An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»Ώ*JAMI'IN SIRRI* *C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK... (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ _Wednesday 13/9/2023 September_ *Ina mik'a jinjina gdy Yabo gadik ilahirin Masoyana nakusa Dana nesa Wad'an da nasani dama wad'an da bansani ba, Sak'onninku suna yawan zuwa gurina Koda yaushe Inajin dad'in Haka Ina Gdy πŸ™ sosai Allah YABAR ZUMUNCI* _Fatan Alkhairy gadukan masoya na, Ina d'aga Miki Hannu my Husna πŸ₯°, Yabonki k'aunar ki duk na dabanne kina k'aunar Mujaheedah saboda Allah Nima ina Inayinki overπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ_ ```BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM``` *Free πŸ…ΏοΈ 1 to 5* .......Tuk'i take Cikin had'ad'd'iyar Motar ta bak'a sai shek'i na sabun taka take daganin motar kasan An zuba million Kafin A siyeta, karatun Al Qur'ani ketashi A motar inda duk inda tawuce zaka iya Jin sautin karatun, Go slow tasamu gabanta , Siririn tsaki taja Had'id'a karkata motar tata tabi cikin wata k'aramar hanya, Duka gidajen Unguwar na Talakawa ne kallonsu take jefi jefi tana girgiza A ranta tana Fad'in "Allah ka wadatamu karabamu da talauci" Nidai Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ nace Ameen Har Tana gaf da barin Unguwar kwatsam saiga mutum tabige, ita kanta batasan Taya Akayi ta bigeshi ba, Cikin tashin Hankali ta tsaida motar tafito, Koda tafito wasu maza biyu har sun K'araso Gurin, "Nashiga Uku, ku dubamin dan Allah Bai mutu ba dai ko," tafad'a cikin Rud'ewa ganin bakinsa na fidda jini "To ke malama mahaukaciyar Inace kina Tuk'in ganganci A Y'ar k'aramar Unguwa irin Wannan,"? "Ai kasan Y'aY'an masu Kud'i Haka suke ba Tarbiya ba tsoron Allah balantana girmama D'an Adam musamman talaka ma," d'ayan ya fad'a yana gefe Abunsa baiko K'araso ba Duk da taji Zafin kalaman nasu Amma hakan ta dake tace"Ku taimaka ku samin shi mota muje Asibiti kada ya mutu," "Wa wllh nidai ba ruwana nayi Nan Sabi'u mutafi kawai,"? "Haba banyin Allah wannnan ai Rashin Imani ne bayan Ank'ad'eshi Kuma harta nemi taimakonku kan Akaishi Asibiti Amma sai ku k'i,"? Wani dattijo dayazo wuce yayi maganar "Baba mudai bazamu iyaba domin dukansu bamu San ko d'aya ba Kai inzaka iya to bismilla" suna Gama Maganar suka wuce Abunsu, Girgiza Kai kawai tsohon Yayi tareda taimaka mata Yasashi set d'in baya Yace"Maza yarinya jeki ki Kaishi Asibitin Allah ya tsare Ni nawuce," "To baba na gode ga wannnan" wasu Y'an Kud'i tabashi sannan tashiga Motar taja Cikin k'ank'anen lokaci ta iso wata Kasaitacciyar Asibiti, tanayin parking ta fito tare A rikice ta k'walawa security d'in Kira Suka Kamashi Sukayi ciki Dashi, Take Akayi Emergency Dashi, Safa da marwa tafara A waje Tama kasa Shiga ciki Saboda fargaba, Bayan wasu Awanni saiga wani doctor ya fito Yana goge gumi da sauri Tak'arasa kusa Dashi Tace"Baidai mutu ba ko doctor,"? "Come down docter Nainaaa kema fikita ce Amma kinkasa control d'in kanki Wai ma Taya hakan tafaru,"? "Kaga doctor Kafin muyi wannnan maganar Fara fad'amun Wane condition patient d'ina yake ciki" Ajiyar Zuciya ya sauke yace"Gaskiya Kamar Yasami loosing memory nasa Amma bazamu iya gasgatawa sai in ya farka" "Na Shiga Uku Ni Nainaaa, Bari na Shiga na ganshi," Bata jira Ansarshi ba tafad'a d'akin, K'ura Masa Ido tayi Yana kwance samb'al da kusan duk Rabin jikinsa rufe da zanen gadon, gansa kuwa Yasha bandage, Fuskarsa ta k'urawa Ido, duk da bacci yake cikin halin Ciwo hakan Bai Hana bayyanar tsantsar kyawonsa ba, shid'in mai Kyau ne Zuciyar ta tafad'a, Zama tayi D'aya daga Cikin kujerun d'akin ta lumshe idanuwanta gajiya takeji Sosai dama badaga gida ta fito ba tadawo daga wani k'auye ne bayan takaimusu tallafin magana sai ga Wannan Abun Kuma yasata zuwan Asibitin dole, Sai kusan 4:30 ya farka A hanakali ya bud'e idanuwansa Ya sauke kan kyakykyawar budurwar da yagani kusa Dashi zaune, k'ura Mata ido Yayi Sam batasan ya farka ba Domin Hankalinta ya Soma komawa gida Gurin Ummen ta, d'agowar da zatayi taga idansa k'yar Kanta, Da sauri tamik'e Tsaye tana Fad'in................... _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 *JAMI'IN SIRRI* *C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK... (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY. loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ *FREE πŸ…ΏοΈ 6 TO 10* ..."Sannu bawan Allah meke maka ciwo Yanzu,"? K'uramata Ido Kawai Yayi daga bisani ya d'auke kansa, Kasage tayi tana kallonsa tana tinani iri can saiga doctor San Yashigo "Ah patient d'inki ya farka docter Nainaaa Baki fad'amun ba,"? "Jikina duk ya mutu doctor San baiyi magana ba Ina tsoron banice silar rasa bakinsa ba," ta K'arasa maganar tana sake Zama cike da damuwa "Ah docter Nainaaa ki kwantar da hanakali in Sha Allah everything will be okay, bara nayi checking d'in sa nagani," Gwaje gwaje Yafara Masa Sannan Yace"Abokina Sannu, meke maka ciwo,"? Shima Ido kawai ya zuba masa baiyi magana ba, "Kagani ko doctor na Shiga Uku" "Come down Nainaaa, kada kisaka damuwa ranki d'an Adam fa bazai iya gujewa K'addarar saba," "Abokina kana wane gari Ina Y'an uwanka suke,"? Nanma shuru Yamasa baiyi Magana ba, "Wai Anya Wannan ba kurma bane kuwa? Kuma Kodai maganar loosing memory d'insa ya tabbata ne,"? "Ina tsammanin hakan Gaskiya Amma Akwai buk'atar Asami K'wararrin likitan brain su duba shi," "Kenan Zan fita Dashi waje,"? "Eh to Kafin Nan dai zanyi Magana da doctor najib Yafara dubashi tukuna idan yaga da yuwuwar fitarshi waje Kinga sai Aje," "Ni Yanzu matsalata ma Rashin maganar shi, bamusan kowa nashi ba balantana mu sadashi da Ahlinsa," "Eh Kam Kuma da wannnan Amma Yanzu kije gida ki huta Nainaaa Ni zankula Dashi dama yau till down Zanyi," yak'arasa maganar Yana daga Mata gira, Dariya tayi kyawawan hak'waranta Suka bayyana Ta mik'e Tace"to Ina godiya doctor San sai goben," Matsawa tayi kusa dashi tana Masa murmushinta maikyau Tace,"Allah yabaka lafiya patient zanje gida nadawo gobe please kafara magana kaji," Murmushi kawai doctor San yayi sukayi Sallama tawuce Shikuwa Saida ta fita yasaki d'an murmushi tareda rufe idansa bacci ya d'aukesa Shiga motar ta tayi tana gyara Zama taji ringing wayarta Koda ta d'auka taduba missed calls tayi dayawa duk na Ummee sunfi yawa Kafin tayi yunk'urin Kira wani Kiran Yasake shigowa Cikin hanzari ta d'aga "Kina Lafiya kuwa daughter meke faruwa inata kiranki but not respond," "Comedown Amma Ina Lafiya kawai nasami wata matsala ne nabige wani Amma Yanzu dai ganinan zuwa gidan" "Subhanallah to da sauk'i kuwa," "Eh Amma da sauk'i ganinan dawowa ma k'arsa maganar," kit ta k'atse Kiran Tada motar tayi tawuce, Wani makeken gida Naga tayi Hong Aka bud'e mata tashiga parking motar Tayi tafito sai yanzu na k'aremata kallon, doguwace basosai ba tanada tsayin gashi da k'aramin Baki Hasken fatarta badayawa ba kallo d'aya zaka mata kasan naira tasamu gurin zama jikinta, K'asaitaccen palourn nasu tashiga da sallama bakowa sai TV dake Aiki shi kad'ai, D'akin Amma ta nufa tarar da ita tayi Zaune tana Azkar d'in ta Da sallama tashiga d'akin tana zama gefen gadon tace"Ash wllh Ammaa nagaji dayawa kaina sai Ciwo yake Saboda gajiya," "Eyyerh Sannu daughter Yanayin Aikinku ne Haka Yanzu shi Mai jikin yaji sauk'i,"? "Eh Ammaa but still baiyi magana ba bansani ba ko kurma ne dai," "To Allah dai yabashi Lafiya Yanzu jekiyi wanka kici Abinci kiyi sallah sannan kije b'angaren Abbanki ki gaida Momynku," "Ni wllh Ammaa banason zuwa gaba d'aya part d'in Nan Wllh Matar Nan Bata sona, Ni Allah ya rufamin Asiri dayasa ke kina Raye Kuma kina kusa Dani da bansan yazanyi ba, kin hanani kukan Rashin mahaifiya, Ammaa Allah yasaka Miki da Alheri," "Ameen, Nainaaa kenan to kobata sonki tinda ta Aure Ubanki ai Dole tasoki wannnan k'in kuma ita tashafa kedai kada ki fasa mata biyayya, Ummeenki kuwa verry soon zata dawo garemu in Sha Allah," "Allah yasa hakan Ammaa inacikin kewarta , bamusan wane take Ciki ba, ko ta manta Dani ne, watak'il Kuma Ammaa Bata Sona shiyasa ta Barni," "Nainaaa Uwa Uwace kuma koyaya ne tana k'aunar Y'arta na tabbata tana cike da kewarki," "Amma Ammaa baikamata laifin Daddy ya shafeni ba Dan ya rabu da ita Bai kamata Nima ta watsar Dani ba, kawai sainakejin Ni banida wata Uwa kece Kawai Ammaaa," "Nainaaa kinsan fa idan Aka rabu tsakanin miji da mata idan mijin Mai Kud'i ne tofa da wuya yabar yaransa gurin matar, Kuma Koda ya barsu idan zatayi Aure Dole fa sudawo gidan nasu Uban, to Balantana yarda Daddyn ki yake Sonki ai bazai iya Bari tayi wani Auren taje dake Agolanci ba bayan ke ganaki Gidan Uban," "Hummmmmmm Ammanaaa kenan nadai gano kinayin Ummeena da yawa shiyasa, Nidai bazan daina Fad'in Bata Sona ba kawai ta sallamani tinda ta rabu da Daddy," mik'ewa tayi tafito d'akin ta nufa iya tsaruwa d'akin ya tsaru komai pink Toilet ta fad'a tayi Wanka tayi sallah taci Abincin sannan ta fito parts d'in ta nufa Koda ta Shiga can sainaga Wanda tafito Ashe bama Kyau bane Domin wannnan kam ba'a maganar had'uwa Anzuba dukiya Sosai, Zaune ta tarar da Mommy ta d'aura k'afa d'aya Kan d'aya Tana Danna waya k'afafunta kuwa Y'an Aikinta suna Mata tausa "Ina wuni Mommy" A walak'ance ta dubeta Kamar bazata ansa ba sai Kuma Tace"Uwar gantali sai Yanzu kikaga damar zuwa gaida ni, kunacen keda wannnan Muna fukar Matar Kuna gulmarda kuka Saba ba, hunmm ai wllh nakusa maganin ku duka, Ni tashi ficemin A palourn Mai Bak'in hali da naci," Mtssswww Itadai kanta k'asa duk da tanajin zafin zagin Amma batace Komai ba, kawai Dan takasa sabo da cin mutuncin Mommy ne amma ba Randa Bata zaginta musamman idan Daddy bai Nan sauk'in ta d'aya tanada Ammaaa da Tabbas zaman gidan saiya gagareta, "Haba Mommy Dan Allah ki sassautawa Baiwar Allah Nan ," "Iyee Haira Ni kikewa fad'a? Wato gaki ke sallamammiya ke Mai Y'ar uwa ko? To wllh har ke Zan had'a dake nayi maganin ku banza shasha kawai," Mik'ewa Nainaaa Tayi tafice cikin sauri Haira tabi bayanta tanajin Mommy na zage zage Amma Bata dawo ba, Rik'o hannunta tayi tace"Dan Allah sister na kiyi hak'uri bansan meke damun Mommy ba Amma dai ko Yaya ne kada wannan matsalar ta shafeni nidai wllh ke Y'ar Uwatace Kuma duk rintsi Muna tare, Kawai ki k'ara hak'uri," Murmushin yak'e kawai tamata tareda cire hannunta daga nata tawuce, Saida ta b'acewa ganinta sannan tadawo palourn lokacin Sagar yayanta Yadawo Suka had'e sukamata Tass itadai Bata tankasu ba Kuma tasa A Ranta ba Wanda zai rabata da Nainaaa wllh.. Tana komawa d'akinta tashiga tafad'a Kan gado tana tinanin rayuwa tana kuka har dai bacci B'arawo ya sace ta...... To nace Assubah tagari................................ _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 *JAMI'IN SIRRI* *C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY. loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ _Friday 15/9/2023 September_ *Free πŸ…ΏοΈ 11 to 15* .....Jimawar da tayi batasami baccin ba Hakan yasata makara, "Daughter Wai bazaki fita Aiki bane Yau," Mik'ewa Tayi Tace"wllh Ammaaa yau baccin ne Yakasa barin Idanuwana," "Daughter Dole bacci yasaki gaba, Baki kwantawa da wuri ga Yawan tinani kada kijawa kanki wani ciwon daban, Yanzu tashi kiyi Wanka kizo kiyi break fasts," Mik'ewa Tayi tashiga toilet Already tayi sallah shiryawa Tayi tafito parlourn harta zauna zata Soma cin Abincin wayarta tafara k'ara doctor San tagani Rubuce Tana d'agawa Tace"I'm so sorry doctor but I'm coming now" tana Gama Fad'in hakan ta k'atse tareda mik'ewa "Ah tafiya zakiyi bakici komai ba,"? "Ammaaa kin manta Inada patient Kuma better tinkan Akirani Yakamata na kasance wurin, Amma Asamin A baskets sainje Masa dashi ma," Delu Mai Aikinsu tazuba Mata takai mata mota Sannan tashiga tawuce, Parking motar tayi sannan ta d'auke basket d'in tashiga ciki, direct office d'inta tashiga saida tagama settling komai nata sannan tafito office d'in doctor San taje but Yana Rufe hakan yasa tanufe D'akin da Aka kwantar da mutumin Tura k'ofar Tayi da sallama tashiga Dukansu Ido suka zuba mata bama kamar guy d'in domin ta burgeshi Sosai Komai nata slow cikin natsuwa da Hankali Doctor San Yace"Kin manta Damu ba Kuma inatason naje gida Amma ba dama," "Dan Allah kayi hak'uri wllh na makara ne Amma Yanzu gani Yaya Ake Ciki kayi Magana da doctor najib d'in,"? "Eh yazo tin jiyan ma Kuma yaduba komai normal Saidai eh Yasami loosing memory d'insa Saidai idan yaga wani Abu daya shafe Rayuwarsa tabaya to zai iya tinawa ya dawo daidai," "To Amma doctor San Maganar tasa kuma fa," Hahahaha"kinzata Wai Bai magana Yanzu ma Saida mukayi magana dashi yace ruwa Saidai na lura miskiline na K'arshe shiyasa duk Magana inbatazama dole ba tofa bazai yi taba," Maida kallonta tayi kansa saitaga ya d'auke Kansa yawani had'e Rai Matsawa Kusa Dashi Tayi ta zauna Had'id'a zuba masa Abincin da tazo dashi pepper soup ne da shinkafa mik'amasa Tayi Tace,"Kaci Abinci kadaina B'ata Rai bafa da gangan na bigeka ba, Ni banma San na bigeka ba Kawai saiganin ka nayi kwance idan za'ayi tuhuma Kai Zan tuhuma d'an Samari," tak'arasa maganar tana wani farr da idanuwanta Murmushi ya sub'uce Masa Dan shi harga Allah dariya tabashi, "Yawwa idan kanayin magana da murmushi to Zan fasa tuhumarka, Yanzu kaci Abinci ka Huta Kafin nagama da Sauran patient d'ina sainazo Muyi Magana dakai," Bata jira Ansarshi ba tawuce dama doctor yajima da fita, Saida tafita sannan ya d'auke Abincin yaci, Tajima Kafin tagama tadawo Zaune ta tarar Dashi ya jingina da gadon, Sallama Tayi Ai kuwa ya Amsa Ahankali Saida taji wani iri dajin saukar Muryarsa, Zama tayi daga cikin kujerun d'akin Tace"Sannu bawan Allah yajikin naka," "Da sauk'i" Yafad'a Atak'aice idanuwansa na rufe "Masha Allah A yanzu dai kasami sauk'i kaga Yakamata Asallameka so Ina zankaika Ma'ana Ina Ahlinka suke," Shuru harta cire ran Zaiyi magana Sannan ya Ware manyan idanuwansa kanta cikin sanyi da Alamar tausayi Yace"bansani ba nima bansan kowa ba saike, Ni ba d'an Nan garin bane Amma namanta Ina nake bansan Komai game Dani ba Yanzu," Wasu Hawaye Suka Soma silalo Masa Cikin Jin tausayinsa Ta matso inda yake tace"kada kadamu Akai nice silar faruwar Komai Dan Allah ka yafemin zanje dakai gidanmu ka zauna Kafin Allah yasa Katina Komai naka, Amma ya sunanka,"? "Sunana Abbas Shine Kawai Zan iya tinawa saboda Naga wannan tare dani, karancin passport d'auke da sunan Abbas Akai, Amma hakan zaiyu kuwa? Iyayenki zasu Bari na zauna daku bayan basusan Ni kowaye ba, ko Ni bansan waye Ni ba balantana nayi musu bayani idan Suka buk'ace hakan," "Kada kadamu Kan wannnan idan nayi musu bayani zasu fahimta Kuma ma Daddy na bayanan A Yanzu Amma nasan very soon zai dawo, Yanzu ka d'auki duk Abunda kake buk'ata Kazo muje kawai," tana gama maganar tafice Binta Yayi da kallo Yana Aiyana Abubuwa dayawa Aransa Had'id'a sakin murmushi, _NI DAI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ KALLON IKON ALLAH KAWAI NAKE NAKASA FAHIMTAR KOMAI GAME DA WANNNAN MUTUMIN," Saida tagama Komai sannan Sukayi Magana da doctor San ya rakosu har mota suka wuce shikuma ya koma, Kallon hanya Kawai yake har Suka Isa bawanda Yayi magana Bayan Tayi parking ta fito tareda Kiran Mai gadi da Sauran masu kula da Gidan Tace,"kunga wannnan bak'ona ne, so Yanada ikon Shiga ko fita duk Sanda yatashi idan Kuma wani yanemi Wani Abu kanshi kawai kuce yasameni, banason sa'ido ko Shiga hurumin da baishafe mutum ba, Ina fatan kun fahimce Ni," "Eh madam munfita Kuma in Sha Allah zamu kiyaye," "Yawwa Masha sunanshi Abbas, so Shine kawai zaku iya komawa Kan Aikinku nagode," "Muje ciki ko Abbas" Binta Yayi Suka Shiga parlorn Kallo Yafara k'arewa palourn "Zauna Bari Nakira Ammanaaa ku gaisa" Gyad'a kansa Kawai Yayi tareda zama, itakuma tahaye sama D'aga kansa Yayi Yana kalle kalle can idanuwansa suka fad'a kan wani photo k'ato Dake manne A bango, Itace cikin shigarki Likitoci da Sauran mutane gefe sai sai wani mutum data rik'e shima Yana rik'e da ita suna dariya ga A Ward's tsakansu, "Ba shakka wannnan Shine," Ya fad'a cikin zuciyarsa tareda cije lip's d'insa na sama, Jin Alamar Ana saukowa k'asa yasa da sauri yakoma ya zauna, Fitowa sukayi tareda wata mata, Sauka yayi k'asa Yana gaida Matar Cikin fara'a ta Ansa Tace"A'a tashi ka zauna Abbas ai tafad'a mun komai kada kadamu bamuda matsala kasake ranka kaji ka d'auka kamar gidanku, Kuma itama ka Zama yayanta idan kaga tayi kuskure kamata fad'a ta Gyara, Ai Nainaaa mutuniyar kirkice tanada tausayi fatanmu Allah yabaka lafiya Kawai," "Ameen Ameen Ammaaa Ngd in Sha Allah zanzamo Nagari gareku," kansa A k'asa yake Maganar K'uramasa Ido tayi tana murmushi itadai Yana burgeta Wllh, "To kin fad'ama Daddyn ki Saboda gudun matsala" "Ammanaaa kinsan samun wayar Daddy it's not easy Always he is busy but I will trying to charts on WhatsApp," "Hakane Amma kiyi gaggawar fad'a Masa kinsan Yanayin gidan naku dai," Tak'arasa Maganar tana mik'ewa "Ammanaaa Ya Hassan ya kirani yace gobe zasu dawo fa," "Eh Nima sun fad'amun Allah ya dawo Mana dasu lafiya kawai," "Ameen Ameen, Zan Nuna Masa inda zai zauna" "Eh Hakan ya kamata kam," " Maida kallonta tayi gareshi kanshi Ak'asa, ga Alama Dai yana kunyar Ammaaa "Ya Abbas kaidana Jin Kunya ko wani d'ari d'ari everything will be normal bamuda matsala ko gun Daddy bazan Samu matsala ba Domin yana sona kuma Yasan bazanyi Abu Mara Kyau ba, so tashi na nuna maka inda zaka zauna," Tashi sukayi suka nufe waje wani parts dake kusa Dasu Yana Rufe ta kaishi d'akin 2 ciki da palour sai kitchen store dama Toilet, D'akin ya had'u ba datty Komai Pink ne ciki shima, "Fatan d'akin ya maka," "Sosai ma kuwa yayi Kyau musamman tsarinsa da kalarsa Komai Pink Amma na Mata ne ai," Dariya Tayi Kafin tace"itace best colors d'ina Pink shiyasa duk Abunda Yake Under control d'ina nakan Masa zab'i irin nawa," "Ai Kam dai Yayi Kyau Sosai, Nainaaa" "Au kasan sunana Ashe,"? "Habadai sau nawa Aka Kira sunanki gabana? Ai dole na rik'e," "Um hakane Bari na Barka kahuta ko, sai Anjima Amma idan kana buk'atar wani Abu kamin Magana Kuma ba shamaki ka iya zuwa part d'inmu Koda bana Nan Ammaaa tana Nan zata yimaka koma meye," "Ina godiya sosai da wannan karamcin Nainaaa Allah yasaka da Alkhairi Yabani damar yimiki Abunda Kika min koma fiye da Hakan My Nainaaahh," Yaja sunan Cikin Cool voice d'insa, Sosai taji dad'in hakan murmushi Kawai tamasa Had'id'a juyawa tafice................................ _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 *JAMI'IN SIRRI* *C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY. loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ _SATURDAY 16/9/2023 SEPTEMBER_ *Free πŸ…ΏοΈ 16 to 20* _SECON TO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH_ *IDAN KINA SO KANA SO KABIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA MASU SIYE KU FITARMUN DA BOOK KUDA ALLAH BAMASU KARANTAWA BASU BIYABA SUNAGANIN SUNSAMI BANZA KUMA KUDA ALLAH, BAZAN YIWA KOWA ALLAH YA ISA BA AMMA KUNSAN BAKUMIN ADALCI BA HAKAN YASA NACE KUDA ALLAH,.. 300 NE KAWAI BA YAWA, ALLAH YASA MUDACE AMEEN* ...........Kwanaki sunfara tafiya inda Yanzu satin Abbas 3 Cikin gidan shak'uwa soyayya Mai tsanani tashiga tsakaninsu Musamman Nainaaa sosai take son Abbas ba kad'an ba, Kullum suna tare indai tadawo Aiki ko in bataje ba, Duka Ahlin gidan sunsan da Soyayyar da ke tsakaninsu,, Yanzuma tana Zaune A garding d'in gidan tana Shan iska laptop ce gabanta tana Magana da Daddy, "Allah daddy mutumin kirki ne na k'agu kadawo ku had'u Daddy harda Aiki nakeson kabashi, Daddy yaushe zaka dawo,"? "Oh Daughter Lalle wannnan Yaron kina Sonshi ba kad'an ba, Amma kina ganin Bawata matsala kinsan fa d'an Adam sanin sirrin zuciyar mak'iyi sai Allah, sautari Mutum zai rab'ekane don biyan buk'atar sa dazaran Yasamu saiya gujeka," "Daddy shikam ba Haka yake ba, Kuma in Sha Allah had'uwar mu Alkhairi ce nidai da Zuciya d'aya nake tare dashi shima hakan ne in sha Allah," "Shikenan daughter nalura dai wannnan Abbas d'in yagama siyemin zuciyar Y'a, in Sha Allah cikin satin Nan zandawo Kinga saina zauna dashi daganan muyi Abunda yadace Ai duk Abunda kikeso shi Zanmiki daughter," "Yawwa Sweet Daddy Inasonka Sosai, bay bay," ta k'atse Kiran Duk Abunda take Yana hangosu ta window d'in d'akinsa domin tanan garding d'in yake, murmushi Kawai yake zubawa Had'id'a cizar lip's d'insa, Komawa yayi ya zauna Yajanyo wata jaka Naga ya fidda wata laptop Yasoma dannawa Yajima Yana Aikin sannan ya Rufe, Jin motsinta zata shigo yasa Yayi sauri b'oye laptop d'in da jakar duka Yadawo Cikin sauri ya kwanta Had'id'a rufe idanuwansa Kamar Mai bacci, Da sallama tashigo Ganin Yana bacci yasa tayi murmushi Had'id'a juyawa tafice, A parlourn ta tarar dasu Duka suna fira gwanin Sha'awa itama ta zauna Suka soma tanajin inama Ace su Daddy da Ummeen tane haka? Saurin kawar da tinanin tayi domin zai iya sakata damuwa Kuma Babu Abunda ta rasaga Ammaaa, itadai batasan dad'in Uwa ba hakama Mahaifinta batasan shak'uwa ba Saidai suyi waya ko video call on WhatsApp tana wata bataga mahaifinta A Zahiri ba, batasan Aikin me Yake fita ba, Always Yana k'asar waje Abun Yana damunta Amma Batada yarda zatayi, *SU WAYE SU NAINAAA?* Alhaji Salman Cikakken d'an kasuwa ne Wanda duniya tasan da zamansa Yana had'akar kasuwa da mutane daban daban Cikin kasuwancin nasa ya had'u da Alhaji Sale Mai gold suka Soma kasuwanci tare, sosai suke Samun riba kuma Ahankali Aminci yake k'aruwa tsakaninsu, hakan Yasa sale Mai gold yabawa sale Mai gold yabawa Salman Auren k'anwarsa Hajara bayan tanuna tana sonshi shima Haka, Sosai Aka Sha biki saidai Abunda Basu sani ba Alhaji Salman Yanada mata A b'oye batare da Yafad'a musu ba Wadda ko iyayensa basusan da Aurenta ba, zaman lafiya suke cikin wasu Y'an Shekaru Tasami Ciki ta haife Y'arta Mai Suna Nainaaa zo kaga murna tattali kulawa soyayya wadda Daddy yake yiwa Nainaaa Domin sunan mahaifiyarsa data rasu Aka samata, Duk wata k'addara tashi dawasu company wad'anda Yasami ta k'ark'ashin Alhaji Sale Mai gold yayan Hajara duk ya mallaka Komai da Sunan Nainaaa, Koda d'ayar matarsa Mommy taji hanakalinta Yayi Mugun tashi ganin ta Shekara dashi Kuma ga d'anta Namiji Amma ba'a yimasa wannnan Kyautar ba sai waccan Mai kamada Aljanu, hakan Yasa taja k'awarta Suka garzaya Bak'in daji inda bokan Tsauni sukayi Mugun Asiri ga Alhaji Kuma ranar ta kwaso kaya suka dawo gidansu Nainaaa, Suna Zaune palourn itada Alhaji suna fira Cikin Soyayya y'arsu naga Hannunsa Yana mata Wasa A Lokacin Bata Wuce wata 3 ba, Kwatsam saiga Mommy tafad'o d'akin ko sallama Babu tafara masifa, "Lalle Alhaji wato Saboda ka Aure Y'ar masu Kud'i Shine zaka walak'anta mu to muma mundawo Nan da Zama ba inda zamu," Mik'ewa tsaye Ummee Tayi Cikin mamaki tace,"Baiwar Allah lafiya Zaki shigowa mutane cikin gida Haka kina d'aga Muna murya," "Ke dakata kada ki fad'amun maganar Banza Ni Nan dakike Gani Ni matarsa ce wannnan Kuma d'ansa sai d'an k'aramin cikinsa dake jikina yanzu haka, dama Bai fad'a Miki Yanada mata ba ya Aure ki,"? Cikin tashin Hankali ta juya ta kalle Daddy da kansa ke k'asa ya kasa magana Saboda Kunya Tace"kenan Abunda wannnan Matar ta fad'a Gaskiya ne," Kasa magana Yayi Dariya Mommy ta shek'a tace"Taya ko zai fad'a Miki tinda bakece gabansa ba tinfarko saboda Tara dukiya ya Aureki yanzu Kuma muntara to saiki k'ara gaba, Kai Alhaji Salman ka saketa Tak'ara Gaba," "Kije na sakeki saki d'aya Hajara, Kuma ba Wanda zai rabani da Y'ata Wllh duk duniya," Yana Gama maganar Yawuce d'auke da Yarsa, Kuka ya kwacewa Ummee tana danasanin Auren Daddy, Haka Mommy tasa d'anta Sagar yama Ummee walak'anci ya korata waje bako takalmi, Tana kuka tabar Gidan, ba kalar wahalar da Bata Sha Saida tasamu wani gida Aka d'auketa Ai katau Sannan tasami Kud'in komawa gida labari tabawa yayanta tana kuka, Abun yayi matik'ar k'ona Ransa Shida d'ansa Na'if Kuma ya kullace ganin bayan Daddy, Koda sukayo bincike ba inda Basu duba ba Amma ba ko Alamar Daddy ya kwashe komai nasa yabar gari, Bayan yabasu wata takarda Mai d'auke da shaidar mutuwar Nainaaa, Hakan yak'ara d'aga hanakalin Ummee har Rashin Lafiya tayi Domin tana masifar son Y'arta, da kyar Asami ceto Rayuwarta Bayan wasu shekaru ta Aure wani mutum Saidai koyaya ne Zuciyarta nagun Salman Allah baisawa Auran Albarka ba suka Rabu, A yanzu duk Iyayen Salman sunjima da rasuwa Y'ar Uwarsa Binta ce kawai tarage Ammanaaa tana Auren talaka yaronta d'aya Hassan Domin Hussain d'in sa ya rasu, mijinta bamai k'arfi bane hakan Yasa Alhaji Salman ya maidasu Sabon gidansa daya Gina A Abuja suka tare Dukansu Nan yabata Nainaaa Rik'o domin Mommy Tace Wllh bazata Rik'a taba, Ammanaaa tayi fad'a Sosai ga d'an Uwanta na wannnan Abun dayayi Amma baice Komai ba Domin kuwa sihiri Yana yawo Kanshi, Ammanaaa tarik'e Nainaaa tamkar itace ta haifeta kulawa Sosai take bata, duk iya k'ok'arin Mommy ganin taga bayan Nainaaa da Ammaaa Abun ya faskara Hakan Yasa ta d'aura musu muguwar tsana A gidan, Tayi duk Abunda zatayi Wanda ko Labarin Hajara Daddy baison Yaji Kuma ya damfareta Kud'i Masu nauyi yakawo gida Mommy ta kwashe, tayi sama da Fad'i Dasu Amma ya kasa magana, Abunda duk Basu sani ba tindaga Kan Rabuwarsa da Ummeeen Nainaaa zuwa Kud'insu daya damfara duk Aikin sihiri ne Mommy Tayi Kuma Sagar dayake ma kallon d'ansa yana kashe Masa duniya ba d'ansa bane d'an bokanta ne can tasamo cikin Amma ta Nana Masa Batareda ya sani ba, Hairat ce kawai Y'arsa Shiyasa take k'aunar Nainaaa... *MUNDAWO LABARIN.....* Tsaf suka shirya ita dashi gwanin burgewa suka fito, "Wai nikam Ina Zamuje ne my Nainaaa,"? "Oh my Abbas bafa saidaka Zanyi ba," "Hahaha Inama Zaki iya Saida gudan jinin Masoyin ki," Dariya tayi tana bud'e Masa motar "yau Kai zakayi driving d'inmu," "Laaaa My sister and brother Shine zaku fita badani ba? Aikuwa Allah ya kawoni Dan Dani Za'a," tana Gama maganar tashige bayan motar Dariya sukayi duka suka shiga Suma Suna fira, "Ina muka nufa ne wai," "Wannan Mall d'in kasan gobe Daddy zai dawo shine nakeson muyi siyayya," Cije lip's d'insa Yayi cike da Samun nasara Yace"Amma kuwa nayi farinciki da Zan had'u da Daddy zakuyi surprise Ashe," "Surprise kuma,"? Cikin sauya Akalar maganar Yace" Eh surprise d'in ganin surukinsa ba, Munkawo, mushiga," Rufe fuskarta tayi suka fito Suna dariya, Ciki Suka Shiga suka Lodi Kaya sosai, wani zobe Mai Kyau ta d'auko takama Hannunsa tasa Masa A yatsa Tace" wannnan Alk'awarin mu ne, Ina sonka sosai my Abbas kaine farinciki na kada ka juyamin Baya domin Zan iya Shiga wani Hali idan kabarni Ina sonka so Wanda bazan iya Fad'ar farkon Saba balantana k'arshensa Ina sonka duk da bansan kai waye ba, Kuma na Yarda na Aure ka duk da bansan suwaye Iyayenka ba, Dan Allah kada kacutar Dani Abbas," Tak'arasa Maganar tana zubda Hawaye Jikinsa yayi mugun Sanyi Zuciyarsa tabuga da k'arfi wata zufa tasoma k'aryo Masa, Cikin k'arfin Hali da Yak'e Yace"Ina tare dake my Nainaaa, Shima ya d'auke d'ayan zoben A zurfa da ke Hannunsa ya samata," "Oh sarakan soyayya Nima dai Allah yaban nawa Masoyin sai mutafi ko nawuce Abuna," Dariya sukayi suka wuce...................... _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 *JAMI'IN SIRRI* *C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY. loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~DπŸ‘¨β€πŸ’»* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ _SUNDAY 17/9/2023 SEPTEMBER_ *FREE πŸ…ΏοΈ 21 to 30* ```LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH,.. IDAN KINA KANA SO TO KABIYA 300 KAWAI KA MALLAKE ABUNKA, IDAN KINSAN DAN KIFATARMUN BOOK WAJE ZAKI SIYA TO KIBAR KUD'IN KI NABAR LITTAFINA IDAN KIKA SIYA KIKA FIDDA IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYABA KAWAI KEDA ALLAH DOMIN NA WAHALA GURIN RUBUTUN ABUNA, KUMA BA SATAR FASAHA NAYI BA NAYISHI NE DA BAIWAR DA ALLAH YAMIN TO DAN ALLAH KADA KI KARANTA COMPLETE BUK D'IN NAN IDAN KESAN BAKI BIYA BA DAN ALLAH``` ........Gaba d'aya gidan ya Kaure da k'amshi sai soye soye da girke girke Ake ta ko wanne fanne domin Mommy nayin nata Nainaaa ma sunayi itada Ammaaa Yau gaba d'aya Tayi busy shiyasa ko Hospital Bata shiga ba ko wurin Abbas yau Bata lek'a ba Domin tin Assubah take Aiki, Tsaye tayi tasa fruit d'inda take yanka Agaba tadaina Aikin Hairat ce tashigo kitchen d'in tana Fad'in"Sister Nainaa kizo muma muje tarbo Daddy Airport gasu Mommy suntafi," Shuru tayi Domin Sam hankalinta baya gurin, Dafa Kafad'arta Hairat tayi Cikin damuwa tace"Sister meke damunki wannnan dogon tinanin fa,"? Sai A Sannan tadawo hayyacinta, ta kalle ta tayi shuru batayi magana ba, "Haba sister Nainaaa Meyasa kike min haka? Baki K'aunata Sam Baki d'auke Ni cikin Y'an Uwanki ba Yarda ma kike k'aunar Ya Hassan shida yake d'an K'anwar Daddy wllh nida muke Uba d'aya Baki min wannnan k'aunar kodan nafito daga tsatson mommy,"? Kama Hannunta tareda yin murmushi tace"bako d'aya Hairat Kuma zakiga canji tare Dani in Sha Allah kiyi hak'uri Komai ya wuce, mema kike cewa,"? "Idan har da Gaske kin d'auke Ni Y'ar uwa ba Y'ar uba ba to ki fad'amun meke damunki meyasa ki wannnan tinanin,"? Hunnmm"wllh bansani ba Hairat Amma Tinda natashi nakejin fad'uwar gaba dama bugawar zuciya sosai Kamar wani Abu mara Dad'i zai faru, har mafalki nayi Amma nakasa gane meye Kuma Kan waye," "Oh sis mafalki ba Gaskiya bane tayu duk ma d'aukin zuwan Daddy ne tinda Yana zuwa sai maganar Amarcewa wannnan Shine fargabarki," tak'are maganar tana dariya Itama dariya Tayi tace"bakida dama Yanzu kindaina kunyata," "Habadai ai Kan Auren ku da bro Abbas ba kunya, Kinga Tashi muje muma A taro Daddy Damu," "To Muje" Aje kayan tayi suka fad'ama Ammaaa sannan suka fito, "Bara nacema Yazo muje" Nocking k'ofar Tayi tad'an Jima Kafin ya bud'e murmushi suka sakarwa juna, Tace"jirgin Daddy ya sauka Yanzu Zamuje Airport ne kazo muje," "Kai haba Daddy ya sauko, Masha Allah, Yanzu kinsan me bazan Sami zuwa ba Zan k'ara kintsa kainane Kafin ya iso sai mu had'u," "Kintsawar me kuma saikace yau Za'a d'aura Auren,"? "Nainaaa Kenan bazaki ganeba ne nidai kuje kawai sai kundawo yanzu bara nashiga wanka idan kundawo sai mu gaisa dashi," "Shikenan tinda kace haka sai mundawo," "To Allah ya tsare" "Ameen" Wucewa Sukayi Yakoma d'akinsa yau farinciki yakeji Sosai Ransa Fess domin daf yake da cinma Burinsa, waya Yafara nidai bansan meyake fad'a ba Kawai Naga ya tsuke fuska Yana Magana k'asa k'asa ne, Koda suka Isa jirgin Daddy ya sauka Yana saukowa Kan jirgin da gudu Nainaaa da Hairat suka rungumeshi suna murna, Hakama mommy duk wani Bak'in halinta ga Nainaaa b'oye shi tayi Suka rankaya mota suka nufe gida, Jin k'arar shigowarsu yasa ya lek'o ta window yana ganin fitowar su murmushi Kawai yake ya koma Yana Shirinsa Cikin Bak'in suit, Kai tsaye palourn daddy suka Wuce, Yace"Yato Yanzu kubari nayi wanka idan nafito sai kowa yazo muyi fira," Hakan kuwa sukayi Saida Yayi wanka Yashirya tsaf Cikin had'ad'd'iyar jallabiyarsa Yafito palourn Ancika Masa daining da Abinci tare Suka zauna suna CI suna fira gwanin Sha'awa Saida suka Gama suka dawo tsakiyar palourn Suka cigaba da fira, "Yawwa mamana kije kizo da bak'on naki na ganshi yanzu ya kamata mugana Ai," Cikin Jin Kunya tamik'e tana Fad'in"to Daddy" Nocking tamasa ya bud'e k'ura Masa Ido Tayi Ganin ya shirya cikin suit Bak'i Amma fa yayi kyau ba kad'an ba, "Ya Abbas Irin Wannan Shirin Haka saikace zaka wani Aikin,"? Murmushi Yayi Yace"Daddy yace nazo ba, kidai muje Kawai ai yau Rana ta musamman ce Yau zanyi surprise D'INKU duka," "Allah ko to bani Nasha ko kad'an ne,"? "Habadai Ina Kika tab'a gani ko ji Ai Saidai Acan muje kawai," Jerawa Sukayi suna fira har Suka Isa palourn yashiga komawa tayi d'ayan kujerar ta zauna shikuma ya zauna k'asa Yana gaida Daddy "Ansawa Daddy Yayi Cikin fara'a yace Sannu Ai naji Labarin ka Sosai Kawai sai yanzu Allah Yayi zamu had'u," "Eh Daddy Hakane Sannu da zuwa ya Hanya," "Alhamdulillah," Fira suka hau tadashi A sace yake tab'a Wayarsa Yana gamawa ya Tura ta Aljihu, Mik'a masa Hannu Daddy Yayi Yace"kazo mu gaisa Mana ai Yanzu mun Zama d'aya Abbas tinda har Y'ata take sonka," Cikin Jin kunya ya mik'e tsaye Yanufe sa Yana Isa inda yake yasa Hannu bayan wandonsa saiga Bindiga Yaciro ya d'aurawa Daddy Agoshi tareda cewa "you are Under Arreste Alhaji Salman" Dukansu cikin tsananin mamaki Suka mik'e tsaye Banda Nainaaa da idanuwa Kawai ta zuba masa Cikin k'arfin hali Daddy yace"Arrested for what," "Idan mukaje zakaji, kanayin wani motsi wllh saina fasa kanka da Bindiga," Yana Danna wani madanni take d'akin Yacika da sojoji ko wanne Cikin bak'ak'en Kaya kuma d'auke da k'atuwar bindiga, "Zo kasaka Mai Handcuffs mutafi," Ganin Za'a sawa Daddy handcuffs d'in yasa ta mik'e Cikin Yanayin mamaki tsoro fargaba tace," Are you out of your Sense Abbas mahaifina zaka kama mahaifina zaka sawa Handcuffs kodai kasha giya n,....," "Ke Yarinya ki iya bakinki kisan da wa kike magana Ogerh ne gabanki yafi Gaban Raini, yanzu saina fasa kanki da bindiga," "A'a dakata better tasan Komai A Yanzu," "Ni ba Abbas Sunana ba, Na'if sale Mai gold shine Cikakken sunana, nazo ne daga cikakken sashen bincike na Farin Kaya wato C.i.d in shout Ni *JAMI'IN SIRRI C~I~D* ne daga Babbar Headquarter dake Abuja, kawai Aikina yakawo Ni Rayuwarki Domin Kama wannnan Azzulamin Uban naki," "Abbas kasan me kake fad'a kuwa,? Hatsari Zama Asibiti loosing memory Soyayyata Duka cikin Aikinka ne Kenan," "K'warai kuwa Nainaaa, Duka nayi Amfani dake ne dama Sauran likitan dakika sani Ni sukewa Aiki saboda Ni doctor San Yakoma wannnan Asibitin taku Ni lafiya nake bana tare da komai," Wasu zafafan Hawaye suka Soma gudana daga idanuwanta Tace,"Meyasa zakayi Amfani da Ni gurin kassara rayuwata,? Me mahaifina yamuku," "Laifinsa Mai girman ne domin Ni kaina ya cutar da Ahlina Kuma ya sace dukiyar mu Kuma mun kamashi da safarar miyagun kwayoyi musamman Cookie hodar iblis, Kaisa mishi handcuffs d'in muje," "Okay Sir," Saka mishi handcuffs d'in yayi suka jashi zasu fita Cikin sauri ta Shiga gabanshi Hawaye kezuba daga idanuwanta Tace"kacutar Dani cuta mafi Muni karabani da Sauran farinciki na Natsane ka Na'if wllh Allah bazai Barka ba Kuma Sainayi Shari'a dakai wannnan b'acin Sunan da Kama mahaifina bazai tafi Abanza ba, kayi Amfani da Raunina da Soyayyata ka rabamu da farincikinmu Allah ya Isa tsakanina dakai," Sosai kalamanta suka masa zafi Amma ya daure fuska d'aure suka fita da Daddy Cikin Gidan, "Shikenan shegiyar yarinya takawo Annoba da kanki kinkawo K'arshen mahaifinki hasararriya kamar dai uwarta," Mommy tafad'a cikin kuka da barin d'akin Durk'ushewa k'asa Tayi tana kuka Mai ban Tausayi tana Fad'in"Kenan harda soyayya ta Duka Shirice Wai Abbas ne ya yaudare ni,? Ammanaaa ku tayar Dani daga wannnan mugun mafalkin danake,"........................................ *Kash gashidai MUNKORO Amma Saidai Kash laifin Dad'i k'arewa, Anan Free page YAK'ARE idan kina Kana so kabiya 300 Kawai ka MALLAKE naka,* _SHIN YA ZATA KAYA KUNA SANE CEWA YANZU WASAN YA D'AUKI ZAFI KUWA? HUNMMMM YANZU ZAMU FARA LABARIN, SHIN DADDY ZAI KUB'UTA KUWA? SHIN DA GASKE ANKAMASHI DA SAFARAR MIYAGUN KWAYOYI? SHIN INA LABARIN MAHAIFIYAR NAINAAAHH ZASU HAD'U KUWA? WACE TARBA NAINAAA ZATAWA MAHAIFIYAR TA? SHIN NA'IF ZAI GANO NAINAAA ITACE YAR AUNTYN SA KUWA? WANE HALI ZAI SHIGA IDAN YAGANO CEWAR NAINAAA Y'AR UWARSA CE? SHIN SOYAYYAR SU TACIGABA ZASUYI AURE KUWA? WANE IRIN MATAKI NAINAAA ZATA D'AUKA??????? TO DOMIN SANI MU KASACE CIKIN NEXT PAGE KUMA DA 300 D'IN KU KADA KIBARI KADA KABARI WANNNAN K'ASAITACCEN LABARIN YA WUCEKA.............. JAMI'IN SIRRI C~I~D.... HUNMMM RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI A MALE.........._ _KUTAYANI ADDU'A ZANYI EXAM KUMIN FATAN NASARA FANSSS,_ _BASEEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels