An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»ΏAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ 2/1/20, 5:08 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ Page 1 πŸ”œ _Alhamdulillah dukkan godiya yanaga Allah daya sake bani aron lokaci domin rubuta DAN DAUDU KO DAN LUWADI wanda na dad'e inaso na rubuta saidai abubuwa sukasha kaina_ _Labari ne daya k'unshi fad'akarwa, ilimantarwa, zaburarwa, gami da nishad'arwa hardama soyayyah._ _ina fatan Allah yabani ikon rubuta abunda zamu k'aru dashi, ya haneni rubuta abunda zai zamo silar lalacewar mu, ina fatan idan kun karanta kuyi aiki dashi musamman iyaye mata da matasa._ *Ina maraba da dukka masoyana a duk inda suke a fad'in duniya, harma mak'iyana ina alfahari dasu sai dai ina rok'on Allah yayi mun tsari da sharrin su* Don Allah duk wacce takaranta tayi share basai anyi nisa kuyi ta cewa daga farko ba plxπŸ™ ✍ SABITU kyakkyawan saurayi ne matashi wanda a k'alla zai kai shekaru 27, zaune suke shida abokan sa'idon sa a bakin titi jikin shagon abokin su, kullum anan suke wuni sa'ido kasancewar basuda wani sana'ar yi, duk wanda yazo wuce wa sai sun tofa albarkacin bakin su, ko mota ce ta wuce sai sunyi magana akanta kullum aikin kenan. Yauma kamar kullum zaune suke sun jeru akan bencin dake jikin shagon, wata dalleliyar motace ta tsaya a gabansu, dagani kasan kud'in ta ta zarce tunani, sake baki Sabitu yayi yana ayyanawa a ranshi inama shine a cikin wannan motar, har hangoshi yayi tare da sabowar budurwar shi aciki suna zaga gari, don dama Sabitu badai neman mata ba, zungurin da abokinsa Nasir yayi masa ne ya dawo dashi daga duniyar tunani. "kai d'an iska tunanin me kakeyi ne haka". Nasir yafad'a idon shi akan motar, burin su suga wani hamshak'in ne aciki, duk sun zuba ido burin su suga mutumin dazai fito aciki, koma yayane dai sun san ba k'aramin mutum bane. Sabitu ya bud'e baki zaiyi magana wata had'add'iyar budurwa ta fito aciki, gaba d'aya zuba ido sukayi harda hanci suka kasa motsi domin ba k'arya ta had'u iya had'uwa. A gabansu ta tsaya muryar ta ashak'e kamar me mura ta ce "don Allah ina tambaya ne"! Da sauri Nasir ya ce "kiyi tambayar ki domin babu wanda bamu sani ba a anguwar nan". Taji dad'in amsar don haka ta ce "Alhaji Ma'aruf! Ko kunsan gidan shi"? Ai kafin wani yayi magana Sabitu ya amshe da fad'in mak'wabcina ne muje nakai ki har gidan shi". Nasir najin haka ya ce shima wlh sai yaje don Sabitu bazaiyi rakiya shi kad'ai ba, sauran nata washe baki sunga had'add'iyar budurwa. Wani irin k'amshi me dad'i motar take fitarwa, gaba d'aya sun shagala ganin cikin motar komi nata daban, duk gayu irinna Sabitu yau yayi mummunan raina gayun nashi. Har k'ofar gidan suka kai ta, Sabitu duk shi ke kwatancen gidan, Alhaji Ma'aruf shima babban mutum ne duk anguwar ba wanda yakaishi arziki. Wani irin kallo me wuyar fassarawa budurwar ta jefi Sabitu dashi wanda sai da tsik'ar jikin shi ta tashi, murmushi ta sakar mishi a karo na farko cike da jan hankali ta ce "Nagode k'warai, sai dai baku fad'amun sunan ku ba". Sabitu da duk jikinshi ya mutu kasa magana yayi, sai Nasir ne ya koro mata sunayen su. Juya ido tayi ta ce "Malam Sabitu sakamun Numbanka anan". Ta fad'a tana mik'a mishi tsadadden wayarta, kafin kace kobo ya karb'a ya jera numbansa, bata sake kallon su ta shige gidan ba tare da ko godiya ba. Jingina Sabitu yayi da katangar gidan yana sauk'e numfashi, Nasir ya ce "yaya dai mutumin, duk naga ka narke". Murmushi Nasir yayi ya ce "kaje gida ka sauk'e gajiya domin nasan halinka, yanzu haka jarabar ce ta motsa daganin jan jiki". Ya k'arasa maganar yana dariya, tsuka Sabitu yayi yana harararsa sannan ya wuce abunshi yana tunanin 'yar budurwannan. Gidan fess k'amshi sai tashi yakeyi, ko sallama beyi ba ya shiga falon nasu, Suwaiba dake kallo a d'an k'aramin Tv ta d'aga kai tana kallonshi, tab'e baki tayi ta ce "jarabebbe wlh yau kam ba'a kaina zaka sauk'e ba, kaje can ka k'arata". Uban tsuka Sabitu yaja sannan ya wuceta ya shige d'akin barcin su, gaba d'aya Netwok d'inshi ta daina aiki, burinshi kawai yaji service a tare dashi, lumshe idanuwa yayi yana tunanin wace zai k'ira ta rage masa zafi, domin Sabitu bashi da hak'uri ko kad'an, an aura masa Suwaiba amma sam bata isarsa, hasalima kullum cikin fad'a suke. Juyin da zaiyi yaji wayarsa tana kuwwa, ganin bak'uwar numba yasa bai d'aga da wuri ba, harta kusa katsewa sannan ya d'aga. "Sunana Saleema, ana k'irana da Leema". Yaji amfad'a da shak'ekken murya kamar na budurwar d'azu, d'an lumshe ido yayi domin baisan meyasa ba muryarta bata mishi dad'i, amma ita d'in ta had'u sosai, kusanma bai tab'a ganin me kyawun halitta irinta ba. Cikin sanyin murya ya ce "ban gane wacce take magana ba". Wani iska ta hura cikin jan hankali ta ce "wacce kukayi wa rakiya d'azu, na k'irane nace maka nagode". Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk'e. "Haba godiya kamar wani aiki". "Aiki ne mana tunda na tayar daku kuna hutawa". D'an dariya Sabitu yayi ya ce "aikin da mukayi ai yafi zaman banzan". Salima tayi murmushi na kazo hanu yaro, "baka tambayeni meyasa na karb'a numbanka ba"? Gyara kwanciya yayi yana tunano irin daular daya gani tattare da ita amma harta iya magana dashi yana talaka, talakanma wanda ko ciyar dakan shi baya iya yi, hatta kayan sawarsa mahaifiyar sa ke d'inka masa... Tunaninsa ya katse da yaji tana cewa "tunda naganka naji nakamu da sonka". Wani wawan runguma yayi wa pilow ya ce "me kikace"? Dariya tayi ta ce "kazo da dare muyi magana". Zumud'i ya kashe Sabitu baima san ta kashe wayarba, wani mahaukacin ihu yayi dayasa Suwaiba shiga d'akin da gudu, ganin ihun farinciki ne yasa taja ta tsaya tana takaici, yanzu hakan akan mace yake wannan ihun, mtsss taja tsuka ta ce "kadai sa Allah a ranka Sabitu, ina rabaka da d'aukan alhakina". Ko kallon ta beyi ba ya mirgina yayi rub da ciki yana murmushi. 2/1/20, 5:08 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 2 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ _Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga mu'ata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_ ✍ Wanka Sabitu yayi na kece raini, ba laifi yayi kyau sosai, Suwaiba sai kallon shi takeyi ba bakin magana, tana son mijinta sosai amma rayuwarshi yana bata haushi, kallonta yayi ya ce "kin kafeni da ido, ina fatan ba hanani fita zakiyi ba"? Haushi ya kamata ta ce "ina ruwana da fitarka, Allah ya had'aka da aljanar dare". Dariya yayi Sabitu yayi ya ce "indai macece aljanar ta kwana gidan sauk'i". Fuskar shi fal dariya ya fita, hawayene ya gangaro a fuskar Suwaiba, a fili ta ce "dole na nemar wa kaina mafita, ga talauci ga rashin kulawa ga neman mata, da wanne zanji". Kuka ta fashe dashi kamar koda yaushe. Gidan Alhaji Ma'aruf ya nufa, tun daga nesa kana hango hasken wutan lantarki daya zagaye gidan duk da kasancewar babu wutan nepa a lokacin, wayar shi ya ciro ya danna k'iran Saleema, wacce yayi saven da Leema, sai da yak'ira sau biyu kafin ta d'aga, muryarta me bashi haushi yaji tana cewa "ka iso ne masoyi"? "Na iso". Ya fad'a yana takaicin jin muryar. Minti 2 tsakani tafito harabar gidan, umurni tayi wa megadi akan ya shigo da Sabitu cikin gidan. Har Falon Alhaji Ma'aruf aka kai Sabitu, sai zare ido yakeyi yana ganin had'uwar wajen, "gaskiya kud'i yayi a rayuwa". Ya fad'a a ranshi. Alhaji Ma'aruf ya hango cikin kujera, gefensa Saleema ce zaune tana tsiyaya ruwa a cup, wani yawu ya had'iye ganin shigarta, dogon riga ta saka amma duk halittar yanayin jikin ta a bayyane, komi motsawa yakeyi, take kanshi ya d'au caji, tunda ya shiga Alhaji Ma'aruf ya kafe shi da ido yana wani irin murmushi. Muryar Saleema ya tsink'aya tana ce wa "k'araso ku gaisa da kawuna Masoyi". Tafiya yake kamar me sand'a, sunkuya wa yayi a gaban Alhaji Ma'aruf yace "Barka da dare alhaji". Memakon ya amsa sai hanunshi ya mik'a mishi alamar musabaha zasuyi, da sauri Sabitu ya mik'a mishi yana sunkuyar dakai kaman mumini, wani irin damk'a yayi wa hanun Sabitu daya sashi d'agowa da sauri, gani yayi Alhaji fa ya wani lumshe ido. Murmushi Saleema tayi ta janyo Sabitu ta ce "masoyi muje muyi magana". Kunya duk ta kama Alhaji ya wayince yana susa kai. Tana rik'e da hanun Sabitu suka b'ulla wani k'aramin Falo, hanunta laushi kamar auduga don haka Sabitu yayi ta matsawa a hankali. Sai da ta zaunar dashi sannan ta ce "ka saki jikin ka nan gidan kawuna ne, nan part d'inshi ne, part d'in matan shi yana sama". Kan Sabitu ya d'aure yana tunanin meyasa Saleema bata kaishi saman ba toh, kamar tasan tunanin da yakeyi ta ce "hayaniya yayi yawa acan shiyasa na rok'eshi ya bamu aron nan. *GARIN GOMBE* Farar yarinya ce wacce bazata wuce shekaru 6 ba, shinkafa da mai da yaji takeci wanda ta zuba yaji har abincin yayi jaa, tana ci tana shushutu, zafin yajin yasa da k'yar take magana. "Innah yaushe Yaya Saleem zai zo ne". Innah ta dungure mata kai cikin takaici ta ce "ban sani ba ja'ira, ina raba ki da cin yaji taurin kunne ya miki yawa". Zunb'ura baki Elham tayi tafara gunguni, ganin ranta ya b'aci Innah ta hau dariya tana rarrashin ta. *************** Hira sukayi ba wani me yawa ba Sabitu ya tafi cikin farinciki domin Salima tayi masa alk'awarin zata aure shi, kai tsaye gidan Umman shi ya nufa, tana kishingid'e ta fara bacci taji Sallamar tilon d'an nata, zama ta gyara tana washe baki ganin yanda yayi kyau. "ina aka fito haka naji sai k'amshi kakeyi". Ta fad'a tana matsa mishi gefen ta alamun ya zauna, zama yayi ajikinta lamar k'aramin yaro yace "daga gida nake Umma, Suwaiba ma tana gaishe ki". Tayi dariyar jin dad'i ta ce "lafiyan ta k'alau ko, Allah yasa dai kana kula da 'yar mutane, kasan mutanennan sun maka gata". Rausaya kai yayi kalan tausayi ya ce "haba Ummah, bazaki tambaya ko ina jin dad'in zama da itaba sai kiyi ta cewa ina mata wani abun". Kama baki tayi tana kallon shi. "Yoh dan ubanka wazan tambaya". "to Umma ni ba wannan ba, dama nazo nafad'a miki ne aure zan k'ara". Tsananin mamaki yasa Umma sake baki tana kallon shi, b'acin rai fal ranta ta ce "Sabitu kasan me kake fad'a kuwa? Ka kiyayeni fa, tashi ka tafi tun kafin raina yagama b'aci". Sum sum ya tashi yafita yana k'ananun magana. Sai kunjini anjuma 2/1/20, 5:08 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 3 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ *Na sadauk'ar da wannan page d'in ga _AISHA BICHIKI FANS_ da _BICHIKI HAUSA NOVELS_* *KUCI GABA DA CMMNT AISHA BICHIKI TAKU CE* ✍ Tun safe take zun b'ura baki Innah ta kasa gane kanta, fushi takeyi sosai k'iris take jira ta fashe da kuka. "Elhaman Innah me kike so ne, wannan b'ata ran duk na menene, kina so Inna ta shiga damuwa ne"? Turo baki Elham tayi ta ce "ki kaini gidan Uncle". Kamota Innah tayi gami da d'aurata a cinya ta ce "shine kike b'ata rai, ki karya maza yau ana tashi a makaranta zan kai ki can". Tsalle ta farayi a jikin Innah tana kai mata kiss ta ko ina, kallon yarinyar Innah keyi tana murmushi, ganin ta fara hajijiya ta ce "kinga zo na shafa miki mai ki tafi kada kiyi latti. Innah tana shafa mata mai tana ta tsalle irinna k'ananun yara, Uniform ta sanya mata ta rayata ya mata jakarta sannan ta kamo fuskarta ta tofa mata addua. "ki kula banda wasa kiyi karatu sosai kinji". Kai ta d'aga tana murmushi, har k'ofar gida Innah ta rakata tana mata adduan adawo lafiya, dayake makarantar ba nisa nan da nan ta isa, kwata kwata su 15 ne a ajinsu, ko wani d'alibi da wajen zamansa, wajen zaman Elham na gaba kasancewar tafi kowa k'okari a ajin, tana shiga Auntyn su ta shiga, yawancin karatun nasu da wak'a ake musu shiyasa nanda nan sun d'auka kasancewar su 'yan Nuesury. Ana tashi brck ta cilla da gudu tayi gida, Inna dake hura wuta taji motsin shigowar ta, da hanzari ta bita d'aki tana mamaki yau me yasa suka tashi da wuri, tun kafin Innah tayi magana ta ce "Innah yau da wuri aka tashe mu saboda sun san zanje gidan Aunty Khairat". Salati Innah tayi ta kamo kunnen ta tace "Elham ba na hanaki k'arya ba, saboda kawai zakije wani waje sai a tashe ku? To ko shugaban makarantar iya kaci, kuma nafasa kaiki kiyi maza ki koma makaranta Jaka da hijabin ta cire ta fara birgima tana kuka, sanin halin ta na kafiya ya sa Inna ta ciro wayarta a bakin zaki ta shiga lalub'o Numban Sameer. Da kukan Elham ya fara cin karo ta cikin wayar, d'an murmusa wa yayi ya ce "Innah ina kwana". Katse shi tayi ta ce "kazo ka d'auki wannan fitinanniyar taku tun kafin ta cika mun gida da mutane". Dariya yayi ya ce "To Innah, amma Saleem har yau baizo ba"? Cike da takaici tace "wlh kuwa Sameer, Ko na k'ira numban shi yanzu bata shiga" "kiyi hak'uri Innah kada ranki ya b'aci tunda bamu san me ya rik'e shi ba, in Allah ya yarda zai dawo". "Allah yasa haka, saika zo d'in, ka gaishemun da Khairat d'in". Innah ta fad'a tana katse kiran, tunda Elham taji me ake fad'a tadaina kukan, ido ta zuba wa Innah tana murmushi, ai kuwa tana gama wayar ta d'ale Innah tana dariya, murmushi Innah tayi ta sab'ata a baya taci gaba da aikin ta tana tunanin rigima irin ta Elham. ************************************* Soyayya me k'arfi ne ya shiga tsakanin Saleema da Sabitu, bashi da burin da ya wuce auren ta gashi mahaifiyar shi tayi tsayin daka tace ba auren da zai k'ara sai yayi hankali, wani irin kyauta Alhaji Ma'aruf ke masa na ban mamaki, yanzu shi yake cefenen gidan sa, kaya masu tsada kuwa kullum cikin shigarsu yakeyi, abokanshi suna ta sanya wa Alhaji Ma'aruf albarka acewarsu mutumin arziki ne, duk wanda Sabitu zai kai masa da sunan neman taimako to yakan taimaka musu da gaggawa, don haka Sabitu yazama kamar babban yaronsa, yakan aikeshi har wani gari ba tare da d'ar ba, suna cikin wannan halin ya damk'a masa gida me kyaw wai saboda zai auri Saleema. Ko da Umma taji labari tayi murna sosai, dakanta taje tayi masa godiya na irin hidimar da yakeyi da d'anta, ita dai Suwaiba sam takasa yadda da wannan kyauta, tanaji ajikin ta kamar ba alkairi bane, sai dai ta danne tana taya mijin ta murnan samun ci gaba, har lokacin bai daina neman mata ba, Saleema kuwa ba abunda ya shiga tsakanin su acewarsa auren ta zaiyi, itama bata bari ya mannu da ita sosai, sai dai takan haukata shi da kiss kala kala wanda yake kusa zaucewa, dazaran zai fara wasa da jikinta takan bashi hak'uri akan yabari suyi aure tukunna. Wannan kyaututtukan da Alhaji Ma'aruf yakeyi wa Sabitu yasa Umma ta amince ya Auri Salima, da kunya ta hana auren tunda yana kula da d'anta. Murna a wajen Sabitu kamar zaiyi hauka, Suwaiba tasha kuka ba mai rarrashinta, mahaifinta kad'ai yayi mata nasiha tare da bata hak'uri akan ta kwantar da hankalin ta. Zaune suke shida Saleema tana masa lissafin abubuwan da za'ayi a bikin, komi sun tsara shi yadda ya kamata, ba wani biki sosai za'ayi ba acewarsu Alhaji bayason bidia, har lokacin Sabitu bai tab'a ganin iyalan Alhaji ba kuma hakan bai tab'a damun shi ba. A haka aka sanya bikin Saleema da Sabitu bayan ta kaishi wajen iyayen ta sun gaisa a cikin garin Bauchi. ************************************** Elham farinjini ne da ita, duk rashin kirki irinna Khairat matar Sameer tana son Elham sosai, yadda Innah ke biyewa shirmen ta haka Khairat ke biye ta, idan taje gidan komi ita take mata, hatta makaranta ita takan kaita dakanta ta d'auko ta duk da babur suke hawa, wannan dalilin yasa Sameer yake matuk'ar son khairat, duk abunda zai so Elham to shima yakan so shi har cikin ranshi... Wannan shine mafari!! Waye Sameer da ahalinsa? Waye Sabitu sannan waye Saleema? Ku biyo ni cikin labarin✍ 2/1/20, 5:09 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 4 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ *Na sadauk'ar da wannan page d'in ga _AISHA BICHIKI FANS_ da _BICHIKI HAUSA NOVELS_* Biki saura kwana 2 amma ba wani alamar za'ayi hidima ta gefen amarya, Ango Sabitu kam gidansu cike da jama'a na birni dana k'auye, kowa na tofa albarkacin bakin sa akan yaushe Sabitu yayi hankalin rik'e mata 2, dangin Suwaiba da suka taru a gidanta kowa shawara yake bata akan kada ta kuskura ta bishi sabon gidan da aka bashi, tayi zamanta tunda ba wani nutsuwa yayi ba, itama tayi na'am da shawarar domin dama tana buk'atar hutu. Mahaifinta har canza mata kayan d'aki yayi duk saboda ya kwantar mata da hankali, yasan ba k'aramin hak'uri takeyi ba. 'yan uwanta da suka zo gyara mata d'aki sai bayan isha suka tafi, bayan sun kimtsa mata komi harda mata zanen flower me kyau, suka yarfa mata kitso, mahaifiyar ta tayi mata d'inkuna sunyi kala 10 duk don ta samu nutsuwa, da yake Sabitu na samun kud'in banza dubu 200 yabata akan tayi gyara, ko naira bata tab'a ba ta ajiyesu. Sai kusan 11 yadawo gidan duk agajiye saboda zirga zirgan hidiman biki, gidan yayi d'as gwanin sha'awa, idanuwa ya zuba wa Suwaiba ganin ta masa kyau, ko kallo be isheta ba balle ya samu daman bijiro mata da jarabar sa, tsuka yayi ya ce "mace har mace babu tattalin miji". Maganar ta doke ta sosai, amma ko kallon shi batayi ba, tana ganin ya shige d'aki ta tashi ta zauna, memakon maganar ta bata haushi sai tafara dogon nazari akai, gaba d'aya jikinta yayi sanyi tafara tunanin anya ba gaskiya ya fad'a ba, can dai ganin zata sa kanta adamuwa tayi kwanciyar ta a falon tana tuna bak'in halayen Sabitu, da wannan tunanin tayi bacci zuciyarta far haushin sa. Gogan naku kuwa ko ajikin sa, wayarsa ya d'auka ya danna k'ira wa Saleema sukasha hirarsu duk da baison jin muryar amma ta iya hirar dayake so, anan ta shaida masa gobe zata koma garinsu saboda acan za'a d'auko ta. Da safe Sabitu ya shirya a gurguje saboda kada Saleema ta tafi basuyi sallama ba, dai dai k'ofar gidan Alhaji Ma'aruf yaga Drivern sa na fito da akwatinan lefen da yayi wa Saleema, yawancin kayan ciki Saleemar ne ta siya da kanta, akwatina 5 masu shegen kyau, yana gani aka zuba a but d'in motan Alhaji Ma'aruf, har zai k'arasa sai yayi turus. Kyakkyawan Saurayi yagani ya fito daga cikin gidan, jikinsa sanye da k'ananun kaya amma kallo d'aya zaka masa kasan masu tsadane, gashin kanshi dake kwance luf irinna asalin bafulatani wanda yasha gyara sai shek'e yakeyi, hanunsa d'aure da agogo sunfarin Gucci, farine sol kamar katab'a jini ya fito, kallonshi Sabitu yakeyi ko kyaftawa babu, ga wani tsananin kamar da sukeyi da Saleemar sa harta b'aci, nan ya tabbatar yayan Saleema ne. Da sassafar ya isa wajen amma yana isa saurayin yana shiga mota cike da wani irin taku na gayen da aji ya zauna masa. Alhaji Ma'aruf ya matso kusa dashi da sauri ya ce "Sabitu kaine tafe da sassafe"? Cikin jin kunya ya ce "dama nazo akwai sak'on da zan bawa Saleema ne". Alhaji ya ce "Ashha, ai tun asuba ta tafi, taurin kunnene da ita ina Bauchi ina Gombe nace ta bari tabi d'an uwanta ma tak'i, amma ai gobe zuwa dare an kawo maka amaryar ka kada kasamu damuwa"! Ya k'arasa maganar yana bubbuga kafad'an Sabitu, murmushi Sabitu yayi ya russuna ya ce "nagode oga, Allah ya k'ara girma". Kada kadamu Saleema ai 'yata ce, idan kana buk'ar wani abu ka turomun ko ta text ne". Godiya Sabitu yayi sannan yabar gidan. Sanin gidansu acike da bak'i yasa ya koma gidanshi domin ya huta. *GARIN GOMBE* Innah tana tsince zogale duk kewar Elham ya dameta, idan ta tuna rigimarta takanyi dariya, lokacin k'arfe 12 na rana taji Sallamar almajirin ta dake zuwa mata aika, tana d'aga kai taga suna shigo da akwatina shida 'yan uwanshi, mik'ewa tayi ta ce "kai Garbati a ina ka samo wa'innan jakkunan". Yana dariya ya ce "Alk'ur'an Yallab'oi ne ya dawo yana waje". Tana jin haka ta gane Saleem yake nufi domin yallab'oi yake cemasa, washe baki tayi cike da d'oki na murnar ganinshi ta ce "A lallai muna da bak'o, zo kaje kafad'awa khairat tayi maza ta shirya Elham ka d'auko ta mutumin nata ya dawo". Da gudu kuwa ya fice shima yanata murna domin suna mqtuk'ar son Saleem, mutum ne da bashi da girman kai kowa nashi ne, akwai zafi amma sai an tab'o shi ne, don haka babu wanda ya tab'a lura da zafin nashi, har fiye da minti 30 Bai shigoba yana can yana gaisawa da mutane, Innah sai lek'e takeyi domin ta matsu ta ganshi tayi kewarshi sosai. Dak'yar yasamu ya shige gida harda d'an gudunsa, gun Innah yayi data kasa b'oye farincikin ta, ya rungumeta cike da kewa, dariya tayi ta ce "sakarni yanzu jikin ba k'wari idan ba nema kake ka k'arasa ni ba". Saketa yayi amma yana rik'e da hanunta, kallon shi tayi k'asa da sama gaba d'aya ya canza sosai alamar jin dad'i yafito sosai ajikin sa. "Mu shiga ciki kasha ruwa ka kwaso hanya, memakon kayi waya a tanadar maka abinci sai kayi durowan yesu"! Maganar tabashi dariya ya ce "Ina sarkin kukan naki naji gidan yau shiru". Ya fad'a yana d'an dube dube, baki ta tab'e ta ce "tanacan gidan Sameer kasanta bata son zama waje d'aya, duk inda tasan za'a rik'a biye mata toh akwai mannewa". Dariya yayi kafin yayi magana sukaji Sallamar Khairat, tana goye da Elham sai cakulkuli take mata duk ta haukata ta, ai tana arba da Saleem ta diro da gudu ta fad'a jikinsa tana dariya, sai kuma ta saki kuka tana shure shure, dariya Khairat tayi ta ce "wlh Innah yarinyar akwai iskanci, bakiga yanda tasa nayi ta dariya a hanya kamar sabon hauka, idan nasauk'e ta kuma tayi ta kurma ihu". Dungure kanta Innah tayi ta ce "Ja'ira bakya sake zuwa ko ina ba ae". Saleem daya zuba mata ido yana dariya ganin dagaske take kukan, rungumeta yayi ya shiga rarrashin ta yana cewa idan kinyi shiru zan baki sweet". Shiru tayi tafara jan ajiyar zuciya, Innah ta ce "Ohh ni Habiba, me aka miki kike kukanne". Mele baki tayi ta ce "Bazan sake zamaba Uncle Saleem zanbi". Khairat fita tayi ta shigo da basket d'in da suka zo dashi, a gaban Innah ta dire ta ce "gashi Innah a baiwa bak'o nasan baki dafa abinci dashi ba". "yo inama nayi girkin yazo ba tsammani". Dariya sukayi duka sannan aka shiga gaisawa. Sameer ma anan ya wuni suka ta hiran bayan rabo, nanfa Saleem ya shirgo musu k'aryar aikin gwamnati wani ogansa ya samar mishi, duk wata yana d'aukar albashi me yawan gaske kasancewar yayi karatu sosai duk sai suka yarda, ya ce musu har gida ya siya a Bauchi, su kuwa sukayi ta murna Innah nasa mishi albarka. Akwatinan daya zo dasu ya janyo yafara musu bayani, "wannan kayan ogana ne zai aurar da 'yarsa angama komi Allah yamata rasuwa, shine mijin ya ce bazai amshi komi ba don haka Ogana yabani yace nakawo wa k'anne na, gashi k'anwar tawa bata girma ba". Ya gama maganar yana shafa kan Elham datayi bacci a cinyar sa, Sameer ya ce "Babban Yaya dama wlh jira muke kadawo kafito da mata 'kaga sai ka ajiye akwatinan kayi auren ka dashi". Harara ya watsa mishi ya ce "malam ina fad'a maka na samu aiki kana maganar aure, ni gaskiya ba yanzu ba". Inna ta sake baki ta ce "Haba Saleem, kana ganin k'anin ka tun yaushe yayi aure ace kai ba dama amaka magana sai rai ya b'aci"? Susa kai yayi ya ce "Innah yanzu dai ki rabar da kayannan daga baya sai muyi magana, tunfa wancan shekarar kike cewa kin samar mun mata ko kin fasa ne"? Dariya tayi ta ce "shak'iyyi tashi maza kaje ka huta, kaima Sameer kaga dare yayi kaje Allah ya muku albarka, da Ameen suka amsa sannan ta shigar da Elham d'aki dake bacci harda minshari. 2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 5 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ _wallahi cmmnt d'inku yayi ta bani dariya🀣🀣 nidai ba ruwana idan Saleem yajiku kuna had'a shi da Saleema🀣_ _Sabitu yananan yana ja muku Allah isa da kuke had'ashi da aljana_🀣🀣🀣 https://m.facebook.com/AISHA-Bichiki-265061884086077/posts_to_page/?ref=opera_speed_dial ✍ Washe gari ta shiga hidimar raba akwatinan da Saleem yazo dashi, da kanshi ya kwasar wa Elham kayan kwalliya masu yawa, Innah sai tsiya take musu wai zata ga a fuskar da za'a shafa wannan tarkacen, dariya yayi ya ce "kedai Inna yi mata wanka kiga irin kwalliyar da za'ayi, Elham sai murna takeyi tana mak'ale da shi, duk cikin mutanen da tasani a rayuwarta tafi son Saleem, duk da kowa na k'ok'arin ganin farincikinta tafi k'aunar Saleem, idan baya nan ne kawai take mak'alewa Sameer. Kusan rabin kayan wa Khairat aka d'ibarwa. K'arfe 2 na rana Saleem na zaune gaban Innah yanata shirga mata k'arya wayarsa dake hanun Elham ta fara ruri, k'arb'a yayi yad'an saci kallon Innah, ganin hankalin ta baya kanshi yasa ya fice da sauri, yana gama amsa wayar ya dawo ya zauna a gaban Innah, akwatin gabanta wanda ya tara tarkacen Elham ya matsa dashi gefe ya ce "Innah k'iran gaggawa ne ya sameni yanzu". Da sauri ta d'ago tana kallon shi, murmushi ya sakar mata ya ce "Innah kada ki wani d'aga hankalin ki, duk sati zan rik'a zuwa miki kinsan yanzu tunda nasamu aikinnan ba hutu kuma, yanzu haka Oga yace nayi maza nazo akwai takaddun da zan bayar nawa, inaga k'arin girma za'ayimun". Ajiyar zuciya Innah ta sauke ta ce "Shikenan Saleem Allah ya tsare hanya, ka kula da aikin ka sosai banda wasa dashi, a zamaninnan ba kowa ke samun aiki ba, tunda kasamu sai ka rik'e shi hanu bibbiyu, sannan ka nutsu sosai ka samo wacce zaka aura domin nagaji da ganin ka haka". Hannuwan shi ya sanya ya tallafo fuskarta ya manna mata kiss yana murmushi ya ce "Insha Allah Inna duk abunda kike so shi za'ayi, kada Kiyi kewata da yawa inanan tare dake a zuciyata, inaso wataran na gina miki k'aton gida yanda munafukannan zasuji haushi Innah". Hawaye ne ya gangaro mata, da sauri ya shiga goge mata su yana fad'in "Menene haka Innah, kina so ki hanani tafiya ne"? Murmushi ta k'wak'ulo ta ce "Farinciki ne Saleem". Had'a fuskan su yayi yana dariya, Elham da tayi tsaye tana kallon su sai taji babu dad'i jin wai Saleem zai tafi, da sauri ta fad'a bayanshi ta fara kuka tana cewa "zanbika Uncle Saleem". Juyowa yayi ya ce "haba sweet heart kema kinsan dole dake zan tafi, d'auko jakar kayanki kizo mutafi". Cike da murna ta ce "na gidan Aunty Khairat". D'agata yayi sama yafara juyata tana k'yalk'yale dariya ya ce "sako hijabi muje mu d'auko". Da gudu ta fad'a d'aki tana murna, Inna sai murmushi takeyi. Tundaga zauren gidan ta fara k'walawa Khairat k'ira tana ce wa "ki fitomun da kayana zamu tafi da "Cweet heart d'ina". Dariya Khairat ta fito tanayi ta ce "ohh zanga randa zaki daina ce masa Cweet heart, wlh matarsa fasa bakin ki zatayi". Dariya Elham tayi domin bata fahimci ina maganar ya dosa ba". Shi kanshi Saleem dake bayansu dariya yakeyi. Da wayo da dabara yabarta a gidan ya d'au hanyar Bauchi. ************************************** Gidan Alhaji Ma'aruf ya cika da mutane anata shagalin biki, ni harna fara tunanin kodai dama akwai mutane a gidanne ban tab'a ganin su ba. Dangin ango Sabitu ma biki sukeyi sosai suna masa fatan shiriya. Bayan Isha aka d'auko amarya Saleema data k'udindine cikin mayafi, gida ya cika ana gud'a harda mak'wafta da yaran anguwa, kowa na lek'awa yaga amarya amma fuskarta a rufe sai k'awayen ta da suka kewaye ta. K'arfe 10 kowa ya watse aka bar amarya ita kad'ai, yaye mayafin tayi tana murmushin da ita kad'ai tasan manufarshi. Cikin Zumud'i Sabitu ya shigo gidan har yana hana abokan sa shiga saboda kishi, tana jin motsin shi ta janyo mayafin ta mayar kanta, ledan hanunshi ya ajiye a gabanta ya haura kan gadon, bakinshi a washe yafara mata kirari dake nuna farincikinsa, ace warsa sai yanzu yasan yayi aure, mayafin ya yaye yana lek'a fuskan ta, tasha kwalliya tayi kyau matuk'a, rungumota zaiyi ta shagwab'e fuska da muryarta mara dad'i ta ce "Masoyi saurin me kakeyi, ni wlh duk na gaji". Gab'on naku ya washe baki ya d'auko ledar ya bud'e mata kazar amarcinta, cikin yanga ta rink'a ci, shi kuwa Sabitu zumud'in gurzar amarya ya hanashi zagewa yaci, duk da irin munafukin yunwar dake addabansa, Saleema dake ganin take takensa tayi murmushi kurum a ranta. Tana gama ci tasha yogurt d'in tayi nak abunta, kallon Sabitu tayi ta ce "kaje d'akin ka kayi wanka zan shirya". Hanunta dayasha lalle ya kamo ya manna mata kiss ya ce "kinsan munyi tanadi a wannan daren ki shiryamun sosai yanda zanji dad'i". Itama sunbatar hanunshi tayi ta ce "to masoyi". Yana fita ta sanya key a k'ofar ta d'ale gado tayi kwanciyar ta, nanda nan kuwa bacci ya d'auketa. Wanka yayi sosai ya feshe jikin shi da turare tako ina ya sanya jallabiya ya tafi d'akin amarya, ko gajeren wando bai saba wai kada ya takura mishi domin a matse yake sosai, yana tura d'akin yaji a rufe, waro ido yayi yafara d'an bubbugawa yana k'iran sunan ta, jin shiru yasa ya koma falon yazauna ya ce hala wanka takeyi, remot ya d'auka ya kunna Tv yafara kallo amma hankalin shi naga amaryar sa, yananan zaune har hak'urin shi yafara gazawa domin wani irin matsanancin sha'awa ke damunshi, yayi k'ok'ari kwana 2 bai nemi mace ba yana tanadi wa amarya shiyasa gaba d'aya yafara fita a hankalinshi, jin mararsa ta fara k'ullewa yasa ya koma jikin k'ofar nata ya fara bugawa, Saleema baccin ta take sha don haka batama san yanayi ba, tun na bugawa a hankali har yafara bugawa da iya k'arfinsa kamar wani zararre, rik'e mararsa yayi dake ta neman agaji yashiga buga k'ofar baji ba gani. Mak'wabcin su Alhaji Sammani ne yaji bugun yayi yawa kasancewar garun gidan nasu d'aya ne, matarshi ya kalla ya ce "kubra kinajin abunda nakeji kuwa"? Kubra ta ce "tun d'azu nakeji duk tsoro yakamani". Alhaji Sammani ya ce "Allah yasa ba b'arayi bane". Kubra tace "Ameen, gari na wayewa zanje na duba nagani, inaga gidan da aka kawo amarya yau ne". Janyota Sammani yayi ya ce "kiyi bacci duk kin wani birkice". Sabitu ganin babu sarki sai Allah yasa ya koma d'akin nasa ya rink'a murk'ususu har asuba sannan bacci ya kwasheshi. 2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 6 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ _Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga munata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_ ✍ Asuban fari Saleema ta tashi, tayi sallar asuba sannan tayi wanka, shigan less tayi wanda ya karb'eta matuk'a, tayi kyau sosai ta fito amarya rass abunta, sai lokacin ta bud'e k'ofarta ta nufi kitchen, ba komi a ciki sai Indomee, kayan aiki kuwa babu abunda babu aciki, guda 4 ta d'iba ta dafa, ta d'umama sauran kazarta na jiya ta d'aura akan indomi d'in, haka ya cika k'aton trey d'in don dama Saleema badai ci bafa kamar wani k'aton gardi🀣 Lokacin k'arfe 8 na safe, zama tayi a falo ta kunna Tv tafara cin abunta hankali kwance, motsinta ya fito da Sabitu wanda tashin sa kenan, tsaye yayi a gaban ta yana had'iye yawu, shigar tata tayi masifar tafiya dashi, ga mahaukacin yunwan da yakeji cikinsa harna kukan yunwa, da fushi ya tashi amma ya nemi fushin ya rasa. Kai ta d'aga ta kashe masa ido ta ce "Masoyi ka tashi? bismillah zauna muci". Haushin ta ya kamashi watau batama san halinda ta barshi jiya ba, basarwa yayi dake yana jin yunwa ya zauna sukaci tare, sai kallon k'aton hanunta yakeyi wanda yafi nashi sosai, ga wani gargasa na kwantaccen gashi a hanun, da sauri ya d'aga ido yana satan kallon ta, lomarta kawai takeyi har tana lumshe ido. Kallon ta Sabitu yake tayi zuciyar shi na bugawa da baisan dalili ba, murmushi ta sakar mishi ta ce "kallon fa"? Shima murmushi yayi wanda kana gani bai kai zuci ba, kallon ta yakeyi ya kasa daina wa, bai tab'a k'are mata kallo ba sai yau, wani bak'i bak'i yake gani wajen gashin bakin ta kamar gashi... Ganin irin kallon nasa yasa Saleema ta tsargu, tashi tayi ta koma kan cinyarsa ta zauna amma bata sake nauyin ta akansa, tsikar jikin Sabitu ya tashi jin yanda hanun Saleema ke shafa fuskar shi, cikin siririyar murya wacce bai tab'a jin tayi ba ta ce "kayi hakuri jiya bacci ne ya tafi dani, amma yau tare zamu kwana koh". Gaba d'aya kan Sabitu kuncewa ne kawai beyi ba, taushin hanun ta kad'ai ya isa ya susuta shi balle irin kallon da take jifansa dashi, d'an kwanto da ita jikinsa yayi yana sauke numfashi, murya a sark'e ya ce "zanje nayi wanka don Allah kada ki gudu"! Murmusawa tayi ta ce "Toh Masoyi". Yana shiga d'aki Kubra na doka Sallama a falon, mik'ewa Saleema tayi cike da mamaki ta nufi wajen tana tunanin waye da wannan sammako haka, tana bud'ewa tayi arba da Kubra dake zare ido, lokaci guda ta saki murmushi, itama Salima murmushin tayi ta ce "Bismillah shigo". Kubra ta ce "A'a anjuma zan shigo mugaisa, dama nazo ne naji ko a gidannan ne b'arayi sukayi ta buga k'ofa"? Waro manyan idanuwa Saleema tayi ta ce "b'arayi? Gaskiya banan bane don bamuji wani motsi ba, kuma akwai me gadi banji yace komi ba". Kubra ta ce "Toh madallah, ni zan koma idan kina buk'atan d'an aika kiyi magana saina turo miki yaro na". Saleema ta ce "ai kuwa nagode kituro mun shi yanzu, dama inata tunanin a ina zan samu yaro na aika". Kubra ta washe baki baki ta ce "bari na turo miki shi, duk abunda kike buk'ata ki aikeshi, yaron kishiya ta ce, sam bayajin magana, idan yamiki kwab'a ki zaneshi". Mamaki ya hana Saleema magana, ido ta zubawa kubra dake ta zuba kamar an tambaye ta, ganin ba shiru zatayi ba ta ce "toh nagode sai anjuma". Zama Saleema tayi tana tunanin maganar Kubra, watau d'an kishiyarta ne, to ina Maman shi.... Sallamar yaron ya katse mata tunani, kyakkyawa ne yaron zai kai shekaru 10, wankan tarwad'a dashi, kayanshi duk a kod'e alamun dai bashi da sutura, murmushi me had'e da ma'anoni Saleema tayi sannan ta amsa gaisuwar da yake ta jifanta dashi, a take ta d'auko kud'i ta rubuta masa abunda take buk'ata ta mik'a masa. Harda russunawan sa alamun yaron yanada hankali. Yaron yana fita ta juya zatayi d'aki idanuwan ta suka sauk'a kan Sabitu, yana sanye da kayan shan iska, matsawa yayi daf da ita ya ce "Amarya baki laifi". Murmushi tayi ta ce "anya kuwa". Matsawa yayi sosai jikin ta ya ce "ke zaki bada wannan shaidar, ko baki gani akanki ba". Fari tayi masa da ido ta ce "wannan ai ba laifi bane". Washe baki yayi ya ce "muje nabaki amsa, don wlh a matse nake". Cikin jan hankali ta ce "shknn masoyi, nidai amun afwa ina fashin Sallah". Wani irin zabura Sabitu yayi ya ce "kada kimun haka zan iya shiga wani hali Saleema, idanma tsoro kikeyi zan miki a hankali" Ture hanunshi a jikin ta tayi ta ce "nifa bana son fitina, ba'a takuramun, idan kana buk'atar kud'i kayi mun magana amma na fad'a maka halin da nake a yanzu". Binta da kallo Sabitu yayi cike da tashin hankali yama kasa magana, yana gani ta shige d'aki zuciyarshi ta shiga harbawa da sauri yana tunanin abu 2 daya kasa fassarasu. Tsuk'a yayi ya d'auko key d'in motar Saleema dake hanunshi ya fice a gidan, me gadi na bud'e masa yaron da Saleema ta aika na shigo wa, baiko tsaya bi takanshi ba ya hura wa motar wuta yayi gida abunshi cike da son kasancewa da Suwaiba, dama duk lokacin da ta k'ak'are masa ananta yake sauk'ewa... *KUYI HAK'URI INA GANIN SAKONNIN KU KAINA KE CIWO SOSAI*.... _Allah yayi albarka wa iyayenmu_ 2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 7 Kuyi hakuri najina shiru kwanaki da yawa... _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ _Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga mu'ata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_ ✍ Kai tsaye yaron data aika ya shiga falon yana doka Sallama, jin shiru yasa yafara k'arewa falon kallo, jin motsin bud'e k'ofa yasa ya waiga da sauri, murmushi Saleema tayi ta ce "shigo mun dashi ciki". Tana fad'a ta koma tayi zamanta akan gado. Da Sallama ya shiga ya ajiye sannan ya mik'a mata canjin, girgiza kai tayi ta ce "ka sayi omo da canjin ka wanke kayan ka". Dariyar jin dad'i yayi yafara jera mata godiya. "menene sunanka"? Tayi tambayar fuskanta nakan wayar hanunta. "Ahmad". Ya bata amsa. d'an kallonshi tayi ta ce "ina mamarka"? Ya ce "Mamana ta dad'e bata nan, ta tafi garinsu har yanzu bata dawo ba". Ajiye wayar Saleema tayi ta zubawa Ahmad ido, can tayi ajiyar zuciya ta ce "kana zuwa makaranta"? Ya ce "da ina zuwa amma yanzu bana zuwa, Babana ya ce bashi da kud'i, 'ya'yan Aunty ne kawai suke zuwa". Murmushi Saleema tayi ta ce "zan baka kud'in makaranta ka koma kaji, sannan zaka rik'a zuwa kana tayani aiki, har kaya masu kyau zan siya maka". Ahmad sai washe baki yakeyi yana murna, yaron yanason karatu sosai amma bai samu wannan damar ba, gashi har kaya masu kyau za'a siya mishi, zai zama kamar abokansa, don haka yayi ta murna yana mata godiya. Yana fita yaje yasami abokanshi ya ce "Zai koma makaranta, suma sukayi ta murna don suna son Ahmad". Da gudu yayi gida abunka ga yaro, ba ruwanshi da abunda Kubra ke mishi yaje yasameta da zancen, kama baki tayi tana kallon shi harya kai Aya, jawoshi tayi ta matse kunnenshi tace "Yanzu Ahmad harka barbad'a mata sirrin gidannan"? Tsaban jin zafi har hawaye yafara yi, cikin azaba ya ce "Aunty wlh bance mata komi ba, kiyi hak'uri". Rankwashi ta sakar mishi me zafi ta ce "zanje yanzu naji me kace mata, munafukin Allah kawai". Hankad'ashi tayi ta zari mayafi ta nufi wajen Saleema. Saleema na yanka Salad a kitchen taji shigowar Kubra tana karad'a Sallama, aranta tace "na shiga uku me kuma yadawo da wannan matar". Hanunta ta d'auraye ta fito falon, a zaune ta same ta tana bin ko ina da kallo, Saleema ta washe baki ta ce "Auntyn Ahmad ko"? Kubra ta gimtse fuska ta ce "naji wani magana ne abakin Ahmad, shine nakasa zama sai da nashigo, ace daga tarewarki jiya har Ahmad ya kawo miki gulmar bai zuwa makaranta, kumafa bakowa ya hanashi zuwa ba iskanci da rashin ji yakeyi aka koroshi, shine nazo nafad'a miki kada ki wahalar da kanki ba karatun yakeyi ba, zancen sutura kuwa yana dasu dai dai gwargwado wlh k'in sawa yakeyi". Ta gama maganar tana k'ifi k'ifi da ido, Saleema ta gyara zama ta ce "kinsan yara sai hakuri, musamman idan bakai ka haifesu ba". Kubra najin haka ta washe baki ta ce "wlh kuwa, sai aga kamar mugunta kake musu, yaronnan shekararsa 4 kenan a wajena amma mutane basu ganin wahalar danakeyi dashi, hakanan uwarsa ta d'auki kishin banza dani tak'i zama tabarmun masifa". Murmushi Saleema tayi cike da mamakin Kubra. Nan Kubra tabata labarin mahaifiyar Ahmad da bak'in kishinta har ya sa aka sake ta, shine ta tafi da 'yarta macen wai gudun kada ta lalace tabar namijin. (Wannan shine babban kuskuren da mace take tafkawa, kibar d'anki sabod rashin tunani, lalacewar maza shi yafi komi sauk'i a yanzu, Namiji shike sata, shaye shaye, yayi garkuwa da mutane duk saboda rashin ingantacciyar rayuwa da tarbiya, dazaran kin haifafa dole kiyi hak'uri da duk bak'in wahalar da zakisha agidan aure, domin babu wacce zata kula miki da abunda kika bari, kuma ba gidan da zakiyi aure ki tafi da d'an wani auren ya d'ore, kin tafi kin bar yara kina rayuwa me dad'i bakisan ya tarbiyar yaranki yake ba, so don Allah mata ku jure ku daure ku reni yaranku kodan saboda ragewar gurb''ataccun mutane acikin al'umma, idan d'anki d'aya ya lalace tofah sai ya lalata fiye da mutane 100). Saleema ta matsa kusa da Kubra tace "amma maman Ahmad bata kyauta ba, amma hakan zai zamo miki alkairi matuk'ar kika bani had'in kai". Karkace kai Kubra tayi ta ce "tayaya? Ban fahimceki ba". Saleema tayi murmushi ta ce "Ahmad zai zamto yanamun aikatau, ni kuma zan rik'a biyan shi duk wata dubu 20, ke kuma saiki karb'e kud'in kinga kafin wani lokaci kin tara kud'i". Waro ido Kubra tayi har mayafinta yana fita, ta dafa Saleema ta ce "Amarya dagaske kikeyi"? Saleema ta washe baki aranta tace "mayyar kud'i bazaki bani wahala ba ashe". A fili kuwa cewa tayi "Dagaske nakeyi, yanzu dai anujuma ki turo mun shi yayi mun wanke wanke". Wani irin dariya Kubra tayi ta ce "to amarya, gaskiya kina da kirki, zan turo shi anjuman". Nan sukayi Sallama ko wacce zuciyarta cike da farinciki. Sabitu yana isa gidanshi ya tarar a rufe, kallon narkeken kwad'on dake jikin k'ofar yayi yana sauk'e ajiyan zuciya, tunani yashiga yi ina Suwaiba zataje alhalin bata tab'a haka ba, watau yawo ta farayi don taga baya gidan, cike da b'acin rai yashige motar ya nufi gidan mahaifiyar shi, tundaga k'ofa yake doka sallama yaji shiru, don haka yashige d'akin yana k'iran ta, idanuwansa ne sukayi arba da suwaiba tana kwance a gadon, baccin ta takesha hankalin kwance, Wani munguwar sha'awarta ta kamashi, da sauri ya isa gareta har yana had'a hanya, tafin hanunta ya kamo yafara murzawa a hankali, zunb'ur ta mik'e tana ware idanuwanta akanshi, haushi ne yakamata aranta ta ce "wannan wani irin masifane". Durowa tayi daga kan gadon ta tsaya a gabanshi tana k'are mishi kallo, dariya tayi ta ce "Ango kasha k'amshi, yaya naganka a firgice". Harara ya watsa mata ya ce "wuce muje gida". Kallon raini ta masa wanda yasa yasha jinin jikinsa, ta ce "da da yanzu akwai banbanci, nadaina zama kana morata a lokacin da kaso kana wulak'antani, nasanka farar sani Sabitu, haka kawai bazaka zo kace mutafi ba, kumama ni babu inda zani sai ka gama amarcin ka". Ta fad'i maganar cike da b'acin rai, marairaicewa yayi yana rok'onta amma fir tak'i tanka masa, Sabitu bai iya jurewa buk'ata ko kad'an, a haka mahaifiyar shi ta tarar dasu, kallo d'aya ta musu ta fahimcesu, don haka ta d'aure fuska ta ce "wuce kabar gidannan, aure kwana biyu kazo neman fitina, ko bakasan sai kayi kwanaki 7 ba? Wuce tun kafin na sab'a maka". Kamar zaiyi kuka yabar gidan yanajawa Saleema Allah ya isa data hanashi sak'ewa da ni'imarta, figar motar yakuma yi ya ayyana aranshi ko ta k'arfi yau sai ya k'waci hakkinsa a wajen Saleema komi fashin sallan datakeyi🀣 ******************* Kamar yadda Kubra tayi mata alk'awari haka ta turo mata Ahmad yayi mata wanke wanke, memakon ta bashi wanke wanken sai tace yafara gyara mata d'aki, sororo Ahmad yayi yana kallon d'akin domin a gyare yake tsaf, ga masifaffen k'amshin dake tashi tako ina, ko akwai gyaranma shi baisan ta ina zai faraba domin bai iyaba. Saleema ce ta katse masa tunani ta ce "ka hau kafara gyara gadon mana". Cikin in ina ya ce "naga a gyarene". Dafa kafad'arshi tayi ta ce "bari nad'auko wani bedsht d'in ka canza wannan yayi datti". Shi dai binta kawai yakeyi da kallo, ta yaye nakai d'in ta mik'a mishi, ganin ya tsaya ta ce "nasan baka iya ba muje na koya maka yanda ake shimfid'awa". Hanunsa ta kamo suka haura kan gadon, cikin nutsuwa take gwada mishi yanda ake gyara gadon, a haka suka gyara tsaf, sannan taja hanunsa sukayi toilet, nanma ita ta taimaka mishi suka gyara, suna gamawa ta jashi jikin shower ta saki ruwa akanshi me d'an d'umi, a razane ya ce "Aunty fanfo kika kunna sun jik'amun kaya". Murmushi tayi ta ce "wanka zakayi zan baka wasu kaya kasaka, cire wa'innan d'in kayi wankan.... " Batakai ga k'arasa maganar ba taji an banko k'ofar d'akin, cikin sauri ta lek'a taga Sabitu sai huci yakeyi shi a dole da shirin kota kwana yazo, juyawa tayi ta kalli Ahmad ya rakub'e a gefe yana b'arin sanyi, da alamun bai saba shiga ruwa ba, da hanzari ta isa ta cire masa rigar ta ce "kayi wankan ina zuwa". 2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 8 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ _Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga mu'ata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_ *Wanda sukayi ta k'irana sunamun yaya jiki bazan misalta muku farincikin danaji ba, nagode sosai da adduoi* *wacce taga ban bud'e sakonta ba don Allah kada kuyi fushi sak'onne da yawa, a hankali zan bubbud'e, ina alfahari da dukka masoyana sosai* ✍ Tana fitowa ta nufeshi tana dariya, d'aure fuska yayi alamar ba wasa, ta lura da yanayin sa amma ta basar, sannu da dawowa tayi masa tana lek'a fuskanshi dayake ta juya shi. Fuska a d'aure ya ce "Abunda kika mun kinga ya dace kenan, gaskiya ni bazan iya jurewa ba". Itama d'aure fuska tayi ta ce "daga aure kwana 2 ka fara k'orafi, idan kayi hak'uri nanda sati biyu komi zai dai daita". Wani irin zabura Sabitu yayi yace "Sati biyu za'ayi me"? "zanyi wanka". Ta bashi amsa a tak'aice. Matsawa yayi kusa da ita ya ce "me kike nufi"? Juyawa tayi da nufin barin wajen ya rik'o k'aton hanunta, ita duk hankalinta yana kan Ahmad. Janyota yayi da k'arfi ta fad'a jikinsa, ya lumshe ido murya can k'asa yace "Kada kimun haka Saleema, bazan iya jurewa ba, bana iya kwana banyi ba wlh ki taimakamun". Hankad'ashi tayi ta ce "Bansan yaya kake so nayi ba, ko baka gane me nake nufi bane"? Sake matsota yayi yana rok'onta, ganin ya gama birkice mata yasa ta hankad'a shi kan gadon, ta haye kanshi ta fara wasa da duk wani sassan jikinsa cikin k'warewa, sarrafashi takeyi sosai shikuma duk yagama birkicewa ninshi kawai yakeyi yanajin dad'in da bai tab'a jiba, da sannu ta samu ta rabashi da kayanshi, saida ta tabbatar yagama kamuwa ta ture shi tana maida numfashi. Da sauri Sabitu ya kamota idanuwan shi a rufe ya ce "ina zaki je, kada kibarni a haka". Motsin fitowar Ahmad daga toilet ya sanya Saleema ware ido akansa, cikin hanzari ta mik'e ta nufeshi, hakan yasa Sabitu bud'e idanuwan shi, cike da mamaki yake bin Ahmad d kallo, gaba d'aya jikinsa a sake yake yakasa magana, rik'oshi Saleema tayi ta ce "muje kasa kaya katafi gida, kada ka sake wasa a kusa da kwata kaga jikinka sai wari yakeyi". Wannan maganar yasa Sabitu yagane ya fad'i a kwatane, amma da zai fita yaga shigowar yaron, mik'ewa yayi da hanzari ya ce "Wannan yaronfa"? Murmushi tayi ta ce "aikensa nayi ya fad'a a kwata, shine nace ya wanke jikinsa". Shiru Sabitu yayi, nan kwakwalwar sa tafara tunanin irin romancn d'in da Saleema ta birkita shi dashi, yana gani taja Ahmad suka fice sannan ya sauk'e ajiyar zuciyar cike da tunani kala kala, bargon da ya rufe jikinshi dashi ya yaye sannan yasanya kayanshi, jinshi yakeyi wani iri sam bashida kuzari, ga wani irin tunanin dayake fizgar zuciyarshi wanda sam yakasa tantance shi, akwai abunda yake son sani amma bazai iya furtawa ba, yayi dad'e yana tunani sannan ya mik'e ya shiga yayi wanka, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar babu alamun angonci ko amarci a tare dashi. D'akinsa ya nufa domin shiryawa, Saleema tana kitchen tana had'a musu abinci, k'amshi duk ya cika gidan, memakon yaji dad'i sai haushin ta ne ya kamashi, harda hararan hanyar kitchn d'in🀣 (harara a duhu). Daya shoga d'akin harda banko k'ofa da k'arfi. Wayarta ne ya fara ruri dake falo, da gudu ta isa ta d'auka, ganin me k'iran yasa ta dafe k'irji, cikin sanyi ta ce "me kuma Alhaji Ma'aruf yake nufi". Kitchn d'in ta koma sannan ta fara amsa k'iran... "ok". Shine kawai abunda ta fad'a ta katse k'iran, wani dogon ajiyan ajiyar zuciya ta sauk'e, a gurguje ta gama jalof d'in shinkafa da makaroni dayaji kayan lambu, saida ta jera komi taje ta fesa wanka, mai masu sanyin k'amshi ta shafa da turare masu k'amshi, wandon jins ta saka da k'aramar riga ja da zanen flower fari a gaban rigar, badon d'an kunne da gashin kanta ba zaka iya rantsewa k'irar maza gareta domin faffad'an k'irjinta yanda ya fito sosai, hijab ta sanya har k'asa sannan naga ta ciro gashin kan nata wanda yasani zare ido ganin attached ne irin hulannan, a kan mirror ta ajiye sannan ta cire 'yan kunnayen ta ajiye su, komi cikin sauri takeyi da alamun itama saurin takeyi, cikin sand'a ta fice daga gidan harda d'an had'awa da gudunta, sai da tayi tafiya me nisa ta isa babban hanyan da zai sadata da titi, wayarta ta ciro ta d'anyi danne danne alamar ta tura sak'o, ko minti 2 ba'ayi ba Alhaji Ma'aruf ya iso wajen da galleliyar motarsa datasha bak'in glass, Saleema na shiga ta ce "washh wlh ba k'aramin gajiya nayi ba da wannan tafiyar". Kallon ta Alhaji Ma'aruf yayi yana wani shu'umin murmushi ya ce "yanzu hutu zai samu, amma a cire wannan hijabin". Dariya Saleema tayi ta ce "dole nacire domin ya dameni". Hanunta Alhaji Ma'aruf ya rik'o ya manna mata kiss ya ce "nayi missing sosai". Nan yaja motar a hankali suke tafiya yana matsa mata hanu har suka isa katafaren gidansa. ************** Baccin wahala ne ya d'auki Sabitu sai la'asar ya tashi, kallon agogo yayi yana mamakin irin baccin da yayi, da hanzari ya mik'e ya wanko bakinshi sannan yaje ya sauk'a akan abincin da yagani a jere, saida yaci sosai yasha Zob'on sannan ya nufi d'akin Saleema, ganin d'akin a d'an hargitse yasa ya d'au Saleema wanka ta shiga, zama yayi a bakin gadon yana rarraba ido, nan idanuwan sa suka hango masa gashin kan Saleema sai shek'i yakeyi, da hanzari ya tashi ya isa wajen, mamaki ne ya kamashi a ranshi ya ce "dama k'arin gashi takeyi, to yaya gashin nata yake"?πŸ™†β€β™€πŸ€£πŸ€£ K'awayen Saleema kun banu anfara ganokuπŸ˜… 2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ *D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I* πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯ Page 9 *Zahra ina matuk'ar alfahari dake nagode da kulawa sosai* Masoyan nasan kuna ji dani kamar yadda kuke ji da uwar mijin ku😜😜😜😜😜😜 So idan kun karanta ku rik'a turawa saboda bana samun daman hawa wtsp sosai, masu cewa daga farko don Allah lokacin da aka fara abu inkin san zaki karanta kiyita tarawa kina ajiyewa abun da yawa wani lokacin bana samun lokacin bud'e sak'o ma. Kuyita hak'uri dani readers nasan kuna k'osawa😍 _*RUBUTAWA:*_ *AISHA BICHIKI* _Princess Eshat Aysm_ _Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga mu'ata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_.... ✍ Sosai yake kallon gashin yana muzurai da bai san na menene ba, komawa yayi ya zauna yana jira ta fito, ganin shirun yayi yawa yatashi ya lek'a toilet d'in, wayam yagani ba kowa, mamaki ya kamashi, nan ya nufi d'ayan d'akin nanma bata nan, wasa wasa har magriba babu Saleema babu labarin Saleema. Memakon yayi Sallah sai ya kunna kallo zuciyar shi na d'an harbawa yana tunanin ina Saleema taje bada izininsa ba, ranshi yayi mummunan b'aci, anfara k'irayen Isha Saleema ta shigo gidan, sanye da dogon hijabinta kamar malama, binta yayi da kallo sama da k'asa, ga wani masifaffen k'amshin da take fitarwa me tsananin tsuma zuciya, sake had'e rai yayi ya ce "ina kika fito". Rausayar dakai tayi ta ce "kayimun afwa matar Alhaji Ma'aruf ne sukayi accident aka kaita asibiti, shi kuma baya gari shine ya k'irani yace naje na dubata ba kowa a wajenta, nayi ta jira ka fito najika shiru masoyi". Cikin tausayawa Sabitu ya ce "Allah sarki yanzu yaya jikin nata"? Sai da tayi kalan tausayi ta ce "baza'a ce komi ba amma taji ciwo sosai, yanzu haka an turamu Egypt ne jirgin Asuba zamubi". Zunb'ur Sabitu ya mik'e ya ce "An turasu dai, wlh babu inda zakije, haba haba wannan wace irin rayuwane". Kallo Saleema ta tsareshi dashi ganin yanda ya kid'ime, tayi murmushi ta ce "ni zanje nayi Sallah na kwanta nagaji sosai". Binta yayi da kallo harta shige d'aki, kanshi ya dafe a fili ya ce "na shiga uku, dole na koma wajen Suwaiba nasan yanzu ta koma gida". Jan k'afarshi yayi yafice a gidan. Saleema najin fitarshi tayi dariya ta ce "Na aure ka ne kawai don kazamo garkuwa a gareni Sabitu, dole nabika a hankali". Tayi maganar a ranta gami da shigewa kitchen ta samarwa kanta abunda zata ci, cikin sauri ta wanke bakinta ta zari hijabi tayi gidan Kubra. Gidane madaidaici me kyau, baza'a k'ira me gidan da Talaka ba saidai a sashi a layin masu kud'i amma ba cancan ba, a hankali ta tura k'ofar gidan ta shiga, tsaye tayi tana tunanin abunyi, can dabara ya fad'o mata ta nufi k'ofar da zai sadaka da cikin gidan, tun kafin ta gama shiga takejin shewan Kubra, wajen ta nufa kai tsaye sannan ta doka Sallama, sai da tayi sau uku Kubra ta fito tana gyara d'aurin zaninta, amsa sallamar tayi cikin farinciki ta ce "Amarya kece a gidan da dare haka, Allah yasa lafiya". Murmushi Saleema tayi ta ce "wlh harna kwanta na tuna kayan Tea d'ina nayi kyauta dashi, shine nazo ko Ahmad ne yarakani na siyo kada natashi da yunwa idan gari ya waye". Washe da baki Kubra ta ce "Haba Amarya harsai ya rakaki, ki bashi kawai ya siyo miki sai ki jira shi". Saleema ta katseta da cewa "aikan yanada yawa Auntyn Ahmad nafiso naje da kaina". Kubra ta ce "To bari na tasoshi ai harya fara bacci ma, wa'innan yaranne idonsu biyu wai suna kallo". Dariya kawai Saleema tayi, tana tsaye Kubra ta fito da Ahmad yanata magagin bacci, ruwa ta watsa masa a ido ta ce "yaro sai shegen iskanci zaka warware ne ko sai na maka duka". Sanyin ruwan ya sashi bud'e ido sosai yana cewa kiyi hak'uri bazan sake ba. Hankad'a shi jikin Saleema tayi ta ce "kayi maza ka rakata saura kayi ta mata shirme a hanya". Hanunshi Saleema ta kama suka fice tanayi wa Kubra godiya. Memakon yanda ta ce saita nufi gida dashi, key ta sanyawa d'akin ta sannan ta dubi Ahmad ta ce "zakaci abinci"? Kamar tasan yana jin yunwa da sauri ya ce mata "zanci". Abincin ta zuba masa kad'an sannan ta d'auko masa gasasshiyar kazar da taji albasa da kayan k'amshi ta ajiye masa, harda su lemo me sanyi kaman wani babba. Allah sarki Ahmad dad'i kaman ya kasheshi, hakanan yaji k'aunar Saleema ta cikasa har yana ayyanawa inama itace mahaifiyar shi, (dukkanin rai tana matuk'ar k'aunar me kyautata mata). Kubra sam bata bashi abinci sosai, idan ya karya da kunu to sai dare yakuma cin abinci, harya saba da hakan. Sosai yaci kazar bayan ya cinye abincin tass, satan kallon Saleema yayi sannan a hankali ya ce "Aunty nagode". Murmushi tayi ta ce "kullum idan kanajin yunwa kana zuwa zan baka abinci me dad'i kaji". Dad'i ya kamashi yana murmushi ya ce "toh". Komawa kusa dashi tayi ta zauna ta ce "Gobe zaka rakani wani waje, shiyasa na siyo maka kaya mekyaw, zakaje koh"? Tayi maganar tana janyosa jikinta, dariya yayi sosai yakasa cewa komi, dad'a haurawa dashi jikin ta tayi sosai ta ce "Ammafa sai kayi wanka sosai, ka dirje jikinka kada ace kai k'azami ne". Da dariyar sa ya ce "Auntyna ne bata bani sabulu idan zanyi wanka". D'an ware ido Saleema tayi ta ce "haka kake wanka babu sabulu kullum? Meyasa baka fad'awa Babanka"? Cikin wani yanayi na tsoro ya ce "idan nafad'a Aunty dukana zatayi". Hawayene yafara sauk'a a kumatunsa alamun dai yana shan wahala a wajen matar Baban tasa. Hakanan tausayin yaron yakama Saleema, kallon shi takeyi sosai tana tunanin k'udirinta akanshi, hanu ta sanya ta share masa hawayen, cikin sigar rarrashi ta ce "yanzu ka girma Auntyn ka zata daina dukanka, idan taga ka zama d'an gaye bazata dake ka ba, amma sai kamun biyayya, duk abunda nasaka kayi kada kayimun musu kaji"? Kai ya d'aga mata alamar to, cikin dabara ta rungumeshi sosai a jikinta ta ce "ka d'aukeni tamkar mahaifiyar ka, komi zan maka kada kadamu, zan baka ilimi idan ka girma na gina maka gida harda mota"! Shikam yanason wannan zancen don haka yayi ta dariya yana murna, Saleema nata hure masa kunne tana dad'a mannashi ajikin ta, gaba d'aya ta shagaltar dashi duk wani burinsa na yarinta duk tamasa alk'awarin cika masa su, sai data duba time taga 12 saura sannan ta sauk'e shi da sauri ta ce "maza kaje gida dare yayi, da Asuba kazo kayi shirinka anan sai ka rakani wani waje ko"! Ta fad'a tana janyo drowan gadonta, kud'i kimanin dubu biyar ta zaro ta sanya masa a hanunsa ta ce "ka kai ma Auntynka kafad'a mata gobe zaka rakani kasuwa". Haka Ahmad yabar gidan cike da farinciki da d'okin gari ya waye, ji yake kamar yadawo wajen Aunty Saleema da zama ta samar mishi farinciki kamar mahaifiyar shi. Koda sak'o ya isa wajen Kubra tsalle da murna ta rink'ayi tana lissafin daga yanzu zata fara lissafin kud'in da zata tara, harda cewa Ahmad yaje yayi bacci kada ya makara da tashin asuba. ****************** Sabitu yana fita gidanshi ya nufa kai tsaye, tunda yaga gidan a bud'e wani farinciki ya mamaye shi, da Sallamar sa ya shiga kamar abun arziki, Suwaiba nakan Sallaya tana addua saida gabanta yafad'i dataji muryarsa, zama yayi a gabanta yana washe baki ya ce "kin dawo ne"? Sharesa tayi, adduar ma kasayi tayi, k'arshe mik'ewa tayi ta ninke abun Sallan tayi hayewan ta gado ta kwanta. Da saurin shi ya isa yana kallon ta, dariya ma yabata ganin yanda duk ya susuce, da alamun ya wahaltu sosai, da abayane haka yake zuwar mata da masifa da k'arfi ya karb'i hakkinsa ya fita yana zaginta, lallai Sabitu yafara laushi, mamakinta d'aya yaya akayi haka ta faru bayan yanada amarya ta nunawa a Jarida, maganar k'awarta ta tuna da take ce mata "kada ki kuskura ki bashi kanki harsai yayi watanni kusan biyu dayin Aurensa, dole zai fara girmamaki yana d'aukin ki, amma kin bari yazamar dake kamar wata tinkiya". Zunb'ur ta mik'e tana harararsa jin yafara matsowa jikinta sosai, duk da tausayin sa ya kamata hakan bazai hanata neman 'yanci ba, cikin muryarta me sanyi ta ce "Kada ka kuskura ka tab'ani Sabitu, wlh kana tab'ani na gama aurenka har abada". Mamaki k'arara a fuskarshi ya bita da kallo, baisan lokacin da hawaye yafara sauk'a masa ba, wai shi Sabitu ake garawa haka, kwanciya yayi rubda ciki akan gadon ya fara tunanin farkon Auren sa da Suwaiba da irin zaluncin da ya rink'a zuba mata tana jurewa, har mace yakan kawota ya kwanta da ita a gabanta batada ikon hanawa, kukan zuci yakeyi sosai da bai san na menene ba. Matsanancin tausayin shi ne yakama Suwaiba, ta kwanta can nesa dashi itama tana share hawaye, da haka bacci ya kwashe shi, ita kuma ta mik'e tafara Nafila domin kai kukanta ga mahaliccin ta. An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels