An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels NAMIJIN GASKE Littafi na daya Complet Na Shuraih Usman Namijin gaske Part 1A (c) shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part A . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Saurayi ne kyakkyawa ma'aboci kyawun fuska, wacce duk ya macen da yai arba da ita sai kware masa. Babu komai ajikinsa face wata falmara ta fatan zaki, falmarar ba'a rufe madannin ta ba, hakan tasa dukkan ilahirin kirjinsa a bayyane yake a fili, Gaba daya kirjinsa waje yake, hakan ce ta bayyana surar kirar jikinsa, ko ina ajikinsa a murmurde suke, a yayin da wasu guruna suka bayyana bisa tumbinsa kai kace baya cin abinci ne. A kasansa kuwa wata gajeriyar wando ce iya guiwa , ya sanya ,rike yake da gabjejiyar itace a hannunsa . Yana tafe yana waige waige koda zaici karo da abinda ya fito nema, kai da gani kasan wannan kyakkyawan saurayin farauta ya fito yi, . Yana tafiya yana gunaguni a cikin zuciyarsa kuwa tunani yake "wai yayane anya wannan karon da sa'a kuwa, Ni dana ke fitowa farauta na kamo manyan namun daji masu ababen al'ajabi, Kuma cikin kwanaki biyu rak nake kamosu sannan na tasamma gida,amma wannan karon gashi har na tasamma kwanaki hudu amma ko tsuntsu banyi arba da shi, Maganar tasa ta katse a dalilin wani gurnani daya ji, Ai koda yaji wannan gurnanin sai ya cika da farin ciki ainun bisa ganin wahalarsa tazo karshe, . Gurnanin yaci gaba da kusanto shi, ta cikin wata duhuwar sarkakiya ne gurnanin ke fitowa. Nan ya tasamma wannan sarkakiyar, koda ya rage baifi saura kadan ya karisa ba, kawai gani yayi wata murgujejiyar damisa ta fito daga cikin sarkakiyar ta bayyana a gabansa, . Ya dubi wannan damisar sai ya ganta lafceciya, sai yayi murmushi sannan a fili yace da alamu dai yau zan koma izuwa gida da karamin nama. Itako damisar sai dalalar da yawu take bisa kasa, Yau kwanakinta kusan goma kenan bata dandani Nama ba , kullum sai ciyayi take ci Toh yau ga tsuntsu daga sama gasasshe, . Mayunwaciyar Damisar tayi ruri sannan ta fada kan jarumin saurayin , Nan suka zube kasa gaba dayansu Damisar tana bisansa sai kokarin farke wuyansa take da hakoranta, a yayin da shi kuma saurayin ya rike habarta da hannunsa, sannan yasa kafa ya taka ta , take damisar tayi sama yadda kasan an dauketa da majaujawa , koda damisar ta fado bisa kasa sai tayi wata irin kara sakamakon jin zafin takun da saurayin yamata . . Saurayin ya mike tsaye sannan yayi wata irin tsayuwa irin na Mazan kwarai, . Damisar na ganin haka sai ta kara dumfaro shi da nufin tai tsalle ta diram mai a wuya, Koda tai tsallen da nufin ta fada akan wuyansa sai kyakkyawar saurayin ya sanya hannunsa guda . Ya rike mata makoshi, sai gashi murgujejiya kuma lafceciyar damisar na wutsil wutsil a hannunsa kai kace, masunci ne ya kama kifi. . Take saurayin ya daga damisar sama sannan yai jifa da ita , koda yai jifa da ita sai taje ta gwaru da wani babban bishiya , take bishiyan ya fadi rikica, Wannan damisar ko shurawa batai ba, Kyakkyawan saurayin yazo gaban gawar damisar , ya tsugunna da nufin ya sabata a kafadarsa yayi gida, . Ba zato babu tsammani kawai sai ya fara jin Dirdir gowan wasu abubuwa a bayansa, Koda ya juya don yaga mene wannan. Anan ne yayi arba da su, Wasu gabza gabzan Arnan daji ne, Su wayannan arnan dajin suna sanyene warki na fatun mesa,dukkanninsu kamanninsu da fasalin surar jikinsu dayane , Lafta lafta ne ma'abota tarin damatsa babu kaya a jikinsu face wannan warkin na fatan mesa, . Daya daga cikinsu yazo gab da wannan kyakkyawan saurayin yace " yakai wannan kyakkyawan saurayin kayi sani cewa ka aikata babban kuskure a garemu wanda hukuncinka shine kisa mafi muni" . Cikin gadara saurayin ya dubi arnan dajin nan wayanda adadinsu yakai dari yace "Ku sani ni bansan mai na aikata a gareku ba da har zaku yanke wannan hukuncin akaina " . Shugaban arnan dajin ya daka masa tsawa sannan yai nuni da dan yatsansa izuwa ga gawar damisar nan yace "shi wannan damisar daka hallaka , shine mafi kusanci ga abin bautarmu, duk wata bukata da muke da ita ga abin bautarmu muddin muka kama kafa da wannan damisar toh take abin bautarmu yake biya mana buka tunmu. . Kasani yakai wannan gafallallen saurayi, ako wacce rana mun kasance muna farauto ma wannan damisar mutun daya don tayi kalaci da shi, Haka muka kasance muna yi har tsawon wasu shekaru, Kwatsam sai gashi an wayi gari mun fita nemo wa damisar abin kalacinta, har muka debi tsawon lokaci bamu dawo ba, Hakan yasa yunwa ya addebeta ta fito neman wanda tsautsayi ya kasa dashi, sai gashi ka kashe mana ita, Abisa wannan mummunan zunubin daka aikata mana ne shugabanmu Boka Abulzulmu ya turo mu damu yimaka kisa irin ta wulakanci , Don haka ina umartarka daka bani kanka cikin maslaha nai maka kisan sauki, " Koda jin haka sai kyakkyawan sauyarin ya tuntsire da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan yace "Ashe ma mugun iri na rage A doron kasa kunga yanzu babu wata rai dazata kara salwanta a dalilin wannan Damisar" Yana rufe bakinsa sai shugaban arnan dajin yayi kukan kura sannan nufo kan saurayin, hannunsa rike da sharbebiyar takobi, Koda yazo daf da saurayin sai ya kai mai sara da nufin ya cisge mai kai, cikin zafin nama saurayin ya sunkuya saran tabi iska, . Kafin shugaban arnan dajin ya sake kaimai wani saran . Sai kyakkyawan saurayin yayi wuf cikin zafin nama ya kirba ma shugaban arnan dajin dundu a baya, Nan take shugaban arnan dajin ya kwalla kara sannan yayi taga taga tamkar zai fadi amma sai ya tirje, take ya furzar da jini daga bakinsa. Saurayin baiyi kasa a guiwa ba ya kama kan shugaban arnan dajin ya murde, karan karyewan kashi ta bayyana, duk wata gaba ta daina motsi ajikin shugaban arnan dajin, . Kyakkyawan saurayin yai jifa da gawar izuwa ga sansanin da arnan dajin ke tsaitsaiye, . Wasu arnan daji biyu suka cafe gawan amma sabida karfin jifan da saurayin yayi da gawan sai da suka zube kasa gaba dayansu. . Koda arnan dajin suka ga abinda saurayin ya aikata ga shugabansu sai dukkaninsu suka yi kururuwa sannan suka zare makamansu, nan suka rugo da gudu da nufin su isa wajen da saurayin yake su gididdibashi gida gida. Shi ko saurayin koda yaga sun nufoshi sai yayi murmushi sannnan ya gyara tsayuwansa. Koda arnan dajin suka kariso wajenda saurayin yake sai sukai mai rubdugu. Shi ko saurayin koda yaga haka sai ya sanya dukkan karfinsa ya tarwatsasu, hohoho!! Da mutum yana wajen yanaganin yanda mutun daya ya gagari daruruwan mutane lallai daya tabbatar da cewa wannan kyakkyawan saurayin ya cika NAMIJIN GASKE mai tarwatsa maza. . Arnan dajin sai kai masa sara da suka suke , shi ko ya wanzu yana mai zullewa da gociya, Babu abin da zaibaka mamaki da saurayin face ganin ko makami babu a hannunsa. A duk lokacin daya samu arnen daji ya kirba mai naushi ko dundu. Nan take zakaga mutun ya fadi wanwar akasa ko shurawa bazai yiba . Sai da aka dauki tsawon lokaci ana wannan fafatawan inda saurayin yai ta ragargazar arnan dajin , Har ya samu nasarar karkashesu gaba daya. Sannan ya dauki gawan damisar ya azata bisa kafadansa, yayi tafiyarsa . Tafiya yake har ya kawo bakin wata bukka , sannan yayarda gawar damisar a kasa, . Ya nufi wani turki ya zauna , Zamansa keda wuya sai waya kyakkyawan mace ta fito daga cikin wannan bukkan . Wannan matar zata kai shekaru hamsin da doriya amma in kaganta kace yar shekara talatin da wani abune. Matar ta dubi saurayin tace dashi "MUHAISIN sai yau kadawo" Jarumin saurayin da aka kira da muhaisin ya dubi wannan matar yace "Ummi na kenan kisani dadewar danayi ta samo asaline daga rashin samun dabbar danake nema" . Wannan matar sunan ta hamasiya sun kasance suna rayuwa acikin wannan kungurmin dajin shekara da shekaru ita da danta muhaisin Tun muhaisin bai mallaki hankalin kansa ba Ya taso ya tsinci kansa acikin wannan daji, Tun baifi shekaru tara a duniya ba mahaifiyanshi hamasiya take ganin ababen al'ajabi a tattare da shi. Don alokacin baifi shekara tara a duniya ba amma sai taga ya fita da nufin zai je farauta, in ya fita kuwa baya da wowa sai bayan kwanaki biyu . Nan zai dawo da manyan namun daji wayanda ko rikakken mafarauci ma sai yayi da gaske kafin ya kama irinsu . Tun hamasiya tana al'ajabi har tazo ta daina ,bangaren jarumta kuwa duk yawan abokan gaba tarwatsasu yake, kuma shi baya fada da makami don ko dabbobi ma wuyanzu yake murdewa. Tun da yake a rayuwarsa bai taba yin yaki ko fada da makami ba da zallan karfin damtse yake yakan ayari guda na yan fashi, da kuma gungun yan harin sumame. Haryanzu da kwai wasu yanfashi dake tarkonsa Su yan fashin sun riga da sunsan yafi karfinsu shi yasa da sun hadu sai kaga yan fashin sun ruga a guje . Ace warsu wai lokacin haduwarsu baiyiba tukun idan lokaci yayi su da kansu zasu nemeshi, . Alokacin da muhaisin ya mallaki hankalin kansa sai ya fara tambayar hamasiya mahaifinshi Hamasiya takance da shi mahaifinsa ya rasu. . Alokacin da hamasiya tazo gaban muhaisin don taga alamun gajiya ajikinsa sai taga gefen damtsensa na zubar da jini , nan da nan hankalinta ya tashi ta yagi wani kyalle dake rataye bisa wannan turkin , sannan ta kama hannun muhaisin tana daure mai wannan raunin . Nan ta tambayeshi meya ji mai wannan rauni, Bai boye mata komai ba , ya labarta mata artabonsa da arnan daji . Koda hamasiya ta saurari labarinsa sai nan da nan kwalla ya cika mata idanu, koda muhaisin ya lura da yanayin da mahaifiyarsa ta shiga sai ya ce" yake ummina shin ina dalilin zubar da hawayenkinnan , " Hamasiya tayi sauri ta share kwallan tace" yakai dana kayisani bako maine ya sanya ni zubda hawaye ba face tuno da mahaifinka da nayi, Lallai ka gaji mahaifinka dana." . Muhaisin najin haka sai ya durkusa bisa guiwowinsa yace" Na rokeki ummina daki sanar dani labarin mahaifina da kuma dalilin dayasa muke rayuwa a cikin wannan kungurmin dajin" . Koda jin wannan tambayan sai Hamasiya ta mike tsaye sannan ta nufi wannan bukkar koda tazo gab da bukkan sai ta tsaya ta dafa bukkan da hannu daya sannan ta juyo ta dubi muhaisin tace " yakai dana hakika yau kayi mani babban tambaya , hakika bawai banason sanar dakai labarin mahaifinka bane sai dai, bana son tuna baya, bana son tuna babban masoyina abin kauna na" koda tazo nan a zancenta sai wasu kwalla na bakin ciki suka gangaro bisa kuncinta. . Muhaisin ya kariso wajenda take sannan yace "Ya ummina hakika kece kadai nake gani nakejin farin ciki a cikin zuciyana, bana son ganin zubowan kwallanki, bana son jin labarin muddin hakan zai tsaida zuban kwallanki" . Hamasiya najin haka sai ta tausaya ma muhaisin ainun ta sanya hannu ta tallafo habarsa tace "Yakai dana kasani Mahaifinka Gawurtaaccen Sarki ne Adali mai jinkan talakawa, Mahaifinka shike mulkin birnin Tehran . Kamanninka dana mahaifinka sak babu banbamci, Sunansa Sarki HINZUR IBN HUMAS" . Namijin gaske 1 Part 1B (c)shuraih usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part B . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Kimanin shekaru ashirin da suka gabata a birnin tehran , birnin tehran babban birnine wanda mutanen cikinsa yawancin sana'arsu itace Noman kayan Abinci iri iri, Kasuwar garin nacine a duk mako. Kuma daga wasu garuruwan sukan ziyarci wannan kasuwa a duk makon da zaici, . Al'umman birnin tehran ma'abota son zaman lafiya ne, A yayin da adalin sarkinsu hinzur bin humas, ya tsaya tsayin daka wajen yada zaman lafiya a duk sassan birnin . Sarki hinzur babban sadaulkine wanda duk ilahirin nahiyar babu sadauki kamarsa. Ya kasance yana da wani dan uwa mai Suna Humaiz bin Humas . Shi Humaiz yan uba suke da hinzur wannnan tasa ya kullaci hinzur sosai a cikin zuciyarsa, Wacce har takai ta komo So yake yaga bayan sarki hinzur sannan ya kwaci mulkinsa. Duk da kuwa alokacin matsayin wazirin tehran yake. Duk wani bakin ciki da hassada gami da kyashi da yake wa sarki hinzur bai taba Nuna wa a gabansa ba, hasalima irin biyayya da so da kauna da yake nuna wa hinzur kai kace tamkar da gaskece amma na ciki na ciki . Waziri humaiz yasan bazai iya tarar sarki hinzur gaba da gaba ba, don kuwa linzami tafi karfin bakin kaza. Hakan tasa yaje ya samu wasu yanfashi a wajen gari cikin wani kungurmin daji , nan take ya zayyane masu bukatarsa na son su taimakeshi su hada karfi da karfe, don su kawar da sarki hinzur a ban kasa. . Shugaban yan fashin mai suna kallabu ya dubi waziri humaiz bayan sun gama sauraron bayaninsa yace da shi , "Yakai wazirin birnin tehran hakika kazo mana da abinda muka dade muna jira tsawon wasu watanni, lallai kasani wannan taimako daka nema daga wajenmu tamkar mune muka nemi taimako daga gareka" Waziri najin haka sai ya cika da tsananin mamaki sannan ya dubi kallabu yace "shin kai kuwa wannan shugaba ta yanfashi meye dalilin ka na fadin hakan" Nan take Kallabu ya bushe da dariya saida yayi mai isarsa sannan ya dubi Waziri humaiz yace da shi "yakai humaiz kai sani cewa mun dade muna son ganin bayan sarki hinzur bisa takura mana da yayi, lallai zamu taimakeke ba tareda mun karbi ko kwandalarka ba, Abin dana ke jimana shakka iyace ta yaya zamu ratsa har mu shiga gidan sarki hinzur . Humaiz najin wannan tambayar sai yayi murmushi sannan yace" indai maganan shiga gidan sarkine toh lallai ina tabbatar maku shan ruwa ma ya fishi sauki a wajena, domin kuwa akwai wani hadimina da zansa ya jagoranceku har zuwa turakar sarki" ." Koda yamma tayi sai shugaban yanfashi da yaransa kimanin su dari biyar, sukayi shiri irin ta fatake sannan suka tasamma birnin tehran . Koda suka iso bakin kofan birnin tehran sai masu tsaron kofa suka tsaida su, Wani badakare wanda da alamu shine babba acikin dakaru masu tsaron kofan garin ya kusanto gaban wayannan yanfashi wayanda suka yi shirin fatake ya tambayesu "Yaku wayannan ayari su waye ku , sannan Me ke tafe da ku izuwa wannan kasa tamu mai tarin daraja" . Koda jin haka sai kallabu wanda yabadda kamanninsa ta hanyar nade wata katuwar rawani a kansa ya dubi wannan dakare yace "Yakai wannan mai tsaron kofan kasani mu fatakene sannan bada niyyar komai muka iso wannan birnin ba face don kasuwanci" Shugaban masu tsaron kofan yace "Wacce irin haja kuka dauko" Kallabu yai nuni da hannunsa ga bayansa wasu rakumane a kalla sunkai hamsin dauke da manyan sundukai a bayansu, Sarkin kofa ya iso gaban rakumi daya sannan ya bude sunduki daya daga cikin sundukannan , Babu komai aciki face kayan masarufi kama daga dangin zinare har zuwa kan su murjani da yakutu. Nan take shugaban masu tsaron kofa ya bada umarni da a bude musu kofa su wuce . Koda suka shigo birnin tehran basu zame ko ina ba sai cikin kasuwan garin , inda suna isa suka tarar da wani hadimin waziri humaiz . Wannan hadimi yai masu jagora izuwa wata babban gida ta sirri wacce ta kasance mallakin waziri humaiz ne. **** ***** Can cikin talaitainin dare kuwa dukkan wayannan yan fashin sunyi mugun shirin yaki. Kai kace yakin duniya zasuje Gama kimtsawarsu keda wuya sai hadimin waziri humaiz daya jagoranci su kallabu izuwa wannan gida ta sirri ya shigo garesu . Sunan hadimin KAMSAS kuma shine amintaccen hadimin waziri humaiz Kamsas ba karamin hatsabibi ba ne don kuwa duk cikin hadiman waziri babu wanda yake matukar ji dashi tamkar kamsas . Nan kamsas ya dubi kallabu yace " ya shugabana Muna iya tafiya yanzu" . Ta bayan gari suka bi gudun kar wani yaji takun sawaye ya yawaita ya farka daga barci. Ba a dadeba suka fara hango kofan gidan sarki, masu gadi na nan sai zagaye suke ta ko ina Koda kallabu yaga haka sai ya dubi kamsas "Shin ta ya ya kake ganin zamu ratsa wayannan da karu masu tsananin yawa wayanda na tabbata ko munyi nasarar gamawa da toh sai nayi asarar dakaru masu yawan gaske .daga karshe kuma in muka shiga gidan sarki ragowan sauran dakarunsa su karisamu. Kamsas na jin haka sai yayi murmushi sannan yace "ya shugabana kai dai ka tsaya zakaga ta yadda zamu samu nasarar shiga gidan kuma batare da mun raunata badakare ko guda daya ba" . Kamsas na gama fadin haka sai ya rike hannun shugaban yafashi kallabu sannan yace mai yai ma yaransa umarni da kowa ya rike hannun juna, Cikin dan kankanin lokaci sai gaba daya yan fashinnan suka rirrike hannuwan yan uwansu. Nan take kamsas ya fara fadin wasu kalmomi daga cikin yaren girkawa, Take sai wata guguwa bayyana , koda bayyanar guguwar saita nufosu tana zuwa wajenda suke sai ta suresu tai sama da su ****** ***** Marubuci:- Shuraih Usman Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% (c) shuraih Usman 2017 Typing:- shuraih 99% Namijin gaske 1 Part 1C (c)Shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part C . A cikin farfajiyar gidan sarki hinzur dakaru sai kai kawo suke duk da yake cikin darene amma farfajiyar gidan a haskake take yadda ko Allurace ta fadi sai anganta, . Ba zato ba tsammani sai gani akayi wata iriyar guguwa ta bayyana Gaba daya dakarun gidan suka mai da hankalinsu ga wannan guguwa, cikin kankanin lokaci guguwan ya lafa , koda bacewan guguwan sai su kallabu suka bayyana suna masu rike hannuwan junansu. Dakarun sarki hinzur na ganin bayyanarsu sannan sukaga dukkansu suna dauke da muggan makamai, Take sukayi kukan kura sannan suka zare makamansu daga cikin kufe, Sannan suka afka ma su kallabu, Su kuwa su kallabu koda ganin haka sai suma sukai kukan kura sannan suka falfala da gudu don su tarbi dakarun sarki hinzur, Nan aka rincabe da azababben yaki Farfajiyar gidan bakajin komai sai karafkiyar takubba da karajin Dakaru, jini sai malala yake tamkar an yanka wani babban dabba, Aikoda aka fara wannan yaki sai dakarun sarki hinzur suka raina kansu , domin yan fashin wani irin salon yaki suke ,sannan gasu da juriya dacin rai da naci, don sai kaga badakare ya zabga masu sara a jikinsu jini yayi fallatsi, amma sabida tsabar naci haka zasu cigaba da yakin . A yayin da dakarun sarki suka fahimci muddin akaci gaba da wannan gumurzu toh yan fashin na iya karar da su gaba daya, hakan tasa wani badakare mai matukar girman jiki ya falfala da gudu izuwa wani bangare na gidan, Koda ya je wajenda yake son zuwa . Wata irin dogon ginice mai tsayi wacce a samarta akayi mata rumfa, Irin wannan ginin ana amfani da sune ta hanyar ganin wanda yake wajen gidan sarki ko ta hanyar sada wani sako, ajikin ginin da kwaita iriyar matattakala ta katako, da isan wannan badakare sai ya kama wannan matattakala ta katako, ya fara hayewa izuwa saman birnin ko da yakai ga karshen ginin sai, ya dauki wata makekiyar mabushi, yana dauka ya kafata abakinsa sannan ya ringa busawa har tsawon wasu dakiku sannan ya saurara. . A yayin da ake tsaka da gumurzu lokacinda su kallabu suka fara cin karfin dakarun sarki hinzur Suna kara kusantar asalin babban kofan da zata sada mutum izuwa cikin falon gidan sarautar, , Alokacinne suka ji wata irin busa na tashi,koda kallabu ya saurari wannan busa sai zuciyarsa ta bashi lallai ba lafiya ba, hakan tasa ya ayyana aransa ya kamata suyi sauri su aikata abinda zasu aikata su wuce abinsu, Rashin sani tafi dare duhu, lallai da yanfashinnan sun san abin da zai biyo baya toh da sun gaggauta barin wannan gidan sarautar don ceton rayukansu, . Wannan busar bana komai bani illa busan Yaki, kuma sanar da mutane cewa gari babu lafiya. . Kwance yake bisa shimfidarsa daga shi sai gajeran wando, duba daya zakai mai kagane cewa yana jin dadin wannan baccin da yake Gabjejen katone baki amma bakinsa bawai irin baki kirin nan bane, , Ba kyakkyawa bane amma kuma ba a kirashi da mummuna ba, Yana da tarin damatsa, jikinsa a cure take a waje daya , Kamar acikin mafarki sai yaji wannan busa , zumbur ya mike sannan ya natsu don kara sauraron busar tabbas wannan busace dake tabbatarda cewa birnin nan na cikin tashin hankali, nan da nan ya sanya kaya ajinkinsa, sannan ya sanya sulken yakinsa, Ya daoki takobin sa ya rataya , sannan ya fito farfajiyar gidan Nan da nan ya nufi turkin dawakansa da zuwa ya haye kan wata bakar doki Take dokin tai rimi sannan ta fice daga cikin gidan. Wannan gabjejen mayaki ba kowa bane face sarkin yakin birnin Tehran mai suna ZABBAGI bin SHARMIL . Abin da su kallabu basu sani ba shine A lokacinda suka isa gidan sarki hinzur Dakarun da suke fada dasu dakarune masu kare lafiyan sarki su dubu daya, . Su wayannan dakaru basa rabuwa da wannan gidan sarautar sai sati yadda za'a canja da wasu su wayannan suje su huta . Acikin gari kuwa koda Mayaka da dakaru suka ji wannan busa , Nan da nan duk wani mayaki kuma dakare na wannan birni yayi shirin yaki sannan aka tasamma gidan sarki, Sabida karan busar daga cikin gidan take fitowa, Sarki hinzur na turakansa sai sharbar barci yake kwatsam sai yaji karar wannan busar acikin kunnuwansa Nan take ya mike daga kwancen daya ke , Koda ya fahimci busar na fitowa daga cikin gidansa ne sai ransa ya baci, Cikin kankanin lokaci gagarumin shigar yaki irin ta sarakai, ya dora takobin sa akan kafadarsa Cikin hasala da zafin rai ya bangaje kofan turakanshi take kofan ta fadi kasa shirim, Kofar na faduwa ya fito ya fara tafiya cikin izza koda yaga yayi tafiya mai dan tsayi amma bai hadu da dakarunsa ba, sabanin da, sai ya kara fusata nan da nan ya falfala da azabaBben gudu Cikin kankanin lokaci ya iso bakin babban kofan da zata sadashi da farfajiyar gidan, Cikin kunan rai ya daki kofan da kafansa take kofan ta fadi rikica , Kofan na budewa sarki hinzur yai arba da wayannan yan fashin sai ratattakan dakarunsa suke. Nan take ya kwala wata irin kara wacce tasa gabadaya mayakan suka tsaida yakin sannan sukai dubi izuwa wajen da yake tsaye . Yanfashin naganin haka sai suka falfalo da gudun tsiya don su afka ma sarki hinzur Sarki hinzur na ganin haka sai shima ya ruga da gudu don ya tarbesu, Koda ya rage baifi saura taku kadan ba tsakaninsa da yanfashin sai ya daka tsalle yai sama , a saman ne cikin zafin nama ya shafttare, Makogwaron yanfashinnan da sukai kansa su biyar. . Nan fa sarki hinzur ya cigaba da sara da suka baji ba gani duk inda ya nufa sai de kaga sassan jikin mutun na yawo bisa sararin samaniya, yadda kasan ana sassabe a gona, tabbas masifa ba' a samata rana lallai da mutum yana wajen yana ganin irin yanda sarki hinzur ke yiwa wayannan yanfashi kisan gilla toh daya tabbata lallai sarki hinzur ya cika NAMIJIN GASKE duk girman kato sai dai kaga yayi tsalle ya saka takobinsa ya farke masa ciki take zakaga jini yayi tsartuwa, cikin kankanin lokaci sarki hinzur ya kashe kasu biyu cikin kaso uku na yanfashin . Koda yan fashin suka fuskanci muddin aka cigaba da wannan yakin a haka toh tabbas nan da wasu yan dakiku za'a karar da su Ai nan take yanfashinnan suka fara neman hanyar tsira, cikin masifaffen gudu suka tasamma kofan fita daga gidan da nufin su fice daga gidan sarautar, Bazato sai gani sukai kofan gidan ta bude da kanta Budewar kofan keda wuya sai ga sarkin yaki zabbagu ibn sharmil da mayaka abayansa kimanin milyan daya , Nan fa sarkin yaki ya cigaba da fille kawunan yanfashinnan shi kallabu koda ganin haka sai ya hankalinsa yayi matukar dugunzuma take ya sadakar cewa ya rigaya ya mutu, Tsulum sai ganin Kamsas yayi ya bayyana agabansa yana baiyana ya kama hannun kallabu yana shirin furta kalmomin dazu kenan kawai sai gani sukai sarki hinzur ya baiyana a gabansu Cikin matukar hassala sarki hinzur ya daga takobinsa sama da nufin ya fille kan shugaban yan fashi kallabu da kuma kamsas , Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu Sai........ . SAI ME SHIN AGANINKU KALLABU ZAI TSIRA DAGA KAIFIN TAKOBIN SARKI HINZUR KUWA . Namijin gaske 1 Part 1D (c)shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part D . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu Sai wata iriyar guguwa mai karfin tsiya ta bayyana cikin kankanin lokaci guguwar ta zuke kallabu da kamsas. . Koda ganin haka sai ran sarki hinzur yai matukar baci nan da nan ya auka wa sauran yanfashin da suka rage, Cikin kankanin lokaci aka karkashe dukkan yan fashinnan, A sannan ne sarki hinzur ya dubi sarkin yaki zabbagu yace da shi "Ya kai sarkin yaki birnin tehran shin ta ina wayannan runduna suka bi har suka shigo cikin wannan fadan" . Sarkin yaki yace " ranka shi dade ina kwance bisa shimfidata naji sautin busa toh a sannan ne nasan an kawo mana harine ," Wani badakare dake gefe yazo ya durkusa agaban sarki hinzur yace"ya shugabana muna cikin aikinmu na bada tsaro , kwatsam sai gani mukayi sun bayyana rike da makamai a hannuwansu" . Koda sarki yaji haka sai ya bada umarnin a kwashe gawarwakinsu a tafi a kona, nan ya wuce zuwa turakarsa , Washe gari kuwa afada sarki hinzur ya nuna tamkar bai damu da al'amarin daya faru jiya da dare ba . Amma a boye ya saka wani bokansa mai suna KAMSUSULJANI yayi masa bincike . Kwanaki suka ringa ja harzuwa watanni biyu acikin watanni biyunnan abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har da aurena da sarki hinzur, Al'amarin ya kasance ne wata rana sarki hinzur na zazzagaya gari yana duba yanda talakawansa suke kamar yadda ya saba aduk karshen shekara . Ni kuma alokacin banfi shekaru goma sha tara ba , nazo kasuwa zan siya kallabi, kawai sai ganin cincirindon jama-a nayi a waje guda dana tambaya kome ke faruwa sai aka sanar dani cewa sarki hinzur ya kawo ziyara , kawai sai na tsinci kaina ina mai karissawa. Wajen, Don nasha jin labarinsa da kuma irin yabonsa da jama'a keyi, amma ban taba ganinsa ba . Ashe dai kyaututtuka yake rabawa wa jama'a , Dogon layi akayi a yayin da shi kuma sarki hinzur yake gaban wata rumfa dankarere ,agabansa wani makeken teburine akan teburin kuwa kyaututtukane kala kala , Banyi kasa a guiwa ba nima nabi layi , har layi yazo kaina , Kaina na sunkuye ina dago kaina nai arba da kyakkyawar fuskarsa ma'abociyar murmushi , nan take naji zuciyata ta buga, Maimakon sarki hinzur ya miko mani kyautar dake hannunsa sai ya kura mini ido kaman yana nzarin wani abu a tattare dani ,koda naga haka sai na sunkuyar da kaina kasa, Ina sunkuyar da kaina kas ne idanuwa suka ci karo da abin da ya tayarmin da hankali Bakomai bane illa wata zabgegiyar macijiya baka kirin, jelar macijiyar da sauran jikinta yana kasan teburin a yayin da kan macijiyar ya leko ta saman teburin daidai saitin hannun sarki hinzur, Nan take macijiyar ta fiddo da harshenta , ai koda naga haka sai nayi wuf cikin zafin nama na bangaje hannun sarki hinzur ,da hannuna kafin na kauce da hannuna sai wannan macijiyar ta dankara mani cizo a hannu, nana na kwala ihu daga nan ban san meya faru gareni ba. . $ai farkawa nayi na ganni acikin wata kimtsastsiyar turaka bisa wata luntsumemiyan katifa na alfarma wannan turaka ta isa daular duniya don kayan dake cikinta yayi hannun jarin wani attajirin. .na mike zaune Kofan dakinne ya bude sannan wata kuyanga ta shigo , koda wannan kuyanga taga na farka sai ta washe baki sannan tamin sannu na amsa mata cikin boye murya , Fitan kuyangan keda wuya sai naji takun sahun mutun yana nufo dakin , ya bude kofa ya shigo ya kariso har inda nake zaune bisa katifa , Bakowa bane face sarki hinzur , yai mani sannu da jiki sannan ya fice, Ficewarsa keda wuya Sai wasu kuyangi suka shigo nan suka tasar dani sannan suka shiga bayi sukai mani wanka bayan mun fito daga bayine suka zaunar dani bisa wata kujera, . Anan sukai mani kwalliya sannan suka sanya mani wani tufafi na yadin alharini. Sannan suka ce dani naje sarki naso yayi magana dani. . Acikin wata turaka na sameshi kai alokacin in ka ganni kace sarauniyar duniyace , doguwar rigace sanye a jikina rigar an yimata ado da duwatsun lu'u lu'u sannan na yafa wata mayafi wadda akayi mata cin baki da zubar jadi, wannan mayafi ya rufe mani ilahirin fuskata . Bayan na zaune a daya daga cikin kujerun dake cikin turakar sai na yaye mayafin dana rufe. Fuskata da shi , koda sarki hinzur yai arba da fuskata sai ya mike tsaye yana mai cewa " tsarki ya tabbata ga wanda ya kagi wannan kyakkyawan halittar" . Koda naji sai na sun kuyar da kaina kasa cikin jin kunya Sarki hinzur yacigaba da cewa " ya ke wannan sarauniyar kyawawan duniya kiyisani a lokacin dana dora idanuwana akanki tunanina,hankalina,dakuma natsuwata duk sun guje daga gareni, Banki nayi shekaru ina kallon wannan kyakkyawan fuskar taki ba, Kiyi sani yake wannan kyakkyawa wannan sarki yazo da kogon barar sa gareki da jin cewa zaki amshi tayin soyayyarsa" . Koda naji yayi shiru sai na dago kai na dubeshi nace "Yakai wannan sarki ma'aboci a dalci, kayisani cewa babu wata ya mace da zatayi arba da kai sonka bai shigeta ba, Kasani tun alokacin dana fara ganin ka naji ina matukar kaunarka,"nayi shiru cikin kunya Anan dai mukai ta hira cikin nishadi In ka ganmu sai ka rantse munfi shekaru muna tare . Aranar sarki bai fita fada ba Bayan kwana uku aka daura aurena da sarki hinzur sai da aka kwashe kwanaki goma ana ta shagulgulan bikinmu Abun babu kama hannun yaro .******* ** Al'amarin waziri humaiz kuwa tun dayaga shirin daya shirya na halaka dan'uwansa baiyi tasiri ba sai ya shiga kulle-kulle ya kulla wannan ya kwance wannan har dai daga karshe wata dabara ta fado masa. ****** ** Al'amarin boka kamsusulajani kuwa bayan yayi bincike a hallaran tsafinsa sai ya gano cewa waziri humaiz ne keson kashe sarki hinzur Sai yaki fada ma sarki gaskiyan Al'amarin . ****** ** Sarki hinzur kuwa yayi tacin amarcinsa ya kasance baya zuwa fada sosai kuma kullum cikin farinciki yake Wata rana a fada ana cikin fadanci sai ga wani badakare yazo gaban sarki ya tsuguna yace "Ranka shidade wani bakone akofa yace wai daga birnin KuFA yake kuma yazo ya isar da sakone, Nan sarki yace abarshi ya kariso Koda zuwan wannan manzo sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa wajen sarki sannan ya fidda wata takarda ya mika ma wani badakare, Take maga takarda ya karbi takardan yafara karantawa kamar haka . Sako daga sarki hurshad bin harush mai mulkin birnin kufa zuwa ga aminina sarki hinzur bin humas, dafatan kuna cikin koshin lafiya kai da al'ummarka kayi sani cewa ban rubuta wannan wasikar don komai ba face don na sanar da kai cewa, matata kuma abar begena ta haifa mani santalelen yaro ayanzu haka dai na zama baba, sannan ina gaiyatarka walimar radin suna , dagamai mulkin birnin kufa sarki hurshad bin harush, . Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar . Marubuci:- Shuraih Usman Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% (c) shuraih Usman 2017 Typing:- shuraih 99% Namijin gaske 1 Part 1E (c) shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part E . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar . A washe garin ranar ne sarki hinzur ya shirya nima ya sanar dani, na shirya muka tasamma birnin kufa dagani sai sarki hinzur da kuma dakaru goma kacal, . A tarihin sarki hinzur baya tafiya da dakaru masu tsaron lafiyashi, don wani sa'in ma shi kadanshi yake shiri ya tafi rangadi, Koda yan fashi, ko wasu muggan dabbobi sun tareshi kuwa, take yake tarwatsa su duk yawansu, Muna tafe bisa dawakai nida mahaifinka a cikin wata daji mai dogayen itatuwa . Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani nayi sarki hinzur ya dakata, Nima sai na dakata na dubeshi nace "Yakai mijina kuma abin kaunata shin ina dalilin tsayuwarka acikin wannan dokar daji mai mugun yanayi" murmushi kawai yayi sannan ya bingiro kasa, yafado daga kan dokinsa, Toh anan ne naga abin daya tayar mani da hankali, acaccake a bayansa kibau ne har guda biyar, Koda ganin haka sai na sauko bisa dokina , sannan na karisa wajen dayake kwance bakinsa sai aman jini yake, Na tallafo kansa ina mai fashewa da kuka, su ko dakarun da muka fito da su suna zazzaune bisa dawakansu. Nan na daka musu tsawa kan cewa su fara binciken wanda yayi wa sarki haka. Wani daga cikinsu ya bushe da dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dubemu yace "Kusani yaku wayannan sarakan yau kam kun gamu da ajalinku" Sarki hinzur najin haka sai yayi wuf ya mike yayi tsayuwa irin ta manyan sadaukai tamkar babu abinda ya sameshi, sannan ya zaro takobinsa yace da wayannan dakarun "Ai NAMIJIN GASKE baya faduwa kasa banza, shin kuna tsammanin wayannan kibau din da kuka harbeni da su zasu illata nine hakika kunyi babbar kuskure domin kuwa jinake tamkar Allurai kuka sossaka mini" Yana gama fadin hakan ya falfala da azababben gudu don ya isa wajen da suke, ai koda ya rage baifi saura taku biyu ba tsakaninsa da su sai ya daka tsalle sama , ya sanya kafafuwansa ya doki dakaru biyu dake kan doki , take suka fado kasa daga kan dawakansu. Cikin zafin nama ya sanya takobinsa ya guntule kawunansu. . Koda sauran dakarun suka ga haka sai suka ruga aguje don su tsira da rayuwarsu, duk sun kasance suna kan doki shi kuwa sarki hinzur bisa kafafuwansa ya falfala aguje don ya cimmusu, Nan dai aka kasa tsere tsakanin dakarun da kuma sarki hinzur Cikin kankanin lokaci ya cimmusu, nan take ya daka tsalle sama a samanne tun kafin ya sauko kasa ya sanya takobinsa ya shaftare makwogaron dakaru uku nan suka fadi matattu. . Koda ganin haka sai sauran dakarun suka zage damtse sai gudu suke a yayin da shi kuma sarki hinzur ke biye da su abaya, koda sarki hinzur yafara jin gajiya , sai ya yar da takobinsa sannan ya kwala ihu wanda ta haddasa karamar girgizar kasa, Take tsuntsaye suka ringa canja sheka, Take dawakan da dakarun suke kai suka firgita ainun da wannan ihu, nan suka tsaya cak suka ki gaba sannan suka ki baya, a haka sarki hinzur ya kariso , Koda zuwansa sai dunkula hannu yaiwa doki daya naushi take dokin ta fadi akas sumammiya Cikin zafin nama ya cafe wuyan badakaren daya ke kai sannan ya murde . Cikin kankanin lokaci duk ya karkashe wayannan dakaru , Koda yagama kashe su sai yazo inda nake a durkushe ina kuka Ya mika mani hannu don na mike tsaye Kawai sai gani nayi kibau ta hudo ta gadon bayansa ta fasa kirjinsa cikin azama na mike na tallafeshi ina mai kiran sunansa cikin karaji, . Ya lumshe idanuwa sannan yace " yake abar kaunata hakika naji bakin cikin rabuwar da zamuyi na umarceki daki gudu don ki tsira da rayuwanki" Cikin sheshshekan kuka nace mai"yakai miijina alfaharin qalbina,kayisani babu abinda zaisa na rabu dakai a kowanni hali ka tsinci kanka aciki duk rintsi duk wuya ina tare da kai , Ko mutuwace ta zo daukarka toh sai dai ta dauke mu gaba daya " Ina gama fadin hakanne sai muka ji an bushe da dariya a bayanmu, koda muka juya sai mukayi arba da waziri humaiz shi da dan fashi kallabu sai kyakyata dariya suke, . Nan take hawayen bakin ciki ya zubowa sarki hinzur ya dubeni yace "Na rokeki da ki gudu don ki tsira da rayuwarki..." Maganar tasa ta katse a daidai lokacin da wata kibau ta cake sa acinya Nan take ya fadi kasa yana mai aman jini, Yasake cewa " ki gudu ki tafi ki barni" Ba don son raina ba haka na falfala da gudu nayi cikin dokar daji, koda kallabu yaga na ruga sai shima ya biyoni, Koda ya zo wucewa ta gefen sarki hinzur sai sarki hinzur ya gabza mai wata naushi a yayan marenansa, take kallabu ya durkusa sannan ya kama wajen da hannayensa bisa jin wata muguwar zogi, Damar da sarki hinzur ya samu kenan cikin zafin nama ya zare takobin kallabu a kugunsa, Sannan ya fille mai kai take dungulmin kan tayi tsalle ta fado a gaban waziri humaiz, . A lokacin waziri humaiz na rike da kibau a hannunsa , cikin har zuka ya yarda kibau din gefe, Sannan ya zaro takobinsa ya fuskanci sarki hinzur, Nan fa suka rugunzume da azababben yake, nan fa waziri humaiz ya wanzu yana kai ma sarki hinzur sara da suka, shi kuma sarki hinzur ya wanzu yana mai karewa, sannan kuma yana maida martani, sai da aka shafe kimanin sa'a biyu ana wannan gwagwarmayar toh a sannan ne waziri humaiz ya tuna cewa ya riga daya illata sarki hinzur koda gama aiyana hakan aransa sai ya yarda takobinsa sannan ya yage rigan dake jikinsa, Lallai shima waziri humaiz ba karamin kato bane don kuwa jikinsa a mummurde suke, Faruwan keda wuya shima sarki hinzur ya yar da takobinsa ya tsaya atsaye toh sai a wannan lokaci ne sarki hinzur yafara ganin jiri a sakamakon jininsa dake zuba, Nan suka afka ma junansu, wannan karon salon fadan ya canja don cikin dakiku kadan suka hada ma junansu jini da majina, , Sarki hinzur ya gaji likis amma saboda tsabar juriya da naci hade da cin rai Tabbas badun sarki hinzur ya kasance NAMIJIN GASKE ba toh da tuni waziri humaiz ya gama da shi. Koda suka ga tsagwaron karfin su yazo daya sai kowa yaja baya ya tsaya, nan sukai cirko cirko suna kallon juna, Cikin matukar fushi sarki hinzur yace"shin yakai dan uwana kayi sani daka zo ka sanar dani cewa kana son mulkina toh tuni na baka, amma tun da ka biyo ta wannan hanyar ne lallai ina tabbatar maka sai na hallaka ka ayau dinnan" . Koda waziri humaiz yaji haka sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dubi sarki hinzur yace mai "Ni ba dan'uwanka bane kada ka sake ka sake kirana da dan'uwanka'kayi sani tun muna kanana mahaifinmu yake nuna matukar kauna agareka, Kulawar dayake baka sam ni baya bani, sannan maimakon ni danake Babba na gaji karagar mulkinsa amma sai ya nadaka a matsayin sarki alhalin kaine a kasa dani, tun daga wannan lokaci na fara kulla tarko ina ta kaima ka hare hare amma kana ketarewa, toh yau gashi ka fada a cikin babban tarkona wadda ina tabbatarma ayau dinnan zan halaka, ka sannan inbi matarka ita ma na hallakata" Koda gama fadin hakan sai sarki hinzur ya kauma waziri humaiz wata naushi adaidai makogaro da nufin ya fasa mai makogoro cikin zafin nama humaiz ya goce sannan ya fidda wata yar karamar wuka a kugunsa cikin shammace ya soka ma sarki hinzur wukan a cikinsa, nan take sarki hinzur ya kwala kara wacce ta amsa a gaba daya ilahirin dajin Nan take sarki hinzur ya fadi matacce . Koda waziri humaiz yaga ya samu nasarar kashe sarki hinzur sai ya nausa cikin daji nemana, nikuma alokacin ina saman wata bishiya na rakube sai kuka nake tayi . Yadda agaban idanuwana aka kashe mani masoyi, . Bayan tafiyarshine na sauko daga kan wannan bishiyar sannan na nausa daji . Alokacin ina dauke da cikin ka wata takwas haka na kariso wannan waje a matukar galabaice. Na hada sanduna,itacuna na sana'anta wannan dan karamin bukkar haka na cigaba da rayuwa acikin wannan jejin har sa'ar dana haifeka . Babu abinda nake ci face yayan itatuwa ,da kuma tsuntsaye sune abincina a haka na raineka ka girma." . Koda hamasiya tazo nan a labarinta sai taa dubi muhaisin tace mai"toh dana kaji labarin mahaifinka sarki hinzur bin humas na birnin tehran wanda ayanzu ya zama tarihi" Koda hamasiya ta kawo nan azancenta sai taga fuskar muhaisin ta jike sharkaf da hawaye nan ya mike tsaye sannan ya rungume mahaifiyarsa yana mai fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki. . Marubuci:- Shuraih Usman Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% (c) shuraih Usman 2017 Typing:- shuraih 99% Namijin gaske 1 Part 1F (c) Shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part F . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Acan birnin tehran kuwa tun lokacin da sarki hinzur ya mutu, sai aka rada waziri humaiz, a matsayin sarki. . Nan fa waziri humaiz ya dawo izuwa sarki humaiz, Nan ya fiddo da asalin siffarsa ta mulkin zalunci, Mutanen birnin tehran sun koka sosai akan wannan mulki nasa, Ya kara yawan haraji, bisa na da, kuma bai dauke wa kowa ba, yaro,jinjiri,babba,tsoho, dole su biya, Laifi kadan talaka zaiyi yanzu zaisa ayanke masa hukuncin kisa Su ko attajirai na matukar jin dadin mulkin nasa , Rabon da a shimfida irin wannan mulkin zaluncin tun zamanin wani gawurtacce kuma sadaukin Azzalumin sarki mai suna Lu'umanu (A duba kundin tsatsuba) . Wata rana sarki humaiz na barci sai yayi mafarkin wai ga sarki hinzur ya dawo izuwa birnin tehran Yana zuwa ya nufi gidan sarauta Da zuwansa gidan ya shiga dakaru suka taso masa amma koda sukayi arba da tsohon sarkinsu Sai suka zubda makamansu, Nan sarki hinzur ya dakumo wuyan sarki Humaiz, Bayan ya hada masa jini da majina ya luguigita shi, Sai ya sanya masa igiya a kafa sannan ya daure igiyar a jikin doki, nan ya hau kan dokin sannan ya zabureshi, Wannan dokin yai ta tsala gudu, bai tsaya ako inaba sai da ya kariso tsakiyan gari, Koda mutane sukai arba da sarki hinzur sai suka kamu da matukar farinciki , Nan take sarki hinzur ya dubi jama'an garin yace da su"Ya ku al'umman birnin tehran shin kuna son wannan sarki naku kuna jin dadin mulkinsa ,koko a'a na kashe shi" . Gaba daya jama'an garin sai cewa suke akashe shi, la'ananne,azzalumi,akashe shi kawai Nan take sarki hinzur ya sauko daga kan dokin daya ke kai sannan ya amshi takobi a hannun wani badakare, ya daga sama da nufin ya fille ma sarki humaiz kai. Humaiz na bada hakuri amma ina Nan take sarki hinzur ya sauke mai takobin.... . A daidai wannan lokaci ne sarki humaiz ya farka a firgice, wata kyakkyawar mace dake kwance agefensa ta mike , cikin kissa tace "Ya masoyina shin meke damunka ,da har ka farka haka a firgice" . Murmushi yayi yace"Wani mugun mafarki nayi " Yana gama fadin hakan sai ya sauko bisa kan luntsumemiyar katifan da suke kwance akai, . Cikin kankanin lokaci ya sanya kayansa, sannan yayi tafi da hannu, Gama tafinsa keda wuya sai ga wasu dakaru su biyu sun shigo cikin turakar, dakarun suka russuna a gabansa nan ya umarcesu dasu tafi su kira masa boka kamsusulajani, Nan suka fice. . Cikin kankanin lokaci sai ga boka kamsusulajani ya bayyana acikin turakar , Yace "ya shugabana shin me nene dalilin daya sanya kace ayi kirana," Sarki humaiz yace" yakai boka kamsusulajani kayi sani yau nayi mugun mafarki wanda ya tsorata ni ainun,dalilin kiranka kuwa so nake ka fassara mani wannan mafarki tawa, . Take ya kwashe labarin abinda yagani acikin mafarkinsa ya sanar da shi, Koda boka kamsusulajani yaji haka sai yace ya shugabana, ina bukatan lokaci don nayi bincike bisa halwar tsafina " Sarki humaiz yace" na baka daga yau zuwa gobe da safe lallai ina son jin fassarar wannan mafarki," Koda gama fadin haka sai boka kamsusulajani ya bace bat. Washe gari a fada ana fadanci ayayin da kowa ya lura da hankalin sarki humaiz ya dugunzuma ainun,sabanin da dazakaga sai annashwa yake yana keta dariya . Kwatsam sai gani akayi boka kamsusulajani ya bayyana tsulum acikin fadan, Wasu fadawa har sun tattara rigunansu da niyyar su ruga amma koda suka ga boka kamsusulajani ne sai hankalinsu ya kwanta . Nan ya kwashi gaisuwa a wajen sarki Srki humaiz ya sallami kowa a fadan fada ta rage su su biyu, Sarki humaiz yace "gareka boka kamsusulajani shin me ka ganpo abinciken dakayi," Nan take boka kamsusulajani yafara bayani kamar haka" hakika mafarkinka sai ya tabbata..." Sarki humaiz ya daka masa tsawa yace"ashe kai wani sakarai ne ban sani ba tayaya mutumin dana kasheshi da hannuna zai dawo ya kasheni, ko ka taba ganin anmutu an dawo ne" Boka yai murmushi yace "eh ba'ataba mutuwa an dawo ba , amma kasani alokacin daka kashe sarki hinzur ai baka kashe matarsa hamasiya ba,babban kuskuren daka aikata kenan, Kayisani koda hamasiya ta tsira daga hannunku, tana dauke da ciki wata takwas, kuma ta haife wannan da nata yanzu haka ya girma ya zama gawurtaccen jarumi, kuma gagarabadau, lallai ina sanar da kai cewa yana nan zuwa birnin ka nan da yan wasu lokuta kuma ya kasheka sannan ya amshe mulkin mulkin mahaifinsa . Koda sarki humaiz yaji haka sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ,nan ya dubi boka kamsusulajani yace dashi"toh shin yanzu ina mafita, . Boka kamsusuljani yace" mafita dayace " Cikin kaguwa sarki humaiz yace "yakai dirkan birnin tehran gaggauta sanar dani mafitar da ka samo mana" . Boka yace "bakomai bane wannan mafita face ka mallaki Wata KAMBUN TSAFI wacce aka killace ta a tsibirin bahar jallus" . Boka kamsusulajani ya dubi sarki Humaiz bin Humas yafara bashi labari kamar haka . Kimanin Shekaru aru aru da suka shude A Cikin wannan birnin Na Tehran anyi wani gawurtaccen Azzalumin sarki mai suna LU'UMANU na birnin Tehran a duba KUNDIN TSATSUBA . Shi wannan sarki mai suna Lu'umanu yana da wata kambu na tsafi wacce take daure a hannun hagunsa, Da wannan kambune yayi amfani inda yai ta shimfida mulkin zalunci , Har lokacin da wani ma'abocin bakon Addini ya hallakashi . Yanzu kambun tsafin na ajiye a tsakiyar tsibirin bahar jallus, Muddin ka mallaki wannan kambu toh duk duniya babu wani jarumin da bazaka taka ba, Sai ka zama guguwar Annoba mai shafe birane, Akwai wasu Manya manyan sarakunan aljanu na duniya baki daya guda goma sha bakwai da ke ma wannan kambu bauta, Muddin ka mallaki wannan kambun toh duk zasu da wo karkashin ikonka, . Ita wannan kambu tana tattare da alkaluman sihirin tsafi guda dubu Kasani muddin ka mallaki wannan kambu toh tamkar ka mallaki wayan can sihirin tsafin ne, , A baya jarumai, sadaukai, da Mazan kwarai, duk sun rasa rayukansu bisa mallakar wannan kambu ta tsafi, . Kayisani yakai wannan sarki Kafin ka isa tsibirin bahar jallus kuwa sai ka bita cikin wasu mugayen dazuka guda biyu, . Dajin farko ana kiransa da suna Burkum Babu komai acikin wannan daji face dandazon yan fashi wayanda adadinsu yafi milyan Su wayannan yanfashi sun kasance mugayene sam basu da imani ko kadan don ko bera sukai arba da ita toh take suke gutsutstsure namanta su rabata ga junansu yadda kowa sai ya samu . Komai suka samu raba daidai suke da ita yadda kowa zai samu duk kankantashi kuwa, . Atarihin wannan daji babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya taba ratsawa ta cikin wannan daji a raye, Kai muddin mutum ya shiga wannan daji toh tamkar ya shiga lahira ne don kuwa baza a sake jin duriyarsa ba . , Daji na gaba kuwa ana kiransa Da suna Darul marid babu komai acikin wannan daji face wasu irin zabga zabgan maridai wayanda adadinsu yakai dubu . Su wayannan maridai kaifi ko tsini baya tasiri ajikinsu face zagwaron karfin damtse, don sun kasance suna masu baiwa jikinsu horo ta hanyar shan wani tsumi wanda muddin suka sha toh ko kwana zakayi kana saransu , Ba za su san kanayi ba . A tarihin duniya baki daya ba'ataba samun wanda ya ratsa ta cikin wayannan dazuka guda biyu sannan ya fito a raye ba walau mutum ko aljan, . Shi kuwa tsibirin bahar jallus, duk yafisu masifa da bala'I Don kuwa wasu irin Aljanu ne a wajen Su wayannan aljanun suna da katon kai kaman randa sannan sai sililin kafafuwa wanda ke barazanar karyewa a ko wani lokaci, , Aljanun gaba daya jikkunansu launin ja ne, Da sun hadu da mutum ko aljan nan take zasu zuke jinin jikinsa, ta hanyar taba sassan jikinsa . Su wayannan aljanu suke tsaron wannan Kambu ta tsafi . Lallai tafiya neman wannan kambun tsafi bakaramin masifa da bala'I bane Don kuwa NAMIJIN GASKE ne kadai zai iya tunkarar wayannan masifu batare da yaji tsoro ko shakka acikin zuciyarsa ba ." Koda boka kamsusuljani yazo nan azancensa sai yaga sarki humaiz ya bushe da dariya al'amarin daya bashi mamaki kenan Sarki humaiz ya dubi boka kamsusuljani cikin yarda da kai yace "Lallai ko zan rasa rayuwata sai na mallaki wannan kambun tsafin kuma ina sanar dakai cewa ka shirya don kuwa da kai za'ayi wannan tafiyan . SHIN SARKI HUMAIZ ZAI SAMU NASARAR MALLAKAR KAMBUN TSAFI KUWA . WANI IRIN MASIFU DA BALA'IEU ZAI HADA DASU . SHIN BOKA KAMSUSULLAJANI ZAI AMINTA YAYI WANNAN TAFIYA MAI MUGUN HADARIN KUWA . INA LABARIN JARUMI MUHAISIN DA MAHAiFIYARSA . SHIN ZAI SHIRYA YAZO BIRNIN TEHRAN DAUKAN FANSA . WANI KARAN BATTA ZA'AI TSAKANINSA DA SARKI, HUMAIZ, . Domin jin wayannan amsoshin sai ku tsumaye ni a littafi na biyu . NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . SHEKARAR RUBUTAWA:- 2017 Addreshi:- tshon/kasuwa gidan malam Usman ,nasarawa state Keffi . Akwatin waya:- 0908626148,08133209890 . Kagaggen labari daga shuraih Usman SADAUKARWANE GA M.malam Usman M.hajiya Maryam Mujahid hamza(mijin biza) best friend forever Sis.Zainab Usman Bro.abdulaziz Usman Sis.Amina Usman BAN MANTA DA KUBA Dahiru Usman Diffusion(D.U.D) Anas aliyu katuka (bin malik) Suleiman ishaq(Big army) Abdullahi Isa (B.O.C) Dafatan kuna cikin koshin lafiya Alhamdulillah An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels