An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»Ώ[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ 1 Kuka take sosai har tana shid'ewa ,Yarinya ce 'yar wata ukku kyakykyawar gaske Fara sol Kamar 'yar turawa , kallo Daya zaka Mata kasan cewa ta galabaita tun tana kukan da hawaye har sun daina fitowa , Abun mamaki duk wannan kukan da take tana rik'i ne a hannun wani matashin saurayi Wanda bazai wuce shekara 30 zuwa 32 ba , tunda yarinyar ta Fara kuka kanshi yak'e k'asa , fiye da minti talatin ko motsin kirki yakasa Yi duk kuwa da irin yadda kukan yarinyar ke soya mashi zuciya , yanajin kukanta har cikin ruhinshi Amma tsabar tashin hankalin da yake ciki ya Sanya ko motsin kirki yakasa Yi, A hankali ya d'ago manyan idanunsa Wanda suka rine sukayi jajir yayinda jijiyoyin kansa suka firfito ,kallo Daya namasa Saida na firgita , isashen namiji ne ajin farko Kuma k'ak'k'arfa gaba Daya jikinshi a murd'e yake duk wasu alamun k'arfi sun bayyana a jikinshi , Akan yarinyar ya sauke idanunshi kamun a hankali yafara jijjigata , jakar dake kusa dashi ya bud'e wata 'yar gora ya d'auko ya bude ya kafawa yarinyar a baki , ruwa ne ,takuwa Sha sosai sannan a hankali tayi shiru tana ajiyar zuciya, Kamar wata Mai wayo Haka ta kafe shi da ido suna kallon junansu , a hankali wasu hawaye masu zafi suka Fara sauka akan fuskarsa , _Bazan yafe ba , bazan ta'bawa yafewa Wanda duk ya jefa rayuwata a wannan had'arin ba ,tabbas sai na dauki fansa Koda Zan rasa Raina sai na dauki fansa wannan alkawari ne_ _Bazan baka *Muneeba* ba har sai kayimun alk'awari biyu, na farko inason kayimun alk'awarin bazaka ta'ba zuwa Neman fansa ba na biyu Kuma inason ka *Ajiye aikinka na d'an sanda* idan ba Haka ba to bazan ta'ba baka 'yata ba *Hisham* gara ta mutu a nana Hisham ta k'arasa maganar cikin tsananin azabar da takeji ga jini na fita ko ta ina a jikinta,_ Magan ganunta suka shiga dawo Masa cikin kunne Kamar yanzu take fad'a Masa , Rik'e kansa yayi dayaji Yana juyamasa Kamar zai cire yayinda zuciyarshi ke mashi wani irin zafi Kamar zata fashe, tsabar bakin ciki yasa ya fasa wata irin k'ara wadda Saida dajin ya amsa kuwa , hakan kuwa ba k'aramun razana *Muneeba* yayi ba nan ta fashe da wani irin kuka a gigice, Tashi yayi da ita a hannunsa ya duk'a ya dauki Yar k'aramar Jakarshi ya juya yaci gaba da nausawa a cikin jejin, Dajine Mai matukar girma da had'arin gaske Haka yarinka ratsawa ta cikinshi Babu alamar tsoro a tare dashi, yayinda Muneeba take goye a bayanshi tana baccin wahala, ................✍🏼 *Pls ku taimaka ku tayani share in ya karbu zanci gaba, yan bati siddan asha karatu lfy wannan free ne daga taku 'yar mutan sokoto mmn Yusuf Mai kayan mata*πŸ€— MARYAM UMAR ABDULLAHI CE........✍🏼 [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_2 ..............Yayi tafiya Mai nisan gaske kamun yasamu gidin wata babbar bishiyar mangoro ya zauna Yana maida numfashi , zuwa wannan lokacin ita kanta Muneeba ta gaji da baccin hawalar da ya sureta ta tashi , saboda yanayin yadda ya goyata din ma ya Isa ya wahalar da ita, Wannan karon batayi kuka ba sai sauke numfashi da takeyi a hankalai hannunta Yana cikin bakinta tana tsotsa yayinda take kallonshi tana wutsil-wutsil da kafafu irin na yara, Shima idon ya tsuramata cikin matuk'ar damuwa da tausayin tilon 'yarshi hawaye ne suka Fara fita daga idonshi suna sauka akan fuskarta , hawayen da bayajin akwai Ranar da zasu daina zuba, Jin saukar danshi akan fuskarta yasa ta bingile da dariya a hankali ya sakar Mata murmushi ganin yadda take dariyar ,sun shagala sosai Kamar daga sama yafarajin wata irin suwa kadan kadan , juyawa yayi yafara dube_dube , aikuwa sai ganin k'aton maciji yayi ya laulaye waje Daya ya fasa kanshi Yana fitar da harshenshi irin yadda maciji keyi in yaso mugunta , A firgice ya mik'e tsaye Yana maimata innalillahi wa Inna ilaihin raji'un Sam ba kanshi yakeji ba Muneeba yake ji da don ta shine da baik'i macijin Nan yayi ajalinshi ko ya huta da wannan bak'incikin, Take wata zuciyar tace mashi _kana nufin zaka iya mutuwa ba tare da ka dauki fansa akan mak'iyanka ba ? Yana da matukar muhimmanci ka rayu yazama doli karama abunda aka maka_ duk acikin Yan second yayi wannan tunanin , Macijin kuwa ya tare hanya ba inda zai ra'ba ya wuce , gashi kiris yake jira ya motsa ya kawo mashi Sara , ganin Babu yadda zaiyi Haka yafara motsa kafarshi a hankali , aikuwa Kamar jira macijin keyi yayi kanshi gadan-gadan da sauri Hisham ya d'aga k'afa da niyar guduwa Amma kamun kyaftawar ido macijin ya kawo mashi Sara a k'afa , wata k'ara ya saki saboda azabar da yaji taga-taga yayi zai fad'i Amma Yak'i yarda ya Kai k'asa hannunsa na rik'e da Muneeba k'am kamar zai maidata ciki, Yink'urawa maciji yayi yak'a Kai mashi wani Sara a k'afa take yak'ara sakin wata azababbiyar k'ara Wanda baisan sanda ya saki Muneeba ba ya fad'i k'asa , take duniyar tafara juyamashi idanunshi suka Fara gani dishi-dishi hannunshi ya d'aga yanata son yakai ga Muneeba Amma yakasa a hankali idunshi suka Fara rufewa ,yayinda yakejin wani irin zafi a k'asan zuciyarshi , tausayin Muneeba dakuma rashin daukar fansarsa , inaaaa yakamata na rayu, yakamata na rayu wannan itace kalmar da yayi ta nanatawa har idonshi suka rufe ruf, Muneeba kuwa tana gefe tana rusa kuka kamar zata tashi wajan don taji ciyo a kanta sanadin fadowar da tayi daga hannunsa , a hankali macijin Nan yafara kusantar ta har yaje inda itake , kuka takeyi sosai yayinda macijin ya fasa Kai da nufin saranta, Kai *Hajar* kamar kukan yaro nakeji ko, ? " Eh Nima naji saratu na dauka ko kunne na ne yaji , "to amma mi zai kawo yaro cikin wannan k'asurgumin dajin Mai had'arin gaske ,? Wanda mu kanmu da muke da tsarin jikinmu ba k'aramun fama mukeyi da miyagun abubuwan dake cikin dajin Nan ba, "Kinga saratu ba wannan ba zo muje muga Mike faruwa Haka suka mik'e da azama suka nufi inda sukejin kukan yaron, Kamar daga sama suka hango yaro kwance Yana tsala kuka ga Kuma maciji yana Shirin saranshi, cikin matuk'ar zafin nama da k'warewa Hajar ta fito da bakar ta ta saita macijin , cikin matuk'ar k'warewa ta sake mashi kibiyar suttt sai a tsakkiyar kanshi , take yayi wata irin gumza.yafara birgina a k'asa ,kamun kace mi ya mutu a wajan , da sauri Hajar ta k'arasa ta dauki Muneeba tafara jijjigata cikin harshen fillanci take cewa da Muneeba tayi shiru, Itama saratun cikin fillancin take cewa ke Hajar Taya Zaki dauki yaro daga ganinshi bazaki tsaya har ki tantance ko mutum ne ba , inba hakaba Taya za'ace an samu yaro anan shi kad'ai" ?..............maganarta ta katse ne lokacin da sukayi ido hudu da Hisham kwance ba alamar Yana numfashi , Aguje sukayi kanshi suna dubashi , ganin saran maciji a k'afanshi yasa suka zaro ido waje cike da tashin hankali , Nan Hajar ta dubi saratu tace "Saratu Yi sauri kije ki kiramana Baffah yazo ya dubashi , Hajar inaga fa ya mutu kawai kizo mu koma gida inyaso sai mu tafi da wannan yaron daga baya su Baffah suzo su tafi da gawar, "Aa Sarah Bata tunanin ya mutu kawai kije ki Kira Baffah Ni Zan tsaya anan ................... *daga alkalamin Yar mutan sokoto maman Yusuf* Karki wuce baki karantaba kila ki amfanaπŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ» πŸƒπŸ’ πŸƒπŸ’ *MAGUNGUNAN CIWON SANYI (TOILET INFECTION)*πŸ‘‡πŸ» πŸƒπŸ’ *KARIN NI'IMA DA GAMSAR DA MAIGIDA*πŸ‘‡πŸ» *CUTA DA MAGANI*πŸ’Š πŸ’Š πŸƒπŸ’ *_Mu na rokon da Allah ya bamu lafiya ingantatta kuma yasa kaffarane_* . _A gwada daya daga cikin wadannan_ :πŸ‘‡πŸ» 1- A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi. πŸ’πŸƒ 2- A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Ya na fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. πŸ’πŸƒ 3- A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono a na sha. Ya na magance matsalar ruwan infection. πŸƒπŸ’ 4- A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba. πŸƒπŸ’ 5- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushe wa da rashin gamsuwa. πŸƒπŸ’ 6- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma ya na kara ni’ima. πŸƒπŸ’ 7- A samu Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma ya na sa matsewa. πŸƒπŸ’ 8- A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barko no da Raihatul Hubbi, sai ta da ke su ta yi yaji tadinga cin abinci da shi. Ya na saukar da ni’ima damagance duk matasalolin sanyi. πŸƒπŸ’ 9- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu ya na maganin kuraje da kaikayi da fitar ruwa mai wari. πŸƒπŸ’ 10- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Ya na wanke dattin mara kuma ya na samar da ni’ima. πŸƒπŸ’ 11- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai tahada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta nasha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali dayakullum kafin ta karya. Wannan ya na maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa. πŸƒπŸ’ 12- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki daukisala daya ki yi matsi dashi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku. πŸƒπŸ’ 13- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda ki yi matsi da shi.Ni’ima Ba Sassauci Da farko daki samu kaza budurwa wadda ba ta fara kwai ba.Sai ki cirere hanjinta ta cikin dunbutu tunda ba a bukatar ayi mata gunduwa-gunduwa. Sai ki gyara ridinki (kantu) kishanya ya bushe sai ki daka shi. Kina iya tafasa kazar sannan sai ki zuba ridin ta cikin zunbutun kazar. Sai kisamu abu ki daure zumbutun; sannan ki hada kayan miya kadan sai ki kara zuba nonon rakumi a cikin kayan miyar ki hada ki dafa har sai sun dahu sai ki sauke. Ki cinye ki shanye romon πŸ˜‹ Sannan a ranar ki jika kanumfari ya jiku sosai. Ya zama ruwan shanki. Muna sayarda ingantattun kayan mata zafafa masu kyau da inganci don neman Karin bayani sai a tuntubeni ta wannan number 09035027743 . β€’-------β€’β€’βˆ†πŸƒπŸ§‘πŸƒβ€’------- [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_3 ...................cikin minti 15 saiga su Baffa shida yaranshi maza su biyu Halliru da Abubakar Wanda suke Kira da Habu, da yake akwai Dan tafiya tsakanin inda suke dakuma inda fulanin suke zaune, Da sauri Halliru da Habu sukayi kanshi suna fad'in subuhanallahi, Baffah kam zuba mashi ido yayi Yana karantarsa don sanin ya mutu ko kuwa bai mutu ba, Hannunshi yakai saitin zuciyarshi kamar 2mnt yaji zuciyarshi na harbawa kad'an kad'an , Alhamdulillah ya furata kamun ya dubi yaran yace " yawwa Yana raye Kai Habu daukomun ruwan ganyen can nasa mashi, Wata k'ak'k'arfar aziyar zuciya Hajar ta sauke ga idonta duk hawaye , ba k'aramun dadi taji ba don wannan yarinyar take tausayawa , Ruwan magani Baffa yasa mashi a wajan kamun ya dauko wani farin magani ya shafa mashi ya dauko wani kyalle ya daure wajan sannan ya umurci yaran da su kamashi su tafi dashi, Dak'yar suka kamashi suka daukeshi sai Nishi sukeyi don Hisham ba k'aramun kakkarfa bane donma sun Saba da wahala da juriya ne da bazasu iya daukanshi ba, Haka suka tafi dashi Hajar na rik'e da Muneeba yayinda Saratu ke rike da jakar kayan Hisham, ************************ Subuhanallahi Malam mi yake faruwa ne ,? Ba komai Hajo wani bawan Allah ne su Hajar suka samu maciji ya sareshi a k'afa shine suka kirani mukaje akazo dashi. Ayya Allah ya bashi lafiya da fatar dafin bai shiga jikinshi sosai ba, ta fada cike tausayawa, "Dafi kam ya shigeshi sosai sai dai fatan Allah ta tashi kafad'arshi , gashi wannan shegiyar macijiyar Nan ce ta sareshi *(Gajera)* , "Gajera shin Malam ? Tayi maganar tana dafe gaba , *gajera* wata macijiya ce mai matukar had'arin gaske ko acikin macizai ita din dabance dafinta Yana da matukar hadari a jikin mutum, "Kije ki dauko mun magungunan da nake amfani dasu ki dafamun na dafawa inason Daya farko shi zai Fara Sha , "To Malam" Dauko mashi magungunan tayi ta ajiye mashi ta dauki Wanda zata dafa ta koma can tsakar gidan inda suke girki ta yayo Kara ta rura wuta ta wanke tukunya ta Dora maganin sannan ta dawo kusa da Malam ta zauna tana kallon yadda yake sawa Hisham magani ga ciyon, Hajar kuwa na gefe sai faman lallashin Muneeba takeyi ta dauko zanen innarta ta goyata tanajin wani irin son yarinyar , dama Haka Hajar take Allah yayita da shegen son yara Kamar mi kasancewar itace k'arama a gidan tana masifar son yara , shiyasa takejin kamar Allah ya kawo Mata kyautar muneeba ne , Kallonta Inna tayi tayi dariya cikin harshen fillanci tace tofa su oo ansamu abunda akeso anyi 'ya to ai sai ki samu waje ki zauna ko tunda tayi bacci ,dariya tayi wadda ta fito Mata da ainahin tsantsar kyau da Allah yayimata tace Kai Innata banfa gaji ba in na zauna tashi zatayi , " "Ke kika jiyo " cewar Inna , Baffa yajima yanama Hisham magani Saida yaga ya farfad'o yasa aka dauko ruwan maganin aka bashi baisha da yawa ba ya janye yanason ya tambayi 'yar shi Amma yakasa magana a Haka wani nauyayyan bacci yayi awon gaba dashi dama maganin Yana saka bacci , Tashi Baffa yayi yaja su Habu suka koma wajan kiyo bayan yace da Inna ta kula da marar lafiyar, Muneeba Bata jima tana baccin ba ta tashi saboda muguwar yunwar da takeji, Inna ce ta k'arbeta ta debo sabuwar madarar Shanu tafara Bata, aikuwa kamar jira take Nan take tafara Sha har tana k'warewa saboda ba k'aramun yunwa taji ba tunda suka bar gida ruwa ne kawai Hisham yake Bata , don tsabar tashin hankalin da suka tsinci kansu aciki yasa Sam baiyi tunanin dauko Mata wani abun da zataci ba , sai a hanya ne ma yasamu ruwan da yake Bata, Bayan tagama Sha ne Inna ta debo ruwan zafi ta Mata wanka , Saida ta gasata sosai sannan ta dauko kayanta ta maida Mata , aikuwa nan take sai yarinyar tafara lumshe ido alamar bacci , Zane Inna ta dauko zata goyata ,ai da sauri Hajar ta k'araso Kamar zatayi kuka tace aa Innata nidai ki bani d'iyata Ni Zan goyata bangaji ba, "Aa Hajar wannan shegen goyon naki bazataji dadinshi ba kinga alamu sun nuna a gajiye take kibari na goyata ta samu bacci Mai kyau daga Baya sai ki k'arbeta , " "Aa nidai Inna kibani ita Zan goyata da kyau, πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈdafe Kai Inna tayi don tasan halin Hajar da shegiyar rigima indai akan yara ne yanzu ma tasan ba k'aramar rigima za'asha ba duk lokacin da wannan kadon yasamu lafiya yace zai tafi da 'yarshi, Goya Mata ita tayi taje taci gaba da aikinta, Ganin hakan yasa Hajar sulalewa tabar gidan cike da farinciki sai tafiya take tana shilla sandarta a sama tana 'yan wak'e-wak'enta, gidansu saratu ta nufa Kai tsaye, Da sallama ta Shiga gidan , innar saratu na tsakar gidan tana daka ta amsa Mata , gaisheta Hajar tayi sannan tace Inna Ina Sarah, ? "Taje zata yomun itace Zan Dora girki ,Amma yanzu zata dawo,..........ko rufe bakinta batayiba sukaji sallamar Sarah ,tana ganin Hajar ta Yar da itacen ta nufeta tana cewa , "tun d'azu nake sauri nasamu itacen Nan na dawo inje gidanku ganin wannan yarinyar tayi maganar tana nuna Muneeba, Washe baki Hajar tayi tace aikuwa Inna Bata ma San na fito ba da bazata barni na fito da itaba nikuma so nake muje wajan wasanmu da ita yau mun huta da wulk'ancin da su wuro ke Mana , Haka suka fita cike da farinciki don Sarah ma ba bayaba don itama ita kadai ce a gidansu ba wa ba k'ani shiyasa itama takeda son yara sosai yanzu kuwa sai farinciki sukeyi sun samu yarinya Mai kyau Kuma Yar gayu ba irin yaran garinsu ba, Wajen da Sarah take kiyo sukaje , wajene da mutane da yawa ke taruwa a wajan maza da Mata da shanunsu don yin kiyo kasancewar wajan yazama magudanar ruwa ga Ni'ima ciyayi da sauransu , Haka zasu zauna suyita fira da wasansu , inda da yawa masu ke zuwa da kannensu irin su wuro da Habeeba da yake wajan bashida nisa da inda suke zaune, Haka Sarah da Hajar zasuyi ta daukar kannen nasu Amma in Yan wulakancin suka motsa sai su hanasu shine yau suke murna suma sunada yarinya Kuma Mai kyau Aikuwa suna zuwa k'awayensu sukayi masu caaa suna kallon yarinyar tareda yaba kyaun ta duk da su dinma ba baya ba wajan kyau na bugawa a jarida to Amma yanayin shigar Muneeba da yadda akayi Mata gyaran gashi da wasu kananan ribom shi ke rudarsu Hajar sai dadi takeji ana yaba 'yarta Kamar yadda take cewa , ************************ Kamar a mafarki yafara tuno abunda ya faru dashi ,gefe Daya Kuma *Lauratu* yake gani cikin mawuyacin hali tana Kiran sunanshi , a firgice ya farka ya tashi zaune yafara dube dube, a hankali ya furta Muneeba!! Zaro ido yayi cikin tsananin tashin hankali da k'arfi yace Noooooooo Muneeeebaaaa !!!!! Aguje Inna ta k'araso inda yake cikin harshen fillanci take cewa , "Lafiya dai dannan,? Ina ne yake maka ciyo? D'ago Dara daran idonshi yayi da suka rine da ja ya zuba Mata su, Ba k'aramun razana Inna tayi da yanayinshi ba ga wani kallo da yake jifanta dashi Wanda bayako k'yaftawa ,tuni jikin Inna yafara rawa, "Ina Muneeba "? Itace tambayar da ya jefa Mata , Inna ba wata hausar kirki takeji ba ta fahimci abunda yake cewa Amma tarasa ta yadda zatayi mashi bayani , cikin fillancin dai takara cewa yaronka Yana wajan Hajar ka jira yanzu zata dawo...........a tsawace yace "Ina 'yata take ? Wannan karon kam sai da Inna tayi baya Kamar zata fad'i saboda yadda yayi Mata tsawar ,ganin jijiyoyin kanshi sunfara tashi yasa Inna fita daga dakin a tsorace ,ganin hakan yasa ya Mike tsaye da kyar ga shi yakasa taka k'afar a Haka ya dafa kyauren bukkar ya fito bai ko kalli Inna ba yayi hanyar barin gidan , Da sauri Inna ta bishi ta na Yi mashi alama da hannu akan ya tsaya zataje ta kawo mashi Yar shi, doli ba yadda ya iya don yakasa tafiya da k'afar ya Zame a wajan ya zauna , Nan take abunda yafaru dashi yafara dawo mashi kamun kace mi gaba Daya jijiyoyin jikinshi sun tashi kanshi ya rike da yaji Yana barazanar fashewa yayinda muryarta ke mashi amsa kuwwa a kunne ,gefe Daya Kuma muryar Amminshi ce yakeji akowane bangare na gidan tana amsa kuwa, .......... *_shalele nidai Allah yagani banason wannan aikin naka na d'an sanda* *mizai hana ka canza_ _wani , hankalina yakasa kwanciya shiyasa tun farko banso kayi wannan aikin ba don nasan waye Kai nasan halinka Sarai Amma ka kafe sai kayi*_ Dafe kanshi yayi da sauri kamun ya buga wata irin k'ara , k'arar da tayi sanadiyar zubewarshi a wajan a some , hakan kuwa yayi daidai da k'arasowar Baffa gidan Wanda dawowarshi kenan , Da sauri yak'ara inda yake Yana Kiran subuhanallahi Hajo Hajo yaji shiru tsaki yayi Yana tunanin inakuma ta tafi ita da aka barwa marar lafiya tsaki yak'ara Yi kamun ya tashi ya samu ruwa ya yayyafa mashi ,ajiyar zuciya ya sauke kamun a hankali ya bude idanunshi , bude idonshi yayi daidai da shigowar Inna tareda dasu Hajar , Akan Muneeba yafara sauke idanunshi , wata k'ak'k'arfar aziyar zuciya ya sauke kamun ya Mika hannu da nufin amsarta , da sauri Hajar ta goce ta koma baya kamun su Ankara har ta Sanya Zane ta goyata tafara tafiya tana cewa Yi hakuri *Hamma* bacci takeyi , kajira ta tashi sai na kawota tana gama fadin Haka ta k'arasa shigewa cikin 'yar bukkarsu, Baffa da Inna kuwa baki suka saki sukabi Hajar da kallon mamaki ga yarinya ido biyu kiriri zatace tana bacci Amma ba abun mamaki bane don sunsan waye Hajar akan son yara Kamar mayya Haka take indai akan yara ne, Hisham kuwa a zafafe ya bita da kallo cikin bacin Rai ya yunkura zai tashi..................✍🏼 *Akwai Zafafan Kayan Mata masu kyau da inganci ga Mai bukata ta tuntubeni ta wannan number 09035027743 *Karki wuce baki karanta ba Mai yiwuwa ki amfana*πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ» 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 *MATSALOLINMU MATA GRP* πŸ‘©β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘¦ *BY MAMAN YUSUP* _09035027743_ *BUDURCINA…..……1* Da sunan allah mai rahma mai jinkai tsira da aminci su kara tabbata ga manzan tsira manzan rahma annabi muhammadu sallalahu alaihi wa sallama ina farin cikin gabatar muku da dan takaitaccen littafi me muhimmanci ga rayuwar aure tareda addu’ar allah yasa albarka acikinsa Rayuwar farin ciki tareda samun kulawa ta soyayya da yabo akoda yaushe shine burin β€˜ya mace ma’ana shine abunda mace tafiso fiyeda komai a duniya domin kuwa duk irin arziki da jindadi da mace ta samu bazasu bata nutsuwaba matukar ta rasa kwanciyar hankali tareda miji kuma kowa ya sani kwanciyar hankali a gidan miji ba abune sai mace ta isa aure ake zaunarda ita ayita mata fadaba tun tana karama ake dorata akan hanya me kyau tayanda zatasan ita wacece ta hanyar bata ilimin addini dana zamani wannan shine ginshiki me samarwa mace farin ciki tareda miji a rayuwar aurenta Tabbas akwai gagarumin banbanci tsakanin rauwar mace data namiji domin shi namiji yakan rasa abubuwa da dama na rayuwa amma ita rayuwar ta bashi damar samunsu sabanin mace wanda da zaran ta rasa abu a karo na farko tofa Akwai yiwuwar rasa farin cikin ta na har abada kamar yanda ayanzu wasu ke nadamar kankanin kuskure da suka tabayi arayuwarsu Amataki biyar ne mace ke rasa budurci ta hanyar saduwa da namiji wanda idan ta tsallake wadannan to tabbas tayi gagarumar nasawa a rayuwar ta mijinta na farko shine zaisanta 'ya mace 1 _ mataki na farko shine lokacinda take karama idan har bata samu kyakyawar kula da tarbiya ba hakan yana faruwa da ita saboda kusan duka yara da ake yiwa fyade zakaga rashin kulawa ne tareda sakacin iyaye kuma irin hakan yafi kasancewa idan yarinya bata gaban mahaifiyarta 2 Mataki na biyu kuma talauci lokacinda mace keda bukatu na yau da kullum amma ya kasance babu wanda zai dauki nauyinta mata da yawa sun rasa budurcinsu ta wannan hanyar 3 mataki na uku lokacinda mace ke tsakiyar Sha'awa babu abinda takeso fiyeda aure zakaganta da samari samada biyar To amma kuma babu wanda zata aura daga ciki saboda iyayenta karatu sukeso tayi hankalinsu baya kan wane hali take ciki da suwaye take mu'amala? Ina take zuwa? Suwaye kawayenta? Koda yake ana samun wanda mijin aurene bata samuba ko kuma iyayenta basuda halin yin aurenta to wannan halin ba karamin hadarine ga 'ya mace ba 4 mataki na hudu kuwa shine mace marar kamun kai idan har mace ta zama me mu'amala da maza dole hakan ta iya faruwa da ita inda zakaga wasu acikin abunsha ake saka musu magani idan har mace tanason tsallake wannan matakin tofa dole ta zama me kamun kai tareda kiyaye kanta da mu'amala da maza barkatai 5 a karshe kuma akwai soyayya yayinda mace ta hadu da wanda takeso takanji babu abinda zai nema wajenta ta hanashi tofa anan idan akayi rashin sa'a wannan saurayin nata yaso yaudararta nanfa zai mata alkawarin zai aureta to amma bayan ta amince nan zata gane asalin shi wanene kunga wadannan matakai guda biyar sune sukeda muhimmanci a rayuwar mace da zaran ansamu matsala a daya daga ciki tofa nan mace zata shiga halin rashin tabbas akwai tambayoyi da wannan littafin zai amsa misali akwai masu tambayata tareda neman shawara akan acikin maza guda biyu wanne yafi dacewa mace ta aura amatsayin miji? 1 na farko namijinda ya sadu da mace kafin ayi aure 2 na biyu kuma wanda yasan an taba saduwa da mace amma yace zai aureta ahaka To idan ace dukkansu sunason auren mace kuma tanada zabi wanene daga cikinsu zata aura ta samu kwanciyar hankali? to inaga ai wannan amsar a bayyane take abun dubawa anan da zargi da gori wanne zaki iya jurewa? Kinsan dai mijin farko dole kullum zaiyita zarginki bazai taba sakankancewa dake akan shine kadai ya sanki a matsayin 'ya maceba wannan kuma yana ransa yayinda kema da zaran kin ganshi da wata hankalinki zai kasa kwanciya shikuma miji na biyu kasan cewar yasan abunda ya faru dole kisha gori domin duk lokacinda abu ya hadaku a b kinsan me zai faru ballantana ya auro wata tofa saidai ki tushe kunnenki sai kuma wata tambayar wai mace tana rasa budurcinta ta wata hanya bayan saduwa? Amsa…eh tabbas tana iya rasawa ta hanyar bude kafafunta ko hawa keke da tsalle da sauransu to amma ba daya yake da wanda aka sadu da itaba dalili kuwa anan fatar ce take iya fashewa ko tsagewa amma saduwa fatar tana fashewa sannan kofar ta bude kunga akawai banbanci don kuwa duk yanda mace tayi matukar ba saduwa tayi da namiji ba to babu yanda za'ayi mijinta yayi tunanin wani abu Sai kuma wata tambayar tayaya mace zata gane tana bude? Wannan kuma zamu duba bayanai da masana sukayi akan budurcin mace kamar yanda wani marubuci dan kasar india ke cewa alamomi hudu sune suke nuna gaban mace yana bude koda na miji be sadu da itaba 1 akwai fitar iska me kamada tusa 2 yatsar mace ta tsakiya wato ta kusada manuniya ta shiga gabanta ba tareda taji zafiba 3 mace ta tsuguna babu wando amma taji iska yana shiga 4 mace taga jini tareda zafi kuma ba lokacin al’adaba misali ko tana tsallaka wani abu makamancin haka HANYOYI HUDU DA FATAR GABAN MACE KE FASHEWA Kai tsaye zamu tafi zuwaga magungunanda suke matse gaban mace koda ta bude kai kodama haifuwa tayi kuma zamu fara da maganin bature daga bisani mu tafi izuwa maganin gargajiya YANDA AKE HADA MAGUNGUNAN GARGAJIYA MASU MATSE GABAN MACE gajeriyar hanya ta matse gaban mace gam itace gabaruwa da aloebera Idan kika samu bagaruwa saikiyi garinta shine zaki hada da ruwan aloebera kiyi matsi bayan sa'a daya ki wanke Sannan kisamu kanunfari kizuba agarwashi kiyi tsugo akayi sanna kizama me yawan matsi da miski Wannan kuma ganyen gwaiba mai kyau zaki samu ki wankeshi saiki tafasa sosai saiki zuba acikin wani ma zubi da zaki iya shiga sai kinyi mintuna goma saiki fita sannan kisamu gabaruwa da kimba kadai ki tafasa su sosai kinasha ruwan safe da yamma... Ana iya jika kwaro da man kadanya da ruwan aloebera sai man zogale ana matsi dashi kullum zuwa kwana10 1 alobera (aloevera) 2 Karo (jirai) 3 man zaitun (olive oil) 4 kanunfari (Cloves) ki sami alobera da Karo ki saka kanunfari ki tafasa saiki tace ki ajiye ruwan ya zama shine ruwan tsarkinki idan kuma kinaso kiyi sha yanzu magani yanzu to kin matse ruwan alobera saiki hadashi da man zaitun kiyi matsi dashi gam gam kenan HANYAR MATSI DA ITATUWA dan bagigita/da tsintsiyar maza/da saiwar taba/da sassaken baure da gishirin gallo/sai kanunfari/da kuma goro duk wadannan da kika gani hadasu waje daya akeyi adafasu saisun tafasa saiki tace ruwan Ki ajiyeshi ya zama ruwan tsarkinki shi kuma wannan itatuwan ki ajiyesu domin Zaki iya sake amfani dasu Ko kuma kiyi garinsu madadin goro saiki saka gabaruwa saiki ajiye garin kina zuba cokali daya acikin ruwa kina dafawa kina tsarki kisamu kamar sati daya kinayi SAI KUMA RUMAN Yanda ake matsi da ruman shine zaki samu kwallon mangoro amma dan cikin zaki cire ki shanyashi taredashi bawon ruman bayan sun bushe saiki dakasu ki kwabashi da farar zuma da turaren miski farin kina matsi dashi idan ya jima kadan kamar sa’o.i biyar (5hours) saiki wanke da ruwan *DAGA MASARAUTAR ZAFAFAN KAYAN MATA DA BASU DA ILLA DAGA TAKU MAMAN YUSUP MUNA SIYARDA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU MATUKAR KYAU DA INGANCI SAYEN DAYA KO SARI GAMAI BUKATA ZASU IYA NEMANA TA WANNAN NUMBER 09035027743* AMMA DON ALLAH WADDA BATA SHIRYA SIYA BA KARTA NEMENIπŸ‘πŸ» [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_4 .............da k'yar ya dafa Baffa ya mik'e tsaye , a zuciye ya juya zai Fara tafiya , wata k'ara ya saki jin wani irin ciyo ya ziyarceshi Babu shiri ya koma ya zauna ya na maida numfashi hade da runtse idanunshi, Murmushi Baffa yayi a zuciyarshi Yana cewa too fa Hajar yau kin gamu da gamonki ga Wanda yafiki son d'iya don wannan da alama ko aro bazai iya baki 'yarshi ba, Afili kuwa cewa yayi "kaga bafa zaka iya taka k'afarnan a yanzu ba , saboda dafin yariga da ya shiga jininka sosai doli zaka zauna anan Koda na sati biyu ne ayi maka magani inba haka ba zaka iya samun matsala da k'afar Nan zuwa gaba , macijin da ya sareka yanada matukar had'ari , daga Haka Baffa ya kamashi ya mayar dashi cikin bukkar Nan, Tun yanasa ran za'a kawo mashi Muneeba har ya hakura ,saidai a zuciyarshi wani d'aci yakeji yanajin Kamar yaje ya kama wannan yarinyar yayi Mata shegen dukan tsiya, Tabbas yazama doli yayi nesa da wad'an nan mutanen don bayason suyi rayuwa da kowa a kusa dasu bai yarda da kowa ba don haka bazai zauna da kowa ba , sannan bayason 'yarshi ta shak'u da kowa inba shi ba , shikadai zai kula da tilon 'yarshi wadda ita kadai ta ragemai a rayuwa ita kadai ce danginshi a halin yanzu ,zai zamo Mata uwa Kuma uba a rayuwa Sam bazatayi kukan maraici ba, Haka yayi ta sake sake har bacci yak'ara awon gaba dashi, *********************** *GARIN LAGOS* Motocine guda biyar suke tafiya a jere dukkansu bak'ak'e wulik' , gudu suke Kamar zasu tashi sama , tun suna tafiya cikin gari har suka fara ratsawa cikin dazzuka , a Haka suka rinka gudu sunyi tafiya Mai nisa kamun su yanki wata hanya suka Kara nausawa acikin jejin , Abun mamaki sai gasu agaban wani makeken gida Mai kyaun gaske Wanda kallo Daya zaka mashi kasan cewa naira tayi kuka a wajan ,k'aton get din gidan wani basamuden mutum Kuma k'ak'k'arfa ya bude masu , Wajan da aka tanadar don ajiye motoci sukayi parking, sannan suka firfito, ba k'aramun firgita nayi ba lokacin da nayi arba da wad'an mutanen , kowace mota mutum biyu ne aciki , gaba dayansu sanye suke cikin bak'ak'en Kaya suna sanye da tabarau bak'i Wanda yakusa mamaye Rabin fuskarsu maza TAKWAS ne mata biyu , sai dai ba bambanci tsakanin mazan dakuma matan saboda duk shigarsu iri Daya dai dai da hular da suke sanye da ita iri Daya ce wadda ta kasance Ja , kallo Daya zaka masu kasan cewa Sam Basu had'a hanya da tausayi ba , fuskarsu a had'e take Kamar hadari Wanda kana kallonsu zaka hango tsantsar rashin imani a tattare dasu ,tafiya suka farayi a hankali cikin wani irin salo har suka k'arasa babbar k'ofar da zata sadasu da babban falon gidan,. Wow shine abunda na fada lokacin da nayi arba da wannan had'ad'd'en falon Mai matuk'ar girma da kyau Babu ce kawai Babu a falon, , Basu tsaya anan ba direc suka nufi wani korido sai gasu a wani Dan k'aramun falo Wanda ya tsaru iya tsaruwa don ya doke na farkon a komai, Kujeru ne kusan goma Sha biyu a wajan ,goma suna gefe yayinda aka tsara wajan ko Ina kujera biyu da table a tsakiya , an shak'e table din da kayan ci da Sha kala-kala, sai kujeru biyu a gefe Wanda mutanen ke fuskantarsu , zama sukayi bisa kujerun wasu suka Fara danne-dannen waya yayinda wasu suka bude computer da suke rike da ita suka Fara bincike a ciki, abun mamaki tunda suka fito daga motocinsu har zuwa wannan lokacin ba Wanda yayiwa wani magana acikinsu , Kamar 20mnt sai ga wata makekiyar kofa ta bude ,sai ga wani mutum ya fito Yana sanye da shadda Fara Kal dinkin babbar Riga ya kafa wata bak'ar hula Wanda kana kallo kasan ba k'aramun tsadane da ita ba, mutumin bak'i ne wulik' Yana da manyan ido jajaye yayinda fuskarshi take a had'e Wanda hakan yak'ara fito mashi da ainahin muninshi , Alhaji Saminu Sulaiman kenan Mataimakin gwamna a jahar Lagos , Fitowarshi keda wuya duk mutanen Nan suka mik'e tsaye cikin girmamawa, a tare suka furta welcome sir, gyad'a kanshi yayi a hankali kamun ya nemi waje ya zauna Akan daya daga cikin kujerun Nan biyu da sukayi saura, Zaman suma sukayi suka nutsu don jin abunda shugaban nasu zaice, Gyaran murya yayi a hankali yace , " Ina jinku ya ake ciki, ? duk da shekaranjiya na tsinci labarin da yafi kowane labari a wajena Wanda hakan ba k'aramun sanyani farinciki yayi ba hakika kunyimun abunda naji dadinshi sosai duk da dama can ban taba saku aiki ya gagara ba , Amma duk da Haka inason ji daga gareku, Daya daga cikinsu ne ya Mike Wanda ya kasance shine babbansu gaba Daya Mai suna *big boy* cikin muryarshi Mai kama da injin markad'e yafara magana , yace , "Ai oga yadda kabamu umurni haka muka aiwatar ba tareda tausayi ko Imani ba sannan munyi komai cikin taku bamu bar kowace shaida da zata sa a gane cewa ba gobara ce ta tashi a gidan ba , Saida muka masu hukunci Mai tsanani sannan muka sakar masu gas muka toyesu tass inada tabbacin ko tokarsu baza'a samu ba , yakarasa maganar Yana wata irin dariyar jin dadi, Wata irin dariyar basawa Alhaji Saminu ya fashe da ita wadda kanaji kasan ta mugunta ce yajima Yana babbakata sannan ya shiga yiwa kanshi kirari , Duk Wanda yaci tuwo Dani Miya yasha Saini kurungu mugun dutse Murucin kan dutse nake banfitoba Saida na shirya Nine mugu uban miyagu Yaro yarone baisan wuta ba sai yataka Ta'bani kuwa daidai yake da ta'bo ajalinka .......... Daga Haka Kuma sai yafashe da wani irin kuka Yana fad'in inaaa ban huce ba banajin na huce haushi na sai yaushe ne sai yaushe zanci cewa na huce akan abunda wannan Dan banzar yamun !!!!!! Duk yaran tsuru sukayi suna kallonshi da tsoro. Abunda zai iya aikatawa , suna ganin to miye ya rage Kuma tunda ya dauki fansar shi mafi munin fansa to mikuma zai dameshi , idan bai hak'ura ba to da waye zaiyi tunda Wanda yakeyi dominshi ko 'tokarshi Babu a doron k'asa!! A tsawace yabasu umurnin su 'bace mashi da gani kamun ya tashi ya nufi wani daki gaban wani makeken photo ya tsaya ya tsurawa pic din ido bako k'yaftawa , Su big boy kuwa tashi sukayi suka fita daga falon suka shiga motocinsu sukabar cikin jejin kamar yadda suka shigo, ************************ Zaune take Akan makeken gadonta kanta yana cikin k'afafunta tana sanye da riga da wando masu matuk'ar laushi da tsantsi yayinda sukabi lafiyayen jikinta suka lafe ,kanta Babu dakwali yayinda dogon gashinta da yake harmutse ya sauko saman kafadunta har ya rufe Mata fuska baki daya , Wata yarinya ce da bazata wuce shekara 16 ba ta shigo tana sanye da uniform na Yan aikin gidan ,hannunta rik'e da k'aton tire Wanda ta shak'owa uwar dakinta kalolin abinci akai ,saboda tun kwanaki biyu da suka wuce Bata k'ara Sanya wani Abu a cikinta ba da sunan abinci , A hankali ta taka har inda take cikin tattausan lafazi tace " ranki ya dad'e ga abinci irin Wanda kikeso na girka maki don allah ki daure kici kinga Momy gaba Daya ta d'aga hankalinta saboda halin da kike ciki sannan..... .........hannu ta d'aga Mata kamun ta d'ago da kanta a zafafe cikin ficewar hayyaci idanunta Kamar gauta saboda tsabar ja Kai kace ba a ta'ba hallitar fari acikinsu ba, cikin wata irin tsawa tace " Ina Wasa dake ne ? Ina ruwanki Dani ! Na mutu Mana dame zai shafeki ! Oya maza kibar nan Kuma kar nakara ganin shegun kafafunki anan wajan, inba hakaba wallahi sai na karyasu tayi maganar idonta a juye Kamar wata Yar k'waya , Azabure wannan Yar aikin tabar dakin jikinta har rawa yakeyi tana rayawa aranta lallai abun na madam kullum Kara gaba yake to Allah ya kyauta , (nace Amin dai) Ke Haule ya akayi Bata kar'bi abincin ba ? "Eh hajiya tace karna Kara zuwa inda take inba hakaba zata karyani , Shiru hajiya Aisha tayi da alamar damuwa a fuskarta tace "jeki kawai" Tashi tayi ta tafi dakin yarta *Amna* yadda Haule ta barta Haka Momy ta sameta , zama tayi a gefenta ta dafata tace kinga Amna kiyi hkr ki rungumi kaddara wannan damuwar da kikeyi ba ita zatasa wanda ya mutu ya dawo ba tunda............bige hannun uwar tayi tace "Ni kidaina ta'bani ke ba Momy na bace Sam bakwasona tunda kuka zabi rabani da farincikina , miyasa miyasa Momy ya zakuyi Haka akan son zuciya ??? to inaso kisani daga ke har Dad bazaku sake ganin farincikina ba har abada duk da inaji a jikina Yana raye , tabbas Yana raye...............✍🏼 Tooooo wata sabuwa sukuma wadan nan daga inaπŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€” *Karki wuce baki karantaba kila ki amfana*πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ» MAGANIN NANKARWA Assalamu'alaiki Auntyna barkada war haka Dan Allah ki taimaka min da maganin nankarwa stretch marks Nagode sosai Allah Ya Kara basira Ameen Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi da suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da ciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri wato daga fitowar sa zasu iya bacewa gaba daya amma barin shi ya dade kan hana sa bacewa gaba daye sai dai zai dushe ya zama dan kadan kadan ake iya gani Suna fitowa ne a wurare kamar haka :- Cikin mace daga kasa (mara) Cinya Saman mama Mazauni Saman hannu ta wuraren hammata Da sauran su. ME KE KAWO NANKARWA ? Akwai abubuwa da dama da suke sa nankarwa kamar:- 1-daukan ciki zuwa haihuwa (wannan shine babban abinda ke kawo nankarwa) 2-ramewa tashi daya (ga mutum mai qiba) 3-yin qiba tashi guda (ga mutum mai rana) 4- gado daga mahaifiya 5-jinya na tsawon lokaci 6- damuwa mai yawa da makamantar su MATAKAN NANKARWA Yana da matakai guda uku gasunan kamar haka:- 1) farko fitowar sa zaki gansu sirara yana da pink kala sannan yakan yi kaikayi wannan matakin bashi da wahalar magani 2) zai zama ja ko ruwan bula sannan girman su zai karu yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai iya bacewa ki ya ragu ya danganta da yanayin jikin mutum 3) zai zama fari ko ruwan silva wannan kam yana da matukar wahalan magani sai an jure shims din sai dai ya ragu ba wai ya bace baki daya ba. HANYOYIN MAGANCE NANKARWA Ruwa Ruwa da Kuke gani yafi komai mahimmanci a jikin dan Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun fata kuma da hana wasu cututtuka da dama kama fatar mutum da wuri. MISALIN YANDA ZAKA SHA KOFI 8 ZUWA GOMA ACIKIN KO WACCE RANA -Kofi 2 da zaran kin gama wanke baki da safe. -Kofi daya bayan karin kumallo -kofi Daya Kafin azahar kisha -kofi Daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci. -kofi daya da la'asar. -kofi Daya kafin abincin dare kofidaya bayan kin gama ci. MAN CIKA-GIDA (CASTOR OIL) Wannan man yana da Matukar amfani wajen magungunan da suka shafi fata kamar maganin pimples, cin zanzara, tabbai da sauran su. YANDA AKE AMFANI DASHI Ki dibi kadan sai ki sa a wuta yayi dumi sannan ki shafa a duk inda kika san yana da nankarwa ajikin ki da dumi duminsa ba yanda zai kona ki ba. Kiyi hakan har na tsawo wata guda. Ko kuma ki shafa man sannan ki dauko yadi mai taushi na cotton ki rufe wurin dashi ki Zuba ruwan dumi a gora ki riqa dorawa a saman yadin. ALOE VERA Ki tatse farin ruwan aloe vera kullum ki riqa shafawa a wurin idan ya bushe sosai sai ki wanke da ruwan dumi Ko kuma ki diba man aloe vera din chokali daya ki hada da vitamin E oil capsule daya ki shafa a wurin. FARIN KWAI K fasa Kwai daya ki cire kwaiduwan kwan ki yar sai kiyi amfani da fork ko whisker kiyi ta kada farin kwan har sai yayi kauri ya yi fari tas kamar cream sannan ki shafa a wurin nankarwan ki barshi ya bushe sannan ki wanke da ruwan sanyi kiyi tayin hakan har na tsawon sati biyu. RUWAN LEMON TSAMI ki matse lemun tsami sai ki diba ruwan ki riqa shafawa in circle a inda nankarwan suke har sai kinga ya bushe ki barshi bayan minti goma ki dauraye da ruwan dumi. Ko kuma ki hada ruwan lemun da ruwan nukakken cucumber sannan ki shafa. SUGAR Ki hada suga da almond oil ko zaitun ko man kwakwa da ruwan lemun tsami ki shafa tsawon minti goma sannan ki shiga wanka. RUWAN DANKALI Ki fere dankali sai ki dauki guda daya ki dan jajjaga ki shafa ruwan a inda nankarwan take idan ya bushe zaki ga yayi fari sai ki wanke da ruwan dumi ki shafa zuma ko zaitun ko man kwakwa. MAN KADE yawan shafa man kade a wurin ma yana rage shi sosai. Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zaran sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ce babu kemikal acikin ta dan haka yana daukan lokaci kafin aga canji kamar Sati biyu idan baki ga chanji ba sai ki dauki wani kuma. Allah shine masani. Allah yasa mu dace. A yayin da ta fito, ta kan zamewa mutane karfen kafa domin ta na da wahalar fita. Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba Hanya ta 1: Dankalin hausa Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antioxidant. Haka kuma dankali yana dauke da sinadarin vitamin c, potassium, thiamin, riboflavin, iron, zinc da sauran su. Yanda ake amfani da shi: A yanka Dankali sannan a shafa a hankali a kan nankarwar. Sai a barshi na tsahon mintuna 15 zuwa 20, sannan a wanke da ruwan dumi. A maimaita haka a kullum Hanya ta 2: Aloe Vera Ruwan da ke cikin Aloe vera yana dauke da sinadarin Collagen wanda aka san shi da gyara fatar da ta lalace da kuma kara dankonta, kyanta da kuma yarintar ta. Yanda ake amfani dashi: A karya ichen Aloe vera guda sai a shafa ruwan a kan nankarwa. A barshi tsahon awa 2 zuwa uku sai a wanke da ruwa. A maimata hakan a kullum har sai an samu sakamako mai kyau Hanya ta 3: Man kadanya da Koko butter Hadin Man kadanya da Koko butter yana dauke da sinadarin vitamin E da kuma sinadaran da ke hana fata lalacewa Yanda ake amfani da shi Za’a samu koko butter karamin cokali 2, da man kadanya shima karamin cokali 2, sai sinadarin vitamin E karamin cokali 1. Za’a narka man kadanya da kuma man Koko butter sai a kara vitamin E din a ciki a gauraya. Za’a dura gabadaya a cikin mazubi a ajiye a na shafawa a kan nankarwar kullum. Hanya ta 4: Lemon tsami Acid din dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen warkar da ciwo, kurajen fuska da kuma nankarwa. Yanda ke amfani da shi: A yanka Lemon tsami gida 2 sai a shafa shi a gurin da nankarwar take. A barshi na tsahon mintuna goma sai a wanke da ruwan dumi. Ko kuma a hada ruwan Lemon tsamin da ruwan kokwamba a shafa a wajen. A yi hakan a kullum idan ana san samun sakamako mai kyau Hanya ta 5: Man zaitun Man zaitun yana dauke da sinadaran vitamin A da E wanda suke kara gudun jini zuwa karkashin fata da kuma kara laushin jiki. Suna kuma hana lalacewar fata. Yanda ake amfani dashi: A dan dumama Man zaitun a wuta, kar yayi zafi da yawa yanda zai kona fata. Sai a shafa a gurin da nankarwar ta ke. A yi hakan da safe da yamma a kullum. *Daga taku har kullum mmn Yusuf Mai kayan Mata*😍😍😍😍😍😍 [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_6 ............"Alhajifa akwai matsala wallahi gaba daya narasa gane kan yarinyar nan , yanzu fa kwana ukku kenan ko ruwa bata sha ba numfashima nema yake ya gagareta , tayi maganar tana zubar da hawaye "..... Zaune yake akan kujera gaba daya Ya had'a d'an k'aramun gajimare a wajan ,saboda tabar da yake ta zuk'a tun d'azu tada k'are zai kunna wata, ita kanta momy dauriya kawai takeyi amma gaba daya hayak'in ya dameta, ganin duk maganar da take bai kulataba yasa ta fashe da kuka tana cewa, "Haba alhaji kanajina fa amma kayi shiru yarinyar nan ita kad'ai muke da ita a yanzu zamu iya rasata a kowane lokaci sannan.......... "Wata uwar tsawa ya daka mata wadda saida ta zabura , idanunshi da suka rine sukayi jajir ya zubamata yana mata wani shegen kallo na nuna tsantsar takaincinshi akanta, "Waini Hindatu mi kikeso namaki ne da kike zancan Amna, ta mutu mana , d'ana mafi soyuwa a gareni ya mutu ma na hakura bare wata Amna , kina ganin saboda wani banzan bori nata zan kasa aikata abunda ya dace ne wallahi koke da kika haifi Zayyan kika mashi irin wannan abun irin hukuncin da zan maki kenan bare wasu banzaye , In taga dama ta ware in bata ganiba kanta , ba wanda zai mutu a yanzu ya dameni tunda har narasa Zayyan yayi maganar wasu zafafan hawaye na sauko mashi ," a zuciye ya tashi ya shige bedroom dinshi , yana shiga dakin ya zubawa wani makeken photon wani kyakyawan saurayi ido , saurayin yana sanye da k'ananan kaya irin masu matse mutum din nan , ya kafa wata shegiyar hula irin ta gayu yayinda ya zazzago wandonshi k'asa sosai irin dai wanda gayu ke yayi , wuyanshi sanye da sarkar gold hakan ma kunneshi manne da dan kunne irin wanda gayu maza ke sawa sai katon galss din da yakusa mamaye Rabin fuskarshi , photon kato ne kamar ka kira shi ya amsa , akalla sai da ya shafe awa daya a wajan yana kallon hoton tareda cin burika kala kala gefe daya kuma hawayene ke mashi zuba kamar anbude famfo, Tashi momy tayi dakyar tabar falon zuciyarta kamar zata fashe yanzu in tarasa Amna ya zatayi da rayuwarta, su biyu kawai take dasu a duniya gashi ta rasa babban d'anta a sakamakon azzalumin mijinta wanda baisan komaiba sai zalunci , yanzu kuma ga halin da tilon 'yarta take ciki wanda batajin zata ta'ba yafe masa matuk'ar ta rasata, dakin Amna ta nufa yadda ta barta haka ta sameta , tana kwance tazubama silin ido yayinda hawaye ke mata zuba ga kuma numfashinta da yake sama da k'asa kamar zata shid'e Zama tayi kusa da ita ta dafa kanta tace , "Kiyi hakuri Amna ki kwantar da hankakinki insha Allah ko zan rasa raina sai sama maki farinkinki , nasan bamu kyauta ba ,munbi son zuciya gashi reshe ya juye da mujiya inason ki kwantar da hankalinki insha Allah zamu samu mafita don inaji ajikina nima yana raye kamar yadda kike fad'a," A hankali ta d'ago da kanta takalli momy tace "kinyi alk'awari momy??" "Eh Amna namaki Alkawari don nagane ubanki bashida imani bashida tausayi to daga yau na dawo daga rakkiyarshi , zan tayaki bincike har allah yasa mudace ," Cikin matukar murna da farinciki Amna takama hannuwan momy ta rik'e gam tana zubar da hawaye yayinda fuskarta ke dauke da murmushin jin dadi , saidai takasa cewa komai don sam batada kuzarin da zata iya wata magana, DA haka mommy tasamu ta lalla'bata ta yarda zata kaita asibiti, jikin momy har rawa yakeyi ta dauko wayarta takira daya daga cikin direbobin gidan don yazo ya kaisu asibiti, haka kuwa akayi wata tsadaddiyar asibiti sukaje inda dama acan suke zuwa , Ba 'bata lokaci ba likitoci suka rufu akanta tunda dama sun santa ,bayan sungama dubata sunmata duk abunda ya dacene suka bata gado suka daura mata drip da allurai sannan suka tafi ba a dauki lokaciba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita saboda alluran da akamata bayan sun gano bata samu isashen bacci, Momy kuwa tana zaune tazuba mata ido tana kallonta yayinda zuciyarta ke tuhumarta akan alkawarin da tayiwa yar tata ta ina zata samu wanda yariga da ya mutu????πŸ€” ************************* A hankali ya furta "to shikenan Baffah nagode sosai Allah yasa hakan shine alkairi, Allah kuma yasaka maku da mafificin alkhairi, Cike da farinciki Baffah yace "Amin amin Hisham naji dadin amincewarka , Allah yagani inajinka kamar d'an uwana , ina jin tausayinka sosai ganin irin halin da kake ciki duk da bansan abunda yake damunka ba amma nasan ba k'aramun abu bane zai raboka da gida da wannan jaririyar , bazan matsamaka don ka gayamun damuwarka ba Duk da inason jin damuwar taka, amma Duk lokacin da kaga yakamata ka sanar dani to ina maraba watak'ila bazan rasa taimakon da zan maka ba, Yanzu zan tafi daji akwai magungunan da nakeson debowa zansa Habu da halliru su hada maka taka bukkar anan filin dake waje, "To shikenan Baffah nagode sosai , " Nan Baffah yamasu sallama ya fita , Inna dai na gefe tana wanki tana kuma sauraron maganar da sukeyi , itadai batajin dadin wannan hukunci na Baffah ba don wannan mutumin da gani zaiyi wuyar zama gashi kullum cikin muzurai kamar zaici babu , ita kam harga Allah tsoronshi takeji, sai dai fa itama tana son wannan 'yar tashi yara na burgeta sosai kasancewar tajima rabonta da haiguwa tun daga Hajar gashi har Hajar ta girma, Shikam tuni ya lula duniyar tunani , yanajin zazzak'ar muryarta na dawo mashi cikin kunne , *" aa Hisham barin wannan aikin zaifi zama alkhairi a garemu saboda zaka iya sanya 'yan k'asa a cikin farinciki amma bazaka iya sanya ahalinka ba , zaka iya bada kariya ga mutanen k'asar nan amma bazaka iya bada kariya ga ahalinka ba Hisham* Dariyar da Muneeba da hajar ke k'yalkyatawa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yashiga , a hankali ya dago da idonshi da suke fitar da wani irin yaji saboda tananin 'bacin rai ya zuba masu, Ido hudu sukayi da Hajar aikuwa tuni tasha jinin jikinta nan da nan jikinta yafara rawa ganin wani birkitaccen kallo da yake mata, a hankali cikin tsoro tafara daga k'afarta tana nufar inda yake zaune , Har k'asa ta duk'a cikin rawar murya tace *"sannu Hamma* baice mata komai ba sai kallonta da yakeyi , Wasu yawu ta had'iye duk a zataonta fushinsa akanta ne a hankali ta ajiye muneeba a kusa dashi tace "gata Hamma dama najene na nunawa k'awayena 'ya ta" to to to shine yanzu nace bari na kawo maka ita ,tayi maganar.a tsorace sai faman k'yafk'yafta mayan idaunta masu kamar madara take, Kallon mamaki yamata ,yana mamkin karfin halinta wai 'yar ta , bai kulata ba ya dauki muneeba ya tashi da kyar yanufi waje da ita, Kamar wata zararra haka ta tashi tabi bayanshi cikin in ina tace Ham..mah..ina zakaje da ..ita,? Juyowa yayi ya kalleta da rinannun idanunshi wanda babu shiri taja baya a tsorace ,baice mata komai ba yajuya yayi tafiyarshi, zata koma binshi taji an rik'e mata hannu, juyowa tayi don ganin wanda ya rik'eta , ganin Inna tayi ranta a 'bace cikin harshen fillanci tace , "Wai ke hajar miyasa bakida hankali ne , ina ruwanki da inda zai kaita yarki ce ko yarshi , kincika shishigi wallahi ina jiye maki ranar da zai gaji da halinki don wannan da ganinshi bashida sauk'i ," "nidai innarmu ki bari nadubashi kar ya gudu da yarinyar " tayi maganar kamar zata fashe da kuka, Cikin takaici inna tace to wallahi ba inda zakije maza ki koma ki zauna Allah yasama yayi tafiyar tashi inga yadda zakiyi, Haka Hajar ta juya ta koma tana hawaye don gani take kamar Hisham dauke mata yarta zaiyi ya gudu (karfin hali 'barawo da sallama🀣) Hisham kam can karkashin Wata babbar bishiyar gamji ya samu waje ya zauna yana yiwa 'yarshi wasa ganin yadda take dariya kadai ya sanyashi farinciki kadan kadan yakejin nauyin da zuciyarshi tayi mashi yana raguwa wannan dalilin yasa sam bayason yayi nesa da yar tashi ,don kallonta ne kadai ke sanyaya zuciyarshi a yanzu, yajima sosai a wajan kamun yakoma gidan Baffa wanda zuwa lokacin Hajar kuka take sosai gashi Inna ta hanata fita ,aikuwa tanajin sallamarshi Ta kwasa a guje taje ta babbanbare muneeba a jikinshi wadda tajima dayin bacci , bata ko kalleshiba ta shige cikin bukkarsu da munneba , πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈdafe kanshi yayi irin ta dameshi din nan kamun yayi tsaki ya gayar da Inna sannan ya shige cikin bukkar Baffa wanda anan ne suka saukeshi. *Washe gari* Kamar yadda Baffa yace haka akayi Habu da Halliru harma da wasu daga cikn abokansu sani da sule suka had'a ma Hisham yar bukkarshi , acan filin dake bayansu kadan , bukkar ba a cikin gidan take ba hasalima akwai yar tazara tsakanin gidan na Baffah da inda bukkar shi take saidai suna hangen juna kasancewar wajan filine fetal, Bayan sun gama komai ne suka sanya mashi gadon kara aciki sannan suka kwashe yan kayanshi suka kai mashi can tare da tarkacen maganinshi da yakesha , Inna kuma tabada wani zanen sak'i suka sanya mashi abakin k'ofa akayi labule dashi, Bayan dawowar Baffa yaduba aikin yaga sunyi komai yadda ya kamata ,sai ya umurci Hisham da ya dawo nan da zama, Sam Hisham bai yarda yabar 'yarshi ba tare da ita ya koma bukkar , Kwance yake akan gadon karan dake bukkar yana k'arama wajan kallo wasu hawaye masu zafi suka zubomashi yayinda gefe daya kuma yake murmushi wanda har saida gefen kumatunsa suka lotsa , mamaki yakeyi wai yau shine acikin irin wannan wajan a matsayin humallinshi lallai duk wanda baiji tsoron Allah ba yayi aikin Banza , ko a mafarki bai ta'ba tunanin yin wannan rayuwarba , lallai Allah mai hikima ne Allah ne kadai yasan abunda yake nufi da hakan , fatanshi daya Allah ya kare mashi 'yarshi daga idanun mak'iya masu son ganin bayanta, haka yayi ta tunane tunanen rayuwa da irin sauyin da tazo mashi dashi cikin k'ank'anin lokaci, ya rasa komai ya rasa kowa , Sannu a hankali rayuwa tana tafiya komai yana sauyawa , yanzu Hisham. watansa Ukku a garin su Hajar tuni yaji saukin k'afarshi Muneeba kuma tak'ara wayo sosai yanzu watanta shida har tana rarrafe , kuma har wannan lokacin Inna ke kula da duk wasu hidindinmunta iyakar Hisham agyarata a kawo mashi a wajanshi take wuni amma a wajan inna take kwana tun bayaso har doli ya hak'ura , don ko bai kaitaba sai wannan mayyar ta faki idonshi ta lalla'bo ta d'auketa ,...................✍🏼 *Pls ina bukatar comment inkuma book din baya maku dadine ku fada sa a sauya da wani amma rashin comment zai iya zama sanadin rashin post akan lkc* *karki wuce baki karantaba*πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ» πŸ…±οΈabu sama da yajin 'ya'yan citta a duk wani yajin maza da ake da 'ya'yan itatuwa, yanda yajin keda zafi haka namiji keda zunzurutun zafin sha'awa da jurewa saduwa na tsawon lokaci me yawa, haka zalika yajin 'ya'yan citta shine hade da itatuwan gargajiya mafi girma amaganin maza a kasar hausa wanda dai ake kira yaji, shine kuma ake kira (ginger seed) ku bincikashi, mun taba kawo muku abaya, anasha da shayi babu madara sannan kuma anasha lokacinda ake gida kamar bayan magriba, sannan yanda ake shansa kuma rabin cokali babba, bayan haka kuma koda mutum bayada aure zai iyasha, amma mazane zallah banda mata. πŸ…°οΈana samun garin 'ya'yan citta, da dan kamaru, sai ginsine, da kwallon dabino, sai namijin goro, da farin gagai, sassaken marke, wadannan ana hadasu waje daya ayi garinsu, sai a tankade sosai shikenan an kammala hadashi, [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_5 ...........Kamar a mafarki yafara jin kukan Muneeba, da hanzari ya bude idonshi sannan ya tashi tsaye da k'yar , a Haka ya fito tsakar gidan yanajin kukanta har tsakkiyar zuciyarshi, ji yake kamar yaje ya shak'e wannan yarinyar Mai shegen shishshigin tsiya, Truss yaja tsaya ganin Muneeba a hannun Inna tana Mata wanka Wanda akanshi ne take kukan , ajiyar zuciya ya sauke don harga Allah yaji dadin ganin Inna nayiwa Yar lelen tashi wanka , zamewa yayi a wajan ya zauna a hankali Yana sauke ajiyar zuciya , ido ya zuba masu har Inna tagama Yi Mata wankan sannan ta dauko madarar Shanu Mai dumi tafara Bata , Tasha sosai sannan ta dauko man shanu ta shafa Mata a matsayin mai, jakar dake kusa da ita ta bude wadda ta kasance ta Hisham ce ta dauko Mata wasu riga da wando masu kauri ta Sanya mata sai ga Muneeba ta lafe ajikin Inna tana ajiyar zuciya tare bingirewa da dariya , Kallonsu kawai yakeyi cike da jin dadin ganin yarshi cikin farinciki, yanaso yace Inna tabashi ita Amma bakinshi yamashi nauyi , yanajin tunda wannan bala'in yafaru dasu maganarshi k'ayadadda ce Sam bayason yin magana ko Yaya ne , Sam Inna tabasan da zamanshi ba a wajan , Saida ta juyo sukayi ido hudu, Saida gaban Inna ya fad'i don harga Allah tsoron mutumin nan takeji , saidai ganin yau fuskarshi da d'an sassauci yasa tayi k'arfin halin cewa , "Akawo maka yarinyar ne "? Kamar jira yake yace "eh" a hankali, Inna zata tashi sukaga ta shigo Kamar an harbo kibiya , bata tsaya ko inaba sai inda Inna take , jikinta har rawa yake ta kar'bi Muneeba, sai washe baki take ganin yadda kayan suka k'ara fitowa da kyaun yarinyar, a hankali ta ce Mata " *Bingel'am* sunan da take fadama Muneeba kenan , Inna dai sororo tayi tana kallonta kamun cikin harshen fillanci tace "je ki kaita wajan Babanta , ...... Kamun ma Inna ta rufe bakinta Hajar takai bak'in kofa tana Shirin fita take cewa bari nazo innata Zan nunawa kawayena ita ne, Kasancewar duk da harshen fillanci sukayi magana yasa Hisham bai fahimci abunda suke cewa ba , Amma fa yacika yayi fam Kamar zai fashe idanunshi sun k'ank'ance tsabar bala'i sai huci yakeyi , Yana ganin yarinyar nan tayi bala'in Raina mashi hankali , to zaibar gidan nasu a yau din inyaso yaga ta inda zata sake ganin Muneeba ,wannan wace irin jaraba ce shida 'yarshi Amma ana Raina mashi hankali yakula kan yarinyar na rawa in batayi hankaliba sai yayi Mata saiti, Tashi yayi da k'yar Yana taka k'afar a hankali yabi bayanta , Inna kuwa ganin yanayinshi yasa takasa Yi mashi magana don ita harga Allah tsoro yake ba , azuciyarta kuwa sai Allah Allah take kar yaje ya halaka Mata yarinya a banza don ta kula Sam baisan Kara ba , Ina laifin Hajar don tanuna k'aunarta ga 'yarshi , d'an tsaki tayi sannan ta tashi tafara ayukkanta duk da a k'asan ranta tunani take yadda za a kwashi Yan kallo tsakaninshi da Hajar , don tafi kowa sanin yarta da rigima akan yaran mutane , Duban duniya yayi Amma ko Mai kama da Hajar baigani ba , Kamar walk'iya ta 'bace mashi , dafe kanshi yayi cikin tsananin 'bacin Rai Nan take kanshi yafara ciyo Babu shiri ya Zame a wajan da yake ya zauna,Yana dafe da kanshi , jira kawai yake yaga ta inda wannan jarababbiyar yarinyar zata 'bullo ya kar'bi "yarsa ya k'ara gaba , Yajima awajan Amma shiru ba Hajar ba labarinta , a Haka Baffa yazo ya sameshi , da sauri ya k'arasa kusa dashi Yana cewa " lafiya dai yaro mi kake anan "? "Ba komai " yace da Baffah cikin hade gira don Sam baiso tsohon ya riskeshi ba yaso wannan yar banzar ta kawo mashi yarshi ya k'ara gaba , don yanajin nauyin Baffah sosai bazai iya tafiya a gabanshi ba , Kamashi Baffa yayi a hankali suka koma cikin gida , zaunar dashi yayi a tsakar gidan bisa wundi shima ya zauna Yana fuskantarshi, tuni Baffah ya karanci damuwarshi , yasan damuwarshi Bata wuce ta wannan yarinyar ko 'yarshi ce ko Kuma kanwarshi ce Allah masani, Amma dai kallo Daya zaka masu kaga tsantsar kamar da sukeyi da juna, "Ina son ka gayamun sunaka, Baffa ya fad'a yana kallonshi, "Sunana Hisham" "To malam Hisham inason ka daukeni a matsayin mahafi ko wani abokin shawara ,in bazan takuraka ba ko Zan iya sanin abunda ya faru daku da rahuwarku,? Saboda na fuskanci kana cikin tsananin damuwa tareda k'unar zuciya , Ina kallon tsantsar tashin hankali da son cigaba da rayuwa acikin k'wayar idanunka , to koma dai minene Ni wannan yarinyar ita nake tausayi bansan abunda ya raboku da garinkuba kuka zo Nan Amma tabbas akwai matsala don zakasa rayuwar wannan yarinyar a garari , duk da bansan ya take a wajanka ba Amma dai kallo Daya na Mata nasan cewa jininka ce ,to Amma abun tambaya anan shine *Ina mahaifiyarta take*?? Mi ya faru dakai da har ka dauko wannan jinjirar ka rabota da mahaifiyarta, kayi hkr in na fada maka abunda baimaka dadi ba ,Sam banso shiga sabgarka ba to Amma abun Yana dauremun Kai kullum tambaya anan shine to ina mahaifiyar yarinyar nan take Tunda Baffah yafara magana ya sunkuyar da kanshi tuni idonshi suka yi jajir yayinda jijiyoyin jikinshi dana kanshi suka tashi har wani rawa rawa naman fuskarshi keyi tsabar bacin rai tare da k'unar da yakeji a zuciyarshi , A hankali ya d'ago da kanshi ya dubi Baffa cikin wani irin yanayi yace, "Kayi hak'uri , kuma yau zamu tafi naji sauk'i" Zuba mashi ido Baffah yayi yana nazarinshi , haka kawai yakeji k'aunar yaron tareda tausayinshi , yasan koma minene ya raboshi da gida to ba k'aramun abu bane, nisawa Baffah yayi yace, "Ka gayamun abu d'aya , shine inason insan matsayin wannan yarinyar a wajanka " " *'ya ta ce Baffah"* a hankali kamar mai koyon magana ya fada kanshi a k'asa " to shikenan Allah ya rayata akan sunna yayiwa rayuwarta albarka a hankali ya furta "amin" tareda jin wata irin soyayyar dattijon, Shirune ya ratsa wajan na dan wani lokaci kamun Baffah ya nisa yace , "Amma miyasa kakeso tafiya ne , ko akwai inda zakaje ? Sannan har yanzu baka gama warkewa gaba daya ba ko akwai abunda ake maka wanda bakajin dadi ne anan, ? "Aa Baffah Kawai dai inason tafiya ne" "To akwai inda ka nufa ne daga nan?" A hankaki ya girgiza kanshi Ajiyar zuciya Baffa ya sauke cike da tausayin wannan bawan Allah yace , " ina neman alfarmar da ka zauna anan na d'an wani lokaci saboda yarinyar nan karkayi sanadin rasa rayuwarta, in ka nausa wannan jejin bakasan iya inda zai kaika ba , jejine mai matukar girma da fadi da babu kamarshi anan Nigeria Sannan dajine da yake da matuk'ar had'ari mu kanmu ba abanza muke zaune anan ba , duk dama kowane lokaci zamu iyayin hijira daga wannan nahiyar zuwa wata nahiyar kasancewarmu fulanin yawo bamuda takamammen wajan zama , Yanzu lokacin da macijin ya sareka itama k'iris ya rage ya sareta Allah ya kawo Hajar ita ce ta kashe macijin kaga da bamusan abunda zai faru ba karkaci gaba da tafiya a haka kar kasamu kanka a inda bazaka iya kare kanka ba ma bare kuma wannan yarinyar, Ina Neman alfarmar ka zauna anan na wani lokaci har yarinyarka ta k'ara wayo kaga a yanzu bata shan komai sai madara , zaka wahalar da rayuwarta in kaci gaba da tafiya da ita a haka koma ka rasata baki d'aya tunda bata iyacin komaiba , Akwai fili anan bayan gidan nan zansa amaka bukka anan saiku zauna , kamun muga abunda Allah zaiyi , don Allah karkacemun aa, **************************** Tafiya take cikin sauri tana waiwaye tana sanye da bak'ar abaya da bak'i hijab fuskarta sanye da nik'ab yayinda hannayenta da kafafunta ke sanye da safa , abakin wani dan madaidaicin gida ta tsaya tareda ciro wayarta ta kira matar gidan , ba a jimaba kuwa aka bud'e mata k'ofar ta shiga, Matar gidan na gaba itakuma tana bayanta har suka k'arasa falon gidan , zama sukayi akan kujerun dake falon , Sauke ajiyar zuciya matar tayi tareda cewa "wash Allah yau na gaji da yawa wallahi ,tayi maganar tana cire nik'abin fuskarta, Hmmmm aike kikaji zaki iya ,wallahi Asmy yakamata ki rabu da wannan cess din hakanan tun kema ba a sanwaltar da rayuwarki ba , mutumin nan dai ko k'anen ubanki ne yakamata ace kin shafawa kanki lafiya hakanan tunda abun yafi karfinki, Ta shi wadda aka kira da Asmy tayi tsaye ta cire hijab tareda abayar dake kijinta abun mamaki sai ga kayan *'yan sanda* sun bayyana ajikinta, firij ta nufa ta dauko lemu ta bude murfin ta kafa kanta ta shanyeshi tass sannan tayi jifa da goran , jakar da tashigo da ita ta dauko ta bude ta fito da laptop ta bude tafara danne-danne aciki , Tsakin maigidan tayi tace kefa tsiyata dake kenan tsabar iskanci mutum yana maki magana zakiyi banza dashi, Nisawa Asmy tayi tace "Hmmm Humaira bazaki gane bane , saifa nasan yadda akayi *yalla'bai* ya rasa ransa tabbas bazan saurara ba har sai nasamu gaskiyar abunda nakeson na sani koda kuwa nima zan rasa raina ne, "Abunda nake nuna maki Asmy bakida k'arfi da ikon da zakija da mutanen nan , bance karkiyi bincikeba amma tunda kin gano abun yafi karfinki to yakamata kibarwa Allah komai tunda bazaki iya komai ba , " "Aa Humaira zan jajirce inaji a jikina zanyi nasara , idan har dukkanmu zamuja bakinmu muyi shiru to tabbas bamuyiwa yallabai adalci ba , mutum jajirtacce mai aiki da dukkan gaskiya da rikon amana wanda samun irinshi yanada matukar wahala a yanzu , mutum ne da bashida tsoro ko kad'an wannan yasa ya jajirce don ganin mutane sun samu zaman lafiya wanda alokacinsa ne duk wani tantiri ya shafawa kansa lafiya , amma yanzu kiduba kika cikin lokaci kankani abubuwa da yawa sun canza yanayin tsaro da doka dakomai ya canza , tabbas munyi rashin *Jami'i* na kwarai 😒tayi maganar cike da damuwa da bakinciki, Wayarta ta dauko takira wata number , hello Jabir ya ake ciki,? Daga can 'bangaren Ya amsa da cewa , "Madam har yanzu ina kan bincike amma har yau bansamu wata alama da zata warwarema zare da abawa ba, " Dan Jimm tayi sannan tace " to shikenan kaci gaba da sa ido sannan ban yarda da kowa ba duk abunda zakayi kayi acikin sirri," "To shikenan Madam ko mi ake ciki zan kiraki, "Aa Jabir ban yarda da kira ba ni zan kiraka in bukatar hakan ta taso " "Yes ma" Daga haka sukayi sallama itakuma taci gaba da dannar laptop dinta, ************************** Innalillahi wa inna ilaihin raji'un don Allah Malam ka cire damuwar mariya a ranka Shin da wanne kakeson muji da rashin mariya ko da wannan ciyon da yake damunka , sanin kankane wanda ya mutu bazai dawo ba zaluncine anriga an zaluncemu ba abunda muka iya saidai mu barwa Allah, Tari yake sosai da kyar yasamu ya lafa mashi , yana sauke numfashi ,gefenshi kuma sulaiman ne da Hadiza sai shemau wadda itace k'arama a gidan , Cikin galabaita yafara magana yana cewa " doli in damu Inno sun cuceni sun kashemun 'yata da banida kamarta sun rabani da farincikina ,yarinya mai nutsuwa da ladabi da biyayya , mutuwarta ba shine abunda yake tayarmun da hankali ba kamar sanadin mutuwar tata , saboda zalunci suka rink'a yi mata *fyade* har sukayi ajalinta wannan wane irin rashin imani ne, bazan ta'ba yafe masu ba , kullum burinta tayi karatu mai zurfi amma yanzu sunyi sanadin mutuwarta ba tareda ta cika burinta ba ya karashe maganar yana zubar da hawaye duka yaran kuka sukeyi to bare kuma inno , Tunda suka rasa mariya sukayi k'aura da farinciki duk da ba mutuwar ke k'ona masu raiba sai sanadin mutuwar,............✍🏼 *Rashin comment dinku zaisa in ajiye book din nan gsky bana bukatar stecker ko tnx comment kawai nakeso inba hakaba zan ajiye don inada aikinyi zanbata awa ukku ko hudu inyi typing amma bazaku iya bata minti biyar ba kuyi mun comment*πŸ€”πŸ€”πŸ€” *KI KARANTA ZAKI KARU SIRRIN HUNTU KO NACE GONGOLI* πŸ…±οΈabbar ciyawar maganin gargajiya daga yankin kudu masu yamma na yankin afurka musamman kasashen renon kasar faransa, haka zalika wannan magani daya shahara a kowanne fanni musamman wajen tsaftace gaban mace kamar mejego wanda take bukatar kamshin gaba idan kuma matsi akeso ana hadashi da gabaruwa da saiwar kalgo ana tafasawa ana zama acikin ruwan, wannan ya inganta a bangaren maganin gargajiya tun ba yauba, asalin sunansa kuma da yaren faransa GONGOLI πŸ…±οΈayanin yanda yake warkarda cututtukan gaban mace kuma ana aiki dashi da lemon tsami da ganyen gwaiba shine ake jikasu su jika sosai ana tsarki da ruwan, baya bari wata cuta ta shiga gaban mace, wannan koda mace tanada abokan zama masu daukeda ciwon sanyi bazai shiga jikintaba domin akwai babbar garkuwa a tattare da wadannan magungunan wanda haryanzu an tabbatar basu da wani illah ga lafiya matukar aka kiyaye aiki dasu, πŸ…±οΈangaren shahara da yayi kuma a yanzu ya zagaya duniya ta yanda wadanda basu dashi ayanzu ya iskesu, harma yanzu ana amfani dashi kadai dinsa ta hanyar jikashi da ruwa anasha domin riga kafin kamuwa da cututtuka maza harda mata πŸ…±οΈayan wannan ana hada maganin samun ni,ima dashi, da wanke mara yanda ake ana tafasa shi da zobo da kanunfari idan ya tafasa atace ruwan asaka Zuma ko mazar kwaila anasha. *KU TAYA YARONA ASLAM DA ADDU'A YAU YA K'ONE DA RUWAN ZAFI*😭😭😭😭😭😭😭😭 [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ https://chat.whatsapp.com/J1pyWjlxrS74JrGU3faQE7 *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_7 ...................da k'yar suka samu tarin ya lafa mashi , ruwa yaya sulaiman ya d'auko ya bashi ya sha sannan ya d'auko magungunan shi yabashi ya sha , da yake akwai mai sa bacci aciki baijima bacci yayi awon gaba dashi , Ajiyar zuciya suka sauke dukkansu yayinda suka tsurawa Baban nasu idanu kowanensu zuciyarshi kamar zata fashe saboda k'uncin da suke ji a zukatan nasu, Baba Inno tana daga gefe ta zuba uban tagumi cikin matukar damuwa , tarasa yadda zatayi da malam don ganin ya cire wannan damuwar a ranshi amma abun ya faskara , tanajin tsoron ta koma rasa mijinta bayan rashin 'yarta da tayi, saboda abun ya ta'ba malam sosai fiye da tunani gashi har damuwar tana barazana ga lafiyar shi, Tashi Hadiza tayi tafara yan aikace aikacen gidan inda tayi shara sannan ta dora masu girki ,shama'u kuma ta had'a kwanikansu tafara wanke wa , yayinda yaya sulaiman ya tashi ya fita shagonshi , Sulaiman yana sana'ar dinkin tela Kuma Alhamdulillah yana samun abunda yarufawa kansu asiri dashi don shi yake dauke da nauyin gidan gaba daya , rashin lafiyar Baba ne yasa yanzu yarage fita shago saboda shi yake kula da Baban don jikin nashi yy tsanani sosai, ........................................... "Hello Alhaji " " Wai kina ina ne tun d'azu ina nemanki " "Alhaji muna asibiti fa" "Ke da wa kenan"? Wasu yawu ta had'iye kamun cikin rawar murya tace "Alhaji Amna na kawo fa ,na gayamaka jikinta yayi tsanani sosai" "Da izinin wa kika fita " "Haba Alhaji wai mi kakeyi hakane , *Amna* fa nake gayamaka batada lafiya , ya kake abu kamar wanda baya cikin hayyacinshi , to ina asibiti kuma Ni zan tsayawa 'yata har tasamu lafiya , " tana gama fadin hakan ta kashe wayarta ranta na k'una , tunani take anya mutuwar Zayyan bata taΙ“a kwakwalwar mijin nata ba kuwa , duk irin tsananin son da yakewa Amna yau itace kwance rai a hannun Allah amma ko a jikinshi, ....... Alhaji Saminu sulaiman kuwa k'asak'e yayi yana kallon wayar , shi Hindatu ta kashewa waya ,lallai ta aikata babban kuskure kuwa ,daga haka ya fito daga Ι“angaren yanufi harabar gidan , yana fita securityn shi suka taso aguje suka bude mashi mota shiga yayi gidan baya yayinda suma suka shiga motocinsu suka bar gidan aguje, ........................................... Zaune yake cikin wani k'asurgumin daji ,dajine mai yawan yalwan tsaunika wanda suka k'awata wajan yayinda suka yiwa wajan wata irin rumfa mai ban sha'awa ga iska mai matuk'ar dad'i na kadawa , Zaune yake yayi tagumi yanajin wani irin rad'ad'i na zaga karkashin zuciyarshi abubuwa da yawa na dawo mashi acikin kanshi banda burin daukar fansa ba abinda yake cikin zuciyarshi, kamar daga sama ya hangeta tana nufo inda yake ,kallo Daya zaka Mata ka hango tsananin damuwa da tsananin tausayinshi aciki idanunta, Da sauri ya mike tsaye yana zaro idanunshi yayinda yake nunata da yatsa a hankali ya furta *Momma* Murmushinta Mai kyau tayi mashi kamun ta kira sunan da take kiranshi dashi tace *"shalele* " Da sauri yayi nufin d'aga k'afarshi don zuwa inda take amma abun mamaki sai yakasa koda motsi ne haka ya zuba mata idanu yanason yin magana amma yakasa , A hankali tafara magana tana cewa " kayi hakuri Hisham kayi hakuri Allah yana son masu hakuri kuma yana tare da masu hakuri, kabarwa Allah dukkanin al'amarinka shi zai maka sakayya , amma inason kacire burin daukar fansa aranka , ka kula da 'yarka ka kula da 'yarka ka kula da 'yarka.......daga haka tafara ja da baya tana murmushi tare da daga mashi hannu , Yanason yy magana amma yakasa yanason yabi bayanta kar ta koma 'bace mashi amma yakasa yanaji yana gani har ya daina hangota yayinda idanunshi ke zubar da hawayen bakinciki, ..... Kamar an sakar mashi baki haka yaji a firgice ya kwala kiran sunanta "Mommaaaaaa" Afirgice ya farka daga dogon bacci da yakeyi , tuni ya had'a zufa sai maida numfashi yake kamar wanda yayi gudu yajima a haka har yadan yara samun nutuwa a zuciyarshi , Yau kwana hudu kenan da yake irin wannan mafarkin , tabbas yazama doli ya kauda idonshi daga mak'iyan shi ya hakura da daukar fansar , duk da kuwa bashida wani buri da yawuce hakan , zai nisanta kanshi da duk wani abun da zai sa ya tuna baya zai dauki yarshi ya nisanta ta da mak'iyanshi, wad'an da yasan cewa matuk'ar suka san cewa Muneeba tana raye to tabbas zasuyi k'ok'arin ganin bayanta , zai tsaya mata zai inganta rayuwarta zai k'yalesu badon yana tsoronsu ba sai don ganin ya tseratar da rayuwar gudan jininshi, yajima a haka yana sak'a da warwara yayinda wani irin fushi mai tsanani ya bayyana akan fuskarshi yayinda manyan idonshi suka k'ank'ance suka shige ciki sosai jijiyoyin kanshi suka tashi yayinda mak'ogoronshi ke kaiwa da komowa yana had'iyar wasu yawu masu matuk'ar d'aci , yanajin numfashi shi nayin sama sosai a hankali bakinshi ya bude yafara karanta _innalillahi wa Inna ilaihin raji'un_ ya dauki akalla 30mnt a haka kamun yafara samun sassauci acikin zuciyarshi, duba tsadadden agogon hannunshi yayi yaga k'arfe 3:30 na dare tashi yayi ya fito waje ,tsaye yayi Yana k'arewa wajan kallo , fili ne fetal sai bukkokin fulanin da zaka gani tsili-tsili garin yayi tsit , bakajin komai sai tashin kukan tsuntsaye , alwala yayi yakoma cikin bukkar ya tayar da Sallah , haka yarinka jera nafilfili har akayi asuba ,bayan yayi sallar asuba ne ya koma ya kwanta zuciyarshi cike da tunanin ta inda zai fara, *Washe gari* Misalin k'arfe 8:30 ya tashi daga nauyayyen baccin da ya dauke shi , wajen da aka dan zagaye mashi da sunan ban d'aki nan ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito ya wanke bakinshi da fuskarshi sannan ya nufi wajan su Baffah, Suna zaune a filin gidan suna karyawa yayinda Baffa yake gefe yana hada wasu magunguna Hajar na gefe itada Muneeba tana bata d'umamen tuwon da suke karyawa dashi , sai faman wasa take mata suna dariya, A hankali yayi sallama ya shigo gidan jikinsa duk a sanyaye , amsa mashi sukayi , har k'asa ya duk'a ya gayar da Baffah da Inna , amsawa sukayi cike da farinciki don Allah ya gani suna matuk'ar kaunar Hisham da tausayinshi , sun fahimci mutun ne mai nutsuwa da hankali ga girmama na gaba dashi sannan a d'an zaman da sukayi sun fahimci mutum ne mai gaskiya da rikon amana ga uwa uba Addini, "Hamma Hisham ina kwana " cewar Habu da Halliru , amsawa yayi tare da tambayar su aikin da suka tafi yi jiya cikin gari , nan suka shaida mashi komai lafiya qalau, Juyawa yayi ya mayar da kallonshi wajan da Hajar da Muneeba suke wadda yana lura da ita tunda yarinyar taji muryarshi take ta zillo tanason ta rarrafo inda yake amma Hajar ta hanata sai faman matseta Take a jikinta tana 'yan harare harare , Yana yin arba da kwanon tuwon da take d'urawa 'yarshi ya had'e fuska cikin tsawa yace "keeee wai bana hanaki d'urawa yarinyar nan tuwo ba tunda sassafe sai kinsa tayi k'aton ciki ne, sau nawa zan gayamaki bata isa cin abinci ba , ina madarar da ake bata ne"? Turo bakinta tayi tace to ai itace takeson cin tuwon nikuma 'ya ta tanason abu bazan hanamata ba ta k'arasa maganar tana murgud'a Dan k'aramun bakinta , "Ke Ni kike murgudawa baki lallai bakisan waye Hisham ba ina tausayinki ne wallahi da tuni na 'ballaki oya kuma maza ki saketa tun d'azu takeson zuwa wajena amma kin hanata tsabar kin rainani, ko ?" Shiru tayi batace komai ba sannan kuma bata saki Muneeba ba duk kuwa da irin yadda yarinyar keson k'wacewa taje wajan babanta don ta saba da Hisham sosai tun bata kai haka ba tafara shaida shi, Ganin batada niyar sakinta yasa Inna d'agowa daga gyaran waken da takeyi cikin harshen fillanci tace "Wai ke Hajar wace irin yarinya ce miyasa bakyajin magana ne bazaki saketa ba taje wajan Babanta , Cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka tace "Innarmu kina gani fa duk abunda nake ma yarinyar nan bata gani kullum tafinson taje wajan Babanta a kaina to wallahi wataran sai na boyeta ma inda bazai koma ganinta , Baffa kam dasu Habu Banda dariyar diramarsu ba abunda sukeyi don in da sabo yanzu sun saba da diramar Hajar da Hammanta kusan kullum sai sun raba hali akan Muneeba , saboda Hajar tana kishin Muneeba sosai ko kadan batason taga yarinyar na kula wani indai ba itaba shikuma Hisham yana jin haushin yadda take kanainaye mashi yarinya wani lokacin ma ganinta sai yamashi wahala sai ya zare mata ido sannan take sararawa duk da haka kwana biyu zata dawo da halinta , Hakanan badon taso ba ta saki Muneeba aikuwa da sauri ta rarrafa sai wajan Abbanta sai faman washe mashi baki takeyi irin na yara , D'aukarta yayi ya rungumeta yana bata kiss a goshi yace *sweet heart* kina lafiya ? dariya kawai take mashi , Hajar kuwa sai faman hararar Muneeba take tanajin haushin yadda takema Hisham dariya harda kyalkyatawa, Wajan da Baffa yake zaune ya nufa ya zauna kusa dashi yace "Baffah magana nakeson muyi kuma don Allah inason ka fahimceni Baffah , " "To Hisham Ina saurarenka" Cewar Baffah bayan ya mayar da hankali shi ga Hisham din, Sunkuyar da kanshi yayi a hankali yace "Dama Baffah na yanke shawarar zan bar wannan jejin ne zan koma cikin gari da zama saboda wasu dalilai nawa , ada naso na zauna anan saboda wani kudiri nawa to amma izuwa yanzu na hakura da duk wani burina inason inyi nesa da idon sani ta ko ina don ganin nabawa 'yata ingantacciyar rayuwa, saboda haka nakeson ka fahimceni Baffah , Shiru ne ya ratsa wajan da yake duk suna jin abunda yake fada , Habu da Halliru duk sunyi tsuru tsuru jikinsu a sanyaye don sukam harga Allah basa son rabuwarsu da Hamma Hisham don su murna suke sun samu babban Yaya , Kamar daga sama sukaji ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya mai saurare cikin siririyar muryarta mai kama da sarewa tafara fadin "Wallahi Allah sai dai ka tafi kai kadai ,haka kawai kullum burinka ka rabani da 'ya ta ai nariga na ganoka wallahi Allah Baffah saboda Ni kawai yakeson yayi tafiyarshi don baya sona , tayi maganar tana bubbuga k'afafunta a k'asa cike da shagwa'ba wanda gefe daya Kuma take cike da tashin hankali kar Hisham yarabata da Muneeba , Inna ce ta harareta kamun tace wallahi in nak'ara jin maganar ki anan saina tattakaki , shashashar kawai , zumbura bakinta tayi tareda kara fashewa da kuka , azuciye ta juya ta shige cikin bukkarsu , Duk abunda take Hisham harararta kawai yake ta k'asan ido , yarinyar tana shige mashi hanci da yadawa ,in banda darajar iyayenta da tuni ya Sa'ba mata kamanni don shi ya tsani yaro sagartacce kuma marakunya to ita kuma yakula anan tafi auki , Baffah ne yayi gyaran murya ya dubi Hisham yace .........................✍🏼 Wai wacece mariya??? Wacece kuma Amna Wanene zayyan mi akama zayyan da mahaifinshi ke aikata wasu abubuwan kanshi Mi ya fito da Hisham daga gidane ??? Su waye mak'iyanshi da suke neman ran 'yarshi Hmmmmmmm akwaifa cakwakiya mai girma anan gaba kudai ku kasance tare da Ni don jin yadda zata kaya😍😍😍😍😍 *Aslm sister fatan kuna lafiya , ina matan aure yan mata masu shirin yin aure harma da zawarawa masu shirin shiga daki to ku garzayo nesa tazo kuma nazo maku da ingantattun kayan mata masu kyau da inganci irin wadan da baku saba gani ba , sayen dai dai ko sari ina Sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah, don neman kafin bayani ku tuntubeni ta wannan number 09035027743 mmn Yusuf Mai kayan mata yar mutan Sokoto sakkwatawa masu maida k'asari zuma*πŸ’ƒπŸ»πŸ‘πŸΌπŸ’ƒπŸ»πŸ‘πŸΌ *KARKU MANTA KASAITACCIYAR MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_8 ......................"aa baza'ayi haka ba Hisham , narasa wane irin mutum ne kai , kacika kafiya akan ra'ayinka , da kai kadai ne to da zan Barka ka tafi duk da muna matuk'ar son kasancewarka a tare damu , A iya zaman da kayi damu na tsawon wata ukku acikin wannan jejin na tabbatar ka fuskanci wasu daga cikin abubuwan masu matukar had'ari dake faruwa acikin wannan yankin, saboda haka inhar ka daukeni a matsayin uba to ban yarda kaje ko ina da wannan jinjirar ba kajira akwai lokacin da Yakamata ka tafi in lokaci yayi Ni da kaina zan umurceka da ka tafi , A hak'ik'anin gaskiya Baffah bayason tafiyar Hisham ne saboda abubuwa da yawa da suka tsorata shi dangane da Hisham din tabbas Hisham yana buk'atar taimakon shi , don in har yace zai bar wannan jejin a wannan lokacin to komai zai iya faruwa da rayuwar shi , wannan yasa ya hanashi tafiya ,yanaso sai ya gama bincikenshi akan Hisham kamun ya samu hanyar da zai taimaka mashi , Kanshi a k'asa yace "To shikenan Baffah zan zauna anan din Allah yasa hakan shi yafi alkhairi kuma bazan sake maka maganar tafiya ba har sai inkai ka umurceni dayin hakan Nagode sosai Baffah Allah yasaka maku da mafificin alkhairi, ka maye Mani gurbin da narasa a rayuwata Baffah yanzu banida kowa sai kai sai 'ya ta Muneeba , " "Sai kuma mu Hamma Hisham" cewar habu yana sakar mashi murmushi , Shima murmushin yayi yace "Hakane habu kudin wani 'bangarene na rayuwata kun so ni da dukkan gaskiya alhalin bakusan koni waye ba Nagode sosai ," Kamar ancillota haka ta fito tana washe baki kamar mai tallan makilin cikin sassarfa tace yawwa Hamma Hisham ko kaifa amma in kace zaka tafi ai kaci amanata wallahi don nasan mutuwa zanyi in ka daukemun yarinya katafi , yawwa Baffah Gara da ka hana mashi tafiya wallahi , kaga yanzu ba wanda zai rabani da 'yata. Ko *MUNNI* tayi maganar tana had'a fuskarta data Muneeba tana dariya, Dariya Baffah yayi yace ai nikam zansha kallon duk lokacin da Hisham yace zai rabaki da wannan yarinyar , Turo bakinta tayi tace to kai yanzu Baffah sai ka zuba mashi idanu kana kallo har ya rabamu ??? tayi maganar kamar zatayi kuka, Dariya Habu yayi yace " kekam Allah ya maki son yara irin wannan k'arfin hali haka ai inaga duk randa kika haifi naki ko kallonsu bazaki bari ayi ba, Halliru yace " ai mu zuwan Hamma Hisham ya taimakemu don in ka kula yanzu yaushe rabon da akawo mana k'arar Hajar akan 'ya'yan mutane da take daukewa tazo nan dasu wanda da yawa wad'anda basu santa ba suke dauka ko cutar masu da yara zatayi , amma yanzu shiru ba ruwa ta da kowa sai Muneeba, Habu yayi dariya yace "daina yabonta ba'a yabon dan kuturu sai ya shekara goma da yatsa don wallahi indai Hajar ce ko gobe taga yaron da yayi mata sai ta daukeshi , sunjima suna tsokanarta ita kuma tanata yi masu tsiwa don Hajar badai tsiwa ba , Baffah da Hisham kuwa sai firansu suke a hankali inda Baffah ke k'ara bashi shawarwari akan zamantakewar rayuwa , Yajima agidan har sai da shima ya karya da tuwon Inna sannan ya tashi ya dauki 'yar shi yakoma wajan bukkarshi dama bashida wajan da yake zuwa daga gidan Baffah sai kuwa Bukkarshi inda ya zame mashi matsayin gidan shi , nan zai zauna yayi ta yiwa 'yarshi wasa yau ma hakan ce ta faru zaune suke a k'ark'ashin wata bishiya iska mai dadi Yana kad'awa yayinda Muneeba keta wasanta a wajan sai 'bingila dariya take , shikuma duk inda ta yi yana biye da ita da kallo murmushi d'auke akan fuskarshi yayinda wani 'bangare na zuciyarshi ke matuk'ar tausaya mata , duk da shi d'in ma abun tausayi ne , Kamar daga sama yaji sallamarta, "Assalamu alaikum Hamma Hisham inuwa ake sha ?" Kauda kanshi yayi daga barin kallonta batare da yace mata komai ba , "Oh Hamma Hisham bakada lafiya ne ? Naga kamar kanajin zazza'bi shine nace bari nazo na tayaka zama kar *MUNNI* tayi kuka ba mai kula da ita akusa ," Nan ma shiru yamata , dama yasan kwanan zancan zuwa kawai tayi ta dauke mashi Muneeba ,yarasa wace irin yarinya ce mai shegen nacin tsiya ,duk lokacin da taganshi da yar shi tofa duk yadda zatayi sai tayi taga ta dauke ta , Ganin har yanzu bai kulata ba yasata k'arasawa wajan da Muneeba ke wasa ,zama tayi kusa da ita ta rink'a yi mata fira tana dariya Muneeba ma sai dariyar take duk da batasan abunda ake ba , ganin kamar hankalinshi baya kansu yasa ta d'aukar Muneeba a hankali ganin har lokacin bai juyoba yasa ta fara tafiya kadan kadan ta bayan bishiyar tabi yadda bazai ganta ba , tana ganin tabar bakin bishiyar aikuwa tuni tafara zuba sauri harda had'awa da gudu ta nufi wajan da suke kiyo da k'awayenta , tana tafe tana aikin dariya ganin tayiwa Hamma Hisham wayo, Shi kuwa duk abunda take yana kallonta ta gefen idanunshi ya k'yaleta ne kawai saboda ya gane indai ya biye mata to kullum sai ta sakashi ciyon kai, *Agurguje pls saboda inason mushiga gundarin labarin ne* Haka rayuwa tayi ta juyawa dasu inda yanzu Hisham yasaba da zaman shi cikin fulanin sosai kuma yanajin dadin rayuwar shi a haka yayi sabo da mutane da yawa a ruggar sosai suke ganin girmanshi da k'imarshi inda yanzu yake da shekara 3 a wannan ruggar , Muneeba tayi wayo sosai kullum zaka ganta mak'ale da Abbanta wanda take kira da *sweety* Kamar yadda shima yake kiranta da hakan wanda ta koya daga gareshi ne, Duk da yana ganin lokaci yayi da zai bar wannan ruggar amma sam yakasa yin hakan saboda alkawarin da ya daukarwa Baffa dakuma sabon da yayi da Yan k'auyen musamman ma su habu da suke daukarshi a babban wansu, Hajar yanzu anzama 'yan mata tanada shekara 17 har ana maganar aurar da ita ga saurayinta Nura wanda ya kasance d'a ne ga aboki kuma aminin Baffa , Nura yanason Hajar sosai itama tana sonshi saidai son da yake mata yafi wanda take mashi nesa ba kusa ba , tuni iyayenshi suka so a d'aura aure amma da an tayar da maganar shikenan Hajar zata fara tayar da hauka zanga zanga itace suman k'arya itace sambatu da fisge-fisge kamar wata mai aljanu , wanda hakan yasa ake ta d'aga auren ,kuma abunda yake basu mamaki shine da an d'aga zancan auren to shikenan zata koma normal , wannan yasa iyayen ke tunanin ko aljanu ne suka shafeta sai faman nema mata magani akeyi amma a banza , sau biyar kenan ana saka mata rana abun na warwarewa , wannan yasa Nura ya sameta yana kuka da magiya akan ta taimaka ta yarda asa masu rana don shi harga Allah bai yarda da zancan wasu aljanu ba, ta fadi duk abunda takeson yamata alk'awarin zai matashi inhar baifi karfinshi ba Aikuwa tanajin hakan ta karkace kai ta janyo d'ankwalinta a goshi irin ture kaga tsiyar nan cikin yamutsa fuska tace " Nifa bawai sonka ne banayi ba a'a auren ne dai bazanyi ba gaskiya don in nayi aure bansan uban da zai kulamun da d'iyata ba wannan dalilin ne kawai yasa kaga duk akasa mana rana zan rinka abubuwan nan bazan bari ba sai an daga bikin , Jikinshi na rawa yafara magana da cewa "Wallahi Allah Hajar in har kin yarda zaki aure ni wallahi na yarda kije da 'yar ki zan rik'e Maki ita Amana Kamar Ni na haifeta" ................... " Da gaske kake Hamma Nura ?? Tafada fuskarta kamar gonar auduga, Shima cikin fara'a yace "wallahi da gaske nake Hajar indai wannan ne matsalar to ki kwantar da hankalinki, Cikin tsananin farinciki tace amma naji dadi Hamma Nura yanzu kam kaje ka samu Babanka ka gaya mashi su turo asa rana na amince tafad'a cike da wauta , Shima cike da murna yace yawwa Hajarata bari in tafi yanzu da zafi zafi akan daki k'arfe " , "tace to Hamma Nura bari naje nima nafara hada mana kayanmu nida MUNNI ta , bata jira cewarsa ba ta juya ta koma cikin gida da saurinta, Yana ganin ta juya yabi bayanta da harara dama tuni yayi zargin hakan shiyasa ya biyo mata ta bayan gida , tsaki yayi yace shashasha ai wallahi ko 'yar Dan uwanki ce baki isa kijemun da ita gida ba bare kuma yarinyar da baki had'a komai da ita ba, indai samu ayi auren zakisha mamaki na , ina sonki sosai amma sam bazan yarda kijemun da wata yarinya ba don Ni ba mahaukaci bane , daga haka ya ka'ba rigarshi ya nufi gidansu cike da murnar zai mallaki masoyiyarshi, ......................................... "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un , Amna mizan gani haka , shaye shaye a gidan nan , mikikeso kija mana agarin nan , kina kallo an tsayar da ubanki a matsayin *d'an takarar gwamna* amma shine kikeso ki janyo mana idon mak'iya , yanzu mi kike tunani idan har abokan adawarshi suka san da wannan abun da kika tsiro.... Ko kallon momy batayi ba sai dakinta da ta nufa tana tangand'i hannunta rik'e k'ananun kwalabe har ukku tana sanye da riga da wando wanda suka matseta sosai suka fitar mata da surar jikinta kanta ba d'ankwali sai dogon gashinta da ya kwanta har gadon bayanta, Fisgota momy tayi cikin tsawa tace wai ba magana nake maki ba ...........cikin Muryar maye tafara magana tana cewa " Indai abunda nake zai sa azzalumi mijinki ya fad'i a wannan za'ben to wallahi yanzu na fara , kuma inaso kisani sai nayi ajalin mijinki da hannuna da wannan hannun nawa tana magana cikin matukar maye wanda har baka fahimtar abunda take cewa sosai daga nan ta zarce da wasu irin surutai da momy takasa tantance abunda take cewa , Dafe kai momy tayi zuciyarta kamar zata fito waje tsabar tashin hankalin da take ciki...............✍🏼 *Zanyi kokarin ganin nadinga maku post akan lokaci saidai ba lallai kusamu typing din da yawa ba saboda abubuwa sunmun yawa inkuma da yawa kukeso to zan dinga yi duk bayan kwan biyu* [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ -9 ......................da murnarshi ya shiga gidan da sallama , Inna talatu na tsakar gidan tana surfe ta amsa mashi, "Inna daka akeyi ne"? "Eh Nura , daga ina haka kai da kace yau bazaka dawo da wuri ba"? "Sosa kanshi yayi yana 'yar dariya yace Inna Dama wajan Baba nadawo Allah yasa bai fita ba" "A'a bai fita ba yad'an zagaya ne" Suna haka sai ga malam Buba , gaisheshi Nura tak'arayi da jiki kasancewar yana fama da zazza'bi shiyasa ma yau bai fita ko ina ba , "Nura mi ya dawo dakai kuma yanzu kai da kace zakayi nisan kiyo ? " "Wallahi Baba akan maganarmu da Hajar ne naje mun daidaita kanmu yanzu insha Allah baza'a sake samun wata matsala ba shine nakeson ka aika wajan Baffanta ak'ara sa mana rana insha Allah yanzu ba abunda zai koma faruwa tuni na shawo kan matsalar , "Ka shawo kan matsalar kamar yaya , ai wallahi ni nagaji da gafara sa banga k'aho ba , Ni dama ban yarda da wasu aljanu ba iskancine kawai , to inaso kabude kunnenka da kyau kaji daga yau ba kai ba wannan yarinyar nariga da nagama magana zamu had'aka aure da 'yar uwarka Dije ranar juma'a in Allah ya kaimu za'a kai kud'in aure. Don haka kar ink'ara jin maganar wata Hajara kaji na gayamaka , kai inbada ma kake wani sakarai har yaushe zakaje ka d'ad'd'agowa kanka gandamemiyar budurwa kamar wannan , ga yara 'yan mata masu tasowa amma ka bige da neman wata hajar , to ban yarda ba dama can kasan Ni bawai inaso had'in bane don dai ubanka ya kafe ne kurum yanzu kuwa bazan yarda ba , cewar Inna cikin masifa , Inna talatu masifaffiyar macece ta bugawa a jarida , wannan yasa Malam Buba yake matuk'ar tsoronta sam baya iya taka Mata birki duk abunda zatayi tazama itace mijin shine matar , dama can batason wannan had'in na Nura da Hajar malam Buba ne ya kafe har yasamu ya shawo kanta ta yarda , yanzu kuwa ganin abubuwan dake faruwa yasa ta yanke shawarar hadashi da yar k'anwarta Dije ko yanaso ko bayaso Tunda tafara magana zufa ke ketowa Nura ta ko ina , cikin tsananin tashin hankali yace " don Allah Inna karkimun haka kimun rai wallahi inason Hajar sosai kuma namaki alkawarin ba abunda zai koma faruwa kuma" ............cikin masifa tace " son nata ya dade bai kasheka ba to wallahi bazaka aure ta ba dama can ba sonta nakeba Dije zaka aura kaji na gaya maka, daga haka ta kwashe hatsinta ta nufi inda suke ajiye ruwa ta zuba tafara wanke surfen tanata zabga mita , "Baba kanajin Inna abunda take cewa amma kayi shiru bakace komai ba, yafad'a kamar zai fashe da kuka, " Kayi hakuri Nura , jiya ba k'aramun tashin hankali na fuskanta ba daga wajan talatu akan maganar nan ,nayi iya yina amma ta kafe kadai san halinta Sarai in takafe akan abu , ni wallahi babbar damuwata ma shine Baffah Ja'in bansan abunda zance mashi ba nayi nayi ta yarda ko don na fita kunyar Ja'in Amma tak'i kayi hakuri kamata biyayya Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, " Hawaye Masu zafi suka wankewa Nura fuska, wani irin zafin Hajar yakeji sosai ,don a ganinshi duk ita taja mashi da yanzu anjima dayin auren su , haka ya tashi jiki ba kwari ya fita daga gidan ,yanufi inda ya baro dabbobinsu tare da abokan shi, Haka kuwa akayi ran jumu'a aka kai kudin auren Nura da Dije , Su Innar Hajar sai kawai ji sukayi ankai kudin auren Nura , Inna kuwa ta shiga damuwa ba kad'an ba ,don bata da babban burin da yafi taga auren Hajar kodon ta huta da tsegumin mutanen garin , Baffah kuwa ko a kwalar rigarshi sam bai wani damu ba saima addu'a da yayi akan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, Uwar gayyar ma bata wani damu ba sai cewa tayi Allah ya raka taki gona, ........................................ Afusace ya shigo gidan kamar zai tashi sama , momy na zaune a falo tabuga uban tagumi tanajin duniyar na juya mata , tabbas abunda suka shuka ne suke girma , ta rasa Babban d'anta yanzu kuma tana nema ta rasa 'yar ta wadda ita kadai ta rage mata a yanzu , "Ke Hindatu Ni zaku tozarta a garin nan , Ni zaku zubarwa da mutunci , wato kin had'a baki da 'yarki kunason kuga bayana ko ? Inba hakaba tayaya ina matsayin da takarar gwamna a jahar nan amma kiyi saken da zaki bar 'yarki tafad'a wannan halin , duk wani wajan iskanci za'a sameta a wajan ya kikeson mutane gari su lalleni in sukasan cewa 'yata Yar k'waya ce , sannan abokan adawata kinsani inhar suka san da wannan matsalar to na kade har ganyena , yanzu takai har office ake iskoni ana gayamun abunda yarinyar nan keyi a garin nan to wallahi kija mata kunne inba haka ba wallahi daga ke har ita sai kunyi dana sani , kindai san waye Saminu sulaiman daga haka ya juya fuuuuu yabar falon, Hawaye ne suka zuboma momy tanajin zuciyarta kamar zata fashe tsabar bakin ciki a hankali tace ya Allah wannan wace irin masifa ce daga wannan sai wannan , doli zan dauke Amna daga garin nan har zuwa wani lokaci inba hakaba komai zai iya faruwa tasan halin mijinta Sarai zai iya kawar da duk wani mahaluki da zai kawo masa cikas daga cikar burinshi na zama gwamna Amna kuwa bata ma san yanayi ba tana daki kwance sai sharar bacci take daidai da takalmin kafarta bata cireba shekara biyu kenan da tajefa kanta a wannan halin sanadin k'awarta Lawisa , tun bayan da ta babbatar da cewa tarasa masoyinta da gaske ta d'auki damuwar duniya ta Ι—orawa kanta kullum ciki kuka da damuwa take , wanda har hakan ya haifar mata da ciyon zuciya mai tsanani, da wannan damar k'awarta Lawisa tayi amfani wajan cusamsta ra'ayin yin shaye shaye acewarta kayan maye sune kawai zasu taimaka mata wajan kawar mata da duk wata damuwarta , ......................................... Alhamdulillah yanzu jikin Baba yayi sauki sosai , zuwa wannan lokacin sun fawwalawa Allah komai sunci gaba da gudanar da al'amuransu na yau da kullum , duk da ada Baba yaso subar garin gaba daya saboda yadda yakejin garin yamashi k'unci da zafi , sai da k'yar Yaya sulaiman ya shawo kanshi akan ya hak'ura ya barwa Allah tunda in sun bar garin basu san inda zasu nufaba , wannan yasa ya hak'ura doli don ba yadda zai yi sai dai har wannan lokacin bayajin dad'in zaman garin abubuwan da suka faru baya sun kasa gogewa a zuciyarshi, ......................................... Acikin wannan lokacin ne wata annoba ta shiga ruggar su Baffah Ja'in , inda dabbobinsu suka rink'a mutuwa kusan kullum sai sun rasa wasu daga cikin dabbobinsu , wannnan abufa ya tashi hankalinsu matuk'a , gaba daya yan ruggar sun d'aga hankalinsu , kunsan Fulani da shanu🀣 Acikin sati d'aya sai gashi sun tafka asara mai yawa , sunyi iya bincikensu don sanin abinda ke faruwa da dabbobinsu amma basu gano komai ba , Wannan yasa manyan cikinsu suka yanke shawarar tashi daga garin gaba daya , Asalin su Baffah Ja'in fulanin yawo ne basuda takamammen wajan zama , duk inda suka ratsa sukaga cewa wajan zai masu to zasu yada zango a nan nawani lokaci , wani wajan sai suyi shekara d'aya wani biyu wani ma bazasu wuce wata shida ba yadanganta da yanayin wajan idan yayi masu , kuma a haka duk inda suka yada zango in wata daga cikin 'ya'yansu ta samu mijin aure a garin indai har sun yarda da tarbiyyar shi to zasu bashi auren yarsu kuma ahaka in lokacin tashinsu yayi zasu tafiyarsu su barki to fa daga nan sai dai in kunada rabon koma ganawa da juna tunda basuda takamammen wajan zama , saidai zasu sanar da mijin ainahin inda tushen su yake kodon wata rana, Duk inda sukaga yamasu to kowanensu zai d'ibi iya inda yakeso yakafa yar bukkarshi babu zancan wani zagaye gida da sauransu saidai suna bawa juna tazara a tsakaninsu , Duk inda suke sauka basu ta'ba jin dadin zama ba kamar wannan jejin ba, duk kuwa da irin yadda dajin keda had'ari amma sukam sosai sukejin dadin zamanshi saboda jejine mai yawan fadamu da k'orsmu ga Ni'ima , Babu wani waje da suka ta'ba dad'ewa irin dad'ewar da sukayi a wannan wajan Amma bullowar wannan al'amari yasa doli ungulu zata koma gidanta na tsamiya, Nan suka yanke shawarar nan da kwana ukku zasu yi hijira daga wannan nahiyar zuwa wata , Lokacin da Baffa ke sanar da ahalinshi sun shiga tashin hankali ba kadan ba don sunyi sabo da garin ba kadan ba , Sai dai duk tashin hankalin da sukeji bai kama k'afar wanda *Hisham* ya tsinci kanshi aciki ba , yaji wani gingimemen tashin hankali wanda ko lokacin da zai bar mahaifarshi baiji irin shi ba , tuni abubuwan da suka wuce suka fara dawo mashi tuni kanshi yafara juyawa yayinda idon shi suka k'ank'ace suka shige ciki bayan wani irin ja da sukayi kamar an watsa mashi barkono , Miyasa rayuwa take zo mashi da abubuwa marasa dad'i ne irin wannan yarasa kowa nashi lokacin da yake da buk'atar taimako Allah ya had'ashi da Baffah da iyalanshi ,a yadda suka daukeshi har mantawa yake da cewa sud'in ba 'yan uwanshi bane ya sakankance dasu sosai sai gashi Ζ™addara zata koma shiga tsakaninshi da farincikinshi a karo na biyu , hawayene masu zafi suka gangaro daga kyawawan idanunshi yayinda numfashin shi har sark'ewa yake tsabar tashin hankali, ashe da yake ta cewa zai tafi yabarsu ashe bazai iya aikata hakan ba , bai tabbar ba sai yanzu da yake ganin Ζ™addara zata rabasu yanaji kuma yana gani, Sai da gaban Baffa ya fad'i lokacin da ya kalli yanayin Hisham , shi kanshi tunda suka yanke wannan hukuncin yake cikin matukar damuwa da tashin hankali akan Hisham , shine kadai ne damuwarshi tunda in da sabo sun saba da irin wannan tashin to amma abun damuwar shine ya rayuwar Hisham zata kasance ya rabuwarsu zata kasance, A hankali Baffa yafara bashi baki yana nuna mashi muhimmancin yarda da Ζ™addara don yasan a wannan lokacin doli zasu rabu yaci gaba da cewa "ina tausayinka sosai Hisham ina tausayin irin rayuwar da kakeyi ,nasan ba k'aramun abune zai raboka da gida ba acikin irin wannan yanayin , amma ina maka addu'a da fatan alkhairi a rayuwa , sunjima suna tattaunawa shida Baffah duk da Baffa ne kawai ke maganar wanda shima k'arfin hali ne kawai yakeyi , Hisham kuwa sam yakasa magana ma wani irin shock yakeji gaba daya jikinshi rawa yakeyi , Gefe daya Kuma habu da Halliru ne sai faman hawaye sukeyi basu taba damuwa da tashin su daga wani wajan zuwa wani wajan ba sai a wannan karon saboda Hamma Hisham ,gaba daya sun d'aga hankalinsu, gefe d'aya kuma *Hajar* ce ta haΙ—a kanta da gwuiwa kuka take har na fitar hankali saboda ta tabbatar da yanzu kam zata rabu da Muneeba da gaske kuka take har muryarta ta dashe Inna tayi lallashi har ta gaji, ga Muneeba zaune kusa da ita ganin Hajar na kuka yasa duk ta damu takasa sukuni sai ma kukan da itama tafara ahaka bacci ya kwasheta ajikin Hajar duk ta mak'alk'aleta , Kallo Daya Hisham yayi masu yaji wani abu mai kama da tausayi ya daki zuciyarshi da k'arfi , wani tausayin Hajar da 'yar shi ne ya daki kirjinshi ya tabbata da zasuyi kewar juna sosai musamman ma munee yasan kamun ta saba da rashin Hajar zata wahala sosai wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa Sam baiso 'yarshi ta shak'u da kowa ba don kar wani lokaci hakan ya zame masu barazana , Dare yayi sosai amma basuda niyar tafiya su kwanta Baffa ne yayi karfin halin yimasu magana akan suje su kwanta zuwa safe zasuyi magana , haka kowa ya tashi jiki a sanyaye suka nufi makwancinsu , Gaba daya haka zuciyoyin wadan nan bayin Allah suka kwana cikin matukar damuwa ga wata irin kewa da sukeji tun basu rabu ba, Hajar sam batayi bacci ba tsabar kukan da takeyi saidai akai akai zata dauki fitila ta haska fuskar Muneeba sai ta jima tana kallonta saikuma ta fashe da kuka, Kwance yake sam yakasa runtsawa zuciyar shi kamar zata fito waje idonshi kuwa banda tsiyayar da hawaye ba abinda yakeyi , *Yanzu haka zaku rabu da Baffah batare da yasan waye kai ba , duk irin wannan hallaci da yayi maka tabbas Baffah ya cancanci yasan ko kai waye* wani sashe na zuciyarshi yayi mashi wannan tambayar , Da sauri ya zabura ya tashi zaune Yana fad'in tabbas *Yakamata yasan waye Ni doli zan bashi tarihina kamun rabuwarmu*.................✍🏼 Nagaji sai gobe🀨🀨🀨 09035027743 *MAYUKA MASU KARA NI,IMA* πŸ…°οΈ farkon shekarun balaga na kowacce mace musamman dai dai lokacin da take fara al'ada, tana fara ganin ruwa wanda ake fadawa ni,imar mace, yana dan yauki kadan haka zalika yana kama da ruwa dan danonsa kuma kamar an hada sugar da gishiri, ruwan yana iya canjawa kodai daga matsalar ciwon sanyi ko kuma wanda ake cewa dattin mahaifa, ko kuma yanayin maganin ni,ima da mace tasha kalarsa ya canja, haka zalika dandanonsa, wannan ni,ima kenan a takaice. πŸ…°οΈ na samun mayuka wadanda kasashen turawa ke sarrafawa wadanda ake matsi ko kuma sha, wanda suke tatso ni,ima ajikin mace da wuri kodai haka kawai ta zama da danshi ko kuma lokacin sha'awa, amma a bangaren mayuka daga magungunan muslinci akwai wadannan da suma ana amfanin dasu ta wannan fannin wato maganin ni,ima kuma anashan cokali biyune safe da yamma, mayukan da ake hadawa waje daya sune kamar haka 1 man ridi 2 man zaitun 3 man kwakwa 4 man habbatussauda *Daga taku mmn yusup mai kayan mata*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° [6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ--10 ..................Asubar fari salla kawai yayi ya nufi gidan Baffa , zuwa lokacin har jiri ke d'ibanshi , ga wani zazzaΙ“i da yake ji, Kasa shiga gidan yayi saboda har yanzu garin da sauran duhun asuba , shi kanshi yasan bai kamata yazo yanzu ba sai dai kawai yakasa hak'ura ne ,ji yake kamar idan ya jima baizo ba zaizo ya tarar basa nan, Zama yayi a wajan gidan inda ya haΙ—a kanshi da gwuiwa yama rasa wane irin tunani zaiyi, Yashafe fiye da awa a wajan sannan Allah ya kawo Baffah ya dawo daga masallaci shida su Habu, Har suka k'araso wajanshi baisani ba don yayi nisa cikin tunanin rayuwa , Dafashi Baffa yayi yace ......."Hisham wane irin tunani kakeyi hakane , so kake ka haifarwa kanka da wani ciyo ne, " Firgigit yayi yana kallon Baffa , ........"bansan da zuwanku ba Baffa ina kwana," ...."lafiya qalau Hisham , miyasa ka zauna anan ai da sai ka shiga gida ko" Shiru yy baice komai ba , daga nan su habu suka gaisheshi sanna suka dunguma suka shiga gidan tare, Inna na gindin murhu tana hada wutar da zata dama masu kunu dashi sukayi sallama suka shigo, Gaishe da Baffa ina tayi kamun su Hisham su gayar da ita, Zama sukayi akan tabarma d'aya duk sunyi shiru kowanensu da tunanin da yakeyi , sai can Hisham ya numfasa yace "Inason magana dakai Baffah, Kallonshi Baffa yayi yace " lafiya dai Hisham ? Ko akwai abunda yake faruwa ne ,?" "Bakomai Baffah kawai dai inason kasan koni waye , inason ibaka *labarina* ne inaji baidace mu rabu a haka ba batare da kasan ko ni waye ba , duk da banida niyar sanar da kowa asalin waye ni tunda na tsinci kaina a wannan sabuwar rayuwar to nayi kudurin bawanda zai san koni waye to amma kai naji inason na gayamaka asalina da abunda yaraboni da asalina yayi shiru sakamakon tuna abubuwa da yawa da suka faru dashi, Murmushine ya bayyana akan fuskar baffa , cikin farin ciki yace " Tabbas najima inason sanin ko kai waye Hisham , sai dai banason takura maka ne shiyasa ban sake tambayarka akan abinda ya raboka da gida ba , zanyi matukar farin ciki idan har kabani labarinka, Tashi Baffa yayi yashiga cikin yar bukkarshi sannan ya umurci Hisham da ya biyo bayanshi, tashi yayi yabi bayan Baffa , Habu da Halliru harma da Inna Sam basuji dadin hakan ba don sun so suma suji labarin Hamma Hisham, Ganin hakan yasa Inna taci gaba da aikin hada kayansu yayinda habu da Halliru suka fita wajan da dabbobinsu suke don duba lafiyarsu , Hajar kuwa tana cikin yar bukkarsu itada Muneeba wanda bacci yayi awon gaba da ita saboda rashin baccin da batayiba jiya , sam batasan wainar da ake toyawa ba, A hankali ya bud'e bakinshi yafara magana yana cewa, " *Mun kasance* yan asalin garin Sokoto acikin garin shuni , mu Fulani ne mahaifiyata da mahaifina duk yan Sokoto ne ,mun kasance bamuda yawan zuri'a sosai saboda k'arancin haihuwa da dangin mu suke dashi tun tali-tali mahaifina da mahaifiyata yan uwan juna ne auren zumunci aka masu , mahaifiyata ita kadaice a wajan iyayenta wanda Allah ya masu rasuwa tun tana yarinya , a hannun mahaifin Abbana ta girma , Kakana malam Muhammad yanada matan aure biyu kuma dukkansu yan uwansa ne da yake basu cika auren bare ba a zuri'arsu , Inna Habiba itace uwargida sai Inna Indo , akwai zaman lafiya sosai a tsakaninsu da fahimtar juna, Inna Indo itace tafara haihuwa a gidan , inda haifi d'anta mai suna Abdullahi , Abdullahi nada shekara 4 itama Inna Habiba ta haifi danta inda yaci sunan Abdurahaman , yaran sun tashi cikin tarbiya da kaunar junansu , Abdullahi nada shekara 14 inda Abdurahaman yakeda shekara goma alokacin ne rikon mahaifiyata ya dawo hannun malam Muhammadu saboda rasuwar iyayenta wanda suka rasa ransu ta hanyar gobara da ta tashi a gidan nasu kamun a kawo masu dauki har wutar taci jikinsu sosai kwanasu daya Allah yamasu rasuwa, Alokacin tanada shekara 4 a hannun Inna Habiba take zaune Malam Muhammadu yayi kokari sosai wajan tsayin daka don ganin yaran nashi sun sami ilimin arbiya dana boko, Bayan wasu shekaru alokacin *Maryam* wato mahaifiyata tazama budurwa sosai alokacin ne daga Abdurahaman har Abdullahi suka nuna suna sha'awar aurenta , ganin hakan yasa Malam Muhammad yabata za'bi a cikinsu , kai tsaye ta za'bi Abba na wato Abdurahaman , Abdullahi da mamansa sunji haushi sosai wanda har saida takai Abdullahi baya shiga duk wata harka da ta shafi Abbana , ya dauki karan tsana ya dora mashi , kishi yake dashi sosai *wannan shine mafarin lalacewar kyakkyawar alak'ar dake tsakanin mahaifina da yayanshi Abdullahi* Bayan wani lokaci akayi bikin Abbana da momma na a Nan cikin garin Sokoto suka fara zama, shekara d'aya da aurensu akayi bikin Abdullahi da matarshi Asma'u wadda suke kira da Nana , wadda ta kasance 'ya ce ga abokin malam Muhammadu, Abdullahi kasuwanci yakeyi ,yana yawon garuruwa kuma Alhamdulillah yana samu sosai , yayinda Abbana ya dage akan karatun shi wanda bashida burin da yafi ace yazama *dan sanda* (police) bayan gama karatunshi bai jima ba aka daukeshi aikin dan sanda kamar yadda ya karanta , inda ya fito da matsayin inspector, yayi farin ciki sosai hakama iyayenshi , inda yafara aiki gadan gadan, cikin gaskiya da amana , Abbana ya kasance jajirtaccen Jam'i, mai kishin k'asarsa , wanda gaskiyarsa tasa yayita samun karin girma a wajan aikinshi , inda daga baya aka mashi transfer zuwa Lagos, *Mafarin duk wata matsala* Saida Momma na ta shekara 7 sannan Allah yabata ciki na , kuma har wannan lokacin suna zaune a Lagos a unguwar *Small lando* Sunyi matukar farin ciki da samun wannan cikin nawa ba kadan ba , tun a lokacin suka dauki son duniya suka dorama cikin saidai cikin na bata wahala sosai ,duk wata kulawa da take buk'ata to tana samu daga Abdurahaman sosai yake tsaye wajan ganin ya bata kulawa , ahaka har cikin ya isa haihuwa , a wata safiyar jimu'a bayan masallaci Allah ya sauke Maryam inda ta haifi danta fari tass dashi ba abunda ya baro na mahaifinshi , Abdurahaman yayi murna da farinciki a wannan rana kamar ba gobe , haka yayita sadaka ga mabukata , gefe daya Kuma wata irin soyayyar danshi ce ke shiga lungu da sako na zuciyarshi, ranar suna yaro yaci suna *Hisham* bayan sati Daya da suna Abdurahaman ya kwashe mai jego tareda dansu suka nufi Sokoto , acan ya barsu ya koma wajan aikinshi , da niyar in tagama wanka zaije ya dawo dasu, Bayan sari ukku, Alokacin satin Maryam biyar da haihuwa tana samun kulawa sosai tayi bul-bul abunta itada baby ran Alhamis kwatsam sai Inna Habiba ta tashi da ciyon ciki , wasa wasa sai gaba abu keyi tun tana daurewa har ta sanarma da Inna Indo , kamun zuwa wani lokaci inba Habiba tafita daga hayyacinta sai mirkususu take , babu shiri Inna Indo ta aika a kirawo malam , Maryam kuwa tuni hankalinta in yayi dubu to ya tashi hawayene kawai ke zuba a idonta ganin yadda uwar mijinta kuma uwarta ke cikin mawuyacin hali na ciyo, Lokacin da malam yazo har tafita daga hayyacinta sam bata gane wanda yake kanta , arikice Yakamata suka nemo taxi suka nufi babban asibin garin wato asibitin daji , kasancewar akwai nisa sosai tsakanin shuni da cikin gari yasa kamun suzu har Inna Habiba ta suma , Suna zuwa aka wuce da ita emergency, Basu wani dau lokaci suna dubata ba Allah yamata rasuwa , Ba k'aramun gigicewa da rudani Inna Indo da Malam suka shiga ba jin cewa wai Inna Habiba ta rasu , jikin malam na rawa ya dauko waya ya kira yaranshi ya gayawa Abdullahi amma bai gayawa Abdurahaman ba yadai ce mashi komai yakeyi ya ajiye yazo gida , Abdurahaman fa ya tashin hankalinsa don ya tabbata ba lafiya ba tunda har yaji irin wannan kiran daga mahaifinshi , ba abunda bai sak'a a zuciyarshi ba , a ranar ya hawo jirgi ya nufi Sokoto , Lokacin da yayi arba da gawar mahaifiyarsa ba k'aramun firgici ya shiga ba , yayinda komai ya tsaya mashi cak yarasa wane irin tunani zaiyi , haka ya tsurawa gawar ido kai kace ita yake kallo amma sam hankalinshi tuni yabar jikinshi , tsabar tashin hankali da yake ciki Bama ya iya banbance abubuwan dake faruwa a gidan , ganin halin da yake ciki yasa Malam Muhammad janye shi ya fita dashi daga dakin , dakinshi ya kaishi nan ya zaunar dashi yarinka bashi baki da yimashi nasiha inda yarinka janyo mashi ayoyi da hadisai masu magana akan yarda da Ζ™addara yajima yana bashi baki kamun a hankali yafara dawowa hayyacinshi , aikuwa take ya fashe da wani irin kuka mai matukar ban tausayi..................✍🏼 *ZAN BAKU TARIHIN IYAYEN SHI NE A TAKAICE SABODA MUSAMU MUSHIGA GUNDARIN LABARIN* *Kuyi hkr da wannan kunsan bangama warwarewa ba sai a hankali* πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ» πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« *SHAHARARRA KUMA K'ASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA _MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TA SAKE ZO MAKU DA KAYATATTUN KAYAN MATA ZAFAFA MASU KYAU DA INGANCI SAYEN DAYA KO SARI INA SOKOTO INA AIKAWA KOWANE GARI A NIGERIA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH KUDAI KU MATSO KAR AYI BABU KU KAYANMU NA MUSAMMAN NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» 09035027743 *KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA MUKE DASU* maganin sanyi Maganin KIBA Maganin rage tunbi da kiba Maganin sanyi na maza Maganin gashi - Yana Sanya tsawon gashi Hana karyewar gashi bakin gashi yana maganin sali kurajen Kai da sauran matsalolin Kai *Akwai zafafan kayan Mata Kamar jaka* Gumar Madara Gumbar gero Gumbar Jan icce Gumbar Sha ki matse Gumbar sa buzu kuwa Gumbar tada zaune tsaye Gumbar ridi Gumbar shinkafa Gumbar Aya Gumbar ukku bala'i Sarauniyar gumba Da dai sauran kalolin gumbunan da muke dasu *Kalolin gari* Dakan jaraba Kinfi budurwa Jita salaf Garin mallaka Dakan Ni'ima Bita zai-zai Sabon budurci Mai kwamson gyada Dakan tabaje Dakan kishiya in bakiyi bani waje Dakan Amare Emergency Dakan sa buzu kuwa Dakan sha yanzu magani yanzu Da sauran kalolin da ban fada ba 09035027743 mmn yusuf skt *Munada kalolin matsi da basuda illah Kuma masu matukar aiki da Kara lafiya ga HQ* Matsin mallaka Matsin a Daren farko Matsin sabon budurci Danba gigita Matsin kishiya in bakiyi bani waje Matsin Dan la'asar Gam-gam Matsin kinfi budurwa Matsin rantse bakida kishiya Matsin Dan mannau Matsin k'yallen al'ajabu babban sirri kenan Da sauransu *AKWAI* original Dan goshi ba bugi ba tare da Mahadi shi Original man ayu Original man damo da kitsensa dan goshi sabon salo wanda ake amfani dashi ga mara *Muna dahuwa Kamar haka* Dahuwar kaza Kazar yar gata Kazar Amarya Kazar maijego Ciccibi Yan shila Nama dambun nama Wanda yake jimawa ajiki Kifi Da dai sauransu *Daga gefe Kuma akwai* 1,Maganin kiba maisa cikowa da laushin fata, 2,maganin gyaran nono 3in1 3 na hips mai ingaci dake aiki a cikin sati daya Kalolin sabulun wanka masu gyara fata da Sanya hasken fata mai kyau Sabulun tsarki Yana maganin duk wata matsala ta HQ Yana matsi ciki da waje Yana saukar da Ni'ima Turaren jiki Turaren daki Turaren tsugunno Tsarkin jaraba Dan la'asar na Sha Kayan gyaran jiki na Amare irin su dilka halwa sabulun Amare turarrukan Amare masu gyara fata da Sanya k'amshi ajiki Hatsabibin turarene Hatsabibiyar humara Kalolin humara Colecca Sirrin mallaka na tafin kafa hmmm yar uwa jaraba kiga abun mamaki Dama sauran abubuwan Dana manta ban fada ba duk zaku samesu a wajan yar mutan sokoto mmn yusuf skt *A'bangaren girki ma muna bada namu tallafi akwai curry kala kala Masu kamshi da bada launin abinci nai kyau da jan raayi yara da oga ga abinci ki hjy* 09035027743 *A'bangaren tsumi ma ba'a barmu a baya ba akawai* Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin madarar Ni'ima tsumin tabajeπŸ’ƒπŸ» Shayin Amare Tsumin nono rakumi Zumar Mata mai ridi & zumar. Icce xallah tamasu jego Tsumin ruwa lumtsum Tsumin Sabon budurci Tsimin bita xaixai Tsimin makalemata Tsimin sa sambatun oga Da dai sauransu 09035027743 *Muna hada kayan Mai jego abubuwan da zasu dawo Mata da martabanta a wajan maigida kasancewar duk wadda ta haihu to ni'imar jikinta na tafiya sosai hakama HQ dinta zai bude to muna hada kayanda zasu dawo Mata da martabanta zata matse sosai ciki da waje Kamar bata haihu ba da Wanda zasu dawo Mata da martabanta akan kudi kalilan*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Hakama zawara Mai Shirin yin aure muna hada Mata kaya masu taken ubanka sabon budurciπŸ’ƒπŸ» Hakama budare muna hada kayan gyaran Amarya ciki da wajenta zatayi das abunta gwanin sha'awa sauran bayani Kuma ango ne zai yi makiπŸ˜‰ Karku manta da sunan maman yusuf yar mutan sokoto Address _unguwar Makerar Assada area sokoto Phone number _09035027743 do neman Karin bayani πŸ‘πŸ½ *Don Allah don annabi duk wadda Bata shirya siyaba kar tamun magana tabari sai ta shirya tukunna kar mu batawa juna lokaci* πŸ€—πŸ€—πŸ€—πŸ€— [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_11 .........................Sati biyu da rasuwar Abbana ya koma Lagos saboda aikinshi ,inda yabar Momma har ayi sadakar arba'in sai yazo sukama tare, Hakan kuwa akayi ana saura kwana biyu ayi arba'in saiga Abdurahaman ya sauka a garin Sokoto , Maryam tayi farinciki sosai da ganin mijinta , duk tabi ta rame saboda tunanin Inna Habiba da rashin mijinta a kusa , duk da tana samun kulawa daga wajan Inna Indo da Malam Muhammad hakan bai hanata shiga matsananciyar damuwa ba , saboda inba Habiba tayimata komai a rayuwa ita take gani a matsayin mahaifiyarta shiyasa duk sai taji gidan yafita ranta tana dai zaune ne kawai Hisham kuwa yayi bul-bul dashi Masha Allah yayi jiki sosai farinshi yak'ara fitowa , ga yalwan suma kamar dan indiyawa , Malam Muhammad ma yayi farinciki da ganin d'an nashi sosai, don yana tausayin Abdurahaman da Maryam sosai don yasan irin shak'uwar dake tsakaninsu da Inna Habiba , Kwanansa biyar a k'auyen suka tattara suka koma Lagos , Haka a rayuwa tayi ta juyawa yau fari gobe bak'i inda Abdurahaman yayi suna sosai da farinjini saboda yadda yake aikinshi cikin gaskiya da amana sosai akeji dashi agarin na Lagos yatara masoya masu dinbin yawa kamar yadda yatara mak'iya masu tarin yawa , don da yawa wad'an da basasonshi kama daga manyan masu kudi yan siyasa saboda shigema yaransu hanci da yakeyi dakuma wasu daga cikin *yan sanda* 'bata gari wanda basa kishin kansu da kasarsu saboda tsabar bakin ciki da hassada. K'iyayyar da akema inspector Abdurahaman yasa har anfara farautar rayuwarsa ko ta ina anyi ta kafa mashi tarko amma cikin ikon Allah yana tsallake wa , ahaka kwanikka suka rinΖ™a shud'ewa sattika na wucewa hakama watanni da shekaru , *Bayan shekara 20* Acikin wannan shekarun abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda rasuwar malam Muhammadu shekaru takwas kenan da suka wuce , tun bayan rasuwar shi Abdurahaman ya k'auracewa Sokoto sam bayason zuwa garin sai doli hakama Maryam , suna jimawa sosai kamun su ziyarci garin , sai dai akai akai Abdurahaman yanama Inna Indo ake sosai kama daga kudi sutura ko kayan abinci , duk da kasancewar Abdullahi ma nada abunshi dai dai gwargwado kuma yana kulawa da mahaifiyarshi sosai hakan bai hana Abdurahaman yimata hidima ba amatsayinta na matar mahaifinshi kuma wani 'bangare gwaggonshi , A wannan shekarar ne Hisham ya k'are karatunshi na secondry cikakken saurayi dan shekara 20 k'ak'k'arfa kuma shahararren Gaye Dan wanka ,yaro mai farinjinin samari da 'yan mata , Hisham yaro ne kyakykyawa na bugawa a jarida , farine tass wanda har wani yellow yellow yakeyi , yanada manyan idanu wanda suke a lumshe koda yaushe ina har kaga idanunshi sun fito sosai tofa ranshi ne a 'bace yanada dogon hanci sosai wanda yak'ara k'awata mashi fuskarshi, Hisham mutum ne mai fara'a sosai wanda yanada wuya kaga bacin ransa mutum ne Maison mutane sosai da wasa da dariya , yanada barkwanci sosai wanda ko iyayensa bai bariba haka ya mayar dasu kamar wasu kakanninshi wannan yasa mutane kesonshi sosai kowa nasa ne, mata kuwa kamar zasuyi hauka saboda Hisham amma shikam sam baya kulasu dukda yakeda sakin fuska amma sam baya bawa mace damar da zata furta mashi kalmar so , Idan ka ganshi zaka dauka yakai shekara 25 saboda yadda yake da manyan ga'b'bai ga tsayi irin na asalin jaruman maza , Ba karamin so iyayenshi ke mashi ba , gashi har zuwa lokacin ko 'batan wata Momma bata k'ara yiba , shiyasa Suka dauki duk wani so da kauna suka d'ora akan Hisham , Hisham yarone mai tsananin hak'uri da tarbiya , da wuya kaga fad'anshi , sai in ta 'baci amma yanada zuciya da rik'o sosai , sannan baya yafiya ga duk wani wanda yaci amanarsa , Yana tsananin son iyayenshi fiye da komai a rayuwa ,kamar yadda suma suke kaunarahi da alfaharin samun d'a kamarshi, Lokacin da takardun shi suka fito sunyi kyau sosai wannan yasa bai dauki lokaci ba ya jona karatunsa na digree a fannin computer, Yau ma kamar kullum ya dawo a gajiye saman mashin dinshi bayanshi kuma Ibrahim ne Abokinshi , wanda sau da yawa zaka gansu tare in baya gidansu Ibrahim to Ibrahim yana gidansu, sun shak'u sosai wanda har hakan yasa iyayensu suka kulla zumunci mai k'arfi a tsakaninsu, "Assalamu alaikum Momma! Momma , tun daga harabar gidan yake k'walamata kira har ya shigo cikin falon , ganin bata falon yasa yakoma bud'e murya yana fadin " Momma wai kina ina ne"? Fitowa tayi daga kitchen dafe da kanta ,tana zabga mashi harara tace "wai kai *shalele* sai yaushe zaka girma ne" "Sai sanda kika haifamun k'ane Momma " Yafad'a Yana dariya , Ibrahim ma dariyar yake don inda sabo yasaba da rigimar Momma da Hisham Harararshi tayi tace " Aikuwa sai dai karka girma d'in don Ni yanzu bawata haihuwa da zanyi," "Aikuwa wallahi zansa Abbana yayi aure don Ni k'anne nakeso ,kuma kinsan in nacewa Abbana yayi aure yi zaiyi yafad'a cikin murtuk'e fuska kamar gaske," Sanin halinshi yasa Momma saurin karaya "tace kai Shalele yanzu sai kasa ayimun kishiya don dai kai baka kishina ko ," Duk yadda sukaso rik'e dariyarsu kasawa sukayi daga Hisham har Ibrahim dariya suka fashe dashi harda buga k'afa k'asa , suna mamakin kishin Momma sosai sam batason ayi mata zancan kishiya ko da kuwa cikin wasa ne , bare ita a ganinta Hisham zai iya sa Abbanshi ya k'ara aure saboda yadda yake matuk'ar kaunar yara , kuma tsaf tasan Abdurahaman zai iya yin duk abunda Hisham keso koda kuwa ita batason abun, shiyasa yake fakewa da hakan Yana zolayarta aduk lokacin da yakejin shak'iyancin shi, "Au dariyama nabaku ko, kuma wai Ibrahim harda kai kake biye mashi bayan kasan shi bawani sanin ciyon kanshi yayiba , tafad'a tana hararar Hisham ," Cikin dariya Ibrahim yace " manta dashi Momma shima wasa yake ai Abba kam shi da aure sai a lahira in anayi ," "Injiwa" cewar Abba da shigowar shi kenan yaji Ibrahim na wannan maganar , yayi maganar Yana dariya , Dariya sukayi dukkansu yayinda Hisham ya tashi da sauri ya rungume Abbanshi ,yana fadin "welcome Abba , " "Yawwa son kana lafiya, ya school ?" "Alhamdulillah Abba, Zama sukayi a kujera d'aya inda Hisham yake manne da Abban kamar wani yaron goye, har k'asa Ibrahim ya duk'a ya gayar da Abba , kamo hannunshi Abba yayi yana amsawa yace " tashi mana Ibrahim zauna anan ya nuna masa kusa dashi inda sukasa Abban a tsakiya , fira suka ci gaba dayi inda Momma Takoma kitchen don k'arasa girkinta , Kallon Ibrahim Abba yayi yace Ibrahim kana kallona da abokinka sam yakasa cikamun burina ko , nayi lallashi har nagaji amma yaron nan ya kafe akan ra'ayinshi , nikuma harga Allah bani wani buri irin naga Hisham ya gajeni , ina matukar son wannan aiki nawa , shiyasa nayi sha'awar ace Hisham ya gajeni ta hanyar yin *aikin dan sanda* yazamo kamar Ni , kuma nasan a yadda yake da k'wazo da jajircewa zai zamo abun alfahari ga k'asarsa amma ina sam yakasa gane hakan ya kafe akan shi doli computer zai karanta , " "Ayi hak'uri Abba asa mana albarka akan wannan din, tunda nima ba yadda banyi dashi ba akan ya daure yayi aikin nan kodon ya faranta maka amma ya kafe akan bayaso " "To shikenan Ibrahim Allah yasa hakan shi yafi alkhairi," "Amin dai Abban shalele ,Gara da Allah yasa bayason aikin nan , don Ni bashi ba wallahi ko kai da zakaji ta tawa da kabar aikin nan don sam babu kwanciyar hankali acikinshi ,mutum kullum cikin yimaka barazana ake amma ka kasa ganewa sai so da kakeyi ka dora d'anmu akai to bazai yiwuba wallahi naji dadin da baya ra'ayin wannan aikin , " cewar Momma , Murmushi Abba yayi yace "Maryam kenan abinda nakeso ki fahimta shine shin idan har mukace zamu zuba idanu munaji muna gani ana zalunci a gari taya zamu samu zaman lafiya da kwanciyar hankali , idan har muka sanya tsoro a zukatan mu taya k'asa zatayi alfahari damu amatsayinmu na masu kare lafiyar al'umma har wasu su gani suyi koyi damu , babu sanda k'asarmu zataci gaba kenan matukar mukace zamu tsaya tsoron kar wani abu yafaru damu yayi tasiri a zukatan mu , k'asarmu cike take da azzalumai kala kala , babu wani babban laifi da ba'a mayar dashi ruwan dare ba a k'asar nan ,kisan kai , cin hanci nashawa, matsalar fyade, fashi da makami , satar mutane, wasu ayi garkuwa dasu wasu ayi tsafi dasu , shaye shaye ,abubuwa da yawa wanda in Zan lissafa maki su sai mu kwana munayi , kuma duk abubuwan nan zakiyi mamakin idan aka ce maki duk dasa hannun manyan mu akeyi abun takaici manyan mu su suke lalata mana yara ta hanyoyi da dama su suke kawo masu kayan shaye shaye, makaman da suke fashi ko satar mutane haka lokacin siyasa zasu dibe makamai subama matansanmu surinka fad'a da junansu suna kashe junansu alhali su yaransu nacan kasashen waje suna holewarsu mu nan suna lalata mana tarbiyar yara suna amfani dasu wajan cimma burinsu ,kuma da sunci za'ben nan bazasu sake bi takansu ba sai kuma in wani zaben ya tashi ,munada matsala fannin ilimi fannin lafiya dakuma fannin tsaro wanda cin hanci da rashawa yasa munkasa samun cigaba a k'asarmu , abun nan nacimun tuwo a kwarya wallahi wannan yasa muka kafa wata k'ungiya ta sirri a tsakaninmu insha Allah zamuyi yak'i da masu gur'bata mana yaranmu zamu kawo gyara insha Allah zamuyi kokari sosai wajan ganin mun fahimtar da matansanmu halin da suke ciki ko Allah zaisa. Su farka , inkuwa kanemi yimana taurin kai to tabbas zaka fuskanci hukunci daidai da abinda ka aikata , kedai kici gaba da tayamu da addu'a insha Allah ba abunda zai faru , dama can mafi yawa barazana ce kawai ba abunda zasu iya yi mana, "To shikenan yaya Allah ya taimakeku akan niyarku ta alkhairi , Ni wallahi ba abunda yake damuna yanzu kamar yawan fyaden nan da akeyi ba manyan ba ba yara ba Allah dai yasa mufi Ζ™arfin zuciyoyinmu , duk suka amsa da Amin, Tunda aka fara maganar baice komai ba saida jikinshi yayi sanyi sosai tabbas yasan gaskiya mahaifinshi yake fada , k'asarmu tana buk'atar nagartattun Jami'ai wanda zasu kawomata gyara da cigaba ,sai dai shi gaskiya sam aikin *yan sanda* baya burgeshi , Haka sukayi ta tattaunawa tsakanin Momma da Abba da Ibrahim , gogan kuwa k'ala baice masu ba , dama haka yake wani Lokaci in Yan rashin son maganar Yana kusa, Anan sukaci abincin rana Sannan suka sake fita, _________________________ Wai Alhaji manu kana kallo wannan k'aramun k'waron yana mana wasa da hankali , mi kake tunani idan har su goga suka sanar dashi wani bau akanmu , kaima kasan asirinmu yagama tonuwa , babu wani sirrinmu da goga baisani ba , Ni banma san ta yadda akayi ya tsaya shashanci har wannan banzan ya kamashi ba , Tunda aka fara maganar Alhaji Manu baice komai ba sai faman shafa gemunshi yakeyi yana wani cije baki , Alhaji Musa yace " Alhaji manu yakamata fa kace wani abu kabarmu sai zuba mukeyi , yanzu fa gaba daya wad'an nan kayan suna hannun *yan sanda* mi kake tunani idan har suka duba kayan nan sukaga abunda ke ciki , sannan babbar matsalar itace Goga , ina jin tsoron yaji wuya ya fada masu gaskiya, Gaskiya Yakamata asan abunyi , don nidai komai za'ayi karku yarda sunana ya fito ciki , yafad'a Yana huci zuciyarshi kamar zata fito tsabar bacin rai, Gyaran zama Alhaji Manu yayi cikin muryarshi mai kama da ganga yace " kai kolo kiramun wayar inspector Haruna, " Cikin wata k'atuwar Murya yace " angama mai gida" kana jin muryarshi kasan acikin maye yake sosai , sai wani lumshe ido yakeyi, "Mikake nufi ne Alhaji Manu , kasan abunda kake fada kuwa , ? Inspector Haruna fa kace , kokasan duk wani k'ulli da Inspector Abdurahaman yakeyi tare sukeyi da Inspector Haruna, " Wata mahaukaciyar dariya Alhaji Manu ya bushe da ita yace " ba abunda bansani ba Alhaji Musa , Inspector Haruna namune na jima da sayeshi Ni yakewa aiki a yanzu ba k'asarshi ba don haka ku kwantar da hankalinku a wannan karon b.................kolo ne ya katseshi da cewa "Oga gashi akan layi, " Amsar wayar yayi ya kara a kunne , cikin isa yafara magana, "Kana jina ko Haruna inason a yau duk yadda za'ayi kaja abokinka zuwa wani wajan , kasan karyar da zakayi mashi ya bika zan turo maka inda nakeso ka nufa dashi kuma ka tabbar kayi aikinka cikin taku don kasan halinshi kamar mai gani har hanji nikuma kasani sam ban yarda da kuskure ba, " Angama ranka ya dade yadda kace haka za'ayi ina saurarenka sai ka turo daga haka sukayi sallama suka kashe wayar , Ajiye wayar Alhaji Manu yy yana wani murmushin mugunta yace "kuje kuyi baccinku harda munshari a yau matsalar mu tazo karshe ,.................✍🏼 🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴 *Shin yar uwa ko kinsan illar da sanyi (infection) yake da ita ajikin mace kuwa* Sanyi yanada matukar illa ajikin mace fiye da tunaninki yar uwa , kina iya kamuwa da ciyon sanyi ta hanyar yin fitsari a inda mai ciyon tayi fitsari ko rashin tsabtar banΙ—aki, haka mace tana sanyawa mijinta kamar yadda shima mijin zai iya sa mata ciyon so da yawa wata tun tana k'arama zakiga tana fama da wannan matsalar ta infection sai dai da yawa bazai bayyanaba sai tayi aure, Ciyone da yake hana ma'aurata jin dadin rayuwarsu ta aure yana dauke duk wata ni'imar mace yana bude gaban mace yana hana mace sha'awa yana hanata jin dadin saduwa yanasa mace ciyon mara Wanda in yy yawa yana hana mace haihuwa , Yakamata mu tashi tsaye yan uwa don yak'i da wannan babbar cuta da ta addabi mata, Kadan daga cikin alamominshi Jin zafi lokacin saduwa ko bayan saduwa K'aik'ayin gaba Kurajen gaba Fitar ruwa masu mabanbanta launi, Rashin sha'awa Bushewar gama Da sauransu , Wanan yasa mukazo maku da sahihin maganin sanyi yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci yana wankin duk wani dattin mara yana maganin ciyon mara sosai duk wata mai matsalar sanyi ta jaraba wannan ingantaccen maganin zatarabu da matsalar sanyi da ikon Allah don neman karin bayani 09035027743 don Allah sis in baki shirya siyaba karki nemeni kibari sai kin shiryaπŸ€—πŸ€— Mmn yusup ceπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ-12 ..................daga Alhaji musa har Alhaji Buba dariya suka fashe da ita , cikin matuk'ar jin d'adi da jinjinama Alhaji manu don sun san tunda har ya fad'a masu hakan to tabbas yasamo masu mafita , "Da kyau alhaji manu aikinka yana kyau , shiyasa nakeson aiki tare da kai , da fatar kad'a manashi zakayi inda ba'a dawowa , don wallahi gayen nan ba k'aramun samana ido yayi ba , bazai ta'ba k'yalemu ba ,gashi narasa abunda yasa *yallabai* yakasa saukeshi akan muk'aminshi bayan yana kallon irin 'barnar da yake mana ," cewar alhaji musa , Dariya alhaji manu yayi yace akwai dalilin da yasa *yallabai* ya zuba mashi idanu amma yanzu komai yazo k'arshe , sai dai in yaje lahira yaci gaba da aikin acan , " Gabad'aya dariya suka fashe da ita tareda tafawa , alhaji Buba yace "Kai amma Alhaji manu gaskiya ka iya sharri wato ma a lahira zaici gaba da aikin nashi kenan ,yafad'a yana dariya," "Kwarai kuwa" Cike da farinciki sukaci gaba da k'ulle-k'ulle su ganin sun samo mafita , --------------------------------------- Kwance yake a falon akan kujera sai faman latse latse yake a waya , fitowa momma tayi daga bedroom dinta , Kallonshi tayi tace "Wai kai kam shalele hannunka baya gajiya da latsar waya ne , ? ayita abu babu gajiyawa sai kace ibada , akan wayar nan ko abincin kirki baka iya zama kaci , wai nikam mi kakeyi acikin wayar ne, ? Dariya Hisham yayi yace kai momma kullum sai kinmun magana akan wayar nan , "Yawwa wai har yanzu Abbana bai dawo bane tun d'azu fa shi nake jira " "Nima bansan abunda ya tsayar dashi ba yau tun dazu nake zuba idon ganinshi don yacemun bazaijima ba amma kaga shiru, k'ila akwai abunda ya tsayar dashi," cewar momma, "To nidai zanje gidansu Ibrahim zan duba mamanshi batada lafiya nasan kamun na dawo ya dawo akwai maganar da nakeson muyi dashi , " Hajiya Rabi ce ba lafiya amma shine baka gayamun ba d'an nan , wai miyasa kake hakane ai danasani da naje dubata ko" 'Dan yatsina fuska yayi yace kiyi hakuri momma na manta ne " "Ai haka zakace tunda kai kullum cikin mantuwa kake , sam baka daukar komai da muhimmanci shiyasa in an tambayeka sai kace ka manta to ka gaishemun da ita kamun nazo" "To momma sai nadawo in Abbana ya dawo kice ya jirani plss" daga haka yajuya yafita daga falon , ------------------------------------- Banda Ihu ba abunda yakeyi ,kamar zai tada wajan , Daure yake hannu da k'afa yayinda suka juyar da kanshi zuwa k'asa k'afafuwanshi suna sama a d'aure ,kwana ukku kenan da ake gana mashi azaba amma dayake mutum ne mai matukar taurin k'ai da kafiyar tsiya sam yak'iyin bayani, Ruwa masu matukar sanyi d'aya daga cikin jami'an dake wajan ya dauko cike da boket suka kwara mashi su wanda haka yayi sanadiyar farfad'owarshi a firgice sakamakon suman da yayi saboda wahalar da yakesha , bai gama dawowa hayyacinshi ba d'aya daga cikinau yacire belt yafara dukanshi dashi iya karfinshi , ai kuwa nan ya buga wani uban ihu yana rok'onsu akan su daina dukanshi, Zaune yake cikin office dinshi banda zarya ba abunda yakeyi gaba daya ihun wannan wawan ya hanashi sukuni , yarasa wane irin mutum ne haka mai matuka kafiya kamar mutanen farko, tsaki yaja.cikin matukar 'bacin rai da gajiyawa ya juya yabar office din nashi ya nufi inda ake dukan wannan mutumin, Duk abunda ke faruwa Inspector Haruna yana kallo ,gaba daya baya cikin nutsuwarshi ganin irin yadda ake azaftar da Goga ,yana matukar jin tsoron goga yafara gajiyawa ya fad'a masu gaskiya, gaba daya yakasa zaune yakasa tsaye , Yana haka ya hango fitowar inspector Abdurahaman a harzuk'e ya nufi inda ake dukan goga , Hankalinshi ne yayi mugun tashi nan da nan yafara tunanin abunda zaiyi don ganin ya dakatar da Abdurahaman daga zuwa wajan ,don inhar ya kar'bi ragamar azaftar da Goga wallahi komai zai iya faruwa don mutum ne da yasan duk wata makasar mutum cikin kankanin lokaci zai iya gigita tunanin goga, DA sauri ya fitar da wayarshi ya kira alhaji manu , a hankali ya Fara magana , "Maigida akwai matsala fa , yanzu haka inspector Abdurahaman ya shiga wajan da aka kulle goga ana gana mashi azaba ,yakamata kayi wani abu don in har yajima aciki to komai zai iya faruwa , " Daga can 'bangaren da sauri alhaji manu ya mik'e tsaye batare da yace komai ba ya tsinke wayar da sauri , sannan yafara kiran wata numbar , Daga can 'bangaren aka dauka tare da cewa "hello" Hello sir yakamata kayi wani abu yanzu akace wannan mayen nacan ya tsare goga da tambayoyi, "What? Okay zan san abunyi yanzu , aka fad'a daga d'ayan 'bangaren sannan ya kashe wayar ,kiran inspector Haruna yayi sunjima suna magana kamun sukayi sallama , ***** Tsaye yake ya tsare Goga da manyan Idanunshi masu rikita marasa gaskiya , kallo daya Goga yayi mashi jikinshi yafara rawa saboda tsabar k'warjinin da allah yayi mashi , sun jima suna kallon kallo a tsakaninsu kamun a hankali Goga ya sadda k'anshi k'asa don sam yakasa jurar kallon shi zuciyarshi sai d'al-d'al takeyi , Takowa yafarayi a hankali ya nufi inda aka daure Goga yayinda duk wani taku da zaiyi daidai yake da bugawar zuciyar Goga , yana zuwa kusa dashi ya tsugunna dai dai wajan kanshi dake lilo yasa hannunshi da damk'i sumar kanshi ,hakan yayi daidai da kiran wayarshi da akayi , ganin wanda yake kan layin ne yasa ya mik'e da sauri tareda k'ara saita kanshi sannan ya dauki wayar, "Hello sir " ya fad'a , bansan abunda aka ce mashi ba sai k'amewa yayi tareda cewa "okay sir " juyawa yayi da sauri ya fita daga wajan , barin office d'in yayi gaba d'aya ya dauki motarshi yabar station d'in, Ajiyar zuciya Goga yayi cike da jin dad'in tafiyar gayen nan (kamar yadda suke fada mashi) yayi imani wannan aikin oganshi ne don haka duk da yanashan matuk'ar wahala to zai k'ara dagewa don yasan bazasu ta'ba barinshi a hannun police ba doli zasu fitar dashi, Sai misalin k'arfe 11pm ya kamo hanyar gida ................✍🏼 *kuyi hkr banso na tsaya anan ba amma aiki yahana nayi maku da yawa amma insha Allah Gobe zanyi maku* *KWANCIYAR SAMUN CIKI* πŸ…°οΈkusan kowanne namiji lokacinda yayi inzali yana fitarda kwayoyon halitta sama da 1,000,000 saidai yayinda allah ya kudira za'a samu ciki dayane ke shiga mahaifa don zama dan adam amma duka sauran zuba yakeyi, πŸ…°οΈkwai yanayin kwanciya kuma wanda lokacinda na miji yayi inzali baya shiga mahaifa harma wasu suna daukan hakan amatsayin tazarar iyali wato mace ta hau kan namiji yayinda yake kwance wannan lokacin maniyi yakan dawo amma wannan be ingantaba don ana samun kuskure, πŸ…°οΈkusan kashi tamanin cikin dari (80%) na mata nan take maniyi ki zuba daga jikinsu koda kuwa wacce irin kwanciya akayi da zaran namiji yayi inzali to zataga maniyin yana zuba wasu kuma matan sai daga baya wannan kuma baya hana mace samun ciki domin lokacinda allah ya hukunta samun cikin to kwayar halittar zata shiga, πŸ…°οΈmma fa wasu daga cikin mata namiji yakanyi inzali amma babu wani abu dake zuba wajenda ta tashi kamar babu abinda akayi wannan yana zubane lokacin fitsari saidai kalilan ne daga cikin mata masu wannan baiwar, kankantar gaba bayada nasaba da rashin samun ciki domin masana sun tabbatar indai gaban namiji zai shiga da 2 inch tana iya samun ciki koda kuwa bata gamsuwa dashi saidai idan ya gaza haka ne to wannan baya cikin maza masu al'aura bazaiyu mace ta samu ciki ta dalilin saduwa dashi ba, πŸ…°οΈn tabbatar mace ko namiji akwai mataki da ciwon sanyi zaikai inda zai hana samun ciki, kamar ita mace zai hana maniyin namiji shiga mahaifarta, yayinda shi kuma namiji maniyinsa zai tsinke sosai ya zama kamar ruwan famfo har ma kwayoyin halittarsa su mutu bazaiyi ya bawa mace cikiba, *Muhadu a gobe insha Allah*πŸ₯° [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_13 ..................zaune ya tadda Momma akan darduma tana karatun Alkur'ani , da sallama yak'arasa shiga falon fuskarshi dauke da murmushi , saida takai aya sannan ta d'ago da kanta cikin yanayin fara'a ta amsa sallamar tashi tareda yi mashi Barka da zuwa , Amsawa yayi yayinda yake zama kan kujera , tashi tayi taje ta ajiye Alkur'anin acikin wata loka sannan ta dawo inda yake , duk'awa tayi a hankali tafara cire mashi takalmin k'afarshi tare da safa ta ajiye gefe sannan ta gyara zamanta tafara matsa mashi kafafun ,lumshe idonshi yayi a hankali lokaci daya yaji duk wata damuwarshi ta yaye duk zafin da kanshi ya dauka wajan aiki sai gashi a hankali yanajin kamar bashiba , A hankali ya furta " miyasa har yanzu bakiyi bacciba , ba nace ki daina tsayawa jirana har wani lokaci baki kwanta ba bayan kinsan cewa kinada buk'ar hutu sosai ," "Hmmm kai ma dai Abban shalele kasan cewa bazan iya kwanci ba tare da naga dawowarka cikin gidan nan ba koda kuwa zaka kai karfe biyu na dare , sai dai idan na tabbatar da bazaka dawoba kana aikin dare wannan ne kawai zaisa na kwanta amma in dai nasan zaka dawo to kuwa doline in jiraka ko karfe nawa zaka kai, Murmushi Abba yayi yanajin wani son matarshi na K'ara ratsa jijiyoyin jikinshi saboda irin yadda take tsananin bashi kulawa kamar wani yaron goye , duk da shekaru sunja har gashi sun ajiye saurayi amma sam hakan baisa ta daina bashi kulawa kamar yadda tasaba ba kullum zaka samesu cikin farinciki kowanensu kokari yakeyi yaga ya farantawa d'an uwansa , rik'o hannunta yayi yace zo muje kiji wata magana , Murmushi kawai tayi ta kama hannunshi ta mike suka nufi bedroom din Abba , Ba k'aramun faranta ran junansu sukayiba a wannan dare wanda bazai taba gogemasu ba acikin kundin tarihin rayuwarsu , darene da suka faranta ran juna kamar zasu had'iye juna , sunajin wani irin farin ciki kamar wasu sababbin aure , har karfe 2:30am idonsu biyu sai daga bayane suka tsarkake jikinsu sannan suka fara sallar nafilfili , sai da sukayi sallar asuba sannan suka kwanta bacci ,aikuwa bacci mai nauyi ne yayi awon gaba dasu , da yake weekend ne shiyasa suka shari baccinsu hankali kwance , Misalin k'arfe 9am yunwa ta fito da Hisham daga dakinshi don dama shikam sam baya wasa da cikinshi , direct dinning ya nufa , amma mi sai ganin table din yayi wayam ba komai akai , d'an 'bata fuska yayi don Allah yagani matsananciyar yunwa yakeji, turo dan bakinshi yayi gaba kamar wani k'aramun yaro yafara k'unk'uni yana cewa "Oh wai tsoffi ma sun iya soyayya dubi har yanzu wai Momma bata dora girki ba ko sai yaushe zamu karya yau? Yayi maganar Yana rik'e ha'ba , " "In kaji haushi kaima sai kayi auren ai " Yaji an fad'a a bayansa , juyowa yayi yana d'an sosa kanshi yace "Barka da safiya Abba an tashi lafiya" "Lafiya qalau son an Gama tsegumin mu ?" Dariya Hisham yayi yace to ai Abba.... bari dai kawai yafad'a Yana dariya " "Shak'iyin yaro ai da ka fad'a kawai tunda ka mayar damu wasu sa'anninka , yanzu dai maza ka shiga kitchen ka sama mana abunda zamuci don Maryam tana bacci kuma baza'a tasheta ba sai ta tashi da kanta" Turo baki Hisham yayi kamar zaiyi magana sai kuma yafasa ya tashi ya nufi kitchen din Yana Dan babbuga k'afa k'asa K'amar wani k'aramun yaro, Da kallo kawai Abba ya bishi yana murmushi , tsakanin Maryam da Hisham baisan wayafi so ba yana masu wata irin soyayya mai matukar zafi , don a halin yanzu bashida wanda ya kaisu sune duniyar shi yana fatan Allah ya tsare mashi su ya kauda idon mak'iya daga kansu don ya sani sosai ake bibiyar rayuwarshi kawai Allah ne bai basu Sa'a akanshi ba har yau , Hisham kuwa sai mita yakeyi a kitchen don yunwa yakeji sosai cikinshi sai k'ugii yakeyi, dankali ya soya da k'wai ya dafa ruwan zafi ,sannan ya dauko sauran farfesun da Momma tayi masu jiya da dare ya d'umama sannan ya kwaso kayan ya kawo kan table Hisham ya iya kalolin abinci sosai kasan cewar duk lokacin da Momma zatayi aikin tare dashi takeyi yana tayata , tun yana k'araminshi har kawo yau indai yana gida to zaka sameshi tareda Momma yana tayata aiki , wani lokaci ma har shara da wanke wanke shi yakeyi kamar wani mace ,har wannan lokacin Abba yana zaune Yana duba jarida , Juyowa yayi da sauri jin yadda k'amshin abincin ya bugi hancinshi , dama shima yunwar ce ta tayar dashi daga bacci , murmushi yayi yace "sannu da aiki Son Bari na taso na cika cikina ," Dariya Hisham yayi yace " Abba bazaka jira Momma ba yau kai kadai zakaci abincin ne," "Babu ruwanka d'an sa ido " cewar Abban lokacin da yake zama kan kujerar , dariya kawai Hisham yayi baice komai ba yafara zuzzuba masu dankalin da wainar kwai tayi kyau har tagaji sai kamshi ke tashi, sannan ya haΙ—a masu tea suka fara karyawa , sunaci suna dan ta'ba fira da wasa da dariya in ka gansu sai ka dauka abokai ne , "Sannunku wato kuna nan kuna karyawa kun manta dani ko" cewar Momma da tun dazu take tsaye tana kallonsu cike da so da kauna tana alfahari da mijinta dakuma d'anta kallonsu kawai yana sanyata cikin farinciki , Da sauri duk suka kalli inda take , taci kwalliya sosai tayi d'as abunta kai bazakace ta ajiye kamar Hisham ba , tashi Hisham yayi ya riko hannunta yana cewa "zo muje Momma ki karya Abba ne yace wai mu k'yaleki muci abunmu," hararshi tayi bata ce komai dagashi har Abban dariya sukayi mata , gaida Abban tayi sannan Hisham ya gaisheta daga nan ya hada mata nata abincin tafara ci , haka suka gama cin abincin suka koma kan kujerun falon suka zauna sunata fira cike da annashuwa , haka suke ko yaushe kowaye yazo gidan sai wannan family ya burgeshi saboda yadda suke matukar bawa junansu kulawa kullum zaka samesu cikin farinciki da wasa da dariya, Kallon Hisham Abba yayi yace Son anfara siyar da form na *aikin dan sanda* har na siya maka ma na mantashi a office Amma gobe zanzo dashi sai ka cike ko? Yayi maganar Yana kafeshi da ido, Tunda yafara maganar banda kallon Abban ba abunda yakeyi acikin zuciyarshi kuwa mamakin dalilin Abba na kafewa sai ya gajeshi da aikin *dan sanda* yakeyi ,miye acikin aikin inbanda wahala kullum sukenan basu nan basu nan wajan kama tantiran masu laifi duk don su samu k'asarsu ta gyaru kamar sauran k'asashe amma abun yana tashi a banza ,duk girman laifin da mutum zai aikata ga hujja da kwararan shaidu kiri kiri amma hakan bazai hana manyan mu shige da fice don ganin an saki wannan mai laifin ba saboda duk wani babban laifi da ake aikatawa mafi yawa zaka samu da hannun manyanmu aciki , haka kwanaki kiri kiri a unguwar su aka kama wani matashin saurayi da yara sama da biyar ya sacesu yana shirin hallakasu aka kamashi amma abun takaici ko sati baiyi ba aka rufe case din aka sakeshi, to in irin haka na faruwa tun farko miye amfanin kamashi kenan taya za'a samu wani cigaba ,in hakane miye amfanin aikin ma gaba daya ,shi wannan abun naci mashi rai sosai ba komai yasa yake k'in aikin *dan sanda* ba saidon wallahi in ya shigeshi abubuwan da zasu faru ba masu kyau bane don duk wanda ya kama da aikata babban laifi irin na kisa ko fyade bare kuma satar yara wlh zai iya kashe mutum komai za'ayi sai dai ayi , wannan dalilin ne yasa yak'i yarda ya karbi tayin Abba don bafa zai iya dagawa kowa k'afa ba , yayi zurfi acikin tunanin da yakeyi gaba daya idonshi sun kada sunyi jajir ga jijiyoyin kanshi duk sun tashi sunyi rida rida gaba daya fuskarshi ta sauya tayi jajir alamar ranshi ya Ι“aci matuk'a, gefe daya Kuma wani irin tausayin Abbanshi ne ya kamashi , ya tsaya kai da fata yana aiki bisa gaskiya da amana duk da burin samun cigaba ga k'asarsu amma kullum abun k'ara ta'bar'barewa yake , Hisham yanada hakuri da fara'a uwa uba wasa da dariya to ammafa yanada matukar fushi idan ranshi ya Ι“aci komai zai iya aikatawa , shiyasa yake dannar zuciyarshi ba kasafai yafaye bari wani abu ya bata ransa ba, Gaba daya iyayen kallonshi sukeyi suna ganin yanayinshi sun san ran yan maza ya 'baci shiyasa ba wanda ya sake mashi wata magana , A hankali ya tashi baice komai ba yabar falon dama gidan baki daya, Ajiyar zuciya suka sauke a tare , cikin sanyin jiki Momma tace " wai Yaya miyasa kakeson sai yaron nan yayi aikin nan na police miyasa bazaka rabu dashi yayi abunda yakeso ba , Ni banga abunda yake cikin aikin ba wanda har zakayi ma danka sha'awar shiga ciki banda tashin hankali miye aciki , Ni wallahi ko kai da zaka taimakeni da ka ajiye aikin nan , " Murmushi kawai Abba yayi yace " to shikenan uwar gida daga yau bazan sake yiwa danki wannan maganar ba tunda naga kamar kinfi sonshi dani" Dariya tayi tace "daka kyautamun kuwa Ni da zaka taimaka ma da har kai ka ajiye aikin da zanyi farinciki marar misaltuwa, "Hmmm bazaki gane ba Maryam kanki kawai kika sani shiyasa amma idan har jami'ai masu gaskiya sukace su ajiye aikinsu saboda tsoron abunda zaije yazo to ta Ina kk tunanin zamu samu ci gaba , ai daga lokacin kasarmu zata kara shiga rudu da tashin hankali kowa zaiyi abunda yakeso tunda babu wanda ,zai taka masu birki , amma idan har muka jajirce sai kiga zuwa gaba komai yazama tarihi mun koma kamar sauran k'asashen da sukaci gaba wanda akullum haka muke fata , " To shikenan Abban shalele Allah ya dafa maku ya shige maku gaba ya tsare ku daga dukkan sharri na mutum da aljan , " Ameen my dear haka nakeson ji , yanzu zan dan fita zanje office ne akwai inda zamuje da inspector Haruna tun jiya yake damuna amma bazamu jimaba zamu dawo insha Allah, "To shikenan.allah ya tsare ya dawo dakai lafiya , " "Amin amin ya Allah ki lallasarmun dan lelen naki kamun na dawo nasan yayi fushi Dani sosai , "Ba ruwana wannan tsakaninku ne ta fada tana dariya" Har ya kai bakin kofar sai kuma ya dawo janyota yayi jikinshi ya sumbaci goshinta kamun yamata wani irin kallo sannan ya daga mata hannu yasakai ya fita , Tajima tsaye a wajan kamun tayi murmushi ta koma cikin falon direct kitchen ta nufara tafara kokarin hada masu abincin rana, *********************** Sama da minti 30 suka shafe suna tafiya akan titin , yayinda inspector Haruna ke tukin motar Abba kuma na gefenshi yana karanta jarida , a hankali ya ajiye jaridar ya d'ago da kanshi ya dubi inspector Haruna yace " wai Haruna ina muka nufa ne , Ni nakasa gane inda zancanka ya dosa , shi wanda kace ya kiraka d'in akan muzo zai bamu wani sirrin kana da tabbacin ba tarko ya had'a mana ba , in har yanada gaskiya mi zai hana ya samemu a office a maimakon yace mu muje musameshi , " "Ai ranka ya dade ya gayamun cewa bayason yaje ofishinmu ne saboda duk wani motsinshi ana sane komai zai iya faruwa dashi idan har akasan cewa yabada wata masaniya akan su Alhaji Musa, wannan yasa nace to ya bari mu zamuzo wajanshi sai muyi magana, Wani banbarakwai Abba yaji zancan don gaba daya baiji ya gamsu da bayanin Haruna ba , d'an musk'utawa yayi yace "koma dai minene banajin akwai alkhairi a tafiyar nan ,ina ji ajikina kamar wani tarko ne kawai , " Jin hakan yasa gaban Haruna faduwa da kyar yasamu ya daidaita nutsuwarshi gudun karya ganoshi , yasan waye Abdurahaman mutum ne mai saurin fahimtar abu ko yaya kake da rashin gaskiya to zai iya ganoka , "Cikin inda inda yace to ranka ya dade ko mu juya ne ? tunda kanajin tsoro" "Ba tsoro nakeji ba jikina ne yake bani babu alkhairi a tafiyar nan amma muje Allah ya shige mana gaba, " Ajiyar zuciya Haruna ya sauke don yaji tsoron kar yace su koma , Shiru ba wanda yakoma magana acikinsu har wani tsawon lokaci , har suka zo inda suka shirya kulla-kullarsu , Suna zuwa daidai wajan wani waje mai tudu da rafi waje ne da gefe da gefen titin suke da gangara sosai suna zuwa dai dai wani icce wanda dama dashi sukayi alama ba zato ba tsammani sai gani Abba yayi inspector Haruna na kokarin bude murfin motar bayan kuma ga motar tana gudu , kamun ya bude baki yayi magana har Haruna ya bude gambun motar yafad'a waje aikuwa kamun kace mi yafara gangara lokaci d'aya ya haΙ—awa kanshi jini da majina kamun ya bugi wani katon dutse dake wajan lokaci daya ya some a wajan, Abba kuwa ganin fitar Haruna ba k'aramin daga mashi hankali yayi ba ga motar na gudu cikin tsananin zafin nama yayi wata sufa sai gashi a kujerar mai tuk'i duk a kokarinshi na ganin ya tsayar da motar , kamun yayi hakan kuwa tuni wata k'atuwar mota ta nufoshi gadan gadan bai ankaraba sai ganinta yayi ta nufoshi aguje , ganin tana daf da k'arasowar wajanshi ne yasa ya runtse idanunshi da sauri tareda ambatar *La'ilaha illallah muhammadun Rasulullah* kamun k'yaftawa ido wasu hawaye Masu zafi da k'una sun wanke mashi fuska , duk da yana cikin wannan bala'in saida ya hango fuskar tilon danshi dakuma salihar matarshi , aikuwa kamun yagama dawowa duniyar da ya tafi tuni motar nan tabi ta kanshi ta take sannan direban ya dawo ya bugi motar da k'arfi tuni itama motar ta fara gangarawa gefen titin .........................✍🏼 *Sanarwa sanarwa sanarwa* *Daga yau littafin jami'in dan sanda yakoma na kud'i saboda rashin comment dinku sam bana samun kwarin gwuiwa akan book din nan bansani ba ko salon labarin ne baimaku ba to zan sani a yanzu in har Kuna tare da wannan littafi ga mai bukata zata iya neman ta wannan numbar 09035027743* Kudin littafin 200 ne kacan 🀝🏼 *SIRRIN WANKIN MARAH*πŸ‘©πŸ»β€πŸ¦°πŸ‘©πŸ»β€πŸ¦° πŸ…±οΈabbar hanyar samarda ni,ima ta hanyar aiki da abincin gargajiya na gida, wanda shidai wannan tsumin asalinsa wanke mara yake musamman mata wadanda ni,ima ke basu matsala ta sanadin toshewar mara, wanda zakaga mace tasha tsumi, da garin ni,ima masu kyau amma ta kasa ganin ni,ima da wuri, to ackin hanyoyinda akebi don samarda ni,ima harda wanan hanyar wanda ta inganta koda mace tanada ciki zata iya amfani dasu, anaso asha sau biyu wato safe da yamma, a wuni daya, πŸ…±οΈabban abunda zaki fara shine ki wanke aya sannan saiki jika sai kuma kisamu gyada danya, saiki zuba musu ruwa kadan wanda adadinsa be wuce lita dayaba, daga nan saiki gurza kwakwa aciki, ki saka kanunfari kadan, saiki yanka lemon tsami daya sannan ki bari su jika saiki markada, sannan ki tace, acikin ruwan zaki jefa mazar kwaila koda dayane wato rabin kifi amma babba, shikenan ki jira dan wani lokaci tana jika kin kammala. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_13 ..................zaune ya tadda Momma akan darduma tana karatun Alkur'ani , da sallama yak'arasa shiga falon fuskarshi dauke da murmushi , saida takai aya sannan ta d'ago da kanta cikin yanayin fara'a ta amsa sallamar tashi tareda yi mashi Barka da zuwa , Amsawa yayi yayinda yake zama kan kujera , tashi tayi taje ta ajiye Alkur'anin acikin wata loka sannan ta dawo inda yake , duk'awa tayi a hankali tafara cire mashi takalmin k'afarshi tare da safa ta ajiye gefe sannan ta gyara zamanta tafara matsa mashi kafafun ,lumshe idonshi yayi a hankali lokaci daya yaji duk wata damuwarshi ta yaye duk zafin da kanshi ya dauka wajan aiki sai gashi a hankali yanajin kamar bashiba , A hankali ya furta " miyasa har yanzu bakiyi bacciba , ba nace ki daina tsayawa jirana har wani lokaci baki kwanta ba bayan kinsan cewa kinada buk'ar hutu sosai ," "Hmmm kai ma dai Abban shalele kasan cewa bazan iya kwanci ba tare da naga dawowarka cikin gidan nan ba koda kuwa zaka kai karfe biyu na dare , sai dai idan na tabbatar da bazaka dawoba kana aikin dare wannan ne kawai zaisa na kwanta amma in dai nasan zaka dawo to kuwa doline in jiraka ko karfe nawa zaka kai, Murmushi Abba yayi yanajin wani son matarshi na K'ara ratsa jijiyoyin jikinshi saboda irin yadda take tsananin bashi kulawa kamar wani yaron goye , duk da shekaru sunja har gashi sun ajiye saurayi amma sam hakan baisa ta daina bashi kulawa kamar yadda tasaba ba kullum zaka samesu cikin farinciki kowanensu kokari yakeyi yaga ya farantawa d'an uwansa , rik'o hannunta yayi yace zo muje kiji wata magana , Murmushi kawai tayi ta kama hannunshi ta mike suka nufi bedroom din Abba , Ba k'aramun faranta ran junansu sukayiba a wannan dare wanda bazai taba gogemasu ba acikin kundin tarihin rayuwarsu , darene da suka faranta ran juna kamar zasu had'iye juna , sunajin wani irin farin ciki kamar wasu sababbin aure , har karfe 2:30am idonsu biyu sai daga bayane suka tsarkake jikinsu sannan suka fara sallar nafilfili , sai da sukayi sallar asuba sannan suka kwanta bacci ,aikuwa bacci mai nauyi ne yayi awon gaba dasu , da yake weekend ne shiyasa suka shari baccinsu hankali kwance , Misalin k'arfe 9am yunwa ta fito da Hisham daga dakinshi don dama shikam sam baya wasa da cikinshi , direct dinning ya nufa , amma mi sai ganin table din yayi wayam ba komai akai , d'an 'bata fuska yayi don Allah yagani matsananciyar yunwa yakeji, turo dan bakinshi yayi gaba kamar wani k'aramun yaro yafara k'unk'uni yana cewa "Oh wai tsoffi ma sun iya soyayya dubi har yanzu wai Momma bata dora girki ba ko sai yaushe zamu karya yau? Yayi maganar Yana rik'e ha'ba , " "In kaji haushi kaima sai kayi auren ai " Yaji an fad'a a bayansa , juyowa yayi yana d'an sosa kanshi yace "Barka da safiya Abba an tashi lafiya" "Lafiya qalau son an Gama tsegumin mu ?" Dariya Hisham yayi yace to ai Abba.... bari dai kawai yafad'a Yana dariya " "Shak'iyin yaro ai da ka fad'a kawai tunda ka mayar damu wasu sa'anninka , yanzu dai maza ka shiga kitchen ka sama mana abunda zamuci don Maryam tana bacci kuma baza'a tasheta ba sai ta tashi da kanta" Turo baki Hisham yayi kamar zaiyi magana sai kuma yafasa ya tashi ya nufi kitchen din Yana Dan babbuga k'afa k'asa K'amar wani k'aramun yaro, Da kallo kawai Abba ya bishi yana murmushi , tsakanin Maryam da Hisham baisan wayafi so ba yana masu wata irin soyayya mai matukar zafi , don a halin yanzu bashida wanda ya kaisu sune duniyar shi yana fatan Allah ya tsare mashi su ya kauda idon mak'iya daga kansu don ya sani sosai ake bibiyar rayuwarshi kawai Allah ne bai basu Sa'a akanshi ba har yau , Hisham kuwa sai mita yakeyi a kitchen don yunwa yakeji sosai cikinshi sai k'ugii yakeyi, dankali ya soya da k'wai ya dafa ruwan zafi ,sannan ya dauko sauran farfesun da Momma tayi masu jiya da dare ya d'umama sannan ya kwaso kayan ya kawo kan table Hisham ya iya kalolin abinci sosai kasan cewar duk lokacin da Momma zatayi aikin tare dashi takeyi yana tayata , tun yana k'araminshi har kawo yau indai yana gida to zaka sameshi tareda Momma yana tayata aiki , wani lokaci ma har shara da wanke wanke shi yakeyi kamar wani mace ,har wannan lokacin Abba yana zaune Yana duba jarida , Juyowa yayi da sauri jin yadda k'amshin abincin ya bugi hancinshi , dama shima yunwar ce ta tayar dashi daga bacci , murmushi yayi yace "sannu da aiki Son Bari na taso na cika cikina ," Dariya Hisham yayi yace " Abba bazaka jira Momma ba yau kai kadai zakaci abincin ne," "Babu ruwanka d'an sa ido " cewar Abban lokacin da yake zama kan kujerar , dariya kawai Hisham yayi baice komai ba yafara zuzzuba masu dankalin da wainar kwai tayi kyau har tagaji sai kamshi ke tashi, sannan ya haΙ—a masu tea suka fara karyawa , sunaci suna dan ta'ba fira da wasa da dariya in ka gansu sai ka dauka abokai ne , "Sannunku wato kuna nan kuna karyawa kun manta dani ko" cewar Momma da tun dazu take tsaye tana kallonsu cike da so da kauna tana alfahari da mijinta dakuma d'anta kallonsu kawai yana sanyata cikin farinciki , Da sauri duk suka kalli inda take , taci kwalliya sosai tayi d'as abunta kai bazakace ta ajiye kamar Hisham ba , tashi Hisham yayi ya riko hannunta yana cewa "zo muje Momma ki karya Abba ne yace wai mu k'yaleki muci abunmu," hararshi tayi bata ce komai dagashi har Abban dariya sukayi mata , gaida Abban tayi sannan Hisham ya gaisheta daga nan ya hada mata nata abincin tafara ci , haka suka gama cin abincin suka koma kan kujerun falon suka zauna sunata fira cike da annashuwa , haka suke ko yaushe kowaye yazo gidan sai wannan family ya burgeshi saboda yadda suke matukar bawa junansu kulawa kullum zaka samesu cikin farinciki da wasa da dariya, Kallon Hisham Abba yayi yace Son anfara siyar da form na *aikin dan sanda* har na siya maka ma na mantashi a office Amma gobe zanzo dashi sai ka cike ko? Yayi maganar Yana kafeshi da ido, Tunda yafara maganar banda kallon Abban ba abunda yakeyi acikin zuciyarshi kuwa mamakin dalilin Abba na kafewa sai ya gajeshi da aikin *dan sanda* yakeyi ,miye acikin aikin inbanda wahala kullum sukenan basu nan basu nan wajan kama tantiran masu laifi duk don su samu k'asarsu ta gyaru kamar sauran k'asashe amma abun yana tashi a banza ,duk girman laifin da mutum zai aikata ga hujja da kwararan shaidu kiri kiri amma hakan bazai hana manyan mu shige da fice don ganin an saki wannan mai laifin ba saboda duk wani babban laifi da ake aikatawa mafi yawa zaka samu da hannun manyanmu aciki , haka kwanaki kiri kiri a unguwar su aka kama wani matashin saurayi da yara sama da biyar ya sacesu yana shirin hallakasu aka kamashi amma abun takaici ko sati baiyi ba aka rufe case din aka sakeshi, to in irin haka na faruwa tun farko miye amfanin kamashi kenan taya za'a samu wani cigaba ,in hakane miye amfanin aikin ma gaba daya ,shi wannan abun naci mashi rai sosai ba komai yasa yake k'in aikin *dan sanda* ba saidon wallahi in ya shigeshi abubuwan da zasu faru ba masu kyau bane don duk wanda ya kama da aikata babban laifi irin na kisa ko fyade bare kuma satar yara wlh zai iya kashe mutum komai za'ayi sai dai ayi , wannan dalilin ne yasa yak'i yarda ya karbi tayin Abba don bafa zai iya dagawa kowa k'afa ba , yayi zurfi acikin tunanin da yakeyi gaba daya idonshi sun kada sunyi jajir ga jijiyoyin kanshi duk sun tashi sunyi rida rida gaba daya fuskarshi ta sauya tayi jajir alamar ranshi ya Ι“aci matuk'a, gefe daya Kuma wani irin tausayin Abbanshi ne ya kamashi , ya tsaya kai da fata yana aiki bisa gaskiya da amana duk da burin samun cigaba ga k'asarsu amma kullum abun k'ara ta'bar'barewa yake , Hisham yanada hakuri da fara'a uwa uba wasa da dariya to ammafa yanada matukar fushi idan ranshi ya Ι“aci komai zai iya aikatawa , shiyasa yake dannar zuciyarshi ba kasafai yafaye bari wani ab [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_14 .................har k'arfe biyu bai dawoba ,gaba d'aya Momma tashiga damuwa gashi sai kiran wayarshi takeyi amma a kashe ,tunani takeyi to mi ya tsayar dashi har wannan lokacin bayan yace mata bazai jima ba ,sannan ga al'adanshi ma baya fita ko ina in weekend ne wuni yakeyi a gida idan kuwa har wani uzuri ya fitar dashi tofa bazai jima ba zai dawo, Tunda ya fita daga gidan bai zame a ko'ina ba sai gidansu Ibrahim , yana zuwa ko cikin gidan baishigaba ya wuce dakin Ibrahim ciki ciki yayi sallama ya shiga dakin, Ibrahim na zaune Yana aiki a laptop dinshi yaji sallamar abokin nashi , kamun ma yayi wata magana har Hisham ya haye kan katifarshi yayi ruf da ciki batare da ya ko kalli inda Ibrahim yake ba , Ganin hakan yasa Ibrahim ya kyaleshi don yasan ko yayi mashi magana bazai kullashi ba juyawa yayi yacigaba da aikinshi , Yana nan kwance tsawon wani lokaci kamun bacci 'barawo yayi awon gaba dashi, fiye da awa biyu yana bacci kamun ya tashi a firgice yana nanata kalmar innalillahi wa inna ilaihin raji'un, cikin kankanin lokaci ya hada wani uban zufa, sai fama sauke ajiyar zuciya yake , duk sakamakon mummunan mafarkin da yayi akan Abbansa, mafarkin yayi Abbanshi na cikin wani surkullen daji mai matukar ban tsoro sai faman gudu yakeyi kamar ba gobe yayinda wasu mutane suke biye dashi da muggan makamai suna neman su kasheshi , shikuwa Abba banda gudu da kiran sunan Hisham ba abunda yakeyi har yakai ga ya k'ure hanyar ba sauran inda zai gadu ganin hakan yasa ya runtse idonshi yafara maimaita kalmar shahada , yayinda mutanen suka tsaya akanshi sai faman babbaka dariya sukeyi wanda dariyarsu ke amsa kuwa acikin dajin , daya daga cikinsu ne ya daga takobinshi ya sarewa Abba kai wanda hakan yayi daidai da k'arasowar Hisham a wajan , wani irin ihu yayi kamun yayin kan mutanen nan amma kamun yak'arasa sun 'bace 'bat babu su babu alamarsu , haka ya karasa wajan Abba aguje saidai kamun ya k'arasa ne ya farka a razane, "Lafiya dai Hisham "? Cewar Ibrahim da shigowar shi kenan ya fito daga cikin gida, Girgiza kai kawai Hisham yayi don yama kasa magana gaba daya jikinshi da harshen shi sunyi mashi nauyi ga wani bugu da zuciyarshi keyi , a hankali ya mike tsaye ya sanya takalminshi batare da yacewa Ibrahim komai ba yakama hanyar fita daga dakin, Ganin hakan yasa Ibrahim ajiye abincin da ya karbo masu wajan mamanshi ,janyo kofar dakin yayi ya rufe da sauri yabi baya Hisham don sam bai gamsu da yanayin da yagani a tattare da abokin nashi ba , Ζ™arara yake hango tsananin tashin hankali a cikin kwayar idonsa, Jiki a sanyaye yayi sallama akofar falon kamun ma Momma ta amsa mashi ya d'age labulen ya shiga, Zaune take akan kujera ta buga uban tagumi ,gaba daya jin yanayinta takeyi ba dadi saidai tarasa abinda yake damunta , shiyasa ta alamk'anta hakan da rashin dawowar mijin nata, Zama yayi ya gaisheta kamun yace " Momma Abba fa"? "Abbanka ya fita tun d'azu tun bayan fitarka amma har yanzu bai dawoba sannan nayita kiran wayarshi amma bata shiga ," tafad'a cikin matukar damuwa , Dum dum dum gabanshi yayi wani irin bugu da karfi , amma tuni ya daidaita nutsuwarshi ya zaro wayarshi yafara kiran Abban , shima dai bata shiga ba ,suna haka Ibrahim yayi sallama ya shigo , bayan ya gaida Momma ne ya nemi waje ya zauna , ganin damuwa Ζ™arara akan fuskokinsu ne yasa ya dubi Momma yace "Momma lafiya dai naga kamar kuna cikin damuwa?" Murmushin karfin hali tayi tace ba komai Ibrahim kawai muna jiran Abbanku ne ya fita tun d'azu amma har yanzu baidawoba , " "Ayya Momma kila wani abun ne ya tsareshi amma insha Allah zai dawo bada jimawa ba " "To Allah yasa , ku tashi kuje kuyi sallah sai kuzo ga abinci can kuci kamun yazo", "To Momma" cewar Ibrahim, Shikam gogan ko bakin magana baisamu ba don sosai ya tsorata da mafarkin da yayi, A hankali ya furta " amma Momma Ina yace maki zaije ne?" "Wallahi bai gayamun ba yadai ce mun zasu fita ne shida inspector Haruna" Jinjina kanshi kawai yayi sannan ya tashi ya koma dakinshi , alwala yayi yayi Sallah shida Ibrahim sannan suka koma falon Momma alokacin itama ta idar da salla kenan. Zamansu kenan sukaji ana buga get din gidan ****************** Acan 'bangaren su Abba kuwa lokacin da abun ya faru akan idon wasu bayin Allah su ukku aikuwa a firgice suka rafka salati tareda juyawa aguje suka nufi motar da Abba ke ciki , zuwa lokacin kuwa tuni mutanen dake wucewa sun fara tsayawa kamun kace mi wajan yacika da jama'a haka aka taru da kyar aka 'ban'baro Abba daga karkashin motar , gaba daya fuskarshi tayi dameji ga kafafuwanshi da hannayenshi duk sun karairaye jini kuwa yace ina bakayi bani waje tuni wajan ya jike da jini , ahakan kuwa cikin ikon Allah yana numfashi saidai in yaja numfashi sai yayi kusan minti biyu kamun numfashin ya dawo , gaba daya mutanen dake wajan suncika da tausayinshi masu raguwar zuciyar tuni sun fara kuka , ganin har lokacin yana numfashi yasa wani saurayi ciccibarshi ya sanya mota suka nufi hospital mafi kusa dasu , Sai bayan tafiyarsu ne sannan wasu suka lura da inspector Haruna yashe a kasa cikin halin suma shima nan suka kwasheshi sukabi bayansu Suna zuwa basuyi wata wata ba suka karbeshi ganin kakin 'yan sanda ajikinshi , emergency aka nufa dashi ,likitoci biyar ne akanshi suna faman ceton rayuwarsa , duk da kuwa su kansu sunsan ba lallai ne ya rayu ba ganin irin halin da yake ciki , Haka suka share sama da 30mnt kamun Allah yayi ikonsa , Allahu Akbar Allah mai yin yadda yaso alokacin da yaso duk da Abba yana cikin mawuyacin hali kuma baisan inda kansa yake ba amma Allah yabashi ikon yin kalmar shahada yayin fitar rayuwarsa wanda su kansu likitocin sunyi mamakin jin magana a bakinshi, bayan sun cire mashi kowace na'ura da suka sa mashi ne sukaja farin kyalle suka rufeshi, sannan suka fara fitowa dai bayan dai, Nan suka sanar da mutanen da suka kawo shi Allah yamashi rasuwa , Duk da basu sanshiba amma sunji mutuwarshi sosai wannan saurayin kuwa harda hawayenshi , ganin kayan yan sanda ne ajikin Abba yasa ya fito yanufi babbar HQ ta yan sanda , nan ya zayyanemasu duk abunda ke faruwa , haka aka hadashi da wasu yan sanda suka nufi asibitin, Lokacin da sukayi arba da gawar ba karamin firgita sukayi ba ganin fuskar inspector Abdulrahaman nan suka kira HQ suka fadin abinda yake faruwa , ai kamun kace mi asibitin yacika da jami'an yan sanda kota ina , masu jin dadi naji masu jin ciyon tashin nagartaccen Jami'i nayi , a haka aka tura wasu daga cikin yan sandan akan suje su sanar a gidansa , shine fa suka zo suna buga get din gidan, Jiki a sanyaye Ibrahim yaje ya bude get din, ganin yan sanda abakin k'ofar ba karamin kayar mashi da gaba yayi ba wanda baisan dalili ba, Gaisawa sukayi kamun suka ce mashi suna sallama da matar gidan ne , Jin haka yak'ara hautsina ma Ibrahim hanji , amma haka nan ya daure yace "to shikenan kushigo daga nan zanje in gayamata , " suka amsa da "to" "Momma Wai wasune keson magana dake" ............. Kamun yak'ara magana Hisham yayi zubur yace " su waye"? "Bansansu ba amma dai nagansu da kayan yan sanda" cewar Ibrahim Ai kamun ma su farga har Hisham yakai waje inda Momma da Ibrahim suka rufa mashi baya, Daga Momma har Hisham saida gabansu yayi mugun faduwa lokacin da sukayi arba da wadan nan yan sandan , cikin sark'ewar murya Hisham yafara jefo masu tambayoyi batareda ya tsaya gaisawa dasu ba, "Lafiya mi yake faruwa mi kukazoyi nan ina Abbana yake yanadai lafiya ko" ?? Haka yayita jera masu tambayoyi , D'aya daga cikinsu ne yayi karfin halin cewa "ka kwantar da hankalinka dama munzo tafiya daku ne saboda sir yasamu had'ari a hanyarsa ta zuwa gwangulori yanzu haka yana hospital shiyasa mukazo tafiya daku, Wani irin sarawa kan Hisham yayi da k'arfi kamar an buga mashi guduma da sauri ya sanya duka hannayenshi ya tallabe kanshi da yakeji kamar ba'a jikinshi yake ba sai maganar wanna mutumin kemasa amsa kuwwa a kunne tabbas wani mummunan abu yafaru da Abbanshi koda ganin yadda mutumin ke magana yana sunne kai ,kamun kace mi juwa tafara daukarshi taga-taga yayi zai fad'i da sauri Ibrahim ya rikeshi , basu ankaraba sai jin faduwar Momma sukayi timmm ak'asa ta fadi babu numfashi, Da sauri Ibrahim ya sakeshi ya nufi Momma yana kwala kiran sunanta a firgice , Hisham kam tuni yayi mutuwar tsaye kwakwalwar shi ta tsaya cak yakasa tuna komai a hankali idonshi yafara rufewa sai gashi shima a kasa a some..............✍🏼 *Littafina yakoma na kud'i 200 Kuma kowane lokaci zan iya dakatar da post dinshi har sai a paid grp Wanda rashin comment ne ya janyo hakan , kuma ko yanzu kuka canza ton zan canza Nima nabarshi a free dinshi kamar yadda nayi niya daga farko*😎😎 *Sannan na rokeku ku taimaka ku tayani share*πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: .aπŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 _wannan page nakine my *khairat isiyaku* kiyi yadda kk so dashiπŸ₯°πŸ₯° πŸ…ΏοΈ_15 ……...................wata irin k'ara Ibrahim ya fasa tareda kiran Hishammm sakin Momma yayi ya dawo wajan shi yana bubbugashi duk ya firgice yama rasa abunda zaiyi ,ganin hakan yasa wani daga cikin yan sandan yin azamar fita daga gidan motar da suka zo da ita ya bude ya dauko ruwa a gora yakoma ciki da sauri , nan yashiga yayyafawa Hisham ruwan ba'a dau lokaci ba ya farfado a razane yana kiran sunan Momma , hangota da yayi a kwance a wajan data fadi ne yasa ya zabura da karfi ya nufi wajen da take , d'ago kanta yayi ya d'ora bisa k'afafunshi yafara kiran sunanta da k'arfi , "Momma Momma ki tashi ki tashi nace muje mu gano halin da Abba yake ciki , ki tashi Momma Abbana Abbana kazo kace ta tashi arikice yake maganar daga nan kuma sai yafara sambatu wanda sun kasa fahimtar abunda yake cewa , ganin Momma bata farfado ba kuma suna k'ara 'bata lokaci da Hisham ma baya hayyacinshi yasa d'aya daga cikinsu kallon Ibrahim yace ku kamata musata amota muje asibiti zaifi , haka kuwa akayi Ibrahim shi kadai ya dauketa ya sanyata amota sannan ya kamo hannun Hisham suka shiga , direc suka nufi asibitin da aka kai Abba. Suna zuwa likitoci suka rufu akan Momma cikin ikon Allah bata dauki lokaci ba ta farfaΙ—o , sai dai tana farfadowa da kuka ta farka sai kiran Hisham takeyi, likitan ne yafara kwantar mata da hankali akan ta tsaya za'a kira mata shi amma ina sam tak'i k'arin ruwan da aka sanya mata ma tuni ta fisge hannunta ta mike tsaye ,ganin hakan yasa yabada umurnin a je a kira Hisham , Banda Safa da marwa ba abinda yakeyi har wannan lokacin yakasa tambayar halin da mahaifinshi yake ciki saboda yana fargaban abunda za'a gayamashi wani irin zufa ne mai zafin gaske ke keto mashi ta ko ina kamar an masa wanka da ruwan zafi , ahaka wannan ma'aikacin jinyar ya taddashi , nan ya gayamashi likita na nemanshi , tun bai k'arasaba ya juya da sauri ya nufi inda aka shiga da Momma, Tana ganinshi ta k'arasa wajanshi da sauri tace " Hisham ya jikin Abbanka mi yasameshi ka ganshi kuwa yanadai lafiya ko ?? Tunda tafara jero mashi tambayoyin ido kawai ya zuba mata yana kallonta , a wannan lokacin sam bazaice ga abinda yake tunawa ba gaba daya komai ya tsaya mashi tunda yaga irin yadda asibitin yacika da jami'an tsaro sai shige da fice sukeyi yasan tabbas sai Allah idan Abba yana raye , Jan hannu Momma kawai yayi batare da ya bi takan likitan ba suka fita daga dakin , direct wajan mutanen da sukazo dasu ya nufa yana zuwa cikin sark'ewar murya yace masu "a ina Abba yake"? Duk diriricewa sukayi kamun daya daga cikinsu yayi masu jagora zuwa dakin da gawar Abba take, Tunda suka nufi wajan gabansu ke wani irin bugu kamar zai fashe a haka har suka shiga dakin, Dukkansu cak suka tsaya a inda suke suna k'arewa farin k'yallen da aka rufa mashi kallo wanda gaba daya ya 'baci da jini , Jiri ne yafara d'iban Momma a haka tarink'a tafiya har ta k'arasa inda gawar take a hankali ta sanya hannunta wanda yake rawa sosai tafara janye farin k'yallen, runtse idonta tayi da k'arfi kamun kuma a hankali takoma budesu ta zuba mashisu ko k'yaftawa batayi yayinda a lokacin komai tsaya mata yayi tana kallon abun kamar a mafarki sai fatan take Allah ya tayar da ita daga wannan mummunan mafarkin da takeyi , Shafa fuskarshi tayi a hankali tare da furta " "Abban shalele" Abban shalele da gaske mutuwa zakayi kabarmu , ? Kar ka mana haka Yaya ka tashi Sam bazamu iya rayuwa ba in babu kai ganin har yanzu bai motsaba yasa tafara magana da karfi tana Kiran sunanshi tareda jijjigashi tana kiran karya mutu ya tashi , Matsawa dan sandan yayi kusa da ita sannan yasa hannu ya janyo farin kyallen yakoma rufe Abba dashi ,cikin matukar tausayawa yace " Hajiya saidai muyi hakuri Allahn da yabamu shi ya karbi abunsa , sai dai mubishi da addu'a kawai , Girgiza kai Momma tafarayi tana ja da baya har takai da bango durk'ushewa tayi a wajan tana wani irin jan numfashi zuciyarta kuwa kamar zata fasa kirjinta ta fito tsabar bugun da takeyi , kamun bugun zuciyarta ya tsaya cak ta koma sulalewa ta fadi a wajan a some , Dan sandan ne yayi saurin fita kiran likita yayinda akabar Hisham nan tsaye ba um ba um um shi baiyi gaba ba kuma baiyi bayaba yayinda idonshi ke kafe akan gawar mahaifinshi duk da faduwar da Momma tayi hakan baisa ya juya ya kalleta ba ,kalaman wannan ma'aikacin kawai yakeji yana mashi amsa kuwa acikin kunne *_Allahn da ya bamushi ya k'arbi abunshi_* Ahaka wasu likitoci biyu suka shigo suka shiga bawa Momma taimakon gaggawa yayinda wannan dan sandan yaja hannun Hisham suka fita haka yarinka bin shi kamar wani wawa sam yakasa gane komai yakasa fahimtar komai yakasa aikata komai sai zuciyarshi dake mashi wani irin lugude mai tafe da tsantsar fargaba, Office din babba likita suka nufa don yin duk wani cike cike don karbar gawar , haka akasa Hisham ya rattaba hannu aka gama duk wani cikwu-cikwu aka basu gawar , Haka suka dauko gawar a motar asibiti suka nufi gida , Lokacin da suka zo har kofar gidan tafara cika da mutane nan aka shiga dashi aka mashi wanka aka shiryashi cikin likkafani , har wannan lokacin Hisham yakasa furta koda kalma d'aya ne yayinda idanunshi da zuciyarshi suka soye sam ba alamar hawaye a idonshi , Acan asibiti kuwa Momma tana farfadowa bata sauke idonta a ko ina ba sai akan gadon da taga gawar mijinta a kwance ,dubawa tayi da kyau tare da sake murza idonta amma har lokacin bataga komai ba a zabure ta tashi tana fadin "ina mijina ina kuka kaimun mijina , ? "Kiyi hkr Hajiya sun tafi da gawar gida kizo muje akwai wad'an da aka bari idan kin farka sai su tafi dake cewar likita, Gawa gawa gawa fa yace kenan da gaske ne tarasa mijinta uban danta majinginarta kuma majibincin lamarinta , a hankali cikin wata irin murya ta furta " *Innalillahi wa inna ilaihin raji'un Alhamdulillah ala kulli halin* a hankali taji wata irin natsuwa da tawakalli ya ziyarceta , tunawa da tayi ai tanada Allah kuma shine gatan kowane bawa , sannan Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i daga nan taci gaba da ambaton sunan Allah yayinda a hankali wata irin nutsuwa ke k'ara shigarta , ahaka har suka isa gida , Lokacin da tayi arba da taron jama'a k'iris yarage bata koma faduwa ba haka dai ta daure tana tafe tana dafa bango har ta shige cikin gidan , A falo ta tarar da mata dank'am matan abokanshi ne da makota sai k'awayenta nan ta ra'basu ta shige cikin bedroom dinta ta mayar da kofar ta rufe kamun ta zame anan wajan ta saki wani irin kuka mai ban tausayi, Bayan an shirya shi ne aka nemi Momma da Hisham da suje suyi mashi addu'a , Addu'a sosai Momma tayi mashi tanayi tana kuka mai tsuma zuciya yayinda Hisham yakasa koda motsa bakinshi ne bare yayi magana sai dai idanunshi da suka kad'a sukayi jajir ga wani girma da suka k'ara abun tsoro , ganin yakasa yin komai ne aka dauke gawar akayi waje da ita inda za'ayi mashi sallah, Bayan angama sallah ne aka nufi mak'abarta , sai a lokacin Hisham yafara dawowa hayyacinshi , lokacin da aka bashi gawar ne don ya sanya mahaifinshi da kanshi wani irin sanyi mai haΙ—e da makyarkyata suka kamashi gada daya jikinshi rawa yakeyi sam yakasa rike gawar sai da aka taimaka mashi bayan an sakashi ne aka rufe kamar yadda akema kowane mahaluk'i alokacin ne wani marayan kuka ya kwace mashi mai tafe da wani irin sauti mai taba zuciya lokaci daya wani tari mai karfi ya sark'eshi kamun kace mi yazube a wajan a some , Nan aka daukeshi wasu suka nufi wajan amsar gaisuwa abokanshi kuma suka nufi asibiti dashi , Kwana sambatu Hisham yayi kamar wani mahaukaci sabon kamu , Ibrahim da wani abokinsu Aliyu ne a wajanshi , Momma kam tuni k'arfin imani ya shigeta ta fawwalawa Allah komai sai addu'a take ma mijinta saidai duk da hakan takasa tsayar da hawayenta musamman in ta tuna da Hisham , *Washegari* K'arfe 10am na safe a Lagos tayi masu , Abdullahi ne da Inna Asabe sai matarshi da yaranshi , suma tunda labari ya riskesu jiya suke cikin tashin hankali musamman ma Abdullahi yayi kuka kamar ba gobe yayi dana sani tafi cikin kwando haka kawai akan mace ya dauki tsanar duniya ya daurawa tilon d'an uwanshi akan *mace* yafita sabgarshi baya shiga duk wani abinda ya shafeshi yayi watsi da zumunci duk akan mace yanzu wa gari ya waya gashi nan yarasa tilon d'an uwanshi da bashida kamarshi duk duniya , mahaifinsu har ya mutu yana masu nasiha akan su kula da zumunci Amma duk da haka baisa ya gyara tsakaninshi da dan uwanshi ba to ga irin ta nan yarasashi a lokacin da yafi buk'atarshi Kuka yake sosai yana neman yafiyarsu lokacin da yakewa Momma da Hisham gaisuwa da yake tun da sassafe Hisham ya baro asibitin batare da an sallame shi ba , duk da har wannan lokacin bai gama dawowa daidai ba , Nan Alhaji Abdullahi da iyalanshi suka zauna har aka gama amsar gaisuwa , saida akayi kwana bakwai sannan yayi shirin komawa tareda matarshi bayan ya ajiye masu duk wani abunda yasan zasu buk'ata tareda gaya masu duk abunda sukeso su kira su gayamashi , anan aka bar inna Asabe don tace anan zata zauna tarink'a debewa Momma kewa har ta saki jikinta , don ta kula daga Momma har Hisham basu gama dawowa hayyacinsu ba barinsu su kadai zai iya haifar masu da wata matsalar saboda yawan tunani da damuwar da suke ciki, Agurguje plsπŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„Zan baku agurguje saboda inason mushiga gundarin labarin ne don wannan sharar fage ne kawai kuma sam ba wannan matsalar ce ta rabo Hisham da gida ba cakwakiyar tana gaba😍😍 *Bayan wata shida* Zuwa yanzu komai yazama tarihi Alhamdulillah daga Momma har Hisham sun mik'a lamarinsu ga Allah suna rayuwa cikin farin ciki , saidai yanzu gaba daya Hisham ya canza yakoma shiru shiru sam bayason abunda zaisa yayi magana yakoma miskilin karfi da yaji Momma ma yanzu saidai taga murmushinshi amma badai dariya ba ga wani fad'a da ya taso mashi abu kadan zai kama masifa a haka dai sukaci gaba da rayuwa kuma har wannan lokacin inna Asabe tana tare dasu duk lokacin da tace zata tafi yanzu Momma zata fara koke koke shiyasa yanzu har ta daina cewa zata tafi , Dayan bangaren kuwa kkowanne da damuwa dankare acikin zuciyarshi saidai suna kokarin nunawa juna basa tare da wata damuwa , Momma tana zargin kashe mata miji akayi saboda wasu dalilai amma takasa gaya kowa batasan yadda Hisham zai dauki al'amarin ba shiyasa taja bakinta tayi shiru , Yayinda a 'bangaren Hisham yake ta tunanin ta yadda zaiyi ya shawo kan Momma ta barshi *ya cikawa mahaifinshi burinshi na zama _Jami'in dan sanda_* Yau ma kamar kullum suna zaune a dining suna karyawa ya d'ago kanshi yace "Momma akwai maganar da nakeson muyi amma don Allah inason ki tsaya kiyiwa abun kyakkyawar fahimta Kuma pls momma karki ce Zaki hanani don Allah ," "Ina jinka Hisham gayamun mi kake so , "? Cikin inda inda yace Momma dama shekaranjiya ne naje na cike Form na aikin *dan sanda* to inatason namaki bayani amma...............baisamu damar k'arasawa ba sakamakon wani irin tari da ya sark'e Momma , a rikice ya debo ruwa zai bata amma ga mamakinshi sai gani yayi tasa hannu ta ture ruwan tareda wurga mashi wani irin kallo wanda tunda yake da ita bai taba ganin tayi mashi koda makamancin shi bane ga wani tsantsar tashin hankali da fushi hade da masifa da ya hango acikin kwayar idanunta , Pls momma .............hannu ta daga mashi kamun ta tashi tabar wajan batare da ta ko kalli inda yake ba,.................✍🏼 *Zanyi aike Kano da Zamfara gobe kuma kudin motar kyauta ne maiso ingantattun kayan mata tayimun magana ta pc ngd* 09035027743[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 _wannan shafin nakine my takwara (Maryam taly) kiyi yadda kk so dashi_πŸ₯°πŸ₯° πŸ…ΏοΈ_18 .......................sati na zagayowa yafara fita aiki , inda Momma tayi mashi nasihohi masu ratsa zuciya da addu'o'in samun nasara , haka ya fita yanajin wani irin farin ciki a zuciyarshi wanda yarasa gane kona minene , amma tabbas a yanzu yanajin son aikinshi har cikin zuciyarshi , Satinshi d'aya da fara aiki DPO Huzaifa Umar ya fahimci irin nagartar da Hisham yake da ita , aiki yakeyi tuk'uru da dukkan gaskiya da amana uwa uba tsantsar k'warewar da yake da ita akan aikin kamar wanda ya jima acikin aikin , wanda ba komai ne ya janyo hakan ba sai tsabar kaifin basira da irin horon da ya samu akan aikin, Wannan dalilin ne yasa sir Huzaifa ya janyo shi ajiki tare da k'ara mashi k'warin gwuiwa akan yadda yake gudanar da aikinshi , sannan ya damk'amashi case din wasu Criminals da ake nema ruwa a jallo , amma kamasu ya gagara saboda wadan da ake d'orawa akan case din tuni an siyesu shiyasa suka kasa aiwatar da komai akai , sai dai surink'a nuna suna iyakar k'ok'arinsu akai, Asmy da Jafar da Zubair su Sir Huzaifa ya za'ba a matsayin wad'an da zasu taimakawa Hisham akan case din kasancewar su amitattu a gareshi , Cikin ikon Allah kuwa sai gashi acikin kwana ukku kacal Hisham da abokan aikinsa sun samu nasarar kama mutanen da ake nema tsawon shekara biyu amma ankasa kamasu saboda halin nigeriyanci da akeyi a k'asar nan, Wannan nasarar da Hisham ya samu ba k'aramun janyo mashi farinjini yayi ba a hukumar tasu ta yan sanda, yayinda d'ayan 'bangaren yafara tsonewa wasu ido a hukumar in da suke ganin doli su tashi tsaye don ganin wannan sabon zuwan bai sha gabansu ba a hukumar tasu, Jin dadin wannan aikin ne yasa sir Huzaifa zak'ulo wasu cases da suka gagari sauran 'yan sandan ya d'ora alhakin bincikensu akan Hisham , Sai gashi cikin kankanin lokaci sunan Hisham yayi amsa kuwa a cikin hukumar tasu harma da wajen gari , aiki yakeyi tuk'uru don zak'ulo duk wasu 'bata gari dake cikin garin na Lagos , babu ruwanshi da kudink'a ko muk'amin ubanka duk wanda ya kama da wani laifi to zai gurfanar dashi a gaban hukuma ne , Lungu da sak'o suke shiga suna kama masu laifi kamar 'yan fashi da makami , masu garkuwa da mutane, k'ananan 'barayi, masu yiwa mata da k'ananun yara fyade , wadan da sunema yafi tsana akan komai , sai kuma 'yan shaye shaye kamun kace mi tuni labarin *ASP Hisham Abdurahaman* ya karad'e garin na Lagos inda jama'ar gari ke jinjina mashi tare da yimashi fatan alkhairi don hak'ik'a ya kawo sauyi mai d'umbin yawa acikin garin , duk wani iskanci yanzu sai dai ayi shi a 'boye don ya hanawa kowa sakat , musamman 'ya'yan masu kud'i da suke ganin ya shige masu hanci da yawa ,yayinda iyayensu ke ganin cewa ya takurawa Ζ΄aΖ΄ansu da yawa , Acikin kame kamensu ne suka kama yaran su Alhaji Manu su ukku , kolo, kunama, da kuma Goga, sun kamasu ne a lokacin da suke k'ok'arin shigowa da hodar ibilis , duk da kuwa sunyi matuk'ar shirya shirin da yanada wuya agane mi suke dauke dashi , sai dai cikin ikon Allah kallo Daya Hisham yayi masu yaji bai aminta dasu ba wannan yasa yabada umurnin da abuba kayan da suke dauke dasu , Da fari sam basu damu ba don aganinsu ba mahalukin da zai gane shirinsu , "Sir na duba bakomai aciki gaba daya kifi ne acikin motar , " cewar wani dan sanda , Zama Hisham ya gyara akan saman motar da yake zaune fuskar nan tashi ba alamar sassauci aciki yace " ku k'ara dubawa dai" Nan suka shiga bincikar k'atuwar motar da aka ciko taf da danyen kifi cikin kwalaye ,har zuwa lokacin basuga komai ba , yayinda su Goga keta aikin murmushi don sun san bazasu ta'ba gane komai ba, Ganin hakan yasa Hisham tasowa da kanshi inda yayi tsaye yana k'arewa kifayen dake cike acikin kwalaye , umurni ya bayar akan a dauk mashi kwali daya , Da hanzari Jafar ya dauko ya kawo inda yake , alama yayi mashi da ya bud'e kwalin , Ido ya zubama manya manyan kifayen yana kallo , sai can idonshi ya sauka akan wani sirrin zare dake wajan cikin kifin , Duk'awa yayi a hankali ya sanya hannu ya ta'ba wajan , ganin da gaske dai alamar dinki yake gani yasa wani daga cikin yan sandan akan ya dauko abu ya 'bare mashi cikin kifin, Tunda su Goga sukaga hakan cikinsu ya duri ruwa nan fa suka nemi hanyar guduwa sai dai babu dama don tuni yan sandan sun zagayensu da bindigogi tunda suka fahimci kudurinsu, Aikuwa ana 'bare cikin kifin sai ga ledar hodar ibilis aciki , dukkansu mamaki da tsoro ne ya kamasu ganin wata sabuwar hanyar yaudara da aka samu tabbas wadan nan mutanen suncika hatsabibai , nan sukaci gaba da duba kifayen duk wanda suka bude to zasu samu leda biyu ko ukku aciki , wannan yasa aka rufe motar aka hannuntata ga yan sanda yayinda su kuma su Goga aka wuce dasu CID diret don case dinsu babba ne, Aikuwa lamarin ba k'aramun d'aga hankalin su Alhaji Musa yayi ba don kayan da aka kama kayane na miliyoyin kud'i , abun yazo masu a bazata don sun riga da sun sakankance akan cewa bawata matsala don sun siye duk wasu jami'ai Da kayan zasu iya biyowa ta hannunsu, Babban tashin hankalinsu ma shine yaransu da aka kama , kar su bayar da wata masaniya akansu , Gaba daya a rikice suke duk da sanyi AC dake falon sai hada zufa sukeyi , Alhaji manu kuwa sai faman shafa sank'on kanshi yakeyi yanajan tsaki gaba daya yarasa abinda zaiyi, A fusace Alhaji Buba yace " wai tsayama tukunna wane mai tsautsayin ne ma da k'arar kwana har yayi gigin shiga hurinminmu irin haka , mi yake tak'ama dashi ne , lallai sai ya dandana kud'arshi tunda har ya yarda tsautsayi ya sanya shi shiga gonarmu , Alhaji Manu ka kira mana Zakari inason sanin wanene mai wannan zarrar acikin hukumar tasu, Daukar wayar yayi ya dannawa Zakari kira , bugu biyu Zakari ya dauka tare da fad'in " ina kwana oga, " Bai amsaba yace " nasan kasan duk abunda yake faruwa , wanene shi dami yake tak'ama sannan mi ake ciki a yanzu ,??" Ajiyar zuciya Zakari ya sauke yace "oga wallahi akwai matsala don in har bakuyi wani abuba da gaggawa to komai zai iya faruwa , don wannan yaron bashida mutunci ko kadan , jiya agaban idona akayi komai sai dai banida ikon hana komai kasancewar yana gaba dani , maganar da nake maka yanzu haka yaranku basu cikin station din Nan tun jiya aka wuce dasu C I D don .............. Katseshi Alhaji manu yayi cikin tsawa yace kai banason maganar banza to ku miye amfanin ku kenan miye amfanin makuddan kud'ad'en da muke baku ne , yazama doli kuyi wani abu inba hakaba wallahi duk sai kun had'u da fushina , Gaba daya jikin Zakari ya dauki rawa don an sakashi cikin tsaka mai wuya , cikin rawar murya yace " oga Yakamata fa ka fahimci maganata abun nan fa babba ne sam ya wuce tunaninku , yaron nan wlh ba k'aramun hatsabibi bane sannan ya samu goyon bayan D P O yadda baka tunani duk abunda yakeyi ma da d'aurin gidinshi yakeyi shiyasa baya shakkar uban kowa , sannan duk wani babba da yake cikin jami'a mu sun san da maganar kuma yanzu haka zancan da nakemaka zancan turasu kotu akeyi , abunfa ya wuce inda kake tunani wallahi , shegen yaron nan zuwan jiya jiya yazo duk ya tayar mana da hankali ya shige mana gaba bamuda wani motsi yanzu a hukumar sai abunda ya aikata yanzu haka jiya da dare dan gidan ministan Kudi ya kamo ya sank'ama a cell har yanzu ankasa fitar dashi don kiri kiri oga ya goya mashi baya , yanzu dai ya kamata.....................cikin tsananin 'bacin rai da tafasar zuciya Alhaji manu yace to wai shi wannan yaron dan gidan uban waye haka , waye ubanshi a garin nan , mi yake tak'ama dashi da har zai zo ya ruguzama shirin da muka shafe shekaru munayi ," ....... "Oga ka kuwa san ko waye wannan yaron ? To wannan yaron ba d'an kowa bane sai d'an *inspector Abdulrahaman* sannan yayi gadon kafiya da taurin kai irin na ubanshi kai harma ya zarta ubanshi da muguwar ak'ida ," nan Zakari ya karkace baki yarinka zuba yana fada masu abunda yasani akan Hisham , Tun lokacin da Zakari ya ambaci sunan Inspector Abdurahaman daga Alhaji manu har su Alhaji Musa basu sake fahimtar abunda yake cewa ba ,da yake wayar a hans free ya sakata , lokaci d'aya sukaji zukatansu sun buga a tare da wata irin fargaba da basu taba jin irinta ba , lokaci daya suka fara sharce zufa , Dama inspector Abdulrahaman yana da d'a , ? Kuma har wanda ya girma haka , d'ansa ne kokuma d'an 'yanuwansa , tambayoyin da sukeyi acikin zukatansu kenan, sunjima a haka an rasa wanda zai fara magana acikinsu sai can Alhaji Buba yayi tsaki yace " shima zamu turashi inda muka tura ubansa ne, daga haka ya mik'e ya Shige cikin wani d'aki , dukkansu da kallo kawai suka bishi duk da suma sun kasa gane abunda ya haifar masu da wannan fargaban , abunda Basu ta'baji akan wani mutum ba,....... *********************** Da sallama suka shiga gidan , tana tsakar gida tana wanke wasu kwanuka yayinda take taunar cingum k'as k'as tana Yan wak'e wak'enta , duk da taji sallamar da akayi hakan baisa ta d'ago da kanta ba ma bare ta amsa sai wake wak'enta takeyi, K'wafa Mansur yayi baice mata komai ba yaja hannun Abokinshi Ibrahim suka wuce dakin yayan nashi, Yana kwance bisa katifa sai ma ka kula da kyau ne sannan zaka san da mutum a wajan saboda yadda ciyon ya cinyeshi gaba daya banda k'aton kai ba komai ajikinshi duk ya yamushe ya k'ank'ance yayinda yake fitar da numfashi da k'yar tsabar yadda yake jin jiki , da sauri Mansur ya k'arasa kusa dashi yana riko hannunshi yace " sannu yaya Haruna ya jikin naka , ? Kayi hakuri yau banzo da wuri ba nima na tashi da ciyon kai ne shiyasa , kamashi yayi ya tayar zaune ya jingina shi da bango sannan ya dauko ledar da yazo da ita, shayi ya hada mashi yabashi yasa sosai sannan ya fara bashi maganinshi , acikin zuciyarshi kuwa Banda tsinema matar yayan nashi ba abunda yakeyi, sai k'wafa yakeyi , Ibrahim ma jiki a sanyaye ya zauna daga gefe yana yiwa yayan na Abokinshi sannu da jiki cike da tausayawa, harda yar kwallar shi don Ibrahim akwai tausayi sosai , A hankali Haruna yake amsawa yayinda ya kafe Ibrahim da ido yana tunanin a ina yasan fuskar nan ne, Can Allah yasa ya tuna , aikuwa a zabure yayo kan Ibrahim din da nufin isowa wajanshi amma sai yakasa saboda rashin karfin jiki, yafito Ibrahim yarinkayi da hannu alamar yazo inda yake , Da sauri Ibrahim ya karasa kusa dashi , hannu biyu yasa ya rike hannun Ibrahim din yana numfashi da k'yar yafara magana wanda da kyar ma akejin abunda yake cewa , "Dan samari kamar nasanka a gidan marigayi inspector Abdulrahaman ko ?" Gyad'a kawai Ibrahim yayi yana mamakin dalilin shi nayi wadan nan abubuwan don shi kam dama kallo Daya yamashi ya tuna ya sanshi abokin aikin Abban Hisham ne ashe shine yayan Abokinshi Mansur, Maganar Haruna ce ta katse mashi tunanin da yakeyi jikinshi har wani rawa yakeyi yaci gaba da cewa , " don Allah ina yaron Abdurahaman , dakuma matar shi , don Allah Dan samari ka taimaka kayi mun wata alfarma don darajar Annabi Muhammad SAW kayi duk yadda zakayi don ganin ka tahomin da matarshi dakuma d'anshi anan , akwai buk'atar in gana dasu , abune mai matukar muhimmanci agareni in gana dasu kamun dan sauran lokacin da ya ragemun ya cika don Ni nasan wannan ciyon bai mai barina bane na riga da na yanke kauna da sake taka k'asa sai dai nasani Alhaki ne ke bibiyata wanda inhar ba na rok'i yafiyar wad'an da na cuta ba bazan ta'ba ganin da kyau ba duk da kuwa Ni kaina nasan lokacin yin hakan ya riga da ya k'uremun kuma nasan bazasu ta'ba yafemun ba yayi maganar wasu hawaye Masu dumi da yaji suna gangarowa daga cikin kwamin idanunshi, "Haba yaya kai kullum bakada magana sai kiran Alhakine ke bibiyarka , bayan kuma nasan duk zafin ciyo ne kayi hakuri insha Allah zaka warke kamar ba kaiba amma Yakamata karage sawa kanka damuwa hakanan kar abun yayi maka yawa yaya , yafad'a kamar zai zubarma da yayan nashi hawaye, Murmushi mai ciyo yayi yace " bakasan komai akaina ba Mansur Ni azzalumi ne Ni maha'inci ne Ni maciyi amana ne na ci amanar aikina da al'umma ta , sai dai abu mafi girma da na aikata wanda sanadinshi ne na hadu da wannan jarabawar sai gashi babu wan Babu k'ane ban tsira da komai ba sai tarin walana da dana sani, abu daya zakuyi mun shine ku taimaka kuzo mun da wadan nan bayin Allah ko na samu sassauci akan abinda nakeji ajikina , wanda har lokacin hawaye basu daina zuba a idonshi ba, Daga Mansur har Ibrahim kansu ya k'ulle sun kasa gane zantukan na Haruna , amma ganin yadda ya rikice masu yasa suka mashi alkawarin gobe da safe zasuzo mashi da wadan da yake nema din, Sai a lokacin ya saki ajiyar zuciya tareda gaya masu don Allah sucika alk'awari, *Washe gari* A gurguje yake shiryawa don yau yaso ya makara sosai , bayan ya gama shirin shi tsaf cikin kakin shi na yan sanda wanda yake matuk'ar yi mashi kyau da kara mashi haiba abunka ga farin mutum kuma isasshen namiji mai jini ajika, turare ya dauka yana fesawa sannan ya dauki agogonshi da hularshi ya fito daga dakin , dakin Momma ya nufa , da sallama ya shiga tana tsaka da gyara kayanta da aka amso guga taji sallamarshi , Murmushi ta saki lokacin da tayi arba da d'an nata masha Allah son kowa kin wanda ya rasa , har kasa ya duka ya gaisheta kamun ya mik'a mata agogon yace " yawwa Momma doramun agogon nan, Murmushi tak'ayi tace kai dai shalele ta'bararka tayi yawa wallahi ace har yanzu k'ato da kai ka kasa iya sa agogo kullum sai dai ka bayar a sakama , amma ai duk abbanka ne ya sagartaka da yawa komai sai dai yamaka kamar wani k'aramun yaro, Murmushi yayi yace kai Momma nikam kullum sai kinyimun jawabi akan saka agogon nan gaskiya zanyi zuciya in koya in huta Nima, yafad'a Yana wani yamutsa fuska , "Hmm inda Kanada wannan zuciyar ai da tuni kayi , Ni yanzu dai kazo ka nemi matar aure ko nima na huta da shiriritarka kaje can matarka tayi maka," Taf wa zaiyi aure yanzu Momma kofa shekara talatin banyi ba gaskiya ba yanzu ba sai na k'ara girma, " "Aiko baka isaba don kaji na gaya maka insha Allah kamun karshen wannan shekarar doli kayi aure don banga abunda kake jiraba," Jin maganar tafara tsawo yasa yace kinga Momma zan tafi yanzu kiyimun addu'a in nadawo sai muyi maganar , " Ajiyar zuciya ta sauke kamun tayi murmushi tace *kowa da wannan kayan k'ima yake samu amma kuma sauk'e hak'k'in al'umma da amanar kayan su suke samar da k'ima ta gaskiya karka karya doka sannan kuma karka bari a karya doka fatan nasara shalele adawo lafiya*. Tunda tafara magana yake murmushinshi Mai burgewa kamun yace " Nagode sosai Momma" sannan ya juya yabar gidan, ___________ "Ibrahim wace irin magana kakeyi ne to nikuma miye had'ina dashi naga tun rasuwar Abba ko inuwarshi ban sake gani agidan mu ba , " "A'a Hisham karkayi saurin yanke hukunci acikin fushi kabari muje sai muji koma minene sannan Ni akwai abunda nake zargi tabbas akwai wani boyayyen abu da yakeson fada wanda kuma ya danganci Abba ne shiyasa yakeson ganawa daku," Shiru Hisham yayi na wani lokaci kamun yace " to amma Ni kadai zanje bazan tafi da Momma ba koma minene in na koma zan gaya mata, " Okey ba damuwa yanzu kagama aikin da kakeyi sai muje don na gayama Mansur cewa ya jiramu , Gyada kanshi kawai yayi yaci gaba da duba wasu takardu , duk da haka kawai gabanshi ke faduwa lokaci daya kuma sai yaji bai yarda da wannan kiran ba tabbas akwai wani abu Yakamata ya hanzarta yaje koma minene sai yaji da wannan shawarar ya ajiye aikin da yakeyi yacema Ibrahim "muje" ________________________ Minti 15 sai gasu a kofar gidan, gaisawa sukayi da Mansur sannan yayi masu iso acikin gidan , wanda tunda suka shigo unguwar gaban Hisham ke tsananta bugawa wanda yarasa dalilin hakan, Wani irin yunk'uri Haruna yayi sai gashi a k'asa ya fad'o daga saman katifar , bai damu da ciyon da yaji ba yayin faduwar don ko yaya bayason abunda zai taba jikinshi ko ina ciyo yake mashi , da sauri duk suka nufeshi suna da nufin kamashi suna jera mashi sannu cike da tausayawa matuk'a , Hisham ma jikinshi yayi sanyi wani irin tausayin shi yakeji har k'asan zuciyarshi , Mansur ne yakamashi ya maidashi akan shimfid'ar shi yana cewa " haba yaya miyasa zaka tashi so kake kajima kanka ciyo ne , Gaba daya jikin Haruna rawa yakeyi sai hannu yake mik'ama Hisham alamar yanaso ya matso kusa dashi , tasowa yayi yazo kusa dashi ya zauna yana furta "sannu Baba" Allah ya baka lafiya ," Haruna kuwa ba komai ne ya firgita shi ba kamar ganin Hisham sanye da kayan *Yan sanda* kuma dauke da babban matsayi , tambayoyine fal a ranshi amma yakasa furtasu saboda yadda bakinshi ke rawa ,sai dai wani bangare na zuciyarshi najin dadin ganin Hisham a wannan matsayin wanda ko ba komai zaifi jin dadin ja da mak'iyanshi , Da kyar yasamu yafara magana , aikuwa cikin kuka da rawar harshe yafara neman afuwat Hisham kamar zai duka mashi sai kalma daya yake nanatawa *yaci amanarsu don Allah su yafe mashi* Hisham bai fahimci komai ba hasalima gani yake duk zafin ciyo ne ,ganin haka yasa Mansur cewa "haba yaya ka nutsu kayi mana bayani mana ka sanyamu a duhu bamu fahimci komai akan maganarka ba , su wa kaciwa amana ?? Hisham ya nuna da hannu sannan yashiga basu labarin abunda yafaru tun daga farko har zuwa karshe , Tunda Hisham yafara fahimtar inda zancanshi ya dosa jijiyoyin kanshi da wuyanshi suka fara mik'ewa yayinda idonshi ya kad'a yayi wani irin ja mai ban tsoro gaba daya farin idonshi ya tafi , dai dai da jijiyoyin idonshi sun mik'e tsaye hannayenshi kuwa sai wani rawa sukeyi lokaci daya jikinshi ya murd'e duk wata siffar k'rafinshi ta bayyana k'undar hannunshi kuwa har wani irin rawa take tsabar tsananin 'bacin ran da ya tsinci kanshi aciki , Ibrahim da Mansur kuwa kamar wadan da aka dasa ko motsi sun kasayi sai ido da hanci da baki da suka saki suna kallon Haruna , yayinda suke jifanshi da wani irin kallo mai tattare da tsana, K'arar da sukaji itace ta dawo da hankalinsu cikin tsoro duk suka dubi inda suke kiyo k'arar , Hisham ne ya sa k'afa iya k'arfinahi yayi Ball da Haruna wanda saida ya tashi sama ya dawo k'asa wannan yasa ya saki wata razananniyar k'arar da ta karad'e gidan gaba daya , .....................πŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈ Mun shiga tara Hisham zai ida gawar da batashi baβ˜ΉοΈπŸ˜‚ *Zanyi aike Kano ,Zariya , Abuja, Kaduna , Lagos Maison INGANTATTUN KAYAN MATAN na yar mutan Sokoto mmn yusup yayi magana a hada da nashi ngd*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_16 .........................zaune suke cikin wani k'ayattacen falo wanda babuce kawai babu acikinshi , ga sanyi AC da wani daddad'an k'amshi na tashi , kowanensu Yana hakimce akan kujera ,kallo Daya zaka masu kasan cewa lalli wad'an nan alhazan sunci sun tada kai da nera suturar jikinsu ma in ka kalla kasan ba k'ananan mutane bane , 'dayan 'bangaren kuma ,yan jagaliyar su ne a tsaitsaye kowanensu rike da zungureriyar bindiga fuskar nan tasu ba alamar imani , Alhaji Manu da Alhaji Musa da Alhaji Buba shahararrun yan kasuwa ne wanda sukayi suna a cikin garin na Lagos har ma da kewayenta, masu kud'i ne na gaske wanda ake damawa dasu suna da kamfanoni shaguna gidajen abinci da gidajen mai da sauransu , duk wanda ya sansu da wadan nan abubuwan ya sansu sai dai ta k'ark'ashin k'asa sud'in sun kasance azzalumai ne ga k'asar tasu don sun kasance manya manyan masu shigo da miyagun kwayoyi kayan maye kala kala ,duk wanda yake hark'allar Miyagun kwayoyi to zaka samu a k'ark'ashinsu ya ke ta nan ne suke samun mahaukatan kud'ad'e ,yayinda gefe daya suke shigo da gur'bataccen magungunan asibitin daga k'asashe daban daban ,wad'an da sun kasance masu cutarwa ne ga lafiyar mutum duk wanda yayi amfani dasu a hankali a hankali zasu rinΖ™a kassara rayuwarshi batare da ya sani ba ,su kuwa hakan ba damuwarsu bace tunda biyansu akeyi sunacin dudduniyar k'asarsu, Ta dayan bangaren kuma suna nunama jama'a cewa su mutanen kirki ne ta hanyar yin sadaka gina masallatai makarantu bada tallafi ga mabuk'ata wannan yasa mutane da yawa suke son su dayi masu kallon mutanen kirki , wanda dama su haka sukeso bawai don Allah sukeyi ba a'a sai don ganin sun kauda idon mutane daga kansu , Wannan yasa hankalinsu yayi mummunan tashi lokacin da inspector Abdulrahaman yasan sirrinsu wanda yayi barazanar tarwatsa muguwar manufarsu , Har gida sukasa akayi masu kiranshi , batare da wata damuwa ba ya amsa kiran nasu , inda suka bashi mak'uddan kudade akan ya janye idonshi daga kansu sannan karya kuskura ya tona masu asiri inba haka ba kuwa zasuyi duk yadda zasuyi don suga bayanshi , , alokacin sam Abba bai wani damu da barazanarsu ba kuma kai tsaye ya gayamasu bazai amshi ko sisinsu ba sannan bazai fasa kai wannan case din kotu ba tunda yanada duk wata hujja a hannunsa , haka nan ya juya yayi tafiyarshi yabarsu baki sake, Tun daga lokacin suke bibiyarshi tare da yimashi barazana kala kala , da farko sunki kasheshi ne saboda sunason su sani shi da gaske yanada wasu hujjoji akansu kamar yadda ya fada kokuma yafad'a ne don yayi masu barazana , in da gaske ne taya zasusan shirinshi da inda yake da hujjojin, Sai dai abunda basu sani ba shine abba bashida wata hujja k'wak'k'wara sai goga gashi shikuma goga yaki bada hadin kai dukda irin azabar da ake gana mashi , wannan yasa lokacin da suka gayyaceshi yaje anan ya shirya masu tarko don kuwa duk maganganun da sukayi dashi ya nad'esu tsaf a wayarshi , Alokacin da suka samu labarin daukar da Abba yayi ne wanda ita kadai ce hujjarshi yasa suka yanke shawarar kashe shi kawai Alhaji Manu Yana kan kujera Yana zuk'ar taba duk ya had'a d'an k'aramun gajimare a wajan , meeting sukeyi akan wasu kaya da zasu shigo dasu , do neman hanyar da zasu wuce da muggan makaman batare da wata matsala ba, D'aya daga cikin masu tsaron k'ofar ne ya shigo ya d'an rank'wafa alamar girmamawa yace " sir kana da bak'o yana waje yace yanason ganin ka ne," Saida ya share sama da minti ukku sannan ya dubi security yace "wanene wannan " "Inspector Haruna ne" "Ok kace ya shigo " "To sir" juyawa yayi ya fita daga falon, A hankali inspector Haruna ya shigo yana wani dudduk'ewa yana washe baki sai faman zabga masu kirari yake yana mik'a gaisuwa , Dukkansu ba wanda ya dubi inda yake , tun yanasa ran cewa zasu bashi izinin zama har yafara sarewa ganin sama da 15mnt ba wanda ya kalleshi acikinsu sai faman shaye shayensu sukeyi suna tada hayak'i, Yawu ya had'iye da k'yar ganin yadda Yan jagaliyar ke yi mashi muzurai kamar wasu zakuna, "Mike tafe da kai "? Cewar Alhaji Manu "am am dama Alhaji zancan kud'i da kukace zaku bani ne *Naira miliyan ashirin* to naji shiru har yanzu gashi har anyi watanni , ga wannan ciyon da naji a kaina lokaci da wannan had'arin ya faru ya fara damuna sosai har yanzu fama nakeyi dashi kuma likita ya tabbatar mun da cewa nasamu matsala acikin kaina ne.doli sai anyimun aiki kuma kudin sunada yawa sosai yace rashin yin aikin nan zai iya haifarmun da babbar matsala anan gaba san."..................... "Kai dakata don Allah kazo sai zuba kake sai kace wani Radio , yanzu kai in Banda cewa d'an mahaukaciya ne kai taya kake tunanin zamu baka kudi har miliyan ashirin , ubanmi kamana da zamu baka wannan uwar dukiyar , to kaji da kyau ko sisi bazamu baka ba , inace tun farko munbaka one million to kaje sun isheka inba hakaba abunda yasamu dan uwanka kaima zai iya samun ka, " cewar Alhaji Manu, Alhaji Musa da Alhaji Buba kuwa ko kallonshi basuyi ba , ganin hakan yasa ya tashi jiki a sanyaye ya fita daga falon , tafiya yakeyi yana hada hanya gaba d'aya sun rusa masa babban burinsa ,tuni ya riga da ya shirya yadda zai gudanar da sabuwar rayuwa idan har suka bashi kudinshi miliyan ashirin kamar yadda suka mashi alk'awari , wani irin tururi zuciyarshi keyi yanajin wani irin bakinciki , d'ayan gefe kuma ga matsalar da yasamu yayin yimasu wannan aikin don saida ya share wajan sati Daya a asibiti sakamakon buguwar da kanshi yayi wanda har gashi hakan ya zame mashi matsala don in ciyon kan ya tashi haka zai koma kamar mahaukaci yana ihu da buge buge tsabar azabar da yakeji , dama shirinshi shine suna bashi kudin zai fita kasar waje amashi aikin sauran sai ya ja jari kawai , don a niyarshi ma zai ajiye aikinshi ne yafara kasuwanci tunda banza ta samu, to sai gashi cikin kankanin lokaci sun rusa mashi komai Kuma bazai iyayin komai ba!!!! " Inaaaa wallahi bazai taba yiwuwa ba suna nufin sunci moriyar ganga kenan bayan duk irin kokarin dana masu , sannan ga kasadar da nayi wanda gashi nan na hadu da ciyo mai matukar had'ari ga cin amanar abokina da aikina da nayi sannan ace duk wannan ya tashi a banza to wallahi bazai taba yiwuwa ba wallahi koni ko su sai dai ayi mutuwar kasko, " sambatun da ya rink'a yi kenan bayan ya dawo gida ya kulle kanshi a daki , daga baya ma tsabar bacin rai bai san sanda yayi zaune dirshan ba yafara kuka wiwi kamar wani karamin yaro,........ __________________________ "Assalamu alaikum , " yayi sallama tareda d'age labulen falon , Momma ce da Inna Indo zaune suna karyawa , Inna Indo ce kawai ta amsa mashi amma Momma ko kallon inda yake batayi ba , tadai amsa sallamar acikin ranta, sati Daya kenan da yayi mata maganar son shiga aikin d'an sanda ,tun daga lokacin ta dauke mashi wuta , ta daina shiga sabgarshi gaba daya , fushi takeyi dashi sosai , ta yadda zai dauki abun da muhimmanci , tasan Hisham bayason fushinta ko kad'an duk yadda yakai ga son abu data nuna bataso to zaibar abun duk yadda yakeson shi kuwa , amma abunda yake bata mamaki shine yanzu k'iri-k'iri ya kafe akan ra'ayinshi , duk kuwa da irin fushin da takeyi dashi, Kusa da Inna Indo ya zauna yana gayar da ita kamun ya juya wajan Momma yace "Momma Ina kwana," Shiru bata amsa mashi ba , har cikin ranshi yanajin ciyon yadda mahaifiyar tashi ke fushi da dashi amma ya zaiyi tunda ya dauki alk'awarin sai ya cikawa mahaifinshi burinshi, "Momma izuwa yanzu Yakamata ki fahimceni sam bana kafe akan ra'ayina bane don na 'bata maki , a'a kawai dai inason na cikawa Abbana burinshi ne , kema kin sani Momma sam wannan aikin baya raina amma a haka na ajiye nawa ra'ayin don ganin nayi abunda mahaifina yakeso , ki tuna Momma ko a ranar da zai bar duniya saida yayimun magana akan wannan buri nashi , ai Yakamata ki bani goyon baya , insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi Momma , "Runtse idonta tayi yayinda wasu hawaye Masu zafi suka zubo mata cikin Muryar kuka tace " kai yaro ne Hisham har yanzu da k'urciya a tare dakai , sam bazaka iya hangowa kanka abinda Ni nake hango maka ba , sannan indai har Ni na haifeka to inason kabar wannan maganar don sam bazan ta'ba yarda kayi wannan aikin ba , nasanka nasan halinka shigarka wannan aikin zai iya ...................." Haba Maryamu karki yiwa d'anki baki mana miye aibun wannan aikin ne da kike k'iyayya dashi haka , Ni banga abun tashin hankali ba anan , tunda har ya nuna ga abunda yakeso kibarshi yayi aikinshi mana , tunda kinaji yace saboda mahaifinshi zaiyi, shin ke bazaki iya goya mashi baya ba don ganin kin tabbatar da burin mijinki ya tabbata ba akanshi , na tabbatar da in kece kika mutu da irin wannan burin to duk yadda Abdulrahaman zaiyi sai yayi don ganin yacika maki burinki koda baki a duniya haba Maryam kiyi hkr ki bishi da addu'a kawai shi zaifi, Batare da Momma tace komai ba ta tashi tayi shigewarta d'aki tabarsu anan , tana shiga ta fad'a saman gado tare da sakin wani marayan kuka yayinda kewar mijinta ta dawo mata sabuwa , Batason Hisham yayi wannan aikin ne don tana gudun watarana ya binciko gaskiyar abunda ya faru da Abbanshi ta tabbatar da sai ya dauki fansa bazai taba yin shiru ba , in hakan ta kasance tayaya zai iya ja da wadan nan hamshak'an mutane , karshenta shima su samu sharrin da zasuyi mashi , taya zata juri wani abu yasamu Hisham a yanzu shikadai take kalla taji dadi batada kowa sai Allah sai Hisham taya zata bari tanaji tana gani ya jefa rayuwarshi a hadari irin wannan,...... Dukkansu da kallo kawai suka bita lokacin da take shigewa dakin , ajiyar zuciya suka sauke yayinda gaba daya Hisham yaji duniyar na juya mashi kwata kwata ya tsani ganin 'bacin ran mahaifiyarshi ,tunani yakeyi ko ya hakura da aikin ne kawai kamar yadda takeso,! Wata zuciyar tace zaka iya hakura da burin mahaifinka kuwa wanda ka dauki alk'awarin sai ka cika mashi shi , kawai kaci gaba da lallaba Momma insha Allah zata sauko ta amince , haka yayi ta sake sake a zuciyarshi, Dafashi Inna tayi tace " karka damu Hisham zata sauko ne kuma nakama alk'awari. Zan shawo maka kanta insha Allah," Yawwa Inna Indo dakuwa kin kyautamun sosai wallahi, Acikin satin kuwa Inna Indo ta samu ta shawo kan Momma da lallashi da wa'azi , a wannan ranar Hisham yayi farinciki sosai , bai zame ko ina ba sai inda ya ajiye form din da yasiya , ya dauko shi ya ciccike komai sannan. Ya dauka ya fita dashi , Bayan wata daya komai ya kammala aka tura su makarantar koyon aikin dan sanda inda daga wannan zuwan bazasu dawo ba sai sun zama cikakkun *jami'an tsaron na police* Wata d'aya kenan da yaje wajansu Alhaji Manu , tun daga lokacin yake shirya masu tuggu kala kala amma yakasa samun nasara akansu saima barazana da suke masa don shekaranjiya har gidanshi suka turo mashi yan daba inda suka kama matarshi da yaranshi suka rufesu a cikin daki shikuma suka tu'beshi suka zaneshi tass saida jikinshi ya farfashe sannan suka mashi barazana da cewa idan har bai dauke idonshi daga kan su Alhaji Musa ba to zasu rabashi da duniyar baki daya , Aikuwa ya tsorata da lamarinmu sosai don yasan Daga su har uwayen gidan nasu basu da k'warar imani zasu iyayin komai don ba abunda aka isa ayi masu ,gashi tun daga lokacin ciyon kanshi keson tashi kullum baya bacci yarasa abinda ke masa dadi duniya , sai yanzu yafara nadamar abunda ya aikata ma Abokinshi dakuma cin amanar kasar shi.....................kai nagaji sai jibi kuma...πŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ *Kuyi hkr rashin jina kwana biyu nayi rashin waya ne* *Please comment and share*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° *ZANYI AIKE KANO DA KATSINA ABUJA KADUNA DA ZARIYA MAISON INGANTATTUN KAYAN MATAN MASU KYAU DA INGANCI TAYI MAGANA TA PC KO TA KIRA WAYA NGD 09035027743* πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ https://chat.whatsapp.com/LdqBkVqx2KX5S37HviKf4U *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_17 _*BAYAN WANI LOKACI*_ .......................... Cikin ikon Allah da iyawarsa yau Hisham Allah ya cika mashi burinshi kuma burin mahaifinshi , yasamu tsananin horo da sanin makamar aiki wanda duk wadanda sukayi aikin tare gaba daya yasha kansu ya zage ya koyi komai da dukkan zuciya wannan yasa yazama gagara badau kuma zakaran gwajin dafi ,inda ya fito a matsayin *babban Sifeta* na wannan yakin , Kyakkyawan matashi dan shekara 28 fari ne tas mai cikar zati yanada tsayi sosai da siffar k'arfi , kallo Daya zaka mashi kasan cewa wannan majiyin k'arfi ne saboda yadda yanayin jikinshi ya nuna , gaba daya jikinshi a murd'e yake irin na Jaruman maza , ba k'aramun kyau yakeyi ba acikin *Kakinsu na 'yan sanda* ga wani irin k'warjini da haiba da suke k'ara mashi , Lokacin da Hisham ya shigo gidan sanye da kakinshi na *yan sanda* tsaye kawai Momma tayi tana kallonshi ,yayinda idonta suka cicciko da hawayen farinciki , tsawon lokaci kenan bata danya tilon d'anta a idonta ba , saidai tana mamakin irin yadda yak'ara girma da zama cikakken namiji adan k'ank'anin lokaci irin wannan , gaba d'aya takasa wani motsi ganin yadda Hisham ya rikid'e yakoma sak Abbanshi komai da komai musamman da ya saka wannan kakin, Shima idon ya tsura mata yana murmushi wanda ya k'ara fito da kyaunsa , ganin halin da Momma tashiga ne yasashi k'arasowa da sassarfa ya rungumeta tareda da sauke ajiyar zuciya , itama ajiyar zuciyan tayi tare da saka duka hannayenta ta rungumeshi ta fashe da kuka , don gaba daya takasa rik'e kukanta Hisham ya tuna mata da mijinta tanajin tamkar mijinta ne ya dawo , gefe daya kuma cike take da farinciki Allah ya cikawa mijinta burinshi sannan d'anta yadawo kusa da ita , jan hannunta Hisham yayi sukashiga cikin dakin wanda har lokacin Momma bata daina zubarda hawayen farinciki ba, "To miye kuma na kuka Momma ? Inace farinciki zakiyi Allah Yasa na dawo gareki kuma da d'umbin nasarori , " "Doli nayi kuka Hisham narasa mahaifinka kaikuma kayimun nisa , Inna Indo wata biyu kenan da ta koma gida bayan tayi tayi dani akan nabita can gida amma nakasa yin hakan saboda kai , nikad'ai nake rayuwata agidan nan kewa tayimun yawa sosai yanzu kuwa kuka farinciki nakeyi da Allah ya nunamun wannan rana ka gama lafiya , ina rokon Allah da yayi maka jagora akan wannan aiki naka ka kasance mai nasara akan mak'iyanka ," "Amin Amin Momma na" yafad'a cike da shagwa'ba , murmushi Momma tayi tana maijin farinciki , "Momma nifa yunwa nakeji wallahi don yanzu sam bana jimirin yunwa " yafad'a Yana wani karya wuya, "To ai laifinka ne shalele da kayi mana zuwan bazata , da ka fad'a ai da yanzu ancika gabanka da kalolin abinci sai wanda ka za'ba, " "To ai Momma inason inbaki mamaki ne shiyasa , " "To naji bari naje na samamaka abunda zakaci kafin nan kayi wanka ka huta sai kabani labarin irin nasarar da ka samu , "To shikenan Momma Bari naje nayi wanka nazo," Wanka yayi ya shirya cikin farar riga da bak'in wando takalminshi ma bakake sai sumar kanshi da ta kwanta luf-luf kamar ya kafa hula tasha gyara sosai sai kyalli takeyi don ba karamin kudi yake kashewa sumarshi ba, in ka gamshi kamar wani Balarabe ko ba'indiye saboda yadda yakeda cikar suma da sil'bi irin ta fulanin asali, Zamansa babu wuya sai ga Ibrahim ya shigo gidan aguje jin cewar babban Abokinshi ya dawo , aikuwa nan suka rungume juna cike da tsantsar farinciki da kewar juna, nan suka zauna suna firar yaushe gamo , " "Abokina kaga yadda ka koma kuwa sai kace wanda yake rayuwa a cikin k'ank'ara gaba daya yanayinka da komai ya canza , anya kuwa ka maida hankali kayi abunda ya kaika kuwa , yafad'a Yana dariya" "A'a banyi abunda ya kaini ba dan rainin hankali , kana kallona kasan ba haka na tafiba duk na rame nayi duhu saboda wahala shine zaka wani ce wai nayi kyau " "Allah abokina bakaga yadda ka koma ga wata irin murdewa da jikinka yayi irin na asalin jaruman maza gaskiya ina tayaka murna don nasan ba k'aramun rububi zakasha ba wajan yan mata yafad'a Yana dariya , "Kai mata suka dama" cewar Hisham , suna haka Momma ta fito masu da daddad'an abinci data girkama Hisham sai k'amshi ke tashi , nan suka zauna sukaci suka k'oshi sannan sukaci gaba da fira ,sunjima anan sannan suka yiwa Momma sallam akan zasuje majalisarsu inda abikansu su gaisa , A wannan rana daga Hisham har Momma Basu runtsaba kwana sukayi suna firan yaushe gamo yayinda Hisham ya gayamata irin gwagwarmayar da yasha tareda nasarorin da ya damu da kuma irin matsayin da yake a yanzu , sannan nan da sati Daya zai fara zuwa aiki, Fatan alkhairi sosai tamashi tareda yi mashi nasihohi masu shiga jiki akan duk halin da gaishiga to ya tsare gaskiyarsa , ******************* Har wannan lokacin ba abunda ya canza akan muguwar sana'ar da su Alhaji Musa keyi , komai yana tafiyarmasu yadda suke so don ta kowane fanni sunada yaran dake masu aiki, jami'an tsaron dake masu aiki kuwa bazasu k'irguba , shiyasa suke abunda sukeso alokacin da sukeso , duk wanda yayi yunk'urin shiga gabansu kuwa to tabbas zasu kaudashi ko wanene kuwa , ana wannan yanayin ne aka canza D P O Hamza khamis wanda ya kasance yana daya daga cikin wad'an da suke bawa su Alhaji Musa goyon baya akan mugun abunda suke aikatawa , saboda mahaukatan kudin da suke damk'a mashi , wanda shima dasa hannunshi a kisan Jami'i Abdurahaman , wato Abban Hisham , Da farko sam basu wani damu ba tunda suna ganin duk wanda za'a kawo shima zasu siyeshi in yaso sai ya d'ora daga inda Sir Hamza ya tsaya , sai dai mi lokacin da aka gabatar da sabon D P O *sir Huzaifa Umar Abdullahi,* sai kallo ya koma sama don sam wannan ba irin wanda suke tunani bane mutum ne tsayayye mai gaskiya da amana uwa uba tsaye yake akan aikinshi sam ko waye kai ka yarda kashiga komarshi tofa sai kasan ka ta'bowa kanka tsuliyar dodo , mutum ne marar tsoro kuma dan kasada , Mutum na farko da suka fara tura masa da nufin ya janyo ra'ayinshi alokacin saida ya karya k'afar mutumin sannan yasa aka rufeshi tsawon sati biyu sannan yasa aka sakeshi zuwa lokacin kuwa tuni Ζ™afarsa ta ru'be banda fitar da ruwa mai doyi ba abunda takeyi , Wannan al'amari fa ya tsoratasu matuk'a saidai sun sha alwashin sai sunga bayanshi kota halin k'ak'a kamar yadda sukema duk wani k'aramun k'waron da yace zai kawo masu wargi a harkansu, *********************,, Kwance yake gala gala duk ya fita hayyacinshi ,ya rame sosai ba komai ajikinshi sai jijiya da k'ashi gaba daya ciyo ya cinyeshi sai kanshi da yayi wani irin k'ato , idan ka kalleshi doli yabaka tausayi , Da k'yar muryarshi ke fita , tun d'azu sai faman k'walawa matarshi kira yake Amma tanajinshi tayi biris dashi sai ma faman jan tsaki takeyi irin ya matsa mata dinan, Hawayene masu zafi suka zobo mashi ,fitsari yakeji tun d'azu amma matarshi Amina tanajin yana kwala mata kira amma tayi masa banza , bayan duk abinda ya sameshi sanadinta ne , don duk abunda yake samu kanta yake k'arewa duk abunda tagani ko bashida halin siya matashi haka zata yi tsaye tace sai ya siyamata , haka zaije duk yadda zaiyi sai yayi don ganin yasamo kudi yayi mata abunda takeso , don Allah ya dora mashi sonta mai tsanani da wannan take amfani tana juyashi son ranta duk abunda yasamu a gindinta dana yan uwanta yake k'arewa amma shine yanzu don Allah ya jarabceshi take wulakantashi yadda taga dama , bata tausayinshi kokadan , Gashi kullum ciyon kanshi k'aruwa yakeyi anyi magani har angaji anzubama sarautar Allah ido , don takai yanzu ko abincin da za'aci a gidan wuya yake masu bare wani kudin magani , Kusan kullum sai yayi kuka mai yawa idan ya tuna ya gamu da wannan ciyon ne alokacin da yaci amanar abokinsa , tabbas yasan wannan ciyo nashi *Alhakine* sakayya ce kawai Allah yayiwa Abdurahaman tun ba'aje ko'ina ba , gashi nan shi ya huta ya tafiyarshi shikuma yabarshi cikin tarin sark'ak'k'iya da wahalhalu na rayuwa tareda d'umbin nadama marar iyaka , tunda abun yafaru baikoma lafiya ba inda ciyon yafara yawa ne aka sallame shi awaja aiki acewarsu sai yaji sauki ya dawo to maimakon dauki a'a saima abunda yayi gaba ga matarshi gaba daya ta juya mashi baya ,haka yayita kuka mai ban tausayi , yana tausayin kansa sosai amma yasha alwashin. Sai yasa an nemo mashi iyalan Abdurahaman ya fayyace masu komai tareda neman gafarar su...............✍🏼 😣😣 *yau dai abun bawani armashi wallahi yau banajin typing din sam amma kuyi hkr mutara a page na gaba*πŸ˜‰πŸ˜‰ *SANARWA*πŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ *Ina matan da suke fama da butsarin namiji wato namiji marar sakin fuska namiji masifaffe namijin mai wuyar sha'ani , murdadden namiji dakuma namijin dake wulakanta matarshi ko namijin da kikeso amma baya sonki* *Ko wanda kishiya tasha gabanki sam mijin baya ganinki sai dai kishiyarki to ku garzayo wajen Mmn yusup mai kayan mata domin samun wani taimako wanda ya kasance ingantacce ne wanda ba bokanci acikinshi sai dai tarin taimako ,idan har aka baki wannan taimakon to insha Allah kekam matsarki tazo karshe zaki samu mijinki a tafin hannunki zai kasance baya ganin kowace mace agabanki zai kasance mai tausayi da jin kai a wajanki , zai kasance mai sauraranki da baki* *lokacinshi akoda yaushe zuciyarshi zatayi laushi akanki duk wani zafin kai nashi to zai sauka da izinin Allah , wannan taimakon 3000 ake badashi wadda ta shirya to tamun magana ta pc ko kuma akira numbar kai tsaye , duk wadda takeso zatamun magana ne sai na mata cikakken bayani akan abun don wannan bayanin nayishi ne kawai a tak'aice, don* *Allah in baki shirya ba karkimun magana mu batawa juna lokaci kibari kin shirya sannan*πŸ™ŒπŸ»πŸ™ŒπŸ» 09035027743 call or Whatsapp mmn yusup sokoto,* *Karku manta ba tsibbu ko bokanci acin harkarmu Ayar Allah ce kawai*πŸ₯°πŸ₯° *Maison taci gaba da samun wanna littafin akan lokaci ga link Nan tayi join Amma don Allah in baki karantawa karkishi inkuma kinsan bakya iyayin comment nanma karkishiga don Allah* [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_20 ...................wani irin hucin zafi ya fitar daga bakinshi jin furucin Momma , hannu biyu yasa ya damk'i sumar kanshi da k'arfi kamar zai cireta yana fadin "Miyasa miyasa Momma tuni zuciyarshi ta karye durk'ushewa yayi a wajan tareda fashewa da wani irin kuma mai tsuma zuciya da ban tsoro , kuka yakeyi wanda tunda uwarshi ta haifeshi bai ta'ba yin irinshi ba ,baima san yadda akeyin kukan ba don shi tun yana yaro abune mai wuya kaga hawayenshi bare kuma kukanshi , Jin sautin kukanshi ba k'aramun dukan zuciyar Momma yayi ba hankali tashe ta zabura ta bude d'akin ta nufi falon , Tana zuwa ta iske Ibrahim na lalla'bashi duk ya rikice saboda ganin irin kukan da Abokinshi keyi wanda har ya zarta hankali dukda ba ihu da kururuwa yake hawayene kawai sai sheshekar da yakeyi wanda takeyi kamar zata tafi da numfashin shi , Cikin sanyin jiki ta k'arasa kusa dashi ta sanya hannunta cikin nashi ,d'ayan kuma ta rink'a shafa kanshi dashi a hankali, Jikinshi yayi zafi sosai hakama kanshi kamar garwashi , haka yake tun yana yaro in ranshi ya 'baci tuni zazzafan zazzaΙ“i zai rufeshi , Yadda Momma ke mashi yasa a hankali jikinshi yafara rage tawar da yakeyi ya fara samun nutsuwa yayinda zafin zuciyarshi ke raguwa a hankali ,ajiyar zuciya kawai yake saukewa , ganin hakan yasa Momma tafara mashi nasiha mai ratsa zuciya , saida ta kwashe sama da 30mnt tana mashi nasiha da kawo mashi hujjojinta na hanashi abunda yakeson aikatawa , Har lokacin baice komai ba sai zamewa da yayi ya kwanta akan k'afafunta tareda sake runtse idonshi , Ibrahim dake gefe yana kallon su yayi gyaran murya yace " duk abunda kika fad'a Momma kinada gaskiya kuma banga laifinki ba , domin taron wad'an nan mutanen kamar taron aradu da ka ne , hatsabibaine na gaske sannan komai zasu iya aikatawa ga duk wanda yace zaija dasu , to amma hakan bashi zaisa mu zuba masu ido suci bulus ba yazama doli muma muyi amfani da matsayinmu wajan ganin mun kwatowa kanmu 'yanci A matsayin da Hisham yake kai a yanzu a dakuma matsayina na babban *Lauya* mai zaman kansa zamuyi amfani da wannan damar don ganin cewa mun gurfanar da wadan nan azzaluman agaban koto ,Kuma zamu jajirce don ganin cewa an hukuntasu dai dai da abunda suka aikata ............." A'a Ibrahim bazaku iya ja da wadan nan mutanen ba, ina gudun abunda yafaru abaya ya sake faruwa , bakuda karfin da zaku ja da wadan nan mutanen sunfiku komai tunda suke da abunda zasu iya juya duk wanda sukaso a lokacin da suka so ,.................."a'a Momma Ina tabbatar maki da zamuyi nasara akansu , karki hanamu don wannan jahadi ne zamuyi ko ba don mu ba bakisan iyakar mutanen da suka jefa a hadari irin wannan ba bakisan iya adadin mutanen da suka cuta ba ,tabbas zama da irin wadan nan mutanen ba karamin hatsari ne ga al'umma koba komai harda k'asarmu zamuyiwa aiki, zamu shiga mu fita har sai munga cewa sun fuskanci hukunci daidai da laifinsu insha Allah kuma nasan DPO ma zai mara mana baya sosai, Tunda Ibrahim yafara magana Hisham ya kafeshi da ido bayako k'yaftawa tuni k'wak'walwarshi tafara aiki lokaci daya wani tunani ya fado mashi a rai , tabbas da wannan hanyar zaiyi amfani wajan ganin sunyi mutuwar walakanci , duk da ba haka yaso ba amma zaiyi amfani da wannan damar don ganin bayan azzalumai ,duk acikin ranshi yake wannan tunanin don har wannan lokacin yakasa bude bakinshi ma bare yayi magana , Momma da ta jima shiru batace komai ba , sai can ta sauke ajiyar zuciya tace "to shikenan Ibrahim Allah yamaku albarka Allah ya shige maku gaba , tabbas Allah yana bayan mai gaskiya don haka nabaku goyon baya dari bisa dari ", Daga haka sukaci gaba da tattaunawa da Ibrahim , Hisham kam baice masu kala ba saima idonshi da ya rufe kamar mai bacci azahiri kuwa tuni ya lula duniyar tunanin yadda zai gudanar da shirinshi cikin kankanin lokaci don bazai iya jure tsawo lokaci batare da ya kawar da wadan da suka shiga tsakaninshi da farincikinshi ba , Bayan tafiyar Ibrahim magani Momma tabashi kasancewar har lokacin jikinshi da zafi sosai alamar zazzaΙ“i ,baijima da shan maganin ba bacci yayi awon gaba dashi don kaso mafi yawa na daga cikin damuwarshi ya sauka kasancewar ya samo bakin zaren, ________________________ Washe gari Da wuri Hisham ya tashi yayi wanka tareda shirin shi na fita aiki , a falo ya tadda Momma zaune ta buga uban tagumi tana tunanin da ya zame mata jiki , ba abunda yake damunta irin kad'aici ,sosai takeson d'an nata yayi aure kodon ta huta da zaman kad'aicin nan amma taga alamar shi babu ma wannan a gabanshi , ko maganar aure bayaso ayi mashi gashi kuma yanzu yanason sa kanshi a wata sabuwar rigimar itakam da zai yarda da ya rabu dasu da sannu Allah zaiyi maganinsu don zalunci baya taba d'orewa, A hankali taji hannunshi akan nata , juyowa tayi ta zuba mashi ido ,murmushin karfin hali yayi mata kamun cikin shak'ak'k'iyar muryarshi da bata fita sosai tun jiya yace "kiyi hkr Momma kiyi mana addu'a ba abunda zai faru insha Allah, daga haka ya mik'e yanufi hanyar fita cikin takunshi na cikakken namiji maiji da karfi da k'urciya, Bin bayanshi kawai tayi da kallo har ya kai bakin k'ofa tace "haka zaka fita bazaka karya ba,"? Batare da ya juyo ba yace " na koshi Momma," yasa kai yayi ficewarshi , Office dinshi yafara zuwa saida ya rage wasu ayukkan sannan ya fito ya nufi office din DPO Huzaifa Umar , Da sallama yashiga office din , bayan ya sara mashi ne yabashi izinin zama , gayar dashi Hisham yayi kamun yace "sir wajanka nazo da wata muhimmiyar magana ina fatan zaka goya mana baya ta yadda zamu samu abunda mukeso ," Ajiye biron dake hannunshi sir Huzaifa yayi ya zubama Hisham idanunshi yana nazarin shi kamun yace " ok Hisham ina saurarenka ,mi ya faru ?? Duk abunda ya faru tun daga farko har karshe Hisham ya sanar dashi zuwa lokacin idanunshi sun sake rinewa sosai da tsabar fitina da burin daukar fansa, Tunda yafara maganar DPO ke kallonshi shima idonshi har ya kada yayi jajir tsabar yadda labarin ya ta'bashi , ranshi ya sosu sosai don ba abunda ya tsana kamar irin yadda ake raina *Jami'in dan sanda* abun yana mashi ciyo sosai yadda duk wani abunda zai faru yan sanda sune farkon wad'an da ake nema Don kawo d'auki a wajan , haka zasu shiga duk hadarin waje don ganin sun Bama al'umma kariya amma sukuma mutane basuda abun wulakantawa sai *dan sanda* bashida wata k'ima ko wata daraja a idanun jama'a saboda kawai 'bata garin cikinsu wanda kuma ba duka aka taru aka zama daya ba , Yayinda gefe d'aya masu mulki da masu kudi kecin dudduniyar yan sanda masu gaskiya da rikon amana saboda kawai takamar sunada kudi da mulki wanda suke ganin sunfi k'arfin hukunci duk abunda zasuyi shiyasa duk Jamiin da yace zai ja dasu to kuwa zasuga bayansa ne ta hanyar amfani da karfin mulki da kudi wajan saukeshi daga kan aikinshi yayinda wasu ma zasu kaudasu daga doron kasa kamar yadda sukayi akan mahaifin Hisham wannan ba sabon abu bane amma tabbas a wannan karon shima zai tauna tsakuwa don aya taji tsoro indai yana kan wannan kujerar tasa to tabbas sai yaga abunda ya turewa buzu nadi lokaci yayi da zasu tashi tsaye don memawa kasarsu da jami'ansu 'yanci bazasu sake yarda da wani tozarci ko cin zarafin *yan sanda* ba insha Allah, "Wannan babban al'amari ne wanda doli sai yaje sama zanyi iyakar kokarina na ganin munsamu goyon baya daga sama kuma daga wannan lokacin bazamu sake saurarawa ire-iren su Alhaji Manu ba a garin nan zamuyi fito na fito dasu ai ba wanda yafi karfin hukuma dama can k'yalesu akeyi amma yanzu kam ya isa haka ," Cikin tsananin farinciki Hisham yafara mashi gdy duk da har wannan lokacin ba fara'a a fuskarshi amma a maganarshi kawai za'a fahimci yaji dadi sosai , File din da ya shigo dashi ya mikawa DPO yana cewa " wannan file din akan cases din yaran da muka kama ne da hodar ibilis to bincike ya nuna mana cewa yaran su Alhaji Manu ne , inaga da wannan damar zamuyi amfani wajan gurfanar dasu agaban alkali , sanna daga baya zan shigo da wannan case din , " Duba file din DPO yayi da kyau kamun ya jinjina kai yace "eh tabbas kayi tunani kuma cikin ruwan sanyi zasu shigo hannu , amma kamun nan kana buk'atar kwararre lauya wanda yasan aikinsa don hatsabibancinsu yanada yawa inhar bakada kwararan hojjoji to abune mai sauki su juya case din zuwa kanka , sannan Yakamata kasan halin da Inspector Haruna yake ciki kayi kokari kayi control din fushinka akansa don zai mana amfani, " Ok sir zanyi duk yadda kace , amma maganar lauya inada lauya yanzu haka , Haruna kuma anijima zamuje wajanshi ," "To shikenan Allah ya shige mana gaba" "Amin sir ngd sosai" Daga haka yabar office din dama station din gaba daya , _______________________ Direct office din ibrahim ya nufa inda ya gayamashi duk yadda sukayi da DPO , Ibrahim yaji dadi sosai inda sukaci gaba da tsara yadda zasu gudanar da bincikensu, ______________________ Hisham, Jafar, Asmy, gaba daya sun duk'ufa akan binciken da sukeyi a boye saboda munafukan cikinsu wadan da son abun duniya ya rufewa ido suka sayarda yan cinsu ga azzalumai , Cikin ikon Allah komai yana zuwa masu cikin sauki don sam basuyi zaton zasu samu sauk'in bincikensu irin haka ba , yaran su Alhaji Musa sun taimaka masu k'warai wajan basu hadin kai kasancewar ba karamar azaba Hisham ke gana masu ba cikin kankanin lokaci suka fita daga hayyacinsu da sun gashi take jikinsu ke fara rawa,, duk tambayar da zai masu kuwa take zasu bashi amsa har rigegen fada mashi sukeyi , (hhhhhhhhhhh su Goga anji maza) ________________________ A yau sukayi gagarumin shiri na zuwa kamo su Alhaji Musa inda dama can duk wani motsinsu akan idon jami'an tsaro ne don tuni aka sanya masu ido sosai , shiri sukayi sosai sanin cewa su Alhaji Manu da muggan yan daba sosai wadan da suke amfani da muggan makamai wanda suke fatan har su sukama shiyasa tun farko basu kama kowa ba sunason ne su hada masu tarkon da zasu kamasu gaba daya, ______________________ Zaune suke sunyi jugum jugum ,ba k'aramar damuwa suke ciki ba ganin k'aramun abu yana nema yafi karfinsu , sun rasa dalilin da wasu abubuwan ke faruwa dasu , yanzu duk yadda zasuyi wani sirri ko a waya ne to sai sunji maganar ta fita sun rasa wake masu zagon kasa ne , waya shirya ganin bayansu ne ,?? bayan duk wasu kadarorinsu a hankali iftila'i ke fada masu d'ai bayan d'ai , sosai suka fara zargin junasu da cin dudduniyar juna inda suka fara tada jijiyar wuya , sai daga bayane Alhaji Buba ya ankarar dasu akan Yakamata koma minene to subar k'asar kawai har komai ya lafa sai su dawo kuma zasu samu damar da zasuyi nazarin inda aka samu wannan 'barakar, gaba d'ayansu sun yarda da wannan shawarar wannan yasa sukayi shirin barin kasar zuwa Dubai, Abunda suka tarar ne yayi bala'in daga masu hankali don sun nemi paspo dinsu sama ko k'asa sun rasa , wannan yasa suka hadu gidan shak'atawarsu don neman mafita, Suna haka suka fara jiyo jiniyar motocin yan sanda tacika wajan , mamaki ne da tsoro suka kamasu lokaci daya ganin inda suke sam ba'a cikin gari bane dajine sosai wanda ba wanda ya san da gidan dagasu sai yaransu , to mi hakan ke nufi kenan ???? Kamun suyi wani yunk'uri har yan sanda sun cika gidan inda suka fara yin gaba da yaransu kamun suma su fito dasu , kallo kallon sunakayi tsakaninsu da Hisham inda suke mashi kallon zamu hadu da kai yayinda shikuma yake masu kallon na gama daku, ahaka aka sanya su a mota akayi gaba dasu ,su Hisham saida suka shiga gidan sukayi bincike kamun suka fito suma suka bi bayansu, _____________________________ Kotun tacika makil ba masak'ar tsinke , kowa so yake yaga yadda wannan shari'ar zata kaya da mutanen da kowa kema kallon mutanen kirki ashe su din sun kasance azzalumai masu ha'intar kasarsu ta hanyar shigowa da muggan makamai kayan maye da lalatattun magunguna wadan da Allah ne kadai yasan iya adadin rayukkan da suka salwanta a sanadiyar su, jamaar gari sai Allah tsine suke masu , Bayan gabatar da shaidu da kwararan hojjoji kotu ta gamsu da cewa Alhaji Buba da Alhaji Musa da Alhaji Manu suna aikata laifukan da ake zargin su akai sannan tabbas hukunci zai tabbata akansu kamar yadda kundin mulkin k'asar ya tanada , ana shirin yanke masu hukunci ne Bariste Ibrahim Umar ya mike tsaye ya shigar da k'ara akan kisan Da su Alhaji manu sukama Jami'in dan sanda Inspector Abdurahaman , Jin wannan bayanin yasa kotun harmutsewa da hayaniya jin wata sabuwa kuma inji yan caca , Yayinda cikinsu Alhaji Musa yayi wata irin murdewa tuni suka fara zare idanu alamar rashin gaskiya gashi dama a tsorace suke da hukuncin da za'a yanke masu sai ga kuma wannan tashin hankalin, Da kyar aka samu mutane suka nutsu inda aka shiga gabatar da Shari'a yadda Yakamata , su Hisham sun tanadi duk wasu shaidu da zasu bukata don basa son ko kad'an ad'aga shari'ar sunfi son yau yau ayita ta k'are kawai, Acikin shaidun sun gabatar da record din da shi marigayi inspector Abdulrahaman yayi a wayarshi lokacin da suke mashi barazana ,wanda tuni wayar na hannun Momma sai a wannan lokacin ya tabawa Hisham wayar ,dama kuma tana sane da wannan daukar don a kanta ne ma ta boye wayar, Sannan sun gabatar da direban babbar motar wanda aka biyashi don ya haddasa hadarin , Saikuma yaran da suka taimaka wajan ganin shirinsu ya tafi dai dai , Shaidar su ta karshe shine Inspector Haruna wanda aka shigo dashi a keken guragu saboda sam bazai iya tashi ba bare har yy tafiya, Shi yayiwa kotun cikakken bayani akan yadda suka shirya komai har zuwa lokacin da suka samu nasarar aikata shirinsu yakuma gabatar ma da kotun dun wani recording da ya rink'ayi dasu Alhaji Musa a duk lokacin da suke magana batare da sun sani ba , Nan aka bawa magatakarda ya jona ga tv yadda kowa zaiji , aikuwa sai ga muryarsu Alhaji Musa radau lokacin da suke kulle kulle su, da wannan kwararan hojjoji da shaidu kotu ta yanke masu hukuncin Daurin rai da rai agidan kaso tareda horo mai tsanani hade da tarar kudi masu yawan gaske ,haka aka kada keyar su Alhaji Musa tareda direban da wadan nan yaran nasu da Inspector Haruna zuwa gidan maza ,yayinda mutane keta Allah wadai dasu suna tsine masu , ____________________ A wannan rana Momma tayi kuka mai yawa kukan farinciki Allah ya nuna mata ranar da ta jima tana jira an hukunta wadan da sukayi sanadiyar rabata da farinkinta , sai yanzu tasamu wani abu da yayi mata tsaye a mak'oshi tun lokacin da ta fuskanci kashe mata miji akayi ya fada , Hisham da Ibrahim kuwa cike suke da farinki suma duk da ba haka sukaso ba sun so ne a yanke masu hukuncin kisa nan take to amma yanzu ma Alhamdulillah, DPO ma yaji Dadi sosai koba komai sun rage mugun iri, *BAYAN SHEKARA DAYA*.............✍🏼 *Mun kada labarin su Alhaji Musa ne a gurguje don suna bata mana lkc inason mushiga gundarin labarin ne ,tabbas cakwakiya na gaba wannan sharar fage ne* *YAKAMATA MUSAM WADAN NAN TAMBAYOYIN*πŸ‘‡πŸ‘‡ Miyafaru da Hisham yabar gida Ina Momma take da Abokinshi ibrahim Wacce Mariya da ahalinta suwa sukayi mata fyade har tarasa ranta , wanene zayyan wacece Amna su waye iyayensu Wanene Amna keso sannan waya kashe zayyan Wanene Baffah da ahalinshi Ya makomar Hisham da Muneeba idan su Baffa suka tafi suka barsu *_tambaya mai muhimmanci shin ina mahaifiyar Muneeba*????? Miyafaru da ita sannan wace fansa ce Hisham yake cewa zai dauka Shin zai dauki fansar ne kokuwa zai hakura ??? *Hmmmmmmm akwai rigima sosai a gaba yanzu book ya fara ku taimaka kubani hadin kai wajan yin comment ta yadda zakuci gaba da samun typing akai akai* Pls ku tayani shareπŸ₯° [6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *_domin shiga grp dinmu na Telegram Danna wannan link din_*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ https://t.me/joinchat/WBy_jhN2F8-1BJ0z1jtqsQ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_19 ....................cikin tsananin tsoro duk suka zaro idonsu tareda d'ora hannunsu akaiπŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈganin irin shurin da Hisham yayi da Haruna wanda k'ara d'aya yayi bai koma koda motsi ba , gaba daya idonsu kamar zasu fado k'asa yayinda cikinsu yayi wata irin murd'awa , Hisham kam baima kula da Haruna ya daina motsiba tsabar yadda zuciyarshi da idonshi suka rufe , sai ma k'ok'arin sake dukanshi da yakeyi , aikuwa 360 Ibrahim ya k'araso kusa da Hisham ganin ya daga k'afa zai saike d'auke bawan Allah da wani zazzafan shuri wanda yanada tabbacin in yayi mashi shi sai Allah idan ,zai rayu wannan yasa ya rik'e Hisham gam cikin rawar harshe yake fad'i , " Pls Hisham ka dawo cikin hankalinka mana ka tsaya muyi komai a nutse karkayi mana kisan kai pls ," Duk maganar da yakeyi sam Hisham baijinshi sai ma k'ok'arin k'wacewa da yakeyi, Matar Inspector Haruna kuwa tun lokacin da Haruna yabuga wannan uwar k'arar ta rugo aguje zuwa d'akin , ganin abunda ke faruwa ne yasa ta fita aguje tana ihu da kiran ataimakamata za'a kashe mata miji , kamun kace mi har gidan yafara cika , Samarin unguwar da zafinsu suka shigo amma ganin Hisham sanye da kayan yan sanda sannan kallo Daya zaka mashi kasan cewa tabbas wannan ,Zaki ne da yake ganiyar farauta duk wanda yayi gigin shiga gabanshi kuwa to tabbas sai dai uwarshi ta haifi wani bashi ba , wannan yasa suka maida wuk'ar suka shiga lalla'ba Hisham da kyar tsoffin unguwar suka samu suka raba Hisham da Haruna wanda baimasan inda kansa yake ba, Ibrahim ne ya sanya shi mota sannan yaja motar aguje suka bar unguwar don ya tsorata da yanayin abokin nashi tabbas in aka barshi zai iya kashe Haruna , gashi zafin zuciya yasa baiko bari Haruna yabashi shaidun da yace zasu taimakamashi wajan kama wadan nan azaluman ba , Mansur kuwa da yayi mutuwar zaune sai yanzu ne yasamu damar iya motsa jikinshi tabbas ya tsorata da muguwar zuciya irin ta yayan nashi , ashe haka yayan nasu yake ashe k Zai iya kashe mutum sukutum saboda kudi kuma mutumin ma Abokinshi wato shiyasa yake yawan faΙ—in Alhaki ne ke bibiyarshi ashe shi yasan mugun abunda yake aikatawa wama yasan iya adadin mutanen da yakashe saboda son zuciya gashi nan yanzu wa gari ya waya , ina wadan da yayiwa aikin suke , ? Sun gujeshi saboda yagamayi masu amfani , Duk da yanda yakejin zafin shi kanan ya daure yasamo mai nafef suka sanyashi suka nufi asibiti dashi don har wannan lokacin bai farfado ba, Direc gida Ibrahim ya wuce dasu zuwa lokacin gaba daya Hisham yagama ficewa daga hayyacinshi sam baya gane komai sai wasu irin surutai yake marasa kan gado , don abun ba k'aramun dukan k'wak'walwarshi yayi ba musamman da Haruna yamashi bayanin duk irin yadda suka shirya wannan had'arin gaba daya Abbanshi kawai yake gani a idonshi kamar a gabanshi hadarin ya faru, Kamashi Ibrahim yayi suka shiga cikin gidan , a falo suka tarar da Momma , Tana ganinsu a wannan halin ta zabura a firgice tana tambayar abunda ya faru, "Lafiya Ibrahim mi yasameshi, tayi maganar a tsorace don ganin halin da d'an nata yake ciki yayi mugun bata tsoro don bata taΙ“a ganinshi a irin wannan halin ba ko lokacin mutuwar mahaifinshi kuwa , Zaunar dashi ibrahim sannan ya dubi Momma cikin karfin hali don shima ba k'aramun tashin hankali ya tsinci kanshi aciki ba yau yace " bakomai Momma ki kwantar da hankalinki ki tofa masa addu'a PLS ko ya dawo cikin hayyacinshi ," "Yazaku shigo cikin irin wannan yanayin sannan kacemin ba komai Ibrahim , ?" Tayi tambayar jikinta na rawa, "Kinga Momma ki kwantar da hankalinki an gaya mashi maganar da ta d'aga hankalinshi ne amma kibari ya nutsu zan maki bayanin komai ," Da mamaki Momma ta dubeshi har zatayi magana kuma sai ta fasa ta nufi Hisham ta zauna a kusa dashi tafara tofa mashi addu'o'i , inda daga baya tafara maimita innalillahi wa Inna ilaihin raji'un , a bayyane , a hankali shima yakama yana maimaitawa ,ganin hakan yasa Momma tayi murmushi a ranta don tasan koma minene to yanzu zai samu nutsuwa , aikuwa sai gashi a hankali yafara dawowa cikin hayyacinshi , lumshe idonshi yayi yanajin yadda kanshi ke wani irin sarawa kamar zai cire ga gawata irin k'ishi da yake ji bakinshi ya bushe sosai amma sam yakasa bude baki yayi magana , sun jima a haka sai da suka tabbatar da yadawo cikin hankalinshi sannan suka sauke ajiye zuciya gaba daya ,yayinda Momma ke cike da tunanin abunda yasamu dan nata har yafitar dashi daga hayyacinshi , Juyowa tayi ta zubama Ibrahim ido tace "Ibrahim ka gayamun mi yake faruwa , sam karka 'boyemun komai Ni musulma ce kuma nasan Ζ™addara mai kyau ko akasin haka nayi imani ba abinda zai samu mutum face da sanin Allah ta'ala , nasan Allah baya Ι—orawa bawa abunda bazai iyaba don haka ka gayamun kawai ko na samu nutsuwa a raina, Hmmmm Ibrahim yayi ajiyar zuciya kamun a hankali ya bud'e bakinshi yace " Momma dama akan Abba ne....., Wani irin fad'uwa gaban Momma yayi amma sai ta danne tace " ina jinka wane Abban kenan?" "Abba dai na nan gidan Momma Abban Hisham , to daga wajan Abokinshi Inspector Haruna muke , bisa dalilin son ganinku da yakeyi keda Hisham , to sai dai Hisham yace bazaije dake ba sai dai yaje shikad'ai inyaso koma minene shi sai ya gayamaki , Nan dai yashiga bata labarin abunda ya faru tun zuwansu har kawo yanzu wanda tunda yafara maganar Momma ke kuka sosai har yagama bata labarin wanda zuwa lokacin shima kukan yakeyi saboda yadda yake matuk'ar jin tausayinsu a ranshi yana tunanin in shine wannan al'amarin yafaru dashi ya zaiji , Cikin muryar kuka tafara magana , "Dama nasani ,najima da sanin cewa kashemun miji akayi saboda kawai an tsani irinsu a k'asar nan duk wani wanda yace zai kawo gyara a kasar nan tamu to za'a waye gari ne babushi a doron k'asa miye laifinsu?? saboda kawai suna aiki akan gaskiya? Ko saboda basa goyon bayan zalunci da azzalumai ,? shiyasa aka za'bi kawarda ire-irensu a doron Ζ™asa, wannan dalilin ne yasa na tsani aikin nan nashi saboda a kullum cikin barazana yake sun jima suna shirya mashi gadar zare kamar yadda suka jima suna kawarda ire-irensu ak'asar nan" Tunda tafara magana daga Hisham har Ibrahim ido suka zubamata da mamakin kalaminta , cikin karfin hali Ibrahim yace , "Amma Momma kinsan da wannan kuma kikayi shiru babu wani mataki da aka dauka"? "Hmm wane mataki za'a dauka ibrahim , ko in nayi magana zasu dawomin dashi ne ,sun riga da sun cuceni sun rabani da bangon jinginawata banida kowa sai Allah sai shi da Hisham ,nasan ba abunda za'yi ko na d'aga maganar nan mussaman ma da banida wasu kwararan hojjoji, ko inada hujjar ma bawani amfani don mai kudi shikeda hujja a yanzu akoma minene , sannan ina 'boye komai ne saboda Hisham nasani in ya sani komai zai iya faruwa don bazai taba yafe masuba kamar yadda suma bazasu taba kyaleshi ba zasu iya bin duk wata hanya don ganin sun cutar dashi kamar yadda suka cutar da mahaifinshi , abunda kuma bazan iya jura ba a wannan lokacin Hisham shikadai nake kallo naji dadi wannan yasa tun farko na barsu da Allah nasan Allah ba azzalumin bawansa bane ko yaushe ne Allah zai Mana sakkaya in a duniya in a lahira, Izuwa yanzu kam idonshi ko kalluwa basayi tsabar jan da sukayi kamar jini zaifita daga cikinsu a hasale ya mike tsaye lokaci daya ya kaima wani table dake kusa dashi duka wanda ya kasance na glass ne aikuwa nan take ya tarwatse yayinda lokaci daya hannunshi yafara zubda jini saboda glass din da suka shigar mashi a hannu , wani irin gurnani yakeyi kamar wani zaki cikin kakkausar murya yafara magana , " "Wallahi wallahi duk sai na shirya masu gadar zaren da zata rufta dasu wallahi sai naga bayansu da hannuna yadda suka kashemun mahaifi haka zan bisu d'ai bayan d'ai ina kashesu inyaso nima a kasheni amma tabbas bazan barsu ba , bazan taba barinsu ba *sai na dauki fansa* wannan alkawarine, Dukkansu idanu suka zaro suka zuba mashi don kuwa yanayinshi ya firgita tunaninsu kallo Daya zaka mashi ka tabbatar har cikin zuciyarshi ne zai iya aikata abinda ya fad'a ga hannunshi na zubar da jini sosai amma bai kulaba kamar ma ba a jikinshi ciyon yake ba , wani irin tsoro ne ya daki zuciyar Momma lokaci daya ta fashe da wani irin kuka kamaun tafara magana , "Hisham indai Ni na haifeka to tabbas ban yarda ka dauki hukunci da hannunka ba ban hanaka neman hakkinka ba amma bata wannan hanyar ba idan kuwa har kace zaka dauki hukunci a hannunka to kuwa bazan taba yafe maka .........daga haka ta juya tayi shigewarta d'aki tana gunshek'ar kuka gaba daya sun tado mata da mikin mutuwar mijinta ga kuma halin da Hisham yake ciki ta tabbatar da idan har ta kyaleshi to zai iya kisan kai wanda bata fatan hakan sam...............✍🏼 *Narage yawan typing sai naga yanayin comment dinku tukun*😜😜😜😜 *Akwai zafafan kayan mata kala kala hade da ingantacce maganin nono maganin sanyi maganin hips magani kiba uwa uba kalolin kayan mata naji da fadi kedai garzayo kar abaki labari ina Sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_21 *_BAYAN SHEKARA DAYA_* ......................Watanni hudu kenan da akayi za'ben sababbabin gwamnoni ak'asar ta Nigeria , Emeka John shine yasamu nasarar lashe za'be a garin na Lagos inda *Alhaji Saminu sulaiman* yake a matsayin mataimakin shi , wato *Deputy governor* , wata daya kenan da rantsar dasu da akayi , Alhaji Saminu sulaiman yakasance haifaffen garin na Lagos ne tun kaka da kakanni , shi din tashin Lagos ne gaba da baya , asalin iyayenshi bawasu masu kudi bane saidai sunada rufi asiri sosai ta yadda har suka samu damar Bama yaransu ilimin zamani wato ilimin boko kasancewar Saminu yanada kokari sosai da son karatu saboda babban burinshi a rayuwa yasani bazai taba cikaba sai yanada ilimin boko , sam iyayensu basu damu da 'ya'yan nasu suyi wani karatun Islama ba saboda ba wannan ne a gabansu ba boko kawai sukasa a gaba , rayuwarsu rayuwa ce ta yanci duk abunda sukeso shi sukeyi ba kwaba ba hantara ahaka har Saminu ya kammala karatunshi , yasha wahala da gwagwarmaya sosai kamun yasamu cikar burinshi , inda kudi suka tsaya mashi aka fara damawa dashi , har yakai wannan matsayin da yake kai a yanzu na *Mataimakin gwamna* , Su hudu ne a wajan iyayensu maza ukku mace d'aya , wanda Alhaji Saminu shine babba acikinsu , Matarshi d'aya Hajiya Hadiza wadda suke kira da Mom , mom asalin shuwa'arab ce tanada tsananin kyau sosai kamar balarabiya, wanda wannan kyawun nata shi yaja ra'ayin Saminu gareta wanda hakan yana d'aya daga cikin burikanshi nason ganin ya ajiye mace mai tsananin kyau ta gaban kwatance , yadda zata haifa mashi yara kyawawa , Yaransu biyu *Zayyan* shine babba sai *Amna* dake binshi yarane da suka tashi cikin tsananin gata marar misaltuwa wanda ko uwar data haifesu bata isa ta ta'basu ba Musamman *Zayyan* wanda babu abunda Dad keso kamarshi , wannan yabawa Zayyan damar yin duk abunda yakeson ba k'wafa ba hantara , idan nace komai to ina nufin komai , saboda duk abunda , Zayyan zaiyi to dai dai ne a wajan mahaifinshi , Zayyan dan casu ne sosai don aduniya ba abunda yake burgeshi kamar rawa da wak'a , wannan yasa duk da karatun da yayi a k'asar waje akan wak'a yayishi , bashida aiki sai yawon clube clube Shine shaye shaye da neman mata kamar hauka ,yadda yakeda kyau mai daukar hankali da yadda yake 'bari da kudi yasa mata ke bibiyarshi kamar hauka , wanda takai har a cikin gidansu ma kwana yake da mata kuma Dad Yana sane ya kyaleshi a cewarshi bazai takurama yaronshi ba , abun na damun Hajiya Hadiza kwarai amma ba yadda ta iya don tasan tariga da ta tafka babban kuskure tun lokacin da ta za'bi Saminu sulaiman a matsayin uban 'ya'yanta , sai yanzu take Allah wadai da halinta nason abun duniya wanda shine ya mata jagora ga auren miji irin Saminu , Amna ma bawata cikakkiyar tarbiyane da ita ba sai dai da sauki ba kamar yayanta Zayyan ba , itadai tafi auki wajan yin muguwar shiga kamar ba diyar musulmai ba kullum shigarta iri daya ce 'bingilallun k'ananan kaya riga da wando ko riga da siket irin masu fitar da tsiraici bata damu dasa d'ankwali ba ma bare akai ga wani abu waishi gyale , haka zata sake dogon gashinta har gadon baya kamar wata yar indiya ,duk inda zata haka take zuwa tana rayuwarta ne yadda takeso a cewar ta kayanmu na hausawa nauyi suke mata sam bazata iya sasu a jikinta ba Sai dai ita duk abunta bata huld'a da maza ahaka suke rayuwarsu cike da 'yanci babu kwaba babu hantara, ____________________ Yauma kamar kullum tafe suke a mota shida shak'iyan abokanshi gudu sukeyi na fitar hankali ga kid'a dake tashi amotar kamar zata fashe sai ihu da iface iface sukeyi acikin wannan yanayin suka shigo unguwar gwagulori , Tsaye yake yana jiran wani mai nafef ya wuce ya tsallaka titin , sam bai kula da motar dake tafe ba kasancewar motar aguje take kamar walk'iya shikuma gadan gadan yanufi titin zai tsallaka , baiyi aune ba sai ganin mota yayi gabanshi ta tunkaro shi gadan gadan, kamun ma yayi wani yunk'uri tuni sunbi ta kanshi sun wuce sai ganin yaron akayi yayi sama ya fado tim kanshi ya fashe hakama hakoranshi tuni suka zazzage tsabar buguwar da ha'barshi tayi ,tuni jini ya Ι“alle mashi kota ina, su kuwa banda ihu da kirari ba abunda sukema Zayyan wani daga cikinsu yace da kyau baba shiyasa kake burgeni Allah don in ba haka akema 'ya'yan talakawan nan ba sam bazasu shiga hankalinsu ba inbanda iskanci kazo kana wannan tafiyar sai kace titin na ubanka ne , daya daga cinsu ya zuk'i taba ya fesar da hayakin yace bar Dan bura'uba Ni shiyasa bana masu sassauci duk shegen da nagani akan titi yana tafiyar tak'ama tuni zan bi takanshi inyi tafiyata kuma ba abunda za'ayi don mune da garinnan ,wani irin ihu suka koma sanyawa lokacin da suka hango wata tsohuwa akan titin zata tsallaka , aikuwa saura k'iris su dauketa Allah yataimaketa wani saurayi da yaga tahowarsu yayi hanzarin janyota gefen titin da sai dai wata ba itaba , tsaki Zayyan yayi don yaso ace ya banke tsohuwar nan amma Allah ya taimaketa haka dai sukaci gaba da tafiyarsu suna shak'iyanci akan haya, kamun kace mi mutane sun taru akan hanyar inda akayi kan yaron aguje sai dai tunda ya fado ko shurawa baiyiba yace ga garinku nan , mutanen da abun yafaru a gabansu sun girgiza sosai sunkuma tausayawa iyayenshi , acikinsu ne aka samu wanda yasan iyayen yaron inda aka je aka gaya masu wannan bakin labarin , sun girgiza matuka kuma sunshiga matukar tashin hankali.................yau dai banji labarin nayimun dadi ba sai gobe nacigaba β›ΉπŸ»β€β™€οΈβ›ΉπŸ»β€β™€οΈ πŸ‘©πŸ»β€πŸ¦° *INA MAFITA*???πŸ‘©πŸ»β€πŸ¦° *BY MMN YUSUP*πŸ₯° Zaune suke acikin katafaren falon da yagaji da had'uwa sai dai kallo d'aya zaka masu ka tabbar suna cikin danuwa matuk'a ,duba da yadda kowaccensu ta buga uban tagumi tare da fad'awa cikin kogin tunani, Su ukku ne a falon , Zainab Aisha da Balkisu k'awayene tun na yarinta duk inda zakaga daya to sauran ma zaka gansu duk da auren da sukayi hakan bai sa k'awancensu yayi rauni ba saima abunda yayi gaba, yanzu kuwa babbar matsala ce ta tarasu agidab Bilkisu gaba dayansu suna cikin matsalar da sun rasa hanyar da zasubi don ganin sun daidaita rayuwar aurensu suma su samu farinciki kamar kowace mace da ta amsa sunanta agidan mijinta, Suna haka sukaji sallamar k'awarsu *Sharifa* wadda dama zaman da sukayi jugum jugum ita suka tsaya jira aikuwa sunajin sallamarta gaba dayansu suka d'ago kansu suka zuba mata ido cike da sha'awa ganin yadda take das das abunta kullum kara kyau take saboda yadda take samun kwanciyar hankali agidan aurenta , ba kamar su ba da kullum cikin rashin zaman lafiya suke da mazajensu , Rungume junansu sukayi suna murnar ganin juna bayan sun natsu ne Sharifa ta dubesu tace wai yanaganku duk wani iri kamar kuna cikin damuwa , "AI in kinji damuwa d'aya kenan yar uwa muna cikin babbar matsala dukkanmu kedai ki fara hutawa sai musan abunyi don naga wankin hula yana neman kaimu dare ," cewar Aisha , " wane irin hutu kuma aisha ai banga ta hutu ba kun dagamun hankali pls kumin bayanin abunda yake faruwa ko nasamu nutsuwa ," Hmmm ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke tace dukkanmu matsalarmu kusan iri d'aya ce duk da ta wani 'bangare munsha bambam , " Plss billy kumin bayani yadda zan fahimta mana, Waccan matsakar dai ce da na taba gayamaki tsakaninmu da mazajenmu yanzu fa abun yy tsamari don wallahi baban sadik gab yake da yimun kishiya saboda matsalar da muke fuskanta , cikin matukar damuwa taci gaba da cewa tun ba yau ba kinsan ina fama da matsalar ciyon sanyi (infection) to itace fa yanzu abun yayi yawa sosai kullum cikin zubar ruwa nake mabanbanta kala ga k'aik'ayin gaba in nafara susa kamar zanyi hauka gaba daya ya daukemun ni'ima kullum cikin jin ciyo nake lokacin saduwa ko bayan saduwa haka wani lokaci zanji kamar an yayyakamin gaba na wannan yasa yanzu nake gudunsa sosai sam banason ya kusanceni sannan in zanyi wata daya bazanji ina sha'awar mijina ba wannan matsalar tasa yanzu sam bamuda zaman lfy kullum cikin tashin hankali muke fushi yakeyi dani sosai narasa abunda zanyi nayi magani har nagaji amma bawani canji kuma ada lafiyata qalau sam ba haka nakeba tafada hawaye na zubomata , "Murmushi shareefa tayi tace wannan itace matsalarki ???" Kallon mamaki tayimata tace eh amma miyasa kk murmushi bayan kinji irin matsalar da nake ciki , ? Murmushi ta komayi tace zakisan dalili nan bada jimawa ba, Kallonta ta mayar ga A'isha tace ke kumafa minene matsalar ki , ? Tsaki A'isha tayi tace don Allah sharifa ki ajiye harkan wasa wanna fa ba abun wasa bane muna cikin matsala ta yadda baki zato amma ki................daga mata hannu sharifa tayi tace " ki gayamun matsalar ki kawai A'isha insha Allah matsalarku tazo karshe , "Wato babban abunda ke damuna duk baifi wanna ramar da nakeyiba , kin ganni banrasa komai ba amma kullum kamar ana dibana ana miya dani , ga k'ank'antar Nono gakuma rashin hips idan na juya maki baya Kamar an daurawa muciya zane kinadai ganin yadda nake to shikuma maigidan ba abunda yakeso ajikin mace kalam cikar kirji dakuma baya wannan yasa yayita siyamun maganin turawa wanda zan dan ciko amma abun ya faskara , to yanzu in Gaya maki zancan da akeyi yaje ya nemi auren wata yarinya yar duma duma babu abunda batada shiyasa duk na shiga tashin hankali don nasan matukar akayi auren nan wlh na kade har ganyena Ni ba auren shi ne damuwata ba a'a ina gudun tazo gidan nikuma nakoma yar kallo tunda Ζ™arara yake nunamun banida abinda yakeso ajikin mace to ya kike gani idan har yasamu abinda yakeso ai.doli nazama yar kallo kawai," Ajiyar zuciya sharifa tayi tace naji taki matsalar kekuma fa Zainab naga kin yi wani zama kamar wata randa tayi maganar tana dariya, Murmushi Zainab tayi tace Ni abu biyu ke damuna gaskiya Na farko wannan k'ibar da ta addabeni kamar ana hurani ga katon tunbi wanda duk yadda zanyi kwalliya bazatamun kyauba a gaskiya inason inrage kibar nan don tana takuramun a mafi yawan lokuta , mussamman ina muka kebe da oga bana iya aiwatar da wasu abubuwan saboda yadda jikina kemun nauyi gashi mijina dan duniya ne dan rayuwa ne amma wannan k'ibar tana takuramana sosai , Abu na biyu kuma *k'arancin ni'ima* ina fama da rashin Ni'ima sosai wanda kesa sam mijina baya samun gamsuwa yadda yadace , muna zaman lafiya da baban Nura kuma yanamun kawaici sosai baicika nunamun ba ,amma Ni da kaina na fuskanci baya samun gamsuwa dani shiyasa sai ya share sam da sati Daya bai nemeni ba shiyasa nakeson na samu *mafita* tun kamun yagaji da yimun kawaici , Nisawa tayi tace to Alhamdulillah kamar yadda nayi maku bayani insha Allah dukan ku matsalarku tazo k'arshe , " "Ta yaya kenan "? Billy ta tambaya ' "Ta hanyar had'aku da fitacciyar matar nan mai saida kayan mata wato *Maman yusuf* zata gyaraku ciki da waje kuma adan kankanin lokaci wanda ina mai tabbatar maku da ku kanku sai kunyi mamaki , A'isha tace "kinga fa sharifa munyi ta jaraba magunguna fa amma sam bamu daceba kar itama muzo mu siya baimana aiki ba" Hmmm A'isha bakisan waye 'yar mutan Sokoto ba ina mai tabbatar maki da insha Allah matsalarku tazo karshe , don nima wata Hajiya ce ta taΙ“a hadani da ita lokacin da nake fama da matsalar budewar gaba , nima a lokacin nashiga tashin hankali wlh saboda yadda gabana ya bude sosai ga yawan tusar gaba musamman in muna tare da oga in gayamaki haka abun ya budemun kamar wani rame tun yana hakuri har yakai da yimun magana akan *Yakamata na gyara kaina* lokacin da nake gayawa makociyata Hajiya farida ita ta hadani da *maman yusuf* cikin ikon Allah kuwa ban rufe sati ba sai gashi nakoma normal tun daga lokacin nake siyan ingantattun kayan ta nake amfani Dasu , ita tamun wani hadi na mallaka aikuwa ku kanku shaida ne akan irin zamantakewar da nakeyi da maigidana , ba boka ba malam sai zafafan kayan da zata hadamaki wanda zaisa mijinki yaji babu wadda yakeson ji da gani sai ke, Ke Billy zaki samu ingantaccen maganin infection Wanda zai wanke maki duk wani dattin mara zaki hade sosai sannan cikin kankanin lokaci ni'imar jikinki zai dawo kamar korama , duk wata matsala ta infection Zaki rabu da ita da ikon Allah, Kekuma A'isha zata baki maganin k'iba Dana hips da na nono ina mai tabbatar maki da zakiyi mamakin yadda zaki koma yar duma duma zakiyi kiba mai kyau ba mai yawa ba sannan hips. Dinki da nonon ki zasu ciko sosai kishiga cikin jerin mata masu aji ina gayamaki na tabbatar da sai kin zo har gida kin godemun , badai bukatar mijinki ki ciko ko ta ina ba to kuwa zaisha mamaki nan da dan lokaci," Kallon Zainab tayi tace na dawo gareki zainab , *maman yusuf* tana hada wani maganin sliming na rage kiba da tumbi wanda maza da mata suna amfani dashi , maganin na ruwa ne a galam take sayar dashi in har kika saye wannan maganin to ina mai tabbatar maki da cikin sati Daya zuwa kwana goma zakiga yadda zaki sauya zaki rage sosai sai dai ba yadda ramar zata maki illa ba don wata ramar sam batayi ba a rayuwa , sannan wanna. K'aton cikin naki cikin kankanin lokaci zaki nemi shi ki rasa cikinki zai shafe kamar ba shiba wanda hakan zai bayyanar da ainahin shap din ki , Matsalar rashin Ni'ima kuma zata hada maki da *zafafan* kayan mata wanda zasu balle duk wata hanyar ni'imarki da ta toshe zaki samu Ni'ima irin wadda akeso mai yauk'in nan daga lokacin da kikafara amfani da kayan to kinyi bye bye da matsalar bushewar gaba, Ina har kun shirya kuna rike da kudi to kuzo mu garzaya wajanta don ba'a sanya da irin wannan matsalolin yanzu sai kaji labari ya canza indai wadan nan mazan ne,, Cike da zumud'i da farinciki farida tace " wai kina nufin duk wadan magungunan zamu samesu a wajanta ?? "Kwarai kuwa fiye dasuma zaku samu don ba kalar kayan gyaran mata da bata sayarwa , bayan ga hakan tana bada Maganin hawan jini Maganin ciyon suger Maganin olsa Maganin kuraje kowane iri ne Maganin ciyon zuciya Sanna tana hada sabulun gyaran jiki wanda zai gyara maki fatarki tayi kyau da kyalli , Ni kaina da sabulunta nake wanka shiyasa zakuga kullum jikina kamar na jariri sabuwar haihuwa saboda laushi da santsi Kayan mata kuwa bamasa lissafuwa in ana maganar kayan mata in aka kai ga maman yusuf to ankai kankat don ba abunda bazaki samuba Tana hadin sabon budurci ga wacce tsautsayi ya fadamata na matsalar fyade ko kuma zawara da zatayi aure takeson ta hade ciki da waje kamar budurwa da sauransu Tana hadin kayan mallakar miji ba boka kuma malam zaki mallaki mijinki a tafin hannunki sai dai mallaka ba irin wadda zata kauce hanya ba a'a mallaka irin wadda zata janyo maki hankalin mijinki aduk inda yake hankalinshi yana kanki sannan zai rinka yi maki zazzafar soyayya ta yadda zaki samu kwanciyar hankali a zamantakewar ki ..........kai in nace zan lissafa maku abunda maman yusuf ke yi to sai mu kwana anan bangama ba amma muje ku ganewa idanunku, Dukkansu ajiyar zuciya suka sauke cike da gamsuwa da bayanin shareefa , Billy tace amma a yadda kk fadi kila kayan zasuyi tsada ko? "A'a Billy kayan maman yusuf sam basuda tsada komai zaki samu cikin sauki da rahusa kudai ku zo muje To bari naje na debo kudi don har wanna. Hadin mallakan bazan bari ya wuceni ba gsky ina da bukatar shi, "Gaskiya ne Billy nima bazan bari ya wuceni ba tunda gashi ana zancan yimuni kishiya cewar aisha Dariya shareefa tayi tace to yanzu dai kuzo muje yadda zamu dawo da wuri , Zainab tace wai ita maman yusuf din a ina take ne , *"Tana nan cikin garin Sokoto unguwar makerar Assada area* sannan tana aika kayanta a ko ina a fadin Nigeria da Niger cikin aminci da yardar Allah, To nidai bani number ta zamu dinga gaisawa ina neman shawara sannan duk abunda nakeso zan dinga zuwa da kaina basai na jiraki ba , To shikenan bari nabaki koba komai in kikayi serving number ta Zaki dinga ganin zafafan kaya a status dinta , 09035027743 ga numbar ta Nan ga Mai bukata zai iya tuntubarta ta hanyar kiran waya kokuma WhatsApp, Fitowar Billy ne yasa duk suka mike suka dauki jakukunansu da gyalensu suka fito direc motar shareefa suka hau suka doshi gidan maman yusuf mai zafafan kaya mata na mutunciπŸ₯° *Wannan sakone daga Hajiya Maryam wadda kukafi sani da maman yusuf mai kayan mata* Duk abunda kukaji mun ambata harma da wanda ban ambataba to muna siyar dashi cikin sauki da rahusa kuma muna aikawa kowane gari a cikin fadin Nigeria. Ina maraba daku🀝🏼🀝🏼🀝🏼🀝🏼🀝🏼 *Pls yan uwana musulmi ku taimaka ku tayani yada wannan post din alfarmar annabi Muhammad SAW* NgdπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 09035027743 [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_22 ..................gaba daya iyayen yaron a rikice suke , musamman ma mahaifiyar yaron wadda ita ce ta aikeshi ya siyo masu mai zasuci abinci' ashe ajakinsa ke kiransa , Babansa kuwa kallo Daya zaka masa kasan cewa yana cikin wani hali, don yama kasa magana , da kyar ya bude bakinshi ya dubi babban d'anshi kamal yace " kamal ku kamashi muje gida haka Allah ya nufa muje amasa sutura akaishi gidanshi na gaskiya amma ba inda za'a kaimun gawar d'a don ko anje ga hukuma ba abunda zasuyi akai ,Allah zai mana sakayya," da yake mutane da yawa sun bada shawarar aje police station akain report , Kamal baice komai ba ya duk'a ya dauki gawar yaron yayi hanyar gida yayinda sauran mutanen suka mara mashi baya , sai dai idan ranshi yayi dubu to ya 'baci tabbas lokaci yayi da zasu nemawa kansu mafita saboda wannan shine karo na ukku kenan da shaid'anin yaron nan ke take masu yara a unguwar Yana kashesu har lahira kuma ansan shine amma ankasa yin komai akai to tabbas a wannan karon sai sun dauki fansa sai sun hadu sun kasheshi in yaso suma a kashesu amma bazasu barshi ba, wannan shine tunanin da kamal keyi bashi kad'ai ba harda sauran yaran unguwar wanda yayi mugun 'bata masu rai sunci alwashi iri iri akansa , _______________________ Aguje suka shigo gidan wanda saura kad'an suyi awon gaba da Baba mai gadi saida yayi wani irin tsalle ya kauce masu dama ya saba da irin wannan halin na Zayyan shiyasa duk lokacin da ya bude mashi get yake yin saurin yin ta kanshi don yasan tsaf zaibi ta kanshi ya wuce ba abunda za'ayi , shiyasa kullum cikin zullumi yake yana tsoron ranar da tsautsayi zai afka mashi , Bayan yayi parking ne suka fito Zayyan ya dubesu yace "to friends kuje part Dina ku jirani zanje wajan Dad na samo mana kudin nan don banason aikin nan ya wuce satin nan komai shaf shaf za'ayi inason yafi kowanne gidan rawa da yake cikin garin nan ," Dariya suka sa da sowa suna cewa sai babban yaro kace zamu k'ara fasowa don wallahi babu kalar iskancin da bazamuyi ba aciki don lokacin mu ne doli muyi yadda mukeso ,cewar daya daga cikinsu , aikuwa nan suka sake sa ihu , d'ayan yace " to amma baba kaga ganin dakus d'inka zai bamu kud'in nan kuwa kamar yadda kace , ? " Kallon k'asan ido Zayyan yayi mashi yana cewa " kana shakku ne ? to kasani ba abunda Dad bazai iya bani ba amma ina zuwa gaka gasgata hakan, " Daga haka ya juya yafara wata irin tafiya ta cikakkun yan iska wanda kansu ya waye da iskanci ,sanye yake da wata damammiyar riga bak'a sai farin wando wanda ya tsaya mashi iya gwuiwa ya wani zazzago wandon har ana ganin wandonshi na ciki , kanshi kuwa anyi mashi kitso akai kamar wani mace kasancewar Allah yayi shi da yalwan gashi sosai ,wuyanshi wata sark'a ce ta gold sai waalwalniya takeyi , kallo Daya zaka mashi ka dauka sam bai hada hanya da Musulunci ba don sam ba alamar hakan , cikin tafiyarshi ta cikakkun gayu ya k'arasa babban falon , Da fito ya shiga falon mom ce da Amna zaune a falon ko kallon inda suke baiyi ba yanufi hanyar part din Dad, Cikin takaici Mom ta dubeshi tace "kai Zayyan zo nan " Cak ya tsaya daga inda yake sannan ya juyo ya kalleta fuska a daure don kar ma ta kawo mashi wasa don yasan halinta kullum cikin sa mashi ido take akan harkokinshi yakula tana fifita Amna akanshi , cikin daurewar fuska yace "Ya dai" yayi maganar Yana yamutsa fuska, Dak'uwa tayi mashi tana cewa "ubanka kai da yadai d'in wato Zayyan har kullum bazakayi hankali ba ko kai kenan kullum bakasan kayi sallama ba a waje sannan kashigo ka ganni amma bankai matsayin da zaka gaida Ni ba ina matsayin uwarka, bayan tunjiya da safe a rabona da kai bansan gidan uban wa kake zuwa ba har ka kwana to wallahi kashiga hankalinka , kabi duniya a sannu tun kamun lokaci ya k'ure maka , sannan a yau basai gobe ba ka tabbatar da ka kunce wannan shegen kitson da kayi wa kanka kamar wani mace a..............cikin hasala ya katseta da cewa ohhhh Mom Wai miyasa kikeson takurama rayuwata ne gaskiya Ni banason sa ido Yakamata ki barni nayi rayuwata yadda nakeso tunda ba akanki nake zaune ba , daga haka ya juya yayi shigwarshi part din Dad, "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un Allah gani gareka wannan wace irin masifa ce ,tabbas ance kwad'ayi mabud'in wahala , da banbi son zuciyata ba wata kila da bangamu da wannan tashin hankali ba, Zama tayi da'bas a wajan gaba daya ta rasa tunanin da zatayi,lamarin Zayyan yafara bata tsoro kullum abun nashi gaba yakeyi sannan bai tsoron uban kowa sai Ubanshi shikuma so ya makantar dashi sam baya ganin laifin d'an nashi ma bare yace zai tsawatar mashi dafe kanta tayi cike da damuwa, Amna kuwa banda latsar waya ba abunda takeyi duk da tajinsu sarai amma ko kallo basu isheta ba , itama sanye take da mini siket ja sai yar wata bingilar riga mai hannun bes rabin nonuwanta duk a waje amma bata damu ba sai dogon gashin kanta da yake kwance har gadon bayanta, Kallonta Mom tayi cike da takaicin halinta na shariya cikin daka tsawa tace " ke wai don ubanki ba nace kije ki cire wadan nan banzan kayan da kika saba kamar wata arniya , Itama cikin jin haushi ta mike tana buga kafarta tace " kai Mom kin cika masifa wallahi daga haka ta juya da sauri tayi hanyar party dinta cike, da jin haushin momin Tata, Mom kam in da sabo ta saba da rashin girmamawar da yaran ke mata , har fiye da haka ba tasha zaunar dasu tana yi masu nasiha akan rayuwa amma kullum kamar Kara zugasu takeyi ,ajiyar zuciya tayi tace "addu'a ita kadai ce mafita, "Dad kudi nakeso kabani" "Mizakayi da kudi son?" "Dad gidan rawa zan bude nawa na kaina don a yadda nake babban yaro Yakamata ace inda nawa gidan rawa na kaina ," Dan jimmm Dad yayi sannan ya nisa yace , " Bawai zan hanaka bane ko banason baka kudin a'a , ina tunanin kana ganin babu matsala yin hakan bayan kasan inada burin zama gwamna anan gaba , kasan halin mutane yakamata ka dinga sanin abinda zakayi saboda idon mak'iya don kasan idan har nasamu kujerar Gwamna to kai kanka ka haye wanda ina fatan daga gwamnan na koma d'ane kujerar shugaban kasa, kaga shikenan k'asa tazama tamu sai yadda mukayi da ita wannan shine babban burina a rayuwa kuma nafara ganin nasara tunda nafara tsallake mataki na farko wanda zai sharemun hanyar da zanbi wajan ganin na cika burina," Wata irin dariya Zayyan yayi yace "kai Dad har k'asa na hango kaina a villa wallahi , amma dai Dad Ina bukatar kudin nan gaskiya don nayiwa friends Dina alk'awarin Zan gina mana gidan rawa , kuma bazan fasa ba don ba girma na bane magana biyu ,kawai kabamu zansan yadda akayi sunana bai bayyana ba zamuyi komai a sirrance, " "Ka tabbata?" "Yes Dad" "Okay nawa ne kudin?" "5million ne Dad" "To shikenan anjima zakaji alert kasan don kai kawai nake neman kudin don haka ba abunda zaka nema ka rasa my son," Wani tsallen dadi Zayyan ya buga tareda rungume mahaifin nashi yana cewa ina sonka Dad don kai kadai kake sona bari naje wajan friends Dina mufara tsara yadda zamuyi aiki," Cikin murmushi da jin dadin ganin yadda dan nashi ke farinci yace "ok son " Aguje ya fito daga part din yana ihun murna inda yabar Mom anan ya sameta ko kallonta baiyi ba yayi ficewarshi . _________________________ Unguwar gwangulori, Malam jibirin haifaffen garin Lagos ne duk da Asalin iyayensa yan Birnin Kebbi ne ,cin rani ne ya kawo mahaifinshi garin na Lagos har daga baya ya gidandance inda ya aure matarshi Inna Suwaiba , wadda ta kasance yar uwarshi ce , malam jibirin shi kada ne dansu a duniya har lokacin da Allah yayi masu rasuwa, Malam jibirin talaka ne sosai wanda kullum sai yafita ya nemo sannan za'aci a gidansa ,da matarsa daya Inna Hauwau , yaransu hudu Sulaiman shine babba sai Mariya dake binshi sai Hadiza da shema'u auta, Yara ne da suka samu tarbiya sosai daga wajan iyayensu , dukkansu masu nutsuwa ne kuma sun iyama talaucinsu , Duk da talaucin da suke ciki malam jibirin yayi iyakar k'ok'arinshi na ganin ya'yan shi sun samu ilimin zamani dana boko , Alhamdulillah yanzu haka sulaiman ya haΙ—a degree dinshi tun shekarar data gabata sai dai halin da ake ciki na Nigeriyanci yasa har yanzu bai samu aiki ba sai dai bai zauna haka ba don dama yana dan taba Ι—inkin tela to Alhamdulillah yanzu ya kware sosai kuma yana samu dai dai gwargwado da wannan sana'ar yake samu yana tallafawa iyayenshi dakuma karatun k'anenshi, Mariya ma tagama secondry inda sukayi had'a k'arfi da k'arfe suka sama mata admission a makatar koyon aikin jinya , wanda shine babban burninta a rayuwa taga ta zama ma'aikaciyar jinya, haka ta dage sosai tana karatun ta cikin kwanciyar hankali don burinta baiwuce tafara aiki ba don ta tallafawa iyayenta itama don nauyi yayiwa yayanta yawa shikadai ko shima zai samu saukin wani abun, "Assalamu alaikum Inna sannu da gida " "Yawwa mariya andawo kenan " "Eh Inna na dawo yau kam munjima sosai gashi na kwaso rana da yunwa sosai wallahi , Allah yasa dai akwai abinci a gidan," tayi maganar lokacin da take zama akan tabarmar da Inna ke zaune ,ajiye jakar litaffanta tayi a gefe tare da fadin wash Allah wallahi yau najigata sosai, Inna ta tabe baki tace to ai ke kikaji zaki iya ba yadda banyi dake ba akan ki yarda a tsaida Ranar aurenki da wannan yaron Nura yaro mai mutunci da nutsuwa kika k'i kikace ke karatu zakiyi ai sai ki daure don ba abunda yake samuwa abanza batare da ansha wahala ba bare ilimi ," Kai inna kullum sai kinyi maganar Nura a gidan nan nifa ban ce bana sonshi ba amma dai ina zai iya jirana to don inasha Allah sai nacika burina, " "To Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" cewar Inna don itakam sam bata wani son karatun tafinson ta fitar da miji tayi aure, "Sannu da dawowa Anty , " Yawwa khadija , dauko mun abincina naci don Allah yunwa nakeji sosai " "To anty , Bayan tagama cin abincin ne ta d'ibi ruwa a rijiya taje tayi wanka don samun saukin zafin da takeji,bayan ta fito ne ta tarar Babanta ya dawo nan ta zauna sukaci gaba da fira gaba daya, ___________________________ Zaune suke a babban falon mahaifinsu , gaba dayansu a tsure suke suna jiran abunda mahaifin masu zai yanke a kansu , mussaman ma *Lauratu* duk da sanyin AC da fankokin dake katon falon hakan bai hanata zufa ba kamar an watsa mata ruwa tsabar rud'anin da take ciki don tasan Mahaifin nasu bashida wasa ko kadan sannan yana da tsauri akan ra'ayinsa tana gudun abunda ,zaije yazo karfa garin sanya tayi saken da za'ayimata sakkiyar da babu ruwa , Ummi kam sai kallonsu takeyi yadda suke tsuma kamar wadan da aka gurfanar a gaban alk'ali , sosai suka bata dariya amma ta danne don kar su kawo masu wargi, Gyaran murya Abban yayi ya dubi yayan nashi bayan ya ajiye jaridar dake hannunshi ya ce " ya mukayi daku ??? Saida gabansu ya fad'i musamman ma Lauratu don Zainab kam da dan sauki sauki don itakam tasamu mafita , cikin inda inda Zainab tafara magana, "am dama dama yaya Nasir yace zai turo magabatansa wajanka tayi maganar cikin rawar harshe dakuna kunya, Daga Abba har ummi murmushin farin ciki sukayi kamun su mayar da dubansu ga Lauratu cikin daurewar fuska Abba yace "kefa?" Cikin daburcewa tafara magana kamar zatayi kuka tace "don Allah Abba kayi hakuri kadan k'aramun lokaci wallahi har yanzu bansamu wanda yayi dai dai da rayuwata bane amma.........cikin daka tsawa yace " rufemun baki shashasha mai kunnen k'ashi , wato ke duk maganar da za'a maki ta bayan kunnenki take bi ko ? Tun yaushe nake baki lokaci amma har yanzu kin kasa zuwa da magana daya k'wak'k'wara ,to bari kiji in gayamaki wallahi nagaji da zama daku a haka ba aure daga nan zuwa wata daya in baki kawo Wanda kk so ba zan zaba maki duk wanda yayimun da kaina kin kuma Sanni bana magana biyu don haka ya rage naki ko kiyi amfani da damar ki ko kuma kibari ta su'buce maki ,ku tashi kubani waje , har rigegen tashi sukeyi sum sum sukabar falon , Alhaji Abubakar mainasara kenan da iyalanshi , matar daya Hajiya Sa'adatu wadda suke kira da Ummi sai yaransu biyu Lauratu da Zainab wadan da sukadai suka suka haifa , Lauratu babbar likita ce a babban asibitin acikin garin na Lagos tanada shakara 28 a duniya sai k'anwarta Zainab mai shakara 27 aduniya kasancewar shekara daya ne a tsakaninsu itama tagama karatu ta ma'aikaciyar banki ce Asalin Alhaji Abubakar mainasara bafulatanin Sokoto ne aiki ne ya kaishi Lagos amma duk yan uwanshi suna Sokoto ,hakama Hajiya Sa'adatu , Lauratu da Zainab kyawawane sosai irin na asalin fulanin Sokoto Lauratu doguwar mace ce sosai tanada dan jiki amma ba sosai ba Allah ya zuba mata kyau najiki dana fuska , don duk abunda namiji keso a jikin mace to Lauratu ta hadashi , komai nata cif cif yake gwanin sha'awa , tana samun masu sonta sosai amma ita sam auren baya gabanta aikinta kawai tasa a gaba , hakama k'anwarta Zainab wannan yasa Abban ya bude masu wuta sosai akan su fitar da mazajen aure , shine Zainab ta gabatar da Nasir wanda ya kasance dan yayar Ummu ne dama yajima yana son zee sosai amma taki bashi dama sai a wannan karon da taga Abba na neman ya aurar dasu ga koma waye takuma san halinshi idan har ya fada tofa bazai taba canzawa ba, Hawaye ne suka zubo a fuskar Lauratu cikin matukar damuwa ta Ι—ora hannunta akai tareda fadin na shiga ukku tayaya zan kawo miji a cikin wata daya kacal............................naso yafi saidai wlh hannu ya rikeπŸ˜‚πŸ˜‚ Ilove You wujiga wujiga masoyan mmn yusup inayinku over 😍😍😍😍😍😍inajin dadin comment dinku sosai Allah yabar kaunaπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ *Zanyi aike zafafan kayan mata Kano da Katsina maiso tamun magana* 09035027743 [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *Mallakar* *Maryam Umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar* *Minene Asalina* *Mutum ce kuwa* *Husna ko Huzna* *And now*πŸ‘‡πŸ» *Jami'in d'an sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_23 ........................."idan fa bakiyi da gaske ba wallahi Abba zai baki mamaki anty ,kinga dai yayi ta baki lokaci amma har yanzu kin kasa kawo mutum daya acikin samarinki , kuma kinada su bare kice babu wanda yake sonki , " Yamutsa fuska tayi cikin matukar damuwa tace , " bazaki gane bane zee nifa wallahi gaba daya banida tsarin aure a yanzu sannan wadan nan samarin nawa Ni ba wanda nakeso acikinsu gaba daya basumun ba narasa yadda zanyi gashi ga dukkan alamu a wannan karon Abba bazai dagamun k'afa ba" tayi maganar kamar zata fashe da kuka, Dariya zee tayi tace "kina bani mamaki anty idan har kikace babu tsarin aure a rayuwarki , shin abunda nakeson na sani shine auren ne bakiso gaba daya ko kuwa akwai lokacin da kike ganin Yakamata kiyi auren , ? Yakamata dai kisani ita rayuwar mace Ζ™alilan ce kinada shekara 29 bakiyi aure ba sai yaushe zakiyi ? Yakamata dai kiyiwa kanki fada dai don ita mace babu lokacin da ya dace tayi aure kamar lokacin da ake yayinta ake sonta rashin yin haka kuwa yanasa akai lokacin da zata rasa manemi duk kyauta da matsayinta kuwa sannan................"ke ya isa don Allah karki cikamun kunne da iyayinki na banza ki barni da abinda ya dameni, dariya zee tayi tace "bawani anty kawai dai bakison gaskiya ne amma dai kiyi tunani don wallahi Abba a shirye yake daya aura maki Koma wanene ,cikin damuwa tace " wannan shine abinda yake tsoratani yazama doli na fitar da daya daga cikin manema na tun kamun Abba ya fitarmun da kanshi ," Cikin zumud'i da jin dadi zee tace "yawwa anty don Allah ki fitar da Abdul wallahi duk yafi wad'an da suke zuwa wajanki sannan zakuyi matukar dacewa da juna wallahi ," "Nikuma bai mun ba zee don haka bazan za'beshi din ba mutum.sai shegen girman kan tsiya da jin shi wanine mrtsss ,daga haka ta tashi ta shige toilet ________________________ Tun bayan abunda yafaru gaba daya halayen Hisham suka canza , mutum mai fara'a wasa da dariya yanzu yakoma kamar wani dodo tsabar daurewar fuska yanzu ko Momma Bata cika ganin dariyarshi ba ,gaba daya ya mayar da kanshi busy aike yake yi da dukkan karfinshi ba dare ba rana ,baya ragawa duk wani azzalumi duk wanda yakama da wani laifi to fa sai ya tabbatar da an hukuntashi koshi waye , saboda jajircewarshi da aiki da gaskiya yasa yayita samun k'arin girma daga wannan sai wannan har inda yanzu Allah yasa aka mashi *mataimakin commissioner* na wannan yanki , yaji dadin wannan muΖ™amin sosai don yanzu yak'ara samun damar da zaiyi yak'i da azzalumai lokaci yayi da Yakamata su samu canji acikin wannan garin na Lagos , Alhamdulillah komai na tafiya yadda yakeso kuma cikin ikon Allah cikin kankanin lokaci ansamu canji mai yawan gaske a jahar sai sambarka , wannan jajircewar tashi ba k'aramun farinjini ya janyo mashi ba ga talakawan garin don yanzu duk wanda aka zalunta matukar ya kawo kukanshi a hukumar to kuwa Hisham zai tsaya tsayin daka wajan ganin ya kwatar mashi yancinshi, wanna yasa ya samu daukaka sosai fiye da tunani, dayawa zakaga unguwanni sun lika fotunanshi saboda tsabar yadda suke sonshi da kaunarahi, Momma najin dadin yadda dan nata ke gudanar da aikinshi dakuma irin daukakar da yake samu amma acan k'asan zuciyarta kullum cikin tsoro da zullumi take don tasan doli ne d'an nata yayi mak'iya da yawa wad'an da basason gaskiya da ci gaban kasarsu , saidai tana mashi addu'a sosai tasan ba wanda ya isa yayi mashi wani abu sai da izinin Allah, Abu daya ke damunta dashi shine rashin yin auren shi , tayi magana da fushi har tagaji amma har yanzu kullum maganar sa daya ce bai tashi yin aure ba sai lokacin da ya dibama kanshi, tasha hadashi da yayan k'awayenta amma yana guje masu duk wadda aka kawo mashi sai yace bata mashi ba , tarasa yadda zatayi dashi , Yauma kamar kullum yana zaune a dinning Yana karyawa ta fito daga dakin ta zama tayi kusa dashi tace "shalele da karfe nawa zaka dawo yau ? "Cikin muryarshi mai cike da jarumta ya amsa da cewa " sai dare zan dawo Momma yau inada ayukka sosai a office, " "To koma dai minene inason ka dawo da karfe hudu akwai inda zaka rakani kuma saura kak'i zuwa kaga abunda zan maka, Dafe kanshi yayi cike da damuwa yace ohhhh Momma rakiya fa nikuwa ina zan rakaki sai kace wani mace , nasan dai bazai wuce gidajen k'awayenki ba kiyi hkr zan turo direba ya kaiki kinji," "Karma ka fara kai nakeson ka kaini kuma doli ne kazo kaji na gaya maka, " Kamar zaiyi kuka ya amsa mata da "to" don yasan tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i kila takoma nema mashi wata yarinyar ne shiyasa takeso tajashi suje ,shi kam yaga ta kansa kullum Momma cikin talansa take sai kace yarasa masoya gashi sai ja mashi raini takeyi wajan yara Ζ™anana , 'bata fuska yayi cikin shagwabar da shi kanshi baisan yayita ba yace "amma Momma saboda Allah haka zakiyi ta talla ta sai kace narasa mai sona kuma ............."kai rufamun baki kullum maganarka daya ce baka rasa masoya ba nikuma banga alamar hakan ba don haka bazan gaji da nema maka ba kuma wannan karon in har kawatsamun k'asa a ido nikadai nasan abunda zanmaka kaji na gaya maka tunda har yanzu kai bakasan cewa ka girma ba a matsayinka ai bai kamata ace bakada mata ba don aure shine cikar mutuncin kowane mutum , baice komai ba haka ya ajiye abincin da yakeci ya tashi yabar gidan, Momma kuwa bata damuba don tasha alwashin komai zaiyi a wannan karon bazata daga mashi k'afa ba bakomai ne yasa takeson yayi aure ba saidon wannan bakin halin da ya daukama kanshi mutum kullum fuska a hade kamar hadari ba wanda yake ganin damanshi ita kuma tafison ya dawo ainahin Hisham dinshi mai sakin fuska da dariya da tsokana sam ta tsani wannan sabon halin nashi wanda take ganin idan har yayi aure matar zata taimaka mashi wajan canza shi ya dawo kamar da, _________________________ Gaba dayansu a buge suke yau sunsha sunyi tatil sai raye raye sukeyi mata da maza kuma abun takaici abun tausayi dukkansu yara ne sosai da bazasu wuce 22 to 25yrs ba abin karin bak'inciki da takaici mafi yawansu 'ya'yan mu na hausa Fulani ne ,mafi yawansu ya'yan manya ne masu kudi da masu mulki , iskanci suke kala kala acikin gidan rawa wanda ya kasance mallakin Zayyan ne, Shikuma shaid'anin yana gefe akan wata kyakkyawar kujera irin ta sarakai ya hakimce , mata biyu ne a gefenshi sai faman shafashi sukeyi suna sumbutarshi tako ina ba kunya ba tsoron Allah yayinda yan korenshi ke gefenshi suna k'ara zugashi da yi mashi kirari irin wanda yakeso , Sun shagala sosai ba zato ba tsammani yan matan nan sukaga Zayyan ya hankadesu da k'arfi har saida suka fad'i , daga yan matan har abokanshi da sukaga abunda ya faru ido suka zuba mashi da mamakin ko lafiya, Yamutsa fuska yayi cike da shak'iyanci yace "abokai nifa yau ranar ta mussaman ce agareni ina bukatar abunda zai sanyani nishadi sosai , wani daga cikinsu yace " wane irin nishadi kake nema da ya wuce wanan ne babban yaro , ai babu wani nishadi da yafi wadan nan kayan da ka ture kawai kabada kai ka kwashi rabonka Baba, Tsaki Zayyan yayi yace " kai nifa yau wallahi babbar harka nakeso kota wane hali ,wad'an nan duk tsaffin hannu ne yau sabuwa dal aleda nakeso gaskiya......wani irin ihu suka sanya suna dariyar shak'iyanci da yi mashi kirarin da suka saba idan ya tafka wata ta'asar , Yan matan kuwa wani irin haushine ya kamasu musamman ma surayya wadda ake kira da sury yar minister ce Allah ya jarabeta da mugun son Zayyan Wanda ba komai ke rudarta akan shi ba irin tsananin kyaun da yake dashi , kuma a sanadin soyayyarshi ne ta samu kanta a wannan halin shine mutum na farko daya fara saninta 'ya mace kuma bayanshi bata kula kowa amma ta kula tuni ya jefata kwandon shara tunda yasamu abunda yakeso yakewulakanta ta ,cikin jin haushi kamar zatayi kuka tace "haba dear abunda kakemun ka kyauta kenan miyasa kake wulakanta Ni ne bayan kasan irin son da nake maka, abunda kakemun yayi yawa dear yakamata karinka tausayamun , Ina tsananin sonka da kishin ka amma nakula kai sam bakama san inayi ba , kasan bakincikin da nakeji aduk lokacin Dana ganka da wata mace , wannan kaskar ma don narasa yadda zanyi da ita ne na barta tana ra'barka amma daga yau zan fara daukar mataki akan duk shegiyar da na koma ganinka tare da ita wallahi "tayi maganar a haukace tana nuna d'ayar budurwar dake kwance har yanzu tun da Zayyan ya tureta , ita kam sama sama ma take jinsu don gaba daya Zayyan ya daga mata hankali wanda batajin zata iya hakura dashi , tashi tayi tana layi takoma nufo inda yake , cikin fitar hayyaci kamar wata zakanya ta far mashi da salon wasanninta ,tsabar rashin kunya sam bata damu da mutanen dake wajan ba sai kokari take tasamu abunda takeso gaba daya tsabar jaraba yasa takasa control din kanta , ba zato ba tsammani sai gani akayi sury ta nufota da kwalba gadan gadan kamun suyi wani yunkuri tuni ta kwada mata kwalbar akai , wata gigitacciyar k'ara yarinyar tafasa ,take kanta yafara fitar da jini sosai , banda ihu ba abunda takeyi , Duk mutanen wajan tsai akayi ana kallonsu amma ankasa samun wanda zasu taimaki yarinyar ,shi wanda akayi domin shi ma dariya abun yabashi haka yarinka sakin murmushin shi mai kyau wanda ba k'aramin k'ara fito da ainahin kyaushi yake ba, cikin rashin damuwa sury ta dauki jakanta tayi tafiyarta, Wata yarinya ce ta k'araso a guje tana tambayar yarinyar da aka fasama kai tana cewa " ke taly mi yake faruwa ne waya maki wannan aiki , arikice take magana da yake batasan abunda yafaru ba fitowar ta kenan daga d'aya daga cikin d'akunan dake wajan ita da saurayinta ta hango k'awar tata a wannan halin kuma kowa ya zuba mata ido anrasa wanda zai taimaka mata, Kamata tayi tayi hanyar waje da ita , sanyata tayi a mota taja aguje tabar gidan rawar ta nufi asibiti da ita don ganin yadda tafara layi alamar jinin yafara bugeta, Zayyan da abokanshi kuwa ko a jikinsu saima dariya da sukeyi ,tashi Zayyan yayi ya dube su yace kunga kuzo muje yau zamu fita farauta don wallahi sai na samo sabuwa dal a leda , ihu sukayi tareda fadin "yau zamu ga mai tsautsayin da zata shigo hanyarmu,hhhhhhhhh, Fita sukayi suka shiga Ζ™atuwar motarsu suka fice daga gidan , *************************** Da kyar ya ajiye ayukkan dake gabanshi ya baro office din ya nufi gida, tafe yake a motarshi sai faman gungini yakeyi gaba daya Momma ta takura mashi akan sai yayi aure shikuma sam baida ra'ayin aure a yanzu shi matan ne ma bala'in haushi suke bashi wallahi , Da sallama ya shiga falon ,Momma na zaune cikin shirinta tsaf shi kadai take jira ,ta amsa sallamarshi , gaisheta yayi ta amsa zai zauna kenan tace "a'a karka zauna maza kaje kayi wanka ka ciremun wadan nan bak'ak'en kayan ka nemi manyan kaya kasa kazo mu tafi kuma karka kuskura ka batamun lokaci , Baice komai sai yamutsa fuska da yayi ya tashi ya nufi dakinshi, Wanka yayi ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda ruwan k'asa ya daura hularshi kalar aikin shaddar sai tsadadden takalminshi suma dai kalar aikin shaddar ne yayi kyau sosai daukar agogonshi da farin glass dinshi yayi ya fito daga dakin , Hannu ya mik'awa Momma ta Sanya mashi agogo sannan ta tashi suka fita , sai faman washe baki takeyi tanajin dadi , azuciyarta kuwa sai addu'a take akan Allah yasa yarinyar tayi mashi don tasan hali ba yau yasaba bata kunya ba, ************************* Tafe suke kamar kullum akan titin sai faman shek'a gudu sukeyi kamar zasu tashi sama yayinda music da iface ifacensu ya cika motar , a haka har suka zo wata unguwar talakawa nan suka rage yawan gudun da sukeyi a hankali suka fara bin kowane lungu da sako na cikin unguwar , cikin ikon Allah kuwa Allah ya hadasu da wasu yan mata biyu 'yan makarantar secondry sun taso daga school suna tafiya a hankali suna dan ta'ba fira, Tundaga nesa suke k'are masu kallo , tuni Zayyan ya k'uresu da ido yana nazarin wadda zai za'ba aciki, Cak ya tsaida idonshi ga d'ayar wadda ta kasance fara tass kuma doguwar mace ga kallo Daya zaka Mata kasan cewa ta tara abubuwan da duk namiji zai so a wajan mace , cikin wani shu'umin murmushi ya nuna masu ita , A take suka kunna motar suka bi bayansu don har sun Dan gotasu k'ad'an, suna zuwa dai dai inda 'yan matan suke suka tsayar da motar , cikin matukar zafin nama da kwarewa suka cafko yarinyar suka turata mota suka shiga Zayyan yaja motar aguje inda sukabar dayar yarinyar na zunduma ihu da kiran a taimaka mata 'barayi ne , kasancewar wajan ba mutane sosai da kyar mutane suka fara taruwa akanta wanda zuwa lokacin ko k'urar motar su Zayyan babu a wajan,.................... πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« *SHAHARARRA KUMA K'ASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA _MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TA SAKE ZO MAKU DA KAYATATTUN KAYAN MATA ZAFAFA MASU KYAU DA INGANCI SAYEN DAYA KO SARI INA SOKOTO INA AIKAWA KOWANE GARI A NIGERIA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH KUDAI KU MATSO KAR AYI BABU KU KAYANMU NA MUSAMMAN NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» 09035027743 *KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA MUKE DASU* maganin sanyi Maganin KIBA Maganin rage tunbi da kiba Maganin sanyi na maza Maganin gashi - Yana Sanya tsawon gashi Hana karyewar gashi bakin gashi yana maganin sali kurajen Kai da sauran matsalolin Kai *Akwai zafafan kayan Mata Kamar jaka* Gumar Madara Gumbar gero Gumbar Jan icce Gumbar Sha ki matse Gumbar sa buzu kuwa Gumbar tada zaune tsaye Gumbar ridi Gumbar shinkafa Gumbar Aya Gumbar ukku bala'i Sarauniyar gumba Da dai sauran kalolin gumbunan da muke dasu *Kalolin gari* Dakan jaraba Kinfi budurwa Jita salaf Garin mallaka Dakan Ni'ima Bita zai-zai Sabon budurci Mai kwamson gyada Dakan tabaje Dakan kishiya in bakiyi bani waje Dakan Amare Emergency Dakan sa buzu kuwa Dakan sha yanzu magani yanzu Da sauran kalolin da ban fada ba 09035027743 mmn yusuf skt *Munada kalolin matsi da basuda illah Kuma masu matukar aiki da Kara lafiya ga HQ* Matsin mallaka Matsin a Daren farko Matsin sabon budurci Danba gigita Matsin kishiya in bakiyi bani waje Matsin Dan la'asar Gam-gam Matsin kinfi budurwa Matsin rantse bakida kishiya Matsin Dan mannau Matsin k'yallen al'ajabu babban sirri kenan Da sauransu *AKWAI* original Dan goshi ba bugi ba tare da Mahadi shi Original man ayu Original man damo da kitsensa dan goshi sabon salo wanda ake amfani dashi ga mara *Muna dahuwa Kamar haka* Dahuwar kaza Kazar yar gata Kazar Amarya Kazar maijego Ciccibi Yan shila Nama dambun nama Wanda yake jimawa ajiki Kifi Da dai sauransu *Daga gefe Kuma akwai* 1,Maganin kiba maisa cikowa da laushin fata, 2,maganin gyaran nono 3in1 3 na hips mai ingaci dake aiki a cikin sati daya Kalolin sabulun wanka masu gyara fata da Sanya hasken fata mai kyau Sabulun tsarki Yana maganin duk wata matsala ta HQ Yana matsi ciki da waje Yana saukar da Ni'ima Turaren jiki Turaren daki Turaren tsugunno Tsarkin jaraba Dan la'asar na Sha Kayan gyaran jiki na Amare irin su dilka halwa sabulun Amare turarrukan Amare masu gyara fata da Sanya k'amshi ajiki Hatsabibin turarene Hatsabibiyar humara Kalolin humara Colecca Sirrin mallaka na tafin kafa hmmm yar uwa jaraba kiga abun mamaki Dama sauran abubuwan Dana manta ban fada ba duk zaku samesu a wajan yar mutan sokoto mmn yusuf skt *A'bangaren girki ma muna bada namu tallafi akwai curry kala kala Masu kamshi da bada launin abinci nai kyau da jan raayi yara da oga ga abinci ki hjy* 09035027743 *A'bangaren tsumi ma ba'a barmu a baya ba akawai* Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin madarar Ni'ima tsumin tabajeπŸ’ƒπŸ» Shayin Amare Tsumin nono rakumi Zumar Mata mai ridi & zumar. Icce xallah tamasu jego Tsumin ruwa lumtsum Tsumin Sabon budurci Tsimin bita xaixai Tsimin makalemata Tsimin sa sambatun oga Da dai sauransu 09035027743 *Muna hada kayan Mai jego abubuwan da zasu dawo Mata da martabanta a wajan maigida kasancewar duk wadda ta haihu to ni'imar jikinta na tafiya sosai hakama HQ dinta zai bude to muna hada kayanda zasu dawo Mata da martabanta zata matse sosai ciki da waje Kamar bata haihu ba da Wanda zasu dawo Mata da martabanta akan kudi kalilan*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Hakama zawara Mai Shirin yin aure muna hada Mata kaya masu taken ubanka sabon budurciπŸ’ƒπŸ» Hakama budare muna hada kayan gyaran Amarya ciki da wajenta zatayi das abunta gwanin sha'awa sauran bayani Kuma ango ne zai yi makiπŸ˜‰ Karku manta da sunan maman yusuf yar mutan sokoto Address _unguwar Makerar Assada area sokoto Phone number _09035027743 do neman Karin bayani πŸ‘πŸ½ *Don Allah don annabi duk wadda Bata shirya siyaba kar tamun magana tabari sai ta shirya tukunna kar mu batawa juna lokaci* πŸ€—πŸ€—πŸ€—πŸ€— [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *MALLAKAR* *Maryam umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ *Mutum ce kuwa* *Minene asalina* *Husna ko Huzna* *and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ *Jami'in Dan sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ24 ...........................wani farin k'yalle suka shak'a mata a hanci , kamun kace mi jikinta ya saki gaba d'aya , cikin second 5 sai gata ta 'bingire da bacci , wata dariyar shak'iyanci suka fashe da ita suna fad'in sai oga , sai oga, shikuwa gogan sai faman hura hanci yakeyi, yayinda yakejin kanshi yayi sama sosai , sai wani lumshe ido yakeyi yana budewa gaba daya gani yake kamar mortar bata sauri , don ba karamun daukar hankalinshi babyn tayi ba sai wani kallonta yakeyi k'asa k'asa ta madubi yana hadiyar yawu, a haka sukaci gaba da sharara matsiyacin gudu a hanya suka nufi wani gidan shak'atawar mahaifin Zayyan , abakin get din gidan suka tsaya Hon yafara da karfi kuma a hasale don ba abunda yatsana kamar jira, Aguje mai gadin ya fito daga bayi don yanajin wannan hon din yasan na marar mutucin yaron nan ne Wanda in har yakara wasu second din to yasan zai keta mashi rashin mutuncin da ya saba , Cikin zafin nama ya bude masu k'aton get din sannan ya matsa da sauri don yasan karamun aikinshi ne yabi ta kanshi ya wuce , Da yake zayyan gaba daya hankalinshi na wajan wannan yarinyar shiyasa daya fito Sam bai kula kan isah mai gadi ba haka suka kamota suka fito da ita , suka nufi cikin gidan yayinda sukabar isah maigadi rik'e da baki 'bangare daya kuma cike da tausayin wannan yarinyar da iyayenta , yayinda gefe daya yakejin matukar bak'incikin yadda yake kallo ake lalatama yara mata rayuwa kuma ba abunda ya isa yayi , cikin tsananin bak'inciki da k'unar zuciya ya juya yakoma bisa bencinshi ya zauna zuciyarshi Sam ba dadi sai tsinema zayyan da abokanshi yake harma da iyayensu da suka daure masu gindi suna abunda sukaga dama agari, Cikin wani k'ayataccen falo suka shiga daga nan suka bi wani Dan korido sai gasu a wani babban falo mai dauke da d'akuna kusan biyar , d'akin dake can k'arshe suka nufa da ita , kuma har lokacin yarinyar bata San Inda kanta yake ba , suna shiga suka watsata saman wani makeken gado mai masifar kyau da tsada suna dariya , wani Abu zayyan ya dauko daga cikin aljihunshi kamar turare kamun ya haura saman gadon kusa da yarinyar , wannan abun ya fesa mata a fuska aikuwa nan take tafara juye juyen kai kamun ta bude manyan idanunta rass ,waige waige tafarayi kamun cikin second ta tuna abunda yafaru da ita , ai firgice ta tashi zaune Tana waige waige ,ganinsu zagaye da ita ne yasa jikinta fara wani irin rawa tsabar kid'ima tama kasa magana sai kanta da take jujjuyawa , yayinda sukuma suka zuba mata mayun idanunsu kamar zasu cinyeta d'anya ,don sai yanzu suke k'are mata kallo , tabbas ba karamar kyakyawa bace gata komai yaji ajikinta tabbas zasu huta sosai haka suketa ayyanawa acikin ransu fuskantar abunda yake faruwa da ita ne yasa ta sakin wani azanannen kuka mai had'e da tsananin firgici da tsoro , kamar zata shid'e tafara Neman sauka daga kan gadon ,Tana fadin ," suwaye Ku? mi namaku ,? mi zakuyimin? don Allah kuyi hakuri Ku rabu dani , Wata irin dariya sukayi irinta cikakkun yan duniya , zayyan ne yafara matsowa inda take , da sauri ta tashi tafara ja baya Tana kuka tareda girgiza mashi kai yayinda ta had'e duka hannayenta biyu waje alamar ban hakuri ,sai faman rokonsu takeyi akan karsu cutar da ita suyi hakuri su barta ta tafi gida, matsota yaci gaba dayi yana aikamata wani shegen murmushi Wanda kana ganinshi Kasan na mugunta ne ,ahaka har suka dangana da durowar d'akin ,matsota yayi sosai Wanda har sunajin numfashin junansu , yayinda ita kuma ta runtse idonta da sauri cikin bugawar zuciya, hannu yasa ya fisge mata hijabin jikinta , da k'arfi ya furta wowww gaskiya yau na tabbata mai sa'a ,irin wannan kaya haka, lokaci daya ya birkice kallonta yake sama da k'asa kamar wani zautacce , kamun ya hadiye yawu muk'ut, da hannu yayiwa abokan nashi alamar su FIta , da yake suma suman tsaye sukayi ganin asalin kyau irin na cikakkiyar mace wadda ta amsa sunata , su Kansu sunshiga wani yanayi sai dai suna fatan in zayyan yagama da ita suma yabasu ko 5mnt ne don sun sanshi shege ne wani lokacin yanzu sai yayi masu bak'inciki ya hanasu d'anawa , Suna fita zayyan ya finciketa ya watsata saman gadon nanfa suka fara dambe sosai yarinyar Ke kuka da ihun Neman d'auki yayinda shikuma yake kokarin kaiwa gareta , gaba daya ya yagamata kayan jikinta ganin zata bashi wahala ne yasa yarinka zabga mata mari cikin fushi yana fadin "kajini da shegiyar yarinya kina ganin zaki iya hanani abunda nayi niya ne ai wallahi tunda kika shigo hannuna to bazan ta'ba kyaleki ba garama ki tsaya a nutse nayi nagama inada abunyi , " tunda yafara marinta taji gaba daya wutan kanta ya dauke har wani duhu take gani ga azaban firgicin da take ciki ,a tak'aice dai haka Zayyan yayiwa wannan yarinyar fyade tanaji kuma tana gani bayan yagama ma yaranshi suka shiga dai bayan dai suka mata fyade aikuwa zuwa lokacin gaba d'aya jikin yarinyar ya saki numfashinta ya tsaya cak , saida suka nutsu ne suna shawarar yadda zasuyi da yarinyar sannan suka gane cewa bata numfashi , Cikin tsoro daya daga cikinsu ya dubi Zayyan yace oga yarinyar nan ta mutu fa 😳 da sauri Zayyan ya dago kanshi yace "ta mutu"? " wallahi oga bata numfashi innalillahi mun shiga ukku yanzu ya zamuyi oga , ?" Tsaki Zayyan yayi yace "kai don Allah karka 'batamun rai saimi in ta mutu miza'ayi mune fa da garin nan ko ka manta ne, ni damuwata d'aya wallahi yanzu shikenan nayi missing wannan hadaddiyar babyn da wannan ni'imar nida nake murna nasamu mai zafi suk sanda naso zanje har gidansu na daukota , kai gaskiya banji dadiba Sam , amma yanzu ku Daukota kusata a mota muje mu yar da ita tun bata fara mana wari ba anan, Tunda yafara magana suka zuba mashi ido , iskancin Zayyan da rashin imaninshi su Kansu yana basu tsoro don sunkula gaba daya bashida digon imani bare tausayi , duk da zukatansu cike suke da tsananin tsoro da fargaba hakan baisa sukayi mashi musu ba hakanan suka dauke yarinyar suka fita da ita suka sanyata a mota sukabar gidan, Duk abunda sukeyi akan idon isah mai gadi tunda yaga yanayin yarinyar ya firgita ganin yadda suka daukota kamar gawa baisan sanda yafashe da wani irin kuka ba mai tafasa zuciya, inama zai iya tabbas da sai sanyawa yaran nan guba sunci sun mutu don tabbas Barin irinsu a doron k'asa bala'i ne , inba hakaba wannan wace irin masifa ce har sai yaushe ne talakan Nigeria zai samu yanci ne har sai yaushe Nigeria zata fara hukunta azzaluma shuwagabanni k'asar , shikenan duk abunda sukayi ko yayansu sukayi sunci bulus wannan wace irin rikitacciyar rayuwa CE , kai talaka shikenan kazama banza Wanda duk ya debo shararshi sai yazuba a Kanka ,yanzu Allah kad'ai yasan halin da iyayen wannan yarinyar zasu shiga sakamakon wannan zalunci da aka masu, cikin sanyin jiki Dana zuciya yakoma ya zauna kuma har lokacin idonshi na zubar da hawayen tausayin yarinyar da iyayenta yayinda zuciyarshi kemashi sak'e-sak'e yanaji kamar ya kashe yaran , ___________________________ Tunda suka fara tafiya baiyi magana ba sai momma ce keta yi mashi bayanin inda zasuje da kuma yadda take ganin mutuncin hajiya Sara ,(k'awarta) shi dai bai tanka ba don zuciyarshi sai zafi take mashi ko kadan bayason wannan tallan nashi da momma keyi amma ya zaiyi , ya kula a wannan karon ta d'auki zafi da yawa , doli sai yayi takatsantsan don yasamu su rabu lafiya, Momma kuwa tana kule da shi amma shareshi don taci alwashin wannan karon ba d'aga k'afa don ita kam *Samra* tayi mata yarinya mai hankali da nutsuwa, Suna cikin tafiya ne danja ta tsayar dasu akan babban Titin da zai sadasu da gidansu Hajiya Sara, da yake akwai mutane da yawa da suka fara tsayawa inda suma sukabi layi suna jiran danjar tabasu dama , Cikin wani matsiyacin gudu Wanda dama dashi suka saba sukazo wucewa akan titin ga music na tashj kamar zai fasa motar saidai Sam basu samu damar hakan ba saka makon danjar data tsayar da mutane Wanda babu ta inda zasubi su wuce don akwai mutane sosai a gabansu , wannan yasa suka faka motar kusa da motar su Hisham , Cikin jin haushi Zayyan ya daki sitiyarin motar yana Jan tsaki cikin masifa yafara danna masu hon da k'arfi kamar ba gobe yana fadin "kai ji wad'an nan banzayen zasu 'baa mana lokaci , Cikin tsoron da ya rufe abokan nashi daya daga cikinsu ya dubeshi yana cewa " don Allah oga ka kashe mana kid'an nan kabarmu da tashin hankalin da muke ciki don na kula kai Sam ba abunda yake damunka , kuma don Allah kayi hakuri kar kayi abunda zaija hankalin mutane kanmu bare jami'an tsaro ka rufamana asiri har musamu inda Zamu yarda yarinyar nan sannan duk abunda zakayi kayi, Wani banzan kallo Zayyan yamashi yana cewa "wallahi ba uban da ya isa yasa na kashe kid'an nan , kuma inka dameni da surutu to wlh zan iya fito da ita anan in yarda ita inga abunda za'ayi mrtsssss matsoratan banza kawai , " Dukkansu shiru sukayi don sunsan tabbas zai iya don bashida tsoro ko kadan , amma tabbas suna tausayamashi don watarana sun San sai ya janyowa kanshi abunda yafi zare tsawo , Tunda suka faka motar Hisham Ke kallonsu a k'ufule ganin irin tuk'in gangancin da sukeyi ga wani banzan kid'a da suka saka kamar zasu tada gari , yana cikin jin haushinsu ne yaji anfara dannan hon kamar hauka , alamar abasu hanya su wuce , to su suwaye da bazasu iya jiraba ,ranshi ya 'baci sosai gashi motar mai bak'in glass ce na waje baya ganin na ciki , afusace ya bud'e gambun motar zai fito cikin Sauri Momma ta rik'o hannunshi......................... *Allah yagani sabida rashin comment dinku ne yasa na ajiye book din nan , duk da nasan akwai masu yimin comment din daga cikinku saidai hakan bashi zaisa Ku kukasayimun ba don haka in kun gyara nima zan kula sosai don ganin namaku typing din iya yawan comment dinku iya.yawan typing*😁😁😁😁 Inasonku masoyana😍😍😍😍 [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *MALLAKAR* *Maryam umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ *Mutum ce kuwa* *Minene asalina* *Husna ko Huzna* *and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ *Jami'in Dan sanda* https://chat.whatsapp.com/JF7cZ03hT4vGKlos65ybu9 *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_26 .......................kallon ido cikin ido Duke yiwa juna , kamun cikin had'e fuska tare da watsa mashi wani irin kallon kai mugu ne taci gaba da cewa , malam ka rabu dashi haka nan komai yai maka ai bai cancanci irin wannan dukan ba ko don bakasan darajar da jini yake da ita ga d'an Adam ba zakazo kana zubar mashi da jininshi a banza , Wani dan adai daita ne cikin fushi yafara magana yana cewa " Ke Dan Allah rufewa mutane baki daga zuwanki bakisan abunda yake faruwaba zaki hau masifa to wannan da kike tarewa yanzu yanzu nan yakusa kashe wata tsohuwa wajan shegen tuk'insu na ganganci yanzu haka ma sai Allah idan zata rayu kuma a haka baidamu ba saima k'ok'arin guduwa da yakeyi ni wallahi wannan bawan Allah yamun dai dai gara yaci uban d'an iska tunda baisan darajar mutane ba, Jin wannan bayanin yasa jikin laurat yin sanyi saikuma duk kunya ta kamata a hankali ta saci kallon Hisham Wanda har lokacin akwai fushi mai tsanani tattare dashi wannan yasa yakasa yin wata magana saidai yaji haushinta sosai don shi ya tsani rainin wayo ,ganin hakan yasa laurat kamo hannun zee da nufin subar wajan , Wanda haka yayi daidai da zuwa motar yan sanda wajan, yan sanda ne sunkai su shida suka fito daga motar cikin sauri suka nufi wajan da Hisham yake suka k'ame waje d'aya tare da Sara mashi , hakan da mutane suka gani ne ya sasu fahimtar lallai wannan Dan sanda ne kuma acikin yan sandan ma shi babba ne duba da yanayin muk'amin wad'an da suka Sara mashi din, Zee kuwa idanu ta zaro waje cike da tsoro don Allah yayita da shegen tsoron yan sanda , cikin sauri ta rik'o hannun Lauratu cikin k'asa k'asa da murya tace "anty munshiga ukku kin janyo mana masifa don Allah kizo muje tun kamun yasa a kamamu kinji, " Wata harara laurat ta zabga mata don itakam ko a jikinta saima tsaki da tayi sannan ta fisge hannunta daga cikin na zee tayi wucewarta inda motarsu take, da sassarfa itama zee tabi bayanta , koda taje har kauratu ta shiga ta zauna a mazaunin direba tafara kiciniyar Tayar da motar , da sauri itama ta bude gaba ta zauna ta ja sukabar wajan aguje tana maijin haushin tsayar dasu da zee tayi wajan shegen shashancinta, Duk abunda sukeyi Hisham na kallonsu ta k'asan ido kuma yana jinsu don Allah yayi mashi ji kamar maciji , maida hankalinshi yayi kan yan sandan inda yabasu umurnin su tafi da yaron station kuma duk Wanda yazo kar su bada shi har sai yazo gobe, inda shikuma ya juya yanufi motar shi Wanda sai yanzu yake mamakin rashin ganin Momma a wajan, Wayam haka ya tadda motar bakowa a ciki , da sauri ya zaro wayarshi daga aljihu yafara kiran layinta, ringing biyu ta d'auka ,ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa momma kina ina ne nazo baki cikin mortar, dariya momma tayi tace nikam na tsufa a gida yaushe zan tsaya jiranka kaida bansan lokacin da zaka bar wajanba tunda nasan doli zaku kai matar asibiti wannan yasa na fita na tare nafef na tahowata , " "Wallahi momma kin kayarmun da gaba , amma alhamdulillah tunda kina lafiya ganinan zuwa gashi har wani wajan anfara sallah" "To ai shalele kai d'inne sai a hankaki akan wannan aikin naka ,nasan tunda ka kama wannan mai lafin sai inda mai ya k'are kuma , fatan dai jikin tsohuwar da sauk'i ," "Bansani ba momma sai sai nazo daga haka ya kashe wayar tare da Jan motar yabar wajan , yanajin zuciyarshi na bugawa da sauri da sauri wanda yarasa dalilin hakan, _________________________ Gudu suke sosai kamar zasu tashi sama , sunzo daidai inda suka dauke yarinyar da yake dama can hanyar batada mutane don ba gidaje a wajan sai filaye saikuma wani mai tireda daga can nesa da inda suka dauketa , inda shagonshi yake kallon wajan , zaune mai shagon yake shida wasu abokanshi su biyu akan benci da yake baijima da bud'e shagon ba don lokacin da suka dauketa shagonshi a rufe yake shiyasa da tabbas zai gansu alokacin, Kamar k'yaftawar ido sukaga abund'e mota an cillota waje sannan aka koma Jan motar a 360 aka bar wajan kamun kace mi sai k'urar motar kawai, Cikin zaro ido da tsananin tsoro suka kalli junansu kamun suka koma maida dubansu ga yarinyar Wanda basa iya fahimtar halin da take ciki ko kuma wacece saboda d'an tazarar dake tsakaninsu da inda take , " innalillahi Iro mike shirin faruwa ne " d'aya daga cikinsu ya fad'a , "Ina zan sani Abba kawai kuzo muje muyi shahada muga abunda Ke faruwa zaifi, 😳zaro ido d'ayan yayi yace "mii bakuda hankaline to wallahi badani ba wai ganganci haihuwa ga damana kunga ma tafiyata wallahi yanzu wani Abu na faruwa mu yan sanda zasu fara tuhuma , kuma ina Baku shawara da kubar wajan nan zaifi maku , ka rufe shagonka ka k'ara gaba ni nayi nan, yafada cike da tsoron abunda zai iya faruwa suna kallo yayi tafiyarshi, Suna haka sukaga wata yarinya sanye da kayan makaranta irin Wanda yake jikin wannan dake kwance bayanta kuma mazane sunfi su shida saikuma yan sanda su biyu sai faman zuba sauri sukeyi kamar zasu tashi sama , Aikuwa suna hango yarinyar kwance suka kwasa aguje suka nufeta , iyayenta ne su biyu sai yayyunta su hudu sai kuma wannan yarinyar da suke tare lokacin da su zayyan suka saceta itace taje ta fada agidansu tana kuka nanfa suka fito suna nemanta sunyi zagaye har sungaji kamun suka yanke shawarar sanarma da yan sanda to shine aka nemi yarinyar da ta kawo su daidai inda abun yafaru shine suna zuwa suka taddata awajan a yashe, Cikin tsananin tashin hankali ganin halin da yarinyar Ke ciki yasa gaba dayansu suka rikice yayyunta har sunfara kuka musamman da sukaji Baffansu yana cewa ai bata Numfashi , d'aya daga cikin yan sandan ne cikin tausayamasu yace Baba bari mutafi asibiti zaifi kila suma tayi insha Allah bata mutu ba ,d'ayan d'an sandan kuma wajan yake k'arema kallo inda idonshi ya hango mashi su iro sun zuba masu ido, da hannu yamasu alamar suzo ,jiki a sanyaye iro ya rufe shagon suka nufi inda suke , suna zuwa aka kwashi yarinyar suka Sanya a motar yan sandan , nan Dan sanda daya yashiga yaja motar suka nufi asibiti inda d'ayan ya sanya. Su iro da yayan yarinyar d'aya suka nufi station don yimasu wasu yan tambayoyi, __________________________ Saida yayi sallar isha sannan ya dawo gida , wanka kawai yayi ya fito daga dakin nashi yanufi falon Momma , zaune ya sameta tana kallon labarai a tashar Al'jazira ,gaisheta yayi ta amsa tareda cewa "shalele sai yanzu aka dawo " "Eh Momma na tsaya masallaci ne," "To da kyau akawo maka abinci ne ?" "Aa sai anjima zanci" "To shikenan ya labarin 'yata kuma , tund'azu nake jiranka kazo naji yadda ake ciki, " Kallon rashin fahimta yamata yace " wane labari kuma ? Wace 'yar taki ? " Tsuke fuska Momma tayi jin zai fara mata rainin wayo ,cikin tsuke fuska tace 'yata Samra nake.nufi mana , " "Samra ? Wacece haka kuma ? don shi harga Allah ya manta da wata Samra kuma dama can bawai yasan sunanta bane , Cikin fusata Momma tace kaga banson lalata yarinyar da mukaje dazu dazu dakai wajanta shine har zakace ka manta tsabar kai rainani , to inason inji inda aka kwana ne don da wuri zamusa lokacin bikin nagaji da ganinka haka ba sure, Wani makirin murmushi yayi cikin sigar lallashi yace au ai bangane wadda kike nufi bane , dama sunanta Samra masha Allah suna mai dad'i ai da yake ban tambayeta sunanta bane shiyasa bangane ita kike nufi ba, " Kallon tuhuma momma tayi mashi tana tunanin taya har zai kira yarinya suyi fira amma yakasa tambayarta sunanta anya kuwa kodai .......kauda tunanin tayi sannan tace " to yanzu dai ya ake ciki ? Tayi maka ko ? don bamuson aja lokaci, " "Eh Momma tayimun masha Allah ai kin iya za'be kam masha Allah yarinya kamar Zar'be saboda azabar tsawo , aikam tacika mace gaskiya , gata fara Tass ," " Sam murna bata bari Momma ta fahimci sukar yarinyar yayi ba cikin farinciki tace to alhamdulillah masha Allah zankira hajiya Sarah tagayawa mahaifin yarinyar zamu aiko anjima zan kira kawunka da abokan Abbanka sai Susa rana suje Neman auren, Cikin fad'uwar gaba da tsoro kar yayiwa kanshi salalar tsiya fa yace "Aa momma afara tuntu'bar yarinyar Aji ta bakinta karku yanke hukunci batareda da anbata damarta ba , atambayeta aji in ta amunce kinga shikenan , " "Kaga karka damu indan ta Samra ne dama can Kaine abunji amma ita kam tuni ta amince ,cikin tsoro ya zaro ido waje tare da cewa "nashiga ukku Allah gani gareka," Cikin mamaki tace "kashiga ukku kuma ? Ancema ka kwantar da hankalinka tuni ta amince to wane ukku ka shiga ,ada kamun muje kanata bak'in rai yanzu kuwa gani d'aya har ka zauce haka algungumi anaso ana munafurci ni bari kaga naje na kira hajiya Sara tayi maganar tana mikewa tsaye tayi shigewarta dakinta ta barshi nan yana rabon idanu kamar Wanda yayiwa sarki k'arya, Hannu bibbiyu ya dora akai kamar wani mace yace yau nashiga Tara bama ukku ba Allah ka dubeni wannan yarinyar ko a lahira akabani ita ai nasan banyi abun kirki ba wallahiπŸ™ŠπŸ˜Ήtashi yayi yakoma d'aki cike da zullumin ko barazanarsa zatayi aiki akan yarinyar kuwa , ya zaiyi in yarinyar bataji gargad'inshi ba , ! Wata zuciyar tace mashi kai kwantar da hankalinka ai da ganin yadda ta tsorata bazatayi gigin cewa tana sonka ba da wannan tunanin yasamu nutsuwa, Laptop d'inshi ya janyo yafara late latse tsawon awa biyu yayi yana wani aiki aciki kamun ya rufe , wanka ya sake tareda yin alwala yayi shafa'i da wuturi sannan yayi shirin kwanciya don baccine sosai a idonshi , sai dai kwanciyar shi keda wuya ya nemi baccin ya rasa sakamakon fuskar kyakyawar yarinyar dake mashi gizo, gaba d'aya yanayinta yake gani lokacin da take masa masifa da Dan bakinta mai kama dana yara yayinda dimple d'inta na gefen dama Ke lo'bawa sosai Wanda yake k'ara ma fuskarta kyau , gaba daya ya shagala da tunanin wannan yarinyar da baimasan a duniyar da take ba , sai faman murmushi yakeyi Wanda shi kanshi baisan yanayinshi ba , sai samun kanshi yayi da ayyana inama itace Momma ta za'ba mashi ba wannan tinkiyar ba yarinya Sam ba fasali ba aji irin na mata gatanan dai sakakaka kamar ansako shanuwa tsaki yayi a fili yace " kai miye hakane ina ruwana da ita akanmi zan tsaya tunanin wata mace har ta hanani bacci yazama doli na yak'iceki koda Ke mayya ce to ni nafi karfinki banza masifaffafiya kawai ,mrtsss yak'ara jan tsaki a haka ya gyara kwanciyarshi yafara salatin annabi a hankali kamun kace mi bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi, _______________________ Washe gari da wuri ya shirya ya nufi office ,yana zuwa ya nemi ganin Wanda ya wakilta don kula da tsohuwar da aka bige jiya, inspector Sale , yana shigowa ya Sara mashi tare da cewa good morning sir , "morning " yace mashi yaci gaba da tattara wasu takardu saida yagama ya dubeshi da kyau yace "ya jikin matar nan kuwa da sauk'i ? sannan ansamu wani Dan uwanta ne ? " "Jikinta da sauki sir Allah ya taimaka bata wani ji ciyo sosai ba yar kurkurjewa CE kawai sai buguwa da bayanta yayi sosai amma da sauk'i , ansamu yan uwanta yanzu haka kuma likitan yabada tabbacin nan da kwana ukku zasu sallameta tunda jikin da sauk'i , Ajiyar zuciya yayi yace "to Alhamdulillah anjima zanje naduba jikin nata , Allah yakara tsare gaba , Sale ya amsa da amin , bashi takardun yayi yace zaka iya tafiya ga wannan ka kaiwa sajen Abubakar shi yasan inda zai kai ," "OK Sir yes sir ya Sara mashi ,maimakon ya juya ya tafi sai kuma ya tsaya yana yan soshe soshe , kallonshi Hisham yayi tare da d'age mashi girarshi d'aya yace da matsala ne ??" Cikin in ina yace "am dama maganar yaron nan ne tun jiya mahaifinshi Ke zarya anan Ashe wai d'an alhaji Kabir naira ne to shine suketa zarya anan , " ya k'arashe maganar a sanyaye ganin wani mugun kallo da ogan nashi yayi mashi cikin kaukausar murya yace "to sai akayi Yaya ? Karka sake zomun da. Wannan maganar banshirya ganinsu ba zaka iya tafiya , cikin jin haushin ogan nashi ya juya tareda cewa sorry sir yafita daga office din yana mai tsinewa Hisham don yaso samun kudin da alhaji kabir yamashi alkawarin zai bashi inhar yayi masu kokarin da aka basu Berlin yaron. Sai misalin k'arfe 4 na yamma yabar office din yanufi asibitin da aka kwantar. Da matar nan tareda insfector sale , A hankali suka murd'a hannun gambun suka shiga ciki , tsaye take tana wasu rubuce rubuce akan file. Din matar , k'amshin turarenshi ne yafara yi masu sallama a d'akin , kamun ya shigo bakinshi dauke da sallama, d'ago kan da laurat zatayi ne idonta yafad'a cikin nashi , gaba dayansu saida zuciyoyinsu suka buga kamun suyiwa junansu kallon ido cikin ido ......................kai nagaji don Allah sai kuma gobeπŸ™„πŸ™„πŸ™„ JAMIIN DAN SANDA FANS 2 BAKU COMMENT YAKAMATA KU GYARA DON WALLAHI ZANKAI INDA ZAKU BUKACE LITTAFIN NAN AMMA BAZAKU SAMU BA HAKAMA GRP DIN *MMN YUSUF FANS* ZAN CINCI MASU COMMENT MUKOMA GEFE MUYI ABUNMU TAU KUMA BA YANZU BA SAI LOKACIN DA BAZAKU IYA JURAR RASHINSHI BA NIKUMA ALOKACIN ZAN RAMAπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *masuyimun comment ngd sosai Allah ya biyaku ya faranta maku kamar yadda kuke farantamun duk wadda tamun comment ina gani kuma inajin dadi saida bazan zamu damar binku dai bayan dai ina gdy ba saboda idona sake ciyo saboda hasken wayar amma ina ganinku kuma inajin dadi ngd sosai* πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kijiβœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ» Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi* Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi Maganin hawan jini Maganin sugar Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya, Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi *Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜ wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi maganaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 07069711327 [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *MALLAKAR* *Maryam umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ *Mutum ce kuwa* *Minene asalina* *Husna ko Huzna* *and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ *Jami'in Dan sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ_25 ............................."kaga banason fitina rabu dasu duk Wanda yayi nagari kansa amma har yaushe zanbari ka tsaya wani kula irin wad'an nan mutanen salon ka k'ara 'batamin lokaci don kar kaje ko ? To ba inda.zaka fita don nasan hanyar guduwa kake nema tunda inba haka ba ai yanzu ba'a fagen aiki kake ba , Shiru Hisham yayi don maganar gaskiya kowaye acikin motar to ya bashi haushi sannan haka kawai yaji yanason yaga wane d'an iskan ne acikin motar, ba tare da yace komai ba ya koma ya gyara zamanshi tareda rufe k'ofar Wanda a dai dai lokacin aka basu hannu , ai kamun ma suyi wani motsi tuni motar su zayyan ta kutsa a inda aka fara samun hanya sabida wucewar na gabansu take suka wuce da gudu kamar walk'iya suka halba titin , k'wafa kawai Hisham yayi tareda bin motar da harara, sannan ya kunna tashi motar yaja suka dauki tasu hanyar inda sukayi hannun Riga dasu zayyan , Tafiyar minti goma sukayi suka k'arasa unguwar su hajiya Sara , unguwa ce ta masu hannun da shuni , unguwar shiru shiru Sam ba hayaniya sai iska mai dad'i dake k'adawa a hankali , Hon sukayi mai gadi ya bud'e masu k'aton get din gidan , a hankali Hisham ya k'arasa inda aka tanada don ajiye motoci , gida ne k'aton gaske Wanda kallo daya zaka mashi kasan cewa an narkar mashi da dukiya mai tarin yawa, kallon gidan yakeyi a hankali yayinda yake mamakin ina Momma tasamo wad'an nan hamshak'an mutanen kuma , πŸ€” dafe kanshi yayi cikin matuk'ar 'bacin rai don shi Allah yagani masu kudin nan basa burgeshi Sam bayason mu'amala da Wanda yasan yafi k'arfinshi don gudun wulak'anci amma shine yau momma zata kawo gidan mutane a matsayin Wanda take tallanshi ai a take yaji zuciyarshi tafara tafasa haka dai ya daure yafito daga motar jiki a sanyaye don ganin Momma ta fita har tayi gaba, Aguje tafara saukowa daga matakalar benen tsabar Saurin da takeyi har had'a matakala biyu takeyi bakinta kuwa kamar zai yage waja. Kiran Momy Momy Momy, kanajin muryarta zakasan cewa tana cikin matuk'ar doki da farinciki , Anan falon k'asa wata hakimar mata ce zaune acikin kujera ,matar k'atuwa ce masha Allah tanada jiki sosai Wanda har k'ibar taso tamata yawa , cikin tsabar sauri tafara cikiniyar mik'ewa tsaye kasancewarta k'atuwar gaske yasa saida takwashe wasu second kamun tasamu ta mik'e duk da tanacikin Sauri kuwa, Afusace tafara magana " Ke Ke wai kekam wace irin shashashar yarinya ce ,yau kwana nawa kenan ina jan kunnenki akan karki kuskura kiyi mana wannan shashancin naki da kika saba , to ahakan kikeson yace yana sonki gani nan kullum bakida nutsuwa , wallahi in kikayi wasa wannan murd'ad'd'en yaron bazai yarda ya aureki ba don haka garama ki kama kanki da wannan banzan rawar kan naki," Turo bakinta.tayi sannan ta murgud'a baki tace "to ni miye laifina nagansu fa sunzo ne ina sama naga shigowarsu shinefa zanje na tarbosu, " Cikin takaici matar da aka kira da momy ta watsa mata harara tace to uban waye yace kizo tarban nasu ? Oya don Allah maza ki koma kuma karki kuskura kifito har sai na nemiki shashasha kawai, turo bakin tak'ayi kamun cikin jin haushi ta juya ta nufi wani daki dake cikin falon, Komawa momy tayi ta zauna tana jiran shigowar bak'in nata , da yake akwai tazara sosai tsakanin wajan ajiye motocin da k'ofar shiga gidan, Da sallama Momma ta shiga falon , cikin farinciki da murnar ganinta momy ta amsa mata sallamar tare da fadin oyoyo hajiya maryam sannu da zuwa sannu da zuwa , cikin farinciki itama momma Ke amsa mata kamun ta zauna a d'aya daga cikin kujerun falon , bayan sun gaisa ne da tambayar lafiyar juna hajiya Sarah takasa hak'uri tace Aminiyata ina d'an nawa yake ne banganshi ba, " "Hmmm aikin San halinshi yana waje bari na kirashi ta waya nace yashigo," "A'a karki kirashi bari na tura *Samra* ta shigo dashi kawai , murmushi momma tayi kamun tace yawwa hakan yayi kirata taje ta shigo dashi, " Mulmulawa momy tayi da kyar ta tashi tanufi haryar dakin da Samra take , koda tashiga dakin samun Samra tayi gaba madubi sai faman k'arawa face dinta kwalliya take , kuma masha Allah tayi kyau sosai kasancewarta dama can kyakyawa ce saida kwalliyar tayi mata yawa wannan yasa takoma kamar wata aljana tsabar yadda aka fente fuskar nan, Rik'emata hannu momy tayi tace "to ya isa haka sarkin kwalliya maza kitashi kije ki shigo da saurayin naki yana waje sauran karki nutsu kije kina wannan rawar kan ya rainaki, Cike da murna ta mik'e tana cewa kai momy nifa da hankalina nasan yadda zanyi agabanshi , bari naje kar ya gaji da jira da sauri ta ra'ba ta gefen momy ta fice daga dakin, Tun daga nesa yake k'are mata kallo ta k'asan ido tafe take kamar zata kifa saboda wasu shegun takalmi da take sanye dasu masu masifar tsini , Samra doguwa ce irin sosai din nan fara CE tass tanada doguwar fuska mai dauke da dogon hanci da manyan idanu fatare Tass sai d'an k'aramun bakinta Wanda ya k'arawa doguqar fuskarta kyau ,atak'aice dai Samra kyakyawa ce sosai a fuska saidai batada cika irin ta cikakkiyar mace doguwace sosai kuma siririya ce wadda ta tafi samk'am kamar muciya Sam ba gaba bare baya , gata da shegen son saka takalmi mai tsini wannan yasa take k'ara tsawo marar fasali , cikin yan seconni yak'are mata kallo azuciyarshi kuwa tsaki yayi yace " wai wannan abun momma take mun fatan in aura sai kace Wanda ya rako maza duniya , haba , to in auri wannan ince na auri mi, ai da duk wata rashin sa'ar aure ta tabbata a kaina wallahi mrtsssss yaja wani dogon tsaki afili Wanda tsakinshi yayi daidai da isowarta kusa dashi , Bakinta kamar zai yage saboda fara'a tace " Dear sannu da zuwa ygd wai momy tace ka shigo daga ciki, " Kamar ya falla mata mari haka yaji data kirashi da Dear amma dai ya danne jin haushin shi ,ba tare daya kalli inda takeba ya daga k'afarshi yafara tafiya, Da Sauri ta biyoshi tashiga gabanshi don yimashi jakora , tafiya suke yana k'arewa d'an k'ugunta kallo awa na sauro (injishi )😹 azuciyarshi yake cewa oh Allah mai iko wannan in auren akayi ma ko a ina zata ajiyeni da wannan k'ugu nata kamar na 'yan shila sai wasu dogayen k'afafu haka kamar na barewa wannan da alama ma zatafini tsawo , komai ya tuna kuma sai yayi saurin cewa astagfirullah afili tare da kauda isonshi daga kanta Wanda yayi daidai da shigarsu cikin k'ayataccen falon gidan inda momma da momy keshan firansu , Har k'asa ya duk'a ya gayar da Momy , itama cikin jin dadi da murna take amsa mashi gaisuwarshi , daga nan tasa Samra ta rakashi falon bak'i, Saukar ban girma akama Hisham da momma , inda yan uwan samra maza da mata suka rink'a zuwa suna gaisawa dashi daga nan aka kaishi har falon Daddyn samra suka gaisa , Alhaji usman sahabi yaji dadin ganin Hisham a matsayin surukinshi Wanda yana fatan hakan ya tabbata tabbas yasan da yarsa tagama dace da nagartaccen miji kamar Hisham, bayan dawowarsa ne falon bak'in ya buk'aci ganin Samra zasuyi magana daga momma har Momy rasa Wanda yafi wani murna da farinciki akayi don suna ganin Hisham shima yakamu da son Samra tunda har gashi yanacewa akirata zasuyi magana, Cikin karad'i da rawar kai da ya zame mata jiki tayi sallama ta shigo , badon yasan darajar sallama ba to da bazai amsa mata ba don haka akwai wani haushinta yakeji musamman da yaga yadda iyayensu suka dauki abun da gaske , Samra kam Sam bata damu da yanayinshi ba saima zama da tayi akusa dashi tana yi mashi wani fari da ido tare da cewa "yawwa dear gani ," juyowa yayi ya fuskanceta sosai suka kalli juna ido ciki. Ido , tsuke fuskarshi yayi tamau lokaci daya ya koma ainahin Hisham d'inshi lokaci daya ya juye mata izuwa wani jarumin namiji Wanda kallo daya zaka mashi ka kirashi da suna Jarumin jarumai haibarshi da k'warjininshi ne suka cika mata ido Wanda hakan yasa ta sauke k'wayar idonta daga cikin nashi a hankali zuciyarta na bugawa ga wani tsoronshi da ya shigeta lokaci daya, Cikin jarumar muryarshi yafara magana yana cewa, "Ke d'ago kanki ki kalleni ," a hankali samra ta d'ago manyan idonta ta zuba mashi Wanda zaka iya hango tsoro k'arara acikinsu , tsaki yayi sannan yacigaba da cewa " kinga nayi maki kama da shashasha ?? Ko ni sa'an wasanki ne ?" Da mamaki take kallonshi saboda mamkin tambayoyin nashi Sam bata fuskanci abunda yake nufi ba, cikin sanyin murya tace "ni bangane abunda kake nufi ba, " ta karashe maganar da murgud'a mashi baki Wanda yazame mata jiki yin hakan, Cikin fushi yace "to yanzu ko zaki gane , inason kifita a hanyata Sam bakimun ba kuma bazan aureki ba , don haka inason kisani kuma kisa aranki ni bazan iya aurenki ba don bansan abunda zanci ajikinki ba Ke in banda ma karambani inake ina ni ai wallahi namaki yawa tako ina don haka inason yanzu kije ki gayawa iyayenki bakya sona bazaki aureni ba in kikayi haka to kin taimaki kanki da kanki , " Cikin tsiwa da rashin kunya Wanda dama can d'abi'arta ce tace "to in kai bakasona ni ina sonka kuma mamanka tana sona don haka sai na aureka in yaso ka kasheni in.............wasu yawu masu kauri ta had'iye da k'yar lokacin da tayi arba da bindigar daya zaro daga cikin k'ugunshi ya nunata da ita kamar zai harbeta da gaske , cikin kakkausar murya yafara magana yace , "zakiyi abunda nace ko bazakiyi ba , ? Kisani in kika kuskura kikace ma iyayenki da mahaifiyata kina sona to sai nafasa kanki da wannan bindigar , kuma banyarda ki gaya masu yadda mukayi dake ba kawai kice masu bakyasona banyimaki ba inba hakaba sai nafasa shegen kan nan naki mai rawar tsiya da wannan bindigar ,ya k'arasa maganar yana gyara kunamar bindigar , Ai a firgice samra ta duk'a tanabashi hakuri akan yayi hak'uri bazata gayawa kowa ba kuma bazace tana sonshi ba don Allah yayi mata rai kar ya kasheta ,wani munafukin murmushi yayi ganin plan dinshi yatafi dai dai nan yasata ta share hawayen tareda gyara fuskarta sannna yace mata ta tashi ta tafi , aikuwa kamar jira take kamar walk'iya haka tabar wajan don ta tsorata sosai da lamarinshi dama can samra matsoraciyace ta bugawa a jarida, Ganin hakan yasa yayi ficewarshi shima daga d'akin yayi waje cike da farinciki , yana zuwa inda yayi parking ya bude motar yashiga yana sauke ajiyar zuciya ji yake kamar an sauke mashi wasu kaya , Samra kam jiki na rawa tahiga falon batare data kalli inda su momma suke ba ta haura sama da sauri ta shige dakinta,tana zuwa ta fada bisa makeken gasonta tasaki kuka ,yayjnda maganganun Hisham Ke mata amsa kuwa acikin kunne, Sukam basu kawo komai ba musamman momma ta Dauka duk kunya ce nan tayiwa hajiya Sara sallama saboda magariba takusa inda hajiya Sara ta rakota har wajan motar Hisham nan suka k'arayin sallama da alkawarin zasuyi magana ta waya komi kenan , suka juyo suka dauki hanyar gida, Ganin Hisham cikin farinciki da walwala ba kamar yadda suka taho ba yasa momma farinciki a zataonta ya kar'bi tayinta ne ,taso ta tambayeshi amma kuma sai taga bari kawai ta barshi har su k'arasa gida sai suyi magana, Sunzo daida wani round danja ta koma tsayar dasu , nan take tunanin mortar d'azu ya fad'owa Hisham arai , yarasa abunda yasa yakejin haushin rashin ganin mai wannan mortar , amma ba komai in kare na yawo zomo na yawo watarana za'a had'u don tsab ya rik'e number mortar, Kamun abasu hannune wani mai mashin yazo aguje Sam baiyi tunanin tsayawa ba haka ya wuce ta gabansu aguje yana wani tuk'in ganganci kamar titin na ubanshi ne Wanda zuwanshi yayi daidai da zuwan wata tsohuwa zata tsallaka titi aikuwa babu zato babu tsammani saiji akayi yayi sama da wannan tsohuwar ta fad'o Tim tareda FASA wata uwar k'ara , Cikin wani irin zafin nama Hisham ya b'alle murfin mortar yafita aguje yayi kan mai mashin din nan da yaketa son ya gudu amma mutane aun karamashi cafko wuyanshi yayi yayi gefe dashi yafara zuba mashi mari kamar an aikoshi , Wanda a daidai wannan lokacin ne danja tabasu damar su wuce , nanfa mutane suka fara tafiya yayinda wasu sukayi parking a gefe don ganin yadda zata kaya , tsohuwar kuwa tuni Hisham yabada umurnin akaita asibiti yayinda shikuma yayi waya a station dinsu akan aturo mashi yan sanda su tafi da yaron , kuma har lokacin dukan yaron yakeyi gaba daya ya hada mashi jini da majina, Adai dai wannan lokacin motar su Lauratu ta sawo kai wajan ganin mutane sosai a wajan ya tabbatar masu da ba lafiya ba , zee ce Ke Jan motar don haka ta gangara gefe tayi parking tana cewa "anty inaga ba lafiya muje muga abunda yake faruwa pls , Dafe kanta lauratu tayi cikin jin haushi tace " wai zee sai yaushe zaki daina wannan halin naki nabin diddigi inaruwanki da abunda yake faruwa don Allah ni kija mota muje agajiye nake wallahi ga kaina na ciyo sosai , " "Haba anty don Allah kibari muje mugani mike faruwa kikasani ma ko wani mai Neman taimakone mu taimakamashi , inkuma bazakije ba ni kijirani yanzu zan dawo bari naga mike faruwa,daga haka batajira cewarta ba ta bude gambun ta fita ta nufi wajan da taron yake , Girgiza kai kawai laurat tayi tana mai mamakin halin kanwar tata na shegen ganin k'wam , kamar ba zata fita ba kuma sai taji bari taje ta ganewa idonta tunda zee tasasu tsayawa , A hankali ta fito daga motar ta rufe , sanye take da doguwar rigar atamfa kalar sararin samaniya rigar tayi mata cif ajikinta saman rigar kuma farar rigace irin ta likitoci ajikinta sai k'aramin farin gyale da tayane kanta dashi ,fuskarta fayau bawata kwalliya sai farin glass irin nasu na likitoci Wanda yakara haska kyakkyawar fuskarta , a hankali take tafiya tanufi inda ake hayaniyar , zuwanta yayi daidai da wani shuri da Hisham yayiwa gayen nan mai mashin , wani irin zaro idanu tayi cikin jin haushi da tsawa cikin siririyar muryarta ta cewa Hisham " kai wane irin mugu ne kai kam mi yaimaka da zaka mashi irin wannan dukan , wane irin rashin imani ne zakama d'an uwanka musulmi irin wannan dukan , kasan darajar da jinin d'an Adam yakedashi kuwa ko kasan ..............wani irin kallo da Hisham ya watsa mata ne yayi sanadiyar rufewar bakinta batare data shirya ba , lokaci d'aya zuciyarshi tayi wani irin bugu da baita'bajin irinshi ba idonshi yak'ara warewa akanta yanamata wani irin duba mai.......................✍🏻 *wadan da basu comment wlh zanfara cireku ba ruwana GRP din da banawa ba kuma in naga baku comment to zan daina turawa* [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *MALLAKAR* *Maryam umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ *Mutum ce kuwa* *Minene asalina* *Husna ko Huzna* *and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ *Jami'in Dan sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ-28 ........................."Ke banason shashanci wani irin zai kashe ki kuma , ? " "Wallahi momy kasheni zaiyi haka fa yace .....saikuma takasa k'arasawa tuno da gargad'in da yayi mata, " uhumm ina jinki yace mi " momy ta tambayeta , "Bakomai momy nidai kawai bana sonshi , " cikin mamaki momy ta tsareta da ido ganin ita ta nace akan tanason Hisham tun ganin farko da tayi masa lokacin da suka kaima hajiya maryam ziyara, wannan yasa cikin hikima ta janyo hankalin hajiya maryam akan su had'a yaran nasu aure don k'ara dank'on zumunci , ta 'boye cewa Samra CE Ke son Hisham din, _anya kuwa yarinyar nan batada aljanu_ ta raya a ranta batare da tasake cewa komai ba ta juya ta fita daga d'akin, direct saman Daddynsu tayi , Da sallama ta shiga falon nashi yana zaune akan wani kyakyawan kafen ya kishingid'a da waya a hannunshi yana daddanawa da gani wani yake nema a wayar, zamanta yayi daidai da kara wayar da yayi a kunnenshi , nan yafara magana da Wanda yake kan layin sunjima suna waya kamun suyi sallama ya katse kiran , juyowa yayi ya kalleta da kulawa yace " yadai madam lafiya kuwa na ganki kamar kina cikin damuwa?" "Hmmm ba doli ka ganni cikin damuwa ba Daddyn samra al'amarin yarinyar nan ne yafara bani tsoro , wai tanacan tana kuka akan batason Hisham bazata aureshi ba , bayan kuma ita tanace akan tana sonshi ,tunani nake anya kuwa yarinyar nan batada aljanu duba da yadda kwata kwata batada mashinshini ban ta'ba ganin wani saurayi ya biyota yace yana sonta ba, tun bata damuwa har tazo tafara damuwa har kuka takeyi akan hakan, to yanzu daga sama tasamu yaro kamar Hisham amma wai tace bata sonshi gaskiya da walakin goro a miya inaga yakamata a nema mata magani in ba aljanu ne suka aureta ba,tayi maganar cike da damuwa, Nisawa Daddyn samra yayi yace " wannan ai iskanci ne taya zata maidamu kananun mutane bawani aljanu iskanci ne da ta'bara ni nagaji da zamanta a gidan nan don haka bazan bari wannan yaron ya su'buce mata ba tunda ita batasan inda yake mata ciyo ba" yafada cikin jin haushi , Mommy ma batace komai ba don Allah yagani itama batason yarta ta rasa wannan Damar ,wannan yasa ta yanke shawarar tunkarar momma da maganar don Susa lokacin auren anan kusa, __________________________ "Subuhanallahi ita samra CE tace hakan ? To amma mi yake faruwa naga kamar tana farinciki a lokacin sai kuma yanzu daga baya tabamu matsala ,?" Daga can aka amsa da cewa " wallahi kuwa hajiya maryam gatanan duk ta rame kullum cikin kuka tun ina daukar abun a wasa har tafara bani tsoro batada aiki sai kuka da damuwa shine nace ko zamusa lokacin auren nan kusa kila in taga an daura auren ta hakura ?" "Aa hajiya bazamuyi hakan ba ai yanzu andaina yayi auren doli kidai kara lallabata har kisamu ta yarda zaifi yaran yanzu in basason Abu to ba'a tirsasamasu don in aka sasu doli to abun bazaiyi kyau ba," "To shikenan zank'ara lalla'bata insha Allah," nan sukaci gaba da tattaunawa kamun sukayi sallama suka ajiye wayar, Hisham da yake zaune a gefe yana cin abinci tuni ya zubama Momma manyan idanunshi don tuni ya fahimci inda zaican ya dosa , kallonta yake cike da damuwa a fuskarshi kamar gaske acikin zuciyarshi kuwa ji yake kamar ya taka rawa sai dariyar mugunta yakeyi , cikin marairaicewa kamar gaske yace " Momma mi naji kuna fad'a ne ? Badai my samra CE tace batasona ba to amma ni miye abun k'i ajikina Momma , dama irin wannan nake gudu shiyasa banason wannan tallan nawa da kikeyi yanzu gashinan kin jamun zasu wulakantani bayan kuma na kamu da son yarinyar yanzu ya zanyi kenan , yafada kamar zakiyi kuka, Dafashi momma tayi tace "karka damu shalele insha Allah komai zaizo da sauki tunda iyayenta naso nasan zasu shawo kanta, (ba doli su so ba tunda zasu yimun shak'e inba shiba wane namijin ne zai kwashi wannan yarinyar da gabad'aya babu kayan wasa a jikinta) ya fad'a a ransa , Sam baisan cewa a fili yafad'a ba saida yaji momna tace " mi kake cewa ,?" Dan daburcewa yayi yace aa Momma cewa nayi akwai abarta tunda tace banyi mata ba kar a tsaurara bincike Ku kyaleta kawai don ni nayi alk'awarin bazan ta'ba auren yarinyar da ta furta cewa bata so na ba , kuma nasan girman alk'awari don haka bazan karya shi ba taje can Allah ya had'a kowa da rabonsa amma tabbas bazan aureta ba tunda har ta furta da bakinta bata sona ,yayi maganar yana had'e fuska sosai ,Momma zatayi magana ya tareta da cewa " don Allah Momma kibar maganar nan Sanin kanki ne bazan taba karya alk'awari ba duk alkawarin da nayi to sai na cikashi kawai kiyi hakuri , " Cikin sanyi Momma tace to shikenan Shalele dama kai nakeji gashi ka fad'awa soyayyarta karkazo abun yana damunka , Mahaifiyarta kuwa banida matsala dasu tunda ta 'bangarensu ne aka samu matsala," wani shu'umin murmushi yayi tareda cewa " karki damu Momma acin watan nan zan kawo maki yarinyar da zan aura. Nayi maki alk'awari, nan da nan Momma ta washe baki tana cewa to alhamdulillah shalele nasan zaka kawo tunda kace kayimun alkawari Allah yabaka ta gari " yace "amin" __________________________ Agurguje take shiryawa ta fito tsaf cikin uniform dinta a tsaitsaye ta dauki kunun da inna Inno ta jiye mata tafara sha , batasha da yawa ba ta ajiye ta juyo tana kallon iyayenta tace "Baba Inna ni zan tafi makaranta sai na dawo , " Atare sukace "to Mariya adawo lafiya Allah ya tsare, cikin jin dadi ta furta "amin amin , " kallonta ta mayar ga Yayanta Sulaiman tace " Yaya na shirya muje ko ," karkacewa yayi ya sanya hannunshi a aljihu ya dauko kudi Dari ukku yabata yace " yau ilyasu baya nan wani uzuri yasa yafita da mashin din nasa bare na amso na kaiki gadai wannan ki hau nafef kuma ki saye wani Abu kici in antashi insha Allah zanzo na daukoki nasan kamun sannan ya dawo, " "To shikenan yaya nagode sai na dawo" tajuya tanufi hanyar fita daga gidan, "anty ki sayomun awara in zaki dawo kinji ," cewar Asmau yar autar Inna inno , cikin murmushi da kaunar 'yan uwan nata tace " to Asmaun inna zan kawo maki insha Allah , daga haka ta fice daga gidan tana sauri don yau ta makara sosai , Asmau da khadija ma bayan sungama karyawa makarantar suka wuce inda sukabar Yaya sulaiman sai Baba , Inno tana kicin tana shara yayinda Baba yake gefe shida yaya sulaiman suna tattaunawa , cikin jimamai Baba yace , " to yanzu kai sulaiman ya kakeganin zamuyi nidai banida kudin nan wallahi kasani kaikuma abubuwa sunyi maka yawa naso Mariya ta canza karatun nan amma ta kafe ita sai karatun aikin jinya takeso to ni Ina naga kudin da zanyi mata laluran makarantar dashi , " Nisawa yaya sulaiman yayi yace " karka damu Baba insha Allah komai bazai gagaraba , kaga Mariya tanata kokari sosai banason kokarinta yatashi a banza sannan wannan karatun ne kawai zatayi kaga tasamu aiki kai tsaye yanzu ni ba gashi nan ba shekara ta ukku da hada degree na amma aiki ya gagareni sai dinki doli nakeyi , to ita in Allah ya taimakemu tana gamawa zakaga tasamu aikin nan kuma albashinau yanada tsoka kaga shikenan abubuwa zasuyi mana sauki sosai ,akwai wasu kudi da nake Tarawa acikin asusuna zan fasashi nayi mata laluran makarantar nasan insha Allah zasu isa Allah dai ya shige mana gaba, daga Inna har Baba murna suka farayi don sunason cikar burin 'yar tasu sosai wadda ta taso da wannan ra'ayin ne tun tana k'arama , nan sukaci gaba da Sanya mashi albarka da yi mashi addu'o'in samun nasara a rayuwa yadda yake dawainiya da kannenshi batare da gajiyawa ba yanasa iyayen farinciki da alfahari dashi, ____________________________ Zaune suke a office din Hisham , Baban Safiya ne da k'aninshi sai Babban yaronshi Zakari , nan suka koro mashi bayanin abunda yake tafe dasu da kuma yadda akayi suka zo wajanshi don an tabbatar masu da zasu samu adalci a wajanshi shiyasa direct sukazo wajanshi, Tunda suka fara magana ido kawai ya zuba masu cikin tafasar zuciya ,ba k'aramun bak'inciki yaji ba da suka gaya mashi bayanin da likitan yayi masu na cewa ba mutum d'aya ne yayi mata fyad'e ba ,tunanin yakeyi irin azabar da zai ganama wad'an nan azaluman idan yakamasu , ga tausayin mahaifin yarinyar ganin yadda yake zubar da hawaye da tsufanshi da komai cikin k'wafa da takaicin abun yace , Inason Ku kawomun yarinyar da abun yafaru agabanta yanzu sannan samarin da sukace sunga lokacin da aka dawo da ita suma inason ganinsu , nan da 40mnt , nuna zakari yayi yace "kai zan hadaka da yaranmu biyu kaje ka kaisu inda abun yafaru daga nan kuzomun da samarin da yarinyar , kaikuma Baba inason ka kaini asibitin yanzu inason ganin yarinyar da kuma likitan da ya dubata , " cikin farinciki duk suka mik'e ganin yadda ya kar'bi k'orafinsu hannu bibbiyu ba zancan wulakanci ko yawo da hankali , wani sanyi sukaji acikin zukatansu don suna ganin kamar ma an kama masu laifin angama, Lokacin da Hisham yaga Halin da safiya take ciki saida yaji kamar ya zubarmata da hawaye har lokacin bata cikin hayyacinta don data farka da bige bige da ihu da sambatu take farkawa wannan yasa suke banka mata alluran bacci , yaso yasameta acikin hankalinta don doli akwai tambayoyin da yakeson ta amsa mashi , haka dai ya hak'ura doli ya nufi office din likitan, Likitan na ganinshi ya mik'e tsaye tare da bashi hannu suka gaisa cikin mutuntawa , nan yayi wa likitan bayanin abunda yake tafe dashi, Murmushi likitan yayi yace " nasani yalla'bai hasalima ni nabasu shawarar su damk'a case din a hannunka ko zasu samu adalci Don wallahi an cutar da yarinyar nan cuta mai yawa Wanda sai tsananin rabo ne in zata rayu sunyi mata raga-raga da mutuncinta cikin rashin imani , wallahi na tausayawa iyayenta sosai , zan baka sakamakon binciken da akayi mata ka gani , nan ya dauko wani file ya mik'awa Hisham yana kara yi mashi bayanin abunda Ke ciki, Hisham gyad'a kai kawai yakeyi idanun nan nashi sun kad'a sunyi jawur fuskarshi ma tayi ja sosai kallo daya zakayi mashi kasan cewa yana cikin tsananin fushi da tafasar zuciya, Yajima a office din kamun yayi ma likitan sallama yabar office din , nan yabar su Baban akan zai nemesu in bukatar hakan ta taso, ______________________________ Daga asibitin ofishinsu ya koma ,koda yaje har Zakari yazo da yarinyar nan maisuna haulatu k'awar safiya dakuma su iro mai shago, da hannu kawai yayi masu alamar da su biyoshi , da sauri suka mik'e tsaye sukabi bayanshi , yana shiga ya d'ane kujerarshi yana jiran shigowarsu , Jiki a sanyaye suka fara shigowa bakinsu dauke da sallama Don sun tsorata da yanayin shi sosai kallo d'aya sukayi mashi suka tabbatar da ba wasa acikin al'amarinshi, a hankali ya amsa sallamar tasu batare da ko su sunjishi ba , tsaye sukayi suna jiran suji abunda zaice , jikinsu sai k'yarman tsoro yakeyi musamman ma Haulatu , gyara zamanshi yayi tare da sassauta fushinshi Don ya kula sun tsorata dashi yace " Ku zauna tambayarku zanyi kuma Ku tabbatar kun sanar dani abunda kuka sani, Da sauri suka gyada Kansu alamar amsawa , ta kan Haulatu yafara , kallonta yayi yace "ki gayamun abunda yafaru daki-daki a wancan ranar , sannan ki gayamun abunda zaki iya shaidawa agame da mutanen , " Cikin hawaye tafara bashi labarin abunda yafaru tun daga farko tashinsu daga makaranta har kawo sanda suka dauke safiya, jinjina kanshi yayi yace " to zaki gane samarin su nawa ne ?? Sannan zaki iya gane mutanen in kika gansu ? " Cikin rawar murya tace " aa bansan kosu nawa bane amma zan iya gane d'aya daga cikinsu Wanda shine ya fito ya janyota motar , jinjina kanshi yayi yace " to bayan wannan ba abunda zaki iya tunawa , ? Cikin tabbatarwa tace " *narik'e number motarsu yalla'bai* " Cikin jin dadi yace wow good yan mata kinyi kokari maza rubutamun number anan , kindai tabbatar da itace ko ?" "Eh yalkabai ", to da kyau maza rubutamun , saida ta rubuta ya dauka ya duba sannan Yakoma kan samarin suma dai tambayoyin yayi masu kamun ya sallamesu su tafi , zakari sai dadi yakeji gani yake kamar ma ankama mai laifinnan sai jinjinama Haulatu yakeyi da har tayi kokarin rik'e number motar, Wunin yau gaba daya Hisham akan wannan case din yayi shi sai misalin goma na dare sannan Yakoma gida bayan yagama duk wani bincikenshi kuma yagano ko suwaye masu laifin jira kawai yake gari ya waye ya kaddamar masu don sai ya gurfanar dasu agaban koto saidai duk abunda zai faru yafaru, Wanka yafarayi bayan yaje gida sannan ya ci abinci kamun yayi shirin kwanciya , kamar daga sama tunaninta ta ya fad'o mashi sai kyakkyawar fuskarta keyi mashi gizo ,wani sanyayyan murmushi ya saki Wanda baimasan lokacin da yayi ba a hankali ya furta Preety kinada kyau, Tunawa da yayi cewa yanada number ta yasa ya dauko wayarshi yafara kiran layinta ba tare da yasan abunda zai CE mata ba, a hankali wayar tashiga kuma duk bugun da zatayi dai dai yake tafiya da bugun zuciyarsa, a dai dai wannan lokacin kuwa Laurat na zaune adakinta abun duniya ya dameta ko yau saida Abbansu ya titsiyeta akan ta fito da mijin aure inba haka ba lokacin da ya diba mata ya cika to zai bayar da ita ga Wanda yaga dama ba ruwanshi, tayi zurfi cikin tunani kamar daga sama taji ringing din wayarta , a hankali ta dauko wayar ganin bak'uwar number yasa ta share wayar har ta katse sai da aka sake kira sannan ta dauka , cikin sanyin muryarta ta furta " *Assalamu Alaikum*" wani luuuuu yayi da idanunshi jin muryarta har tsakkiyar kanshi....................nagaji tunda ko comment bana samu😼😼😼😼😼 *wlh nakusa mayar da book dina na kudi akan rashin comment dinku musamman yan GRP din *Jami'i fans 2 da maman Yusuf fans da sauran grps saidai duk Wanda yakemun comment to zancigaba da bashi a kyauta Don dama banyishi da niyar siyarwa ba amma da biyu babu gara daya* ____________________________ Mmn Yusuf Dr mata sokoto πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kijiβœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ» Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi* Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi Maganin hawan jini Maganin sugar Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya, Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi *Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜ wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi maganaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 07069711327 [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *MALLAKAR* *Maryam umar Abdullahi* (Mmn Yusuf) *Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ *Mutum ce kuwa* *Minene asalina* *Husna ko Huzna* *and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ *Jami'in Dan sanda* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍 πŸ…ΏοΈ--27 ........................cikin tsuke fuska ya k'arasa shiga d'akin , don ya lura wannan matar yar rainin hankalice yanzu sai ta nemi kawo mashi wargi in taga fuska , itama cikin had'e fuska ta dauke kanta daga kanshi tana mamakin yadda kayan yan sanda sukayi mashi wani irin kyau kamar sabodashi akayi su , bata ta'ba ganin Wanda kakin yan sanda sukama kyau irinshi ba ,a hankaki ya k'arasa kusa da tsohuwar nan da sauri wani saurayi dake zaune kusa da ita ya mik'e tsaye cikin girmamawa yace " barka da wuni yalla'bai , ga wajan zama" yayi maganar yana k'araso mashi kujerar da ya tashi akanta , Kai kawai ya d'aga ma saurayin kamun ya k'ara janyo kujerar ya zauna a hankali ya kalli tsohuwar da kulawa yace " Sannu iya ya jikin , " ? Cikin muryar jin jiki tace "naji sauk'i d'an nan kuma nagode da taimakonka gareni Allah yayi maka albarka Allah ya shige maka gaba a dukkan al'amarinka Allah ya tsareka da sharrin duk wani abun sharri allah yasa kagama lafiya ngd sosai , " Cikin jin dadin addu'arta yace Amin iya ba komai ai yiwa Kaine Allah ya k'ara sauki , dukkansu da amin suka amsa , Laurat tunda ya matso kusa da ita tarink'ajin wani iri ga gabanta dake fad'uwa kusancin da suka samu yasa tana shak'ar daddadan k'amshin turarenshi gaba daya sai taji ta daburce rubutun da takeyi ma takasa k'arasawa wannan yasa ta juya da sauri tabar d'akin , yayinda Hisham ya bi bayanta da wani irin kallo ta k'asan ido Wanda ba Wanda zai fahimceshi , 'boyayyar ajiyar zuciya ya sauke a zuciyarshi yake cewa , wai wannan wacece ne ?? Laurat ma tana fita ajiyar zuciya tayi sannan a hankali ta nufi office dinta tana tunane tunane, Kallon saurayin yayi yace "am bawata matsala dai ko ? Ko akwai abunda kukeda buk'ata ne?" "Aa ranka ya dade alhamdulillah babu matsalar komai sai dai tunjiya take rigima akan itadai a sallameta ta tafi gida ko yanzu kamun ka shigo rigimar da takeyi kenan , " Jinjina kai yayi yace OK zanyi magana da likitan inba damuwa sai subata sallaman tunda jikin da sauki sosai ,"mik'ewa yayi tare da zaro kudi masu yawa yabawa yaro tareda cewa Allah ya k'ara lafiya , nan yaron da tsohuwar suka hau godiya da yi mashi kyawawan addu'o'i yayin da shikuma yafita yana mai jin dadin , don a duniya ba abunda yakeso kamar yaji ance *Allah yayi mashi albarka* Direct office din likitan ya tambaya aka nuna mashi , ba tare da tunanin komai ba ya murd'a hannun gambun ya shiga bakinshi dauke da sallama , Fitowarta daga bayi kenan daga ita sai doguwar rigar jikinta sai wata lallausar hula bak'a dake kanta ,kasancewar rigar tata black and red ce sai tak'ara haska farar fatarta tayi mata cif ajiki ksancewarta mace mai murzajjen jiki gashi Allah ya hore mata k'ira mai daukar hankali tanada cikar kirji da baya sosai Wanda in tana tafiya komai na jikinta Ke kad'awa Baren ma wannan rigar data kamata sosai , ganin ba ko wane yasa ta cire hijabinta da rigarta ta likitoci ta shiga bayin Wanda fitowarta yayi daidai da shigowarshi office din, Da sauri taja baya kamun cikin sauri ta janyo hijab din ta ta Sanya , Kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi tareda jin wani irin yanayi Wanda bai ta'ba fuskantar irinshi ba , a zahiri kuwa ta'be bakinshi yayi ya lumshe idonshi ya bude a hankali tare da d'aga k'afarshi zuwa inda take tsaye , zaro manyan idonta tayi ciki hade fuska da fushi tace " kai waye , akanmi zaka shigomin office bada izinina ba , oya maza ka ficemun anan tayi maganar a tsiwace tana nuna mashi hanya da hannunta, Murmushi yayi cikin ranshi afili kuwa wani banzan kallo ya wurga mata sannan yaci gaba da tafiya saida yazo daidai inda take tsaye kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya juya ya janyo kujerar da marar lafiya Ke zama ya zauna yana fuskantar babban teburin da Ke office din , Hararar bayanshi laurat tayi kamun tayi k'wafa ta zagayo ta gabanshi ta zauna akan kujerarta suna fuskantar juna, sun jima a haka kowannensu yakasa yiwa danuwanshi magana , ganin sun kwashi mintina bashida niyar magana ne yasa ta d'ago a hasale tace "wai malam lafiya kuwa ko bashinka naci da zakazo har office dina kayimun zaune batare da izini ba kuma kaja kayi shiru kana k'arewa mutane kallo tayi maganar tana yamutsa fuska , don harga Allah tagaji da kallon da yake mata tanajin yadda idanunshi Ke yawo ajikinta , ba tare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace " awace unguwa kike ?kallonshi tayi da mamaki jin yadda yayi mata tambayar a kausashe kuma ya fuske kamar bashi yayi maganar ba , ganin kamar yazo da rainin hankaline yasa ta janyo laptop dinta tafara wasu yan Danne danne aciki, Ganin hakan yasa shikuma ya kai hannu ya dauki wayarta dake ajiye a wajan , cikin sa'a kuwa ba Lock numbarshi ya sanya ya kira sannan ya ajiye mata wayarta ya tashi cikin tafiyarshi ta cikakken namiji yabar office din nata , batare dayayi abunda ya kawo shi ba, da wani irin kallon mamaki ta bishi kamun tayi k'wafa tana hararan inda yabi ya wuce, Hisham kam k'iris ya rage ya saki layi don ganinta a wannan shigar ba karamun hautsina mashi man kai yayi ba , karfin hali kawai yayi bainuna ba don gudun raini mamakinshi shine ai bayau yafara ganin mata kala kala da shigar da take nuna tsiraici ba amma bai tabajin irin wannan ba sai a kanta to mi hakan Ke nufi kenan , kuma da yaje ya dauki number ta mi zaiyi da ita ne mrtsss yayi tsaki yana maijin haushin kanshi , karfa yarinyar ta dauka wani abune ta nemi rainashi a banza a haka ya karaso inda yabar su sajan sale , nan yabashi umurnin yaje ya nemawa tsohuwar sallama in ba wata matsala , "okay sir " yace ya juya ya tafi shikuma yashiga mota yana jiranshi, ____________________________ Kallo daya zakayi masu kasan suna cikin matuk'ar tashin hankali , kowa ka kalla zaka hango tsantsar tashin hankali da wani irin fushi akan fuskokinsu , a hankali dattijon yafara basu hakuri yana cewa " kuyi hakuri wannan itace kaddararmu wadda bazamu iya kauce mata ba , hakika an cucemu anyi mana tabon da har mu mutu bazamu iya mantawa dashi ba , ina rokonku da kuyi hakuri don inku kuna wannan koke koken to ita kuma *Safiya* fa ya kukeso tayi doli sai mun kawar da tamu damuwar don ganin tasamu kwanciyar hankali ,yanzu likita yana nemanmu bari muje muji mi ake ciki, " Har yagama maganarshi ba Wanda yace k'ala saidai masu kukan sun yi shiru sai ajiyar zuciya sukeyi , hannun k'aninshi Dattijon Yakama suka nufi office din likitan, Da sallama suka shiga bayan sun gaisane yabasu izinin zama , zama sukayi suna fuskantarshi saida yagama wasu rubuce rubuce sannan ya cire farin glass dinshi ya dubesu cike da tausayawa yace , "to alhamdulillah Baba mun samu mun shawo kan matsalar don gaskiya da farko har naji tsoro don k'iris yarage yarinyar ta kamu da ciyon *yoyon fitsari* to Allah ya tak'aita mun shawo kan matsalar , sai dai duk farkawan da zatayi a firgice take farkawa tana sambatu shiyasa mukeyi mata alluran bacci , a gaskiya an lalata rayuwar yarinyar nan anzalunceta sosai don bincikenmu ya nuna ba mutum daya bane yayi mata fyade akalla zasukai mutum ukku ko hudu , Da sauri Dattijon ya runtse idanunshi yanajin zuciyarshi kamar zata buga saboda wani irin nauyi da zafi da takeyi mashi , wasu hawaye masu zafi suga gangaro mashi , shima dayan dattinjon hannu yasa ya goge kwallar data cika mashi ido ,Wanda halin da suke ciki yasa sunma kasayin magana sai ajiyar zuciya, Cikin tausayawa likitan yaci gaba da cewa abunda yasa nayi kiranku shine saboda inbaku wata shawara na tabbatar duk wad'an da sukayi wannan aikin to ba kananan mutane bane doli akwai abunda suka taka ,duba da bayanin da muka samu na irin motar da suka dauketa aciki ,don haka nake ganin mi zai hana Ku damk'a wannan case din a hannun mataimakin commissioner *Hisham Abudrahman* inaga shikadai ne zai iya tsaya maku akan wannan case din har a kwatowa yarinyar nan hakkinta inba hakaba wahala kawai zakusha arink'ayi maku yawo da hankali , ina da tabbacin insha Allah zaku samu adalci a wajansa, Cikin murya mai tsananin rauni da karaya dattijon Wanda ya kasance mahaifin yarinyar yace " kayya d'an nan bana tunanin zamu samu wani adalci anan tunda har yanzu bamusan ma waya aikata mata wannan aikin ba , cuta ce dai anriga a cucemu saidai Allah zai sakamana , " "Aa Baba Ku daure Ku nemawa yarinyar nan hakkinta an cuceta sosai Wanda yakamata ace an hukunta koma waye ,saboda barin irinsu a doran k'asa bala'i ne bai kamata a zuba masu ido ba suna yadda sukaga dama ba , karka damu da rashin sanin su waye , shi zai ganosu duk inda suke a garin nan yasan aikinshj fiye da tunaninka sannan yana aikishi ne bisa gaskiya da amana uwa uba *Kishin k'asa* Wanda ba kowa keda wannan ba kai dai kuje Ku kai report a hannunshi kuma karku kuskura Ku sanar da wani daga cikin police din dake hukumarsu har sai kun Ganshi da kanku sannnan Ku sanar dashi inba haka ba komai zai iya faruwa don mafi yawansu masu kudi suke yiwa aiki karshenta in baka iya kama barawo ba shi yakamaka , " Gyaran murya d'ayan mutumin yayi Wanda k'ani ne ga mahaifin safiya , yace , mun gode sosai likita tabbas zamuyi amfani da shawararka don inhar ba 'a kamo azzaluman nan ba aka hukuntasu to bazamu ta'ba jin dadi ba doli su fuskanci hukunci daidai da abunda suka aikata ,ni dama banida niyar k'yalewa wallahi sai inda k'arfina ya k'are , nan dai likitan yaci gaba da yi masu bayanin yadda zasu tunkari Hisham da kwatancen inda zasu sameshi cikin sauki , ___________________________ "Ke wai mi yake damunki ne yarinya kamar mai aljanu , inace da kanki kika dameni akan ba Wanda kikeso sai Hisham ,d'azu ma kamar zaki take kan jariri saboda zumudin zuwansa , shine yanzu zaki wani ce ba kya sonsa , shin shi baice bayasonki ba sai kece zakice bakya sonshi ,to ubanwa kikeso ,wallahi ki dawo hankalinki tun kamun damarki ta kufce maki , don bana tunanin zaki samu mijin da ya kama ko kafar Hisham ne , sha sha sha kawai wadda batada nutsuwa to aure anyi angama bkisani tun da shi yanasonki kuma uwarshi ma tana son..........kuka mai k'arfi Samra ta fashe dashi tana cewa nashiga ukku don Allah momi karku auramun shi wallahi kasheni zaiyi........................✍🏻 *Kuyi hakurin rashin jina kwana biyu yarana suka kwanta asibiti amma alhamdulillah sunji sauki har anbasu sallama saikuma muka shiga bikin yayana shiyasa kukaji shiru* *AKWAI INGANTATTUN KUMA ZAFAFAN KAYAN MATA NA YAR MUTAN SOKOTO BA ABUNDA BAMUDASHI NA GYARAN AURE KEDAI GARZAYO KAR AYI BABUKE AJIYATA , MASU BUKATAR SIRRIKAN MALLAKA MUSAMMAN MASU MAZA MASU MURDADDEN HALI KU GARZAYO ZAKUSHA MAMAKIN YADDA ZAKU DAWO KUNA JUYA ZUCIYAR MIJINKU MATAN DA SUKE CEWA VASA SAMUN ALKHAIRIN MAZAJENSU KU GARZAYO πŸ’ƒπŸ» *Gareku yan Niger duk maison kayan yar Niger ta yi magana muna aikawa ta hanya mai sauki adukkan garuruwan dake Niger don Neman Karin bayani 07069711327 mmn Yusuf Dr mata* [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* πŸ…ΏοΈ_29 .......…..............."Helloo " tasake cewa jin shirun yayi yawa ne yasa ta yin tsaki tana niyar kashe wayar a hankali cikin jarumar muryarshi yace " karki kashemun waya, " cikin mamakin Mai maganar ta d'ago wayar tasake kallon number tabbas batasan number ba Amma Kuma kamar taso ta gane Mai muryar , maida wayar tayi a kunnenta cikin hasala gundura Mai nuni da an takura mata tace " waye Kai ne miye dalilinka na kirana ?" Lumshe idanunshi yayi Don lokaci daya muryarta ta hargitsa mashi lissafi , cikin wata kasalalliyar murya yace wanne kikeson kisani acikin biyun , waye ni ko kuma dalilin kiranki ,? A hasale tace "duka biyu nakeson sani" Murmushi yayi Mai sanyi yace "to mijinki ne uban 'ya'yanki , dalilin kiranki Kuma ni kaina bansani ba Amma kiyi tunani Kila Zaki gano Mana dalilin Kiran, " tsaki laurat tayi cikin jin haushi ta katse Kiran , tana kananun maganganu kamun taci gaba da tunanin da takeyi , ba'ajima ba taji shigowar sak'o a wayarta , tana dubawa taga number d'azu ce kamar bazata duba ba saikuma ta bude sak'on , gani tayi anrubuta *_ba'ayimun tsaki ki kiyaye wannan sannan kishirya tarban mijinki gobe zan iya zuwa kowane lokaci_* tsakin tasake tare da yin cilli da wayar tana fadin aikin banza kawai, nan ta tashi ta nufi falo jin yadda Ammi ke kwala mata kira, 'bangaren Hisham kuwa cike da farincikin jin muryarta yayi bacci Mai cike da mafarkanta gefe daya Kuma cike da tunanin yadda zaikama tantiran nan cikin sauki da hukuntasu daidai da laifinsu _____________________________ Washe gari Tun safe laurat ta shirya ta nufi asibiti ko gaisawa da iyayenta Bata tsaya yi ba gudun haduwarta da Abbansu haka ta tafi ko karyawa batayiba ,Zee sai dariya take mata da tsokanarta , Bata tsaya biye mata ba tayi tafiyarta , lokacin da iyayensu suka sauko don yin breakfast Zee kawai suka iske a falon , har k'asa ta duka ta gaishe da iyayen nata cikin fara'a suke amsamata kamun Mami tace Ina laurat ne ko Bata tashiba ,"aa mami ta tashi harma ta wuce hospital, "Har ta fita fa kikace , shine bazata tsaya mu gaisa ba kamun ta tafi," "Taya zata tsaya bayan Kuma mune take yiwa gudun ai zata dawo ta sameni ne, cewar Abba, " Zee cikin danne dariyarta tace "aa Abba Kiran gaggawa akayi mata ne shiyasa , " jinjina kanshi kawai yayi tareda cewa "Allah ya dawo da ita lafiya, zee da Mami suka amsa da Amin, ____________________________ Zaune yake a office dinshi aiki yakeyi sosai yau tun safe Bai huta ba har gashi karfe 4:pm wayarshi ya dauka ya dannawa wata lamba Kira , ba'a jimaba aka dauka tareda cewa "Barka da rana sir ,"ba tare da.ya tsaya amsa gaisuwarta ba yace "Asmey ya akayi fatan komai na tafiya yadda muka tsara, "cikin ladabi irin na oga da yaronshj ta amsa da cewa " eh sir komai na tafiya daidai yanzu haka suna gidan gonar Mataimakin gwamna Alhaji saminu, "ok aikinki na kyau kici gaba da bin diddiginsu zuwa 5pm zamuzo " cikin Sara mashi kamar Yana ganinta tace okay sir , kashe wayar yayi yafara Kiran number Jafar, K'arfe biyar a wajen gidan gonar Daddyn zayyan tayi masu , nan suka Danna kansu cikin gidan kansu tsaye , da sauri Mai gadi ya taso Yana tambayarsu mi sukeso wa.suke nema, batareda Hisham yayi magana magana ba ya zagayeshi ya nufi ainahin k'ofar gidan gadan gadan, da sauri maigadin ya yunk'ura zaisha gabanshi Amma mi saiji yayi an rik'e shi ta baya , juyowa yayi zaiyi magana inspector Jafar ya tareshi da cewa *kana tare da Mataimakin commissioner yan sanda* don haka kashiga hankalinka, wani yawu Mai kauri maigadin ya had'iye take jikinshi yafara rawa don mutum ne Mai bala'in tsoron yan sanda , batare da sunbi ta kanshiba suka marawa Hisham baya , Zaune suke a babban falon gidan sun baje kayan shaye shaye kala kala akan table Zayyan ne sai abokanshi su biyu sai budurwarshi sury ,sauran abokan shakiyancin nashi basa nan , ba zato sukaga an turo k'ofar falon da k'arfi , a fusace Zayyan ya d'ago kanshi a tunaninshi wani daga cikin ma'aikatan gidan ne ya shigo masu, Saidai ganin *Jami'an 'yan sanda* yasa shi maida maganar da yayi niyar yi sai wani mugun kallo da yake auna masu na mi kukazo yi don Sam ba alamar razana a fuskarshi , hakama abokanshi kasancewarsu 'ya'yan manya sun San ba abunda 'yan sanda suka isa suyi masu ,saidai sury ta razana sosai don ita Sam babu sanin iyayenta aduk iskacin da takeyi Kuma tana mugun tsoron Daddynta don mutum ne Mai zafi sosai , Kallon kallon sukeyi tsakaninsu da su Hisham Wanda tuni zuciyarshi ta kawo mashi iya wuya ganin Dan iskan kallon da suke jifansu dashi Sam ba alamar razana a fuskokinsu, da hannu kawai yayiwa sauran alama da su kamasu , don in yaci gaba da tsayuwa haka agabansu komai zai iya faruwa tsabar tsanarsu da yakeji, Da sauri yan sandan suka nufesu da nufin kamasu , ko motsi basuyiba sun zubama yan sandan nan ido cike da izgili , sai sury ce tayi yunk'urin guduwa ,Hisham har ya d'aga k'afarshi da niyar barin d'akin , kamar daga sama yaji muryar Zayyan cikin izgilanci da nuna isa da tak'amar shi wani ne yace " Kai d'an gidan uban waye da zakazo har nan ka kama Dan gidan SAMINU SULAIMAN , cak Hisham ya tsaya zuciyarshi kamar zata fad'o k'asa runtse idonshi yayi da k'arfi jin yadda Zayyan ya ambaci mahaifinshi ai kamun kyaftawar ido Wanda duk Wanda yake wajan bazaice ga lokacin da Hisham ya k'araso gaban Zayyan ba kamun ma zayyan yayi wani yunk'uri tuni Hisham ya zabga mashi wani mashahurin Mari Wanda saida gaba daya wajan ya amsa , lokaci d'aya ji da ganin Zayyan sukayi k'aura daga jikinshi luuuu yatafi zai fad'i cikin zafin nama Hisham yakoma taroshi ya watsa mashi wani Marin a dayan gefen fuskarshi nan take ya furzo jini daga bakinshi saikuma yakata tarin wahala yanayi jini na zubar mashi ta hanci ta Baki, a firgice sauran abokan nashi suka matsa wajan yan sandan nan suna Mika masu hannu alamar su kamasu.jikinsu Banda rawar mazari ba abunda yakeyi , sury kuwa tuni ta saki fitsarin tsoro da firgita sai faman kuka takeyi jikinta na rawa tsoro biyu ya shigeta Daddynta da Kuma wannan Dan sandan da take ganin da alama bashida Imani kwata kwata, Zayyan kuwa lokaci d'aya fuskarshi ta haye tayi sumtum gaba daya kamanninshi sun canza cikin yan seconni , zubewa yayi a wajan Yana maida numfashi don yamakasa yin ihun saboda azabar da fuskarshi da bakinshi ke yi mashi ,d'aga k'afa Hisham yayi zai nausheshi a ciki cikin sauri ASP Jafar ya janye Zayyan Yana cewa " aa oga kayi hakuri Don Allah in kaci gaba da dukanshi zai iya mutuwa wallahi, wani mugun kallo Hisham yayi mashi na zamu had'u kamun ya juya yabar falon gaba daya , mutum biyu ne suka rik'o Zayyan don lokaci d'aya yafita hayycinshi sai layi yakeyi Sam yakasa tsayuwa da k'afafunshi Kuma har lokacin jini nayi mashi zuba ta hanci ta Baki, abokanshi kuwa suna gaba 'yan sandan na biye dasu abaya har inda sukayi parking motocinsu , nan suka dannasu aciki suma suka shiga sukaja sukabar gidan gonar suka nufi station dinsu, Mai gadi na ganin tafiyarau shida wasu sauran ma'aikatan ai take ya fito daga ma'boyarshi wayarshi ya fito da ita yafara Kiran Daddyn Zayyan, saida yayi Kira biyar ba'a d'auka ba sai Ana shida ne aka dauka , PA dinshi ne ya amsa wayar da cewa Hello , cikin rawar jiki data murya Mai gadin yafara magana Yana cewa " oga ka gayawa Mai gida wasu 'yan sanda sunzo har nan gidan gonarshi sun tafi da Zayyan da abokanshi bayan uban dukan da sukayi mashi sunyi mashi jina jina wallahi sai Allah idan zai ray......... Batare da yak'arasa jin sauran maganar tashi ba ya katse Kiran da sauri ya nufi wani d'aki Yana k'wank'awasawa ,afusace akace waye ne , cikin kwantar da murya PA yace "oga akwai matsala ne yanzu aka Kira daga can gidan gonarka akan wai wasu yan sanda sun je har can gidan gonar sun kama maigida Zayyan da abokanshi wai harda dukanshi sukayi, a zabure Daddyn Zayyan ya ture karuwarshi dake kwance dare dare bisa jikinshi suna lalabe lalaben juna ,tare da fadin "what wane Mai tsautayin ne Kuma ya shiga gonata a yau , Ashe dama akwai wani Dan sanda Mai k'warin gwuiwar da har zai iya sa hannunahi ya daki Zayyan Kuma yakamashi , nan take idanunshi suka riked'e sukayi jajir tsabar 'bacin rai don Allah yagani ko kuda bayason ya ta'ba jikin zayan da sunan cutarwa , don shi da abu yasamu Zayyan gara shi ya sameshi shiyasa baya ragawa duk wani shege da zai nemi shiga rayuwar tilon d'anshi , cikin kissa da kisisina karuwar ta matsoshi tana cewa "sweet darling mi yake fatuwa ne tayi maganar tana laluban bakinshi wani mugun Mari ya yarfa mata cikin karaji yace "ke bakida hankali ne ko bakiji abunda akayiwa d'ana ba to maza ficemun yayi maganar Yana nuna mata k'ofar "oya maza 'bacemun da gani kamun na canza maki kamanni, cikin matukar gigita da tsoro ta kwashi kayanta ta Sanya tafita daga d'akin jaka da takalmi a hannu ,tsaki yayi kamun ya mik'e ya dauki kayanshi ya Sanya, wayarshi ya dauka yafara Kiran manyan ma'aikatan *yan sanda* don yaci alwashi bazai taba ragawa duk wanda yayi gigin shiga gonar d'anshi ba , wajan mutum ukku yayi waya dasu kamun ya tashi ya fito daga d'akin direct wajan motocinshi ya nufa inda.yaranshi da securitynshi suma suka shishshiga motocinsu direc yabasu.umurnin su dauki hanyar Lagos , aguje suka bar haraban gidan shak'atawarshi dake garin Abuja suka halba titi Gudu sukeyi sosai kamar zasu tashi sama don suna matukar tsoron fushin ogan nasu don sun sani bashida Imani ko kadan, ___________________________ Tunda su Hisham sukaje station suka watsa su Zayyan a cell aka k'argamesu kowa yakoma office dinshi , zaman Hisham da kamar minti ashirin sai gashi ya samu Kiran gaggawa daga shugaban hukumarsu Wanda shine shugaba gaba d'aya , bai kawo komai ba ya tashi ya nufi office dinshi , har wannan lokacin babu fara'a a fuskarshi don sosai yakejin kamar yaje ya shek'e yan iskan yarancan da iyayensu ke daure masu gindi suna abunda suka ga dama, Da sallama ya shiga office din ogan nashi ,k'amewa yayi tare da sarama ogan , kamun yace sir gani ance kana kirana, Waje ogan ya nuna mashi da hannu alamar ya zauna, zama yayi batareda yace komai ba don ya fahimci ogan nashi kamar Yana cikin damuwa , "Am Hisham wad'anne Yara ne kuka kama yau da yamma Kuma suna Ina, "? Jin wannan maganar yasa Hisham game nan da can cikin tsuke fuska don karma oga yaga damarshi yace "wasu tantiraine da aka kama da laifin yin fyade Wanda yanzu haka yarinyar batasan Wanda yake kanta ba ko ta rayu ko ta mutu , yanzu haka suna cell Kuma insha Allah agobe goben nan zamu makasu kotu don su fuskanci hukunci daidai da abunda suka aikata, , Murmushi ogan yayi ganin yadda Hisham kecin magani Yana magana cike da tabbatarwa azuciyar shi kuwa cewa yake saidai kayi hakuri Hisham a wannan karon doli zan taka maka birki don gudun fadawarka wata musiba , Shima ogan hade fuska yayi Don ya fahimci Hisham zuma ne saida wuta , yace " Hisham inason nan da minti talatin ka saki yaran nan wannan umurni ne Kuma ba daga gareni ba Nima daga sama na ne , " A razane Hisham ya d'ago kanshi ya zuba mashi manyan idanunshi da suke dama a rine saboda 'bacin rai ,cikin wata kakkausar murya kamar Wanda yake magana da yaronshi ba oganshi ba yace " akan wane dalili oga ? Ka ko ji abunda na gayama yaran nan sun aikata ,? Sunje sun sace yarinya su biyar suka hadu suka keta mutuncinta sannan ace munkasa daukar mataki ,wane hali kakeson yarinyar da iyayenta su shiga ne , wai har sai yaushe ne masu kudi da manyan masu mulki zasu daina juya 'hukumar jami'ai a Nigeria ne , har sai yaushe Jami'ianmu zasu farga sufara kishin kansu ne , muna da duk wata dama da zamu iya hukunta koma waye Amma miyasa zamu zubar da damarmu mu tsaya wadansu 'bata gari suna juyamu yadda ransu keso mu Kuma saboda matacciyar zuciya da son abin duniya mu tsaya suna takamu yadda sukaga dama suna juyamu kamar waina a tanda ,basa shayin aikata kowane irin laifi saboda suna ganin sun fi karfin hukuma , 'ya'yansu sune 'ya'ya , da an ta'basu zakaji kowa na magana Amma duk abunda zai samu 'ya'yan talakawa ba Wanda zai damu dashi ,sunsa mutane nayi Mana kud'in goro suna zaginmu akan rashin adalcin da mukeyi masu duk wani Mai burin ganin ya tsaya akan gaskiya to ko ta halin Yaya sai anga bayanshi wasu da yawa saboda tsoron rasa aikinsu sun kasa tsayawa suyi aiki da gaskiya kamar yadda sukayi alk'awari wannan wace irin rayuwace shiyasa har yanzu munkasa samun ci gaba a kasarmu ta kowane fanni saboda azzaluman cikinta basu taba Bari muryar masu gaskiya yayi amo har ya amsa kuwar da kowa zaijita , to Ni bazan sakesu ba doli sai nabiwa yarinyar nan hakkinta komai zai faru ya faru, ya k'arashe maganar da huci Mai zafi Wanda yake nuna alamar yakai kololuwar fusata, Jinjina Kai ogan yayi tabbas yasan duk abunda Hisham ya fad'a gaskiya ne Kuma shima zaiso a hukunta yaran don laifinsu babba ne ,to Amma inda gizo ke sak'ar shi kanshi ba laifinshi bane daga samanshi ne umurni aka bashi wanda rashin bin umurnin kan iya jefasu a wani yanayi ciki kuwa harda rasa aikinsu , a bayan fage kuwa shi kanshi Yana tsoron hatsabibancin Alhaji Saminu tabbas isarshi da ikonshi ba akan Yana Mataimakin gwanna bane kad'ai aa akwai wasu matakai da ya taka Wanda yasa yake tare da manya sosai hatsabibine na karshe sannan bashida Imani ko kadan shi kuwa bazaiso tarihi ya maimaita kanshi ba ,bazaiso Hisham ya fuskance kalubale kamar yadda mahaifinshi ya fuskanta ba, dukda ya yarda da jarumtar yaron da kaifin basirarshi Amma hakan bashi zaisa yabashi damar jayayya da irinsu Saminu sulaiman ba, gyaran murya ogan yayi yace "Ka fahimceni Hisham Kai kanka kasan bana d'aya daga cikin irin wadan nan azzaluman shugabannin Amma ba isa in Hana Wanda suke sama Dani aikata abunda sukeso ba Wannan umurni ne aka bani Kuma kaima Ina baka umurnin kaje ka sakesu , kayi hakuri inkare na yawo zomo na yawo watarana za'a had'u ne , sannan Ina jiye maka hatsabibancin Alhaji Saminu sulaiman bakasan waye shi ba wallahi ya wuce duk inda kake tunani, sannan zai iya aikata komai akan wannan yaron nashi , in nace komai to Ina nufin komai don haka kaje ka aikata abunda na saka, Gaba daya zufa ce ke tarfatsomashi jikinshi har rawa yakeyi akan 'bacin rai , tunani yakeyj yanzu ya zaiyi da iyayen yarinyar mi zai ce masu wani kallo zasuyi mashi wani kallo zasuci gaba da yiwa hukumarsu ne , yanzu shikenan wadan nan yaran sunci bulus kenan inaaaaaaa wallahi bazai yuwubaaaaaa da k'arfi ya bugi tabale din kamun ya mik'e ya fita afusace ko Yar sarawar da akema ogan baiyi ba kamar yadda Bai jira izininshi ba yayi tafiyarshi, Yana fita inda suka ajiye su Zayyan ya nufa , kamar Allah ya aikoshi haka ya hausu da duka da belt dinshi aikuwa tuni suka fara zunduma ihun neman dauki kamun kace mi ya hada masu jini da majina da sauri sauran yan sandan suna rirrikeshi sanin halinshi in ranshi ya 'baci zai iya aikata komai da kyar suka samu suka fitar dashi waje suka sanyashi a motarshi ,da sauri Jafar ya shiga gidan gaba yaja motar da sauri sukabar station din, lokacin k'arfe 7pm , adai dai lokacin ne ogansu ya iso cell din nan yabada umurnin a bud'esu , ganin halin da suke ciki ne yasa yabada motarshi akan akaisu har gida don Alhaji Saminu sulaiman ya tabbatar masu da karsu kuskura ya sanyo k'afarshi acikin garin na Lagos ba tareda an sako mashi d'anshi da abokanshi ba, haka nan 'yan sandan nan sunaji suna gani suka kashe su suka Sanya a mota suka nufi gidan Mataimakin gwanna masu kishin kansu da k'asarsu na bak'inciki da abun yayinda 'bata garin cikinsu ke jin Dadi da farincikin yau dai anyi nasara akan Hisham saboda sunajin haushin yadda ya hanasu rawar gaban hantsi, _____________________________ Momma na zaune a falo ta idar da sallar magariba kenan tana lazimi taji shigowar mota gidan , tana nan zaune tana jiran taga shigowar Hisham sai taga shiru shiru Bai shigo ba , sai can tafarajin Ana kwad'a sallama abakin k'ofar shigowar falon, haka kawai taji wani irin faduwar gaba Wanda saida ta danne saitin zuciyarta da hannunta kamun a sanyaye ta amsa sallamar tare da bada izinin shigowa , ahankali ya shigo falon har k'asa ya durkusa ya gaisheta a hankali ta amsa gaisuwarshi tana cewa "lafiya dai Jafar ,?Ina Hisham din,? " "Lafiya qalau Momma oga Yana mota an 'bata mashi rai ne a station shiyasa Yana cikin fushi sosai nayi nayi ya fito daga motar ma Amma yaki shine nace bari na gayamaki ," Cikin sauke ajiyar zuciya momma tace to alhamdulillah bari naje nayi mashi magana nagode kaji Allah yayi maka albarka , ai ka kyautamun da kadawo dashi gida Ni bansan inda shalele yasamo wannan bak'ar zuciyar ba wallahi a da dai Sam ba haka yake ba,tayj maganar lokacin da take ficewa daga falon zuwa inda Jafar ya paka motar , Yadda Jafar yabarshi haka suka sameshi ya jingina da kukerar motar idonshi a lumshe hannayenshi yayi baya dasu ya tallabe kanshi ,farar fuskarshi ta koma jajir , kallo daya Momma tayi mashi tasan cewa ba k'aramin fushi yake ciki ba tabbas ankai mak'urarshi ne , batare da tayi magana ba ta sa hannunta ta janyo hannunshi dake bayan kanshi , babu musu ya bude idanunshi tareda fitowa daga motar yabi bayanta inda take rik'e da hannunshi kamar wani karamin yaro , haka suka rinka tafiya har suka shige falon ,Jafar dake binsu da kallo ya girgiza kanshi tareda shiga motar yabar gidan shima, _____________________________ K'arfe 9pm daidai sukayi parking din motocinsu a harabar gidan , har wannan lokacin afusace Alhaji Saminu sulaiman yake , duk da kuwa yasamu labarin tun 7 Zayyan Yana gidanshi da abokanshi harma ankira likitansu yabashi taimakom gaggawa don lokacin da aka kawoshi ko numfashi da kyar yakeyi don ya daku sosai a wajan Hisham , Buzun buzun haka ya wuce ya nufi hanyar da zata sadashi da babban falon gidan , Ba tare da wata sallama.ba ya afka falon Yana huci , Momy ce zaune da Amna momy zaune take ta zuba tagumi cike da alhinin abunda yasamu Zayyan dakuma fargaban irin tijarar da Daddyn shi zaiyi akan hakan , Amna kuwa wayarta kawai take dannawa Sam ba alamar wata damuwa a fuskarta don ita a ganinta wannan shi ya shafa ba itaba batada case da shi, Ba tare da ya ko kalli inda suke ba yabi hanyar da zata sadashi da part din Zayyan don yasan Yana can, Kwance ya sameshi Yana bacci gaba daya fuskarshi ta haye ta kumbura sosai sai wasu wurare ajikinshi duk sun farfashe alamar duka , cikin tsananin bakin ciki da takaici hade da rashin Imani da tausayi yafara magana idonshi a juye kamar wani dodo " wallahi na rantse da sarkin dake busa numfashi duk wanda yayi maka wannan gangancin sai ya gwammacewa mutuwarshi da rayuwarshi ....................... *Littafina yakoma na kudi saidai ba yanzu ba sai mungama book 1 don na gaji da Dan kwairo kullum cikin baran comment to zai koma na kudi ehe*πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„ *Amma wadanda sukemun comment sukam zasu samu a kyauta insha Allah* [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* πŸ…ΏοΈ_30 ..........."innalillahi wa inna ilaihin rajiun, wai Hisham mi yake damunka ne ? Kayi magana mana tun d'azu Ina maka magana Amma ka kasa cewa komai," juyo kanshi yayi ya d'aura akan kafafunta Yana sakin ajiyar zuciya Mai k'arfi, shikad'ai yasan irin zafin da yakeji a zuciyarshi musamman in ya tuno fuskar safiya da Babanta , yanzu wane irin kallo zasuyi mashi tabbas zasuyi zargin an saye shi ne da sa hannunshi, cikin huci da tsananin takaicin da yake ciki yafara magana Yana cewa " har yaushe sai yaushe k'asarmu zata gyaru sai yaushe za'a daina kashin dankali a k'asar nan , kullum manya su suke danne na k'asa dasu, zalunci yayi yawa sosai a k'asarmu Kuma ba Wanda zai iya daukar wani mataki kullum tsoro da zullumi da mutuwar zuciya su suke k'ara jefamu a halin da muke ciki ,kowa Yana tsoron yayi magana wani abu ya sameshi to shikenan mu a haka zamuyi ta rayuwa kenan talaka bashida wani 'yanci na kansa duk sharar da aka kwasa a zuba mashi , 'a'a bazai yiwu ba bazan zuba ido suci bulus ba doli sai na k'watowa yarinyar nan hak'inta kota halin Yaya wannan alk'awari"............"dakata Hisham" Momma ta katseci cikin sauri don tunda yafara magana jikinta ke rawa duk da Bata fahimci abunda yake magana akai ba , Amma ta fuskanci inda yasa gaba ,cikin rawar harshe tace "Hisham ka nutsu ka gayamun abunda ke faruwa ko na baka shawarar da ta dace inason ka rink'a sarrafa fushinka kar watarana ka aikata aikin Dana sani Wanda bana fata ,Amma wannan fushin naka yayi yawa in Abu ya dameka karinka maimaita innalillahi wa inna ilaihin rajiun zakaji sauki a zuciyarka kaji" Daga kanshi yayi alamar amsawa kamar k'aramin yaro , cikin hikima da dabara momma ta samu ya gaya mata abunda yake faruwa , ai kamun ma ya k'arasa tuni momma tafara zubar da hawaye jikinta har rawa yakeyi cikin wata irin murya Mai cike da tashin hankali da bayyanar da zallan tsoron da take.ciki tafara cewa " Hisham ka duba girman Allah ka janye wannan case din , don Allah ka fidda hannuka daga ciki, banason. Kana shiga irin wad'an nan case din Hisham sunfi k'arfinka ,bazaka iya komai akai ba kabarsu duk Wanda yayi na gari kansa , Amma don Allah karka je ka janyomin abunda bazan iya dauka ba kasani Kai kad'ai gareni Kai nake kallo naji sanyi ba uwa ba uba ba miji ba marik'ana ba wa ba k'ani ka tausayamun bazan iya jurar wani abu ya sameka ba tunda kasani ba Imani ne da mutanen nan ba, ba abunda bazasu iya aikatawa ba indai akan take gaskiya ne Kai shaida ne akan mahaifinka ,a irin hakane aka kashe shi idan suka cutar dakai a wannan karon bazan iya jurewa ba don Allah Hisham ,ta k'arasa maganar tana had'a hannayenta da nashi cikin kuka, Tuni zuciyarshi tak'ara hasala ga kukan mahaifiyarshi da yakejin kamar Ana zuba mashi darma a azuciya cikin sanyi da raunin da zuciyarshi tayi akan mahaifiyar tashi yace " Momma ya zanyi ? Zaluntarsu fa akayi Kuma zalunci Mai matukar girma yanzu shikenan a haka zasu zauna cikin bak'in cikin zaluncin Da akayi masu ..............katseshi tayi da cewa Hisham na k'are magana inason ka janye hannunka a wannan case din , insha Allah Allah zai bi masu hakkinsu Allah ba azzalumin bawansa bane saidai bawa ya zalunci kanshi , da sannu Allah zaiyi Mana maganinsu da sannu zasu girbi abunda suka shuka da hannunsu, " Batare da ya sake cewa komai ba ya mik'e ya nufi d'akinshi zuciyarshi kamar wuta yanajin in Bai hukunta wadan nan shegun yaran ba bazai taba samun nutsuwa ba Amma doli zai zare hannunshi akan case din saboda Momma , shi ya sani basu isa suyi mashi komai ba saidai zai barsu ne saboda kwanciyar hankalin mahaifiyarshi, alwala yayi ya gabatar da sallar magrib da Isha alk'ur'ani ya dauko yafara karantawa a fili cikin zazzak'ar muryarshi yajima sosai Yana karatun kamun ya rufe littafin ya ajiyeshi inda yake ,yakoma bisa gadonshi ya kwanta , sai a lokacin yaji zuciyarshi tayi mashi sanyi sosai lumshe idonshi yayi da son yayi bacci ko zaiji saukin ciyon da kanshi keyi mashi , a hankali kyakyawar fuskarta tafara yi mashi gizo kamar dai jiya babu shiri ya bud'e idanunshi tare da dafe kanshi hannunshi Yana mamakin yadda ya manta da zancan zuwa wajan yarinyar nan, da sauri ya dauko wayarshi ya lalubo number ta wadda yayi serving da *Likita* bugu biyu ta dauka cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa tace "assalamu alaikum " Saida ya lumshe idonshi ya bud'e kamun ya amsa mata sallamar tata cikin Jan aji, take ta had'e fuskarta don ta shaida muryarshi shine ya kirata jiya Yana mata rainin wayo, Cikin wata irin murya da shi kanshi baisan yanada itaba yace " Matar kinga yau Baki ganni ba ko nasan kinyi ta jirana wallahi Sam na manta ne Amma insha Allah gobe Zaki ganni kiyi bacci lafiya "ya k'arashe maganar da hura mata wani sanyayyen kiss Wanda taji iskanshi har a kunnenta Wanda take tsikar jikinta ta shi da sauri ta cire wayar a kunnenta kamun tayi wani yunk'uri ma har ya kashe wayar tashi, tajima tana kallon wayar cike da wani irin yanayi Amma takasayin tunanin komai sai can Kuma tayi tsaki tana mamakin rainin hankalinshi , wai ya manta Kuma a hakan wai sonta yakeyi tsaki tayi tana jifa da wayar tare da k'ara gyara kwanciyarta , Hisham kamnan take bacci yayi awon gaba dashi cike da annashuwa Kai kace bashine.yake cikin matsanancin fushi ba a d'azun' ___________________________ WASHE GARI Sosai ake bawa zayyan kulawa wanda alhamdulillah ya fara jin sauk'i ,kumburin fuskar ma yafara sacewa , Momy sosai take kula dashi Amma Amna ko sau d'aya bataje ta gaidashi ba saima haushin yadda duk Daddyn da momy suka damu akanshi takeji, Yanzu ma Daddyn ne zaune agefen makeken gadon da Zayyan yake kwance Yana shafa kanshi a hankali tare da k'ara kwantar mashi da hankali akan zai daukar mashi fansa akan duk wani Wanda yake da hannu da ta'ba lafiyarshi , Yana jirane yasamu sauki ta yadda zaiga yadda zaiyi da wannan banzan Mataimakin commissioner din, ____________________________ Tunda yazo office yau yakasa ta'buka komai har na tsawon awa biyu , gajiya yayi da zaman kamun ya tashi yabar office din , direct asibiti ya nufa inda aka kwantar da Safiya ,da sallama ya shiga d'akin , mamanta ce zaune kusa da ita tana rik'e da hannunta sai fisge fisge takeyi tanason cire k'arin ruwan da aka samata , ga wani kuka da takeyi wanda komai rashin imaninka sai ka tausaya mata ,itama mamar kuka takeyi tana rirrik'eta da Bata Baki,tashinta kenan daga alluran baccin da akayi mata d'azu da safe , zuba masu jajayen idanunshi yayi da suka canza nan take a hankali fushinsa na jiya ke dawowa , daurewa yayi ya matsa inda suke kallon maman yayi yace " "saketa Mama, " "Yalla'bai zata jima kanta ciyo ne" "Saketa zata daina " Jin hakan yasa batayi musu ba ta saketa zama yayi kusa da ita yafara mata magana a hankali Wanda ko maman bataji abunda yake ce mata ba , nan take ta nutsu tare da zuba mashi kumburarrun idanunta don gasgata maganar da yake fad'a mata , jinjina mata kanshi yayi alamar hakane , lumshe idonta tayi a hankali wasu hawaye masu zafi suna zubo mata , kamun tayi baya ta kwanta ,mamaki ne ya rufe maman ganin duk irin lallashin da sukeyiwa Safiya Bata ko daga ido ta kallesu Amma gashi cikin yan seconni Hisham ya bi da ita cikin ruwan sanyi , wani girmanshi ne da kaunarshi suka k'ara kama maman sai addua take zuba mashi Yana amsawa da Amin cikin tausayinsu ,lokaci. Da zai wuce ne yake barmata sakon Yana neman Baban safiya a office in ya zo ,to Mama tace mashi kamun suyi sallama ya tafi, ____________________________ Hisham ne zaune tare da Baban safiya da kanenshi office dinshi , da k'yar ya daure yayi masu bayanin halin da ake ciki tare da sanar dasu an kar'be case din a hannunshi yanzu case din Yana hannun manyanshi Wanda shi bashida wani abu da zai iyayi akansu sai yadda sukayi sai dai yayi masu alkawarin abunda akayiwa safiya bazai taba tafiya a banza ba inaha Allah zaisan matakin da zai dauka haka dai yayi ta kwantar masu da hankali ,saidai hankalin nasu yakasa kwanciya sunga samu sunga Rashi tabbas wanna. K'asar tamu abun tausayi ce yanzu shikenan. Talakan Nigeria bashida wani yan cin Kai ??? Kullum sukenan zasu zauna a mulkin mallaka ? Sosai Baban safiya ke kuka da idanunshi tare da adduar Allah yasakama 'yashi yasan in sunfi karfin hukuma ai bazasufi k'arfi. Allah ba, da k'yar Hisham ya lallabasu suka tafi ,cikin rashin jin dadin zuciya yabar office din shima yanufi gida, _________________ Misalin k'arfe 4 ya isa gida a massalaci yafara tsayawa yayi sallar la'sar kamun ya k'arasa gida , koda yazo ya tarar da momma Bata nan dama ta gaya mashi zataje gidan k'awarta hajiya Hadiza , wanka yayi ya canza kayan aikinshi , cikin wani tsadadden bak'in yadi Mai shara shara ya shirya Wanda ya k'ara haska farar fatarshi yayi mashi kyau sosai bak'in takalmi yasa sai agigonshi fari Mai azabar tsada da kyau , farin glass dinshi ya dauka ya Sanya ,Masha Allah yayi kyau sosai kamar ka saceshi ka 'boyeπŸ€ͺ a gurguje yagama Shirin ya fita ya dauki wata bak'ar motarshi wadda Tasha wanki da guga sai daukar ido takeyi direct unguwar su laurat ya nufa kasancewar tun kwanaki yayi bincike akanta sosai yasan komai akanta sai abunda ba'a rasa ba wannan yakara bashi k'warin gwuiwa akanta don tasamu yabo ita da iyayenta sosai , A bakin get din ya tsaya ya dauko wayarshi ya Danna mata Kira , sai wani farinciki yakeji daga can k'asan zuciyarshi ,Yana jin kanshi wani daban don Bai taba zuwa zance ba baimasan yadda akeyin zancan ba ,daga kafadunshi yayi afili Yana cewa ai sai ta koyamun don da alama ita tasan yadda akeyin zancan, har wayar ta tsinke Bata d'aga ba , tsaki yayi ya sake Kira ringing biyu ta dauka tare da yin sallama, cikin lumshe idonshi ya amsa mata sallamar ya Dora da fadin "da bakiyi niyar dauka bane ko kuwa Jan aji ne ? Bai bata damar magana ba yace kifito ki shigo Dani Ina k'ofar gida, Dam dam zuciyarta ta buga tana mamakin wai wannan wane irin karfin hali yake dashi, kallonta zee tayi tace "lafiya anty, ?" "Hmm inafa lafiya wani dan rainin hankali ya sakoni agaba gashi Abba Yana nan bansan ya zanyi ba , wai gashi a k'ofar gida ," "To Kuma anty bake kikace yazo ba ?" "Taya zance yazo bayan banko sanshi ba Ni banma San inda yasamu number ta ba wallahi, don Allah ki taimaka kije ki koreshi tun kamun Abba ya ganshi kinsan dai kiris yake jira Dani wallahi ,dariya zee tayi tace "okay to Bari naje Naga ko waye " "Yawwa my swt.sis don Allah taimaka" Gyalenta ta dauka ta yafa tafita a hankali ta nufi bakin get din tana dariyar Shirmen lauratu na korar samari ita kam in taga yayi mata wallahi bazata koreshi ba shigo dashi zatayi sai dai duk abunda za'ayi ayi,da wannan tunanin ta k'arasa get din ,bude karamar k'ofar tayi ta fita ,motar ta nufa tana k'wank'awasawa a hankali kasancewar motar Mai duhun glass ce Bata ganin Wanda ke ciki , A hankali ya bude motar yafara fito da k'afarshi ,gaba daya zee ta k'ara waro idonta don ganin Wanda zai fito daga motar, fitowarshi gaba daya yasa ta kusan fasa ihun murna ,da k'yar ta danne murnar ta cikin rawar jiki tafara gaisheshi bakin nan kamar gonar auduga don ba karamun ganin dacewarshi da antyn nata tayi ba ,cikin farin ciki tace "sannu da zuwa Yaya anzo lafiya yagida anty tana ciki tace nayi maka iso , Murmushi yayi don lokaci d'aya zee ta shiga ranshi rawar kanta na kara bashi dariya , rufe motar yayi Yana amsa mata gaisuwarta kamun yabi bayanta suka nufi cikin gidan ...............nagaji sai gobeπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* πŸ…ΏοΈ_32 ......................... Zee na barin wajansu falon Abbanta ta nufa Allah Allah take taje takai masu labari Kuma tanason tayiwa antynta d'aurin talala ta yadda bazata iya dagule lamarinba kamar yadda takeso don takula in ta biye ta tata zatayi masu buk'ulu ne, bayan Kuma duk munafurci ne don ba Wanda zaik'i wannan gayen , "Assalamu alaikum" tayi sallama abakin k'ofar falon, Wa'alaikussalam shigo" cewar Momy , cikin zumud'i ta shigo falon sai washe Baki takeyi , "Ke lafiyarki kuwa kike wani washe Baki kamar Mai tallan makilin ," cewa Momy , "Ai Momy wani abun alheri ne ya samemu yanzu dai Antyna tayi free ta huta da k'orafin Abba ,"ta fad'a tana dariya tare da kallon Abban , harararta tayi tare da ware hannunshi akanta yace " kinci gidanku Zainabu Ni kike cewa Ina k'orafi rainin naki Kuma yanzu a kaina ya dawo ko "? Dariya Momy tayi tace oho yau dai anji kanku ai in tanamun shak'iyanci nayi magana kace na takurata ai yanzu gashi nan tafara dawowa kanka, Murmushi Abba yayi yace " ai bazaji kanmu da uwata ba saidai waccan sarkin rashin jin 'yar Taki , yawwa uwata zo nan gayamun minene yake faruwa , da sauri ta k'arasa kusa da kafafunshi ta zauna cikin zumud'i tafara magana , "Am Abba albishirinka Bata jira cewarshi ba taci gaba da cewa , yau dai kayi sabon suruki Abba , Anty Tasamu Wanda takeso wallahi Abba baka ganshi ba ya had'u sosai gashi kyakykyawa ga shi Dan gayu ga nutsuwa Allah Abba in ka ganshi kallo daya zakayi mashi kaji ya burgeka tayi maganar tana washe Baki kamar wata karamar yarinya , daga Abban har Momy dariyar shirmenta sukayi yadda take Abu kamar wata Yar shekara 6 dama zee Kam badai ta'bara ba , Momy tace " to Zee basai yayar Taki tana sonshi ba tunda Kiri Kiri yarinyar nan kamar Mai aljanu duk Wanda zaice Yana sonta shikenan batada makiyi sama dashi kawayenta duk sunyi aure Amma ita ko a jikinta duk akayi magana tace ita ba Wanda takeso ," "Aa Momy wannan kam tana sonshi sosai don sun kwana biyu suna waya ma kamun yazo Kuma da kanta ta gayamun wannan tana sonshi ai yanzu ma tanacan wajanshi a d'akin Baki , To Alhamdulillah Allah ya tabbatar da alkhairi cewar Abba cike da farinciki don Allah yagani zaman yaran nan a gabanshi yafara isarshi shiyasa yakeson ya sauke nauyin da Allah ya Dora mashi ya aurar dasu ko yasamu nutsuwa ,Momy ma taji Dadi sosai sai adduar alkhairi take , nan suka ci gaba da tattaunawa akan maganar suna jiran Laurat ya shigo suji daga bakinta,. ____________________ Hisham Kam cike da farinciki ya nufi inda ya ajiye motarshi ya bude bayan motar ledojine kusan hudu masu k'yalk'yali kowacce shak'e da Kaya ya dauko ya nufi wani Dan saurayi da bazai wuce 20yrs ba Yana can gefe Yana wankin Kaya ,sallama yayi mashi da sauri saurayin ya tsame hannunshi ya nufoshi Yana gayardashi amasawa yayi kamun yabashi ledojin yace " don Allah ga wannan ka kaima yarinyar gidan " to Alhaji wacce acikinsu , Dan murmushi yayi yace pretty zaka kaiwa kace inji *Dan sanda* wasu kudi ya fito dasu yabawa yaron yace wanna naka ne daga haka ya juya yabar yaron sake da Baki da tunanin wacece Kuma pretty??? , Tafe yake a mota Yana tuki a hankali wani irin farinciki da nishad'i yake ji Wanda Yama rasa Kona minene , Yana cikin wannan yanayin ne kamar kyaftawar ido aka hasko mashi fuskar safiya acikin idanunshi , nan take yanayinshi ya sauya daga farinciki zuwa fushi mai tsanani ahaka dai yaci gaba da tafiya Yana sauri ya isa gida kamun afara kisan sallah, ___________________________ Yalla'bai kayi hakuri wannan ba abune Mai yiwuwa ba Nima bansan miyasaba bansan kuma daga Ina ne ba Amma tabbas Hisham yanada d'aurin gindi a sama korarshi a aiki ba abune Mai sauki ba sir zai iya haifar da babbar matsalar da bakayi zato ba , don haka kayi hakuri nidai ta 'bangarena ba abunda Zan iyayi da nayi maka kaima kasan wannan sir , Wani irin huci Mai zafi Daddyn Zayyan ya fitar cikin hasala ya nuna Wanda suke magana dashi yace ,"karka gayamun maganar banza Mana , wanene Hisham Kuma mi akayi akayishi ubanwa ya tsaya mashi a garin nan, oh Yana da d'aurin gindi wannan yabashi damar ya ta'ba yarona , hmmmm tabbas yayi ganganci duk shegen da ya nemi shiga gonata to ba makawa sai na hanashi jin Dadin rayuwa , naso nasa akoreshi ne daga aiki sannan daga baya na wulakanta rayuwarshi , to yanzu ma bazan barshi ba Zan dauki mataki da hannuna Kuma kaima kasan abunda Zan iya sannan Zan binciko uban da ya daure mashi gindi a k'asar nan ma ba a garin nan ba ya k'arasa maganar Yana dukan table din dake wajan da k'arfi ai kuwa take kayan dake bisa suka watse cikin huci ya Mike tsaye tareda nuna mutumin yace ka jirani kaima Zan dawo kanka , ba Wanda ya isa na sashi Abu yayimun jayayya ,daga haka yabaza babbar rigarshi yabar office din, wani irin zufa ne ya yankowa mutumin cikin tsananin tashin hankali yafara girgiza kanshi yasan waye Alhaji Saminu Sulaiman yasan abunda zai iyayi , tabbas bazai taba sa hannu a Kori JAMI'I Mai gaskiya da samun irinshi a wanna lokacin yanada wuya ba kamar Hisham saidai Yana tsoron abunda zai iya samunshi ,dafe kanshi yayi da dukkan hannu biyu Yana adduar Allah ya kare Hisham daga sharrin wadan nan shedanun mutanen , ____________________________ "Kai Mariya karatun nan naki Yana cin kudi sosai yanzu Kuma Ina zamu samu wannan uban kudin ,nikam dama kin hak'ura da wannan karatun kina ganin yayanki Bai aje ba baiba wani ajiya ba duk Dan abunda yasamu akan karatun nan naki yake karewa gashi har yanzu Baki gama ba bare a San ran cin amfani, Sosai ta fito da manyan idanunta waje cikin sark'ewar murya tace In ajiye karatu fa kace Baba , yanzu wannan wahalar da mukayi sai ta tashi a banza kenan Baba" ta k'arasa maganar kamar zata kuka , "To ya zamuyi Mariya haka Allah yaso don nikam bansan a Ina Zan samo maki wannan uban kudin ba , Kuma sulemanu ma bana tunanin a wannan karon yanadasu bare yabaki, " "Aa Baba bazata dakatar da karatunta ba indai Ina Raye insha Allah sai Mariya ta cika burinta na zama ma'aikaciyar jinya ," cewar Sulaiman Wanda yashigo gidan yanzu ya tsinci zancan da sukeyi, Duk ido suka zuba mashi jin abunda ya fad'a ,cikin karfin hali Baba yace kayya dai sulaimanu yanzu ma wasu kudin za'a biya Wanda bana tunanin kanadasu bare ka biya Nima don ba yadda zanyi ne shiyasa nace abarshi kawai, Murmushi sulaiman yayi yace nasan da zancan kudin baba wannan yasa nayi tanadinsu tun kamun a bukacesu ,akwai wani adashen da na shiga tun watannin baya insha Allah nasan zasu Isa abiya kudin makarantar anjima zanje na amsosu insha Allah gobe sai takai kudin, Daga Baba har Inna Indo Banda addua da sa albarka ba abunda suke yiwa sulaiman suna alfahari da Dan nasu sosai shiyasa suke mashi wani irin so , Mariya kuwa tuni hawayen sun wanke Mata fuska tanajin wata irin kaunar Dan uwan nata da tausayinshi da sauri ta k'arasa inda yake ta rungumeshi cikin farinciki tace "nagode yayana Allah yasaka maka da mafificin alkhairi Allah ya daukaka ka yakara maka budi akan harkokinka ngd sosai Yaya , murmushi yayi yace bakomai K'anwata in nayi maki kamar kaina nayiwa fatana dai ki tsaya ki kula da karatunki Allah yasa adace duk suka amsa da Amin kamun sukaci gaba da tattaunawa, _________________________ "Hello sir " aka fad'a cikin wata hargitsatstsiyar murya Marar Dadin sauraro , a dayan bangaren akace "Yawwa big boy kana jina ko , akwai hoton da Zan turo maka tare da adireshen Mai hoton da dik wani abu da ya shafeshi inason kufara bibiyarshi inason sanin komai game dashi acikin kwana biyu kacal don haka banason shirme a aikina kasani , " "Yes oga za'ayi komai kamar yadda kace Kuma akan lokacin da ka bayar , " Batare da ya sake magana ba ya kashe wayar , sannan ya tura masu duk wani abunda ya shafi Hisham hotonshi cikakken sunanshi wajan aikinshi da Kuma unguwarsu , bayan ya tura ne yafara zagaya d'akin Yana tunanin irinn hukuncin da zai yiwa Hisham don har yanzu Zayyan baigama warwarewa ba ga k'afarshi da har yanzu yakasa taka ta da kyau saidai yayi dingishi yanajin ciyo sosai in yaga yadda d'anshi ke tafiya sai kace wani gurgu , mrtsss yayi tsaki tare da k'wafa afili yace zamu hadu ne, (Hhhhhhhhhh nikuma nace wanzam kenan bakaso ga jikinka) _____________________ Washe gari Momy ce da Abba zaune a kan dinning suna karyawa bayan sun gama ne ya dubeta yace "Wai momyn Yara ya kukayi da 'yar Taki ne nayita jiran naji kince wani abu Amma shiru itama tun jiya take wasan 'buya Dani ," "Hmm Alhaji kenan nayi Mata magana Amma sai wani kwane kwane takemun da alama dai zancan Zee ne itama tana sonshi may be kunya takeji murmushi Abban yayi yace to alhamdulillah kiramun ita naji waye shi inason inganshi sannan nayi bincike akanshi don banason tarayyarsu tayi nisa batare da na Yi bincike akanshi ba , " "Hakane to Bari na kirata, .............nagaji sai gobe kumaπŸ€ͺπŸ€ͺ [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* πŸ…ΏοΈ_31 ...................Falon da Abbansu ke sauke bak'i ta kaishi sai nan nan take dashi cikin fara'arta da takasa gushewa tace "yawwa Yaya zauna anan zanje na kawo maka ruwa dakuma antyn , " Murmushi yayi Mai kyau yace " to k'anwata Ina jiranki" Fita tayi da d'an gudunta tanufi falonsu inda tabar Laurat acan , da k'arfi ta turo k'ofar Wanda yasa laurat juyawa da sauri tana kallonta , aikuwa tana shigowa falon tafara tik'ar rawa tanayi tana juyi,tsaki laurat tayi tace "kefa Shashasha ce rawar mi kikeyi , ya tafi ne ko Yaya"! "Kai anty irin wannan kamu haka kinga kuwa gayen nan wlh ya had'u iyakar had'uwa zakuyi bala'in dacewa dashi Allah anty , " "Ke bashi na tambayeki ba cewa nayi ya tafi ko Yaya ? Tayi maganar ranta a had'e "Ya tafi Ina Anty? 😳ta fad'a tana zaro ido ai wallahi ba zamu saki tukunya mukama murhu ba ke kinganshi anty ta Ina zanyi wasa da irin wannan damar da mukasamu ai wallahi wannan ko bakya sonshi to shi Zaki aura don ni yayimun sosai Bari ma nayi sauri na Kai mashi ruwa kekuma ki hanzarta kidan sake Kaya kishafa Yar powder kije Yana d'akin bakin inba haka ba wallahi yanzu zanje na hadaki da Abba kin Kuma San tsaf zan iya" ta fad'a tana wani juya duwawu tayi kitchen don hada mashi abun Sha, Dafe kanta tayi cikin takaicin kanta da ta tsaya aika zee bayan tasan halinta Sarai yanzu ya zatayi kenan ? Yazama doli ta hanzarta zuwa ta sallameshi tun kafin zee ta had'a Mata bom agidan ,tana nan tsaye tana tunanin abunyi zee ta fito daga kitchen hannunta dauke da wani madaidaicin tire inda ta hado mashi lemu da ruwa da cek ,ta gaban Laurat ta wuce har takai bakin k'ofa ta juyo tace " pls anty don Allah kije ki canza kayan nan kizo kinji wallahi gayen nan yayi bala'in dacewa dake Amma na yarda in kin ganshi baiyi maki ba to shikenan sai mubashi hak'uri, tayi maganar tana wani marairaicewa kamar marainiya ,harara Laurat ta banka Mata da manyan idanunta tace "wallahi ba abunda Zan canza tunda bani na gayyatoshi ba ahaka zanje Kuma ki ajiye kayan nan don ni ba fira Zan je hakuri kawai zanbashi na dawo ," " In mayar fa kikace anty Aa wallahi Ni ban iya rowa ba ai bak'onk'a annabinka Ni dai kiyi sauri don Allah,daga haka ta wuce ta barta tsaye , K'wafa kawai Laurat tayi kamun ta janyo hijab dinta ta Sanya Wanda da kadan ya wuce gwuiwarta , tana sanye da doguwar rigar atamfa wadda tayi Mata d'ass ajiki ta Kuma bayyanar Mata da shape dinta sosai ,don laurat akwai k'ira sosai komai yaji ajikinta wannan yasa take yawan amfani da hijab da wuya ka ganta da gyale , a sanyaye ta nufi sashen da suke sauke bak'i zuciyarta na bugu sosai , haka kawai Kuma sai naji tana muradin taga wannan isashshen da yake yi Mata magana cikin Isa da gadara kamar wani ubanta, Tun daga waje tafarajin karad'in zee sai surutu take zuba mashi kamar wata karamar yarinya , haushine yak'ara kamata jin yadda zee ke karad'i cike da zubda aji tsaki tayi acikin ranta tana tunanin irinn hukuncin da zatayiwa zee, Ciki ciki tayi sallama ta shiga d'akin, da sauri ya d'ago da kanshi ya zuba Mata narkakkun idanunshi Yana amsa sallamar tata ciki ciki kamar yadda tayi, lokaci d'aya zuciyarta ta buga da k'arfi ganin Wanda yake zaune dama wannan Dan sandan ne yake kiranta,a Ina yasamu number ta to Kuma ya akayi yasan gidansu ne mima yakawo shi to ,? daburcewa tayi ganin yadda ya zuba Mata idanu ,dama wannan Dan rainin hankalin ne yake kiranta a waya,? Tak'ara tambayar kanta da k'yar ta tattaro nutsuwarta gudun kar ta bada kanta , had'e Rai tayi don karma yaga damarta a nutse ta k'arasa cikin falon sosai kamun ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna , a hankali take satar kallonshi gefe daya Kuma zee take zubama harara kamar idonta zasu fad'o k'asa ,dariya zee ta fashe da ita tana cewa "kinga anty maida wuk'ar bani na kar zomon ba rataya aka bani Ni tafiyata ma zanyi , "ta juya tana kallon Hisham tace Yayana sai anjima ko afito lafiya cikin murmushi yace to k'anwata nagode sosai kinji don Naga kinfi yayar Taki hankali, da dariya zee tabar falon don taga yadda antyn ke cika tana batsewa,cikin ranta kuwa addua takeyi Allah y tabbatar da alkhairi don itakam Hisham yagama burgeta sosai tayiwa yayarta sha'awarsa, Jikinta har rawa yakeyi jin yadda idonshi ke yawo a jikinta da k'yar ta daure tace "Ina wuni" Ajiyar zuciya ya sauke cike da kasala yace "ai na dauka Baki iya gaisuwar bane , " wani kallo ta aika mashi cikin turo Baki tace "mi ya kawoka gidanmu"? Murmushi yayi yace "Matata nazo na d'auka" "Matar ka ? Wace Matar ka anan , to malam an rigaka sai ak'ara gaba ko zaka dace don na lura Kai ko neman So baka iya ba sai .......shiru tayi bata k'arasa ba , Cikin jarumar muryarshi yace " Ina saurarenki saimi ?? Ki k'arasa Mana ,turo bakinta tayi tana magana k'asa k'asa ,murmushi yayi yace "inba tsoro ba ki fad'a Mana ,juyar da kanta tayi gefe tana cewa "pls in bakada abun cewa inason Zan koma , "Ina zakije Baki amsamun soyayyata ba ? Taji ya fad'a kamar maiyin rad'a, "Soyayya ! wace irin soyayya Kuma ai na gaya maka anrigaka yanzu haka saura k'iris a dauramun aure so kayi hakuri pls , Har yanzu murmushin yakeyi cikin yanayin tsokana yace "Jan aji zakiyimun bayan Kuma nasan bakida wani mashinshini ai k'anwata zee ta gayamun komai tace kinyi kwantai don haka kawai kibada Kai karkiyiwa kanki asarar santalelen saurayi kamar Ni ,ki Bari na rufa maki asiri nayi wufff dake ,ya k'arasa maganar Yana had'iye dariyarshi ganin yadda ta cika tayi fam kamar zata rusa ihu cikin tsananin 'bacin rai da takaicin zee ta hayayyak'o mashi kamar zata cinyeshi da masifa , d'an mitsitsin bakinta ya tsurama ido Yana kallon yadda yake motsawa komai nata cikin nutsuwa masifar ma sai tayi Mata kyau komai nata burgeshi yake ,tana cikin masifar ne batare data Ankara ba sai jin numfashin mutum tayi a kusa da ita ,da sauri ta waro idanunta waje tare da ja da baya ganin yadda ya matso ta , ahankali yafara tafiya Yana nufota ita Kuma tanaja da baya tare da Yi mashi gargad'i da idanunta da suke cike da masifa, Ahaka har suka dangana da bangon d'akin hannuwasa yasa ya dafe bangon gefe da gefenta ya zamanata ya Sanyata a tsakkiya , kallon ido cikin ido suke yiiwa juna yayinda wad'ansu kibiyoyi ke fitowa daga idanunsu suna shiga cikin junansu kasa jurewa kallonshi tayi don lokaci d'aya ta nemi nutsuwarta ta rasa wani irin maganad'iso takeji Yana fisgarta daga cikin idon nashi kamar mayen k'arfe , ga kusancin da ya Samar a tsakaninsu wannan yasa takasa wani taka'bu jikinta ya saki sosai , "Maimaita abunda kikace , yafad'a cikin wani irin salo Wanda yak'ara narkar da zuciyar Laurat , turo bakinta tayi tana gunguni ,kamun ta d'ago idanunta ta zuba mashi harara , murmushi Mai kyau yayi Mata kamun yaci gaba da cewa " nidai Allah yagani tunda nayi niyar taimaka maki na dauke ki daga gidan nan to bazan fasa ba , nasan Allah zai bani Lada don haka zanje namasu Abbanki da maganar ko ya Kika gani yayi maganar Yana d'aga Mata girarshi daya cikin wani salon da shi kanshi baisan yayi ba Kuma sai hakan yayi masifar Yi mashi kyau , kauda kanta tayi daga kallonshi Jin yadda zuciyarta ta harba da k'arfi tare da kar'ban duk wani sak'o da yake aika Mata Sam takasa samun wata nutsuwa , ga magana tanason tayi Amma Sam takasa wani bak'on yanayi takeji Yana shigarta Wanda ya Sanyaya Mata jiki sosai , murmushi Mai kyau yayi ganin tarkonshi yakama kurciya , janyewa yayi daga kusa da ita ya d'anja da baya Yana dubanta yace " Ni Zan koma don Naga lokacin sallah Yana k'aratowa Amma jibi zanzo na gana da Abba don haka ki gaya Masa ,sannan in kinshiga ciki pls ki turomin k'anwata nayi Mata sallama kinji yafada Yana d'aga Mata hannu sannan ya juya yafara tafiya , har yakai bakin k'ofa yaji tace " in ka tafi basai ka dawo ba don Babana bazai taba baka Ni amatsayin Mata ba ta fad'a a tsiwace don taji haushin yadda takasa yi mashi duk wata rashin kunya da ta kullomashi , Murmushin gefen Baki yayi batare da ya juyo ba yace "akan mi fa "? Cike da gadara tafara taku har tazo Inda yake tace "saboda aduniya kalma daya Tak Abba ya tsana " "Ko Zan iya sanin wace kalma ce "? Saida ta rausayar da Kai sannan cikin jin Dadin zata kuntata Masa tace " *Police* A hankali ya juyo ya zuba Mata idanu Wanda take jikinta yafara tsuma Babu shiri ta duk'ar da kanta k'asa , cikin k'asaita yace Mata "nikuma nayi maki alkawarin sai ya so wannan kalmar fiye da tunaninki daga haka yajuya yabar falon cike da nishadi don ko kadan maganarta Bata razanashi ba a tunaninshi kawai ta fad'a ne don ta Bata mashi rai.......... FATAN KUNYI SALLAH LFY *HAPPY SALLAH HAPPY SALLAH* πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ *Dr Mmn Yusuf (likitar Mata)*😍😍😍 *BONONZA BONONZA BONONZA* *Karku Bari abarku a baya don mace Mai gyara kanta Bata boranci , kayane ingantattun Kuma zafafa ,na sakesu a arha don tayaku murnar shagalin sallah dakuma Amaren bayan sallah Yan Mata da zawarawa uwar gida da amarya ku garzayo ku kwashi rabonku kar ayi babuku, Sam karku Bari wannan damar ta wuce ku karku manta MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI Kuma a Dade anayi sai gaskiya namu ba irin nasu bane kayanmu na musamman ne domin jin Dadin ma'aurata Babu kalan kayan matan da bamudashi kedai garzayo kar abaki labari mmn Yusuf Dr Mata farincikinku takeso*😍😍😍😍 *Ina Amaren da suke k'amas komai a bushe to kuzo nazo maku da ingantattun kayan gyaran jiki Wanda Zaki ciko gaba da baya kuyi d'ass abunku gwanin sha'awa* *Amaryar dake da matsalar rashin nono ko hips ko siranta yayi maki yawa kike buk'atar kidan ciko to kizo na tanadar maku ingantaccen maganin nono da maganin hips da maganin k'iba ta yadda Zaki kankarowa kanki martaba a wajan oga ,uwa uba SAHIHIN MAGANIN SANYI Wanda yakeda. Matukar muhimmanci ace kowace amarya tafarayi kamun komai don indai kinada ciyon sanyi to duk abunda zakiyi amfani dashi to bazaiyi maki wani tasiri ba AMARE YAKAMATA A KULA KAR AJE AYI TA BARNAR KUDI A BANZA ANA GYARA BAYAN GA SANYI BA'A MAGANCESHI BA* *Wadda take fama da rashin sha'awa , rashin niima kullum kasanki a bushe to ki garzayo wajan mmn Yusuf Dr Mata Zaki rabu da wannan matsalar da izinin Allah* *Masu bukatar sabulan gyaran jiki na gani a fad'a masu sa jiki yayi kyau yayi lumi-lumi yayi haske Mai kyau bana bilicin ba yacire maki duk wani tabo ko kurji da yake jikinki ,da shahararrar DILKA Mai maida tsohuwa yarinya ga k'amshi Mai Kama jiki gasa sulbi da santsin fata kamar ta jariri to ku garzayo Kuma ku kwashi rabonku a farashi Mai sauki ,wajan mmn Yusuf Dr Mata Ina sokoto Ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah adade anayi sai gaskiya* 07069711327. Call or WhatsApp Pls wadda Bata shirya siya ba kar tamun mgn serious pls kibari in kin shirya sai Musa labule πŸ˜‰ banason mu batawa juna lokaci ne ga azumi typing ba dadiπŸ₯±πŸ₯± [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* πŸ…ΏοΈ_33 .......................da k'yar ya bude kumburarrar fuskarshi da har yanzu takasa komawa dai sai saboda sambad'e bad'en da yasha Wanda sanadiyar hakan hak'oranshi biyu na gaba suka fita wannan yasa yakoma kamar wani dodo saboda Muni Kuma dama can ba kyaun ne dashi ba yace ".wai oga yanzu haka zamu k'yale wannan banzan Dan sandan bazamu dauki fansa akan shege ba ka duba yadda gayen nan ya mayar Dani, Ni kaina kunyar kaina nakeji, shiyasa ma yanzu Sam bana fita ko Ina jiya bakaga yanda babys din nan su Sumy suka dingamun dariya ba wallahi naji haushi sosai, cewar d'aya daga cikin abokan Zayyan Mai sun junior, Zaune suke a katafaren falon Zayyan da babuce kawai Babu aciki , Yana zaune akan kujera ya Dora kafa daya Akan daya Yana girgizawa cike da izgilanci yayinda abokan nashi suke zagaye dashi suna jiran umurni ,a hankali ya d'ago da kanshi ya kalli fuskar Junior yace Kaima kasan bazan ta'ba k'yaleshi ba don ba Wanda ya ta'ba yimun irin wannan dukan da yayimun tunda uwata ta haifeni , yanzu haka bincike nakeyi akanshi sosai , Kuma Dad ma Yana nan Yana bincike akanshi saidai Ni bazan wani jira Dad ba da kaina nakeson na dauki mataki akanshi Amma kamun nan sai naci gaba da lalata yanmatan da bayaso ayi Ina aika mashi dasu har office dinshi sai Naga abunda zaiyi sai na wulakantashi kamun nasa a 'batarmun da shege zai gane ya ta'bo Zayyan wallahi yayi maganar cikin tsananin 'bacin rai da fushi , Wani daga cikinsu Mai suna Shams yace "yes sai oga haka nakeson ji babaaa Ni wallahi ma naso ace yanada k'anwa ko Mata billahillazi da akansu zamu sauke iskancinmu inyaso ya hura wuta ya jefamu Allah oga da tsaf zamusa a daure Mana shi Yana kallo muyi masu kaca kaca wallahi Amma ba komai yanzu ma Bata 'baci ba zamu sake aikata fyade ga duk wadda tayi Mana in yaso muzuba mu dashi shege ka fasa , yayi maganar Yana wani cizon Baki irin na cikakkun Yan Daba , daga Zayyan har sauran yaran dariya suka fashe dashi , Junior yace " Kai shams kasan takan tsiya fa Allah har naji haushin da bashida kanwa da munyi mashi abunda har yamutu bazai manta damu ba ,saidai Kash gashi bashida ko daya , Wani mushirikin murmushi Zayyan yayi yace " ai yanada mahaifiya ko, Allah Ni ko akanta Zan iya sauke haushina nasan daga lokacin zai hade zuciya ya mutu shikenan basai na walahar da kaina wajan aikawa dashi ba , gaba dayansu suka fashe da wata mahaukaciyar dariya suna Yi mashi kirarin da suka Saba aduk lokacin da yayi wata tabokara irin wannan , Mom dake tsaye tun d'azu tana saurarensu ta girgiza kanta cikin matukar damuwa da tashin hankali ta k'araso cikin falon tana cewa " Zayyan mi naji kana cewa ? Anya Zayyan kwakwalwarka Bata fara juyewa ba kuwa kasan wanene Hisham kuwa to wallahi tun wuri ka fita sabgarshi inba haka ba wallahi bazatayi maka kyau ba ,daga Kai har uban baka da kake tak'ama dashi , ka daina biyewa mahaifinka da wadan nan shashashan abokan naka suna dauraka a hanyar da bazata 'bulle da Kai ba sannan in ................"ohhhhh Mom ya zakizo ki cikamu da surutu ne , ko kinji na kiraki ne ohh wato ma la'be kikemun ko ,to kibari In mun janyo bala'in ai ba akanki zai sauka ba don haka don Allah mom kije Kuma ki daina irin wannan yawar kina bayar Dani agaban abokai haba , Ni Zan gayawa Dad ma ya siyamun gidan da Zan zauna kawai na barmaki nan Dake da wannan munafukar Yar taki , Baki ganniba ma bare kisamun eyes haba, "Innalillahi wa inna ilaihin rajiun Zayyan Ni kake gayawa wannan maganar , tafad'a kamar zata fashe da kuka , cikin jin haushin kanta da tabiyewa son zuciya wajan za'bar Wanda Bai kamata ta za'ba a matsayin abokin rayuwarta ba tace " shikenan ba laifinka bane laifin ubanka ne da ya daure maka gindi kayi duk abunda kaga dama ,Allah ya shiryeku Baki d'aya daga haka ta juya tabar falon cike da k'unar zuciya, Tana fita Zayyan yayi tsaki Yana gunguni tare da Harare Harare kamun yace Kai ku tashi mubar gidan nan muje gidan gonar daddy don wannan Matar bazata daina takurani ba ko tausayina bataji Anya ma itace mahaifiyata kuwa yafada Yana k'wafa , aikuwa kamun kace mi sun tarkata sun fice a gidan , _________________________ "Assalamu alaikum " tayi sallama cikin shiriritar muryarta , " Wa'alaikissalam shigo ki zauna " cewar Abba , kusa da k'afafun Momy taje ta zauna kanta a k'asa tace "Abba barka da hutawa , " kanshi kawai ya d'aga Mata alamar amsawa sannan yace " Naji sak'onki a wajan k'anwarki tace mun kin samu Wanda kike so harma kun daidaita kanku ko ? to alhamdulillah naji d'ad'in hakan abunda nakeso yanzu shine ki gayamun waye shi inason in gana dashi don sanin asalinshi dayin bincike akanshi ,don haka tunda har kuna waya dashi to ki sanar mashi cewa Ina nemanshi gobe in Allah ya kaimu , Allah yayi maku albarka ya za'ba abunda yafi alkhairi , cike da farinciki Momy ke amsawa da Amin yayinda Laurat tayi suman zaune tana mamakin yaushe tayi da zee akan ta gayawa Abba tasamu miji ne innalillahi Amma wannan yarinyar ta gama da ita , yanzu yadda taga suna farincikin nan ta Yaya zata ce masu ba haka bane , sannan ta yayama zata daga waya ta Kira wannan Dan rainin hankalin tace mashi Wai Abbanta na nemanshi , ai sai ya dauka ma tana sonshi kenan , runtse idonta tayi da k'arfi cikin takaici lallai Zee tayi Mata d'aurin talala yanzu minene mafita , "Laurat lafiya dai Ana magana kinyi shiru, " Zubur tayi tana Yan soshe soshe cikin in Ina tace " ah.. ba..bakomai Abba Zan ..zangaya mashi , Jinjina Kai yayi yace "to shikenan Ina jiranshi don indai nayi bincike akanshi Naga ya cancanta da aurenki to bazamu dauki wani lokaci ba indai a shirye yake insha Allah, " "Allah ya tabbatar da mafi alkhairi Amin" cewar Momy , Sum sum sum Laurat ta tashi tabar falon inda Abba da momy sukaci gaba da tattaunawa akan zanca , Tunda ta fita daga falon take zuba sauri kamar zata tashi sama direct d'akinsu ta nufa tana zuwa ta banka k'ofar d'akin a fusace ta shiga , da sauri Zee ta juyo Jin yadda aka banko k'ofar d'akin ga bakinta taf da wata k'atuwar alewa tana taunawa kamar zata tsinke harshenta don wani shegen Dadi da alewar ke Mata ,da k'yar maganarta ke fita saboda yadda alewar tacika mata baci tace " haba anty wallahi har kin tsoratani irin wannan dukan k'ofa haka Ina nan zaune Ina cin kayan Dadina Zaki razanani ,haba ai wannan daukar hakki ne wallahi , Wata irin harara Laurat ta aika Mata kamar idanunta zasu fado k'asa cikin kakkausar tace " yaushe na ce ki gayawa Abba nasamu Wanda nakeso yaushe mukayi hakan Dake eye , wallahi Zee kifita a idona yanzu ya kikeson nayi da Abba gashi ya kirani Wai na turo mashi shi , to Taya Zan turo shi din ,bayan Babu komai tsakanina dashi kawai Ina zamana kinzo kin sani tsaka Mai wuya saboda neman fitina irin naki ,to ai sai kije ki gaya masu gaskiya don ni ba wani kiranshi da ,zanyi, A hankali zee ta kwashe kayan makulashen da ta zube a gabanta tana kwasa Wanda duk suna cikin tsarabar da Hisham ya aikowa Laurat dasu ,Wanda ko kallon kayan tak'iyi shiyasa zee ke bikinta son ranta da kayan ,cikin nutsuwa ta mayar da komai inda yake sannan ta tashi ta nufi inda yayartata take janyo hannunta tayi a hankali ta zaunar da ita a bakin makeken gadon su tace "don Allah anty kiyi hakuri ki gafarceni banyi hakan da musgunawa a gareki ba saidon inason kisamu makoma Mai kyau ,duk da bansan halin yayana ba Amma Ina kyautata mashi zato kallo daya zakayi mashi kasan cewa akwai hankali da nutsuwa a tare dashi , hakama kallo daya zakayi mashi kasan cewa shin din Mai ilimi ne ta kowane fanni yanayinshi ma ya nuna haka , Ina rokonki da kiyi hkr ki tsaya ki fahimceshi na tabbatar da Zaki sameshi % sannan kinga Abba ma zaiyi bincike akanshi doli sai ya tabbatar da nagartarshi kamun ya yarda yabashi ke , nasan dai a yadda yake kyakkyawan nan bazakice baiyi maki ba anty don bashida makusa, kota Ina yayi burin kowace mace ne ki zauna kiyi tunani ko don ki farantawa iyayenki don tsakanin jiya da yau suna cikin farinciki sosai pls anty kiyi tunani , daga haka ta tashi ta bar Mata d'akin , tana fita tafara tik'ar rawa ganin yadda maganganunta suka Yi tasiri akan Lauratu, Shiru tayi kusan minti talatin tana saka da warwara ta hanga ta hango tabbas gaskiya zee ke fad'a Babu wata makusa atare da Hisham Babu macen da zata ce Bata sonshi saboda ya hada komai da mace zata bukata a wajan namiji , ita kanta tasan Bata Isa tace Bata sonshi ba kawai dai gayen ne Dan rainin hankalin Wai harda cewa zai taimaka Mata yayi wuf da ita sai kace wata wadda tarasa masoya ,ta dauki lokaci Mai tsawo tana tunanin mafita don itadai batajin sonshi haka Kuma batajin Bata sonshi , saidai Abu daya ta sani shine Yana burgeta sosai ,( ahaf Zaki dawo hanya ne yarinyaπŸ˜‚πŸ€£) Tana hakan Zee tak'ara shigowa d'akin ,zama tai kusa da ita tace "yadai anty kin kirashi ne , ? Harara ta banka Mata tace na kirashi nace mashi mi ,dariya zee tayi tace to kwantar da hankalinki na rage maki aiki na kirashi na gayamashi don dama na karbi number shi , wani kallo Laurat ta watsa Mata tace "mi kikace mashi ? Badai kinje kin saki Baki kina zuba zance da Wanda aka tambayeki da Wanda ba'a tambayeki ba kinasa Yana Raina mutane , "Aa fa anty nifa nasan abunda nakeyi cemashi kawai nayi Abba na nemanshi gobe daga haka na kashe wayar " "Kedai Kika sani da shegen rawar Kai mrtss, " Daga haka tafad'a kan gadon ta gyara kwanciyarta cike da tunanin Hisham , _________________________ "Momma Albishirnki " "Goro fari Tass shalele " "To alhamdulillah yanzu dai na wuce Gori na samu maki santaleliyar suruka ,yanzu haka ma Babanta ne yake kirana gobe zamu gana kiyi mun addua Allah yasa yabani ita don Ina sonta sosai," Kafeshi da ido momma tayi don son gano gaskiyarshi in ba shak'iyancin nashi ne ya motsa ba , musamman da Bata taba Jin yace yanason wata mace ba , "Da gaske kakeyi shalele"?? "Allah momma da gaske nakeyi Bari ma na nuna maki hotonta , " Wayarshi ya dauko ya nono wani hoto na Laurat Wanda an daukeshi ne a asibiti kayanta na aikin asibiti ne ajikinta yayi kyau sosai da alama ma batasan an dauketa hoton ba , ya mik'a Mata , K'urama hoton ido momma tayi cike da farinciki tace "Kai Masha Allah shalele Ashe dai ka iya za'be wannan yarinya haka Masha Allah son kowa k'in Wanda ya rasa Masha Allah Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah sarki Samrah Ashe ba rabon ayi da ita bane Allah yabata miji nagari ,wata muguwar dariya ce tazowa Hisham tunawa da fasalin Samrah da yayi a ranshi yace ah toh ak'ara gaba dai da yanzu an shak'amun wannan zar'ben ko inyi Yaya da ita ohoπŸ€” "Yawwa Momma Ni Zan wuce wajan aiki sai na dawo , "To shalele a dawo lafiya Allah ya tsare yabada sa'a " "Amin y Allah Momma daga haka yasa Kai yabar gidan , Direct gidansu Safiya yafara zuwa alhamdulillah yanzu taji sauki sosai sai dai duk yanayinta ya sauya abun tausayi kullum zaka ganta shiru shiru tana tunani sam Bata walwala magana ma sai ta wuni batace kala ba sai yazama doli abun Yana damun iyayenta sosai saidai Babu yadda suka iya sai addua da suke Mata a kullum , gashi makarantar ma anyi anyi Takoma ko zata rage wannan damuwa Amma Taki da anyi maganar ma sai tafara yimasu kuka , wannan yasa mahaifinta ya nemi taimakon Hisham akan yayi Mata magana ko za'a dace ta yarda da maganarshi ganin yadda takebin duk abunda yace mata, *Banso na tsaya anan ba Sam Amma yazama doli wlh banida lfy ku tayani da addua jiya ma shi ya hanani post banajin Dadi wlh kuyi hkr da wannan* *Wadan da sukeso daga farko ga link nan a k'asa kuduba ta Wattpad zaku samu ngd sosai* I think you'd like this story: "JAMI'IN DAN SANDA" by MmnYusuf on Wattpad https://www.wattpad.com/story/269145691?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=MmnYusuf&wp_originator=u5DC1AfUjn3VMvEBRA8AdWZQ%2FFF3m4j3FJj5yG9L%2B7MULqzPeCvhYv%2FmD32Q5erjhTS%2F8%2FwQtAN3lqQl4u0k7nBoC5PhqKfSSTmopPn2C8TGcX0DUDQQBtxZFOZUZVIZ Ngd [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Masu bukatar wannan littafin daga farko su duba wattpad zasu samu ga link din nan k'asa* πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ» I think you'd like this story: "JAMI'IN DAN SANDA" by MmnYusuf on Wattpad https://www.wattpad.com/story/269145691?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=MmnYusuf&wp_originator=VI1NWAufZb0tx3t77W69IEk8v6Q9Hyxe7SN13OW29bnoIlDbsBwOX40OX%2BiagGLOwiWP4bupJY75QC0AYa3IQyOf9C6cNq%2FsfKfEdhq%2FQqp3Wihagg0pTRl7AYJddvQb πŸ…ΏοΈ_34 ...................Zaune suke a falon Abba Yana jiran shigowarshi , hakanan kurum yakejin gabanshi yana fad'uwa yayinda kuzarinshi da k'warin gwuiwar shi yake raguwa , Sam baibi ta kan kayan motsa bakin da aka ajiye mashi ba, zuciyarshi tayi nisa wajan tunanin yadda mahaifinta zai kar'beshi , Sam a Ada Bai dauki maganarta da wani muhimmanci ba sai ma ganin da yakeyi duk cikin son ta 'bata mashi rai ne , Amma miyasa yanzu yakejin fargaban abunda yaji daga bakinta , _"ba abunda Abba ya tsana kamar kalma d'aya , police,_ wannan kalmar ce ke caccakar zuciyarshi da sashi fargaba ,saidai in ya tuna addu'o'in Momma akanshi sai yaji tabbas shine da nasara , Yana haka ya tsinkaye sallamar Abbansu zee cikin kamilalliyar muryarshi Mai cike da nutsuwa da tarin dattako , da sauri Hisham ya mik'e tsaye cikin girmamawa ya amsa sallamar sannan ya durk'usa har k'asa ya gayar da Abban , Cikin fara'a Abban yakamo hannunshi ya tayar dashi zaune kamun yakamo hannunshi sukayi musabaha yayinda yake amsa mashi gaisuwarshi ,sannan ya zauna Akan kujera inda Hisham ya zauna akan kafet din dake malale a wajan , "Aa Hisham hau kujera ka zauna Mana " "Cikin yin k'asa da Kai yace "aa Abba nan ma ya isa ai , nan suka sake gaisawa kamun Hisham yayi shiru Yana jiran yaji ta inda Abban zai fara, "To Alhamdulillah naji dadin ganinka a matsayin Wanda yakeson auren 'ya ta saboda a kallo d'aya naji na gamsu da yanayin nutsuwarka da Kuma tarbiyar ka Amma duk da hakan inason sanin waye Kai ,? Asalinka dakuma aikinka inyaso daga baya Ni sai nakarasa bincike akanka kamar yadda addini ya koyar ,don haka Ina saurarenka ," Jinjina kanshi Hisham yayi yace hakane Abba Kuma hakan da kayi shine dai dai , ni asalin Dan sokoto ne aikine ya kawo mahaifina wannan garin na lagos......nan dai ya fad'a mashi Dan takaitaccen tarihinshi da Kuma matsayin aikinshi , Cike da mamaki Abban yake kallonshi yace " kana nufin kai d'an wajan Asp Abdulrahaman ne ,?ikon Allah girman Dan mutum ba wuya , hak'ik'a nasan mahaifinka sosai munyi Zama na mutunci dashi ,saidai Kai bansanka ba gaskiya , sai dai ta dalilin wannan aikin naka Ina Jin sunanka sosai ,to Amma wani hanzari ba gudu ba Hisham , a hakikanin gaskiya Ni bana ra'ayin irin wannan aikin naka saboda wani dalili nawa tun fil azal Ada gaskiya ba karamun kiyayya nakema ma'aikatan yan sanda ba saboda mummunan halin da suka sanyani bada hak'k'ina ba saboda zalunci da rashin gaskiya, ta dalilin mahaifinka nafara fahimtar tabbas ba duka aka taru aka Zama daya ba mahaifinka yayimun hallacin da bazan manta dashi ba har karshen rayuwata ya bautama kasarshi da jikinshi da aljihubshi dakuma aikinshi Wanda a wannan lokacin samun irinsu yanada wuya sosai Amma mi sai gashi duk abunda yayiwa k'asarshi Bai Hana wasu daga cikin azzaluman Yan k'asar had'a Kai wajan ganin bayanshi ba ,Kuma K'iri K'iri hukumar takasa daukar wani mataki akai har Saida Kai da ya Haifa ka jajirce ka k'wato mashi hak'k'inshi ta hanyar gurfanar da wadanda suka aika mashi hakan agaba kotu hmmm wanna. Abun shi yak'ara Mani tsantsar tsanar da nayiwa aikin Yan sanda , cikin ikon Allah kai kuma sai gashi kazo har ka zarta mahaifinka ayadda kakeyin aikinka cikin gaskiya da Amana nasan bazaka rasa magauta ba musamman ma da ko manyan k'asar nan baka k'yalesu ba ,wannan yasa nake ganin bazan iya baka auren 'yata ba Hisham saboda hadarin Dake tattare da wannan aikin naka _zaka iya bada tsaro ga k'asarka Amma bazaka iya bada tsaro ga iyalanka ba_ idanun mak'iyanka zasu tashi daga kanka ne su barbazu Akan Ahlinka Hisham , tabbas zanso hada iri da Kai don Kai din zinari ne Amma mi hakan bazai samu ba sai in zaka ajiye aikinka na *Dan sanda* Tunda yafara magana zufa ke ketowa Hisham tako Ina , Abu biyu suka taro suka yiwa zuciyarshi rubdugu , na farko tuno mashi gwagwarmayar da mahaifinshi yayi da irin zaluncin da akayi mashi ,na biyu Kuma zancan da yake ta nanata mashi akan bayason aikinshi , maganarshi ta k'arshe ce ta Sanya zuciyarshi bugawa , tabbas yanason. Laurat Amma zai hakura da ita don a duniya ba abunda yakeso sama da aikinshi ,bazai taba ja baya saboda mak'iya ba, kamar yadda mahaifinshi ya jajirce to tabbas shima Koda zai rasa Ransa bazai taba ja baya ba sai inda karfinshi ya kare Kuma bazai d'agama duk wani azzalumin k'afa ba koshi waye wannan alk'awari ne, A hankali ya d'ago kanshi ya kalli Abban yace "Abba naji dukkan bayaninka ,duk da bansan dalilinka nak'in Yan sanda ba Amma inaso kasani Abba ba duka aka taru aka Zama daya ba , tabbas a ko Ina zaka samu nagari kamar yadda zaka samu baragurbi aciki ,idan har mukace zamu rink'a tsoron abunda zai faru damu ko iyalenmu to har yaushe k'asar tamu zata gyaru ne bayan a kullum muna barinta a hannun azzalumai ne doli ne mu tashi tsaye mu cire tsoro mu fuskanci kowane irin azzalumi ,Allah Yana bayan Mai gaskiya Kuma shi zai bamu nasara akansu ta hakanne zamu samu wad'ansu masu kishin k'asa su zaburo don son yin koyi damu Suma Wanda ta hakan ne zamu taru muzama tsintsiya madaurinki daya mu yake duk wani azzalumin Dake cikin kasarmu kowaye shi Amma nuna tsoronmu shi yake dakushemu a kowane lokaci azzalumai suna nasara akanmu ,bayan Kuma ba Wanda ya isa yayi maka abunda Allah baiyi maka ba , don haka Abba inason aikina sosai bazan iya barin Aiki na ba Koda kuwa Zan rasa wadda zata aureni ne , idan maganata ta 'bata maka kayi hakuri Abba, Wani gwaron numfashi Abba ya sauke yace "hakane Hisham kanada gaskiya Kuma tabbas samun irinka a k'asarmu abun alfaharin mu ne ,naji na gamasu da Kai Zan baka auren yarinya ta insha Allah kaje ka turomin magabatanka mu tsayar da magana ,sannan. Baza'a dauki lokaci ba insha Allah inason a hada aurenta Dana k'anwarta zainab , Wata madarar farinciki ce tafara kwaranya acikin zuciyar Hisham ,Sam yakasa rufe bakinshi sai godiya yake zubama Abban kamun suyi sallama ya tafi yanajin kowace k'ofa ta jikinshi iskan rahama na shigarshi ,duk da yaso yasake ganin tauraruwar tashi Amma Kuma kunyar Abba da dokin son kaima momma labari ya hanashi , BAYAN KWANA BIYU Bayan kwana biyu iyayen Hisham sukazo gidansu Laurat inda yayyu Abba su biyu suka karbi kudin aurensu tare da Sanya Rana wata ukku masu zuwa , sunga karramawa sosai daga ahalin na Abba inda suka rabu cikin mutunci Ana yabon juna , Kamar a mafarkin haka Laurat takejin zancan , lallai ta K'ara girmama girman abungiji Abu kamar Wasa Yana nema yazama gaskiya , Sam Bata kawowa kanta aurenta zai yiwu da Hisham ba saboda tsanar da Abban yayiwa duk wani Dan sanda sai gashi cikin sauki Hisham ya shawo kanshi haka ,yanzu ko ya zata kwashe da wannan Dan rainin hankalin oho , ta bangaren zee da momy kuwa kamar zasuyi mi don murna don dukkansu basa son zee tayi aure tabar yayarta a gida sai doli yanzu kuwa kamar anyi masu albishir da gidan aljanna , Bangaren momma ma hakane yau kamar zata take kan jariri tsabar murnar da take ciki ita so tayima a rage lokacin a ganinta wata ukku yayi yawa , Hisham yace."Kai Momma kamar gobe ne fa a wajan ubangiji , Kuma inada aiki sosai agabana inason nafara gyaran gidana sannan Zan Gina maki naki bangaren aciki don bazan iya barinki anan ba gaskiya musamman da mukeda nisa sosai da wannan unguwar , " "Aa Hisham Ni bazan bika ba nafi son nan Dana Saba gaskiya , " "Aikuwa bazan barki anan ba momma don haka kawai kifara Shirin tafiya " daga haka ya tashi yayi shigewarshi d'akinshi, -________________________ "Hello sir , eh sir komai na tafiya kamar yadda kace duk wani motsinshi akan idona yake , yanzu hakama Yana neman aure ne har an tsayar da Rana nan da wata ukku, " "Good big boy aikinka Yana kyau Kuma tabbas ankai wajan da nakeson akai ,yanzu abunda nakeso da Kai shine kaci gaba da aikinka ,Ni zanyi tafiya ne wajan k'asashe biyar akan wasu business nan da wata biyu Zan dawo alokacin ne Zan aiwatar da kudurina akanshi zanga ta yadda zaiyi auren ai, "Okay oga angama am oga Ina bukatar na sigari fa ba kudi a hannuna " "Kwana nawa da nabaku 10million ne kaga banason shashanci kaji ko , Kuma ya maganar wancan aikin Dana saku na Alhaji kabiru fatan dai komai Yana tafiya yadda yakamata , " "Komai normal oga yanzu haka yarinyarshi tana hannunmu sai mungama razanashi sannan zamu fara magana dashi , " "Good aikinku Yana kyau yanzu inason duk wata kadara da kuka San Alhaji kabiru ya mallaka inason d'ai bayan d'ai kufara banka masu wuta sannan komai zakuyi kuyi cikin tako Sam karku yarda asamu wata shaida da zatasa agane sa wutar akayi, zakuga alert " okay sir angama daga suka kashe wayar, _________________________ Sannu a hankali soyayya Mai k'arfi da shak'uwa suka k'ullu tsakanin Hisham da Laurat ,sosai suke zuba love kamar ba gobe ga tsantsar kulawa da suke da junansu , duk da hakan Basu daina fadan da sukeyi ba don duk lokacin da suka had'u to sai sun raba hali (da alama dai haka nasu salon soyayyar yake, πŸ˜‰) AGURGUJE BAYAN WATA BIYU DA SATI BIYU, sosai 'bagarorin biyu suke shirye shiryen bikin 'ya'yansu , Baffan Hisham yazo daga sokoto yayan Abbanshi da matarshi dakuma yayanshi sai Inna asabe itama tuni tazo sai faman shirye shirye suke , Hakama 'bangaren su laurat Yan uwansu na nesa tuni sunfara zuwa saboda gaba daya kwana goma ne suka rage adaura auren, A 'bangaren Alhaji Saminu kuwa tuni yagama shirya duk wani Shirin da zaiyi a wannan karon don yaci alwashin bazai taba Bari ayi wannan auren ba hasalima yanaso ne a kashe mashi Hisham din gaba daya aranar da za'a daura mashi auren ko Kuma Daren d'aurin auren, yaci alwashin sai ya kuntata mashi ta hanyar sawa ayiwa amaryarshi fyade a gabanshi sannan shima su aikashi inda baa dawowa, BAYAN SATI DAYA Yau saura kwana ukku d'aurin auren ayau narba akayi kamu awani shahararren hotel Wanda ya k'ayatar sosai ango da amarya sun zuba kyau sosai ran jumu'a zasuyi walima Wanda iya Mata ne kawai zasuyi sai assabar da zasu gudanar da dinner ,bayan d'aurin aure, Da misalin k'arfe 8pm tafe suke a motar da aka tanadarma amarya da ango , wani abokin Hisham ne Mai suna Yazid yake Jan motar yayinda sauran abokan angwaye da kawayen amare tuni suka tsufa a gida sai Yan wadan da baza'a rasaba na kusa dasu , saboda sun tsaya ne Saida sukaga tafiyar kowa sannan , Motar dake dauke da Zee da angonta Abdul ne agaba sai motar wasu daga cikin abokan Hisham din ,sannan tasu Hisham itace a k'arshe , tafiya suke a hankali yayinda gaba daya Hisham yake Jin kansa a wani lasalance Wanda ba komai ne ya canza mashi yanayi ba kamar wani irin sihirtaccen k'amshin turaren da yake fitowa daga jikin amaryar tashi yanashiga kowane sako da lungu na jikinshi Yana aika mashi da zazzafan sak'o , tun Yana daurewa har hakurinshi ya Gaza ya janyota jikinshi cikin kasalalliyar murya yace "irin wannan k'amshin haka baby Mai shiga jiki da 'bargo da kinsan yanayin da yake saukarmun da bakiyi amfani dashi a yanzu ba gaba daya ya tayarmun da ........bai k'arasa ba yadora hancinshi akan dokin wuyanta Yana shakar k'amshin da kyau, (hmmmm kadan daga cikin aikin hatsabiban turarruka na maman mamah Yar mutan Niger wadda take zaune a Kanon dabo GRA tanada turarruka masu gigita nutsuwar mai gida ya nemeki ko bashida niyaπŸ’ƒπŸ’ƒ 08142577927 ga number ta gamai bukata) Lokaci daya Laurat ta rikice abunda Bai taba faruwa da itaba , mutsu mutsu tafara zata kwace Basu Ankara ba saiji sukayi yazid ya taka wani wawan birki Wanda yasa suka juyo a firgice suna salati , a tunaninsu ma wani suka buge Amma abun mamaki sai gani sukayi mutane sun zagayesu kowannesu sanye da fuskar roba yayinda hannayensu ke rik'e da muggan makamai, "Hasbunallahu wa ni'imal wakel Innalillahi wa inna ilaihin rajiun shine abunda Laurat da yazid suke fad'a cike da firgici , kamun Laurat ta fashe da wani irin kuka , yazid kuwa muk'ut haka ya had'iye Dan sauran yawun da ya rage mashi , babban tashin hankalinshi shine gaba daya motocin da suke tare sunyi masu nisa sanadiyar gudun da sukeyi bare su San halin da ake ciki , Shikuwa Hisham shanyayyun idanunshi da suka Kara shigewa ciki saboda fitina ya zuba masu Yana kallonsu dai bayan dai , Cikin wani irin sauti Marar Dad'i d'aya daga cikin mutanen ya buga masu tsawa akan maza su fito waje , kamun ma ya rufe bakinshi yazid da Laurat sunfito jikinsu na mazari cikin mugun tsoron abunda zaije yazo , wata tsawar suka sake dakama Hisham Akan maza ya fito waje ,a hankali ya bude k'ofar motar ya fito shima yanayi masu kallon ido ciki ido, irin kallon nan na Kar tasan Kar, Babban cikinsu ne ya k'araso kusa da Hisham yace welcome Jamiin Dan sanda JAMI'I Mai gaskiya hhhhhhhh yaudai k'aryarka ta k'are dama can k'yaleka akayi kana tsula tsiyarka saboda baka samu daidai da Kai bane yanzu kuwa ka tabo Zaki alokacin da yake tsakkiyar farautar abunda zaici ,hhhhhhh ango ango gaskiya na tausaya ma malam Hisham , gaba dayansu mutanen suka kwashe da dariya Wanda suke su shida ne Dama saidai kallo daya zakayi masu kasan cewa sudin majiya k'arfi ne sannan Sam Babu alamar Imani ko tausayi a tare dasu , ganin yadda suke babbaka dariya Mai cike da izgilanci da rashin Imani yasa Laurat Kara fashewa da kuka tana rokonsu akan don Allah suyi hakuri karsu cutar dasu , K'arasowa babban nasu yayi kusa da ita Yana Kare Mata kallo yace " wow a gaskiya malam Hisham ka iya za'be irin wannan zukekiyar yarinya haka Kai gaskiya zamu more da yawa to irin wannan ai ko oga baice muyi Mata fyade ba to yazama doli mukwashi gara bare Kuma yace muyi , Jin wannan maganar yasa Yan hanjin Lauratu hautsinawa nan take numfashinta yafara sama sama tsabar rud'anin da tashiga da tashin hankali , Hisham kuwa ko d'ar baiji ba sai kallon ukku saura kwata da yake aika masu ......................✍🏻 *Mmn Yusuf Mai kayan mata* πŸ˜‰πŸ˜‰ *munada zafafan kayan Mata Ina sokoto Ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah maiso PC 07069711327 call or WhatsApp* [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_MALLAKAR_* ~MARYAM UMAR ABDULLAHI~ ( _MMN YUSUF_) *_________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* πŸ…ΏοΈ_35 ....................."Kai ku wuce muje ,Kuma wallahi k'wak'waran motsi kukayi sai na tarwatsa kan mutun da bindigar nan , yayi maganar yana fito da bindiga daga k'ugunshi , ai kadan yarage yazid ya saki fitsari a wando ganin bindiga kuru kuru, Laurat ma kasa motsi tayi idonta a waje cikin tsananin firgita take kallon bindigar da marik'inta , tsawar da ya koma daka masu ce tasa Laurat da yazid fara tafiya har suna kusa fad'uwa saboda rawar da jikinsu keyi, Hisham kuwa a hankali yafara tafiya Yana bin bayansu yayinda hannayenshi ke saman kanshi, bayan daya daga cikinsu yagama cajeshi tsaf ya tabbatar da baya tare da wani makami, mutum biyu ne a gabansu biyu a bayansu sai d'ayansu a gefensu na dama d'aya a gefen hagu , sunyi masu k'awanya , da yake wajan wajene da bashida hayaniya ko kad'an saboda k'arancin gidaje da abun hawa Dake wajan , Wata siririyar hanya suka bi dasu wadda ta yanka tayi cikin wani Dan k'aramun jeji Dake wajan, Tuni yaron dake hannunsu na hagu ya shagala da kallon bayan Laurat ganin yadda take tafiya ko Ina na jikinta Yana motsawa , kasancewar doguwar rigar Dake jikinta ta wani yadin material ce Mai rawa rawa anyi Mata dinki dai dai da jikinta irin dai dogayen rigunan da akeyiwa Amaren yanzu wannan yakara taimakawa wajan bayyanar asalin hallitanta ,kallonta yake Yi Yana lashe Baki kamar tsohon maye idanunshi kuwa tuni sun k'ara rinewa tsabar jaraba Allah Allah yake suk'arasa ya far Mata don yasan ba karamar gara zai kwasa ba, Kai sikam gaskiya Yana ganin yafi kowa Jin Dadin wannan aikin da zasuyi, ............duk halin da yake ciki Hisham na kule dashi , aikuwa ji yake kamar Ana tsatstsaga zuciyarshi da wuk'a wani kallon gefen ido yakema mutumin cikin wani irin 'bacin rai na bala'i ,lokaci daya shima idonshi suka riked'e suna fidda wani irin yaji acikinsu ,ga wani k'aton Abu da yazo ya tokare mashi mak'oshi kamar zai hallakashi da k'yar ya had'iye wasu yawu masu d'aci Yana tunanin yadda zaiyi dasu , Kasa hakuri mutumin yayi ya d'aga hannunshi zai shafi duwawun ta da suke fisgarshi awar mayen k'arfe duk ta rud'ashi har ya manta abakin aiki fa suke, .......tuni Hisham ya ankare da abunda yake Shirin yi , aikuwa cikin tsananin zafin nama irin na Wanda yasamu kwararren training ya fisge k'atuwar addar Dake hannun mutumin Dake hannunsu na dama kamun kace mi yakawo hannun wannan gayen Sara , aikuwa Basu ankaraba sai ji sukayi mutumin ya buga wata irin k'ara wadda Saida Dan k'aramun dajin ya amsa kuwa ba karamun razana sukayi da Jin karar tashi a bazata , wannan yasa duk suka juyo kanshi a sittin.kamun sugama fahimtar abunda ke faruwa tuni Hisham yayi wani tsalle kamar d'an biri sai gashi agaban babbansu Wanda shine yake rik'e da bindigar , cikin second yabashi wani uban naushi afuskarshi Wanda yasa shi daukewar wuta na wuccin gadi , kamun yagama dawowa dai dai Hisham ya fisge bindigar ya Kara maka mashi wani nauyayyan naushi a muk'amuk'inshi , take k'aton mutumin ya zube k'asa warwas jini na fita ta hancinshi da bakinshi , duk wannan abun yafaru acikin Yan seconds Laurat da yazid sun rud'e sosai , ganin abunda yafaru ga hannun wannan mutumin Yana reto don k'iris yarage ya guntule hannun, ganin abunda yafaru da ogansu yasa daya daga cikinsu Kama yazid ya d'ora mashi k'atuwar wuk'ar Dake hannunshi a wuyanshi Yana kallon Hisham cikin fusata yace "Ka ajiye bindigar nan kayi saranda ko yanzu na fille mashi Kai wallahi ," Hisham kuwa saitasu da bindigar yayi Yana huci yayinda ya janyo hannun Laurat ya mayar da ita bayanshi , jikinta Banda cira ba abunda yakeyi tsabar rikicewa da rudani yasa ko kukan ma takasayi kana kallonta kasan tuni ta fice a hayyacinta, Jin abunda mutumin yake fad'a yasa yazid sakin fitsari Babu shiri tuni idonshi sun Raina fata musamman da ya ga yadda Hisham ke tsaye ya saitasu da bindigar Sam bashida niyar sauketa kamar yadda suka buk'ata saima tsananin fushi da yake hangowa acikin idonshi, Batare d'a Hisham ya kula ba daya daga cikinsu ya jefa mashi wani k'aton dutse a hannunshi Mai rik'e da bindigar , take bindigar tayi tsalle tafadi can nesa dasu cikin ciyayin Dake wajan, aikuwa ganin hakan yasa suka nufoshi su hudu da addunasu da niyar su sassara shi , kamun kace mi wajen ya har mutse Sara da suka suke kawo mashi kota Ina Amma cikin ikon Allah ba Wanda yake samunshi , sun dauki 5mnt ahaka kamun yasamu nasarar kwace addar daya daga cikinsu yafara Kare kanshi da ita , cikin kwarewa da sanin makasar mutum yarinka samun sa'arsu Yana naushinsu agefen wuya kamun kace mi duk sun zube a wajan suna murkususu rik'e da wuya Wanda sukejin kamar ransu zai fita saboda ba karamun naushi yayi masu ba , wayarshi ya fito da ita yafara Kiran yaranshi , ba'a dauki lokaci ba sai ga amintattun yaranshi su Jafar da asmy da sawu mutum hudu , Kusa da babbansu Hisham ya tsaya Wanda har lokacin baigama dawowa dai dai ba , k'afarshi yasa ya dakeshi ak'irji tare da buga mashi wata irin tawa yace "uban waye ya aikoku wajena ,?wane Mai gangancin ne yake neman shiga gonata " Cikin rawar jiki data murya ogan yafara magana a galabaice yace "deputy Governor ne Alhaji Saminu Sulaiman don Allah kayi hakuri yalla'bai, batare da Hisham yace komai ba yabawa yaranshi damar kamasu su tafi dasu , nan take suka tarkata mutanen suka sasu a mota sukabar wajan a guje , Juyawa Hisham yayi Yana kallon yazid da Laurat da har lokacin Basu Gama dawowa normal ba , dafa kafadarahi Hisham yayi yace "kayi hakuri abokina kuzo muje ,hannun Laurat ya riko suka fara tafiya , binshi takeyi kamar rakumi da akala don Sam takasayin tunanin komai ,motarsu suka shiga wannan karon Hisham ne ya tuk'a motar don ya tabbatar da yazid bazai iya tuki ba a wannan halin, tafiyar kusan minti 15 ce ta kawosu gidansu Laurat Wanda sun tarar su zee tsaye abakin get din hankali a tashe suna tunanin abunda ya tsayar dasu wani ikon Allah Kuma ba Wanda yy tunanin kiransu a waya, Kallon ta yayi har yanzu a hargitse take yace " yakamata ki sa nutsuwa a ranki don karsu fahimci abunda yafaru , sannan ban yarda ki gayawa kowa abunda yafaru ayau ba kirik'eshi aranki wannan umurni ne ,d'ago kanta tayi ta watsa mashi wani mugun kallo cikin tsiwa da fad'a tace "aikuwa yazama doli na fada don bazan ta'ba gangancin aurenka ba a wannan yanayin Ni ban shiryama mutuwa ba wallahi haka kawai bazaka cajamun tashin hankali ba , inkuwa har ka nace kana Sona to tabbas saidai ka ajiye wannan aikin Naka da Babu kwanciyar hankali a cikinshi , Ina dalili tunda nake ban taba shiga tashin hankali irin wannan ba sai yanzu tarayyata dakai aa wallahi da sake da............."keeee ya isa hakan fita kibani waje karki Kara batamun Rai kinzo kinsa wani shegen Riga da wani figaggen kyale kinsa sai wani kallonki ake Baki barni da wannan 'bacin ranba Zaki karamun wani oya don Allah malama kificemun a mota Kuma Kar Allah yasa ki k'i yin abunda nace , Gaba daya wutar Laurat ta dauke gaskiya tayi Mata yawa har takasa cewa komai , tana hango tsananin kishinta a idanunshi Wanda komai zai iya faruwa in taci gaba da Zama kusa dashi , bude motar tayi a hankali ta fita batare da tak'ara kallon inda yakeba tayi shigewarta gidansu da yake su zee tuni sun koma ciki tun lokacin da suka ga isowar motarsu, Cikin sa'a kuwa ta tarar da ba mutane a falon da sauri ta wuce bedroom din su ,tana shiga tafara cire kayan jikinta tana jifa dasu tana hawaye , toilet ta shiga ta sakarwa kanta ruwa tana kuka Mai cin Rai da anbaton innalillahi wa inna ilaihin rajiun , wannan wane irin bala'i ne k'asarmu take ciki , Wanda manyan k'asar ma sune da kansu suke aikata rashin adalci ga talakawansu yanzu badon Allah ya tsare ba da shikenan hakanan kattin banza zasu keta Mata alfarmarta Wanda tajima tana tanadawa tsayin shekaru bataji ba Bata gani ba batasan tsakaninsu ba saboda kawai rashin tsoron Allah da rashin Imani, tajima a bandakin Saida taji mutane sunfara taruwa a d'akin sannan ta daure tayi wanka ta fito rik'e da kanta Bata kulasu ba tafara Sanya kayan baccinta duk kuwa da maganar da suke Mata tana gamawa ta haye gado ta lullube kanta bayan tace masu kanta ke ciyo, ............................... Tunda tafita daga motar ya fisgeta a fusace yabar k'ofar gidan yazid sai hakuri yake bashi ,duk da akasan ranshi Sam baiga laifin Laurat ba don ta tsorata ne shi kanshi har yanzu a tsorace yake don har ya sare ga sake rayuwa ,shima gidansu ya kaishi bayan sunyi sallama ne ya juya ya dauki hanyar gidan Alhaji Saminu cike da fushi , (tau faπŸ™Š) A hanya ya tsaya yayi sallar Isha Wanda dama basuyi ba sannan yak'arasa gidan , Mai gadi ne ya leko Jin Ana hon , bude k'aramar k'ofar yayi yafito ya nufi Hisham Yana zuwa yace " bawan Allah wa kake nema ne , "Deputy Governor nake nema fatan Yana nan , " " Eh Yana nan saidai baya ganin bak'i a daidai wannan lokacin Kuma Bai ce akwai Wanda zaizo wajansa ba don haka kayi hakuri ka koma ko ka kirashi kanemi izini awajanshi, " "Aa bazan koma ba akwai buk'ar ganin nashi ne a yanzu , kasancewar securityn Jami'in dan sanda ne yasa Hisham fito da l D dinshi ya nuna mashi, take security ya Sara mashi kamun ya juya da sauri ya bude mashi get din gidan ,a tunaninshi wata matsalar ce ta taso , Parking Hisham yayi a tsakkiyar filin wajan , Bai damu da inda ya ajiye motar ba ya fito ya doshi wasu ma'aikata Dake d'an nesa dashi , Suma ID dinshi ya nuna masu kamun ya tambayesu inda zai ga maigidan , Wani part Mai shegen kyau suka nuna mashi tare da gayamashi Amma Yana meeting ne ,Bai sake bi takansu ba ya doshi part din kamar gidan ubanshi Sam Babu tsoro ko fargaba atare dashi, Bakin k'ofar ma wasu securitys ne suna ganin ID dinshi suka barshi ya wuce da tunanin k'ila shima Yana cikin masu meeting din, Baijira komai ba ya bude k'atuwar k'ofar da yake kyautata zaton anan ne suke meeting din don Yana jiyo maganganunsu sama sama , Da sauri duk suka juya Jin aturo k'ofar falon batare da neman izininsuba cikin tsananin mamaki Alhaji Saminu Sulaiman ya mik'e tsaye Yana nunashi da yatsa yayinda sauran mutanen ma suke binshi da kallon mamaki da raini ganin yadda ya shigo masu ba sallama bare neman izini gashi ya tsaresu da ido Yana yi masu kallon ukku saura kwata, A gefe d'aya Kuma tunda aka budewa Hisham k'ofa Amna na tsaye saman bene tana hangen shigowar motar , ganin batasan motar waye ba yasa ta kafe motar da ido, ba k'amun bugu k'irjinta yayi ba lokacin da tayi arba da daurarriyar fuskar Hisham Mai cike da fushi da kwarjini, ,idonta ta lumshe tasake budewa akan kyakyawar fuskar shi, duk da dare ne Amma tarr take hango fuskarshi saboda kwayayen lantarkin da suka haska gidan kota Ina fess tamkar Rana ,a hankali ta furta wow tana kallonshi har lokacin da ya nufi sashen mahaifinta , atake ta yanke cewa tabbas tasamu mijin aure irin kalan da takeso kenan miji na nunawa sa'a son kowace mace ,don tafiyarshi kawai ta Isa ta nuna mata shidin jarumin namiji ne ,kiss tayi ta hura mashi Wanda shi baimasan tanayi ba har yayi shigewarshi ,aguje ta juya daga inda take tafara saukowa daga benen tana k'walawa mom Kira, "Kai matsiyaci ubanmi yasa ka shigomin gida kuma har nan cikin falo na ,da izinin ubanwa kayi wannan gangancin, lallai tsagerancinka yayi yawa Amma Zan nuna maka naka kadan ne,"yafada Yana huci da mamakin ya akayi suka tsira bayan su yaran sun kirashi sun tabbatar mashi da cewa suna hannunsu a d'azu, Batare da Hisham yayi magana ba yafara tafiya , kukerar da ba kowa ya janyo ya zauna ya Dora k'afarshi daya akan daya ya kallensu a dak'ile yace, "Minene dalilinka na son shiga rayuwata minene a tsakaninmu da kakeson ka 'batamun Rana Mai matukar muhimmanci a gareni , ? Kasan wahalar da nasha kamun nasamu yarinyar nan kuwa yafad'a Yana jujjuya hannunshi fuskarshi Sam bazakace Yana cikin damuwa ba Kuma magana yake hankali kwance kamar baisan girman abunda yake aikawata ba, yaci gaba da cewa , Anya Kai kasan girman soyayya kuwa , ? Soyayyar da nasha wahala kamun nasameta shine kukaso ku wargaza tare da dukkanin burina a Rana d'aya ?? Ku a tunaninku hakan zai yiwu cikin sauki , hmmm yayi wani murmushi na tura haushi kamun yaci gaba da cewa , a gaskiya da wani abu yasamu matata da bazance ga abunda Zan aikata ba wannan yasa nazo nayi Jan kunne da fatan za'a kiyaye , " "Kai yaro ka iya bakinka tun kamun ka tsinci takalmanka a hannu bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane yanzu sai nasa a 'batar dakai daga duniyar ma Baki daya , matsiyaci dan talakawa kad'ai har kanada k'warin gwuiwar shigomin gida ka gayamun magana to wallahi sai Naga uban da ya daurema gindi aduk fadin k'asar nan da har kake iya kallon idona ka gayamun magana," "Ok badai zaka janye ba kenan , ? Cewar Hisham ,yaci gaba da cewa to shikenan idan zaka turo yaran naka yakamata kasan irin wadan da zaka tura , ba ririn wadan da ka tura yau ba , kaje ka turamun wasu Yan koyo sunsa fad'an ko wani armashi baiyi ba mrtss ,Kuma wallahi wallahi kajawa d'anka kunne idan har yasake aikata abunda ya aikata wlh zakuyi Dana sanin sanina da kukayi wannan shine gargadina na karshe a gareku , na barka lafiya, " Yafada Yana juyawa "Idan yak'i kiyayewar fa mi zakayi ? "Banason na fad'a maka abunda zanyi ne ai ," " To shikenan kaje kayi duk abunda zakayi nikuma a lokacin Zan iskeka har office Dinka da takardar k'arin girma ," Murmushi Hisham. Yayi yace "to godiya nake ranka ya Dade , fatan alkhairi, yafada Yana sarama Alhaji Saminu kamun ya juya ya fita har lokacin da murmushi a fuskarsa Wanda a zuciyarshi sam ba haka bane wani irin zafi da Kuna yakeji mussaman in ya tuna kukan Laurat da maganganunta , Fitowarshi tayi daidai da zuwan Amna wadda takasa hakurin har ya fito ta biyoshi , ganin murmushin fuskarshi yak'ara dulmiyawa da ita wani irin narkewa zuciyarta tayi da sonshi yayinda ta kankame hannayenta ajirji tareda lumshe ido tana shak'ar k'amshin turarenshi , har yazo ya giftata batasani ba da sauri ta bude idonta tabi bayanshi da Dan gudunta don yanayin tafiyarau ba daya , sanye take da mini siket Baki sai farar Riga wadda takamata sosai da kadan ta rufe cibiyarta , kanta ba dankwali sai dogon gashinta da yazubo har bayanta Amna kyakykyawa ce ajin farko kana ganinta kaga bafulatana sannan tana kamanni da Zayyan sosai kasancewar duk mahaifiyarsu suka biyo, Har ya bude motarshi ya shiga ta k'araso tana haki hannu ta d'aga mashi cikin muryarta Mai Dadi tace HI πŸ‘‹πŸ» kallonta yayi a d'age take ya hango tsantsar kamanninta da Zayyan , maida kallonshi yayi ga shigarta Yana mamaki Wai a haka diyar musumai ce mrtssss tsaki yayi kamun yayi ribos da k'arfi Wanda Saida Amna ta Fadi saboda yadda ta jingina da motar , bai ko bi ta kanta ba yabawa motarshi wuta yabar gidan , inda yabar Amna cike da tsananin begenshi a zuciyarta Sam bataji haushin abunda yayi Mata ba saima burgeta da yayi Kuma taci alwashi sai yazama mallakinta ko Ana ha maza ha Mata , (tofaaaaπŸ˜…aiki yasamu Mata) Hisham Bai koma bi takan Laurat ba kamar yadda itama ta shareshi saidai takasa fadawa kowa abunda yafaru,kamar yadda yabata umurni, Allah yagani tana k'aunar Hisham fiye da tunaninta Wanda batasan lokacin da zuciyarta ta afka haka ba wannan yasa takasa fad'a don in Abbanta yasani wallahi tsaf zai Hana auren nan ,sai dai tasan tabbas rayuwarsu na cikin hadari in akaci gaba da tafiya a hakan, , (Ashe duk burgar banza ce🀣🀣) A yau Assabar aka daura auren Laurat da Hisham Akan sadaki 50k taro yayi taro manyan k'asar sunzo sosai mussaman manyan jami'ian Yan sanda, da Governor da tawagarshi Mataimakin governor ne dai baizobaπŸ˜‚anyi shagali sosai inda bayan d'aurin aure maza suka dunguma hotel din da aka Kama don yin liyafa yayinda wajan Mata suka zarce da yinin biki , k'arfe 8pm aka fara gudanar da dinner wadda ta k'ayatu sosai saidai amarya da ango sun Sha kunu kowannesu cike yake da Dan uwanshi, k'arfe 10pm aka tashi daga dinner din inda aka wuce da amarya gidanta ....................✍🏻 *To alhamdulillah ,masoya da abokan arziki inason in shaida maku cewa littafin Jami'in dan sanda yakoma na kudi sakamakon rashin comment da bana samu daga wasu sai Yan k'alilan don haka duk maiso tabiya 200 nasata a paid grp Kuma insha Allah zakurinka samun post akai Kai don musamu mugashi da wuri Wanda dama rashin comment dinne ke.dakatar Dani daga typing Koda yaushe, maiso tamun magana ta wannan number. 07069711327 WhatsApp kad'ai pls , Banda Kira , zaku turo ta account kokuma katin MTN ngd sosai Allah yabar kauna* *Mmn Yusuf* [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA* πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_* *_wannan littafin na kudi ne a yanzu yakoma na kudine saboda wasu dalilai maiso tabiya 200 ta karanta 07069711327_* πŸ…ΏοΈ_36 .........................Masha Allah gidan amarya ya had'u iya had'uwa komai a tsare kana kallon gidan kaga gidan 'yan Boko Sam ba wata kwamacala aciki komai an ajiyeshi inda yadace , 'Yan kawo amarya sai yaba kyau da tsarin gidan sukeyi , ahaka suka nufi sashen da akayiwa momma acikin gidan don damk'a Mata amanar amarya Lauratu , Sanye take da wani Cotton less bak'i Mai adon fararen duwatsu sai Wal Wal sukeyi , anyane Mata kanta da farin gyale Mai masifar kyau takalminta da Jakarta ma farare haka sarkarta da awarwaraye Masha Allah tayi kyau har tagaji ga uban k'amshin Dake tashi a jikinta Mai masifar Dadi da shiga Rai , a hankali sukayi sallama abakin k'ofar Fallon , amsa Masu akayi da Basu izinin shigowa , wata k'anwar Abbansu ce rik'e da hannun Laurat a hankali take Jan hannunta har suka k'arasa gaban momma sannan ta zaunar da ita ak'asa kusa da k'afafun momma nan suka shiga gaisawa da gabatar da amarya , falon na momma cike yake da 'yan tarbar amarya su Inna Indo da wasu daga cikin dangi da sukazo daga sokoto sai kawayenta wanda mafi yawansu matan abokan mahaifin Hisham ne , Anyi masu tarba ta mutunci sosai Inda momma ta janyo Laurat ta d'orata akan kujerar da take zaune ta rungumeta tace " kudaina wani wahalar da kanku na cewa kunbani amanar Lauratu ,don Lauratu ba a matsayin sirika zata zauna Dani ba amatsayin 'ya take a wajena , Allah yagani inason 'ya mace sai gashi Allah Bai baniba yanzu kuwa gata nasamu ta sanadin 'Dana don haka karku damu Laurat tana tare da mahaifiyarta fatanmu dai Allah yabasu zaman lafiya da zuri'a masu albarka , dukkansu da Amin sun amsa cike da farincikin kalaman Momma , sannan sukayi masu sallama tareda mik'a amarya sashenta sannan sukabar gidan , Zaune take ita kad'ai a tsakkiyar gado ta lullube kanta da gyalenta har fuskarta kamar dai yadda akasan amaryar hausa fulani, gaba daya zuciyarta a hautsine take , Tama rasa tunanin da zatayi , tunda abun nan yafaru komai nata ya canza tayi sanyi sosai kullum cikin zullumi da fargaba take ,tunani take Anya kuwa tayiwa kanta adalci , Anya Bata Sanya kanta a had'ari ba ,auren Wanda ake farauta ido rufe takowane fanni , wata zuciyar tace Mata _aa Laurat bakiyi ganganci ba hasalima auren mutum kamar Hisham abun alfaharinki ne mutumin da ya tsaya iya gaskiyarshi yake yiwa k'asarshi aiki yake yak'ar azzaluman cikinta Wanda yakawo sauyi sosai acikin garin nan , Wanda da Babu irinsu to da k'asar mu tak'ara shiga garari fiye da Wanda take ciki a yanzu , Kuma Allah Yana bayan Mai gaskiya insha Allah Babu abunda zai faru sai alkhairi, kiyiwa mijinki kyakyawan fata Kuma ki tayashi yaki Akan makiyanshi sannan ki k'arfafa mashi gwuiwa akan aikinshi_ , jinjina Kai tayi tana amanna da wannan shawarar ta zuciyarta insha Allah zata cire komai ta kula da mijinta Kuma duk Wanda ya ta'ba Mata miji to sai inda karfinta ya kare , don tasan ba abunda mutum ya isa ya yayiwa wani mutum sai dai in dama can kaddararka a hannunshi take, Wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali taji suna shigarta duk wani tsotonta da fargaba sun fice Mata fitttt ( haba kokefa jaruma Matar jarumi🀣🀣🀣) Dirin motoci ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi , ai take wata sabuwar fargaba ta shigeta tana tunanin ko ya zata kwashe da wannan Dan rainin hankalin oho, Hisham ne da abokanshi su hudu Wanda sukayi mashi rakkiya , duk da yace bayaso haka nan suka nace Saida suka biyoshi, wajan Momma suka fara shiga suka gaisheta inda Inna Indo tashiga tsokanar Hisham Ana dariya Bai tanka Mata ba sai harara da yake banka Mata , momma tace "kaci gidanku Hisham uwar tawa kake harara ne , " "Barni da Dan banza Inka matsamun yanzu sai naje na dauke amaryar Inga ta tsiya , " wani murmushi yayi yace inkin fasa ban gode maki ba, " duk dariya suka Sanya ganin yadda yayi maganar nan dai sukayi masu sallama suka nufi sashen ango da amarya , suna shiga ya tsayar dasu anan falo yace " to Masha Allah rakkiyar ta Isa haka don wallahi Babu k'aton da zai kallemun Mata abanza , ku ajiyemun ledojin anan kuyi tafiyarku nagoda sosai Allah ya huta gajiya, Dukkansu Baki suka saki suna kallonshi dayan yace " tooo lallai ma mutumin nan mu zaka Kora don kaga mun gama maka wahala ko , Ibrahim Yana dariya yace kunga ku barshi kuzo muje muma Allah ya kaimu mu Rama , " "Amin" hisham yace Yana turasu Akan sutafi yarufe k'ofar , yazid yace " to Allah dai ya shiga tsakaninka da wannan amaryar irin wannan daukar hankali karkaje ka halaka Yar mutane shiyasa Ni da 'ya ta bazan bawa tuzuru ba wallah , "Eh naji dai kutafi Allah ya kiyaye hanya ,hakan suka fita suna dariya shikuma ya kargame kofa, Duk rigimar da sukeyi tana jinsu , tana mamakin wai wannan wane irin Hali gareshi ne mutane suzo maka lalura amma kana wani korarsu , to Allah ya kyauta , Sallamar shi ce ta katse Mata tunanin ta inda zuciyarta taci gaba da bugawa , da kyar ta amsa sallamarshi cikin sanyin muryarta, A hankali yafara nufo inda take yanajin wani irin farinciki Wanda Bai taba Jin irinshi ba hannayenta ya zubama ido yadda suka Sha kunshi ja da Baki Wanda ya kwanta lif akan fatarta Zama yayi kusa da ita Yana cewa "Kinga bude fuskarki nagani don Ni ba wani Baki da Zan siya yafada Yana kumshe dariyarshi don son ya takarota , aikuwa yayi nasara don take tafara cika tana batsewa saidai batace komai ba Kuma Bata bude fuskarta ba, hannu yasa ya yaye Mata mayafin , take yafara tasbihi ga Allah acikin zuciyarshi yayinda wani sihirtaccen k'amshi ya bugi hancinshi Wanda har Saida ya lumshe idonshi da k'arfi Yana Kara bude kofofin hancinshi Yana shakar k'amshin , (hmmm turaren mmn mamah kenan karku Bari abaku labarinshiπŸ˜‹) sake bude idonshi yayi ya sauke akanta Wanda tuni idanun nashi sun lumshe sosai Yana Kare Mata kallo , ba zato saiji tayi ya fisgota ya had'ata da jikinshi yabata wata kyakyawar runguma inda ya Dora kanshi akan wuyanta yanajin kamar ya shige cikin jikinta saboda yadda k'amshin jikinta ke fisgarshi , mutsu mutsu tafara zata kwace zuciyarta na bugawa Amma takasa don ba karamun riko yayi Mata ba har tagaji tayi luf ajikinshi yayinda zuciyoyinsu ke bugawa fiye da misali, sun Dade a hakan kamun ya dagota a hankali cikin kunnenta ya ce " ke tashi ki ciyar Dani kizo mu kwanta bacci nakeji," zaro ido tayi waje tana mamakin kalamanshi kamar ya ta ciyar dashi Kuma, Wai wannan wane irin ango ne Allah ya hadata dashi itakam , wato itace ma zata ciyar dashi a maimakon shi ya ciyar da ita lallai wannan ko acikin Yan rainin hankali shi oga ne , kwace jikinta tayi taja baya tana gunguni , baiji abunda take Fadi ba yakula bakin tsiwar ya mutu yau, "To tunda bazaki ciyar Dani ba to Ni Bari na ciyar dake Amma kisani Ni bazan ciyar da ke.abanza ba doli sai........ Bai karasaba ya saki wani munafukin murmushi , kamun yace je kiyo alwala muyi nafila , batace komai ba ta tashi tanufi bandakin inda ya Rakata da ido Yana dariyar mugunta, bayan ta fito shima shiga yayi yayi alwala ya fito inda yajasu sallar raka'a biyu sukayi inda yayi Mata tambayoyi Akan addininta Kuma alhamdulillah tabashi amsa yadda yakamata , daga nan yaje falo ya dauko masu kayan da su Ibrahim suka siyo masu , bayan ya ajiye yakoma kitchen ya dauko filet da wuk'a sai kofuna biyu ya dawo har lokacin tana inda yabarta a zaune , nan yazuba masu gasasshen nama Wanda yaji Hadi sosai sannan yazuba masu fresh milk nan yafara Bata abaki tun tana kin ci har tafara amsa Bata wani ci da yawa ba tace ya isheta , aikuwa nan ya birkice Mata akan doline itama tabashi abaki kamar yadda yabata , cikin matukar kunya da nauyi tafara bashi Naman yanaci Yana korawa da milk bayan sun Gama ne ta tattare wajan sauran kayan tasa a frij , duk da yaso su watsa ruwa Amma hakan ya gagara saboda wata irin masifaffar sha'awa data taso mashi Wanda har yake mamakin dama yanada sha'awa irin hakane aikuwa nan yayiwa Lauratu daukar jarirai ya nufi gado da ita. Hakika Laurat taga soyayya wadda Bata taba tunanin zata samu makamanciyarta ba , Bata taba kawowa ranta Hisham Yana kaunarta har hakaba Tasha ruwan kalamai har tarasa inda zata sasu ,gaba d'aya ya gigitata da salon soyayyarshi Wanda har hakan yasa ta iya jurema bukatarshi batare data nuna gajiywa ba gefe daya Kuma hawayen farinciki takeyi da adduar Allah ya basu zaman lafiya, Hisham ma Yana cikin farinciki sosai don ya tsinci kanshi a yanayin da Sam baiyi zato ba ,wannan yasa yaji duk duniya bayan momma yanzu ba abunda yakeso kamar Laurat yanajinta a kowane sako da lungu na jikinshi , haka ya kwana yana sallah Yana mika godiyar shi ga Allah da irin baiwar da yayi mashi don tabbas matarshi Yar baiwa ce, Kasancewarta Likita yasa tun a Daren tabawa kanta duk wani taimako da ya dace da, WASHE GARI K'arfe 9 Momma ta Aiki Aisha Yar wajan Baffansu Hisham ya kawo masu breakfast dinsu , lokacin Bata tarar da kowa a falonba sai kawai ta ajiye akan table tayi tafiyarta , sai wajan goma saura suka farka daga nauyayyen baccin da kwashesu bayan sallar asuba , wanka sukayi suka shirya cikin shadda iri d'aya kalar sararin samaniya inda akayiwa Hisham dinkin da gayu ke yayi a yanzu anyi mashi kwalliya da zare kalar blue mai duhu inda hularshi da takalminshi ma suka Zama blue Mai duhu yayinda fuskarshi ke fitar da wani irin annuri na anganci, gimbiyar kuwa doguwar Riga aka Mata wadda Tasha fentwork blue yayinda gyalenta da takalminta suka kasance kalar aikinta , Masha Allah ga sihirtaccen k'amshin jikinsu daya hade Dana juna kana kallonsu kaga ango da amarya Wanda suka dace da junansu , ahaka suka fito falo ,nan suka karya sam_sama kamun suka nufi sashen Momma don gaida ita da bakin da Basu Gama tafiya ba, Tunda suka doso falon Momma ke zuba murmushi bakinta yakasa rufuwa sai Masha Allah take fad'a , sallamar su CE ta ankarar da mutane falon isowarsu aikuwa nan aka yayyabesu Ana yabawa da kyawunsu ,har k'asa suka durkusa suka gayarda Inna Indo da Matar Baffansu inda sauran yaran suka gaidasu sumu , kamun suka mike suka nufi inda momma take wadda Sam takasa dauke idanunta akansu , Laurat zata duka momma ta tarota da sauri inda tahadata da Hisham ta rungume tana maimaita kalmar alhamdulillah, Laurat nauyi da kunya hade da soyayyar Matar ne suka cikata , cike take da farinciki sa'ar sirika da tayi tun jiya da aka kawota Taji kalaman da tayi akanta take Jin kanta sakayau tanaji aranta bazatayi missing mahaifiyarta ba tunda tana tare da momma , sunjima a sashen har Saida Yan uwan Laurat suka fara zuwa ganin daki sannan ta koma 'bangarenta inda Hisham ya fita wajan abokansa badon yaso ba , BAYAN SATI BIYU Soyayya ruwan Zuma , wata irin soyayya ake gudanarwa tsakanin Hisham da Laurat tuni sun cure sun Zama Abu daya sunajin in Babu dayansu dayan bazai iya rayuwa ba , hakama tsakanin momma da Laurat zamansu abun sha'awa komai Bata Bari momma tayi tana Bata girmanta sosai Inda kullum momma ke Kara alfahari da ita tare da Taya Dan ta murnar sa'ar Matar da yayi , a yau Monday hutunsu ya kare zasu koma aiki , inda. Hisham ya siyawa Laurat mota Yar karama Mai shegen kyau don zuwa aiki , ahaka sukaci gaba da gudanar da aikinsu hankali kwance Wanda so da yawa kamun su dawo momma ta dafa masu abinci basuda matsalar komai , duk da Sam Laurat batason yadda momma ke wahalar da kanta wajan Yi masu aikin abinci tafiso tabari idan ta dawo ita sai ta dafa masu ...............fatan alkhairi Laura Hisham😍😍😍 *Hmmmmmmm tana k'asa tana dabo* *Masu bukatar wannan littafin su biya 200 nasasu a grp don daga next page bazan sake turashi ko inaba sai Wanda suka biya* [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA* πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_* *_Wannan littafin na kudi ne a yanzu maiso tamun magana zaku biya 200 only ta account ko katin MTN 07069711327_* πŸ…ΏοΈ _37 ......................Bafa zaka samu yadda kakeso ba ta wannan hanyar , abun ya dauremun Kai sosai a binciken da nayi na gane cewa yaron nan yanada d'aurin gindi sosai ga manyan k'asar ciki kuwa harda shugaban k'asa wannan yasa yake duk wani bura'uba ak'asar nan , yanzu haka naji rad'e rad'in cewa za'a kara mashi girma zuwa babban matsayin na I.G na Nigeria Baki daya ,mi kake tunani in hakan ta faru ?baka tunanin hakan zai iya kawo Mana cikas sosai a harkar kasuwancin mu ,? kawai duk yadda zakayi kayi ka kashe yaron nan gaba daya kowa ya huta don zamanshi a raye ba k'aramar barazana ne ga rayuwarmu ba , dama dai kasan nasan bawai saboda abunda yayi wa yaronka kakeso ka dauki fansa akansa ba kawai ka la'be ga sabara ne kana Harbin barewa don haka yakamata muyi Mai yiyuwa gaskiya komai Yana gaf da lalacewa, cewar Alhaji Ilyas babban Dan kasuwar da akeji dashi a fadin garin na Lagos Kuma abokin kasuwancin Alhaji Saminu Wanda Allah ne kad'ai yasan tsakaninsu Amma tabbas duk abunda suke kulkawa to ba na alkhairi bane , lokacin da Hisham yazo gidan Alhaji Saminu Alhaji Ilyas Yana d'aya daga cikin wad'an da ya tarar dasu a falon tun daga lokacin yafara bincike Mai tsauri akan Hisham don ason samunsu shine Susa a saukeshi daga kan muk'aminshi inda halima a aikinshi gaba d,aya , sannan su wulakanta rayuwarshi kamun su aikashi inda ba'a dawowa Wanda hakan zai K'ara tsoronsu a zuciyar sauran Jami'an Dake son shige masu hanci da kudundune , Tunda Alhaji Ilyas yafara magana yake zagayen falon hannayenshi goye a bayanshi , cikin tsananin fushi yafara magana "Aa Alhaji Ilyas bazan taba kasheshi a yanzu ba doli saina wahalar da rayuwarsa baisan wanene Saminu ba da Bai shigo har cikin gidana ya gayamun magana ba bayan yagama zautamun yarinya yanzu gaba d'aya yadda kasan mahaukaciya haka Amna ta koma akan doli shi takeso Ni kuwa Dana barta da wannan tsageran yaron nafison Naga gawarta , yasha shigarmun hanyar harkokina Wanda baida masaniyar nawa ne wannan yasa nake daga mashi kafa saboda banason a fahimci abubuwana sai gashi tsautsayi yasashi taba yarona wannan yasa na fake dashi don daukar fansa don a Yan watannin nan ba k'aramar Aasara ya jazamun ba, don haka tabbas sai nabi duk wata hanya da yakamata nabi don kuntata rayuwarshi ,sai nasa yayi mutuwa dubu kamun yayi daya kwakkwara, muje zuwa Hisham ya furta hakan cin tsawa da huci, Girgiza Kai Alhaji Ilyas yayi yace aa abokina kawai kayi yadda nace don wallahi Dan hakin daka Raina shi yake tsone maka ido kayi maganinshi tun kamun lokaci ya kure maka , don haka Ni Zan tafi kayi tunani, " daga haka yabar gidan shakatawar Dad din inda mafi yawa anan suke gudanar da duk wani abun da ya shafe kasuwancinsu , (ko wane irin kasuwanci ne wannan πŸ€”) Sanye take da wando fari iya gwuiwa sai karamar Riga Mai hannun bes red ,tana zaune a k'asa ta had'a kanta da kafafunta inda dogon gashinta ya barbazu a saman kafadunta da fuskarta kuka take kamar ranta zai fita lallashin duniya mom tayi akan ko breakfast ta tashi tayi Amma Taki , tsawon sati biyu kenan tana cikin wannan halin tun lokacin haduwarta da Hisham acikin Daren ta gayawa Daddyn ta shi takeso aikuwa take ya zabga Mata wawan Mari in da ya tabbatar Mata da ko maganar wannan yaron yasake ji daga gareta to sai ya kusa kasheta agidan , a yanzu babbar damuwarta Bai wuce na rashin sanin inda zata sake saka wannan saurayin a ido ba hasalima batasan wanene shi ba a Ina yake ya sunanshi duk Bata sani ba wannan yasa kullum take cikin kunci da koke koke a tunaninta Dad dinta zaiji tausayinta ya Nemo Mata shi tunda tasan tabbas shi yasan wanene tunda har gashi yazo inda yake, Zuwa wannan lokacin Zayyan da abokanshi sun warke rass ,Kuma ba abunda ya sauya a halayensu saima abunda yayi gaba yanzu Dadyn Zayyan ya siya mashi wani dank'areren gida acan kusa da gidan gonarahi ba abunda Babu aciki na more rayuwa nan suke shek'e ayarsu , bin Mata Kuma kamar bunsura kullum cikin Tara Mata suke a gidan suna abunda sukaga dama ,ga Dan banzan shaye shaye, yanzu sai yayi sati biyu Bai lek'a gida ba Kuma har wannan lokacin Yana nan da tunanin hanyar da zaibi don daukarwa kanshi fansar abunda Dan sandan yayi mashi tunda yaga kamar Dad yakasa, ________________________ Su Hisham Kam yanzu hankalinsu kwance ba abunda yake damunsu , sai zuba soyayyarsu da bawa junansu kulawa suke yayinda kullum suke cike da farin ciki Sam Hisham ya manta da wasu Wai su Alhaji Saminu abunda ke gabanshi kawai yakeyi , Laurat ma aikinta takeyi cikin kwanciyar hankali inda ta dage sosai wajan taimakawa marasa k'arfi da jikinta da aikinta da aljihunta , wannan yakara Mata daukaka sosai awajan aikinta kowa sonta yakeyi da Yaba kirkinta , ************************* BAYAN WATA HUDU Kwance suke akan makeken gadonsu ta shige cikin jikinshi sosai tana shak'ar k'amshin jikinshi Mai Sanyata nishadi a yanzu , idonta biyu ba bacci take ba saidai idonta a rufe yake kamar Mai baccin , yayin da Hisham ke baccinshi hankali kwance ,hannunta ta Dora saman k'irjinshi a hankali tana shafa kwantaccen gashin Dake kwance luf akan faffadan k'irjinshi Wanda take matukar so sosai , kamar acikin mafarki yakejin hannunta na yawo ajikinshi , a zabure ya farka Yana Kai dubanshi inda agogon d'akin yake , zaro ido yayi ganin har 8 ta gota kamun ya juyo da kallonshi inda take Yana harararta , dariya tafashe dashi tace "to Kuma Ni mi nayi daga tashinka zaka wani fara zubamun harara tafad'a tana munguda mashi bakinta, k'wafa kawai yayi baice komai ba ya tashi yanufi bayi don yin wanka , yayinda Laurat ta rakashi da ido cike da son mijinta juyawa tayi tasake kwanciya don gaba daya batajin karfin jikinta kwana biyun nan dauriya kawai takeyi musamman ma data fahimci abunda ke damunta a matsayinta na Likita ta fahimci tanada shigar ciki , wannan yasa gaba daya yanzu takejin kanta wani iri ga muguwar kasalar Dake damunta da jiri akai akai jiri ya kwasheta sai tayi sauri ta zauna , ciyon Kai kuwa ba'a magana sannan tarasa yadda zatayi ta fad'awa Hisham tanada juna biyu hakanan taji tanajin kunya sosai , Bayan ya fito sauri sauri ya shirya cikin uniform dinshi na aiki Wanda suke k'ara fito mashi da kwarjinin da Allah yayi mashi , zuwa tayi gabanshi tafara Sanya mashi agogonshi Wanda tasani bazai iya sawa ba kamar wani yaro cikin Yar dariya tace "Habibi duk fushin ne haka , janyota yayi ya had'ata da jikinshi ya na kallon cikin idanunta yace , "Ai sanin bana iya fushi Dake shiyasa kike mun abunda kikaga dama , tun da asuba na gayamaki ki tayar Dani k'arfe bakwai akwai inda zani shine Kika barni inata sharar bacci kamar kasa , " "To kayi hakuri Nikaina ban farka da wuri ba bacci Mai nauyine ya daukeni banjima da farkawa ba Nima," "Wai kwana biyun nan duk kin canza komai naki ya canza sannan na fahimci kamar ma bakida lafiya Amma kina kokarin 'boyemun , gayamun Mike damunki? Kwantar da kanta tayi a k'irjinshi tana murmushi tace "ni ba abunda yake damuna Habibi", "Aa ban yarda ba ga jikinki nan da zafi zafi , kina Likita guda Amma kina Wasa da lafiyarki ko ? "Bafa wani Abu bane Habibi abun farin ciki ne , " kallon rashin fahimta yayi Mata cikin jin kunyar shi tace babynka ne yake wahalar dani kwana biyun nan" ta k'arasa maganar da 'yar shagwa'ba , 'dagota yayi da sauri Yana fito da idonshi waje cikin had'ewar harshe yace "pls Banda Wasa da gaske kike ? Da gaske kinada cikina ajikinki Laurat ? A hankali ta d'aga mashi kanta tana murmushi wani uban tsalle ya buga kamar karamun yaro tare da dunkule hannunshi Yana fadin yessss kamun Kuma ya zubee wajan yayi sujuda Yana Mai nuna godiyarshi ga Allah sai kirari yakewa sarkin sarakuna tare da fadin alhamdulillah Alhamdulillah Allah na gode maka, Yana dagowa Kuma ya rarumeta da k'arfi ya rungumeta ya rink'a bata kiss Mai zafi kota Ina tare da zuba Mata sambatun so da kauna ,kamar Wanda aka tainkara Kuma sai ya saketa da sauri ya juya yabar d'akin sauri yake kamar yatashi sama don ya Matsu ya gayawa Momma wannan albishir din ,tun a waje yake kwalama Momma Kira , aikuwa da sauri ta fito suka had'u afalonta inda ya shigo kamar daga sama ,yadda taga fuskarshi yasata sauke ajiyar zuciya tana cewa Kai shalele Naga sadda zaka girma Kai Kam wallahi ka tsoratani irin wannan kira haka, shi Bai ma kula da mitar da takeyi ba sai zuwa yayi ya rungumeta Yana cewa "congratulation Momma kin kusa Kai ga jika ,Lauart tana dauke da ciki a yanzu ,yafada cike da doki kamar ya janyo haihuwar yakeji, Wani irin murmushi ne ya kwacewa Momma Wanda kana kallo kasan na tsantsar farinciki ne , a hankali ta shafa kanshi tare da cewa alhamdulillah Allah mun gode maka Allah ya sauketa lafiya yabamu masu albarka ," kasa amsawa yayi don sai a yanzu Kuma ya kejin kunyar Momma 'Dan Sosa kanshi yayi Yana sakinta daga rungumar da yayi Mata Yana wani sinne Kai ,dariya tayi tace "ja'iri sai yanzu ne zakaji kunyar ai Nikam kariga da ka rainani shalele Ni Bari naje Naga jikin d'iyar tawa dama kwana biyu Naga kamar batajin Dadi Amma sam ban kawo cikine ba Ashe alkhairi ne ,daga haka ta fice daga sashen inda tabar Hisham nan tsaye ,zubewa yayi akan kujera Yana shafa sajenshi farin cikin da yake ciki yasa Yama manta da wani fita Aiki....... Tunda daga lokacin suke bawa laurat kulawa sosai fiye da zato sun dauki duk wani so da kauna sun d'orashi akan cikin nan komai suka gani na Yara zakiga sun siyo sun ajiye abun kamar hauka , ba momma ba ba uban gayyar ba abin nasu dariya yakeba Laurat sosai , cikinta nada wata shida Hisham yasa ta dauki hotu a wajan aiki a cewarshi shima da zai samu hutun dauka zaiyi su zauna suyi zaman jiran isowar babyn su Bata so ba haka ta hakura don tasan ko momma bazata Bata goyon baya ba indai akan wannan cikin ne , ....................................... Wallahi yau rashin mutunci nakeji Kuma duk Wanda tsautsayi ya hau kanshi to ba ruwana Zan sauke akanshi ne cewa Zayyan Yana wani zuk'ar shisha , "To oga in hakane mi zai Hana mu saukeshi akan Dan sandan nan Mana , cewar wani daga cikin yaranshi da har yanzu idoshi daya Bai koma daidai ba saboda bugun da yasha a hannun Hisham Wanda ba ranar da bazaiyi maganarshi ba, "Yes ka kawo shawara junior hakan za'ayi dama inajin haushin Dad yakasa yin komai akanshi yanzu muje mu samu wata hadaddiyar babe mu 'barshe shegiya sai muga abunda zai iyayi tunda yace shi Mai aiki da gaskiya to zamuga ko zai iya kamomu a Karo na biyu yanzu ne zamu fara wasan tsakanina dashi !!!?? "Tunda suka fara magana wani da ake cema wizy yace "taf wallahi wannan aika aikar badani ba ku Kuna ganin yadda bawan allah nan yadda yayi Mana dukan mutuwa badon Allah yasa munada sauran numfashi ba Allah da tuni mun tsufa a lahira don haka nidai nayi nan badani ba wallahi Kuna ganin mutum hannayenshi kamar k'arfe duk duka daya sai kaga stars aa wallahi yafada Yana barin falon dama gidan Baki daya , Sauran Kam duk suna bayan Zayyan da haka Suma suka kwasa suka shiga k'atuwar motar da Zayyan ke Hawa suka harba titi, _________________________ "Inna nagama da komai ga abincin sai kici gaba da dubawa Ni zanje wajan Jamila tayimun kitso nagaji da Zama da kan nan haka , " " To Mariya bazaki tsaya kici abinci ba tun safe fa bakici komai ba nasan kinajin yunwa matuk'a ki tsaya in kinci abincin sai ki tafi," " Aa Inna bazan iya jiraba yanzu Zan dawo don ba Mai yawa zatayimin ba kawai nagaji da Zama dashi ne , " "To shikenan tunda kin kafe Allah ya tsare sai kin dawo ," "Amin Inna " "Anty Zan biki don Allah ," cewar Asmau , "Ok Asmau zo muje dama banason fita Ni kad'ai , nan suka Sanya hijabansu sukayi wa inna sallama suka tafi , Tafe suke a hanya kasancewar akwai Yar tazara tsakaninsu da gidansu Jamila , asmau tana rik'e da kwalbar man kitso sai surutu take zubama yayarta , kamar daga sama saiji sukayi ansha wani wawan birki agabansu Wanda yasasu saurin ja baya cike da razana don harga Allah sun dauka motar bigesu zatayi kamun sugama dawowa daidai tuni na motar sun fito sun sunkuce Laurat sun jefata a mota kamun suka tasheta suka bar wajan cikin matsiyacin gudu kamar guguwa , Wata razananniyar k'ara Asmau ta saki kamun tabi motar aguje saidai kamun kace mi ta daina hango motar haka ta juya gida tana wani irin kuka kamar ranta zai fita ta gigice ta dimauce ta fita a hayyacinta Allah ne kawai ya mayar da ita gida lfy................... *Indai inada masoya Kuma Kuna Yi na kamar yadda kuke fad'a , to in gani ak'asa gsky ta hanyar siyan littafin nan naira 200 kacal ngd sosai da kaunarki gareni my fans*😍😍😍😍 Don Allah don Allah don Allah in bazaki iya wahalar da kanki wajan yimun comment ba to don Allah kirike TNX DINKI KO SITIKA wlh Allah yagani na tsani tnx da sitikan nan πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» [6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA* πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *_KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_* *_Wannan littafin na kudi ne a yanzu maiso tamun magana zaku biya 200 only ta account ko katin MTN 07069711327_* _ina Mai baku hakuri a page din baya nayi mistake wajan sa sunan Mariya sai nasa Laurat mistake ne Mariya aka dauke ba Laurat ba_ πŸ…ΏοΈ_38 ................."Subuhanallahi ke Asmau lafiya , mi ya sameki haka kike irin wannan kukan , Ina yayar Taki take ne , " Gaba daya Asmau takasa magana sai nuni take Mata da hannu cikin ficewar hayyaci Wanda yasa hankalin Inna mummunan tashi cikin wata irin tsawa tace " kiyimun magana Asmau nace Ina yayarki take Kuma mi ya sameki , " Da k'yar ta bude bakinta cikin hard'ewar harshe tace " ...wasu..'yan ..'yan...yankan..Kai ne suka ..dauketa sun ..tafi da ..ita Inna " ,caraf a kunnen Baba da Yaya sulaiman,da dawowarsu kenan suka tsinci wannan mummunar maganar , a hanzarce Yaya sulaiman ya k'araso inda take kafad'unta ya rik'e Yana girgizata cikin rud'ewa da zancanta yace " ke Asmau ki nutsu Mana kiyi Mana bayanin abunda yafaru , su waye suka dauke ta Kuma garin Yaya ", Da k'yar ta tsayar da kukanta saidai hawayen idonta sun kasa tsayawa tace "Muna cikin tafiya har mun kusa Kai gidansu Jamila , daidai k'aton filin nan da ake aiki sai kawai mukaga mota tayo cikinmu sosai ,kamun muyi magana kuma wasu maza suka fito suka dauke Yaya suka sata a mota suka gudu da ita" ta k'arasa maganar tana sakin kuka, Gaba daya jikinsu rawa yake Banda innalillahi wa inna ilaihin rajiun ba abunda suke fad'a Inna kuwa har tafara kuka inda Baba yayi zaman Yan bori Yama kasa magana Banda girgiza ba abunda jikinshi keyi ,tunaninshi ya tsaya cak da k'yar yasamu yafara maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihin rajiun ,Yaya sulaiman kuwa tuni idanunshi sun kada sunyi jajir ,waye ya dauke mashi k'anwa, mi tayi masu, mi suke nema, mi zasuyi Mata , su waye sukeson su datse masu Dan guntun farincikin da suke ciki , hannu biyu yasa ya dafe kanshi da yakejin Yana barazanar tarwatsewa , kallonshi ya maida ga iyayenshi , inda yake hango tsantsar tsoro da tashin hankalin da suke ciki , wani nauyi yaji ya ziyarci zuciyarshi cikin zafin nama ya juya zaibar gidan , Cikin muryarshi da ta dishe lokaci daya kamar Wanda yayi kuka yace "tsaya sulaimanu Ina zakaje " cikin wani irin raunin murya sulaiman yace " zanje inda abun yafaru ne Baba ko Zan samu wadanda akayi abun a gabansu inyaso daga nan Zan wuce police station nakai report, " "To shikenan sulaiman jirani muje bazan iya Zama ba muje Allah ya tak'aita Mana wahala Allah ya tsare Mana ita aduk inda take Kar Allah yabasu ikon cuta Mata , nan suka amsa da Amin inda Baba da sulaiman suka bar gidan a hanzarce inda sukabar Inna da hafsat a tsakar gida suna zubar da hawayen tashin hankali, Lokacin da suka Isa wajan sun iske mutane awajan sosai kasancewar lokacin da abun yafaru yafaru ne aka idon mutum biyu wani tsoho Dake Zama agefen hanyar Yana bara saikuma wani Mai caji da yake can tsallake yanada tazara da wajan saidai kasancewar Yana fesin wajan yasa komai yafarune akan idonshi saidai kamun yayi wani motsi ma tuni motarsu ta 'bacewa ganinshi , wannan yasa aka taru a wajan Ana maida yadda akayi , Zuwansu Baba ne tsohon da saurayin Mai caji suke k'ara Gaya masu yadda akayi dakuma Basu shawarar su hanzarta Kai report ko Allah zaisa adace kasancewar Basuyi nisa ba a duk inda suke , nan suka juya suka nufi station din, Cikin ikon Allah Kuma sai suka nufi babban ofishin Yan sanda ,wato reshen su Hisham , Afujajan suka Isa station din kana ganinsu kasan hankalinsu a tashe yake , nan suka bukaci ganin babbansu , kasancewar Hisham Bai nan sai aka kaisu wajan ASP Garba , Saida ya'bata lokaci Mai tsawo kamun yabasu damar shiga inda yake , tunda suka shigo yake binsu da wani kallon rainin hankali don yasan wadan nan dai komi sukazo dashi ba wani abun kirki za'a samu a wajansu ba, Gaisheshi sukayi ya amsa batare da yabasu izinin Zama ba yace "Mike tafe daku ? Yaya sulaiman ne ya zayyane mashi duk abunda yafaru , tun fitowar su Mariya har dawowar Asmau da Kuma bayanin da suka samu daga mutane wajan, Tunda yafara magana ASP Garba ke kallonshi bayan yagama ne sannan ya dubeshi yace " to yanzu mi kukeso ayi maku ne " don wannan matsalar dai kunsan ba k'aramar matsala bace , "Hakane sir shiyasa ai muka zo nan ataimaka Mana abincika mana inda yarinyarmu take Kar rayuwarta ta salwanya abanza don Allah yalla'bai cewar sulaiman Yana hada hannuwashi wajan rokonshi , Nisawa ASP yayi yace " to shikenan. Insha Allah zamuyi iya bakin kokarinmu ,Amma kamun sannan zaku bada wani Abu asa Mai don kunsan abun nan ba karami bane doli zamu tura Yaranmu kowane sako da lungu na garin nan don ganin mun gano maku yarinyarku don haka zaku bada dubu hamsin na Mai insha Allah yarinyar ku zata dawo cikin aminci Cikin mad'aukakin mamaki suke kallonshi kamun Yaya sulaiman yace " haba yalla'bai wane irin dubu hamsin Kuma , muna gayamaka an dauke yarinyarmu sannan kana zancan mubaka dubu hamsin ,to gaskiya mu ko dubu goma ta kanmu bamu da ita a halin yanzu ," Wani kallo ASP Garba yayi mashi kamun yace to tunda bakasan ya zakayi ba ai sai ku tafi ku jira dawowar tata duk sanda sukaga damar mayar maku da ita ," "Haba Dan nan Taya zakace haka don Allah ka taimaka Mana nayi maka alkawarin in aka ganota Zan Nemo maka kudin inbaka don Allah yalla'bai , cewa Baba da duk hankalinshi ya tashi ganin inda yake sa ran za'a kwatar mashi hak'k'inshi a Nemo mashi 'yarshi sai gashi Abu Yana nema yazama kasuwanci , (ya Allah ka gyara Mana k'asarmu😭😭) Wani malalacin kallo ASP yabisu dashi kamun yace to naji zaku iya tafiya in mun samu wani labari akanta zamu nemeku , daga haka yaci gaba da rubuce rubucen da yakeyi , Wani irin haushi da takaici ne suka rufe Yaya sulaiman gefe daya ga tsananin tsoro da fargaban abunda zai iya samun 'yar uwarshi Saidai Babu abunda zai iya Yi wasu hawaye ne masu zafi suka sauko mashi inda yaja hannun Baba suka bar office din zuciyoyinsu na k'una da bugu kamar zasu fasa kirjinsu su fito, Baba kam dauriya ce kawai yake Amma shikad'ai yasan abunda yakeji ,k'irjinshi yakejin kamar zai 'balle gida biyu yasan tabbas ciyon zuciyarshi ne yake neman tashi abunda yayi shekaru rabon da ya taso mashi , bayan fitowarsu rasa inda zasu dosa sukayi , nan suka Kara tabbatar da tabbas talauci mugun ciyo ne don da su din wasu ne da yanzu ko'ina ya dauka da zancan batan yarsu da tuni anfara bincike akai Amma yanzu duba kamar ba Dan mutum ne ya 'bata ba ko dabbar mutum ta 'bata yaci ace an tausaya Masa bare da sukutum Amma wannan *Dan sandan* don rashin Imani har yake zancan subashi wasu makuddan kudade da su kansu Basu mallakesu ba , Haka suka rinka yawo a gari Basu nan Basu nan har bayan la'asar zuwa lokacin yunwa da k'ishi ma ya ishesu Babu yadda suka iya doli suka juya gida , Nan suka iske Inna kwance zazzafan zazzabi ya saukar Mata tunda suka tafi banda kuka ba abunda yakeyi Khadija ma bayan dawowarta daga aike da Inna tayi Mata tasamu wannan mummunan labarin nan ta zube tana kuka Asmau ma kuka anrasa Mai lallashin wani , acikin wannan yanayin suka samesu ,wani Abu Mai d'acine ya ziyarcesu ganin halin da Inna da yaran ke ciki gashi Suma dauriya ce kawai sukeyi Amma tabbas suna cikin raunin zuciya sosai , kallo d'aya Inna tayi masu tasan Babu nasara a galabaice tace "ya ake ciki malam ?? Batare daya kalleta yace " sai addu'a Inno addua kawai zamu ci gaba dayi har Allah ya bayyana Mana ita ,munje wajan 'yan sanda yanzu munkai report ki kwantar hankalinki insha Allah za'a ganta lafiya, " cikin k'ok'arin danne kukanta tace " Allah yasa malam Amma inaji ajikina duk inda Mariya take tana cikin mawuyacin Hali, " to Amma malam mi zai Hana mu Kai sanarwa gidan radio ko Allah zaisa adace , " "Aa Inno ba amfani kai sanarwa gidan radio saboda Mariya saceta akayi bawai 'bata tayi ba , addu'armu kawai take buk'ata a yanzu Inno , yafada cikin wani irin yanayi Mai nuni da karfin halin danne zuciyarshi ne yakeyi kawai , innalillahi wa inna ilaihin rajiun yadda wadan nan bayin Allah sukaga Rana haka sukaga dare ,wuni ranar ba Wanda ya sawa cikinshi komai acikinsu kasancewar dama can abincin Rana ne Mariya ta Dora masu kamun ta fita saigashi ko nuna abincin baiyi ba suka samu wannan mummunan labarin tun lokacin ba Wanda yasake kula da wata tukunyar abinci , Washe gari haka suka sake zagayawa tsakanin inda abun yafaru da wasu wurare Dake kusa dasu kamun suka wuce police station , wannan karon ma ASP Garba kawai suka iske nan yake Gaya masu ba wani labari suje sukara hakuri , daga haka yayi shigewarshi office Yana mita kasancewar dama shigowarshi kenan yayi Karo dasu , Wani da ake cewa sajen Musa ne yabi bayansu har sunkusa ficewa daga police station din ya dakatar dasu don yayi mugun tausaya masu tunjiya yake tunanin halin da suke ciki kasancewar Yana nan lokacin da sukazo , Gefe ya jasu cikin sauri yafara magana yace " kunga wajan can kuje can ku zauna kamun oganmu yazo in yazo zanzo na kiraku insha Allah in kuka ganshi zai tsaya tsayin daka wajan ganin an Nemo maku yarinyarku duk inda take a fadin garin nan , Fuska cike da farinciki suka fara Yi mashi godiya da Yi mashi addua , yace "ba komai kudai kuje ku jira insha Allah kukanku ya kare , " ________________________ "Kai maman biyu gaskiya nagaji tun jiya nake Abu d'aya ko tausayina bakyaji jiyafa ko bacci Baki barni nayi ba akan tausar nan, " Yamutsa fuska tayi cikin yanayin shagwa'ba tace "To Habibi Ni ma ai bana samun baccin Kuma kana ganin yadda k'afafun nan suka kumbura doli sai Ana daddanamun su kaga tsakanin jiya da yau ai sun rage ko ? "Tayi maganar cikin sigar tambaya , "Hmmm Ni Kam Naga d'a da wuya, da hakan ai gara kawai na dauki cikin na haife abuna , Amma a ce kullum banida hutu aiki sai Wanda Kika manta saboda kawai Zaki haifamun baby , "yayi maganar Yana yamutsa fuska kamar zaiyi kuka don harga Allah yagaji tunjiya take wahalar dashi tana baccinta Yana Mata tausa daya daina zata tashi tafara rigimar kafafunta ciyo da yaci gaba sai ta bingire da baccinta tabarshi da aikin tausa ( hhhhhh maganin maza kenan gara araba wahakar ai malam HishamπŸ€ͺ ) Da k'yar yasamu ta rabu dashi wanka yaje yayi yayi Shirin zuwa aiki Saida ya taimaka Mata ya rakata sashen Momma kamun ya fito yanufi motarshi ya shiga inda ya tasheta yanufi office din, *Daga dai insha Allah free pages sun Kare sai Wanda suka biya maiso ta turo kudinta 200 amma daga wannan page din to na yankeshi sai Wanda ya biya* *Zan rinka post in nayi yau to bazanyi gobe ba sai jibi Amma zanyi kokari narinka Yi maku page Mai tsawo* ngd mmn Yusuf Mai kayan mata πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kijiβœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ» Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi* Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi Maganin hawan jini Maganin sugar Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya, Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi *Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜ wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi maganaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 07069711327 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels