An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels WATA SAKAYYAR............1 NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA Godiya tatabbata ga Allah mai kowa mai komai dayasake hadamu cikin wannan littafin.tsira da Amincin Allah dukara tabbata ga shigabammu Annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya. WATA SAKAYYAR..........kamar yadda kukaji NA ambaci sunan littafin dashi,labarine mai dauke dajan hankali da darasi da Harkallah.duk acikin wannan 'yar karamar kwakwalwar tawa zanshirta wannan labarin,mai dauke da wa'azantarwa. Kabi ahankali mai karatu,don Allah idan kaga kuskure acikin kalaman dazanyi amfani dasu acikin wannan Dan littafin kasanar dani,kagyara Mani,domin kuwa labarine mai dauke da wa'azantarwa. Idannayi amfani dawata Kalmar wadda batayi maka/maki ba,ayi hakuri,banyi amfani dawannan damar don inbata ran wani ko wataba,kuma banwuceyin kuskure koyin badai daiba. Nidai fatana akoda yaushe shine,kadauki abinda yakeda kyau acikin labarin,abinda yake bamai kyauba kawatsar dashi. WATA SAKAYYAR SAI A WURIN ALLAH!!!!!!!!!!!!!!! Zaune take tana ninke kayan yaranta dasuka dawo makarantar Islamiyya,tana shiryasu acikin jaka,Abakinta kuwa istigfari kawai take karantowa,domin kuwa yazama jikinta,koda yaushe bakinta yana cikin ambaton Allah. Haka takammala gyaran kayan sannan tazauna bakin gado,ta canza istigfarinta takoma karanta HASBIYALLAHU WANI'IMALWAKIL. Zuwa can sallamar kawarta tajiyo,maman Hafsat tashigo dakin tare dafadin,kina zaune kenan?nayi sallama naji shiru,Maman bata nanneko? Tace e taje barkane dakuma wata tarewa,da diyar kawarta keyi,tunda Azaharma tabar gidan. Maman Hafsat tace kebakije tarewarba kenan?koda yakema kebason zuwa sha'aninnika kikeba,kice tarewa taje?kaih! 'Yankwanakinnan dai anata aure,kinsan kuwa Hasana ta gidan malam Haruna itama sati mai zuwa ake daura mata aure? FA'IZA tace aure kuma?to INA wancen auren datayi? Maman Hafsat tace wancan auren ayya mutu,gashi har zatasake wani. Fa'iza tace ikon Allah ita kuma irin tata kaddarar kenan,aure-aure,itakau kome kejamata saurin kashe aure? Maman Hafsa tace sabodataga idan takashe auren tanasamun wani mujin dawuri,amma data ga idan takashe auren tana daukar shekaru wani mujin baisamuba,aibatayi gigin kashe aurebtaba,amma kinsan Allah Faiza,da Hasana tafito gidan muji adaddafe take gama idda,tamkar mazan najiranta. Faiza tace ni wannan Abu har mamaki yake bani,kiga wasu matan nan danan da aurensu yamutu saikiga sunsamu wani mujin sun aura,kuma kaga bakyau suka fikaba,ba ilimi suka fikaba,ba natsuwaba,NA rasa irin wannan Abu Allah dai yasa mudace. Maman Hafsat tace wallahi kuwa,amma kema fa'iza yakamata ace kinsan abinda kike ciki yanzun,zamannaki yayi yawa agida,shekara da shekaru tunda Aurenki yamutu!har yanzun gashi shiru. Faiza tace lokacine,idan lokacin yayi saikiga nayi auren. Maman Hafsat tace kaih!!amma duk dahaka shirunnaki yayi yawa,infa kika zaunafa saikita rayuwa ahaka,kina cewa lokacine,amma za'a iya cinkaro da wata matsalar dazata iya hanaki yin aure,gara kinemi magani idan wata matsalarce arabaki da ita,haba!!shekara goma ko kare baitaba zuwa yace yana sonkiba!kuma sannan harkiyadda da cewa bakida wata matsala!wallahi wata lalura NA iya hana azoace anasonki. Fa'iza tace ga Allah nadogara,shi zayyimin maganin komai,imma iska gareni ko wani sihiri akayimani,idan Allah yakawo lokacin auren dole iskarnan takauce tabarni inyi aure,inkuma sihirine wallahi Allah shi zayyimin maganinsa sihirin yakarye,ba wurin Wanda zanje nemanmagani,zawarci dai bani kadai bace bazawara. Maman Hafsat tace aikaji matsalar taki,koda bake kadai bace bazawara,aisauran zawarawan,ana zuwa ace anasonsu,koda ba aurensu za'ayiba,ammake matsalar takifa,koda wasa bawanda yataba cewa yabasonki,Tabbas!!ansan aure lokacine,to amma arika cewama anasonka Aida dadi,bamayi jimgimba,duk yadda akayi wannan matsalar taki akwai abinda kefaruwa dake. Duk yadda akayi wannan matsalar taki akwai abinda kefaruwa dake bahakananba. Faiza tace:Tonidai inata Addu'a kodayaushe,imma wata matsalarce Allah yakawarmin da ita,idan kuma jarabawace daga lillahi Allah yabani ikon cinyeta. Maman Hafsat tabita da Ameen,dai dai sanda akakira sallar magariba,faiza tatashi tadauki buta tayi alwalla,tareda umurtar 'ya'yanta suma suka dauki butoci,sukayi alwalla. Maman Hafsat kuwa tayi sallama dasu tatafi gida,itama tayi tata sallar. Misalin karfe goma sha daya nasafiyar ranar Asabar,su faiza suka taso makarantar islamiyya,tare suka jero da Maman Hafsat,suka tafo kamar yadda suka saba tafiya da dawowa makaranta atare,,suna tafe suna taba firarsu,musamman akan darasin da akayi masu,a ranar. Maman Hafsat tace kaih!yau naji dadin karatun muallimah!nafahimcesa sosai,amma kinga Nahawu haryanzun bana fahimtarsa,wahala yake bani,wani lokacimma da malamin yashigo yafara karatun,yana farayimana li'irabi,kawai sai inma bacci nake,sabida tsabar bana fahimta,amma kinga Hadith da Alkur'ani,wannan har kosawa nake ranar yinsu tazo. Faiza tace shima nahawun nace kirika zuwa,Wanda akayimaku inkara yimaki bayani,watakila nikirika fahimtar nawa. Maman Hafsat tace gaskiya kwakwalwata bazata iya daukar Bahawuba,bata daiki Tajweed bama yaza'ayi tadauku Nahawu? Fa'iza tace aikaji matsalar taki,saurin karaya gareki,bawanda aka haifa da iyawa,kowafa koyo yayi,kirika dagewa kina jarabawa. Maman Hafsat tace kedai bashshi kawai,hidimar 'ya'yama ta isheni,tunda banyi karatun da yarintataba,kekau ai malamace,shiyasa da karanta kike ganewa. Wai Fa'iza yamaganar Addu'oin da malam yabayar? Faiza tace:INA amfani dasu sosai,kinsanni bana wasa da Addu'a,kodon wannan rayuwar danake ciki,Allah yakawomin sauyinta,inayin addu'oi sosai. Maman Hafsat tace hakane,amma kinsan wani Abu fa'iza?koda kina yin Adduar kirikasa malamai sutayaki,kinsan Baki dayawa,wani daya roki Allah saikiga cikin gaugawa Allah yabiya bukatar,wani kuma yaytayin addu'ar amma kaji shiru,Allah natuba. Fa'iza tace wallahi kuwa hakane Maman Hafsat,Nice sallar dare,nice duk wata Addu'a,kosunayen Allah da akabamu zanrike inje intayi,shekara da shekaru,INA wannan halin,amma bawani canji,yadda akedai haka ake,ko Alama!koda wasa!!wanima yace Faiza INA sonki wallahi babu,Addu'ar dai yinake-,yinake,don dai ba'acewa kayi kagaji,amma wallahi Maman Hafsat harna fara sarewa,dacewa anya kuwa zan kara aure?shekara goma koda wasa wanima yace yanasona ba'ataba ba,duk dadai akwai wadanda sunmafi shekara goman suna zawarcin,amma susai inga niyyar Aurenne basuyiba,tunda anazuwa ace anasonsu,amma nifa? Babu Wanda yataba zuwa yace yanasona,Addu'ar nan nayi-nayi har yanzun shiru,yadda kikasan ba a kar............... Kaih!karmadai inyi sabo,ya Allah kakawomin iyakar wannan zawarcin!wallahi nagaji Maman Hafsat, ace duniyarnan babu Wanda zaizo yace yanasonka,sai kace muguwar haja,inda ace inada zawarawa zanrika samun wani Abu daga wurin su,amma dai dai da omo ko sabulu banida Wanda zayyimin kyautarsa,sai dai innina nemi kudi nasiya dakaina,ga yara inada su,banida mai tallafamini sai Allah,wannan Abu yana dagamin hankali,shiyasa hankalina yatashi nakeso inyi aure,amma ace INA mace Nike daukar hidimar kaina data 'ya'yana,aiwallahi akwai wahala. Maman Hafsat tace gashi kuma wannan Dan banzan mujinnaki ko............. Faiza tayi saurin cewa mujin watadai!!karki kara kiranshi da mujina,wallahi ko firarsa banaso anayimin,wannan Azzalumin!;Wanda baisan ciwon kansaba!!kanada 'ya'ya bakasan yasukeba,bakasan cinsuba!bakasan shansuba!!baruwanka da ciwonsu!!don yanzunfa 'yata khadija batasan Babantaba,saidai acemata tanada Baba,amma bata taba ganinsaba,baima zuwa ballantana musa ran zayyi mana wani Abu kodon 'yayannan,duk gaba daya hidimarsu yasakar Mani,HAKIKA WATA SAKAYYAR SAI A WURIN ALLAH!!!!! Maman Hafsat tace kema kuma danaki laifin,dabaki taba daukar 'ya'yanki kin kaisu wurin ubansuba,suganshi suga danginsu. Faiza tace Allah yakiyaye!!shibaidamu dasuba,sai nice zan kwashesu inkaisu,salon inje ace Neman gyaran aure nake,ba kisan gulmar garinba kenan,danaje za'ace gatanan kila so take yamaidata dakinta,anga zaman zawarcin baci,Allah yakiyaye bazaniba! Nadaiyya alkawarin duk ranar danayi aure zanje inkaisu,amma ayanzun banida aure,ace sonake yamaidani,AA Allah yasauke. Maman Hafsat tace toke baki tunaninma koshine yayi maki wani saddabarun donya hanaki aure?tundafa badon yanaso kuka rabuba. Faiza tace:gaskiya bazai iyaba,bazan dauki alhakinsaba,Nina zauna dashi,nasan halinsa,nasan abinda zai iya,nasan abinda bazai iyaba,ban taba tunanin cewa wai sihirine akayimani aka hanani aureba,tsofon mujina bazaitaba yimin Asiriba,kawai dai nafi dauka cewa lokacine bayyiba,to amma abinda yafi damuna shine,inrika ganin Alama,ma'ana arikacewa anasona mana,amma kodaya bamai tayani,idanna tuna wannan inyi kukana ingaji. Maman Hafsat tace tokisa atayaki da Addu'a mana,yanzun anan cikin unguwarmu ga malam shehu mai Almajirai,koshi kikaje kikayima bayani,in Allah yataimaka saikiga karshen abin yazo. Faiza tace nifa gaskiya bana son fara shiga malamannan,saboda..................... Maman Hafsat takatseta dacewa to aisaikita zama!abin baidameki bane!!baki gaji dazama gidankuba,bakisan Annabi (S A W ) yace malamai magada Annabawa bane,yadda zasu roki Allah nan danan aga biyan bukata,kesaikiyi shekara kinayi,batayi matsayin tasu tarana dayaba,domin kuwa su bakin su koda yaushe cikin ambaton Allah yake,sallolin nafila basa yankemasu,kuma kedakanki kinsan muyi Hadisinnan. ( daga abi Huraira Allah yakara masa yadda yace:manzon Allah (S A W ) lallai Allah madaukakin sarki yace:duk Wanda yayi gaba da masoyina,to yayi shirin yaki dani,kuma bawana bazai taba kusantuwa dani da abinda nafisoba,kamar abinda na farlanta akansa,kuma bawana bazai kasance yanayin nafilfiliba,harsai nasoshi,to idannasoshi,zan kasance masa jinsa dayakeji dashi,in kasance masa ganinsa dayake gani dashi,inkasance masa hannunsa dayake tabawa dashi,inkasance masa kafarsa dayake tafiya da ita,kuma idan yarokeni wallahi zan amsamasa,idan yanemi taimakona wallahi zan taimakesa.Bukhari yaruwaito. Faiza kokin mantane?acikin Arba'una Hadith yake,Hadisi na Talatin da Takwas,abinda yasa nakeso kisa atayaki da rokon Allah domin bakisan bakin waniba,wani zai iya kasancewa daya daga cikin waliyyan Allah,idan har akayi sa'a shine to daya roka Allah zai amsa,kinga nan danan sai bukatarki tabiya. Faiza tace to tunda har Allah yafadi suffofin waliyyan,sai kawai inkara dagewa da sallolin nafila,konima zanzama daya daga cikin su,amma ince wani yarokar Mani Allah,aikamar natura Dan sakone,inroka dakaina mana,kinsan kuwa zuwa dakai yafi sako. Dai dai nan Maman Hafsat tadafa kyauren kofar gidansu,tatsaya,domin kuwa suzo dai dai inda zata shiga gida,sai kuma tatsaya tace: Tsiyata dake faiza taurinkai,duk yadda akayi dake baki yadda,amma tunda kince haka,mubari idan munkoma makaranta muyi tambaya: SHIN YA HALATTA MUTUM YASA AYIMASA ROKON ALLAH,ATAYASA ADDU'A??????? To idan mukaji amsar da malam yabamu,komunaso kobamaso saimuyi amfani da ita,Allah dai yasa mudace ,sai anjima. Sukayi sallama tashiga gida,faiza kuma tawuce nasu gidan. Ranar Asabar misalin karfe uku narana,Maman Hafsat tashigo gidansu faiza,mahaifiyar faiza tagani zaune tana yankan kubewar miya,ta gaisheta sukadan taba fira Maman Hafsat tace INA Faizar naga bangantaba? Mama tace tana kitchen tana hada wuta,sannan takwala mata kira. Tafito tareda fadin aiwai Maman Hafsat CE?shigo mana. Maman Hafsat tace AA bashigowa zanyiba,dama nazone infadamaki yau ake auren Hasana,Dana gayamaki,daurawa datarewa,kushirya idan anyi sallar la'asar Whatsapp number 09162526909 Kishirya idan anyi sallar la'asar,kizo gidammu muwuce. Faiza tace to shikenan,Allah yakaimu. Cikin wasa da tsokana Maman Hafsat tace,gara dai kirika FIFA,ba kodayaushe kina cikin gidaba,daga gida sai makaranta,kuma kiyi kyalliya sosai,don kema sonake ashekararnan azo naki auren,saboda mungaji daganinki agida,kifayo kwalliya hada jambaki! Abinma sayyabata dariya,mama tace Allah yakawo muji na kwarai aimuna fata,itama tatafi dakinta tahuta hakanan,kowa dai dairin kaddararsa,ita kuma Hasana irintata kaddarar kenan,aure da anyi baya zuwa ko INA,Allah dai yasa mudace. Maman Hafsat tace Ameen,tare dafadin faiza inajirankifa,yanzun zankoma gida inyima yara wankane sutafi islamiya naga uku tawuce,yanzun kinji la'asar,tamike tsaye tareda tafiya tana kara cewa:faiza kisanyo kayanki wadanda sukafi kowanne kyau,kisha turare,kidau make up sosai,Allah yahadaki da wani dan gayun. Sumama da faiza dai dariya suke,maman Hafsat tatafi gida. Misalin karfe biyar na yamma,Faiza tashiga gidan maman Hafsat. Kin dai shiryako?nasan ki danawa wurin shiri. Maman Hafsat tace nashirya mana,nadaukama bazakiba,tunda gashi har biyar takusa. Faiza tace zani mana,kinsan taron bikin yanzun saida yamma,shiyasa natsaya nakintsa sosai. Maman Hafsat tace kingakau yadda kikayi kyau faiza!!dama kin iya irin wannan kwalliyar kike zaune haka?haba da walakin,Aida kina daukar wanka da kwalliya,haba dayanxun ba wannan maganar akeba,tafada tana dariya,tareda kara fadin: Hala kinwuto 'yansa idonnan har sun kafa majalisa? 'Yan zaman zana'ida bagawa. Faiza tace keko maman Hafsat kinsama wadannan bayin Allah ido,daga suna zaman kan hanha shikenan saikice sa ido suke? Maman Hafsat tace aiko kallon matan mutane kawai kezaunar dasu,in mace zata gitta insuka fara kallonta harsai tabace,har wani lekota suke,auu!!canzakiga sun saki haba suna kallon mata,sunsan kowace mace a unguwar nan,sunsan gidansu,in budurwace sunsani,inbazawarce sunsani,in matar aure CE sunsanta sunsan waye mujinta,hakan kuma bai hana subita dakallo harsai sundaina ganin ta,karmadai inkinyi kwalliya,mace intazo dai dai saitinsu har tuntube take tana hardewa,koke NA tabbatar sun kalleki,yadda kikayi wannan kwalliyar,daka wuce kuma ahau labarinka,baza'a dainaba,sai kuma inhan hango wata tazo wucewa sai asaki tata fitar akama tata. Faiza tafashe da dariya,tace gaskiya maman Hafsat akwai ki da sharri!!Tonidai basu kalliniba,ballan tana ince sunsamin ido,ni tunda nake wucewa tagabansu lafiya lau nake wucewa,BAN TABA GANIN SUNA KALLONABA,harma indaga ido inkallesu,sai inga kowama hidimarsa yake baidamu daniba,ammake kullun saikince sunsamaki ido. Maman Hafsat tace tokeko wace irin mace CE dabasa kallon ki?wadanda kowa yayi masu shaidar kallon matan tsiya,amma kekice basa kallon ki? Maman Hafsat takuma cewa wasa dai kike.Allah natuba indai balalura garekiba,to komindai munin mace intazo wucewa saisun kalleta,ballan tanake. Faiza tace abar Maganar,dauko hijabinki muwuce,yamma karayi take,suka fita gidan baki dayansu. Ranar Lahadi suna cikin Aji,misalin karfe goma nasafe. Malamin dakeyimasu Tajweed yashigo,yafara karatu,yanayimasu bayani. Maman Hafsat ta nutsu sosai dukda wannan darasin yana bata wahala sosai,domin kuwa ba fahimtarsa takeba,amma awannan lokacin hankalinta da idanunta nakan malamin,da abinda yake karanta masu,ita iyakar gaskiyarta yau saita iya karatun nan tafahimceshi Bayan malam yakammala karantawa,yayi masu bayani sosai,sannan yajefo tambaya,kamar haka. (Idan aka samu nunussakina sai mimunmushaddada tabiyo bayanta,ya akekiran wannan hukuncin?) Budar bakin maman Hafsat da karfinta irin yau tafahimci karatinnan,tace: NUNUN MAKIYYA!!! Gaba daya aji akafashe da dariya,hatta shi kansa malamin saida tabashi dariya...... Hattashi kanshi malamin saida tabashi dariya,yace gaskiya baki tare damu,in inakaratunnan ina hankalinki yake zuwa?tunda muke Tajweed kintabajin na ambaci wani hukunci da nunun makiyya? Tace malam naji kacene,nunun daurarriya sai mimun tabiyo bayan ta,toshine nace nunun makiyya,aikaga ganunun ga mimun,ita mimundin batana nufin makiyya bane?? Malam yace maman Hafsat idan ina tambayar 'yan aji kidaina samin baki,wannan karatun anyishi maimaicine ake,amma haryanzun baki fahimtaba,kiyimin shiru. Faiza tace wallahi maman Hafsat kekike bada amsar nikejin kunya,wane irin nunun makiyya?dama akwai nunun makiyya a Tajweed?To bama kigane Tajweed ya za'ayi kigane Nahawu? Barikiji,idan mimun mushaddada tabiyo bayan nunussukun,ana kiranta. (Al-idgamun nunussakinati bi gunnah) Maman Hafsat tace to shikenan narike wannan. Faiza tace Allah yasa da gaske. Bayan malam yakammala karatun zai fita,maman Hafsat tace ya mu'allim!inada Tambaya. Yace to naji,ammafa kiyi tambaya ta hankali,nasan halinki. Tace Shinyahalatta mutum idan wata damuwa tasameshi yasa atayishi da Addu'a? Malam yace sosaima kuwa,domin kuwa bakasan ta bakin Wanda za'aamsaba,kamar ninan idan wani Abu yasameni zan iya zuwa wurinku Ku dalibaina,ince kutayani da Addu'a,wannan yahalasta,shirkace ba'ayadda da itaba,misali zuwa wurin Boka,sabo dawata 'yarbukata taka,kakwashi jiki kaje wurin boka wannan haramunne,sai dai katashi kayi sallar nafila ko Azumi,sallar dare karoki Allah,kuma kina iyasa kawarki ko malaminki kokuma duk Wanda kika yadda dashi,kice matsala kaza tadmsameki atayaki da Addu'a. Duk sanda mutum yayi Addu'a"Allah yakarba,koda bakaga biyan bukatar akusaba,wani lokacin Allah yana jinkirtawa,kayi fatan wannan jinkirin yazamemaka Alkairi. Kuma ba'acewa angaji da rokon Allah haryanzun bukata bata biyaba,wata kila wannan bukatar dakake nema ba Alkairi bace agareka,idan kayi Addu'ar sai Allah (S W T) yajuyar maka da Adduar tawani bangaren,karshenta akwai wani Abu dazai cutardakai,ko wani mummunan Abu zaisameka,to sanadiyyar wannan Addu'ar da kakeyi,sai Allah yakawar maka da wannan mummunar kaddarar. To kunga Amfanin Addu'a kenan,don haka kodayaushe mudage dayin Addu'a . Allahu a'alamu. Dukkan 'Yan ajin suka bude baki sukace:mungode ya mu'allim!! Bayan wasu 'yan watanni suka samu hutun makaranta,don haka Faiza tayi shirinta tatafi kauyensu,inda aka haifi mahaifinta. Taje lafiya,Gidan yawane sosai,dakin gwagwgwo Hauwa tasauka,dama nan take sauka idan tazo garin. Gwagwgwo Hauwa matar yayan Babantace,mace CE maikirki sosai,suna zaune atsakar gida misalin karfe Tara na safe. Saiga wani yaro bai wuce Dan kimanin shekara gomaba,yashigo gidan,yana rataye dawata jakar fata,acikin ta magunguna yake sayarwa kala-,kala,na gargajiya,yana Talla yana fadin. Kusai maganin miyagu. Maganin sammu. Maganin ketara. Maganin makaru. Maganin baki. Maganin kambun baka. Maganin.............. Kafimma yagama fadin sauran magungunan,Hansai datake tsaye tana surfen masara aturmi,tace Yaka mai maganinnan kona miyagu masiya. Yaro yashigo ya kwance magunguna anata siye,mutane dayawa acikin gidan sun anshi maganin. Ita kuwa Faiza kallon ikon Allah kawai take,watakan su yanzun dasuketa rububin siyen wannan maganin,ko amfanin mezayyimasu oho?anje anyo sassake-sassake adaji ance masu magani sundage sai wani siye suke,Allah yakyauta. Aka kammala siye,yaro yakalli Faiza yace kebazaki siyaba? Tace me zanyi dashi?Allah yakiyaye!! Yace baiwar Allah ki amsa zayyimaki amfani,domin kuwa akwai matsala ataredake,kinada lalura sosai ajikinki,mai wahalar magani,ammani idan ki kabani abin sadaka zan iyarabaki da ita,kuma............... Takatseshi dacewa Dallah Dakata!!nikarkayimin janye-janye!lafiyata lau!!INA zaman zamana lafiya..... Takatseshi dacewa Dalla Dakata!!nikarkayimin wani janye-janye!lafiyata lau!INA zaman zamana lafiya kakiramin lalura!!kai duk cinikin dakayi acikin gidannan bai ishekaba,dole saikaci dani?Allah yasauke!!! Yakara kwantar dakai yace:baiwar Allah ki amsa zayyimaki amfani,domin kuwa kinada lalura mai wahalar magani,amma awannan karon dazaki amshi maganina Allah zairabaki da ita. Tace kai yaro! Dukfa dadin bakinka bakacin kudina,ni inatare da Allah bawanda ya isa yacutar dani,don haka kadama kayimin janye-janye,kace iska gareni ko sihiri akayimani,ko magani zan amsa,zan amsa awurinkane? Yabude baki yana dariya zayyi magana, Hansai tace karabu da ita ba amsa zatayi ba,su 'yanburnine ba amfani sukeyi da irin wadannan magungunanba. Yace to shikenan. Masu siye sukagama siye Yakama hanya yatafiyarsa. Misalin. Karfe Tara nadare,suna zaune acikin dakin Gwagwgwo Hauwa daga faiza sai Gwagwgwo Hauwar,sunata fira,anan Gwagwgwo Hauwa ketambayerta. Wai Faiza bakiso kiyi aurene?kokinfiso kizauna kita renon 'ya'yanki?yakamata ace kinyi aure yanzun,shekara kusan goma kina zawarci,yakamata kiyi aure tunda yaran suna iyayima Kansu komai,saiki barma innarkisu,Allah shike rayawa,tunda yanzun mazan baso suke ajemasu da Dan waniba,yakamata kifitar damuji kiyi aure hakanan,tin kafin afara yimaki surutu. Faiza tace wallahi Gwagwgwo nima inaso inyi auren,Allah ne baikawo mujinba. Gwagwgwo Hauwa tace cikin zawarawanki zaki fidda daya,kada kitsaya zaben wani mai kudi,rufin Asirinki aidakin mujinki,kindaima Sani tunda kinada iliminnan,kuma haryanzun kinazuwa islamiyya,kinsan lada da falalar datake game aure,Mara aure baya samunta,yadda zakuyi aikin lada keda me aure bafa za'abaku lada dayaba duk abinda zakiyima mujinki ladane,kiyima kanki fada kiyi aure hakanan. Gaba daya jitayi idanunta sunciko da wasu zafafan hawaye,azuciyarta tace don basusan nafisu damuwa dason yin auren ba,shiyasa take fadin haka,ni kaina kodayaushe Addu'a nake Allah yakawomin muji nakwarai. Kawai saikuma tayanke shawarar tasanar da ita dalilin dayasa haryanzun batayi aureba. Faiza tace gwagwgwo nima inaso inyi aure,abinne yagagara,nikaina narasa gane meke damuna,tunda aurena yamutu nafara zawarci,BA'A TABA CEWA ANASONABA,to taya za'ayi nayi aure??? Gwagwgwo tace dagaske faiza?tsawon Shekara gomafa? Faiza tace gwagwgwo koda wasa wani baitaba zuwa yace yanasonaba,nikaina INA cikin tashin hankali amma dai inata Addu'a,Allah yakawomani iyakar abin. Gwagwgwo Hauwa tajinjina kai,tace aiko zama baigankiba faiza,tashi zakiyi kiyi dagaske,ai wannan yazama lalura,sai dai duk satin duniya kaji ana daurama 'yammata da zawarawa aure,kai banda naka?kuma bama rana,tunda bakisa rai,to bakisa rai mana,ai in anazuwa ace anasonkama shine zakasa rai,amma shiru!!aiko faiza zama baigankiba,tashi zakiyi duk inda ake Neman magani kinemeshi,inba hakaba rayuwarki takare azawarci,kwanakifa bajiranki sukeyiba,shekara goma bako kare shege!!!yazoma yace yana sonki,wannan wane irin bala'ine?a'ah!tashi zakiyi kinemi magani,wallahi bakiga tazamaba. Nan take faiza takarajin hankalinta yatashi,tace inatayin Addu'a sosai. Gwagwgwo tace aiduk dahaka saikin hada da magani,shima magani airokon Allahne,yanzun zazzabi ko ciwonkai Yakama ki kikishan magani,kice aikina Addu'a?dole kokina Addu'a saikin hada da magani,ki dauka kawai wannan halin dakike ciki ciwone kinemi magani. Faiza tace gwagwgwo harkinsa naji tsoro,nakuma tuna da maganar yaronnan na dazun,mai tallar magani,dayacemin inada lalura mai wuyaragani,banasofa zancensa yazama gaskiya. Gwagwgwo tace ai gaskiyar yafadamaki,domin kuwa rashin aure ko rashin masoyi ciwone,kazauna kai arayuwarka bawanda zaice yana donka,Ayyazama ciwo. Faiza tace wurinwa zan anshiagani?banason fadawa ga halaka ko shirka. Gwagwgwo tace yaronnan daya kawo magani dazun........ Gwagwgwo tace yaronnan daya kawo magani dazun dakin amsa. Faiza tace haba dai maganin wannan yaron ba'abinda zayyimani,ganinake kawai duk shirmene. Gwagwgwo tace:a'a faiza ba'araina magani,komin kankantarsa,dakin amsa,ba'asan inda za'adaceba,nikaina nan Ayace akan hakan,domin kuwa natabayin wani ciwo. SHAKARA TALATIN BAYA. Ciwo mai tada hankali,duk Wanda yaganni yasan yaddanake lokacin da inada lafiya sai yayimin kuka,sai an kwantar dani sai antayar dani,komai sai anyimani,alokacin hatta hankalinama soyayi yagushe. Ace hawan jinine. Ace sammune. Duk wani babban Asibiti dakikasani a kasarnan munkwantashi,kudi kuwa sunsha kashi,hatta gonakimmu da kiwukammu daga nawa harna mujina Dana iyayena saida suka kare,sakamakon wannan lalura. Ayi na hausa,ayi nagargajiya kisauki ciwon bayayi,duk inda akaji mai bada magani tabullu sai ankaini kominnisan garin,Amma inahh!sai Dana shekara goma sha biyar dawannan lalura,gaba dayama har angaji ansama sarautar Allah ido,wasuma suce lokaci kawai akejira. Wata rana lokacin zafi,akayimin shimfida tsakar gida,duk muduka muna nanwaje ana kwanciyar zafi. Saimukayi bakon mai bada magani,a can gindin itaciya yadaura lasifikarsa,yanata tallar maganinsa,bayan anyi sallar isha'ine kuwa bana mantawa,ayadda yake tallar maganin yana lissafo lalurori kala-kala,sai naji harda irin tawa,kinsan mai ciwo duk inda yaji magani gani yake za'dace,nace ma mujina a anso Mani wancan maganin da ake tallah. Saude kuwa NA zaune tace:kajiki Hauwa yanzun wancan maganin kike tunanin zayyimaki?duk kudin da aka kasa na Asibiti bayyiba,da wurin manyan masu magani,sai wannan Dan balo-balo dinne zaki tunanin zayyi maki?asara dai kawai kikeso akara. Saikuwa akaki bada kudin a ansomani wannan magani,har yakusan tashi,saiga musa mahaifinki,alokacin bayyi aureba. Nace musa idan kanada kudi ka anso Mani wancan maganin da ake tallah. Yace to. NAIRA GOMA GOMA MAGANIN YAKE,UKU ASHIRIN Haka aka ansomanishi,kullun maganin kananane,kulli uku tsawon kwana uku zanyi amfani dashi,NAYI. Yau shekara Ashirin da biyar kenan rabon dako makamancin ciwomma yakara tasomin,narabu dashi,Allah yarabani da wannan ciwon sanadiyyar wannan magani,anyi mamaki sosai,don kuwa fara amfani da wannan maganin cikin sati saida nafara yima kaina wanka da kaina. Don haka faiza duk inda kikaji magani ki amsa kawai,Allah shine mai warkarwa. Kuma haryau danake baki wannan labarin baikara dawowa garinnanba,bankuma karajin labarin inda wannan mai maganin yabulloba,dama yawon tallarshi yakeyi,mai rabo kuma ya amsa Faiza tace Tabb!dijan!!Allah mai iko,Allah yasa mudace,toshi yaron dazun daya kawo tallar magani dannan garinne? Gwagwgwo tace a'a shimadai kawai yazone,kuma ba lallaima yakara dawowaba,haka masu magunguna suke shigowa sutafi,wani har abada baki kara kojin labarinsa. Faiza tace to Allah yasa mudace Satinta biyu awannan kauyen,tadawo gida. (Karka manta mai karatu kana tare da littafin WATA SAKAYYAR......1 na fateema Dahiru Funtuwa Binta whats app number 09162526909) Ranar wata juma'a da yamma,faiza taje gidansu maman Hafsat,suna kofar daki zaune sunata fira. Maman Hafsat tace wai yaushe zaki shirya muje wurin malam Shehu dinnanne?yakamatafa,gara kifara sanin halin dakike ciki. Faiza tace zanje,amma kibari musa rana. Maman Hafsat tace to shikenan saikin shirya. Faiza tace aibakisamma abin dariya Abin haushiba,tafiyarnan danayi kauye,kawai INA zaman zamana lafiya,wani mai bada magani yakalleni,yace wai inada lalura,kwata-kwata yaronnan bai wuce Dan shekara gomaba,wai inba shi sadaka zai bani magani,kekinji daukar magana!! Maman Hafsat tace irin yarannanne wadanda iskoki ke budemasu ido suke bayar da magani ,Aida kin amsa.............. Aida kin ansa. Faiza tace yakike haka maman Hafsat?wannan aikauce hanyane,duk Wanda zai fada maka lalurar ka batare daka sanardashiba,to aiko yake da Aljanu ,kuma Bokane,saikace banida ilimin islama,sabida wannan matsalar bazan yadda inkauce hanyaba,Allah shiya jarrabeni da wannan lalurar, kuma shine kawai Wanda zai iya rabani da ita,bawani mai aiki da Ajanuba. Maman Hafsat tace:Aida kintsaya kinji wace lalura zaice tana damunki,shin sihirine koko iskoki?da saiki kara samun haske. Faiza tace Allah yasauke!aibamma tsaya sauraronshiba,kadama insaurareshi yabatamin tunani,yacemin sihirine akayimani,yasa inzo inta hasashen ko wanene ko wanene,yagurbatamin tunaniba,yasanyamin zargin mutanen dabasuyimin komaiba,Akarshe kuma bazai iya yimin maganin ba.Tunda daikince muje wurin M-Shehu mai Almajirai saimu jaraba aishi malamine. Maman Hafsat tace to Allah yasa mudace. Bayan kwana uku kuwa suka shirya sukaje wurin m-shehu,bayan anyi sallar isha'i,suka sameshi adakinsa,yayi masu izinin sushigo. Bayan sun zauna suka gaisheshi. Yace:bayin Allah meke tafe daku? Maman Hafsat tace malam wurinka mukazo,domin ataimaka atayamu Addu'a ,tunda ga Almajirai atare dakai,bamusan inda za'adaceba. Yace hakane meke faruwato? Faiza tace natabayin Aure haihuwata hudu da mujina sannan mukarabu,to tunda muka rabu nadawo gida inata zawarci ,shiru haryau shekara goma kenan koda wasa wani Namiji bai taba cewa yana sonaba,tun abin baya damuna harya fara dagamin hankali,duk da inayin Addu'a ammadai haryanzun shiru. M-shehu yace ikon Allah,shin ba'ataba zuwa ance ana sonki bane koko dai anazuwa dawowane ba'ayi? Tace ba'ataba zuwa bane. Yajinjina kai yace to shikenan,wannan duk mesaukine,muji daiko?insha Allahu za'anemosa,ki kwantar da hankalinki,babu abinda yaga gari Allah,kici gaba dayin Addu'a ba'asarewa,nima zansa ayi ayi saukar Alkur'ani agani,saikuma za'ayi sadaka,insha Allahu komai zaizo dasauki,wannan ai abune mai sauki awurin Allah,bakomai Allah yanasane da halin dabawansa yake ciki. Faiza tace to nawane za'a bada,? Yace a'a ai abin sadakane kawai zaki bayar,duk abinda Allah yahore,da safe za'sayi wani Abu,ko kuli-kuli ko fanke ayi sadaka dashi,saikuma saukar Alkur'ani danace maki,saikuma wasu magunguna da za'arubuta wasu daga cikin ayoyin Alkur'ani awanke sai ajika maganin da wannan rubutun idan yabushe zansa adaka idan kikadawo zanbakishi,sannan infadamaki yadda zakiyi amfani dashi,Allah yasa mudace,amma muji kamm!za'anemosa. Faiza tadauki 5k tabashi tace gashinan ayi sadakar dakuma abinda za'anema bahadin magungunan. Yasa hannu yakarba tare dafadin Allah yakarba,Allah kuma yabiya bukata. Suka amsa da Ameen,sannan suka tafo gida,tareda fatan Allah yasa anyi asa'a. Nan sukazo sunaba mamansu faiza din labari. Tace toyaza'ayi?ainema yazama dole,Allah yakawo maki iyakar abin,aibazan hanaba,dolene mutum yatashi yanema,wannan zama ayya isa hakanan,Allah yasa adace,amma ace kaita rayuwa ahaka,tunda aurenta yamutu bawani aidolene kanemanma kanka mafita. Ranar wata juma'a,ranar zasu koma wurin m-shehu,faiza tayi wanka tashirya,tafara biyama maman Hafsat. Tana shiga gidan tace kee!maman Hafsat yau naga abin mamaki!! Maman Hafsat tace meyafaru?? Faiza tace majalisarnan ta 'yan sa'ido!kofar gidanku!kinga yadda suke kallona kuwa?hada wani cemin saikin dawo!nida har in bar wurin babu Wanda yake daga ido yakalleni,amma shine yau harda yimin magana. Maman Hafsat tace to aiko inaga wata lalura gareki tasa maza ko kallon ki basayi,ballantanama suce suna sonki,keee!!!wannan Abu dame yayi kama?amma insha Allahu komai yazo karshe!kice har magana sukayimaki??!! Faiza tace hummf kedai bari,nihar abinma mamaki yabani,tunda nakewucewa tagabansu ko dago ido basuyi...... Faiza tace humf!kedai bari,nihar abin mamaki yabani,tunda nake wucewa tagabansu,ko dago kai basayi sukalleni amma waiyau harda yimin magana,kedai shirya muwuce wurin malamin nan. Maman Hafsat tadauko hijabinta,basu biya koinaba sai wurin malam shehu mai Almajirai. Bayan sun zauna suka gaisheshi,yayi masu sannu dazuwa,sannan yacigaba dacewa: NASA anyi rokon Allah sosai,an sauke Alkur'ani,anyi sadaka,da izinin Allah kuma zamuga hasken abin. Sannan yacema Faiza kina mafarkin ruwa ko iska? Tace a'a amma lokacin da inabudurwa nayi fama da irin wadannan mafarkan,da kuma lokacin da inada aure,amma gaskiya yanzun ba nayi,tundayake INA amfani da Addu'oi sosai. Yace toh!shikenan,ba matsala,kinsan abinda kefaruwa dake? Faiza tayi saurin dagokai takalleshi,don taji abinda zaice. Yace gaskiya DUHU ne yagitta maki,kinada tsananin duhu sosai,tayadda babu yadda za'ayi wani yace yanasonki,amma insha Allahu za'aita Addu'a ,arabaki da wannan duhun. Tace DUHU malam? Yace e duhune yaguttamaki,amma karki samu damuwa,wannan bawata matsala bace babba,za'ayi maganinta,za'arabaki da ita. Sannan yadauko magunguna dakuma ruwan Addu'a yamika mata,sannan yayimata bayani akansu,dayadda zatayi amfani dasu,cikin kwanaki hudu,saiki dawo kifadamin yadda kikaji. Takarba tace toshikenan,sannan sukayi godiya suka tafo. Ahanya Faiza kecema maman Hafsat,kinji kuma wata matsala,wai duhune yagittamin,shin wane irin DUHU kenan? Maman Hafsat tace Sihiri ko iskoki yana iyazame maki DUHU arayuwarki,kingadai magana ta tafara fitowako?bayadda za'ayi ace mace kanarki San kowa kin Wanda yarasa ace batada mai sonta,sai dai in lalura ,yanzun inda kin zauna kinata cewa aure lokacine sai dai kita zama ahaka,domin kuwa babu ranar dazakiyi aure,sai ranar da wannan duhun yabarki,shikuma duhun bazaitaba rabuwa dakeba,inba magani kikayiba,ayya zanemaki tamkar ciwone shi wannan duhun,dole saikin nemi maganinsa, Allah yasa munfara a sa'a. Faiza tace Ameen. Haka dai rayuwa taita tafiya,tayi amfani da maganin tanajin dadi ajikinta,sai kuma sa rai datake yi naganin ko za'adace wani yace yana sonta,don haka takedan kasancewa cikin farin ciki. Amma lokacin da batayin maganimma kosarai batayi,hidimar gabanta kawai take. Amma abin mamaki harya zuwa wannan lokacin saidai saran kawai,ammafa bawani canji,canjinta daya datake lura dashi,shine lallai yanzun idan tana tafiya maza na iya dagon ido sukalleta,amma da bata samun koda hakan,komin kwalliyar data dauka kuwa. To ganin anakallonta shine ma take karasaran wata rana za'ayi mata magana,amma dai haryanzun babu Wanda yataya. Duk ranar dasu kaje wurin m-shehu kuwa abinda yake fara tambayar ta,( WANI YAZO KUWA???) Tana bashi amsa dacewa babu Wanda yazo,amma inasaran in Allah yayadda za'a samu. Yace Tabbas!aikin yanayin haske sosai,amma nayi mamakin da haryanzun babu Wanda yazo,amma babu komai,za'azo din,ai Allah aka roka,kuma bazai taba bari muji kunyaba. Haka dai rayuwa taci gaba DA tafiya saidai saran kawai, amma haryanzun babu Wanda yazo, WATA RANA suna zaune tare da maman Hafsat da kuma mahaifuyar Faiza din,sunata kara tattauna wannan lamari dayake ta faruwa. Alokacin kuwa wata makabciyarsu tashigo kitso wurin faiza din,tana dai jinsu sunata firarsu. Har maman faiza nacewa:to aini dama bin malamannan sai ahankali,saidai aitayimaka gafara sa bakaga kahoba,saidai kaita sarai amma bawani canji,kawai Faiza kihakura,kibari, 'yankudinnan dakike samu ya isheki kiyi wata bukatar dasu,amma kita kaima malam yana cinyewa,dakin samu 'yankudi bakida wani buri sayyazakiyi ki kaima malam. Maman Hafsat tace to mama ausadaka akeyidasu bacinyewa yakeba. Maman faiza tace yo itama aubukatar sadakar take,yanzun dai ga wankin yaranta can yataru,ko omo batashi,sai yawo suke... Sayyawo suke cikin dauda,amma yanzun haka batunanin siyen omon takeyiba,tana nan tana tunanin yatayi tahada dubu daya ko Dari biyar takaima malam,dama kinsanyama rayuwarki hakuri kizauna kawai kirike 'ya'yanki,kibasu tarbiyya kihakura kawai duk ranar da Allah yakawo lokacin Aurenki zakiyi,amma wannan bin malaman tadama kanki hankaline kawai,kuma abinda kikeso haryanzun baisamuba. Jamila wadda faiza keyima kitso tasaka baki cikin maganar,tace mama kuma aibazai yuwu dakuruciyarka ace kaita zama ahakaba,kowace mace dai tana bukatar ace takama dakinta,dukkowace mace data taba zama dakin kanta,bataso tadawo gidansu tatsugunna,dai dai dasati daya indai bada bakunta tazoba. Inko zawarcine duk wadda tagama idda sotake tasamu tayi aure,amma wannan zama NA faiza aidolenema tatashi tanemi magani,amma kunje wurin malam shehu kuwa? Maman Hafsat tace aican mukezuwa. Jamila tace yawwa! Ainasan yanabada wannan taimakon,kuma anadacewa sosai,gashi babu shirka ahidimarsa,shifa in Allah yataimakeka,ka anshi magani wurinsa,CIKIN KWANA HUDU BUKATA TABIYA!! Da izinin Allah bantaba ganin Wanda yaje wurinsa baidaceba,kuma karkarima andade asamu sati daya saikaga bukata tabiya. Faiza tace sati daya kuma?aini akalla munkai wata biyar kenan muna zuwa wurinsa,amma haryanzun babu wani canji,shiyasa kullun innacemai bawanda yazo wurina har mamaki yakeyi. Maman faiza tace humf!kudai kukasani!wani ya isa yasauyamaka kaddararkane?komin rokon Allahn da za'ayidai sai lokaci yayi. Maman Hafsat tace:Allah maman su faiza ana iyayimaka sammu don ahanaka aure,ninamafi zargin tsofon mujinta. Maman faiza tace bawanda yaisa yacutar dawani saida izinin Allah,kada kuzama kamar bakuda ilimi mana,kuna zuwa islamiyya kuma kunkaranta Hadisin. (Daga Baban Abbas,Abdullahi Dan Abbas,Allah yakaramasu yadda yace:watarana nakasance abayan Annabi tsira da amincin Allah sutabbata agareshi. Sayyace yakai yaro lallaini zansanar dakai wadansu kalmomi,kakiyaye dokokin Allah zai kiyayeka,kakiyaye dokokin Allah zaka sameshi agabanka. Idan zakayi roko karoki Allah,idan zaka nemi taimako kanemi taimako awurin Allah. Kasani daduk mutane zasu taru akan su amfanar dakai dawani Abu ,bazasu iya amfanar dakai dakomaiba,saida abinda Allah yarubuta agareka. Kuma dazasu taru akansucutar dakai dawani Abu ,bazasu iya cutar dakai dakomaiba saida abinda Allah yarubuta akanka. Andauke Alkalumma takardu sunbushe,Tirmuzi yaruwaito,kuma yace Hadisine maikyau ingabtacce. Acikin wata ruwaya yawanin tirmizi,kakiyaye dokokin Allah,zaka saneshi agabanka,katuna da Allah lokacin dakake cikin yalwa,zaituna dakai alokacin tsanani,kasani duk abinda baisamekaba,dama baikasance zai sanekaba,kuma duk abinda yasameka dama baikasance zai kubucemakaba,kasani lallai nasara tana tare dahakuri,kuma lallai farin ciki yana tareda bakin ciki,kuma lallai tsanani yana tareda sauki. ARBA INANNAWAWI (ARBA INA HADITH,hadisi nagoma sha Tara.) Donhaka faiza kiyi hakuri,ko sihirine akayimaki,Aida sanin Allah,saida yaddar Allah sannan sihirin yakamaki,toki dauka kawai wannan yanadaga cikin kaddararki wadda kuma bazata taba sauyuwaba,tunda haka Allah yarubutamaki ita. Kufa iyakacimmu aikatawane kawai,domin kuwa komai Allah yariga yarubutashi,kuma bazamu iya sauyashiba,Aure-mutuwa-haihuwa idan lokacinsu yayi bamai iya dakatar dasu,idankuma lokacinsu bayyiba duk yadda kakosa dole kayi hakuri kajira lokacinsu,gaugawa bataki baceba faiza,kamata yayi ki tattara zancen aure ki ajiyeshi gefe,duk abinda kikanema kikula da 'ya'yanki kawai kici gaba dabasu tarbiyya. Jamila tadanyi dariya tace kaji maman faiza,itakuma saitayi zaune ahaka?bata bukatar aure,haba aibazai yuwuba. WATA SAKAYYAR........1 Sai dare yayi kowanacan tareda mujinta,ita saita kwanta itakadai,aida tausayi,duk kannanta nakwana daazajensu ita sai ita,kuma bama rana,aineman magani yazama dole Maman Faiza tamike taredafadin,Bari inje induba girkina. Tana wucewa su Jamila suka fashe dadariya itada maman Hafsat,wato mama taji firar zatafi karfinta tatashi tatafi. Itakuwa faiza jinsu kawai take,gawani kullutu yazo yatokare mata makogwaro,Wanda tarasa dalilinsa,hawayene kawai kekokarin fitowa daga idanunta tana kokarin maidasu. Haka takai hardare tarasa abinda keyimata dadi. Misalin karfe uku nadare tatashi,tayi sallar Nafila,tafara Addu'a. YA Allah kayayemani wannan kuncin danake ciki. Allah kasabyamin farin jini. Allah kabani masoya. YA Allah kazaba Mani muji NA kwarai. Allah ka iyakancemin wannan zawarcin. YA Allah wannan DUHU danake taredashi Allah kayayemanishi. YA Allah kahaskakani. YA Allah ta gabas,data yamma. Ta kudu data Arewa,Allah kafitomin da muji mai Albarka. Allah kayafe Mani zunubaina, ka yafemani kura kuraina. Tadauki lokaci tana karanto Addu'oi kala-kala abakinta,daga karshe taita karanta salatin Annabi (S A W ) har bacci yadauketa. Saida akakira sallar Asuba,tatashi tayi RAKA'A TANUL FAJIR sannan tayi sallar asuba. Nan taci gaba dazama harrana tafito,dama bata komawa baccin safe,Al-Kur'ani take dauka taita karantawa harrana tafito. Misalin karfe Takwas nasafe, 'yarta khadija tashigo,bayan tagaisheta tace mama, malam fayayi maganar kudin wata,tun wancan satin bakibaniba. Faiza tayi shiru,fonta manta da maganar kudin watan yarannan,tace: To yanzun dai banida kudi,kuje kuzauna nanda kwana biyu idannasamu zanbaku kukai. Khadija tace to mamammu aikoromu za'ayi. Tadaka mata tsawa,bacewa nayi kuje kucire kayan kuzaunaba!!kocewa nayi kuje makarantar?kubar zuwan innasamu nabaku kunje,tunda kokunjedai koroku za'ayi. Kuma kinatsu agida,saura kitafi yawo,iyacidai aikene aita aikenku,kowane yaro yatafi makaranta saiku,wannan ya aika-wannan ya aika,Allah dai yarufamana Asiri. Khadija tawuce,sukaje sukacire kayan makarantar gaba dayansu. Faiza tafara tunanin inakuma zata samu kudin dazataba yarannan sukoma makaranta,haka wancan watan saida yayi sati biyu basujeba,Toh!Allah yakawo hanya. Misalin karfe Hudu NA yamma,maman Hafsat tazo wurin faiza,bayan sun gaisa take cewa: Dazun INA tafiya baje siyo kayammiya,dayake duk yara suntafi makaranta,saina hadu da malam shehu,zashi gona,yake tambayata kina INA?yaga kinrabu da zuwa. Nace kinanan lafiya lau,shine yace idannazo wurinki infada maki yanason ganinki. Faiza tace wallahi maman Hafsat nida nama hakura kawai,wannan dai Abu Allah yayi Mani maganinsa,kumani yanzun konacema zanje wurinsa banida kudi,kumani banaso inta zuwa banda kudi. Maman Hafsat tace hakane,amma kuma ai ansan halin da ake ciki,taimakamaki kawai zayyi,kidai shirya kije kiji Neman dayake Maki. Faiza tace toshikenan,nidai banda kudi,hakanan zani. Maman Hafsat tace kije hakanan din,aidai kinji abinda zaice maki. Karfe biyar nayi,faiza tashirya tatafi wurin malam shehu mai Almajirai,bayan sun gaisa yace: Faiza kwana biyu? Tace malam kuma lafiya lau,nadai rabu dazuwane. Yace tome yasa? Tace hakanan malam,abinne naga sai ahsnkali,haryanzun daishiru,nida harma nahakura. Yace inayimaki bakin kokarina,al-amarinne yayi Nauyi dayawa,gaskiya bantabayin aiki irinnaki Wanda yadauki jinkiri hakaba,idnnayi Rokon Allah to acikin ikonsa ba'awuce sati daya bukata batabiyaba,amma naki gashi haryanzun,meke faruwa dakene? Shinko zaki iya tunawa,kokin tabayin wani laifi Babba Wanda yasa haryanzun bukatarki bata biyaba? Faiza tadanyi jimm! Tana nazari,sannan tace gaskiya a iyasanina bazance gawani laifi babba Wanda bazan iya mantawa dashiba,tsakanina da Allah saidai kananun kura-kurai kawai, wadan da baza'arasa kowane bawa dasuba,sannan bana wasa da ibada,koda yaushe kumani onacikin yin istigfari,gaskiya malam babu. Bayan malam yagamajin maganganunta sosai,sannan yace toshikenan,amma yaya mu'amalarki da mutane?baki taba cutar wani ko wataba? Kinsan kana iyayin wani laifi,ko kayima Allah kokuma bawansa,sai Allah yahukuntaka tun aduniya. Misali:keko kintabayima Allah wani laifi ko kin cuci wani bawansa,sai yakeyimaki hukunci da abinda kikafi so,yahanaki mujin aure sakamakon wannan laifin? Faiza tace gaskiya babu,INA zaune dakowa lafiya. Malam yace: TOYAYA KIKA ZAUNA DA TSOFON MUJINKI????????? Nan da nan daji gabanta yafadi,domin koda wasa bataso taji anyimata maganarsa,domin kuwa bazan dadi tayi dashiba,kaddaracema tasa harta iya Tara 'ya'ya Hudu dashi,wadanda gasunan kuma yasakarmata dawainiyarsu,nan danan taji idanunta sunciko da hawaye. M-shehu yalura da hakan,yace kifadamin yaya kikayi zamantakewa tsakaninki damujinki????kifada Mani kada kiboyemani komai,domin asan ta yadda za'abulloma al amarinnaki. Karshenta akwai wani zunubi dakika taba dauka,Wanda Allah yakeyimaki hukunci da hanaki mujin aure,azaman takewardakikayi da mujinki. Faiza tabude baki tace. SUNANSA GARZALI. Munyi zaman aurene dashi,irin aurennan da akecema , BAZA FITA HAKKINABA NI KUMA BAZANYIMAKA BIYAYYABA!!!!! Ahaka mukayi rayuwar zaman auremmu. Hakika zanfada maka irin zaman da mukayi da GARZALI,zama NA rashin fahimtar juna. Farkon Al-amarin dai shine,munyi..................... Is'haka neyashigo gidan da kuka,Dan dan fauzane,yayan khadija,yana kuka yana fadin,mama kizo ga khadija can antafi da ita Asibiti,batada lafiya!!mamammu mutuwa zatayi!! Faiza najiyo muryarsa tayo waje dasauri,tatarbi ishaka,tace meke faruwa?? Yace kgadijace ankaita Asibiti asume,batasan inda kanta yakeba,sai jini yake zuba ajikinta. Faiza tace hatsari tayi? Yace a'a kizo muje. Cikin sauri kuwa faiza tabiyo bayansa don ganin meyasamu 'yartata. Kwance tatarar da khadija,batasan Wanda kekantaba,sai jini daya bata mata kafafuwa. Afirgice faiza tace meyasameta!!?akace kuntafi Asibiti? Mama tace tana kuka,daukota kawai akayi daga waje a some,wanine yayimata fyade. Faiza tafasa wata gigitacciyar kara,tareda fadin,mama waye shi!!? Mama tace bamu saniba kawai dai dauko mana ita akayi ahaka,bamusan Wanda yayimataba,yanzun dai jira muke asamu tafarfado,sai asanyamata ruwan dumi,inya kama sai atafi Asibiti,daharmun dauketama zamu tafi,saikuma muka tuna bamuda kudi. Faiza kanta juyawa kawai yake,cikin sambatu tana fadin. Waye wannan?waye shikuma ya aikata mata haka?khadija ta! Inna lillahi wainnailaihirrajiun,takara fashewa dakuka,tareda girgiza khadija,datake kwance akan tabarma. Tana fadin zadai tatashiko?bakasheta akayiba? Mama tace kiyi hakuri faiza zata tashi,debo ruwa akara yayyafa mata. Cikin rawar jiki tadauko ruwan sanyi tamikama mama,aka kara yayyafa mata,amma shiru. Wani irin tashin hankaline yakara ziyartar faiza,shindamema zatajine? Datalaucin daya ishesu zasuji koko dawannan mugun Abu dayasamu diyarta?koko da matsalar datake tareda ita tarashin aure? Batasan lokacinda takara fashewa dawani matsanancin kukaba,gashi basuda kudin dazasu kinkimeta sukai Asibiti,inma sunje ana iyacewa saisunzo da dansanda,to duk inasukaga kudin dazasuyi wannan cuku-cukun? Don haka kawai duka hakura dukaita iya bakin kokarinsu,sai zuwa dare sannan tafarfado. Bayan tasamu kanta sosai,ake tambayarta waye yayimata haka? Tafada masu.... Tafada masu,wanine nan anguwarsu,aiko adarennan,faiza tayi nufin taje tasameshi,hardakin dasuke kwana,amma akafada mata bayanan. Nan take tambayar samarin dakin,sukace mata bazo kwanaba yau. Tace:towa yasan inda yake yanzun? Wani yanakwance cikin barci yace: wai surajo ake nema? Faiza tace e kokasan inda yake? Yace dazundai kafin magariba munhadu dashi yake cemin idan inada kudi inrantamai zai tafi legos,nacemai banidasu,sayyace zaitafi yanema awani wuri. Sai daya daga cikin samarin dakin yace aiko yasamu kudin nan bazai samu tafiya yauba,saidai dasafe yayi sammako,karshenta dai yana shagon baya,dakinsu kamisu. Faiza tace inane dakin? Yace meyafarune,dai dai lokacin dayake tasowa daniyyar zairakata. Tace nemansa nake ruwa ajallu!! Yace lafiya daiko? Tace 'yata zankarbarma hakkinta nalalata mata rayuwa dayayi,tafada masa abinda yafaru. Yace kaih!kaih!!kaih!! To Allah koyasa bai guduba,don Tabbas naji yana cewa Lagos zashi. Suna zuwa kofar dakin yayi sallama,sannan yace subudemai shigowa zayyi. Bagaddama suka budemai,yanashiga yace mata gayacan!!! Tace Alhamdulillahi! Fito!! Yawani tokare yana fadin lafiya! Wanda yarakotadin yace a'a bazaifitoba,gashinandai munrike makishi,donyana iya fitowama yaruga,nan zamu tsaremaki shi harkije kinemo 'yansanda. Nanfa samarin dakin sukaita lafiya-lafiya!!yabasu labarin abinda yasa take nemansa,duk kuwa suka bada hadinkai akahanashi fita,don inyafita baza'akara ganinsaba,aiko suka sakashi atsakiya,don kada yagudu. Duk dahaka hankalinta baikwantaba saida takarasa kannanta maza sukazo donsu kara tsarematashi kafin safe. Tunda sassafe kuwa tafara Neman mafita,inda zata samu rancen kudi,domin tamikama 'yansandashi. Tarasa yadda zatayi,saita dauko wasu Turmin zani dataketa ajiyarsa,daniyyar in Sallah tayi zata dinkama yara,to bayadda zatayi,wannan zani tadauka tatafi bin gidajen dillalai. Bayan tatafi mama nazaune da yarinya agabanta,sukajiyo sallama,cikin hanzari dakuma mamakin muryar dataji tana sallama agidan,tamike tsaye,tare da tunanin shin meyazoyi?waya sanar dashi? Yana shigowa abinda yafara fadi: Khadijar ce anan kwance?meyasa ba'akaita Asibitiba? Mama kuwa mamaki ma gaba daya yahanata bashi amsa,sai cewa tayi waya fada maka? Sannan yace Inakwana mama? Tace lafiya lau inakaji wannan labarin? Yace fadamin akayi,shiyasa nayi sammako nazo,amma dai yanzun afara kaita Asibitin,sannan indawo inyi binciken wane DAN ISKANNE YAYIMA 'YATA HAKA!!!!!wallahi sai inda karfina yakare!!saina kwatar nata hakkinta!!! Dai dainan maman Hafsat tashigo gidan,tana salati,tace kai jama'a!wannan wane irin abune?Ashe haka tafaru?sai yanzun nakeji! GARZALI yace aiba yadda zanyiba!!karamar yarinya kamar wannan!!aisai inda kargina yakare!!adai kaita Asibitin adawo,sainayi kararsa,sai anyankemai hukuncin dayahau kansa!!! Maman Hafsat tace Tabbas!!haka yakamata,aidolenema adauki mataki!saboda gudun kara faruwar haka anan gaba,Faiza tagane yaron kuma tasa antsare matashi,lallai wallahi kadage sai ankwato mata hakkinta! GARZALI yadauki khadija yafita da ita Maman Hafsat tace waye wannan??? Maman faiza tace humf!Babansune,kinganshi,nigaba dayama mamaki yarufeni,koya akayi yasan dawannan abin?kinganni nayi tsaye inakallon ikon Allah,mutum kamar daga sama. Maman Hafsat tace labarin duniya aibaya boyuwa,yanzun haka wani yaje yafada masa. Maman faiza tace ikon Allah bari nabishi muje Asibitin,mama tafita suka wuce. Maman Hafsat tana zaune tana jiran dawowar faiza. Kimanin mintina goma shabiyar saiga faiza tashigo,tana fadin maman Hafsat nasamo kudin!!aiyyau wannan mutumin sayya gane kuskurenshi!!!karamar yarinya kamar khadija zaka lalata!! Karamar yarinya kamar khadija zaka lalata!zaici ubanshi kuwa wurin police!! Maman Hafsat tace aininamaga kokarinki,dabaki fara tsinkamai mariba!komin girmansa,tunda bayada gaskiya,aiyau zaigane kuskurensa. Faiza tace humf! Kedai bari,INA maman take? Maman Hafsat tace sunwuce Asibiti. Faiza tace ya'akayi?jikinnatane yarude?INA suka sami kudin? Maman Hafsat tace kedai bari,abin mamaki,Babansune yazo,Ashe har mota gareshi?amma baya kulaku,Ninagama ajikinsa bawata alamar wahala,nifa nadauka talaucine yasa baya kulaku,aiko yazo ranshi abace,yadauki 'ya yatafi kaita Asibiti. Faiza tace kenifa banganeba,wane Baban kikenufi? Maman Hafsat tace GARZALI mana. Faiza tace GARZALI?meyakawosa?waye yafadamasa??? Maman Hafsat tace oohoo!!nimadai zuwa nayi nataddashi. Ran Faiza yayi mugun baci,tace maman Hafsat bari naje Asibitin,Fuuuu!tafita gidan cikin sauri. Tana isa Asibitin kuwa tatarar dashi,yanata kumfar baki,akan sayya dauki mataki akan Wanda yalalata rayuwar 'yarsa. Yana ganinta kuwa yace:yauwa Faiza!INA Wanda yayima yarinyarnan fyade?ance kinsa anrikeshiko?fadamin INA yake,kokuma muje kinuna manishi,in makashi a Coute bada wani bata lakaciba!!don yau................ Tace Dakata da Allah!kai harkanada bakin dazaka iya fadin wannan maganar?kai Asuwa?wane karambanima yasa kadaukomin 'ya kakawota Asibiti?sanyaka nayi?? Wallahi Garzali akan wannan maganar ta fyade,baikamata kana saka bakinkaba!duk waye yajawomana hakan?dukkaine,nayi nadamar kasancewarka amatsayin uban 'ya'yana. Annabi (S A W ) yayi gaskiya,dayace kazabama 'ya'yanka uwa tagari,ta ishi hannayenka,to kamar hakanema idan uwa tazabama 'ya'yanta uba nagari ,wallahi Garzali indakai mutumin kirkine,da wannan matsalar bata samemuba,Kaine musabbabin haddasamana ita!kai yanzu atunaninka har wani mataki zaka iya dauka?bakaji kunyar fadin wannan maganarba!nikadai yakamata inbugi kirji ince zandaukarma 'yata mataki bakaiba!kuma kaikaje kayi tunani da kanka,kaga abinda kake fadima yadace yafito daga bakinka!! Garzali!kafita harkar 'ya'yana!!dama bakomai kakeyimasuba!!sai wannan zaka kwaso jiki kace kazo karbarma 'yarka hakkinta!dalilinmeto??asunan kanawa? Mama tataso tace ya isa hakanan Faiza,kibarshi ya karbarma 'yarshi hakkinta,Wanda dama kema kudurinki kenan,abinda yawuce yawuce kawai. Garzali yace:aiduk duniyarnan bawanda ya isa yahana insa ahukunta wannan la'anannen daya lalatama 'yata rayuwa,mama kibarta kawai,nibazan fasa abinda nayi niyyaba,kuma natabbata itama tanaso akwatoma khadija hakkinta,ninedai data tsana,shine zatazo tayi wata burgar banza da wofi,kuma natabbatar abinda keraina itama shine yake aranta. Tace karya kake garzali!bazamu taba hada kuduri daya nidakaiba!!hanyar jirgi dabam ta mota daban!!kuma nice da nasara akanka,bazaka taba cimma kudirinkaba!! Ada nayi niyyar inkwatarma 'yata hakkinta nikadai,amma tunda kasa baki kudurinka bazai taba cikaba!! Tana gama fadin haka tabar Asibitin dasauri. Dakin samarinnan kawai tanufa,tana zuwa tace: Surajo kasamu kudin motar jiya dakayi niyyar guduwa? Yace bansamuba. Tace kukwanceshi. Samarin sukace yaza'ayi mukwanceshi?muna kwanceshi guduwa zayyi. Tace Ku kwanceshi kawai bashi ya aikataba,sannan tamikamai kudin dasuke hannunta,tace gashi kayi maza-maza kagudu,kada kabari akamaka,duka kudin data saida Atamfar nan tamikamasa. Sannan tawuto gida cikin wani irin yanayi,data kasa gane meke damunta,tana zuwa tafada daki taci gaba da kuka mai tsuma zuciya. Maman Hafsat ce tashigo gidan,tasameta tafara bata hakuri. Itadai kuka kawai take,takuma kasa cemata komai,suka dade ahaka maman Hafsat nata bata magana,ita kuwa kukanta kawai takeyi. Zuwacan Garzali tashigo gidan yana fadin: Amma gaskiya faiza kinbani.... Amma gaskiya Faiza kinbani mamaki!ya akayi kikasa akasakesa? Maman Hafsat tayi saurin kallon faiza tace wakikasa akasaki? Garzali yace yaron dayayma khadija fyade,waishine tasa akasakeshi!bayan tayi kokari tasa anrikematashi. Maman Hafsat tace garin yaya hakan tafaru faiza?Guduwafa zayyi yanzun shikenan yaci bilis!kinkausan abinda kikayi? 'Yarkicefa za'akwatarma hakkinta. Garzali yace baici bilisba! Wallahi saina dauki tsatstsauran mataki akansa! Maman Hafsat tace bayan yagududin? Gashi bata fadamana kodan inabane. Garzali yakalli faiza faiza yace gaskiya baki kyautaba!kifada mana kowayeshi,kokuma inazamu sameshi?kokuma harke saina dauki mataki akanki!! Tace bazan fadaba!!yaci bulus din!!saboda baka isa muyi tarayyadakai wurin kwatoma 'yata hakkiba!bazan taba yadda ra'ayinmu yazo daya nida kaiba!!kai harkanada bakin dazakace kazo karbarma 'yarka hakkinta?kai hakkokinnata nawane katake? Maman Hafsat tace faiza yanzun balokacin wannan maganarbane, 'yarkuce 'yarshice,wannan iftila'i yafaru akanta,tunda har Allah yasa yazo kamata yayi kuhada karfi kukwatarma yarinyarnan hakkinta,duk wani fushi dakikeyidashi,kamata yayi ki ajiyeshi gefe,Ku tunkari wannan matsalar gaba daya kedashi. Faiza tace maman Hafsat bazaki fahimci komaiba,bakisan miye tsakanina dawannan Azzalumin mutuminba!!iyakar abinda kikagani kawai kikasani. Barin danayi akasakeshi shine daidai hukuncin daya kamata inyima garzali,domin yakara tabbatarma dakansa cewa narabu dashi har abada,kuma bazamu taba hada ra'ayi daya nidashiba! Sannan takalleshi sosai tace: kai baka dace daka zama uban 'ya'yanaba! Mace mai kyawawan halaye da kyawawan dabi'u da ilimin Addini da aiki dashi,bai kamata ace ta auri muji mai mugun hali da jahilci da mummunar dabi'a irinka!! Kai yanzun don har anyima 'yarka fyade kanada bakin dazakazo kace zaka karbar mata hakkinta?kai harka manta dacewa munanan halayankane suka jefa 'yarka ahalin datake yanzun ,Garzali kaje kayi tunani da kwakwalwarka kaga matakin dakakeshirin dauka akan Wanda yayima 'yarka fyade yadace daka daukeshi? Dai dainan wasu hawaye suka zubomata,tace: lallai Annabi ( S A W ) yayi gaskiya dayace kazama yayaka uwa tagari,to kamar hakanema idan uwa tazabama 'ya'yanta uba nagari. Nayi nadamar kasancewarka amatsayin uban 'ya'yana! Kada kamanta Garzali abinda kayine.............. Dai dainan kuka ya kwacemata,takasa idasa fadin abinda yake bakinta,tashige cikin daki dasauri tana rizgar kuka. Nan tabar Garzali tsaye cike dajin haushin daya kasa fahimtar inama maganar Faiza ta dosa?har a lokacin ranshi abace yake,kuma cike da alwashin sayya dauki matakin dayayi niyyar dauka akan Wanda yalalata rayuwar khadija,lokaci daya kuma haushin faiza yakara turnukeshi,domin kuwa talalatamai wannan shirinnasa,yanzun inazaiga wannan yaron?bayan tasa yagudu. Cikin fushi yace: baki isaba Faiza!kamar yadda kikasa yagudu haka zaki nemosa,kokuma duk hukuncin danayi niyyar dauka akansa insaukeshi akanki!!!don wannan varazanar banzace kikeyimani!!! Sannan cikin. Fushi yafita yabar gidan. Maman Hafsat natsaye tana kallon ikon Allah,cike da mamakin wannan Al amari dayake faruwa,shinma wai duk menene musabbabinsa? Ahakadai tashiga dakin da Faiza take,zaune tasameta tana aikin kuka,zuciyarta cike da kunci da bakin ciki. Zaunawa tayi Daf!da ita,tace Faiza gaba daya wannan Al amarinnaku nakasa gane kansa,duk daban taba ganin mujinkiba,sai wannan karon,amma hakan kawai yanunamani cewa lallai bakuyi zaman dadi da fahimtar juna atsakaninkuba,kuma hakan yatabbatarmin dacewa,koda Garzali yanada laifi a zamantakewar da kikayi dashi abaya to lallai kema kina dashi. Faiza tadago kai takalketa tace: bazaki taba fahimtar halin wannan Azzalumin mutuminba!gani daya kadai dakikayimasa,bai isa yasa kice kin tantance halayensa da dabi'unsaba! Maman Hafsat natsani Garzali!! Bana sonsa! Banason duk wani Wanda yake sonsa,tun lokacin Dana aureshi natsanesa! Maman Hafsat takara kallonta cike damamaki,tace: tun lokacin dakika auresa kikatsaneshi? Meyasa hakato? Kintaba zama da kishiyane? Humf! Faiza tayi ajiyar numfashi,tareda share hawayen dasuka jikemata fuska,sannan ta sassauta muryarta tace: Banzauna da kishiyaba,Asalima saubayan barabu dashi sannan yakara aure,nasanki da zargi,don kada kiyi tunanin ko kishiyace tarabani dashi,Toni banzauna da kishiyaba,dagani saushi mukazauna,har Auren yamutu,sannan kuma yayi watsi damu,yasakarmin dawainiyar 'ya'yansa, khadija bata sanshiba,don miye yanzun don wani iftila'i yafadomata zaizo yabugi kirji yace yazo karbar mata hakkinta!shi hakkokin nata nawa yatake? Maman Hafsat tace kuma da alama yanason 'ya'yansa,tunda dibifa yadda ya hakikice akan wannan al'amarin,anya kuwa faiza bawani sihirin akayimasa akarabashi da 'ya'yansaba? Faiza tace bantaba zargin hakanba,kawaidai mugun haline irinnasa,don bakiji labarin yadda nazauna dashibane. Maman Hafsat tace fadamin yaya kikazauna dashi? Faiza tace hakika nayi zama da Garzali irin zamannan barashin fahimtar juna,zamane Wanda bazaka fita hakiinaba nikuma bazanyimaka biyayyaba,hakika yanzun nan zanbaki labarin irin zaman damukayi da Garzali. WATA RANA................ Sallamar maman Faizace takatsemasu firar dasukeyi,don haka sukayi saurin amsawa gabaki dayansu. Cikin fushi maman Faiza tashigo,taredayima faizar fada,dacewa: Wannan wane irin haukan banzane! Yaya zakisa asaki mai laifi,al halin laifinnan keyayimawa!wannan wace irin zuciyar babzace gareki! Kina ganin hakan dakikayi shine zaisa ran Garzali ya baci! To wallahi koda ranshi yabaci naki sayyafi nashi baci? Tayaya kikeso dole laifin da ubansu yayi maki kuma kihuce akan 'yarsa?to kisani wannan bawata mafita bace kikafito da ita maibullewa! Kullun Addu'a muke Allah yakarkato da zuciyarsa akan 'ya'yansa,kikasani ko dalilin hakan Allah yajuyo da hankalinsa akan 'ya'yan. Nan dai tarufeta da fada,ita dai faiza banda kuka da kuncin da takeji acikin zuciyarta,ba abinda takeji,don kuwa harlikacin batayi nadamar wannan mataki data daukaba,domin gani take wannan shine dai dai abinda zatayima Garzali,donya dandani bakin ciki da takaicin dashi yafara jefa rayuwarsu aciki,kuma yakara tabbatarma dakansa cewa ta tsaneshi,kamar yadda tatsaneshi tun afarko,don haka koda wasa bazata taba yadda suhada ra'ayi daya ita dashiba. Nan dai maman Fauzar taitayimata fada,ta inda takeshiga batanan take fitaba,dinta nunamata irin kuskuren data tafka akansawa datayi akasaki yaron dayayima khadija fyade. Maman Hafsat kuwa kasa cewa komai tayi,don gaba daya ita kantama yakulle,wani lokacin taga laifin Faizar,wani lokacin kuma tace ayyakama ayimata uzuri,domin kuwa ita tazauna da Garzali,ita tasan ukubar daya ganamata,wadda takasa mantawa da ita,tasa harta dauki wannan matakin. HAKIKA ZANSO INJI WANNAN LABARI NA RAYUWAR AUREN FAIZA DA GARZALI Haka dai taita tunani,daga karshe takomaba maman Faiza hakuri. Awunin Ranar haka Faiza tawuni cikin kunci da bakin ciki,Wanda azuciyarta har takecewa inama mutuwa tayi da irin wannan tashin hankalin,kuka dai tayi shi harba iyaka,gabakin cikin ketama 'yarta budurci da akayi,ga Garzali kuma yazo yakara bata mata rai,don Tabbas! Dabaizoba saita karbarma 'yarta hakkinta amma zuwansa yalalata mata wannan kudurin,yanzun shikenan Wanda ya aikata wannan laifin yasha? Yatafi abanza kenan? Amma dukda haka idan tatuna yadda Garzali yake hakikicewa akan sayyabima khadija hakkinta,tatuna yadda ranshi yabaci,yadau zafi,haryana rantsuwar sayyasa anhukunta yaronnan. Idan tatuna cewa tawargazamai wannan shirin,saitaji farinciki yamamaye zuciyarta,hartadanyi dariya,takara godema Allah dabaisa Garzali yayi nasarar kama yaronnanba....... Tasandai ko banza shima ta Dan danamai wani bakin cikin dabazai manta dashiba. Domin kuwa tatsanesa!tatsani farin cikinsa! Haushinsa takeji!! Garzali yazo yagama fadansa da kurarinsa yabar garin,domin cewa yayi baiga amfanin zamansaba. Azuciyar Faiza tace:Allah yasa kayi hatsari ahanya kamutu kowama yahuta! Insan cewa 'ya'yana marayune kotallafi Marika samu. Abangaren maman Hafsat kuwa,azuciyarta tana kara rayamata cewa lallai akwai abinda kefaruwa gameda Faiza,amma tafi danganta abin dacewa sihirine akayimata,domin inba sihiriba waye zaiki 'ya'yansa? Koda sunyi fada tsakaninsu baikamata ace yawatsar da 'ya'yansa ba,kamar yamanta dasu,anya kuwa wannan Al-amarin babu sammu acikinsa?? Gashi kuma Faiza tacika taurin kan tsiya! In ance tanemi magani saitace shirkane,duk inda akace game magani ta amsa sai tace Bokane,ninama rasa yadda zanyi da ita,tunda NA malan shehu dinnan abin yakici basaimuje wani wurin ba,amma taki yadda. Amma dai nasanyadda zanyi. Saitadan jima tana tunani,sannan tace yawwa!! Kauyensu Faiza zani! Ainasan garin muntaba zuwa tareda ita,yaronnan mai magani daya taba ganinta yace tanada lalura shizanje innemo duk inda yake, tun lokacimma data amshi maganin dayanzun anwuce wurin! Tatsaya kinibibin cewa ai Bokane. TONI NAYI ALKAWARIN DUK INDA YARONNAN YAKE ZANNEMESA IN'ANSAMMATA MAGANI AWURINSA. KODA KUWA YARON ZAI KASANCE BA MUTUM BANE!!!!!!! Misalin karfe Hudu nayamma,Faiza nazaune,akayi sallama,akace ana sallama da Faiza. Tasanya hijabinta tafita. Malam shehu tagani,tasandai yazone yayi masu Allah kyauta,bayan sungaisa,tace bari nadaukoma abinzama. Yace a'a kibarshi kawai. Sautashiga gida takira maman ta,m-shehu yayi masu Allah yakyauta,tareda jajantamasu. Maman Faiza ymtayimai godiya sosai gameda kokarin dayakeyi akan Faiza NA Adduoi,sannan tashiga gida. Har lokacin idanun faiza juwur suke,tana digar da hawaye lokaci zuwa lokaci. M- shehu yace jarrabawace,komai dakike gani yasamu bawa kaddarace,kuma musulmi kedauka. Tabbas indai kace kayi imani da Allah tokadingi gamuwa da jarrabawa kenan arayuwarka,saidai muyi fata da Addu'a Allah ya jarrabemu da Kaddarar da imaninmu zai iya dauka. Yaci gaba dacewa rannan dakikaje wurina,kinso kifara bani labarin yadda kijazauna da tsofon mujinki,sai kuma wannan kaddara tafaru,Wanda yayi sanadiyyar tafowarki gida baki fadaminba, to aibafasawa za'ayi ba,idan komai yalafa hankali yakwanta kisamu lokaci kizo kifadamani don musan ta yadda zamu bulloma Al amarin. Tace to shikenan malam insha Allahu zanzo,dai dai lokacin datake kara share wasu hawaye dasuka gangaro a idanunta. ( mai karatu kada kamanta kana karanta littafin WATA SAKAYYAR.....1 Wanda Fateema Dahiru Funtuwa Binta ta wallafa, gamai Neman marubuciyar kai tsaye domin bada shawarwari ko wani karin bayani zai iyasamuna tawannan Number. 09162526909 ) Malam shehu yace sai hakuri,Allah yakiyaye gaba,amma dai duk dahaka Faiza kinyi kuskure babba da kikasa akasaki yaronnan,kowannan kadai yayta sanyaki bacin rai domin baki bima 'yarki hakkinta ba,kuma bakiyima kanki adalciba,idan har anasakin masu laifi aikinga baza'adaina aikata laifinba,kowama sayyayi abinda yaga dama kenan. Faiza tace gaskiya nayi niyyar inbima 'yata hakkinta amma tunda babanta yashiga cikin maganar nan dolene inhakura da ra'ayina,kodan ganin nashi kudurin baicikaba. M-shehu yace tome yasa hakan?? Faiza tace Saboda natsanesa!banason farin cikinsa kamar yadda bayasonnamu! Saina wargaza tsarinsa kamar yadda yawargaza tsarin rayuwarmu! Saina sanya Mashi kunci da bakin ciki azuciyarsa kamar yadda yakeso ya dawwamar damu acikin kunci da bakin ciki arayuwarmu!!!! Yabarmin 'ya'yansa baisan cinsuba,baisan shansuba,baisan suturarsuba,baisan ciwonsuba,duk wata dawainiya da uba yakamata yayima 'ya'yansa bayayi..... Yasakarmin dukkan wahalarsu,nikuma bakarfi gareniba.Hakika WATA SAKAYYAR SAI A WURIN ALLAH!!! Allah ya isa tsakanina da Garzali!! Dai dainan takara fashewa da kuka,sannan tana fadin,hakika malam idanna fada maka yadda bayi zaman aure dashi, dawahalar danasha nida 'ya'yana awurinsa,saika tabbatar dacewa matakin Dana dauka akansa yayi dai dai dashi,saika yadda dace duk wata hanya dazanbi domin in muzgunamashi itace tafi cancanta dashi daga gareni. ALHAMDULILLAH! Anan nakawo karshen littafi nadaya,mai karatu biyoni acikin littafi NA biyu donjin yadda zata kasance. Shin maman Hafsat zata samu nasarar haduwa da wannan yaronnan mai magani??? Wadanne irin kalu abale zata fuskanta awurinnemansa???? Tunda dai munsan cewa Gwagwgwo Hauwa ta fadama Faiza cewa masu magani shigowa kawai kauyen suke sutafi,ba lallaima kakarajin duriyarsuba. Shinko mai maganin zai iyaba Faiza magani dukda tayi mai wulakanci afarko???? Yaya labarin rayuwar Auren Faiza da Garzali takasance????atsawon zaman dasukayi harta haifi 'ya'ya hudu dashi??? Shin Faiza zatayi aure koko kaddararta kenan?!?? SHIN MENENE AINIHIN MATSALAR FAIZA????? Kai daikasance tareda Fateema Dahiru Funtuwa Binta. Maman Rukayya. MARUBUCIYAR LITTAFIN BABBAR HUJJA 1&2&3 KWATAR KAI 1&2&3 RUDANI 1&2 WATA SAKAYYAR........ ________________________________________ Wani yanki daga cikin littafin BABBAR HUJJA 2 Yadauki waya takira number Alhaji Salisu,bayan sungaisa,tace: Yaya dana nakirakane insanar dakai cewar wannan auren najanye zancensa,kayima 'yarka wani mujin ba Dana ba. Alhaji salisu yace bangane mekike fadaba,kina nufin kice auren Hafsat da Ahmad anfasashi? Tace kwarai kam!anfasashi,kayi hakuri yaya banayi hakan bane don in wulakantakuba,a'a nayine kawai domin hakan shi naga yafi dacewa,saida safe. Ta kashe wayar. A lokacin kuwa kuka wiwi Ahmad yakeyi kamar mace,donya tabbatar anrabashi da Hafsat kenan. Tace kayi hakuri Ahmad,nasan rabuwar masoya akwai ciwo,to amma kaitaka tazama doleni,don haka kayi hakuri. Cikin kuka yace to umma kifadamin menene dalilin? Tace zanfadamaka Ahmad,amma bari musamu lokaci mai tsawo tukunna,domin inbaka labarin kokuma dalilin dayasa nakiyadda ka aure Hafsat,tashi katafi dakinka,Randa kasamu lokaci kazo insanar dakai labarin. Alhaji salisu yana ayije wayar ,yadauki mukullin motarsa cikin hanzari batare dayayima kowa salkamaba,yafigi motar da karfi,sai gidan Dan uwansa Alhaji Sani. Acikin dakinsa Wanda yake saukar baki yasauki Dan uwannasa. Alhaji Sani yace lafiya dai naganka yau duk arikece haka? Aidole kaganni arikice Sani!dominnazo maka dawani mummunan labari!!mai tada hankali !! Waikamar Hajiya Aisha takirani awaya yanzun take shaidamin danta yafasa auren 'yarmu!!! Alhaji Sani yayi saurin mikewa tsaye,tareda cire hularsa yajefar,zufa tafara tsatstsafomai adukkan ilahirin jikinsa yace: Anfasa auren Hafsat da Ahmad???????amma wannan mata tacuceni!shiyasa tunfarko nace ayi auren nan kafin tadawo!akakibin shawarata!!toga irintanan. Gaba dayamani kunrikitamin lissafina yaya!!adalilin Auren nikaina nasaran wasu mahaukatan kudi dazansamu!!ammako Aisha talalatamin lissafina!!ta cuceni yayah!!!! Alhaji salisu yamike tsaye tareda dafa kafadar Alhaji Sani yace: Bakai tacutaba Nita cuta!domin kuwa hatta kayan dakin yarinyarnan kasar waje natura aka siyosu,nakashi kudin dani kaina nasan dukiyata taraurawa,domin inasa ran za'asamu wasu bayan auren nan,domin idanna aurar da Hafsat ga Ahmad tankar wani jarine nazuba Wanda nake hangensa kusa-kusa,amma tazo tatarwatsamin wannan shirin!! Don haka bakai tacutaba Nita cuta!nima din bata cuceniba kanta tacuta!!domin wallahi bazanyi asaraba!!!matsalarmudai kudiceko? Tobasaita hanyar wannan auren kawai zamu sanesuba. [19/12, 10:16 pm] Fatima Dahiru Funtuwa: AKWAI WATA HANYAR!! Alhaji Sani yace tayaya za'ayi musamu wata hanyar? Kaidai kawai Aisha Tagama watsa mana shirimmu! Saida nagama karantar da yarinyarnan kwantar dakai,da lallashi domin tasamomana abin hannunsa,amma lokaci guda an lalata mana wannan shirin!toma miyene dalilinta NA fasa auren nan?kodai tagano shirimmune? Alhaji salisu yace ko daya mummunar Akidar Nance,dakuma riko da abinda yafaru tsakaninmu tunna yarinta,shine takeso tadawo dashi sabo. Alhaji Sani yace aini nasha abinda yawuce yariga yawuce kenan,to lallai kam!!Aisha tadeboma kanta!! 'Yan ubancinne zata nuna mana yanzun?? Alhaji salisu yadafa kafadarsa yace kakwantar yace kakwantar da hankalinka,ninasan abinyi!dani take magana! Sannan yafito cikin gidan yana kada makullin motarsa,tareda yin kwata,yanufi inda motarsa take yakuma figeta da karfi. ________________________________________ Wani yanki daga cikin littafin BABBAR HUJJA 2 Dai dainan Alhaji salisu tashigo falon ,suna hada ido da H-Aisha yabata Ransa tagaisheshi ko amsawa bayyiba,kawai sayya hauta da fada. Wallahi Aisha kinbani mamaki!!ayanzunke harkinfison dangin mujinki akannaki dangin? Kika hana Ahmad ya auri Hafsat amma kikayadda ya auri suhailat! Munsan matsayinmu awurinki!baki daukemu bakin komaiba!amma ba komai kanki kikayimawa! Tace yaya bawai naraba auren Hafsat da Ahmad bane akannaso,kawai narabane domin cika umarnin iyayemmu,amnani inason Hafsat. Yace Ohoo! Ta haka kikabullo! Toshikenan tundake abin duniya awurinki baya wucewa,kinyi yadda kikeso!sannan ranshi abace yabar gidan cikin sauri yana saba BABBAR Riga, Gidan Alhaji Sani kawai yanufa. ..............to kaji dai abinda yafaru tsakanina da ita,wannan gaba tunta iyaye,nazafin kishi dasukayi,Ashe ita tana nan tana rikommu dashi!!! Alhaji Sani yace to nagane,Ashe shiyasa tazo tahana wannan auren? To INA Alhaji salisu, Alhaji salisu yace gani. Alhaji Sani yace badai matsalatmu kudi bace? To akwai yadda za'ayi asamesu,mubar zancen wannan hadin auren,mukoma ga yaya za'ayi musamu kudin da zamuyi alfahari dasu har 'ya'yammu,sanin kankane H-Aisha tanada dukiya shiyasa takemana abinda taga dama!aure yarage saura kwanaki kadan tazo tarusa manashi! Niharnafara lissafin irin ma'aikatun dazangina adalilin wannan aure,tazo talalata Mani shirina! To akwai sake!!! Kawo kunnanka infadamaka yadda za'ayi. Alhaji salisu yasunkuya,shikuma Alhaji Sani yana radamai WATA magana ,wadda akarshe suka kyakyace da dariya harda dafa hannu. ________________________________________wani bangaren daga cikin littafin BABBAR HUJJA 2 Cikin falon Alhaji sulaiman din suka sauka ,baysan sungaisa,tareda kara jajantama juna,sannan suka tanbayeshi sun kira sun ambaci abinda za'abasu? Alhaji sulaimsn yace a'a tunda ga wannan rana basu kara kiraba,dama kuma daboyayar number suka kira. Alhaji Sani yace to aishikenan duk dadai munsan matsalar bata wuce takudi,kuma Tabbas zasu kira susanar dakai,to amatsayinmu NA 'yan uwanta wadanda tayima gata arayuwarsu,saboda duk wani yanayi najin dadi da muka tsinci kammu aciki yanzun itace sila,don haka mukaga mune yakamata mubiya wadannan kudi idan sunfada, Yasa hannu yamikama Alhaji sulaiman Akwatin dayake hannunsa,yace:gashi million gomane gudummuwa daga wurina. Alhaji salisuma yamikamai NASA Akwatin yace: nima gatawa gudummuwar million gomace nima,saboda mune yakamata mufansheta,amatsayinmu NA 'yan uwanta,domin kuwa mun tabbatar kudin da zasu bukata bazasu wuce million Ashirinba,to shine mukaga yakamata mumuhada kudin................ TIRKASHI !!!!!mai karatu maza kabemi wannan kayataccen littafin donjin yadda za'akwashe da wannan harkallah mai dauke dacin amana, hikima dakuma dubara wurin boye babban laifin da suka aikata,hakika labarin BABBAR HUJJA yazo dawani sabon salo naban mamaki Daukar fansa ! Riko ! Dakuma zazzafar soyayya bantausayi Kadai maza nemi naka akan kudi naira 300 kacal. [20/12, 12:17 am] Fatima Dahiru Funtuwa: WATA SAKAYYAR........1 NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA PAGE 11 Sai dare yayi kowanacan tareda mujinta,ita saita kwanta itakadai,aida tausayi,duk kannanta nakwana daazajensu ita sai ita,kuma bama rana,aineman magani yazama dole. Maman Faiza tamike taredafadin,Bari inje induba girkina. Tana wucewa su Jamila suka fashe dadariya itada maman Hafsat,wato mama taji firar zatafi karfinta tatashi tatafi. Itakuwa faiza jinsu kawai take,gawani kullutu yazo yatokare mata makogwaro,Wanda tarasa dalilinsa,hawayene kawai kekokarin fitowa daga idanunta tana kokarin maidasu. Haka takai hardare tarasa abinda keyimata dadi. Misalin karfe uku nadare tatashi,tayi sallar Nafila,tafara Addu'a. YA Allah kayayemani wannan kuncin danake ciki. Allah kasabyamin farin jini. Allah kabani masoya. YA Allah kazaba Mani muji NA kwarai. Allah ka iyakancemin wannan zawarcin. YA Allah wannan DUHU danake taredashi Allah kayayemanishi. YA Allah kahaskakani. YA Allah ta gabas,data yamma. Ta kudu data Arewa,Allah kafitomin da muji mai Albarka. Allah kayafe Mani zunubaina, ka yafemani kura kuraina. Tadauki lokaci tana karanto Addu'oi kala-kala abakinta,daga karshe taita karanta salatin Annabi (S A W ) har bacci yadauketa. Saida akakira sallar Asuba,tatashi tayi RAKA'A TANUL FAJIR sannan tayi sallar asuba. Nan taci gaba dazama harrana tafito,dama bata komawa baccin safe,Al-Kur'ani take dauka taita karantawa harrana tafito. Misalin karfe Takwas nasafe, 'yarta khadija tashigo,bayan tagaisheta tace mama, malam fayayi maganar kudin wata,tun wancan satin bakibaniba. Faiza tayi shiru,fonta manta da maganar kudin watan yarannan,tace: To yanzun dai banida kudi,kuje kuzauna nanda kwana biyu idannasamu zanbaku kukai. Khadija tace to mamammu aikoromu za'ayi. Tadaka mata tsawa,bacewa nayi kuje kucire kayan kuzaunaba!!kocewa nayi kuje makarantar?kubar zuwan innasamu nabaku kunje,tunda kokunjedai koroku za'ayi. Kuma kinatsu agida,saura kitafi yawo,iyacidai aikene aita aikenku,kowane yaro yatafi makaranta saiku,wannan ya aika-wannan ya aika,Allah dai yarufamana Asiri. Khadija tawuce,sukaje sukacire kayan makarantar gaba dayansu. Faiza tafara tunanin inakuma zata samu kudin dazataba yarannan sukoma makaranta,haka wancan watan saida yayi sati biyu basujeba,Toh!Allah yakawo hanya. Misalin karfe Hudu NA yamma,maman Hafsat tazo wurin faiza,bayan sun gaisa take cewa: Dazun INA tafiya baje siyo kayammiya,dayake duk yara suntafi makaranta,saina hadu da malam shehu,zashi gona,yake tambayata kina INA?yaga kinrabu da zuwa. Nace kinanan lafiya lau,shine yace idannazo wurinki infada maki yanason ganinki. Faiza tace wallahi maman Hafsat nida nama hakura kawai,wannan dai Abu Allah yayi Mani maganinsa,kumani yanzun konacema zanje wurinsa banida kudi,kumani banaso inta zuwa banda kudi. Maman Hafsat tace hakane,amma kuma ai ansan halin da ake ciki,taimakamaki kawai zayyi,kidai shirya kije kiji Neman dayake Maki. Faiza tace toshikenan,nidai banda kudi,hakanan zani. Maman Hafsat tace kije hakanan din,aidai kinji abinda zaice maki. Karfe biyar nayi,faiza tashirya tatafi wurin malam shehu mai Almajirai,bayan sun gaisa yace: Faiza kwana biyu? Tace malam kuma lafiya lau,nadai rabu dazuwane. Yace tome yasa? Tace hakanan malam,abinne naga sai ahsnkali,haryanzun daishiru,nida harma nahakura. Yace inayimaki bakin kokarina,al-amarinne yayi Nauyi dayawa,gaskiya bantabayin aiki irinnaki Wanda yadauki jinkiri hakaba,idnnayi Rokon Allah to acikin ikonsa ba'awuce sati daya bukata batabiyaba,amma naki gashi haryanzun,meke faruwa dakene? Shinko zaki iya tunawa,kokin tabayin wani laifi Babba Wanda yasa haryanzun bukatarki bata biyaba? Fa An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels