An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌼🌼RAYUWAR JANNAH🌼🌼 BY Maryam Muhammad Bellow (SECTARY OF THE ASSOCIATION) Daga alk'alamin✍Oum Amjad Marubuciyar 'yan biyu (kyautar Allah) And now Rayuwar jannah💋💋 ____________________________________ *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION 💫P.E.W.A💫 Home of Perfect Writer's together we stand🤝 ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️* Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️* ___________________________________________________________ Bismillah Rahamanin Raheem Ina Rokon Allah S W A yabani ikon rubuta abunda yake dai dai wanda al umma musulmi zasuyi amfana da shi kuma suyi aiki da shi Al farm Manzon Allah S A W 🙌🙌 Paid Book Free page 1&2 K'auyen k'auran namoda dake cikin jahar Zamfara state akwai wani k'aramin k'auye *Barkeji*. Malan Amadu yana daya daga cikin mazauna garin matar shi d'aya da 'yarsu d'aya sunan matar shi Azumi,amma 'yarsu na kiranta da "mama", Sunan 'yar "Jannah"yarinya ce 'yar shekara goma sha biyar bayan an haifi k'annenta mata su ukku sai namiji guda amma dukan su basu dad'ewa suke mutuwa ,namijin yafara mutuwa kafin matan su mutu, Malan "Amadu" babu abunda yake so Kamar 'ya'ya maza Allah baibashi yasamu guda yana murna sai gashi sati biyu yayi a duniya ya koma ga mahallicin mu,ya dauki tsanar duniya ya d'orama "Jannah" a cewar shi itace mai canye mai 'ya'ya musamman d'a namiji ta canye har da matan da suke jinsi d'aya(ma'ana mata 'yan uwanta) bata bari ba har su ta canye ,gashi amfanin gonar shi yadaina al barka talaucin duniya ya isheshi yasha mai kai bai San yazaiyi da rayuwar shi ko kad'an malan Amadu baison "Jannah" mahaifiyarta tayi kuka har tagaji ya daina abunda yake ma yarinyarsu ,amma yak'iji kullum tsanar ta k'aruwa take mutanen gari kowa yasan halin malan Amadu baya k'aunar "Jannah"wasu har zaginshi sukeyi Akan tsanar da yake nunama 'yar shi , Makarantar allo kawai take zuwa itama ba kullum ba Dan in aka korota Akan kud'in laraba sai tafi sati biyu bata koma ba saboda babanta bazai biya mata ba , Yauma Kamar kullum zaune "Jannah" take tana wanke allon ta saboda zatayi sabon rubutu da aka bata A fusace mahaifinta yashigo gidan ko sallama bai yiba, "Jannah" na ganinshi tamik'e tana neman hanyar guduwa saboda indai ta tsaya to ko batayi laifi ba zai Fara dukanta ganin yatsare hanya da zata gudune yassa ta tsugunna a inda take tana kuka tana fad'in "Don Allah baffa kataimakeni kayi hakuri kar ka dakeni wallahi Bani bace nake kashe 'yan uwana ba Aradu ni ba mayya bace don Allah kayi hakuri karka dakeni "tak'arasa maganar cikin matsanan cin kuka jikinta sai 6ari yake , Maganganun nata ne suka k'ara fusata malan Amadu don haka a fusace yayi kanta yafara dukanta tako ina bugun ta yakeyi Kamar Allah ya aiko shi Matsiyaciya har kina da bakin magana kin kashe min 'ya'ya kin d'oramin talauci sannan kizo kina Bani hakuri? Muguwa azzaluma kawai wallahi sai na walak'anta ki haka yai mata dukan mutuwa wanda ko tashi bata iyayi sai kuka take yi tana kiran "Mama kizo ki taimakeni don Allah baffa zai kashe ni kinji mama" ke kinsan Bani nake canye mai 'ya'ya ba don Allah "Mama" kicemai Bani bace " Mama kuka takeyi zaune a gefen tana kallon yadda malan ke fitarwa da "Jannah" jini amma bazata iya hanashi ba saboda yace duk Randa yake dukan "Jannah" tazo ta taimake ta a bakin Auren ta, Kuma abun ya had'u biyu mama macece mai matuk'ar hakuri har bada kwatancenta akeyi game da hakurin ta,Malan sai da yaga "Jannah" ta dai na numfashi sannan ya daina dukan ta yasa k'afa yafice daga cikin gidan,da gudu "Mama" ta d'ebo ruwa ta yayafamata "Jannah"wacce ta sume saboda azabar da tasha ,bayan ta farfad'o mama takai mata ruwa tayi wanka tagasa ciwo dataji gaba d'ayansu kuka sukeyi cikin dasashiyar murya "Jannah" ta kalli mama tace "Mama don Allah ki kaini gurin baffa na wannan bashine baffa na ba" kuka mama tasa ta rungumota jikin ta tace "Jannah baki da wani uba a duniya sai shi shine mahaifinki ki dunga yi mai Addu'ar shiriya amma tabbas shine mahaifinki ki daina neman wani uba bayan shi " Haka mama taita kwantar mata da hankali harta hakura ta daina kuka sai dai ajiyar zuciya da takeyi , haka *Rayuwar jannah* take tafiya a gidan mahaifinta wanda take ganin Kamar ba shine mahaifinta ba,haka mahaifinta yaci gaba da ganamata Azaba tun ina yana dukanta tana kuka har yanzu ta daina jin zafin shi Dan ko kukan ta dai nayi Yau an koro "Jannah" daga makaranta Kan kud'in Laraba jiki Asanyaye tashigo gidan d'akin mahaifiyar ta tashiga,ta zauna tayi tagumi lokacin mama ta shiga toilet tana fitowa taga cinyayin silifas din "Jannah" a bakin k'ofar d'akin ta ,Ajiye butar dake hannuta tayi tanufi d'akin koda ta shiga "Jannah" bataji motsinta ba saboda tayi nisan da tasaba a cikin tunani , Tausayinta ne yakama mama jitayi hawaye nabin fuskar ta jawo "Jannah" tayi jikin ta sai a lokacin"Jannah" ta dawo daga duniyar data tafi. 3&4 "Jannah" lafiya kike kuwa meya sameki kikazo kika zauna Anan kina tunani ina makarantar" cikin kuka "Jannah" tace "Mama kud'in laraba aka koroni kuma nasan ke bakida shi baffa ne kawai zan tambaya kuma kin San indai naje dukana zaiyi " tak'arasa maganar da kuka share mata hawaye "Mama" tayi sannan tace "karki damu 'yata kije kimasa magana inya dukeki yau wata rana goyaki zaiyi ko ba yau ba "Jannah" ni nasan komai ni San jifa k'asa zai fad'o kuma duk girman gari akwai k'arshe nai ke da mahaifinki bai so in sha Allah sai ya shiga k'ark'ashin inuwarki kijure duk wata wahala da zai baki bayan wuya sai dad'i kinji ko Dan haka tashi kije ki tambaye shi in sha Allah zai baki " jiki A sanyaye "Jannah" tanufi d'akin mahaifinta, Daga bakin k'ofar ta tsugunna tayi sallama Bai amsa mata ba yanufota a fusace tun Kan yaji abunda ya kawota yakifeta da mari har guda ukku sannan yace "Aradu "Jannah"da badan kurwata tafi taki k'arfi ba da tuni kin canye ni meyasa bakida fahimta ne nifa ba sonki ne banyi ba meyasa dole sai kinzo wurina ki nisanta kanki dani Dan gudun kada wata rana a wayi gari na kashe ki saboda k'iyayyar danake miki" "Baffa uba baya k'in d'ansa haka shima d'a baya k'in Iyayen shi wallahi baffa koda ka kashe ni nayafe maka don Allah baffa kataimakeni kabani kud'in laraba malan ne yakoroni ta k'arasa maganar tana kuka" hannu yasa cikin aljihun shi ya dauko wata tsohuwar naira hamsin yabata tana murna ta amsa ta juya zata tafi ya dakatar da ita yayo kusa da ita yace. "Wallahi har abada bana k'aunar ki ina Rokon Allah da yayi gaggawar d'aukar ranki kafin bak'in cikin ki yakashe ni yasa Nina mutu "Jannah" wallahi natsani ganinki " yana kai wa nan yajuya yashige cikin d'akin inda sabo "Jannah" tasaba da irin wannan kalaman a wurin mahaifinta,d'akin mama taje ta nuna mata kud'in tana murna tajuya ta koma makaranta tabiya kud'in,Rayuwa taci gaba da tafiya a haka kullum ba sauki sai wurin Allah Yau chairman din garin yayi rabon kudi inda malan Amadu yasamu dubu goma Ay baffa jinshi yayi Kamar an sashi a aljannah kasuwa yabiya yasiyo balango na d'ari biyar mai dadin gaske sannan ya wuto gida, Da sallama yashiga gidan wacce rabon shi da yinta ya mance Da fara'a mama tafito tana amsa sallamar ,ganin fara'a a fuskar shi ne yasa ta dauko masa tabarma ta shimfida mai suka zauna sannan yace cikin fara'a "Azumi ay yau take sallah a gidan nan Dan har balango na sawo miki na jika biyu da rabi Dan kici kiji dad'in bakin ki Nasiru chairman ne yayi rabon kudi shine nima yabani dubu goma,"Alhamdulillahi natayaka murna Allah ya amfana" k'unshin naman yacire a Aljihun shi yabata yace taci nan mama tafara cin naman suna fira sallamar"Jannah" ce ta dakatar dasu da dawowar ta kenan daga makaranta kenan , Tana shigowa Annurin fuskar baffa ya 6ace yakoma Kamar wanda aka masa mutuwa daga gefe ta tsugunna tana musu sannu da gida ,mama ce kawai ta amsa amma banda baffa "jannah" ganin mama nacin namane yasa hankalin ta ya koma wurin Dan rabon su da nama shekara guda kenan ,mik'a mata sauran naman mama tayi jiki na 6ari tamik'a hannu zata amsa Dan dama tuni yawonta bakin ta ya tsinke, Wani a zababben mari da baffa ya dauke ta dashi sannan ya rufe ta da duka sai da yayi mata dukan daya janyo mata targad'e a k'afa ,mama bak'in ciki yasa tamik'e ta shiga d'akin ta tana jiyoshi yana fad'in "wallahi baki isa kici naman nan ba bak'ar matsiyaciya hankad'eta yayi yasa k'afa yafice daga gidan yana bala'in shi yabarta nan wurin jiki duk a fashe sai kuka take yi gwanin ban tausayi Allah yakawo miki mafita *JANNAH* ta alkhairi. Mama da yake ta iya gyaran targad'e ita ta gyarawa "Jannah" targad'en sannan ta koya mata yadda akeyi ,koda dare yayi baffa k'asan shimfidar shi ya Adana sauran kudin shi cikin dare yana bacci 6era yaja kudin zuwa bakin ramin shi,koda gari yawaye baffa yakasa fita sallar Asuba yayi saboda neman kudin shi dabe gani ba koda yaga bai gansu ba cikin fushi yafito tsakar gidan baiyi wata wata ba yarufe "jannah" da duka tako ina wacce ke tsugunne tana k'ok'arin had'a murhu dukanta yake yana fad'in "Au Dan jiya na hanaki cin nama ne shine kinka sacemin kudina?to wallahi kinyi k'arya dole sai kin fitomin da kud'ina bak'ar muguwa mayya azzaluma 6arauniya bak'in cikin ki bazai kashe ni ba ki fitomin da kud'ina duk inda kika kai su" "wallahi baffa ni bansan kana da kudi bama bare na dauka kayi hakuri don Allah" Mama ko in banda kuka Babu abunda takeyi,shi ko baffa dayaga ya caje "Jannah" baiga kudin ba bud'ar bakin shi sai cewa yayi "Aradu awa ukku nabaki kije kwanar Dan audu kiyi karuwanci kizo kibiyani kudina in ba haka ba abakin auren uwarki ,jin furucin shine yasa tari ya sark'e mama tun tanayi a tsaye harta kai ga tafadi jini nabiyo bakin ta dakyar tace "Jannah"matuk'ar ba fyade aka miki ba duk ranar da son zuciya ko wahalar rayuwa tasa kika zubarda mtuncin ki a waje ba a gidan mijin ki ba ban yafe miki ba " da gudu "Jannah" tayi wurin mamarta tana kiran sunan ta shi ko baffa d'akin shi yakoma daniyyar dauko magani yajik'awa mama abunda yagani ne yabashi mamaki kudin shi ne bakin ramin 6era da sauri ya dauko yaduba Babu abunda yasame su yasaka a aljihun shi sannan ya dauko maganin yafito,koda yazo wurin mama numfashin na sama sama tace "Amadu na yafe maka Allah ya dawo daki Kan hanyar gaskiya Jannah kiyi hakuri da duniya da mutanen cikin ta Allah ya al barkaci rayuwar ki in sha Allah bazaki ta6e ba" dakyar tagama furta mata maganar daga k'arshe tace ga garinku nan tunda baffa ya fahimce mama ta mutu ya zube a wurin yana fad'in "Tur dake Jannah yanzu mahaifiyarki takuma sai da kika kasheta mai nayimiki kika kashe min iyali? Allah ya isa tsakanina dake " yasake rushewa da kuka ,ita ko Jannah jin mama ta mutu ne yasa ta yanke jiki tafadi k'asa sumammiya .muje zuwa Oum Amjad ce wasan yanzu aka Fara kudai ku hanzarta payment kar abaku labari 5&6 Ihun baffa ne yajanyo hankalin mutane da yake Asuba ce shiyasa suka jiyo shi nanfa mutane sukaita shigowa bakin baffa yak'i rufuwa kowa yazo sai yace mishi Jannah ce takashe uwarta wata ce ta d'ibo ruwa ta watsawa Jannah ta farfad'o sai kuka takeyi gwanin ban tausayi haka tanaji tana gani aka had'a gawar mahaifiyarta aka mata sallah Aka kai ta makwancin ta na gaskiya Allah yajik'anki mama ke kuma Jannah Allah yazama gatanmu gabaki daya Amin,duk mai imani yaga Jannah sai ya tausaya mata lokaci guda tafita hayyacin ta in banda kuka Babu abunda takeyi shiko baffa maimakon yayima matar shi Addu'a sai la'antar Jannah yakeyi wai taka shemai mata haka akaita zaman makoki har akayi arba'in din mama Jannah bata koma dai dai ba, Bayan wata hudu da rasuwar mama baffa ya had'u da wata bazawara mai suna Laure ya aure ta Laure irin tsofaffin karuwan nan ne Dan haka tana shiga gidan baffa bala'in shi ya k'aru Akan nada a wurin Jannah komai na gidan ita takeyin shi Dan har cikin dare take zuwa d'iban ruwa gashi da nisa wurin a tsakanin su haka zata kwana a hanya Dan ko a mashin ne za'a kai ka sai ka biya naira d'ari biyu kafin kaje bare ma Jannah ga jarkunan ruwa guda hud'u haka take tura kuran baiwar Allah,baffa bai ta6a kallon hakan a matsayin cutarwa ga Jannah ba sai ma dad'i da yakeji tuni ta daina zuwa makarantar allon shinkafa da wake Laure take dafa mata ta turata wurin tallah ga Jannah mai Kan tallah ce tana fita take k'arewa hakanne yasa Laure ta koma dafa mata sau biyu a rana safe da yamma take kaiwa yanzu Babu hutu a rayuwar ta ba irin wahalar da Jannah batasha kuma duk da haka a wannan halin da take ciki mahaifinta ko gaishe shi tayi baya amsawa sai dai ma yarufe ta da duka ko sau d'aya Laure bata ta6a cetonta ba,Ana haka ne wani kanin Laure yazo daga garin su murna wurin Laure Kamar me shima baffa yayi murna da zuwan 'Dan yaro ba kad'an ba ,To dama gidan d'aki biyu ne d'aya na Jannah d'aya na baffa da Laure Dan haka koda dare yayi baffa da kanshi yakai 'Dan yaro d'akin Jannah wai zai dunga kwana a nan d'akin kafin yatafi Jannah ko Ido kawai take warowa ganin ta d'aki d'aya da k'ato a shimfid'a d'aya,koda baffa yafita a d'akin'Dan yaro zuwa yayi ya kulle k'ofar da sakata sanana yazo kusa da Jannah ya kwanta cikin dare Jannah ta farka taga 'Dan yaro yacire mata Riga sai matse mata k'ananun na shanunta yakeyi wa 'Yan da yanzu ne farkon fitowarsu kuma sai zafi suke mata da sauri tamik'e zaune bakin ta narawa tace "meyasa kakeson zubarmin da mutunci na don Allah,?" Dariya yayi sannan yasake shafota yace "saboda mahaifinki bai nuna kinada mutunci ba tunda ya iya had'ani dake mukwanta wuri d'aya" kuka Jannah tasa mishi tana bashi hakuri amma ina 'Dan yaro sai k'ok'arin rabata da kayanta yake cikin sa'a Jannah ta k'wace kanta a hannun shi tafita tsakar gidan tana kuka ,da gudu baffa da Laure suka fito baffa yace "Dan uwarki meya faru kikema mutane kuka tsakar dare?baki narawa tace baffa 'Dan yaro ne yaciremin kaya yana son iskanci dani " Carab Laure ta kar6e maganar tace kaji munafuka lokacin da kike rabawa 'yan tasha ubanwa kikayima kuka sai yanzu dan sharri irin naki zaki ce wai 'Dan yaro uban me zaiyi dake " baffa ne yak'arasa wurin Jannah yarufeta da duka sai da yayi mata lilis sannan ya hankad'ata cikin d'akin da 'Dan yaro yake ciki yace "bak'ar munafuka kyayi kya gama yanzu kuma sharri kika zo dashi to wallahi munfi k'arfinki " daga haka suka juya d'aki shida Laure suka rufo k'ofa , 'Dan yaro ko murna ce takamashi Dan haka wurin Jannah yanufota tana tsugunne tana kuka hango shi tayi zaizo wurin ta takwasa a guje tafice ma daga gidan gudu take ba kama hannun yaro har ta isa gidansu wata k'awarta Aisha kuma Innan Aisha tana da mutunci Baban Aisha yarasu dayake gidajen k'auye ba kowa yake rufe k'ofa ba Dan haka shigewa Jannah tayi tabaje tsakar gidan koda 'Dan yaro yabiyota bai ganta ba yakoma gida yana cizon yatsa , A tsakar gida Jannah takwana ko Riga Babu a jikinta da Asuba innan Aisha ce tafara fitowa koda taga mutum kwance tsakar gida bataji tsoro ba abunka da mutanen karkara kanta tsaye taje wurin Jannah tana tambayar lafiya waye farkawa Jannah tayi ganin Innar Aisha ce yasa yafase da kuka tace "Inna nice Jannah Inna tace lafiya Jannah kika kwana tsakar gida nan Jannah takwashe komai tafad'awa Inna" tsananin tausayin Jannah ne yasa Inna kuka kamota tayi ta rungume ta cikin kuka tace "kiyi hakuri Jannah in sha Allah nan gaba zakiga amfanin rayuwarki kibarma Allah komai yana sane da halin da kike ciki" daga haka d'aki takaita nan Aisha taita kuka tana tausayin kawarta kaya tabata tasanya bayan tayi wanka tayi sallah taci d'umamen tuwo sannan tanufe gidan su , A tsakar gida tasamesu suna karyawa Babu wanda yadamu da ita bare yatambaita daga ina take kayan tallah ta d'auka tafice zuwa wurin tallan bayan ta amshi kudin mota hannun Laure Dan akwai nisa wurin da take zuwa tallah, Da misalin karfe goma na safe bayan fitar Jannah tallah hajiya mai Makkah ta sauka a cikin garin Barkeji gida gida take bi tana neman yara da uwayen su keson bada su akaisu saudiyya aykatau ayko duk gidan da tashiga Babu mai bada 'yar shi kowa yak'i a haka harta shiga gidansu Jannah 7&8 Da fara'a Laure ta tarbeta koda hajiya saude taima mata bayanin abunda yakawo ta ba k'aramin dad'i tajiba auna cikin tattaunawa Jannah ta dawo daga wurin tallah nan take Laure tace Hajiya ta tafi da Jannah ta bata lokacin mahaifin Jannah baya nan Laure ta yanke hukunci dubu d'ari biyu hajiya taba Laure ay jiki na rawa ta amsa Kamar wadda aka sa a aljannah murna da godiya Kamar hauka sabon kamu cikin masifa Laure tasa Jannah had'a kayanta kuka Jannah takeyi tana bata hakuri amma tak'i sauraron ta daga k'arshe ma ta rufe ta da duka ganin zata 6ata mata lokaci ne yasa taje da kanta tahad'o mata 'Yan tsumukaran kayanta a Leda tamik'a mata tace da hajiya saude gatanan hajiya taja hannnu Jannah suka wuce daga gidan,haka Jannah tanaji tana gani aka sakata a mota hajiya saude ita kuma ta kulle motar suka tafi ko da baffa ya dawo Laure tabashi dubu sittin sannan tace"naga harkar k'aruwa ce shiyasa nabada ita nan ne Abuja za'a kai ta Babu nisa zata zatayi aikatau duk bayan wani lokaci zatazo ganin gida" baffa ko damuwa baiyi ba yashiga sawa Laure al barka suko mutanen gari kowa yadauka antafi da Jannah wurin yawon bariki ne ko da labari yazo a kunnen baffa ko damuwa baiyi ba Dan yasan hassada ce tun Jannah tana kuka har ta hakura ta dai na haka suka cigaba da tafiya hajiya saude najanta da fira ga sanyin a.c yana busowa ay Jannah sai bacci ya dauke ta har suka isa Abuja birnin tarayya bata sani ba koda hajiya saude tayi parking Jannah bata sani ba sai da ta tashe ta a firgice ta farka haka hajiya tajata zuwa cikin gidan Jannah sai k'auyanci takeyi saboda wannan shine Karon farko data ta6a shigowa cikin birni birnin ma a Abuja kunga ko dole tayi k'auyanci koda suka shiga ciki 'yan mata ne zaune cikin falon sai wata babbar mace a tsaye gabansu tana koya musu wani Abu koda Jannah ta lurada kyau Ashe tafiyar Jan hankali ake koya musu ganin sune yasa matar zuwa da fara'a tace "Hajajo mutanen Makkah ina kika samo wannan sabuwa farar Zuma haka?dariya hajiya saude tayi sannan tace "Hmmm ke dai bari Uwani wallahi a can wani k'auye na siyota a farashi mai sauki dubu d'ari biyu kin ganta nan na kawota nasan zamu samu dubunsu a jikinta saboda in kin Lura yarinyar akwai k'ira a jikin ta" dariya Uwani tayi sannan tasa hannu ta shafi fuskar Jannah wadda tunda suka Fara magana take waro Ido Kamar tsohowar mayya sannan tace "zancanki gaskiya ne nasan tana isa birnin Jidda hajiyar sama zata gyarata kamin tasata a kasuwa Dan haka yanzu kije da ita Amata passport Dan banson suyi sati biyu a k'asar nan batare da an aunasu ba kuma kinga k'afar ta akwai Faso ga kanta sai tsami yake saboda haka ki kaita saloon a gyara komai najikin ta yadda yakamata kinsan halin hajiyar sama bata son k'azanta" tafawa sukayi sannan hajiya saude tace "naga 'yar mai duguri tana nan Dan haka in mun dawo daga saloon zan kaita can a bata kayan mata Dan tajik'u da kyau saboda kinsan halin larabawan nan basuson suji rami sunfison kullum sujiso cikin damuna" wata uwar shewa sukayi sannan hajiya saude tayiwa Jannah umurni data taso suje Babu musu Jannah tabita saboda bata gane manufar zancensu ba wurin gyaran k'afa da gyaran kai ta kaita aka gyara Jannah sai gata tafito fess da ita ,wurin passport sukaje nan ma akayi mata daga nan sai wurin mai maganin mata suka wuce nan akai ta d'orawa Jannah magunguna Akan dole take sha duk da batasan ma'anar su ba Amman tanajin a ranta ba abun cutarwa bane harda na tsugunawa sai da suka mata sune dai basu dawo gida ba sai wajajen shad'aya na dare. Muje zuwa Oum Amjad ce yanzu aka Fara💗💗💗 *Littafin Rayuwar jannah* *na kudi ne Akan naira 400 kacal 👌zaku iya biya ta wannan account din* *2152266594* *Maryam Bello* *u b a* *sai a turamin da evidence ta wannan number* *09163353050* *bansan Kati* .. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels