An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SADAUKI BURHAAN na JAMEEY YAR MUTAN KANKIA *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _Godiya ta tabba ga Allah(SWT) daya sake aramana lokaci,inda muka sake haduwa a cikin wannan labarin mai_ _dinbin tausayi da ilmantarwa....Allah yahadamu da mafificin_ _alkhairin dake cikin_ _wannan littafi_ ```Wannan labarin kirkirarran labari ne kamar yanda na fada maku abaya tun farkon labarin.....``` *Jinjina da tarin godiya ga masoyana naga addu'ar ku marar iyaka* *Allah yasaka maku da alkhairi,Allah yabar kauna ina tareda ku iya* *wuya so na hakika nike maku irin trillions din nan* Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku (300) domin karin bayani tuntubi wannan number👉🏻 08160508316 Acct detail 0777512438 Access Bank,Jamila Abubakar Bello. _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA ƊAYA "Allah yaja da ran Sarauniyar Zairana kiranki ya riskeni."ya sadda kansa kasa yana sauraron yaji kiran da uwar gijiyar tashi tayi mashi. wani irin wulakantaccen kallo ta watsa mashi da sauri Ado ya sake sunkuyar da kanshi kasa yana jin wani irin mummunar faduwar gaba baki daya jikin shi ya hau bari baisan sadda ya sake russanawa ba yafara neman afuwar ta. shiru ne ya sake gauraye illahirin ɗakin kamar bakowa wajen kowa ya shuga taitayinsa. cike da gadara gamida ta wata irin masifaffiyar izzah da takeji duk a lokacin,tafara magana cikin tarin miskilanci da nuna karfin ikon mulki....."sai yanzun kaga damar zuwa kirana."? "Allah ya yuci zuciyarki ba da gangan naki zuwa ba Mai Martaba ne ya tsayar da ni kiman aikin rai!"sake sadda kansa yayi kasa yanajin zuciyarsa kamar ta fado kasa."Dallah yiman shiru karka cikani da wadannan munanan maganganun naka masu saka mutun ciwon kai."Tuba nike uwar gijiyata kimin aikin rai."kallan sa ta kumayi a karo na biyu sannan ta cire kai gefe tace."labari ya sameni ance gobe zakuje Kasuwar Gobir siyan bayi ko."? "Eh ranki shidade."Idan kunje ina so kaduba mani bayi guda biyu masu inganci da aminci ina bukatar mace daya namiji daya." "Angama ranki shidade Allah yakara maki lafiya."karka kuskura ku kawo mani raggon bawa, muddin hakan takasance kashinka ya bushe idan kunne yaji......" _Hmmm wani aikin sai gimbiya Zubaina....ko za'a dace da jajirtaccen_ _bawan da take bukata?_ "Allah yataimakeki bazaki sameni da sabama umarnin kiba zan jajirce inga na samu maki bawan da ya dace dake wannan hakkina ne a matsayina na masu kula da bayin wannan masarauta."ya rage naka zaka iya tafiya."Allah yakara girma ki huta lafiya." Ga baki daya wajen kowa ya kama kanshi banda hidma na abinda sukeyi bakaramin canzawa Zubaina tayi ba sun rasa gane kanta bata ɗagawa kowa kafa cikin ZAIRANA labarin Zubaina ya karade ko ina kowa shakkunta yakeyi....tun gimbiya Amina na kwatantamata harta kyaleta ta saka mata ido saboda Mai martaba bai son ana takurata ya dauki son duniya ya daura mata kasancewar yanzun ita kadai yake yawan gani a cikin ya'yan sa...... _BURHAAN_ zuwa yanzun Masarautar Burhaan ta hargitse ta gama rikicewa ba abinda akeyi a cikin ta sai mulkin zalinci da kaskanci. mutane cikinta basu da 'yanci ko kadan banda wulakanci ba abinda ake masu.....duk abinda bayin Masarautar zasuyi basuyin dai dai daga bugu sai aikin wahala ba sauki hatta masu mukamamma basuyin wani motsin kirki a cinin Masarautar. gimbiya Saude ke ba baiwarta aikin gyaran lambu kasancewar bata son kowa na zuwa lambun ta idan ba wanda ta aminta da shi ba. wannan baiwar na cikin aiki tana rage ciyawun dake cikin lambun sai taga wasu irin manyan bakaken layu suna fidda hayaki....bakaramin tsorata tayiba har saida ta buga uban ihu mai razanarwa. Da sauri gimbiya Saude ta shigo ta iske layun suna ta fidda hayyaki batasan sadda ta cakumi wuyan baiwar ba taita dukan ta kamar zata kasheta. wani irin kuka ta fashe dashi mai cin rai tanaji tana gani aikinta ya gama lalacewa..... Badan komai ba saboda ba'asan kowa ya gansu muddin sukai kwana bakwai a binne cikin ƙasa.Sarki Abduljalal zai mutu.... data gaji da dukan baiwar ta jata kasa ta hada ta da Barde,koda ta iske Barde baki daya baya cikin hankalin shi."ka hukunta man ita."batajira cewar shi ta baro mashi ita. Kuka kawai takeyi ga tsoro da razana ya gama kamata. Barde na tasowa yahau ta da duka kamar zai kashe ta ihu kawai takeyi cigaba da dukan ta yaci gaba dayi daga haka ya afka mata yai mata fyade saida yaimata kaca kaca sannan ya kyaleta jini ke zuba a kasanta haka yabarta a ya she kamar zata mutu numfashinta na fita sama sama ɗai ɗai kuma baifasa bugun baiwar nan ba ranar haka yaita haike mata cikin kankanin lokaci numfashin ta ya dauke baki daya. ______________ tunda galadima Hamza ya shigo fa'da yaketa kankanci da wukanta mutane gashi ya hana kowa magana saidai ido da suke bin shi dashi. Sawa yayi a ka kira masa sarkin taska yana zuwa yakai gaisuwa cikin girmamawa dan shirune ya biyo baya sannan Hamza ya bukaci da Sarkin Taska da ya fiddo mashi kudi."akwai abubuwan da yaka mata ace anyima Masarautar nan"sadda kanshi kasa Sarkin Taska yayi yace."Allah yataimakeka kudin dake hannuna ba masu yawa bane."Mikake nufi."? "Allah yataimakeka ka aiko an karba kwanakin baya."wannan shike nuna zaka ha'inci fa'da ko? yau zaka dandana kudar ka kuma ya zama dole ka fiddoma talakawa kudaden su bana tantama kaine ka cinye dukiyar nan."ranka shidade walahi ko anini banci ba kaimin aikin rai."yiman shiru zakayi bayani ne."yanaji yana gani Hamza ya hana shi magana daga."aje a garkame mani shi gidan yari da sannu saina bankado duk wasu azzalumai maha'inta."yasa akai ram dashi akayi gidan yari dashi. (Idan nine kadan kuka gani da sannu saina mayar da kowa cikinku abin tausayi a cikin Masarautar nan koda dan uwana ne Abdullahi ya zama wajibi kuyi biyayya ko kuna so ko bakya so da Hamza Muhammad kuke magana matsiyata daku!) _Allah ya kyauta wannan wane kalar zalinci ne anya Masarautar Burhaan akwai Allah a cikin lamuranta_ 🤔 Haka kowa yakama gaban shi harta kai ga yanzun kowa na gudun zuwa fa'da gudun kar Hamza ya wulakanta mutun ko ya janyo wani sharrin yace kai kayi dan yaci mutuncin ka ko Abdullahi shima baicika son zaman fa'da ba saboda ya fahimci ba wanda Hamza bazai iya wulakantawa ba,baki daya Masarautar Burhaan tana kalkashin ikon sa. ************ Yau kimamin kwanan su Sadauki ukku suna tafiya kuma duk a kasa suke janshi idan sun tsaya to abinci zasuci suma sai sunci sun rage su yammashi ko ruwa diga mashi sukeyi a baki ya hade,baki daya yagama galabaita ko bacci aka kwanta shi baida arzikin ko mayafin dazai shimfida haka zai kwanta a kasa kamar marar galihu....basu suka isa Gobir ba sai wajen karfe biyun rana sadda suka isa Sadauki yagama galabaituwa da duka jikin shi duk sahun duka. suna isa suka samu waje daban suka sa igiya suka daure kafar shi kamar wani rago,tunda aka shigo dashi mutane sukai ta ribibin shi kamar sunga nama kowa so yake ya siye shi bare yanda suka ganshi kyakkyawan gaske dashi cikin kankanin lokaci akafara cinikayyar shi sai fasama masu kai akeyi Cinikin sai ya koma gasa kowa bajintar sa yake nunawa ta fidda zunturutun kudi tashin farko mile saba'in aka taya Sadauki sukace albarka wani yace tamanin nan ma sukaki harda wanda yace mile dari amma sunce albarka basu taba kawo bawan dayakai darajar mile talatin ba tunda sukaga ana rububin sayen Sadauk sai suka kara daura guri akan shi kowa yaki yarda ya hakura da cinikin shi,suma sunki sallama shi har dare yayi anki karasa cinikin Sadauki aiko cikin kankanin lokaci wajen yayi tamkam da mutane kowa yana son yaga wanene wannan bawan mai farin jini har haka duk wanda yaga Sadauki sai yaji tausayin shi ya kama shi daganin shi ba ainahin bawa bane jikin shi kadai zaka kalla kasan yasaba da hutu,shiko sai binsu yake da ido kamar wani gele abu kamar wasa har wajen ya makare da mutane har ankai mile dari da hamsin amma sunki siyarwa...... kafin kace me sai aka fara sanar da isowar mutanen Zairana tunda Ado yayi ido hudu da Sadauki yaji ya bala'in shiga ranshi da ganin shi zaiyi juriya da yawa shima ya shiga fafatawa a cikin masu gasar cikiniki.....tashin farko mile dari biyu yasa Sadauki duk wanda ke wajen nan saida ya tsaya ya kalli Ado wani irin girman kai ya sake hawan mutanen da suka kawo Sadauki nan suka ce albarka Ado yasaka kallan Sadauki da kyau daga sama har kasa yai masa kallan tsaf."konawa akasai wannan bawan ba'a fadi ba ya hada komai kyawu da kwarjini ga tarin haiba duk ya hada."ya ayyana aransa bai musaba yace yasa shi mile dubu dari ukku da hamsin baki daya wajen nan aka hau ihu dan duk wanda ke wajen yakasa ja da Ado..... koda suka ga kowa ya gaza sunsan bazasu kara samun sama da cinikin Ado ba, suka amince ya fiddo kudin su ya basu, suka kwance shi nan ya tambayi sunan shi dayake duk sun rude saboda sunga kudi suka ce sunan shi UMAR ba karamin dadi Ado yaji ba kama hannun Sadauki yayi yaje ya sai mashi abinci ya bashi,kamar tsohon mayunwaci haka Sadauki ke hannu baka hannu kwarya har kwarewa yake kai kace wani zai anshe mashi abincun sannan yaba shi ruwa ya sha..... cikin yan mintoci har Sadauki yayi bacci shidai Ado yarasa dalilin dayasa Sadauki ya shiga cikin zuciyar shi a lokaci daya. nan suka tashi ya ida siyan bayin su da mace guda daya da ya siyeta a mile saba'in sunanta Hafsat, suka samu waje suka kwanta shi da mutanan shi kowane bawa na kwance waje amma ya shigo da Sadauki cikin daki a shimfida daya suka kwanta kowa saida yai mamaki amma bata magantuwa sunyi tunanin kodan ya siyeshi da tsadane shiyasa yake bashi kulawa. kowa bacci ya dauke shi tunda sukai asibar fari sukai sallah kowa ya hau dokin shi suko bayi suka daure su a jikin doki da igiya,koda wani babban bawa yazo daure Sadauki hanashi Ado yayi saida kowa yayi mamaki daura shi yayi agaban dokin shi duk da banisa sosai da Zairana a cikin yini daya suna iya isa take saida hassada ta shiga a tsakanin bawannan da Sadauki da haka suka cigaba ta tafiya zuwa MASARAUTAR ZAIRANA..... Writer of👇🏻 •Nana Jawaheer •Gimbiya Hakima •A gidan Haya •Sanadin Link •Bayima 'yayane •Barawo ne paid •Sanadin Soyayyar minti •Alqalami S1 •Bakin jinina ya jaman S2 •Qaddarata S3 •Haka Allah yaso S4 •Lokacine S5 •Daukar fansar budurcina paid •Bani bace paid •Bansan inda suke ba paid •Buɗaɗɗiyar Soyayya paid •Danginmu ne Sila paid •Izzah ko Mulki And Know •Sadaukin Burhaan paid _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share saboda Allah🥰 *SADAUKIN BURHAAN*.. _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA BIYU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku (300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello shedar biya ta wannan layin 08160508316 Sarki Abdulbasit Abdulkarim cikin turakarsa yarasa abinda ke masahi dadi abubuwa sun coshe mashi banda tunanin Burhaan ba abinda yakeyi yaji shiru daga bangaren su ba amo ba labari tunda akayi bikin su Asma'u....ba Mardiyyah bare yasa ran ganin ko Sadauki ne yazo kullun dasu yake kwana a cikin ransa yarasa me ke mashi dadi a rayuwar shi ta duniya hakan yasa Jakadiyarsa tayi masa kiran gimbiya Zainab bata jima ba ta iso ta zauna kallo daya tayima mijinta ta gane tsatsar damuwar da yake ciki,cikeda kulawa ta soma tam bayarsa abinda ke damunsa cikin tsatsar kulawa bai bata lokaci ba yaima iyalin nasa bayanin komai... itama cikin damuwar take jin shirun yai yawa."yakamata kaje da kanka kaji ko lafiya."tayi maganar a matukar raunane ɗan shiru yayi alamun mai nazari yace." ya dace nafara tura ɗan aike daga bisani zanje da kaina gaskia ina cikin damuwa marar misaltuwa."Allah yasa muji alkhairi."amin." Abangaren Umm Aisha itama lamarin duniya duk ya tarar mata yaimata yawa ta rasa abinda ke mata dadi idan tayi magana sai mijinta yace ta cika san ya'ya bata da kara Mardiyyah tafita kawaici da sanin yaka mata tanaji tana gani saidai tasa ido amma kullun tana cikin damuwa da zulumi gashi ya hanata zuwa Burhaan yace saidai idan Asma'u ta haihu sannan zataje baki daya. ******************* Basu suka isa Zairana ba sai wajen karfe biyar na yamma ba inda suka wuce sai sansanin bayi wani katon wajene Sarkin gida ya damka ma bayin da kanshi ya basu masauki amma ya ware Sadauki da Hafsat ba inda ya wuce dasu sai wajen Zubaina kasan cewar tana cikin daki nan ya tsaya dasu babban ɗaki. Fadila tayibmashi iso zuwa wajen gimbiya Zubaina bayan kakar minti sha biyar ta fito cikin shigar alfarma bakaramin kyau tayi ba,a tsugun ne ta iske su,sai aikin kallon ɗakin Sadauki keyi,wajen ya kayatar dashi ainun. kowa saida ya kawo gaisuwa wajen gimbiya Zubaina amma banda Sadauki daketa faman karewa dakin kallo. Baki daya hankalin ta kacokam na kansa ta shagala da kallon irin kyau da tsarin hallittar da Allah yaima Sadauki...rabon da taga kyawu irin nashi bazata iya tunawa ba tajima bata ga kwakkyawan mutun kamar Sadauki ba,tafi karfin minti biyar tana aikin kallan sa har saida hadiman dake wajen suka gane kallar kallan begen da uwar gijiyar tasu take masa."tubarakallahu ahasanil kaliƙin lallai Allah ya gaza halittarsa yanda yaso."ta furta a zahiri tanaci gaba da baya kyawunsa a ranta hatta Ado saida ya kalli Zubaina saboda yasan halinta ba komai ne ke birge taba amma sai gashi tayi santin kyawun Umar.... koda yake dole a yab kalar hallittar shi saboda mutum ne cikakken mutun mai tarin cikar haiba da kyawun sura saida Ado yakara magana a karo na ukku sannan Zubaina ta dawo hayyacin ta..... Kallansa tayi na sheke ta kauda kai ta basar dayake Sarauta jinintace take ta wayance ta fara masifa."Ado wannan wane irin sakaran bawane ka kawo mani."ranki shidade bawan nan yana da nagarta."shine bazai iya kawo gaisuwa a wajen uwar ɗakinsa ba bayan kowa ya kawo tashi gaisuwar uban wa yafi."?a gadarance tayi maganar tana kada kafa daya saman daya saidai har yanzun tana satar jallan Sadauki ta gefen ido kallan da ba kowa zai gane tanayi masa shi ba. tarin fargaba ya rufe Ado yafara ma Sadauki faɗa."bazaka gaishe da uwar gijiyar ka ba."dan kalan Ado yayi ya kauda kamsa batareda ya kalli inda gimbiya Zubaina taje ba ya gaisheta da muryar amo wadda ke karade zukatan maza du da yana cikin ganiyar sihiri hakan bai hana muryar Sadauki fitaba kamar ta da ba wanda dole sai mai sauraron sa ya shiga taitayin sa,koda zai gadata atakaice yace."iyani."badan yaso na ya gaidata dama shi ba mai yawan son magana bane bare yanzun da bai cikin hayyacin shi.... tunda ya furta kalmar inayi gimbiya Zubaina tayi mutuwar zaune a rayuwarta ta duniya tana san Jarumin namiji kuma Jajirtacce wanda idan yai magana ansa isasshshe kuma cikakaken namiji ne yayi ta.... koda kasan cewar Sadauki bawa amma saida taji ya birgeta har a cikin zuciyar ta a karon farkon da wani da' namiji yafara birge Zubaina a tsawon rayuwar ta...... Da kyai ta saita kanta ta dan basar ta sake duban Ado."dagani bawan nan akwai shi da girman kai Ado kuma ina ganin bazamu shirya da shiba duk da ina son hudda da mutane masu nuna izzah ta tarin gadara kodan in gyara masu zama...da dad bawan ya fiye izzah da yawa."zai kasance kamar yanda kike bukatar shi ranki shidade."minene sunan bawan."Ado ya bude baki zai bata amsa da sauri ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu da alama tafisan taji daga bakin sa. Saidai kamar tana magana da dutse yayi banza da ita saidata ta daka mashi gigitattar tsawa saidai duk da haka inda take Sadauki bai kalla ba,hakan ba karamin bata ran Zubaina yayi ba saida ta kuma maimaita masa tambayar."ya sunan ka."?Baki daya kwakwalwar Sadauki ta daure ta coshi ya kasa tuna komai."UMAR."yace batareda yayi tsammani ko zato ba....yanda ya furta kalman cike da kasaita gamida nutsuwa yasata kara rudewa.....tunda take bata taba ganin bawa mai nuna isaba kamarsa ba aranta tace(saidai kace Sadaukin Burhaan da yaya Ammar dinta ke bata labarin shi.) _zancen kikeso Zubaina ance rashin sani yafi dare duhu kuma_ _karamin sani ƙunƙumine....Sadauki ne dai yazama bawa kuma bawan ki_ Tunda ya fadi kalmar Umar ta rikinka maimaitawa kamar wata addu'a haja taje maimaita suna a saman kabbanta sai taji yamda ya fada yafi dadin sauraro...Kallan kanshi yakeyi yanda yaji ta kara kiran shi da Umar alamun dashi take magana dama yaji kalmar sunan ne a bakin Ado da haka yake kiran shi,shima yake amsawa, dan haduwar Sadauki da Ado harya saki jikin shi da shi,ganin shike kyautata mashi,itadai Zubaina sai kara gayama Allah takeyi tsabar yanda kyawun shi ke fisgarta..... Abinda ta fahimta kamar tunda Umar yazo bai tsaya ya kalleta ba abinda tasani da wahala da hadu da mutane basu yaba kyawunta ba amma ta lura banda Umar kallan tama baiba bare ya yaba kyawun nata, saima ita data bige tana yaban nasa kyawun abunda bata taba yiba a rayuwar ta ta duniya ba sai yau kuma akansa.....kiran da tasake yimasa ne."Umar." yasa shi ya daga idanuwan masu tsananin haske fara kal kal dasu ya aza akan fuskar ta, duk Sadauki nafama da halin mantuwa saida yaji faduwar gaba ya riske shi cire kansa yayi daga kallansa sai kuma ya sake kallan Zubaina sai ya samu kanshi da sakin murmushi....ba karamin shagaltuwa Zubaina tayi ba da kallan Sadauki wani irin kayataccen kyaunsa yakara bayyana ga kwarjini da haibarsa duk sunkara bayyana a tare dashi.... ta rasa meke damun ta, saida tayi karfin zuciya sannan tacema Ado."abama Umar mai yiman aikin wanki."angama ranki shidade."miye sunan dayar baiwar."Hafsat."ta amsa mata cikin girmamawa."zata dinga gyara mani daki,da kawo mani abinci,da hada mani ruwan wanka."umurnin ki abin alfaharina."jinjina kai tayi cikeda izzah sannan ta kalli Fadila wadda mamaki ya gama kamata ganin uwar dakin ta ta rude danganin Umar sai kace wani mutun mai daraja gashi bata dauki bawa a wata tsiya bada."ke kuma Fadila zaki cigaba da kula da lamurana na yau da gobe dani Kaina ya kamata ace zuwa yanzun kin huta."insha Allahu zanyi duk abinda kika umurce ni."tayi mata godiya mai yawa,koda Ado zai tashi fada mata yayi yanda ya siyo Sadauki saida tayi mamaki sosai, amma da takara kallan shi sama sa kasa tasan yafi karfin kudin da aka siye shi dasu koba komai Umar akwai kyau da tsari..... sannn ya fada mata kudin daya sayi Hafsat tace."ba laifi ai itama tanda kyau."nan tayi masu izzini dan suje su huta kafin gobe su cigaba da aikin su.... haka suka tashi kowa ya kama gaban shi.amma daki daya da Sadauki suka zauna shi dai ya nasan Sadauki..... Ranar gimbiya Zubaina yini tayi da tunanin Sadauki a cikin zuciyarta ★★★ Ba abinda kema sarki Abduljalal dadi a duniya dan shi zuwa yanzun kaf lalurar shi bata damun shi irin bakin cikin bacewar ɗan shi Sadauki yasan yayi rashin jajirtaccen da' gashi baida laiya bare yabi hanya ko Allah yasa ya dace da shi a cikin duniya wannan lamarin shike sa Sarki Abduljalal kuka da idanun shi,harya kai fagen da Saminu ya fahimci damuwar shi shi kanshi lokaci zuwa lokaci idan ya tuna da uban gidan shi ya bata sai yayi kuka a boye gudun karya karyama Mai martaba zuciya saidai yaita bashi hakuri a kowane lokaci..... tunda Barde yagama haikema baiwar nan ashe rai yayi halinsa saboda azabar da tasha gimbiya Saude da Masau'da suka shigo wajen shi da niyar su sa akaita gidan yari suka tadda ta a ya she su kansu duk rashin imanin su saida suka kauda kai, baki daya jikinta jini ne sannan ya gama wulakanta tata,da sauri Masau'da ta isa ta dago baiwar nan kamar ta zubda mata hawaye dan kuwa Saude kasa isa wurin tayi.....budewar dakin kwanan sa keda wuya yaga su Saude a falan shi amma ko kunyar su baiji bare nauyin su,haka yai masu sannu sannan ya karkace su zai wuce aiko Saude ta rike shi."haka nayi dakai Abbas bana ce ka ladabtar min itaba shine zaka haikema yar mutane?"Dallah Goggo ki sakeni ko inshara maki mari harkin isa kitisani a gaba kina cewa na haikema yar mutane daman idan zan huta saina nemi izinin ki dole in shana da ita agabanki ma zan iya aikatawa bare bayan idonki,kuma wannan wulakantacciyar baiwar zaki cema yar mutane,daga ita har iyayen ta wahalallu ne fa!"tunda Masau'da ta fahimci Barde ya kashe yarinyar nan amma yake tada jijiyoyin wuya batasan sadda tazo ta wasga mashi mariba saida ya gigice."dan mi zaki marar mani jika."inji Saude."dan yaimani rashin kunya ke yai mawa."? Dalla mmata harara Masa'uda tayi tace."tafican sakarai dake,angayamaki danke na mare shi karewar rashin kunya koda zai maki yanda yaima wannan baiwar saidai in kalla ko dungurin shi bazanyi ba...na mareshi ne dan yasan abinda ya aikata ya munana tunda yarinyar nan ta rasa ranta ta sanadiyar keta mata haddi da jikanki yayi."baki daya Goggo ta rude idan wannan abin ya fita waje lallai zai taba darajar mulkin da dan'ta keyi.....sake dauke shu da tafi tayi amma ko ajikin Barde cigaba da wakewaken sa yayi ya fita ya barsu cirko cirko take Saude ta barke da kuka,itako gimbiya Masau'da zuciyar ta fas tasamu taban da zata yaki abokin gabarta dashi wato Hamza dan itama ta samu takafa tata sarautar tunda yanzun bata ita yakeba daga ƙauri sai guiwa..... _Ikon Allah yauga soyayya ta zama kiyayya tsakanin aminan nan guda biyu_ _wato Galadima Hamza da Gimbiya Masau'da koya zata kaya kubiyoni sannu a hankali zakuji cakwakiyar_ _da zata wakana a cikin Masarautar Burhaan_ _JAMEELAH JAMEEY❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA UKKU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello shedar biya ta wannan number 08160508316. *Godiyar ban girma da jingina a gareku masoyana na nesa da na kusa nagode sosai da nuna kauna a book din SADAUKIN BURHAAN,sannan masu man maganar n cigaba da Izzah ko mulki nasan maybe basu fahimta ba,ai Sadaukin burhaan shine cigaban izzah ko mulki kije ki duba last page din Izzah ko mulki zakiga nasa sunan ai ngd sosai🥰* Baki ɗaya hankalin gimbiya Saude yai mummunan tashi da sauri ta rike gimbiya Masau'da tana rokonta arziki akan karta bari wannan abinda yafaru ya fita....saidai abin mamaki gimbiya Masau'da taki yarda a gadarance tace."matukar Hamza bai dauki mataki akan ɗansa ba saina tona asirin Barde kowa yaji abinda ya aikata ba Burhaan kadai ba saina yayata lamarin nan ya karaɗe kaf illahirin Kasar Cameroon bama iya nan ba kadai sai zancen nan ya zaga sassan duniya kowa sai yaji abinda Yarima Barde ya aikatama Baiwa." Lallai kama hankalin Saude yayi matukar tashi banda zufa ba abinda ke tsatsifo mata duk jarabarta tana shakkar tsatson su Masau'da da irin shakiyancin ta. Ba yanda tayi iya da haka suka sabe sukabar sashen Barde a zuciyar Saude ko so take tana fita idan dare yayi tasa a badda gawar baiwar nan dan asirin jikinta dana mulkin ɗanta ya rufu ita kuma Masau'da burin ta ta turo uwar bayi da wasu bayin a sashen Barde da niyar gyara zasu ganema idanun su abinda ke wakana,tasan koda za'a kashe su bazasu yarda ba sai sun nemi hakkin su ita kuma idan taga Hamza yaki basu hadin kai saita rubuta wasiku ta aikama Sarakuna da sauran masu hannu da shuni tasan zasu tayata yakar Hamza kafin tafara turo mashi da bamabaman asiran su...... tana komawa da saurinta tasa aka kira mata uwar bayi tareda yar aikenta suka dawo baki dayan su suka zube kasa suka kwashi gaisuwa fadada fara'ar ta tayi tace."Uwar bayi kije da kanki keda wasu daga cikin bayu zaku gyara sashen Yarima Barde yanzun yanzun nan."angama ranki shidade Allah yataimakeki lafiya."gyada mata kai tayi ta fita da saurinta,da shu'umin murmushi ta raka bayan ta.batareda bata lokaci ba ta kwashi bayi har hudu sukaje sashen Barde suka fara gyara ko ina sannan ta turo wasu karamin falo suna shuga sun fara aiki suka ga mutun yashe duk jini jikinta ihu suka kwada da sauri uwar bayi ta duka tana kallan fuskar ta taga ashe Yusrah ce mai gyarawa Yarima Sadauki daki,ba karamin kaduwa tayi ba baki daya wajen nan suka hau uban kuka kamar zasu mutu saboda yarinyar kirki ce, shiyasama Sadauki yace taciga da yimashi aiki, shi kanshi yarinyar tayi mashi ba ruwanta da son abin duniya kaf turakar bayi ba yarinya mai kamun kai kamar ta da sanin yaka mata ba kamar Yusrah....uwar bayi tasa aka maida mata kayanta sannan ta fito ta kirawo wasu bayin suka dauke ta sai fa'da duk abin nan Masau'da na kallan bayin nan sai murna takeyi yau asirin Barde zai tonu suna shiga fa'da dogarin Hamza ya daka masu tsawa amma sun rigada sun kekashe ko shakka babu a fuskokin su, hakan yasa Hamza ya daga mashi hannu sannan yayi shiru a tsakiyar fa'da suka shimfideta kallo daya Hamza yai mata sannan ya maida kallan shi ga uwar bayi cikeda tuhuma ba kunya balle shakka tace."danka Barde yaima yar mu Yusrah fyade ta sanadiyar hakan ta rasa rayuwar ta shiyasa muka kawoma fa'da dan ta kwatar mana hakkin mu." ba takaran Hamza ba hatta Abdullahi dasu Shamaki da sauran dagatai da fadawa saida suka girgiza dajin maganar ta,dman anyi sa'a ranar fa'da ta cika tamkam da yan adam.zufa ke ketoma Hamza tako ina amma a zahiri sai cewa yayi."har wani yan'ci ne daku da zakizo fa'da kima mana izgilanci nasan ɗana bazai taba haikema yarku ba."Allah yataimake ka idan har nayima Yarima Barde sharri raina fansa ne akansa."a fusace Galadima Hamza yace."minene aibun Abbas dan ya huta da baiwa? kwananta ne yakare shiyasa ta mutu dan haka kuyi gaggawar kauda mani da wannan baiwar tunkafin ku fuskanci mummunan hukunci."ba bayin nan kadai ba duk wanda ke cikin fa'dar nan saida maganar galadima Hamza ta girgiza su Shamaki ne ya nuna mashi rashin kyautawar hakan yace."ranka shidade koda baza'a hukunta Barde ba ya dace kai masu magana mai dadi dan su rage radadin da zuciyoyin su ke ciki a halin yanzun.*"kamar jira ya hau Shamaki da masifa sunaji suna gani aka sama Hamza ido yace."ku bace man da gani matsiyata."cike da kulewa uwar bayi tace."A halin yanzun zamu dauki yarmu dan mu kaita makwancin ta amma kasani koda irairen mu zamu kare kaf wlh bazamu hakura ba kamar yanda kace muba masu daraja bane hakan bazaisa adinga wulakanta mu ba munaji muna gani,kasani cewa bayima ya'yane....ankama mutane masu daraja an wulakanta su balle mu damuka saba da wahala da ganin wulakanci, bazamu damu da abunda zakayi mana ba,kuma bazamu fasa neman hakkin mu ba."uwar bayi ta gama maganar cikin tafasar rai da kunar zuci."ku dauketa muje a shiryata saidai kasani wadannan mutanan sune shaidar mu akan ɗanka yaima yusrah fyaɗe kowa yaga yanda jini Ke fita daga kasanta har yanzun idan kuwa ka gardama ba majin kunyar budewa kowa ya gani."tunkan ya musa ta bude duk wanda ke wajen saida ya kauda kai gefe har shi kanshi Hamzan yakasa magana.wasuma har kuka sukeyi sannn suka dauke ta suna kuka suka tafi da ita turakar bayi... duk wanda ke fa'dar nan saida ya tafi harda Abdullahi ya kasa tsayawa daga shi sai dogarinsa aka bari jiyake kamar yai kuka,yasan bayin nan sun fishi gaskia amma bazai bari ɗan shi ya wulakanta taba a cikin Burhaan. Duk abin nan da akeyi labari ya karade Burhaan koda Hamza ya kira Barde ya tambaye shi bai musaba amma saiya dinga magana cike da gadara baisan sadda ya wanke shi da mari ba. "kai mahaukacin inane da zaka kashe yar mutane ina laifin kadinga binta a hankali kana hutawarka da ita,ko kasan abinda ka aikata zai taba mulkina? da darajar Burhaan? yanzun gayacan za'ayi mata jana'iza kasani naji kunya a gaban mutane masu daraja ka wulakantani." baki daya kwakwalwar Saude ta gama kullewa ita dai tasan daga ita sai Masau'da sukaga gawar yarinyar nan amma ya akai bayan da wowar su za'ace har ankaita Fa'da. Aranta take killata kodai Masau'da tayi mata ture dan ta huce haushinta tasan takun sakar dake tsakanin ta da Hamza ba. Tana cikin tunanin ta taji muryar Masau'da na magana"A gaskia banji dadin abunda da ɗanka Barde ya aikata ba gashi anatacin ganiyar mulki harka kara kyau gaskiane giyar mulki tana ratsaka kaga abinda ɗan kuka yajama uban sa minene mafita Hamza?"dariyar shaƙiyanci ta kece da ita. "Fitarma daga gida Masau'da tunkan nayi maganin ki."Kaga kar kaiman ihu Hamza,bayan baki daya duniya ta gama sanin abin dake faruwa kuma ya amsa laifinsa duk wani mari da zakai mashi bazai wankeku ba a idon duniya yakamata a matsayin ka na mai rikon kwaryar mulkin Burhaan ka fito a gaban kowa ka hukunta Barde yanda duniya zata shaida muddin ka kasa hakan lallai bazamu yarda ba...ai ciwon ya'mace na mace ne inda yarka Safiyyah akaima haka nasan kisa ya dace ga wanda ya aika ta abin yanzun Masarautar Burhaan tasa ido taga hukuncin da zakai ma danka Barde...ka kuskura kace zaka mareni zan fita waje infadama duniya akan nafada maka gaskia shine kace zaka haike mani sabkda na kare kaina ka marina."kallan Masa'uda kawai yakeyi yana mamakin ta itama kallan ɗage takeyi masa tana cika tana batsewa cikeda izzah gamida gadara a hankali ta tako zuwa gabansa tace."Hmmm Hamza kenan!ya kake ganin wannan maganar idan har ta fita waje mikake zato."? Murmushi ta kuma saki na raini taci gaba da cewa."Kaga Hamza kayima Masau'da biyyayya tunda nafika iya tuggu da iya taku idan ba hakaba nida kai muzuba mugani."kallanta kawai yakeyi yana tattare maganganun ta zuwa ma'aunin mizani domi rarrabewa."bari injema mutanan can gaisuwar rasa yarsu kafin muji abinda zaka yanke akan dan ka."kanshi ya buga a jikin bango ya fashe da marayan kuka yanajin tsananin bakin ciki a cikin zuciyar shi."Shikenan Barde kagama zubda mani ƙima da daraja inaji ina gani makiyana nayimani dariya ya kake son inyi da raina?Umma yazama dole in salwantar da rayuwar Masau'da na fahimci zata zamo mani barazana a rayuwa ta, tunda tagama sanin sirrina."lallai da ka tabbata nonona kasha ba yanda banyiba akan ta sirrin ta abin nan amma taki dama jira nike idan dare yayi mu binne gawar yarinyar nan da kanmu, shine tayi mana cinne dan tasa mulkin ka zai samu tan gyarɗa."lallai Goggo kamar dai bake kika haifi ne walahi billahi saidai idan nazama gawa sannan hakan zai faru nayi imani da girman mulkin gidan mu muddin da raina saidai koni ko Masau'da........ ```Allah sarki rayuwa kenan yauga soyayya tazama kiyayya shiyasa duk abinda zamu aikata musa Allah a ranmu,Allah ka rufaman asiri kasa mudace``` ```Kamar yanda kuka sani wannan labarin na``` *SADAUKIN BURHAAN* *na kudine akan naira 300 kacal duk mai bukatar wannan littafi ya tuntubeni ta wannan number 08160508316 sayen nagari maida kudi gida* *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA HUƊU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello shedar biya ta wannan number 08160508316. Yakasa zaune yakasa tsaye addu'a kawai yakeyi abubuwa dayawa sun sha mashi kai baki daya duniya tayi mashi ƙunci yarasa inda zai saka kanshi. zuwa yanzun har Asma'u tafara suma kamar mai iska ko wadda iska ta taba haihuwa ta gagareta koda mai gidan yace ya shigo ya duba halin da matar shi take ciki kin shiga dakin yayi saboda baisan yaga tsaraicin ta badan komai saboda ba matar shiba ce kuma yana bala'in kishin dan uwanshi duk da mutanan basu san ba matar shi bace,matar gidan ce ta fita da gudu ta kira wata tsohuwar mata aikinta kenan karbar haihuwa duk wahalar ta Allah ya hore mata dubaru na haihuwa gari gari ake zuwa a dauketa ta karbi haihuwa da sassarfa suka shigo da wani akwati akabasu waje ita da Asma'u tafara jika magani ta bude bakinta ta zuba mata ta hade a wahale sannan ta shafa mata a fuskarta baki daya cikin Asma'u ya juya da karfin gaske kamar zai tsago cikinta ya diro kasa. matar ta shafa mata wani maganin a saman mararta cikin ikon Allah ko minti goma ba'ayiba cikin rahamar Allah haihuwa ta taho gadan gadan cikin tausayinsa da rahamar sa Asma'u ta sintilo kwakkyawan ɗan'ta mai kama da uban sa kwabo da kwabo,tana haihuwar sa ta suma bata san inda kanta yake ba,daman tun tana nakudar matar gidan ta dafa ruwan zafi amma baki dayan su hankalin su ya koma kan ɗan saboda tunda aka haifeshi baiyi kuka ba shiyasa hankalin tsohuwar nan ya tashi ta daga shi ta sadda kanshi kasa tana buga mashi kugu amma yayi shiru ba alamar kuka da jaririn yayi hakan yasa ta dibo wani magani ta jika ta siyaya mashi a baki kamar aikin sihiri sai a lokacin ya duka uban kuka inyarare yarare haka yake rere kuka take Shattimah yayi sujjada ya godema Allah yasan Asma'u ta sauka lafiya,aje shi gefe tayi sannan takoma kan Asma'u.... ita kuma matar gidan da tsohuwar ta kira da Zaliha ta debo ruwa ta wanke jaririnta tas sannan takara tsarkake shi,sannan ta dauko kaya ta saka mashi takai ma Shattimah shi tunda ya kalli yaron nan Shattimah ke kukan farin ciki. itako Asma'u takai awa daya sannan ta dawo cikin hayyacin ta, wannan tsohuwar da suke kira da inna ita tayima Asma'u wanka da kanta ta gasata tsaf. Bakaramin farin ciki ya kama Shattimah ba bayan la'asar inna tagama gyara Asma'u taba Zaliha magunguna tace abata a kunu ko a cikin fura na sati biyu nan ta kira Shattimah tace."ɗan da aka haifa jifa ta same shi tun yana cikin ciki dan gaskia da kyal zai rayu koda ya rayu zai sha wahala kafin yasamu lafiya, amma a dinga yi mashi wanka da garin maganin dana baku."nagodw inna zamu kiyaye da izinin Allah."godiya ya sake yimata sannan ya bata kudi masu tsoka yakara mata godiya mai tarin yawa duk abin nan ashe Zaliha taji ba karamin tausayawa Asma'u tayiba gata da karancin shekaru amma ta hadu ta iftila'in rayuwa danma Allah yasa rayayya ce da anrasata. bata bata lokaci ba ta hadama Asma'u kunun kanwa,ta zuba mata maganin da inna ta bata ta matsamata saida ta shanye shi tas,cikin ikon Allah sadda za'ayi mangariba ruwan nono yazo nan Zaliha ta gwada mata yanda zata shayar da jaririn ta,ba laifi yana sha. lokacin da Asma'u ta dauki dan'ta ba karamin son shine ke shigarta ba a lokaci daya sai kallan shi takeyi cikeda so da kauna koda batasan yanda Sadauki yake da yana yaro amma tasan suna kama da jaririn ta,ana gama isha'i Shattimah ya shigo da Malan Audu sunan mai gidan kenan ya dauki dan yai mai addu'a sannan yai masu barka yaba Shattimah jaririn,sai kallan dan yakeyi yana karaji yana shiga cikin zuciyar shi,kallan ta yayi yace."wane suna kika zabawa dan naki."? Kallan shi tayi cike da mamaki"da'na fa kace karkaman ta yanzun baida uban da ya wuceka a duniya karka manta yaya Moh'd baida kamarka dan haka na mallaka maka wannan damar ka zaba mashi suna"Hmmm Asma'u kenan kinsan Sadauki bai cikin hayyacin shi komai zai iya aikatawa amma walahi duk duniya baida buri da ya wuce na wannan ɗan kuma yana son shi yana kaunar shi kune iyalin shi kuma kune farin cikin shi inasan ɗan uwa na kuma ina kaunar sa ji nike kamar ciki daya muka kwanta dashi...wlh Asma'u duk abinda zamuyi ma Sadauki dagani har Tafeedah bazamu biya shiba,duk cikin mu bamai mutunci da kishin dan uwan shi kamar Sadauki shiyasa kikaga naba rayuwar shi mahimmanci kiyafe mashi lallai an cutar dake amma kisani bayin kanshi bane bake kadai ba duk wani makusancin shi anzalince su wannan ɗan na Muhammad Abduljalal Muhammad ne,ki fada mani mikike so a sama yaron nan."? "Shikenan na fahimce ka, kuma nayafema yaya Moh'd, ina son kasa mashi AHMAD. arazane Shattimah ya kalleta"miyasa bazaki sama shi sunan Mai martaba ba?" ajiyar zuciya ta shide tace."ko shi kanshi abinda mahaifin shi zaiyi kenan ka canci haka kabada gudunmuwa mai yawa daga rayuwata data wannan yaron haka rayuwar Abba da Ammi harda Juwairiyyah dashi kanshi Sadauki kabamu gaggarumar gudunmuwa bamu da abinda zamu saka maka da shi daya wuce ince Allah yasaka maka da mafificin alkhairi Allah yabar zumunci mai daurewa har abada."bakomai Asma'u ba abinda ban iyayi akan iyalin Sadauki Allah yarayama na shi cikin aminci da turbar addini."Amin ya Allah."nan yaima shi huɗuba yasa mashi Ahmad kamar yanda ta bukata..... "gashi Allah yaraya Ahmad bisa sunnar ma'aiki(SAW) kuma Allah yakara maki lafiya mai anfani."Amin yayana." _ZAIRANA_ Sadauki ne ya hada kayan wanki kamar yanda uwar gijiyar shi ta bukata yana gama hadawa ya tafi bayan sashen ta yafara wanki duk da bamasu yawa bane amma jiyayi kamar sunkai kala hamsin saboda bai saba da wahala irin wannan ba amma haka yasama kanshi jajircewa ya fara ɗikar wanki kamar ba gobe bai dauraye kaya sai ruwan yakoma fas sannan.... Zubaina ba ma'abociyar zuwa bayan gida bane amma saboda ta dinga ganin wulgin Umar tana jindadi shiyasa ta zagayo baya ta zauna saman kayatacciyar shimfidar ta hadimanta nata yimata tausa amma baki daya hankalin ta na kan Sadauki koda ya karasa wankin ko kallan inda take baiyi ba ga gifta ta gefenta yayi shanyar kayan.... ita kuma duk sadda Umar yaki yimata magana ba karamin bata mata rai yakeyi ba acewar ta ai bawan ta ne dole yaimata biyyayya shi kuma baisan yawan magana shiyasa ko sun hada ido yake nuna kamar baisan da itaba bayan yagama shanyar shi ya hada kaya zai tafi ta kirashi."UMAR."tsayawa yayi saidai bai juyoba kuma bai tafi ba yakai minti ɗaya kafin ya juyo a miskilance tahowa yayi inda take kamar baisan taka kasa haka yake tako cikeda izzah kallan shi kawai Zubaina keyi koda ya iso tsaye yayi akanta maimakon ya duka sai ya tsaya a dakile yace mata."gani."tun daga sama har kasa take kallan shi a ɗage sannan tace."haka ake girmama mutane a garin ku."? yi yayi kamar baisan da shi take ba,saida fadila tace mashi."Umar ka duka."a nutse ya duka saidai yaki kallan fuskar gimbiya Zubaina."Umar miyasa baka girmama na sama dakai."?kallan daya watsama gimbiya Zubaina saida ya haddasa mata faduwar gaba dakewa kawai tayi a kausashe cikin muryarsa mai amo yace."bangane mi kike nufiba."?Baki daya kwarjinin shi ya hanata magana saidai kallan sa da takeyi.....sake tamke fuskarsa yayi yace."kinyi shiru?karfa kimanta Umar nike kuma bawane ni marar yan'ci taya zanƙi mutunta mutane bayan kullun sai Abba Ado ya fadaman waye ni da matsayina nidai bana son shiga rayuwar mutane balle wa'anda suka fi karfina,karki manta ke fa uwar daki na ce,kada kiga inayi maki magana ba yanda kike so ba,nasan da sannu zan koyi komai....nabarki lafiya gimbiya Zubaina." Tunda taji Sadauki ya ambace sunanta sai taji kamar yafi kowa iya sarrafa shi baki daya amon muryarsa da sautinsa ke yawo cikin kunnuwanta yana ratsashi ta ko ina har ya tafi batasan ya tafi ba, saida ta dawo daga tunanin data lula sannan taga bainan a sanyaye ta tashi suka mara mata baya takoma dakinta tarasa meke damun ta gamida Umar gashi koda batasan soyayya ba tasan ba son shi takeba, dan tasan ba haka so yake ba,itadai kawai tasan Umar na burgeta amma aiba abinda zatayi da BAWA a matsayinta ba gimbiya Zubaina mai takama da kyawu gamida usuli. Mardiyyah ce zaune a cikin gidan yarin gilba ta rasa mike mata dadi tun tana kuka har ta dangana zuwa yanzun duk tayi baki ta rame kamar ba ita ba,duk da tasamu labarin mijinta bai mutu ba amma bai hanata shiga damuwa ba musamman batan da dan'ta yayi. labari ya samesu Barde yaima Yusrah fyade taji dadi matuka amma bataji dadiba da Yusrah ta rasa ranta ba,duk da suna gidan yari daya da Juwairiyyah amma ta rabu da haduwa da ita sau biyu a sati ake fiddo su asasu aikin wahala a nan ne suke haduwa da yarta. Waziri Bashir ko fitowa ba'a barin shi yayi tsaro ake bashi bana wasaba, yau yana daga cikin ranakun da Hamza yaba Hajara yar waziri Bashir damar ganin mahaifinta saida aka caciketa tas sannan ta shiga koda ta isa sashen shi ba karamin kuka tashaba yanda taga mahaifinta ya lalace ya rame ko magana bai iyayi sosai tsabar azaba daya sha. koda yaga yarsa murmushi kawai yakeyi na murnar ganin tilan yarsa,saida ta duba taga ba mai kallan ta sannan ta saka hannu cikin iner dinta ta fiddo daurin fura taba mahaifinta ya shanye ta dauko wata ledar ruwa ta kara bashi ya shanye sannan ta sake ledojin cikin jikinta ba karamin dadi waziri Basheer yaji ba nan ta fadama shi ranakun da zata dinga zuwa ta duba shi,nan ta fada mashi yanda sukayi da Hamza ya tsorata yana shakkar su Hamza kuma baisan yaga abinda zai taba mashi iyali suna cikin ganawa akace mata lokacin su ya cika nan tayi mashi sallama ta tafi. Safiyyah ce kwance magashiyan yau kimamin kwanan ta bakwai tana nakuda amma haihuwa taki kowa ya fidda rai ba irin maganin da basu bata ba amma ba amo ba labari duk ta kumbure ta suma har kabari angina mata amma saita farfado raban da gimbiya Kursiyyah tayi bacci harta manta danko Goggo saidai tayi gyangyadi daga zaune, amma tunda gimbiya Masau'da tazo dubata sau daya ba takara bi ta kansu ba,koda ta kawo masu maganin nakuda tana tafiya suka yarda shi acewar su karta cutar masu da diya.... ```Haka rayuwa take duk abinda kakeyi haka kake ganin kowa yana aikatawa ga rashin yarda da kowa,ba'aima Allah dubara kaidai ka kamanta gaskia komai kankantar ta,Allah na tareda mai gaskia``` Da haihuwa ta taho gadan gadan saita koma duk wasu dubarun su sun kare har bokayen su sunyi sun gaji sai da sukaga zata wuce kiyama sannan suka fara addu'a amma saida ta kara kwana ta yini sannan Allah yakawo haihuwa a shitatan haihuwar dire tayi aiko ta diro yarta mace mai kama da yan uwanta dandai ita baka ce diyar koda suka duba suka ga 'ya mace suka haifa ba karamin bakin ciki suka shigaba ji suke kamar su kashe yar dan takaici da bakin ciki koda Hamza yasamu labarin haihuwar diyar tasa da sauri ya shigo dakin amma ana bashi yaga ya'mace ce saiya dungurama uwar diyar ba karamin tashin hankali Safiyyah ta shiga ba, duk da taso ta haifi na miji amma da taga macen sai taji tana son yarta a haka,ita ko Kursiyyah murmushin yake kawai takeyi amma badan tana murna ba dan karta nuna ma Safiyyah batasan yarta taji ba dadi dan tasan soyayyar da' da mahaifi, ba kunya Hamza yace ma Barde."ka dauko yar nan a kasheta saboda bata da anfani a wajen mu nida nikeso tsatsona suci gaba da mulkar Burhaan amma saita fara da 'ya mace."kuka Safiyyah ta kece dashi ta hana yarta taita kuka tace."ina son ya'ta a haka."Goggo ta hana su daukar mata ɗiya acewar ta ai yanzun tafara haihuwar wani lokacin ta haifi na mijin,sannan Hamza ya kyale mata diyarta....ranshi ba dadi haka ya fita yana bambamin bala'i. _Allah karabamu daga aikin jahilai minene aibun ya' mace,wani lokacin ma tafi namijin amma_ _yanzun saboda gado sai mata aita hauka kedai kinemi mai albarka,_ _ya'mace kyautar Allah ce Allah ka azurtamu da zuri'a mai anfani kuma mai tsoron Allah 🙏_ Haka rayuwa ta kasance Safiyyah bata iya baccin kwarai saboda taba diyarta kariya kar a halaka mata ita,ta sama diyarta Kursiyyah sunan mahaifiyar ta,ko arzikin huɗuba bata da ita ga uwa bamai ilimin addini ba bare tayi mata da kanta..... Shiko Sadauki koda yakoma masaukin su kwantawa yayi sai yaji uban gidan sa na kiran shi,koda ya ta shi murmushi ya sakar mashi yace."sannu da dawowa."Yawwa Umar ya aiki."lafiya lau."takarda ya dauko ya bashi yana budewa yaga daurin kifi yaji dadin karramarwa da yayi masa budewa yayi yafaraci saijin dadi yakeyi. shiko Ado duk sanda yaga Umar na farin ciki sai yasamu kan shi cikeda nutsuwa sai yaga kamar ɗan shi Umar dan dai ya rasu tun yana yaro saidai shi baki ne,Sadauki ko farine kuma kyakkyawa ne ajin farko. Ado ya tuna da sakon Yarima Ammar ya maida dubansa ga Sadauki yace."Umar idan kagama zan aike ka wajen Yarima Ammar..... *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA BIYAR *Masu tambayar nawa zasu sayi document na Izzah ko Mulki kusani free book ne Sadauki ne na kudi shima akan naira 300 kacal,Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyanki ta wannan lamba 08160508316.zaku iya cigaba da biyan kudin ku dan kasancewa cikin grp.* Koda yaji Abba Ado ya ambaci Ammar hakanan yaji gaban shi na faduwa ya rasa dalili. koda ya gamacin soyayyen kifin da Abbansa ya siyo masa kaya ya mika mashi yace."Ka kaima Ammar kace injini kaji ɗan albarkana."kwatancen wajen yai mashi bai jima ba yatafi. tun daga taskar bayi ake kallan shi kowa yana fadin albarkacin bakin sa akan kyawun sa tun bai damuwa da irin kallan da suke mashi harya fara tsarguwa da kanshi,sadda kanshi yayi kasa yaci gaba da tafiyar shi har ya isa sashen Ammar neman izini yayi hadiminsa yai mashi iso zuwa wajen shi a falo ya iske shi zaune. tunda Sadauki ya taho Ammar ya rasa natsuwar shi baki daya kallan bege da so yake masa..yana iskwa gaban Yarima Ammar ya duka ya gaida shi sannan ya dauko kaya yabashi yace."inji Ado yace inkawo maka."hankalin Ammar ba akan aiken Sadauki ya ya mika masa yake ba baki daya yana kan fuskar shi yagama shagala da kallansa yanda yaga yaki karba hakan yasa ya dago kansa a hankali ya dubi Ammar yaga kallan shi kawai yakeyi yarasa dalilin dayasa mutane ke kallan shi irin haka kodai yana da wani aibun ne a jikin shi shima kallan kanshi yakeyi saidai baiga abunda suke kallo a jikin shi ba..... Sadauki yata shi zai tafi batare da ya jira umurni daga Ammar din ba."Tafeedah."yakira sunan shi take saida yaji kirjin shi ya buga jin kalmar Ammar ya ambace dashi cigaba da tafiya Sadauki yayi batare da ya dawo ba da sauri Yarima Ammar yasha gaban shi."bakaji ina maka magana."? Dan rufe manyan idanuwansa yayi ya bude yace"Sunan daka kirani da shi ya sakani rudani....abinda nasani sunana Umar kuma ni bawa ne."mamaki karara saman fuskar Ammar yasan dai baiyi kama da bawa ba bako shakka ya hada jini da jinin sarauta ko masu tarin arziki yanayinsa kadai ke fallasa nasabar sa."kafadaman gaskia dai."?"Iyakar gaskyar kenan abunda na sani ma fada maka."sake maimaitamin abinda ka fada."dan murmushi ya saki wanda ya kara bayyana usulinsa da kyawunsa yace."Umar sunana kuma ni bawa ne."ba dan an aminta dakai ba amma zaka iya tafiya."a hankali ya dan karkarto da kansa ya dubi Ammar kallo daya ya sake cire kansa gefe yace."ka tambayi Ado zai baka labarina." Har yanzun zuciyar Ammar ba harbawa badan komai ba yana mamakin lamarin Umar aransa yana ayyana abubuwa da dama aransa."haka Allah ke halittarsa kayimani kama da wani abokin arzikina sunan shi Tafeedah saidai ba anan garin yake ba garin su da nisa gaske a kasar Cameroon yake cikin Masarautar Burhaan."du da kasancewar Sadauki na cikin yanayin asiri hakan bai hana gaban shi faduwa ba ya tsananta faduwa sosai ya shiga cikin dogon tunani amma yakasa tuna komai....saima aikin kallan Ammar din yakeyi kamar wanda ya rasa wani abu nashi....izinin tafiya yai mashi."shikenan Umar zaka iya tafiya saidai zan nemeka zuwa wani lokaci."gyada masa kai yayi sannan yai mashi godiya ya tafi. ranar Ammar kwana yayi yana tunanin Umar yayi mamakin yanda yayi Kama da Tafeedah,sai tuno ranar da sukazo wasan da'ba yakeyi. shiko Sadauki koda ya koma daki ɗan gutun bargon shi ya shimfida ya kwanta,sai tunanin maganar da Ammar yai mashi yakeyi har yayi bacci bai tuna komai ba,wannan kenan. Zaune take a dakin gimbiya Bilkisu sai murmushi takeyi ita kadai da kaganta zakasan tana cikin farin ciki,sai magana gimbiya Bilkisu takeyi mata saidai baki daya hankalin ta ya tafi wajen tunani har saida ta taba ta sannan ta dawo cikin hayyacin ta."lafiyar ki kike tunani irin wannan? inata magana amma baki jini ba?" shagwabe fuska Gimbiya Zubaina tayi cikeda sangarta tace."Ummi walahi tun shekaranjiya nikejin nishadi a raina narasa abindake damuna,kulun ina cikin farin ciki da nishadi."hmm ya'ta kenan fadaman miyasame ki na farin ciki."murmsushi tayi tace."kiyima yarki addu'a kawai....ina son zuwa wajen Anty Mabaruka ina kewarta sosai."da shashantar da zancen ta hanyar kawo labarin Mabaruka."da kin kyauta saidai kinsan Abban ki bai son kina masa nisa."Ummi nasan bazai hanani zuwa wajen Antina ba"Allah yasa." "Amin Ummi."sake gyara kwanciyar ta tayi tad daura kanta saman cinyar ta tace."yaufa nan zan wuni wajenki bansan hayaniya zan shiga daki in kwanta."yakamata kici abinci."nakoshi daga wajen Anti Mufeedah na gudo,ita dole saina tayata aiki yaya Aryan, zaiyi baki."shine ko kitayata."haba Ummi duk hadimanta saina tayata aiki dazun muke abu daya nagaji shiyasa na gudo nan in huta."Kema watarana kinaso atayaki aikin ai"idan na huta anjima zanje intayata."shikenan ya'ta ki huta lafiya." ********************* Wai kai yaushe zaka daina wannan damuwar iyeh? bakada aiki sai yawan tunani gaskia muddin bazaka rage wannan damuwar ba ranka ne zai mugun baci."kiyi hakuri Umma narasa yanda zan cirema kaina wannan damuwar saidai nakasa kullin raina nabani Juwairiyyah na cikin damuwa,gasu Ammi suma suna cikin yanayi...wallahi Umma ko bacci nike sai Sadauki ya fadomani a cikin zuciyar ta"Hakuri zakayi Mukhtar addu'a kawai zamu dinga yimasu yafi wannan damuwar? jiba kaga yanda ka koma ko abinci baka san ci duk kayi baki ka rame...gaskia banjin dadin ganinka a haka indai kanasan kaga farin cikina yakama ta kadaina wannan damuwar."shikenan Umma inaso insamu lokaci in kaima Umman Shattimah ziyara."daka kyauta gaskia...yanzun dai yakamata kaje kahuta hakanan."Toh Umma sai anjima."Haka rayuwa takasance ga Tafeedah baida wata walwala balle ya samu sukuni tunda ya baro Burhaan yakasa samun nutsuwa sai yaga kamar akwai abinda ke faruwa da yan uwan shi...... Akwana atashi yau ake sunan Asma'u ba kananan kuɗi Shattimah ya kashe ba shida Malan Audu sukaje kasuwa suka sawo duk abinda ake bukata ko rago saida ya yanka ma Asma'u ukku,kamar yanda kuka sani yaro yaci suna Ahmad.gayyatar mutane malama Zaliha tayi duk wata mace dake kauyen nan saida ta shaida sunan Ahmad akaci kasha har akabar shi ko washe garin suna bayan angama soye saida Asma'u tasa Zaliha ta dibe nama ta aika mutanan karkaran nan, sannan ta dibarma mutanan gida,wata katuwar silba ce ciki akasama Shattimah yasamu wani waje ya juye haka kowa yaita farin ciki nan mai jego taci gaba da samun kulawa ta musamman. -------------------------- Sadauki ke sallama da gimbiya Zubaina yakai minti shabiyar tsaye bata fito ba baki daya ya gama kulewa wannan zuciyar na nan ba abinda ya sauyata koda ta fito cike da izzah gamida kasaita ta isa saman killatacciyar kujerarta ta zauna wadda ta kawati da ado.na lu'u lu'u da jawhar a jikinta. kallo daya tayi mashi ta kauda kai,yanda taga yasha mur ya turnike fuskarsa ba alamun annuri a cikinta saima ya kara mata kyau,takai minti biyar zaune amma Sadauki bai bi ta kanta ba bare yaje wajenta yakai gaisuwa saida taga yaki karasowa inda take sannan ta kira shi...."Umar bazaka isoba koni zanzo in sameka anan."sai a lokacin ya iso inda take saidai ko kallan ta baiba balle tasa ran gaisuwa a gareshi....kayan wankin ya mika mata hakan ba karamin bata mata rai yaiba,daga tsaye ya bata kayan.....da masifar ta ta rufeshi"waikai wane irin mutun ne kanada hankali kuwa? gimbiya Zubaina kake ba kaya a tsaye ko da'a babu? meyasa kake son batamani rai ne wai?baka iya gaisuwa ba? baka mani magana cikin biyayya a matsayinka na bawa na!ya kake so inyi maka ne."?kallan ta kawai yakeyi mamaki take bashi shi baisan me take son yaimata ba, tasa shi aiki yayi me kuma mi take so yai mata."kiyi hakuri."Dago kyawawan idanuwanta tayi ta daura masa tanajin wani irin nishadi na ratsata wanda takasa gane na minene ya bata mata rai amma kuma ta gaza hukunta shi."yanzun me kike so in maki."?ya tambayeta batareda ya sake kallanta ba"Ohni Zubaina wannan wane irin bawa ne mai yawan miskilan ci shidai ko magana zai mani a takaice yakeyin ta daganin shi baisan yawan magana...kuma tunda yana bawana ai baida wani zabi."a zahiri tace."inaso duk bayan wasu lokuta kadinga zuwa kana gaidani ba lallai wanki ne kadai aikin kaba,yanada da kyau ace kana cikin hadimai na masu kulawa da duk wasu bukatu."Ohh ni Umar wannan yarinyar ta cika san izzah da gadara kodan taga tanada kyau shiyasa take nuna isa? nifa bansan aikin wahala wai duk inda zata inbita tana mace sai kace wani akalan ta "Me kace? "Allah yakaimu." Murmushi kawai tayi mashi duk abinda yace taji shi,shima sai ya tsinci kanshi dayi mata murmushi..... Wanda yai silar tsayawar numfashinta na wucin gadi ta rasa dalilin dayasa Umar ya shiga ranta ba kadan ba bata san taga ko faɗa tanayi mashi....kaji wai shi baisan wahala daganin jikin ka yasaba jin dadi amma ko ya'akai yazo a bawa ikon Allah....aranta take sake sake duk akan Umar din."zan iya tafiya?"Ba damuwa."ta bashi amsa tana ci gaba da kallansa."godiya nike uwar gijiya ta,ki huta lafiya."gyada mashi kai kawai tayi gashi tanasan taji amon muryar Umar din yana magana kasan cikakken namiji ne yayi maganar daman tana saon Jarumin na miji gaskia Umar yayi saidai bawa ne..... yau gimbiya Mabaruka ta tashi da nakuda cikin ikon Allah batafi jimaba ta haifo yarta mace kwakkyawa da ita ba karamin farin ciki Haidar yayi ba, tsabar murna ranar ko Mabaruka tasha kyautuka,daman shi yafisan diya mace a rayuwar shi ya dauki son duniya ya daura a diyar tunda aka haifeta da kyal yake ba yan barka ita kullin tana hannun shi kamar ya hadeta dan kauna ```Hmm wayaga su Haidar anzama Abba Allah ya raya` ****** Yau ake sunan 'yar Safiyyah kai kace ba'a komai Hamza ya hana taron suna dan kawai an haifi mace ko ragon suna kin siya yayi ga duk kudin data tara a wajen Sadauki ya anshe ya cinye saidai Jarmai shi ya siyo mata rago daya ya yanka mata aka sha sunan Kursiyyah tana cemata Amira...ita kanta Safiyyar duk ta rame tayi baki sabida bata samun kulawa ko kadan tunda ta haihu danma tana samun dan rangwami wajen Umman ta.... Zaliha ce keta kuka yau su Asma'u zasu wuce hatta Asma'un kuka take saboda ɗan zaman datayi dasu har sun saba wanda yau kwanan su ashirin da daya da haihuwa kimamin sati ukku kenan amma ji sukeyi kamar sun shekaru aru aru tare. Shattimah ya basu kudi masu yawa sannan sukai ban kwana ya daurata a doki,ya anshi ɗan ya rungume a doki sukaciga ba da tafiyar su..... Baki daya bayin Burhaan tunda akai addu'ar bakwai na Yusrah kullin sai sunje fa'da sunyi zanga zanga wanibi Hamza ya kyalle su,wani lokacin kuma yasa aita dukan su amma hakan bazaisa su daina ba duk sun kara zama abin tausayi,tsabar rashin yan'cin da suke fama dashi a cikin Burhaan..... Labarin haihuwar Mabaruka ne ya karade Zairana sai murna akeyi yau kimamin kwana biyu kenan da haihuwar. gimbiya Rukayya tacema Zubaina ta shirya zasuje Agadas suga jaririya.... tana murnar zuwa taga yar uwarta da jaririyar su,amma zuwa yanzun tasaba da Umar bata san yana mata nisa ta fahimci idan tana ganin shi yana sakata nishadi saidai haryanzun ta rasa dalilin hakan...amman tafi ganin kawai dan yanada kwarjini da haiba shiyasa..... Tofah wata sabuwa inji yancaca nikam in akalar Zubaina ta fuskanta ko kusan abinda take nufi sai naji daga gareku. Shiri kawai gimbiya Rukayya takeyi yau zasu tafi Agadas wajen Mabaruka dan ko Sarki Abdurrahman haka ya hada sha tara ta arziki yace aikaima diyar shi,gimbiya Amina ba abarta abaya ba ita tahada kayan uwa... Abangaren Zubaina kuwa jitake kamar karta tafi batasan Umar naimata nisa ko kadan ganin shi nakara debe mata kewa tunda Fadila ta hadama uwar dakinta kayanta take ta dube dube ko zataga Umar ya shigo amma shiru kuma har magana saida taimashi akan ya dinga shigo wa akai akai amma baizoba, wannn dalilin ne yasa ta kudurci a zuciyar ta lallai saita yima Umar wulakanci ta fahimci baibin dokokin ta,yana bawanta zai dinga bijirewa umarnin ta. har Mai martaba ya aiko ta fito ita ake jira amma Umar ba amo ba labari haka ta fita duk batajin dadin jikin ta,ta fahimci Umar ya shiga ranta kuma tana tausayin shi abinda bata taba jiba akan dan Adam sai akan shi yanzun tana kimanta bawan ta, gaskia wannan lamarin na damunta,harta isa sukayi sallama da Mai martaba suka kama hanya. kafin su fita kofar Masarautar zairana ta hadu da Umar ya guyo uban itace abayan sa zaikai madafa inda akema bayi abinci kallan shi kawai takeyi a take taji tausayin shi,kuma taga sun hada ido dashi tana kan doki,saidai shidin ko kallanta bai kuma ba bare tasaran zai gaidata,gashi dasu Umman su take balle tayi mashi magana. haka Zubaina ta tafi tana mamakin halaye irin na Umar shidai mutun ne wanda duk mulkin ka ko arzikin mutun bai damun shi,balle yadinga yimaka daddoha yana kamun kafa,kamar yanda sauran bayi keyi,ba abinda yake hada shi da Zubaina sai gaisuwa,yaimata aikin da ta sashi. daman shi baisan yawan magana ko kadan shiyasa bai shiga harkar kowa, sai Abba Ado shima ya dauke shi mahaifin shi, shiyasa wasu bayin ke ganin cewa Umar ya fiya girman kai dan yana ganin Allah yai mashi kyakkyawar halitta shiyasa yake ganin kamar yafi kowa,dan ma yazo a bawa aida abinda zaiyi sai yafi haka.... (Allah Sarki da kunsan waye Umar da baku fadi hakaba mutumin da ya manta kanshi da kowa nashi taya zai san abinda ake kira girman kai? Kawai dai rashin son magana jinin shi ne da kasaitar da kuke fada duka) _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHIDDA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biya ta 08160508316. Ku hanzarta ku mallaki naku domin wannan tafiyar ta dabance,na tabbata bazakuyi dana sanin siyen sa ba,kunji salon Izzah ko Mulki to yanzun wasan zai soma domin ba'ayi komai ba,kedai ki kasance da Jamila yar mutan Kankia🥰 Zuwa yanzun gimbiya Masa'uda ta addabi rayuwar Hamza banda zagon ƙasa ba abinda takeyi masa ba kadan ta saki jikinta da bayi ba hakama talakawan Burhaan badan komai ba kawai dan ta cimma burinta. shiko Hamza yabi ya damu kanshi akan labarai daketa yawo akan abinda Barde ya aikata ya ketawa BAIWA haddi magana ta karade illahirin kasa da kewayen kasar Burhaan da,harya fara samun sakonni daga sassa daban daban na kasar Cameroon da sauran Masarautu daban daban dan tabbatar da gaskiar lamarin da ake shashi fade akai.... kuma yasan ba mai mashi wannan tuggun kamar Masa'uda shiyasa yasa a ranshi sai yayi maganin ta. Koda su Zubaina suka isa cikin Agadas baki daya tarasa mike mata dadi danma ganin Umman ta shiyasa ta saki jikinta dayake ita ranar zata koma Zubaina da gimbiya Rukayya su za'a baro,tunda suka iso Haidar ke murna yanata dawai niya dasu,har yanzun idan ya kalli Zubaina saiya kara yabawa da kalar baiwae da Allah yaimata shidai yana kaunar Zubaina duk da ya fidda son ta a zuciyar shi amma yasan kaunarta ajinin shine,ba karamin fira sukeyi da Zubaina bana yana jin dadin yanda ta saki jikinta da shi fiyeda Da..... tafiyar da Shattimah keyi da Asma'u harta fara gajiya amma sai yace mata saura kadan su isa.... _Ko ina Shattimah zaikai Asma'u,a sannu dai zamuga manufar shi_ Sadauki ne zaune a dakin su,inda Abba Ado ke kara fadama shi kalar rayuwar Masarautar Zairana da kuma irin dabi'un uwar dakin shi....shidai mamakin ta kawai yakeyi yanda bata da ragi ko kadan a rayuwar ta,shidai bai son mutun mai yawan faɗa amma yasan tanada nata tsarin shiyasa takeyin hakan."kaji abubuwan dana fada maka?Umar ka kiyaye ka zamto mai yawan ɗa'a da biyayya ga uwar gijiyar ka duk abinda ta saka kada kayi mata musu sabida gimbiya ta tsani musu kuma tana son agirmamata sannan tana son a martaba izzar ta." "naji Abba..ni daman bansan hayaniya bazan yadda in shiga harkar taba bare tayi mani ihu."hakane amma kasan aiki da mace duk yanda kake kiyayewa saika kara hakuri da ita."Shikenan Abba zan kula."yawwa dan albarkana...yanzun dauki abincin ka kaci."minene wannan abun Abba."?Murmushi Ado yaima dan nashi yace." wasa-wasa ce nasan zatayi maka dadi."shima murmushin yayi yace"Gaskia ta burgeni dagaji zatayi dadi."kardai ace baka taba cinta ba Umar."? wani irin faduwar gaba ya riske Sadauki sai ya rasa amsar da zaibawa Abban nasa...... Gyara zamansa Ado yayi ya fuskance shi da kyau yace."niko ina so insan kai dan ainahin inane?wane gari kake."koda Sadauki yafara cin abincin shi ajewa yayi yana kallan Abba Ado...... yaka tsareni da kallo har haka lafiya."? "Kai zanyi ma wannan tambayar Abba!waye ni?daga ina nike?Menene asalina."?shekeke yayi yana kallansa cikeda mamaki taya za'ayi mutun magidanci kamar wannan ace baison kansa ba gashi a zahiri ba ciwon haukane ya kamasa ba bare ace baida hankalin da hankalinsa ras ya akai hakan ya faru?rasa amsar da yake nema yayi yaci gaba da kallansa."hmm!banda wannan amsar Abba abinda nasani sunana Umar kuma ni bawa ne! wanda ya saba da wahala marar 'yanci bansani ba ko zaka gamsu da ansoshin da na baka."numfashi mai zafi ya shidar har yanzun baice ma Sadauki komai shima ajiyar zuciyar ya shidar yaci gaba dacewa."bansan kalan wannan tambayar Abba tunda banda amsar su,amma kai idan ka sani ka sanar dani dan Allah waye ni."? Hawaye kawai Ado yakeyi daman shi yadaɗe yana tunanin Umar bai cikin hayyacin shi duk wanda baisan waye shi ba ai dole a tausayama shi da gani akwai lamari mai girma dake tattare dashi.... Sadaukin Burhaan na kudine akan Naira dari Ukku(300)domin karin bayani tuntubi wannan numbar 08160508316.siyen nagari maida kudi gida. tunda Tafidah ya tashi ya gama shiryawa zai tafi wajen Umman Shattimah yana so ya ganta sallama yaima mahaifiyar shi sannan ya hau dokin shi ya kama hanya,saidai daka ganshi zaka san yana cikin damuwa duk ya rame yayk duhu..... tunda Allah yasa aka fiddo su Ammi domin suyi aikin bautar da suka sabayi anan ta hadu da diyarta duk tayi baki ta lalace ta rame ga wani irin mugun zazzabi da take fama dashi amma duk da haka saida aka fiddo ta dauke take da wani dargagen dutse zasu kaishi a wajen aje kayan itacce da manyan duwatsu....daidai ta kusa isa wata irin juwa ta dibeta take fadi saman dutse ya fasa mata hannu jini ya fara zuba da sauri Ammi ta rugu ta rungume yarta ga Asthmar ta,ta tashi daman muddin tayi aiki mai yawa sai tayi kamar ta kasheta haka take mata. kamar jira wani katan dogari yazo yaita buga masu wata gurɗime miyar bulala ba Juwairiyyah hatta Ammi jitayi kamar ta mutu haka yasasu tashi amma Juwairiyyah bata iya ko mikewa,bako tausayi yacigaba da bugunta kamar jaka ko daga hannun ta bata iyawa,da Ammi taga zai kashe mata diya da sauri tazo ta rungume ta sai kuka take,ita ko Juwairiyyah tashin hankali yasa ta suma,duk da haka dogarin nan bai fasa dukan suba saida wani babban bafade yazo ya hanashi sannan ya sahirta masu. wasu bayi ya kira yasa suka dauki Juwairiyyah suka kaita wata inuwa, nan yasa Ammi tacigaba dayi mata fiffita,ko wane bawa saida ya zubdawa su Ammi kwalla wai yau uwar Sadauki ce akema wannan ukubar sai kace bata a kowa,rayuwa kenan..... gimbiya Zubaina a cikin maroon din lace tasha kyau kamar wata amarya anata shagalin suna kai kace itace mai jegon kaya kala daya sukasa da Mabaruka sai zolayar Zubaina ake wai jaririya taci sunan ta lallai soyayya tayi riba...shiko Haidar ya rike hannun matar shi cike da zolaya yace."ga karshen soyayya nan...kawai dai kyautata wane,kuma bai kamata amanta wanda ya hada aikin alkhairi ba." ita dai Zubaina ta rike yarta sai murmushi takeyi duk wanda ke wajen nan saida yayi tubarakallah domin kullun kyawunta kara bayyana yakeyi yanzun take kara zama budurwa. ranar haka aka wuni ana shagali har dare baki daya Zubaina tagama gajiya tana wanka kwanciya kawai tayi amma ta gagara bacci Umar ke fado mata a rai,miyake yi?yaci abinci ko baici ba?abinda taje sakawa aranta kenan ta rasa yanda akai ta damu da bawan nan har haka?kafin wani lokaci har bacci yai awan gaba da ita..... _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Saboda Allah *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA BAKWAI Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello kituro shaidar biyan ki ta 08160508316. Waziri Bashir ne daure kamar wani barawo an riko shi sai dukan shi akeyi ba inda aka gurfanar dashi sai sashen Hamza a kishingide yake ga bayi da hadimai sunatayi mashi hidima,kamar ba gobe. Tunda aka shigo da Basheer ya duka gaban galadima Hamza,duk wanda hamza ya kalla sai yabar falon a sanyaye saida ya tabbatar da kowa ya watse daga shi sai Basheer sannan ya dauko kofi ya zuba ma Basheer dafaffiyar madara sai kamshi takeyi ya mika mashi cike da izzah gamida tsantsar gadara....kallan kofin kawai yakeyi saboda yasan halin Hamza zai iya anfani da wannan damar yaga ya halaka shi."karbi madara kasha koba komai kana bukatar hakan"Aaa nagode ko can bani shan madara."Hmm Basheer kenan dadai bansan waye kaiba,kaga malan umurni nike baka ka maida hankali kasha madarar nan tunkan nasa ka cikin ukuba...inda ina son inkasheka bata hanyar baka madara zanyi nasaraba nabarka ne don kagama shan ukubar duniya sannan ka tafi barzahu kaga Basheer sha madara."yana kyarma ya karba don yasan ba imani Hamza ya cikaba kuma idan yayi magana bai canzawa shiyasa ya karba abinka da maijin yunwa cikin kankanin lokaci har ya shanye madarar nan tas saidai kofin."kokaifa Bashir kasan shi mayunwaci bai jimirin ungu....ka taimaki kanka dan ba abinda Hamza zai fasa kamar yanda kasani meyasa nabada umurnin akawoni kai nan basai mu dinga jayayya dakai, muddin kasanar dani gaskia nayimaka alkawalin zanbaka makudan kudin da harka mutu saidai kaci abinda kaci amma bazasu kareba zan hada maka da jauhar da tarin lu'u lu'u da ingantacciyar azirfa da zinariya zan baka jajayen rakuma har guda goma,da tarin shanuwai da dawakai masu nagarta,sannan zaka dauwama a matsayinka na waziri a cikin Burhaan har abada.....Basheer ina zoben da yaya Abduljalal ya baka."?ya ida maganar yana murmushu. (lallai kam ni Hamza zaima wayo natabbata koda na bashi duk wa'anan alwakalin da yayi bazai mani suba daga karshe zaisa a kashe ni...abin takaicin ma ya maida mani iyalina bayi....kuma bazan iyacin amanar aminina ba,koda zan rasa raina.)"ya da shiru Basheer."? Katse masa saken zucin da yakeyi ta hanyar tambayar shi"Allah yataimakeka ya jada tsawancin kwanan ka Allah ya damkamaka mulkin Burhaan kaifa uban gidana ne walahi billahi da ace nasan inda zoben nan yake ba abinda zai jaman wahalar da kaina har in bata lokaci na mai matukar anfani a gidan Yari kala daban daban ga duka banda azaba da nike sha iri iri, kayarda dani bansan inda zoben nan yakeba da ace nasani da nabaka kodan in samu sa'ida kaiman lamani natuba"lallai Basheer da dai ace ba'a masarautar burhaan aka haifeni ba kuma da ace ba Sarki Muhammad ya haifeni ba da sai kafada mani wadannan kalaman naka walahi Basheer zuciya bata da saukin yaudara balle kayi tunani a cikin zuciyar nan akwai digon tausayi ko jinkai ba abinda bazan iya aikawa ba kaga Basheer karka batama kanka lokaci ka fito da zoben nan Basheer idan ba hakaba lallai zaka rasa ranka a banza a wofi kasa matarka ta shiga takaba, diyarka kuma tazama marainiya daga karshe haka zasu wahala kuma su wulakanta a burhaan kai kwara bayi dasu daman can sun san matsayin su,kuma yarka tazama abin hutawata da nishadantarwa hakama matarka,muddin kace zaka cigaba da taurin kai akan zoben nan wlh ko Abdullahi yace zai yi abinda kayi saina salwantar da shi,kagako dani dashi ba wani bambanci,balle kai da ba abunda ya hadamu sai yan uwantaka ta kakanni zan kasheka Basheer maganar karshe da zan maka ka fiddo mani da Zoben Zarri." "Ohh ni Basheer ya zanyi gashi mutumin nan baida imani tsaf zaya dinga alfasha da iyalina sannan ya wulakanta su, ya zanyi nabani ni Basheer...gaskia bazan iya cin amanar Abduljalal ba yana bukatar taimakona kuma amana ba karamar al'amari bane,? ya Allah ka kawomin dauki."a zahiri yace."Allah yakara maka girma da daukaka karya bata dace dani ba kamar yanda nafadamaka sama da wata bakwai wlh banda labari akan zoben zarri,nasan matsayin shi duk yanda mutun yakai da girma da nuna isa ko son mulki muddin babu zoben zairri ba mutun ba zama Sarki saida rikon kwarya,da ace yana hannuna mizai hana ban bakaba,ai kai ka cancanta da zama Sarki ba wani sadauki ba....... *Sadaukin Burhaan na kudine akan naira dari ukku domin karin bayani nemi wannan lambar 08160508316,siyen nagari maida kudi gida.* _________________ Ba abinda sukeyi sai gyaran wajen dawakai suna gamawa sukaci gaba da basu ruwan sha. Du abin nan Yarima Aryan na tsaye sai kallan Sadauki yakeyi suna hada ido ya kira shi baki daya jikin Sadauki yayi sanyi shidai baisan wani abu na hada shi da masu mulki koda kuwa aike ne, koda yaje hannun shi Aryan ya rike suka tafi wajen wata katuwar baranda ya samu kujera ya zauna shiko kasa ya duka,duk da Aryan ya bashi izinin zama asaman kujera amma yaki zama tunda ya tuna da hudubar uban gidan shi Abba Ado yace karya kuskura ya dinga hada kafada da kafada da ya'yan Sarakai ya dinga basu girma,da wannan dalilin yasa Sadauki yaki zama saman kujera."Allah yataimakeka ba girmana bane ace kana dan Sarki kuma yarima in zauna kujerar daka zauna,kayi hakuri nan ma ya isheni."na fahimta amma duk daya muke kaima mutun ne kamar ni kila kafini daraja awajen Allah a zahiri kuma ka fini komai dandai kazo a bawa....kozan iya sanin sunan malamin.?"Sunana Umar."murmushi Aryan yayi yace."Masha Allah Umar amma kai bako ne ko."? "Eh bandaɗe da zuwa ba"Ayyah bantaba ganinka ba sai yau,amma wakake ma hidima."? "Gimbiya Zubaina."yace cikeda kosawa."kai ikon Allah a iyasanina kanwata bata son maza nayi nata hidima saidai yan uwanta mata amma miyasa ta dauki Umar a matsayin hidiminta?a ransa yake wannan sakar zucin."wane kalan aiki kakema mata?"Ina mata wanki sai kuma tace zan kasance daga cikin masu gadin ta."bakaramin mamaki yake ba Zubaina da ko kayan ta bataso taga wani namiji ya taba, tsabar tsanar da tayima namiji amma wai harta kai da daukar Umar a matsyin mai mata wanki gaskia lamarin akwai ban alajabi da yawa." "badamuwa Umar zan nemeka,ni kuma sunana Yarima Aryan nayi farin cikin haduwa da kai da fatan zaka rikeni amatsayin uban gida kuma abokin ka."Umar nagodiya Allah yakara girma da daukaka."Amin Umar gaskia ka shiga raina bai dace ace kazo a bawa ba."hmm nima haka na tsinci kaina."murmushi ya saki sai kuma yace"haka Allah yaso ganina mai gidana,zan koma bakin aikina sai wani lokaci."gyada masa kai kawai yayi.tunda Umar ya juya yana tafiya Aryan ke mamakin kalar tafiyar Umar a nutse yakeyinta sai kace mai tausayin taka kasa ga tsantsar kasaita gamida izzar da ta game mashi jinin jiki yana mamakin kalr kyawun Umar kuma duk da yana wahala baka cewa BAWA NE shi..... Sarki Abdurrahman ne zaune a Fa'da anata fadanci kowa na fadin albarkacin bakin shi, yaune ake wasan INDAR da marece banyan la'asar tunda aka tashi bayi keta aiki anata gyara filin wasa ga kujeru anjere abin gwanin ban shi a'awa yau kwanan su Zubaina biyu da dawowa amma bata saka Umar a idanunta ba,bakaramin takura tayi ba,amman ta dake tana son ta dinga nisanta kanta da Umar gudun kar yashiga ranta da yawa,saboda ta fahimci bai cika shegema jama'a ba.... har lokacin wasa yayi inda gimbiya Zubaina tasha ado iya ado kamar wata sarauniyar kyau,baiwarta Fadila ta saka mata jar alkabba bisa kayanta ba karamin kyau tayi ba ita kanta tasan tayi kyau sosai. tafiya takeyi kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki ga wata irin kasaita da take ji a tattare da ita duk inda gimbiya Zubaina ta gifta sai an kalleta tsabar haduwar da tayi wajen bayi daban hakama na masu mukami. ga wani irin kamshi tana bazawa,hatta sarki Abdurrahman saida ya yaba da kyawun yar sa,cikin kankanin lokaci hadimai sun kara gyara wajen zaman gimbiya Zubaina koda ta zauna kallanta ya koma kan bayi duk wanda ta hada ido dashi saiya sadda kanshi kasa baki daya hankalinta nakan nemansa saida bata gan shi baifi minti biyarba a fara wasa..... ba tunanin da takeyi sai Umar ita kanta tana mamakin yanda akai Umar bai san mutane shi ba wani ba balle ya dinga bin ra'ayin kan shi,can ta hangi Yarima Ammar da yan tawagar shi sun taho cikin filin kauda kanta kawai tayi can ta dago kai karaf taga Umar bayan Ammar bakaramin mamaki tayiba miy ahada Umar da yaya Ammar? Ta tambayi kanta koda suka hada ido dashi mulmushi kawai yayi mata ya dauke kai bai karabi ta kanta ba.... su Ammar na zama yakama hanya zai tafi wajen bayi amma Ammar ya hana shi tafiya zama yayi daga gefen su. bakaramin bakin ciki ne ya kama idris ba abokin Ammar ne wasa yazoyi tunda yaga Zubaina yaji bala'in sonta ya shige shi,yana haduwa da Umar yaga kyawun da Allah yaima shi sai ya fara jin haushin shi ko kadan baisan yaga Umar na rabar Ammar dan ya fahimci Ammar ya ba Umar mahimmanci.... duk abinda ake baki daya hankalin idriss nakan Zubaina ita kuma Umar kawai take kallo koda idriss ya fahimci Zubaina ta damu da Umar take yakara tsanar Umar jiyake kamar ya halaka shi ya huta,batare da bata lokaci ba aka fara wasa sai kiran Jarumai akeyi gasa ake sawa na kudi sai ku hada hannun aga wamda za'akai hannun shi kasa muddin kaci sai abaka kyauta, baki daya wasan yaima Sadauki dadi sai murmushi yakeyi idan gimbiya Zubaina ta saki kyalle za'a fara wasa haka akaitayi inda Ammar yazo ya kara da abokin gasar tashi cikin kankanin lokaci Ammar yaci baki daya wajen ihun murna sukeyi,shima Sadauki jiyayi kamar anbashi kyauta ganin Ammar yaci... Itako Zubaina mamaki takeyi ganin Umar na murna Ammar yaci wasa.....Can aka kira Yarima Aryan saidai ba amo ba labarin shi ganin bai zoba hakan yasa Ammar yacema Sadauki ya wakilci Aryan,faduwar gaba ta samu Sadauki wasu naganin duk Jaruman dake Zairana a rasa wanda zaisa wakilci Yarima Aryan sai BAWA bawan ma Umar wanda bai san yanda tsaretsaren Masarautar Zairana yakeba?ko cikin bayin ma wasu bakin ciki sukeyi ace daga zuwan Umar har darajar shi ta ɗagu da yawa ace yarima Ammar yasan da zaman shi...... Ko Sarki Abdurrahman bai taba ganin Sadauki ba sai lokacin da Ammar yace shine zai wakilci Aryan amma saida ya yaba da kalar kyawun Sadauki a zuciyar shi, wanda saida ya bayyana a zahiri,Sadauki baiyi auneba yaji mai kiran sunayen yan wasa yana kiran UMAR ADAM ba karamin mamaki yayi ba, da har aka ambaci sunan shi,yana kallan wajen bayi yaga Abba Ado na kara karfafa mashi guiwa..... Cikeda da izzah wadda shi kanshi bai masan yanayin taba ya mike yafara takunsa na kasaita wanda yakeyi lokacin da yake amsa sunansa na Sadaukin Burhaan takun da ya zame masa jinin jikinsa kamar halittarsa ce a haka....hatta Sarki Abdurrahman yayi mamakin ganin yanda Umar yake tafiya sai kace wani Sarki ko dan Sarki.....takun dako masu Sarautar da yawan su sai ankoya masu shi! Da haka ya tafi cikeda nutsuwa a gaban gimbiya Zubaina kallan shi kawai takeyi amma yaki kallanta,saida ta kira sunan shi sannan ya kalleta."Fatan alkhairi Umar."murmushi kawai yayi mata abokin wasan shi na isowa ya kalli Sadauki a kaskance ganin yana bawa,batare da bata lokaci ba akafara wasa.... tunda idriss ya rike hannun Sadauki da gayya daman mugun haushin shi yakeji aka fara karawa da Sadauki shiko ya dauki abin wasa tunda yaga yanda idriss yama yi mashi mugunta cikeda gayya,shima ya kara damkar hannun idriss wani irin masifaffan karfine yazoma Sadauki atake,saida yayi kamar zai karya idriss ba arziki idriss ya buga uwar kara sannan hannun shi yafadi kasa wanwar, bakaramin ihu ya kaure wajen ba hatta Mai martaba saida ya mike tsaye danko gimbiya Zubaina saida ta saki ihun murna,duk wanda ke wajen ita yake kallo hatta Umar din zuwa yayi ya kwashi gaisuwa gun Mai martaba,kallan shi kawai Sarki Abdurrahman keyi yana mamakin samun jajirtaccen bawa kamar Umar a cikin Zairana, gashi da cikar halitta sam bai cancanci ace yazo a bawa ba....haka ya gama kai gaisuwa, daga karshe yaje wajen Zubaina sai murmushi takeyi mashi tanajin dadi a ranta sannan ta bashi kudi masu yawa nan."ina tayaka murna Umar."jinjina kansa kawai yayi kamar bada shi take ba,daga karshe ya koma wajen Ammar baki daya wajen nan sai murna akeyi yana zuwa ya mikama Ammar kyautar da ya samu yace."ka rike ka nemi Yarima Aryan ka bashi."yabo na musamman yasamu a wajen Ammar shiko idriss duk jiki ya mutu, hada hannu kadai da sukayi saida yaji haduwa da Umar ba dadi.... hidimar shi kawai Umar keyi,bakaramin mamaki bane ya kama Ammar ba yana mamakin anya Umar ainahin bawa ne? yana kokoton haka a zuciyar shi,bayan waje ya lafa Mai martaba yasake gabatar masu da kyautuka hadda wa'anda suka fadi duk anbasu kyauta,nan aka sha shagali amma ba komai Sadauki ke ciba,duk abin nan idanun Zubaina na kansa tana ganin yanda bayi keta wawa,amman Umar sai yagunar abinci yakeyi kadan yaci taga ya aje abincin yasha ruwa, ya tashi yai tafiyar zai kaima Yarima Aryan sako.... _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA TAKWAS Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.ki turo shaidar biyanki ta wannan number 08160508316. Koda akaima Sadauki iso ba inda suka wuce sai wajen hutawar Aryan yana ganin shi yafadada annurun fuskar sa yai mashi maraba,dukawa yayi ya gaida Aryan cikeda girmamawa yayin da ɗan shiru ya biyo baya ya karade illahirin wajen."Allah yataimake ka sakone na kawo maka."kallon mamaki yake bin Umar dashi kafin ya amsa ya tambaye shi."waye ya wakilci ni."?dan shiru Sadauki yayi sannan yace."Ni ne"har yanzun bai gama mamakin kalar Jarumtar shi ha yace."Kace muna tareda babban Jarumi a cikin Masarautar tamu yanzun harka iya karawa da idriss dole a yaba maka Umar,gaskia zanso in kasance tareda kai."sadda kansa yayi kasa sosai a hankali ya dago kansa yace."Allah yataimake ka ina godiya,lallai da hakan yamin dadi domin ba karamin girmamawa bane agare ni"yaji dadin kalamann sa yace."Umar haka nan naji kayi mani araina zanso ka kasance a kalkashin ikona,koba komai gaka Jarumi kuma kalar rayuwar ka na burgeni idan kana abu kamar ba bawa ba"Allah yabaka nasara,karka kasa na manta kaina, nidai nasan bawa ne, zanso kabar ni amatsayina,saboda inajin dadin hakan sosai."Umar kenan,bazan takura maka ba,amma zanso kadawo a kalkashina"dan murmushi Sadauki yayi ya kuma sauke kansa kasa cikeda girmmawa yace."godiya nikeyi Allah yakara maka girma,saidai banda iko da kaina,kasani Umar bawan gimbiya Zubaina ne."kafadi gaskia zan nemi alfarma a wajen uwar dakin ka."Allah yakara maka lafiya nagode."kanada girmama mutane,naji dadin kasancewa dakai dahar ka wakilceni....daman ciwon ciki ya rikeni shiyasa ban samu naje wajen wasaba,saidai kwara da ban zoba,gashi babban Jarumin Jarumai ya wakilceni."ranka shidade sa'ar Allah ne kawai tasa muka kai wannan matsayi....Umar bai san komai ba sai tarin bauta,a wajen Jarumta bai san taba"nafahimci baka son ana yaba maka Allah haka kake ba kodaka nike ba"baice komai ba sai murmushin da ya kuma yi.dan shiru ya kuma gauraye wajen a hankali Sadauki ya yunkura zai tashi yace."zan koma mai gida ka huta lafiya."Umar." Sake juyo yayi ya tsaya."rike wannan kyautar kaje kadinga anfani da kudin kaji? idan kana bukatar wani abun kaimani magana"Allah yataimakeka ina Umar da rike manyan kudadade irin wa'annan?karufaman asiri."abinda yafi haka ma zan maka kuma bana san godiya haka nike wannan yana cikin sharuddana zaka iya tafiya."Allah yakara maka girma da daukaka ka huta cikin aminci."yana komawa yabama Abba Ado kyautar sai murna yakeyi sun rasa yanda zasuyi da kudin da aka basu,nan Abba Ado ya aje kudin akasan kayan su haka suka dinga kashe kudin kadan kadan suna hidindimun su na yau da gibe. suna cikin jin dadin su sai ga aike daga wajen gimbiya Zubaina,baisan dalilin dayasa gaban shi ya fadiba, kamar ba zaije ba sai kuma yace gashi nan zuwa..... ★★★ Akwana atashi asarar mai rai su Shattimah har sun shigo kasar Niger suka kama hanyar zuwa Damagaran. ita dai Asma'u mamaki takeyi baki daya tafiyan da sukeyi tayi zatan Chadi zai kaita wajen Alhajin Roowan amma sai taga sun kama hanyar damagaram,basu suka shigo Damagaram ba sai bayan la'asar sakaliya kai tsaye wani irin katafaran gida suka tunkara kallo daya zakaima gidan kasan ankashe mashi kudadi ya gaji da tsaruwa anyi gininsa da tsakuwowi sai jan gargari mai daukar hankalin mai kallo...koda mai gadin gidan yan hangosu da sauri ya kara so cikin farin ciki da jin dadi ya taresu har cikin gidan suka shiga yana ma uban gidan shi maraba da hanya sannan yaima Asma'u barka da zuwa nan suka shiga ciki wani irin katan falo ne ba kowa a cikin shi,wajen yaba Asma'u ta zauna sannan yabi wata hanya ya shiga wani daki yana isa yayi sallama matar dake saman darduma ta dago kanta cike da farin ciki da saurinta ta rungume shi har kukan dadi saida tayi."Ahmad sai yanzun kadawo?"haba Umma na miyasa zaki tada hankalin ki bayan kinsan ina cikin aminci."a hakan zakace kana lafiya kaga yanda karame kuwa mike damunka."? "Umma ai rama bashi ke nuna mutun bai cikin kwanciyar hankali ba."hmm wai ɗan dana haifa da cikina shine zai mani wayo da dubara"murmushi ya saki saman yalwatattar fuskar sa yace."umma ta kibar damuw kisama danki albarka."shikenn Ahmad Allah yaima ka albarka"Ameen Umma na....daman ina tafe da babbar bakuwa tana falo"kallan mamaki tayi masa tace."Allah ya shiryeka Ahmad,shine kabari muka zauna nan muna ta fira gaskia baka kyauta ba"umma hakuri zakiyi"wacece."?"yanzun dai muje zaki ganema idanun ki,tashi mutafi." riko hannun mahaifiyar shi yayi suka fito falo itako Asma'u ta sunkuyar da kanta kasa koda taji maganar su sun takora kasa dagowa tayi har saida suka zauna."Kallanta kawai Hajia Mansura keyi saidai bata ga fuskarta ba."ya'ta barka da zuwa,ya hanya."sai a lokacin Asma'u ta dago kanta sukayi arba da Umman Shattimah saida taji faduwar gaba ta dirar mata a cikin zuciyar ta"wai dama Shattimah wajen Umman shi ya kawoni! A zuci Asma'u take maganar...da sauri Hajia Mansura ta mike ta rungume Asma'u cikin tsananin farin ciki da jin dadi"ya'ta daman kice bakuwar da yake fada? yanzun Ahmad diyar yar' uwata ce bakuwa"?murmushi kawai Shattimah yaima mahaifiyar tasa,kallan su kawai takeyi cikeda tuhuma da neman sanin dalilin dayasa sukazo ba wannan ke dagama Hajia Mansura hankali ba yanda taga ya'yan nata sun rame."Dan Allah kufada mani miyasame ku duk kun yi baki kun rame."ita dai Asma'u kuka takeyi abin gwanin ban tausayi."inalillahi ashe harda jikana akazo." ta anshi ɗan Asma'u dake goyo a saman bayanta."Allah mai girma daka ganshi kaga mahaifin shi yayi kama da Muhammadu kwabo da kwabo."Asma'u fada mani damuwar ku da ganin ku ba lafiya,kufadaman miyafaru."? Shattimah yai saurin taren zancen ta da cewa"Umma kibari anjima zan sanar maki komai yanzun ya kamata ta huta tayi wanka taci abinci zakiji duk abubuwan da suka faru anjima kadan yanzun abata dakin ta."Aaa Ahmad bazan ware mata daki daban ba tareda Halimatu zasu dunga kwana dan ta dinga debe mata kewa tana kulman da jikana bazan yarda ya'ta tayi nisa dani ba."Shikenan Umma,amma ai naji gidan shiru ina Ummin ta tafi."? "ta tafi islamiya,su kuma Jameel da Kamal sun hau dawakai suntafi gwaji daga ni sai ma'aikata da mai gadi."Ayyah Ummana sun barmi ke ba kowa,Abba fa."?"shi kuma ya tafi Kasar Chadi zai gana da yan kasuwa jibi zai dawo"Allah Sarki Umma na shine zasu barmin ke cikin kewa."?murmushi ta sakar ma ɗan nata tace."ai yanzun duk ta kewa ya kare tunda ga ya'ta tazo ga kuma jikana sun isheni komai...tashi muje daki kiyi wanka ki shirya kinji yar albarta."Umma shine ni bazaki ce naje na shirya nayi wankan ba,shine zaki dauke yar ki ki barni."? A sifar zolaya yayi maganar sai a lokacin Asma'u tace."yaya kenan,kodai ka fara kishi ne?banda abunka ana yayin sabo wake ta tsoho"faɗa mashi dai diya ta."shikenan naji nasan dai ba'a canzama tuwo suna"dariya sukayi baki dayan su cikeda nishadi."dan nema baka gajiya da rigima Ahmadu."dakinsa ya nufa yana dariya suma suka shiga daki. Sadaukin Burhaan na kudi ne akan farashi mai sauki hanzarta ki mallaki naki domin karin bayani tuntubi wannan number din 08160508316. _______________ "Yawwa kanwata daman ina son zanyi magana dake."a hankali ta dago kanta ta kaida dukkan hankalinta wajen shi tace."ina jinka."yau naga wani BAWA dana tambaye shi wa yakema hifima sai yace akalkashin ikon ki yake,saidai nayi mamakin jin hakan daga gareshi saidai miyasa kika ɗauki namiji a matsayin hadimin ki"? sadda kanta tayi tadan saci kallan mahaifiyar dake aikin kallanta suna son suji amsar da zata basu"Umar mutumin kirki ne kuma yana da jajircewa wajen hidima shiyasa nace ya dinga yimin aiki kuma nasan zai dinga kulawa da al'amura na."gyada kai Gimbiya Amina tayi tace."hakane....saidai Mai martaba yace bai san da zuwan Umar a cikin Masarautar nan ba shiyasa nace ki nisanta kanki dashi har sai an aminta da kalar halayensa sannan za'aci gaba da mu'ammala da shi."da sauri Zubaina ta dago kanta ta kalli mahaifiyar ta tace."Umma walahi Umar baida wata matsala ki aminta dani."kinga Zubaina bai kamata ki dinga fadar abinda bakida ilimi akan sa ba bakisan waye wannan Umar din ba."shiru Zubaina tayi....Ammar ne yace"Kanwata yana ga kamar bakijin dadi duk yanayin ki ya sauya kodai bakiji dadin zancen bane."?girgiza kanta tayi a hankaki tace."kawai bana jin dadi ne"Ayyah sannu kinji autar Umma ya kamata ki huta dagani har yanzun gajiyar da kuka kwaso bata sake kiba."shikenan zanyi yand kake so"yawwa kanwata,saidai ina neman wata alfarma a wajen ki"alfarma kuma"?ta tambaya dan gasgata abinda yake fada"Kwarai kuwa"wace alfarma ce."inasan ki bani Umar ya koma kalkashin iko na."take yanayin Zubaina ya sake sauyawa batayi zatan zai kuma yi mata maganar Umar ba kallansa kawai takeyi tagaza furta komai...cigaba da cewa yayi."Jarumi kamar Umar bai kamata ace yana hidimtawa mace ba kuma ya dace ace ya kasance cikin jerin Jaruman Zairana."ya ida maganar yaba aje dubansa akanta har yanzun batace uffan ba sai dan rawa da jikinta yafara mata a sannu sannnu alamar karaya da sanyin jiki."bakice komai ba."murmushin dole ta kirkiro ta maida kanta kasa saboda idanun Umman ta dake yawo akanta."Kinga muna da wasan GASA da zamu gabatar a Masarautar KESAR a watan gobe zanso Umar ya karbi gwaji kafin lokaci." Ttunda Ammar ya fara maganar Umar kirjin Zubaina ke dukan tara-tara jitake kamar za'a kwace mata wani abu mai muhimmanci atatatare da ita"Ya dace kice wani abu."? "Yaya ai banda abin cewa amma ina so zanyi magana da Umar abinda yace haka za'ayi."yanda kikace,ba damuwa yar gatan Abba kanwar Aryan Allah ya baki mijin da zai kulamin da ke."Amin yayana."Umma zanje wajen Adda Mufidah tana nema na."cikeda mamaki gimbiya Amina ke kallan yar tata."Da kikace mani nan zaki wuni."? "eh nayi mata alkawali ne shiyasa."kigaishemin da yar tawa"toh...yayana saikajini"ba damuwa. Koda Zubaina ta fita ba inda ta wuce sai sashen ta jitake kamar ta kurma uban ihu tambayoyi take jerawa kanta kala kaka...miyasa yaya Ammar kesan rabani da Umar?bayan shike debe mani kewa! Saman gado ta zauna duk ta rasa abinda ke mata dadi a rayuwar ta duniya tunda ta shiga daki gabaki daya bayinta sun kama kansu sun san idan yanayin uwar gijiyar su ya sauya akwai damuwa kafin kaftawar ido kowa yabar sashen gimbiya Zubaina sai Fadila data bita har cikin turakar ta,cikeda kulawa gaminda tsantsar girmamawa tafara tambayar ta damuwar ta."Allah yataimaki uwar gijiyata hankalina bazai taba kwonciya ba idan ina ganin ki cikin wannan yanayin ba."?banza tayi mata sake sadda knta tayi kasa tace."matsayina bai kai girman da zan dinga jera maki wadannan tambayoyin ba...bazan taba yafema kaina ba idan na ganki cikin damuwa ba,na rokeki ki sanar mani damuwar ki wala Allah mu samu mafita."Sai a lokacin Zubaina ta fadama Fadila yanda sukayi da Yarima Ammar taci gaba da cewa."yanzun minene mafita?"Allah yataimaki uwar dakina....fushi bai kamace ki zuciyar ki mai kyauce ki kara hakuri saboda shiya dace da wannan kyakkyawar fuskar taki mai yalwatacciyar haiba da kwarjini,ina neman alfarma wajen uwar dakina kiyii min izini inyi kiran jajirtaccen bawan nan Umar."kallo kawai Zubaina tabi Fadila dashi take takama kanta"tuba nike ranki shidade Allah yakara maki nasara da nisan kwana."shiru ne mai tsayin gaske ya karade illahirin dakin kafin ta bude bakin ta tace."miyasa kika haka."?"Ina ganin hakan shi zai kawo maki masalaha,ta haka ne kawai zaki fahimci kalar damuwar da Umar yayi dake...kimin aikin gafara idan kalamai na basuyi maki dadi ba."bakaramin nazari Zubaina tayi akan maganar Fadila ba duk da ta gamsu da shawarar ta sosai"shi kenan kije kiyinmani kiran Umar."nabarki lafiya." ★★★ Turaki ne kulle cikin wani wulakantaccen daki wanda gwara gidan yari da shi....Anan gimbiya Saude ke azabtar da bayinta ba wanda ya san da dakin nan,banda azabataccen sauro da kudan cizo ba abinda ke aiki a cikin dakin,ba bugu ba zagi saidai azabar cizon sauro kadai da kudim cizo sunsa Turaki yayi baki jikin shi duk tabbuna tsabar cizon da yake sha na Sauraye,tsabar zalinci irin na Saude sau biyu take bashi abinci,kuma kullun sai kakar tashi ta zage shi tana cewa baida wani anfani a wajen ta tunda bai kinshin iyayen shi. duk abinda zatayi ma Turaki bai damun shi a cewar shi komai zasuyi lokaci ne shidai fatan shi Allah yasa kada su cutar mashi da mahaifiyar shi, kuma kullin idan ya tuna halin dasu Umma Mardiyyah ke ciki sai yayi masu kwalla tsabar tausayin su dayake yi, yana cikin wannan yanayin....sai ga Barde ya shigo yana zuwa ya shararama Turaki wani irin gigitaccen mari da har saida ya rude baki daya bai gani sosai sai bijibiji da yake gani har saida ya taba mashi ido ihu Turaki ya saki ya duke kasa koda Saude tazo tsinar Turaki dinga yi tana."dan iska zakazo kayi tayima mutane kururuwa kamar wani tsohon mahaukaci ba kaga komai ba indai mune....minene anfanin ka tunda bakada kishi kwara ka mutu da ganin ka."shidai tunda ya rike kuncin shi bai kuma cewa komai ba,daman baiyi mamakin jin munanan kalaman kakarsu ba yasan tun ran gini tun ran zane daman can basu san shi tunda bata kaunar uwar shi, ko da sun wulakanta shi bai wani damuwa yasan kiyayyar da gimbiya Saude ke mashi tasamo asali tun kan yazo duniya...saida suka gama zagin shi da dungurin shi,sannan suka aje mashi balgataccen abinci suka rufe shi suka koma cikin gida sai murna suke yi suna farin ciki. zuwa yanzun komai na Burhaan sun bi sun katan tane shi.... gimbiya Masau'da takira uwar bayi har sashenta ta hada mata kayan gara kala-kala tunda ta shigo takai gaisuwar ta wajen gimbiya ta samu waje ta zauna cike da shakku bayan wasu lokuta gimbiya Masa'uda ta kora duk wata baiwarta dake sashen ta hada tTlatu saida ta koreta ya rage daga ita sai Uwar bayi."Mairo."Allah yaja da kwanan gimbiya ta."gyara kishingidar tayi tace."babban abinda yasa nace akira mani ke inaso in sake maki maganar aika aikar da Barde ya aiwatar akan jikar ki Yusrah na fahimci baki daya maganar nan tayi sanyi bayan kuma anzalin ce ku zalinci mafi muni!shiyasa nace ai mani kiranki,kar dai kuce harkun saduda ko kuma kunyafe zalintar ku da akayi."?sadda kanta kasa uwar bayi tayi tace."Allah yataimaki gimbiyar Burhaan inamu ina yafe wannan mugun ta'addancin da akai mana!kamar yanda kika sani anfi karfin mune shiyasa....saboda muna bayi shiyasa ake mana kallan kaskanci ake wulakanta mu ako wane lokaci,yanzun haka da kika ganni da ace zan bude maki bayana ba zaki iya kallan saba tsabar duka da azabtarwar da ake mana duk ranar da mukayi zanga zanga a ranar sai an dukemu an kama mana ya'yan mu maza wa'anda sune jigonmu an kulle su agidan KASO ana lahana mana ya'ya! Allah yataimaki gimbiyata walahi ada nikejin tsoron azaba da mutuwa amma banda yanzun!zuciyar Mairo ta kekashe ta bushe barazana bata taba tsoratani abinda yasa kika ga mun daga kafa ba yanda zamuyu ne kuma raina nayi mani ciwo idan naga ana wulakanta ahalina dan kawai suna BAYI ai Koda muke bayi kowa ya shaida Bayima Ya'yane kamar kowa ba wanda ya diro daga sama haihuwar mu muma akayi."Cikeda kunar zuci take magana kama ganinta zakasan cewa lallai an cutar da ita sosai."kiyi hakuri da kalamai na ranki shidade nayi alkawali koda za'ayi mani gunduwa gunduwa sai na fadi abinda ke cikin zuciyata."shu'umin murmushi gimbiya Masa'uda tayi kasa-kasa tace."Hmm Mairo kenan, kinyi kyan kai....daman haka nike so ku fidda tsoro a cikin zuciyoyin ku ta hakane kadai zan taimake ku."zaki same mu wasu jajircewa."bawai halin da zaku shiga ciki bane damuwata ai abinda yafi hakama ya dace ayi maku kufa bayi ne kuma yan wahala wulakantattu marassa 'yanci"a zahiri ko murmushi tayima Uwar nayi tace"ni kaina mulkin zalincin da akeyi a Masarautar nan ya ishe ni kuma naji dadi dana ga jajircewa da rashin tsoro a cikin idanuwan ki ta hakane kadai zan iya taimaka maku da gudun muwata,dan ganin kun kwaci hakkin ku a wajen Hamza duk da kasancewar shi ɗan uwa a gareni,amma zalincin da aka aikata ga Yusrah ya taba mani zuciya kwarai da ainun!kisani ina bayan ku dari bisa dari saidai ina son duk abinda zakuyi ku dinga shawara dani zan baku goyon baya yanda ya dace."....ikon Allah ko yaushe gimbiya Masau'da tazama mai tausayi ga bayi bayan ba wadda mu kafi fuskantar matsaloli da wahalhalu a wajensa kamar ta,a iya sanin da nayi mata bata kaunar bawa tsakanin ta da bayi sai wulakantarwa da tozarwa.....gashi lokaci kankani ta sauya tanajin tausayin mu ko dai yanzun sun daina jituwa da Hamza ne shiyasa take neman yi mashi bore? kodai kawai taji tausayin mune har cikin ranta shiyasa take san ta taimake mu? A jiyar zuciya ta shide tace."mu dai indai zaki bamu hadin kai akan damuwar mu ba ruwanmu da sauyawar ki dan kema ba tabbas ke gareki ba kuma baki da gwani."dago kanta tayi tana murmushi tace."nayi nazari iya nazari dan inga da wa'anne kalmomi zan iya godewa uwar gijiya ta dasu amma na rasa.....ina rokon Allah yasaka maki da mafificin alkhairi saboda samun jajirtacciya irinki a cikin Masarautar Burhaan bakaramar nasara bane mungode da goyon bayan da kika bamu yanzun haka zanje in samu yan uwana insanar dasu komai saimu sake sabon shiri komai kenan zakijini Allah yakara maki daukaka."hmmm ai daukaka ta bai wuce ingan ni a bisa karagar mulkin Burhaan ba,a matsayin na sarauniya Masau'da ba yar Sarki Kabir Usman ba,daga lokacin shikenn burina ya gama cika in taka duk wanda naga dama a lokacin dana so......a zahiri murmushi ta kuma saki tace"Amin Mairo naji dadin addu'ar ki agareni sannan ina sauraranki dan haka kije kukara dage damtse akan kudurin mu."insha Allahu yanzun kuwa."jijina kai tayi tace."nasan idan nace ki tsaya kiyi liyafa anan baka zaki saki jikin ki da kyau ba....kinga duk wannan garabasar ta ki ce keda iyalanki a matsayinki na uwar bayi, kuma tsohuwar mai kula da sashen mijina Sarki Abduljalal,ki saka yan uwanki su kwashe muku kuje kuci kusha kafin naji amsoshin ku"Farin ciki ya dira a zuciyar Uwar bayi ganin irin kabakin da Gimbiya ta hada mata "lallai kam bansan wane kalar farin ciki zai samu yan uwana ba idan sukaga wannan sha tara na arzikin sabida raban da inci makamancin wannan abincin tun lokacin Sarki Abduljalal nada cikakkar lafiya tabbas shidin mutumin kirki ne sai gashi kina koyi da halayen mijinki, gaskia duk wani bawa dake cikin Burhaan ya gama samun uwar daki jajirtatta kamarki muna godiya mai tarin yawa."murmushin yake kawai tayi mata."Yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka ba abinda ya sauya daga cikin zuciyar Masau'da ba saima tarin manya manyan kudurai da nike dashi walahi koni kaina ina neman tsari daga kaidina,da kikema Abduljalal fatan alkhairi gwara matacce da shi sakarkaru da ku walahi saina shayar daku bakar guba,nidai fatana ku maraman baya har in gama cima burina in kawo karshen Hamza."a zahiri tace"kai Mairo ji nike kinfi kowa iya fatan alkhairi duk abinda nayi maku yiwa kaine kedai ki dauki kayan da nahada maku kije ina sauraron ku."Allah yatai maki uwar marayu,saikin jini."gyada mata kai kawai tayi cike da tausayin kalar rayuwar da zasu fuskatan ka." Tana fita Talatu na shigowa ta zauna gabanta suka hau maida yanda akai."Hhhhh Talatu kinga uwar bayi tafita jikinta na rawa taga abin duniya wai harni take kira da uwar marayu."take ta daure fuska kamar ba ita tagama kecea da dariyar mugunta ba tace."hmm lallai kam aini saidai in karasa maraya."gaskia ne uwar gijiyata basu san dawa suke magana ba fatana ki zama Sarauniyar Burhaan komai ya dawo a kalkashin ikon ki,a lokacin zasu san wacece uwar marayu."Bassu kawai Talatu dani suke zancen."dariya suka sake cewa da ita...... JAMEEY❣️ *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA TARA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello. Kituro shaidar biyanki ta 08160508316. _Shafin kyauta ya kusa karewa yar uwa hanzarta ki mallaki naki domin tafiyar ta musammance._ "Barka da war haka uwar gijiyata kiran ki ya riskeni ina fatan lafiya."?sunkuyar da kanshi yayi kasa yana sauraron abinda zatace mashi...a ɗage ta kalle shi daga sama har kasa,a hankali ta mike tsaye tafara kewaye shi cike da takun kasaita tana mashi kallan kaskanci tafi minti ukku tana zagaye Sadauki kafin ta koma ta zauna saman kujera ta harde kafa ɗaya saman daya tana karkadata a hankali cigaba da watsa mashi wulakantaccen kallo tayi a gadarance tace"sai yanzun kirana tafara samun ka."? "Allah yaimaki yawan rai ko wancan lokacin da kiranki ya samenu bani lafiya zazzabi ne ya rufe ni shiyasa banzo ba."Kai Umar."ta daka mashi firgitatar tsawa tace."Kai har kanada wani zabin da ya wuce nawa? kai har wani 'yanci gareka da zakace saboda baka lafiya bazaka ansa kiran uwar gijiyar kaba."?kafeta da manyan idanunsa yayi masu tsananin haske da tarin kwarjini a cikin babu abinda ya tsana a duniya kamar ranin wayo."bada kai nike magana ba"ta kuma daka mashi gigitattar tsawa,ransa ne ya sosu yanda mace ke juyashi kamar wata waina son ranta dan kawai yana bawanta."Ni mizance maki tunda nafada maki uzuri na...."wani irin gigitaccen mari ta dauke Sadauki dashi zuciyar ta na tafasa,kallanta kawai yake daga sama har kasa yana al'ajabin halayen ta"harka isa ina magana kana yi! waye kai?da har gimbiya Zubaina na magana kana maida mata son ranka."? Tunda ta mari Sadauki mamaki ya kama shi koda ya kasance bawa amma bazai juri wulakanci kalar wanann ba"Allah ya huci zuciyarki Umar na tuba...bansan hakan zai bata maki rai ba ne,Allah yabaki hakuri."wawa da kai! kada kaga dan inajin nauyinka ka dinga yin abinda kaga dama a cikin Masarautar walahi tsab zan koya maka hankali! ka bude kunawan ka kaji abinda zan fada maka da kyau."wawa dakai!"abinda yake maimaitawa kenan kalmar da tayi masa girma a zuciya wai shi take kira da wawa,daurewa yayi ra hanyar danne bacin ransa yace."shikenan,ina sauraran ki"ɗan uwana yazo mani da magana akan ka yana so ka kasance dashi zai saka daga cikin Jaruman Masarautar nan saboda ya baka gwaji zakuyi gasa,shine nace zan fada maka idan ka amince shikenan,amma kasani kana a kalkashin ikona, kana bukatar kasancewa da yaya Ammar."? rasa abinda zai ce mata yayi....yasan dai zama da Yarima Ammar a wajen shi bakaramin cigaban shi bane Kasancewar yana son ya mai dashi dan uwan sa kuma yafi masa zama a kalkashin mace sannan kuma yana ganin muddin yace ma Zubaina yafi son zama dashi sai taga kamar baidamu da ita bane shiyasa kuma abinda ya fahimta ita din ta damu dashi sosai."Umar kafaman ra'ayin kan ka"dago kanshi yayi dake sadde kasa yace."Allah ya yaimaki uwar dakina banda wani zabi da ya wuce naki a matsayi na bawan ki banda wani ra'ayi ko zabi daya wuce naki."sanyayyar ajiyar zuciya ta shide wadda ba lallai ka gane tayi taba tace."Umar ada kabata mani rai saboda ni nadamu dakai kana nuna halin ko in kula akaina sannan uwa uba baka bin umurni na bayan kowa yasan tunda Zubaina take ba wanda ya taba yimata gardama ko ta taka dokarta sai.kai wannan dalilin yasa na kara jurewa har hannuna ya sauka a saman kuncin mutun mai dibin daraja a wajena banji dadin abinda ya faru ba Umar."a hankali ya dan rankwafar da kanshi sannna yace."nima banji dadin yanda naga ranki ya sosu ba ina fatan zaki yafema Umar"murmushi ta sakar masa tace."bakomai Umar yanzun zan ma yaya Ammar magana....kasani nidai bana san kana mani nisa shiyasa kaga nadamu da kai ya dace kana zuwa akai akai."shikenn gimbiya ta yanda kike so haka za'ayi."Umar ga abinci nan kadauka kaci,na fahimci kamar baka karya ba."rausayar da kanshi yayi yace."eh hakane saidai ni ban cika damuwa da karin kumallan safe ba, nagode ranki shidade"Aaa Umar in dai ka amince kana kalkashin ikona toh kaci abincin nan dan kai kadai nasa aka kawo shi."jinjina kansa yayi yace."nagode."ba haka yaso ba saboda bai son ya kara bata mata raine shiyasa yadauka ya ci kadan sannan yai mata godiya hakanan ta kyale shi gudun karta ta kura mashi amman tasan bai koshi ba yana shan ruwa ya nemi izinin tafiya so yake yaga Abban shi tunda suka tashi yau basu hadu ba."toh Umar kagaida gida."badan taso ba tabar shi ya tafi arayuwar ta idan tana tareda Umar takanji nishadi a cikin zuciyar shi nan tayi mashi izinin tafiya koda ya kusan sansanin bayi a hanya ya hadu da Yarima Ammar zuwa yayi yakai gaisuwa fuskar Ammar a sake ya amsa"ina fatan kasamu sakona a wajen gimbiyar ka"Eh Allah yakara maka girma da daukaka nasamu amma a wajen ta zakaji komai."badamuwa Umar "nagode ka huta lafiya."yana shiga dakin su ya iske Ado baidawo ba zama yayi saman tabarmar kaba,yana tuna yanda sukayi da Zubaina, wai shi zata mara gaskia ba dan tana uwar dakin shiba kuma gimbiyar Zairana da sai ya raina mata hankali,amma baida zabi tunda a kalkashin ikonta yake..... ________________ Koda Asma'u tagama shiryawa cikin wata atamfa tayi mata kyau sosai,jikinta yayi kyau jegon da takeyi ya karbeta sosai tana gama cin abincin ta sannan ta fito falo ta zauna. Baki daya suna zaune falo gefen Halimatu ta zauna nan ta iske Shattimah yana ba Umma labarin abubuwan da suka faru dasu har saida suka zubda masu hawaye cike da tausayin halin da suka shiga,ga tausayin Sadauki daya ratsa su a take takara son Asma'u aranta da ɗan Sadauki tunda Asma'u tace mata sunan shi Ahmad sunji dadi kuma nan Hajia Mansura takara yaba ma danta akan jajircewar da yayi."Allah yaimaka albarka Ahmad yanda ka taimaki matar dan uwanka kayima zumunci hidima kaima Allah yabaka wanda zaiyi maka."Amin Umma."janyo Asma'u tayi jikinta tace."Sannu ya'ta ki kwantar da hankalin ki nan ma gidane duk abinda kike so zamuyi maki kinji."toh Umma nagode Allah yakara girma."Amin."Allah ya kubutar dasu cikin halin da suke ciki Allah ya toni asirin su Hamza."amin Umma ai mutanen Burhaan ba Allah aran su."Allah ya maida masu aniyar su."amin." Sarki Abdurrahman bai samu damar zama fa'da ba saboda ya tafi wani taron Sarakuna a kasar Kesar,saidai dan uwanshi Abdussalam. sawa yayi aka kira mashi Ado ya yana zuwa yakai gaisuwa sannan ya akai mashi izinin zama ya zauna."Ado nakira ne domin in tambayeka akan yaron nan Umar tun ranar daya fanshi Aryan a wajen gasar nan da akayi nakasa mantawa da yaron nan a raina,wanene Umar."? "Allah yataimakeka Umar dai ba kowa bane face bawa kamar yanda kasani...na siyo shi a kasuwar gobir kamar yanda aikina yake, kuma gimbiya Zubaina ita ta bukaci in samo mata bawa jajirtacce shiyasa na shiga filin da'ga har aka saidamin shi,wannan shine abinda nasani gami da rayuwar Umar."gaskia ne Ado baza'a kira Umar a bawa ba ni kaina nayi zaton ko ɗan dan uwanka ne bacin da hakan ya bayyana a tattare dashi,saidai kana ganin Umar baida wata illa kuma zaici gaba da yima yar mu hidima."? "Eh ranka shidade,Umar mutumin kirki ne kuma bai cika damuwa da harkar kowa ba hidimarsa kawai yakeyi."tabbas Umar ya cika Jarumi zaka iya tafiya"toh ranka shidade katashi lafiya Allah yakara maka nasara"Amin."sarkin zagi ya amsa. *Ku hanzarta ku mallaki naku domin wannan tafiyar ta dabance,na tabbata bazakuyi dana sanin siyen sa ba,kunji salon Izzah ko Mulki to yanzun wasan zai soma domin ba'ayi komai ba,kedai ki kasance da Jamila yar mutan kankia*😍 *BURHAAN* "Ke uwar me kikeyi nan? nafahimci kune masu yimana lekan asiri ko?ku ke fidda mana sirrika a waje ko? yau kashin ku ya bushe."jikinta na rawa ta zube kasa."Allah yataimakeki kimin aikin rai walahi bada wata manufa mukazo nan ba tsautsayi ne ya giftama hanya ne ta biyo damu tana shiyasa,kiyi mana aikin rai"kuyi mani shiru munafukan banza munafukan wofi,yau dinnan sai kun kwashi kashinku a hannu."muntuba kimana aikin rai tsautsayi ne ya biyo damu tanan bamu san an hana bi tanan din ba."Maimuna maza kije ki kiramani Darwami ya koya masu hankali."angama uwar gijiyata Allah yabaki nasara."Goggo ni nasan halin wa'annan mutanen kingan su nan suna bayan Mardiyyah shiyasa suka kara zama munafukan gaske"yau din nan saina koya masu dasari daganan bazasu sake munafurci ba."suko duk sungama tsorata da lamarin gimbiya Saude sun san ba imani garesu ba,danko Jummai da ladidi saidai ido suke ranawa dan sun san bazasu ragama suba ko kadan kasancewar su hadiman gimbiya Mardiyah..... Koda darwami yazo ba irin wulakanci da bai masuba ga dukan su yanayi kamar wasu jakuna hatta gimbiya Safiyya saida ta tausaya masu, dan tasan cutar da akeyi a cikin Burhaan ya wuce misali,amma dole mutun yasaka ido koda suka gama dakuwa sawa tayi suka dinga shara da debe ciyawu kullin sai darwami yai masu bulala talatin. Sarki Abduljalal ne kwance,zuwa yanzun ciwon shi ya wuce misali sauki sai wajen Allah yanzun ko furar da yake samu yasha ada ta gagareshi,shi kanshi Saminu zuwa yanzun ya fara fidda rai da samun Mai martaba,yauma haka ya tashi da amai yana ta suma duk ya gama galaibaita amma kaf Burhaan daga Saminu sai su ladidi su kadai keba Mai martaba kulawa,wannan kenan Galadima Hamza tareda kaninsa Abdullahi suna tattaunawa."Abdullahi ya dace ace zuwa yanzun Abduljalal ya mutu yaka mata ace kowa ya manta dashi a cikin Masarautar nan....kuma ga kalubalen daje fuskantar mu a kowane lokaci ga Masau'da na kulamana munafunci da sharri kullin so take ta yaɗa maa da'na sharri a wajen manya manyan kasar nan,dan ya tabamani darajar mulki na,yanzun mikake ganin yakama ayima muguwar matar nan."? Shiru Abdullahi yayi yana sauraron dan uwan nashi aransa yana ayyana abubuwa da yawa."Hmm Hamza kenan!koda kasamu duniyar ka hatta ni da muke takamar cikin mu daya mantawa kayi dani sai yanzun zaka nemi shawarata wato so kake na baka goyon baya ka kara mantawa dani walahi bata yuyuwa ni kaina sai inda karfina ya kare bazan zauna ba wankin hula ya kaini dare ba idan har akayimin ban rama ba,lallai kam da ban haihu ba" dan murmushi ya kakaro a saman fuskar shi yace."Allah yataimake ka ni kaina lamarin nan yana bani mamaki ainun.....narasa abinda zan fada komai ya cakude yanzun dai ya kamata muje wajen Goggo nasan ita zata samar mana da mafita"Shikenan ɗan uwana haka za'ayi."Hmm sai yanzun kasan ni ɗan uwan ka ne amma da kasamu duniya saika manta dani daga kai sai matarka da ya'yanka ko Goggon baka damu da ita ba!ai Masau'da tafika gaskia kaci amanarta ne shiyasa zata rama abinda kai mata"yanzun tashi muje muji yanda zamuyi akan wannan matsalar da muke fuskanta."mikewa Abdullahi yayi suka tafi wajen mahaifiyar su. ★★★ Gimbiya Saratu zaune a sashen ita da bokarta sunata sihirin su daman aikin su kenan sun riga da sun saba da kulle kullen su na tsafe tsafe....suna cikin hada kullaliyar su saiga mai kulawa da bangaren ta ya shigo yafada mata tayi bako,tace ya shigo da shi bayan sun shigo ya basu waje...cikeda mutuntuwa ɗan aiken nan ya bata takarda yace."daga Masarautar Burhaan gimbiya Masau'da ta aiko ni."madallah."ta amsa cike da murna da tarin farin ciki tana shirin ganin kalar albashir din da yarta ta aiko mata dashi,nan tasa aka bashi masauki ya huta kafin zuwa gobe....bakaramin dadi yaji ba,nan gimbiya Saratu ta bude takardar yarta cike da zumudi tafara karantawa... _Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan kina lafiya...Umma kamar yanda kika sani kinbar Masarautar Burhaan da tarin nasarori dayawa amma yanzun nasamu damuwa kamar bani a kowa banbancina da baiwa kadan ne! galadima Hamza yazama Sarkin Burhaan saidai shi kadai yake cin karan shi ba babbaka sai kuma uwar shi,ya manta dani kwata kwata...koda nayi mashi magana har marina saida yayi ya wulakanta nu har yana ikirarin sai ya ga bayana zai kashe ni yanzun haka komai na Burhaan ya katantane banda bakin zalinci ba abinda ya aje har ni bai kyaleba nazama abin tausayi na shiga damuwa marar misaltuwa umma,dan Allah kitaimaka mani ina bukatar agajin ki dake na dogara...inafatan zaki kasance cikin aminci bissalam daga yarki Masau'da Kabir Usman Burhaan_ Zazzafar ajiyar zuciya gimbiya Saratu ta sauke ta gama duba wasikar yarta bakaramin tashin hankali ta shiga ba da tsananin fargaba zufa je tsatsifo mata tana sharcewa ranta a dagule ta kalli bokanyar ta tace"lallai kam Hamza ya tabowa kansa fitinar duniya ni za'aima dibar albarka da raina za'a wofintar mani da ya'ta! Hamzan banza Hamzan wofi!yoni inda ace Masau'da da tasha nonona batayi tunbiɗi ba ita kadai zata iyayin maganin karamin ɗan iskan nan,wato nagama yimasu wahala shine zasu manta mani da yar diyar tawa gefe ko?sucigaba da cin karan su ba babbaka,walahi muddin na haihu sai na maida Hamza ya zama abin tausayi a cikin Burhaan sayayi dana sanun cin amanar ya'ta da yayi....ita kanta Saude saina bata mamaki sai sunsan suna magana da gimbiya Saratu Sarauniyar Yurii ya zama dole ya'ta sai tazama Sarauniyar Burhaan komai rintsi komai wuya koda zan rasa raina."kwarai kuwa gimbiyata umurnin ki kawai nike jira."ba saina tsaya yimaki bayanin komaj ba ina san kiyi gaggawar hada mani da asirrai zanba wannan bawan yakaima ya'ta bazai bar Masarautar nan ba sai mun hada mashi manyan asirran da za'a kai ma Masau'da sai mun ladabtar da wa'annan matsiya tan mutanen maza kifara aikin ki."Angama sarauniya ta yanzun kuwa,me kikeso ai mashi kisa ko a haukatar da shi? ya susuce yanda daya tunkari karagar mulki zata dinga bashi tsoro har sai ya'ta ta mulki Burhaan yanada ranshi da hankalin shi, kinga karshe bakin ciki da takaici su zasuyi ajalin shi...kinga in mukace za'a haukata shi ko kashe shi ai bamu more masa ba saboda baisan Masau'da ta zama Sarauniya ba,amma idan yagani da idan shi kinga mun cika burin mu."dariya suka sheke dashi tace."mu keyi amma mu kejin tsoran ku kina wuta yanda ya kamata a gujeku sarauniya Saratu yanda kike so haka za'ayi."cigaba da aikin ki nasan zakigama komai da wuri"umurin ki abin tunkaho agareni angaishe da sarauniyar Yurii uwar gida ga Sarki Kabir Usman an buga dake anbarki Allah yataimake ki."Jinjina kanta tayi tabajin dadin kirarin da bokatar keyi mata. JAMEELA JAMEEY❣️ Share Saboda Allah *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA GOMA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.ku tura shaidar biyan ki ta wannan lamba 08160508316. Tankameman waje ne daya gaji da tsaruwa da ado ba abinda babu a wajen yasha kayan alatu na more rayuwar yau da kullun Sarakuna ne cikeda wajen cikin babban dakin taron Masarautar Kesar kowa ya zauna suna tattaunawa akan wasan da za'a gabatar a watan gobe inda za'a saka gasa a tsakanin Masarautun Nahiyar baki daya. Sarkin Kesar ya kara yima Sarakuna godiya mai yawa yanda suka karbi takarda gayyatar da yayi masu sannan aka zabi kasar shi a inda suka gabatar da zaman ya cigaba da cewa."kamar yanda kowa ya sani an tsaida inda za'a gabatar da wannan muhimmin wasan idan Allah yasamu cikin rayayyu za'a gabatar dashi cikin Masarautar SIRIKA saidai nayi mamakin rashin ganin Sarki Abduljalal duk da kasancewar Sarkin Sarakuna kuma uba agaremu ya kamata ace idan irin wannan taron yatashi ya dinga zuwa ko ya aiko da wakilin shi,kuma zanyi anfani da wannan damar wajen kara mika godiyata ga Masarautar Burhaan yanda suke ba da taimako ga kasashe daban daban... zamu tsaida lokacin da zamu kaima wannan adalin Sarkin ziyarar bazata bayan angama gabatar da gasar da za'a gabatar bada jimawa ba."kowane Sarki yayi amanna da maganganun Sarkin Kesar din sannan sun kara goya masa baya akan ziyarar da zasu kai Masarautar Burhaan din."gaskia ne munji dadin maganganun ka Allah ya muna mana lokaci lafiya kodan yanda Abduljalal ke daukar gabata da taimakon al'umma ya cancanci ayi mashi ziyarar ba zata domin mu gaida shi mun tabbata zamu samu karamci sosai kuma zaiji dadin ziyarar da zamu kawo mashi."cewar Sarki Abdulwahab. Sarki Abdullatib(Sarkin Sirika)ke tambayar Sarki Abdurrahman maganar yar shi gimbiya Zubaina."nasamu labarin tayi aure banji dadi da baku gayyaci Masarauta ta ba."Sarki Abdurrahman yace."ban kyauta ba saidai ina maka albishir...wannan wasan da za'ayi da ya'ta Zubaina zanzo yanda kowa zai ganta kuma ai kaga Masarautar ka nan za'ayi wasan kaga sai takara sanin iyayen nata sosai"da naji dadi Allah yakaimu lafiya."Amin." bayan sun gama gabatar da muhimmin zaman da sukayi suncima matsaya suna gamawa kowa ya koma masaukin shi abin yayi tsari sosai.bayan Sarki Abdurrahman yakoma masaukin shi yagama kimtsawa zai kwanta aka sanar masa da isowar Sarkin Sirika,bayan ya amsa mashi sallamar da yayi mashi ya samu waje ya zauna suka kara gaisawa"nasan zakayi mamakin sake ganina bangaren ka"hakane amma nasan koma minene yanada matukar mahimmanci."kwarai kuwa akan maganar Sarkin Burhaan ne gaskia yaka mata ace wannan wasan da za'ayi ya halarce shi sannan yazo mana Jaruman shi,musamman Sadauki muna bukatar ganin shi."Murmushi Sarki Abdurrahman yayi."ni kaina zanso inga wannan yaro badan komai....saboda inada labarin Jarumta da jajircewa irin ta yaron nan."gaskia ne."ajiyar zuciya marar sauti Sarki Abdurrahman ya saukar yace."Kwanaki na gayya ce su zuwa Zairana wasan daba kuma sunzo saidai banda Sadauki kasancewar bai jima dayin aure ba."shiru Sarkin Sirika yayi yana sauraron Sarkin Zairana(ikon Allah....yanda ya'ta Rahama ta sussuce akan son Yarima Sadauki ace yayi aure ban saniba ya zanyi yanzun? ya'ta daya tilo ace zata rasa abinda take so shekara da shekaru tabbas akwai damuwa."a zuci yake sakesaken sa....maganar Sarki Abdurrahman ta katse mashi sakar zucin da yakeyi."Ashe Sadauki yay aurei."? "ya jima da aure shiyasa ma bai samu damar zuwa ba,amma nasan wannan karon mahaifin shi zai turo shi,ni kaina yaron nan yai mani Allah yai mashi haiba da tarin farin jini,kuma yayi suna a ko ina"Allah yakaimu lokaci lafiya nima zanso in sansa a zahiri kamar yanda na kiyaye sunan shi.."murmusawa Sarkin Sirika yayi.sannan sukaima juna sallama ya koma masaukin shi. Koda asuba tayi kowa ya gama shiryawa sannan sukaima juna sallama....kowa yayi zummar komawa Masarautar sa,suka rabu cikeda kewar junan su....cikin ikon Allah lokacin da biyar din yamma tayi Sarki Abdurrahman ya dawo gida bakaramar murnar dawowar shi akeyi ba abin ba acewa komai kwana biyu kadai da yayi baya nan ji suke kamar yayi shekara bai nan,suna jin dadin Sarkin nasu,su Ammar sukazo yima mahaifin su barka da wowa,sun jima a turakar sa suna fira irin ta uba da ya'yan sa ana kiran sallah kowa ya tafi masallaci domin yin sallah. ______________ Iso yasa akayi mashi har cikin turakar gimbiya Zubaina tana zaune ta gama sallah tana karatun alqurani mai girma saiga Fadila tazo ta zube gefenta har saida takai aya sannan fadamata zuwan Yarima Ammar,a zahiri tayi mamakin zuwan shi duk da ba yau yafara kawo mata ziyara na amma saita ce ya shigo yana shigowa ya zauna akan kujera,ta gaishe da yayan nata cikeda girmamawa ya amsa cike da sakin fuska..."kinsan ance mai nema baya taba fushi....dama akan maganar da mukayi da ke shine nazo inji amsarki."hakane yayana nima nayi magana da Umar shima ya nuna mani gamsuwar hakan saidai gaskia ina son Umar ya kasance a wajena....saidai kamar yanda zakuyi gasa kuma naga kunasan zaku tafi dashi na amince da hakan,saidai ina bukatar aiki da Umar."shikenan mungode saidai naso ace baki daya Umar ya dawo kalkashin ikona bansan in ganshi yana hidima amatsyin bawa kyanshi ya kasance a cikin manayan Jaruman Zairana"sihirtacciyar ajiyar zuciya ya sauke yace."kayi hakuri gaskia zama da Umar kadai yasa naga kyawawan dabi'u attatare da shi kuma nakara samun ilimi daidai gwargwado nasan zaka fahimce ni"ba damuwa zanyi nazari akai....saidai kisa aranki daganan har sai mundawo GASA sannan zaki ga Umar,saboda muna som ya maida hankalin shi waje daya hakan kamar zaifi."yaya kana ganin...."haka nafaɗa Zubaina bana son musu" ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu."yanda kace haka za'ayi." sallama yai mata ya tafi......yana fita ta kishingida tana tunanin ta yanda zata iya rabuwa da Umar har tsawon mako biyu bata ganshi ba tasan zata takura sosai....ba yanda ta iya tunda an nuna mata fin karfi. ★★★ Zaune yake yadawo daga karbo abinci yana shiga dakin su yafaraci ga wara muguwar yunwa tana dawainiya dashi yanda yake cin abincin kai kace bai taba cin abinci ba sai hannu baka hannu kwarya yakeyi.....koda Ado ya shigo ya iske dan na shi bai koshi ba daukar nashi yayi ya bashi,dama shi har daki akesa bayi sukawo mashi nashi saboda zuwa yanzun ya zama babban bawa ko aiki baiyi saida susa bayi aiki kuma shike zuwa ya sawo bayi idan yaga bawa baida isassar lafiya ko bazai iya muriya ba, sai su siyar su dauko wasu shiyasa wani lokacin har fadanci yakeyi kuma ba sashen da bai shiga a cikin Masarautar tsabar aminci da akayi da shi...saida Sadauki ya koshi sannan Ado ya dauka yaci yana gamawa Umar din ya tashi zai fita dakatar dashi Ado yayi"Umar zanyi magana da kai."komawa yayi yazuna"inajinka Abba"kamar yanda kasani dazun Yara Ammar ya same ni yace gobe da karfe bakwai na safe ka shirya za'a fara baka gwaji zaka zauna cikin jaruman Zairana saidai dole ka kara maida himma akan abinda akasa ka!"ɗan murmusawa yayi yace."Haba Abba ina Umar ina zama Jarumi, ina tsoron kada mutanan ne sun sani a hidimar su inzo in fadi kaga ai naji kunya Sannan na kunyata mutane masu matukar daraja.... kar su ga danna shigarma Yarima Aryan wasa rannan su daukeni matsayin wani jarumi."dariya Abba Ado yayi yace."Ummarul-Faruq kenan kai Jarumi jajircewa kawai zakayi."Abbana niba Jarumi bane ainahin yanda akeyin wasan jarumta ma ban sani ba, bare har in zama jarumi."Hmmm Umar kenan,artaba dakai kadai batare da gasa ba....dole gaban maza ya fadi balle kuma kazo a matsayin Jarumi yakamata ka dauki gabata da girman da Allah yadora maka kuma ka kara godema Allah saboda wannan ba karamar baiwa bace Allah yamaka ba...saboda haka karka kuskura kace zaka sare kazama Jarumi kuma gwarzo Allah yaimaka albarka"Amin Abba nagode da kwarin gwiwar da kake bani." ----------------------- "Allah yataimakeka sannu da hanya"yauwa gimbiyata,ina yan uwanki."? "Gasunan tafe ranka shidade dagani ka kwashi gajiya."murmushi yai mata yace."Gaskia kam,amma gajiya tabi jiki ba kamar jiya na.....ya ya'ta Mufeedah tanata fama ko?Allah yasauketa ladiya kullun tausayin yarinyar nan na kara kamani"Amin ranka shidade,dayake tanada karfin halima."Allah Sarki, kinga da Allah yasa mijin Zubaina bai mutuba nasan da Allah yanzun naga jikana mafi soyuwa a gareni."Allah yataimake ka kadai nuna kaunar yarinyar nan fiye da kima"Aminatuna kenan, kaf Ya'yana ba wanda bana so abinda yasa kikaga inaba mamana kulawa fiye dasu kinga ita ce karama a cikin su,amma kaf ya'yana ba wanda yafi wani duk daya suke a wajena."murmushi tayi....suna cikin labari sai gasu gimbiya Bilkisu da Rukayya sun shigo suka zauna gefen mijin nasu suka sashi tsakiyar su kowa a cikin su na kokarin kyautatama mijin nata"Abban Ammar ya hanya."? "alhamdulilah...ku sanar da ya'yan ku gobe da misalin karfe goma ina bukatar ganin su a turaka,amma ba laifi idan kuma kun kunzo,amma kusani wannan zaman na ya'yana ne."Allah yakaimu lafiya."Amin." gimbiya Rukayya tafara bashi tufa yana ci daman dakin ta yake suna mashi fira su kuma sauran suka fara yi mashi tausar kafa baruwan su da mugun kishi,soyayya sukema junan su gwanin birgewa koda agaban ya'yansu ne ba ruwan su da wata kunya har sun saba saboda zuriyar Sarki Abdurrahman zuri'a ce mai hadin kai da sanin yakamata dama da Zubaina kadai yake samun sabani a cikin ya'yan shi itama wajen fidda miji ne.koda tayi auren farko yace bazai kara takura mata ba,zai aura mata zabin ta idan ya dace da ita. sunjima suna cin abinci tare da mijin su sannan ya tashi ya shirya ya tafi wajen mahaifiyar shi suma kowa ta koma sashen ta.... ___________ " tashi ki shiga wanka kinji yar albarka kinga kada ruwanki ya huce....na fahimci baki san kina wanka da ruwa mai zafi dama yaran zama ni kunfiya san jikin ku dayawa"murmushi tayi tace."Umma duk nagaji shiyasa kibari saida safe sa nayi yanzun bacci nikeji Umma."kinga zaki tashi kokuwa saina saba maki!."a shagwabe Asma'u ta tashi cikeda kasala ta shiga ban daki."salan kuma ki watsa ki fito dan nasan zaki aika."Umma zanyi Allah."ah toh nadai fada maki."Hajia Mansura ta dauki jikan nata tayi mashi wanka sannan ta shirya shi tsaf kamar ka sace shi yanda yayi kyau, da tagan shi sai taga kamar Sadauki..... tana tayi mashi rawa Asma'u ta shigo dakin ta fara shafa mai."Umma na kedai kin fiye jida dan nan naki kamar yafi kowa"murmushi tayi tace."kinji abinda kika fada dama yafi kowa kuma kinsan sabon jini da shiga rai dole in so shi sosai kinga bari in tashi in shiga madafa inga yanda suke aikin nan kinsan yau Abban ku zai dawo dole in tsaya da kaina in girka abinci"Umma kenan, rayuwar ku tayimani....kwara akara kulamana da Abban mu."Hmm yar nema kema kinzama kamar yayan ku kenan ba ruwan shi da kunya."Umma ai dole muyi raha da iyayenmu,ba rashin kunya bane"ke daman bazaki yarda ace ga laifin da Ahmad ya yiba....bari intafi kada ki rikeni da surutunki kisa aimani ba daidai ba."Umma nima zan shigo natayaku aiki"Aaa kedai ki kulaman da jikana yafi wannan aikin lada,kindai ji abinda na fada maki ko."? "Umma dan Allah"nadai fada maki"shikenan Umma na saikin dawo."tana shiga madafa ta fara hada girkinta ita da yan aiki suna mika mata kayan bukata,sannan ta hadama mijin ta kunun Aya saboda yana son shi sosai tana gama hadawa taji an rungume ta."Ummana ina kwana."Lafiya lau sai yanzun ka fito?karfe goma yanzun fa."duk na gaji kinga jiya nabi su Kamal munyi gwaji doki,kuma kinga na rabu dayi shiyasa."ai kun kyauta yanzun kaje ga kalacinka can na ajemaka a dki "Umma na koshi banjin zanci abu mai nauyi yanzun saidai ko bakin shayi ne idan akawai zan sha"wahala taka Shattimah....wai kai baka gudun kada yunwa takama ka"?murmushi ya sakar mata yace."inda sabo na saba Umma dako shayin ma ban iya sha"lallai kam ya kamata ka dinga cin abinci mai nauyi."Shikenan Umma yanzun dai bani shayin in fara sha daga baya naci abincin"ko kaifa."dariya sukayima juna cikeda so da kaunar juna..... Bayi ne da yawa a bakin sashen Galadima Hamza sai uban hanaya ke tashi wajen suna kiran."bamu amince da mugun zalincin da ake mana ba dole akwatar mana hakkin mu."amma kamar ba asan sunayi ba, sun kai sama da awa biyu suna abu guda sai lokacin Yarima Barde ya fito ya tsaya a sheke yake kallan su,baki daya suka nemi suyo kanshi daya bayan daya yake kallan su idanun sa suka sake dallo wata kyakkyawar baiwa....take ya saka sha'awarta a cikin zuciyar shi,gigitttar tsawa ya daka masu mai firgitarwa."waya baku damar zuwa wajen Mai martaba?miyasa zakuzo kuna zanga zanga har wannan wajen?wannan rashin sanin kimar nagaba ne!kodan kunga ana kyaleku shiyasa zaku dinga fidda jiniyoyin wuya kuna mana hauka....kamar dai kun manta ko su waye ku a Masarautar nan."munzo a kwatar mana hakkin mu akan kaika yanda kaco zarafim yar mu bataci ba bata sha ba."dariya ya sheke da ita ta shakiyanci yace."miye a ciki kamar ni Yarima Barde na shakata da diyar ku,bayan itadin baiwa ce, yakama yayi ku godewa Allah da har Barde kamar ni dan Sarki jikan Sarki tattaba kunnan Sarki kuma haifaffan Burhaan ya hada jiki danl yarku ai kun samu tabaraki."wannan zalinci bazan zamu yarda ba koda ire iren mu zasu kare sai mun kwatarma kammu 'yanci."wani bawa ke fadan haka. "Kai darwami,kawo mani waccan baiwar ka kai mani ita sashena yau zan gwada masu karshen tasha." ba tareda bata lokaci ba darwami ya damketa yafara janta baki daya bayin nan sukayi kanshi suma suna janta ga Sarkin bulala na dukan su kamar jakuna haka sukaita wulakanta su, aduk suka karaya yanda sukaga ana dukan su kamar za'a kashe su, Hamza ne ya fito cikin bangaren nashi a matukar kufule kana ganin shi kasan ya gama fusata da kama darwami mummunar tsawayi har saida suka firgita yace."karka kuskura ka kara jan yarinyar nan kasa ba kada hankali ne? zaka dinga jantabaceman daga ni idan ba haka ba zaku sha mamaki.A sanyaye suka wuce shima darwamin tafiya yayi."sannan ya koma kan bayi yace"ku kuma daga yau na kawo karshen wannan zanga zangar da kukeyi a cikin Masarautar nan!idan ba haka ba walahi ni nan Sarki Hamza saina karar da ahalinku kaf!ku baceman da gani tunkan dare yai maku marassa mutunci ni zaku wulakanta?ku a suwa zaku dinga ja da karfin iko da izzata har kun isa kuja da karfin mulki irim na Sarki Hamza kuna bayin? idan kuna gani kuna takama da shakiyanci ni zan gyara maku zama a cikin Masarautar nan dan haka ku kama gabanku tun muna shaidar juna! ke kuma uwar bayi da kai shugaban bayi daga kanku zan fara nuna misali."baki dayan su duk suka tsaya cirko cirko....Sarkin horo kasan abinda ya dace dasu."rufe bakin Hamza keda wuya ya farmasu da duka da halbi cikin kankanin lokaci dogarawan sa suka masu ruf da bulalu.tunda Hamza yabada umurni yakama gabansa ya shiga cikin turkar shi...... *Ku hanzarta ku mallaki naku domin wannan tafiyar ta dabance,na tabbata bazakuyi dana sanin siyen sa ba,kunji salon Izzah ko Mulki to yanzun wasan zai soma domin ba'ayi komai ba,kedai ki kasance da Jamila yar mutan kankia😍* _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _KARSHEN SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA ƊAYA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyan ki ta wannan number 08160508316. *BURHAAN* shigar shi dakin keda wuya ya sake wanke Barde da mummunan mari....ransa na matumar kuna da tarin bakin ciki lullube a cikin kokon zuciyar shi isakar bakinsa mai tsananin zafi ya fesar yace."tir da kai Abbas kabani kunya!bantaba zaton haka kake ba ka keta rigar mutuncina da ta martaba ta agaban BAYI kake wulakanta kanka da kanka kana ɗan Hamza!amma ka maida kanka wawa sakarai idan kana bukatar hutawa da waccan dakikiyar jakar baiwar har sai kabari wani ya sani balle kasa aka ma maka ita da karfi ashe kai wawane ban sani ba baka da fikirar da zakayi amfani da ita bazaka iya anfani da mulkin ubanka ba amatsayin ka na Yarima Barden Burhaan kuma mai jiran gadon karagar mulkin wannan Masarautar! shine zaka zubda girman ka da darajar ka gami da kimar ka tir da kalan halayen ka kabani kunya kuma kayi asara!"haba Mai martaba kawai dan na nemi baiw....sake wanke shi da mari har saida sauran zantukan sa suka tsaya cak a cikin bakin shi"ka kuskura nakara jin bakin ka billahilazim saina baka mamaki!duk iskancina da tijarancina bana bin mata!...kagan ni nan ni ba sakarai bane kuma ni jajirtacce ne kuma jarumi gwarzo banda tsoro ko kaɗan, kuma ni da kake gani na ina san girmana ban yarda araina ni ba! sai kai shashasha! kana da'na na jinina zaka zama sakarai! gaka dai da sunan Jarumai amma kwara sanhwami dakai kayi asara Abbas...kash kaicona wai ni BAYI zasuyi ma bore duk saboda kai Abbas! Badan komai ba saboda na haife ka,saidai kai bakasan allanka ba saboda baka iya wanke saba."kayi hakuri Abba."kayi gaggawar barin wajen nan idan ba haka ba saina baka mamaki shashasha dakai!."sadda kansa Barde yayi yanajin yanda mahaifinsa keta faman fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Masa'uda ce tafe cikeda kasaita gamida izzah ga tunkaho tanayi saman hanya kana ganinta zakasan kalar farin cikin da takeji tsabar dadin da takeji ganin bayi nayima Hamza bore....tana shawo kwanar da zata sadata da sashen Galadima Hamza ta hangi Sarkin horo na dukan bayi kamar wasu jakai da sauri ta karaso bata san ta dakama shi tsawa ba ta nunashi da yatsarta manuniya."Karka kara dukan su! mamugunta azzalimai bayan kun gama zalintar su shine zaku bisu da duka."Allah yataimaki gimbiyar Burhaan...dama Sarki Hamza ne yasaka ni"batacemin daga ba Hamza ko Abduljalal ne! na haramta duk wani zalinci wuce kabani waje tunkan na saba maka."da sauri yabar wajen shi da 'yan ta wagar shi. Ɗago uwar bayi tayi tanajin tausayin su cikin sigar tuggu da munafunci tana basu hakuri,sannan tasa suka koma sashen su."Kubar komai a hannuna zan neme ku da kaina."mungode Allah yasaka da alkhairi."Amin."da haka suka tafi....banda kallan harara ba abinda take masu ga mugun nufi da kudure kudure cike a cikin zuciyarta.... cikeda gadara ta shige sashen Hamza."bazaka wuce kabar man waje ba ko sai ranka ya baci."kayi hakuri Abba natuba kayafe....tafin da sukaji anayi ne ya dakatar da Barde daga maganar da sukeyi baki dayan suka waigao sukaga Masau'da tana ta murmushin mugun ta tanaci gaba da tafin da takeyi a hankali take tako har zuwa gaban su."Hmmm Hamza kenan!manya manyan Burhaan ashe har wasan namu yakai haka? Tunkan tafiyar tai nisa harka soma marin d'an ka bayan gorin dakake mashi ashe kaimakasan shi din mazinaci ne lallai Hamza! Ashe hat kafara sarewa! hhhhhh."ta kece da matsiyaciyar dariya har saida illahirin falon ya dauki karar dariya taci gaba da cewa."ni jikanyar Usmanu! gaskia wasan nan nayi mani kyau iya kyau komai yayi....Hamza karka manta yanzun akara fara wasan! muddin kace zaka watsar da Masa'uda bazaka taba jin dadin zaman duniya bare kaji dadin rayuwar Burhaan."gelele haka Hamza kebin Masa'uda da kallon mamaki da al'ajabi."abin kunya wai yau BAYINE kema Galadima Hamza bore duk a cikin Masarautar nan! Hahahhha gaskia kabani mamaki daka kasa hukunta d'an ka kodan gujewa mulkin fadawa halaka nasan bazaka so karagar mulkin Burhaan tafi karfin ka ba."banda idanu da ya iya zubawa Masa'uda har yanzun ya gaza katabus mamaki da al'ajabin ta kawai yakeyi ba dan baiyi zaton bazata iya yi masa haka ba yasan abinda yafi hakan ma zata iya yi masa kawai yana mamakin kalar Jarumtar ta ne...."wayyo har kabani tausayi kanin Abduljalalu kamar ba kaiba.....duk takama da girman jurerar mulkin a haka?hmmmm karka damu Hamza,komai zai wuce kai dai kayima yayarka Gimbiya Masa'uda biyayya ko kasamu karbuwa a cikin Masarautar Burhaan kada zauna da Mulki amma ba mutane kaima kasan aikin banza ne,Jama'a itace ɗan Adam komai girman sa ko mulkinsa mutane sune rigar mulki."wani irin takaici ne ya tokare kirjin Hamza jiyayi kamar yai kwalla idanun sa sun koma kamar jan gauta a zahiri sai ya wayance ya kece da mahaukaciyar dariya saida yayi mai isar sa sannan yace"hahahhhh....Masa'uda kenan..!"tafa hannayen sa yayi saida suka bada sauti n gaske sannan yafara zagayeta cikeda izzah yaci gaba da cewa."sirri sirri!duk abinda kikeyi a tafin Hamza kike kema kinsan haka! Kar nike kallan ki a cikin Burhaan....hmmm karki manta na iya wanke allona kuma na sansa sannan ina ankara dake lokaci na dibar maki.kigama shakiyanci ki da kike ikirarin da'na ya nemi baiwa kisanu isa ce tajawo hakan!kalle ni da kyau Masau'da kika kuskura kikace zaki kara shiga sabgata hmmm! harkin bani tausayi....sannan na haramta kalmar yayata a bakin ki idan ba haka ba saina datse tsinnan harshen ki ko Abduljalaal dakike gadara dashi na girmi wannan a halin yanzun bare ke shashasha baki isa kija da Sarki hamza ba ki kama kanki." "Hmmm da gaske? sarki sarki,su Sarki manya! yaushe aka fige bare a sha roman??? waya shaidaka a matsayin Sarkin? kace dai Galadima Hamza mai rikon kwaryar mulkin Burhaan kanin Sarki Abduljalal."tayi maganar tareda wani irin shu'umin murmushi mai dauke da ma'anoni....."ballagaza shashasha idan ana maganar mutane wake sakoki? wai har kinsan dadin miji? bayan ke da kanki kika cuceshi sannan kika jefa shi cikin musiba da bala'i? Hmm nafahimci cacar baki da jaka kamarki lallai kam ba karamar asaraba ne a wajen Hamza! Sannan da kike takama ni ba Sarki ba ne to kisha kurumin ki saura kiris dubatan mutane su shaida Sarauta ta,jahila kece kanki ke cikin tukunya” waro idanuwanta tayi woje tsabar razana da kalamin sa tana mai cewa“ni kake fadama kalmar jahila?." "Bace min da gani tunkan in baki mamakin da bakiyi zato ba! Sakara aura ka jakar mata ballagaza wadda batasan kimar kanta ba ki rubuta ki aje saina gyara maki zama a cikin Burhaan"zazzafan iskar bakin ta ta fesar tana huci tace."Mu zuba mu gani ni da kai shege ka fasa" "Ke malama da kata karki kuskura ki zagi mahaifina matukar tsautsayi yasa kika zage shi saina wanke ki da mari"iyyeh ɗan karamin ɗan iska! Yaushe daren yayi bare garin ya waye kul! Na haneki artaba sa gimbiya Masa'uda ba dadi yaro ko tsohonka ya ya iya dani bare kai karen kaɗa miya! karka kuskura da uban ka nikeyi! ko uwar ka Uursiyyah bata isa inyi da ita ba bare kai! kaga wancan aura kan? jakin mazan? toh da shi nikeyi bakai ba,dakiki mazinaci....."ya daga hannu zai wanketa da mari kenan,Hamza ya hana shi."kyaleta Barde dani take wasan! kai dai ka gujema idanun mujiya...zaki iya tafiya jahila,marar 'yanci."Kayi magana mai anfani Hamza dani kake zancen." tana fita ya dawo kan Barde"kaga irinta ko Abbas?Masa'uda da kake gani bakaramar shaidaniya bace,ita din makirace ajin farko ka kiyayeta! Kabani kunya bakada amfani agareni ni koda nayi tashen hatsabibin cina banjama uba na zagi ba sai kai! da kimata ni Hamza Muhammad Abduljalal ni ake gayama magana irin wannan duk saboda kai! kaskantattun bayi na suyi mani bore duk saboda kai! gaskia kayi asara walahi saina hana kowa motsi cikin Burhaan."Abba kayi hak...."ɗaga mashi hannu yayi a fusace tareda rufe idanunsa da yakejin su kamar zasu fado kasa tsabar zafin da suke mashi yace."Kai Barde karka kuskura kabari in bude iduna na ba tareda kabar wajen nan ba baka da anfani agareni! Kana nufin a haka zamu dauwama a mulkin Burhaan ɗin?kana ma ya'yan mutane fyaɗe? a haka zaka amsa sunan yarima mai jiran gado?.......Hmm,ba'a Yarima ɗan iska! haka kaga Yarima Sadauki nayi? ga aji ga kasaita,ga tarin haiba,banda miskilancin shi mai aji ga tarin izzar mulki uwa uba kyau da Jarumta wani abun sai amale Sadauki yayi a rayuwa! Sannan shidin mai kishin ubansa ne banda zuciya bai son raini uwa uba shidin mai tarin ilimi ne komai ya gama hadawa ina ma ace ni na haifi Sadauki lallai kam da nayi takama a nuna gadara,a cikin dubatan mutane, sai dai kash ashe wawa sakarai na haifa marar hankali"Abba kadaina ai baitani har haka dan Allah"dallah bacemin dagani malan ni da kake gani ina da kishin kaina dana 'yan uwa na, bacemin da gani!" ba shiri Barde yafita cike da bakin cikin kalmomin mahaifin shi..... *Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari ukku kacal,Acct details 0777512438 Access Bank,Jamila Abubakar Bello.Ku tura shaidar biyan ki ta wannan no 08160508316.* Kwance take saman tafkeken gadon ta wanda yasha ado na sarauta sai tunani takeyi,hawaye keta zirarowa a gafen idanunta ba abinda yake taba mata zuciya yanda Ammar ya rabata da bawanta Umar ta karfin iko,lamarin ya taba mata zuciya."bazan tata iya hakura da rashin Umar agareni ba,taya za'a rabani da shi dan Jarumi nima saboda Jarumtar shi nike son shi,bazai taba yuyuwa dole inyi magana da Mai martaba."hawaye dake ziroro mata sukaci gaba da sauka saman kuncin ta. Fadila keta faman yima Zubaina Sallama sam bataji taba har saida ta tabata sanann ta dawo firgigi cikin hayyacin ta"Fadila ke ce,yaushe kika shigo ban saniba."? "Allah yataimaki gimbiya ra na dade da shigowa baki jini bane...Allah yasa dai lafiya."?ajiyar zuciya ta fesar tace"Bakomai."murmushi ta saki tace"har na samu sassauci a cikin zuciya ta,farin cikin ki shine nawa gimbiya ta Allah yabaki nasara....daman gimbiya Bilkisu tace in fada maki,Mai martaba nasan ganinki a sashen shi yanzun yanzun."a tsorace ta kalli Fadila duk da bata bari taga karayar ta fili ba tace."ko lafiya."? "Allah yataimake uwar gijiya ta, ina ga kamar ku duka yake nema...saboda na ga Raliya ta shiga sashen Yarima Aryan shima sakon Mai martaba ya riske shi,Allah ya karamaki tsawancin kwana yaka mata kitashi bansan inga ana jiran ki."banjima da tashi daga bacci ba,naso insake shiryawa sannan"wannan girmanki ne,saidai baki da wata atattare dake kamar yanzun kika gama shiryawa kinyi kyau kuma dama ke din mai kyau ce, kibari idan kindawo saiki sake siryawa."toh Fadila yanda kikace haka zakiyi"nagode da karamci uwar dakina ga alqabbar ki."saina dawo"Allah yatsare hanya......Allah yataimaki uwar ɗaki na mikike bukatar a dafa maki."? "kisa ahaɗa mani farfesun kifi."angama ranki shidade saikin dawo."tana fita bayin daketa fama da aiki suka duka sai gaisheta sukeyi amma ko kallo basu isheta ba wasu kuma ta daga masu hannu harta isa wajen Mai martaba. Bayan sun amsa mata sallama ta samu waje ta zauna kusa da Yarima Aryan sannan ta gaishe dasu cikin girmamawa kowa ya amsa. "mama na miyasa kullin idan zanyi zama daku kece karshen zuwa kin cika shiririta"Allah yabaka yawan rai aimin afuwa ban dade da riskar sakon ka ba,amman ayimin afuwa"bakomai ya'ta matso kusa da Abban ki."matsawa tayi kusa dashi ta zauna."yasa hannunsa gefen fuskar ta ya shafa a hankali yace."Allah Sarki da yanzun ya'ta Mabaruka tana nan tare daku...Allah yaimaku albarka"Amin Abba....sannu da dawowa."yauwa,ya'yana abin alfaharina ina fatan kuna lafiya."? "Lafiya lau Abba."gyaran murya Mai martaba yayi yaci gaba da cewa."godiya ta tabbata ga Allah daya hadamu baki dayan mu a wannan waje....dalilin dayasa nasaka a kira mani ku ina son in isar maku da wani muhimmin sako munyi zama da manyan Sarakuna masu girma kamar yanda kuka sani da ance za'a gabatar da Gasa a Masarautar Kesar....saidai Sarkin Sirika ya nemi alfarma akan ayi shi a Kasar shi kuma za'ayi tsawon sati daya acan amma kwana biyar za'ayi ana wasan idan Allah yakaimu.....Ammar kaida dan uwan ka kune jarumai na yana da kyau ku jajirce sosai fiye da tunanina kuba jaruman ku horo na musamman fiye da Da......kunga yanda Jaruman Burhaan suke da jajircewa,har yanzun kaf Masarautun nan banga kamarsu ba, ina son kusani suma an aika masu da gayyata nasan zasu zo duk da Sarkin su baizo zaman da mukayi ba nasan dai akwai dalilin rashin zuwan shi,kuma shi aka ba shugaban taro."Allah yataimake ka, kace a wannan karon zamu hadu da Sadauki kenan."insha Allahu haka muke tunani."ranka shidade.....insha Allahu zaka samemu da jajircewa akan aikin mu"Allah yasa,ina alfahari daku Allah yaimaku albarka"Amin ranka shidade." Maida dubansa yayi ga Zubaina dake fa faman wasa da zoben gold daketa walauniya saman yatsan ta yace"ya'ta."? "na'am Allah yakara maka tsawon rai"sako daga Sarkin Sirika,yace in gaishe ki sosai sannan yace idan za'aje gasa inje mashi dake,ko kina bukatar zuwa."? "ina amsawa nagode da karamci....eh Abba ina son zuwa"shikenan mamana Allah yakaimu lafiya."Amin." "haba ranka shidade da ita za'a tafi?mace ce fa."? "Aminatu kenan,minene a ciki? yana da ɗiya fa ga gimbiya Rahama zasuyi kawan ce"shikenan Allah yakaimu da rai da lafiya"Amin."sake gyara kishingiɗarsa yayi yace."Babban dalilin kiran ku,akan bawan nan ne Umar."wani irin mummunan faduwar gaba ya doki zuciyar Zubaina har saida ta tafe kanta daurewa kawai tayi har saida Umman ta ta kalleta da alamar tambaya....tayi saurin sunkuyar da kanta a kasa jikin ta yai sanyi sosai." ban laminta da zaman shi cikin Masarautar nan ba....raina nabani akwai wani babban al'amari atare da yaron nan! anya ainahin bawa ne shi? kai da wuya."Ranka shidade...."yimin shiru Ammar ban baka damar magana ba"Allah ya huci zuciyar ka."ya sadda kansa kasa."dan haka inaso akira mani Ado yabani tarihin sa."rufe bakin sa keda wuya sai ga Abdussalam ya shigo da cikin so da kaunar junan su suka rungume juna ya zauna gefen dan uwan na shi....duk suka gaishe da Baffan nasu cike da girmamawa.." "ban laminta da Umar ba bana bukatar saman shi cikin Zairana."Allah yaimaka yawan rai ayi mani izinin magana"ba damuwa Abdussalam zaka iya magana."duk da yanzun na riski tattaunawar ku amma ya kamata kabi abin nan a hankali,kwanaki nasa ankira mani Ado na zauna dashi a fa'da duk saboda Umar yafadaman abinda yasani akan shi, lallai Umar bawa ne ya siyoshi a kasuwar gobir bayan jajircewa da yayi akan siyan shi wanda ya tadda manyan bayin Masarautu daban daban na karawa wajen siyen shi ta dalilin uwar dakin shi Zubaina aka sawo shi mafarin zuwan shi kenan wannan Masarautar mai albarka"Abdussalam kenan wannan shi kadai ne asalin Umar."? "Allah yataimake ka kamar yanda yazo a Bawan sa mu dauke shi a haka,tunda rabin bayin Masarautar nan suma a haka aka sawo su kuma bamu damu da sanin asalin su ba"kwarai kuwa kanina amma ai bana tunanin wannan yaron ainahin bawa ne shi." "nima haka yaya nayi wannan tunanin kamar yanda nace zamu amshe shi a cikakken bawan sa a yanda yazo mana kuma mai mamu hidima kamar kowa."Shikenan haka za'ayi."wani irin ajiyar zuciya Zubaina ta sauke sirrance tana kara godema Allah..."Allah yataimake ka ina neman izinin magana"injinka Ammar "kamar yanda muka sani Umar bawa ne amma bai dace da hidimar yau da kullun ba, saboda Allah ya bashi karfin hali da jajircewa shiyasa muke neman alfarma a wajen ka da abamu shi ya kasance a cikin jerin jaruman mu zamu bashi gwaji na musamman"Ammar kenan kasani ba Bawa ba jarumta, bawa bawane kubar shi a matsayin bawan shi saidai zaku iya tafiya dashi dan yai maku hidima"Ranka shidade kataimaka mana ka barshi a cikin Jaruman mu"Aryan karka kuskura inkara jin maganar Umar anan wajen...kamar yanda nace za'aje dashi Sirika amma a matsyin mai kula da Jarumai "ranka shidade kana ganin hakan ya dace."? "Kwarai kuwa Abdussalamu"shikenan." "daga karshe ina son kowa ya shaida ban laminta Umar ya zauna da ya'ta Zubaina ba,amatsayin hadimin ta ba.....namiji bai dace da yiwa ya'ta hidima ba sai dai yan uwan ta mata kamar yanda al'adarta take akan Umar ba za'a fara ba,shima bawa ne kamar kowa"baki daya numfashin Zubaina neman daukewa yake kanta yafara sara mata....."Ranka shidade wanki kadai yake mani kuma shidin jajirtacce ne"ni Abdurrahman Abubakar daga yau na haramta maki shi bare har yayi maki wata hidima, zansa a shiga cikim sansanin bayi jakadiya taje ta debo maki bayi mata matasa masu jiki a jiki kiyi yanda kikeso dasu amma banda Umar bake ba shi.....kusani bawa namiji bai isa yazama hadimin ta Ya'ta ba"Abba dan Allah kabarman Umar yaimani hidima ina so....kallan da gimbiya Amina taimata yasata hadeye yawun bakin mai tsananin daci....."Mamana Kenan yaushe kikasan dadin aikin namiji da har zaki dinga hadani da Allah duk akan Umar?....lallai kam indai ni din mahaifin ki nedaga jinina kike ba Umar ba zama hadimin ki.....ku kuma Ammar na aminta Umar ya dinga kula da bukatun jaruman ku sannan dashi zamu tafi Sirika dafatan kun fahimta"eh ranka shidade Allah yakara girma mungode"ba laifi....mamana kinji me nace maki."? "Eh Abba naji" "Da kyau haka nike so zaku iya tafiya"Allah yakara maka lafiya kuta shi cikin aminci "Amin." Suma matan shi basu jima sukai masu sallama kowa yakama gaban shi suka bar shi shida ɗan uwan shi,suka ci gaba firar su. Sadaukin Burhaan na kudi ne ki hanzarta kibiya domin jin dadin karatu yar uwa shafin karshe ya kare daga wannan siyen nagari maida kudi gida. Koda gimbiya Zubaina ta koma daki tana shiga ta fada saman gado sai uban kuka takeyi kamar ranta zai bar gangar jikin ta ga uban ciwon kai daya turniketa jitake baki daya Masarautar ta fita a ranta...."na bani ni Zubaina mike shirin faruwa da nine?miyasa Abba bai san abunda nike so a rayuwa? a haka yake nuna yafi sona yanzun ma hadimin nawa dana zaba dakaina shine zaice bai yarda ya zauna a tareda ni ba😭 meyasa na koyawa ma kaina sabo da Umar! nabani ni Zubaina ya zanyi da rayuwa ta!." koda Fadila taga shigar uwar dakinta a gigice ta biyo bayan ta ko magana bata ji idonta ya gama rufewa kuka kawai takeyi duk ta fita hayyacin ta ko da akace za'a aura mata Yusoup Shehu bata shiga damuwa ba kamar wannan lokacin ba, dukawa tayi ta fara ba Zubaina hakuri sai a lokacin Zubaina taji sautin maganar ta...."ubanwa ya baki damar shigomin cikin daki na ni sa'ar kice."?baki daya jikin Fadila yahau bari."Allah ya huci zuciyar ki Fadila ce" "ki uwar Fadila ce! fitarmin daga daki karna sake ganin kowa a sashena kinaji na."? "Eh...kihuta lafiya."da sauri ta fita har yan hanjinta ke kadawa tana zuwa babban falo duk ta sallami bayi tace sai an neme su,suma daman duk sun tsorata da yanayin da suka ga Zubaina daman ko gaishe ta basuyi ba gudun kar su shiga cikin bala'i.....kowa ya kama gaban shi itakuma Fadila ta koma dakin ta duk a cikin sashen gimbiya Zubaina..... Ranar Zubaina kuka take yi kamar ta mutu ko falo bata kara fitowa tana cikin daki sallah kadai take tashi tayi,wannan kenan..... Anan nakawo karshen shafukan Kyautan wannan littafi na Sadaukin Burhaan yar uwa bazan ce komai ba saboda kinji nasa salon kamar yanda kikaji na Izzah ko Mulki ba'ayi komai ba domin yanzun wasan ya soma ya wannan katamurmurar zata wakana? Bazaki samu wannan ba sai kin mallaki naki akan farashi mai sauki da arha naira 300 ta Acct no 0777512438,Access Bank,Jamila Abubakar Bello shidar biyanki ta wannan number 08160508316.idan kika bari akayi babu ke ansha da rabon tafiya ta daban ce siyen nagari maida kudi gida. JAMILA JAMEEY. (Yar Mutan Kankia) Share Saboda Allah. *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA BIYU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shidar biyanki ta wannan number 08160508316. *Assalamu alaikum yan uwa ina fatan kowa yana lafiya,jiya nayi posting last free page saida na duba nagani mistake nayi ba nan nayi niyar tsayawa ba ga cigaban free pages nan.* _Ina kara jinjina ga masoya yanda kukayi payment na book din nan Allah yabar so da kauna ina maku albishir da_ _mungama free pages zamu cigaba da posting paid pages son so nike maku irin billions din nan._ A bangaren gimbiya Bilkisu,baki daya matan sa suka hadu sai al'ajabin lamarin mijin su sukeyi saidai sun rasa dalilin sa na yin hakan....saboda tunda suke dashi ba bawan da aka taba siyowa yace bai aminta dashi ba sai UMAR sun san dole akwai babban dalilin dayasa aikata hakan...."Umman Aryan ina mamakin lamarin Mai martaba abinda ya akaita yau ya firgitani sosai saboda ance za'a saka Umar cikin jarumai ya hana abin da yafi bani mamaki yaron nan akwai shi da Jarumta gashi yanada jajircewa lamarin yaron nan kamar ba bawa ba,saboda yana da nagarta."ajiyar zuciya gimbiya Aminatu ta aje tace."Bilkisu kenan,ni kaina lamarin mai martaba yana tsorata ni"gaskia ne ranki shidade....ni kaina Umar ya kwanta min arai ga sanin darajar manya idan yana wani abun kamar wani ɗan basarake"fatan mu dai Allah yasa haka yafi zama alkhairi."Amin."cewar gimbiya Rukayya....."abinda ya kara daure min kai yanda ya raba Umar da Zubaina yarinyar nan tana jin dadin yanda yake mata hidima."kada kice haka Rukayya ni hakan ma yai mani daman kyau ace taci gaba da zama da hadimai mata yan uwan ta hakan kamar zaifi "Gaskia ne shine kimarta ma."Allah yai mana jagoranci."Amin."da haka sukaci gaba da tattaunawa rabi duk akan lamarin mijin su ne. Ba abinda Sadauki keyi faman shara tare da bayi sai aiki sukeyi kowa da kalar abinda yakeyi daga wani bangaren kuma bayi ne aketa bugu dagani dai akwai abinda sukayi....wani bawa ne yazo kiran Sadauki suka tafi tare dashi har bangaren Yarima Aryan a can suka iske Yarima Ammar koda bawan nan yakai shi fita yayi ya bar su. Izinin zama sukayi mashi ya zauna cike da ladabi sannan ya gaishe su cikin girmamawa."yauwa Umar barka...daga ina kake."? ɗan sadda kansa yayi kasa kadan yace."daga wajen aiki nike sai ga kiranku ya sameni"gyada kansa Ammar yayi yace."daman dalilin kiran da akai maka muna son mu sanar dakai cewa da ance za'a saka cikin Jaruman mu saidai duba da yanda mukeda yawan Jarumai shine Mai martaba yace zaka kasance mai ba jarumai kulawa tunda kanata jarumta da jajircewa." a hankali Sadauki ya dago kansa ya kalli Yarima Ammar yace."nagode Allah yakara girma duk abinda kukace haka za'ayi zabin ku shine nawa"bakomai Umar,sannan zaka shirya a watan gobe zamuje dakai wajen gasar da za'a gabatar a Kasar Sirika sai ka kara kulawa da al'amuran Jaruman mu sannan daga yanzun da kai zamu dinga zuwa wajen gwaji yana da kyau duk abinda zamu dinga aiwatar wa sai kadinga kulawa da kyau saboda bukatar hakan idan ta taso"in sha Allahu zan kula da kyau Umar godiya mai tarin yawa banda bakin da zan gode maku Allah ya saka da alkhairi."yima kai ne Umar....Mai martaba yace zaka daina yima Gimbiya Zubaina aiki zaka tsaya tareda Jarumai kana basu kulawa...komai kenan idan mun dawo zamu san abinda yakamata ka dinga yi."Shikenan Allah yakaimu lokaci lafiya." _WASHE GARI_ Jarumai ne saman dawakai sai uban gudu sukeyi suna kaiwa wajen wata tuta sai bada gwaji akeyi abin gwanin ban shi'awa Umar ne zaune hannun shi ɗauke da kaya sai fiffita yake yima manyan Jarumai yana basu ruwa ranar yini sukayi suna rali anata tantance gwanayan da zasuyi wasan duk abinda sukeyi Umar na ganu kuma yana hardacewa cikin kan shi,saidai duk lokacin da zai ga suna gudu saman dawakai ji yake kanshi kamar zai rabe biyu tsabar yanda yakejin juwa na dibarsa baki daya yarasa abinda ke mike mashi dadi a rayuwar shi ta duniya..... koda Ammar ya fahimci halin da Umar yake ciki da sauri ya karaso inda yake ya dafa kafadar shi yace."Umar mike damun ka."? "Kaina ke mani ciwo."sannu kaje gida ka huta."gyada kansa yayi sannan yai mashi godiya ya tafi ji yake kamar kanshi zai fadi ƙasa da kyal yasamu ya isa gida ya kwanta ba abinda yake gani idan ya rufe idanun shi sai sukuwar dawakai anata wasa saidai ya kasa gane su waye akan dowakan sai uban ihu da mutane sukeyi baisan sadda bacci ya dauke shi ba..... Bayan kwana biyu gimbiya Zubaina ce zaune cikin kayan buzaye sai uban kuka takeyi kwana biyun da tayi bata ga Umar ba jitake kamar ta shekara bata gan shi ba,banda aikin kuka ba abinda takeyi duk ta rame tayi duhu,ta maida kuka kamar ibada kwantawa tayi taci gaba da rera kukan ta marar sauti. Fadila ta shigo wajen uwar gijiyar ta gabanta ta duka tace."Allah yataimake ki uwar ɗakina kasancewar ki cikin wannan yanayin yana daga min hankali damuwa bata kamata da ke ba Allah yataimaki gimbiyar Zairana."a hankali ta ɗago kanta ta dallama Fadila uwar hararar wadda tasa Fadila saurin mikewa jikinta na rawa ta fita kai tsaye wajen Yarima Ammar ta nufa,iso hadimar sa tayi mata tana zuwa ta zube kasa takai gaisuwa sannan tace."Allah yataimake ka halin da uwar ɗakina ke ciki ya daga mani hankali ainun taki ci taki sha bansan ko zata iya sanar maka damuwar ta ba."ita Zubainar? ke cikin hali?muje inji abinda ke damunka."toh ranka shidade."gaba yayi tabiyo sa baya suna isa ya shiga wajen Zubainar har yanzun tana aikin kukan ta duk sallamar da yayi bataji sa ba har ya isa inda take ya zauna gefen ta, ba tai aune ba taji ya dafa kafadar ta cikin sanyin murya sa son kwantarwa kanwar tasa da hankali yace"Mike damunki kike kuka."?da sauri rungume shi taci gaba da kukan da takeyi marar sauti rarrashin ta yaci gaba dayi har saida tayi."fadamin mike damun ki."bansan ya zanyi ba Yaya,yanzun Mai martaba ya rabani da Umar har abada."kalaman ta suka sauka cikin dodon kunnen sa zuwa zuciyar sa har saida ya rabata da jikin shi yana kare mata kallo yana so ya gasgata lamarin ra abinda take fada daga iya bakin tane kadai ko har cikin zuciyar ta ne ba kadan yayi mamakin jin abinda kanwar tashi ke fada ba."akan Umar zaki zauna kina kuka?haba kanwata yanzun kamar ke kina gimbiyar Zairana zaki dinga kuka akan namiji?haba kanwata kece fa gimbiya Zubaina wadda sunan ta ya karade ko ina har ake takara a kanki shine zaki dinga kuka dan an rabaki da Umar."? "Ina san Umar yaci gaba da yimin hidima kamar yanda nasa aka siyoman shi kaima kasan inason mutun jajirtacce mai jajircewa shiyasa nike kaunar Umar."banda kallan mamaki ba abinsa yakema Gimbiya Zubaina baki daya ya kasa gane kurman zancen da takeyi masa."ban fahimce kiba Zubaina."ina son yaxi gaba da zama a kalkashin ikona."Haba kanwata,kidaina wannan maganar tunsa Mai martaba yace bai bukatar ganin Umar a matsayin hadimin ki kema ki hakura,idan hadimai kike so akwai kala kala sai kin zaba."Nasani Ya Ammar kaima kasani bantaba nuna ina son bawa yai mani hidima ba sai akan Umar."Naji minene dalilin ki na son Umar yai maki hidima."? "Saboda shidin Jarumi ne kuma gwarzo."ajiyar zuciya ya shida a hankali sannan ya riko hannayen ta yace."Tabbas Umar jarumi ne na gaske saidai ya dace ki hakura dashi kamar yanda Sarki ya bukata,sannan zamu aje shi dan kulawa da jarumai kinji."? Itama ajiyar zuciyar ta sauke tace."shikenan,idan kuka gama gasar zaku dawo min dashi."? gyada kansa yayi yace"zamu duba yuyuwar hakan keman kinsan Mai martana bai sauya magana ian har yayi ta ki daure ki sadaukar da Umar ga Masarautar kodan farin cikn Mai martaba."toh yaya na yanda kace haka za'ayi."ina alfahari da ke kin kyauta haka nike so."murmushi ta sakar masa ya jima yana kara kwantarwa kawar tasa da hankali kafin yai mata sallama ya tafi..... _MASARAUTAR SIRIKA_ "Zaki iya zuwa ki sanar mashi bani da lokacin ganawa dashi,idan yaga dama ya dawo zuwa gobe sannan kadda ki kuskura ki bari kowa yakara shigowa sashe na har sai zuwa gobe kema idan kin kai sakon zaki iya tafiya sai gobe kidawo ki sanar da mai kula da ficen sashena kada yabar kowa ya shigo kodakuwa dan gida ne yazo neman ganawa dani kice mashi ni gimbiya Rahama bani da lokacin ganawa da kowa sai gobe in Allah yakaimu ina fatan kin fahimta? sake rankwafar da kanta tayi kasa tace"Allah yakara maki girma da daukaka na kiyaye komai umurnin ki shine abin tinkaho na yanda kikace haka za'ayi." "dolen ki kiyi biyayya Murjanatu." (Allah sarki rayuwa.....gimbiya Rahama kenan,mai takama da gadara gamida tsantsar izza mulki wadda take takama da usuli 'ya daya tilo ga Sarkin Sirika ya dauki son duniya ya daura mata bai hadata da kowa ba yar da zai iya komai akan ta) Tana gama fadar haka takoma ta kwanta saman gado tare da yin doguwar mika taja bargon ta mai tsananin laushi ta lullube jikinta ta rufe idanuwan ta kamar mai bacci. Sarki Abdullatib ne tareda Shamaki suna tafiya a tsanake sai dogarawa dake take masa baya kai tsaye sashen yarsa ya nufa duk inda zai wuce hadimai da sauran bayi keta kawo gaisuwa har ya isa sashen gimbiya Rahama yana shiga ya tadda mai kula da ita da sauri ta zube kasa ta gaishe shi."Allah yataimakeka gimbiyar tayi bacci bari in mata magana."Aa rabu da ita ta huta da kyau kikara kulaman da ita."angama ranka sgidade."harya juya zai tafi ya waigo yace."idan ta tashi kice mata ina san ganinta sashena."angama ranka shidade."nan suka juya suka tafi tareda tawagar shi. Duk abin da sukeyi gimbiya Rahama najin su kamar jira takeyi mahafinta ya fita ta kwallawa Murjanatu kira,jikin ta na rawa ta isa gabanta ta zube."ranki shidade gani."dauketa tayi da mari har saida ta rike kuncin ta tace."tuba nike,ranki shidade Allah yakara maki nasara kimin aikin gafara."Yimin shiru haka nace maki kifada? bana ce maki kice ban bukatar ganawa da kowa ba sai gobe."? "Allah ya huci zuciyar ki bakina yayi kadan ya furtawa Mai martaba kalmar nan ba"Maimartaban ubanki ne ko uba na."? "Allah yakara maki yawan rai mahaifin ki ne."Mtsw aikin banza aikin wofi dama danshi nake bada wannan sakon nasan zai isa kunnen sa,amma saboda ke dakikiya ce shine kika bata mani shiri"tuba nike bansan haka kike nufiba Allah ta huci zuciyar ki"aikin banza sama ba gane abubuwa kike ba,bacemin da gani, tunkan ranki yai mugun baci."kitashi cikin aminci." "mtsw dubeki baiwa dake yar wahala." A sanyaye Murjanatu ta fita ta koma wajen aikin ta kamar yanda uwar dakin ta,ta bukata. ba karamin bacin rai gimbiya Rahama ta shiga ba taso ace tafadama mahaifin ta sakon ta, tasan zai damu sannan zai kara daukar abinda take so da mahimmancin gaske,kuma tasan zai nema mata alfarma wajen Sarki Abduljalal,tasan zata dace da auren Yarima Sadauki, musamman yanda ta jima tana dakon son shi a rayuwar ta..... _Tirkashi masoyan_ *daukar fansa* _kunji abinda gimbiya Rahama tace,tajima tana dakon son Sadauki 😂_ _________________ "Umar katashi haka nan, baccin mi kakayi kaga lokacin sallah yayi,anya lafiyar ka ƙalau kuwa."? A hankali yayi mika sannan ya zauna yana addu'a yace "Eh Abba,banjima da dawowa daga masallaci ba, ina wajen gwaji kawai naji kaina naiyi mani ciwo shine nadawo na kwanta."ya kakejin kan naka yanzun."da sauki,walahi dana rufe idanuna sai in dinga ganin dawakai da mutane akai suna ihu saidai bangane ko suwaye ba, kuma bana iya tuna komai."hmmm yaro man kanza, baka ganin kullin kana hudda da dawakai sai inga kila dan kuna gwajin nan ne shiuasa kake ganin dawakan." Girgiza kansa yayi yace "Aaa Abba basuyi kama da kalan dawakan Masarautar nan ba....."kaga da'na karka damu kanka ba wata matsala, mafarki ne kawai kuma kasan ba gaskia bane"Shikenan Abba, yau yarima Ammar ke fada mani Mai martaba ya hani yima Zubaina aiki, sannan yace bazan kasance daga cikin Jarumai ba,saidai in zama mai basu kulawa kuma dani za'aje Sirika."karka damu da'na hakan ma bakaramar daukaka bane a wajen ka idan munje ka dage akan aikin ka"Abba kaima da kai za'aje? "Kwara dagske kaga ni ne shugaban bayi"kace nima ɗan Sarkin bayi ne."? "Kwarai kuwa da'na ni ne Adamu Sarkin bayin Zairana lallai kan kaf nahiyar mu ba wanda baisan niba, shiysa kaga bani aikin komai kuma har bayi nayi mani hidima sannan banda shamaki da fa'da damu ake fadanci, sannan ba bawan da ban sani ba kaf Masarautar nan "Kai tab kana kokari Abba amma suna dayawan gaske"nasani rabi da kwatar su dakaina na siyosu wasu kuma anan aka haifesu kaga ai baza suyiman alaye ba, saidai ko naman ta sunan bawa"hakane Abba na Allah yatayaka riko." "Amin da'na"Allah yaimaka albarka"Amin Abbana." ______________ Waziri Basheer daure cikin rana ga uban dukan shi anayi kamar wani bawa ba abinda yakeyi sai salati yana gayawa Allah halin da yake ciki,duk irin azabar da Hamza ke gana mashi Basheer bai da niyar fadar inda zoben nan yake,sawa yayi bayi suka dauko kattin duwatsu suka azama mashi bisa kirji baki daya numfashn sahi ya dauke ga uwar rana anayi amma ba ko digon tausayi cikin zuciyar Hamza, hakan ya tafi ya barshi ko ajikin shi...... zuwa yanzun Sarki Abduljalal ko gane mutane baiyi,ba wanda ya damu da shi daga yan uwansa har Masa'uda ba wanda ke duba shi sai Saminu,halin da yaga Mai martaba ya shiga,bakaramin tashin hankali ya shiga ba,yana cikin alhinin halin da Mai martaba ke ciki sai ga gimbiya Sa'adatu ta shigo itama sai a boye take kawoma Saminu magani tace ajika a bashi idan Allah yayarda zai samu sauki..... "Saminu ya jikin na shi."da sauki ranki shidade saidai bai cin komai."Allah Sarki komai yana da lokaci ga magani kaba shi yasha gobe zan aiko hadimata ta kawo maka magani ka jika saika shafa mashi a jiki."toh ranki shidade."ta dan jima kafin ta koma sashenta tana mai tsananin jin tausayin mai martaba a ranta. Koda Masa'uda ta tashi da kanta ta aiki Talatu wajen bokanta zata anso mata sako a cikin gaggawa saida dare tafara sannan ta fita ta hanyar sirri ranar ko gezau Gimbiya Masa'uda ta kasa Allah Allah take Talatu taje ta dawo batare da ansamu matsala ba..... A bangaren gimbiya Juwairiyyah ba abinda takeyi sai kuka tana kara yima mahaifin ta adduar samun lafiya,sannan a bangaren zuciyar cike take da begen dan uwanta fatan ta Allah ya maido shi gida lafiya sannan Allah ya dawo cikin hayyacin shi duk inda ya tsinci kanshi,baki daya hankalin ta nakan ahalin ta duk halin data tsinci kanta bai damunta tasan wuya bata kisa sai kwana sun kare. `FA'Da` Galadima hamza zaune saman karagar mulki sai busa iska yake yana nuna isa da tsantsar gadara yasa an kamo mashi Shamaki an gurfanar dashi cikin fa'da kamar wani katan barawo."Allah yataimakeka gashi mun kawo shi. a dage yake kallan Shamaki kamar wani marar yanci,shiko yayi zugun kamar wani munafuki ranshi bakikkiri ganin irin cin fuskar da Hamza ke yi mashi tunawa yayi yaga su keda fa'da amma yau shine za'asa dogarawa su kamo shi a gaban bayin Burhaan lallai ko kadan hamza bai san kimaba"kai Ibrahim bada kai nike magana ba."? "Allah yataimake ka banji ba."minene dalilin dayasa ka daina zuwa fa'da."? "Ranka shidade banda cikakkiyar lafiya."Kataba ganin inda ake fa'da babu Shamaki."Allah yakara maka lafiya ba'a taba yiba kuma baza'a taba yiba"daga yau karka kuskura kara rashin zuwa fa'da koda zaka mutu sai kazo Fa'da kanajina"insha Allahu zan kiyaye."sannan ka maida hankali ka nemo duk kayan da kasan ana anfani dasu idan za'a nada Sarki,saboda sati mai zuwa nikeso ka tabbatar dani a matsayin Sarki Burhaan."ba Shamaki ba duk wanda ke fadar saida ya kalli Galadima Hamza cikeda mamaki."da yardar Allah zanyi iya kokarina kuma zan dauko komai ake bukata saidai dole saida zoben nan sannan zaka tabbata a Sarkin wannan Masarauta na dindin din."nafika sani kaidai kayi abinda na umurce ka"angama ranka shidade."daka kyauta ma kanka....zaka iya tafiya"nagode,Allah yakara girma da daukaka." ______________ "Barka da hutawa Abba"yauwa ya'ta,sannu da zuwa,taho wajen Abban ki mai kaunar ki."a hankali ta karaso kusa da mahaifin nata ta zauna"Abba na sakon ka ya same ni."hakane gimbiyar Sirika,dama ina san infada maki nan da sati biyu za'ayi wannan gasar shine nike san in fada maki ki shirya sosai yanda yaka mata ina son duk wanda yazo yasan cewa kece gimbiyar wannan Masarauta.sannan ina son kowa ya shaida ke cikakkiyar yar Sarkin Sirika ce wadda ta ansa sunan ta."shikenan ranka shidade zanyi iya yina kuma zaka yi farin ciki saidai ina fatan an gayyato yan Masarautar Burhaan nasan yarima Sadauki zai zo ko Abba."? "Ya'ta kenan an aika masu da takardar gayyata amman inasa ran zasu anshi gayyatar mu."Allah yasa Abbana."a hankali ya riko hannun ta yace."haba diyata mizai hana bazaki cire Sadauki a cikin zuciyar ki ba."da sauri ta mike tsaye tafara yan dire diren ta kamsr wata karamar yarinya tsabar shagwaba da sangarta"wayyo Abba nidai gaskia bazan iya hakuri da Sadauki ba kaima kasan shi nike son aure tun ba yau ba"ya isa naji,nasan bakisan cewa Sadauki yayi aure ba ko."? take numfashin gimbiya Rahama yafara sauyawa zuciyar ta tafara bugawa da sauri sa sauri batasan sadda ta fara kuka ba."haba Rahama ta,kukan me zakiyi hakan ba girman ki bane"ranka shidade kasan bazan iya zama da kishi ya ba."yanzun dai kitashi kije ki kwanta zuwa wani lokacin zan samo mana mafita kinji yar lelena"yanzun ranka shidade haka zaka zauna kana goyon bayan yarka akan abinda bazai yuyuwa ba kasan yarka ba aurenta yaron nan zaiyi ba saboda yagama samun wadda yake so yayi auren shi, daman fa bai san tanayi ba." "Karki kuskura ki kara fadar wa'annan mugayen kalaman ga ya'ta"daga nafada maka gaskia Allah yabaka hakuri "bani bukatar gaskiar ki bacemin daga ni kada ranki yai mugun baci gimbiya Sadiya"Allah ya huci zuciyar ka"aikin banza aikin wofi."tana fita ya riko Rahama yace."kiyi hakuri kinji muddin Sadauki yazo wajen gasar nan dakaina zan gaya masa irin son da kike mashi"yauwa Abba na ina alfahari da kai."yimin dariya."dariyar tayi masa yaci gaba da kara mata kwarin gwiwa wannan kenan..... _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA UKKU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.Shaidar biyanki ta wannan namba 08160508316. Dauke yake da kaya a hannun shi ya nufi sashen gimbiya Zubaina cikeda nutsuwa yake tafiya a kame kamar mai tausayin taka kasa,duk inda zai gifta idanun mutane a kansa musamamn yan uwansa bayi sai kallan shi sukeyi suna zaginsa wai ya cika wuce wuri da daukar kai komai sai ya nuna yafi kowa,alhalin shi din ba kowa bane duk abinda sukeyi Umar najin su amma bai nuna ya damu ba saboda yasan jin zafi sukeyi mashi dan ma Allah yasa ya hadu da Abba Ado yasan da sai yasha wahalar su, yana isa ya tsaya bakin turakar ta saidai ba kowa wajen wajen sashen Fadila ya nufa yai mata sallama sannan ta fito daga dakin ta....tayi mamakin ganin Umar saboda taga ya rabu sa zuwa akalla yakai sati biyu bai zo aikin shiba,gaishe ta yayi sannan yace yana bukatar tayi mashi iso zuwa wajen uwar dakinta.... shiga tayi ta taddata sama kujera zaune a dan makimancin dakin da take hutawa ta harde kafa daya sman daya cikin wata doguwar riga mai masifar kyau ga kyakkyawan gashin kanta kwance lif a saman gadon bayan ta koda Zubaina ta kalli Fadila take kauda kai batareda tace mata komai ba... dukawa tayi bisa guiwowin ta gaida gimbiya Zubaina saidai ko amsawa batayi ba ita kanta tarasa damuwar uwar gajiyar ta.....cikeda ladabi fada mata sakon Umar da sauri Zubaina ta kuma kallon ta fuskar ta cikeda alamar tambaya..... "Allah yataimaki uwar dakina,Umar kesan ganin ki yace ayi ma shi iso."kallan da Zubaina tayi mata kadai shi ya baiyana mata amsarta godiya tayi sannan ta fita bada jimawa ba saiga Umar yayi sallama,tunda ya shigo gimbiya Zubaina ta kafe Umar da manyan idanuwan ta masu firgitar da wanda ake kallo kanshi sadde a kasa harya karaso gabanta a hankali ya duka gaban ta cikeda girmamawa,bata daina kallan Umar ba,ta rasa dalilin dayasa take jin Umar din a ranta."Allah yaja da ran gimbiya ta, barka da hutawa ranki shidade,uwar dakina tafi ta kowa alkhairi ina fatan kina cikin aminci da walwala,Umar na kawo gaisuwa Allah yakara maki lafiya da nisan kwana."har yanzun kansa na sadde kasa. Sihirtacciyar ajiyar zuciya gimbiya Zubaina ta sauke yayin da sanyayyiyar ratsastsar muryar sa na yawo cikin kunnuwan ta amon sautin sa na yawo a sassan jikin ta a hankali ta ware idanun ta masu tsanamin haske ta kuma azawa saman kyakkyawar fuskar sa tana mamakin yanda akai yau Umar yai mata magana mai tsawo tkamar haka abinda bai taba yi mata ba tasan komai nasa a takaice yakeyin sa....tunda yayi maganar yake sauraron yaji amsar da uwar dakin sa zata bashi sai yaji tayi shiru a hankali ya dago kansa ya daura idanunsa akan fuskar gimbiya Zubaina kwana biyun da yayo bai ganta ba sai yaga ta rame masa duk da takara kyau da haske."Allah yasa uwar dakina tana lafiya."?ya tambaye ta cikeda kulawa,dan murmushi gefen baki ta saki wanda ba lallai ka gane tayi shiba muryarta a matukar sanyaye tace."Umar."sake kallan ta yayi yace."Allah yataimake ki."miyasa ka daina zuwa waje na."maida kanshi yayi kasa yace."tuba nikeyi uwar daki na ba daga gareni ba ne sako nw daga Mai martaba yace in dinga kula da Jarumai sannan ya haneni da kasancewa mai maki hidima ina fatan zakiyimin afuwa"waya fada maka wannan sakon."? "Allah yaja da ran gimbiyar Zairana Yarima Aryan ne"ajiyar zuciya ta fesar tace."Shikenan,Umar kaman ta nafada maka bana aan kana yimin nisa."Allah ya huci zuciyar ki,kasancewa ta bawa kaskantacce bai kamata ya kasance da gimbiyar da labarin ta ya karade illahirin Nahiyar nan ba kiyi hakuri hakan ba girman ki bane,kuma matsayina bai kai nan ba."Karka kuskura bakin ka yasake furta kalmar kaskanci agabana,kafi karfin kaskanci Umar,duk bawan da gimbiya Zubaina tasa da kanta a kawo shi zuwa gareta yafi karfin kaskantacce....badan kai ka furta wannan kalmar ba lallai da sai na datse harshen ka!ka kiyaye gaba Umar "Allah yataimakeki uwar gijiya ta,Umar na tuba" "ba laifi girman ka ne,ko kana da bukatar wani abu."? "Aaa,banda bukatar komai,fatan Umar akoda yaushe ki kasance cikin aminci." bakaramin dadi Zubaina tajiba harda murmushin ta,shima din murmushin yayi mata,shi kanshi saida yakara tabbatar da tsarin halitta irin ta gimbiya Zubaina. Shiru ne ya karade illahirin wajen na yan dakiku lafin yace"Allah yataimakeki sako ne daga gimbiya Zinatu tace in kawo maki."a hankali Zubaina ta ansa ta aje gefenta tana jin farin cikin ganin Umar."Allah yakara girma da daukaka zan koma bakin aiki na."mikewa yayi ya juya zai tafi."Umar."Wani kalan yanayi ya dirar mashi wanda ya kasa gane irin shi a hankali ya juyo da fuskar shi ya kawata ta da annuri"wane kalan aiki zakayi."? "uban gidana ya umurce ni zanje wajen Jarumai."kada in sake jin bakin ka ya ambaci kalmar uban gida ni kadai ce uwar dakin ka."zan kiyaye da izinin Allah."yauwa,zaka iya zuwa ka kula dasu kamar yanda Mai martaba ya bukata."Umurnin ki shine abin alfaharina,Allah yakara maki lafiya"girman ka ne Umar zaka iya tafiya"godiya nike."tafiya yayi gar yakai bakin kofa zai fita ta kuma kiran shi.....sake juyowa yayi ya kalleta"ga wannan kayi afani dasu wajen bukatun ka kuma bance kaiman musu ba."wannan ba karamin girmamawa bane agareni Allah yakara girma da daukaka."Amin."fita yayi inda yabar Fadila a nan ya isketa sallama yai mata sannan ya tafi. kiran gimbiya Zubaina ra tsinkaya da sauri ta shiga ta duka gabanta "Fadila ki hada man kayan da zan sa."angama ranki shidade." Ranar haka Zubaina ta wuni cikin farin ciki tagama yarda cewa Umar ya shiga cikin ranta tasaba dashi tana mamakin yanda tayi saurin sabo da shi."ranki shidade angama hadawa."sannu Fadila zauna." Zaman tayi tana jan Fadila da surutu kamar ba ita ba,itama Fadilar firar take mata saidai aranta tana zargin uwar dakin ta,na son Umar amma bata kaida tabbatar da zarginta akai ba,tasan muddin hakan ta kasance lallai uwar dakin ta zata shiga matsala a wajen mahaifin ta saboda duk yanda yake sonta bai yarda da wulakanci ba kuma shi bai da gwani...."Fadila hadaman ruwan wanka yau ina so zanje ziyara."angama ranki shiade." bada jimawa ba ta gama hada mata ruwan wanka."angama hadawa ranki shiade."tahi tayi ta shiga wanka. ★★★ Gimbiya Saratu dauke da wata katuwar kwarya,ta gama ware magungunan da suka gama hadama gimbiya Masa'uda itada bokanyarta kowa ne hadi da sukayi sun gama fada mata yanda zatayi anfani dashicikin wata katuwar leda ta saka shi. ita kanta tasan sun hadama su Hamza, mugun tuggu.dariya ta kece dashi ta kalli bokanyar ta tace."aikin ki na kyau yau din nan zan tada bawan da zakai man asirran nan,saina tarwatsa rayuwar mutanen cen,ymuddin Yalwa tayi anfani dasu yanda ya dace na tabbata Hamza bazai kara tasiri ba a Masarautar Burhaan ba."hakan yana da kyau."tasa baiwarta ta kiramata bawan da zata aika bada jimawa ba suka shigo ya gaishe da gimbiya Saratu sannan ta mika mashi leda"ka rike ledar nan da kyau kamar ranka!karka kuskura kaba kowa wannan sakon sai gimbiya Yalwa hannun ka hannun ta."angama ranki shidade."ga guzurin da zaka rike har ka isa,ka kara kiyaye wa."angama Allah yataimaki sarauniyar Yurii."gyada kai tayi sannan ya kama hanya. ___________ koda gimbiya Zubaina tagama shiryawa fitowa tayi itada da Fadila ba inda suka sauka sai sashen Yarima Ammar wajen Gimbiya Zinat suna shiga ta samu waje ta zuna,ita kuma Fadila ta gaishe da gimbiya Zinat sannan ta basu waje."Wannan irin kyau?kai autar Umma kinga yanda kika kara kyau?saidai kace wata sarauniyar kyau."hmmm Adda na kenan,kedai kina san ki yabeni kawai."dama nasan bazaki yarda ba amma da ace kin kalli madubi daya baki amsa."dama na gani kyau ba tareda kwalliya ba"?murmushi gimbiya Zinat tayi tace."kin san kyawawa ko ba kwalliya kyau sukeyi."shikenan naji nasan dole sai kinsa na yarda nagode da yabawa."Hmm naji dai."fira suka cigaba da yi."kinga har na manta dauko mani dambun nama na."Ayyah kanwata kiyi hakuri banyi zaton yau zaki zo ba,aida na ajemaki."tabb yau koda mijin ki yazo nan,bazan yarda ba sai kinyo mani"bata kai haka ba ai amma nan zaki wuni ko."? "Aa zanje wajen Umma." bari in tashi yanzun nan zan hadama tauraruwa ta abinda take so"Aa bazan wuni ba nacema Umma yau zanje wajen ta kuma nasan ni take jira dana tsaya, ki tabbata ina binki bashi."Shikenan,amma dai zaki jima wajen Umman ko."? "Eh zanjima"ba damuwa sai kin jini."yawwa Anty na nagode."rungume junan su sukayi sannan Zubaina ta fita zuwa wajen gimbiya Amina. Tana shiga sashen mahaifiyar ta,ta same ta zaune samana sallaya tana lazumi har kasa ta duka ta gaishe da Umman ta,itama Fadilar gaishe ta tayi cikeda girmamawa,har zata fita ta kirata tace." Fadila dauki abinci kici."nagode Allah yakara girma."dauka tayi tanajin dadi a ranta godiya tayi sannan ta tafi. "Ranki shidade barka da hutawa"yauwa Zubainatu kin fito."Eh,Umma daga gidan yaya Ammar nike"kin kyauta,zumunci abune mai kyau"Umma yaushe zamuje wajen Umma Rukayya."? Rike baki tayi alamun maganar tazo mata a bazata tace"Hmm Zubaina kenan,kema kinsan Abban ki bazai taba bari keyi mashi nisa ba"Umma ki tambayar mani shi"kirufaman asiri Zubaina! Ina ni ina turakar Mai martaba da wannan zancen? ina magana cewa zaiyi nike zugaki dan kidin ga yawo, duk yanda baki tunani Abban ki ya wuce da tunanin ki yanzun ya gama rudewa ni har tsoro yake bani,kwarama kije kisamu Hajia kila idan tafada mashi bazai yi musu ba,niko idan nayi magana zai iya kullata ta,tunda ba kaunar abinda zai rabeki yakeyi ba."Umma ba wani abu bane fa magana kawai zakiyi mashi..."kinga Zubaina bana son musu ina fata kin fahimce ni." "na fahimta."kin kyauta"shiru ya karade illahirin dakin Zubaina tace."Umma kina ganin Abba ya rabani da Umar wai baya son yai mani aiki"wani irin kallo ta aika mata kamar bataji taba tace."mi kenan."? "Umar mana gaskia ina son amaido mani bawana."Kedai bakijin magana Zubaina Umar din mi? so kikeyi kisa ubanki ya wulakanta ni ko? wato kedai Zubaina duk abinda iyayen ki keso ba shi kike so ba ko? miya hada ki da hadimi namiji?Dan takamar ke kikasa a sawo shi sai me?kefa da bakinki kika ce baki son namiji a kusa dake,duk kin tsane su har gadara da ikirari kikeyi kina cewa mijinki na nan zuwa ko kunyr iyayen ki bakiji sai yanzun?zaki zo kina maganar Umar?wai amaida maki shi a matsayin hidimin walahi Zubaina ki kiyayeni,ni bana ciki da sakarcin ki!" "Kiyi hakuri Umma,badan komai yasa nike son sa ba saidan Jarumtar sh"kada in sakejin wannan bakin naki ya furta kalmar Umar a matsayin hadimin ki idan ba kuma jin haka saina fasa maki baki!koni uwarki ban isa ubanki ya bada umurni in bijire masa ba ballan tana ke da bai wuce akarya ki ba."idanuwan gimbiya Zubaina har sun sauya launi"Umma ki fahimce ni ban..."zan wanke ki da mari kika kuma magana yanda ba kowa wajen nan zan zaneki sai kin rasa mai cetonki sakarai shashasha ana nuna maki gaskia kina bijirewa ki kara cewa uffan kigani yanzun jikin ki zai gaya maki."hawaye suka fara sauka saman kuncin ta.sai fada Gimbiya Amina keyi. Ammar keyi tayi masu Sallama amma basu jishi ba yanda yaga mahaifiyar su na fada hakan yasa ya karaso da sauri yasan halinta bata iya fushi ba tana iya lakada mata duka kamar yanda ta fada dama tana jin haushinta duk abinda zatayi sai Mai martaba ya dinga ganin laifinta duk abinda zata aikata sai yakare kanta yace ita ke sata"dan Allah kiyi hakuri Umma"kyaleni da yarinyar nan,dagani jikinta ya rabu da zafi shiyasa,kuma ai uban naku shine ya sangartata bai san yaga ana mata fada idan bashi kadai ba idan kuma tayi laifinta sai yakare kaina sai kace wata marar 'yanci."Allah huci zuciyar ki Umma kidaina fadan nan."_dole nayi fada Ammar,ke kuma kikara yiman maganar kina son amai da maki Umar matsayin hadimin ki,walahi koda zanyi dana sani saina maki dukan mutuwa,shashasha dake"Umma,dan Allah kada ranki ya baci nasan daga nan ma tabar maganar baki daya."kaifa ke cimata albasa Ammar."sai kuka takeyi ba abinda ta tsana a duniya irin fada,hakuri Ammar yaita bata"Umma kiyi hakuri,bansan ranki zai baci ba"taya zaki sani tunda ba hankali ya wadace ki ba."Ammar yai taba Umman su hakuri sannan tayi suna cikin zaman kuramen da suka tsunduma sai ga yar aiken gimbiya Zinat ta shigo ta kawo ma gimbiya Zubaina dambun naman ta izinin tafiya akai mata sannan ta tafi. Dishes din Umma ta bude sannan ta samu faranti karami ta zuba mata ta mika mata saboda tasan halin gimbiya Zubaina duk yanda takai ga san abu matukar akai mata fada ko ranta ya baci bazata ci abun ba wannan dalilin na daya daga cikin dalilin da yasa Sarki Abdurrahman bai san yaga 'yarsa na fushi"Maida hankali ki cinye shi duka"na koshi."harara ta wurga mata cikeda tsare fuska tace."ba neman ba'asi na tambaye ki umurtar ki nayi."ba shiri ta fara cin naman tana ajiyar zuciya Yarima Ammar keba kanwar ta shi hakuri harta dan saki jikinta saboda Zubaina na mugun shakkar gimbiya Amina tunda ta fahimci kalar son da mahaifin ta ke mata shiysa ita kuma bata mata da sauki musamman idan tana wulakancin ta saboda bata son ta kara sangarcewa.... Maganar mai martaba suka tsinkaya yana shigowa baki dayan su suke gaishe shi saman wani babban kafat ya zauna wanda yake dauke da kilissai kala kala bayan ya zauna gimbiya Amina ta dauko katon tire dauke da kayan marmari iri iri ta aje mashi sannan ta aje mashi kwaryar dafaffiyar madara"barka da rana ranka shidade"yauwa gimbiyata ya fama da jama'a."Alhamdulillah."shiru ya dan biyo baya ya gyara zaman shi ya maida dubans ga Zunbaina dake ta faman fushi yace."Mama na ya zaki tisa abinci a gaba kina yaguna idan baiyi miki ba ki aje mana."kamar jira takeyi ta ture flat din gefen ra."Jiya nasa Jakadiya ta kawo mani su Hussain akace sunyi bacci."Allah ya taimake ka,basu jin magana da sungama wasa sai suyi bacci da wuri"ai haka yara suke saidai addu'a,kaga sai su tayani fadanci....Allah yaimasu albarka "Amin." "Mamana wai mike damun ki naga duk yanayin ki ya canza"? "bakomai Abba."nafi kowa sanin farin cikin ki,masto kusa dani, fadaman minene da muwarki."? " kaina ke ciwo"saidai baki saba karya ba Zubaina." (yanzun idan nafadama Abba akan Umar ne Umma tayimani fada mizai faru?nasan ba ita kadai ba hatta ni sai raina yai mugun baci zaice na raina shi ban girmama umurnin shi ba.)"Mamana tunanin mi kike."? Murmushi ta dan kakaro tace"daman ina san kaiman izini zan kaima Umma Rukayya ziyara."har yakai tuffa bakinsa kenan ya aje,sannan ya kalli Zubaina saidai kalla mamaki yake mata...."kinsan me kike fada?ni ne zanbarki kiyi tafiya mai nisa har zuwa Kasae Cameron? lallai kam kema kinsan hakan ba mai yuyuwa bane bazan iya bari kiyi irin wannan doguwar tafiyar ba,koda aure yakai ki can saidai dan ba yanda zanyi ne"Abba kwana daya da yini mun isa kuma saika hadani da bayin da zasu rakani"Mamana kenan kinsan me kike fada kuwa?ni Abdurrahman zan hadaki da bayi kawai dan zaki kaii ziyara? Kuma ba muharramki ba, naji zan hadaki da bayin dawa yakama ta kuyi tafiyar."? Ya karashe maganar yana mata murmushi. Ammar ya kalli Umman su cike da mamaki yaga Mai martaba zaima Zubaina rijiya.cikeda zumudi tace"Abba,saika hadani da uma....kallan kinsan sauran umman ta ta aika mata da sauri ta sadda kanta kasa cikin sanyin murya tace"wa'anda kaga sun dace Abba."haba gimbiya Amina bai kamata kidinga yimata hannunka mai sanda ba,kibarta ta fadi ra'ayin kanta." "ki ida fadar abinda kikayi niya kinji ya'ta ko kina nufin bawan nan Umar."? "Allah yataimake ka bakina yayi ya kadan ya furta sunan Umar agaban ka bayan kace baka son ko a hidima na ya kasance taya zance shi" gyada kansa yayi cikeda gamsuwa yace."kin kyauta ma kanki Mamana.....sannan ni bazan barki kitafi wajen Rukayya ba, saboda tafiyar tayi mani nisa kuma bana san kina nisa."toh Abba." kada kidin ga jin haushin mahaifin ki da gangan kinji har yanzun baki tambayata abinda ya dace dake ne shiyasa, ni kuma duk abinda kike so zan maki amma fa sai abinda yake dai dai dake idan naga zai cutar da rayuwar ki lallai bazan taba yimaki shiba ki tambayi mahaifin ki duk abunda kike so ni kuma zan maki shi "toh Abba nagode Allah yakara girma"Amin mamana tafi ta kowa."Murmushi tayi. "Ina fatan gwajin da ake bayarwa yanayin yanda ake so ko."? "Eh,ranka shidade."Allah yataimaka." Sadaukin Burhaan na kudi tuntubi wannan number 08160508316.domin karin bayani. Koda Talatu ta dawo wajen bokanta wani irin magani taba gimbiya Masa'uda kasakasa take mata bayanin shi da yanda za'ayi anfani dashi ba karamin dadi taji ba ganin yanda aikinta ya fara kyau."angaishe ki Talatu ina alfahari da ke,kice yanzun Hamza zaizo hannu."kwarai kuwa sai yanda kike so da kowa."nagode maki." _Kowane irin aiki ne boka yaba gimbiya Masa'uda....muje zuwa muga yanda zata kaya👀_ Bakaramar ukuba Turaki ke shaba kullun da kalar walahar da yake sha baida wani galihu a cikin Masarautar kamar bai akowa. Abdullahi yazo wajen mahaifiyar shi yakawo mata karar Hamza."yanzun dai kayi hakuri Abdullahi kaga dan uwan ka ne shi."Haba Goggo akan mi zan kyale shi duk ya mallake komai ya hana kowa sakat ga rashin tausayin da yake nunawa ga bayin sa kuma yasama matata ta kunkunmi ya hanata sakat haba Goggo."gimbiya Saude tace."ka bari zanyi ma Hamzan magana sannan maganar matar ka da kakeyi ka manta da wannan zancen tunda ma matarka da danka basu da wani anfani agaremu."haba goggo bai dace kice haka ba." suna cikin magana sukajiyo kakarin da Turaki keyi kamar zai mutu da sauri Abdullahi yata shi da gudunsa ya nufi dakin da aka rufe shi amma mahaifiyar shi ta hana shi mabudin dakin, yanajin danshi na neman taimako amma taki bude mashi daki,saida taga dama sannan ta bude dakin yana shiga wani irin wari da tsami ya daki hancin shi,da sauri ya dauko dansa zuciyar shi ba harbawa yanda yaga wulakancin da ake masa har saida yayi kuka tsabar tausayin sa daya kama shi jikinsa na rawa ya dauki ruwa yaba shi yasha,Goggo tace."idan kagama tausayin nasa saika maida shi ko."? "Bazan maida shi ba Goggo bayan da za'ayi inaji ina gani aka she mani da'na."bazaki abinda nike fada maka."kiyi hakuri bazan iya ba."da taga yafi karfin ta saita kyale shi. bayi yasa suka dauki Turaki aka kai mashi shi sashen shi duk ya gama fita hayyacin shi..... Bamda bala'i ba abinda takeyi tana cewa."saina tsine maka Abdullahi matukar baka maido Turaki ba saboda banga anfanin shi ba..... ____________ Tafeedah ne ya tsaye gaban mahifiyar shi ya gama shirin sai zai tagi damagaram zai gaishe da Umman Shattimah saboda yasan tana kewar danta,yana gama shiryawa ba inda suka wuce sai wajen dawakai ta rike mashi sirdi ya hau sannan yai mata sallama tayi masa addu'a sannan ya kama hanyar tafiya damagaram..... A sashen gimbiya Rahama kuwa zuwa yanzun ba abinda takeyi sai kuka kmar ranta zai fita daga gangar jikinta daga taji Sadauki yayi aure kuma ita tasama ranta bazata auren mai mata ba,shiyasa ta daga hankalin ta bata da aiki sai kuka ga tsananin son Sadauki ya rufe mata ido soyayar da bai san tanayin ta ba ga tsananin kishi ta saka a ranta wai bata iya zama da kishiya. Ba irin bakin da mahaifiyar ta bata bata ba amman a banza ba abinda ya sauya sai lma karuwa da kukan keyi ita janta gimbiya Karima harta sa mata ido sannan zuciyar ta na cikeda tausayin yarta.... itako Safiyya duniya tayi mata tofin Allahi tsinw komai ya rude mata bata samun sukuni ga kowa sai wajen mahaifiyar ta duk rame kullun sai mahaifin ta yai mata gorin akan ta haifi ya' mace ba wani sauyi ya tsaneta ita da yar ta, ga bai kaunar diyar ta ko miskali zarratin kullin cikin zullumi taje duk tabi ta lalace kamar ba ita ba tsoron ta daya kada mahaifin yasa aka kashe mata 'ya tasan zai aika,shiyasa bata samun cikakkiyar nutsuwa. ________ Umar ga fura ka tashi kasha kada yunwa tayi maka illah"toh Abbana walahi duk na gaji shiyasa."Allah Sarki Umarul-faruq kayi hakuri, wata rana sai labari kaji."toh Abba na."zama yayi yafara shan furar."Yau saura kwana bakwai muje wajen gasar nan"aje ludayin hannun sa yayi yace."ashe har lokaci yayi gaskia ni bana san zuwa."Haba Umaru ba saboda me."? "Saboda mutane bana son su"Murmushi Abba Ado yayi yace."Umar kenan, ai mutane rahama ne"hakane bana son ina ganin su dayawa."Hmm zaka saba kaji."to Abba." _Yau Sadauki ke fadan baisan shiga cikin mutane Allah karaba mu daga sharrin sihirin Amin🙏_ Kwatan tama Umar ya dinga yi har saida ya daura shi saman hanya, amma sannan ya aminta zaije,aran shi yana mamakin halayen Umar shidai har yanzun yana son yasan asalin Umar dan de ya fahimci baisan maganar tunda har yanzun baisan me zaice ba game da kanshi. saidai a wani sashen na zuciyar shi gani yakeyi anya Umar bai cikin turbar sihiri? antaba mutun da girman shi yace baisan waye shi ba? da iyayen sa!gaskia dole ya tashi tsaye kodan yasamama Umar magani dan yanaji a ranshi akwai babban al'mari atare dashi...... *Banda VTU idan kati ne kiyi snap din shi sai kituro mani ta namba ta dana bada MTN kadai* _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA HUƊU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shedar biyanki ta wannan layin 08160508316. Bana son VTU kituro credit ta hanyar numbar dana bada sama. _MASARAUTAR SIRIKA_ Bayi da sauran hadimai keta aiki cikin masarautar ba abinda suke kokarin yi sai sai gyara sukeyi ko ina na cikin Sirika....yau yakama saura kwana ukku afara gabatar da gaggarumar gasa wadda ta karade illahirin kasa baki daya harda makwabtan ta da wasu sassa na Africa baki daya. uban bayi ne keta rabama bayi yan uwansa aiki kowa ya zakade yana aiki kamar ba gobe A cikin dakuna da aka tanada dan bawa bakin da zasu zo suma uwar bayi da sauran hadimai mata sun bazama sai gyara sukema dakuna nan abin dai ba'a cewa komai,hidima akeyi cikin Masarautar ta Sirika ba dare ba rana kamar anayin wani gaggarumin biki haka ake hidima. Sarkin yaki ne wajen Sarkin dawakai inda yasa hadimai suka gama gyara wajen dawakan sannan suka ware ingantattu kuma nagartattun dawakan da za'a gabatar da gasa dasu yayin da Jaruman Masarautar keta karbar gwaji kamar ba gobe burin kowace Masarautar ta lashe gasa kowa so yake ya zama zakaran gwajin dafi. Sarkin yaki na gamam basu gwaji aka ware mutun goma sha biyar ya tantace wa'anda suka amsa sunan cikin jerin manyan Jaruman Sirika sune zasu wakilci masarautar su a gasar. Koda Sarkin gida ya tabbatar da angama gyara komai yanda ya kamata sanarma dogarin Sarki Abdullatib yayi bayan Mai martaba ya tashi daga Fa'da suka biyo wajen domin yin rangadi ko ina ya gama gyaruwa an shirya shi musamman masaukin baki wani irin katafaran waje mai dauke da ɗakuna bila adadin wa'anda suka gaji da kayan alfarma da alatu a cikin na more rayuwae yau da gobe an wadata ko wane daki da shimfidu gwanin burgewa ga bayi a jibge wa'anda zasu dinga kula da wajen da duk abinda ke cikin sashen ana bashi kulawa ta musamman saboda komai na Masarautar sun gama tsara shi sannan kowa yasa aikin shi, Sarki Abdullatib na gama rangadi shida jama'ar suka raka shi zuwa Turakar shi. Washe gari da safe da kisalin karfe goma Sarki Abdullatib ya hada gaggarumin zama na gaggawa a fadar sa sannan ya bukaci Sarkin yaki da uban bayi su halarci taron kafin wani lokaci fa'da ta cika dankam da dan adama kowa ya samu sakon Mai martana bayan kowa ya hallara Sarki Abdullatib ya shigo tareda Wazirinsa sai kuma Shamaki suna isowa kowa ya mike tsaye fadawa suka rufe Sarki da manya rigunan su ya zauna kowa ya kai gaisuwa ga Sarki sannan suka zauna."gyara zaki gyara ginzi Allah yataimaki Sarkin Sarakai angaishe da Sarki mai adalci Sarkin Sirika Allah yataimaki mahaifi g Gimbiya Rahama gaba salama baya salama."Sarkin zagi keda koda Sarki a hankali ya daga mashi hannun alamun yai shiru,gyaran murya Sarki yayi cikeda kamala yace"godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da yasake hadamu a wannan waje,kamar yanda muka sani munje munyi taro da manyan Sarakuna an tsaida za'ayi babbar gasa a Masarautar Kesar amma duba da yanayin nisan da mukayi da sauran Masarauti da kuma kaunar zumuntar da muke so takara karfi a tsakanina da yan uwana Sarakuna wannan dalilin yasa na nemi alfarma aka maido babban gasar da aka kwashe shekaru masu yawa a hadata sai gashi ankawo ta cikin wannan Masarautar ta mu ta Sirika mai tarin albarka,lallai kam wannan ba karamin alfahari bane agaremu....saboda haka nike san inkara jan hankulan ku kukara zama masu mutunta jama'a da kimanta su kodan daukaka darjar Masarautar mu,sannan mukasance masu aminci da karamci ga bakin mu,ina kara nusatar daku akan misali dana jima ina baku kuma bazan fasa bada misali da mutanan Burhaan ba Masarauta ce babba mai dinbin tarihi a kasar hausa duk irin girma da tarin dukiyar da suke gadara da ita basu fasa taimako ga al'umma ba da jajircewa dan ganin sun gina al'umma ba, ina san ran zamu koyi dasu koma fiye dasu Sarkin su Sarki ne mai adalci,ina fatan zaku fuskanci sakona sannan ina san Sarkin yaki da sauran Jarumai da ku dage damtse wajen ganin kunyi kafada da kafada da jaruman Burhaan wanda muke ganin a duniyar mayaka da Jarumta ta gidan sarauta har yanzun basu da tsara...sannan ina kira da uban bayi da ka maida hankali ga bayin masautar nan wajen gani sun bada himma ga yin da'a ,mutuntawa da karrama bakin mu, su zam masu nuna kara,saboda kowa zai yaba akan kokarin ku koda sun koma gidajen su kuma a isarmin da sakona ga uwar bayi takara kulawa da bayi mata....Daga karshe ina kara jan kunne ga Jaruman mu su kasance masu kishin zuci sannan ku kasance masu nuna kara ga sauran abokan ku Jarumai tunda ku aka iske,ina fatan Allah yabamu nasara mai daurewa."Amin,Allah yataimakeka muna rokon Allah yabamu tsawan rai da lafiya mai anfani"Amin zaku iya tafiya daman wannan shine maka sudin hada wannan muhimmin zaman yakamata ku kara daukar shi da mahimmanci." _____________ Sarki Abdulbaseet Abdulkareem zaune a saman karagar mulki anata fadanci amman baki daya hankalin shi na wajen Sadauki yana tunanin shirun da yaji tayi yawa danko a ranar ya tada dan aike da wasika zuwa Masarautar Burhaan ana cikin fa'da saiga dan aike daga masarautar Sirika an aiko mashi takarda,ana kawowa maga takarda ya amsa bayan izini da Sarki yai mashi.... "dan samari daga ina."?magatakarda ya tambaye shi sadda kansa yayi ya dan rankwafa cikeda girmamawa yace."Daga kasar Sirika nike sakone mai mahimmanci zuwa ga wannan Masarautar mai albarka."magatakarda gareka."cewar Sarki AbduAbdulbasit. Budewa yayi yafara karanta ta kamar haka _Assalamu alaikum_ ```Amincin Allah yatabba a cikin wannan Masarautar ta Roowan mai dinbin tarihi daga masarautar Sirika ina fatan sakona ya isa zuwa ga uban kowa Sarki Abdulbasit Abdulkarim muna mika sakon gayyata agareka kai da jama'arka zuwa gasar da za'a gabatar a cikin masarauta taa ranar sha biyar ga watan jumada akhir,dafatan zaku amshi sakon gayyatarmu daga Sarki Abdullatib Muhammad Sirika, bissalam ``` Allah yataimakeka kaji abinda ke ciki"Gyaran murya ya danyi cikeda kamala yace."shikenan duk da kasancewar kunsan halin da nike ciki, a halin yanzun bana jin zan iya zuwa wata gayyata kamar yanda mukasani a ranar nake shirin zuwa kasar Burhaan domin jin halin da iyalina suke ciki duk da kasancewar na tura masu da dan aike kuma zamuyi tafiyar ne da Jarumai na,bacin haka da naturasu dan su wakilci wannan Masarautar tamu mai albarka, a matsayina na uban ga Sarakuna bai kamata ace ban samu damar zuwa ba."Allah yaja da kwanan ka ai sahun giwa ya doke na rakumi."hakane shamaki,amman nasan yanda za'ayi zuwa gobe insha Allahu."Allah ya nuna lokacin lafiya,Allah yataimaki Sarki mai adalci."Sarkin gida kaba bakon mu masauki mai kyau da tsari? "Allah yataimakeka anbashi harda wa'anda zasu bashi kulawa kafin zuwa ya wuce"aikinka na kyau sarkin gida"godiya nikeyi Allah yakara maka lafiya da nisan kwana."Amin Sarkin gida Sarki ya amsa."cewar Sarkin zagi...... Sadauki na kudi akan naira 300 rak tafiyar ta musamman ce. Halimatu ta ruga da gudun ta,ta ɗane saman mahaifin ta."sannu da zuwa Abba."yawwa autar Abba."tunda Halimatu tayi ihun murna yan gidan baki daya kowa ya fito da sauri su jamil da Kamal suka rungume shi sai murnar ganin mahaifin su sukeyi, suna cikin jin dadin su sai ga Hajia Mansura ta fito hannun ra dauke Ahmad tana mashi wasa tana ganin mijinta cikeda farin ciki ta rungume shi baki dayan su suka ta zauna sai murna sukeyi fira suka soma kowa na tambayar shi hanya."gimbiyata ina muka samu kyakkyawan yaro haka masha Allah."Murmushi ta sakar masa tace."Jikan ka ne." mamaki kwance a saman fuskar shi yasa hannu ya amshi yana mashi sahihin kallo dke tuna mashi da wani abu ko mai son tantance wani abu."duk inda wannan yaron yafito jinin Muhammadu ne"Murmushi ta kuma sake mashi tace"kwarai kuwa dan shi."jini ba wasa kamar yaron da ubansa harta baci kice sun kawo mana ziyara?mine sunan shi."Allah sarki haka dama kama ta gaji haka ai sunan aminin nashi yasan ya."Ahmad ko Mukhtar."Ahmad."cewar Halimatu."Allah ya raya mana."Amin."ina Asma'un."? Ya kuma tambaya yana daura Ahmad saman jikin shi yana mashi wasa."tana fitowa"Allah sarki ya'ta baiwar Allah Asma'u badai hakuri ba"gaskia kam."fira yakeyi da iyalin shi gwanin birgewa....sallamar Shattimah suka tsinkaya baki dayan su suka maida kallan su gare shi yana ganin mahaifin shi cikeda farin ciki yazo ya rungume shi murnar sukeyi tsabar farin ciki dama sunjima basu hadu ba"inata kewarka Ahmad miyasa kayi mani nisa."?a hankali suka saki juna sannan Shattimah ya zauna gefen kafar mahaifin shi yace "nima nayi kewar ka Abbana kana raina kullin kawai dai abubuwa ne suka cakude mana sakdai yanzun komai ya daidai ta da iznin Allah"jibi yanda ka koma daganin ka kana cikin damuwa."bakomai Abba."badan ya yarda ba ya kyale dan nashi Koda Asma'u ta fito kasa ta zauna ta gaida shi cikeda ladabi sannan tayi mashi barka da hanya"yawwa ya'ta sannu nayi farin cikin ganin ku naji dadin zuwan ku sosai,Allah yaimaki albarka."Amin Abba sannu da hanya"yauwa ya'ta."fira yaransa kowa ke mashi musamman abubuwan da suka faru da baya gida saboda mahaifin su fataki ne bai zama dan kasuwa ne sun jima suna fira cikin tsantsar shakuwa da junan su daga bisa ya mikama Jamil Ahmad, yata shi suka shiga daki shida matar shi dan ya samu shirya kafin ya fito suci abinci. "Nikam ya lanarin Tafeedah."? Cewar Kamal."murmushi Shattimah yayi yace."kullun yana raina amma nasan zaizo nan saidai kafin nan inaso intura mashi da sako."Allah yakaimu nayi kewar Ya Mukhtar."hmm ina ruwan Tafidah."haka suka zauna kowa da abokin labarin shi kana ganin su kasan basu cikin damuwa bansa Asma'u data zurfafa cikin tunanin mijin ta ba karamin kewar shi tayi ba tana ayyanawa a ranta ko wane hali yake ciki? ji take kamar tayi kuka musamman idan ta tuna halin dasu Ammi ke ciki haka Mai martaba ko ya warke wani sashen na zuciyar na ayyana mata kodai ya rasu basu sani ba,hawayen da suka ziraro mata tayi saurin gogewa batareda ta bari kowa ya gani ba musamman Shattimah bai so yaga tana tunani..... Ki hanzarta ki mallaki naki kada ayi babu ke Sadaukin Burhaan kenan. Yauma kamar kullin Umar suna filin gwaji inda Jaruman su keta ansar gwaji na musamman sai faman sukuwa sukeyi da dawakai wasu na wasan takubba yayin da wsu ke tsere ba kadan suke bada gwaji ba,zuwa yanzun duk abinda sukeyi Umar yagama haddacewa kaf cikin kwakwalwar shi dan dai shi bai taba gwaji ba saidai ya kalla idan sunayi yana gani har suka gama komai suna gamawa ya kwashe kayan aikin yakai ma'ajiya sannan ya kama hanyarsa ta zuwa gida akan hanyar tafiya gida ne ya hadu da Laminu babban bawa ne da shi akaje aka siyo Umar ko da Sadauki ya ganshi saida ya shaida shi har kasa ya gaishe shi saboda Laminu na saman Sadauki. Kamar jira ya hau Sadauki da zagi."naji ance dakai za'a tafi Sirika walahi sai nayi maganin ka harka isa aje dakai wannan gasar komu da da muka dade cikin Masarautar nan da kyal aka zaba damu sai kai."? Shiru Sadauki yai mashi sai aikin kallan sa yakeyi kara kulewa Laminu yayi yace." sannan kuma naji ance kai ne zaka jagoranci masu kula da jarumai ko."?gyada kansa Sadauki yayi batareda yace komai ba.."walahi sanaui maganin ka dan na fahimci kowa kai yake so harda yarima Ammar kai yake so ko."?wannan karon Umar ya daina mamakin Laminu kuma bai fasa kallan sa ba da ido kawai ya bishi baice uffan ba har yagama maganganin shi ya tafi cikeda tsanar Umar aran shi. shidai Sadauki yana mamakin yanda wasu mutanan basu da hankali yanda yaga Laminu na tada jijiyoyin wuya duk akan aikin wahalar har wani abun bata rai ne da hassada abinda bai sani inda akwai yanda zaiyi daya yace bai zuwa shine yake bala'i dan karamin tsaki yaja ya tafi. Sadaukin Burhaan na kudine kibiya ayi tafiyar nan dake ba algush a cikin wannan tafiyar nasan zakiji dadin sa siyen nagari maida kudi gida. Jameey❣️ *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA BIYAR Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shidar biyan ki ta wannan layin 08160508316. "Allah yataimaki gimbiyar Zairana,zuciyata bazata taba samun nutsuwa ba idan ina ganin ki cikin damuwa bana samun sukuni a raina,kiyi hakuri uwar dakina banajin dadi kullun idan ina ganin bacin ranki"cewae Fadila ta karasa maganar tana sadda kanta kasa yayin da take ci gaba da dannawa uwar gijiyar ta kafafun ta a hankali."dole in shiga damuwa Fadila inajin daci raina duk abin da nikeso mahaifina bai mani shi,yanzun fa so nikeyi yabarni in tafi wajen Umma Rukayya ya hanani ga shi ya rabani da Umar ya zanyi da raina!"cikeda da tausayawa Fadila tayi kasa da muryarta cikim sanyi murya tace."Allah ya huci zuciyar ki,kidaina bata ranki akan wannan abun ina da yakini idan aka dawo daga gasa zai maido maki Umar l,nima kaina ina san in dinga ganki cikin farin ciki da walwala."ɗago jajayen idanuwan ta tayi da suka sauya launi tace."Fadila mi kika fahimta a tsakanina da Umar."? Bakaramin faduwar gaba ya riski Fadila ba har saida ta dan dafe kirji sannan ta sadda kanta kasa da sauri zuciyar ta na halbawa da sauri da sauri shiru tayi ta zurma cikin tunani( wannan amsar a bayyane take,uwar ɗakina ta afka tarkon son Umar!saidai bakina yayi kadan ya furta wannan kalamar kamar gimbiya Zubaina ta afka son BAWA saidai na fahinci har yanzun bata fahimci son sa take ba saboda tarin kuruciya irin tata sa wauta,natabbata idan wannan maganar ta fita daga bakina tabbas sai Sarki Abdurrahan yasa an sokeni lallai kam bazaki taba jin mutuwar Sarki a bakina ba dama.ance bakin wawa akejin zance)ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta dago idanunta ta aza akan Zubaina har yanzun ita take kallo alamun ansarta take bukata."Allah yakara maki lafiya da nisan kwana,ba wani abu ke tsakanin ki da Umar ba, sai tarin tausayin da kuma tarin kwarjinin shi da haibar shi su suka taru a cikin ranki zuciyar data shagala da yawan bege da dinbin tausayin Umar a koda yaushe."itama ajiyar zuciyar ta fesar tace."hakane Fadila ban da tausayi mi gimbiya Zubaina zatayi da BAWA? duk da wani lokacin raina na rayamani kamar zuciya tayi nisa a cikin kaunar Umar saidai kullun sai na karyata kaina,musamman ma yau da kika kara tabbatar man da taysayin shi nikeyi kuma na kara gasgata hakan"Allah yataimakeki uwar gijiya ta lallai dole ayima Umar san barka da Allah yasa shi a cikin ranki a matsayin shi bawanki wan da yafi kowa daraja a wajen ki"Fadila kenan, ke ke yima Umar kallan BAWa,zuwa yanzun ina kallan Umar kamar ɗan uwana yafi karfin bawa a wajena....lallai kam!narasa dalilin dayasa Umar yasamu masauki mai dinbin daraja a wajena,ace kamar ni gimbiyar Zairana na damu da Umar abin takaicin bawa ne shifa?wannan shine abinda ban taba yima wani ɗa namiji ba a rayuwata ta duniya"wannan haka yake ranki shidade amma karki damu in Allah ya yarda Umar zai dawo a karkashin ikon ki, a karo na biyu"Allah yasa Fadila."Amin."inasan ki shirya yau zan kaima Hajia ziyara sannan ina son zan kewaya lambu dan in mike kafafuna."angama ranki shidade,Allah yataimaki gimbiyarZairana." ________________ "Ku shiga ku fiddo mani shi!har ya isa in saka doka ya karyaman ita a matsayina na Sarkin Burhaan."baki daya dogarawan suka afka cikin sashen waziri Abdullahi da sauri gimbiya Sa'adatu ta shiga tsakanin su da ɗanta tana kuka tana basu hakuri amma saboda rashin imani irin na hamza sawa yayi akai wurgi da ita,Turaki yana ji yana gani mahaifiyar sa ta buge kai da bango jini na zuba,baki daga kattin Allah ta'ala sun kama shi kam....karar da gimbiya Sa'adatu ta saki ce yasa Abdullahi fitowa da gudu tun daga turakar sa yayi wajen iyalinsa daga shi sai doguwar jallabiya fara, tsaye yayi tsabar mamaki da al'ajabi yanama Hamza kallan mamaki,sai lokacin yayi kan matar shi ya dagata yakira baiwarta takaita cikin daki,dan ta bata kulawa..... "kai kuna da hankali zaku kama mani ɗa?ku sakarmin da'na."baki dayan su sukayi shiru suna gudun kada su sake shi su fada cikin tarko da kalar zaluncin irin Hamza,koba komai sun san Abdullahi yafi shi saukin hali"Bakuji abinda nace maku ba ku sakarman da'na tun kafin dare yai maku."koda suka ga Hamza baiyi magana ba sai suka sake shi,yayin da ya watsa masu wata irin matsiyaciyar hararar da yasa suka sake kama Turaki,sannan yai masu nuni da ido suka fita da shi. Abdullahi na kawo karfi zai riko Turaki,yasa Darwami ya rike shi zagaye Abdullahi yafara cikin kaskanci yace."Haba ɗan kanina mi kake kokarin yi haka?hmm na fahimci baka san wasa da wuta ba dadi ba! akan d'anka kake tada jijiyoyin wuya? ashe kasan dadin sa?hmm Garkuwan Burhaan kenan,ka saurareni da kunnen basira walahi tallahi koda Barde ne ya juyaman baya abun da zansa ayi masa kenan koma fiye da haka,amma shine kaje da kafafunka ka kwance shi ko?kaima ga ɗa,kai kasan baccin darajar muna ciki daya da kai kayi kadan Hamza yasa doka ka karya man?" a fusace yayi maganar."Damuwar ka ce Hamza baka isa ka kashemin da'na ba duk abinda zakayi nayi maka kawaici amma baka gani kalli yanda kamaida mani ɗa kamar marar galihu ba wani cikakken karfi a tare dashi duk yabi ya lalace,kai kasan ni bazan iya yima ya'yanka haka ba,kamanta duk tashi fadin da a kadinga yi akan Barde dani akeyi shi amma abanza yanzun ni zakaima haka?da'na tilo tal so kake in rasa shi kenan?duk wulakanta iyalina da zanyi ina son su!kuma dakasa akayi jifa da matata har kanta ya fashe kaji tsoron Allah Hamza,ina kaunar ta a haka walahi na gaya maki kayi gaggawar dawoman da da'na tunkan makiya suyi mamu dariya a cikin Masarautar nan."Hahhahh,Abdullahi kena lallai kam kayi kyan kai hmm kajini da kyau ni bazan iya wannan sakarcin ba ina magana kana yiba a gaban kaskantattun mutane,idan hakan ya dameka kasa meni sashe na."yasa kai ya fita shiko Abdullahi ya daukar ma ransa akan ɗansa saidai kowa ya rasa ransa,dan bazai iya jurar wulakan ta ɗansa da akeyi ba,shida man tuni ya sare da lamarin dan uwan shi yaaa azzalumi ne kansa kawai yasani...... koda ta shiga sashen shi bata iske kowa ba wani bakin magani ne ta ciro a zanin ta ta zuba cikin furar Hamza ta motse ta sannan tabi ta hanyar baya ta fita ba wanda ya ganta,bayan ta fita bada jimawa ba ya dawo duk ransa a bace,ace war shi dan uwan shi yaimashi rashin kunya akan ɗansa yana zama sabuwar Jakadiyar daya dauka ta shigo ta bashi furar shi bayan ta fita har zai sha sai ya aje ya sake fita a har zuke ya nufi sashen Umman shi, yafada mata abun da Abdullahi yai mashi har dare baidawo ba hakan yasa Jakadiya ta dauki kwaryar fura taba wasu bayi tace su shanye gudun kar tayi tsami,tunda gimbiya Masau'da ta koma sashen take murna dan dama bokanta yace da Hamza yasha furar take zai mutu amman har kusan mangariba shiru ba wani labari har akai sallar isha'i hakan yasa ta shirya da kanta ta tafi sashen gimbiya Saude dan tasan zata samu wani labarin ko yaya yake..... ★★★ suna gama gwajin karshe Ammar yakara yimasu fatan alkhairi sannan suka fidda mutun sha biyar wa'anda za'ayi gasar dasu suna suka zama zakarun gwajin dafi a Masarautar dasu za'a tafi Sirika sai sarkin bayi da Umar sai kuma Idris da kananun bayi guda goma,yau takama saura kwana biyu ayi tafiyar Yarima Ammar ya umurci kowa ya fara shiri kafin lokaci..... Ki hanzar shiga cikin jerin da zasu kasance a cikin wannan tafiyar domin ta musamman Sadaukin Burhaan kenan cigaban izzah ko mulki. "Umar ina so daga z gobe ka hado kayan tafiyar ka kadawo sashena kana cikin yan tawagata,kuma koda munje can ka kasance a cikin Jarumai Kamar yanda Mai martaba ya bukata."Allah yataimake ka ina godiya Allah yasaka da alkhairi"kafi karfin haka a wajena ina san in tambaye ka abubuwa masu matukar mahimmanci da amfani idan mundawo Sirika"Allah yakaimu ranka shidade."Amin."suna cikin magana sai ga dan aike daga Sarki Abdurrahman,bayan anyi mashi iso yafadama Yarima Ammar sakon Mai martaba...tare da Umar suka fito ya nufi bangaren Mai martaba yana isa yayi sallama suka amsa mashi Yarima Aryan ne kadai sai Sarki Abdurrahman bayan ya zauna yakai gaisuwa wajen Mai martaba sannan ya samu waje ya zauna"dan shiru ne ya biyo baya na yan dakikai kafin Sarki Abdurrahman yace."nasa akira mani ku domin insan dami dami kuke bukata, dan gane da kayan da zaku tafi dasu,ku fadi duk abinda kukasan Jaruman ku zasu nema."? "Allah yataimakeka muna bukatar dawakai masu nagarta da aminci kamar guda talatin saboda muna da Jarumai guda sha biyar sai manyan bayi guda biyar sannan mun hada da bayi goma wa'anda zasu kara taimaka mana a cikin wannan tafiyar, kuma mun ware mutane biyar da za'ayi wasan takobi dasu daga ciki akwai Aryan sai ni,akwai Mansur da Yazid sai kuma Lukman,duk da kasancewa akwai Sarkin yaki a cikin tafiyar."Masha Allah,madallah da samum jajirtattun ya'ya kamar ku."godiya muke ranka shidade mun gama shirya komai lokaci kawai muke jira."Naji dadin aikin ku komai na tafiya yanda ya kamata kun birgeni,sannan ba abinda zaku bukata musamman kayan guzuri"Eh ranka shidade munsa sun hada kayan su cikin shiri,komai mun tanada kafin zuwan lokaci"da kyau Aryan"ina so a dubma ya'ta a cikin dawakan ta a zabi wanda yafi kowa ne lafiya da nagarta daga nan ku kara ware dawakai hudu wa'anda za'a hada Zubaina dasu a matsayin masu kulawa da al'amuran ta."angama ranka shidade."daga karshe zamu tafi da Shamaki sai kuma Waziri na akwai maji dadi sai kuma Garkuwan Zairana kunga duk dani muna bukatar dawakai biyar kenan daman kowa nada nashi kunga jimlar dawakan mu sun kama guds arba'in kenan.bayin mu sun kama guda sha biyar sai dawakan jarumai sun kama suma sha biyar sai tawaga ta data Zubaina munkama mu goma duka sun kama arba'in cif daga karshe ina san ku kara jajirce lwa kamar yanda kuka saba Allah yai maku albarka"Amin,Allah yakara girma da ɗaukaka."gobe idan Allah yakaimu zan zauna da Sarkin taska sai Majidadi da Sarkin yaki dan musan me zamu bukata har muje mu dawo batareda mun samu wata damuwa ba....duk da nasan Sarki Abdullatib zaiyi iyakar kokarin shi amman bana san nauyi yai mashi yawa."Allah yaja da ran Sarki hakan ya kamata muyi...Allah ya karramaka lafiya."Amin." ranar yini sukayi suna fira da mahaifin su rabi da kwata duk akan yanda zasu tsara tafiyar su Sirika sukeyi.yana jin dadi aransa sannan yana alfahari da ya'yan sa...... Washe gari Umar keta fama hada yan kayayyakin shi cikin wata bakar jikka ta Abba Ado yana gama hadawa yayi sallama da Abban shi "To Ummaru sai ka kara kula sannan ka kasance mai ɗa'a kaji."To Abba zan kiyaye da izinin Allah."da haka ya tafi wajen Yarima Ammar koda ya isa mai tsaron sashen ya tsayar da Umar yana shi shiga ya kai wajen awa biyu sannan yabar shi ya shiga ciki bawansa yai mashi sallama da Ammar bayan minti goma ya fito yace Umar ya shiga yana shiga karamin falon shi ya zauna kasa yana kallan tsaruwar da haduwar da falan yayi bai jima da zama ba Yarima Ammar ya shigo...Sadauki ya gaishe shi cikeda ladabi,fuska sake ya amsa cikin jin dadi,"Umar har kagama shiryawa"eh ranka shidade, gama kayana nan"toh Umar sannu da kokari ina so ka kara jajircewa kaji bani ba kowa na san Jarumtar ka da kuma jajircewar ka kada kaga na damu inyi tafiya da kai nasan zaka samu daukaka sannan zaka zama mutun mai kima da daraja a cikin Zairana, ldaga lokacin da Jarumtar ka da hazakar ka suka bayyana a bainar Jama'a."in sha Allahu zan kokarta."Umar mahaifin mu yana son Jarumai kuma duk wanda yasan labarinsa yasan shi din Jarumi ne,bai kasance daga cikin raggaye ba, shiyasa yake ba Jarumai muhimmanci a rayuwar shi,tunda yaga kokarin ka a ranar daka amsarma Aryan wasa,wannan ne yasa yace atafi dakai Sirika sannan ka kara kulawa da Jarumai saboda idan aka saka sauran yan uwanka bayi zasu ga kamar ba'ayi masu adalci ba shiyasa kaga munce maka ka kara kula da yanda muka gabatar da wasannin mu saboda tsaron lalura Allah yabamu sa'a." "Amin...da izinin Allah bazaka taba samun damuwa da niba duk abinda kukayi agabana Umar ya kiyaye shi"Allah yakara maka basira Umar." "Amin....Umar na godiya da nuna min karamci,Allah yakara maka girma..... _____________ Ɗan aiken gimbiya Masau'da ya dawo,koda ya iso bakin Masarautar Srkin kofa ya tare shi dama Hamza ya bada doka karya kuskura yabari wani ya shigo cikin Masarautar koda kuwa dan Masarautar ne."Kai tsaremin shi yanzun zan dawo."angama." yasa wani bawa ya tsare shi,sai da yabari ya tashi dan kewa yawa ya fakaici idan bawan nan ya boye asirran da aka bashi kalkashin wani ganye mai duhu ba wanda ya gan shi Sarkin kofa ne yazo tareda Darwami yana zuwa ya tisa keyar shi yakai shi gaban Hamza cikin fa'da. kallan da Hamza ya aikama wanann bawan saida yasa hantar shi ta kada tsabar tsorata."na tuba ranka shidade kaimin rai walahi bansan an hana shigowa ba, ka ga farceni."tun kan ya rufe bakinsa take Darwami ya ballawa bawan nan wani irin masifaffan mari mai rudarwa."kai harka isa kacema Mai Martaba ya hana shiga,daga ina kake bayan ba wanda yasan da fitarka,dama an rabu da ganin ka a cikin Masarautar nan"jikin Yautai ya hau mazari ya rasa abinda zai ce yasan dai kashin shi ya bushe musamman idan Hamza yaji gimbiya Masa'uda ce ta aike shi shiyasa aka rabu da ganinsa sake falla mashi mari Darwami yayi yace."ba dakai ake ba."tsoro da firgici suka rufe shi ya dago fuskar sa data suntume ya sake duban Hamza a karo na biyu ya sake sunkuyar da kanshi zuciyar na bugu da karfi ya..... _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA SHIDDA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.kituro shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316. "Allah yataimaki Sarkin Burhaan ina nan ba inda naje walahi."Kai kafada mana gaskia idan Sarki ya gano kayi masa karya sai yasa an soke ka da mashi."Darwami yayi maganar a matukar tsawace har saida Yautai ya girgiza fuskokin su kadai ya kalla ya fahimci gaskiar abunda suke fada komai zasu iya yi mashi yace."Allah kuwa ba inda naje amma yau da safe na taje na ansoma gimbiya Masa'uda sako."Sakon mi."? Ranka shidade munyi rahin sa'a da rashin da cewa wanda zai bani sakon bai nan sai dai nadawo hannu biyu."dama nasan ba wanda ya aike ka daya wuce wannan makirar matar Masa'uda karya kakeyi ina ta aikeka."?sai.a lokacin Hamza ya tambaye shi."Iya kar gaskia ta kenan ranka shidade walahi ban anso sakon ba."Darwami." Allah yakara maka girma da daukaka."bai jira wata wata ba ya fara zanar bawan nan da bulala har saida yayi mashi ligib, sannan yasa akai shi magar kama aka rufe shi. A tsora ce ta mike tsaye lokacin da sako ya isa kunnuwan gimbiya Masau'da da sauri tata tafi wajen Hamza, har lokacin yana zaune cikin fa'da ta shigo batareda neman izini ba,yanda suka gatan ta a harzuke baki daya wajen duk suka fita suka basu waje daga shi sai ita,bayan sun gaisheta ta fara magana cike da gadara"Dama akwai lokacin da kafara hana ayi aike a cikin Masarautar nan? ko kuma wannan wani saban fi ilin ne na daban wanda da bansan da shi ba."? Kallan kaskanci yake jifanta dashi daman yasan zatazo shiyasa tasa aka garkame amintaccen bawanta gidan yari mikewa yayi cikeda gadara gami da ratsastsiyar izzah yace."Ke Masa'uda bude idanuwan ki ki kalleni da kyau kinsan nafi karfin rashin da'arki na fuskanci kaf Masarautar nan cikarta da batsewarta ba wanda ke haye mani kai tsaye batareda ko ɗar ba saike!wannan shine karon karshe da zaki sake yin wannan gigin walahi matukar kika kara shiga gonata sai na baki mamaki kuma ni na bada damar kar a sake abar kowa ya sake shigowa Masarautar nan daga dan gida har bako muddin ya shigo cikin Burhaan a tabbatar da an gurfanar da shi a gabana....balle wani wulakantaccen bawan ki, nina bada izini da kar a kuskura abar shi ya wuce har sai angur fanar mani dashi naji wane munafunci yaje ya aika ta."hhhhh Hamza kenan,walahi kayi karya ace amatsayina na gimbiya Masau'da kuma Sarauniya Burhaan ace ni zanyi aike kace zaka tuhume shi,wanann ba hurumin kaba ne dan haka kayi gaggawar sakarmin bawana cikin kwanciyar hankali."dauke ta yayi da mummunan mari"ke harkin isa ki dubi idanuna kifada mani wannan kalmar?bazan saki ba kiyi gaggawar barin fa'dar nan tunda ba nan aka haifi ubanki ba ina gargadar ki daga rana irin ta yau kada inkara ganin kafarki nan,idan ba haka a walahi da kike ganina nan banda ragi balle rsgowa kuma banda kara,tsab zan zaneki kuma saina kaiki cikin turakar bayi zan wulakanta ki,shasha sha"Hamza ni kamara."?murmushin shakiyanci yayi yace"Kina mamaki ne? idan bai shigeki ba sai inkara maki wani."Lallai Hamza walahi daga yau hannunka yagama taba fuskata,idan ko ka kara marina nayimaka alkawalin nadama da tarin dana sani kuma walahi saina rama"hhhhhhh yaro yaro ne baisan wutaba sai ya taka yaro man kaza,Hmmm Masa'uda kike kowa ma?ko mijin ki Abduljalal bai isa ba balle kaskantatta irin ki da bai wuce in wulakanta ba."saidai mu wulakanta juna Hamza nafada maka kayi kadan ka tuhumi bawana koda kuwa abinda yayomin ba mai kyau bane wannan kuma bai dameka ba kuma ina kara fada maka da babbar murya ka fiddo min bawana ina fatan ka fahimta."ko amsa bai bata banda wulakantaccen kallan kinyi kadan da yake aika mata a fusace ta fita ta nufi gidan yari...... ```Allah sarki dayake bukatar ta ce yau ga gimbiya Masa'uda ta kama hanyar zuwa gidan yari,amma da aka kama abokiyar zamanta da diyar mijin ta,harta manta dasu a duniya,balle suyi tunanin zata kai masu ziyara rayuwa kennan``` _Allah karabamu da sharrin makiya mahassada ka rabamu da mugayen mutane Amin ya rabbil alamin🙏Sadaukin Burhaan na kudine akan naira 300 ki tuntubi wannan layin 08160508316. "Goggo ki umurci Hamzanya fito min da ɗana na gaji da abin da yake mani ba yanda za'ayi ace ya dinga wulakanta mani iyalina, dan kawai yana takama da mulki shine zai dinga aikata abinda yaga dama a lokacin da yaso na rantse da girman mulkin gidan mu idan har yace zaici gaba dayi mani wulakanci billahillazi la'ilaha illahuwa sai kowa yaji mu dashi cikin Masarautar nan." ajiyar zuciya mai zafi ra sauke tace "Yanzun Abdullahi akan Turaki zaka dinga tada jijiyoyin wuya har kake son ka wulakanta dan uwan ka abanza da wofi."Gwaggo ɗan uwa fin ɗa yayi ina son da'na dole inyi magana ai."suna cikin magana sai ga hamza ya shigo ya tadda Abdullahi nata masifa,"ni dai nafada maki Goggo kiyi gaggawar sa shi ya sakar mani da'na dan bazan iya jurar ganin shi haka ba."kuka ta kece dashi tana."Abdullahi ni!kake gayama mugayen maganganu irin wannan duk akan d'anka kake wannan kumfar bakin."daga fadar gaskia."rabu dashi goggo bazan saki dan nasa ba yayi abinda zaiyi,ni zaka dinga gayama haka kana man tirere"nayi maganar ko akwai abinda zakayi."?mamaki a saman fuskar Hamza ya fahimci lamarin Abdullahi so yake ya ta'azzara bai tashi tashen kunyar shi ba saida tsufa ya soma taso mashi sannan yake tashen fitsara."Abdullahi Hamza kake fadama magana?shi zaka ce yai duk abinda zaiyi,da raina ban mutu ba kuke so ku wulakantani aje ace gakucan kuna musanyar yawu da junan ku,ciki daya fa ba wasa ba, yayan ka zakacima mutunci akan ɗanka lallai Abdullahi kace wani abu."Amma Goggo ai kema kinsan ba'a kyauta manba,dan yana takama yana yayana bashi zaisa ya daukarmin ɗa ba yana wulakanta shi duk yabi lalace yanda yake son ya'yan shi suna yanda sukaga dama a cikin Burhaan haka shima Turaki yanada 'yanci, ai shima da'ne,kum kema uwace ya zakiji idan akaima danki haka? indai kina so ki ga ya'yanki cikin hadin kai mai daurewa toh kisa d'anki ya sakarmin da'na."lallai Abdullahi ina sarkin Burhaan kake cacar baki dani toh bazan saki Turaki ba sai naga karfin ikonka,tunda kanuna mani tsaurin ido, ni dama tuni nike zatan kanajin haushina Abdullahi dan kaga nike mulkar Burhaan,kanaso kahade mani kai da Masa'uda ko? walahi kar nike kallan ka."lallai Hamza haka kace?tunda nike bantaba zuwa wajen Masa'uda ba da sunan in hada kai da ita dan in cutar da kai, lallai kam idan nayi haka da nayi asara! amma tunda tanan ka bullo yanzun zan hada kai da ita zan mai data tamkar uwata."zuwa lokacin Hamza yakai bango baisan sanda ya shaki Abdullahi ba ya bugar mashi fuska take jini ya balle,Saude tafara ihu hakan yasa Masa'uda shigowa da sauri zata wuce taji ihun ta tana isowa da da sauri ta shiga tsakanin Hamza da Abdullahi. Kallan kaskanci take aika Hamza tana murmushin keta da mugunta tace."Haba Hamza yanzun har lalacewar taka har takai haka da jininka kake fada? La'ilaha ilallahu...Goggo tun baki mutuba har zuri'arki ta farrake sun fara jin hushin junan su, abin mamaki....kaiko Abdullahi miyaja maka fada da yayanka kamar mahaifin kane fa a gareka"cikeda kissa take maganar."karki kara cewa mahaifina ne walahi da wannan abun!gwara Abduljalal yafi min koda yana mulkinsa ba kalar cin fuskar da ba muyi mashi,amma shi tattashin mu yake baisan yaga ko kadan munyi mashi bore amma sai Hamza da muke ciki daya dan haka muddin yaki sakarman da'na ba ruwana da mahassada sai inda karfina yakare walahi"bango Hamza yakaima duka sannan ya watsama Masa'uda wulakantaccen kallo yace."mi yasa kike saka mani ido ne me ruwanki tsakanina da dan uwana, kika kuskura na lissafa ukku walahi saina karya ki."maida wukar bani nakai zoman ba kajj Sarki Hamza idan haka ake Sarki da anyi asara ace Sarki ba aji ko kadan Allah ya kyauta."a fusace yai kanrta da sauri Abdullahi yaja hannun Masa'uda suka bar dakin, duk kiran da Saude keyi mashi a banza,shiko Hamza runtse idanun shi yayi yanajin dacin maganganun Masa'uda koda ya bude ba Abdullahi ba alamar shi, wani irin kuka Saude ta fasa ta fadi kasa tana."Kun tona mani asiri Hamza yanzun wannan na nuna Abdullahi yakoma bayan Masa'uda."tsaki Hamza yaja ko kallan uwarsu baiba balle tasa ran zai bata hakuri ya fita a fusace ya nufi fa'da ranshi na mashi daci saboda ance yayi bako daga Sirika..... Yana isa fa'da kowa ya mike aka gaishe shi sannan ya zauna cike da izzah bayan yan sakanni magatakarda ya anshi sakon da aka aiko,nan Sarki Hamza yaba magatakarda damar karanta sakon da aka aiko mashi..... _Assalamu alaikum_ ```Sakon gaisuwa marar iyaka daga Sarki Abdullatib Muhammad zuwa ga Sarki Abduljalal Muhammad ina fatan sakona ya riskeka fatan kana cikin koshin lafiya,ina mai shaida maka ranar sha bakwai ga watan jiya munyi taron Sarakuna amma bamu ganka ba,duk da kasancewar Sarkin Sarakai kuma kaine shugaban taron nan,zamu gabatar da gasar nan a Masarauta ta a watan gobe sha shidda ga watan jumada akhir,muna gayyatar hazikan Jaruman masarautar ka,da fatan za'a karbi sakon gayyatar mu daga Masarautar Sirika zuwa ga Masarautar Burhaan,bissalam``` Tunda hamza yaji an ambaci Sarki Abduljalal wani irin bakin ciki ya turnike shi, jiyake kamar ya fasa ihu amma ya daure yace aba dan aike masauki kafin gobe za'aba da sakon da zai maida ma Sarki Abdullatib kafin lokaci yayi. Yana komawa sashen shi sai musiba yakeyi."ina Sarkin shine za'a dinga jinjine gefe kamar wani katako kowa Sarki Abduljalal nagaji."aganin shi hakan kamar cin mutunci ne ace yana gabatar da mulki amma za'a rubuto wasika da sunan wancan miskinin Sarkin,sunan da yasa Abduljalal kena Miskini saboda bai iya komai, yazama dole yasa Shamaki ya na ɗashi a matsayin Sarki na dindindin sannan yasa ya turama sauran Sarakuna takarda dan su shaida shine Sarkin Burhaan. _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA BAKWAI Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.kituro shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316. *BURHAAN* Tafe take cikeda izzah tana taka kasa kamar bata so sai shan kamshi takeyi ba inda ta zarce sai babban gidan yarin Gilba,tana isa baki daya hadiman dake wajen suka zube kasa suka kwashi gaisuwa daga masu hannu tayi cikeda gadara da sauri mai tsaran gidan yarin ya iso gabanta ya zube jikin shi na bari ya gaishe ta cike da girmamawa."ina bukatar ganawa da bawa na."angama ranki shidade." da sauri ya bude mata kofa,ita da baiwar ta Talatu suka shiga tana take mata baya tsaye tayi ta harde hannayen ta saman kirjin ta tana karema illahirin gidan kallo gaba da yamma kudu da arewa juyawar da zatayi ta hangi gimbiya Mardiyyah ita da hadimai sunata aiki,murmushin gefen baki ta saki a hankali take tako zuwa wajen Mardiyah tana aika mata kallan kaskanci da wulakanci."Baiwa ta,ashe aiki akeyi."duk hadiman dake wajen suka zube duka gaisheta daya bayan daya suka bar wajen daga ita sai Mardiuya da har yanzun taki dago kanta bare ta kalli inda take."sannu ko."?ta kuma fada tana dan yamutsa fuskar ta."a hankali ta mike tsaye tana aika mata ballagazazzan kallo mai dauke da tsantsar tsanar ta cikin kwayar idanunta,ta watsar taci gaba da aikin ta ganin taki yi mata magana hakan yasa ta koma nesa daga ita,ta kira wani bawa yana isowa tasa yai mata kiran gimbiya Mardiya."Allah yataimaki gimbiyar Burhaan, gimbiya Masau'da nasan ganin ki." kallan kaskanci take aikama Masa'uda kallan kinyi kadan"kaje kace mata idan tana bukatar ganina zata iya zuwa ta iskeni da kanta"Angama Allah ya fiddaki cikin kuncin da zalincin da azzalumai suka saki muna tareda ke uwar marayu." Koda Mardiyyah na cikin gidan kaso amman har yanzun bayi na mutunta ta fiye da kima kuma ta kara samun daukaka marar misaltuwa bata taba sanin tana da masoya kamar haka ba saida ta tsinci kanta a cikin halin rayuwa...yana zuwa ya fada mata sakonta kaf ba abinda ya rage..murmushin takaici tayi sannan tayi mashi izinin tafiya."Allah yataimakeki gimbiyar Burhaan me zai hana kisa ayimata dukan tsiya wanda sai tayi dana sanin fada maki kalar wa'annan maganganun."Aaa Talatu bakiga yanda duk ta lalace ba kullun cikin ukuba take,hmm Hamza kadai ya isheta ko a haka akabar ta lallai tasha ukubar rayuwa,yanzun bata gabana ta Hamza nikeyi,muje gunta."....zaune suka isketa ita da gimbiya Juwairiyyah da bayi sunayi mata tausan kafafun ta,tsaye tayi akan su tana aika masu da kallan tsana tanaji kamar ta halakasu a cikin zuciyar ta,tsawa ta daka masu mai razanarwa har saida suka razana."ku baceman dagani munafukan banza munafukan wofi."da sauri bayin nan sukabar wajen ya rage daga Juwairiyyah sai gimbiya Mardiyyah, kallan kaskanci take jifan su dashi a hankali tafara taku tana dukan tafin hannun ta cikin dayan hannun ta takai gauro takai mari a harzuke tace."Ke har kin kai matsayin da sarauniyar Burhaan zata kiraki kice bazaka ki zoba a matsayin ki nawa? ta baiwa wulakantatta wadda bai wuce in saidaki ba." gefe gefe gimbiya Mardiya ta duba sannan ta kalli bangaren damar ta da haggun ta kamar nai neman wani abu."ke mi kike dubawa ba dake nike magana ba."? Sai a lokacin gimbiya Mardiyah ta kalle ta."Au ai Sarauniyar nike nema yaushe kika iso nan din."da sauri gimbiya Masa'uda ta runtse idanun ta tanajin dacin maganar ta tace."kwarai kuwa nice Sarauniyar,kisan abinda zaki dinga fadaman idab ba haka sai kin banbance tsakanin aya da tsakuwa."A wulakance gimbiya Mardiyah take aika mata da gantalallan kallon da ita kanta saida ta raina kanta da kanta"Hmmm ta yaro kyau take bata karko.....Masa'uda kenan! ashe da Sarauniya nike magana ban sani ba? lallai karfin halin ki na burgeni,wannan wasan yai mani dadi....karki manta turakata kikazo kika iskeni kuma nike da iko da nan wajen,kidawo cikin hankalin ki tun da wuri idan ba haka ba hmmm kema kinsan sauran."karya kike walahi kina baiwata kice zaki gyara mani zam kinyi kadan." "Ko? ki dubeni da kyau Masa'uda kada ki manta kina gaban gimbiya Mardiyyah matar Sarki Abduljalal uwa ga Sadaukin Burhaan magajin gobe mai jiran gadon karagar mulkin Masarautar nan..."ya isa kada bakin ki ya kuma gigin kira wannan shegen yaron a gaban idanuna."ke din banza kema kinsan ba'a haifeki ba....kice zakizo har cikin gidana a cikin turaka ta sannan kice zaki nuna min gadara kinyi kadan,daga yau sai yau muddin lallatattun kafafun ki suka kara takowa har inda nike lallai saina nuna maki karfin ikona"mamaki da al'ajabi ya gama kashe Masa'uda."ni zaki kalla ki dinga fadaman kallar waɗan nan bakaken maganganun."? "Kwarai kuwa...matukar baki bar wajen nan ba sai nasa duk bayin dake nan wajen sun lakada maki dukan tsiya."nidin Mardiya."ko kina tantama? Hamza yayi kadan yadubi kwayar idona ya gayaman wa'annan maganganun ba tareda nasa yayi nadamar hakan ba,balle ke da baiwata tafita daraja da komai sakara wawiya dakikiya dake."kuka ne kawai Masa'uda batayi ba saboda bata tsammaci haka daga gareta ba."walahi harna manta dake a cikin tarihin rayuwa ta,sai yau!yau dinma da kyal na shaidaki tsabar lalacewar da kikayi...zaki iya kama gabanki tunkan dare yayi maki."Lallai kam! dama tabaki Mardiyyah har yanzun baki ladabtuba,da kike gadarar ke matar Sarki Abduljalal ce ai kin makara da wannan gwara gawa dashi kinga baida wani anfani... balle wani banzan Sadauki wanda ma anmanta da rayuwar shi baki daya haka zaki karata a matsayin baiwa ke da yarki."ni nafi karfin intsaya ina cece ku ce dake dacan banyi ba,balle yanzun danasan darajar kaina data rayuwar iyalina,da kike ikirarin gwara gawa da mijina,ai cuta ba mutuwa ba,kuma zai warke da iznin Allah kuma zanci gaba da ansa sunan yar Sarki jikar Sarki matar Sarki uwar Sarki kuma kakar Sarki, kinga ko nafiki daraja nesa ba kusa ba,sannan awajen ku ne labarin Sadauki ya kau....saidai kisani kullun sai bayin Burhaan da sauran mutanan kirki sunyi masa addu'a saboda kullin zuciyoyin su cike suke da began jajircetacce kuma Jarumin nan dake saka zukatan azzalumai razana a duk lokacin da aka ambaci sunan sa sai tsoro da fargaba ya cika zukatan su,yayin da talakawa suke kasancewa cikin nishadi da annashuwa kuncin dake cikin zuciyoyin su na wankewa wannan ba kowa ba ne sai Muhammad Abduljalal Muhammad Sarkin Burhaan wanda gadon karagar mulkin Burhaan ke jiran shi cikeda bege....hmm ni nafi karfin ki,Masa'uda."Dafe kanta tayi da sauri ji take kamar kwakwalwar ta zata tarwatsw zuciyar ta kamar zata kufto daga kirjinta ba kadan maganganun ta suke neman haukatata ba,baya baya tayi zata kife kasa da sauri Talatu ta tareta ita kanta duk jikinta yai sanyi likis karfin hali kawai tayu tace."Ni kike gayawa magana son ranki sai nayi maganin kidani kike zancen.....karki damu Mardiyyah zaki ga abinda zan maki a halin yanzun batake nike ba."hmmm ina jiranki ni har akwai abinda zaki iya yiman wanda Allah baiyi man ba?ba abinda ban gani ba na rayuwa! indai kece ina sauraran duk wani makircin ki a tafin hannuna yake kuma narigaki nace Allah"kifadi son ranki zamu gauraya"ke Masa'uda kama gabanki tunkan dare yayi maki"zantafi dan ba nan kadai nazo ba amma ki saurari sako na"damuwarki ce,sakarai marar hankali."Har ta juya zata tafi ta dafa kafadar ta,a kufule Masa'uda ta juya."kunyi sake ɗan zaki ya girma ku jira saka makonll ku bada jimawa ba."dariyar shakiyanci gimbiya Mardiyah ta kece da ita hakan saida yai sanadiyar bugun zuciyar gimbiya Masa'uda rasa abin cewa tayi,guiwa sage ta tafi kamar tayi kuka taga ba abinda ya sauya ga kishiyar tata maimakon tayi sanyi sai takara ke kashewa bata tsoron kowa domin kwayar idanunta sun shida hakan. harta isa sashen maza bata kula ta iso saida Talatu ta hankantar sa ita sannan tasa wani babban mai kula da sashen, yakaita wajen bawanta Yautai koda ta isa yana ganin ta take yafara murna kamar wanda aka ba kyautar hajji,sawa tayi aka fiddo shi suka samu waje suka zauna ta fara yimashi magana da ido."barka da zuwa uwar dakina"yawwa Yautai ina sakona."zai magana kenan yaga Hamza, tsaye akan su tunda aka ga Masa'uda ta shigo gidan kaso akafada mashi, hannuwan sa hade a kirjin sa su kawai yake kallo da ido yautai yai mata nuni amma taki waigawa dan tagane Hamza ne."Allah yataimakeki danaje kasuwar ban same shi ba hakan yasa nadawo,ina shigowa sai sarkin kofa ya tareni sannna Sarkin horo ya tafi kiran mai girma Hamza,dana duka wajen wani ganye mai duhu banfi minti biyar ba saiga Darwami ya kama ni yakaini gaban fa'da daga nan aka gurfanar dani a nan wajen Allah yakara maki daukaka, harda taro da sile duk an kara mani dasu,ina maki fatan nasara uwar dakina, sannan kada kajarki ta rinjaye ki ki manta da ragamar ki cikin wani hali....."tsawar da Hamza ya doka masu ne yasa su tashi,murmushi kawai tayima Yautai sannan tace."shikenan zaka iya komawa inatareda jikkata duk rintsi duk wuya sannan akalata na tare dani ka kwanar da hankalin ka."godiya nike uwar dakina,Allah yakara maki girma da daukaka."dan danan Hamza yasa aka kara garkame Yautai saida yasha duka sannan. kallan bacemin dagani tunkan na wulakan taki a bainar jama'a ya aikama gimbiya Masa'uda,yayin da itama take masa kallan kayi kadan.... sannan ta juya tacigaba da tafiya Cikeda izzah gamida kasaita harta fita ranta fas tasamu labari mai dadi,haka ta koma tana jiran dare yayi kafin su dauko sakon su. ______________ Tafidah ya iso kasar damagaram ba inda ya sauka sai cikin katafaran gidan su Shattimah koda mai gadi ya ganshi ba karamar murna yayi ba,da sauri ya dauki kayan Tafidah ya kai mashi har cikin gida yana mashi maraba da zuwa a cikin katan daki ya zauna hadiman gidan suka dinga kawo gaisuwar su ga Tafidah. yar aikin gidan ce keta dauko kulolin abinci tana ajewa a saman wani katan kafat da kawatu da taein kilissai masu ban shia'awa da birgewa tana ganin Tafidah itama da saurin ta tazo ta gaishe shi sai murna takeyi ya ansa cikin farin ciki da sauri taje ta fada Hajia Mansura tayi babban bako."wanene Lami."? "Ranki shidade gani da ido ya kori ji Allah yataimake ki."batare da bata lokaci ba Hajia Mansura tana shigowa falon idanunta sukayi tozali Tafidah wani irin farin ciki ta lullube cikeda bage da tarin jin dadi ta rufesu da sauri suka rungume juna sai jin dadi sukeyi kowa da kalar farin cikin da yake ji a cikin zuciyoyin su"Mukhtar ashe da rabon zan kara ganinka?nayi kewar ka da'na."Kidaina kuka Umma nayi kewar ki."kama hannunsa tayi suka zauna tace."ko bakace komai ba da angan ka ansan kana cikin damuwa ka daina damun kanka."Umma narasa yanda zanyi na cire kaina cikin damuwa amma nakasa,kullun cikin zullumi da tunanin nike kwana,idan na tuna halin da yan uwana suke ciki"haba Mukhtar ka daina damuwa Allah natare dasu a duk halin da zasu kasance,komai zaizo cikin sauki da izinin Allah... muje ka shirya kaci abinci."har daki Hajia Mansura ta raka Tafidah masu aiki suka aje mashi kaya sannan ta fito. saida gaban shi ya fadi daya shigo dakin abubuwa da dama yake tunawa amna rayuwar su,hakanan yaji ranshi ya bashi Shattimah ya dawo gida kanshin turaren da dakin ya kama kadai ya bashi tabbacin hakan,tashi yayi ya shiga wanka. "Nikan Lami har yanzun yaran nan basu dawo ba?ga Mukhtar ya iso ba kowa a gida sun maida hawan dokin nan kamar ibada haba."Hajia ai kinsan haka suke amma yanzun zasu dawo."Allah kyauta har yanzun Asma'u bata tashi ba."Eh Hajia saidai Ahmad shima yaba wajen Indo."ai shikenan." shiryawa yayi cikin wani yadi mai ruwan madara bakaramin karbar sa yayi sosai yai masa kyau turare yadan shafa arabian perfumes yana gama kimtsawa ya koma saman gado ya kwanta daman duk ya gaji ji yake baki daya jikin shi kamar ba nashi ba. tana tashi wanka kawai tayi sannan tayi sallah tana gamawa ta shiryawa sannan ta wuce dakin Umma isketa tayi zata fito gaishe ta tayi."yawwa ya'ta anta shi."eh Umma."riko hannun ta Umma tayi suka fito falo."ya'ta yau kinsha bacci ya kike jin jikin ki? "Bakomai, kawai kasala nikeji amman yanzun naji dadin jikina."sannu."inda suke cikin abinci suka shiga shiryawa. Gajiya da kwanciya yayi ya tashi ya zauna saman gadon ya dauki alqurani yafara karantawa cikin sanyin murya yajima yana ta karatunsa yana kara samun natsuwa cikin ruhinsa. Tunda ya doso wajen yake jiyo karatun alqur'ani na tashi a hankali muryar datayi sanadiyar bugun zuciyar shi yayin da yaji gaban shi Na faduwa, sanyin kamshin turaren daya tsaya masa cikin kwakwalwar sa ya fara sunturi cikin hancinsa kara saurin tafiyar sa yayi saboda ransa da gangar jikinsa yabasa ba mai irin wannan kamshin sai Tafeedah saidai yana kokon tan hakan duk dayasan komai jimawa zaizo kodan ya nemi labarin su duk tako daya da zaiyi na kusanci da dakin haka yake kara jin sautina karatun alquranin jikinsa na rawa yasa hannu ya bude dakin idanunsa sukayi arba da Tafeedah baki daya numfashin shi ya tsaya cak na wucin gadi tsabar mamaki,shi kanshi Tafeedan yanajin anshigo dakin yasan aminin nasa ya dawo,a hankali ya dago kanshi yayi ido hudu da Shattimah wanda ya gaza kwakwaran motsi tsabar mamaki,wani irin sanyayen murmushi suka sakarma junan su mai narkar da zuciya da sauri Tafeedah ya aje quranin ya mike yana nuna Shattimah ya kasa ko magana tsabar farin cikin daya lullube zukatan su ba abinda keyi sai hawayen farin ciki da sauri cikeda garaje suka rungume junan sy sai kuka sukeyi kamar wa'anda aka aiko ma sakon mutuwa,sun kusa minti biyar a rungume da junansu kowa najin yanda kirjin dan uwa shi ke bugawa haka hajia Mansura ta shigo dakin ta iske su sunata kuka kamar me, tsayawa tayi tana mamakin kallar kaunar da sukema junan su, magana tayi masu amman ba mai jinta a cikin su har saida ta shigo sannan ta tabasu sannan suka saki juna, saman gado Tafeedah ya zauna,ya rasa mi yakeji Hajia ta zauna ta riko hannayen su tace. *Yar Mutan Kankia❣️* *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA TAKWAS Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello,shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316. _ZAIRANA_ Fadila tagama hada kayan uwar dakin ta tsaf a cikin jikka,itama ta samu wata karamar jikka tasaka kayanta,bata jima da gama kimtsa kayan su ba sai ga gimbiya Zubaina ta fito daga wanka da sauri Fadila ta isa wajenta ta zube saman gwiwar ta tafara tayata shiryawa."Allah yataimaki gimbiya mu kadai ake jira."masharci ta dauka ta fara sharce mata dogon gashin ta a hankali."dawa dawa kika ga za'a tafi."Allah yakara maki lafiya,harda Umar duk nagani sai kuma uwar bayi."daure mata dogon gashinta tayi da ribom sannan tace."yayi kyau."a hankali gimbiya Zubaina ta mike ta dauki kayan su na al'ada ta saka kana ganin ta zakasan ita din cikakkar buzuwa ce kayan sunyi bala'in yimata kyau kuma sun karbi fatar ta sosai,jar alqabba ta daura saman kayan."ba abinda kike bukata."ba abunda nike bukata ranki shidade." suna fita bayin da za'ayi tafiyar dasu suka rugo da gudu suka kwashi gaisuwa sannan suka daukar mata kayan ta,suka tafi sashen Mai martaba,saida ta shiga wajen Hajia ta tayi mata sallama sannan ta wajen gimbiya Bilkisu can ta iske gimbiya Rukayya tareda yarima Ammar sukayi masu ban kwana sai zolayarta sukeyi."Allah yasa kuje lafiya ku dawo lafiya."Amin."suka amsa rakkiya sukayi masu suna shi masu albarka. Baki dayan suka fito basu jima da fitowa ba suka kama hanyar tafiya Masarautar Sirika. ★★★ Sarki Abdulbasit Abdulkarim zaune cikin Fa'dar shi ya tara baki daya hakiman shi bayan kowa ya hallara yai masu bayani akan sakon gayyatar da Masarautar Sirika ta aiko masu,sannan ya nuna masu anfanin zuwa wasan yaci gaba da cewa."saidai ni yace masu zanyi tafiya mai matukar mahimmanci,saidai na umurci ko wane Hakimi a cikin ku,kuda Jarumai ukku ukku a kowace shiya sannan ina so zuwa gobe za'ayi wannan tafiyar."angama ranka shidade Jarumai sun karbi gwajin daya dace Allah yakaimu lafiya."Hakimin Sumani shine zai wakilci wannan tafiyar,ina maku fatan alkhairi."godiya sukai mashi,sannan yasa Sarkin Taska yaba Hakimin Sumani kudi masu yawan gaske saboda suyi guzuri,sannan ya hadasu da Dawakai masu nagarta da aminci,baki daya suka kama mutun talatin zasuyi tafiyar duk da bayin su,fatan alkhairi Sarki Abdulkarim yai masu suka tsaida lokaci da misalin karfe takwas na safe zasu dauki hanya. ___________ tunda aka aiko da sako Sarki Hamza yarasa yanda zaiyi da ranshi ga Sarki Abduljalal baida lafiya kuma yasan Sarakuna na bala'i bashi matsayi da mahimmancin gaske kasancewar shine Sarkin Sarakuna...yasan matukar suka samu labarin rashin lafiyar shi,tabbas zasuyima Burhaan tsinke dan su nema mashi magani, idan ko har ya kuskura sukazo lallai asirin shi ya gama tonuwa,kuma yasan kashin shi ya bushe,abinda yasani bazai taba bari susan Abduljalal bai lafiya ba."matsiyacin gashi yaki mutuwa saboda taurin rai irin nashi."ya fada yana kaima iska duka."babban kuskuren dana tafka yanda ba kama rabi da kwatar Jaruman Burhaan na daure su gidan yari baccin haka da sai in tura su sannan sai insa Shamaki ya wakilce su."ya fada kamar wani zararre yace."ba yanda zanyi saboda duk wahala tasa sun lalace,matsalar daya kowa ne Sarki so yake yaga Sadauki dan iskan yaro,idan ma na data su sunje zasu ce ina Sadauki?ya akai baizo ba!kuma na tabba yanda 'yan Masarautar nan basu sona tsab zasu tona mani asiri suce munyi mashi kurciya yabi duniya! nasan daga ranar asirin mu yagama tonuwa yanzun minene mafita."? Shi kadai keta surutan shi kamar zararre ba abinda yake nema sai mafita yanda zai sanar dasu baida damar zuwa wasan da za'a gabatar....ranar dai haka Hamza ya wuni yana neman mafita saidai yakasa samarwa kanshi mafita.da haka yakoma fa'da yakira magatakarda yasa aka mai dawa Sarkin Sirika amsa sannan yasa aka kira mashi dan aiken da aka aiko mashi ya bashi takardar sannan ya hada shi da guzuri harda kudi masu nauyi saida ya bashi da haka yakama hanyar komawa gida. tafiya tayi nisa gasu Umar har sun kusa shiga kasar Sirika baifi awa biyu ba sukai,waje suka samu suka yada zango da gudu Idris ya iso ya rikewa Zubaina sirdi ta sauka,cikin kankanin lokaci bayi suka fara hada abinci kafin wani lokaci aka fara raba abinci aka bawa. Zubaina dasu Ammar sai Mai martaba zaune a masaukin da aka tanadawa mahaifin su kafin su huta suci gaba da tafiya,Umar yakawo masu abincin cike da girmamawa ya duka ya aje masu sannan yakai gaisuwa wajen Mai martaba,ya ansa cike da annuri,nan ya gaishe da su Ammar suka amsa sannan ya aje masu abincin cike da da'a, shidai Sarki Abdurrahman na mamakin Umar yanda yake gabatar da ayyukan shi,kamar wani dan babban mutun cikeda nutsuwa bayan ya gama kawo masu abincin su, sannan ya koma wajen Abba Ado sukaci nasu a tare sannan kowa ya gama suka kara hutawa bayan sallar la'asar sukeyi sallah lokacin rana tayi sanyi sukaci gaba da tafiyar su cikin aminci..... ___________ "Godiya zakuyima Allah daya sake hada fuskokin ku a wannan lokacin...farin ciki shine ya dace da fuskokin ku bawai kuka ba."insha Allahu Umma."yawwa,kuyi sauri ku fito ina jiran ku Allah yaimaku albarka."amin Umma."suka amsa baki dayan su.Wanka Shattimah ya shiga ba tareda ya kuma cewa komai ba.harya shiga ban daki ya rasa gane kukan mi yakeyi na murna ne ko akasin haka...koda Shattimah ya fito murmushi ya sakarma Tafidah ji yake kamar ya hadiye shi tsabar kaunar da yake mashi a matsayin shi na ɗan uwan shi wani irin shauki da kaunar juna ke fisgar su sai suke gani kamar a mafarki haduwar data zame masu ta bazata kallan juna kawai sukeyi kamar masu baki."Tafidah..Shattimah"suka ambaci sunan juna atare baki dayan su suka saka dariya suka sake rungume juna cikeda so da kauna,zama sukayi gefen gado kowa da abinda yakeji a ranshi"kaga yanda ka koma?nayi kewarka dayawa kullun kana cikin zuciya ta"rike hannun shi Tafidah yayi yace."nagodema Allah daya sake hadamu cikin aminci Shattimah ina Ammi?ina Mai martaba?ina Juwairiya?ya labarin Asma'u."?a jere ya jefomasa tambayoyin ya kafesa da idanunsa yana jiran amsar sa."share hayawen da suka zibo masa yayi yace."ka gafarceni Mukhtar nasan nayi maka laifi."laifin me?bakaimin komai."akan na tseretar da rayuwar Asma'u na baro Ammi da Abba,Juwairiyama bani da labarin su."ajiyar zuciya ya shide mai nauyin gaske yace."ina sonka dan uwana kaci jarumi ko nine abinda kayi shi zanyi kasani ina tareda kai duk wuya duk runtsi."tare suka fito wajen Umma hannun su sarke dana junan su.da salama dauke abinki su basu iske kowa ba sai Asma'u da Halimatu suna fira sai dariya sukeyi abunsu,sallama suka sakeyi a karo na biyu,Asma'u ta dago kanta ta amsa masu sallamar take idanuwan su suka hudu dana Tafeedah a kidime irin kidimar dake nuna tsantsar maki a saman fuskar ta, ta mike tsaye har jikinta yadan hau kyarma tsabar mamaki sai take ganin kamar abinda take gani a gaske ne kodai mafar ki takeyi shima kansa anasa bangaren haka yake yana cike da al'ajabin ganin Asma'u duk dayasan Shattimah ya taho da itaba saida bai tsammace ta nan din ba."Tafeedah kaine?kodai mafarki nikeyi."Murmushi ya kirkiro yalwatacce yace."Nine ba mafarki kikeyi ba."girgiza kanta tayi alamun bata yarda ba ta dubi Shattimah dake ta murmushi tace."Ya Ahmad dagaske ne Ya Mukhtar ne."? "haba dai kanwata,ki kwantar da hankalin ki mana abinda kike gani gaskia ne....Tafidan Sadauki ne dai wanda kika sani aminin Shattimah masoyi ga Juwairiyyah,yaya ga Turaki shi ne dai."ajiyar zuciya ta shide sannan ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya dur kushewa kaaa tana kuka,Halimatu ke bata hakuri itama hawayen takeyi. Hajia Mansura ce ta fito da sauri ta iso wajen su ta daga Asma'u tana bata hakuri,dan tasan babban abinda zai sata kuka ba wani abu bane illa mijinta data tuna tasan da ya na nan tabbas yana tareda da abokansa kuma aminansa yau gashi ta gansu tare da juna bashi...tajima tana lallashin ta kafin ta daina kukan da takeyi."Ashe rabon rai kanga rai."Jamil ya fito daga dakin shi yana murnar ganin Tafidah."Jamil manya dan kanina ya girma."kwarai kuwa Mukhtar kaga dai yanda ya koma."Sannu da zuwa Abba."yawwa da'na ya hanya."Alhamdulillah."baki dayan su suka runguma suka zauna saman katon kafat shimfide anjere kayan abinci akai da kayan marmari iri iri kowa ya zauna duk wanda kagani a cikin gida zakaga yanda suke cikin farin ciki,suka hau cin abincin su cikin farin ciki da jin dadi. Suna gama cin abinci aka hau fira kowa na maida yanda akayi,Lami ta dauko Amir ta kawoma Umma ce ta."Hajia ya tashi."af kinga murna tasa na manta da angon nawa."ga dan ku."ansar shi Tafidah yayi ya kwantar da shi jikinsa yana jin kaunar yaron har cikin zuciyar shi kallansa kawai yakeyi ba abinda yake gani a jikin fuskar yaron sai Sadauki."Allah gwanin yau nine rike da jinin Sadauki Allah Sarki." hawayen farin ciki yaji sun shido mashi da sauri yasa hannu ya share."Allah yarayaka bisa tafarki madaidaici."Amin."suka amsa,yana karajin son shi da kaunar shi har cikin zuciyar shi."kawo Amadun ka huta."Murmushi yayi yace."Umma ban gaji da daukar shi ba."toh shikenan."wasa ya dinga yima yaron yana karajin tsantsar son shi,sun jima suna fira, kiran sallar da akayi ne ya tada su daga firar da sukeyi sannan ya mikama Umma suka tafi masallaci. _SIRIKA_ Tamkan take da yan Adam anata hada hada ba abinda akeyi sai tarbar baki kamar ba gobe ba abinda sukeyi sai murnabaki keta zuwa daga ko ina na kasar da sassa daban daban na duniya ba abinda Sarki Abdullatib keyo sai basu masauki mai kyau da tsari,Sarkin shela ke sanar da isowar Sarkin Kesar bakaramar murna Sarki Abdullatib yayi ba da kanshi yaje ya tarosu cikeda farin ciki baki daya suka dunguma suka rakasu masaukin su.ranar haka suka wuni suna tarar baki ta ko ina..... _Yar Mutan Kankia❣️_ *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA SHA TARA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316. Sun iso Kasar Sirika da misalin karfe hudu na yamma basu wani bata lokaci ba suka dauki hanyar shiga cikin Masarautar kai tsaye, saidai duk motsin da Umar zaiyi yana cikin idon gimbiya Zubaina baki daya ta mayar da hankalin ta rankata kaf akan sa tana alkinta abubuwa da yawa atare dashi babban abunda ta fahimta shidin mutun ne mai kirki mai tsananin girmama na gaba dashi....yar tafiyar nan da sukayi tare takara ganin kyawawan dabi'un Umar da girmama mutane ka tawadu'u bai damu da komai ba ya rike matsayin da Allah ya kaddara mashi na BAWA.wannan itace babbar dabi'ar dake kara burge gimbiya Zubaina ga Umar takara yarda da yanayin sa na rashin son yawan magana da hayaniya shidin mutun ne ba bai shiga harkar kowa.Batayi aune ba taji anata uwar shela tun daga nesa aka fara sanar da isowar mutanen Zairana. Yayin da Jaruman Sirika ke tsaye bakin kofa suna jiran isowar su cikeda farin ciki suka taresu sai murna sukeyi cikin kankanin lokaci Sarkin Sirika da sauran Sarakuna wa'anda suka rigasu isowa suka fito suka tari Sarki Abdurrahman cikin karramawa da tsantsar girmamawa cikin kankanin lokaci labarin isowar mutanen Zairana ya karade illahirin Masarautar kai tsaye sashen baki aka nufa dasu aka basu masauki mai kyau da tsari wanda ya dace dasu aka warema kowa da'irar shi dama wajen Jarumai daban,gimbiya Rahama ita ta tari gimbiya Zubaina tasa bayin ta suka kaimata kayanta dakin ta,sannan ta hada Fadila da babbar baiwar ta Murjanatu haka suma sauran bayin da akazo dasu masauki uwar bayin Masarautar ta basu,sai murna sukeyi abin dai sai wanda ya gani. Shi kanshi Umar masaukin su aka basu,a cikin manyan bayi ya zauna tareda Abban shi.ranar har marece baki aketa tara daga sassa daban daban na duniya musamman lardin Afrika. danko mutanen Roowan suma sun iso kuma anbasu masaukin su mai tsari da nagarta,su kuma Hakiman da sukazo masaukin Sarki Abdulbasit akaba su aka mutunta su yanda ya kamata bada jimawa ba yan Masarautar Yurii suma sukazo suma aka karrama su cike da girmamawa da karamci,shima Sarki Kabir Usman yayi farin cikin haduwa sa yan uwa shi Sarakuna. Koda gimbiya Zubaina tagama wanka ta sake kayadoguwar riga marar nauyi ta saka saboda duk ta gaji sabili da tafiyar da suka kwasa mai nisan gaske. gimbiya Rahama ta shigo dakin da Zubaina ke ciki tsaye tayi tana mamakin kallan halittar da Allah yaima Zubaina tana al'ajabin kallar kyau da take dashi wanda ganin ta yafi jinta yanda ake gayawa mata wacce gimbiyar Zairana sai taga kamar masu bada labarin ta suna karage mata kyawunta gani dai ya kori ji inji malan bahaushe.duk da ada da takejin labarin kywunta sai take ganin kamar harda zuzzutawa saidai yau takara yarda da ganin Zubaina yafi jinta,Allah yayi halitta dole ake saka gasa akan aurenta saboda ta cancanta....ɗan gyaran murya tayi sannan ra kumayin sallama a hankali gimbiya Zubaina ta juyo ta kalli gimbiya Rahama sannan ta dan saki murmushi a saman fuskar ta saidai ba lallai bane ka gane tayi shi a hankali gimbiya Rahama ta karaso ta zauna saman gado fuskar ta dauke da murmushi,itama murmushin tayi mata,sake yimata sannu da hanya tayi sannan tasa aka shigoma da Zubaina kayan abinci masu dadi da tsari na alfarma."ga abinci kici kafin mu kara gaisawa,angaishe da gimbiyar Zairana"ina godiya gimbiyar Sirika ki huta lafiya" dan rausayar da kanta tayi tace."Allah yasa nabarki lafiya." _______________ Koda dare yayi ranar su Shattimah basuyi bacci baki dayama basujin baccin fira kawai sukeyi duk abinda yafaru saida Shattimah yafadama Tafidah komai duk daga farko har karshe ba abinda yakeyi sai kuka suna kara tausayin Ammi da Mai martaba aran su dan lokacin da Tafidah yabar Burhaan abubuwa basu cabe da yawa ba kamar yanzun." ina son insan wane hali kabar Juwairiyyah? gyada kansa yayi ya numfasa yace"Gaskia tana cikin hali bata da wani gata tunda nabar Burhaan da Allah suka dogara shine zai masu gata saboda har dukan ta Barde keyi saboda yakasa samun ta a ya'mace shiyasa ya dinga gana mata azaba iri iri daga karshe na maidota wajen Mai martaba ba irin bala'in da ba'ayi ba nida su Hamza,ana nan naji su Hamza sunyima Asma'u mugun tuggu da surkulle zasu kashe Asma'u cikin dare,a daren ranar na gudu da Asma'u.....yanzun haka Ahmad baida cikakkar lafiya sihirin da suke aiko mata ya jefe shi yanzun haka magani nike nemar mashi"Allah Sarki abin gwanin tausyi.kayi kokari matuka ka taimaki zuri'ar Sadauki ka zama dan uwa na rufin asiri a Allah yasaka maka da alkhairi."amin."ni kaina bansan dame zan gode maka ba,Allah yabar zumunci mai dorewa"Amin...yanzun abinda nikeso mu samu lokaci mu koma Burhaan"Nima abin da nike so kenan yaushe zamu koma."? "Zamuyi magana da Umma komi kenan kaga sai mu shirya muje ba zato ba tsammani."Allah yakaimu."Amin." KASHE GARI Gimbiya Rahama ta shigo wajen gimbiya Zubaina a lokacin da ta iske ta har Fadila tagama tayata shiryawa ta sha kyau cikin wata doguwar riga ruwan hoda da ratsin sararin samaniya sai alkabbar itama ruwan hoda ce(pink) duk wanda yaga Gimbiya Zubaina bako shakka zaiji ta burge shi ita kanta gimbiya Rahama saida ta yaba kyaun da kawar tata tayi saboda ta burgeta samun waje tayi ta zauna Fadila ta gaida gimbiya Rahama sannan ta fita dan basu waje su gana. "barka da zuwa gimbiyar Sirik "yawwa ya gajiyar tafiya."?murmushi tayi tace"Gajiya tabi jiki."masha Allah ya Sirika akwai dadi ko."? "Eh da dadi gaskia."tace tana kara fadada annurin fuskar ta."Sunana gimbiya Rahama Abdullatib Muhammad inamaki barka da zuwa Masarautar Sirika kuma ina fata zaki zama kawata."Allah yabarmu tare....ni kuma sunana gimbiya Zubaina Abdurrahman Abubakar naji dadin kasancewa dake."jinjina kai tayi tace."Daga yanzun kin zama kawata kuma aminiya ta"gimbiya Zubaina na godiya."Murmushi suka sakarma junan su,sukaci gaba da labarin su kamar wa'anda suka dade da sanin juna suna cikin fira sai ga baiwar gimbiya Rahama tazo ta gayama uwar gijiyar ta ta, Mai martaba nasan ganinta a sashen shi itada gimbiya Zubaina."zaki iya tafita." bayan gimbiya Zubaina ta kara kimtsawa sannan suka tashi suka tafi sashen Sarki Abdullatib..... ★★★ Gimbiya Masa'uda tasa aka dauko mata asiran da Yautai ya aje mata suna komawa sashen ta ta bude su sai murna takeyi sannan suka dauki dauri daya taba Talatu tace."Duk wahala ki tabbatar kinje bakin sashen Hamza kin binne shi,kada kiyarda wani ya gan shi."ansa tayi tace."angama uwar dakina cikin daren nan zan binne shi."kin kyauta."tana fita itama gimbiya Masa'uda ta wuce sashen Sarki Abduljalal ta iske shi kwance ko magana bai iyayi saidai ido da yakebin kowa dashi bayan ta zauna Saminu ya gaisheta sannan tace ya bata waje zatayi magana da mijin ta, kamar bazai fitaba, saboda bai aminta da ita ba,saidai baida hurumin yin hakan ya fita ya bata waje."Abduljalal kenan ashe har yanzun baka mutu ba?lallai kam gaskia kayi nisan kwana,kana da taurin rai! yaka mata ace ka huta zuwa yanzun....gashi dai ɗanka yayi batan dabo ya bace babu amo babu labari,sannan ga Matarka can garkame a gidan yari hakama yarka tana can cikin kaskanci da wulakanci,uwa uba kai gaka kwance baka iya tsinana ma kanka komai kazama abin wulakantarwa ashsha Abduljalal dama mutuwa kayi daka huta da ganin kaskanci irin wannan saidai kasani nan da ɗan lokaci kadan zaka zama sakarai wawa da ranka zakaji na zama Sarauniyar Burhaan ta dindin."kallan kawai yakeyi yanajin dacin maganganun sa a cikin kokon zuciyar shi da haka takaraci wulakancin ta takama gabanta. Suna shiga sashen Sarki Abdullatib suka iske manya baki sai raha suke yi,sallama sukayi aka amsa masu sanann suka zauna saman wani kafat da ya gaji da tsaruwa da kayan ado irin na Sarauta komai yayi kyau"Allah yataimakeka barka da warhaka sakon ka ya riskemu"barkan ku da safiya ya'yana,ina fatan kuna cikin aminci."lafiya lau."suka amsa fuska sake."ya'ta ta kikaga Sirika,akwai dadi ko?matso nan mugaisa ya'ta ashe da raban ki gaisa da babanki,ya hanya" a hankali ta matsa gefen Sarki Abdulbasit ta zauna ta sadda kanta kasa cikeda da'a tace."hanya alhamdulillah Abba."? "Masha Allah ya'ta." Gimbiya Rahama ta gaishe da Sarki Abdurrahman cikeda sakin fuska ya amsa.haka Sarakuna sukaita jan ya'yan nasu da fira Sarki Kabir Usman keta kallan Zubaina yana yabawa da nutsuwar ta shima suka gaisa,ranar sun jima sunata fira kowa yaga gimbiya Zubaina daman suna da labarin ta,Sarki Abdurrahman yace."ku tashi ku koma cikin gida kafin Allah ya kaimu gobe za'a fara gabatar da wasa."ku huta lafiya."sukace...tashi sukeyi sukai masu sallama,kowa na yaban su.....ranar ne jajibirin da za'a gabatar da wasan baki sukaita shigowa har lokacin baki basu bar shigowa Sirika ba...haka rayuwa ta kasance kusan lokaci lokaci gimbiya Rahama saita dubo lafiyar gimbiya Zubaina, amma wani lokacin sai ta dinga cewa ta fahimci Zubaina tana daukar kai abinda ta fuskanta tana da miskilanci da tsantsar nuna izzah..... A wajen su Ammar kuwa zaune suke shida Yarima Yusuf sun zama kamar yan uwa sai labarin Sadauki sukeyi sunga har yanzun yan Burhaan basu zoba gashi gobe za'afara gabatar da GASA.suna mamakin kalan halayen shi daman wancan karan ma baizo ba,yanzun gashi baki dayan su shida Jama'ar shi ba wanda yazo.kowa na mamakin yanda akai basu zoba."abunda nike gani yafiye jiji da kaine shiyasa yake ganin kamar yafi kowa."kadai fada nima dai haka nike gani Allah yasa ganinsa yafi jinsa atoh"cewar Ammar."Amin....nidai koyayane ina son inga wannan Sadaukin jibi yanda labarin Jarumtar shi ya karade ko ina."gaskia kam."suna cikin fira suka tsinkayi sallamar Umar amsawa sukayi saidai baki daya hankalin Yusuf ya koma kan kalan Umar ya duka ya gaishe dan iyayen gidan sa,tunda Umar ya duja Yusuf ke kallan shi baki daya kyawun Umar yagama razana Yarima Yusuf gani yake kamar ba mutun ba tsabar mamakin kalar halittar da Allah yai mashi yakeyi.....Yarima Yusuf ɗan Sarkin BAIZA ne wanda ya samu gata mai tarin yawa a wajen mahaifin shi."Umar."Ammar ya kira sunan shi a tausasahe."Allah yataimakeka barka da hutawa"Umar ya gajiyar hanya"alhamdulilah."murmushi yayi yace."ina fatan ka kara shiryawa kasan gobe ne za'a fara wasan nan ko."? "Eh ranka shidade na shirya fatana Allah yabamu nasara"Amin Umar....kaci abinci."? "Eh,dazun yarima Aryan ya bani"yawwa Umar kaje ka kara hutawa kaji"Umar nagodiya,Allah yakara girma Amin Umar."ku huta lafiya."Allah yasa."yana fita sai mamakin sa yakara kama Yusuf yana al'ajabin natsuwar shi yanda yake magana a hankalce har saida yanayin sa ya fallasa shi yakasa hakura saida yayi magana"Ammar wannan yaron yai mani kuma ina son in tabbatar da gaske bawa ne shi "? "Kwarai da gaske...Umar bawa ne miyasa ka tambaya."gaskia ya shiga raina sosai da sosai walahi ina kaunar shi."jinjina kai yayi yace."haka Umar yake akwai shiga rai"amman fa ina san infanshe shi nawa zaka saida mani shi"? "Hmmm,Yusuf kenan....Umar ba bawan saidawa bane, kayi hakuri"miyasa kace haka?har akwai bawan daba na saidawa ba."kwarai da gaske Umar ɗan Sarkin bayin Zairana ne,kuma amintaccen bawa ne na amana"bakomai haka Allah ya kaddara a gaskia ina san Umar"haka yake akwai shiga rai kuma yana da saurin sabo.... ★★★ Tunda suka tashi bayan sunyi sallar asuba wanka Tafidah yayi sannan Shattimah ya shiga suka shirya sannan suka fita zuwa falo suka gaishe da Umma bada jimawa ba su Kamal suka fito suma gaishe da Umman su sukayi sannan sukai mata sallama suka tafi hawan doki itako sai fada takeyi yanda basu gajiya da shiririta, kullin sai sun fita wasan doki kamar ibada sudai dariya sukayi suka tafi kowa ya hau dokin sa suka fita tseren dokin su..... _Yar Mutan Kankia❣️_ *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA ASHIRIN Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyan ki ta wannan layin 08160508316. Tunda a suba akaci gaba da gyara filin wasa,baki daya bayin Sirika aiki sukeyi ba kyakkyautawa kamar ba gobe,cikin kankanin lokaci suka gama gyara ko ina yayi tsaf gwanin birgewa. Kayan wasa akata jidowa ana tarasu himili guda dasu iri iri duk abinda akasan Jarumi zai iya bukata an tanaje shi. A sashen Sarki Abdullatib yana zaune tareda Sarki Abdurrahman bayan sun gama karyawa suna danyin fira jefi jefi kasancewar rana ta daga....Jakadiyar sa tazo ta kawo gaisuwa sannan ta nemawa Sarkin fa'da izinin ganawa dashi bada jimawa ba tayi mashi iso yana zuwa ya zube gaban Sarki ya kai gaisuwa.“Allah yakara maka lafiya sako ne daga Masarautar Burhaan.”batare da bata lokaci ba ya bada umurnin a shigo da shi,bayan ya kai gaisuwa wajen Sarki.“Allah yataimake ka wasika ce daga Sarkin Burhaan.” yana amsar takardar yabashi damar tafiya dama ɗan aiken su ne da suka tura....yana fita bada jimawa ba ya bude wasikar yafara karantawa..... _Assalamu alaikum_ _Ina maku fatan alkhairi marar yankewa dafatan sakona ya sameka cikin aminci daga ni Sarki Abduljalal Muhammad zuwa ga dan uwana Sarki Abdullatib Muhammad ina mai baka hakuri akan rashin halatta ta wajen zaman da aka gabatar naso in zo Allah bai nufaba saboda wasu dalilai ina fatan za'a karbi uzurina...ga gasa iya gasa anhaɗa yakamata ace zuwa yanzun nakai kwana ukku a cikin Sirika saidai hakan bai samuba,ina kara baku hakuri...yau kimamin kwana bakwai na tura Jarumai na a Kasar Mali bazasu da woba sai mako mai zuwa naso na turosu sannan da'na shine shugaban tafiyar da fatan za'ayi mani uzuri koba komai bai dace ace nabar Masarauta ta ba kowa ba fatan za'ayi taro lafiya nagode daga Masarautar Burhaan zuwa ga Masarautar Sirika,bissalam_ Koda Sarki Abdullatib yagama karanta wasikar kallan Sarki Abdurrahman yayi, kana ganin yanayin fuskar shi zakasan baiji dadin sakon ba."sai mu karbi uzurin sa."cewar Sarkin Kesar."narasa wane kalan uzurine Sarki Abduljalal ke dashi duk yanda yake da tarin Jarumai fiye da sauran Masarautu amma ya gaza tado kashi dan su wakilci Masarautar sa."Sarki Abdullatib ya karasa maganar cikeda alhini a ransa."akarbi uzurin shi kun san baida wasa da ace yana da damar zuwa tabbas zaizo koba komai shine shugaban taron nan yanzun haka sunje bad taimako ne kunsan sun saba da taimakon mutane kuma da yasan wasan nan ya kusa lallai da ya tado manyan Jaruman sa,muyi hakuri tunda haka Allah yaso ni kaina naso inga da'na Sadauki amman idan muka gama gabatar da gasar nan,bayan an huta sai mu samu lokaci mukai masa ziyarar ban girma a matsayin shi na Sarkin Sarakuna." Sai kalaman Sarkin Kesar ya wankema sauran Sarakuna bacin ran da suka tsinci kansu nakin zuwan mutanen Burhaan sannan kowa ya amince da shawarar da Sarkin Kesar din yabagar duk kowa baiji dadin rashin halarta su ba saidai sun tsaida magana da an gama GASA zasu kai ziyarar ba zata. Haka abubuwa suka kasance bada jimawa ba aka fara fita filin wasa sai fitowa ake kamar ba gobe duk an gyara wajen yayi kyau wajen Sarakuna daban haka na Jarumai ma daban sannan wajen baki daban hakama wajen bayi da sauran Jama'ar Sirika komai yayi kyau cikin tsari. kowane Jarumi da kalar kayan Masarautar su a jikin su hakama bayin su da kagan su zaka gane ko Jaruman wa ne masarauta ne. Su Yarima Ammar sai shiri sukeyi daka gansu kaga ya'yan Sarakai kowa yasha ado iya ado kamar ba gobe....suna cikin karyawa Umar ya shigo hannun shi dauke da Jarumai sannan kayan jikinsa irin na bayi ne ya saka amman bakaramin kyau sukayi masa ba fuskar shi dauke da annuri,cikeda girmamawa ya gaishe da iyayen gidan sa suka amsa cikin girmamawa."zo muci abinci Umar."ba Umar ba hatta Ammar saida yayi mamaki har da mamakin sa ya bayyana a saman fuskar shi."taso mana."ya sake maganar yana sakar mashi murmushi."na gode ranka shidade nako shi."yace shima yana yi masa murmushin wanda yakara bayyana tsantsar kyawun sa."tubarakallah." Yusuf ya furta a cikin zuciya,saida ta fito a fili."bansan ka da musu ba Umar kazo muci."cewar Ammar,zama yayi a nutse suka fara cin abinci duk wani motsin da Umar zaiyi akan idon Yusuf yana nazarinsa musamman yanda yaga yana gayunar abincin kamar bai son ci babban abinda ta fahimta a tatare dashi ba komai yake ci ba,baiyi aune ba yaga Umar din harya koshi yana shan ruwa yace mike"haba Umar kardai har ka koshi.?"eh ranka shidade" haba daga fara cin abici zaka ce ka koshi kodai ka takura ne."? "Aaa nagode."shidai mamakinsa yake yi miyasa komai nasa na daban ne saidai kace ba bawa ba,ya tabbata bacin wani dalilin ba yanda za'ayi ace bawa yaga kabaki na abinci irin wannan yace ya koshi batareda nuna wata zalama ba....sake maida dubansa yayi akan sa yace."naga ba komai kaci ba? "Allah yakara maka nasara,ba komai nike ci ba"kaga Yusuf,bakasan waye Umar ba ina ga shifa haka rayuwar shi take,tun banjin dadin kawaicin sa har na saba,kuma tunda yace maka ya koshi to ya koshin."shikenan."mikewa sukayi duk suka daura rigar saƙi saman kayan su...Umar yakara gyarama uban gidan shi kayan jikin shi sannan suka fita suna gaba yana bin bayan su,ba inda suka wuce sai wajen yan uwansu Jarumai sukaita gaisuwa suna gabatr ma juna junan su,atare suka dunguma suka nufi filin wasa abin gwanin ban shia'awa...... tana gama shiryawa cikin doguwar riga kalar bila tayi kyau ga gashin ta yasha gyara sai kyalli yakeyi Fadila ta daura maya Jar alqabba saita kara haskata daka ganta sai ka kara kallan kyawun ta,kamar dan ita aka kaga kayan ita kanta saida ta kuma kallan madubi tayi murmushi ita kanta tasan ta gaji da haduwa. baki daya hankalin ta na kan Umar shi kadai take tunawa tasan yana can suna shiri yau dai zaisha wahala wajen kula da Jarumai hakanan ta tsinci kanta da mugun jin tausayin shi a cikin ranta.....itama Fadila rigace ta saka ruwan goro itama tayo kyau, sauran bayinta ma kayansu na bayin Masarautar su suka saka. Tana shigowa ta fara feshe uwar gijiyar ta da turaruka tana gama shiryawa suka fita suka nufi dakin gimbiya Rahama,duk inda zasu wuce sai bayi sun kawo gaisuwa baki daya labarin zuwan Zubaina ya karade illahirin Masarautar ta Sirika duk inda suka wuce kallan su kawai akeyi anata gaishe ta...saidai mai hali dai baya barin halin shi saidai ya rage,ko kallo basu isheta ba yanda take taku cikeda izzah ga wata irin kasaita da gadara amsawa takeyi wani kuma ko kallansu batayi har suka isa sashen gimbiya Rahama. Tana isa sashen gimbiya Rahama baki daya bayin dake tsaron sashen suka zube kasa suka kwashi gaisuwa kai tsaye ciki ta wuce tana taka kasa kamar bata so irin takon nan na kasaitattun mata masu aji wa'anda suka amsa sunan su,tun kafi Zubaina takai ga dakin gimbiya Rahama taji ana sanar da shigowarta har ta iso duk hadiman da ke sashen sukaita kai gaisuwa wajen gimbiya Zubaina,cikin wani makimancin falo tasamu ta zauna ta daura kafa daya bisa daya ta harde inda bayinta sukaci gaba da yimata fita,shirun da gimbiya Rahama taji Zubaina bata karaso cikin uwar daka ba hakan yasa tashi cikin ta fito falo iske tayi zaune ta harde ita kanta saida gabanta ya fadi yanda ta isketa ita kanta tasan Zubaina ta wuce da ajinta duk yanda take takama da kyau saidai Zubaina ta wuce da ita..... murmushi suka sakarwa junan su sai lokacin ta isa wajen Zubaina tana zuwa suka rungume juna sannan takama hannun ta suka shiga cikin dakin ta,saman wata kujera Zubaina ta zauna...Murjanatu ta duka ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa ba yabo ba fallasa amma saika saurara sannan zakaji abin da tace,gimbiya Rahama tasa a kawo mata kayan motsa baki har Murjanatu zata tafi ta daga mata hannu alamun ta gode"haba kawata taya zakice bazakici ba"da kyal ta iya bude bakin ta tace."nayi kalaci"gaskia ban amince ba ko madara ce sai kin sha ba yanda za'ayi ace ki,ki kicin komai."bata karacewa komai ba hakan yaba Murjanatu damar kawo mata dafaffar madara ta duka ta mika mata takai sakan biyar kafin ta miko hannun ta karba. mamaki ya gama kashe gimbiya Rahama yau ta hadu da wadda tafita nuna isa da gadara."lallai kam Zubaina."ta furta a zuciyar taci gaba da shiryawa Murjanatu ma taya har ta ida shiryawa itama tayi masifar kyau, ita kuma makubar doguwar riga ta saka sai ta daura alqabba ruwan zuma...."masha Allah kawata kinyi kyau."cewar Zubaina."godiya mai tarin yawa gimbiyar Zairana."sai a lokacin Zubaina ta sha madarar yar kadan sannan ta aje kofin.a tare suka fito suma suka nufi sashen Mai martaba....da ka gansu sai sun shiga ranka yanda suka hadu sai kace yan biyu...Rahama nashiga ta rungume mahaifin ita kuma Zubaina ta gaishe shi a nutse ya amsa yanajin Zubaina har cikin ranshi bada jimawa ba sauran Sarakuna suka fito suma suka gaishe su,Sarki Abdurrahman ya rike hannun yar shi sannan suka dunguma suka wuce katan filin wasan Sirika suna isowa kowa ya mike ga jerin kujeru nan na royal sun sha ado ta tsakiyar itce ta Sarki Abdullatib ya zauna,sai ta hannun damar shi Sarki Abdurrahman ne ya zauna,a bangaren haggun sa kuma Sarki Abdulmuminu ya zauna wato Sarkin Kesar haka sauran Sarakunan duk suka zauna gwanin birgewa......inda su gimbiya Zubaina da Rahama aka aje masu kujeru guda biyu wajen sy ya gaji da kayatuwa a nutse suka tafi wajen kowa ya zauna cike da izzah baki daya idanun mutane ya dawo wajen su kadai ake kallo lokacin da Zubaina zata zauna saida aka dage mata rigarta kadan sannan ta zauna a hankali,Fadila da murjanatu kowace ta tsaya bayan uwar dakin ta suna masu fita a hankali....tunda Yusuf yaga Zubaina take yakamu da sonta bai kasa a guiwa ba ya nuna Ammar ita yace."nakamu da son ta wacece ita."?Murmushi yayi."gimbiya Zubaina kenan."Zubaina dai wadda nikeda labarin ta."kwarai kuwa....gimbiyar Zairana kenan."kallan shi kawai yayi da mamaki ashe kanwar shi ce daman yanada labarin ta yama san ba zata so shi ba ganin mijinta sai an shirya da haka yabar a ranshi..... Bayan sun zauna bada dadewa ba alqalin wasa yafara shela akan kowa ya shirya za'a fara gabatar da wasa hakan yasa Zubaina ta maida duban ta wajen bayi saidai ba, sake dubawa tayi har ta fidda rai da ganinsa sai ta hango shi layin farko,sai murmushi yakeyi saita samu kanta da yin murmushin ita dai duniya Umar yai mata musamman idan tana ganin sa cikin walwala.... mai sanarwa yace."za'a fara wasan takobi za'a fars da Jaruman Yurii su da na Baizar take aka fara kiran sunan Jaruman da za'a fara karawa dasu, batare da bata lokaci ba suka fita kowa da takobi a hannunsa suka tafi wajen Sarakuna suka kai gaisuwa inda Sarki Abdullatib yai masu nuni da suje wajen gimbiya Rahama ita zata basu izinin fara wasan suna zuwa suka kai gaisuwa ta dauko bakin kyalle ta kalli Zubaina murmushi kawai tayi mata sannan gimbiya Rahama ta saki kyalen, baki dayan su suka koma saman layin da akaima zobe ana hura usir aka fara kaftawa kowa yanaji da Jarumtar shi...sharadin wasan ba'asan mutun ya fita daga cikin layin ko kum aka daka kasa shikenan an cika, akaita fafatawa da juna sunkai minti biyar ana abu daya daman minti goma aka bada,amman ankasa kai kowa kasa har saida aka hada jiki amman ba wanda aka kai kasa,har saida ya rage saura minti ukku lokacin su ya cika sannan Nura jarumin Baizar yakai jarumin yurii kasa....take wajen ya kaure da ihu musamman yarima Yusuf, Nura yasa hannu ya dago abokin karawar shi nan suka koma suka kara mika gaisuwa wajen gimbiyoyin su sannan suka koma wajen zaman su..... Bayan sun zauna da minti goma aka kara kiran wasu Jaruman saidai wannan karan Ammar aka kira sai wani Ahmad daga cikin Jaruman Kesar batare da bata lokaci ba aka fito fili sukaje wajen gimbiya Rahama ta jefa masu wani jan kyalle,aka fara karyawa kowa sai gwada gwanintar shi yakeyi har suka cinye lokacin su, aka kara masu minti biyar haka suka cigaba da karawa ko minti ukku ba'a karaba Yarima Ammar ya fidda Ahmad cikin layin baki daya wajen ya kaure da ihun murna,danko Sadauki murna yakeyi kamar me, haka akaita kiran jarumai kala kala sai ci akeyi,sannan aka tafi hutun minti talatin kafin a cigaba dayin wasa, koda suka koma abinci kawai sukaci sannan Sadauki yasake hadama Ammar ruwan wanka,duk suka sake shiryawa, itama Zubaina tana gama shiryawa madara kawai ta iya sha gimbiya Rahama ta biyo mata sadda suka koma har anfara wasa,suka zauna wannan lokacin Aryan ne a cikin wasa shima haka akaita kaftawa,saura kadan akada Aryan Allah yasa ya tade abokin wasan shi yayi nasara....hatta Sarki Abdurrahman ba karamin dadi yaji ba,da harya fara fidda rai da nasarar dan nasa aka fara raba kayan sha dan jika makoshi sannan aka fara kiran jarumai ana kiran Jameelu Hassan Zairana akaji shiru, tunda aka koma hutu zazzabi ya turnike shi kamar zai mutu shiyasa Sarki Abdurrahman yabar bayi ukku dansu kula dashi, Yarima Aryan ne yaje ya bada sunan Sadauki duk waje yayi shiru ba alamun jamilu can sukaji mai shela na kiran."Umar Adam Zairana."Mai martaba yaita kallan Umar cikeda mamaki shi kanshi baiyi tunanin shi zasu bada ba,yayin da Umar ke waige waige duk mamaki ya kama shi sai yaji kamar ba shi ba saida Ammar yazo yai mashi magana sanann ya fito a sanyaye. Zubaina keta kallan Umar cikeda mamaki da tarin al'ajabi yana fita ya wuce wajen Sarakuna shi da abokin karawar shi suka kai gaisuwa Sarki Abdurrahman sai kallan Umar yakeyi kallan dashi kdai yasan ma'anarsa sannan sukaje wajen su Zubaina wannan karon ita ta dauko farin kyalle tana murmushi ta saki kyallen suka koma filin daga....gimbiya Rahama keta kallan Umar takasa daina kallan shi har saida ta... JAMEEY❣️ Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyanki ta wannan layukan 08160508316/07034464517. Koda Umar suka koma cikin fili hannunsa rike yake da wani irin zareren takobi sai walikiya yakeyi basu wani bata lokaci na suka fara fafatawa shida abokin wasan shi....baki daya mutanen Zairana jinin su na kan hakaifa gani sukeyi kamar Umar zai iya kada su. Wasa yayi zafi inda kowa ke gwada tsantsar iyawarsa da Jarumtar sa saida Jaruman suka kwashe sama da minti biyar suna abu daya...amma abu yaki karewa sai gabzawa sukeyi,yayin da ciwon kai ke dawainiya ds Umar ji yakeyi kamar zai fadi kasa daurewa kawai yakeyi haka sukaita fafatawa cikin ikon Allah Sadauki yasa kirjin shi ya bugi abokin karawar shi take ya fadi kasa wanwar har saida ya wuntsile ya bar cikin layin baki daya....take wajen ya kaure da ihun murna da gudu Jaruman Zairana sukazo suka daga Sadauki sama sai murna sukeyi hatta Sarki Abdurrahman saida yaji dadi aransa...Yarima Aryan kuwa yakasa motsin kirki tsabar mamaki,baki dayan su basuyi zaton haka ba domin duk wanda yaga Umar anayinsa baka taba cewa yasan wani abu Jarumta bare har yakai ga ya kware ga iya sarrafa takobi. Tunda Umar yaci wasa gimbiya Zubaina ke jin dadi ba karamin murna takeyi ba batasan sadda ta riko hannun gimbiya Rahama ba tana tsananin jin dadi,mamakin Zubaina ya lullubeta gashi dai BAWA ne yaci wasan amma sai murna sukeyi akasa zuciyar ta tana yaba yanda Umar din yayi kokari....koda Jaruman suka sauke shi zuwa yayi wajen Sarakuna yakai gaisuwa sannan yaje wajen su gimbiya Rahama yakai gaisuwar girma,dan daga masa hannu tayi kallan sa kawai gimbiya Rahama keyi shiko murmushi kawai yaima gimbiya Zubaina. yata fi zai koma cikin bayi yarima Aryan ya hana shi ya bashi kujera ya zauna cikin Jarumai....Sarki Abdullatib ya tambayi Sarki Abdurrahman."wanene wannan yaron?."shi kanshi saida yayi mamakin tambayar da yai mashi...amma sai ya bashi amsa a takaice"Sunan shi Umar kuma ɗan Sarkin bayin Masarauta ta ne"gaskia yaron nan ya shigar mani a cikin zuciya badan bawan amana bane lallai da ka siyarmin dashi."take Sarki Abdurrahman yaji kishin maganar da abokin shi yai mashi sai yaji bazai iya saida ma kowa Umar ba saboda ya wuce duk wani tunanin shi baki daya"kaga yaron nan akwai nagarta ga Jarumta gashi da kyau kuma dagani yasan darajar nagaba dashi."sake kallan Sarki Abdullatib yayi a karo na biyu sannan ya kara magana a takaice."gaskia ne Umar yana da nagarta saidai kasani tamkar ɗa yake a wajen mu,bacin haka da mun baka shi."shikenan."Basuyi aune ba sukaji ana shelar saka makon wasa da aka gabatar na yau inda Masarautar ZAIRANA tazo na farko,sai Masarautar SIRIKA tayi na biyu,inda Masarautar BAIZAR tayi na ukku,sai Masarautar KESAR ke mara mata baya sai Masarautar ROOWAN ke bi mata sai Masarautar YURII....haka akaita lissafo Masarautu har aka gama kowa ya tafi sai jin dadi sukeyi sai kuma gobe da karfe goman safe zasuci gaba da GASAR...... Tunda gimbiya Rahama takoma daki take mamakin Jarumtar Umar da karfin halinsa duk da gashi bawa,ita dai ranta na bata akwai abun dubawa a cikin lamarin Umar harta kwanta sai kuma ta tashi ta nufi dakin gimbiya Zubaina isketa tayi ta gama tasaka kaya zata kwanta kana ganin ta kasan tana cike da farin ciki marar misaltuwa saboda masarautar su sun lashe gasar farko,sallamar gimbiya Rahama tadawo da ita a tunanin ta."barka da zuwa gimbiyar Sirika."yawwa,yar uwa."bissimillah."ta zauna gefen ta sannan ta fara magana"Ranki shidade har yanzun ina cikin tarin al'ajabi."maida dubanta tayi kaco kam gareta tace."nami nene."? Ajiyar zuciya ta shide a sirrin ce tace."Ina mamakin wannan bawan da ya anshi wasan nan anya shidin ai nahin bawa ne? gaskia yai man kyau da kwarjini da yawa ina mamaki a kan shi har yanzun."wani irin masifaffan kishin Umar ya turnike Zubaina take taji ta tsani yaban da Rahama tai mashi,ita kanta saida tayi mamaki akan me zataji kishin Umar a zuciyar ta?amma saita wayance tace."haka Umar yake akwai shi kwarjini gashi jarumi ne na gaske"amma da gaske shifin BAWA ne."?"Kwarai kuwa shidin cikakken bawa ne."nayi zatan ko siyan shi kukayi."? "Aaa Sarkin bayin Zairana ya haife shi, bawa ne na amana."ɗan rausayar da kanshi tayi tace."gaskia yai mani kinga shi din ba bawan saidawa bane baccin haka dana siye shi"gaskia kam bawa ne na amana."(take takejin kanta a wani irin yanayi tana mamakin yanda idanun kowa ke kan Umar sai taji inama baizo gasar ba)a ranta take sake sake,tabata gimbiya Rahama ta dan yi ganin ta zurma a tunani."lafiya kikai shiru."bakomai."ta dan kakaro murmushi akan fuskar ta da haka sukaci gaba da fira kiran sallar isha ne yasa gimbiya Rahama yima Zubaina sallama sanann tace saida safe,itako Zubaina a lokacin take son ganin Umar kafin ta kwanta.Fadila tasa tai mata kiran Umar tanasan ganin shi...... _Ohh ni🤔 anya gimbiya Zubaina bata afka a tarkon son Umar ba gareku makaranta? Amma taya za'a ace gimbiyar Zairana ta buge da son BAWA??? A bangaren Sarki Abdurrahman ya aika akira mashi Umar koda dan aiken yaje a lokacin suna tareda Yarima Aryan a tare suka taho bayan sunyi sallama akai masu izinin shiga anan suka iske shi da sauran Sarakuna...Sarkin Yurii na gefen Sarki Abdullatib koda suka shigo dukawa sukayi suka kai gaisuwa sannan ya samu waje ya duka kan shi a kasa. Sarki Kabir Usman ne yaketa kallan Sadauki yana so ya shaida shi amman yakasa gane ai nahin inda yasan shi."Umar."a hankali ya dago kanshi yace."Allah yakara maka yawan raibarka da dare"yawwa Umar,ya gajiyar gasa."Alhmdullh"dan gyaran murya Sarkik Abdurrahman yayi yaci gaba da cewa."Kamar yanda kaji kirana dama yan uwana suka ce aikiraka saboda kayi wasa mai nagarta kuma ka birge su ainun."gaskia ne Umar kayi wasa mai nagarta muna maka fatan alkhari Allah yakara hazaka."Amin,Umar nagodiya marar iyaka Allah yakara girma."dan shiru ya biyo baya Sarki Kabir yace."ina mamaki sosai akan yaron nan dagaske shifin bawa ne?"Abokina kenan,Umar amintaccen bawa na ne"ajiyar zuciya yaja yace."Hakane,saidai naso in shaida wannan fuskar"A ina."? Baki dayan suka hada baki wajen tambayar shi"na manta gaskia,ammayaso yai mani yanayi da Sadaukin Burhaan"baki dayan su saida maganar Sarki Kabir ta taba su kowa ya gaza cewa uffan sai kuri da sukaima Umar da ido suna al'ajabin maganar sa saidai sun san Sadauki ya tafi Kasar Mali kamar yanda mahaifin sa ya rubuto masu a wasika."Anya? shima Umar din Jarumin gaske ne,kuma Sadauki ai yayi tafiya."da haka kpwa ga gamsu." "Allah ya bamu nasara."Amin...Umar zaka iya tafiya."Nagode Allah yakara daukaka."da haka ya tafi. Tunda Sarki Abdurrahman yaji an ambaci Umar sunyi yanayi da Sadauki ya kasa zaune ya kasa tsaye ba abinda ke damun shi a halin yanzun sanin ai nahin asalin Umar waye shi?daga ina yake?wane al'amari mutane ke gani akan shi?daga cikin su harda shi karan kanshi!tunda yake bi taba samun bawan da yagaza samun kwanciyar hankali akan shi ba sai akan Umar ganin farko da yai mashi saida ya kokonto akn asalin Bawan taka da akace shidin Bawane a hankali ya koma ya zauna samn kujera ya sauke nauyayyr ajiyar zuciya a zahiri yace."ance Sadauki yaje kasar Mali kai taimako mi zaisa a dinga dnganta Umar da Sadaukin Burhaan!?? Da haka ya watsar da zancen baki dayan shi duk da ya kudurci sai yasa anyi masa bin cike waye ne UMAR!.... Koda suka fita sallama yaim Yarima Aryan yakama hanyar masaukin shi,dan yasan Abba Ado yana neman shi,tafiy yakeyi a nutse kasancewar garin ya yafara duhu sboda wata ya tafara tsufa. Hannayen sa ya goya a saman bayan yaci gaba da takon sa yaji ana kiran shi,a hankali ya waiga yaga Fadila,gaisawa suky sanann ta fada mashi sakon gimbiya Zubaina sai da yaji faduwar gaba ta dirar mashi karon farko da yaji sakon Zubaina ya sashi faduwar gaba badan komai ba saboda baisan me zatace mashi ba,gashi ya gaji da yawa yana bukatar hutawa.a haka ya daure ya bita suka tafi har masaukin ta,sallama sukayi ya tsaya waje,Fadila ta shiga ta fada mata zuwan Umar cewa."ki shigo dashi."angama ranki shidade."bayan fitar ta ta daelwo dashi dauke da sallama a bakin sa ya shigo,samun ta yayi zaune saman dardumar sallah tana tasbihi..tana jin shigowar shi ta bishi da ido harya duka gabn ta ya gaishe ta bata daina kallon saba ta amsawa cikin sakin fuska."ya gajiyar gasa."?sadda kanshi yayi kasa yace."Angodema Allah."murmushi ta sakar mashi du da kans na sadde a kasa tace"Ashe kai Jarumi ne Umar? har Jarumtar ka takai haka."?sai a lokacin ya dago kanshi ya kalle ta ya sake kauda kanshi gefe yace."Allah yakara maki daukaka,ni ba Jarumi bane karambani ne kawai irin na Umar."Umar."ta kira sunan sa a kausashe saida ya sakar mayar da hankalin sa kanta taci gaba da cewa." lallai kai Jarumi ne ,dole abaka lambar yabo."nagode."yace a takaice."Umar."na'am ranki shidade."zanso gobe in Allah yakaimu idan an kammala gasa ina san zan maka wasu 'yan tambayoyi"Allah yasa na sani" ya fada ynajin zuciyar sa na duka kadan kadan."Umar kasani,saboda suna da matukar muhimmanci a rayuwar ka"shikenan uwar dakina,Allah yakai mu lafiya."Amin,zaka iya tafiya."har ya juya zai fita ta kuma kiran sunan sa."Umar."a hankali ya juyo yana kallan ta baice komai ba."ina maka fatan alkhairi,Allah yaci gaba da baka nasara"murmushi ya sakaar mata yace."Amin, nagode saida safe."yajuya ya fita. ______________ Talatu keta waige waige cikin tsakiyar dare hannunta dauke da fitila saida ta tabbatar ba kowa a hanya sannan ta doshi sai sashen Sarki Hamza tana isa ta duka tayi katon rami sannan ta binne wasu manyan layu guda hudu tana gama binne su take kasar ta baje tamkar ba'a taba binne komai tana gamawa da sassarfa ta koma,ta gayama gimbiya Masau'da komai ya kammala."angaishe ki Talatu inajin dadin aiki da ke."ba karamin dadin sakon Talatu taji ba ji take kamar anbata kyautar hajji... shiko Abba Ado koda Umar ya dawo rungume shi yayi sai murna yakeyi saboda shine ya lashe gasar da akasa saboda yafi kowa yin wasa mai kyau da daukar hankalin masu kallo zaunar dashi yayi gefen shi yakara mashi kwarin guiwa,akan yakara dagewa akan gasar da sukeyi sannan yasa shi yaci abinci yayi sallah ya kwanta yana kwanciya yafara bacci ya fara mafarke mafarke mararsa dalili sai kuka yakeyi a cikin mafarkin da sauri ya tashi zaune duk zufa ta keto mashi."lafiya Umar kana bacci kana kuka."ya gaza furta komai sai kallan sa da yakeyi Addu'a Abba Ado yai tayi mashi, shima sai ya samu kanshi da kama addu'ar da Abban shi keyi mashi yana kwanciya baccin ya sake dauke sa,kallan sa kawai Ado yakeyi yana ta'ajjabi yana jin sa ba banza akwai dai abinda basu sani a tattare da d'an sa a hankali ya bushe masu aci balbal dake gefensa tana ci sannan ya kwanta gefen Umar din yai masu addu'a yana ta nazari shima har baccin ya shamma ce shi. JAMILA JAMEEY (Yar Mutan Kankia) Share Pls *SADAUKIN BURHAAN* _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_ A Kingdom Story👑 *NA* *JAMEELA JAMEEY* _(Ya'r Mutan Kankia)_ *BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM* _SHAFIN KYAUTA_ BABI NA ASHIRIN DA BIYU Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyan ki ta wannan layin 07034464517 Shafukan kyauta sun kare domin mallakar naki contact this number 07034464517 kamar yanda kowa ya sani da misalin karfe goma na safe daidai aka fara gabatar da gasar tseren dawakai yau ma kamar kullun an fara gabatar da gasar inda kowace Masarauta suka bada mutun ukku ukku,yayin da Masarautar Sirika ta bada zaratan Jaruman ta guda ukku itama Masarautar Zairana suka fidda gwanayen su hakama ta Kesar,Baizar,Roowan,Yurii da sauran manyan manyan Masarautu. Tsaye suke jere saman dawakai ko wane Jarumi ya hau kan dokin shi.ka'idar wasan za'ayi zagaye huɗu akan doki duk wanda yakai tuta a zagaye na huɗu shine yaci wasan. Batareda bata lokaci ba aka fara fafatawa kowane Jarumi ya dage damtse yana nuna iyakar bajintar shi,gudu sukeyi kamar zasu bar kasar baki dayan su tafiya ce sukeyi mai nisan gaske sukayi zagaye na farko Masarautar Sirika ce akan gaba,a zagaye na biyu Masarautar Kesar ke jan tuta,ana cikin yin zagaye na ukku Aliyu ya faɗo daga saman dokin shi duk yaji ciwuka da sauri masu kula da Jarumai suka rugo da gudu suka dauke shi zuwa wajen da zasu ba shi kulawa. Sarki Abdurrahman ya bada umurni Umar ya fanshi Aliyu batare da bata lokaci ba Sadauki yahau saman doki a lokacin har an kusa kai zagaye na ukku,banda gudu ba abinda Sadauki keyi kasancewar shine karshe sai ba doki wuta yakeyi kamar ba gobe kishin Masarautar shi ya darsu a cikin zuciyar shi,gudun da yake zabgawa bana wasa bane ga wani irin kwarewa da salo da yakeji na fisgar sa cikin kankanin lokaci Sadauki ya zarce kaf Jaruman nan...Ammar kebin bayan shi cikin kaftawar ido Sadauki yakai zagaye na ukku,yana ciro tutar yakaima gimbiya Zubaina tuta,murna da tayi bata misaltuwa yana bata ya juya sadda zai koma zagaye na hudu suma sauran Jaruman har sun harzuka suna san sukai zagayen karshe dama Masarautu ukku sunkai zagayen farko yanzun so ake duk Masarautar data kawo zagayen karshe ita ta lashe gasa.kowa ya zagade basuji basu gani gudu suke bakin rai bakin fama yarima Hashim da Aryan suke tangan,wannan karon Sadauki shine na bakwai, ba abinda yakeji a cikin kunnuwan shi sai kalmar yayana yi sauri yayana! idanunsa ya rufe yana jin zuciyar shi ke bugu da sauri da sauri kamar zata fado kasa kanshi nayi mashi wani irin ciwo kamar zai fita daga kanshi komai ya coshe mashi ya kasa tuna komai sai kalmar da yakeji ta kayi sauri yayana!!kafin kaftawa da bissimillah Sadauki yayi masu fintin kau Allah yaba shi sa'a ya dauko tutar karshe ya juyo da ita a hannun shi baki daya wajen ya kaure da murna tun daga bayi har Sakunan da yan kallo suka hau murna wajen ya kaure da ihu kowa sai murna sukeyi danko Zubaina batasan ta fasa uwar karaba wanda yajanyo hankalin duk wanda ke wajen saida ya juyo yana kallanta. Umar ya isa wajen Sarakuna yakai ma Sarki Abdullatib tuta hannu yasa ya amsa,fuskar shi dauke da murmushi mikama Umar hannu yayi sukeyi musabaha kowa sai murna da farin ciki akeyi sauran Jaruman na isowa suka fara rungume junan su suna taya junan su murna sannan suka koma suka zauna suma zama bada jimawa ba aka fara sanar da sakamako wannan karan sunayen mutane ake kira bana Masarauta ba, alkalin wasa yafara cewa."UMAR ADAM shine ya lashe gasar tseren doki,Ammar Abdurrahman yazo na biyu, sai Hafiz Yunus yayi na ukku,Aryan Abdurrahman yazo na hudu,haka akaita lissafo sunayen Jarumai har akaje ga wanda yayi na talatin,baki daya wajen ya kaure da ihun murna,jarumai suka daga Umar sama sunata murna. Wani irin son Umar ne yakara shiga cikin zuciyar Sarki Abdurrahman yau yakara tabbatar da cikakkar Jarumtar Umar ranar haka akaita farin ciki da murna basu jima ba aka tafi hutun awa biyu. Ammar na komawa yasa aka kira mashi Umar yana zuwa ya bashi abinci da ruwa yasha ya huta. Bangaren Sarki Hamza zaune yake fa'da shida jama'ar shi anata fadanci Sarkin Fada ya iso dan aiken Roowan ya kai gaisuwa sannan ya bada sakon Sarki Abdulbasit Abdulkarim,yana amsa Sarki Hamza yasa aka bashi masauki sannan yasa Magatakarda ya karanta mashi sakon dake cikin wasikar. _Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci fatan sakona ya riskeka cikin aminci,dalilin dayasa na aiko maka da wannan sakon domin in tambayi lafiyar ka data iyalanka kwana biyu banji wani motsi daga gareka ba na damu da yawa yakama ta ace nasamu sakon ka kuma ina zuwa nan da mako biyu insha Allahu,kagaidamin da dukkan zuri'a daga Sarki Abdulbasit zuwa ga Sarki Abduljalal bissalam_ Kallan kallo ya biyo baya tsakanin Sarki Hamza da magatakarda ga fa'da ta cika damkam da mutane fada tayi shiru ba wanda ya iya furta uffan a cikin su,takaici ya cika Sarki Hamza tashi yayi ya bar fadar sanann ya bukaci ganin Magatakarda a sashen shi harya zai fita ya dawo ya kalli Shamaki yace."ka shirya zuwa gobe zaka tabbatar dani a matsayin Sarkin Burhaan."angama ranka shidaede da haka ya fita. ★★★ zuwa yanzun sunfara shawarar yanda zasuyi su koma Burhaan dan su ga halin dasu Ammi ke ciki da dan uwan su,sun jima suna nemawa kansu mafita daga karshe Shattimah yace."zamuje Roowan wajen Nafeesa sati mai zuwa."Allah yakaimu." "Zubaina na isa lambu tasa aka kira mata Sadauki akaro na biyu takai minti Ashirin tana jiranshi ta gaza zaune ta gaza tsaye ji take kamar ta kurma ihu tunda take bata taba jiran wani mahaluki a duniya ba sai Umar tsawon mintoci talatin gajiya tayi da zama ta mike tana fesar da zazzafar isakar bakinta ta juya zata tafi can ta hango shi ya taho cike da nutsuwa yake tako a kame kansa sadde kasa,baki daya hankali da tunanin Zubaina sun koma kan Umar daga nesan take kare mashi kallo mai dauke da tarin shauki yayin da kwayar idonta ke fitar da tsantsar begen sa zuwa ruhinta bata kara tabbatar da zatan ta akan Umar ba sai yanda taga yana tafiyar sa kamar wani ɗan basarake ita dai tasan koda Umar yana bawa ya dace da rayuwar ta da tsarin ta yanzun ne takara tabbatar da Umar shine mijin data dade tana tsumaye mijin ta alakanta dukkan burin ta na duniya akansa mijin daya jima a cikin ruhinta mijin datayi imani shine ta jima tana jira yazo a cikin rayuwar ta....lallai kam idan har abinda takeji game da Umar shi ne SO ya tabbata ta fada a tarkon SON Umar tarkon da bataji zata uya fita cikinsa zuwa yanzun tayi nisa akan son UMAR batajin zata iya rasa shi kuma zata iya komai akan shi harya iso gabanta bata san ya karaso ba kuma bata daina tunanin data lulaba hasalima batasan ya ison ba. A nutse ya dukawa ya gaisheta cikeda girmamawa."barka da wannan lokaci,Allah yataimaki Uwar dakina." kuri tayi mashi da manyan idanuwan ta masu tsananin haske da daukar hankalin wanda aka kallo baki daya hankalin ta na kanshi takasa daina kallan shi labban ta sun mata nauyi ta gaza amsa gaisuwar shi,har saida yakara maimaita gaisuwar da yai mata akaro na ukku sannan ta amsa,tana shide ajiyar zuciya. Cikin takun kasaita ta koma ta zauna saman shimfidar da aka tanadar mata. izinin zama tayi mashi daga gefen ta saidai yaki zama saida yaga baccin ranta sannan ya zauna badan yaso hakan ba."Umar."yaji ta ambaci sunan shi a sanyaye da sauri ya dago kansa take idanun su suka hadu dana juna,kallan ta kawai yake yanda ta furta kalmar Umar cikin wani irin salo marar misaltuwa ya amsa da."Na'am,Allah yaja da ran Uwar dakina barka da hutawa"cikin wani irin amo yayi maganar da muryar sa mai sa zuciya natsuwa."ajiyar zuciya ta shide tace."yawwa Umar."dan shiru ya biyo baya kowa ya gaza furta komai tarasa ta ina zata soma magana shi kuma yayi shiru ne yana jiran yaji umurnin ta saida ta nisa sannan tace."A gaskia Umar ka cancanci kowane irin yabo ka kara tabbatarma duniya waye kai ka kara tabbatar ma Masarautar Zairana kaidin Jarumi ne gaskia Umar ka cancanci abaka lambar yabo kuma ajinjina maka a maidaka Sarkin Jarumai bana Zairana kadai ba idan na kiraka da Sarkin Jaruman Afrika banyi laifi ba saboda kacancan ta,inaimaka fatan alkhairi"dan murmusawa yayi wanda ba lallai bane agane yayi sa ba yace."ina godiya Uwar gijiya ta,Allah yakara daukaki"hmmm...Umar kenan,ada ya daace ka dinga yi mani kallan uwar gijiyarka ba yanzun ba."a hankali ya dago kanshi ya kalle ta yace."ranki shidade...saidai ban fahimce kiba."? "Hakane Umar nasan bazaka fahimta ba,idan na kiraka da Jarumi,gwarzo kuma Sadauki ai ina ga banyi laifi ba ko."? Tunda Zubaina ta ambaci kalmar Sadauki baki daya numfashin Umar ya fara halbawa da sauri da sauri,kanshi ya kulle kam baki daya yarasa mike mashi dadi a rayuwa"Umar."ta kuma kiran shi muryar ta na rawa rawa,sake kallan ta kawai yayi baice da ita komai ba,cigaba da cewa yayi."daga yau sunan Sadauki da kai ya dace."saboda mi."?ya samu kanshi da tambayar ta kai tsaye."dan murmushi tayi tace."Saboda ba'a Sadauki raggo kuma duk mai sunan Sadauki kowa yasan Jarumi ne na gaske,kalar Jarumi irinka bai dace da kowa ba sai da gimbiya Zubaina"hannayen sa yasa baki daya ya dafe kansa yana kallan ta cikeda mamaki bawai mamakin maganganun ta yake ba Aaa yanda take koda shi tana kai shi matsayin da baikai ba."ya kayi shiru Umar."rausayar da kanshi yayi kamar mai tunanin wani abu yace."Allah yai maki yawan rai,kamar yanda kika sani tun asali Umar dai BAWA ne kuma duk wani halin jarumta anahin tama bansan yanda ake yin ta ba,kuma duk abinda kikaga nayi wajen gasar nan bawai iyawata bane daga Allah."nasani Umar du da haka dole ka amsa sunan Jarumai."wannan karonhar ya kosa da maganganun da take mashi baki daya ya gaza gane kansu yanajin ta ne kawai bawai dan yana fahimtar taba kanshi ya coshe ya gaza banbance komai."shikenan saidai kisani duk wannan abun ba gwanintar Umar bane sa'ar ubanjine, ki gafarce ranki shidaee bai dace kina kiran Umar da sunan Jarumai ba kai tsaye ba sunayen Sadaukaiba ba cancanta a gareni ba lallai kam matukar kinayi mani wannan inkiyar zan iya shiga damuwa,kisani Umar ba kowa bane face BAWA marar 'yanci wanda baida kowa dai mahaliccin shi......Bata bari ya ida maganar da yakeyi ba ta daka masa uwar tsawa"Umar!"ta kira sunan sa zuciyar ta ba halbawa kamar zata faso daga kirjinta ta kutto kasa."kada na kara jin bakin ka ya furta kalmar rashin 'yanci a gareka! kai mai 'yanci ne Umar koda ka kasance bawa a idon duniya to kasani a idon gimbiya Zubaina kai ba bawa bane Umar,kafi karfin a kiraka da bawa,kuma ya zama dole ka amsa sunan Sadauki daga yau in dai ni zan kiraka ya zama dole ka amsa sunan Sadauki."yanda ta ida maganar zaka tabbatar da irin zafin da zuciyar ta ke mata shidai bai sake ce mata komai baki daya zancen ta sake hargitsa sa takeyi kansa na kara masa nauyi duk sanda zata kira shi da Sadauki,zaune yake gafenta kawai yana sauraron ta."Umar."ta kuma kiran sunan shi a raunane cikin wata irin siga mai wuyar fassara. "a yau na kara tantance abinda nikeji a akan ka,basan taya zan fara shaida maka abinda ke raina ba."maida dubansa yayi akan ta ya ga tsantsar damuwar dake kwance a saman fuskar ta sai ya samu kansa dajin tausayin ta yace."mike faruwa,mike damunki."bakasan abinda ke faruwaba ko Umar? "Allah ya huci zuciyar ki ban san abinda ke faruwa bako"Inason ka kara bani aran hankalin ka Umar kuma kasa idanun kacikin nawa."shidai kallan ta kawai yakeyi."Umar"ta sake kiran shi,ya amsa atakaice "Na'am."ya maida kansa kasa."ina SON ka Umar."a razane ya dago kansa ya kafeta da firgitattun idanun sa ya gaza furta uffan baki daya kanshi ya juye mashi har juwa take neman dibar shi daga zaunen da yake,rumtse idanuwan sa yayi ya kuma budesu samn kyakkyawar fuskar ta yaja numfashi ya fesar yace."ban fahimce ki ba."INA SON KA."ta sake maimaita mashi da dake itama tana kallansa take ya mike tsaye itana mikewar tayi dukkan su sun kasa furta uffan ita tana sauraron amsar shi,shi kuma kansa ke sarama shi numfashin shi na sarkewa maganar uwar gijiyar shi ta firgita duk wani tunanin shi ta hautsina shi taya za'ayi ace gimbiya Zubaina kamar gimbiyar Zairana ta furta kalmar SO ga bawa kamar shi! bawan ma bawan ta sannan hadimin ta."Baka ce komai ba Umar."juyo yayi daga bayan daya bata hannayen sa sarkafe da juna ya goya su saman bayan sa ya sake kallan ta yace. _______________ Anan na kawo karshen shafukan kyauta na wannan labari gamai bukatar son ci gaba da bibiyar wannan littafi ka/ki hanzarta biyan kudin ku domin ayi tafiyar nan daku, saboda tafiyar nan ta daban ce kuma ta musamman ce akan naira (300) kunji yanda salon sa yake yanzun aka fara wasan inada yakinin zai nishadantar daku zai fadakar daku harma ya wa'azantar daku da izinin Allah. *Akwai grp na maza dana ware maku saboda kuma kun karbi wannan labari zaku cigaba da payment sannan zaku turo shaidar biyan ku ta number da zan bayar* Ya kuke ganin wannan labarin zai wakana?Ga gimbiya Zubaina ta furta kalmar so ga bawan ta Umar kuna ganin zai karbi soyayyar ta?? sai yaushe ne Umar zai dawo cikakken Sadaukin sa?Sadaukin ma na Burhaan??Ya labarin Sarki Abdurrhaman ya zai dauki bukatun 'yarsa? Ya kuke ganin karshen azzalumai zai kasance a cikin wannan labarin?kada ku manta tun daga Izzah ko Mulki kuka ji yanda abubuwa suka wakana har zuwa Sadaukin Burhaan kunsan dai shine jigon labarin,hmm garin dadi na nesa.... _Domin mallakar naki tura shaidar biyanki ta wannan layin 07034464517,acct details 0777512438,Jamila Abubakar Bello,Access Bank._ *Send ur evidence via this number 07034464517,kada ki turo ta wannan layin 08160508316.saboda layin zai kasance kasa...siyen nagari maida kudi gida.* _Yar Mutan Kankia ce❣️_ Share Pls *Kada kifitar mani da littafi waje Sadaukin Burhaan na kudine akan naira dari Ukku domin karin bayani tuntubi wannan layin 07034464517* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels