An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BABBAR HUJJA 1 NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA 📖📚 Wannan littafin na suyarwane,gamai bukata . Akan kudi naira dari uku N 300 Account Number zada ka/ki sa kudin. 1527970269 Access Bank FATIMA DAHIRU Ko kuma kasa katin MTN na naira Dari uku akan wannan Number 09162526909 Gamai bukatar cigaban labarin sayyayi magana ta wannan number 09162526909 Don Allah kada kadauki Number ta kayi Mani magana idan baka tashi siyen littafin ba. Godiya tatabbata ga Allah mai kowa mai komai daya sake hadamu cikin wani sabon littafin. Mai suna BABBAR HUJJA! Tsira da Amincin Allah sukara tabbata ga shugabammu Annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya. Narubuta wannan Dan littafine domin farkar da mutananmu ,musamman. 'Yan mata da samari akan kalubalan da yake acikin soyayya,kawai mutum yayi imani da Allah,akan dukkan abinda baisamekaba,to daga Allah ne,kuma komin son da kakeyima Abu idan ba rabonka bane sayya tseremaka,yafi kyau dukkanninmu mukoma ga mika All amarimmu ga Allah kawai,musamman akan soyayya,domin akan ta zan rubuta wannan Dan littafin. Sodayawa zakiga mutum kina sonshi,kokuma shi yana sonki,amma karshenta abin ba Alkairi bane a tsakaninku,to mafi yawan 'yammata da samari idan hakan tafaru a garesu ,sai kaga suntada hankulansu,har ananeman rasa lafiya. Don haka samari da 'yammata asa hakuri acikin zuciya,komai daga Allane. Wadda kake hangen ko Wanda kike hangen,karshenta ba shine mujin ba. Amma bazance komai ba akan haka ,kubiyoni acikin wannan littafin na BABBAR HUJJA kuji yadda soyayyar wasu masoya zata kasance. Fatanadai a dauki abinda yakeda kyau acikin wannan littafin . Sannan littafin BABBAR HUJJA kagaggen labarine,bawai yaru akan wani ko wata bane,AA kirkirarsa nayi,don haka koda kaga wani Abu kowani hali yayi kama da irinnaka,to bakaidin bane,don WATA kilamani bansankaba ko bansankiba,kirkirar labarinne kawai yazo da haka,don haka idan abin gyarawane ,saika gyara . DAGA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA GARGADI Banyadda ajuyamin wannan littafin ta WATA sigaba har saida izinin marubiciyar. Gaisuwa ga dukkannin masoyayana,aduk inda suke,ina sonku kamar yadda kuma kuke sona . Ayi karatu lafiya Dasallama tashigo falon fuskarta dauke da tsararriyar kwalliya ,wadda yayi mata kyau sosai,tasanya Dan madaidaicin hijabinta ,Wanda yakara fitomata da kyawun fuskarta. Sannu da zuwa yaya Ahmad,tafada dai dai lokacin da take Neman wurin zama nesa dashi kadan. Yadago kai yakalleta,sannan yace:bayan kingama shanyaniko?har nayi niyyar intashi intafi,donnayi zaton ko bakida lokacin da zaki futo inganki. Tace tuba nake yaya Ahmed, Nina isa kazo ince bazan fitoba,kayi hakuri don Allah bansan sauri kakeba,amma kuma yaya Ahmad konakai dare ban fitoba,aibaka iya tafiya bakaganniba,kumafa tsayawa nayi inshirya kawai,amma shine harka gaji da zaman jirana. Yace: yo shirimme kikayi?abinda kwalliyarma ba kyau tayi makiba. Tayi dariya tare da fadin yabawa kayi kenan,lallai yau na tabbatar kwalliya ta taburge yaya na. Yace:haka dai kikace. Tace :kaima haka kagani,tare dasa gefen hijabinta tadan rufe fuskarta. Yace:Hafsat dama nazone insanar dake cewa rana itayau zantafi kano,kuma idannaje akalla zanyi sati acan,shiyasa nace bari insanar dake tun yanzun,don kifara shirin yin kewata. Cikin shagwaba tace yaya Ahmad yanzun nan harsai nayi sati ban gankaba?Ashe kana shirin ka azabtar da zukata biyu kenan,yaya Ahmad bazan iya tsawon sati gida bangankaba,don Allah kasaukaka tafiyar,yaya Ahmad karage kwanakin. Humff!!yayi ajiyar numfashi ,sannan yace:nikaina saida na jinjina tafiyarnan,domin nasan haka saita faru,Hafsat nikaina inatunanin yadda zanje wani wuri inyi sati guda ba tare danazo nayi tozali da wannan kyakykyawar fuskar takiba,no kaina nakan tambayi kaina shin sai wane irin sone muke yima junanmu?Wanda dai dai da kwana daya bama iya hakurin bamuga junaba. Hafsat inasonki,wani lokacin har nakema kaina azarbabin cewa na kagara inga na mallakeki a matsayin matata,awannan rana zan tasaki inta kallonki,karkicefa har saina gaji,a'a bazan taba gajiya da kallonkiba,bazaki taba gundirataba. Yadaga hannayensa sama tare da fadin. Ya Allah ka nuna Mani ranar da Hafsat zata zama matata. Acikin zuciyarta ta amsa da Ameen,sannan afili tace:mezakaje yowa kano? Yace:Abbane ya shaidamin cewa diyar kaninsa. MARIGAYI ALHAJI KABIR take dawowa daga Englar karatu ,to shine waini zanje in tarbeta,daga Air port. Cikin muryar kuka tace amma shine harsai kayi sati. Yace:banda wannan akwai wani aiki dazan yimasa akamfaninsa,to zai daukeni tsawon kwana biyar. Tace:nigaskiya saidai katafi Dani " Yace:kiyi hakuri Hafsat akwai sauran lokacine,idan lokacin yayi ko abayana kikace inzagaye garin Kaduna to inhar zan iya zanyi,to amma yanzun mudan kara hakuri kadan,kokinaso insanar da Abba cewa kince adaura mana Aure dake kafin intafi,sai intafi dake? Tace:Ahh!!kajika saboda nice sarkin marasa kunya? Nina yanzumma zanyi Aureba ,sai nayi digri. Yayi dariya tare da fadin kinjiki ahakadin,sukasa dariya baki daya. Haka sukaita firarsu cike da kaunar juna,hadi da soyayyarsu maiban sha'awa. ALHAJI SALISU mahaifin Hafsat tare da matarsa HAJIYA FATIMA,suna zaune afalonsu. Hajiya Fatima tace:Al-amarin yarannan Alhaji,abin gwanin babsha'awa,sunason junansu sosai,karkaga yadda Ahmad yake diki akan Hafsat ,itama da ance gashi yazo karkaga yadda jikinta ke rawa,kaih!mudai wannan Al amari Allah ya tabbatar mama dashi,kagansu da wasa da dariya,komai sunayinsa gwanin bansha'awa. Alhaji salisu yace:shi Allah haka yake hada siyayyar 'yan Adam,gashi dai mutane dadama suna gudun Auren Zuminci ,amma mudai yarammu Allah ya had a kawunansu,kafin mahaifitar Ahmad din tadawo daga kasar saudiyya ai yaran sungama dai saita Kansu ,wannan Al amari aiba Wanda zaifini jindadinsa. ALHAJI SANI DA ALHAJI SALISU DA MAHIFIYAR AHMAD HAJIYA AISHA,mahaifisu daya ,indashi Alhaji Sani da Alhaji SALISU mahaifiyar su daya,ita kuma HAJIYA Aisha ita kadai mahaifiyar ta ta Haifa,kunga. 'Yan uba Duke kenan. HAJIYA Aisha tare da mujin ta ALHAJI SULAIMAN da daya kawai suka mallaka wato Ahmad ,sunaji dashi sosai,dama kuma ga arzikin. Shi kuwa yayanta Alhaji SALISU yanada 'ya'ya dadama,cikinsu harda Hafsat ,Wanda a yanzun yakeda shekara goma sha Takwas da haihuwa,lokacin da take zama budurwa,sai Allah yahada soyayyarta da Dan uwanta Ahmad,Wanda yazamana Abokin wasantane (kamar yadda mu hausawa mukecewa) Domin kuwa da Babantaba da innarsa mahaifinsu daya,saidai uwace kowa data shi. Alhaji SALISU da kaninsa Alhaji Sani sunyi farinciki da wannan Al amari sosai,domin koba komai zai kara donkon zuminci atsakaninsu,wannan kenan. Ranar Alhamis kuwa dasafe tadauki motarsa,yatafi kano,acikin zuciyarsa cike yake da kewar abin kaunarsa Hafsat. Yasauka gidan,su biyu ya Tatar kamar yadda ya tsammata ,daga kubura sai khadija,sai masu acikin gidan da suketa kaida komowa,sunayimasu hidima, Cikin farin ciki suka tarbi yayan nasu,suka kaishi masauki,tare da kaimai da dadan abinci kala-kala,saida yagamaci sannan suka shigo,India yake domin susake gaisawa. Yace :aah!kanbaina!yakaratu? Sukace lafiya lau yaya Ahmad,yaya wajen acikin ka? Yace :lafiya lau,Abba yace in gaisheku,kuma yace:idan yayarku suhailat tadawo,inkoma daku,don yace yanson ganinku. Kubura tata hannayenta tare fadin Allah sarki!Abbanmu!!inaso Nina inganshi. Khadija tace amma dai ba dadewa zamuyibako?Donni bànso inje wani gari indade. Ahmad yace aidukkece matsalar dama,bakison mutane. Tace yaya Ahmad bahaka bane karatuna. Yace to Al huda huda!karatun guduwa zayyi?komai menenedai tunda Abba yacekije saikin je,inba haka ba kuma injaki da karfina inkaiki. Sukasa dariya baki daya. Tace saikace WATA 'yar yarinya,aibaka iya jana,. Yace Atashi tafiyar kice baki zuwa kigani,da karfi zansanyaki cikin mota,alokacin zaki gane ke yarinyace,suka shekararki nawa? Yayi saurin cewa goma sha shidda! Yace kaji barauniyar shekaru!yaushe kikakai haka? Tace Allah yaya Ahmad bakai,ya kake maidani bayane? Yace:don kinga kinyi jikin girma. Kubura dai dariya takeyumasu,harsai tagaji tace:yaya Ahmad idan kabiyema autannantamu,nanzaka shiririce,ko hutawa,bazaka samu kayi ba, Gashi kuma gobe Aunty suhailat ke dawowa, yakamata kadan huta kasha hanya,sannan ta kamo hannun khadija suka fita,shikuma yasamu Dakar kwantawa bisa luntsumemen gadon dayake cikin dakin. ALHAJI SULAIMAN mahaifin Ahmad,shima su biyune iyayensu suka Haifa,daga shi sai ALHAJI KABIR. Shi Alhaji Kabir 'ya'yansa mata uku,da matarsa HAJIYA RAKIYA,wadanda Allah yayi masu rasuwa asanadin hadarin jirgin sama,Wanda sukabar 'ya'yansu,BABBAR itace SUHAILAT wadda a yanzun ta kammala karatun ta,kuma take shirin dawowa Nigeria daga kasar Engiler. Maibimata itace kubura,wadda itama yayi karatun sosai,amma yanzun harkar kasuwancin mahaifinsu,yadawo hannunta,sannan sai 'har autarsu khadija,wadda a yanzun take shirin kammala makarantar secondary. Su biyu Duke rayuwa acikin gidansu,sai ma aikatansu da suke tare dasu,maganar dukiya kam!!akwaita,dama iyayensu sun mutu sun barmasu ita,kuma kubura nakara tafiyar da harkar dukiyar cikin kwarewa da kuma ilimi. Shekara suhailat biyar a kasar Engiler ,run bayabayan asuwar iyayensu,bata kara dawowa Nageriyaba,saida yanzun data kammala karatun ta,takeso tadawo gida dun!din!!dunn!!! Yayan Babansu Alhaji SULAIMAN,mahaifin Ahmad,yasyaso yaran sudawo wurinsa,amma suka nuna sudai subfiso suzauna inda suka saba,dama ga kubura na harkar kasuwanci,khadija kuma tana karatunta. Was he gari kuwa tunda safe aketa aikaxe-aikace,na hidimar tarbar Aunty suhailat,gidan yadau kanshin gurke-girke da soye soye,kowa magani cikin murna yau sunada babbar bakuwa!!! Kubura da khadija sukayi wanka sukasa kaga masu kyau da tsada, Haka shima Ahmad kana nan kayane yasanya. Sunyi masa kyau sosai,sannan suka Shiga mota,Ahmad yaja suka nufi aanyar cikin jirgin malam Aminu kano. Basu jima sosai ba jirgin ya sauna gaba daya duk sun kosa suganta. Cikin shigar Mayan turawane ajikinta,gawata hular gashi data Sanya akanta,kayan jikinta sun kamata sosai. Ahmad baiji dadiba dayaga 'har uwarsa acikin irin wannan yana yin,tamkar ba 'har musulmibarigarnan tata hatta cibiyarta a wane,ga wani da mammen Wanda dayake ajikinta. Cikin murna tabi. 'Yan uwanta tana rungumarsu,tanayimasu kiss,suma murna Duke sosai da ganinta cikin kishin lafiya. Ahmad bai ankaraba sai jinta yayi tafado cikin jikinsa,ta kankamesa tana fadin ,oyoyo!ya Ahmad,ta kaimai sun bata akumatunsa,shikau yana ta kokarin tureta,amma bata fahimcima hakanba,murnar ganin. 'Yan uwanta kawai take. Tace:YA Ahmad ki irin. 'Har ziyararnan?baka taba zuwa inda nakeba. Cikin 'har dariyarsa dabatakai cikiba,domin ranshi baisoba,ganin kanwarsa da irin wannan shigar,yace: Tuba name Aunty suhailat kiyi hakuri,yakara rungumarsa cike dajin dadin ganin Dan uwanta. Shikuma yace kushuga mota muwuce gida. Sannan suka shigo mortar Ahmad Yakuma tukawa suka tafo gida...................🖊️ Fatima Dahiru Funtuwa Binta,don Allah idan baka shirya siye ba kada kadauki Number ta kabari saika shirya Suna isa gida Ahmad yawuce dakinsa cikin sauri,don yagaji da ganin suhailat airin wannan yana yin. Aranar gidan ya kasance cikin annshuwa da farin ciki,bayan anci ansha,sannan suhailat tashiga yo wanka,tayi kwalliya,sai dai haryanzun wasu kayan turawanne takarayin kwalliya dasu. Suna cikin falon gidan sunata fira irin tayaushe gamo,an hadu da 'yan'uwa. Suhailat tace wai ina YA Ahmad banganshiba?duk gamu munfito falo anata fira,inayashige? Khadija tace yanadaki nakaimai abincine,kila baigama Ciba. Suhailat tamike tsaye tanufi inda dakin Ahmad din yake. Zaune tatarar dashi yanata shafa wayarsa,ga Abincin da akakawomai nan ko tabashi bayyiba. Tana isa kusa dashi tasa hannu takarbi wayar,tace bakaci abincinba. Yabata ransa yace aizanci. Takallai sosai tace YA Ahmad meke faruwa? Yayi banza daita Takumacewa naga bakaci abincinba lafiya daiko? Yace lafiya lau,ya amsa mata adakile. Tace fushi kakeyi ya Ahmad? Yadaure dai yace kekika batamin rai. Saita zauna daf dashi,tace menayi kuma daga dawowa ta? Yadago ido yakalleta sosai gata zaune daf dashi,yace duka shekararki nawa akasar turawan?dahar zaki juyar da dabi'arki irintasu,karki manta kefa musulmace 'yar bahaushe,amma kidubi irin shigar datake jikinki,sannan kuma aikinsa niba muharraminki bane ,domme zaki rika kai hannunki ajikina?tashi kibani wuri. Tabishi dawani irin kallo,sannan tace to ya Ahmad kacemani ba 'yar uwarkabace,shikenan daga dawowa ta saika fara fushi dani,inwani abunnayimaka aibatahaka zaka bullominba,saidai ingaba daya nidince bakason gani,kokuma katsaneni. Yace batsanarki nayiba,amma natsani irin wannan mummunar dabu'ar dakikaxo da ita,kidubi kanki kigani mana,haka kikazo kika tarar DA sauran 'yanuwanki?meyasa kika manta datsarin Addininkine?nida kike gani ba muharraminki bane,ballantana inkin hada jikinki danawa kikeganin kamar ba laifi. Tace ya Ahmad daga dawowa ta zakatirkeni dairin wadannan maganganu?basaikanunamin cewar banida wata daraja awurinkaba,nasani,shiyasa kafara fushi dani don injanye jikina daga gareka,bakomai,tamike cikin hanzari zata fita. Yakira sunan ta dakarfi SUHAILAT! Tajiyo takalleshi. Yace banaso kidauki magana ta dawata manufa,kawai dai gyarawa nakeso kiyi,kisani kinbaro waccen kasar,kindawo cikin 'yan uwanki hausawa,toyakamata ace shigarkima tacanza. Tafita tana fadin nidai takuramin kawai zakayi ya Ahmad. Sannan takoma falon da 'yan uwanta suke sukaci gaba da firarsu. Anan kubura keshaidama Aunty suhailat cewa tare zasu tafi da yaya Ahmad Kaduna,saboda Abba yace yanason ganin su, Ammakinsan abinda nake gudu Aunty Suhailat?damunje zacen aure zaitada mana,don tunbakinan yaketayimin nacin inyi aure nikuma nakafamai HUJJA dacewa saikindawo,toninasan dalilin kiran kirankenan. Waitunda yanzun bakaratu nakeyiba,yakamata inyi aure,nikuma Aunty suhailat ganinakeyi idan nayi Aure yanzun kasuwancinnan gaba daya nakasu zaisamu,idanba adalin muji nasamuba,shiyasa naketazullema auren. Aunty suhailat tace to aikuma aure yazama dole,tunda dai baki isa kikafamai HUJJA dacewa kasuwanci zaihanaki aureba,kadai Allah yazaba abinda yafi Alkairi kawai. Ahaka sukaita firarsu harlokacin sallah yayi sukatashi gaba dayansu sukayi Alwalla sukayi sallah. Misalin karfe Tara na dare,alokacin kowa yashige dakinsa,haka kawai saitaji takasa zama dakinnata,tamike tanufi dakin kanwarta kubura ,tayi sallama tashiga,ita kuma tana zaune gefen gadonta,hankalita nakan Televition din datake kallon. Tajiyo dasauri taredafadin,Aunty suhailat Ashe bakiyi bacciba?nadauka zaki kwata kihuta,saboda tafiyar dakikasha. Suhailat ta zauna kusa da ita,tare da fadin bankwantaba,kubura nakasayin baccine kaya nazokibani,donnalura bazamu shirya da Ya Ahmad ba,muddin bandainasa wadannan kayanba,karkiso kiji irin fadan dayayimani dazun,wai inayin shiga wadda bata daceba. Kubura tace aikunfi kusa,saikije kiduba irin kayandakikeso,aikindawo kuma zakufara,kinsan dai shi yaya Ahmad baya gani ya kyale,donhaka kirika kiyayewane kawai Aunty suhailat. Haba kubura amma daga dawowa ta!aiya kamata yabarni inhuta. Kubura tace to aidai kinsan halinsa tuntuni. Aunty suhailat tace keni bama wannan takawoniba,maganar dakikayi dazun,gaba daya nakasa samun nutsuwa,tunda kikafadamin. Kubura tace wace magana kenan? Suhailat tace tafiyar dazamuyi Kaduna,wallahi maganar Abbace banaso,kinsan shi inyaso Abu,kobaka shirya ba,baburuwansa,yanzun ni daga dawowa ta yaushema nanutsu bawanda zan aura. Kubura tayi dariya,tace humf!baki saniba Aunty suhailat,akwai lokacin daya matsamani sainayi aure,yagadai inata gocemai,kawai sayya kawo Mani wani,waiyazo yaganni innayi masa,kinjifa Aunty Suhailat saikace wata haja!gaba dayama Abba tamkar Neman kai takeyi damu. Todayazo wurinadin nasaki jiki munyi fira dashi sosai,sai daga baya cikin hikima nanunama Abba nifa inada Wanda nakeso,cikin ikon Allah kuma sayya amincemin sahakan,sai cewa yayi to intura Wanda nakesidin,sai kawai nayima Ishak magana. Tofa Abbana yanason ganinka,muka shirya nakaisa suka gaisa,Abbafa saiya bijiromin dazancen aure,A yanzun haka Is'hak yakai kudinneman aurena wurin Abba,nikuma nakibada hadinkai ayi auren yanzun. Har saida yazama na cewa muna wasan buya nida Abba,nidai nadaina zuwa Kaduna,shikuma inyazonan damun gaisa,magana tadaya-tabuyu to taukunsu zancen aurene,shiyasa nikuma damun gaisa zangudu,bana karayadda muko hada hanya dashi. Daga baya saina kafamai HUJJA dacewar inajira saikin dawo,sannan kayi baki daya. Nikuma Aunty suhailat inason kasuwanci na. Aunty suhailat tace ammadai aibazai auri kasuwabako?Allah yakaimu Kaduna lafiya. Washe gari Aunty suhailat tayi wanka tasanya leshi maukyau,dinkinyayi mata kyau sosai,amma saiji tayitayi daban dukkayan suntakurata,batadamu da kyawun dakayan sukayi matmata. aganintadai duk Ahmadne yamatsa mata. Tana zaune a falo tanata latsa wayarta. Ahmad yashugo,cikin yabawayace:haba suhailat kinga yadda kikayi kyau kuwa?gaskiya kayan sunyi maki kyau! Tayi murmushi tace nagode ya Ahmad,amma dai duknaji natakura. Yace ahankali zaki saba,kidaure kici gaba dasawa,amma dakinasa wasu damammun kaya,aikinsan bazamu shirya ba,amma yanzun kin gyara naji dadi sosai kanwata. Cikin jin dadin yadda yakulata,tamike tsaye tare DA fadin fita zakayine? Yace e zanfita aikine,kozaki rakani? Tace mezai hana? Kagama sai inkara ganin garin sosai,inga irin cigaban da aka samu bayan tafiya ta. Yace aiko zakigani,don ansamu cigaba sosai. Tadauko gyalenta tayafa,sannan tabiyo bayansa suka tafi. Suna tafiya yanakara nunamata garin,dakuma irin cigaban da aka samu bayan yafiyarta,don wasu guraremma bataganesu,sayya sanar daita. Kawai saita takaleshi dacewa,yaushe zaka koma? Yace sauran kwana biyar,amma Abba yace daku zankoma,don yanaso yaganku,saboda yarabu dazuwa,kuburace tabatamashi rai,shiyasa yadauke kafarsa dazuwa kano. Aunty suhailat tadanyi murmushi tace kubura tafadamani, waisoyakeyi tayi aure. Yace toke mekika gani? Tace lafiya lau ai,yin auren aishine darajarta,Allah ya tabbatar da Alkairi. Yace Ameen,dama kekawai muke jira,don kubura tafiyar da mujinta tuntuni,nimakuma nafutar da wadda nakeso,kinga sauran ke kawai,Allah tafito maki dashi kafin lokacin,sai ayi gaba daya. Aituni taji wata zufa natsatstafo mata agoshi,cikin karfin hali tace:INA kua kasamo mana matar? Yace diyar wan mamanace,kuma nima munkusa shigar da maganarmu wurin su Abba,nasan dalilin daya yace yanason ganinku kenan. Suhailat taciro Tissue tafada share zufar datake Neman tabbata mata kwalliyar fuskarta,yarasa kuma dalilin DA yasa tatsinci kanta airin wannan yana yin,domin jitake gaba daya karfin jikinta yakare,gawata masifaffiyar kasala data dabaibaye dukkan ilahirin jikinta,batada karfi kwata -kwata,kamar anzare mata lakka,tarufe idanunta,tare da kwantar da kanta bayan kujerar mortar,wani matsanancin tashin hankali yaziyarceta,bata kara fahimtarsa abinda yake fada mataba,saidai tabishi da ummf!kawai,harsukakai inda zasukai,yanaba ta labarin irin shakuwar datake tsakaninsa da 'yar uwarsa Hafsat. Bawani irin yanayi suhailat bakasance,a wadannan kwana kin,koda yaushe tanazaube cikin dakinta,harbatasoma wani yakusanceta,saidai ita kanta batasan ainihin abinda kedamuntaba,itadai yanajinta wata sukuku da ita tsawon kwana uku. Misalin karfe biyar na yamma,kubura tanufi dakin suhailat,kwance tasameta bisa gado tana rungume da filo akirjinta,hartayi sallama batasan tashigo ba,don haka tata bata tana fadin lafiyarki lau kuwa Aunty suhailat? Aunty suhailat tatashi zaune tare satin murmushi,tace lafiya ta lau mana baccine yakeso yadaukeni. Kubura tace acikin kwana ki ukunnan naga kinshiga wani yanayi nadaban,Wanda bansanki dashiba ada,dafarko nadauka cewa futawa kike,amma yanzun nafahimci bahakan bane,Aunty suhailat meke damunki??????????? Maukaratu biyoni apage nagaba Daga maison farin cikinku Suhailat tadafa kafadar kubura,Tace bakomai,kuma nagode da kulawarki agareni,amma ni ba abinda yake damuna. Ya za'ayi kiboyemin Aunty suhailat?waye zaki iyafadama damuwarki Wanda yake kusa dake bayanni?karki manta Aunty suhailat,iyayenmu sunrasu,sunbarmu,don hakabakida Wanda yake kusa dake Wanda yafini,bawanda ya cancanci kisanar dashi wata damuwa taki sama dani,inkuwa harni zaki iya boye Mani matsalar ki,to lallai zakita zama da ita acikin zuciyarki,domin kuwa bakida sama dani. Cikin magiya takara cewa,don Allah Aunty suhailat,kifadamani meke damunki? Suhailat takara kallon kubura,sannan tace:ba abinda zaki iya yimin akan matsala ta,don haka kawai kirabu dani. Yakice haka?ko ban iyayimaki komai,aizan iyayimaki Addu'a ballantanama shawara bazata gagaraba. To shikenan kubura tunda kinmatsa,zan fada maki,amma ki adanamin amatsayin sirrinane,karki fadama kowa. Kubura takara gyara zaman ta,tare da maida hankalinta akan suhailat,Tace:inajinki menene? Atsawon rayuwata,tun kafin intafi Engilar,Allah ya jarrabeni da son ya Ahmad,nayi duk iya kokarin dazanyi,inga nadaina sonshi,abin yagagara,sai dai kuma shirmen banza nakeyi,domin kuwa baisamma inayiba. Kubura tace kawai saboda wannan zaki tadama kanki hankali,to kici gaba da SON shi!Nina tabbatar maki zaya soki,karki mantafa,Aunty suhailat yaya Ahmad fa Dan uwankine,wallahi bazai taba kinkiba,ai wannan abin farin cikine awurimmu!Allah ya tabbatar da Alkairi. Suhailat ta girgiza kanta,sannan tace,aibakisan abinda kefaruwaba,a yanzun haka ya Ahmad yanada wadda zai aura,kuma harsun dai daita . Kubura tace to shine me?namiji daya aimujin mace hudune,kadama wannan yadameki,indai kin tabbatar kina sonshi. Suhailat tace kubura Ya Ahmad bazaisoni da aureba,yana dai sona amatsayina na 'yar uwarshi,amma ayanayin maganganunsa,babu alamar zai taba sona da aure,bashshidai ayi wasa ayi dariya kawai,amma yanada wahala yasoni da aure. Kubura tace haka kike gani Aunty suhailat? Aunty suhailat tace hakanema Tabbas! Kubura tace to akwai yadda za'ayi,yau sauran kwana biyu mawuce Kaduna,don haka yanzun basai gobeba,kitashi kishirya,ni zannema maki mafita,wurin wani malami zankaiki,don bazai yuwu kibason Abu yagoce makiba,muje yatayiki da rokon Allah,kamar yadda kike son yaya Ahmad shima yasoki haka,koma fiye da haka,domin na tabbatar damunje kaduna ,Abba zancen Auren nan zaitada,kuma kinga aibazai yuwu ni inyi aure,yaya Ahmad yayi aure,kemubarkiba,don haka tundawuri munemi maganin abin. Duk dadai abin baikwanta mataba,haka nan ta shirya suka tafi. Suna cikin tafiya take cema kubura,wallahi nadade inason ya Ahmad,amma bazan iya sanardashiba,gashi har yananeman subucemani,INA yimasa wani irin so dani kaina narasa gane kaina,idan ban auri ya Ahmad ba bammasan yazanyiba. Kubura tace kima daina wannan maganar,insha Allahu zaki Aure shi,ba abinda zai hana saidai inbamuje wurin malam musan nanba,domin ni inada tabbaci akan haka,nasha kawo kawayena wurinsa,akan matsaloli daban-daban,kuma anasamun nasara sosai,don gaskiya banga yayi aikin daba'asamu nasara ba,don haka kema kikwantar da hankalinki,kisa arankima kawai kin samu,awannan karamin aikine a wurinsa,in Allah ya yadda sai kin auri yaya Ahmad. Sai Aunty suhailat takarajin karfin gwiwa akan wannan tafiyar tasu. Cikin sa'a kuwa sunsameshi. Malam musa Dattijone fari,Wanda furfura tagauraye gashin kansa Dana fuskarsa,mutumne mefara'a sosai,don haka cikin sakin fuskarsa da karramawa ya karbesu,domin dai dama kubura ba bakuwa bace a wurinsa,tasha kawo mai mutane yana taimaka masu da Addu'a. Bayan sungaisa,kubura tayimai bayani kamar haka. Malam yau kuma. 'Yar uwatace nakawo,akan wata matsala data shamata kai,wani Dan uwammune sunansa Ahmad,to Allah yajarrabeta da sonshi,saidai kuma shi zamma iya cewa baisan tanayiba,to shine mukeso malam yataimaka mata da Addu'a Allah yakarkato da zucuyarsa agareta,dontasamu natsuwa da kwanciyar hankali. M-musa yakara kallon suhailat,yace to baiwar Allah,duk dadai nasan babu abinda yagagari Allah,Allah zai iya sauya Abu aduk lokacin dayaso,ammani nafiso ace abin nan dakikeso yazama na Alkairi agareki,domin idan babu Alkairi acikinsa to barinshi shi yafi,domin kuwa Allah yafimu sanin abinda zaifi zama Alkairi agaremu,idan bai baki abuba,kada kiyi fushi,watakila abin nan ba Alkairi abane agareki. Amma tunda kince agayama Allah,shikenan,duk dadai yama fiki sanin abinda ke cikin zuciyarki. Kafin nan zanyi maki istihara,zanbaki wasu Addu'oi DA zakiyi,nima zanyi anan,domin mutabbatar dacewa,shin abin nan alkairine koko akasin haka,zaki samu abin koko bazaki samuba. Idan babu rabonki acikin wannan Dan uwanaki,to lallai kiyi hakuri,sai Allah yasauya maki da Wanda yafi shi,ni kuma intayaki Addu'ar Allah yacire maki abinda ya jarrabeki dashi,don haka zaku tafi ,nanda kwana biyu saiku dawo,domin muga abinda Allah zayyi. Sukayi godiya ,sannan yadauko wasu Addu'oi yabata,nansukuma,suka ajemai kudi masu yawa. Nan suka tafo.Ahanya kubura na kara tabbatar mata dacewa lallai zasu samu nasara,domin aikin malamin nan,kamar yankan wuka yake. Tayi amfani da Addu'oin nan da M-musa yabata,saidai bawani canji game da yadda take jin son ya Ahmad. Koda yaushe taganshi kara sonshi take,take kumaso ace itace tamallakeshi amatsayin mujin aure ba wataba. Tana zaune itada kubura suna firar gobe zasu wuce Kaduna,kuma gobenne zasu koka wurin malamin su. Suhailat tace kinsan wani Abu kubura? Haryanzun inason ya Ahmad,irin son danake jin bazan iya rayuwa ba tare dashiba,yanzun idan malam yace babu rabona ga ya Ahmad ya zanyi? Kubura tace kimadaina wannan maganar,yaya Ahmad kamar kinsamesa,ai alamun nasarane kiji kina kara sonsa,kuma Nina tabbatar maki dahaka,nubanaso inji kina karyar da zuciyarki,kisa kawai aranki zaki samu,domin dai........ Sallamar Ahmad ce takatsemasu firar dasukeyi,suka amsamai tare da fadin barka dawo kenan? Yace aiko kubura nadawo,nazone insanar daku kufa shirya,Donna gaji dazama garin nan,gobe dawuri zamu tafi,don haka kuyi shirinku tun yau. Kubura tace yaya Ahmad wane irin dawuri,saikace dai ana korarmu,zadai mushirya yau,amma gobennan saikadanyi hakuri,muje mudawo. Yace kinjiki dason yawo,INA kuma zaki? Tace kayana zan amso wurin wata kawata. Yace to don Allah karki bata mana lokaci,don banason mukai azahar anan. Tace. Ahh!insha Allahu bazamukaiba. Yajuyo yakalli suhailat,yace yaya dai kanwata,garinne koko jikin? Tayi murmushi tare dafadin,duka babu Wanda babu. Yace: sub hanallah!tare dakara matsowa kusa da ita,yace meke damunki? Tace kaina naji yana yimin ciwo,amma nasha magani. Dai dai nan kubura tatashi tabar masu falon, Ahmad yace Allah yasauke,amma idan kinji ba dama anjima kishirya sai inkaiki Asibiti. Talumshe idanunta cikin wani irin yanayi mai daukar hankali,tare dasa hannunta tadafe goshinta,tace wash!!Allah na!!cikin shagwaba. Shikuma hankalinsa nakanta,yace suhailat yadai? Tace bakomai. Ya zauna kusa da ita yakafeta da idanu.hartaji tatakura,tace kallon menene wannan? Yayi murmushi yace kyau naga kinyimin,sabanin yadda kikazo daga Engilar,kinga yadda kayan nan sukayi maki kyau kuwa?naji dadi dakika karbi magana ta dawuri haka,nadauka zansha wahala kafin inja hankalinki,wurin sanya tufafi irinnamu,amma sainaga cikin sauki. Tace yaza'ayi kasha wahala,tunda nima banaso insamu matsala da yayana,domin na tabbatar dabandainasa kananan kayaba kullun sai nayi rigima dakai. Yace Tabbas! Don kuwa zantakura maki harsai kibdaina. Baki bani labarin Engiler ba. Tace kaida kaki kawomin ziyara. Yace tuba nake ayi hakuri. Tamakale kafadarta cikin shagwaba tace nakiyi. Yasa dariya tare da daukar filo yajefamata,sannan tamike tsaye tare DA fadin,natafi kira kubura kuci gaba dafirarku,sannan yafita. Washe gari tunda wuri sujashirya suka koma wurin malam musa,domin aranarne sukeso suwuce Kaduna. Cikin sakin fuskarta yayi masu maraba dazuwa,sannan suka gaisheshi,suka zauna kan tabarma. Yafara dacewa. To Alhamdulillahi,ansamu yadda yakeso. Nan danan fara'a tabayyana a fuskarta kubura da suhailat,cikin doki dajin dadi suma sukace,Alhamdulillah!! Yaci gaba dacewa akwai Alkairi hadinki da wannan yaron,Tabbas!Nina gani,kuma zaisoki sosai,kikwantar da hankalinki,amma kikara hakuri,Ahmad shine mujinki insha Allah,zaki Aure shi kuma akwai Alkairi. Kubura tace to malam ammafa nasan akwai wadda yakeso,kuma ita zai aura,yaza'ayi kenan? Malam yace bazai Aure taba,wannan dindai itace matarsa,kuma zanci gaba dayi maki Addu'a. Sannan yadauko wani jiko yabata,yace tashanyeshi anan,sannan yadauki wani rubutu kulli uku yamikamata,yace kwana uku zakiyi kinashan wannan ,sukayi godiya sannan suka tafi. Aranar suka tafo Kaduna,Ahmad ke tukawa sai khadija NA kusa dashi,suhailat da kubura suna kujerun baya, Sun isa Kaduna lafiya Alhaji SULAIMAN mahaifin Ahmad yanada mata,sunan ta sa'adatu,'ya'yansu Hudu da ita,maza biyu mata biyu,Umar da Yusuf,Zainab da Shamsiyya . Bayan tafiyar mahaifiyar Ahmad saudiyya ya aureta,shekararsu shidda kenan da auren,Ita kuwa H-Aisha da daya kawai suka Haifa da Alhaji sulaiman,wato Ahmad. Sunakiranta da Aunty sa'adatu,gidan yakaure da murna,yaran sai tsalle suke,Ga Auncle!ga Auncle!!!yabisu yanadagasu daya bayan daya yana saukewa,don sunsaba dashi,dama yanayimasu wasa sosai ,yana kuma yimasu siye-siye. Bangaren Aunty sa'adatu suka sauka,sukayi abinci sukayi sallah. Shikuma Ahmad gaba daya yakosa yaganshi agaban sahubarsa Hafsat ,don haka yayi wanka yasha turare maikamshi sosai gamidasa bugaggar shaddarsa,yadauki mukullin motarsa sai gidan kawunsa Alhaji SALISU. Hafsat tayi farin cikin ganinsa sosai,ta gaisheshi. Shikuma yana tambayarta ya kewa? Tayi dariya tace aidaga yau takare,tunda gaka INA gani,amma nasha wahala rashin ganinka daka tafi,idanuna sunrasa Amincin da sukafiso. Yace to aigani nadawo,sai suzo suyita kallona harruwan cikinsu ya kafe,nasameki lafiyako? Tace Iee toh!,lafiya lau,tunda nawarke daga jinyar daka Sani,yaya kabarosu? Yace dasu mukatafo sunan gidammu. Tace don Allah!hada khadija?yaushe zaka kawomin kawata?khadija sarkin surutu,kawatace sosai . Yace saidai kekishirya inkaiki. Tace aikasanni bana zuwa gudanku,kawai sai inje gidan surukaina?AA nidai nasan kunya. Yace kuma kinsan wani Abu?inaji ajikina cewa nakusa malkakarki amatsayin matata,domin NA tabbata Abba yana shirin Aurar da 'ya'yansa bada jimawaba,yakika gani?kinshirya??? Yasa dariya tare darufe idanunta,nansukayi firarsu sosai,sannan daga bisani yashiga wurin iyayenta. Alokacin kawunsa Alhaji salisu yananan . Yace A Ah!Ahmad ne?sannudazuwa. Ahmad ya amsa yana wani sunsunne kai waishi kunya yakeji,sannan ya zauna bisa kafet,kansa akasa. Alhaji SALISU yace kasamu Hafsat dinko ? Yace. e naganta yanzumma nafitone gida zanwuce,shine nabiyo tanan, Yace to shikenan yakake ganin tsakaninka da yaribyar?kun dai daita kankune?domin inaso mushuga cikin maganar,saboda babu abinda zamu tsaya jira,kafin H-Ausha tadawo,yazama cewa saidai saidai tazo bikin ,don haka kasanar da mahaufinka idan kunshurya yazo inason ganinsa,domin. Atsaida maganarnan,aibawani juran da za'ayi. Cikin farin cikin dabai taba kasancewa acikinsaba ya tsinci kansa.domin kuwa dama tuni yanajiran wannan ranar,gashi kuwa abin yazo akan gaba,donya tabbatar dama abinda Abbansa keshirinyi kenan,don haka ya amsa mai cikin kunya dakuma jin dadi,sannan yayi sallama yatafi gida . Misalin karfe Tara nadare,lokacin Alhaji sulaiman yadawo gida,yana tare daduka 'ya'yansa,cikinnishadi da farin ciki,ga matarsa Aunty sa'adatu,gaba dayansu duk suna zaune a babban falon gidan. DA sallama yafara magana,sannan yabude masu taron da Addu'a ,yaci gaba cewa To kubura yanzundai Allah yanufemu da ganin dawowar yayarki suhailat,ancedai karshen tuka-tuka-kukk!gashi lokaci yayi,amatsayina na Wanda hakkin aurar daku yake akaina,to yazama lallai inyi kikari insauke wannan nauyin,kinga suhailat,har wasan buya mukarikayi da kanwarki,saboda inajemata da zancen aure,nima Dana ga haka saina zuwa,narabu da ita,inga iya gudunta,badai tace saikin dawo ba,to yau gashi Allah yayi dawowar ki. Don hakani watannan basai yakareba,zan tsaida lokacin aurenku,in Allah yaso gaba dayanku,idanna aurar daku,khadija zata dawo wurina,saitaci gaba dayin jami 'arta anan Kaduna. Yakuma cewa kubura. Tace Na'am Abbah. Kokinsan is'haka yasha zarya wurina,akan zancen Auren ki inakaramai lokaci?To don haka bada jimawaba zanbashi izinin yaturo atsaida lokacin auren. Sannan yajuya da kallon shi zuwaga Ahmad,yace kaikuma ya ake ciki? Gaba daya kubura da suhailat suka maida kallonsu agareshi,suhailat cikin wani irin tashin hankali take kallonsa. Yace Abba dama dazunnaje gidan kawun munyi magana dashi,saiyace yanason ganinka. Alhaji sulaiman yace kundai daita dayarinyarko? Ahmad yace e Abbah. Abba yace to shikenan,Allah yakaimu gobe zanje insamesa,kekuma kubura jibi is'haka zaituro asa rana,saboda.............. Kawai saidai ganin suhailat sukayi tamike tsaye,tanufi daki da sauri ,tana zuwa tafada kan gado,wani irin matsanancin kuka yakwace mata,bajimawa kubura tabiyota,tazauna kusa da ita,tare dasa hannayenta guda biyu tadagota zaune,tace Haba Aunty suhailat miye haka?kibar tadama kanki hankali,har afahimci halin dakike ciki,don yaya Ahmad yace yana Neman auren wata,aiba shine yin aurenba,kima daina damuwa,Nina tabbatar wannan auren sayya lalace,kamar yadda malam yafada,kecedai matarsa,domme zaki rika damuwa tunda wuri haka? Suhailat tashare hawayenta,tace kubura gani nakeyi kamar Ya Ahmad bazai aureniba,ko irin damuwa dani dinnan mafa bayayi,nikuma kullun soyayyarsa kara azabtar dani takeyi,wallahi kubura idannarasa ya Ahmad zan iya mutuwa!! AAh!bari fadin haka Aunty suhailat,mezai hana bazaki aureshiba?zaki aureshi mana. Suhailat tace tobagashi nanba,yana fadama Abba cewar sun daidaita da yarinyarba,kinga bama tani yakeba kenan! Kubura tace to insun dai daita shine auren?aibashine aurenba,kuma kinsani so nawa akesa rana kuma daga baya afasa,nibanaso kikaraya Aunty suhailat,INA tabbatar maki dacewa aikin malamin nan,ba'atabayi ba'asamu nasara ba,kema kuma natabbatar za'samu. Suhailat tasamu karfin gwiwa,gameda zancen da kanwarta kubura takeyimata,don haka tasaki fuskarta,tare DA fadin to shikenan. Dai dai nan Alhaji sulaiman yashigo dakin,tare dayin sallama,yace lafiya?meya samu suhailat din? Tace Abba kaina naji yana min ciwo. Yace Ashsha!Allah yasauke,bari insa Ahmad yakaiki Asibiti,yanzun don kada ciwon kan yahanaki barci. Sannan yafita yasanar da Ahmad yadauki mota yakai suhailat Asibiti, Yace to Abbah Suna cikin tafiya yake cewa,suhailat wannan wane irin ciwon Kaine ? Tunjiyafa kika fadamani,amma haryanzun bai saukaba? Tace yasauka dawowa dai yayi. Yace bakisha magani ba jiyako? Tace nibanshaba. Yakalleta sosai yace saboda me?baki son shan maganiko?to shima din bazamu shiya dakeba,indai bazaki rika kula da lafiyarkiba. Harsuka kai Asibitin ysnayimata magana,Alokacin ita kuma takasa cewa komai,kuma takasa fahimtar shin awane hali take yanzun farin cikine koko akasin haka? Anyimata aune aune sosai,sannan akabasu sakamakon,Ahmad yafara dubawa,lokaci guda kuma yadago kai yakalleta arazane,yace Hipotation?meya hadaki da hawan jini? Tasadda kanta kasa,shikuma yatsareta da idanu,dayagadai takasa bashi amsa,sai ya tafi,ita kuma tabiyo bayansa,suka shiga mota bayan yabiya siyomata magungunan. Bawanda yakara yima wani magana acikin su,kowa da abinda yake rayawa acikin zuciyarshi,har suka isa gida. Suna isa falo ya ajiye magungunan sannan yazauna, yace dauko ruwa kizo kisha maganin. Tabude firij tadauko robarruwa,ya karba yazuba mata acup,sannan yaci gaba da balle mata maganin,daya bayan daya,yana bata tanasha,saida tagama,yace nizan rike maganin,idan lokacin yayi,nizanzo inbaki dakaina,domin nalura basan shan magani kikeba,yatashi yawuce dakinsa . Ita kuma dawani irin kallo,cike da kaunarsa,acikin zuciyarta,bayan yabace mata dagani,tace ya Allah kamallakamin ya Ahmad. Is'haka yaturo da magabatansa,ansanya masu rana da kubura,haka shima Ahmad da Hafsat ansanya ranar Auren su. Watanni shidda Alhaji sulaiman yasanya,yana kuma fatan Allah ya kawoma suhailat nata donya hada yayi baki daya. Sannan yaci gaba da nemamma khadija makarantar dazataci gaba dayi,domin. Kuwa a yanzun soyakeyi tadawo hannunsa dazama. Suhailat na kwance ,kubura nayi mata firfita,duk da sanyin A C dayake bugawa a dakin,amma wata zufa kekara yankomata,tana kara dafe kanta,dayake tsananin yimata ciwo. Kubura tace:ni Al amarinnan Yakima Aunty suhailat har tsoro yake bani,gashi nan danan Dan tashin hankali bawani meyawaba,harciwo yazo yahaye maki. Suhailat tayi saurin bude idanunta,tace yanzun kina nufin abinda yake damuna bawata matsala bace?kina ganifa yanzun ansa ranar auren ya Ahmad da wata,baniba,bakisan yadda nake jinsa bane acikin zuciyata shiyasa,saranar aurenshi da akayi da Hafsat yanunamin cewa bazan aureshiba,domin bawata alama dazatasa afasa wannan auren,shiyasa nayi muguwar karaya sosai kubura,Ya Ahmad barabona bane ,dai dainan kuka yakwace mata,hadi da zazzafan tari.,tace bazan iya auren waniba idan ba Ya Ahmad ba ,INA sonshi. Kubura yace kada kikaraya Aunty suhailat,haryanzun munada sauran lokacin,badai wata shidda akasa ranar aurenba,tozaki iya ganin talalace kafin lokacin,yadawo kuma yace yana sonki,domin ni narigafa NA yadda da maganar malam. Suhailat tace taya za'ayi bazan karayaba?kwata-kwata Ya Ahmad bai taba furtamin wata Kalmar dazan San yana sonaba,kubura juna Daff!,daku rasani,idan ban aureshiba mutuwa................. Kubura tayi saurin rufemata baki da hannunta,cikin tashin hankali,tace bazaki mutuba Aunty suhailat,insha Allahu zaki aureshi ,bari gobe mushirya mukoma kano,saimu sanar da malam halin da ake ciki,in Allah ya yadda komai zai daidaita. Haka kubura taita bata magana harta samu tashawo kanta. Washe gari akaita rabon goron sa rana,ana kaiwa gidajen 'yan uwa da Abokan arziki, hakan yakara tada masuhailat hankali, Don har sunyi shirin tafiya kano. Ciwon ta yatashi,cikin hanzari kuwa akakaita Asibiti ,taimakon gaugawa aka bata sosai,kuburace kejinyarta,Tasamu sauki. Lokacin da Ahmad yazo dubata,yake tambayarta waidama tanada wannan lalurarne? Kubura tace gaskiya bata dashi,daga bayane dai abin yasameta. Yamaida kallonsa akan suhailat,yacewace damuwa kikesanyawa arankine hatta kaiki gahaka? Kubura takalli suhailat suka hada ido. Yamaimaita cikin magiya,yace waimeke damunki?waye yake bata maki rai?miye kika Nema kikarasa? Gaba daya tambayoyin sunyi mata yawa,takasa bashi amsa,saidai kafesa da idanu kawai datayi. Yakara matsowa kusa daita,yace fadamin menene? Dai dai nan kubura ke kyafta mata ido sai tasanar dashi,ita kuma suhailat tagirgiza kai,alamar bazata iyaba,sai wasu zafafan hawaye suka gangaromata. Cikin kika tace Ya Ahmad nima bansan abinda yake damunaba,. Yace to kirika shan maganin ki akan lokaci,kuma kidaina yawan tunani kinji? Ta daga mai kai alamar eh Kwanansu biyu a Asibiti sannan akasallamesu,suna dawowa gida suka shaidama Abbah da Aunty sa'adatu,cewar suna so suje kano. Abba yace toke suhailat jikinnaki yayi saukine? Tace nasamu sauki. Yace to kidaina yawan damuwa,ko Engiler kikeso kikomane? Tace AA Abba Yace tome kikeso?yaci gaba dacewa,kiyi hakuri suhailat,in Allah ya yadda,gaba daya zab aurar daku,bazasu tafi subarkiba,shiyasa nasan ya ranar da tsawo,kafin lokacin kema Allah tafito maki danaki,mujin,kinji,to kikwantar da hankalinki. Gaba daya sunyi mamakin yadda Abba takusa gano miyene matsalar ta. Sai cewa tayi aini Abba dacewa nayi aure nakesoba,. Yace ainasani,ninedai naga dacewar hakan,amma kuje kudawo,za'asan yadda za'ayi,kwana nawa zakuyi? Kubura tace kwana Hudu Yace to Allah yakiyaye. KANO Misalin karfe Hudu darabi na yamma,suka ziyarci gidan m-musa,sun sameshi. Cikin fara'arsa da sakin fuska,data zamemai dabi'arsa,yatarbesu. Su kuma suka gaisheshi,sannan sukayi gaba dacewa. Akan maganar nannedai mukadawo,Ahmad din datakeso dinne akasanyamaranar aure dawata,ita kuma gashi duk takasa kwantar da hankalinta,to shine mukeso malam Asama mana mafita. M-musa yajinjina Kansas sannan yace:Toh!Al amarinne na Allah,lokacin dayawa dama yake badawa,amma Tabbas ni nasan wannan Abu zayayi jinjiri,shikuma jinjiri ga Al-amarin ubangiji alkairine,amma maganar ansanya mashi rana,aiba shine yin aureba,don haka zankumayin bakin kokarina,don ganin Auren nan tadawo gareki,Nina kara tabbatar maki dacewa kecedai matar Ahmad,saidai shi Dan Adam akwai shi da gaugawa,bayasonjinkiri,ammani inakarabaki hakuri,kikwantar da hankalinki,abin nan dakikeso zai samu,zankuma kara baki wani taimako yanzun. Nan da nan yasa Allo yayi rubutu yawan ke,yahadasu DA wasu garin magani,sannan yabata yace ta shanye,bayan nan kuma yabata wasu,yace tafi wanka dasu tsawon kwana uku,sannan yaci gaba da karfafa masu gwiwa,akan lallai bukatar su zata biya, Nan suka kara ajiyemai kudi masu yawa,sannan sukayi sallama dashi. Bayan sunyi sallar isha'i,suna zaune,suhailat kecema kubura. Nikau damukaje wurin malamin nan,saina karajin karfin gwiwa,koba komai dai naji sanyi acikin zuciyata,hankalina yakwanta,kuma nakara yadda da Al amarinnan. Kubura tace aidama Aunty suhailat kekike tadama kanki hankali,ai saranar auren yaya Ahmad,bashine yake nufin kinrasa shiba,kobakomai kuma ai namiji daya mujin mace hudune,nifa nayadda da aikin malamin nan,domin kawayena dadama sun jaraba ,kuma ansamu nasara,shiyasa ni bantaba karaya akancewa bazaki auri yaya Ahmad ba,kawai dai dan jinkirine aka samu ,nikuma NA tabbatar kafin watanni shiddannan,sucika saimunga biyan bukata. Suhailat tace to aini abinda yake dauremin kai shine,malamfa yasha fada Mani cewa nice matar ya Ahmad ta farko,to amma yaya hakan take faruwa? Kubura tadanyi jimm!sannan tace,zai tabbata mubada watanni biyar mugani,idan baisauya ra'ayibsaba,Nina tabbatar kafin lokacimma komai ya daidaita. Amma kuma Aunty suhailat inaso intambayeki. Suhailat tace menene,? Kubura tace nayi mamakin yadda akayi kika kamu da son yaya Ahmad lokaci guda,gashi haryana Neman yasa kirasa lafiyarki,idan baki samesaba,meyasa kike sonsa??? Humf! suhailat tayi ajiyar numfashi,tare dayin wani Dan guntun murmushi,tace: Balokaci guda nakamu dason Ya Ahmad ba,kinsan ita DABI'AR ZUCIYA tanason mai kyau tata mata,tuntuni ya Ahmad yakejidani,idan yazo gidan nan kafin ya ambaci sunan kowa,niyake fara kira,yana Jana ajikinsa sosai,alokacin har daddyn mu NA fadin ba wadda jininsa yahadu Dana Ahmad agidannan irin suhailat kowani wuri zashi sayyace suhailat zoki rakani,kafin yace wani yamikomai wani Abu yace suhailat tamikomai,harya zamana idan Ahmad yazo gidan nan bayacin abinci da kowa saida suhailat,na shaku dashi sosai. To irin wannan kulawar dayake bani,saina dauka soyayyace ta aure bawai ta tsaya ga 'yan'uwantakaba kawai,saina sakankance akan cewa nan gaba Ya Ahmad zai zama mujina. Nayi kewarsa a Engilar sosai,sai dai dayake munayin FIFA dashi ta waya. Kubura idan kikaji yadda muke fira da ya Ahmad zaki dauka wani saurayinane Wanda mikeda Alkawarin aure dajuna,so dayawa inmuna fira dashi kawayena sukan dauka soyayya mukeyi,duk danidama ahaka nadauki abin,amma kuma kawai daga dawowa ta sai ace ansanyamai ranar aure dawata?tayaya za'ayi hankalina bazai tashiba?? Idan kuma hakane miyene ma'anar firar damukeyi dashi awaya,?miyene ma'anar kalamai dakuma soyayyar da yake nuna Mani azahiri,Wanda azuciyarsa Ashe bahaka bane,meyake nufi kenan ??yau darata yake ?idan haryasan ba aurena zayyi ba meyasa ya yadda nasaba dashi?meyasa tun farko bai rika janye jikinsa daga gareni ba?harya bari nayi sabo dashi. Wallahi kubura inason ya Ahmad,idan bai aureniba yacuceni!!! Kubura tace tabdijan!!yanzun samunshi zakiyi ,kiyi mai gwari-gwari,kiji dalilin dayasa yasakar maki jikinsa da kalamansa har kikayi sabo dashi,kiji dalilin dayasa yake fada maki kalaman da wadda kakeso da aurene kawai yakamata tajisu daga agareshi,wannan aiyaudarace!!lallai kisanar dashi abinda alakarki dashi tahaddasa maki acikin zuciyarki. Suhailat tace AA bazan iyaba,amatsayina namace,bazan iyasamunsa infadamai damuwataba,kuma kema koda wasa bance kufada wani sirrinaba,kuyi hakuri kawai,Tabbas idanbarasa Ya Ahmad kuma zaku rasani,donko soyayyar shi bata kasheniba,NIZAN KASHE KAINA!!!! Cikin tsorata kubura tace bazai yuwuba Aunty suhailat!!dolenema saikin aureshi!!bazamu rasakiba,duk tahanyar dazamubi zamubi,wannan ai yaudarace!!! Suhailat tace bakomai ,mudai kara hakuri mugani zuwa wasu watannin,muga abinda Allah zayyi. Kwanansu Hudu a kano,cikin kwana hudunnan suhailat duk ta gama amfani da magungunan da m-musa yabata,sannan sukayi shirin dawowa Kaduna . Bayan sunyi kwana biyu a Kaduna ranar wata juma'a. Dayamma,sunyi wankansu,sunyi kwalliya,Ahmad yashigo falon,ya Tarar da suhailat,cikin fara'arsa,yace kanwata kuzo inji Abba. Tamike tare da fadin gani nan zuwa,tabi bayansa,tana fadin INA Abban yake? Yace mata yana dakinsa,biyoni inrakaki. Tace to yana gaba tanabinsa a baya,tana kara kallonsa,sonsa nakara yaduwa acikin zuci da sassan jikinta. Yana kaiwa kofar dakin sayya tsaya,yace to shiga,nakawoki ko tsoro kikeji? Tayimai wata irin harara dabatasan lokacimma datayitaba,acikin. Idanunta cike datsantsar son sa, Yadun kule hannu zai kaimata duka cikin wasa. Tayi baya dasauri,tana dariya, Yace aidama nace matsoraciyace ke,inba hakaba aikinsan bazan iya bugunkiba. Tace ya za'ayi insani,tunda gashi naga Alama. Yadan bubbugar mata kumatu ahankali yace:kishiga Abban yana nan ciki,sannan yajuya cikin sauri yawuce. Ita kuma tabishi da kallo harya bace mata,sannan tayi sallama tashiga cikin dakin. Yana zaune bisa kujera yace, Suhailat magana dama nakeso inyi dake . Tace inaji Abbah,duk dajin datayi kirjinta na dukan uku uku,don batasan irin maganar dazayyumataba. Yace:suhailat kinada Wanda kikesone?kuma kyka shirya dashi koko? Tace AA tahanyar girgiza maikai datayi. Yace to shikenan,anjima bayan anyi sallar magariba zakiyi bako. Cikin wani matsanancin firgita tadago kai takalleshi,amma saidai bata iya gaddama abinda tazo mata dashi ayanzun,nan da nan taji zufa naneman rufeta,azuciyart tace To wai INA zancen ya Ahmad,kodai bazai soni bane?? Alhja sulaiman yaci gaba dacewa,don haka saiki shirya,Dan Dan wani abokinane,Alhaji Hassan,tummuna yara muke tare dashi,to shima dannashi guda dayane,mahaifin ki Alhaji kabiru yasanshi,duk tare mukataso,to shine mukeso muhada wani zumunci a tsakanin 'ya'yanmu. Gaskiya suhailat idan kika aureshi kin more ma aure,yarone mai natsuwa,ga kwakwkwaran aiki,don Allah kada kibani kunya,ki amince da wannan zabin danayimaki. Nan dai yaita bata magana,Wanda daga bayama daina fahimtar abinda yake cewa tayi,saidai daga karshe taji yace: Jeki cikin gida kishirya,bayan magariba zaituro kiranki. Cikin rashin karfin jiki tatashi tawuce,daki,tana zuwa ta fada kan gado tafashe da kuka. Kubura tamatso kusa da ita,tare da fadin mekuma yabata maki rai yanzun? Suhailat takamo hannunta tareda fadin zauna kiji,sai Abbane yakeso yahadani aure dawani,wai Dan Dan Abokinsa Alhaji Hassan. Kubura tace aishine Wanda Abbah yaturo wurina,to Aunty suhailat ki yadda dashi mana,bayada wata makusa kyakykyawan gaskene,gashi aikin costom yakeyi,Allah kau dakin hakura da wahalar da kanki,indai shidin yace yana sonki,kuma bakiga......... Suhailat ta daga mata hannu taredafadin dakata kubura!ke meyasa bakice kina sonshi ba,lokacin dayazo wurinki,koda banganshiba bazabsoshiba! Kisani kubura anayin Aurene da soyayya ,sannantayi karko,bazan biyema irin. 'Yammatannan da auren kawai sukeso,bawai damuwarsu wazasu auraba,duk Wanda akace yafito kawai saita yadda ta aureshi,ba tare dajin sonshi acikin zuciyarta ba,face dai kawai auren takeso. (Musamman idan mace taso aure,kawai bazata tsaya taduba Wanda yayi dai dai darayuwartaba,kuma take sonsa,AA ita kawai bukatar ta ace tayi aure,saikiga idan akayi auren baya zuwa koina,dasundan Dade da auren shikenan sairashin zaman lafiya,todama bashi takesoba,auren kawai takeso,toyanzun kuma tayi,sai alokacin zata fahimci bamashine yadace ta auraba,saikiga auren baije ko inaba,anrabu) Nikuma sonakeyi inyi aure Wanda bazan fitoba,kuma hankalina yakwanta ga Wanda zan auradin. Don haka daga ba. YA AHMAD ba zan iya hakuri da aure!!! Zandaibi umarninAbbah in saurareshi,amma balallaima in tsaya inkalli fuskarsa dakuma tsarin jikinsa ba,domin kuwa banason abinda zai zamema Ya Ahmad kishirya acikin zucuyata . Bayan sunyi sallar magariba,Bakon yazo. Babu laifi tayaba datsarinsa,da kuma yanayinsa,kobata tambaya ba tasan yarone Wanda Hutu dajin fadin rayuwa suka sanyashi atsakiya,kyakykyawan gaskene, (Bacimmadai SO sone,koni danace tazabeshi tabar Ahmad dinnan,domin kuwa babu abinda yafi shi. Yafara dacewa,suhailat ai inazaton kin samu labarina saurin kuburako? Tace e tafara fadamani. Yace Alhamdulillah.sunana Abdullahi,kuma nazone da kokon barata agareki,domin samun siyayyarki. Budar bakinta sai cewa tayi bazaka samuba,domin kuwa inada Wanda nakeso. Yakalleta sosai tare da fadin niko meyasa Abbah zayyimin hakane?kawai baikara wata magana ba yafita. Dakin Ahmad yanufa,sannan yabashi labarin yadda sukayi da suhailat,yakara dacewa,amma Abba yasan cewa yarinyarnan tanada Wanda takeso yasa Nazi Neman ta? Ahmad suhailat tabani mamaki,banyi zaton haka daga garetaba,nibarasama meyasa Daddyna yakeson dole sayya hada auren da diyar Abokin nan nasaba. Ahmad yace don Allah kada kakaraya,nizan shawo maka kanta,domin kuwa tana jin magana ta sosai. Abdullahi yace to aitace tanada Wanda takeso. Ahmad yajinjina kansa,sannan yace to kaje kasanar da Abbah yadda kikayi da ita,kafin katafi. Yatashi yatafi wurin da Abban yake,tasanar dashi. Shikuma Ahmada nan take yakira suhailat a waya. Tazo,DA sallama tashigo dakin,taredafadin gani Ya Ahmad. Yace meyasa bakison Abdullahi? Tayi shiru. Yace tambayarki nake,waye kikeso? Tadago kai dasauri takalleshi,kamar zatayi magana,sai kuma takasa,tamaida kanta kasa. Yakuma cewa kafadamin waye kikeso? Koko sokikeyi shikenan asanyamaki ido kita zama!to shikenan tunda haka kikazaba,ni inyi aure kubura tayi aure ,kekuma saikita zama agida!tunda haka kikeso. Dai dai nan tafashe dawani matsanancin kuka. Yayi saurin cewa tashi kifita kibani wuri! Sai kiyi shirin abinda zaki fadama Abbah idan yatanbayeki. Tatashi takoma dakinta,cikin wani irin rikicewar tunani. To yaya, Ya Ahmad din da malam yace zaisoni,amma yake fadamin irin wadannan maganganu,na tabbata Ya Ahmad haryanzun baifara sonaba. Alhaji sulaiman yayi mata fada sosai akan abinda tayi masa,kuma ya turketa saita fada mashi Wanda takeso. Sai cewatayi yabata lokaci zata kawo mai Wanda takeso kafin lokacin auren su kubura. Cikin bacin rai Alhaji sulaiman yayi fada iyayinsa,akan yarannan sunwatsamai kada a ido,kawai yana cikin fada saiya tuna aiyanada khadija, 'yar autar su suhailat,nan danan yadai daita zancen auren Abdullahi da ita. Aka kumayi sa'a yaran suka amince. Yayi farin ciki sosai yaji kuma hankalinsa ya kwanta,anan yakara tabbatar da cewa,lallai MATAR MUTUM KABARINSA!!!! Don baitaba tunanin zai aurar da khadija ,awannan shekararba. Aunty sa'adatu taso tanuna bataso ya aurar da khadija ba,tace mai. Alhaji nikuwa kayi saurin yanke hukuncinban,duka khadija shekararta nawa?dazaka aurar da ita?saurin girmane kawaifa datayi. Yace kina nufin khadija bata isa aureba?toya kikeso inyi?kinadai gani naturashi ga kubura,bata aminceba,yanzun kuma ga suhailat itama takiya,to sokikeyi itama khadijar inbari tayi girman da zan kasa bata umarni tabi?tunda tana sonshi yana sonta aiba matsala,badai karatu bane?kotana dakintama zatayi. Mahifinsane yakeso ayi wannan hadin,yaturoshi,nikuma banaso ace ansamu matsala daga garemu,tunda dai harsuka roki wannan arzikin aibaikamata ace mumunkasa bayarwaba,kadai Allah yasa Alkairi acikin wannan Al amarin. Kuma kike wannan maganar,ita kanta hafsat wadda Ahmad zai aura,aiba wani fin khadija tayiba,itama duka basha takwas garetaba?kuma aiba auren dole zanyi mataba,aurene Wanda ya yadda itama ta yadda,fatanmudai kawai Allah ya daidaita zamantakewarsu. Aunty sa'adatu tabishi da Ameen. Acikin satin nan kuwa,Alhaji Hassan yakawo kayan sa ranar dansa Abdullahi,haba daya yahado da sadakin da kuma kayannagani inaso. Anandin kawaima ya kashi kudi,domin. Kufito dasu akeyi daga mota kamar bazasu kareba,harda akwatinanta guda uku,shake da kaya,duk cikin kayan gaisuwa suke,gaba daya mutanan gidan yabasu mamaki,don kodaya basuyi zaton hakaba. Sannan kuma ango yakara ba Amaryarsa khadija kudi naira dubu dari biyu da hamsin,250,000 yace tayi siyayya . Farin ciki awurin Alhaji sulaiman ba'a magana,nan danan itama aka tsaida lokacin Auren ta,dai dai danasu kubura da Ahmad. Kowa yashigo yaga irin kayan da aka shigo dasu sayya rike baki. (Lallai kam!nace wai Arziki nabin wasu suna gocewa!!) Ahmad NA zaune adakinsa misalin karfe Tara nadare,yakira Number mamansa dake saudiyya,yake sanar da ita sa ranar khadija . Yayi mamaki sosai hartana cewa Khadija? Kodai suhailat?? Yace AA momi khadija dai. Tace yo yarinyar hatayi girmane? Yace tayi momi,sannan yabata labarin yadda akayi har Neman auren yadawo akan khadija . Tace Allah mai iko!shiyasan abinda yasa yayi haka,Allah yasa hakan shi yafi zama Alkairi. Sunsha fira da mominsa sosai,hartake fada mai,tafara shirye-shiryen tafowa,amma dai saibikin yarage sauran kwanaki kadan sannan zata dawo. Ahmad yayi-yayi hafsat tazo gidansu wai ita kunya takeji,saidai shine yadauki khadija dakansa yakaimata ita. Taji dadin ganinta sosai,don dama kawance sukeyi duk sanda suka hadu,taje mata da kayan sa ranar ta ,itama hafsat din tatayata murna,nan gidan suka wuni harda Ahmad,sukasha firarsu sosai. Kwanaki nata shudewa,watanni nata tafiya,tun ana lissafin auren su kubura saura wata kaza,yanzun har anzo saura wata guda. Babu wani Abu daya canza tsakanin soyayyar Ahmad da hafsat,kullun kara sonjunansu sukeyi,kuma babu wata Alama korashin dai daito da zaisa afasa wannan auren. Hatta yanzun ita kanta kubura da take karfafama suhailat din,jikinta yayi sanyi,tafara karaya dacewa Ahmad zai auri suhailat. Acikin 'yan watannin nan,kwanciyar suhailat Asibiti uku,domin abimma yana Neman yazame mata jiki,domin. A awon da akayimata na karshe,zuciyartama taharbu,hakan bakaramin tadama kubura hankali yayiba. Kuma acikin watannin nan,zuwansu kano wurin m-musa yafi akirga,kullun kuma magana daya yake fada masu.cewar ITACE DAI ZATA AURI AHMAD!!! To ayanzun sunfara daukar maganar tashima ba gaskiya bace,kawai dai yanayine don yaci kudin su. Ranar da akasallamo suhailat daga Asibiti,suna zaune kubura tace: Nigaba dayama nakasa gane irin wannan rayuwar taki,yanzun gashi kinnace kinason Wanda baimasan kinayiba,sai wahalar da kanki kikayi ,duk Wanda yaxo kice bakiso Wallahi danasani da bamma fara kaiki wurin malamin nanba,domin duk shine yake kara kashe maki jiki da dadin bakinsa,har kike ganin lallai Ahmad zai dawo gareki,to amma tayaya zaidawo gareki baimasan kinayiba?kullun malam shike kara gaya maki lallai zaki auri yaya Ahmad,amma kuma haryanzun gashi shiru,basaiki hakuraba. Allah akaroka kuma shi Allah ba'ayimasa dole,wata kila babu Alkairi a Auren ki da yaya Ahmad,shiyasa Allah yaki bashi damar dazaima furta yana sonki,ballantanama kuma shiga yarinyar dayake so. Sannan takara tausasa muryarta tace Don Allah Aunty suhailat kada kibari DOCTOR AUWAL dinnan shima yagoce,ki tsaidashi ayi Auren nan baki daya,indai basokike Abba yayi fushi dakeba. Suhailat takara kallonta,tace wai kubura wane irin. Aure kikeso inyine?sokikeyi inyi aure da mutumin dabai kwanta maniba?wane irin zama zanje inyi dashi?Toni gaskiya ba irin matannan bane,wadanda su auren kawai sukeso,bawai damuwarsu waye zasu aureba. Kiyi hakuri kubura lallai soyayyar Ya Ahmad tana Daf!!da tafiyar da rayuwata ,bazan iya tsayawa inga auren Ya Ahmad dawata,baniba,don haka ni yanzun inasauraron lokacin mutuwatane kawai,kokuma................ Kubura ta katseta da cewa,don Allah kada kikashe kanki" Suhailat tace to zanyi nisa daku,zantafi inda bazan kara ganin ya Ahmad ba,kuma kudimma bazaku kara ganinaba,domin idan har................... Tari ,tareda daukewar numfashi yasarketa,nan danan tafita haiyacinta,da kyar kubura tashawo kanta,nan danan tadauko mata magungunan ta Tasha ,sannan bacci mai Nauyi ya dauketa. Bayan wasu kwana ki suhailat tana zaune acikin barandar gidan,bisa kujera. Ahmad yazo wucewa,sayya hangota,dasauri yatafo inda take,yayi mata sallama,sannan yasamu wuri yazauna, Yace dama inason inyi maki magana. Tadago manta dasauri takalleshi,tare da fadin inajinka. Yace maganar Dr Auwal CE,naga yadaina zuwa wurinki lafiya daiko? Saita bata ranta,don batayi zaton wannan maganar yazo mata da itaba, Tace lafiya lau,nadai sallameshine. Yakalleta a razane yace kinsallameshi kamaryaya?kina nufin kice shima baki aurensa?lafiyarki lau kuwa? Tace lafiya ta lau,kawai dai Wanda nakeso dinne haryanzun baizoba. Ahmad yayi saurin cewa dama akwai Wanda kikeso?A INA yake?don Allah sanar dani,ko INA yake zanje inneminaki shi,suhailat banaso ayi bikinnan batare danakiba. Ganin datayi mai duk yarude yanason jin amsarta,sai cewa tayi Aiwanda nakesodin basai kaje wani wuri nemansaba akusa yake. Yace akusa yake?don Allah fadamin. Waye,? Tadago kai takalleshi kamar zatayi magana,saikuma tayi shiru,wata zuciyar tace mata kisanar dashi kawai,kome zai faru yafaru. Saitayi tunanin,aikuma Kim makara,domin kuwa ayau saura kwana goma sha Hudu aurensa,zaki bata bakinkine kawai,ki tada hankalinsa,kikuma tada hankalin kowa NA gidan,Alhalin abin nan dakikeso basamuwa zayyi ba,yakamata kawai in................. Ahmad yakatsemata tunani dacewa kanwata ya kikayi shiru,baki sanar daniba,please suhailat menene kikeso?banason tashin hankalinki,yanzunfa kin zama sai lallabawa,kodon lalurar dakike tare da ita,shiyasa nake ganemaki auren Dr Auwal zai zamemaki wata garkuwa tsakaninki da wannan ciwon,domin daganinsa wayayyene,zaikula dake sosai,zaki samu tarairaya a wurinsa,kinga daga nan hankalinki zai kwanta,ciwon dakike tare dashi kuma za'a samu saukinsa,wuddin kika samu kwanciyar hankali. Tace aiwanda yasan hakan kawai yakamata yazama mujina,bawanda ake tunanin zai iyaba. Bai fahimci inda maganart tadosaba. Don haka sai cewa yayi,aishima yasani,tunda kobakomai aishine likitanki,don haka shiyafi kowama Sanin matsalarki, da maganin ta,da matakan da za'abi domin. Kawar maki da ita. Tace badhida atakin dazai kawar Mani da damuwata ahannunsa,maganinsa saidai ya jwantarmin da ciwon,amma ainihin maganin ba'ahannunsa yakeba. Ahmad yayi saurin cewa ainayake? Taluradai haryanzun bai fahimcetaba,koko yagane abinda nake nufi,wulakancine kawai? Sai cewa tayi mubar wannan maganar,acikin sati biyunnan zankoma Engilar,shikenan sai kowa yahuta da damuwata!!!! Cikin sauri da razana yamike tsaye,tare da fadin What!!!mekike nufi suhailat?kina nufin kicema bazaki tsaya ayi bikinnan dakeba ?? Itama tamike tsaye kamar zata tafi ,yasha gabanta,tare da fadin baki bani amsaba. Tace e bazan tsaya ayidaniba,dai dai nan wasu zafafan hawaye suka jike mata fuska, Yace:Innalillahi wainna ilaihirrajiun!!Suhailat bansan damuwarkiba,kifadamin menene??? Tayimai wani irin kallo sannan tawuce,tabarshi nan tsaye yanata nazari. Abin yadamesa sosai,Yakima kasa iya tuna miyene matsalar ta . Hardare yakirata a waya yana lallashinta,amma ita takasa bude baki tace mai shine takeso,ba yadda bayyi da itaba,akan tagayamai damuwarta,amma takasa. Daga karshe saicemai tayi Engiler kawai takeso takoma,shine damuwarta Yace kodai kema auren kikeso kiyi? Tace AA aikaima kasan in aure nakeso inyi inada manema,kawai dai tafiya nakeso inyi,kila zai iya nesantani daga damuwata. Yace to miye damuwartaki. Tayi shiru Yakuma tambayarta miyene damuwartaki??? Sai cewa tayi sirrine Yayi saurin cewa suhailat kobakida lafiyane?kike boyewa,idan bazaki iya fada maniba kifadama wani mana,sai anemamaki magani, Tace ni lafiya ta lau. Yace to shikenan saida safe tunda bazaki fadamaniba. Haka yakwana tunane-tunane,waiko zai iya gano damuwar suhailat,amma takasa. Mai karatu ayi hakuri nan zantsaya,saimun hadu awani page din. Daga maison farin cikinku Fatima Dahiru Funtuwa Haka washe gari yanemi kubura tasanar dashi,kotasan matsalar dakedamun 'yar uwarta suhailat ? Amma sai cemai tayi itama batasaniba,domin yanzun kuwa,ko itama tasha jinin jikinta gameda wannan al amarin,domin kuwa kota sanar dashi babu amfanin yin hakan,abinda dai sukeso basamuwa zayyiba,dole takaraya da zancen malam musa,tunda yanzun gashi saura kwanaki kadan ayi bikinsa da Hafsat,kuma bawani alamu dazai nuna cewa za'aiya fasawa acikin wannan 'yan kwanakin,don haka taki sanar dashi komai gameda sirrin suhailat,don haka yahakura. Tun ana saura kwana biyu H-Aisha tadawo,aketa shirye -shiryen tarbarta,kowa yakosa yaganta,musamman Ahmad,Dan ta guda daya aduniya. Dohaka Ahmad din yasanar da Amaryarsa Hafsat cewa lallai tazo gidan ranar da ummansa zata dawo,domin atarbeta tare da ita. Bayadda ta iya,don haka itama tayi shiri,ranarda H-Aisha zatazo itama tanufo gidan,domin sutarbeta. Ranar Alhamis kuwa misalin karfe Hudu nayamma H-Aisha tana gida,karkuso kuga murna,hard a wadandama basu santaba,('ya'yan Aunty sa'adatu) domin kuwa bayan tafiyarta saudiyya aka auri Aunty sa'adatun. Akahada lafiyayyar Dinner,da dama anriga angama shirya komai kafin ta iso,akaci akasha,sannan aka nutsu. Acikin babban falon gidan suka taru gaba dayansu,anata fira acikin jin dadi,tanata farin cikin ganin 'ya'yanta, Gasu kubura gasu Hafsat,tazo itama da kannanta,bayan sunhuta sosai,tafitoma dasu Hafsat tsarabarsu,tunda tafiya gida zasuyi,taraba sosai tayimasu,saibayan ishsha'i sannan Ahmad yamaidasu gida. Airanar gaba daya suhailat batada sakewa,rannan nata abace,tunda taga Hafsat sai cika take tana kumbura,ballantana idan taga yadda Ahmad ke nan nan daita,kamar zata fashe don cika,karma lokacin dataga Ahmad yadaukesu zai maidasu gida,yadda suketa wasa da dariya da ita,hankalin suhailat yatashi sosai. Sodayawan firar da akeyima acikin falon wani abun bata fahimtarsa,don hankalinta ba'anan wurin yakeba,gaba daya kanta juyawa yakeyi. Har Ahmad yadawo batayi wani kyakykyawan motsi anan wurinba Yana shigowa idonsa akanta,yalura dahalindatake ciki,don haka yaje daf!da ita ya tafa hannayensa dai dai fuskarta,tayi firgigit!!ta tsorata. Yace yayadai sarkin tsoro?? Ta kirkiro wani Dan murmushi tayi mai. Yasamu wuri yazauna,tare da fadin,Ummah na!!nakaisu,su kawu sunce sunayimaki sannu da zuwa,suma sunanan shigowa gobe. Tace Allah yakaimu,sannan taci gaba dacewa. Tsarabarku sai abari sa gobe sannan araba. Ahmad yace toni umma tsarabar mekikayimani? Tace tamefa?niyanzun kayan surukata nasiyo,irin tawa gudummuwar,amma sai gobe zanbaka. Yace kaih!!amma umma kinaji da matarnan tawa,mekika siyomata?? Tace set din akwatinane cike da kayansu,zan bayar akaima surukata tsarba,kafin lefenta yazo. Yace kaih!!amma umma naji dadi,gata dason kwalliya!!umma baki ganiba!!! Tace toya za'ayi nagani Tunda BANSANTABA,A'INA KASAMO YARINYAR????? Kafin yabata amsa sai ganin suhailat sukayi tamimmike akasa,numfashinta yana fita da kyar dakyar,sannan tasamu tafasa wata gigitacciyar kara,data gigita duk Wanda yake cikin dakin. Gaba daya hankalin Iowa yadawo kanta,tuni kubura tafashe dawani matsanancin kuka,don atunaninta suhailat tamutu kawai,gaba daya duk akadaburce,akadebo ruwa akayayyafa mata,amma inah!!tariga tayi doguwar suma. Nan danan akafara kici kicin kaita Asibiti,Ahmad yafita yadauko mota. Sukuma nan sunata kokarin yadda zasuyi sudauketa,sunkasa,har Ahmad din yadawo. H-Aisha tace zoka kama mana ita afita da ita. Shima cikin rudewa,yana zuwa yasungumeta Cak!!yasabata awuyansa,yafita da it's yasanya cikin mota. Kubura da Aunty sa'adatune suka shiga motar,sukabishi,hankalin kowa atashe,haka akashigar da ita dakin Asibitin,taimakon gaugawa akaci gaba da bats. Jinintane yahau sosai,sannan kuma zuciyartama tana Neman tabuga,lallai anaso tasamu bacci ishashshe,kuma banda hayaniya a inda take,domin asamu tadawo cikin hayyacinta. Cewar Dr -Auwal. Donhaka sukabi wadannan dokoki. Sannan yakira Ahmad zuwa opice dinsa,bayan sun zauna,yace: Waime kukeyima suhailatne?hakan take faruwa gareta?? Ahmad yace kamar yadda kake tambayata nima haka nake tambayarta,amma bantaba samun wata amsa daga garetaba,ni kaina inatunanin,akwai wani Abu dayake damunta,amma zurfin ciki yahana tasanar da kowashi. Dr-Auwal yace,to lallai kusan menene matsalarta,sannan kufara magancemata ita,idan ba'akawar mata da abinda kedamuntaba,to lallai hakan zataita faruwa,tanashan wahala,don haka koba kaiba,Wanda yafi kusanci da ita tadaure tasanar dashi matsalarta,domin. Asan yadda za'ayi magance mata ita,idan bahakaba,zataita shan wahalane,umma kwananta bai kareba,amma da angane matsalarta akayimata maganinta shikenan. Ahmad yace to shikenan,mungode,in Allah yaso za'ayi bakin kokari don ganin ansanmiye yake damunta. Washe gari haka akaita zuwa dubata,alokacin tafarfado, 'yan uwa duksunzo dubata,har Ahmad ma dakansa yaje yadauko Hafsat tadubata. Ahmad duk yakwashe yadda sukayi da Dr-Auwal ya fadama mahaifiyarsa H-Aisha,dakuma kokarin dayakeso tayi Mashi wurin gano meke damunta. H-Aisha ta jinjina kanta,sannan tace to lallai yarinyarnan tana acikin matsala,toko aure takesone? Ahmad yace mumada munyi zaton hakan,amma daga baya mukagane bashibane,domin kuwa tanada masu sonta,acikinsu kau harda Dr Auwal,to kinga kuwa matsalarta tadabance. H-Aisha tace to shikenan, in Allah ya yadda za'ayi kokari,zan tuntubeta injimiye kedamunta,sannan tawuce tashiga dakin da aka kwantar da suhailat din. Zaune tasameta bids gado,idanun nan NATA jawur,alamar tayi kuka tagaji. H-Aisha takalleta sosai,sannan tajawo kujera tamatso da ita gefen gadon. Tace suhailat kuka kikayi?meyasanki kuka? Tadago takalli umma,acikin muryar kuka,tace:niba kuka nakeyiba. Yace. Yazikice bakuka kikeyiba,alhalin gashi kuma kinayi,taurin kai ko suhailat?kinaso ki murine? Tagirgiza kai alamar Aa Tomeyasa kinsan lalurar datake damunki,zaki rika kuka,kinaso kullun jininki yayta hawane?kiso koke zuciyarki tabuga kimutu gaba data? Toki kwantar da hankalinki,kicire duk wani Abu dayake damunki na kunci,nan Asibitine Inda akenemammaki lafiya,kinjiko?? Tadaga kai taredafadin eh. Haka sukaita jinyarta kimanin kwana uku sannan aka sallameta Rukayya tashigo,da sallama,tare dafadin,Aunty kizo umma nakira. Tace to jekice ganinan zuwa. Bayan tagama,sannan tatashi tanufi wurin kiran da akayimata. Afalonta tasameta,tazauna tare da fadin gani ummah. H-Aisha tamike tare dafadin taso muje. Tayi gaba suhailat nabinta abaya,harcikin uwar dakanta,sannan tanunamata bakin gado,tace zaunanan. Suhailat tazauna jikinta asanyaye,sannan itama H-Aishar tazauna kusada ita,tadan karkato tana kallonta,sannan tace. Tambayarki nakeso inyi,kitsayar da hankalinki wuri guda,kibani amsa,kidauka cewa ni mahaifiyarkice wadda ta haifeki,zaki iya boye mata wani sirri naki? Suhailat tagirgiza kai tare da fadin AA. H-Aisha tace to kifadamin mekedamunki?meyake yawansawa ciwonki yake tashi? Suhailat duk tadaburce,taji wata zufa naneman ketowa dukkan ilahirin jikinta,tayi imani bazata iya sanar dakowa wannan sirri nataba,koda kuwa zaizama ajalinta,ballantana kuma umma,to ince matame?ince danta nakeso?ai abunema Wanda bazai taba yuwuwaba,to amma yazanyi da ita yanzun data turkeni?dole ko karyace infada mata,don bazai yuwu intafi banbata amsaba,komain......... Suhailat! H-Aisha takatsemata tunani,tace meke damunki??? Suhailat tace iyayena nake tunawa,shine kodayaushe hankalina yake tashi,wataranma ko bacci bana iyawa,shine kawai matsalata. Aiko saita yadda,nan danan taji jikinta yayi sanyi,tace Allah sarki,lallai kinada tausayi,amma kuma kada kimanta,duk fa mairai mamacine,kiyi hakuri,nima nan kinga babu iyayena amma inayin rayuwata yadda takamata,kidaina yimasu kuka,Addu'a zaki rika yimasu,yanzun basa bukatar komai sai Addu'arki,kinji"kar inkarajin kintada hankalinki akan wannan,dakintunasu kiyimasu Addu'a kawai,kinjiko? Tace to ummah. Nan dai H-Aisha taita kwantar mata da hankali,akan hakan,domin ta yadda da abinda suhailat din tafadamata. Sannan dai washe gari tafitoma da kowa tsarabara,tabashi. Koda sukayi fira da maigidanta Alhaji sulaiman ,tasanar dashi damuwar suhailat kamar yadda itama ta sanar da ita Nacewa iyayenta take tunawa,shine yake sanyata damuwa. Saicewa yayi to wannan dalilinne yasa takiyadda da kowane saurayi inyazo wurinta?airashin iyaye bashi zaisa kakiyin aureba,idan harta bullo dahaka tana jayayya da hukuncin Allah ne?donyarabata da iyayenta,saitakibin umarninsa takiyin aure?haba Maman Ahmad,adai kara duba maganarnan. Sannan yasa hannu yadauki wayarsa donyakira number suhailat. Itakuma alokacin suna tare da kubura,suna karatattauna wannan lamari. Suhailat tace kidubafa kigani ,har kayan lefen auran ya Ahmad angama hadawa,amma bawani canji,badole kullun ciwona yadinga hawaba!kwata-kwata ninasan bazan auri ya Ahmadba,ni rokon Allah nake yadauki rayuwata kafin bikin,Donni ranar bammasan irin tashin hankalin dazanshigaba,wuyar dazansha a wannan ranar Allah yayi tawa daita,shiyasa nake fatan ni inmutu kawai!! Kubura tace :koni Aunty suhailat nakaraya da wannan abin,domin tunda mukafara bawani alama,yadda akedai haka ake,immada munaganin wata. 'Yar tangarda gameda aurennasu saimusa rai,to lafiya lau suke,gashi kwata-kwata bikinnan yau saura kwana gomasha daya,. Don inajimma gobe za'akai kayan lefennan. Dai dai nan wayar dake hannun suhailat tayi kara,Number Abbansu tagani,saida suka hada ido da kubura sannan ta daga kiran. Kizo falon Maman Ahmad inason ganinki. Tace to Abbah. Shikuma yakashe kiran, Takalli kubura tace kinjiwai Abba keson ganina,sannan tawuce. Bayan tazauna yace:kikace iyayenki kiketunawa kikeyin kuka?? Ta kuma daure dukda taji tsoron tambayar,tace mai e Abbah. Yace to abinda za'ayi gobe zansa Dr Auwal yaturo akanzancen aurenki,kila inkikayi aure kisamu nutsuwa,kinga zaizame maki uwa yazame maki uba,tunda mubamu ishekiba. Aibatansan sanda wani tashin hankali yaziyarcetaba,cikin rudewa tace:Abbah Wallahi bashinakesoba!! Yace wakikeso?? Tayi shiru,sai kuka yakwace mata. Sukayi maganar duniyarnan,takasa yimasu magana,har dai sukagaji sukarabu da ita. Alhaji sulaiman yace to shikenan,tashi kutafi radda kikaso auren kinfiddo mijin dakanki. Cikin sauriko tatashi tabar dakin. Aranar dayamma,bayan anyi sallar la'asar,H-Aisha nazaune tare da danta Ahmad,takecewa gobene za'akai lefennan,tunda Abbankama yasayo nasa kayan,Nina sayi guda shidda,Abbanka yasayi guda uku,to kaima kaje kahado guda uku,sunzama goma sha biyu kenan. Yace ummah basuyi yawaba? Tace surukata duk tafi karfin wannan,saidai kuma har yanzunfa baka sanar dani wacece zaka auraba. Yace ummah nayi zaton Abba yafadamaki ai. Tace AA bamuyi maganar dashiba WACECE????? Yace ummah Hafsat ce diyar kawu ALHAJI SALISU. Cikin wani irin yanayi,hartana sarkewar yawu amakoshinta,tace WAKACE????? Shikanshi saida yadanji tsoro dairin yadda yaga umman tashi tacanza lokaci guda, Tace diyar Alhaji salisu kacefa???yayana!! Yace shimana umma wani Abu???? Kawai saita mike tsaye,tarika kewaye acikin falon,tana wani huci, Sannan tadawo ga Ahmad takallai tace: DIYAR YAYANA ALHAJI SALISU ZAKA AURA???? Tashi kabarmi daki!!acikin tsawa tayi masa maganar,sannan tazauna visa kujera,tare da dafe kanta da hannayenta gida biyu. Shikuma jiki bakwari yatashi yafita . ALHAMDULILLAHI Mai karatu kabiyoni acikin littafin nagaba donjin yadda zata kasance. SHIN MECECE BABBAR HUJJAR????? Shinko maikaratu yasan cewa yanzumma akafara labari? Kadauka cewa duk abinda akayi abaya tamkar shimfidane. Ynzunfa za'ashiga labarin, Ayanzun darasin yake!! Maikaratu zakasha mamaki,kuma zaisanyaka cikin tunani mai zurfi, Harkallar da take acikin wannan labarin....humwummm!!kaidai biyoni kawai,zan warware maka zare da abawa,saikayi mamakin yadda wannan labarin zaikasance, Akwai harkallah!! Akwai rikita rikita,kaidai kawai saka tugwicin naira Dari uku kacal acikin Account number Dana baka afarko,sannan katuro da shaidar biya ta wannan number 09162526909 Idan ansamu matsalarta rashin account na bank ,toka turo katin naira Dari uku kacal akan wannan number 09162526909 Kadakabari abaka labarin Daga maison farin cikinku Fatima Dahuru funtuwa Binta An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels