An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ _26/7/2023 Jully Tuesday_ *BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM* *Free 🅿️ 1 to 5* .......Wani Matashin Saurayi nagani Zaune kusa da Ahlinsa sai fira suke cikin k'aunar juna, "Samar!" Matar takira sunanshi cikin serious voice, Jin hakan yasa ya maida Hankalinsa kanta Domin ba kasafai take Kiran sunan shi ba, saidai tace tace Soja, hakan ya tabbatar masa Abunda mama zata Fad'i Mai Mahimmanci ne, "Na'am Umma," "Soja kanada Aikinyi Yanzu kuma ko mahaifinka nada Arzikin maka Aure Koda Kai bakada Abun kace Abari kasamu Aiki Yanzu shekara 3 kana Aikin kasami K'arin girma kuma kasami Kud'i to yanzu kasamu Wadda zaka Aura," "Mahaifiyar ka nada Gaskiya Yanzu kayi shekara 30 fa to ya kamata kayi Aure soja,"Cewar Abba Hunmmm: Shikenan In Sha Allah Zan k'ok'arin neman Wadda ta dace," "Masha Allah, Allah yakawo tagari," Wayarsa tafaru ruri sunan Taj ya bayyana Cikin murmushi yad'aga Kiran Yace "Hello my friend Yane,"? A d'ayan b'angaren Akace "normal kaga sak'o ta email d'inka Major Yana nemanmu da gaggawa Kan wani Assignment zamuje,"? Gyara Zaman wayar yayi Yace"Assignment kuma? Bayan Munsami hutun 1 months wane Assignment kuma,"? "Nima ban sani ba wallahi na d'auka ma kaga sak'on da shine zanyi wannan tanbayar Yanzu mukayi magana dasu Sam itama tayi mamakin Abun Amma koma yayane idan muje Abuja Gobe masani," Hunm: "Shikenan badamuwa sai mun had'e goben" Katse Kiran yayi ya duba Email d'in Tabbas Anason ganinsu gobe, Fad'ama Iyayensa yayi suka masa fatan Alheri sannan ya hau Shirin tafiya............ **********"""""""""''******** "Sam wai kina macce Amma baki zama ki huta kullum cikin wahala kibar Aikin mana kinga Adangi sai zagina Ake wai nice na d'aure miki gindi kike Aikin maza kina cud'anya dasu," "Mommy manta dasu kawai cikinsu ba Wanda ya tab'a taimakon mu bayan rasuwar Baba so Yanzu nayi Aiki tuk'uru nasami Aiki gashi harna Samu K'arin girma to baikamata na watsar da damata ba kawai kimin Addu'a Allah ya kareni" "Addu'a cikin ta nake kullum sam to Amma maganar Aure fa"? "Aure lokaci nazuwa Mommy Amma in Sha Allah namiki Alk'awari muna dawowa Wannan Assignment da Akamuna Kiran gaggawa to zanyi," "Shikenan Allah y kareku" "Ameen mommy na Ina sonki" "Nima haka yanzu yaushe zaku"? "Gobe ne, kawaii na shirya kayana ne nasan bazan dawoba daga can zamu wuce Assignment d'in," *********""""'''''''''****** "Jidda Yanzu barina zakiyi kije wannan Aikin? Auren mufa saura sati 3 Amma zakije wani Assignment kibar Aikin mana," "Kaga Bash Koda kasanni kasanni da Aikina Kuma Ahakan kaji kana iya Aurena so kayi hak'uri Mana kasani ko badogon Assignment bane," "Nifa bazan iyaba Ace wai wadda Zan Aura take cud'anya cikin k'attan maza, indai kikaje Assignment d'in to wallahi ki nemi wani mijin," fuuuu yabar wurin, Baki sake tabishi da kallo wai kada taje to soyake tarasa Aikinta bayan Tasha bak'ar wuya Kafin takai inda take yanzu,"? Tabbd'i wallahi bazatayi dagegeduwa Aiki Kam saitaje, Shiga gida tayi wani iri hakan Yasa kaka tanbayar ta lafiya kuwa? Bata b'oyemata komai ba Dan Batada kowa sai ita iyayenta sunjima da rasuwa take hannun kakar babanta ne, Tsaki taja Mtssswww "saboda shi kike damuwa manta dashi idan kikaga Auren baiyuba to Allah Bai bufa ba jeki kiyi Aikinki Ai Namiji Banda Tabbas dama ni na fahimce bawani sonki Yake ba, ki kwantar da hankalinki kinji" "To kaka nagode" Tana komawa dak'i takira k'awarta Sam tafad'a mata itama hak'uri tabata,..... ***********"""""""""""******* Wash gari duka sun had'e Abuja A babbar headquarter ta sojojin Major Sa'id Yafito ya Fara magana bayan Angama zab'ar wad'an da za'ayi tafiyar dasu, Su 4 ne Abokan juna Samir, Taj, Sam Jidda dama sune suka Jima suna Aiki tare saidai Samir shine babba cikinsu, "Abunda Yasa namuku kiran gaggawa shine Akwai wata Annoba data fad'a wani gari, kuma ta rutsa da wata Y'ar k'ank'anuwar yarinyar general wadda bazata wuce shekara 3 Shine mukeson kuje ku ceto wannan yarinyar, sanin kunada k'wazo yasa Nasa daku cikin Wannan tafiyar, Wanda Kai Kaine jagoran tafiyar Captain Samir, Amma sanin makamar daji Emanuel ne Dan Haka ko Ina zaku shiga Saida nasa izinin, ga sauran Abokan tafiya ne Duka ku 200 zaku Domin dajin da Hatsari, Akwai makaman YAK'I da muka tanadar muku sosai, sannan duk Wanda Yadawo daga wannan tafiyar to yanada K'arin girma da kyauta ta musamman Wadda kuma shikanshi general zaima mutum babbar kyauta muddin Aka ceto masa Y'arsa kusani tafiyar dolece kuma kada ku kuskura Arasa Y'ar, Magana tak'are zaku iya tafiya yanzu fatan Alheri da nasara".................... _BASEERA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 or 07031012948 *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ *Free 🅿️ 6 to 10* ......."Taj nifa jikina yayi sanyi Anya wannan tafiyar zanyi ta kuwa,"? Cikin sanyi Jidda tayi maganar, "Haba Jidda kada ki sare Mana kinmanta irin wuyar da kika shiga Kafin kisami wannan Aikin ma? Kuma Kika samu sannan kikayi training ba iyar wuyar da Baki shaba Amma Kika jure har yanzu Kika kawo wannan matakin bugu da k'ari Bakida kowa sai kaka kaka Bata dogara da kowa ba sai ke ki K'arasa cika burinki Mana Zaki iya," "Amma Taj kaduba irin Yawan makaman da Aka bayar zuwa Sojojinda Aka had'amu dasu wannan kad'an ya isa ya tabbatar inda zamu shiga wurine Mai had'ari," "K'awata kada kisaka tsoro kisa su d'auka macce batada jarumta Mana Zaki iya koma meye," Hunmm: "Shikenan Allah yabamu nasara" "Ameen suka Ansa," Tinda Suke zancen Samir kallonsu kawai Yake Amma yasan wannan tafiyar saita banbanta da saura kawai shi ba mutum bane ma'aboci yawan magana shiyasa yayi shuru Amma Yana fatan suyi nasara Kan wannan Aikin,.... Suna fitowa waje inda zasu shiga motar saiga bash Yakira Jidda, cikin mamakin ganinsa Nan taje, "Ya lafaya meya kawoka nan? Tafiyar zamuyi fa," "Yanzu Jidda saikin je kenan, bazaki fasa ba,"? "Kaga mungama wannan maganar tini Anawa tinanin so kabar sauran zancen saina dawo kawai," "Idan kikaje bani bake zaj tura A k'arb'o komai nawa, Zan Aure wata daban," "Allah ya bada zaman lafiya," tace cikin Jin haushin maganar tashi tawuce,. Taj kuwa tinda taje wurin bash ya kejin wani irin zafi mara misaltuwa take ya b'ata fuska ya fad'a motar yana danna Mata Hon cikin Haushin kula bash datayi,. Dariya Sam tayi dama tasani Yana dakon son Jidda kawai ya kasa fad'a Mata ne, domin ganin tana da kayan wani kanta, Samir kuwa murmushi kawai yayi Shiga motar tayi tana Fad'in "Kuyi hak'uri" Cikin d'aga murya bash Yace"Wallahi I'm serious Jidda idan kikayi tafiyar to munrabu kenan!!!," Wani irin d'aci taji Yana taso Mata tindaga Zuciyarta har cikin bakin ta, wannan ai to zarci ne, Luummm shi Ido tayi tana Jin zafin maganar shi, Taj kuwa dad'in maganar tasa yaji Domin koba komai watak'il nasa rabo ne yasa hakan tafaru, "Idan d'an iskan baijaye daga Hanyar mu takashi kawai," Cewar Taj cikin d'aga murya, Satar kallonta yayi still idanta rufe tajingina jikin kujerar motar,. Tafiya maitsawo sukayi inda suna Amfani da computer zuwa taswirar gano dajin, basu tsaya ba Saida sukayi tafiya Mai Nisan Gaske kusan sai magriba, Sannan Suka tsaya domin sallah Sunshiga daji Anan suka kafa tinti harda bacci Nan zasuyi sai zuwa safiya sannan suci gaba da tafiyar,. Masuyin sallah Suka fara, wad'an da basayi kuwa suka Fara cin Abincinsu, Bayan sungama sallah suka Fara cin Abincinsu Jidda kuwa zubawa Abincin Ido kawai tayi tana tinane tinanenta, Cikin sanyi Taj Yace"Jidda Aikinki baya buk'atar dogon tinanin balantana keda Kika shigo babban Assignment, ki daure kici Abincin kinji," Hunmm: "nagode da kulawa" Nan suka kwana lafiya k'alau basu had'u da komai na cutarwa ba, Ahankali Taj yaie shiga Lamarin Jidda harta rage yawan tinanin, Kwana 7 sukayi suna tafiyar sun shiga manya manyan da zuzzuka sun wuce birane da garuruwa , Computer tana Nuna musu sun kusa Shiga dajin, Randa suka cika Kwana 12 suka iso wani dajin Wanda mota Bata shiga inda Taswirar ta Nuna zasubi, Fitowa sukayi Suna nufar dajin datake Wayoyinsu da Computer suka d'auke komai ya daina Halbawa, Cikin mamaki Samir Yace"kunga Computer tadaina Aiki hakan Yana Nuna muna cewa Cewa inda zamu shiga ba Network duk wani Sadarwa baya Aiki wurin," "Yaya zamuyi kenan tinda kusan computer itace d'auke da Abun komawar my dama zuwan namu," Cewar Sam Taj Yace"Saidai mu d'auke duk wani Abu da zamu iya, Sai kuma muyi Amfani da Taswirar takarda, Yanzu Aikinka zai fara Emanuel" Cikin Isa da hura Hanci Yafito tsakiyar su Yace, Kowa Yacika wannan cakar da makaman domin kariya wa kansa tinda motar Bata shiga ciki, sannan wannan zagaye nane so dole kumin biyayya," Yana gama Fad'ar Hakan Yafara lodar nasa makaman A jaka, ganin haka yasa kowa Yafara d'iba, Tsaki Sam tayi Tace"dube shi kamar wani Birin har yake Fad'in Dole A masa biyayya Mtssswwww" "Rabuda banza dama ni haushi yake ban wallahi," Cewar jidda Murmushi Samir yayi"Kunga ku manta dashi kawai muje mud'iba Muma," Kowa ya d'auke Abunda zai iya Koda na lek'a motar Naga sun kwashe makaman dukan ko wanne d'auke da k'atuwar jaka A bayansa Hannuwansu kuwa d'auke da manyan bindigoginsu Suka nausa cikin dajin, Emanuel ne gaba sai Samir, Taj, Sam, jidda sai sauran tawagar tasu ko wanne rik'e da bindiga Kuma A shirye Koda wani Abu zai taso musu, Sunyi nisa sosai domin sunshiga tsakar dajin ba Abunda Suka gani, bakajin komai sai sautin kukan wasu tsuntsaye Yan tsiraru, ga manya manyan itace dogaye Wad'an da suka ma dajin k'awanya, Kwatsam sukaji wani irin gurnani na fitowa ta gefensu Yana nufosu, Cikin tsorata Suka tsaya can bisa d'aga hannu da Emanuel yayi yana wurwurga idanuwa Dan ganin meke Shirin kawo musu far maki,. Kamar daga sama saiga wani gabjejen Zaki Ya fito, Wanda Sam baida shawar kallo, sau d'aya zaka kalleshi kasan lalle bawai iya zakin gaske wanda Suka sani bane, Dole wannan SHAID'ANIN ALJANINE Yadawo zaki, Tsaye yayi yana k'ura musu idanuwansa wad'an da jajir suke hak'uransa Zara Zara masu tsinin gaske, Wani irin Gurnani yayi Wanda Saida dajin Ya Ansa gaba d'aya, kansu Ankara Wasu shirga shirgan zakuna kamar sa suka bayyana bayansa, Tsorata Iya tsorata sun tsorata domin wasu har sun ja baya, Cikin rawar muryar Sam tace"Bana tinanin bindiga zata iya Kub'utar da rayukan mu dole mu k'ara da takubba," Maida bindigar Samir da Sam sukayi zuwa Taj jidda kuwa iya bindigar kawai zata iya rik'awa, Ganin hakan yasa SHAID'ANUN ZAKUNAN suka fad'a musu da mugun nufi....................... Wai koya zata kasance?? Kubiyoni next page Masoyana.... *BASEERATA ITACE ARZIKINA😍* WhatsApp number 07064904617 or 07031012948 *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ *Free 🅿️ 11 to 15* ..........Cikin A zama Suka soma yima zakunan Ruwan wuta da bindigoginsu Amma Har suka iso nufosu ba wanda yasami nasarar samun Koda Zaki d'aya, Suna Isowa Sukayi sufa Kan dakarun Sojojin take suka soma Hallaka duk wanda Sukayi nasarar fad'awa, Sojojin Ihun Wuya A zaba kawai suke zabgawa domin zakunan cikin zafin nama suke kaimusu Hari da Tsinin farantansu zuwa Hak'oran su, duk wanda suka Yaga da K'afar su kuwa tamkar Ansa Wuka Antsaga nama saidai kaga jini ya tsartu wanda Suka Sara ya zabga Ihu ya Fad'i k'asa, Idan kuwa Suka kaima mutum cizo to saidai ya zube matacce domin basu saki Saida wani sassan jikinsa Kuma su had'iye, Samir kuwa fad'a yake da zakunan da tako binsa amma ko Rauni ya kasa musu Domin zafin Naman zakunan yawuce tinaninka Mai karatu, Sam kuwa Gajiya tafara saidai takare harin da zasu kawo Mata Amma takasa maida martani, jidda kuwa duk'e take k'asa kawai tana jiran mutuwar ta Domin tagama Sadaukarwa Akan yau mutuwa zatayi, Emanuel kuwa ya dage sai har binsu Yake Yana ja baya Amma ya kasa nasarar Koda kashe d'aya domin Bak'in zafin nama ga zakunan tamkar takarda hake suke yawo Kan iska, Kafin cikar Rabin sa'a take suka soma yima Sojojin b'arna Domin sunkashe Ak'alla 10 guda 20 kuwa Raunika sosai suka musu, Wani Zakin ya nufo Jidda cikin son ya galgala namanta dawani irin gurnani, Koda taji sautin gurnanin Yana nufota tad'ago, Aikuwa sukayi Arba da idanuwan Zakin da saura kad'an ya cinmata Yana daf da samunta Yayi tsalle da niyar rabata da kanta Baki d'aya, ta rafka uban Ihu, hakan Yajanyo Hankalin Taj wurin ta, Cikin Bak'in A zababben gudu Wanda baisan Yana dashi ba ya falfala zuwa gareta tareda zabtarar wani icce, Zaki Yana sauka daniyar sauke mata Kai k'asa Taj ya isa gareta Ya d'aga Icce Ya zabgawa Zakin Aka, Wani Firgitaccen ihu Zakin yasaki wanda ya janyo Hankalin kowa zuwa Nan hatta su kansu sauran zakunan Saida suka tsaya cak suna kallon irin kashin walak'ancin da Taj yayiwa Uban gayyar nasu, Zakin ya Fad'i k'asa kansa Ya tarwatse jini Yanata malama Ak'asan, Jidda kuwa tsabar mamaki dama kasada irin wadda Taj ya d'auka saboda ita yasa ta zuba masa ido bako kyaftawa, Shikuwa baima lura da yanayin nataba Cikin d'aga murya Yace"Kansu shine lagonsu Ku Hanzarta halbin kawunansu da kukansu Aka," Yana rufe Baki kuwa sauran zakunan suka musu rufduku Aka sake kacamewa Da Bakin Artabo Wanda wannan karon zakunan ne ke bajewa kasa matattu, D'ayan Zakin yasamu nasarar laftawa Emanuel Tsinin K'afarsa A hannu take wurin ya dare sai jini Emanuel ya sandara Ihu da Kiran Jesus, Ya Fad'i k'asa, Aikuwa Zakin ya hayesa daniyar sake cizonsa, Amma Cikin sauri Sam ta d'auke Kan Zakin da halbi da wata k'atuwar bindiga, Yasa Kan Emanuel mattace, Shima Samir Yasami damar d'auke Kan Zakin da takobinsa gangar jikin Zakin ta Fad'i sai jini kawai dake tartsatsi, Ganin An Hallaka Rabin SHAID'ANU ZAKUNAN Yasa sauran ja da baya suka gudu, Zama sukayi gurin suna maida numfashi bama kamar Taj Domin ya kashe zakunan da yawa, Ruwa Jidda ta d'auka ta Aje masa gefensa tana Fad'in"nagode sosai da kaceci rayuwa ta," Baiyi magana ba murmushi kawai yamata tareda d'aukar Ruwan yasha, Emanuel kuwa saida Aka d'auke masa gawar Zakin Sannan yasami iya mik'ewa, da taimakon sauran mutanen Suka masa d'inkin raunin, Kallon Sam yayi Wadda take kusa da jidda suna Magana k'asa k'asa, Yace"kinceci Rayuwata Mai kyau, Ina godiya sosai Amma Kamar bashi ne Zan Rama miki," Cikin Rashin sonyin Magana tace"Mu musulmai idan mukayi taimako badan A Rama Mana muke ba Dan Allah muke Domin shike bamu Lada, kuma shine yabani ikon taimakon ka, Kuma ni Sunana Samarai Dan gajarce sunan kace sam kawai," Murmushi kawai yayi domin dama yajima da k'aunar Sam cikin zuciyar shi Amma Yakasa fad'a mata Domin lokuta da dama Samir Yakan gifta masa ta Hanyar sata wani Aikin ko bata dokar kada tafita, shiyasa ya kejin haushin samir sosai, Wad'an da basu mutu ba suka farfad'o inda wad'anda sukaji Rauni Aka musu dressing Suka D'an matsa daga inda gawarwakin zakunan suke, sannan Suka sake kafa tanti Suka Kwana Anan, Amma cikin zulmi kada ragowar zakunan sudawo,, Har safiya ta waye babu Abunda ya faru, Anan sukayi jinyar kwana 7 suka warke Sannan sukaci gaba da tafiyar, Wannan karon Samir ne gaba sannan Emanuel, Sunyi tafiya sosai suna tsayawa basu had'u da komai ba har tsawon kwana 7, Suka iso wata Hanya, Wadda guda 2 ce rak d'ayar tayi cikin wani kogo Mai zurfin gaske, d'ayar kuma Ruwa ce ke kwarara sosai k'orama ce wurin, Amma manyan kadoji ne ciki suna ta Kai komo A ruwan, Tsayawa sukayi suna kallon kallon domin ko wacce Hanya dole tanada nata Hatsari, Samir Yajuyo yace"Ina Shawara ta Ina kukaga Ya kamata mubi? Domin basai na fad'a muku ba ko wacce hanya da gani tanada nata Hatsarin , kuduba wad'annan kadojin sam bazamu iya fad'a dasu ba, to amma bansan Kuma meye cikin kogon ba, Ina kuke ganin ya kamata mubi,"? "Anya Wai samir bamu b'ata ba? Muna kan hanya kuwa,"? Cewar Jidda cikin d'an tsoro "Eh muna Hanyar Domin ga Taswirar Hannuna munkusa zuwa ai in Sha Allah," "Ya kamata kicirewa ranki tsoro da karaya Jidda kinriga kinzo ba Hanyar komawa ki dogara ga Allah kawai Jidda," Cewar Taj, Gyad'a kata tayi cikin Alamar k'arb'ar zancensa,. Sam tace"Ko Alama bazamu iya fad'a da wad'annan kadojin ba kawai Anawa ganin mushiga kogon kawai" Caraf shima Emanuel ya K'arb'e zancen da cewa"Eh mushiga ciki" Anan kowa ya Aminta Abita kogon, Saidai kuma Anrasa d'aya Wanda zaishiga gaba, Ganin Anata b'ata Lokaci yasa Sam gyara Rik'on takobinta tanufe k'ofar kogon tana Mai Addu'a, "A'a kina hauka bayan kina macce Zaki Shiga gaba Kuma idan wani Abu Ya sameki fa,"? Da mamaki ta kalleshi domin karon farko dataga kulawarsa gareta, Ganin kallon da take masa yasa, Yasa kansa kawai Cikin kogon Yana Addu'a taj yabi bayansa da wasu Sojojin masu manyan bindigogi guda 20 suka wuce sannan Sam da Jidda, Wannan karon jidda Cikin k'arfin guwa take sannan suran Suka shiga, Sunyi nisa sosai cikin tafiyar har sundaina ganin bayansu, Abun mamaki tsakan kogon manyan itatuwa Suka gani sunata ci da wuta inda suke k'yandir d'in kogon, jikin kogon Kamar gini, Tsayawa cak yayi bayan Yahango wani sak'on gefen kogon inda Akayi zanen wata irin k'atuwar macijiya Mai d'auke da kawuna 9 Anrubuta MACIJIYA SARAUNIYA MALGIS MAIKAI TARA, Ganin Samir ya tsaya Kuma ga inda yake kallo hakan yasa sauran ma kallon inda yake kallo Abunda suka gani shine yayi matik'ar d'aga musu Hankali basu gama Shiga figici ba Saida MACIJIYA SARAUNIYA MALGIS MAIKAI TARA Ta bayyana tsakar kogon...,........................ HUNMMM WASAN FA MAIZAFINE FANSS KU SHIRYA AMMA KADA KU MANTA DA BIYAN 300 D'IN KU,....... _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 or 07031012948 *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ *Free 🅿️ 16 to 19* Second to the last page in Sha Allah....... _Thursday 27/7/2023 Jully_ *K'iris Yarage free page ya k'are so ki gaggauta biyan naki Kud'i idan kina 300 ne kawai bada yawa ba, Ada Yanzu zangama Free page d'in Amma wasu Suka rok'a nak'ara so in Sha Allah page Mai zuwa shine na k'arshen free* ...........Fitowa cikin Ramin macijiyar tayi tazuba musu Ido cike da mamakin ganin Yau shekara sama 30 ba'a sake samun wata Halittar Y'an Adam da zasuyi gangancin shigowa masarautarta Koda sauran k'wari basu Isa su shigo Wannan kogon ba Amma Yau Ansamu bil'Adam su shigo Mata ciki, Su kuwa k'amewa sukayi tsabar tsoro Domin sunyi nisa da k'ofar da suka shigo gata fita suna hange Amma tasa jelarta ta tare Hanyar, Cikin Rashin sanin mezai faru yasa Emanuel cewa"Kusaki wuta," Kan ya gama rufe baki shida sauran Sojojin Suka soma halbin MACIJIYAR Rashin sani yafi dare duhu Domin da sunsan Ainahin mezai faru da basuyi gigin Halbin MACIJIYAR ba, Dan kuwa take ta nad'e guri d'aya tamkar Ganwo, Saida taji sun tsakaita halbin Aikuwa tabud'e Baki ta dinga Huru musu Hiska Mai d'auke da wuta, Cikin k'ank'anen lokaci wurin yayi duhu wuta ta soma cin Naman jikin wasu Ihun mazan kawai ketashi cikin kogon Domin duk Wanda wutar tasama tamkar wutar taci kare ne haka mutum zai k'one k'urmus tokarsa kawai zata rage k'asa, Tinda sauran masu Rai sukaga haka suka soma ja baya suna Neman Hanyar Guduwa, Cikin d'aga murya Jidda tace"mafitar mu d'aya muyi gaba mufita cikin kogon Domin idan Mukace mukoma baya munyi wahalar banza ne, Muyi gaba cikin gudu, Inada tabbacin da munfita muntsira," Bata gama rufe Baki ba suka soma gudun tsirar Rai, Iyakar k'arfin su suke gudun inda macijiyar take zallo duk wanda tasoma Saidai ta lak'umeshi, gata da zafin nama, Suna gudu suna halbinta Abayansu, Duk wanda yayi sanya Yaka sance baya tofa saidai wani bashi ba, Suna cikin Bak'in gudun ne Jidda ta taka wani Tsinin Icce Ak'afarta tsininsa Yafasa takalmin nata ya Soki k'afarta, Ta Kwarara Uban Ihu tana neman fad'uwa Amma saboda gudun tsiratar da Rai take Haka ta daure tana gudu da k'afar, Suna daf da futa ganin hakan yasa MACIJIYAR HASALA tabiyo bayansu, Cikin Rashin sa'a tacabki K'afar Samir, Wanda saida Tsinin Hak'oranta Suka soki K'afarsa jini ya tsartu, Ihu yasaki Mai k'arfi tare da yin gaba zai kife Amma Sam Cikin Bak'in zafin nama tajuyo baya ganin Halinda Yake ciki yasa tadawo baya tare da Hira sama Kamar wata iska ta sare Kan d'aya daga cikin kawunan macijiyar, Wanda da shine tayi niyar gamawa da Samir, Jini ya wanke wurin harda fuskar sam, macijiyar ko mawa baya tayi tana Kwarara wani Uban Ihu Wanda take kogon Yafara girgiza Yasoma fashewa duwatsi suna rikitowa k'asa, Cikin zafin nama ta taimaka masa ya mik'e suka Sake falfalawa da gudu Cikin ikon Allah dama k'arfin Addu'o'insu Suka Samu Suka fita kogon, Saida sukayi nisa da kogon sosai sannan suka tsaya, suna maida numfashi, Kallon Samir Sam tayi K'afar tasa tana zubda jini ta taimaka masa Akayi dressing k'afar shi shida Jidda, Ruwa Suka Sha, yau basu tinanin had'a ko wanne tintiba Anan Suka soma baccin wahala, Samar Yanata mamakin yarda Sam ke kula dashi duk da Hakan Bata wani Sakewa dashi saidai sannu kawai take iya cemasa, cikin kwanakin da suka d'auka na jinya Samir yaji son Sam sosai Wanda Yakasa b'oyewa saida Alamar Hakan tafito, itama ta Amince masa dama tajima da fatan hakan, tinda Emanuel ya gano Hakan Yasa Aransa saiya kashe Samir da Hannunsa, Taj kuwa Bai fad'awa Jidda Yana sonta ba Amma Yana Nuna Alamar Hakan, Saidai ita tana sharewa kamar Bata gane nufinsa ba, Domin Anata Cewar Yanzu ba lokacin soyayya bane, Saida Sukayi Kwana 12 wurin Kafin kowa yasami sauk'i masu Rauni, Suka cigaba da tafiya, (IDAN BAZAKA MANTABA MAI KARATU NACE MAKA SU 200 SUKA FITO AMMA A YANZU DUKA BASU WUCE 60 BA DUK SAURAN SUN HALAKA) "wai Har Yanzu bamu shiga dajin bane,"? Cewar Sam "Samir yace mun kusa Mana daga wannan dajin sai Wanda yarinyar take fatan mu d'aya ya zama tana raye," Cikin Ikon Allah, Har suka kusa barin dajin ba komai daya faru suna daf da shiga dajin sai kawai, Sukaga wasu mumanan birarunka sun musu k'awanya Manya manya dasu munana basuda kyan gani.. Cikin kad'uwa Suka cure wuri d'aya Domin dai basuga inda birarunka suka fito ba kawai sunga sunkewaye sune, "Innalillahi wa'inna ilaihin Rajuun" Shine Abunda suka fad'a, A Yanzu ko kayan fad'an basuda saboda sunyi gumurzu da SHAID'ANUN DAJIN Tabbas wannan shine D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU, Basu gama tinin komai ba birarukan Suka soma yun k'urin kamasu, A matik'ar Razane suke ja gefe, Domin Halittar birarunka kawai ta Isa ta razana duk wani Mai kallonsu Koda A film ne balantana A zahiri, girman Baki d'ayan Birin zai Kai had'e gate 2 guri d'aya, gasu munana ga hannayensu da farata masu tsini sai walk'iya suke ga tsini kamar takobi, ga tsawo tamkar samudawa, Hannuwa Suka soma mik'awa k'asa daniyar musu rub d'aya, Amma cikin zafi Suka soma...................... MUHAD'U NEXT PAGE KUMA LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH *Kuyi manage da wannan Wallahi Inada matsalar idanuwa ne kusani Addu'a Allah yaban lafiya, Kuma banajin dad'i Ulcer na damuna wllh ngd Masoyana inajin dad'in comment d'inku Over* _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_ WhatsApp number 07064904617 or 07031012948 *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀* _PAID BOOK #300 ONLY_ _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._ ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝``` _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY* _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._ ```Ina Mata Kai harda ma maza masu fama da ciwon sanyi? Kinkashe Kud'i Amma Baki daceba, to ga waraka tasamu da ikon Allah domin Maman teema tana d'auke da duk kanin maganin matsalar ku, Ina Mata Y'an gayu masu gyaran jiki da Ado da kwalliya? To Kuma komai Akwai, Ina masu fama da HIV? Ina masu fama da k'urajen fuska? Ina masu fama da gisal din Ido? Ina masu fama da K'aron mahaifa? Ina masu fama da Rashin haihuwa? Ina masu samun cikin yana zubewa? Ina masu Neman kayan gyara jikinsu suyi shek'i fata tayi glowing? Ina masu buk'atar kayan kitchen? Ina masu buk'atar kayan sakawa, Ina Mata masu buk'atar gyara Domin haduwa da miji? Ina Masu fama da Ulcer, ciwon baya ciwon k'afa da dai sauransu? To duka kuzo in Sha Allah kunsami waraka da izinin Ubangiji number ta itace 08100100821 MAMAN TEEMA``` *JULLY 29/7/2023 SATURDAY* ```KUYI HAK'URI RASHIN JINA KWANA 2 WLLH BANDA LAFIYA NE ULCER DA CIWON ZUCIYATA YATASHI SAIDA NASHA ALLURAI DA K'ARIN RUWA, PLEASE KUTAYANI ADDU'A ALLAH YARABANI DA CIWON ZUCIYAR NAN DUKA GABA D'AYA HARDA ULCER DAN WLLH SUNA WAHALAR DANI, NGD 🙏 TAKUCE DAI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱``` *Free 🅿️20 to 30* _Last free page, Idan kana kina buk'atar Cigaban Wannan k'asaitaccen labarin to kibiyoni dan mallakar naki, kada kibari Ayi tafiyar Baki, Domin Akwai labari gaba, banfara wannan labarin ba saida k'wak'walwata ta shirya,_ ....Amma sai suka zulle Atare, Haka suke neman kamasu Amma sai zillewa suke Al'amarin da ya fusa birarunka kenan, Cikin fusata Sukayi kansu Atare, Duk iya k'ok'arin su kasa kwantar kansu Sukayi lokacin domin Ance Sarkin yawa yafi Sarkin k'arfi, Haka Suka kamasu suka nausa cikin dajin dasu, Sunyi tafiya Mai nisa kafin sukawo mafakarsu, Wasu Manya manyan itatuwa suka jera Wanda shine dak'insu, Wani kejin itatuwa suka BUD'E Suka jefasu ciki sannan suka wuce, Dube duben wurin Suka shigayi Duk kasusuwan mutane ne sai wari yake "kenan Naman mutane suke ci,"? Maganar da Samir Yayi Aransa kenan Ashe tafito, Wasu mutane Uku Suka d'ago duk sun ya mushe saboda wahala, D'ayan Yace"Sosai basuda Imani balantana tausayi ko wacce safiya mutum Uku suke gasawa su cinye," "Gasawa kuma? Saikace Awakai,"? Cewar Jidda Hunmmmm: "Gwandama Awakai domin In suka fad'a Hannun musulmai Suna tausaya musu, Wad'annan kuwa basusan Imani ba kawai zubda jini Suka sani, Zasu Kama mutum Yana ji Yana gani zasu Wasa matsa fetur sanan su kunna masa wuta, Har ya k'one k'urmus Sannan su zauna suci," "Munshiga Uku hannun mayu muka Fad'o kuma, to Kai yaya Akayi kuka Fad'o hannunsu,"? cewar Jidda "K'addara da k'arar kwana, Zamu wata nahiya daban sai Y'an fashi suka taremu daganan Muka watse shine fa bayan mun Fad'o daji sai wad'annan mugayen biran Suka Kama mu, suka dinga Cinyemu tamkar Ayaba, Yanzu Haka mune Kan layi gobe Izuwa wannan lokacin sungama babbakamu," "Innalillahi wa'inna ilaihin Rajuun Wannan wane irin bala'i ne, munkawo kanmu inda Za'a halakamu daga wannan bala'in sai wannan nayi Dana Sanin wannan tafiyar gashi saboda ita har masoyina na rasa, mu kanmu kuduba yawanmu sanda muka fito amma yanzu kuduba yadda muka rage Duka iya kacinmu 50 sannan Yanzu bamuda tabbacin Kub'uta," Cewar Jidda cikin kuka,. "Kinga Jidda kiyi hak'uri in Sha Allah zamu Kub'uta domin rayukanmu Hannun Allah suke ba Hannun kowa ba, sannan Baki rasa mosoyi ba, muddin Ina raye nine Zan maye Miki gurbinsa," Cike da mamaki take kallonsa Wai so, Amma inta nazarce maganar sa zata iya samun sauk'i Aranta, Washe gari wani k'aton birin yazo Ya bud'e kejin, Janyo wad'annan mutanen uku yayi suna Ihu suna komai ya d'auko su tare A Hannu d'aya Kamar Ya d'auke kara Haka ya rik'e su Yawuce dasu, Yana zuwa tsakiyar fili Ya Ajesu tareda kwara musu fetur suka kunna musu wuta, Ihu suke suna ci da wuta, tinsuna tsaye har suka Fad'i kwance, Suna motsi har suka daina Rai yayi halinsa kenan, Su kuwa ihu suke suna murna da shewa, Haka Suka zauna wurin suka soma cin naman, Iya tsorata su Samir sun tsorata Sosai tinsuna kukan tausayin wad'ancan har suka dawo tausayin Kansu, Saida suka gama cinye Naman tasss sannan suka Sha wani ruwa sai suka b'ingire wurin da bacci su duka, Cikin dakewar Zuciya Samir Yace"ga dama tasamu Kafin su tashi daga baccin mugudu kawai'" "Amma Taya kake ganin zamu gudu wannan keji na itace ne Kuma gashi rufe" cewar Emanuel Yana d'an zabgamasa Harara, Shuru sukayi dukansu domin maganar Emanuel Gaskiya ce, Jidda tace"Amma bazaiyu mu zauna sumuna kisan walak'anci Irin wannan ba, dole mugudu," tana gama maganar tafara duban kejin ganin da igiya sukayi d'aurin Yasa cikin ta kalminta ta Ciro wata wuk'a tafara yankawa Ganin hakan yasa suka matso Suma suna Taya ta, Cikin Ikon Anbaton Allah suke Aikin, cikin k'udurar Ubangiji kuwa suka Sami Y'ar Hanyar wucewa, Ahankali suka soma fita d'aya bayan d'aya har suka fice Duka cikin sand'a sukabar wurin, sunayin nisa dasu suka soma gudu, sunyi gudu Sosai Kafin su tsaya su huta, Samir Yace"Yanzu bamuda komai na fad'a Abunda zaifi kawai musami itacen Nan muyi Makaman fad'a," Hakan kuwa taka sance saida Suka gama sannan sukaci gaba da tafiyar, Emanuel Yace"Wannan dajin shine yarinyar take, Domin ga Yan tsirarukan gidaje Nan" "Amma Yaya Akayi ba kowa, Kamar ma ba'a tab'a samun wata Halittar Y'an Adam Anan ba" Cewar Sam "A'a Antab'a Samu Mana domin ita kanta Y'ar Major d'in tare da Wasu Suka so shak'atawa Sai wani babban bala'i ya bak'ar, domin wannan DUNIYAR SHAID'ANU ce daganan kowa ya halaka ita kawai ta rage," "Yanzu kana nufin da wata masifar Anan kenan,"? Cewar Jidda "Sosai kuwa Domin wannan zatafi ko wacce ma Dan Anan Ainahin SHAID'ANUN suke wad'an da ba mutane ba da zarar sun cijeka zaka zamo Kamar dai su," Cewar Emanuel "Horrors kenan," Fad'ar Taj "Sosai kuwa Domin haka kowa ya Ankare Sannan duk k'aunar ka da d'an uwanka idan har Aka cijeshi tofa Dole A barshi" Motsinda suka Fara jine Yasa su waigawa, Aikuwa Horukan suka gani masu matik'ar yawa suna nufosu, kallo d'aya zaka musu suyi bala'in tsorataka, domin bakunan su jini ke zuba ga manyan Hak'ora, kawunan kansu kuwa Ajuye idanuwansu Arufe Amma suna iya jiyo k'amshin mutane Kuma suna gane inda suke, nufo inda suke suka fara,. Ja baya suka Fara, Ihun da sukaji Abayansu Yasu saurin waigawa, Yarinyar suka gani Wani k'aton maciji Yana Nan nad'eta, Macijin k'ato ne, Bak'i wulik gashi da girman gaske, nad'eta yayi Sosai Yana neman had'iyeta Dan harya Fara Kware baki gashi sai hawaye take tana mik'a musu Hannu Alamar taimakonsu take Nema,. Dukansu A tsorace suke Amma tausayin yarinyar ya tsalgu A zukatansu bama kamar Jidda, basuyi Aune ba kawai saiganin sukayi Jidda ta falfala da mugun gudu tana saita k'aton iccen da suka maida kamar kibiya daidai bakin macijin Yana bud'e Baki daniyar had'iye Yarinyar, Su Samir kuwa sunkasa Koda motsi mamakin Wai Jidda ce yau tacire tsoro ta tinkare mutuwa Dan cetar RAYUWAR wata, shi kanshi Taj mamaki yake Amma Kuma tsoron kada Wani Abu ya Sami Jidda Ya gama cika Ruhinsa,. Tana kusa da zuwa inda macijin inda baifi tako Uku zuwa biyu ba ta daga Wani irin wawan tsalle tamkar Ancillata ta kibiya cikin Mugun nufi da Rashin tsoro ta................................. _WOHOHOOOOOH GASHI DAI MUNKORO AMMA SAIDAI KASH FREE PAGE YAK'ARE, AMMA YANZU AKA FARA WASAN YANZU WASAN ZAI D'AU ZAFI, KOYAYA ZASU K'ARE DA WANNAN MACIJIN ZUWA WANNAN HORUKAN? KO ZASU KUB'UTA SU KUB'UTAR DA YARINYAR KUWA? KO ZASU KOMA GIDA KUWA??? HUNMMM NIMA BANSAN ANSAR WANNAN TANBAYOYIN BA ANSAR SUNA CIKIN K'WAK'WALWATA TA DUKA, IDAN KANA SON SANI, KINA SON SANI TO KU HANZARTA BIYAN NAKU KUD'IN 300 NE KAWAI, KADA KU MANTA NICE DAI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN 👸 OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚_ _BASEERATA ITACE ARZIKINA_ WhatsApp number 07064904617 or 07031012948 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels