An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KWATAR KAI 1 NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA Godiya tatabbata ga Allah dayasake hadamu acikin wani sabon littafin,tsira da amincin Allah sukara tabbata gashugabammu Annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidan sa baki daya, Wannan littafin kagaggen labarine ,bawai yafaru akan wani kowata bane,aa kirkirarsa nayi, GARGADI!!!!!!! Banyadda ajuyamin wannan littafin tawata sigarba harsaida izinin marubuciyar. ******************************** Assalamu alaikum,yayi sallama tare da dage labilen dakin yashiga. Tana zaune bisa kujera ta amsamai,babu yabo babu fallasa,yasamu wuri yazauna gefenta. Tayimai wani irin kallo,shima yakalleta sannan yasadda kansa kasa,yace Suwaiba yayada Tace damefa? Yace nagane kinayimin wani irin kallo,kamar kinga Mara gaskiya. Takara maida hankalin ta sosai akansa,tace yo aiganinayi kashigo dakina yanzun,kumani banga amfanin yin hakanba. Yakalleta cike da mamaki,yace yaufa kwanana TALATIN kenan dayin aurennan,kuma inaga aikamar iyakar kwanakin dakikabani kenan ko?naga suncika shiyasa nadawo gareki yau. Takalleshi ayatsine,takauda kanta,wani takaici yakara isarta,takuma daure cikin rashin damuwa tace:yo har kwanakin suncika?ninaga sunyi sauri. Yayi dariya yace suncika mana,yaunake dawowa dakinki,ai iyakar abinda dama kikabani kenan,kuma aikinga baikamata........... Tadaga mai hannu tare dafadin kaga! Dakata Nasser!batambayarka nayiba!nadai baka abinda kakeso,kuma burinka yacika,kayi Amarya!nayarje maka kaje kayi WATA GUDA adakinta,kuma kayi to magana tame?aiba tambayarka nayiba. Yace AAh !toaini sainaga rankine kamar bayadda nasaba ganinkiba,kuma yau nadawo dakinki,tsawon lokacin danadauka awurin Amarya,yau kuma nadawo wurinki,aikamata yayi inganki kina fara'a,da dokin ganina,kema kizama tamkar Amaryar. Tace niasuwa!!aibankai wannan matsayin awurinkaba,Nasser danakai wannan matsayin awurinka!kanajina kamar Amarya,dabaka dauki tsawon kwanaki TALATIN awurinta baka waiwayeniba!kobanza nasan waceceni awurinka!nasan matsayin daka ajiyeni!kabullomin ta hanyar da Amaryarka zata rainani!domin tasanniba komai bace awurin mujina!kuma kasiyoma kanka rashin zaman lafiya agidanka!! Yace:to dakata suwaiba,nagane inda kikadosa,to amma kuma naga ai kwanakin nan kekika dibarminsu baninadiba dakainaba,kekikaga Dama kikabani,kuma nayi,tomiye kuma abin tashin hankali aciki? Tace:kuma kayi??saboda bakasan darajar matarkaba !kayi watsi da ita tsawon WATA GUDA,saboda kayi Amarya! Yace Toni miye laifina aciki? Tace aibazaka ganiba!abinda idanunka sunrufe!baka ganin kowa sai Amaryarka!!taya za'ayi kaga kayi badaidaiba?aikomai kayi da ita daidaine! Kawulakantani!!!kabiyomin ta hanyar da Amaryarka zata daukeni babakin komaiba!!tunda har mujina zai iya watsidani NA tsawon wani lokaci,batare kuma daka damuba!kaga kenan dani da banza duk dayane!!! Yace suwaiba inda nasan Karin kwanakin dakiyimin zaizama haka dabanyiba,danasan ranki zai baci akan cika umarnin dakikabani da banyiba,amma tunda hakan tafaru kiyi hakuri,abarshi komai yawuce,imma kuskurene nayi tona dauka,don Allah kiyi hakuri. Tace aidama iyakar abinda zaka bani kenan,nikuma kacuceni kacuci banza!!to kakwana da sanin cewa,idan aka kasa samun zaman lafiya agidanka daga irin rashin adalcinkane!! Yace in Allah ya yadda bama abinda zaifaru,sai zaman lafiya,ai Hauwa'un tanada hakuri Tace batambayarka nayi halintaba!nidai inta kawomin raini,adalilin abinda kayimin bahakura zanyiba. Yace abar maganar,Uwar guda sarautar mata!duk yadda kikeso aihakan za'ayi,mulkin gidanfa ahannunki yake,bawadda ta isa takwace maki wannan sarautar,duk yadda kikabi dagidanki ahaka za'abishi,wane umarni zaki bayar kuma yanzun?yafada acikin wasa tare dashafo fuskarta. Bayan kwana biyu ,suwaiba nazaune tare da kawarta FARIDA,wadda takawo mata ziyara,sunata fira. Suwaiba tace:kenifa Farida gaba daya shawarar dakikabani banji dadintaba,hakanan abanza kinsa naba mujina damar yayta kwana dakin Amaryarsa harnawani lokaci,amma bawani abinda yasauya,sunason junansu haryanzun,kuma kekikacemin inbasu lokaci sugama dokin juna tukunna,sugundiri juna,ammani banga alamar hakanba,nabasu danata abanza!!! Farida tace banganeba?kinanufin kice suna dokin junansu haryanzun?to wannan wace irin mayyar kishiyace kikasamu? Toni bari kiji,hakanayima mujina,acikin sati biyu sunfara gundurar juna,saigashi inakallo sukafara tashin hankali,da fadace-fadace,intakaice maki auremma baije ko inaba,dole angulu takomo gidanta natsamiya,muka dawo mukazauna dagani saishi. Suwaiba tace Toni dai wannan shawarar taki batayimani amfaniba,kedai tayimaki,ammani batauiba,don haryanzun rawar kai yake da Amaryar nan,tun INA danne kishina harnafara gajiya,wai dama haka Namiji yake idan yakara sabon Aure?kiga dake da babuke acikin gidamma duk daya,gaba daya idonsa yarufe bayaganin kowa sai Amaryarsa,wallahi Farida na yadda idan mace bata danne zuciyartaba,alokacin damujinta yakara sabon Aure,zata iya kashe nata auren,domin kuwa wani rawar kai zakiga yanayi tamkar baitaba aureba sai akanta,wani abimma idan sunayi tamkar basa ganin idon kowa akansu. Farida tace shiyasa Nina danaga mujina yafara wannan rawar kan saboda yayi Amarya,saina barmashi ita,nace yaje yayta zama daita nawani lokaci yagama dokin sannan yadawo gareni,amma inkika cika shigemasu ranki kullun baci zairikayi,gara inya gama dokin yadawo gareki,kinga saiku zama dai dai. Humf!!suwaiba tayi ajiyar numfashi tace:kedai kinyi nasara,ammani banga alamaba,kullun suna manne dajuna,Farida nayi hakuri sosai nakauda kaina ,amma duk dahaka suna cikani!!! Baburina inkoretaba,amma sonake muzama dai dai nida ita awurin Nasser ,wannan kirinkin dayakeyi akanta yaisheni!!waiyaushene zamu zama dai dai nida itane????? Farida tace kikarayin hakuri,kibada wani lokaci,kigani komai zaiwuce,saikin kara kauda kanki. Suwaiba tace niwallahi gabadaya Nasser ma mamaki yakebani,kiga mutum kamar bashiba,nabashi KWANA TALATIN,amma kodan irimma jayayyarnan bayyiba,wai misalima yace yaya za'ayi inje inyi wadannan kwanaki adakin wata,aibai kamataba,ingaya maki Farida saiyayi mursisi,yaje yayi,kidamuwa bayyiba,harda wanuyimin godiya ,to idan yarinyar nan tarainani! acikin gidan nan,zaiga tashin hankali !!!domin kuwa shiya jawosa!shiya zubarmin da kimata a idonta. Farida tace Ah!gaskiya baikyautaba,domin. Koni danacema mujina nabashi kyautar kwanakina yaje yayi shi adakin Amaryarsa gaskiya saida yaja,Nina kafe nace saiyayi,tokinga aikasan ankulaka,amma kawai daga cewa kaje kayi shikenan kamar dama kanajira,bawata jayayya,gaskiya bayyimaki halacciba,amma bakomai watarana sai labari,Nina tabbatar maki nan gaba saikun zama dai dai,amma saikin. Shanye damuwarki. Suwaiba tace to aishine Abu maiwahala,nagaji! Farida nagaji!!!bazan iya ganiba,kibarni dashi kawai,tundashi baisan Alkunyaba,saimunyi fito na fito dashi ,kafin mudai daita. Misalin karfe Tara nasafiyar ranar Asabar,yayi shirinsa tsaf!,zaifita,tataso dasauri tanufo wurinsa,tare dafadin fita zakayi? Yace:e fita zanyi wani Abu? Tace dama inaso zani gidammu,ko inshirya saika saukeni? Yace yikiyi sauri kada kibatamin lokaci. Tace to shikenan,sannan tayi sauri tashirya tafito,tabiya tayima Hauwa'u sallama,tare dafadin zamu fita,,sai mundawo Hauwau tace saikun dawo,takalli Nasser tace love bye bye kadawo lafiya Allah yatsareminkai,sannan takalli suwaiba tace Aunty saikun dawo. Suwaiba tace Allah yasa,sannan suka fita,acikin motarsa sukashiga,yaja suka fara tafiya Yace kinsan wani Abu suwaiba? Tace saikafada. Yace:Abokina Ibrahim na funtuwa shine yake gayamani zayyi aure,watanni uku masu zuwa. Tace ikon Allah komai da lokacinsa,saiyanzun zayyi aurefako? Yace:e saiyanzun Allah yakawo lokacin,kingakenan inada biki. Tace kwarai kuwa kaga saikatafi da Hauwa'u,itace bata taba zuwa funtuwaba. Yayi dariya yace itama wannan maganar tayice koko? Tace wane irin tayi kuma?dagaske nake katafi da ita. Yace to ai inagudun kada amaimaitane,halinnakune na mata saiku,kuzakuce ayi Abu kuma daga baya yazo yadameku. Tace:toaini gaba daya Nasser mamaki kabani,daga cewa jekayi wata daya,shikenan ko gaddama bakayiba kaje kayi abinka hankalinka kwance. Yace toaini nasha irinhalaccinnanne naku namata kikayi Mani,ganinke shekara Hudu muna tare dake,shine kikatausayamata kikabata wadannan kwanakin,shiyasa banyimaki gaddamaba, To yanzun kuma ga tafiya tatashi,kince intafi da ita,kinga aidole insan kyautar taki iya bakice koko har zuci? Tace dagaske nake kutafi . Yace a'a duk wadda aiki yafada kanta ranar da ita zani,shikenanko? Kafibtakarayin wata magana wayarshi tayi ringing yasa hannu yadaga. Hello babyna yayadai? Tace love yaya hanya? Yace hanya gatanan munatabi,kinfara missing dinako? Tace aiko kamar kasan abinda zan fada maka kenan. Yace tokiyi hakuri kinji,yaumuna tare,indai nine ki kwantar da hankalinki,zandawo dawuri,duk abinda kikeso dani kinga saikiyi,yayi kissing din bakin wayar tare da fadin bye kijirani inanan dawowa. Sannan ya yanke kiran,tare da kara maida hankalin sa abisa titi,yace wai haryanzun bamukai bane? Ita kuma datake gefensa zaune tariga tagama cika makil tace: Aiwai dama Nasser kaiya irin wadannan kalamanni bansaniba?waikokadauka kai kadaine acikin matar nanne? Yace wani Abu kuma nayi? Au!bakamasan abinda kayiba?tobari infito maka a mutum!!Nagaji!cin kashin karen dakukeyimin kaida Amaryarka ya isheni!!! Waini meka maidanine?dani da babuni duk daya!!kainifa nalura tunda kakara aurennan dokinnaka yaki karewa!adadin kwanakin dana Baku yatafi abanza kenan??tunda abin yakici yakicinyewa!!to gaskiya nibazan iyaba!!! Yace yakikeso ayi? Tace saukeni anan nafasa tafiyar!domin tafiya dakaima ba abinda zai haddasamin banda bakin ciki!kasaukeni nace!tafiyar nafasa!!!! Yaja jirki yatasaya tare da kallonta yace waini suwaiba narasa abinda yake damunki,gaba daya kincanza. Tace nicema nacanza?kaibakaga irin canzamin din dakayiba!aikaine kafara canzawa,nima nazame maka haka,kuma muddin badawowa kayi yadda nasanka daba,to haka zakaita ganina nima babu ranar dazan canza!!Aida bahaka kakeba!aurennan dakayi shine yadabarbartaka!!kuma indai bazaka dawo yadda nasankaba to haka zamuyita zama dakai!!babu ranar canzawa! Tabude marfin motar tafita dasauri,tare da tare mai adaidai ta tahau yajuya da ita gida. Shikuma yana zaune yadorakansa akan sitiyarin motamar,yana tunanin irin wannan hali na Suwaiba ,shidai yasan sanda yake Neman aurennan dagoyon bayan ta akayishi,amma yanzun gaba daya tacanza,bata taba nunamai wani bacin rai ko rashin yadda sanda yake Neman aurennanba ,saiyanzun da Amaryar tashigo gida,kodadai haryanzun bata bude baki tacemin aurenne batasoba to ammani miyene na Abu akan saitahau ?shima yana nufin kishi take daitakenan?kodani bantaba ganin ko sa in sa tashiga tsakaninta da Hauwa'uba,suna zaune lafiya ,to ammani meyasa takeyimin haka?wane hali nacanza matane??? Tagirgiza kansa,tare dajin tafiyarma duk tasiremai,don haka yajuya kan motarsa shima yakoma gida. Dakin suwaiba yawuce,yasameta zaune tayi tagumi da hannayenta,hawaye naci gaba da gudu afuskarta,gabanta yazo yatsaya tare dafadin. Innalillahi wainnailaihirrajiun!Suwaiba menayimaki?miyekikaga nacanza maki?Wanda ada nakeyimakishi,yanzun kuma nadaina?menene yake tadamaki hankali gamedanine? Tadago kai takalleshi idanu jajur tace:baikamata kayimin wannan tambayarba,yaya zakudaukeni sakarya dakai da Amaryarka sannan kazauna kana tambayata!inba wulakanciba aitasan inatare dakai dommiye zata kiraka?Kai kuma kasaki jiki kana fadamata wasu kalamai dani tunda nake bantabajin sunfito daga bakinkaba,ai abinda kukeyimin baro-baro yake afili,kaimakasani,basaikatsaya tambayataba. Yace to intakirani ba matata bace? Tace dama haka nakeso kafada!!yadda akaraba kwana,maganarma zan iyasawa Araba!!irin wadannan maganganun tahakura inkun shiga daki can kuyi abinku!amma ba'agabanaba,wannan aicinfuskane!!!taya za'ayi inajinka kana fadamata kalamai wadandani tunda nake bantabajin kafadamani irinsuba!bammasan ka iyaba,sai kawai dalilin ka kara sure saika bijire kacanza dabi arka da halayyarka!!dommiye hankalina bazai tashiba,? Yatsugunna gabanta tareda dafa kafafunta,yace:kiyimin uzurin abinda zaifito daga baki na yanzun,yace wallahi suwaiba haryanzun nakasa gane laifina awurinki,saboda duk abinda nakeyi ganinake dai dai nakeyi,banayin kuskure,amma kuma ban fahimci manufarkiba. Tayi saurin ture hannunsa daga jikinta,tace: aibazaka fahimtaba Nasser!soyayyar Hauwa'u tarufemaka idanu,baka ganin kowa sai ita!itakadaice 'yar lele awurinka,itakadai kakenunama tsantsar soyayyarka agareta,nikuma shikenan kagama yayina!!! Humf!yayi ajiyar numfashi,tare dafadin,meyasa kikeso kifitomin da tsantsar kishinki ta haka?meyasa kike dafani da ruwan Dana kasa fahimtar na sanyine kona zafi?karki manta suwaiba,babu Wanda ya isa yaci zamaninsa sannan yaci nawani,shekara Hudu mukayi nidake muna soyayya,dommiye ita don taxo tayi na WATA DAYA rak!zaki tada hankalinki?kuma naga wata dayannanma aike kikabani shi,bada niyyar kaina nayishiba. Tace nasan haka saita faru!waimeyasa kodayaushe Ku maza Azzalumaine???kai tsakaninka da Allah abinda kakeyima Hauwau a yanzun shi kayimin ada? Yace harwandama yafi nata nayimaki. Tace Toni bansaniba!kuma ban ganiba!ai abinda kuka iya fakewa dashi kenan?dazararkun kara sabon aure!sai kuyita wulakancinku darashin kunyarku agaban matanku,idan mace tanuna ranta yabaci,sai kuce Aida itama anyinata,haka,kuma naga Aida tawuce!inkuma ka isa KATARIYOTA tadawo baya!! Yace to nadai gane manufarki,yanzun kwanakin dakikabani nayi adakinta,sunesuke damunki?toko maida makisu zanyi inkashe wannan wutar? Saijin muryar Hauwau sukayi tadago labilen dakin,tare da fadin: Dagabaya kenan!aiwadannan kwanaki tariga tayi asararsu!inbanda karamin tunani irinnaki,tayaya donkinbani kwana TALATIN da mujina zai gundureni?aisaidai mukara son junanmu! Idan kuwa har Uwar gida zatayi tunanin tadauki kwanakin ta tabama Amarya waidon su gunduri juna ,totayi kuskure!ita meyasa tsawon shekarun dasukayi da mijinta ba sugundiri junaba?sai watace datake sha sha sha!!zata gunduri mujinta?!Toni da Nasser daram dam!!soyayyama bakiga komaiba, Yayi saurin dakatar da ita tare da dagamata hannu cikin tsawa yace:kifita!!kifita nace!!mema yakawo ki dakin? Suwaiba tace barta ta idasa abinda zata fada,koma miye nikai kajawomani!tadakatadimme?bayan tagama fadin abinda zata fada!!komadai nikai kajawomani!kaika fara zubarmin da mutuncina awurinta,shiyasa tasamu damar abinda take gayamin yanzun!!laifin gaba daya nakane!kaika bullo da hanyar da gidanka zaikasa samun zaman lafiya!saboda wallahi kaiba ADALUN MUJI BANE!!!kagama tozartani awurin Amaryarka!tunda hargashi tasamu damar datakeyimin labe. Hauwa'u tace:nibazan iya baki mujina yayi kwana TALATIN adakinkiba,kidai dauka cewar wadancan kwanakin kinyi asararsu,tuna........... Nasser ya katseta tare da turata waje,yace:fita da Allah!wayema yasakoki cikin maganarmu?yakoreta tabar dakin,sannan yajuyo ga suwaiba,yace:aiga irintanan!gashi nan.......... Tace kada kakatayimin magana!fita kaima!!kafita kabarmin daki!!niyanzun ba abinda zaka gayamin insaurareka!!! Yace:amma ai.............. Tace kafita nace!!!!! Cikin fushi yabar dakin,itakuma tazauna wani irin matsanancin kuka maisauti ya kwacemata. Afusace yashiga dakin Hauwau yana fadin,waiwane irinneman fitinane wannan?yakukeso kumayar danine?meyakaiki dakinta Alhalin kinsan inaciki?wane irinneman tashin hankaline was nan?? Takaraso inda yake cikin sanyin jiki,tace: My love bahakabane,takama hannayensa cikin shagwaba tace:,kwantas don Allah,samu wuri kazauna kaji. Humff!yayi sassanyar ajiyar numfashi ,tadago ido takallai cikin fari,sannan tajawoshi tazaunar dashi bisa kujera.tace: Nasan kumfita,amma bansan dawowarkuba,shine naji hayaniya adakin,koda naje kofar dakin zan shiga sainaji kana cemata. To nadai gane manefarki,yanzun kwanakin dakikabani nayi adakinta sune suke damunki?toko maida maki suzanyi inkashe wannan wutar?? Tobansan sanda naji hankalina yatashiba,domin kuwa babu abinda natsana irin kayi nesa dani,inayimaka wani irin sodaban iya nisa dakai NA tsawon sati guda,to amma sai injikana zancen zaka maida mata KWANA TALATIN,gaskiya nibazan iya wannan hakurinba. Yace hakane,amma inaso kifahimta,wannan matsalar bataki bace,tsakanina daitane,batasakaki cikiba,kifita harkarta,babu ruwanki,rigimarmuce nidaita,karki karasa bakinki,tunda take tashin hankalin ta bata tabasakokiba,kinsan kotunyaushe muka fara wannan rigimar ?tunda bata sakaki cikiba INA abinda yadameki?karki kara nagayamaki!! Tace to shikenan Yace tashi muje ki bata hakuri,domin banason rigimarnan tahada dake. Tadanyi jimm!!sannan tace to muje,suka tashi sukanufi dakin suwaiba, Azuciyarta tana fadin ,badon itazaniba,dondai kawai incika umarnin mujina,koba komai zaikara yadda dahankalina,yakuma kara sona amatsayina nameyimasa biyayya,inkuma kara saima kaina daraja awurinsa . Yana gaba tana biye dashi har kofar dakinnata,ya bubbuga dominkuwa tarufeshi GAM!! Yace suwaiba kibude!tareda bubbuga kofar,kubude suwaiba!!! Tace bazan budeba!!saboda babu abinda zakagayamani yanzun !!!!abinda dai kakeso aikayi!don haka katafi kabarni inji da abinda yake damuna!!! Yace kibude kiji abinda yakawomu mana! Tace bazan budeba!!bana bukatar jinkomai daga gareku!!! Yajuya yakalli Hauwau yace tojeki shikenan. Axuciyarta tace Alhamdulillahi!dama haka nakeso hakanan kawai asa inje inwaniba kishiya hakuri,garama dataki budewa. Afili kuma tace:toshikenan love muje ai anjima nanan,sai inbata hakurin. Yace kirabu da ita kawai,kardai kikara shiga tsakanina da ita,kinjiko? Tace to shikenan,in Allah yayadda za'akiyaye. Data gaji dakukanta,saita lalubi wayarta takira Farida. Hello Farida yau anbatamani rai!!kishiyata waitake gayamani nayi asarar kwanakina! Farida tace garinyaya? Suwaiba tace waiharni take cema soyayyama banga komaiba!!wallahi farida laifin Nasser ne kawai!!shine yabata damar tayimin hakan. Farida tace waime yakawo tagayamaki hakan? Suwaiba tace:Nasser ne yace zai maida Mani kwanakina,sabodayaga hankalina yaki kwantawa. Farida tace toke meyasa kika kasa kwantar da hankalinki?abinda yawucefa yariga yawuce,saikuma adubi gaba,kiyi hakuri kawai ki kwantar dahankalinki,wata rana zakiga abin yawuce kamar ba'ayiba. Suwaiba tace tayaya za'ayi hankalina yakwanta farida?kinji yadda suke magana harwani suna suka sanyama junansu,ninaga iskancinnasuma bakarewa yakeba! Farida tace tokema basaiki sanyamai sunanba. Suwaiba tace don tace inagasa daita?kenifa Allah nema yataimakeshi badakinayakeba,yauda saimun kwana tashin hankali!amma bakomai zaidawo ai!! Farida tace kafin yadawo dakinnaki kinhuce,don Allah kirika danne zuciyarki suwaiba,bakomai kedamunkiba ki shine kawai,amma kiyi hakuri komai zaiwuce. Humff!!suwaiba tayi ajiyar numfashi tace:to shikenan sai anjima,nagode. Harmisalin karfe goma sha biyu darabi nadare,yana zaune afalo,tunanin halin matarsa dakuma mene yasauya mata hali lokaci guda,kuma duk iya tunanin sa akan yagano wani Abu dayakeyimata Wanda badaidaiba yakasa. Shimmenakeyima suwaibane?bahaka takeba da,meyasa tasauyamin yanzun?wane laifi nakeyimata?duk yakasa samun amsoshin tambayoyinsa. Kumani a iya sanina Hauwau mai biyayyace,tana batagirmanta suna kuma zaune lafiya,Toni meyasa takeyimin haka?saboda nakara aure kawai??meyasa suwaiba take dafani da ruwan Dana kasa tantance na sanyine kona zafi?metakeso inyimatane tagane inasonta?tagane haryanzun yadda take acikin zuciyata bata canzaba,tasancewa....................... Kamshin turarentane yafara katsemai tunani,yadago dasauri yana kara kallonta,tayi shirin kwanciya bacci,jikinta sanye da kana nan kayan bacci,Wanda duk sukafito da ainihin halittata afili,sai kamshin turare dayake tashi ajikinta,. Takaraso inda yake anatse,shikau idanunsa NA kanta, Hannayensa tafara kamawa,tace love baka saba kaiwa wannan lokacinba,meke faruwa?miyene yakeso yahanamin mujina bacci? Yajanyota yazaunar da ita kankafafunsa. Yace:Afuwan babyna,bawani Abu daya isa yadaga Mani hankali idan inatare dake,domin kuwa keme share hawayenace acikin kowane irin hali,inayina sauran maza Addu'ar samun mace mai kyawawan hali irinnaki,domin kuwa duk Wanda yayi dace dasamun mace irinki yagamayin kuka,I LOVE YOU Hauwa'u,yayimata kiss a kumatunta. Tayi dariya tare dakara narkewa ajikinsa,tace to muje kayi wanka kakwanta hakanan,kaga dare yayi. Yayimata wani irin kallo cike da tsantsar sonta acikin idanunsa,yace to zakiyimin wankanko? Tace to wannan kuma aiba sabon abubane. Sukayi dariya baki daya,tare dashigewa uwar daka,yana sabe da ita akafadarsa. Haka yakasance cikin samun kulawa,a kwanaki biyunnan dayayi adakinta,tana nunamasa tsantsar soyayyar dasai kayi tunanin ma yadda take sonsa shibayama sonta haka,nankau tsabar iyakula da mujine kawai. Misalin karfe biyar nayamma yashiga dakin suwaiba,yanayin sallama saiyafara kwalamata kira,dacewa Sweety!Sweety!!kina inane kifita mana,yakara tura kansa cikin dakin,tare dakara nabatawa haba Sweetyna saikace bakowa? Kafeshi da idanu tayi cike da mamaki,tayi sororo tana kallonsa. Yace AAh!waidama kinajina kikayi shiru? Tace yo aibansan dani kakeba,yau kuma wata sabuwar yaudararce kabullomin da ita. Yace yaudara kuma? Tace yoto aini bantaba jiba,yau kasanyamin wannan sunan kuma? Ya kyalkyace da dariya,yace to aikinji matsalar taki,ko sunanma baki iya amsawa,to bari inkuraki da sunan dakikasaba,Suwaiba!shikenanko?,koshima yaudararce? Tace umfh!!kaidai kasani!niduk wata dubara nan dazaka bullomin da ita kallonka nake karrr!humf waini zaka dauka Mara wayau!yanzunne kasan kakirani da Sweety? Yakama hannunta tare dafadin ajiye kayannan zauna,muyi magana. Tace ammadai aikunne kejiko? Yace nasani amma dai zokizauna kiji. Sannan tazauna,tare dafadin inajinka. Yace yawwa tokokefa,mezaki bani inci? Tace AAh!wannan wace irin tambayace?yawuce abinda kakawo,kaga Nasser dakata!duk wani kwane-,kwane nan dazakayimin na yaudarace kokuma munafunci!bazasu taba wanke laifinka awurinaba!! Yamaimaita,yace laifi?laifi kuma? SHARE!! Suwaiba laifin menayimaki?don Allah sanardani. Tace Nasser aibazaka ganeba. Yamatsa hannunta da karfi,yadda yatabbatar taji zafi,yace kobazan ganeba saikin sanar dani,yakuma daure fuskarsa alamar babu wasa,yace gara ayita ta kare yau!suwaiba yau saikin fadamani laifina koda bazan fahimtaba!! Idanunta sukayi rau! rau!!suka ciko dahawaye,tace Nasser dani kadaice awurinka,yanzun munzama mubiyu,dabiarka da halayyarka tacanza ,koban fadamakaba,kai kanka kasan dabahaka kakeba,Nasser kacanza Mani!dai dai nan hawayen dake kwance cikin idanunta suka ziraro. Hakanan saiyaji tausayinta yakamasa,yasassauta rikon dayayimata,sannan yace: Haryanzun bangane abinda nacanzamakidashiba,akwai abinda nakeyimaki da yanzun nadaina?kokuma akwai abinda nakeyimaki yanzun Wanda bakyaso? Yace a'a amma inaso kafahimta Nasser kowace mace tanada kishi,yin aurennan dakayi naga kabullo dawasu abubuwa dayawa,wadandani bansankadasuba,gaba daya Nasser rawar jikinka akan Amaryar nan taka yaki karewa,kullun dokin ta kake kamarranar akakawomaka ita,ko amgayamaka cewa ni zuciyata tadutsece?banajin zafinkomai idan'anyimani badaidaiba? Bawai inanufin ince banason aurenka daitabane,niban isaba,tunda ya halastamaka,amma nalura soyayyar dakakeyimata nibakayimin irinta,baburina inrabu dakaiba,a'a sonakeyi ka kwatanta adalci atsakaninmu. Yace akwai abinda kikaga nabata kebanbakiba? Tace:a'a. Yace:akwai abinda nayimata kebanyimakiba? Tace:a'a Yace:towane adalci kikeso ayi yanzun? Tadago idanunta jajur takara kallonsa,tausayinta yakara kamashi,duk dayakasa gane laifinsa awurinta. Tace :akwai!duk ranar dazaka koma dakinta akwai banbanci daranar dazakazo dakina Yakara kallonta arazane yace wane irinbanbanci kuma? Tace:doki,zumudi,dakuma kosawa. Yace waye yafadamaki haka? Tafashe dakuka tare dafadin angayamaka nibanida hankaline dabazan ganeba!!itace babynka itace love dinka,itace sweetynka,har agaban kowa kana fada mata haka. Yace toke yanzun bagashi nakiraki da Sweety dinkinki amsawaba,Suwaiba bawani abune yake damunki ba ,KISHINE,kuma duk abinda kika lissafomin amatsayin laifina balaifi bane,bazance Allah yarabaki da kishinnan nawaba,domin hakan yatabbatarmin da cewa kinasona sosai,sai daiince Allah yarage maki zafin kishin,Suwaiba inasonki,Daga kanharshena harcikin zuciyata,abinda nakefadamaki gaskiyane,kada kidauka cewa aurennan danayi yarage wani Abu Daga cikin sondanakeyimaki,haryanzun kina nan kamaryadda kike acikin zuciyata. Kikawar da idanunki Daga kan Hauwa'u,kidauka tamkar babu ita acikin gidanki,kimanta da ita kishareta acikin zuciyarki,saikiga kinzauna lafiya. Amma idan hankalinki NA kanta duk wanimotsinta kina sanya mata ido,to bayadda za'ayi kizauna lafiya ,domin kuwa abinda ba'ayibama sai zuciyarki taraya maki cewa anyi,tokinga daganan sai shedan yasamu wurin zama acikin zuciyarki,yana saka maki sawu abubuwa daban acikin tunanin ki,abindama baifaruba sayya kawatamakishi dacewa yafaru,todaganan shikenan bazaki karasamun kwanciyar hankaliba. Tace to yanzun kananufin duk abinda nace kanayi baizama laifiba? Yace:toh!inkin daukeshi amatsayin laifin shikenan,idan har laifi nayimaki, Yasauko kasa yatsugunna da gwiwoyinsa,yace nadauki laifina dakuma kuskurena,don Allah suwaiba kiyi hakuri,bazansakeyiba,amma inarokonki daki kawar da hankalinki akanmu nida Hauwau,idan kikayi haka zaki zauna lafiya,bakiga ita harkarta kawai takeyi batadamu damuba. Ya miketsaye tareda kamo hannayenta yatadata tsaye suka fuskanci juna,yakafeta da idanunsa,yana kara nazarin fuskarta,haryanzun batasauko Daga irin zafin kishin datake kaiba yayi mata murmushi yace Suwaiba kinasona dayawa. Tace aishiyasa kake wahalar dani. Yace to Daga yau nadaina,jeki shirya kiyi wanka kisanya turare mekamashi,barci zanyi dawuri yau. Tayi dariya tareda an she hannayenta Daga nashi,tajuya tashige daki,don tayi wanka. Shikuma nanyaauna bisa kujera yana tunanin irinwannan kishi na suwaiba,sai dai yanakara godema Allah da abin yatsaya akansa kawai,duk iyafadanta da fitinarta,batayima Hauwau,tsakaninta dashine kawai. Yayi dariya,tare dagirgiza kai yace watankan tunda ninayimata laifin baritahuce akaina nikadai,humf!Suwaiba rigima! Lokaci guda kuma yatuna ranar da Hauwa'un tasamu kwana bakwai agidan,a wannan ranar itace ranar da za'araba kwana,yakuma tuna iyakar abinda yafaru a wannan ranar. **** **** **** **** **** ***** ***** Bayan yataso masallacin sallar isha'ine,yanufi dakin Hauwa'u,yace:baby kizo kisamemu afalo,zamuyi magana. Tace to shikenan gani nan zuwa. Sayyajuya yakoma falo inda suwaiba take zaune tana jiransu,wuri yasamu yazauna tareda saurarawa, domin sunajiran fitowar Amaryarsa Hauwa'u. Lokaci kadan tafito,cikin hijabinta taredazaunawa kan daya Daga cikin kujerun falon,sannan takuma gaishesu. Nasser ne yafara magana dacewa . Alhamdulillah!sallu alannanabiyyul Kareem.yabude masu taron da Addu'a,kana yacigaba dacewa. Kamaryadda Addinin musulunci yatadarma ko wadanne maaurata,yakuma Gina rayuwa akantsari,musamman rayuwar aure,yau Hauwa'u tacika kwana bakwai agidan Aurenta,kamar kuma yadda yake a hadith . Idan ka auri budurwa akan bazawara,zaka kwana da ita tsawon kwana bakwai,sannan ayi rabon kwana. Idan ka auri bazawara akan budurwa zaka kwana da ita tsawon kwana uku,sannan ayi rabon kwana. Amatsayina na auri Hauwa'u budurwa,kwanakin ta suncika,ayaune za'araba kwana,to amma kuma ra'ayinnakune,yadda kukatsara iya adadin kwanakin da kukeso to sai atsaya ahakan. Wannan shine dalilin taraku,dominjinnaku ra'ayin,kwana nawa-nawa kukeganin za'araba? Suwaiba tace toh!yadda dai mafi yawan mutane suka dauka,muma haka zamubi,kwana biyu-biyi kokuma uku-uku. Nasser yace hakane,sannan yamaida kallonsa ga Hauwa'u,yace my love bakice komaiba. Tadago idanunta taredayimai wani irin fari,maidaukar hankali,tace: Yo ai Aunty suwaiba tagama magana duk yadda tayanke dayane. Tunda take maganar nan hankalinsa NA kanta,irin yadda take sarrafa harshenta cikin wata irin yanga fa kissa maidaukar hankali,shikansa yarasa abinda yasa komai nata birgeshi yakeyi,lokaci daya tatafi da ziciyarsa,yadade yana kallon fuskarta,sannan Daga baya yanumfasa,yace Hakane babyna,Suwaiba kinji abinda ta fada,tace duk yadda kikayanke yayi,to amma abinda nakeso infahimta,kwana biyu biyun ko uku ukun? Suwaiba tace biyu biyun sunyi,amma saidai inada magana,amatsayina na mace daya wadda tashekara Hudu awurin mujinta,koda yaushe muna tare,sainaga yakamata inkarama kan wata wadansu kwanaki Daga cikin kwanakina,domin itama tasake da mujinta sosai,kuma amatsayinka nawanda yayi sabon aure,gaskiya kwana bakwai sinyima kadan,ace akagama cin angoncinka,gara inbarku kukara sakewa dajuna sosai. Don haka bayan kwanaki bakwai dinnan da kukayi,na yarjema ka kara WATA GUDA A DAKIN AMARYARKA,wadannan kwanaki TALATIN din kyautarsu nabaka,aci amarci lafiya. Falon yayi shiru nawani lokaci. Sannan Nasser yace to shikenan Suwaiba nagode,Allah yahadamin kanku yazaunar daku lafiya. Baby kinji abinda Auntynki tafadako?to don Allah azauna lafiya,kibata girmanta da matsayinta,da take dashi na UWAR GIDA,sannan idan kin............... **** **** **** **** **** **** ***** Suwaiba tatabashi tareda shafamai ruwan dayake hannunta,cikin dariya tace tunanin mekake? Yace tunanin ki tunda kikashiga nakosa inga fitowarki,INA nan inata tunaninki mai masifar dadi,daya daukemin hankalina,kinyi kyau sosai,sai kamshi kike,yamike tsaye tareda fadin muje,inaso inyi bacci dawuri yau,inada aikin dazan fita tunda safe. Yashiga gaba tana biyedashi abaya,suka wuce dakin. Can cikin dare yafarka,yasa hannu yalaluba,baiji suwaiba ba,yayi saurin murje idanunsa,yatashi zaune. Canya hangeta zaune tasauka Daga kan gadon,tanata sharbar kuka,tayi gaje-,gaje.ya saiko yazo inda take,yace Suwaiba lafiya mekedamunki? Tayi saurin share fuskarta tareda cewa bakomai. Ya tsugunna gabanta sosai,yace yazakicemin bakomai?hakanan zakita kukane?ko wani abukeyimaki ciwo? Tace don Allah kaje kayi barcinka kawai,niba abinda keyimin ciwo! Yakamo hannunta yace to taso muje kizauna kan gadon tanbayarki zanyi. Tace koka tambayeni babu amsar dazanbaka. Yace naji taso dai muje kiji. Dakyar ya lallasheta tataso suka zauna gefen gadon,sannan yakalleta tare da kara tsaida hankalinsa akanta,yace: Kishiko?waimeyasa kike wahalar da kankine akan abinda bakida maganinsa?suwaiba inda ace idanna mayar maki da kwanakin ki TALATIN zamu samu zaman lafiya dake to inaga da inmayar maki dasudin kawai shiyafi alkairi. Tace to aikaji inda matsalar take,zaka mayarmin da kwanakinane kawai domin asamu zaman lafiya,badon soyayya da dokiba,bakuma don son rankaba,a'a saidon kawai asamu zaman lafiya,kaga kenan yasha ban ban da irin kwanakin dakayi adakinta. Nasser duk lokacin Dana tuna sanda nabaka kwanakin nan,ka amshesu cikin doki dajin dadi,harkanayimin godiya hankalina tashi yake,koba komai nasan yadda kakesonta nibaka sona haka,kaga kenan mayarmin da kwanakimma basuda amfani, Nasser ya za'ayi indaina kuka?alhalin ninatabbatar sonda kakeyimata nibakayomin irinsa. Yayi saurin cewa suwaiba waye yagayamaki haka?INA sonki harbansan dawane yare kikeso insanar dake cewa inasonkiba ki yadda.Suwaiba don Allah kibani izinin inmayar maki da adadin kwanakin ki,Nidai kidainayimin wannan kukan. Tace banaso domin kuwa badon kanaso zakayisuba,saidon yazamemaka dole,ninasan cewa nayi asarar wadannan kwanakin har Abada!don haka babu yadda za'ayi karabani da kuka. Yace to kinsan abinda za'ayi?Tashi kiyi Alwallah kiyi Sallah zaifiyemaki wannan yin kukan,da zaman da kikayi kina kuka dama Sallah kikayi kika samarma da kanki kwanciyar hankali,kiroki Allah yayemaki wannan matsalar datake tare dake,tashi muje inrakaki kiyo Alwallah kinji? Tatashi suka shiga,gaba dayansu suka dauro Alwallah,sannan sukayi sallar Nafila raka'a Hudu,sukayi adduoin su. Harzata kwanta yatambayeta,wace Addu'a kikayi?kuma mekika roka,? Tace naroki Allah yakara sanyamaka soyayyata acikin zuciyarka, Yayi dariya tare dafadin kai!kai!!,kaih!!!Suwaiba duk tarin soyayyar ki datake cikin zuciyata sokike akara wata?idan soyayyar ki tafi yadda take acikin zuciyata zata iya fasata,domin kuwa soyayyarki tariga tagama mamaye dukkan ilahirin zuciyata,INA sonki suwaiba,kuma irinnaki son dabanne Dana kowa,kece mace tafarko Dana fara gani kika dauki hankalina, tun alokacin kika dauki mafiyawa Daga cikin bangaren zuciyata kika mamaye,don haka kikwantar da hankalinki,duk wata mace tadaina baki tsoro,domin dai mujinki kafin yaganta keyafara gani,kafin yafara sonta keyafara so. Don haka ba soyayyarkice zaki roki Allah ya sanyaminiba,wannan yariga yasanyata,takuma zauna cikin ikonsa. Abu dayane yake wahalar dake KISHI to shine yakata kuroki Allah ya sassauta maki shi,yarage maki zafin kishinnan,yasanya maki dangana,kinji Suwaiba ta,yafada cikin sigar lallashi. Tadaga kanta alamar e. Yace tashi mukwanta,kidaina damuwa kinji. Aiko duk yadda yaso yafita wurin aiki dawuri,saida yamakara,don haka safe cikin sauri yayi break,yana shiyawa kosallama baije yayima Hauwau ba yafita. Bayan kwana biyu,misalin karfe biyar nayamma,yadawo gida,kai tsaye dakin Hauwau yawuce,bayan yazauna,takawomai abincinsa tare dafadin. Sannu da dawowa,yau dai nagakadade. Yace hakane nadade,wani aikine yatsayar dani,mekika dafamin? Tace abinda nasan kafiso,inaso yau kaci abinci sosai,sannan tafara zubamai,yana kallonta sosai,bayan tagama yace sannu da aiki. Tayi dariya,tace nagode mujina,inajin dadin yadda kake yabamin akan komai. Shidai yakafeta da idanu,sannan yace zauna inason muyi magana. Tazauna tare dafadin,ammadakabari kagama cin abincin. Yace a'a bakomai,maganar tanada muhimmanci sosai. Hauwa'u inasonki,INA kuma kaunar dorewar zaman lafiya tsakanina dake,da kuma abokiyar zaman ki,to don Allah kiduba darajar soyayyar dake tsakanina dake,kiyimin wata alfarma guda daya,Hauwau bakisan halindanake cikiba,INA boyemakine saboda banason tashin hankalinki. Tabbas!!nalura kemacece wadda take farin ciki alokacin data samu mujinta cikin farin ciki,kuma kike bacinrai alokacin dakikaga wata damuwa a idon mujinki,dayawan maza irin matar dasukeso susamu kenan,nikuma Allah ya azurtani da ita. Hauwau kokinsan cewa INA cikin tashin hankali daya hanani walwala?sai dai inaga da taimakonki za'asamu saukinsa,koma maganceshi baki daya,Hauwa'u , Suwaiba tatadamani hankali ,idannashiga adakinta,babu abinda takeyimin sai aikin kuka,nikuma banason inga tana kuka,tatada hankalinta duk iya yadda baki zato,nima kuma tatadamin nawa hankalin,kuma duk hakan bayarasa nasaba da KWANAKINNAN TALATIN FATABAMU NA AMARCI,shine Daga baya take danasani,takuma kasa hakura tadangana. Dai dai nan yasauko Daga kan kujerar,yadurkusa gabanta,yace: Hauwa'u kitaimaka kabani KWANAKINKI TALATIN inmayar mata,kona samu zaman lafiya ,don Allah Hauwau. Humff!! Tayi ajiyar numfashi ,tace:babu abinda zaka nema awurina karasa,babu wani taimako dazaka nema awurina banyimaka shiba,zan iya baka duk wani Abu danamallaka arayuwata,indai baifi karginaba,AMMA BANDA KWANAN AURENA!! Bari inkara jaddada maka Nasser!wadannan kwanaki TALATIN tayi asararsu har Abada!bazan iyabatasuba!kuka kuma taitayi!duk ranar data gaji kokuma ruwan jikinta yakare saita bari!kada kakarayin tunanin cewar donkamayarmata da wadannan kwanakin za'asamu zaman lafiya,kadauka tamkar kakara bankado wani tashin hankaline acikin gidanka!kuma kodawasa kada kakara kawomani wannan zancen!dai dai dakwanana daya bazan iyabataba! Kukaratacan!!kai daita,inkunga dama kukwana kuna kuka tare,ni inanan inabaccina. Yace amma kuma................ Tace:kaga dakata Nasser!innasamma wannan maganarce tasakatsaidani,wallahi daban saurarekaba!kuma wannan maganar nakasheta Daga yau!duk ranar daka kara kawomin ita zanyi fito na fito da suwaiba,domin ita bata isa tahargitsamin rayuwar Aurenaba!shikenan ta tadamaka hankalin da zaka kasa sakewa daniko?to kabarni da ita zamyimaka maganinta!! Yayi saurin cewa a'a banason irinwannan Hauwa'u!tunda muke rigimarmu da ita kintabajin tasakoki aciki?tsakanina daitane kawai,ban tabajin tace ga abinda kikayimataba,don haka banaso rigimar takoma tsakanin keda ita,maganar Mani abarta. Tace Ah toh!aigara inyi maganinsa abin tunda wuri,don karka dauka cewama kowata rana zanyadda. Yasa hannu yature abincin data kawomai,cikin fushi yatashi yabar dakin. Tace haka kawai,mata tatadamaka hankali,don inkadawo dakina kakasa sakewa!donneman tahadani dakai!nasan maganinta!!kila nima sainafito nanuna mata inada 'yanci!kuma gidan mujinane!!! Hakataita fadanta itakadai,tana tattara kayan abincin data ajiye Wannanma aimugun abune!gashi ko abincimma tasa yakasaci!to dani take maga. Baidawo gidan ba sai misalin karfe goma NA dare,tana zaune tanajiranshi,sannan saigashi yashigo,babu dai wata fara'a ataredashi,wuri yasamu yazauna taredacemata. Hadomin ruwan zafi zansha. Tatashi tahadamai,takawomai,sannan tazauna daf!dashi,tace yau shine abincinkako?naga kodarana bakaci abincibafa,yanzun kuma kadawo banga alamar zakaciba. Yace shikadai zaniyasha yanzun. Tatabe bakinta tare dafadin to aishikenan,tasa hannu zata hadamai,yatareta yace bashshi kawai zan hada. Tacire hannunta tarabu dashi,don taga iyakar fushin dayake daita,bata karayimasa magana ba haryagama sha,sannan bataredayace komaiba yatashi yashigewarsa dakin. Tabishi dakallo,yau naga ikon Allah,wannan fushin kuma namenene?tadai tashi takawar dakayan tea din daya sha,sannan tashiga dakin. Kwance tasameshi yanashirin yin bacci,tadafa wuyansa tareda cewa,love bakada lafiyane? Yayi banza daita,yajuya mata baya,tazauna gefen gadon,tace mekake nufi? Yace Hauwau kirabu dani,tunda har inada wata alfarma dazannema awurinki kikasayimin,to gaba dayanku zan tattaraku in kyaleku,randa kuka daidaita kanku aci gaba da zaman auren. Wai Nasser kana nufin indauki kwanakina inbaka?hardon nace bazan bayarba kake fushi,to shikenan nayadda,amma saidai inka amince intafi gidanmu inyi wata guda,sanda kagama kwanakin adakinta saika dawo dani. Yatashi zaune ,tareda cewa,ita gidan su tatafi lokacin data baki nata kwanakin?wata hanyacedai kawai zaki bullomin daita donkibani wahala,kuma kinsan abinda bazai yuwuba kenan,domin. Kuwa hakan wata hanyace kika biyo donki tonamin Asiri,mezaisa bazamuyi hakan dagani saikuba?babu Wanda yasani,amma yanzun inkintafi gidanku,aidole asan dalilin,nima kuma bazan yadda kitafi gidaba itama sanda tabaki kwanakin ta aiba Wanda yasani,don haka nibanyadda kitafi gidankuba. Tace to kasani nima bazan iya bada kwanakinaba,Kikasauko Daga fushin dakakeyi,kokada kasauko duk dayane!taja bargo takwanta tareda juyamai baya. Yatashi danufin zaibarmata dakin,itama yatashi tsaye,tace meyayi zafi shiba wutaba?koma kayi kwanciyarka nisai inbarmaka dakin,gadai falo basai inkomaba,yi kwanciyarka nikagama fitata. Tabarmai dakin takoma falo,bisa kujera tana tunanin wannan kuma wane irin abune?WATA kan shiyayadda inbata kwanakina yakaimata,saboda bayason fushinta,Tab dijan!!!aiko zasu kare afushi,to wannan wane irin sone yakeyima suwaibane?tun farkoma inyasan haka aida baikara aurenba,gaba dayamani nalura sondayakeyima suwaiba yayi yawa. Harya kwanta yakasa runtsawa,shikansa yana ganin abinda yayima Hauwa'u bai kyautaba,komadai metafadamasa,aidon tana sonshine,yakuma tuna irin kula dashidin datakeyi,sayyaga baikamata dalilin wannan yagejetaba yau. Mikewa yayi jiki asanyaye yanufo falon,dai dai inda take yatsaya,yace Hauwau taso kikoma daki. Tace a'a nanma ya'isa,lafiya lau ba abinda zaisameni. Yace tokiyi hakuri kitaso. Tace to'aini ba'abinda kayimin kakebani hakuri,nibakayimin laifin komaiba,nayi maka uzuri akan duk abinda kafadamin,nasan bayin kanka bane,masifar SON suwaibane yarinjayeka,harkake fadamin duk abinda yafito Daga bakinka,wannan kuma bamatsala,nima zanroki Allah yasanyamaka Soyayyata acikin zuciyarka kamar yadda yasanya maka ta Suwaiba,don haka kaje kawai bakomai. Yace me kikeso kice?kina nufin nan zaki kwana?don Allah yihakuri kitaso muje. Tace muje inah?kaida kace zaka iya tattaramu kakyalemu sai sanda mukashirya ayi auren,tome zaisa kazo wurina yanzun?kadan rabu damu zuwa sati biyu kagani koma shiga hankalinmu, Yayi tsamm!!yana nazarin maganar ta,sannan Daga baya yace gaskiya bazan iyaba,don Allah kiyi hakuri Hauwau. Tace au! Ashedama barazanace?muje badon halinkaba. Washe gari dasafe yana tsaye cikin falo yayi wanka yanakara gyara jikinsa,suwaiba tashigo ,tayishirinta tsaf!NA tafiya anguwa,tagaisheshi ya amsamata lokacin dayake gyara maballin rigarsa. Tace nashirya dama inaso inje gidammune,inga iyayena konaji dadi,kuma hankalina yakwanta. Sayyayi tsaye yana kara kallonta,saidaga baya yace wannan wace irin tambayece?wai suwaiba meyasa kikeyimin hakane?yanzun don zaki unguwa saida kikagama shiryawa tsaf!sannan zaki tambayeni?salon ince ban aminceba kuma rai yabaci!to banyadda da tafiyarba!sai kije kicire kayan! Dai dai nan Hauwau tafito,dauke da hula ahannunta,tanufo inda yake tasanyamai,tace: Kai my love kayi kyau sosai,kamar kada kafita. Wani kululun bakin ciki yatsayama suwaiba awuya,battasan sanda tace: Inje incire kayanfa kace? Yace e banyadda tafiyar takiba kizauna gida!! Hauwau tawaigo tayi mata wani irin kallo kamar dabatasan da ita adakinba,sannan takara kallon Nasser tace my love muje ka kara kallonkanka a mudubi,saikaga abinda nake fadamaka gaskiyane,cikin wasa tare kama hannunsa,tace kilama Daga nan inhanaka fita. Ran suwaiba yakara baci,cikin kuluwa tace gaji muguwa!Azzaluma!inda baya fitama kinganshi ki makalemai!to immake mayyace saikin sakeshi!!mayaudariya kawai!! Hauwau tace kitambayeshi kiji nikadaice namakale Mashi?koko dai muka makalema juna. Suwaiba tace kekika makalemaiba,domme zakice sayya shigadaki yaduba madubi?dalla sakashshi!!! Tasa hannu tabige hannun Hauwau dayake jikin Nasser din,takumace baya shiga dakin,ahakan zai fita komin kyandayayi,inbai fita dakyanbama kekin Ganshi?muguwa kawai!!! Hauwau zatayi magana,yasa hannu yarufe mata baki,karki kara magana,dama Neman fitina yakawo ta wurina,inkika biyemata kuma abin zai dawo kanki. Yawaigo yakalli suwaiba,wadda idanunta sungama cikowa da kwalla,yace: Wuce kitafi dakinki!don banga dalilin zuwanki nanba! Hawayen dasuke cikin idanunta suka ziraro,cikin kuka kuma tace:saina tafi gidannamu!don bazan tsaya bakin cikinku yakadheniba!!tafita dasauri. Shikuma yabi Hauwa'u dakinta,yaduba madubi,shima yayabama kansa sosai,yace gaskiyarki Hauwau,nayi kyau sosai,kamar bawanda matansa sukeso su hargitsamai tunani ba, Kamar bawanda kullun yake fama da matansa akan suzauna lafiya ba. Kamar bawanda idanyanemi uzuri wurin matansa suke kasayimasaba,kamar bawanda idan yana............ Tasa hannunta tarufemai baki tareda cewa,ya isa hakanan,naji korafinnaka zayyi yawa. Yace kuma sauri nake. Tace bye bye adawo lafiya. Yana fitowa saida yaleka dakin Suwaiba,don yaga dagaske wai tafiyar zatayi koko?amma sayyaganta kwance tayi Ruf!daciki tana kuka. Yace Suwaiba taso muje inkaiki. Tatashi tana share hawayen fuskarta,tafito sukawuce. Suna cikin tafiya yace ikon Allah!Suwaiba saikace wata karamar yarinya,yanzun danna hanaki tafiya unguwa shine kike kuka? Takallai da gefen idonta tace ni bashi yasanya ni kukaba. Yace to menene? Tace dakai da Hauwau kunayimin abinda kukaga dama,ni wani abimma sai inga dankungannine kukeyi. Yace Allah sarki shidai kishi halittane,Allah yaragemaki wannan zafin kishin,gaskiya kinashan wahala,ai duk macen da kishi yake wahalar da ita tanashan wuya.ninaga wannan Abu tunda yariga yafaru,bakida maganinsa,to mezaisa kikasayin hakuri,ki rungumi kowace irin kaddarace tazo maki. Tace nice maka nayi banyi imani da kaddararba?dakai da Hauwau be kullun sokuke saikun sanyani bacin rai,aikasan inada kishi,amma kukeyin wani abin agabana,kawai don raina yabaci. Yace don muna nuna soyayyar junanmu afili shikenan yazama tashin hankali? Kina nufin yanzun donmunajin tsoronki saimu kasa nunama junanmu irin sondamukeyima juna?saboda munagudun ranki yabaci? Tace basaika gayamaniba Nasser,Nina Sani dukkan ma aurata akwai soyayyar juna atsakaninsu,amma idanyazamana akwai idon mutane akansu saisurika kiyayewa,wani abin sai abarshi kodan kunya. Yace to suwaye mutanan? Tayimai wani irin kallo tace:niba mutum bace?Tasakani da Allah Nasser kana wulakantani!!yanzun kai da Hauwau kuzauna kunayin irin wannan wulakancin agabana,ta daukeni me? Yace Abarmaganar,nasan yanzun ranki yabaci. Tace to aini dama kariga kagama batamani rai!ko daya bason farin cikina kakeba!kai indai wannan Sweety din taka tasamu farin ciki,toko rankowama zai baci babu abinda yadameka! Kuma malamai sunata fadin ayi Adalci-ayi Adalci,ammani bawani Adalcin dakakeyimani!!tunda kullun sokakeyi kaganni cikin fushi!!soyayyace nibazan hanakuba!amma saika rika bari saikunshiga daki can!inda idona bai ganiba!!bansan kuma anyiba!amma wani abimma saikun ganni kukeyi!!saboda kai kullun sokakeyi kaganni INA kuka, Nibanga Amfaninma hada mata biyunkaba!!tunda haryanzun kakasa shawo kammu!!kuma rashin adalcine kawai!!! Ko angayamaka don kana iya ciyar da mata biyu!kabasu wurin kwana kawai shine adalcin?amma kuma gashi baka iya kiyaye bacin ran matanka!!Idan kasan idan kayi Abu kaza,zai iya bata ran matarka,saika barshi,amma kiii kiii kieee!!!!katashi kakaro aure,alhalin kuma ba iya sai saita su zakayiba!!! Yace to sauko ankawo,don Allah Suwaiba kada kikai dare,in anyi sallar magariba kidawo gida. Tace to aini naga kamarma baka damu damaganar danakeyiba. Yace aidama basauraronki nakeyiba,Adalcidai in inayi Allah yasani,badonke nakeyiba,yimaza kifita. Tace to bani kudin dazan hau mashin. Yace bazan bayarba,aigidanku kikazo. Tana fita yaja motar dakarfi yatafi. Misalin karfe shidda nayamma,yadawo yana zaune afalo,yasadda kansa kasa,ranshi abace,donko Hauwau ma batasan yashigo gidanba,sai juya kansa yake kamar yanayimai ciwo,maganganun da Suwaiba tafadamai dazun sune kawai sukeyimai yawo acikin kwakwalwarsa,saboda maganar tatadamai hankali sosai. * kuma malamai sunata fadin ayi adalci-ayi adalci ammani bawani adalcin dakakeyimani!!!! * tunda kullun sokakeyi kaganni cikin hushi!!! * tunda kullun sokakayi kaga INA kuka!!!! * ni banga amfaninma hada mata biyunkaba!!! * tunda haryanzun kakasa shawo kammu!!!! * kuma rashin Adalcine kawai!!!!!! * don kana iya ciyar damata biyu kabasu wurin kwana kawai shine Adalcin!!!! * amma kiiii kiiii keee!!!katashi kakaro aure!!!!!!!!!! Wasu zafafan hawayene suka gangaro fuskarsa,cikin tashin hankali yahau bugun kansa da hannayensa yana fadin. Suwaiba me nayi maki?wane rashin adalcine nakeyimaki?nidai iyakar sanina INA bakin kokarina,wurin kwatanta Adalci agareku,suwaiba menayimakine????? Hauwauce tayi saurin girgizashi,tare dafadin lafiyarka lau kuwa?yakaketa magana kaikadai? Humf!yayi ajiyar numfashi tareda rarraba idanu kamar yayi karya,domin kuwa baisan abinda yake fada yafito filiba, Tazauna tare dacewa mekuma suwaibar tayi maka? Yace a'a bakomai,kawai dai abinda tayimin dazunne yake damuna,amma komaima yawuce, Tace to shikenan. Amma don Allah kadaina tada hankalinka,inka biyema sha'anin mace saita zautaka,saika dauka azuciyarka cewa duk abinda mace tayi kuruciyane da rashin hankali,idan kace zaka biyema mace,to saika aikata badaidaiba, Ita mace kometayi aganinta daidaine,indai akan abinda yashafi mujintane,koda kuwa bata Mashi rai tayi,ita aganinta hakan shine dai dai dashi,kuma mace bata cikayinnadamaba saitaga wuri yakuremata. Don Allah mujina kamaida komai ba komaiba,bana son tashin hankalinka. Ya kirkiro wata dariya hakanan yayi,domin yafaranta mata,amma saiwasu hawaye masu masifar zafi suka ziraro a idanunsa. Tayi saurin kara matsowa jikinsa,tasa tafin hannunta tana share mai. Dai dainan suwaiba tabankado kofar falon tashigo,saikuma tayi tsaye turus!tana kallonsu,saikace takama marasa gaskiya. Kodamuwa da ita Hauwau batayiba,taci gaba da abinda takeyi,taredakara lallashinsa. Suwaiba tashige dakinta taredajan wani dogon tsaki. Nasser da yagigirza kai,taredacewa ni bamuyima haka da itaba,cewa nayi sai anyi magariba,zata dawo. Dama INA nufin innataso masallaci inwuce indaukota,kinga tama hutar dani,amma kuma wannan tsakin datayi namenene? Hauwau tayi saurin cewa haba don Allah meyasa kake kula irin wannan?kadama kadamu da ita,kasan tunsafe take Neman rigima,yanzun Wanda zaibiyemata takeso,to kaji gayacan ma anfara kiran Sallah. Suka tashi suka dauro Alwallar sallar magariba,yawuce masallaci. Saida yatsaya yayi sallar isha'i a can sannan yadawo gida. Aranar kuwa dama suwaiba kekarbar aiki,don haka yana dawowa dakinta yawuce. Kamar yadda yazatadin hakayasameta,rannan mata abace,donshidai ko sallamarshi baiji ta amsaba,imma ta amsa to aciki tayita. Yaji dai shurun tayi yawa,yasa hannu Aljihunsa yaciro naira dubu daya yamika mata. Tayi banza dashi,kamar bata ganshiba. Yace ki amsa mana. Tace tamecece? Yace kudin motar dakikahawo daga gidanku zuwa nan,dama nayi niyyar innafito masallaci zanje indaukoki,saikuma gaki kin dawo. Tace Nasser bahaka kake nufiba,nice zaka dauka Mara wayau!aikai kanka kasan bakayi dai daiba!!inace yau kwananane?amma dana shigo gidan menatarar?shine zakayimin dubara da kudi?to aigidannamu ba matsiyata bane!!anbani kudin motar a can. Ran shi yayimasifar baci,amma saiyadanne bacin ran,yace to amma aini yakamata in baki,kuma baki taba zuwa gidanku nabarki kikayi kudin mota dakankiba.ballan tana kice inaso inwanke wani laifine awurinki. Tace to banaso!!dai dai alokacin datake daukar filo da bargo zatabar dakin. Yariko hannunta tare dafadin,Suwaiba kiji tsoron Allah,Kisani cewa abinda kikeyimin,yafara fita hankali,wallahi abinnaki Suwaiba yafara wuce kishi yafara zama wulakanci da rainin hankali!!to kibi duniya asannu,domin banga amfanin yin fushi akan abinda bakida yadda zakiyi dashiba. Yasa hannu yagizge filon dake hannunta cikin fushi,kuma yace:idan kika fita falo kika kwana bada izininaba!ya ajiyemata kudin yayi shigewarsa wanka,nanya barta tsaye kuka ya kwace mata dakarfi. Yau kimanin watanni uku kenan dayin auren Hauwau,harmadawasu kwanaki. Mahaifiyar Naseerce takirawoshi awaya Daga Funtuwa,take shaidamai tanason ganin sa,dakuma damaga bikin Abokin sa Ibarahim yamatso. Nan yake shaidama mahaifiyar tasa yana nan zuwa cikin satinnan,in Allah yaso. Bayangama wayarne yake shaidama suwaiba cewa,da ita zaifi,domin kuwa Hauwau tace itama zataje Lagos wurin kawunta,kuma duk tafiyar zatazo lokaci dayane,don haka keki shirya sai intafi dake. Tadai amsamai da to. Saidayarage saura kwana biyu tafiyar,take cemai. Kasan wani Abu Nasser? Yace menene? Tace bazani Funtuwa ba. Yace saboda me? Tace kawai dai nidai naji natsani tafiyar,kotunawa nayi cewa zamu funtuwa sai inji raina yabaci,har takaigama yanzun gabana faduwa yake,kai dai Allah yakiyaye hanya adawo lafiya,nidai bazaniba. Yace amma dai banji dadi ba dakikace kinfasa,ko bakijin dadin zama da 'yan uwanane? Tace a'a lafiya lau,ni da innajema sukesona,aita nunani,ana nan nandani,kawai dai nibansan daliliba. Kawai dai naji tafiyar tasiremin,inda ace Hauwau ba inda zata saiku tafi tare. Yace kai aigaskiya bazan hanata zuwa legos dinnan ba,saboda kawuntane yadawo Daga America toshine takeson taje,kuma INA tunanin komawa zayyi idan batajeba kinga kafin takara ganin sa za'adade. Suwaiba tace tokumafa hakane gaskiya,nidai kayi hakuri bazani. Yace a'a bakomai sai intafi nikadai. FUNTUWA Agida FUNTUWA yayi sallar Azahar,sannan yadawo dakin mahaifiyar sa,sunata fira tareda kannansa maza da mata. Kanwarsa Aisha tace yaya Nasir nasha zakazomana da Amaryarka bantaba ganintaba. Yace ai itama unguwa zata,shiyasa bamu tafo tareba. Tace to INA Aunty suwaiba?ita meyasa bakazo daitaba? Yace itama nabarta tayi tsaron gida. Dai dai nan H-Asamau tashigo tareda mai aikinta tanadauke da tiren daakajefo kayan Abinci asamansa. Tace kana nan kuna fira kenan? Yace e inna inajirane inbaci Abinci zan fita,inzagaya inga Abokaina,yasa hannu yabude kular Abincin,kamshi yabugai,yace laaa!inna Dambu?dama saboda kinsan inasonshi kikayiko? Tayi dariya tare dafadin Nasiru kenan,aidama nasan kanasonshi,shiyasa mace bari atarbeka dashi,duk yakabaro gidan? Yace lafiya lau inna suna gaisheku. Saida yaci yakoshi su kadan taba fira sannan yafita,gidan su Ibrahim dinyawuce kai tsaye,nan yahadu da Abokansa,firace takaure tsakaninsu,ballantana dama anrabu da haduwa. Hassan yace kazo bikin tuzuru kenan? Sukasa dariya baki daya,Nasser yace Babban tuzuruma kuwa,kasan saida yagama jama 'yammata aji sannan,gamunan wasummu harda mata bibiyu,shisai yanzun zayyi tafarko. Ibrahim yace kusha kuruminku,badi iyanzumma zakudawo auren ta biyun,ainabarkune dukjugama,ni innatashi akai-akai zanyi su. Nasser yayi dariya cikin girgiza kai yace Allah yatayaka riko,aikasan rike mata biyunnan sai jajurtaccen namiji,mai kokari!kaga shi Hassan tunda yayi tafarko shekara biyar kenan yakasa karawa,kazo Abuja inyi maka budurawa. Hassan yace kasan wani Abu?mata dayannan dai daidahudu nake ganin ta,don hakan ita isheni. Nasser yace inah!!wasa kake bazaka zama jaruminba,kenan? Ibrahim yace to kaga kunfara karaya ko?kuda kukafara auren,nikusa ido kuyi kallo,duk bayan shekara biyu sainayi aure,harsai nahada mata Hudu cuf! Nasser yakara tuntsurewa da dariya,tareda bubbuga kafadar Ibrahim,yace kasankau nanne zaka gane anasonka,ingayamaka kota inatarairayarka za'arikayi,mata hudu!lallai kam!aiko zakaga soyayya! Hakasukasha firarsu cikin wasa tareda zolayar juna,harsaida akayi sallar la'asar sannan sukawuce masallaci baki dayansu. Bayan suntaso Nasser yace yanaso yaje gida,anjima zai dawo,sai afara shirye-shiryen yadda za'ayi hidimar bikin,don atsara komai yadda yakamata,sukayi sallama yahawo motarsa zaitafo gida. Akan hanyarsa ya hangi HABIBA sanyeda kayan makarantar islamiyya,saida yazo dai dai indatake sannan yatsaya,tareda sauke gilas din motarsa,yaleko da kansa yace: Malama Habiba INA zuwa? Cikin mamakin ganinsa yasa hannayenta biyu dake cikin hijabinta tarufe bakin ta tare dafadin. Yaya Nasser yaushe kazo? Yace aibaki bani amsaba. Tace makaranta zani. Yace toshigo inkaiki,kinga Hudu tawuce sosai,yabude motar tashiga,tareda fadin yau kazo? Yace dazunnazo,yaya karatunki? Tace gashi nan muna tayi,Alhamdu lillah,nayi mamakin ganin ka! Yace aiko yaunazo,kina zuwa makarantar boko ko? Tace ainagama, Tace kingamafa kikace? Tace e secondary ba. Yasa dariya tareda fadin tokuma shikenan kin gama karatun? Tace nidai indai ra'ayina za'abi inaso inci gaba. Yace tome zaihana ba'abi ra'ayinnakiba? Saitayi saurin canza firar dacewa,yaya Nasser banfa ganekaba da farko,saida nalura. Yace saboda me? Tace kaga yadda kazama?daba haka kakeba, Yace:AAh!toda yaya nake? Takara kallonsa tace yaya Nasser kayi girma kakara kyau sosai. Yasa dariya yace ashedai haryanzun kina nan yaddanasanki da surutuko?nasha tunda kinyi girma yanzun kinrage surutu. Saikuma taji yabata kunya,tarufe idanunta,tace to saukeni nan ankawo makarantar. Yasauketa tare dafadin ayi karatu lafiya,bye bye, Itama tadagamai hannu sannan tawuce tashiga aji. Misalin karfe Takwas darabi nadare,Nasser nazaune shida mahaifiyar sa,H-Asama'u,suna fira ,takecemai. Nigaba daya Al-amarinka mamaki yakebani,domin ni yanzun bansamma manufarkaba,koko matannakane kasamu 'yan bariki suka sauyamaka tunani oho,to yanzun dakake wannan kauce-kaucen mekake nufi? Nasser yace Inna bawai umarninkine banaso nabiba,a'a yadda za'ayi inrike mata uku shine nake tunani. Tayi saurin cewa hanyar dakabi karike biyun ita zakabi karike ukkun!abinda ba 'ya'ya kuka taraba, Shintomawai dakake wannan maganar ya kakeso ince da iyayen yarinyarnan?kasandai tun mahaifanku nadarai wannan maganar take,kuma Al-kawarine!koko sokakeyi arusashi? Yace bahaka bane ba inna,bazaki fahimceniba,domin niyanzun bamma shirya kara aureba,kuma yarinyarnan kinga karatuma take. Tace to yaya za'ayi infahimceka Nasiru?aini fahimtata dakai dayace!inji kawai ka amsamin ka amince da wannan auren,kuma dakake maganar karatu waya gayamaka bata gama ba?tagama secondary kuma kwanan nan sukayi saukar Al-kur'ani,tome kuma ake bukata?aiyin auren shine kawai darajar 'yamace. Yace Inna secondary fa kikace?ni inna immazasu yadda sai inbiya mata taci gaba da karatun,Wallahi Inna dayafiye mata wannan Auren. H-Asamau tace tunda kai kannan naka gaba sukaciba?kaini duk wannan hanyar dazaka biyomin bafa yadda zanyiba! AH!toh!!karatune kakeso kafakemin dashi,kuma tana iyayinsa adakinka,tunda kaima 'yan bokonnan kake aure,kaga baikamata ita ace batayiba,duk dadai aizaman Aure tajeyi! Nasiru banyi zaton zakayi aure har biyu babu HABIBA aciki ba,amma bakomai haka Allah yahukunta,Allah kuma yatayaka riko. Yace to inna kijira inmunyi magana da Habibar idan tace karatun takesonyi,sai inbiya mata kudin karatun taci gaba,inyaso Daga baya sai ayi zancen auren,sabidani gaskiya banshirya rike mata ukuba. Tace niyanzun bashirinka bakesoba!yaddarka kawai nake nema,domin niyanzun inkayaddama bazaka koma Abuja ba saida Habiba. Arikice yayi saurin dago ido yakalleta muyarsa narawa yace:inna wane irin Aure kuma yanzun?duka yanzunfa banrufe watanni Hudu da auren Hauwa'uba,don Allah inna kidaina wannan maganar,domin ni nanatabbatar yarinyarnan tafiso tayi karatun. Dataga tsabar tashin hankalin dake cikin idanunsa,tagane e lallai dagaske yake,bazai karbi umarnin taba ,sai itama tadaure Fuskarta cikin fada tace: Nasiru bafa shawara nake bakaba!!wannan abun dolene kayi shi!!ai Allah bai hanaka abinda zaka rike koda mata huduneba kuwa!!saboda haka ni wannan yarinyar tayimin!kuma bakama barin garinnan saida ita!!!domin idan katafi bamusan ranar dazaka kara dawowaba,don haka yanzun kaje kayi shawara,ranar da za'adaura auren Abokin ka Ibrahim sai ahada danaka, Yatashi tsaye zufa nawani irin ketomai,dakin sa kawai yawuce yakwanta kan gado,cikin wani irin tashin hankali. INKARA AURE???? Yaketa tambayar kansa,to yaya zanyi dasu kenan?gaskiya da ancuci Habiba in dauki wannan yarinyar insakata cikin wadannan matan,gaskiya akwai matsala,nan take yafara hanho irin tashin hankalin da suwaiba zatayimai,intaji wannan auren,me zabcemasu idannakoma?wace hujjace kuma zankafa masu dalilin kara auren? Haka yakwana juye-juye yana hango irin hargitsewar da gidabsa zayyi,idan yakai Habiba amatsayin matarsa ta uku,asu biyunma ana'irin wannan kishin?inaga kuma yakai wata. Bai samu mafitaba sai misalin karfe uku nadare,sannan dubara tafadomai,nacewa,yaje ya lallashi Habibar,yace zaibiyamata kudin makaranta tacigaba,inyaso Daga baya tasamu wani mujin tayi aure. Sannan yasamu hankalinsa yakwanta,yayi barci. WACECE HABIBA????? Kuma yaya sukayi soyayya da Nasser abaya???? Miye dangan takarshi da ita????? MASHA ALLAH !maikaratu anan zan dakata,Free page yakare,sauran cigaban labarin nakudine, Lallai saika bada tugwicin wani Abu sannan muci gaba da tafiya tare dakai, Inajinjina gawadanda suke bibiyar labarin nan Allah yabar zuminci. ________________________________________ KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN RUDANI NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA Ranar Litinin biyu ga watan FEBRUARY akafara Shari ar H-Amina mansur,kamar yadda akasaba,kowace ranar Monday kotun takancika makil da jama'a. Haka aka fito dasu duk sunfuta kamanninsu,bayannatsu,maga takardar kotun yakira sunan shari'ar da za'afarayi a yanzun,sannan lauyoyi suka gabatar dakansu kamar haka. Sunana Barrister Abubakar Ibrahim,ni loryer ne Daga hukumar kare hakkin Dan Adam,batsayane awurin nan domin kwayoma iyalan marigayiya hakkinsu na kisan 'yarsu da akayi. Daga daya bangaren kuma tace:sunana Barrister Aseenat,ni lauyace wadda nake kare wadda ake zargi da kisan marigayiya Mariya,sannan gaba dayansu suka zauna. Alkali yace daga bangaren kare hakkin Dan Adam ko zaka sanar damu dalilin daya sa kuke zargin H-Amina ita takashe kishiyarta? Barrister Abubakar yasake mikewa tsaye,sannan yayi godiya ga Alkali,yaci gaba dacewa . Ranar Ashirin da uku ga watan January H-Amina da kawarta sunshiga gidan marigayiyar da tashin hankali mai tsanani,Wanda daga karshe har ita H-Aminar tayi ikirarin cewa,lallai bata fita gidan saitaga gawarta,kuma hakan tafadeshine abainar jama'a,bayan kuma tabar gidan dawasu awanni sai aka tarar da gawar mamaciyar adakinta inda aka kasheta da wuka,tahanyar caka mata ita akahon zuciya. Don haka mukeso wannan kotu mai adalci data dauki matakin daya dace akan wannan matar,Nagode. Zuwa can Alkali yace ko lowyer wadda ake zargi tanada abin cewa? Sai itama tamike bayan Barritar Abubakar yazauna. Tace:kwarai kuwa ya mai shari'a. Maganar cewa H-Amina ta ambaci zata kashe Mariya,wannan ba abin mamaki bane,domin kuwa kowayasan zafin kishi ga diya mace,ayayin da irin Abinda yafaru ga H-Amina yafaru agareta,zata iya fadin kowace irin kalmace ayayin da kake cikin bacin rai,harma abinda bazaka iya aikatawaba. Tafadi Kalmar kisane badon zata iya aikatawaba,saidon zafin kishin datake ciki a wannan lokacin,sai kuma wani yayi amfani da wannan damar ya kashe marigayiyar,sannan yajanye jikinsa. Sannan kuma na biyu,H-Amina harta shiga gidan tafito bataga Amaryar mujinnataba,dalilin mujinta daya rufe kofar dakin,don haka inaso kotu tabani dama inyima Alhaji mansur wasu tambayoyi. Maga takarda yafada dakarfi,alokacin da Alkali yabada izinin akirasa. Ina Alhaji Mansur mujin marigayiya!!? A hankali yafito,yaje inda akebukatar yatsaya. Sannan Barrister Aseenat tatafo wurinsa. Tace Alhaji mansur,wayene yarufe kofar dakin Amaryarka ayayin da H-Amina tashigo? Yace:nine. Tace meyasa karufe? Yace saboda INA tsoron haduwarsu,saboda ni na auretane uwar gidana bata saniba,sainayi gudun kada suhadu tabigeta. Tace kana ganin H-Amina zata iyakasheta? Yace a'a bazata iya kashetaba. Tace Alhaji mansur wayene yafara bude dakin bayan H-Amina tatafi? Yace ninafara budesa,sannan nacemata tayi hakuri zantafi kanoyanzun,inbi matata.domin inbata hakuri akan abinda nayimata,sannan nukayi sallama natafi. Tace katabbatar H-Amina tatafi alokacin? [9/14, 5:14 PM] +234 916 252 6909: Yace kwarai tatafi,don alokacin ita takai gida,nikuma nakusa kaiwa,kawai sai akakirani awaya. Daidainan kuka yaci karfinsa,cikin kuka yake cewa,akashaidamani cewa,indawo gida antarar dagawar matata acikin dakinta hankalina yatashi sosai. Barrister Aseenat tace nagode,shikuma yakoma wurin zaman sa yazauna yanata sharbar kuka. Sannan tace ya mai shari'a yakamata ayi duba gamedawannan lamarin,mujunsu yashaida mana cewa sanda aka kashe mamaciyar H-Aminama takai kano,to tayaya wadda bata nan zatayi kisa? Nagode ya mai shari'a,sannan takoma mazauninta tazauna. Bayan 'yan rubuce rubuce da Alkali yayi tare da mataimakansa,sannan yadago kai yace: Ko Barrister Abubakar yanada wani abin cewa? Yamike tare dafadin akwai ya mai shari'a. Yace aiba lallaine sai mutum yana nan zayyi aikata kisaba,zai iyasawa ayimasa,kuma kibakomai kawarta aitanazaune agarin,lallai zata iya biya kokuma tasa kawarta ta aikata,kunga badole saitayi dakantaba. Don haka ba abin mamaki bane don ance lokacin da akakasheta ita takai kano. Don haka nakeso wannan kotu mai adalci data duba wannan maganar tawa,abinciketa sosai domin ataimaka azartar mata da hukuncin dayahau kanta. Nagode yamai shari'a. Alkali yace ko Barrister Aseenat tanada wani Karin bayani? Tace inadashi yamai shari'a,inaso kotunnan mai adalci data duba yanayin maganganun damukeyi,dagani har Barrister Abubakar muna maganane akan abinda bamuda tabbas,dukka akan zargi muke magana,don haka nakeso Courtu tabamu dama domin mugano hakikanin gaskiyar abin. Nagode yamai shari'a,sannan tazauna. ________________________________________ Ranar goma sha shidda gawatan FEBRUARY,aka kuma zama court, domin cigaba da Shari ar H-Amina,kamar yadda akasaba,Barrister Abubakar yafara gabatar dakansa,sannan Barrister Aseenat itama tagabatar dakanta,sannan suka zauna. Mai shari'a yace munji inda muka kwana ashari ar baya,kocikinku akwai Wanda yakara samun wani bayani gameda wannan kisan? Barrister Aseenat tamike tsaye tare dafadin masamu yamai shari'a,amma kafin nan inaso ingabar da Hashimu. Hashimu yafito yatsaya inda ake bukatar yatsaya,sannan itama tataho inda yake,tace: Hashimu ka kwantar da hankalinka,kasanar da kotu wayekai?kuma menene alakarka da mariya? Yace sunana Hashimu,kuma alakata da Mariya tun muna yara taremuke daita,inasonta da aure,kuma mahaifinta yabani,amma daga baya yarasu,dalilin haka saizaman Mariya yakoma kano,bansan alakarta dakowa acanba,daga baya sainaji za'a aurar da ita gaAlhaji mansur,iyakar abinda nasani kenan. Barrister Aseenat tace alokacin dakaji za'a aurar da ita yaya kaji a wannan lokacin? Yace gaskiya banji dadiba. Barrister tace shiyasa kacema mahaifiyarta zata gani? Yace e hakane,shiyasa nace mata zata gani,kuma gashi tagani. Gaba daya hankalin mutanan court don yadawo kansa,aka fara maganganu kasa-kasa,har Alhaji Mansur nacewa: Kaji azzalumin yaro!Ashe shiya kashe ta!bazan yaddaba!!! Hashimu yaci gaba dacewa,nasan duk Wanda yasaba alkawari,sannan abin duniya yarudesa,lallai saiyagamu da jarrabawa arayuwa!hakika mama jummai tadauki alhakina,shiyasa tagamu dawannan iftila in, Barrister tace shiyasa kaje kakasheta? Yace bani nakashetaba,lallai dai nasan dai Allah yayi masu hukunci dai dai da abinda suka aikatamin,amma banyi tunanin tahaka abin zai bullo masuba,hasalimani bansan gidan da akakaitaba. Barrister tace kafito kadama kotu gaskiya batare daka wahalar daitaba,wannan Abu da akayi maka shine yasa kaje kakasheta kenan? Yace bani na kashe taba,domin ranar da akayi kusammani banada lafiya,aranar aka sallamoni daga Asibiti,ibagida kwance . Tace to amma alokacin............... Barrister Abubakar yakatseta da cewa inada korafi yamai shari'a!!! Nemi littafin RUDANI kada kabari abaka labarin!! Fateema Dahiru Funtuwa Binta An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels