k’asa tana dafe da gwiyoyinta hawaye shab’e-shab’e a fuskarta, alamarta ya nuna kamar fad’uwa tayi. Sakina ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Ke kuma lafiya cikin darennan kike kurma uban ihu?” Munirat ta tattaro duk wata nutsuwa Ta saka a fuskarta, bata son Ammin ta fahimci ta ji zancen da take, ta san idan har ta gane zata iya d’aukan ko wane mataki a kanta, don haka murya na rawa ta ce “Ciki na ke azabar ciwo, kuma na zo amsar magani sai na zame anan.” Ammi ta saka hannu ta mik’ar da ita had’e da fad’in Ayya muje ki sha maganin to, ko dai period pain ne?” Ta girgiza kai jikinta a salub’e, kafin ta bi bayan Ammin zuciyarta na sake mamakin halayyar Ammin. Tana shan maganin tayi saurin ficewa daga d’akin, nutsuwa take buk’ata gami da dogon nazari akan maganar nan da ta jiyo, tabbas biri yayi kama da mutum, amma waye uban Hamdan shine abinda ta kasa ganewa. Ta dad’e tana juyi a saman gadonta dafatan barci ya kwasheta amma ina wannan dare kam tuni suka yi hannun riga da barci, ciwon cikin ma tuni ta neme shi ta rasa, k’wak’walwarta ta tafi dogon nazari, tunaninta ya tsaya cak zuciyarta na wani irin bugu bata son abinda take tunanin ya tabbata, bata fata ko kad’an idan hakan ta kasance ba Ammi kad’ai ba su kansu abin kunya ne a wajensu. HAMMAD zuciyarta take ta bata a matsayin uban da yayi cikin Hamda, idan ba haka ba me zai saka y’arsa tayi kama kwabo da kwabo da Hamda, kamar da kana gani ko ba’a fad’a maka ba zaka san sun had’a jini d’aya. Ta runtse idonta wasu hawaye na zubo mata, ya zama dole ta fallasa sirrin nan, ko Ammi Ta hankalta ta nemi tuba ga Allah, Sannan zuciyarta itama ta huta da dogon tunani, idan ba haka ba kuwa tabbas zuciyatta zata buga. Ranar dai kam akan idonta aka yi kiran Assalatu abinda bata tab’a yi ba kenan a rayuwarta. _________________ Sukuku ta tashi da safen, duk da barcin da yake rinjayar idonta, amma ba zata iya yi ba, Neman wanda zata tunkura da zancen take direct zuciyarta ta amince ta jewa da Anty Lauratu da zancen idan yaso ta gaya mata kada ta sake ta ce ita ta gaya mata. Ko da ta fito parlour suna zaune suna karyawa gudun kada Ammin ta jefa ayar tambaya a kanta yasa ta zauna ta fara tsakurar abincin, tana turawa da kyar kafin ta mik’e tana zarar tissue, Ammi ta kalleta “Ke kuma sai ina ina ce yau baki da Lectures?” Munira tayi saurin girgiza kai tana gyara farin glass d’in da ke idonta ta ce “Ammi ina da group discussion amma ba zan dad’e ba zan dawo.” “Ai shikkenan ki dawo da wuri don mu zamu je gidan Kady yayunki suna da bak’i kuma kin san bana son barin shiyyata ba kowa.” Da sauri ta d’aga kai tana ficewa daga parlourn tana jin Najma na cewa ta tsaya tayi dropping d’inta a motar Ammi amma ta zura da gudu, gwara ta shiga napep ba ta san kowa ya san inda zata, musamman Lauratu da bata shiri da Ammi, shi yasa ma Ammin bata bari suje gidanta. A bakin gate d’in gidan mai a daidaita sahun ya ajiyeta ta zaro d’ari biyar ta bashi kafin Ta saka kai Ta shige had’e da cewa ya bar canjin. Lauratun ce kawai a gidan duk yaran sun tafi makaranta, dama babbar y’arta sa’ar Hamda ce. Cikin mamaki take kallon Muniran ta ce “Ikon Allah yau kece a gidan amma dai Sakina bata san nan kika zo ba? Kuma fa yanzu da kika ganni mayafi nake shirin yafawa yau nace a wajen Didi na zan wuni” Munira murmushin yak’e ta saki kafin ta ce “Ya naji gidan shiru?” Lauratu ta ce “Wa zaki samu duk sun tafi school daga ina haka?” Tana murmushin ta ce “Daga gida mana” Lauratu ta sake gyara zama ta ce “Amma dai ba lafiya ba? Don haka kawai Sakina ba zata bari kizo gidan nan ba, haka kawai ta cusa muku k’iyayyata.” Munira ta ja fasali kafin ta ce “Wallahi, Amma ba k’alau ba wata gagarumar magana ke tafe dani amma ban san ta yarda zaki d’auki abin ba, ko ma ta yaya kika d’aukeshi please kada sunana ya shigo.” Nan ta shiga bata labarin da ya hautsina kayan cikin Lauratu kafin ta gama kuwa gumi ya jik’ata sharkaf duk da sanyin a.cn da yake parlourn, hankali tashe ta mik’e tana struggling a parlourn ta ma rasa abin cewa illa zuciyarta da take wani irin duka, fatanta da burinta a lokacin kada Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya, duk da komai ya nuna kansa k’uruk’uru tun a lokacin da ace sun kasance mutane masu tsinkaye da sun fahimci abinda yake tsakanin Sakina da Hammad, kafin cikin Hamda ya bayyana, me yasa idanunsu suka rufe suka kasa gano dalilin takun sak’ar Sakina da Hammad, lokaci d’aya yaron ya juye ya zama mai bak’ar zuciya, ya kuma tsani had’a inuwa d’aya da Sakina Why? Lauratu ta fad’a da k’arfi had’e da rotsa wani verse da yake gefe a fili ta furta tabbas Sakina ta cucemu idan har hasashen mu ya zama gaskiya, tayi wa zuri’ar d’an Borno mummunan tabon da zai bi mu har kan tattab’a kunnenmu a ina aka tab’a yin haka? Ganin yarda hankalinta ya tashi ne ya kad’a hanjin cikin Munira, sam ta manta zafin ran k’anwar ubansu Lauratu, me ya kaita zuwa ta bayyana mata wannan gungumemen sirrin? Cikin rawar murya ta ce “Please Amma, don’t include my name, don Allah.” Ta fad’a tana durk’ushewa a gabanta hannayenta a had’e alamar rok’o. Fuska ba annuri Lauratu tayi mata wani irin kallo kafin ta mik’e ta zari Car key, da wata iriyar murya ta ce “Ba abinda zai saka ni fad’ar sunanki, amma am sorry to say ba abinda zai hanani tonawa Sakina asiri yau, sai dai idan kafin na k’arasa gidan na mutu.” Gaban Munira ya shiga duka, ganin har Lauratu ta kira Umma Asma’u ta rattaba mata bayani, kasancewar ita a dubai suke zaune da yaranta da mijinta ba damar ta zo ji tayi kawai Umma Asma’un ta saka kuka tana fad’in “What a nonsense Lauratu?” D’if ta kashe wayar ta mayar da kiranta kan Gadanga, kafin ta kira Babansu Hammad ta ce tana da meeting da su a sashen Didi kuma urgent ne, hankali tashe duk suka dinga barin wajen aikinsu, suna tafiya gida. A hanya ta sauke Munirat “Ki wuce School kamar yarda kika sanar mata, ba zan ce ke kika gaya min ba Allah yayi miki albarka.” Munirat jikinta a sanyaye ta fice daga motar, tana fatan Allah yasa ba gagarumar matsala ta janyo a familynsu ba sai yanzu take da na sanin fitar da maganar da Ta sani barinta tayi a ranta ko da zata zama ajalinta. ⭐️ Kamar an jehota haka ta shiga b’angaren mahaifiyarta Didi, tana zaune da casbaha a hannunta tana latsawa, idanunta akan a k’warin talabijin tana kallon tashar Saudi Sunna, kasancewarta masoyiyar madinatul munawwara, girgiza kai kawai take tana sauraran hadisai tamkar tana gane larabcin da suke yi. A fitgice ta d’ago tana zube idanunta a kan Lauratu y’ar autarta, cikin masifa ta ce “Amma Lauratu baki da hali ko kad’an wallahi, fisabilillah banda rana ce b sai nace gamo nayi ba ki shigo min haka bagatatan ba sallama, haba kina girma kina cin kashi, wallahi sai da gabana ya yanke ya ce ras Allah ya raba mu da mugun halinki Lauratu.” Da Didin ta dubi yanayin fuskarta da bata cigaba da kwararato ba, sai da ta dasa aya sannan ta d’ago tana duban idanun Lauratun da suka yi jajir kamar gauta, da sauri ta ce “Hasbunallah, Allah yasa Dai ba mijinki bane ya sako ki.” Lauratu ta ja ajiyar zuciya kafin tace “Gwara min ace sakina yayi wallahi, da wannan gundumemiyar masifar da ta tunkaro mu.” Tuna k’irjin Didi ya shiga luguden daka jin zancen Lauratu wace masifa ce da har ta fi saki? Ta jefawa Lauratun tambaya ba tare da ta shirya ba, Lauratu ta saka gefen mayanfinta ta goge hawayenta, Didi ta ja tsaki shikkenan ta faru ta k’are Wata yayi wa ciki, ya tafka miki tsiyar halin mazan kenan? Ko kuwa Kishiya zai yi miki?” Tsaf Lauratu ta shanye kukanta tana girgiza kai ta ce “Wallahi, duka Didi gwara wannan akan masifar da ta tunkaro zuri’armu ta D’an Borno.” Kafin kace me sai ga Didi ta shige toilet da sauri saboda juyin da cikinta yayi, anya Lauratu tana cikin hankalinta kuwa? Ta dad’e a toilet d’in kafin ta fito tana yarfe gumi ta kalli Lauratu “Kinga Lauratu tun muna shaida juna da ke ki gaya min me ya faru? Kafin ki kaini gadon asibiti.” Lauratu ta shiga dube-dube kafin ta ce “Ina Hamda?” Didi ba baki sai d’akin Hamda data nuna mata, Lauratu ta saka baki ta k’wala mata kira, sai ga Hamda ta fito da sauri, don ta san Amman tasu bata son jira. Ido kawai lauratu ta tsira mata ba tare da amsa gaisuwar da take mata ba, ta ce “Kirawo min d’iyar Hammad, Kamla.” Hamda da sauri ta koma d’aki don can ta baro Kamlan tana game da sabuwar wayar da zunnuraini ya kawo mata. Kamo hannunta kawai tayi suka taho parlourn, Lauratu ta k’ura musu ido tana sake jin fad’uwar gabanta na k’aruwa kafin ta ja fasali ta ce “Didi k’ura musu ido ki gano min ko akwai banbancin da ni na kasa ganowa.” Tsaki Didi ta ja kafin ta ce “Kaji min zancen banza, da wofi to tun yaushe ake fad’ar kamanninsu, wani abu ne don ta yiyo kamannin k’anwar ubanta, bana raba d’aya biyu a can ahalina na farko sai kayi shishshigin d’ebo kamannin wani, wanda ba mamaki tun tale-tale kafin a haifeni ma suka zo duniyar suka yi rayuwarsu suka koma, shine Me don Hamda tana kama da Kamla?” Dai-dai lokacin Abbu da Gadanga suka shigo, ido suka zubawa Lauratu don duk hankalinsu a tashe suka taho, sun zata wani abin ne ya samu Didin, ita d’in ma ido ta kafa musu kafin ta ce “Kuyi hak’uri na tasoku rana tsaka, wani abu ne mai firgitarwa yasa na fito da ku daga office, Yaya ka dubi Hamda da Kamla ka gaya min akwai banbanci a zubin halittarsu.” Ta fad’a tana kallon Gadanga, da yayiwa su Hamda k’uri da ido, sai kuma ya girgiza Kai, “Sam ba wani banbanci sai yau ma na sake tabbatar da zahirin kamanninsu da ake ta fad’a a dangi, wani abu ne ya faru?” Girgiza kai tayi kafin ta ce “Hamda ku shiga ciki.” Suka wuce Kuwa suka shiga duk da Hamda hankalinta ya kasa kwanciya, sai da ta rab’e jikin k’ofa. Lauratu taja ajiyar numfashi kafin ta ce “Abbu Kayi hak’uri da abinda zan fad’i amma Hamda ba y’arka bace, y’ar Hammad ce! Kafin tayi aune suka ga Didi tayi wani irin mik’ewa ta kai mata damk’a cikin matuk’ar tashin hankali, da sauri Gadanga ya rik’ota yana k’ok’arin zaunar da ita ta fisge jikinta “Bar ni Gadanga barni in shak’e yarinyar nan ta mutu na daina jin wannan zantukan banzan, mu zata b’atawa sunan dangi wace irin maganar banza ce wannan?” K’arar da suka ji da fad’uwa a k’asa ne yasa suka bazama ciki. Hamda suka gani kwance a corridor ba alamar numfashi tattare da ita hakan ya tabbatar musu da taji zantukan da suke fad’a. Didi ta saka salati tana b’allawa Lauratu harara “Shikkenan kin yi kisan kai, na tabbata yarinyar nan ta ji wad’annan banzayen zantukan naki to wallahi ba zan rufa miki asiri ba, y’an sanda zan kira yanzu su gark’ameki.” Gadanga dai bai ce komai ba ya d’aga Hamda cak ya shigar da ita cikin bedroom ruwa ya shafa mata kafin ta kawo gauran numfashi. Idanunta a runtse ta damk’i hannun Gadangan fad’i take “Baffa da gaske ne abinda kunnuwa na suka jiyo min? Da gaske ne ni y’ar Yaya Hammad ce ba y’ar Abbu ba?” Gadanga ya share zufar da take karyo masa don shi dai a hasashensa akwai k’amshin gaskiya a zancen Lauratu, baya son ya gasgata ne gudun afkuwar wata matsala. Ya kama hannunta duk da idanunta a runtse suke ya ce “Ba gaskiya bane ki kwantar da hankalinki, ba ta yarda za’a yi labarin nan ya zama gaskiya, kina jina?” Hawayen ta share da kyar ta d’aga Kai, shi kuma ya mik’e ya fita parlourn jikinsa a salub’e, gaba d’aya gwiwoyinsa sun sare da kyar yake jansu kada Allah ya tabbatar da wannan zancen na lauratu a bigiren gaskiya. Zaune ya samesu jigum-jigum banda Didi da take ta yiwa Lauaratu masifa kamar zata cinyeta, ita kuma Lauratun ta kafe akan abinda take fad’e gaskiya ne, Abbu dai yana zaune kansa a k’asa shi kad’ai ya san halin da zuciyarsa take ciki a lokacin bai k’i Allah ya d’auki ransa ba kafin tabbatuwar lamarin a bigiren gaskiya. Idanunsa sun kad’a sun yi jazur, fuskarsa kuwa tamkar bai tab’a dariya ba tunda aka halicceshi, kan nasa a sunkuye ya d’ago yana sauke ganinsa akan Lauratu kafin su ji ya ce “A ina kika ji maganar nan?” Lauratu da ta tsorata da ganin yanayinsa musamman yarda ya tsatstsareta da manyan idanunsa da suka jirkita suka koma mata wani iri murya na rawa ta ce “Wallahi ina zaune a gida Munira ta zo ta same ni da zancen..........” kafin ta gama bada labarin tuni zuciyar Didi ta daina aikinta yarda ya kamata fata take ace mafarki take ba gaskiya kunnuwanta suke jiyo mata ba. Shi kuwa Abbu gaba d’aya yaji ana wata irin hajijiya da shi kafin ya kalli Gadanga ya ce “Ka kira min Sakina da Hammad ka kira kuma Sadiya.” Daga haka ya mayar da kansa jikin kujera ya runtse ido da gaske duk da a zaunen yake jinsa yake kamar zai fad’i wannan wace irin masifa ce tayi musu dirar mikiya a zuri’ar D’AN BORNO? Tambayar da yakewa zuciyarsa kenan da yaji tayi masa nauyi kamar Dutse. Didi kuwa bata uhm bata uhm-uhm sai wani irin kallo take bin lauratu da shi tana tunanin anya kuwa Lauratun jinin ta ce da suka haifa ita da mijinta Usmanu? Ban da a gida ta haifeta tabbas da tace an musanya mata Lauratu, saboda halayenta kaf ya sha banban da na yayunta, duk da bata tantama nata halayen ta d’ebe kaf har ma tana tunanin nan gaba kad’an zata shanyeta. Mahmah ce ta fara zuwa jikinta a sanyaye ta shigo tana mamakin dalilin wannan zaman da rana tsaka gagal haka, bata ce komai ba ta zauna tana amsa gaisuwar Lauratu da ta ganta tamkar a firgice. Ita kuwa Sakina (Ammi) da sak’on ya sameta wata iriyar mummunar fad’uwar gaba ce ta sameta hakan ya tabbatar mata koma kiran menene ba alheri bane. Jiki na rawa ta mik’e tana lalubar mayafi don ta san bata da damar da zata kaucewa kiran Didi. Hammad ya rigata zuwa, shigarta parlourn ta hangoshi zaune kan kujera duk da a yanayi na rud’ani yake ba zaka tab’a gane hakan a tare da shi ba, ya san za’a rina ya kuma san irin wannan ranar ko mu dad’e ko mu jima zata zo, ranar da yake mafarkinta yau ga shi ta zo ko da wani ido Sakina zata dubi mutanennan ta basu labarin abinda ya faru? Ya sauke gwauran numfashi lokacin da yaci karo da fararen k’afafun Sakinan tana shigowa falon, sune dai wad’ancan fararen k’afafun da ba zai tab’a manta a yanayin da ya gansu ba a wancan lokacin, ya runtse ido bayan ya hango shigowarta tana taku tamkar bata son taka k’asa haka halittarta take tun fil’azal Sakina mai yanga ce. Tabbas yau zai fito ya fad’i Gaskiya ko ya huta da bak’in cikin da yake kwasa a zuciyarsa shekara da shekaru. Tun kafin ta k’araso taji kanta ya sara ta tabbatar kuma wannan zaman ba na lafiya ba, Allah dai yasa zaman ba akan wancan b’aragurbin k’wan bane da idan ya fashe warinsa sai ya addabi duk wani ahalin zuri’ar d’an Borno zai kuma girgizasu matuk’a da gaske. A can gefen Abbu ta zauna duk da tun da ta shigo bai d’aga kansa ba. yanzun ma bai d’aga ba ya tabbatar dai itace tun bayan da Ya shak’i k’amshin turarenta. Shirun da yaji gurin yayi ya tabbatar masa da cewa ba za su iya tunkararta da zancen ba, hakan yasa kansa na k’asa cikin wata iriyar murya da sam ba tayi kama da ta Abbun ba saboda kaurinta da bud’ewarta ya ce “Sakna ina so ki fad’a min Hamda y’ar waye?” A firgice ta d’ago ta zubawa Hammad ido tana da tabbacin shi ya gaya musu, maganar ta razanata matuk’a ainun duk da ta san lallai lokacin zai zo ba tayi tsammanin zai zo da sauri haka ba, murya a shak’e tana duban Hammad da wani irin yanayi kallo mai fassara tabbas zaka gane kurenka, tayi k’asa da kanta sai ji suka yi ta fara fad’in “Hammad ka cuceni, na San tabbas wannan ranar zata zo, duk da ba a hayyacinka kake ba, amma komai ya faru ne sanadiyyar kayan maye da ya fara sha a lokacin, ba kowa a gidannan duk kun tafi Gwarzo ranar da Baba mak’oci mahafin Sadiya ya mutu a ranar lamarin ya afku, sam ban san ya fara shaye-shaye ba da ban bud’e masa k’ofa a lokacin da yayi bugun ba tsautsayi ina bud’e masa na ji.... sai ta fashe da kuka “Kuyi hak’uri ba zan iya k’arasawa ba abu d’aya na sani Hamda y’arsa ce ta cikinsa. “Kina da Shaida?” Suka ji Gadanga ya ce cikin b’acin rai har a zuciyarsa bai yarda da zantukan Sakna ba. Da sauri ta d’ago ta watsa masa wani kallo kafin ta ce “Eh ina da shaida, ko wannan dawowar ma sai da ya sake turo min sak’on banza ta waya, akan ko na amince na zo na same shi ko ya fad’awa duniya Hamda ba y’ar Abbunsa bace, har cewa yayi sai yayi min Sharri.” Da sauri suka ga Hammad ya mik’e cikin razani ya kai mata wata damk’a. Abbu ne shima a masife ya mik’e ya kwad’a masa mari, yana k’ok’arin buga shi da bango a zafafe Gadanga ya tareshi yana fad’a “Haba Yaya, Ka bari a bi lamarin nan a hankali, ke Sakina ina message d’in da ya turo miki?” Hannu na rawa ta bud’e message d’in ta mik’awa Gadanga Zufa ce sosai ta dinga zuba a jikin Gadanga don dai tabbas ga numberr Hammad ban b’aro-b’aro bayan yayi dialling a wayarsa ya tabbatar ita ce. Sakina Kallon Hammad kawai ta ke tana sakin murmushi k’asa-k’asa. Gadanga tsit yayi kansa a k’asa da wani idon zai kalli Abbu yace masa Eh da gaske D’anka yana neman matarka Abin fa da kunya kuma yana da girma ainun. Bak’uncin shiru ne ya bak’unci falon kowa ya rasa bakin magana zuciyoyinsu ne kawai suke wani irin bugu na tashin hankali, shi kuwa Abbu tuni ji da ganinsa suka yi d’if, Didi kanta ta zama kamar gunki idanunta ne kawai suke kwararar da hawaye amma ko hannu ta kasa d’agawa. Hammad ransa ne ya dungunzuma ya b’aci yana zaune zufa ce kawai take karyo masa bai yi auneba yaji an rafka masa katako a kansa Abbu ne tsaye a kansa Gadanga yayi saurin rik’eshi “Haba Yaya kada ka yanke hukunci cikin fushi mana ka bari mu tabbatar da gaskiyar abinda ta fad’a, ai shi ba muji ta bakinsa ba.” Kuka Ammi ta saka da k’arfin gaske tana sake cewa Wallahi ba k’arya nake masa ba da gaske nake masa.” Abbu zuciyarsa Ta sake tunzira ya sake yin kan Hammad da duka “Ali ka barni na sumar da yaron nan, zata yi masa k’arya ne? Na tabbata abinda ka gani a waya ba abu ne mai kyau ba shi yasa ka kasa nuna min, wallahi ko ka bari na jibgeshi ko kuma na tsine masa, ya tashi yaja shegiyar y’arsa su fice min daga gida na tsani ganinsa.” Kafin su yi aune suka ga Hammad ya mik’e idanunsa sun kad’a sun yi jazur dai-dai lokacin kuma suka ji ihun Khairi tana fad’in Anty Hamda Anty Hamda, Ali yayi saurin shiga corridor d’in sai dai kafin yaje ya tarar numfashinta ya d’auke ya dawo da sauri yana fad’in “Yaya ka bi abin nan a hankali kada azo ana kisan rai ga yarinyar can ta fad’i.” A zafafe ya ce “Ta mutu mana burina ai mutuwarta idan bai janye ahalinsa sun bar min gidana ba wallahi sai na tsine masa.” Da sauri Ali ya juya gurin Didi don yayi mata magana jin bata saka baki ba, sai dai me?daga Didi har Mahmah kamar basa cikin hankalinsu. Yayi saurin kama Didi yana kiran sunanta amma sai yaga ta fad’o jikinsa bata ko motsi da sauri ya hau jijjiga ta hankali tashe yake kiran “Shikkenan wannan masifa tasa mun rasa Didi, yanzu Lauratu kin kyauta da kika kawo wannan zancen Allah wadaran wanda ya fara tono b’aragurbin k’wannan.” Ammi ta zubawa Lauratu ido tana mamakin yarda Lauratu ta san maganar ita duk a zatonta Hammad ya kawo idan kuwa haka ne bai kamata ta tona wa kanta asiri ba, da sai ta kafe akan ba haka bane, tabbas tayi b’aranb’arama. Ita kuwa Sadiya sai a lokacin ta ja wani doguwar ajiyar zuciya a kuma lokacin ta samu damar kwararar da hawaye, sai dai ko da ta juya babu Hammad ba alamarsa a falon. Hankalinsu su kuma gaba d’aya yayi kan Didi sun kinkimeta don kaita asibiti. Gadanga yana ta fad’in a had’a da Hamda da take yashe amma Abbu yace “Wallahi Gadanga zan raba jiha da kai ka sake shiga hurumin Hammad da iyalinsa da gaske nake na rabu da shi har abada tunda har zai iya shiga gonata.” Ras gaban Mahmah ya buga ta juya da sauri don komawa itama a sama ta ji maganar Abbu “Kema kina shiga huruminsa a bakin igiyar aurenki daga rana mai kama ta yau na zare shi daga sahun yarana.” A karo na farko Mahmah ta jiyo ta watsa masa wani kallo abinda bata tab’a yi ba a rayuwarta sai cewa tayi “Sai me don ka sake ni ba zan fasa shiga hurumin yaro na ba, aurennaka da sam ba adalci a cikinsa, ka sake ni mana Ummaru kawai saboda rashin adalci ba zaka tsaya kaji ta bakinsa sai kawai ka gasgata ta kai tsaye, sabida ita bata laifi.” Da sauri Lauratu ta jata jikinta “Kiyi hak’uri Anty Sadiya, kada kiyi haka bari muje asibitin mu dawo na tabbatar Hammad yaron kirki ne wallahi sharrin hatsabibiyar matar can ne, amma yanzu ya d’au zafi da yawa bai zama lallai ya gane yaren ba, idan muka dawo sai ayi zancen a nutse.” Da kyar ta lallab’ata ta yarda ta bisu. ✍🏽✍🏽 Zuciyarsa a zafafe ya sake komawa Falon Didin har a lokacin tana nan yashe a k’asa babu wanda ya sake bi ta kanta, k’wafa yayi ya shiga toilet ya d’ebo ruwa da sauri yazo ya watsa mata, ta kuwa farka idanunta cikin nasa tana sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya. Kuka take shirin sakar masa ya zabga tsaki had’e da b’ata rai ya ce “Kada ma ki fara ba lokacin kuka bane yanzu, lokacin kuka ya wuce tunda kin riga kin fahimci wacece ke, ki mik’e ki tarkato duk wani shirginki da takardun makarantarki ki fito mu tafi.” Ganin yarda fuskarsa take ta tabbatar ba wasa a lamarinsa ya sata ta mik’e ba shiri don ta lura sarai zai iya kai mata duka idan ta kuskurewa umarninsa. Sai dai ina taku biyu tayi ya jita a kansa ta fad’o tsaki ya saka ya tabbatar da gaske ba zata iya takawaba tsam ya mik’e da ita a jikinsa ya shimfid’eta a kujera da kansa ya fad’a cikin bedroom d’inta shi da Khairi suka had’a mata takardunta da litattafanta ko ta kan kayan sawa bai bi ba ya fito har su Kamlan ya tasa a gaba ita kuma ya mik’ar da ita yana rik’e da ita suka nufi mota. Dole ya kaita asibiti kafin aiwatar da duk wani shirinsa. Da mugun speed yake jan motar bai kaita asibitin da suke zuwa ba wani can daban ya kaita, Khairi ya bari a wajenta bayan likitan ya sake tabbatar masa tana buk’atar nutsuwa sosai don jininta yayi mugun hawa. Ya kalleta a zafafe ya ce “Wallahi idan baki daina kuka da sakawa kanki damuwa ba, tsaf zan tattara in tafi in barki idan yaso ko kasheki ne su yi ni ba ruwana, an gaya miki suna da asara ne idan zuciyarki ta buga kika mutu, kina kallo dai suka yi watsi da lamarinki ta tsohuwar uwarsu kawai suke, dama idan na dawo kina kukan nan sai na murje bakinki, ga waya nan Khairi ki kira ni idan tayi kuka, haba fin mutane idon kukan kika yi?” K’asa kawai tayi da idanunta bayan ta d’auke sautin kukan tsaf. Ta bi bayansa da kallo bayan ya tasa Kamla da Abulkhairi a gaba yana fad’in “Muje na kaiku gurin uwarku.” To fa! Mai karatu duka-duka anan na kawo k’arshen free pages amma ina tabbatar muku yanzu labarin ya fara wannan duk shimfid’a ce dad’in yana nan gaba. Kai dai kawai ka biya naka kada ayi babu kai. Ga duk wanda ya siya riba biyu zai had’a don akwai free littafina na zumuncin zamani da zan dinga yi muku posting d’insa a cikin group d’in. Sai na jiku. Normal group 300 Vip 500 Special people wanda za’a dinga turawa privately 1000 kacal Zaka biya ta wannan account d’in 2118666253 UBA sai ka tura shaidar biya ta wannan layin 08033748387. Ku biyo ni don jin yarda ABIN YAKE Jikar Nashe taku ce! [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Ya abin yake? Nazeefah Nashe 08033748387 BONUS PAGE... 16.. (Saboda wasu da suka buk’aci a D’an k’ara musu free pages shi yasa zan d’an k’ara ko 3 pages ne. Zuwa lokacin ku yi ta payment. 3 to 5 pages kawai zan k’ara. Nagode) ____________________________________ Tunda ya isa k’ofar gidan surikansa ya yi parking kansa kawai ya d’ora akan sitiyarin mota yana jin yarda zuciyarsa ke bugawa da tsananin b’acin rai gami da tururin bak’in ciki. Me yasa Abbu zai yanke hukunci cikin fushi ba tare da shi ya ji ta bakinsa ba, ko a kotu ake kafin zartar da hukunci dole sai an ji ta bakin mutane guda biyu. Amma zai bawa Sakina mamaki zai nuna mata shi ma ya iya rashin mutunci kamar ko wane d’an zamani. Ya runtse idonsa gami da cije leb’ensa da k’arfin gaske tamkar zai huda shi, sai kuma ya saki yana furzar da tururin b’acin rai, da gaske sai ya rama yayi alk’awarin yin ramuwar gayya a lokacin da bata yi tsammani ba, sai ya tozartata gaban kowa sai ya kuma fito da ainahin b’oyayyiyan halinta kowa ya gani an kuma yi Allah wadarai da ita. Duka wad’annan zai yi su ne a lokacin da Ta sakankance ta manta da batun Shi kuma zai bayyanar mata a matsayin ramuwar gayya. Wayar hannunsa ya shiga dialing Bayan da yaji Abulkhairi na kiran Dad Dad mun zo ba. Cike da takaici ya d’an shafa kansa. Nanna da take zaune kusa da Mamanta ta d’aga wayar “Ki fito ina waje.” Shine kawai abinda ya ce ya katse wayar, Nanna ta tab’e baki don tuni ta saba da halinsa in dai wannan ne. Mayafinta ta yafa ta fice da sauri don ta ji dalilinsa na zuwa shi da ya ce sai dare zai zo d’aukar ta. Turus ta yi ganin yarda fuskarsa take a matuk’ar d’aure zata iya cewa tun bayan aurensu bata tab’a ganin fuskarsa a wannan yanayin ba. Ko lokacin da yake shiga wancan yanayin idan an b’ata masa rai bata tab’a ganin fuskar sa ta koma haka ba. Ba tare da ya yi magana ba ya bud’ewa yaran k’ofa yana dubanta cikin yanayi na bada umarni ya ce “Ban amince ko da wasa ki je Gidan mu ba, kuma ku shirya nan da 1 week za mu koma inda muka fito.” Idanunsa cikin nata tana k’ok’arin samo kalmar da zata furta masa, tambayarsa take son yi amma kafin furucin ya fito ya ja motar da mugun speed. Nanna ta saki ajiyar zuciya had’e da furta Allah ya kyauta ya kuma saukeke lafiya. Amma wannan jaraba har ina ayi mutum sai kace mai shafar Aljanni. Jikinta a sanyaye ta shiga gidan nasu, Ummanta na ganinta ta ce “Lafiya? Ko k’in zama suka yi ya rakito su nan?” Nanna ta girgiza kai “Ko d’aya, kawo su ma ya yi ya kuma ce ko da wasa kada na sake na koma gidansu, ban san dalili ba.” Umman ta girgiza kai had’e da Lalubo wayarta ta shiga kiran Yayarta. Sai da tayi ringing sosai kafin Sadiya ta d’aga zuciyarta na harbawa dafatan Allah yasa ba wannan labarin mara dad’in ji bane ya je kunnen K’anwarta da wani ido zata kalli y’an uwanta ta ce “Eeh, hakane Hammad ya yiwa matar ubansa fyad’e har ta haifa masa y’a da kunya ai, duk da tana tantama idan har hakan ya faru da gaske. Jin k’anwarta ta Dida na ta fad’in hello Yaya ba kya ji nane? Na ce me ke faruwa a can gidan ne Hammad ya kawo yara har kuma yana gargad’in Nanna da kada ta sake ta sake zuwa ko k’ofar nan gidan.” Sadiya ta saki ajiyar zuciya, murya a dashe ta ce “Wallahi d’an sab’ani aka samu Dida, ta bi umarninsa kada ta zo d’in har muga abinda hali yayi, yanzu haka muna asibiti da Didi bata uhm ba ta uhm-uhm har yanzu kuma likitocin ba su ce da mu komai ba.” Dida ta saki salati kafin ta ce “To Allah ya kyauta, ya yi mana maganin koma menene, ita kuma Didin wani asibiti ta ke sai mu zo ai yanzu.” Kamar ba zata gaya mata sunan asibitin ba sai kuma ta daure murya a cunkushe ta sanar mata, had’e da kashe wayar, tana sake lalaubar numberr Hammad amma still bai kunna wayar ba. Gabanta ne yake fad’uwa bata son Hammad d’in ya je ya aiwatar da wani abu cikin fushi, sai dai ta san bata da halin tafiya ta bar Didi da iyalinta a cikin wannan yanayin. ******** Babu b’ata lokaci Drivern Hajiya Dida ya sauke su a asibiti ita da Nanna da su Kamla da tun bayan faruwar lamarin jikinta ya saki duk da bata da wayon gane komai amma ta tabbatar abin da ya Farun ba mai kyau bane, musamman ganin yarda aka doki Daddynta, bata san me yayi ba abu d’aya ta rik’e da ta ji ana cewa Hamda y’ar Daddy ce. Sun duba Didin zuwa lokacin an kai ta d’akin hutu tun bayan da aka samu nasarar numfashinta ya daidaita, sai dai ba su samu fuskar da za su tambayi kowa komai ba, ganin yarda fuskokin nasu suka bayyana matuk’ar tashin hankali. Sai da Sadiya ta rakosu sannan Nanna ba tayi k’auran baki ba ta ce “Mahmah ina Khairi ne, na ga kowa anan d’in ban ganta ba ko tana gida gurin Hamda” “Bata gida tana asibiti gurin Anty Hamda Dad ne ya kaimu aka yiwa Anty Hamdan allura.” Abulkhair ya fad’a. Nanna bata kawo komai a ranta ba ta ce “Allah sarki me ya sami Antyn ta ku?” “Fad’uwa tayi da ta ji Amma ta ce Daddy ne Babanta, wai Daddy ne ya haifeta...” Wannan karan Kamala ce ta fad’a itama idanunta na zubar da hawaye ta cigaba da cewa “Shine Granny ya Zane Daddy ya doke shi...” Tsoro da firgici ne ya bayyana a fuskokinsu gaba d’aya. Sadiya ba bakin magana sai sunkuyar da kai da ta yi kawai idanunta na zubar da wasu hawaye masu zafi, duk da bata so fitar maganar ba Ta san dole wata rana zata fita, tunda ance zancen duniya ba ya b’uya. Sam basu lura Da Nanna ba sai da suka ga ta yi zaman y’an bori tana shirin rusa ihu Dida Ta zabga mata tsawa “Ki ka fara ihun nan sai ranki yayi masifar b’aci, asiri kike so ki tona mana, Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, Yaya Sadiya abin da nake ji a bakunan yaran nan gaskiya ne?” Sadiya da kanta ke k’asa ta d’aga kai murya a dashe ta ce “Duk da ban ji ta bakinsa ba amma alamu da dama sun nuna haka d’in ne. Wallahi saboda tsananin b’acin rai ji nake dama na mutu na huta.” Dida ta jingina da motar ta bayan ta nad’e hannayenta a k’irji, ta rasa ma me zata ce sai can ta busar da iskar bakinta ta ce “Yaya ya kamata mu ga Hammad ta kowane hali ko da Kuwa a gidana ne.” “A ina zan gan shi, kiran duniya na yiwa wayarsa ta k’i shiga, shi kuma ubansa ya kore shi daga gidan gaba d’aya ba tare da ya tsaya ya ji ta bakinsa ba.” Nanna ce ta mik’e fuskarta a had’e ta ce “Ni na yarda, na yarda jininsa ce sabida a kamanninta da Kamla ya isa ya tabbatar da hakan.” Ta fad’a wasu hawaye na gangaro mata. Sannan ta juya ta kalli Kamla ta ce “Ke ya sunan asibitin da kuka kai waccan shegiyar Antyn ta ku?” Kamla da ta diririce ganin yanayin Mommyn nata da sauri ta ce Standard” Mota kawai suka ga ta fad’a da sauri. Dida cikin masifa ta ce “Ke Nanna bana son hauka bud’e motar nan kafin ranki ya b’aci, hauka ki ke?” Ta san sarai mahaifiyarta kaifi d’aya ce kuma bata da wasa hakan yasa jikinta a sanyaye ta bud’e motar. Ta koma baya had’e da bawa driver da yake can gefe key d’in suka shiga motar gaba d’aya har Sadiya. Nanna sai sake b’ata rai take, tana sake danna kiransa amma bata shiga. Har Driver ya ja motar don isa asibitin Standard d’in. ____________ Daidai lokacin Hammad ya fito daga hotel d’in da ya kama d’aki, zuwa lokacin da zai bar garin, don baya son zuwa gidan ko wane aboki balle aji dad’in tambayarsa dalilin barinsa gida. Sanye ya ke tsaf cikin shigar k’ananan kaya fuskarsa ta yi wasai ya samu nutsuwa sosai, tun bayan da zuciyarsa ta aminta da shawara d’aya da ya yanke. Sai baza k’amshin turarensa ya ke Hugo Boss, duk inda ya bi kuma idanun mutane a kansa saboda yarda yake taku, duk da da alamun b’acin rai a fuskarsa hakan bai b’oye Sirrintaccen kyan da yake da shi ba. Ya bud’e motarsa k’irar Mercedes Benz bak’a wuluk ya shiga. Sai da ya tsaya a eatery d’in hotel d’in ya karb’a musu abinci mara nauyi da drinks sannan ya finciki motar da mugun speed, haka nan yake tuk’insa ko don ya saba da driving d’in Birmingham ne yana mantawa a Nigeria yake musamman Kano garin taron cunkoso. ________ Ko da ya shiga d’akin Khairi kawai ya tarar a zaune da wayar Hamdan a hannunta tana dannawa. Ita kuwa Hamda tana kwance a saman bed d’in idanunta a lumshe, daga yanayin yarda yaga hawaye na zuba a idonsa ya tabbatarwa kansa ba barci take ba. Khairi ta masa sannu da zuwa kafin ta amshi ledar hannunsa don dama yunwa take ji. A bakin Gadon ya tsaya yana k’are mata kallo kamar ranar ya fara ganinta, gaba d’aya ta sake zubewa ta rame lokaci guda. Ya saki siririn tsaki a fili kafin ya bubbuga gefen katifar gadon murya a tsaurare ya ce “Ta shi malama na san kina ji na.” Idanunta da suka jirkita launi daga farare tas zuwa jajaye ta bud’e da kyar ta saukesu a kansa, gabanta na fad’uwa da ta tuna shine wai a matsayin mahaifinta. Tana k’ok’arin bud’e baki tayi magana ya dakatar da ita don ya san ba abu mai dad’i zata furta ba. “Ki rik’e duk wasu tambayoyinki bana son jin su, don ba zaki samu amsa ko d’aya ba.” Ta had’iye wani abu a mak’ogoronta mai d’akin gaske tana mamakin halayyarsa tamkar mai gani har hanji. Ya sake kakkafe ta da ido “Ki mik’e ki ci abinci Malama, zan kai ki wajen passport suna jira na.” Babu alamun wasa a tattare da shi, ta tabbatar a yanayin da take bata isa ta ce masa ta k’oshi ba, don haka ta ja kwanon take away d’in ta d’au cokali kenan aka danno k’ofar aka shigo. Gaba d’aya suka d’aga kai don ganin su waye, Nanna ce a gaba sai Dida da Mahmah da suka shigo sun bar su Kamla a motar. Wannan karan Nanna da gaske take don sam fuskarta ba annurin rahma ta saukesu akan Khairi, had’e da nuna mata k’ofa “Fita Malama, ban ga dalilin da zaki zauna jinyar shegiya ba..” Da sauri mahaifiyarta ta mata wani kallo ganin Hammad ya d’ago a fusace yana wurga mata wani irin kallo mai cike da gargad’i Dida ta ce “Ke Nanna saurara mana, bana son hauka uban wa ya ce miki shegiya ce?” “Idan ba shegiya ba me kike so a kirata Dida? Ni na tabbatar ko Hammad ne yayi cikin ta to uwarta ce ta ribaceshi, bisa son zuciyarta na son haihuwar d’a namiji, don haka Hammad a matsayina na uwarka ya zama dole ka sanar da ni yarda abin yake, kafin ka saka zuciyata ta buga ka yiwa sauran y’an uwanka a sara, don na lura kai baka d’aukeni da muhimmanci ban da haka ai da tun lokacin ka sanar da ni gaskiyar abinda yake k’udundune, yanzu ga shi ita ta wanke kanta kai ta saka ka a bala’i. Gaba d’aya Hamda ji tayi kamar duka sassan jikinta ya daina aiki, kanta kuwa jinsa take kamar ya tsage biyu saboda masifar da take ciki, ina ma rabbi ya agajeta ya d’auke ranta ta huta. A zafafe Nanna ta ce “Kin ga yayi shiru ba zai fad’a bane, sannan Kuma yazo ya tare a gaban shegiyar y’arsa ya nunawa duniya da gaske shi yayi cikinta, to wallahi muddin yace zai dinga shiga huruminta sai dai ya sawwak’a min.” “Saki nawa ki ke so?” Suka ji ya fad’a muryarsa a kaurare ba tare kuma da ya kalli kowa ba, kamar yarda suka tarar da shi idanunsa akan waya har a lokacin hakan yake. Tsoro da razani suka shigesu gaba d’aya, ba su sake firgita ba sai da suka ji ya ce “Ina sauraranki, saboda ina tabbatar muku mahaifiyata ce kawai ba zan iya rabuwa da ita akan wannan yarinyar ba, don haka ba shiga huruminta kad’ai ba daga nan har Birmingham zan tafi da ita zata rayu da nine a k’ark’ashin inuwa d’aya har sai aurenta ya tashi, saboda duk duniya a yanzu ni ne gatanta don haka Idan kin ga ba zaki iya zama da ita ba you are free to go, kada azo ana nayi ba daidai ba..” Tsawon lokaci d’akin ya d’auki bak’uncin shiru baka Jin komai sai saukar numfashinsu da sautin kukan Nanna da furucin Hammad yazo mata a bazata ta kuma rasa a ma’aunin da zata ajiyeshi tabbas idan ya kafe sai ya tafi da yarinyar nan Birmingham ya taro k’wallan masifa.... Jikar Nashe ce... [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE? BONUS PAGE 17 08033748387 ✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 Ajiyar zuciya kawai Hamda take saki, jin zantukan Nanna da suka zo mata a bazata, sam bata tsammaci haka daga bakinta ba, Lura da cewa ta nuna wa yaranta k’auna, amma a yau ta wanke idonta tana furta muggan kalamai a kanta tamkar ma bata tab’a saninta ba, kawai don k’addara ta hau mata. Me yasa ba za su yi mata uzuriba? Dubi da cewa itama ba laifinta bane da bisa son ranta ne da bata amince ta zo duniya ta wannan k’azantacciyar hanyar ba. Ta sake rintse idonta gam jin cece kuce yana sake yawaita tsakanin Nanna da mai gidanta. “Wallahi Mahmah ki yi masa magana muddin ya ce sai ya tafi da ita to tabbas sai dai ya san yarda zai yi da ita ba zata zauna min a gida ba.” Fuskarsa a tamke ya dubeta had’e da furucin “San da na siyi gidan ko aurenki ban yi ba, balle ki ce da kud’inki na siya, idan kin san tashin hankali za ki koma min da shi you better stay at your father’s house.” Zata sake magana cike da zafin rai Dida ta daka mata tsawa “Nanna bana son rashin hankali ki bari a yi komai a nutse. Duk wannan maganar ba ta da amfani.” Kuka ta sake fashewa da shi “To ku gaya masa kada ya tafi da yarinyar nan, wallahi zan iya aikata komai idan na ce komai ina nufin komai.” Cikin b’acin rai ya mik’e zai fice har ya kai k’ofa ya ji Mahmah ta daka masa tsawa. Tsak ya tsaya had’e da juyowa yana facing d’inta. “Me kake nufi da tafiya da ita? Ko kana nufin da gaske ka karb’eta a matsayin y’ar cikin ka, Hammad kada kace min da gaske yarinyar nan jininka ce?” Ya d’ago kai yana kallonta cikin tafasar zuciya sai dai lab’bansa sun gaza furta furucin komai illa idanunsa da suka jirkita launi zuwa ja. Ya sunkuyar da kansa kawai. Har zuwa san da Dida ya fuskanci tabbas ba zaida ce komai d’in ba, ta dafa kafad’ar Sadiya cikin taushin murya ta ce “Yaya mu bi komai a hankali, insha Allah komai zai bayyana kansa, a yanzu na fuskanci halin da Hammad yake ciki sam ba zai iya furta komai ba.” Sadiya ta bud’e baki zata yi magana Dida ta yi saurin girgiza mata kai, don ta lura idan har aka cigaba da kucincina maganar tsaf Hammad zai iya datse igiyar auren y’arta, ko ba haka ba ita Hamdan ce ma ta bata tausayi, ta lura ba a k’aramin rud’ani da firgici take ciki ba, kada a je ta rasa hankalinta ko zuciyarta ta buga haka kawai an saka ta a halin ban ji ba ban gani ba. Idan har Hammad ya matsa sai ya tafi da ita, ita zata rik’e ta madadin a had’a ta da Nanna a zo a haifi d’an da ba shi da ido. Don haka ta girgizawa Sadiya kai alamar kada ta ce komai, ta kuma k’arasa gaban gadon murya a tausashe ta dafa kan Hamda da ya d’au zafi rad’au ta ce “Ki yi hak’uri kin ji, komai zai daidaita ubangiji Allah ya ba ki dangana, duk abinda kika ga ya faru ga bawa muk’addari ne daga Allah kuma bawa ba zai iya goge k’addararsa da Ubangiji yada rubuta masa ba, ki yi ta addu’a a zuciyarki ubangiji Allah ya baki ikon amsa jarabawarki Allahumma la sahla illa ma ja’altuhu sahlan wa anta taj’alal Hazna iza shi’ita sahlan. Tana yaye duk wata damuwa da nauyi zuk’ata.” Daga haka ta yi mata sallama suka fice. Hamda ta bi bayanta da kallo, tana jinjina kyakykyawan hali irin nawannan mahaifiyar Nanna, tunda abin ya faru ita kad’ai ce ta fad’a mata abinda ya kwantar mata da hankali kad’an, ita ce matar da ta lallasheta da furuci mai warware fushin zuk’ata, wani abu kad’an daga cikin abinda yaaka tokare k’irjinta ya sauka, a hankali wasu siraran hawaye suka fara biyo k’uncinta. Ta shiga nanata waccan addu’ar da Dida ta gaya mata. Sai ga shi a hankali barci duk da ba za’a kira shi mai dad’i ba yazo ya d’auketa. Tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Hammad da yake zaune ya zuba mata ido, wani abu mai kama da tausayi yana tsirga masa cikin zuciyarsa, da gaske yana jin tausayinta, idan kuma ya tuna ta hanyar da aka sameta sai ya ji zai iya sadaukar da Duk wani farin cikinsa matuk’ar ita za ta yi farin ciki. Kusan awoyi biyu yana zaune kamar maigadinta yana kallon yarda take sauke ajiyar zuciya cikin barci. Ba ya son ya tasheta duk da kuwa za suje wajen passport, ya fi so ta tashi da kanta. Sai da ta k’ara mintuna talatin akan awa biyun sannan ta farka. Idanunta cikin nasa da ya kafeta da su, da sauri ta d’auke na ta idanun tana tattare gashin kanta da ya kwanto a Saman fuskarta. Da kyar ta mik’e zaune tana dafe pillow, tana mamakin yarda ta yi barci sosai haka. Fuskarsa a d’an d’aure ya mik’e yana gyara wristwatch da yake hannunsa “10 minutes na ba ki, ki yi alwala ki yi sallah za mu je wajen passport kuma kada ki yi taking time sauri nake.” Bai saurari amsarta ba ya fice da sauri. Sai da ta fi minti d’aya a zaune kafin ta mik’e cike da kasala ta shige toilet d’in d’akin. Ita dai da zai bi ta tata da ya kyaleta ta shiga duniya tunda zamanta tare da su a gareta ba shi da wani amfani, musamman da matarsa ta nuna mata k’iri-k’iri bata son zamanta tare da su. Sam ba taga laifinta ba, dama y’ay’a irinsu haka mutane ke gudunsu ba sa son sam su rab’e su, duk da kasancewar ba laifinsu ba ne. Mintuna biyar ta k’ara akan lokacin da ya bata, tuni ya je wajen Doctor ya amshi sallama, bayan Doctorn ya tabbatar masa damuwa ce silar ciwon nata, da zarar an kwantar mata da hankali everything will be alright Insha Allah. A rab’e ya ganta jikin bango, tana hangoshi ta fara wasa da bakin hijabin da yake jikinta. Sai da ya isa gabanta sannan ya duba agogo hannunsa ya sauke kallonsa a kanta. Yana d’an girgiza kai, ba kuma tare da yace komai ba ya juya ya cigaba da tafiya. Ita kuma jin bai ceyi tazo ba kawai sai ta ja ta tsaya. Har sai da ya yi taku goma sai yaga tamkar bata bin sa. Hakan yasa ya jiyo tsaki yaja kafin ya ce “Jira ki ke na zo na d’auke ki ne?” Ya yi furucin ba tare da ya juyo ya kalleta ba. Sai sannan ta bi shi tana mamakin yarda yake mata abubuwa tamkar ana tilasta shi, ya k’yaleta mana ya k’yaleta ta kama gabanta idan yana ganin kamar ta zame masa wani kaya ne. Bai san haushi yake bata ba, idan ta tuna yarda suka bi son zuciyarsu suka samar da ita tada gurb’atacciyar hanya ya zama dole ta samawa kanta mafita ba wani Birmingham da zata bi shi. Ya aura mata Zunnuraini kawai.... Da sauri zuciyarta ta buga ta tabbata da kyar idan zata auru idan har mutum ya san wacece ita? Dai-dai lakacin da ta ci karo da motar ba tare da ta sani ba, shi kuwa yana kallonta ya k’i mata magana yana son ya ga yarda zurfin tunanin nata yaje. Tsaki ya ja, a zafafe ya ce “Ki je ki bugar da zuciyarki a banza garin banzan tunaninki.” Da kyar ta d’ago jajayen idonta tana so tayi masa tsiwa amma kwarjininsa yana hana ta. Musamman idan ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifin gaske.” Sai kawai ta runtse idonta, hawaye na kwaranyo mata ta fad’a motar. Yana kallon yanayinta ta cikin motar har da murgud’a bakin da ta yi, murmushi kawai ya saki ya tabbatar da abinda take k’unsawa a zuciyarta. Yana fara driving taji ya ce “Idan kin gama tsara yarda za ki gudu ki sanar min na baki kud’in mota.” Da wata irin razana ta d’ago tana dubansa ya aka yi ya San Sirrin zuciyarta? ya aka yi ya san abinda take shiryawa, kamar ta tambayeshi sai kuma ta yi shiru tana cigaba da wasa da hannunta Tsawon lokaci suna tafiya kowa da abinda yake sak’awa a ransa, da gaske ba ta son bin sa Birmingham d’in nan amma sam ta rasa k’warin gwiwar da zata kalli fuskarsa ta ce ba za ta je ba. Sun kusa isa gurin ya dubeta ta side d’aya kafin ya ce “Idan ba ki bini Birmingham ba, kina tunanin akwai inda za kije ki samu peace of mind, kina ji dai Mai gidan ya ce Baya buk’atar ganinmu mu bar masa gidansa.” Hawaye ta ji yana son zubo mata “Kada Ki fara min wannan kukan banzan, ki bani numberr saurayinki na yi magana da shi idan yaga ya shirya aurenki ya fito nan da kwana biyar na aura miki shi a wuce wajen, amma idan aka zo bincike wajen su Abbu asiri ya tonu fa?” Rintse idanunta ta yi ita ma tana jin wannan fargabar amma tana tunanin ai ba za su tona mata asiri ba, tunda idan sun tona kan su suka yiwa. “Ki ba ni numberrsa zan yi magana da shi.” Wani dad’i ta ji ya tsarga mata duk da gefe guda tana jin Shakka da kasantuwar hakan, tun da dai an ce zancen duniya ba ya b’uya. Bai sake mata magana ba har zuwa sanda suka isa Immigration office d’in. “Dama da zarar sun tambayi sunanki, kice musu Hamda Hammad na gaya miki.” Ta d’ago tana son tambayarsa ya tsatstsareta da idanunsa “Daga yau na canja miki suna, tunda ance ni ne Babanki, suma takardun makarantar gobe za mu je court ki yi changing name d’inki kin koma Hamza Hammad UU d’an borno.” Tsit ta yi saboda sam ba zata iya magana ba. Ya fice daga motar, kafin ya yi mata magana ita ma ta bi bayansa tana mamakin sunan da ya lak’k’aba mata. ******************* Cikin ikon Allah likitocin suka samu nasarar farkar da Hajiya Didi, ta hanyar gark’ama mata oxygen aka dinga zuk’o numfashinta. Ta farka sai dai sam magana ta d’auke tsaf daga bakinta, ga ta dai idanunta biyu amma ba ta uhm bata uhm-umm sai hawaye da suke kwaranya a idonta sosai musamman idan ta so yin magana ta kasa. Da k’afarta da komai kuma hannayenta suna aiki, bakin ne dai ya d’auke, amma likitocin sun tabbatar musu a kowane lokaci bakinta zai iya dawowa. Hankalin D’an Borno family kam a tashe ya ke matuk’a da gaske, musamman Abbu da lokaci d’aya duk ya fita hayyacinsa, shima a lokacin da za’a aunashi tabbas za’a tabbatar yana buk’atar a yi admitting d’insa a hospital. Ita kuwa Ammi hankalinta a kwance yake ko banza dai ta san ta ture waccan matsalar, musamman ganin kowa hankalinsa ya kau daga kanta. A kuma daren ranar ne Abbu ya turketa da tambayar me yasa sanda abin ya faru ba ta sanar da shi ba.” Cikin muryar kuka ta tabbatar masa da cewa tsananin kunyarsa ne ya sa ta kasa gaya masa kuma da wani ido ma zata iya dubansa ta gaya masa wannan abin kunyar. Kamar zai sake mata wata tambayar sai dai ya ja bakinsa ya tsuke don sosai yake jin haushin tuna lamarin gaba d’aya. Mahmah dai hankalinta ba a kwance yake ba, tana son ta hana Hammad tafiya da Hamda amma Dida ta hanata, ta ce ta kyaleshi ba wani abu bane don ya tafi da itan, ta kuma ja kunnen d’iyarta Nanna akan ta kyaleshi kada ta sake yi masa maganar don a yanayin da yake tsaf zai iya sakinta idan har ta cigaba da jayayya da k’in bin umarninsa. Haka tilas ta hak’ura sai dai ta k’udirtawa ranta sam ba zata bar Hamda ta yi rayuwar jin dad’i ba, tilas sai ta bak’anta mata har ta gwammaci ta bar gidan da k’afafunta. _____________________ Suna fitowa daga Immigration office d’in ta ga ya d’auki hanya bai tsaya ko ina ba, sai wani k’aramin gida. Ba tayi magana ba har ya tsayar da motarsa ya fita ya bud’e k’aramin gate d’in. Ya shigar da motarsa y’ar madaidaiciyar harabar gidan. Zama ta yi har sai da ya ce “Fito mana.” Ta d’ago ido tana dubansa kafin cikin dauriya ta ce “Ya Hammad me zan yi?” Tsahon second yana dubanta kafin ya ce “Umarni na ba ki, ki fito kuma daga yau kada na sake jin kin kirani da Yaya Hammad ai ki na ji aka ce ni d’in ba wanki bane, Ubanki ne don haka ki dinga kirana da Daddy kamar yarda kika ji su Kamla na kira na. Ki fito na ce.” Ganin yarda ya tsare gida ne ya sata saurin fitowa. Gaba yayi a zuciyarta ta ce “Ashe dai mutumin nan mafad’aci ne?” Sai kuma ta kama bakinta da sauri tunawa da ta yi matsayin mahaifi ya ke a wajenta. Idan ta tuna hakan sai ta ji wani iri a ranta. Ya murza key ya tura k’ofar k’aramin parlourn. Sannan ya shiga parlourn tsaf da shi sai k’amshi yake. Tana so tambayeshi gidan waye sai kawai ji ta yi ya ce “Gidan abokina ne, mazaunin k’asar Birmingham, anan yake zama da matarsa idan sun zo hutu, shi yasa nima yanzu nake jin takaicin rashin gina gidan kaina, amma insha Allah soon zan gina ko don gudun kora daga gidan mutane.” Ta juya tana k’arewa madaidaicin parlourn kallo kafin ta ce “To me zan yi anan?” “Zama za kiyi kafin mu san abin yi, idan sauryin naki ya shirya auren sai na aurar da ke, ko ba shi da yarda zai ajiyeki sai na ba shi Aron nan, kafin ya samu inda zai ajiyeki.” A raunane ta d’ago tana dubansa kafin ta ce “Amma Yaya Hammad ba ni kad’ai zaka bari anan ba ko? Ka kawo min ko Kamla ce.” Tsaf ya tsaya ya k’are mata kallo kafin ya saki tsaki ya ce “Idan na sake jin kin kira ni da Yaya sai na murji bakinki, kuma ba Kamla zan kawo miki ba Kamlo zan kawo miki, ba kiji yarda mu kayi da uwarta bane, ko ke kurma ce ba ki ji mai uwarta ta ce ba, idan za ki shirya rayuwa ke kad’ai ki shirya na gaya miki.” Ya fad’a yana shigewa wani d’aki. Hamda ta bi bayansa da kallo hannayenta akan k’uncinta ta zabga uban tagumi, da gaske dukkan lamarinsa mamaki suke bata, shi kamar ma babu abinda yake damunsa daga bayyanuwar Sirrin nan..... Allah dai ya sa Zunnuraini ya shirya aurenta, ta samu zuciyarta da addu’a. To sai mu ce Ameen. Jikar Nashe ce.. [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE? BONUS PAGE 18 08033748387 ✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 Yau Didi jikin sosai ta mik’e idanunta sosai akan y’ay’anta da suka baibayeta zagaye da ita a gadon asibitin. Gwaggonsu Amina ce har a lokacin ba ta iso daga Dubai, don ta ce musu tana hanya a cikin satin mai zuwa. Didi so take ta yi musu maganar Hammad amma ba baki, sai da dabara ta fad’o mata sannan ta duni gadanga ta yi masa alamar ya samo mata abin rubutu. Shi kad’ai take wa fara’a bayan shi ko kallon arziki ba ta yiwa Abbu da Lauratu. Gadanga ya fita zuwa motarsa, ya samo mata littafi sabo da biro yana jin dad’in yau za su San abinda yake ranta. Sam ya mance da wannan hanyar ta rubutu. Yana komawa d’akin ya manna mata biro da takardar. Ta amsa sannan ta fara rubutun duk da dai ta fi ganewa Ajami amma haka ta dagura Hausar. Ina Hammad da Hamda? Shine abinda ta rubuta ta mik’awa Gadanga, ya yi tsai da ransa saboda bai San abinda zai ce mata ba, shi kansa bai ji dad’in hukuncin da Yayan nasu ya zartar be. Sai da ta sake tab’o shi ta tsatstsareshi da ido sannan ya saki ajiyar zuciya a hankali ya ce “Yaya ya kore su.” Didi ta mai da kallonta kan Abbu kafin ta mik’awa Gadanga hannu ya bata takardar da rubuta kalmomi guda uku ta mik’a masa “Ka yi gaggawar dawo da su, kafin na wa ran ya b’aci.” Daga haka ta mik’awa Gadanga takardar ta mayar da kanta Ta kwanta zuciyarta ce ta ke suya Idan ta tuna da lamarin. Abbu kam Shiru yayi fuskarsa a d’aure saboda umarnin Didin ya zo masa a bazata. Sam ba ya jin zai iya yafewa Hammad wannan gungumemen laifin, ita kuma yarinyar da zarar ya cigaba da ganinta tsanarta ce zata dinga hauhawa a zuciyarsa. Sai dai ya san sarai ba shi da ja akan umarnin Didi musamman da ya lura ko son had’a ido da shi bata yi. Ammi kuwa dama ba zuwa take ba, sabida tasirin idanun Didin a kanta yarda take k’in kula ta da banzan kallon da take mata dalilin kenan da yasa ta bi shawarar Kady aka kai Didin wajen malami ya d’aure mata baki, la’akari da duban da take mata ta san zata iya tona mata asiri. Shi yasa a daren ranar ta nemi shawarar Kady ita kuma ta bata shawarar a mannewa Didin baki, ba sai tana magana ba balle ta k’aryata Ta. Shi yasa Ammin take shan shatafinta ko bakomai ta cusawa Sadiya bak’in ciki goma da ashirin, dama ta tsaya mata a rai bata son ganinta burinta bak’in cikin Abin nan ya kashe su ita da Didin idan yaso ta mallaki gida ba wanda zai saka mata ido. Budirinta take sosai, musamman na shirye-shiryen auren y’ay’anta Najma da Nasma, ba ta damu sam da halin da ahalin d’an borno suke ciki ba, cafkar naira take a wajen angwayen son ranta irin surikan da take so kenan, y’ay’anta su samu mazaje na kece raini ba ta damu da wa za su aura ba? Menene halayyarsa? Burinta kawai su samu Hamshak’an masu kud’i wanda suka ci suka tada kai ba matasan masu kud’i ba, shi yasa ba ta kyashin fitar da ko nawa ne akan y’ay’anta don tabbas ta san kwalliya zata biya kud’in sabulu. ****** Tsawon mintuna Ashirin yana zaune cikin motar yana jiran Hakimar tasa Nanna kenan, bai d’auka har a lokacin fushin take da shi ba da bai wahalar da kansa ya zo ba, da sai ya turo mata text ya ce mata jibi za su tafi. Dama yazo ne su fahimci juna ita kuma ta zauna ta na b’ata masa lokaci. A d’abiarsa shi mutum ne da ba ya son rainin hankalin y’a mace sam ba ya jura. Wa la Allah ko don ya taso da taurin zuciya tunda abin ya faru ya dainewa mata uzuri a rayuwarsa. Gani yake duk halinsu d’aya, shi yasa ko da aka ba shi zab’in aure ya ce su zab’a masa ko ma wacece ba shi da lokacin soyayya da y’a mace, shi yasa Sam fushin Nanna ba ya tasiri Akan sa. Sau tari da kanta zata yi fushin da kanta kuma zata sharewa kanta hawaye ta sauko ta zo tana neman sulhu a wajensa. Duka mata kud’in goro yake musu bai tab’a kallon mace ya ji yana sonta ko ya furta mata ba. duk da karakaina da matan suke a kansa da nuna masa soyayya baya jin komai a ransa game da su, shi yasa a yanzun yake mamakin kansa da har ya shiga hurumin Hamda yake tausaya mata, bai San dalili ba, ko don kasancewarta.... tsam ya yi da ransa yana cije leb’e kafin ya sauke ganinsa akan Nanna da take taku tamkar wahainiya duk don ta ja ra’ayinsa, Sai dai ta makaro don sau tari ko a b’angaren mu’amalar aure Nannan ce dai take kawo kanta gareshi ba dai shi ya nemeta ba. Ya lumshe ido bayan ya ja hucin ajiyar zuciya sannan ya danna button motar ta yi unlocking kanta, hakan ya Bawa Nanna damar shiga gaban motar, bayan ta sake d’aure fuskarta tamau, Duk da gargad’in da Dida ta yi mata bata ji ba, burinta ta samu ta lallashe shi ya janye tafiyar da waccan bak’ar yarinyar da haka kawai ta ji ta tsaneta. Murya a shak’e ya ce “Gaisuwar ma sai na rok’a?” Ta kuwa daddage ta cono baki kamar yarda k’ananun yara suke shi sai abin ma ya bashi dariya, amma ya gintse yana sake lalubo k’wayar idanunta ya ce “Me Yasa ba kya son zaman lafiya ne Nanna? Yarinyar nan fa ba ta da wani gata sai nawa idan na barta anan ina ki ke so ta jefa rayuwarta?” “Dida ta ce zata rik’eta.” Kai tsaye ta ba shi amsa. Shi kuwa yana murmushi ya shafi gefen kumatunsa ya ce “Akan me Dida zata rik’eta alhali nine mahaifinta kuma ina raye?” Wani abu ya tokare k’irjin Nanna ta d’ago a fisge tana kallonsa “Da gaske kenan ka amsa kai ne ka yi cikin nata? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna. Don Allah to ya aka yi ka aikata wannan d’anyen Ai kin?” Still yana murmushin ya ce “A yarda labari ya bayyana kansa ance giya na sha ina cikin maye na kusanci uwarta... Ya ja wani numfashi ya fesar da iskar bakinsa “Any way ba wannan ya kawo ni ba, ki zama ready jibi za mu wuce Birmingham kuma ki saka wa zuciyarki hak’urin Zama da ita don ta riga ta zama wani sashe na family na. Amma fa idan kina son zaman lafiya da ni.” Shiru tayi tama rasa abin cewa kafin ta saki wani malalacin murmushi ta girgiza kai “Idan kuma bana son zaman lafiya da kai fa?” “Ki wulak’antata” Direct ya bata amsa ba tare da ya ko kalleta ba. Nanna ta girgiza kai kawai tare da bud’e motar ta fice don tabbas idan ta cigaba da zama zata iya rusa masa kuka ita kuwa sam bata son ya ga karyewar zuciyarta. Ya je yayi ta tafiya da ita amma wallahi ita kanta yarinyar sai ta gudu da k’afafunta saboda izayar da zata dinga mata. Sam bata so yiwa y’ay’anta y’an uba ba Na halak ma balle wannan da ta zo ta haramtacciyar hanya. Tana fita yana jan motarsa da mugun speed don kada ma ta saka ran zai bi ta ya lallasheta. Nanna ta ja sillan k’afafunta ta shige gida ita da kanta ta san bata da wani muhimmanci a wajensa, bai damu da ita ba. _________________ Bai isa gidan ba sai da ya tsaya a wani mall ya siya mata kayan sawa don wanda tazo da su kala uku ne kacal kuma duk ta sakesu kullum wankewa ta ke ta Mayar, har underwears da kayan makeup duk Sai da ya siya mata. Sannan ya samu wani trolley na zuba kaya mai kyau ya siya mata har da hand bag da shoes da turaruka, kaya dai fal masha Allah kamar me. Tana rakub’e zaune kan kujerar parlourn tayi shiru hannayenta zube a kuncinta. Ta ji murd’a k’ofarsa sam bata firgita ba don ta San shine illa iyaka gyara zamanta da tayi had’e da saurin goge hawayen fuskarta, don bata mance gargad’insa na yau da safe ba. Ajiye kayan ya yi a tsakiyar parlourn yana amsa sannu da zuwan da take masa. Direct d’aki ya wuce inda ya ke kwana kafin ya fito fes da shi cikin jallabiya mai gajeren hannu sai zabga k’amshin turaren HuGO BOSS Yake. Kayan ya duba kafin ya ce “Kika kasa bud’ewa ki ga ko menene?” “Wannan ne a gabanka” ta samu kanta da furtawa a zuciyarta. “Na samu wancan saurayin naki ba yarda ban yi da shi ba ya amince ayi Aurenku ya tabbatar min bai shirya ba, har ce masa na yi sadaki kawai zai bayar amma ya k’i. Don haka ki k’addara a ranki dama ba mijinki bane. Na yanke shawarar da zarar mun je can idan kin kafe auren kike so akwai abokina Jamal mazaunin can sai na ba shi aurenki.” Idanu ta zuba masa kafin ta d’auke kai murya a sark’e ta ce “Ni ban ce aure nake so ba, na yi karatun Kawai.” Dole ki yi aure don idan ba aure kika yi ba Nanna ba zata barki ki zauna lafiya a gidanta ba. Ki Zama ready kuma jibi zamu wuce umarni ne kuma ba shawara ba. idan kuma kin ga ba zaki bi ni ba, kina da inda ya fini to ki gaya min na baki kud’in mota.” Shiru ta yi masa kamar ta ce eeh ba zata bi shi ba, amma da gaske bata da wanda ya fishi tunda an ce shine mahaifinta. ____________ Ranar da za su tafi tun wuri ta shirya tsaf cikin kammalalliyar shiga ta doguwar riga samfurin k’asar egypt. Kalar sea blue mai adon baby pink hakan yasa ta nad’e kanta da mayafin ruwan hoda. Ba k’aramin kyau ta yi ba duk da kasancewarta mai duhun kala hakan bai b’oye zahirin kyan fuskarta ba, dirarren jikinta ya bayyana a cikin rigar. Ta zura tattausan takalmi a k’afarta kalar pink. Ta bi jikinta ta feshe da turaren Almukhalad’ bayan ta shafa body mist na kamfanin oud. Sanda ta ji knocking d’insa sannan taja kyakykyawar trolley d’inta. Tsam yayi da ransa yana k’are mata kallo shi kansa bai lura da yarda ya tsatstsareta da ido ba, har Sai da ya ji muryarta tana cewa “Ya Hammad ina kwana?” Tsaki ya ja kafin ya ce “Lafiya lau, sunan nan ba zai fita daga bakinki ba ko?” Sunkuyar da kanta kawai ta yi don bata jure wa kallonsa musamman idan ya kafeta da idanunsa. Bai sake magana ba ya juya ya fice janye da tasa trolley d’in, ita ma ta bi bayansa, tana mamakin yarda gabanta ya ke tsananta fad’uwa a duk sanda suke tare ko ta shak’i daddad’an k’amshin turarensa. A motar ma kasa nutsuwa ta yi, ta shiga danna wayarta tana game, har suka isa k’ofar gidan su Nanna sai sannan ya yi magana bayan ya rage sautin karatun Alk’uranin da yake ji “Ki shiga ki ce su fito, mun kusa makara kada mu yi missing flight.” A diririce ta shiga kallonsa shi kuwa bai sake magana ba illa cigaba da waya da wanda zai karb’i motarsa da ya yi, yana sanar da shi su had’e a airport. Zuciyarta na rawa ta bud’e motar ta fito. Sarai ta san gidan su Nanna don ba wannan bane karan ta na farko a zuwa, sun sha zuwa da Didi biki ko suna ko gaisuwar mutuwa. Tun daga waje ta fara sallama, tsoron Nanna ne fal a ranta, yanayin masifarta yana razanar da ita. Tsaf ta lura Nanna mafad’aciya ce ta gaske. Sab’anin mahaifiyarta Dida da ta kasance mai sauk’in hali. Tura k’ofar ya yi dai-dai da fitowar Nanna daga d’aki, fuskarta a cukurkud’e da alama nasihar da Dida ta yi mata ce ta tunzira Mata zuciya ban da abin Nanna ai gaskiya Dida ta gaya mata d’a dai na kowa ne, kuma duk wanda ya haihu ba halin k’warai bane gareshi ya wulak’anta zuri’ar wani, musamman tunda bai tara sani ga Allah ba balle ya san shi ba zai iya jarrabarsa da abinda ya jarrabi wani sashi daga cikin al’umma ba ki yi nazari da kyau Nanna duniya juyi-juyi ce, idan kin rik’e nasihata za ta amfaneki zubar da ita kuwa zai iya zama da na sani a gareki. Ta mik’e ta fito ba tare da amincewa da shawarar mahaifiyar tata ba. Kicib’us d’in da suka yi a bazata yasa zuciyar Kowannensu ta d’auke wuta na tsawon d’akikai, kafin Nanna ta zabga mata harara ta kuma k’i amsa gaisuwar da take ta jera mata muryarta na rawa. Da gudu Kamla ta zo ta rungumeta a fusace Nanna ta janye ta had’e da jan kunnenta da k’arfi “Last warning da zan miki shine ba ke ba y’ay’ana.....Saboda ni y’ay’ana tsarkakkune da aka haifesu da aure ke kuwa kwamacalar da take kan ki kad’ai ta isa a guje ki, bayan kasancewarki shegiya...” wata irin gigitacciyar tsawa Dida ta sakar mata fuskarta d’auke da b’acin rai ta kalli Khairi “Je ki kira mun Babanku a mota yau da kaina zan ba shi umarnin ya saketa tunda ba ta jin maganata..” [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE YA ABIN YAKE? BONUS PAGE 19... 08033748387 ✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 Nanna jiki na rawa take kallon Dida da nufin bata hak’uri, sai dai Didan ko kallonta ba tayi ba, saboda ranta ba k’aramin b’aci ya yi ba, Ta rasa wace irin k’wakwalwa ce da Nanna sam albasa ba tayi halin ruwa ba. Ko da Khairi ta sanar masa da sauri ya fito daga motar duk zatonsa Nannan wani mugun abu tayi wa Hamda, tabbas yau da ta gane Kurenta. Turus ya yi a bakin k’ofar falon Didan ganin Hamdan lafiya lau take. Cikin sakin fuska Dida ta ce ya shigo ya zauna. Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya daure ya saka kai ya shiga. Bayan amsa gaisuwarsa Dida ta ce “Gata nan Hammad tunda ba taji duk shawarar da na bata game da ta hak’ura ta rik’e yarinyar nan, ka saketa kawai saboda idan ka tafi da ita ba k’aramin tashin hankali zata sakawa zuciyarka ba. D’agowa ya yi idanunsa cikin na Nannan yana mamakin yarda gaba d’aya ta sauya kyawawan d’abiun da ya santa da su. Tsaki kawai ya ja kafin a hankali cikin ladabi ya ce “Ki rabu da ita Dida, kada ma ki sawa zuciyarki b’acin ranta. Da zarar mun je can zan yi solving d’in abin ba dai yarinyar ce bata son gani ba, to muna zuwa zan aurar da ita ta tare a gidanta.” Dida ta saki tsakin takaici “Bata isa ba wallahi, kai da gidanka kana da ikon kawo duk wanda kake son ya zauna tare da kai, sai dai ita ta bar gidan.” Agogo ya kalla murya a cunkushe ya ce “Ki yi hak’uri, ya zame mata tilas ma ta gyara, Yanzu za mu wuce kada mu yi missing flight.” “Shikkenan Hammad Allah ya tsare ya baka ikon sauke nauyin da yake kanka.” Har bakin k’ofa ta raka su, tana sake jan kunnen Nanna cikin nasiha da lallashi. Jikinta dai ya yi sanyi a zahiri amma a bad’inance ita kad’ai ta san takaicin da yake nuk’urk’usarta. ______________________ A tsorace Hamda take sosai a cikin jirgin, musamman kasancewar wannan shine first flight d’in ta. Duk ta bi ta takure kanta ta kasa sukuni, yana lura da duk wani motsinta shi yasa ya ce Khairi ta koma kusa da ita. Khairi kuwa ta murje idonta ta koma duk da hararar k’asan ido da Mommynta take zabga mata. Tun tana tsoro har ta saki jikinta ta zauna ganin tafiyar ba nan kusa bace. Abincin jirgin ne dai sam ta kasa ci saboda aman da take ji, kuma ma yanayin abicin nasu bai yi mata ba. Kusan asuba suka sauka a k’asar ta England cikin birnin Birmingham, sam ba tayi tunanin garin da sanyi har haka ba shi yasa bata tanadi rigar sanyi ba, shima kuma bai yi azancin siyo mata rigar sanyin ba. Sosai ta dinga rawar d’ari hak’oranta na kafkaf kamar za su datse harshenta. Samun kansa ya yi kawai da zare jibgegiyar rigar sanyin da take jikinsa ya mik’a mata. Hannu na rawa ta damk’i rigar ta saka. Tana jin nutsuwa na sauka a ranta. Tsaki Nanna ta ja a fili tana mamakin dalilinsa na kaffa-kaffa da yarinyar har da wani cire rigarsa ya bata, bayan ta san shi da matuk’ar jin sanyi. Bai damu da kallon da take wurga masa ba yayi gaba cikin takunsa na k’asaita. K’arfe 8:00 daidai suka isa bakin gidan su. Ya saka mukulli ya bud’e y’ar madaidaiciyar k’ofa. Gidan na nan tsaf da shi kasancewar yayi wa mai hidimar gidan waya tun shekaranjiya shi yasa ya gyara gidan tas. Sai zabga k’amshi yake. Ta samu kujera ta rab’e ganin ba wanda ya bi ta kanta. Hannayenta zube a k’uncinta tana mamakin yarda rayuwa take juyin waina da ita. Dubi dai yarda lamarin ubangiji yake ikonsa a kanta ko a mafarki ba ta tab’a zatan zuwa k’asar nan ba, sai ga shi Allah ya kawota. Sai dai rashin sanin irin rayuwar da zata yi ne yake fad’ar mata da gaba daga yanayin matar gidan ta fuskanci k’warai ba tayi na’am da zamowarta cikin gidanta ba. Ita kuwa Khairi suna shiga d’aki Nanna ta saka su a gaba da jan kunne, ko da wasa ku ka shiga sabgar shegiyar y’ar can wallahi sai na ci mutuncinku. Kamla idonta ya kawo ruwa sam bata son Mom take hanata huld’a da Hamda, saboda tana son ta sosai. Hakan yasa dole Khairi ta zauna ba tare da ta kira Hamdan sun shiga d’aki ba. Har ya watsa ruwa ya kwanta don Ya huta, sai ya tuna da ita ya san bai zama lallai Nanna ta kaita masauki ba, ba ma wannan ba yana lura da ita a jirgi ba wani abincin kirki ta ci ba. Don haka ya mik’e da sauri ya fita. Hasashensa kuwa ya zama gaskiya don tana rakab’e a kujera ta lula duniyar barci ita kad’ai ce a parlourn kamar mayya, ta takure jikinta da alama sanyi take ji sosai. Hannu yasa ya d’an buga bayanta da sauri ta mik’e a d’an firgice idanunta sun yi nauyi saboda barcin da yake cikinsu. “Me yasa baki shiga d’aki ba?” Ta ware idonta kafin ta ce “Ba’a nuna min d’akinba ai.” Tsaki ya ja ya mik’e hannunsa jaye da trolley d’inta ya ce “Biyo ni.” Murd’a d’akin su Khairi ya yi ga mamakinsa sai ya ji shi a kulle abinda ba a yi kenan rufe d’aki a gidan ko menene dalilin hakan. Ya shiga Knocking k’ofar da d’an k’arfi. Cikin barci Khairi ta farka tana fad’in “Waye?” “Bud’e” ta ji muryar Daddynta, hannu ta sa ta murd’a sai ta ji d’akin is locked sai sannan ta tuna Mommynsu ce ta gark’ame d’akin duk don kada Hamda ta shigo. Murya a tsorace ta ce “Daddy Mom ce ta rufe da key.” Da k’arfi ya ce “For What reason?” Jikin Khairi ya soma rawa don sam bata son tashin hankali a rayuwarta ga shi ta ji Daddy kamar ransa ya yi mugun b’aci, ta kasa cewa komai sai zare ido take. Da sauri Hammad ya juya ga Hamda kawai ya sake ce mata biyo ni.” Direct d’akinsa ya wuce da ita, dole ne ma ya yi maganin Nanna. Ya bud’e wardrobe ya d’au abinda zai buk’ata ya kalleta “Zauna anan kafin na gyara miki wancan d’akin.” Ta bi d’akin da kallo had’uwa da tsaruwar d’akin kad’ai ya isa ya burgeka balle yarda d’akin ya rik’e turarensa k’am tamkar anan ake had’a samfurin turaren kafin ta yi magana ya fice daga bedroom d’in nasa. Ta bi bayansa da kallo kafin ta sauke wata sassauk’ar ajiyar zuciya. Da zata iya kwanciya za tayi kawai amma ta fi so ta watsa ruwa tukun. Don haka direct ta fad’a had’adden toilet d’in nasa. Shi kuwa yana fita d’akin Nanna ya wuce direct, Fuskarsa a had’e sosai. Ya tura k’ofar ya shiga. Nannan tana zaune gaban dressing mirror ta na shafa mai ta ganshi ya shigo da kaya a hannunsa ya zube kan gado. Sannan ya hau gadon ya yi kwanciyarsa ba tare da yayi mata magana ba. Cikin mamaki take kallonsa “Ban gane ba Yallab’ai, ina naka d’akin?” Ba tare da ya kalleta ba ya ce “Yana wajen Hamda.” Da sauri ta mik’e har towel d’inta yana shirin zamewa ta ce “Wani irin abu ne wannan zaka d’au master bedroom ka bata alhali akwai guest room.” Ya d’ago yana tsatstsareta da ido da tilas ya sata risnar da nata idon “Na fiki sanin da guest room d’in na bata nawan. Saboda ita ba guest ba ce yarda kike tak’ama da gidan nan itama haka take tak’ama da shi.” “Wallahi k’arya ne ni da nake matar gida har ka had’ani da ita?” Murmushi ya saki kawai ya ja filo ya kwanta “zuwa ki fitar da ita daga bedroom d’in nan shine kuskure mafi girma da zaki aikata a rayuwar aurenmu, duk ba ke kika jawo ba da ba ki tilastani zuwa Nigeria ta ya kike tunanin duk wad’annan abubuwan za su faru, don haka duk abinda ya faru ke kika janyo.” Daga haka ya lumshe idonsa ya bar ta a tsaye zuciyarta na kissima mata al’amura da dama. Da kyar ta ja sillan k’afafunta ta zira doguwar riga mara nauyi sannan ita ma ta bi gefensa ta kwanta, kusan zata iya cewa wannan shine karo na farko da ya kwanta a d’akinta, kullum ita take kai kanta wajensa. Tsaki ta ja tana tunanin Hamda kwance can a lumtsumemen gadonsu. Sun sha barci sosai don sai da yunwa ta fara nuk’urk’usar ko wannensu sannan suka tashi. Hamda ma yunwar ce ta farkar da ita sai dai tana tsoron fita parlourn, ta ci karo da Nanna, bata san wannan kallon da take jifanta da shi. Da kansa ya mik’e ya fito tunawa da yayi haka ta kwanta bata saka komai a cikinta ba, gwara ma su sun ci abinci a cikin jirgin. A kitchen ya taradda Khairi da Nanna suna dafa noodles don ita kad’ai ce da su a gidan komai sun fitar da shi kafin su tafi. Ya lek’a tukunyar sannan ya juya ya fice. Direct d’akin da take ya nufa har ya murd’a zai shiga sai kuma ya tsaya ya d’an k’wank’wasa. Da sauri Hamda ta zari veil d’in da yake gefenta ta nad’e himulin gashinta da shi. Har yanzu ta k’i amincewa zuciyarta cewa muharraminta ne. Ya tsaya daga bakin k’ofa yana nazarin fuskarta, gaba d’aya yunwa ta riga tasa ta fara fita daga hayyacinta. Ya ja tsaki yana sakin handle d’in k’ofar “Kina jira a zo a baki abiinci ne? Ba zaki zo ki samu abinda zaki ci ba.” Da kyar ta mik’e jiri na d’an d’ibarta kad’an ta saka k’afa zata fito daga d’akin sai gani ya yi tayi baya ta fad’i. Da hanzari ya juyo ya d’aga cak yana mamakin wauta irin tata. Fuskarsa a d’aure ya ce “Wai ke wace irin shashashace? Kin san ba zaki iya tafiya ba wa yace ki taso?” Ya zaunar da ita a gefen gadon sannan ya fice. Tea mai madara had’ad’de Nanna ta ga yana had’awa mamaki ya kusa kasheta a tsaye don dai ta san baya shan irin wannan tea d’in zallar black ko green tea yake sha. Ta kuwa tsatstsareshi da ido “Me zaka yi da shi?” Bai kulata ba ya fice da mug d’in a hannunsa da sauri ta bi bayansa sai taga ya shige d’akinsa, wani irin tuk’ukin b’acin rai ya shigeta. Da sauri ta juya d’aki tana lalubar wayar aminiyarta da take zaune a garin Uk. A tsaye ya mik’a mata mug d’in hannunta na rawa ta saka hannu ta karb’a ta kai bakinta da sauri take zuk’a alamar tana jin yunwa sosai. Juyawa kawai ya zari key d’in motarsa gwara ya je ya samo solution akan Hamda don ya lura zamanta da Nanna ba abu ne mai yiwuwa ba. Shopping zai yi saboda ba su da komai a gidan, zai biya kuma wajen abokinsa Mustafa da suka fara maganar Hamda da shi a waya su yanke shawarar yarda za su b’ullowa Ammi. Da safe kuma yaje makarantar da ya riga ya samar mata admission. __________ Cikin dare Gwaggo Asma’u jirginsu ya sauka daga k’asar Dubai. Duk da gajiyar da tayi amma a daren ranar ta matsantawa mijinta Sheikh Abdallah akan sai sunje sun ga jikin Didi. Ba kowa a wajenta sai Sadiya da Lauratu. Da murna suka tareta bayan an gaggaisa Sheikh Abdallah ya tambayi yanayin ciwon nata. Don ya ga Didin bata magana sai dai kallo da ido. Sai da suka bashi labarin kaf abinda yake faruwa sannan suka ga ya saki murmushi kasancewarsa masani akan cutittuka na shafar jinnu ya tabbatar musu ciwon Didin bana asibiti bane da safe a neman mata sallama shi zai sake dubata. Daga haka ya yi musu sallama ya tafi ya bar matarsa a wajen. Suka cigaba da jajanta lamarin. Asma’un ce ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “Amma Sakina an yi y’ar banza, su kuma su Yaya fisabilillahi ya aka yi suka yarda da wannan tatsuniyar da ta shirga. Duk ma ba wannan ba yanzu ina Hammad da yarinyar me yasa ba’a gwada k’wayoyin halittarsu ba a tabbatar shin y’ar da gaske tasa ce ko sharrinta ne.” Mahmah ta ja mayafi ta goge hawayen fuskarta kasa magana ta yi sai Lauratu ce tace “Ai zancen da nake miki Hammad ya tafi da y’ar Birmingham bayan da Yaya ya koresu.” Rik’e kai kawai Asma’u tayi kafin ta ce “Kash Na so Na zo na sameshi amma bakomai idan ta san wata ai ba ta san wata ba da kaina zan nemo gaskiyar lamarin.” Tun bayan da ya kawo mata abinci da kansa cikin d’aki bai sake waiwayarta ba har safiyar Ranar. Ya shigo fes da shi cikin shigar bak’ar Rigar Hilfiger da brown trouser. Sai jibegegiyar rigar sanyi bak’a a jikinsa kansa kuma sanye da bak’ar hular sanyi da ta rufe masa har kunnensa. Yana shiga tana share hawayen da yake sauko mata. Ya san kukan me take kukan maganganun da Nanna ta dasa mata take, yana jin su. Sharewa ya yi kamar bai gani ba “Mik’e mu je makarantar da za ki fara zuwa.” Ta mik’e cikin sanyin jiki suka fice daga gidan. Sai da suka isa harabar makarantar Aston University da ke Birmingham cikin wata irin murya ya ce “Saura ki shiga kina wannan sussunne kan, kuma kin iya turanci ko?” Sunkuyar da kanta kawai tayi tana jin takaicin maganarsa. Ya fice daga motar ita kuma ta bi bayansa. A hanyarsu ta dawo ya kalleta yana reverse da mota zai shiga layinsu ya ce “Zamanku da Nanna ba zai yiwu ba, don haka na yanke shawarar aurawa Amini na ke.... kin amince?” Da sauri ta d’ago tana kallonsa kafin ta ce wani abu yace “Shine abinda yafi kamatarki a halin yanzu.” [1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: YA ABIN YAKE? LAST FREE PAGE INSHA ALLAH Normal group 300 Vip 500 Special people 1000 sending privately. Payment via 2118666253 U B A Sai a tura shaidar biya ta (08033748387. Ga wanda suka biya akwai kyautar free book d’ina Na Zumuncin Zamani.) An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels