An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ADUL* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *SANARWA* *Dafarko littafinnan na siyarwa ne amma saboda murnar shiga sabuwar shekara yasa namaidashi free* Dz book completely goes to *HASSAN 80k & HUSSAIN 90k* *Special gift to my besty* *UMAMATU UMAR ADAM* *APPIE NEW YEAR 2020* *PAGE 1* Bismillahirrahmanirraheem. Kallo daya zakayiwa gidan ka fahimci cewa talauci yayiwa ahalin gidan katutu sosai a gindinsu,duk da kasancewar gabadaya gine ginen garin na jar kasa ne kuma gajeran gini,amma Wannan gdn daban yake a cknsu don ko arzikin gini da laka ma bai samu ba,ginin langa langa ne itama ta lalace sosai don duk ta bubbule tayi tsatsa,,gajeran ginin bandakin gidan ne kawai na laka amma hatta dakunan ckn gidan na kara ne dama kuma guda 1 ne. Wata matashiyar budurwa ce wadda batafi 18 year's ba tafito daga gidan ckn sauri kafarta na sanye da wani kodadden silifas wanda aka kulle da leda saboda tsinkewar da yayi,kana kallonshi zaka hango tarin dinkunan da akai masa, tana sanye da bluen yadi dinkin riga da zani single, kallo daya zakayiwa kayan kabashi sunan uniform, batada hijab sai dankwalin da ke daure a kanta wanda bai hana dogon kashin kanta da ke kitse da manyan kitso fitowa ba,dogowa ce siririya chocolate colour,tanada tsananin kyau na fada a ko'ina me ban mamaki,idanuwanta manya wanda idon ka kalleta zakayi tunanin tanajin bacci ne,,hancinta dogo ne me tsananin kyaun fasali,,bakinta girmansa dai² gwargwado abin sha'awa,gaban goshinta wani kwantaccen gashi ne baki sidik wanda yai bala'in kara mata kyau kana kallonta zaka fahimci tanada sanyin hali. Ckn sauri take kokarin barin kofar gdn nasu tajiyo muryar mahaifiyarta sama² tana kiran *MUWADDAH! MUWADDAH!!*,murmushi tayi tareda girgiza kai tana buga kafa irin na shagwababbun yara,,da gudu takoma ckn gidan tashiga dakin karansu wanda akaiwa labule da wani yamushasshen buhu,mahaifiyarta na xaune da Kofi a gabanta ta zubawa kofa ido da alamun tana jiran shigowar muwaddan. Tana shiga ta kyabe fuska kamar zatayi kuka, ckn shagwaba tace "Don Allah iyata ki banni nayi tahiyata kada ayi babu niya,,takarasa tana turo baki gaba. Murmushi mahaifiyartata tayi ckn kulawa tace " muwaddatu na ki rage wanga zumudi kyajiya??,,kizo kisha kunun nan ko kadanne banson ganinki da yunwa koda nikuwa zan dawwama cknta,, takarashe ckn raunin murya. Shiru muwadda tayi ckn matsanancin tausayin mahaifiyar tata,Abubuwa da dama ne suka shiga dawo mata tamkar ynz suke faruwa,lokaci guda idonta yakawo kwalla alamun zatayi kuka,kallonta takai kan kafafuwan mahaifiyarta da ke kunbure suntum rabinta a rarake an barbada magani amma hakan bai hana hango kashin kafar ba, wani gigitaccen kuka ne ya kwace mata,durkushewa tayi a gurin tanajin zuciyarta tana mata matsananciyar suya, ckn kuka take cewa "Allah yai miki sakayya iyata!!!Allah yaiwa Babana sakayya!!! Wlh natsenesu!!banida makiyan da suka hisu,,Tabbas bantabba ganin mugaye Azzalumai wadanda kansu kawai suka sani ba tamkar *MASARAUTAR ZINARI*,,,natsanesu iyata!!Wlh bana kaunar ganinsu!!!Takarashe dasakin wani gigitaccen kuka. Cikin dauriyar gaske mahaifiyarta ta janyota jikinta tareda goge mata hawayen fuskarta tana bubbuga mata baya,,tasani tabbas ya cancanta muwadda tayi kuka,amma baxata nunamata hakaba dole ta tausashi zuciyar yar tata saboda shine abinda yafi komai cancanta da tayi ko da kuwa bataso,,cigaba da buga bayan muwaddan tayi har saida tayi shiru sai sheshshekar kuka da takeyi,daukar kofin da ke gefenta tayi tanufi bakin muwadda,,,kauda kai tayi alamun baxata sha ba,Ajiye kofin iya tayi a gefenta tareda kawar da kanta gefe,,dasauri muwadda ta taso tarike hannun mahaifiyarta tareda goge hawayen fuskarta tace " Kiyi hkr kyajiya iyata??To zansha. Ba musu iya tadauko kofin kunun da baifi rabi ba ta mikawa mata,,karba tayi ta kurba sau uku ta ajiye tareda mikewa tace "iyata ni zantahi,ki tayani da addu'a Allah yasa ina daga ckn bayin da sarki zai y'anta yau,,badon kamai ba don nasamu damar kula da ke. Ckn kulawa iya tace " Karki damu diyata nayi miki dama,,maxa ki tahi kar ki makara. Ckn sanyin jiki ta fito daga gidan nasu,,tana tafiya tana sauri tare da sharar hawaye,tayi tafiya mai nisa kafin taxo kofar wani dankamemen gida me tsananin kyawun gaske,,duk iya kulewarka a kallo baxaka hango karshen gidan ba,,gine ne tamkar a kasar turai,bazaka taba tunanin a ckn garin yakeba,,kallo daya zakayiwa gidan ka tabbatar gidan sarauta ne,,A can saman katuwar kofar gidan aka rubuta *MASARAUTAR ZINARI*. Ckn sauri ta wuce masu gadin gidan ta shige ciki,,bayi ne birjik kowa da abinda yakeyi,,dukansu mazansu da matansu suna sanye da yadi blue irin na jikinta amma maza wando ne,mafi yawansu fuskarsu dauke da annuri suke aiwatar da al-amuransu. Kai tsaye wata doguwar hanya tabi,batayi tafiya mai nisa sosai ba sai gata a wani bangare me tsananin kyau,,bayi maza guda biyu suna kofar shiga wajen a tsaye sunyi kekam ko cikakken motsi basayi,,yayinda wasu mata bayi suke shawagi a wajen. Batareda fargabar komaiba tashiga wajen,,hadadden parlour ne mai tsananin kyawun gaske wanda aka kayata da kayan Adon sarauta,,wasu bayi yammata guda 4 suna tsaye a dakin babu wadda takewa yar uwarta mgn,,haka tabi sahunsu ta tsaya a inda suke,,a kalla sunshafe awa 2 tsaye a wajen amma kaf cknsu babu wadda zaka kalla kace tagaji da tsayuwar,don da alama sungama sabawa. Cikin tsananin takun kasaita da kololuwar ji da kai take tafiya tamkar bata kaunar taka kasa,,bayanta wasu bayi ne a kalla sunkai 8 suke take mata baya,, yayinda daga cknsu ke rike da hadaddiyar Alkyabbarta wadda tagaji da haduwa. Suna hangota gabadayansu ckn rawar jiki suka zube suna jero mata kirari,,batare da ta kalli ko dayansu ba taxauna akan hadaddiyar kujerar sarauta,,cigaba da jero mata kirarin sukai ba kakkautawa,a kalla saida suka shafe 20mints suna Abu daya kafin daya daga ckn bayin da ke tsaye tace *GIMBIYA JALILA* ta amsa gaisuwarku yayan talakawa. Sai a sannan suka mike daga tsugunnan da sukayi. Ckn matukar kyama gami da tsananin wulakanci da kaskanci gimbiya jalila ke binsu da kallo,,saukar da kai kasa muwadda tayi don ko kadan bata kaunar kallon fuskar gimbiya jalila saboda tsananin tsanarta da tayi. Wulakantaccen kallon da gimbiya jalila ke aikawa muwadda na musamman ne,,batasan me yasaba yarinyar ba abinda tai mata amma tana tsananin tsanarta fiye da kowa,kuma baxata ce ko saboda kyawun muwaddan bane don itama kyakykyawa ce amma tabbas tsanarta me tsanani ce a ranta. Daga ckn masarautar suke jiyo muryar wani bafade yana sanar da cewa sarki yabada umarnin kowa ya hadu a fada ynz saboda gabatar da yantaccun bayi na Wannan shekarar,,dadi ne yarufe dayawa daga ckn bayin banda muwadda wadda ta tsinci kanta da tsananin bugawar kirji da tsoro dukda cewa tayar darwa zuciyarta tana daga ckn bayin da yakama ace suna sahun farko a wadanda za'a yanta,,ita abinda yasa take kaunar a yantata saboda tasami damar kula da mahaifiyarta yadda yakamata. Gimbiya jalila batayi mgn ba sai baiwar da tayi mgn dazu ce tabasu umarnin yafiya,,said da suka yi gdy sannan suka fita. Suna fita ubaida taja hannun muwadda fuskarta dauke da fara'a tace "muwadda nasan kina ckn bayin da zasu sami yanci yau,,na tayaki murna". Girgiza kai muwadda tayi ckn sanyin jiki tace " Allah yasa ubaidah". Ameen amma nikam nasan ma hadda ke,,saboda kaf gdnnan babu wanda baisanki wajen aiki ba. Shiru muwadda tayi har suka karasa katuwar fadar masarautar inda suka tadda bayi dankam wasu suna farin ciki wasu suna fargaba. Lkc guda wajen yayi tsit tamkar babu wani Abu me rai a wajen sakamakon shigowar *SARKI ALIYU* da ahalinsa. Zubewa sukayi gabadayansu ckn girmamawa suka kwashi gaisu*Y͟'A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k* *Special gift to my besty* *UMAMATU UMAR ADAM* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ *PAGE 2* Bismillahirrahmanirraheem. Sunjima sosai a tsugunne kafin abada umarnin mikewa. Sarki Aliyu da iyalansa suna zaune akan wasu hadaddun kujeru masu tsananin kyawu gefensu bayi nayi musu fiffita sai kuma wasu a bayansu wasu a zaune a gabansu,waziri ne yamike tsaye tareda yin bayani kamar haka: "Sanin kanku ne cewa a kowace shekara a masautar nan ana dibar bayi guda 50 a yanta su,,To ynz ma Allah yakawomu lkcn saboda haka ynz ba bata lkc za'a gabatar dasu,ihu mutane sukasa ckn farin ciki tareda jerowa masarautar kirari,,,tunda waziri yafara mgn kirjin muwadda yake bugawa tanajin ance ynz za'a fara kiran sunan wadanda za'a yanta kafafuwanta yayi mugun sanyi kamar zata zube amma ba dama,don babban laifi ne a masarautar sarki yana zaune ka zauna kaima. Wani bafade ne yamike da zungureriyar takarda a hannunsa yafara kiran sunan wadanda aka yanta,,wajen yayi tsit kowa kirjinsa yana bugu saboda fargaba,,tuni muwadda tagama sarewa ganin an kirawo mutane 46 amma ba sunanta,wasu hawaye ne masu matukar zafin gaske suka shiga tsere a kuncinta,sosai zuciyarta take suya da radadi,bata kara tsinkewa da lamarin ba sai da taga ankira mutum ta 50 ubaidah,ihu suka dauka ckn farin ciki,,tuni wajen yakaure da kide² na farin ciki. Zamewa tayi tafice daga wajen,ko gabanta bata gani dakyau saboda tashin hnkl,,can gefe da fadar tasamu wani dan dandamali ta zauna tareda hada kai da gwuiwa tasaki wani azababben kuka mai cin rai,,Babu abinda yafi damunta sama da kula da mahaifiyarta,inda akwai yanda zatayi jitake dauke mahaifiyarta zatayi su gudu daga Wannan bakar kasar,ynz haka zata kare rayuwarta a bauta??,,kuka take sosai harda sheshsheka tanajin wata muguwar kiyayyar masarautar zinari. Tundaga nesa yarima yusufu yahangota kuma ya ganeta,,da kai yayiwa bayin da ke biye dashi alamar su koma,ba musu suka juya,,tsayawa yayi akanta yanajin yanda take garsheken kuka,runtse idonsa yayi saboda kukan yana taba ransa,zama yayi kusa da ita ckn daddarar muryarsa me sanyi yace *MUWADDAAAT*,,dasauri ta dago tareda ja da baya tana kalle²,,Ajiyar zcy tayi ganin ba kowa a wajen,,ckn sanyin murya me cike da tsoro da rauni tace "Don Allah yarima ka taimakamin ka tahi kar nashiga matsala",,, murmushi yayi ckn tsokana yace " Kinhiya tsoro muwaddatt to sai me don anganmu???ynz dai fadamin me kikewa kuka???,,,,mikewa tayi tsaye idonta har yaciko da kwalla,ckn raunin murya tace "Bakomai", tana kokarin barin wajen,,dasauri yasha gabanta tareda kallonta ido ckn ido yace " Baxan iya yafewa zuciya ta ba indai har naganki ckn damuwa kuma nabakki a cknta,saboda haka ki fadamin abinda akai miki ko kuma kiyi murmushi nagani,,babu yanda ta iya dole tayi murmushin da ke kara mata kyau tana mamakin karamci irin na yarima yusufu bakamar sauran yan gdnba,shima murmushin tareda fadin "ko kefa,ni ynz zamuje kilisa ne ina tunanin kafin badawo kin tahi ne??daga mai kai tayi alamun eh,tanayi tana waige² don Allah Allah take yatafi kar wani yagansu,,sallama yai mata yatafi,Ajiyar zuciya tayi don ita har ga Allah batason yarima yana rabarta don babban tashin hnkl ne a wajenta. Ubaidah ce ta hangota dasauri takaraso wajenta tareda rikota ckn tausayi tace " kiyi hkr kinji muwadda??Allah yasa haka shiyafi alkhairee,,, Hawayen fuskarta ta share ckn rawar murya tace "Ubaida ynz a haka rayuwar iyata zata kare babu cikakken me kula da ita???karki manta ni kadai fa gareka,,Wlh bantaba tsanar wasu mutane ba sama da ba masarauta....dasauri ubaida tarufe mata tareda juyawa tana kalle² da addu'ar Allah yasa ba wanda yagansu,,ckn sanyin murya tace " kidaina irin magannan muwadda,Allah yana sane da iya kuma..... Shiru tayi sakamakon jin sanarwa da akeyi daga ckn masarauta na ana neman kowa da kowa ynz a fada,Ajiyar zuciya muwadda tayi tanajin gabanta na faduwa,Jan hannunta ubaida tayi suka nufi ckn fadar data cika tayi dankam,,Sarki Aliyu yakame akan kujerarsa fuskarsa a hade ynz sabanin dazu da akwai dan annuri,lkc guda jikinsu yayi sanyi kowa yana tsoron abinda yafaru,,waziri ne yamike shima fuskarsa a hade yace ina *KUYANGA MUWADDA??*,,,wani irin masifaffen bugawa kirjin muwadda yayi tamkar zai fado kasa,,karfin hali tayi ta fara tafiya don zuwa gaban fada,,da kallon tausayi ubaida tabita tareda goge hawayen da ta zubo mata na tausayin rayuwar kawar tata kullum cikin matsala,,duk inda muwadda ta gifta sai an bita da kallo har takarasa gaban fada ckn girmamawa ta tsugunna ta sunkuyar da kanta,,wani bafade ne ya taso hannunsa dauke da wata zabgegiyar bulala tanata kyalli,tuni tausayin muwadda yakama daya daga cknsu,,ckn fuskar rashin imani Wannan bafadan yacewa muwadda "Keee baiwa yar gdn matsiyata kinsan mene ne laifinki ????. Ckn dakiya muwadda ta girgiza kai. Wani bafade ne yamike dauke da takarda a hannunsa ya karanta kamar haka:" Kuyanga muwadda ta karya doka ta takwas a gidannan karo na farko,an kamata da laifin tsayuwa da yarima yusufu har tana yimasa murmushi saboda haka zata karbi hukuncinta ynz". Zaro ido mutane sukayi ckn tsananin tausayin muwadda don sunsan babban laifi ne sosai Wannan a masarautar nan. Tunda bafaden nan yafara bayani har yagama muwadda bata dago kanta ba,banda tsananin suya ba abinda zuciyarta takeyi tuni idanunta suka kame babu alamun hawaye,,Wannan bafaden ne yacigaba da bayani "Kuyanga muwadda zata karbi bulala 20 ynz take,sannan zatayi zaman kurkuku na mako daya. Sai a lkcn hawaye ya zubowa muwadda saboda tsananin tashin hankalin wane ne zai kula da iyarta???,Dayan bafaden nan me dauke da bulala ne yashiga laftar muwadda babu tausayi sai da yaimata bulala 20 cifff amma ko motsawa batayi ba,, haka akasa wasu bayi mata sukajata a kasa suka nufi kurkuku da ita,,babban daki ne me tsananin duhu ga tarin sauraye da cinnakai,,suna tafiya muwadda tasaki wani gigitaccen kuka tareda zubewa a kasa tana birgima tareda fadin " Nashiga uku!!ya Allah ja kawomin agaji,,iyata bata iya mikewa komai ni nake mata,,wane zai samo mata abinci??wane zai kaita bayi??wazai debe mata kewa??Ya Allah ka taimakamin ka taimaki iyata,kabata juriyar rashina na kwanakin da zanyi a wajen nan,,,haka tadinga kuka tamkar ranta zai fita babu abinda yake kara tasar mata da hankali sama da yanda rayuwar mahaifiyarta zata kasance babu ita. *************** Tafiya take ckn sassarfa har takaraso kofar shiga part din,da hannu taiwa bayinta alamun su tsaya,kai tsaye tashiga ckn parlourn,wata dattijuwar mata ce fara me matsakaicin kyau zaune akan wata hadaddiyar kujera tanashan fruit din da ke gabanta,kana kallonta kasan tana tsananin ji da mulki da isa,ita kanta matar da tashigo ynz saida ta russuna mata dukda cewa kana kallon shigarta kasan itama jinin sarauta ce,matar ce tayiwa bayin umarnin fita,zama tayi kusa da dayar matar race "Me babban daki akwai babban labari fa". Ajiye tufar hannunta tayi tareda facing matar tace " Fadamin labarin me??". Nan da kwana 8 *YARIMA SAMEER* zai dawo kasar nan. Tuni fuskar matar nan ta fadada da murmushi sosai wanda kana kallonshi zaka tabbatar na tsantsar mugunta ne.wa.*Y͟A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k &HUSSAIN 80k* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________ *PAGE 3* Bismillahirrahmanirraheem. Gyada kai me babban daki tashigayi still fuskarta shimfide da murmushi,maimakon tayi mgn saita janyo wayarta tadanna wata numb tareda karawa a kunnenta,,harta tsinke ba'ai picking ba,ajiye wayar tayi tareda kallon dayar matar tace "Fulani tabbas kinzomin da babban labari mai dadi,saboda yarima sameer yadawo a lkcn da nake bukata ,tabbas bazan taba bari ya....ringing din wayarta ne yakatseta daga abinda take fada,,Picking tayi ckn murmushi tace " Da na na kaina,maman taka ma sai kayi mata Jan aji???". Yarima sameer dake zaune a wani hadadden parlour kan kujera three sitter ya mike kyawawan fararen kafafunsa jin abinda maman tafada yasa ckn shagwaba yace "wane ni nayi wa mama na jan aji,ban kusa da wayar ne fa". Tabe baki me babban daki tayi ckn tsananin tsanar yarima sameer,dannewa tayi ckn kissa tace " Ai ni fushi nake ma da kai yarona,ynz ace xaka dawo amma baxaka sanarmin ba". Murmushi yayi tareda fadin "Afwan mama na,aimin hakuri,mai martaba kawai ma nafadawa amma ko princess bata saniba. Ckn jin haushi tace " Ohhhh kana nufin princess taka ta fini ko??". Dasauri yace "No mamana ai matsayinki da nata daban,amma dukanku mutane ne masu matukar daraja da matsayi tareda kima a ido na,mama u are my mother nd jalila is my beloved wife,so kinga dukanku ai kunada matukar muhimmanci gareni ko??. Hakane amma yakamata kasanarmin ai. Rintse ido yayi tareda fadin " Sorry mama na zan kiyaye". Yawwa ko kaifa da na,anjima zan kiraka ynz inada baki ne,ka kula da kanka kaji??. Ckn jin dadin yanda me babban daki ke kula dashi yace "Tnx mama na takaina. Katse wayar tayi tareda fadin " Sakaran banza,xakasan koni wace,sai na tarwatsa rayuwarka". Ckn karin munafurci da zuga fulani tace "Wlh me babban daki gara kiyi gaggawar aiwatar da nufinki idan ba haka ba kinaji kina gani yaronnan zai hau mulki ya juya kasar nan sannan yasauka dansa yahau,naki yayan ko oho. Dariya me babban daki tayi sannan tace " Amma dai kema fulani kamar sakarya haka kike,anfada miki da haka na zauna ne???surutunki ne yasa bana sanar da ke komai idan nayi amma tsawon shekarunnan ni nahana yarima sameer haihuwa,kuma wallahi bazan taba bari ba indai ina numfashi haka gantalallen yaron nan zai kare rayuwarsa babu da,,ke ko mufeedah da take sonshi inason ya aureta amma ko ita bazan taba bari ta haihu ba da yarima. Zaro ido fulani tayi ckn mamaki tace "Mufeeda yar yayarki fa???". Murmushi me babban daki tayi tareda fadin " Mufeeda ko yar wace kuwa,nifa kisani banida burin daya wuce naga yarima yusufu akan karagar mulki kuma tabbas indai ina nimfashi sai na cika burina. Shine yadace me babban daki don tabbas indai yarima sameer yahau mulkinnan mu kammu munzama abin tausayi. Bude baki tayi da niyyar mgn yarima yusufu yashigo a fusace,ckn bacin rai yace "Haba mama! Haba mama!!Wlh Sam Wannan ba adalci bane ko kadan,,,Mikewa me babban daki tayi tareda karasawa wajen yarima yusufu ta dafa kafadarshi ckn mamaki tace " me kuma yafaru shalele??",,janye hannunta yayi daga kafadarshi yace "Haba mama akanme za'a saka kuyanga muwadda a kurkuku saboda kawai tayimin murmushi,indai adalci za'ayi kamata yayi ace hadda ni za'a kulle saboda nima nayi murmushin,wlh Sam ba adalci ba n.....Tassssss me babban daki ta daukeshi da mari,ckn takaicin halin dannata tace " yarima mai martaba ne baiyi adalci ba kenan???Tabbas bantaba ganin shashashan yarima kamarka ba,kai ko kishin yarima sameer bakayi kayi koyi dashi??yarima sameer a tsawon rayuwata dashi zan iya lissafa maka dariyarsa,kana kallonshi kaga yaro me tsantsar ji da mulki ba kamarka ba sakarai ,shi ko kallon bayi yanayi ne balle yashiga harkarsu???Amma kai akan kaskantarciyar baiwa irin kuyanga muwadda kake tada jijiyoyin wuya saboda bakasan ciwon kanka ba,,to idan barci kake ka farka ka tuna wane ne kai ". Murmushin takaici yayi tareda fadin " Ko zakisaka kaina gabas ki yanka mama baxan fasa fada ba me martaba bai yanke hukunci ckn adalci ba saboda bai hada da niba,kuma mgnr yarima sameer Wannan rayuwarsa daban tawa daban,saboda haka nima a yanzu zanje na rufe kaina a kuskuku har zuwa lkcn da mai martaba ya dibawa muwadda,,yakarasa yana kokarin fita,,A fusace me babban daki ta fuzgoshi idonta har yasauya saboda bacin rai,,ckn masifa da takaici tace "Yarima yusufu kana ckn hayyacinka kuwa???,,kasani Wannan shine mafi girman kaskanci da zakayiwa kanka a masarautar nan, wace ce kuyanga muwadda da zaka damu saboda an rufeta,to inaso kasani indai ka aikata abinda kafada wlh saina wulakanta kuyanga muwadda a garinnan,sai na maidata abin kyama a wajen kowa idan kayi musu jeka ka aikata. Murmushin takaici yayi tareda matsowa daf da ita yace " Narantse da Allah mama abinnan da kika lissafo indai ya tabbata akan kuyanga muwadda to tabbas zai tabbata akan danki yusufu,don zan koma kaskantacce mara yanci ko kadan,,A fusace ta fuzgosa ckn matsanancin Bacin rai tace "Me kake nufi???. Babu abinda nake nufi face abinda nafada ynz,yana gama fadin haka yafice daga dakin a fusace. Sharaf ta zube akan kujera ckn matsanancin bacin rai,kallonta takai kan fulani wadda tasaki baki da hanci tana kallon ikon Allah,ckn bacin rai me babban daki tace " Tabbas fulani yazama dole nadauki tsatstsauran mataki mafi muni akan kuyanga muwadda". Girgiza kai fulani tayi tareda fadin "Karkiyi haka me babban daki, wlh abinda yarima yusufi yafada har zuciyarshi ne,saboda haka ko wani Abu zaki aikata kibari daga baya amma ba ynz ba,,shawarar da zanbaki ynz kije gurin me martaba ki rokeshi a fito da kuyanga muwadda ko dan rayuwar danki. Ajiyar zuciya me babban daki tayi tace " Anya kuwa fulani me martaba zai fito da kuyanga muwadda???kinsan halinsa idan ya yanke hukunci kaifi daya ne. Hakane amma kije ynz ki jarraba. Mikewa tayi ckn sanyin jiki tace "To bari naje,,Tana gab da fita sukayi karo da mufeedah zata shigo,,ckn iyayi mufeeda tace " Yawwa mama gurinki fa nazo,Wai yaushe yarima na zai dawo ne??Wlh na kagu yadawo kimasa mgn ta. Ckn kosawa da mgnr mufeeda tace "Nan da kwana takwas",,,Wani mugun tsalle mufeeda tayi ckn matsanancin farin ciki tayi hugging me babban daki tareda fadin " Wayyo dadi yarima na zai dawo". Ckn takaici me babban daki ta yakiceta daga jikinta tafita don abinda ke damunta ma ya isheta. Mufeeda ko kulawa batayi ba ckn murna tadinga kissima gata a faffadan kirjin yarima anyi aurensu suna soyewa,A fili tace "Gimbiya jalila kinkusa wulakanta". Yarima yusufu yana fita kurkuku ya nufa ,yana zuwa yacewa ma'aikatan wajen su bude yashiga su rufeshi,ckn mamaki da tsoron abinda zai biyo baya sukace " Ranka ya dade a rufeka fa kace??". A fusace yace "Ehh ko bazaku bude bane??. Russuna sukai tareda cewa " Allah ya huci ran yarima ai mana aikin gafara",,daya daga cknsu ne yadauko mukulli ya bude katuwar kofar kurkukun,,cire alkyabba yarima yusufu yayi yabasu sannan yashiga wajen". Sudai gabadaya a tsorace suke,don tashin hankali ne aga yarima a kurkuku, amma ba yanda suka iya tunda umarnin yariman ne. Saboda tsabar kuka idanun muwadda har sun kankance sosai,gawani yaji da suke mata,sun kunbura sunyi suntum tareda matsanancin ja,hakama fuskarta gabadaya tayi jajir musamman kan hancinta,tunanin mahaifiyarta kawai takeyi musamman da lokacin tafiyarta gida yayi,tasan ynz iyarta nasan tana jiran sallamarta,kuma ta tabbata bataci komai ba,,kukan zuciya takeyi sosai don na filin ma yadaina fitowa ynz. Ubaida ce ta lallabo tazo wajen me gadin kurkukun da muwadda take,tsoho ne mutumin sosai,ckn girmamawa ta gaisheshi tareda fadin "Don Allah baba kaimin taimako naga kuyanga muwadda ko na dakika 5 ne. Zaro ido tsohon yayi ckn mamaki yace " Ki turamin asiri yarinya,idan ba so kike nima a rufeni ba". Ajiyar zuciya ubaida tayi don tasan Gaskiya tsohon yafada,ckn sanyin murya tace "To dan girman Allah baba kaimin wani taimako zanbaka takadda ka kaimata",,Shiru yayi nawani dan lkc kafin yace " to yisauro ki kawo",,ckn farin ciki ta ruga da gudu tabar wajen ,bata jimaba sai gata tadawo, takardar tabashi tareda yimasa gdy sosai sannan ta tafi ckn tausayin aminiyarta da mahaifiyarta. Muwadda na zaune ta hada kai da gwuiwa tana kukan zuci,cinnakai sai buga mata cizo sukeyi amma bata kulaba don basu ne a gabanta ba,,har tsohon yabude kofar batasaniba,,tsayawa yayi akanta ckn tausayi yace "kuyanga muwadda",, dasauri tadago rinannun idanunta ta kalleshi,,takaddar yamika mata tareda fadin " inji kawarki tace abaki",,karba tayi shikuma yafita tareda datsawa kofar katon mukullinta,,bude takaddar tayi don ganin abinda ke ciki,,dan guntun rubutu ne kamar haka: *" Kiyi hakuri kawata Allah yana sane da ke kuma zai saka miki ,watarana sai labari,don Allah ki nutsu ki kwantar da hankalinki kibar kuka,nayi miki alkawarin daga yau har zuwa ranar da zaki fito zan dinga kwana a gdnku wajen iya, zan kula da iya fiye da tunaninki saboda haka ki kwantar da hankalinki don Allah!!*",,kuka ne ya kubce mata data gama karantawa,ckn kuka tace "Tabbas kinwuce kawa ubaida kinxama yar uwa,,Allah nagode maka daka kawomin dauki,sosai taki sanyi a ranta don dama mafi yawan damuwarta akan kula da iya ne. Me babban daki tana zuwa kofar shiga dakin me martaba bayin da ke biye da ita suka tsaya a kofa,tana shiga ta taddashi da amarya,haushi taji sosai amma ba yanda ta iya haka ta karasa ciki,taso dai ace shi kadai tasam*Y͟A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ Dz book completely goes to *HASSAN 90k& HUSSEIN 80k* *Special gift to my besty* *UMAMATU UMAR ADAM* *PAGE 4* Sallama amarya taiwa me martaba ta fita bayan sun gaisa da me babban daki,, sbd tasan idan daya daga cknsu tazo wajen me martaba kuma ba ranar girkinta ba mgn zasuyi . Zama tayi kusa da me martaba tareda fadin "Barka da hutawa ranka ya dade". Amsawa yayi da kai saboda Apple dake bakinsa,,ckn kissa tace " Me martaba Ashe dana yakusan dawowa amma ba labari nafara shirin tarbarsa???,,,murmushi yayi sosai da yakular da me babban daki kamar ta makeshi saboda takaici,,ckn annashuwa yace "Auuu dannaki bai fada miki ba??? ai kunfi kusa ke da shi tunda gashi ma harya fada miki yanzu,,haushi ne yakara kamata ganin da tayi dagayin zancen yarima sameer me martaba sai wani washe baki yakeyi,,basarwa tayi tace " Me martaba nazo neman wata alfarma ne a wajenka",,juyowa yayi ya fuskanceta sosai tareda fadin "Inajinki",, Ajiyar zcy tayi tace ", Don Allah me martaba ina neman Alfarmar a fito da kuyanga muwadda daga kurkuku saboda..... Keeeee halima kinsan Abinda kike fada kuwa????,,Me martaba ya fada a tsawace sai da gabanta ya fadi,,,lkc guda annurin fuskarsa ya gushe,ckn fushi yaci gaba" Anya kuwa ba shaye² kika faraba halima???Don nasan bazaki manta wane ni ba da kuma dokata a kasarnan,,narantse miki da Allah babu wani mahaluki da zaiyi laifi nayanke hukunci akansa wani dalili yasa nafito dashi karyane!!! Ai Wannan tozarci ne da wulakanci ace sarki kamata yayi magana biyu,,saboda haka indai kinsan Wannan banzar maganar ne ya kawoshi fitarmin daga daki!!!! Yakarasa tareda nuna mata kofa a fusace,,,Kuka tafarayi ckn kissa da makirci tace "Haba me martaba,,yarima yusufa yanacan fa kurkuku yasa an kulleshi saboda ita ,a cewarshi wai ai tare sukai laifin kuma yace bazai taba fitowa ba har sai kwanakin da aka dibar mata yayi,,Haba me martaba ka dubafa kamar yarima yusufu danka ya kwana a kurkuku ai.......To saime????badai shi yazaba ba???To bari kiji wlh ko shekara na dibarwa kuyanga muwadda yace shima zaiyi babu dalilin da zaisa na fito da ita saboda shi,,ke waima natambayeki mene ne hadin ta dashi???? Ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa har abada. Ni bansan wata alaka da ke tsakanin su ba,,kuma ma mene zai hadasu kuwa???Tausayi kawai tabashi,,ynz me martaba haka zai zauna a kurkuku cinnakai da komai na cutarwa a ciki??? Daga kafada me martaba yayi yace " Shi yaso hakan ai,,kinga ni zanshiga daga ciki,,yakarasa da mikewa yabar parlourn,, kwafa tayi ckn bacin rai tana fadin ",Inda wancen shegen ne me girman kai ai da zaka fito da ita saboda shi,,kai tsaye kurkuku ta nufa fuskar nan a hade kuyanginta na biye da ita. Tana zuwa masu gadin wajen suka zube suna kwasar gaisuwa,batareda ta amsa ba takalli babban cknsu cikin raini da nuna isa da gadara tace " Budemin kofa",,mikewa yayi jiki na rawa ya budemata,,dagawa kuyanginta hannu tayi alamun su dakata ita kuma ta shige,,,a xaune ta sameshi yanacin abincin da ake bawa yan prison din,,dasauri ta karasa hankali a tashe ta dauke kwanon abincin ckn tsananin bacin rai da jin haushi tace "Meye haka wai kakeyi yusufu????Ko ka haukace ne???Wane dan iskanne yakawo maka Wannan wulakantaccen abincin kaci??Kawar da kanshi yayi batareda yace mata komaiba,,haushi ne yakara kamata a tsawace tace " Baka jina ne zakamin banza ina maka mgn???",,Dakyar yabude baki yace "To mama me kikeso nace miki???,,Tambayar ka nayi wane dan iskanne yakawo maka Wannan wulakantaccen abincin????,,Murmushi yayi yace " Mama wulakantacce fa kikace???Karki manta abincin da mutane sukeci ne fa kuma ai nima mutum ne kamar su sannan....Dalla rufemin baki sakarai kawai!!!Wai ni anya kuwa ba sauyo min kai akaiba da na haifeka,,yaro kwata² kamar ba jinin sarauta ba,, to wlh kafin na sabamaka ka taso mutafi daga wajennnan akan wata banza mara gata,,ckn kosawa da mgnr ta yace mamaaaa haba Don Allah wai yaza'ai muyita mgn daya???Nace miki babu inda zanje sai satin ya cika Don Allah kiyi hkr ki banni,,,Ckn takaici take kallonshi tamkar ta makeshi sbd takaici,,rasa abinyi tayi kawai sai tayi kwafa tafice a fusace,,binta yayi da kallo a fili yace "Kiyi hkr mama wlh zan iya komai akan muwadda!!! *{Tofaaa}* Ita kuwa tana fitowa ta kalli ma'aikatan gdn a tsawace tace " Uban waye a cknku yakaiwa yarima wancen dan iskan abincin????,,,Ckn tsoro babban su yace "Wlh ranki ya dade da kanshi yaje dakin girki ya ebo,,wani mugun takaici ne yasake rufeta ganin danta na cknta yarima da Wannan aikin tozarcin,,,A fusace tabar wajen tamkar zata tashi sama. Iya na zaune ta zubawa kofa ido tana jiran sallamar tilon yarta amma shiru gashi har lkcn dawowarta yawuce kuma tasan muwadda batada tsaye² ko ina burinta tazo gd,,,sallamar ubaida ce ta dawo da ita daga duniyar tunaninta,,gabanta ne yafadi sosai,, dasauri tace " Don Allah ubaida kar kicemin wani Abu Mara dadi yasamu muwadda na bazan juraba wlh",,,Hadiye miyau ubaida tayi ckn tsananin tausayinsu,,kakalo murmushi tayi tace "Kayyyy iyarmu babu komai fa,,zama tayi gefen iya tana fadin muwadda tana lpy gimbiya jalila ce tasata wani dan aiki amma anjima zata dawo,,mikewa tayi tace " Iya nasan yanzu kina bukatar ki kewaya bari na taimaka miki,,ba musu iya tamike ta dafa ubaida takaita bayi,,,rufe ido tayi ta gama abinda zata yi sannan takamota suka dawo daki,,,kwanan da ke gefenta tadauko tace "Iyaa ga abinci kici natawo miki dashi daga gd,,budewa tayi taga shinkafa da miya hadda nama,,murmushi tayi tace " Bakya gajiya da dawainiya ubaida,sannu Allah yai miki albarka,,amma abincin sai muwadda tadawo zamuci,,dasauri ubaida tace "A'a iya ai shiyasa ma ta turoni saboda tace hankalinta bazai taba kwanciya ba tabarki ckn yunwa kici kawai ki rage mata,,shiru iya tayi kamar me tunanin wani Abu,zuwacan kuma sai tafaraci,,ruwa ubaida ta ebo mata tasha sannan ta shimfida mata dadduma ta rada sallar magriba a zaune Don lkcnta yayi kuma dama tadauro alwala. Bayan iya tagama azhkar ta juyo ta kalli ubaida data idar da tata sallar ynz,,ckn damuwa tace " Anya kuwa ubaida bakina boyemin wani Abu bane??? Muwadda fa bata taba kaiwa hakaba,, dn Allah ki fadamin idan wani Abu ne yafaru, takarashe kamar zatayi kuka,,,riko hannunta ubaida tayi ckn taushin murya da lallashi tace "Wlh dgsk nake miki muwadda tana lpy sai dai tana kurkuku,,ckn matsanancin tashin hnkl iya taja da baya tareda dafa kirji murya n rawa tace kurkuku!!!!!!u.*'Y͟A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSEIN 80k* ```Special gift to my besty ``` *UMAMATU UMAR ADAM* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ *PAGE 5* Duk yanda ubaida taso ganin iya ta kwantar da hankalinta abin ya faskara,,don rudewa iya tayi sosai tadinga kuka tana surutai tuni wani zazzafan zazzabi ya rufeta jikinta yahau rawa,,da gudu ubaida taje gida tadauko wani maganin zazzabi tabata,bata jimaba bacci ya dauke ta. Tagumi ubaida yazuba ckn tsananin tausayin rayuwarsu muwadda,a fili ta furta Allah ya kawo karshen Wannan kuncin rayuwar taku. Iya fa tariki ce sosai baji ba gani,,babu yanda ubaida bataiba amma inaaa ko abinci iya taki ci sai aikin kuka da kiran muwadda na,,dole ta kyaleta,sai da akayi kwana biyu taga yunwa tana Neman hallakata sannan taci shima kuma kadan. A bangaren muwadda ma zancen daya ne,,ta rame sosai saboda tunanin mahaifiyarta da rashin sanin halin da take ciki,, tasan dole iya zata shiga mummunan yanayi,,taci kuka tamkar ranta xai fita,,bacci kam sai dai barawo,,sosai kiyayyar masarautar zinsari ta karu a ranta. Babu yanda me babban daki bataiba akan taga yarima yusufu yafito daga kurkuku amma kekam yaki,,dole ta kyaleshi tana aiko masa da abinci amma shima yaki ci,,sosai take takaicin halin yarima yusufu,,a cewarta bata taba ganin shashashan yarima kamar sa ba. Yau satin muwadda daya a kurkuku kuma yau ne za'a fitar da ita daga kurkuku,,hakanan kuma yau ne ake shirye shiryen dawowar yarima sameer daga south Africa gobe,,,a Daren ranar duk satar bacci haka yaga muwadda ya kyale har garin Allah ya waye. Tana zaune ta hada kai da gwuiwa tana sana'ar tata taji an bude kofar,,dasauri tadago kanta taga wani bafade yana bude kofar kurkukun,,mikewa tayi tamkar wadda aka tsikara tayo wajen kofa,,ckn tausayawa yace mata jeki an sallameki gobe sai a kiyaye,,ko karasa jin abin da yake fada bataiba tafice da gudu burinta kawai taganta a gida ko ganin gabanta batayi da kyau bata Ankara ba taji tayi karo da mutum,,dagowa tayi idonta yasauka akan gimbiya jalila,,dasauri muwadda ta zube jiki na rawa tafara bawa gimbiya jalila hakuri,,wata kuyanga ce tadaga hannu zata zabgawa muwadda mari gimbiya jalila ta daga mata hannu,,kallon wulakanci da kaskanci take jifan muwadda dashi,,kamar wadda akaiwa dole tace "Tashi ki wuce",,, ba muwadda kadaiba hatta sauran kuyangin sai da suka cika da matsanancin mamaki,,godiya muwadda tadingayi har saida gimbiya jalila tawuce sannan taci gaba da gudunta tafice daga masarautar. Gimbiya jalila kuwa abinda yasa ta kyale muwadda saboda tana farin cikin Prince din ta zai dawo gobe shiyasa zuciyarta take kyall. Kamar kullum yau ma ubaida na zaune tana lallashin iya sai ga muwadda tafado gdn da wani matsanancin gudu kamar wacce aka jefota kai tsaye ta nufi iya ta rungumeta tareda sakin wani irin matsanancin kuka,,itama iya tuni ta fashe da kuka,ido ubaida tasa musu ckn tausayi bata hanasu ba tasan ko tabasu hakuri a banza,,sai da sukayi mai isarsu sannan muwadda tazame jikinta tareda kallon iya ckn bakin ciki tace " Iyata kiyi hakuri don Allah da kuskuren da na aikata aka rufe ni,duk kokarina na ganin na kaurace masa sai da abinda nake tsoro yafaru,,iyata kalli fa yanda kika rame ai da bakisa damuwa a ranki ba tunda zan fito. Murmushin takaici iya tayi tareda girgiza kai tace "Muwadda na kenan,, taya kike tunanin hankali na zai kwanta???Kalli fa yanda kikai wata iriyar rama sai haske kema. Hawayen da ya zubo mata tashare tareda fadin " wlh iya ta bazan daina fada ba natsani masarautar zinari,,bantaba ganin azzalumai masu son kansu kamar su ba,,dasauri ubaida tace "muwadda tun ranar da aka rufeki fa yarima yusufu ma yarufe kansa yace ai tare kukai laifin,babu yanda me babban daki batai dashi ba yafito yaki hala ma yafito ynz bansaniba. Mamaki sosai muwadda da iya sukayi,,tabe baki muwadda tayi tareda mikewa tana fadin " Wannan kuma bangaren su ne bai shafe ni ba,,fita tayi daga dakin tanufi bandaki,,a ranta tana kara girmama matsayin ubaida a gunta don daga gani tana kula da mahaifiyarta tunda ko ynz da taxo akwai abinci me kyau a gaban iya duk da bata ci ba,,sai bayan maghriba sannan muwadda taraka ubaida hanya ta tafi gida bayan inna tagama shimata albarka,,ko a hanya haka muwadda tadinga yiwa ubaida godiya har saida tace "Idan kika cigaba damin godiya zanga kamar baki dauke ni yar iya ba nima" Sannan muwadda ta baryimata gdy. Yau gabadaya masarautar zinari ta kacame da hidimar tarbar yarima yusufu,,zuwa ynz labari yabaza ko ina a garin,,mutanen gidan farin ciki tamkar bakinsu zai yage,yayinda wasu dayawa suke yake. Su muwadda suna bangaren girki don ita dama aikinta kenan a bangaren gimbiya jalila kuma,, girkuna akayi sosai kala kala,,suna ckn yi saiga me babban daki,, zubewa sukayi sukahau gaisheta tana wani yamutsa fuska kamar taga kashi,,ckn gadara tace "idan wani tsautsayi yasa kukai kuskure a girkin dana wlh saina baku mamaki saboda haka ruwanku ne ku kula,,karasawa tayi tana bude kulolin abincin tana gani,,fakar idonsu tayi ta shammace su ta zuba magani a miyar tumatir din da akai masa don tasan yana sonta sosai kuma sai yaci,,daukar kular miyar tayi tana jijjigawa tareda fadin " Kun tabbata miyar nan dai tayi ko??" Dasauri suka amsa mata da eh ranki ya Dade,Ajiye kular miyar tayi tana wani irin murmushin mugunta da samun nasarar babu wanda yaganta a cknsu gashi tayi abinta ckn kankanin lokaci,a ranta tace "Zakasan bakada wayau yarima sameer,,ficewa tayi daga kitchen din bayinta dake kofar ckn din suma suka bita. Gimbiya jalila taci kwalliya sosai tamkar wadda zataje gasar kyau,,wani murmushi ne na musamman kwance a fuskarta,,kai tsaye fitowa tayi daga part dinta don zasuje tarbo yarima sameer ynz, kuyanginta na biye da ita,a fada suka hadu da me babban daki da yarima yusufu da gimbiya jidda da gimbiya farida tareda mufeeda daketa rawar kai tana zumudi,,fitowa sukayi aka bude musu motoci suka nufi airport tareda masu rakiyarsu anata busa algaitu da sarewa. Shi kanshi me martaba farin cikin sa yagaza boyuwa,hakama amarya(mahaifiyar sameer),,sosai me babban daki take jin haushi kamar ta shake su saboda takaici. Basu jima da zuwa ba jirginsu yarima sameer ya sauka,,baza ido gimbiya jalila tayi tana hangen Prince dinta,,can ta hangoshi yana takawa cike da tsantsar takama da nuna iko tareda ji da kai,, kyakykkyawa ne na gaban kwatance,fari tass me hade da rantsatstsen hutu da jin dadi,,duk karshen ji da kai na mace taga yarima sameer sai tayi sha'awar ace nata ne,kallo daya zakai masa ka fahimci yana da tsananin Jan aji,,yana sanye da kayan gidan sarauta da alkyabba wanda sukai masifar yimasa kyau,,bayansa da gefensa da gabansa duk bayi ne,sosai airport din takaure da busa,kowa yasan da dawowar yarima sameer yau,,masu saukowa daga jirgin Kansu sarewa sukeyi suna bashi hanya ckn girmamawa,,da gimbiya jalila idonsa yafara karo,ta kafeshi da idobckn matsananciyar kaunarshi kamar ta cinyeshi saboda axababben so,,murmushin shi me tsada yasakar mata ckn kaunarta sannan yakai dubansa ga me babban daki yasakar mata murmushi, a lkcn yakarasa saukowa,tuni bayi suka zube suna gaisuwa hadda wadanda ma ba nayi ba amma ko arzirin kallo basu samu ba,, da dan gudu gudu gimbiya jalila ta karaso ta rungume yarima sameer ckn tsananin farin ciki,,fuskarsa dauke da murmushi ya shafi gashin kanta sannan ya dagota yacireta daga kirjinsa yayi hugging din me babban daki daketa faman zabga yake amma kasan ranta jitake tamkar ta shake yarima sameer ya mutu ta huta,amma saita dake ta nuna masa farin cikin ta sosai,,gimbiya farida da gimbiya Jidda ne suka gaishe shi ba yabo ba fallasa ya amsa,,ckn tsananin iyayi mufeeda tace "Barka da dawowa ranka ya dade",Ai ko arzikin kallo mufeeda bata samu ba a wajen yarima, sai ma janyo gimbiya jalila dayayi jikinsa yacewa me babban daki " Mutafi gida mama",,Sosai mufeeda ta shaka don a gaban bayi yai mata haka,, kwafa tayi a ranta tace "Wlh sai ka raina kanka yarima ,ni da kai muzuba mugani. Haka suka dunguma gabadayansu suka nufi gida.*'Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k &HUSSAIN 80k* *Special gift to my besty* *UMAMATU UMAR ADAM* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ *PAGE 6* Sosai masarautar zinari da kaure da kid'e² da bushe ²,,gabadaya bayin masarautar an tarasu waje daya ana jiran dawowar yarima sameer,,daga bakin kofar shigowa masarautar wani bafade ya kwala kira da fadin "ga su yarima nan sun iso",, Sosai kidan ya tsananta yayinda masu zirga² suka tsaya da ayyukansu,hanyace sambal wadda zata sadaka da fada,duk iya kallonka bazaka taba ganin tsinke a kasa ba saboda tsananin sharuwar da wajen yayi babu komai akan hanyar,,yayinda mutane suke gefe da gefe,,wasu bayi ne guda goma murtuka² majiya karfin gaske suka wangale tankamemiyar kofar masarautar,,sautin kidinne yasauya yakoma mai sanyin sauraro sakamakon shigowar motocin su yarima sameer, kuma sanin kowa ne baya kaunar hayaniya,,da gudu wasu bayi guda uku suka tawo hannunsu rike da zungureren carpet me tsayin gaske da kyawu suka shimfida bayan motocin sun tsaya,,ckn nutsuwa da girmamawa babban bafadan masarautar yazo yabudewa yarima sameer mota,,lkc guda masarautar tayi tsiit tamkar babu wani Abu guda daya me rai a ckn ta,,kowa yayi kasa da kansa yana jiran fitowar yarima me jiran gado,,ckn takunsa me tafe da jin kai da nuna isa yafito daga motar zuwa ynz fuskarsa a rufe take ,kyawawan idanunsa sanye da glass,,zubewa sukayi gabadayansu ckn nuna tsantsar girmamawa suka hada baki wajen fadin "Barka da dawowa yarima dan sarki jikin sarki me jiran gado,masarautar zinari takace hakanan muma naka ne,takawarka lpy yarima me kyawun zuciya,, haka suka shiga jero masa kirari suna wasashi,waziri ne yakaraso fuska dauke da farin ciki yatarbi yarima sameer, fuska ba yabo ba fassala ya gaishe shi tare da tambayar yasamesu lpy??ckn girmamawa waxiri yace lpy klau dana, ina fatan kadawo kaima lpy,gyada kai yayi batareda ya amsa ba,,waxiri bai damu ba don sosai ma yayi mamaki da yarima ya tambayeshi yasamesu lpy,,,jakadiya ce ta tawo hannunta dauke da wata kwarya wadda aka kawata da zanen gidan sarauta a jikinta, da kyawawan furanni masu kamshi a ciki tashiga watsawa gurin da yarima zai taka,,ckn isa yake takawa taku na zaratan maza masu tsananin ji da kansu,wajen kuwa tamkar anyi barin turare,,gefensa na dama gimbiya jalila ce yayin da gefensa na hagu kuma me babban daki wadda da za'a bincika zuciyarta a halin yanzu yanda takeji to da tabbas idan tasamu wuka zata iya lumawa yarima sameer,bayansa kuma waziri da manyan kasar,kai tsaye ckn fada suka nufa inda me martaba da amarya tareda fulani suke. Ckn matsanancin farin ciki me martaba yataso yayi hugging yarima sameer,,shima yarima ckn kauna yayi hugging mahaifinsa,,a hankali kuma ya zame jikinsa ckn girmamawa ya tsugunna yace "Ina wuni Abbu na nasameku lpy??,,Murmushi me martaba yayi yakamo hannun yarima sameer yamikar dashi tsaye kai tsaye suka nufi kan kayataccun kujerun sarauta,,nan suka sake gaisawa ckn nuna kula da tsananin kaunar juna,su gimbiya jalilsada me babban daki tuni sunyiwa Kansu masauki yayinda su gimbiya farida da mufeeda suka nufi ckn gida,su waziri ma sunyi nasu wajen don basu damar ganawa,,ckn gimamawa yarima yagaida fulani, fuska ba yabo ba fallasa ta amsa,Sam hakan bai dameshi ba,,kallonsa yakai kan mahaifiyarsa amarya wadda farin cikin dawowar dannata yagaza boyuwa a fuskarta duk da tanata kokarin son boye hakan,ckn tsokana yace " Ummi na fatan nasameki lpy??,,Kawar da kanta tayi kamar bataji shi ba,,murmushi yayi sosai yana jin kaunar mahaifiyarshi sosai a ranshi,,tasowa yayi yazo kusa da ita ya tsugguna tare da dora hannunsa akan kafarta,,cire rawanin fuskarsa yayi kyakykyawar fuskarsa ta bayyana,langabe kansa yayi ckn shagwaba yace "Ummi na wai bakiyi kewata ba???",, ckn kunya ta ture hannunsa daga cinyarta tace " Ehhh banyi kewar taka ba ai ni ba uwarka bace ga iyayenka can sunyi kewarka,,murmushin gefen baki yayi wanda ya sake fito da ainahin zallan kyawunsa,,mikewa yayi yana fadin "To shikenan aikam uwata tanaji da ni kwarai,,yafada idonsa akan me babban daki wadda ke ta zuba yake,dariya me martaba yayi ckn nishadi yace " yarima me ruwa biyu kayi fara'a ynz anjima ka Murza kanbun mulki kamar bakasan dariya ba,,dariya sukai dukansu banda yarima da yadan murmusa kadan,zama yayi kusa da me babban daki yace " Mamana ina kanina ne yarima yusufu??",,Eyya ai bayajin dadi ne yana bangaren sa zazzabi yatashi dashi bakaga yanda yaketa zumudin dawowarka ba,,ckn rashin jin dadi yace "Bari naje na duboshi",, Dasauri me martaba yace " me martaba kabari kaje kayi wanka kaci abinci sai kaje ko??",,Amsawa yayi da to don baya taba ketare maganar mahaifin shi haka kuma yana tsananin bin dokar masarautar su da girmamata komai kankantar ta,me babban daki haushi kamar ta fashe don tana gani me martaba a zahiri yake nuna yafison yarima sameer akan yarima yusufu,sallama su yarima sukai musu suka nufi bangarensu. Sai da suka shiga ckn fada sannan bayin suka dago daga tsugunnen da sukayi,,kowa yashiga aikin gabansa,Ajiyar zuciya muwadda tayi a ranta tace " Ya Allah kana gani kuma kasan me yake faruwa,,ya ubangiji kashiga tsakani na da wadannan azzaluman mutanen,,tabota din da ubaida tayi ne yasata juyowa ckn sanyin jiki tace "magana kikeyi??",, Jan hannunta ubaida tayi sukabar wajen,,can nesa a ckn masarautar suka samu dan tsauni suka zauna,,ckn lallashi ubaida tace " Muwadda don Allah kidaina sakawa ranki damuwa,nasan me kike tunani amma inason kidaure kici gaba da addu'a watarana sai lbr,ynz saboda ke fa nake zuwa,,share hawaye muwadda tayi tace "Ni ubaida abinda yake damuwa shine bana kaunar cigaba da kula da bangaren abincin gimbiya jalila saboda daga ita har yarima sameer sunfi tsanata a gidannan fiye da kowa,bansan dalili ba,,takarashe da sakin kuka me rauni,,ckn tausayawa ubaida tace "hakuri dole zaki cigaba da yi tunda bakida mafita,,batareda muwadda tace komaiba ta mike,ganin haka yasa ubaida ma tamike tana fadin " Ya kika tashi???,,saboda kar gimbiya su koma bangarensu suzo cin abinci bananan,,hakane to muje,,suna tafe ubaida tana kara bawa muwadda shawar wari har suka karaso kofar da zata sadaka da bangaren gimbiya jalila sannan sukai sallama ubaida ta juya ita kuma tashiga ciki. Yarima sameer suna komawa bangarensu gimbiya jalila ta cire alkyabbar jikinta,farar doguwar riga ce a jikinta wadda akaiwa ado da fararen stone har kasa masu daukar ido sosai rigar tayi kyau,,gimbiya jalila siririya ce batada kiba ko kadan,me matsakaitan breast hakanan batada wasu manyan hip's, fara ce sosai kamar yarima sameer kuma kyakykyawa ce me ji da kanta,karasowa tayi inda yarima sameer ke tsaye yana karanta wata takadda da yagani,juyoshi tayi tazare masa alkyabbar jikinsa sannan ckn nutsuwa tashiga cire masa kayansa duk yana binta da kallo,towel ta dauko fari kal sabo a leda sannan taja hannunsa suka nufi bathroom,shikam yakoma kamar ba yarima sameer dinnan ba gabadaya yayi laushi,,suna zuwa ta rataye towel din,murmushi tayi tace "my Prince kayi wankan zan fito maka da kaya kafin ka fito"tana kokarin fitowa ya riko ta dasauri,murmushi tayi don dama tasan za'a rina,lakacr dogon hancinsa tayi sannan tashiga kiciniyar cire kayan yana taimaka mata,a tare sukayi wanka ckn nishadi da kaunar juna suka gama suka fito hannunsu sarkaye da na juna,,daga shafawa juna mai yarima sameer yakasa jurewa yashiga romancing dinta kamar zai cinyeta,,lkc guda suka fice hayyacinsu bakajin komai sai tashin nishinsu tareda ihun gimbiya jalila don yarima sameer karshe ne wajen sarrafa kowace irin mace,,sundauki lkc suna Abu daya kafin su kawo,gefe sukayi suna maida numdashi,jiki ba kwari gimbiya jalila ta rungoma yarima sameer ckn sanyin murya tace " Bazan iya misalta adadin kaunar da nake maka ba my prince,bana iya hadaka da kowa a zuciya ta,,ka kasance da ni a kowani irin tanayi don Allah prince!!Wlh ina matukar kaunar ka da kishin ka bazan iya hadaka da kowa ba a raina,don Allah kada ziciyarka ta cuce ni tamin kishiya sakamakon bana haihuwa saboda wlh mutuwa zanyi baz.....harshensa yasa ckn bakinta yashiga aikamata zafafan sakonni saboda bayason ta fadi abinda takeson fada wanda yake ganin har gaba da abada bazaiyuba yahada ta da wata,saida tayi lakwas sannan ya kyaleta yashiga shiryata a haka har tasaki suka shiga shirya juna amma zuciyarta cike da tunanin rashin haihuwarta don sosai abin yake damunta musamman yanda tason yarima sameer yana tsananin kaunar yara dukda kowani lkc shi yake tausarta yana nuna mata komai lkc gareshi idan lkc yayi zasu samu,amma itakam a kage take sosai taga jininta dukda a badini yafita kaunar hakan to amma yazaiyi da yanda Allah ya tsaro musu??Tunda sunyi magani kala² amma ba'a dace ba kuma sosai suke addu'a. Me babban daki ce zaune a parlour'nta ita da fulani tareda jakadiya sai faman zazzaga bala"i takeyi akan abinda yarima yusufu yayi akan kuyanga muwadda don sosai take da mita musamman yanzu dataga yarima sameer taga yanda yake abubuwansa ckn nuna isa da iko sai abin yasake halakata,,jakadiya ce tace "To ai ranki ya dade kamata yayi ki shata mata layi daganan ki aika a kirata ki karanta mata gargadi ne razanarwa wanda ko kallonta yarima yusufu yayi sai ta gudu ballantana ace sunyi magana sa juna,,girgiza kai me babban daki tayi ckn gamsuwa tace " haka za'ayi jakadiya kirawomin ita",,Angama ranki shi Dade "cewar jakadiya yayinda tamike tabar dakin. Kuyanga muwadda awanta biyu da rabi cuur a tsaye tana jiran fitowar su gimbiya amma shiru,haka tacigaba da tsayuwa babu alamun gajiya ko kadan a tare da ita,,a haka jakadiya ta shigo ta sameta,ckn girmamawa muwadda ta gaida jakadiya don ita tanabawa babba girmansa sosai,,kallonta jakadiya tayi sama da kasa sannan tace " kije me babban daki tana kiranki",,Zaro ido tayi ckn tsoro tace "Don Allah jakadiya ki fadamin wani Abu nayi ne???,,Tabe baki jakadiya tayi tace " Idan kinyi wani Abu ai inaga zaki fini sani ,kije dai zakiji",,Ajiyar zuciya muwadda tayi tace "To bari idan gimbiya suka fito sukaci abinci zan nemi alfarma sai naje,,wani mugun kallon raini jakadiya ta watsa mata ckn jaraba tace " Saboda sa'arki tana kiranki ba??? Zaki wuce ko sai naje na hada miki masifa!!!!Dasauri muwadda tafita don tasan halin me babban daki sarai batada kirki ko kadan,,tana tafe tana hadawa da gudu saboda tsoron karsu gimbiya jalila su fito batanan nanma tayi wani laifi,, jakadiya kuwa daganan tayi bangaren amarya kaimata wani sako,,muwadda zatashiga kenan tajiyo muryar me babban daki tana fadin "Ai dan iskan yaronnan daga yau tashi ta kare,,ina me tabbatar miki an kusan shafe labarin yarima sameer a masarautar nan,,don wancen maganin da nasa masa a miyar tumatir mirdemasa yan hanji zaiyi ckn kankanin lokaci zai zama gawa,,ta karashe da kecewa da dariya,,ckn tayata dariyar fulani tace " Kayy Gaskiya fa me babban daki kema bakida dama,amma wani hanzari ba gudu ba kinsan fa dole za'ayi bincike ko??? Murmushi tayi tareda daukar kankana tanasha ckn nuna alamun ko a jikina tace "Tabbas sosaima amma kinsan baza'a taba zargina ba ko kusa,sai dai ma'aikatan da sukayi abincin,,shiru tayi tana wani naxari kafin tace " Tabbas na jefi tsuntsu biyu da dutse daya,saboda kuyanga muwadda ce tayi miyar ita kadai don raba ayyukan sukayi duk da tafisu yi,,Kinga shikenan nagama da yarima sameer da kuyanga muwadda,,sakin dariya sukayi suka tafa,,,muwadda dake kofar dakin taji wani mugun jiri yana dibarta tana shirin kifewa,jitakeyi gabadaya gidan yana juyamata,,sosai kirjinta yahau bugu tamkar ana daka,,k'afewa idonta yayi daboda tsananin tashin hankali babu alamun hawaye a cknsu,,dakyar ta iya aro nutsuwa ta saita kanta ta shiga parlourn bugun ziciyarta yana tsananta wanda da me babban daki da fulani sun kula zasuga yanda rigarta take harbawa ta kirjinta,,gaishesu tayi ckn girmamawa ,,bataresa sun amsa ba me babban daki tajayo kunnen muwadda ta murde saida tayi yar Kara saboda axaba,,ckn bala'i tadinga zazzaga mata tareda jamata kunne tafita harkar yarima yusufu,gyada kai kawai muwadda takeyi badon ta fahimci wasu abubuwan da me babban daki take fada ba don gabadaya hankalinta yayi kan abincin can kar suga shiru gimbiya jalila ta zubamasa ita kuma ta shiga uku,,me babban daki tana sallamar ta tafice da sauri,,ai tana barin parlourn ta ruga da gudu ckn tashin hankali sai zufa takeyi,,tana shiga parlourn su gimbiya jalila suna fitowa ckn shiga iri daya ta bluen alkyabba sunyi kyau matuka,,tsayawa tayi tana raba idanuwa don burinta yazata hana yarima sameer shan miyar nan alhalin yana tsananin kaunarta???Ita dama gimbiya jalila batashan miyar tumatir kwata²,,Sam muwadda tama manta da ana wani durkusawa a kwashi gaisuwa saboda tashin hankalin daya tunkarota*Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟* {Historical Fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k &HUSSEIN 80k* Special gift to my besty *UMAMATU UMAR ADAM* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *PAge 7* Tsananin mamaki ne yakama gimbiya jalila ganin irin kallon da muwadda take musu bako kiftawa kuma babu alamun zata gaishe su,,ckn jin haushi da tsana gimbiya jalila da daka mata tsawa da cewa keeee!!!!!,,,A firgice muwadda tadawo hayyacinta,,rikicewa tayi dasauri ta zube ckn rawar murya tace "Barkanku da fitowa gimbiya da yarima,Allah ya huci zuciyar ku,ayimin afuwa",wani mugun tsaki gimbiya jalila taja tanufi dinning yayinda tuni yarima sameer ya saki hannunta ya karasa don ko kallon muwadda baiyi ba tun shigowar su,ganin haka yasa muwadda ta karasa zuciyarta tana lugude kamar zata faso kirjinta ta fito saboda rashin samun mafita,hannunta yana rawa tajanyo plates tashiga saving dinsu,hadadden dambun shinkafar da akaiwa gimbiya jalila wanda yaji vegetables an yanka nama kananu²,,yaji mai sai tashin kamshi yakeyi,shi tazuba musu gabadayansu,,ckn mugun takaici gimbiya jalila ta daga hannu ta zabgawa muwadda mari wanda saida taga giftawar stars jinta yadauke na wucin gadi saboda azabar mari,,ckn fada da murya kasa² wadda ita a wajenta ta masifa ce saboda tsabar jin kai tace " Ke wacce iriyar muguwar dakikiya ce mara hankali???,,mtsww ke kam ai ko kwakwalwar dabba tafi taki amfani,,narantse da Allah idan bakiyi wasa ba saina wulakanta ki,sai na maidaki abar kyama a idon duniya,shegiyar yarinya me idon mayu saikace mayya,saboda jakanta a gidan ubanki kika taba ganin prince dina yaci dambu???,dasauri muwadda tashiga gyada kai,ckn rawar jiki ta tsugunna tashiga basu hakuri. Duk abinnan da ke faruwa yarima sameer bai kp dago ya kallesu ba,tamkar babu shi a wajen,hasalima wayarshi yake dannawa hankali kwance,sai dai hayaniyar tasoma hawar masa kai,shikam a wajensa ai muwadda batada darajar sa zai ko kalleta ko laifi tayi sai dai yasa a hukunta ta,shifa ko kamarta ma bai sani ba. Wani irin mugun bakin ciki ne Yakama muwadda na wannan wulakancin da cin kashin da ake mata,,a boye ta share kwallar tausayin kanta da mahaifiyarta,wata zuciyar ce tace mata kibashshi yaci mana idan ma ya mutu Allah yagani bake bace kuma koda sun kasheki kansu sukaiwa,,wata zuciyar ce tace mata nahaifiyar ki fa???Kin ajiye me kula da ita???jitai kanta yamata wani irin masifar nauyi tare da sarawa da yakeyi kamar zai tsage,ganin tarasa mafita ne yasa ckn sanyin jiki tajanyo cooler green rice din tashiga zubawa a wani hadadden plate me shegen kyau,cooler miyar ta janyo ta bude sosai kirjinta ya buga wanda yasata rike kanta da sauri saboda yanda yake mata barazanar tarwatsewa,har wani Abu ne me daci ya tsaya mata a makoshi,,wata dabara ce ta fado mata lokaci guda,amma tana tsoron aikata ta dukda ita kadaice mafitar da zuciyarta tabata ynz,don ko giyar wake tasha bata isa taje tace me babban daki ce tazuba magani a miyar ba,tasan karshe dai abin kanta zai dawo saboda haka dole ta aikata ta batada zabi,dagewa tayi dakarfi tasaki atishawa sai miyau a ckn miya,ba gimbiya jalila kadaiba har yarima sameer saida yadago ya kalleta karon farko,lkc guda tsanar muwadda ta tsarga zuciyar shi,gimbiya jalila kuwa saboda tsananin bacin rai tarasa wani irin hukunci yakamata tayiwa muwadda kallonta kawai takeyi,,jikin muwadda ne yadauki rawa don tasan yau dai kashinta ya bushe ,batai auneba saijin saukar cooler miyar tayi a kanta gabadaya ta wanke mata fuska,batasan lkcn da tasaki kara ba saboda zafin miyar tareda Jan yajin daya shigar mata ido,dakarfi gimbiya jalila ta fuzgi kitson muwadda daya ta jijjiga da karfi ta fincikeshi yafita saiga kan muwadda yana zubar jini,,kuka muwadda takeyi sosai saboda tsananin azaba amma dukda haka gimbiya jalila bataji ko digon takaicin muwadda yaragu a ranta ba,muwadda batai zatoba saijin saukar bulalai tayi ta ko ina saboda idonta yana rufe,gimbiya jalila ce tasa aka kira mata gardawan bayin suke dirkar muwadda tamkar jaka,,ihu takeyi tanason yin magana amma ta kasa saboda tsabar azaba,numfashinta ne yafarayin sama² kawai saita zube a sume . Mikewa yarima sameer yayi ckn takaici tabi takan muwadda ya taka mata hannu ya wuce don ko kusa baiji ko digon tausayinta ba,,gimbiya jalila binsa da kallo tayi batabi sa ba don tasan bama zai kulata ba,batai yunkurin sawa asake masa sabon girki ba don tasan bama ci zaiyi ba,,bayinnan tasa sukaja muwadda a kasa tamkar kayan wanki suka fita sa ita har lkcn bata farfado ba. Gimbiya jalila zama tayi akan kujera bayan amfita da muwadda,itadai Allah yasani kwata² batason muwadda ta tsaneta kuma tarasa dalili,canja tunani tayi ta tafi tunanin abinda ke matukar damunta me sanyata kuka wato rashin haihuwa don matuka yana damunta kuma dole tadau mataki akan lokaci. Bayin nan suna fita da muwadda suka jefata wani daki bisa umarnin gimbiya har zuwa lkcn bata farfado ba. Bayan yarima sameer yafito kai tsaye bangaren me babban daki yanufa don yaji cewan yarima yusufu yana can,da sallama ya shiga ya isketa itada fulani suna hira,,zama yayi kan kujera shima ya kame,,gaishesu yayi suka amsa,me babban daki fuskarta dauke da murmushin mugunta tace "Dana nakaina ince dai kaci abinci ka koshi???",, Haka kawai ya tsinci kansa da cewa " Eh naci",Dadi ne yakara kama me babban daki tagama da yarima sameer, don haka tace " kuyanga muwadda ce ma tayi maka don ta iyata sosai",, Batareda yadago ba yace " Ok",dagowa yayi yace "ummana wai ina yarima yusufu ne??Naji ance yana nan. Eh dazu yana nan amma yakoma bangarensa,mikewa yayi yai musu sallama yafita gabadayansu suka bishi da murmushin mugunta,,yana fita me babban daki tace " Saura kiris ka zama gawa don ubanka",,Dariya sukasa hadda tafawa saboda tamusu kyau,ckn dariya me babban daki tace "Bari nasoma murza ido yafara ja yanda zanci uwar kuka d'a zai mutu anjima",Nan ma dai dariya suka shigayi ckn nishadi. Yana fita yanufi part din yarima yusufu bayinsa na biye da su,,suna zuwa kofar shiga suka tsaya shikuma ya shiga,baya parlour saboda haka kai tsaye ya nufi bedroom, yarima yusufu yana kwance haka kawai tunanin muwadda yakeyi yarasa dalili,shidai ya ajiye a matsanancin tausayin ta da yakeyi,yana ganin yarima sameer yashigo yamike da sauri ckn farin ciki yayi hugging dinsa,shima yarima sameer dadi yakeji don yana kaunar yarima yusufu sosai,zama sukayi a bakin gado yarima yusufu yace " yayana ina shirin zuwa gaishe ka sai gaka da kanka ni da nabari ka huta ne zuwa anjima,dan guntun murmushi yarima sameer yayi yace "Dole nazo ba duba lpyr kani na,naji dadi jikin sa saiki ma,haka suka shiga hirarsu gwanin birgewa,yarima sameer yajima sosai kafin yafito yanufi part din mahaifiyar shi amarya. Tana zaune a hadadden parlour'n ta itada gimbiya farida da gimbiya maryam kannensa suna hira bayi kuma mata sunada hada²,yana shigowa bayin suka fice bayan sun zube sun mika gaisuwa,,wani kallo ya watsawa su gimbiya farida ba shiri suka mike sukabar parlour'n,,barareda amarya ta kalleshi ba tace " Akanme zaka korar min yara muna hira"fuskarshi yasaki tamkar ba shiba,murmushi yayi yazauna kusa da ita tareda dora kanshi akan kafadarta,ckn shagwaba yace "Ummina yunwa nakeji kibani abinci",, Sosai amarya takejin kaunar dan nata amma dole sai tayi alkunya,zame kafadarta tayi tana fadin " Jeka ga uwakka can me babban daki tabaka ko matarka",Noke kafada yayi irin na kananun yara wai shi a'a,murmushi amarya tayi tareda kawar da kanta,mikewa yayi dasauri tace "Waima tun dawowarka kaci abinci???,A shagwabe yace " Nidai banci ba naki nakeso",,Zaro ido tayi tamike tareda cire alkyabbar bikinta wani uban ubansun lace ne a bikinta onion colour riga da zani yaci uwar kyau,,sosai yaji dadi ganin umminsa tacire kunya dai yau tana masa girki,sosai yaji dadi saboda haka yabita kitchen din dake parlour'n yana tayata wani Abu,wani lkcn ta kulasa wani lokaci ta share shi,shidai yaji dadi kwarai a haka har suka gama girkin sai tashin kamshi miyar tumatir din take,yanata faman hadiyar yawu.*'Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k &HUSSAIN 80k* Special gift to my bestyna takaina,rabin raina❤ *UMAMATU UMAR ADAM* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *PAGE 8* Cikin nutsuwa yakecin abincin tamkar bayaci saboda yanaci ne yana danne² a waya,,mufeeda ce tashigo dakin bako sallama tazauna kusa da ummi idonta akan yarima sameer wanda baiji shigowarta ba ma,ckn yauki da salon jan hankali tace "Barka da hutawa ya sameer,ina fatan dai baka tare da gajiyar hanya,kallonta ummi tayi saboda salon datayi amfani dashi wajen maganar,sai wani lankwashe murya takeyi kamar lagwani,,idon kujerun dakin sun amsa mata to yarima ma ya amsa mata don banza yai da ita tamkar baiji ba,,ckn jin haushi da halin ko in kula din da ya nuna mata tace " haba yarima wai meyasa kakeson wulakanta ni ne a rayuwarka???Saboda kaga na damu dakaine shiyasa kakemin haka amma...Baijira ta karasa abinda zata fad'a ba yamike tare da watsamata wani d'an iskan kallo wanda saida hanjin cknta suka kada,,kallonsa yakai kan ummi yace "Ummina sai anjima na wuce",, A'a zauna muyi magana" Cewar ummi batare da ta kalleshi ba,zama yayi a kusa da ita yana fadin "Allah yasa dai ummina abin dadi zaki bani",, girgixa kai tayi fuskarta dauke da murmushin da yake kawata kyakykyawar zagayayyiyar fuskarta me cike da haiba,kallonta takaida kan mufeeda daketa kallon yarima tace " Tabbas banajin dadin yanda kuke zama yarima da mufeeda,saboda haka gani ynz kuyi sulhu don bai dace ba ai anxama daya",,Matso kwalla mufeeda tayi tace "ummy wlh tsanata yayi ni bansan me nayi masa ba kina gani fa yanzu na gaishe shi yamin banza kamar baiji ba kuma ai yaji",,kallon yarima ummi tayi yanata danne² a waya tace " Meyasa hakane yarima??Itama fa tamkar su farida take a wajenka",,Cije pink lips dinsa na kasa yayi ckn hadaddiyar voice dinsa me rikata y'ammata yace"Ummina ba kamar su farida ba dai,,kalli fa yanda takemin magana,ai ba haka sukemin ba,Sam yarinyar batada hankali",,Sosai mufeeda taji haushi don haka ckn fushi tamike fuuuuu tafice daga dakin ummi tabita da kallo,,ckn nuna rashin jin dadi tace "Meyasa zakace batada hankali yarima??,, Kamo hannunta yayi yana wasa da ring din hannunta wanda akayi da zallan tataccen gold, ckn shagwaba yace " Ummina batada hankali fa da gaske, ni miye had'ina da ita??,,ummi kwace hannunta tayi tana harararsa tace "Ai ko domin me babban daki ya cancanki kayi mata kara tunda y'ar yayarta ce ai kamar y'arta ce",, Ajiyar zuciya yayi yace " Kiyi hakuri ummi na zan kiyaye",Shiru ummi tayi batareda tasake cewa komai ba,ganin haka ne yasa yamatso daf da ita yace "Ummina kin hakura eye??,,Kawar da kanta tayi a ranta tana jin kaunar danta kwarai", Ganin takara yin shiru ne yasa yakara matsowa yana lekon fuskarta yace " Eye Ummina don Allah kin hakura???,Murmushi tayi tace "Na hakura",, Peck yaimata a goshi yamike tareda yimata sallama yafita,,yana fita yadawo asalin *YARIMA SAMEER* dinshi fuska a tamke ba annuri sam,kai tsaye bangarensa yanufa bayinsa na biye dashi,, duk inda suka gifta zakaga bayi sunzube suna gaisuwa amma ko kallo basa samu daga yarima. Me babban daki ce zaune ita kadai a parlour duk ta sallami bayinta, zuciyarta cike take da mamaki don taji shiru ba labarin ansamu wata matsala daga yarima tunda yasanar mata yasha miyar,,mufeeda ce tashigo dakin tamkar zata tashi sama,ganin haka yasa me babban daki tamike dasauri don a tunaninta mufeeda zata sanar mata wani Abu yasami yarima,amma sabanin haka don ckn bacin rai mufeeda tace " Wai ni umma me kike nufi dani ne???Bafa nadawo gidannan don nasaku a gaba da kallo bane,, na dawo ne domin yarima amma Sam kin kasamin kokari kanki kawai kikasani,yanzu gashi har yarima yana kirana da banida hankali ,,to wlh kiyi wani abu don nayi rantsuwa saina mallaki yarima ko ta halin yaya,saboda haka kisan abinda zakiyi",,,Ajiyar zuciya me babban daki tayi tace "naji,Yaushe yariman yace miki bakida hankali???,, Ckn fushi tace " Yanzu mana muka hadu a d'akin waccen munafukar uwar tashi,wlh itama idan nasamu yarima sai ta shiga uku",,ckn damuwa me babban daki tace "Yana lpy dai ko???",, Shiru mufeeda tayi idonta akan me babban daki tana jefa mata kallon tuhuma,kankance idanu tayi tace " Umma kinyiwa yarima wani Abu ,me kikai masa???,,,Harara me babban daki ta watsamata tace "Uwarki nai masa kinji?",, Ckn rashin yadda mufeeda tace " Umma wlh za'a iya samun matsala idan wani abu yasamu yarimana don zan iya komai akansa",,,Ckn fada me babban daki tace "Keeee mufeeda wlh kifita daga idona na rufe,don wlh idan narufe dake baxakiji da dad'i ba,ni kikeyiwa irin wannan banxar maganar???Ko kinmanta dawa kike magana???Don uwarki fitarmin daga daki!!!!,,,Mikewa mufeeda tayi tana kunkuni tafice daga dakin,, tsaki me babban d'aki tayi tace " Sakaryar banxa ni yanzu takaina nake batake ba don banason ganinsa ma yanzu a duniyar ballantana ki aureshi,zama tayi tana tunanin yanda haka ta kasance bayan yarima ya tabbatar mata da yasha miyar,,a ranta tace "Wlh yarima ko kabuta daga wannan bazan barka ba sai naga karshen ka. Wata kuyanga ce tashiga dakin da akakai muwadda hannunta dauke da wani katon bucket wanda yake cike da ruwan sanyi sosai,tana zuwa ta dagashi tareda juyewa muwadda gabadaya a jikinta bisa umarnin gimbiya don har lkcn muwadda bata farka ba,,wani irin dogon jan numfashi tayi kamar zata shid'e,a hankali tadinga sauke ajiyar zuciya bayan tabude idon ta,, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga tseren zuba ta gefen idonta,sosai takejin rayuwar tamata kunci,har tarasa inda zata saka ranta taji dadi a duniyar nan,,ckn karfin hali ta yunkura ta mike don jikinta ciwo yake mata saboda mugun bugun da tasha,wani mugun sanyi taji yana bugarta saboda kayan jikinta da suka jik'e sharkaf har suna diga,da iskar da akeyi a garin,,tana mikewa tadafa bango dasauri sakamakon jin datayi tana kokarin zubewa saboda jiri,ga kafarta ta hagu ga dukkan alamu tayi targade saboda yanda tarike sosai take mata zafi,,wata iriyar muguwar tsanar yarima sameer da gimbiya jalila ke sake hudata,har takejin dama ta kyaleshi kawai yaci yamutu batada asara ,kuyangar da ta watsawa muwadda ruwa ce tace " Ni narantse kina bani haushi ke kullum sai kinyi laifi saikace ke kadai ke aiki,,ai Allah ya karawa me kaud'i irinki,,Sai kizo kiwuce gida ai tunda lokacin tafiya yayi",,A hankali tafara takawa tana dingisawa har tafice daga dakin sannan itama kuyangar tafito,,kai tsaye muwadda gida ta nufa don ubaida ma bata ckn masarautar saboda tafadawa muwadda dawuri zata tafi tanada uzuri. Koda muwadda takoma gida boyewa iyanta gaskiyar lamarin tayi tace Faduwa tayi a ckn wani ruwa da ke kan hanya shine jikinta ya jik'e k'afarta ma tayi targade,,sosai iya ta tausaya mata sai sannu take jero mata,bayan tayi wanka iya tai mata gyaran targaden sai kuka takeyi,ita kanta ita saida ta goge kwalla,ba'a jima da gamawa ba wani wahaltaccen bacci yayi gaba da ita,,shafa dogon gashin kanta iya tayi ckn tsantsar kaunar y'arta tace "Banyadda kinfadi bane muwadda na saboda kinada nutsuwar tafiya,tabbas akwai abinda yafaru kike boyemin ga shatin bulala nan a jikin ki,,share hawayen fuskarta tayi tace " Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar,yabaki juriya",,Ameen. Gimbiya jalila na zaune a parlour'nta wasu yammata bayi suna zaune suna mata hira jefi²,yayinda wata ke gefenta tana yankamata fruit's tana bata,wayarta ce tayi ringing tana dubawa taga autar su wadda batafi sa'ar muwadda ba,,dagawa tayi ckn yauki tace "Autar Amma yadai??,,,Daga can bangaren cikin farin ciki kanwar gimbiya jalila tace " Adda jalila ya hafsa ta haihu yanzu namiji ,, muna asibiti",,,dad'i taji sosai ckn farin ciki tace "ina hafsan?Bata waya,,Ohhh ni bana gida ki kirasu,,To " tafada tareda katse kiran,,A ranta jitake inama itace ta haihu, gimbiya Hafsa kanwarta ce me bi mata amma y'ay'anta biyu kuma kaf dinsu maxa,tana auren dan sarkin sokoto,saida akayi bikin gimbiya jalila da shekara biyu akayi nata don ita yanzu gimbiya hafsa shekararta 5 da aure,gimbiya jalila kuma 7. Mikewa gimbiya jalila tayi tafice daga dakin kai tsaye tanufi banfarem yarima. Yana zaune a gefen gado yana danne² a laptop tashigo tare da yin sallama,,batareda yadago ba ya amsa sallamar wadda zaka fahimci hakanne kadai idan kakalli motsawar Lip's dinsa,,Zama tayi gaf dashi sosai yanda numfashinsu yake bugar na juna,bai dago ya kalleta ba yacigaba da abinda yakeyi,ckn shagwaba tace "Prince kayi hakuri da abinda ya....wani kallo yawatsa mata wanda yasata jan bakinta ta tsuke don tasan sauran baya kaunar dawo da abinda ya wuce,,ture laptop din yayi yana kokarin mikewa tace " Prince hafsana ta haihu yau",,fuskarsa dauke da murmushi yace "Me muka samu???,,Namiji,tabashi amsa a takai ce, Addu'a yayiwa yaran tare da daukar waya yakira mijin hafsa don abokinsa ne,,bayan sungaisa yaba gimbiya jalila, suka gaisa sannan yabawa hafsa don har sundawo gida ma,,ance jariri yana kama da gimbiya jalila,bayan sun ajiye wayar ne takalli yarima sameer ckn yanayin damuwa tace " Prince Allah yabamu d'a ko y'a,,Wlh jinake inama nice na haihu,,zama yayi kusa da ita tare da zare mata alkyabbar jikinta yace "Ameen,karki damu komai lokaci ne,bata iya sake magana ba sakamakon jin hannunshi datayi akan breast dinta yana wasa dasu,a hankali tafara sauke numfashi tana bankarewa saboda sosai abin yake shigarta,zame rigar jikinta tayi tacire tare da b'alle breziar jikinta tayi cilli da ita,sosai suka fita hayyacinsu suna romancing juna,yayinda tuni yarima yarabu da kayan jikinsa,ckn sambatu gimbiya jalila take fadin " Wayyo Allah my prince don Allah karka rabu dani...Ohhh...washhh....Yarima dadinka zai kasheni...Ina kaunarka dayawa yarima..haka dai taita sambatu shikuma yana rad'amata dad'adan kalamai tareda birkita ta da manyan sakonninshi har sukai release,,gefe suka mirgina suna maida numfashi ckn farin ciki,janyo yarima gimbiya jalila tayi a kunne ta rad'a masa "My prince karfa dad'inka yakasheni watarana kasan salon haukata mace da dad'i,,wlh ka hadu da yawa",,Shima kara rungumeta yayi yace " Kema kin hadu sosai princess bakiga yanda kika gogemin hadda ba???murmushin jin dadi tayi ckn matsananciyar kaunar mijinta,,shafo cknta yarima sameer yayi yace "Ya Allah kasa nayi ajiyata anan yanzu",, yak'arashe da kashe mata ido,Ameen ta amsa tare da sake shigewa jikinshi bacci yayi gaba dasu. Kiran sallar la'asar ne ya farkar dasu,yarima ne yafara tashi sannan ya tasheta,a gurguje sukayi wanka tare da shiryawa yarima yafito masallacin ckn masarautar ita kuma tayi a daki,,tun suna wanka usman abokinsa yake kiransa amma bai daukaba saboda saurin da yake yi,saida yaje yayi sallah yadawo sannan yakira usman din don yayi masa 14 misse called yasan akwai dalili,,yana dagawa yaji muryar usman ckn farin ciki yace " yarima madam tasauka dazu fa munsamu mace",,Murna sosai yatayashi sannan sukai sallama,,gimbiya jalila da ke kusa dashi kuma taji duk wayar da sukeyi,,matsowa tayi tariko hannunsa idonta dauke da kwalla tace "Don girman Allah prince muje indi'a a sake dubamu don Allah",, Kallonta yayi nawani d'an lokaci kafin yace " Princess babu fa wanda zai baki abinda Allah bai baki ba,karki manta ancemana lafiyarki kalau amma mahaifarki bazata iya daukar ciki ba,to me kikeso suyi miki?Abin da mamaki sosai,,,Hawaye ne suka shiga zubo mata ckn rawar murya tace "Don Allah Prince ka taimaka muje,ai da gwaji za'a dace,,tausayi tabashi sosai saboda haka yajanyota jikinsa tare da zaro handkerchief dinsa fari kall yanata buga kamshi yashiga share mata hawaye,ckn sanyin murya yace " Na amince zamuje amma banyanke lokaci ba sai na sanarwa me martaba,,rungumeshi tayi tana godiya ckn jin dadi tare da fatan Allah yasa a dace don tasan me martaba baxai k'i ba,mikewa sukayi suka fito suna manne da juna,suna zuwa kofa suka saki ita tayi bangarenta shikuma yanufi b'angaren me martaba. *Karku manta littafinnan na kud'i ne na maidashi free saboda murnar sabuwar shekara 2020,,To matukar bana samun comment's yanda nakeso zan maidashi na kud'i maganar gaskiy,.* *COMMENTS* *&* *SHARE**'Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟* {Historical fiction} ➰ *STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k* Special gift to my besty Rabin raina *UMAMATU UMAR ADAM* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Munfara biki yau kuma zamu gama ranar Sunday,, banyi muku alkawarin typing a y'an kwanakinnan ba amma idan nasamu time zanyi,idan kunjini shiru sai zuwa Monday insha Allah. *PAGE 9* Duk inda yarima sameer ya gifta zakuga bayi suna zubewa suna gaisuwa,shikam fuskar nan a had'e bai ko daga musu hannu balle ya amsa,yana shiga fada ya tadda me martaba da waziri da alamun magana sukeyi don su biyu ne,sallama yayi sarki da waxiri suka amsa fuskarsu dauke da murmushi,,fuska ba yabo ba fallasa ya gaishe su suka amsa,,ckn kulawa mai martaba yace "Yadai yarima lpy ko???",, gyara zamansa yayi yace " lpy klau me martaba dama muna Neman izininka ne zamu koma India a sake dubamu saboda princess ta damu da yawa",,girgiza kai me martaba yayi ckn tausayawa yace "Ku kwantar da hankalin ku yarima komai lokaci ne karku damu,kuma babu damuwa insha Allah saiku shirya tafiyar,,waziri ne yace " Yarima yana godiya ranka ya dad'e,,godiya shima yarima yayi sannan yasanarwa me martaba haihuwar kanwar gimbiya jalila,sannan yasanar masa dagacan zasu wuce India amma batare zasu tafi ba zaizo yasameta,, ckn farin ciki me martaba yace "Jiya sarki abdulkhareem yakirani yafadamin haihuwar,babu damuwa dagacan din sai ku wuce"sundan jima suna hira kafin yarima yai musu sallama ya tafi. Yau muwadda tunda ta tashi daga bacci take wani matsanancin ciwon kai,,sosai ta daure har tabaro gidan iya bata gane ba don bataso tasani tashiga damuwa,da wuri tazo tayi dukkan ayyukan data sabayi,dakyar ta iya yimusu chips da wainar kwai,sannan tai musu farfesun kifin ruwa da hadadden kunun gyada, tadafa ruwan tea tazuba a flask,gajiya tayi da tsayuwa saboda yanda takejin jiri yana dibarta,zamewa tayi da durkushe a wajen ta dafe kanta tana fitar da wani huci me zafi,da alama zazzab'i ne ya kamata saboda rawar da jikinta yadauka kuma yayi zafi rauuu,,ta shafe fiye da awa daya a haka kafin gimbiya jalila da yarima sameer su fito,yauma kamar kullum shigar su iri daya suna rike da hannun juna,hango muwadda a tsugunne yasa gimbiya jalila tayi tunanin ko bacci take yi,kwafa tayi a fili tace " Yarinyar nan sai na koya miki hankali don na fuskanci kin haukace yanzu,, sakin hannun gimbiya jalila yarima yayi yafita amsa waya,karasawa tayi kusa da muwadda ta zuba mata rankwashi wanda yahana muwadda ko motsawa saboda azaba,don ji tayi tamkar an fuzge mata kai,,ganin haka yasa gimbiya jalila tayi tunanin kamar raini ne yahana muwadda dagowa,,a fusace ta hankad'ata ta bugu da bango saida tayi k'ara saboda tsananin azaba,, dago idanunta tayi da sukayi jajir suna zubar kwalla takalli gimbiya jalila,, durkusawa tayi ckn rawar murya irin ta mara lafiyan da ya galabaita tace "Allah ya huci zuciyarki ranki shi dad'e, ayimun Afuwa banda lpy ne",,, A fusace gimbiya jalila tace " Bakida lpyr uwarki!!Y'ar iskar yarinya,to ko suma kikeyi ni baidameni ba don ba kaunarki nake ba,na tsaneki!!!! Dallah taso kibawa mutane abinci!!!ta fad'a a tsawace,,jiki na b'ari kuyanga muwadda ta mike, dai² lkcn yarima sameer yadawo,zama yayi tayi saving dinsu,tana tsaye a kansu har suka gama,dauke Warmer's din tayi tamaida kitchen tadawo ta gyara wajen,gimbiya jalila ce cikin tsana da wulakanci tace "Keee k'ask'antacciya wuce ki kiramin jakadiya",,, Dasauri tafita gudun kartayi laifi,,tana tafe tana had'a hanya kamar zata kifa,wata kuyanga tagani a hanya ta tambayeta ina jakadiya,amsa mata tayi da tana b'angaren amarya,,tana shiga tazube tana gaida amarya ckn muryarta da bata fita sosai,,da kulawa amarya ta kalleta tace " Yadai muwadda kina lpy kuwa???,,wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata masu zafi,dasauri tace "Eh..eh..ranki ya dade lpy ta kalau ,dama gimbiya jalila ce tace nakirawo mata jakadiya",,, Shiru amarya tayi tana kallon muwadda,kallonta ta maida kan jakadiya tace " jeki kiran da ake miki",,,mikewa tayi taimata sallama ta fita,kuyanga muwadda tana durkushe kanta a kasa tunda ba'a bata umarnin tashi ba,,da kulawa amarya tace "Muwadda matso nan",, Dasauri muwadda tadago idonta tasauke akan amarya don ganin tana nuna mata kusa da ita a matsayin wajen da zata zauna,,dasauri tashiga girgixa kai alamun a'a,,amarya sallamar kuyanginta tayi yaxama daga ita sai muwadda,tasowa tayi tanufo wajen da muwadda ke tsugunne,jin takunta ne yasa muwadda dagowa dasauri,wata iriyar zabura tayi tamike tare da hada hannuwa biyu ckn rudewa tace " Don girman Allah ranki ya dad'e ki koma wlh zan karaso,,murmushi amarya tayi ganin yanda muwadda ta rud'e,ba musu takoma tazauna,ajiyar zcy muwadda tayi ckn sanyin jiki ta karaso wajen amarya ckn muryarta me sanyi tace "Gani ranki ya dad'e",A hankali amarya takai hannunta ta ta'ba goshin muwadda,"subhanallah",, Tafada tare da dauke hannunta dasauri,ckn kulawa tace " Haba muwadda meyasa bazaki fada bakida lpy ba???,,kanta yana sunkuye takasa cewa komai sai hawaye da ke tsere a kuncinta,ckn rashin jin dadi amarya tace "muwadda idan bakida lpy kidinga Neman uzuri kina zama a gida kinji???Ai lpy tafi komai",, Gyada kai muwadda tayi a zuciyarta kuwa cewa tayi ", Ashe da najawa kaina bala'i",, Wani abu amarya ta danna saiga daya daga ckn kuyanginta tashigo tadurkusa tareda fadin " ranki shi dad'e gani"batareda kallon banza da raini ba tace "Kawowa muwadda abinci sannan ki kiramin likitan da yake kula da bayi", Ckn tsananin girmamawa tace " Angama ranki ya dad'e,nabarki lpy",,muwadda a ranta tace "Kukam kunji dad'in ku kunyi dacen uwar daki"don ita ynz haka tunanin abinda zata koma ta tarar na rashin dawowarta da wuri take yi ,dawowar kuyangar nan tayi dauke da hadadden abinci da lemuka da ruwa tareda fruit's aka ajiyewa muwadda,,kinci tayi kanta yana kasa saida amarya tace " muwadda kici mana kisha magani",,Tsakura tafarayi kadan² don ita idan tana rashin lpy matsalar ta kenan batacin abinci saboda indai taci sai tayi amai,aikuwa takai loma ta uku tafara yunkurin amai,da gudu ta mike tafice daga dakin, can gefe ta durkushe tadinga kwararo amai kamar zata amaye y'an hanjin ta,abinda yabawa muwadda tsananin mamaki bai wuce ganin amarya a kanta ba tana jero mata sannu ckn tausayawa,,wata iriyar kaunar matar ce ta shigeta don mu'amala ba shiga tsakanin su takeyi ba batasan halayyar amarya ba,,nan amarya tasa aka wankewa muwadda amai sannan suka koma ciki aka kawo mata sababbin kaya, wanka tasata taje tayi sannan tasa kayan,,tea ta hada dakanta tanufi bakin muwadda xata bata,dasauri takauda kai kanta a kasa tace "Ranki ya dade xansha da kaina",, girgixa kai amarya tayi,badon muwadda tasoba amarya tadinga bata balaifi tasha dad'an yawa,kuma ikon Allah balayi amai ba,nan likita yazo ya dubata akai mata allurai,ba' a jimaba bacci yai gaba da ita",, Kafeta da ido amarya tayi tanajin yarinyar ranta fiye da dukkan sauran bayin gidan,haka kuma tana tausaya mata,gata masha Allah akwai tsananin kyau,sai takeji inama muwadda a bangaren ta take,tasan muwadda akwai tsananin biyayya da rashin surutu,gulma da sa ido irin na gidan sarauta duk bata ckn shirgin,abinda ke gabanta kawai take yi. Bayan jakadiya taje kiran da muwadda ke mata ne tabata umarnin za'ba mata bayi uku wad'anda xa'ayi tafiyar dasu,tashin farko jakadiya tace " Muwadda ta daya sai falmata,sannan nasiba,ina ganin wannan sunyi ranki shi dad'e",,Ckn gyatsine tace "yayi"wai ina kuyanga muwadda'n take???,ckn girmamawa jakadiya tace " Tana wajen hajiya amarya ",,Jin ance amarya ne yasa gimbiya jalila yin shiru don yarima na zaune a wajen. Muwadda tasamu sauki sosai,tana kokarin kiyaye duk wani Abu da zaisa a dinga cimata mutumci amma hakan bai hana aci mutumcinta ba kp tayi laifin kp batayi ba,,,ana gobe tafiya aka sanar dasu,,muwadda bataji dadi ba Sam,amma ubaida ta kwantar mata da hankali xata rika zuwa wajen iya,itama iya bataji dad'i ba amma sosai ta danne ta nunawa muwadda bakomai tunda fa muwadda,,har ta gamsu dasu tasaki ranta,sauran da aka zab'a kuwa kamar suyi hauka saboda zasuhau jirgi,muwadda kuma wannan karonta na biyu kenan. Yau takama tafiya,,jama'a sunfito anatayi musu adawo lpy,dukda basusan abinda zai kaisu India ba,sunje sumyiwa me martaba da sauran y'an gidan sallama,me babban daki dariyar keta kawai takeyi,a ranta take fadin " Wahala ce bata isheku ba,ku da haihuwa sai dai kugani anayi",,Amma a xahiri fatan alkhairee tai musu,, shi yarima bandashi a tafiyar yau,daga baya zai tawo,har airport suka rakasu ,basu jimawa jirginsu yadaga kasar Nigeria mahaifar gimbiya jalila don a masarautar kano take ",,,Danginta sunyi murna da ganinta,,itakam sai sake wulakanta su muwadda takeyi saboda isa,muwadda ta tafi da imanin mutane da yawa,hakan ba karamin sake hasala gimbiya jalila yayi ba don kowa yaganta sai ya tanka,,sai yaxama wulakancin muwadda daban ne,dama kuma tafi tsanarta,ana gobe suna yarima sameer yazo,,gimbiya jalila tana nanike dashi musamman yanda taga y'ammatan suna shishshige masa,donma shima ogan kansa ne wajen shan kamshi ,,anyi suna lpy jariri yaci sunan Abubakar,,anyi taro na karya da karya tareda ji da kai,su muwadda sunga ikon Allah,sunga inda ake wulakanta kud'i kamar bola,,washegarin suna suka wuce India,, bayan maghriba sukaje,a wani hadadden hotel suka sauka,bayan sunyi sallah sukaci abinci,yarima sameer ne yakira likitan da sukazo gani ya sanar dashi gobe zasu shigo asibitin,a ranar gimbiya jalila da su muwadda da wuri sukayi bacci saboda gajiya,banda yarima da ya dauro alwala yazo yadinga sallah yana rokon Allah yasa sunzo a za'a,,yasa sunada rabon ganin kwansu a duniya,,Sai kusan karfe hudu bacci ya dauke shi. Washegari motoci har gida sukazo daukar su zuwa asibiti,,duk inda yarima ya gifta xakuga ana gaishe shi ckn girmamawa,har suka karasa office din likitan,,yana ganin yarima yataso da sauri suka rungume juna,ckn harshen turanci suka gaisa bayan yasa ancika musu gabansu da kayan motsa baki,sudai su muwadda suna tsaye suna gadinsu,sauran sai raba idanu sukeyi sungansu a wata duniya,,bayan sun dan tab'a hira ne likitan yajasu wasu daki yashiga dubasu,su muwadda suna wancen dakin ba farko,akalla yashafe fiye da awa yana dubasu kafin ya gama,hada kayan aikin yayi yamaida inda suke kafin yadawo ckn kulawa da damuwa a fuskarsa yafara musu bayani "A Gaskiya nayi iya yina amma narasa dalili kamar da dai har yanzu mahaifar gimbiya bazata iya daukar ciki ba,,sai dai inada shawarar da zanbaku dukda ban tabbatar zaku dauketa ba",,, Share hawaye gimbiya jalila tayi ckn rawar murya tace " Matukar zatasa naga jini na mezai hana mu dauka",,Kallon yarima sameer doctor yayi,,gyada masa akai yarima yayi alamun "Muna jinka",,, Gyaran murya yayi sannan yace " ina ganin me zai hana a dibi sperm dinku a hada a dasa a wata mahaifar sai ta haifa muku,ai danku ne shima",,,dasauri yarima ya kalleshi yana yamutsa fuska,yayinda gimbiya jalila takafeshi da ido tana murmu*'YANCIN BAYI* {Historical fiction} ➰ *STORY WRITTEN BY*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k* Special gift to my besty *UMAMATU UMAR ADAM* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *PAGE 10* Ganin sunyi shiru ne yasa doctor yaci gaba da bayani"Ni a gani na hakan ba wata damuwa bane indai har zaku samu wadda za'ayiwa dashen,sannan.....Ya isa plz!!Cewar yarima sameer cikin kosawa da maganar doctor,kamar bayason mgn yace "wannan maganar Sam kabarta doctor don abine Wanda baxai yuba,akan me za'a dibi sperm dina Wai a zubawa wata,never!!,ai wannan cutar da wadda aka sawa ne,idan ma batada aure mene matsayin budurcinta???Idan tarasa Shi fa????,,Dasauri gimbiya jalila tace "To ai wannan Abu ne me sauk'i prince,me zai hana tana shiga watan haihuwarta sai ayi c.s a ciro Mana yaron namu??Kaga kenan baza'a samu matsala ba muma Kuma zamu samu cikar burin mu,,,,tunda gimbiya jalila tafara magana yarima yake yimata wani d'an iskan kallon Amma bakida hankali,tana gama magana yaja wani d'an iskan tsaki yamike cikin bacin rai yabar dakin,a ransa yana ayyana cewa lallai gimbiya jalila ta haukace,,,ganin haka yasa gimbiya jalila tamike tsaye idonta akan doctor tace "wannan ba matsala bace doctor zamu dawo Kuma za'ayi dashen",,Gyad'a Kai kawai doctor yayi badon ya yadda zasu dawo din ba don baiga alamar yarima zai amince da hakan ba saboda yanda yaga ya fusata Kuma yasan halinsa. Su muwadda suna inda su gimbiya suka barsu sukaga wucewar yarima sameer kamar a fusace yake,ba'a Jima ba Kuma sai ga gimbiya jalila itama dai kamar tana ckn damuwa,kafin suyi wani yunkuri sukaji muryar ta a tsawace tana fadin "Don ubanku ku mahaukatan ina ne???Uban me kuke jira da baxaku wuce mutafi ba??!!!,dasauri suka rufa mata baya suka fito,suna fitowa suka hango d"aya daga cikin motocin da suka kawosu tafice daga hospital din,ko ba'a fadawa gimbiya jalila ba tasan yarima ne,shiga mota tayi su muwadda ma suka shiga tasu,gimbiya a ranta take fadin "duk abinda xanyi don ganin ka amince zanyi Shi yarima Kuma xaka amince ne,matsala ta daya bansan wa za'ayiwa dashen ba",,Kai tsaye hotel din da suka sauka suka nufa. Yarima sameer ne tsaye gaban mirror yana taje hadadden gashin kansa da ke ta zuba kyalli gimbiya jalila tashigo da alamun itama tayi wanka saboda ta canja kayan jikinta,ta jikin mudubi ya hangota Amma Sam bai nuna yaji shigowar ta ba saima cigaba da shirinsa yayi hankali kwance,ganin haka yasa ta k'araso inda yake tarike turaren da yake fesawa idonta a kanshi,kawar da kanshi yayi tareda sakar mata turaren yadauki wayarsa yana kokarin barin wajen,,dasauri tasha gabanshi idonta taf da kwalla tace "Don girman Allah prince katsaya muyi magana,,Sam baiyi niyyar tsayawa ba Amma jin tace girman Allah yasa yatsaya tareda kafeta da shu'umin idanuwansa Mai dimauta y'ammata,,ajiyar zuciya tayi tanajin yanda kirjinta yake bugawa,dakyar ta saita kanta tace "Mene abin fushi kuma prince??Ai ni a gani na abin farin ciki ne,abinda muka jima Muna nema shekara da shekaru Amma why zakayi haka???,,cikin hasala yarima Sameer yace "Keee karki rainamin hankali nifa ba shashasha bane kuma inada hankali,inason ki fadamin ta yaya su Mai martaba zasu yadda da wanna banzar maganar,,saboda haka yakamata kisan abinda kike fad'a,neman haihuwa ai ba hauka ba ne,sannan ki kwana da sanin gobe zamu koma gida,yakarashe yana kokarin wucewa,dasauri tarikosa tareda sakin wani marayan kuka tana fad'in "prince wannan abin fa ba haramun bane,akanme baxaka tausayamin ba Naga kwaina a duniya,,wlh ina matukar kaunar yara don Allah prince ka tausayawa rayuwa ta karkamin haka,shekara bakwai da aure na fa Amma banda d'an da zankalla naji dad'i,don Allah kayimin wannan alfarmar Naga kwaina d'aya ma Tak a duniya don Allah!!!!!,,,A hankali yacire hannun ta daga rikon da taimasa ganin tana neman sauya Masa ra'ayi saboda jikinsa da yayi sanyi ganin yanda take garshek'en kuka sai tabashi tausayi,Amma da yake namijin duniya ne Sam bai bari ta gane ba illa ma d'an iskan kallon da yabita dashi kafin yarab'a ta gefenta yafice daga d'akin,kwafa gimbiya jalila tayi tana share hawayenta kafin a fili ta furta "Matukar dai ni d'ince jalila dolenka ka amince prince!!!. Su muwadda ne zaune a d'akin hotel d'in da suka sauka,hira sukeyi jefi jefi maganar muwadda bata wuce "Eh" A'a",Saboda gabadaya hankalinta yana kan mahaifiyar ta,tanason sanin halin da suke ciki,tanason jin muryarta Amma ta ina??Tasan dolenta hakuri zatayi har zuwa ranar da zasu koma wadda sudai basu santa ba a matsayinsu na y'an rakiya wadda ba wata k'ima ce dasu ba,,ajiyar zuciya tayi kafin tamike cikin zazzak'ar muryarta tace "Zan d'an fita waje",,Nasiba ce tace "Ai Kam dai kwara kid'an fita kiga yanayin wajen Amma da kin kule a d'aki kink'i motsi,,hmm Koda yake halinki ne haka Sai kace wata jinin sarauta",,,gajeren murmushi muwadda tayi batareda tace komai ba tafita daga d'akin,don inda sabo ta Saba da yanda mutane suke cewa Wai idan tana Abu tamkar jinin sarauta ,jin Kai tareda Shan kamshi,Wanda ita a zahiri batamasan tana da su ba. Tafiya takeyi Amma gabadaya hankalinta bayaga tafiyar,don kallon da tafito yi Sam bashi takeyi ba,,batai aune ba taji tayi karo da mutum ,,dasauri ta tsugunna sakamakon wayar wadda sukai karo da Shi da ta subuce ta fad'i,,dai² lokacin shima yakai hannu zai dauki wayar,,haduwar hannuwansu ne yasa muwadda dagowa dasauri Saboda wani shock da taji,tareda wani mugun laushi na kyakykyawan hannun gami da sassanyan kamshi da yake tashi,,ido hudu sukayi da *YARIMA SAMEER* Wanda yai sanadiyyar bugawar kirjinsu lokaci guda,a Matukar tsorace muwadda tamike cikin rawar murya tace "Don girma Allah yarima kayi hakuri wlh bansani ba,,,batare da yarima ya kalleta ba balle ya kulata yaja dogon tsaki Yana karewa hannunsa kallo tareda yatsina fuska ,jiyake kamar ya shaketa Saboda takaicin goguwar hannunta da nashi,ganin haka yasa muwadda taci gaba da fad'in "Don Allah ka tausayamin ranka Shi dad'e wlh....."Kee!!!! "Yarima yakatseta a tsawace Wanda yasa muwadda zubewa dasauri jikinta yana rawa,ckn hasala yace "Ke wace iriyar mahaukaciya ce mara nutsuwa????Baki iya magana d'aya ba ne??Kindamu mutane da surutu da wani k'azamin banzan bakin ki,mtsewww yaja tsaki yabar wajen,,,Cikin tsantsae takaici muwadda tamike tana share hawayen da yake tsere a kumatun ta,itakam Sam a rayuwa tarasa meyasa masu mulki suke son yiwa na kasansu wulakanci,sunason k'ask'antar dasu su a dole sun fisu,,jitayi gabadaya ma baxata iya fitar ba,jiki a sanyaye takoma d'akin su. Yarima kuwa yaja tsaki yafi cikin kwando,,gabadaya ma kyankyamin hannunsa yakeyi,d'aki yakoma inda ya tadda gimbiya jalila tanata kwasar baccin ta, bathroom yafad'a,yashiga wanka,dirje hannun yadingayi sosai tamkar zai sauya wani,yanayi yana yatsina fuska yana jan tsaki,,yadauki lokaci me tsawo kafin yabarshi haka badon ya yadda yafita yanda yake so ba,,fitowa yayi d'aure da towel hannunsa Kuma wani karami ne sky blue colour Yana goge lallausan gashin kanshi dashi,,shiryawa yashigayi lakwai² skin tamkar wata gold,yadauki lokaci kafin yashirya cikin wasu hadaddun riga da wando yasa masu tsananin kyau da tsada,red nd black colour,sannan yadora jacket a sama,,kamshin sassanyan turaren sa ne ya farkar da gimbiya jalila,,a hankali ta bude idonta tana k'are masa kallo,,wata iriyar muguwar kaunarsa takeji a kowani sassa na jikinta,,a hankali ta zuro k'afafunta tasauko,ra mirror ya hangota Amma bai juyaba,tana zuwa tayi hugging dinsa ta baya ckn iyayi tace "My prince kayi kyau da yawa fa",,Gajeran murmushin sa yayi tareda mirginota tadawo gabanshi,ckn kulawa yace "Kema haka",,Dariya tayi tana k'ara makalkaleshi,ganin lokacin salla yayi ne yasashi zameta Yana fadin "Kije kiyi wanka Kema ni zanyi salla ne",,Dasauri ta rikoshi tasa gwuiwowinra a k'asa tana hawaye tace "Wannan Shi ne karon farko da natab'a neman alfarmarka a rayuwa ta prince,,idan bakayimin va wlh bakin ciki zai iya kasheni,,Zan koma ga mahalicci na da Wannan tabon na kunci,don Allah ka tausayamin ka amince tunda ba haramun ba ne,ko ckn sirri zamuyi abinmu babu Wanda zai sani,wlh zanyi yanda kowa zaiyi tunanin nice na haihu da kaina,,Wannan sirrinmu ne mu kad'ai,,,"Ita Kuma wadda za'ayiwa dashen fa???yajefa mata tambayar,,Dasauri tace "Zatasani Mana prince",,Idonsa a kanta yace "Wace ce ita????cikin zumud'i tace zansamo wlh prince Zan samo,,mikewa yayi yadauki dadduma yatada sallah don matuka karshe tabashi tausayi Kuma ta raunata mishi zuciya tayaji tayi zancen mutuwa,shiyasa har yakejin zai amince,musamman da gimbiya jalila tace Masa zasu iyayi a sirrance har ace itace ta haihu batare da me martaba da kowa yasani ba. Ita kuwa gimbiya jalila kamar tayi hauka Saboda farin ciki,don yarima Yana sallah tana zuba tsalle,hangota takeyi kawai gata rike da baby,,addu'a tashiga you Allah yabasu namiji don Shi tafi so tunda sune masu mulki,,tunani tashigayi wadda za'ayiwa dashen,tanason yarinyar taxama kyakykawa,me hankali,me nutsuwa,uwa uba shiru me sirri,,tunani tashigayi a kaf bayin masarautar su Wace tahad'a siffofinnan,,naxari tashigayi Amma a iya tunaninta tagaxa samu,lokaci guda zuciyarta tabata *KUYANGA MUWADDA!!!*,,,A fili ta maimaita tabbas muwadda itace yarinya me tsananin sirri tareda tsoro,baxata taba tona sirrin ba,,mikewa tayi ckn farin ciki tana tsalle tashiga bathroom yin wanka. Bayan gimbiya jalila tayi wanka tafito tashirya tayi sallah,,sunacin abinci da yarima tanata zubamasa hira Saboda tsananin farin cikin da take ciki,sanar masa tayi yarinyar da ta yanke shawara a kanta,,wani d'an iskan kallon bakida hankali ta wurga Mata,,cikin kissa tashiga yimasa abubuwa tana fad'a Masa dalilanta,da yaduba Kuma Sai yaga gsky tafad'a,,Amma Shi Sam baiso haka ba Saboda baya kaunar ko ganin muwadda Sam,,a Daren ranar suka Kira doctor suka sanar dashi,sosai yayi mamaki kafin yace gobe da karfe 11 na safe suzo da yarinyar ayi aikin tunda tashin yamma zasuyi,,a ranar gimbiya jalila tamkar ta zuba ruwa a k'asa Tasha Saboda farin ciki,,yarima Sameer kuwa yaga tsantsar soyayya tamkar zata cinyeshi a daren ranar. *Plz kutayani addu'a Allah ya shirye ni nadinga typing akan lokaci🤪🤪don wlh naxama lazy wajen typing ynz😰* ```Typing error zaku iya cin karo da Shi don bansamu damar editing ba```shi.*'YANCIN BAYI* {Historical fiction} ➰ *STORY WRITTEN BY*✍🏻 *SURAYYERH B.ABDUL* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ Page d'innan kyauta ne gareki *MUNAYAH* ta Kainuwa fitatttu,ina ganin comments d'inki kuma yana sani nishad'i,godiya tik'a tik'a. *PAGE 12* Wata kuyanga ce tayi sallama ta shigo parlour'n,cikn girmamawa ta zube a k'asa ta ce "Ranka shi dad'e yarima Yusufu ne ya ce yana so a mashi iso wajen ka",sai da ya b'ata lokaci kamar ba zaiyi magana ba sannan ya ce "A shigo da shi",godiya kuyangar ta yi sannan ta fice. Da sallama yarima Yusufu ya shigo fuskarsa d'auke da murmushin da ya zame masa jiki, tasowa yarima Sameer yayi sukayi hugging juna cikn farin ciki,zama sukayi a had'ad'd'un kujerun da suka yiwa parlour'n k'awanya, yarima Yusufu ne ya kalli wajen da gimbiya Jalila take tana cin abinci,cikn tsokanarsa ya ce "Ahhh matar prince don kar na ce zan ci abincin ne ya sa aka k'i yimin magana?,tab'e baki ta d'anyi kafin ta yamutsa fuska,murya k'asa² ta ce "ya kake?, ba yarima Yusufu kad'ai ba kaf d'insu sun ga abin da tayi,amma dayake me sanyin hali ne shi kawai sai ya basar ya ce "ina lpy",. Mik'ewa tayi tareda k'arasawa kusa da yarima Sameer tana wani iyayi ta ce "My prince zan je gidansu yarinyar can ynz",ta fad'a tana nuna Muwadda wacce ta juya bayanta tana kwashe kayan abinci, ba'a ganin fuskarta ta b'angaren da su yarima Yusufu suke,shiyasa ma sam bai ganta ba. Yarima Sameer ya ji haushi da tayi masa maganar a gaban yarima yusufu amma ganin yarima yusufu'n ya sa ya gyad'a mata kai kawai alamun to,peck tai masa a kumatu kafin ta fice. Juyowa Muwadda tayi da niyyar kai kaya kitchen, karaf suka had'a ido da yarima Yusufu,ta d'an tsorata da ganin shi don tana tsoron ya ja mata fitina,shiyasa tayi saurin kauda kanta ta fara tafiya,yarima yusufu da gabad'aya ya d'imauce da ganin Muwadda,wani irin abu yake ji yana fuzgarsa da k'arfin gaske game da ita,zuwa ynz ya tabbatarwa kansa zuciyarsa son Muwadda take yi,kuma da k'arfin gaske,shiyasa ya d'aura d'amarar d'auka tare da rungumar duk wani tashin hankali da zai tunkareshi a hanyarsa ta mallakar ta ,saboda ya riga ya sani ba k'aramin tashin hankali za'a yiba da mahaifan shi a matsayinsa na yarima yace wai zai auri baiwa,tab'osa d'in da yarima Sameer yayi ne ya sashi juyowa da sauri yana murmushi,shi ma yarima Sameer d'in murmushi yayi cikin k'aunar k'anin nasa ya ce "yadai?",sosa k'eya yarima Yusufu yayi kafin ya d'aga ido sama cikin shaukin soyayya ya ce "Wlh ina matuk'ar k'aunar ta",da sauri yarima Sameer yace "Wa kenan?",batare da ya bashi amsa ba ya juyo ya rik'e hannuwansa duka biyun ckn raunin murya yace "Wlh komai zan iya a kanta shiyasa nake tausayawa kaina,ban san cewa haka zafin so yake ba sai a kanta,don Allah yayana inason idan lokaci yayi ka taimake ni ka jajirce wajen ganin na mallake ta, shi ne mafi girman so da za ka nunamin a rayuwata saboda ita ce rayuwata". Cikin tsokana yarima Sameer ya ce "Tabd'ijan!,wace ce wannan k'atuwar b'arauniyar da take neman rikitamin k'ani haka?,kuma y'ar wani sarki ce da kake tunanin aurenta zai zo maka da matsala?. Mikewa yarima Yusufu yayi tare da riko hannun yarima Sameer ya mik'ar da shi sannan ya ce "za ka santa yayana da zarar lokaci yayi,sai dai abu d'aya da zan fad'a maka shi ne yarinyar ba y'ar gidan kowa bace face y'ar talakawa,talakwan ma fitik,shiyasa nakeson ka tsayamin akan aurenta,wani irin kallon tausayi da mamaki yarima Sameer yakebin yarima yusufu dashi,kafin yace "Amma dai k'ani na da wasa kakeyi ko?,y'ar talakawa fa kace?,Shiru yarima yusufu yayi,sbd haka yarima Sameer yaci gaba da magana,"a gaskiya kusan zan iya cewa zuciyar ka batai maka adalci ba da tarasa wadda zataso sai y'ar talakawa,meye haka?kana hauka ne?,to wlh kayi gaggawar cireta a rai saboda sanin kanka ne me martaba da umma bazasu tab'a yadda ka auri y'ar talakawa ba,me zakayi da ita?,ga y'ay'an sarakuna nan da dama wad'anda suke sonka amma zaka ce kana son wata y'ar talakawa?. Zuciyar yarima yusufu ce takai kololuwa wajen b'aci,har wani tafarfasa k'irjinsa yake,lokaci d'aya ya harzuk'a,a fusace yace "y'ay'an sarakunan da kake magana akansu wlh babu wacce takama yatsan y'ar talakawar a daraja da Kama kai,banda tak'ama da rashin kunya me y'ay'an sarakunan suka ajiye?,murmushin takaici yayi kafin yace "Nariga nayi d'amarar duk wani tashin hankali dazai tunkare ni a kanta,kasa ido kayi kallo",yak'arasa a fusace yana k'ok'arin barin d'akin,muryar yarima Sameer yaji yana fad'in"Tabbas zaka jawa yarinyar babban bala'i a garin nan kuwa", dasauri yajuyo idonsa yayi jajir,ckn b'acin rai matsananci yace "Wlh matuk'ar hakan ta faru kusa a ranku kun rasa ni!!!,yana gama fad'in haka yabar d'akin a fusace. Jagwab yarima Sameer yazauna a kujera tareda dafe kansa,ya Salam!,ya furta a fili tareda fuzgar da zazzafar iska,tabbas ya tabbatarwa kansa yarima yusufu yayi nisa,tashin hankalin da zai riskeshi kawai yake jiyemasa,yasan halin me martaba ciki da bai,shikam yarasa ta inda zai b'ullowa matsalar,yasan yarima yusufu yanada matuk'ar sanyin hali amma idan ranshi ya b'aci yanada kafiya da taurin kai sosai,Sam baya tsoron koma mene,tausayin k'anin nashi ne yakamashi sosai sbd Allah yasani yana matuk'ar k'aunar shi,jingina kansa yayi da kujera yana tunanin ta inda zai b'ullowa matsalar, gabad'aya yama manta da gimbiya jalila ta tafi gidansu muwadda. Muwadda kuwa tana kwashe kayan abincin takai kitchen bata dawo ba tabi ta k'ofar baya,gurin tsaunin da ta saba zama ta nufa,tana tafe tana tunanin yarima yusufu yaushe rabon taganshi,muryar ubaida tajiyo tana Kiran muwadda!muwadda!!,juyowa tayi fuskarta d'auke da murmushi,k'arasowa ubaida tayi tana haki tace "Way..yo Allah na gsky nasha gudu,Kai muwadda Kinga yanda kikai kyau kuwa?,dungure kan ubaida muwadda tayi tana murmushi tace "Zaki fara surutun naki ko?",dariya ubaida tayi tace "wlh dgsk,gsky India ta karb'eki,kinsanme?,gyad'a Kai muwadda tayi alamun a'a,jan hannunta ubaida tayi tace muje muzauna kiji,nan suka nufi kan tsaunin suka zauna suna fuskantar juna,ckn dariya ubaida tace "Kee wlh wani mafarki nayi Wai kina zaune akan wata tamfatsetsiyar kujera me tsananin kyawun gaske wadda nidai idan nace zan kwatanta miki yanzu wlh nayi k'arya,kina sanye da wasu irin kaya na sarauta masu tsananin kyawu,alkyabbar ki sai zuba kyalli take,kyakykyawar fuskarki tana fidda wani irin annuri,fad'in kyaun da kikayi k'arya ne,wata yarinya nagani me tsananin kyau babu inda ta baro kamarki ko kad'an ta taho da gudu ckn gwarancinta na yara tana fad'in Ammi!Ammi Kinga Abbu zai kwace min sweet yaba boy ko?,sai Kika d'aga yarinyar dasauri sama kina dariya,dai²lkcn kyakykyawan mutumin da nake tunanin mahaifinta ne yashigo hannunsa d'auke da wani kyakykyawan yaro shima me masifar Kama dashi sak,gyara zama ubaida tayi tana murmushi tace ga mamaki na sai naga ashe mahaifin yaran nan ba kowa bane bace......dasauri muwadda ta katse ubaida ta hanyar cewa "Don Allah ubaida karki fad'amin,mafarki ai ba gaskiya ba ne, ni ubaida abinda ke damuna wlh yau tunda na tashi kirjina yake wani irin mugun fad'uwa,Allah dai yasa ba wani abu mara kyau ne zai faru da ni ba😞,ckn lallashi ubaida ta dafa kafad'arta tace "Kar kisa wannan a ranki muwadda inshallah babu komai kinji?",gyad'a kai tayi tace ameen,haka suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin d'ora girkin rana yayi ubaida taiwa muwadda sallama don ita ynz tunda an y'anta ta aikin kud'i takeyi sab'anin muwadda,har suka rabu muwadda bata ji bugun k'irjinta yadaina ba. A b'angaren gimbiya jalila kuwa tana fita takira Jakadiya tasa aka had'amata bayi guda biyar,ita kad'ai tashiga mota sai me tuk'i, yayinda bayin suke tafiya a k'asa tunda motar a hankali² take tafiya,basu jimaba suka isa gdnsu muwadda tunda dama basuda nisa sosai tsakanin su. Kamar kullum iya na zaune a d'akin ta tana tunanin duniya da gudaliyar y'arta taga shigowar bayi guda biyu da k'atuwar dadduma sun shimfid'a a tsakar gidan,bata tsinke da lamarinsu ba saida taga sun d'auko turare sun shiga feshe gidan dashi,sannan suka d'auko na tsinke suka kunna suka saka,ganin suna Shirin fita ne yasa ta d'aga murya tace "Bayin Allah lpy?,suwaye ku?,basu tsaya bata amsa ba suka fice,ckn matsanancin mamaki tace "Me kenan hakan?",sukuma wad'annan fa?. Gimbiya jalila ce tashigo cikin takun k'asaita da isa ,tana wani yatsina fuska kamar wacce taga kashi,bayinta na take mata baya,yayinda mutum biyu ke rik'e da wata had'ad'd'iyar kujera,ganin gimbiya jalila ba k'aramin firgita iya yayi ba,don kad'an yarage fitsari ya kwace mata saboda tashin hankalin da ta shiga,duk a zatonta wani abu ne yasamu muwadda,da ace k'afafunta lafiyarsu k'alau ta tabbata saita mike a zabure,ckn kula ta fara fad'in "Don Allah karku cemin wani abu yasamu d'iyata. K'arasowa gimbiya jalila tayi ckn d'akin bayan ansa mata kujera ta kame tareda d'ora k'afa d'aya kan d'aya,da ido tayiwa kuyangin alamun subasu waje,a take suka fice. Juyowa tayi ta kalli iya tana wani irin murmushin mugunta tace "Yadai daga gani na sai tsorata?,to ni ba wani abu zanyi miki ba umarni kawai nazo baki,ckn kuka iya tace "Umarnin me?,Murmushi tasakeyi karo na biyu sannan tace "Daga yau inaso kisani y'arki muwadda tadawo da zama a hannu na nawani lokaci,ba ina nufin narik'eta har abada kenan ba,dukda hakanma idan naso zanyi,amma bana buk'atar hakan,a b'angaren kula da ke Kuma zankawo masu miki komai,ke hatta wannan k'azamar cimar taku zaki rabu da ita,idan tagama min aiki na tadawo kisani tadawo kenan don a lokacin zan y'anta ta,Kuma zanmata kyauta badon ta isa ba sai don ganin dama ta,karkiga nazo sanar miki da kaina kiyi tunanin kin isa ne,a'a nazo ne saboda maganar nan sirri ce banason kowa yasani,idan har kikaimin gardama to zakisha wuya ne sannan Kuma narik'e y'arki ko bakyaso,gwarama karki b'atawa kanki lokaci ki amince kisawa kanki hakuri don ni banda niyyar cutar da y'arki,zata dawo lpy amma fa idan kinso. Tunda gimbiya jalila tafara magana iya take wani irin kuka me tab'a zuciya,tasan su gimbiya jalila basuda imani,abinda tafad'a zata aikata harma wanda bata fad'a ba,shiyasa tayi saurin bawa zuciyarta hakuri sbd batason wani abu yasami y'arta,tana fatan Allah yabasu dangana har zuwa lokacin da zasu sake ganawa,ckn kuka tace "Na amince!!,Amma kiji tsoron Allah karki cutar da ita,kallon wulakanci gimbiya jalila taiwa iya tareda fad'in "Sanin kanki ne inda zan cutar da ita kinyi kad'an na b'oye miki ai,dasauri iya tace "Allah ya huci zuciyar ki tuba nake",mik'ewa gimbiya jalila tayi tace "da anjima masu kula da ke zasuzo tare da kayan abincin,gdy iya tayi sannan gimbiya jalila tafita bayan tasake jawa iya kunne akan karta kuskura tayi gangancin fad'awa wani. Suna tafiya iya tafashe da kuka tana wasu irin surutai,addu'a takeyi akan Allah ya tsare Mata y'arta a kowani irin aiki need da zatayi,har gimbiya jalila takoma gida ta turo masu kula da iya,manyan mata guda 2,ga tulin kayan abinci na zamani,amma har lokacin kuka take. Muwadda na tsaye a dinning tana shirya abincin dare datayi gimbiya jalila tazo,dasauri ta durk'usa ta gaisheta,batare da ta amsa ba tace biyoni,ba musu tabi bayanta,sunyi y'ar tafiya me nisa kafin suzo wani d'aki, gimbiya jalila ce tabud'e tashiga sannan muwadda tabi bayanta. D'aki ne madaidaici me kyau tareda band'aki da kitchen a ciki,babu wasu tarkace,gado ne sai sif sai wani k'aramin fridge da fankar k'asa,sai wata katifa sabuwa a gefe,d'akin gwanin burgewa,juyowa gimbiya jalila tayi takalli muwadda wadda ta sunkuyar da kai k'asa tana jiran taji umarnin da gimbiya zata bata,kamar daga sama tajiyo muryar gimbiya jalila tana fad'in "Daga yau wannan shi ne d'akin da zaki dinga kwana,saboda kindawo kwana a gdnnan zuwa wani lokaci!!". Dasauri muwadda ta d'ago cikin tashin hankalin da ya wuce misali tace "Nadawo kwana a gdnnan fa kikace??mahaifiya ta fa??,ckn halin ko inkula gimbiya jalila tace "Natura me kula da ita,don a k'alla zaki shafe kusan shekara a gdnnan batare da kinfita kinganta ba,ke ko harabar gidannan sai naso zaki fita. Wani irin mugun kuka muwadda tasaki ckn tashin hankali take fad'in "Wai ku wani irin muta ne ne da kanku kad'ai kuka sani?,mahaifi na yarasu ta sanadiyyar kula da ku,mahaifiya ta ta nakasa ta sanadiyyar kula da ku,nima haka kukeso nak'are rayuwata cikin kula da ku?,shikenan banda lokacin mahaifiya ta?,karku manta bafa siyo mu kuka....maganar ce ta mak'ale sakamakon d'auke war da numfashinta yake k'ok'arin yi,lokaci guda tayi baya zata zube,dasauri gimbiya jalila tarik'ota tafad'o jikinta a sume. *WAI SHIN MENE NE TARIHIN SU MUWADDA A MASARAUTAR ZINARI?,WANI DALILI NE YAI SANADIN MUTUWAR MAHAIFINTA?,MENE SANADIN CIWON K'AFAR MAHAIFIYARTA?* ```Ku biyo ni a shafi nagaba domin jin answer wannan tambaya.``` An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels