An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Fatima Dahiru Funtuwa: RUDANI 1 Sunana Fatima Dahiru funtuwa Binta Anhaifeni a cikin garin funtuwa jihar katsina,ashera Alif dari Tara da cisain da bakwai (1997) Nayi primary school dina a nan funtuwa, (model 'kur an primary school funtuwa) Haka kuma nayi secondary school dina nan cikin garin funtuwa (Government girls day secondary school funtuwa) Bayannan sainayi aure a zariya, Wannan dai shine takaitaccen tarihina Fatima Dahiru Funtuwa: RUDANI 1 page 1 NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA 09162526909 Godiya tatabbata ga Allah mai kowa mai komai daya sake hadamu cikin wani sabon littafin, tsira da amincin Allah sukara tabbata ga shugabammu annabi Muhammad S A W da sahabbansa da iyalan gidansa baki d'aya Wannan littafin 'kagaggen labarine bawai abune Wanda yafaru da gaskeba,don haka idan kaga yazo daidai da irin naka rayuwar to bakaidin bane don wata kilamani bansan ka/ki ba,shirin labarinne kawai yazo dahaka. GARGADI !!!!! Ban yadda ajuyamin wannan littafin tawata sigarba,kokuma a Dora shi a YouTube bada izininaba,akiyaye. Godiya agareka Yusuf Ibrahim mai Sallah funtuwa, Allah yatsareka yakareka,yabaka abinda kake nema duniya da lahira,yadaukakeka. RU'DANI 1 fateema Dahiru funtuwa Misalin karfe biyar nayamma,lokacin da iska mai dad'i take kadawa,daidai lokacin Alhaji mansur yayi parking din motarsa,adaidai wani gida,dagani gidanna talaka wane,inbandadai da ake gyaransa yanzun,taredayimai kwaskwarima,yafito cikin motar yana kara kallon masu fantin gidan,suka nufoshi cikin sauri suna gaisheshi,shikuma yana amsa masu cike da kulawa tareda yaba yanayin aikinnasu. Bayan ya'kara duba gidan sosai,saiyakoma cikin motarsa,yadauki wayarsa ya lalubi number dayake so yakira,ba'ajimaba tadaga wayar. Yace ranki shidade inanan kofar gida inajiranki. Ta amsa Mashi sannan yakashe kiran. Mintina biyar saigata tafito,cikin shigarta mai kyau,tabude gaban motar tazauna,tareda gaisheshi. Shikuma yabude baki yana kallonta sosai,yace gaskiya amaryata kinyi kyau,kamar dai yau ake kamu! Tasa tafukan hannayenta guda biyu tarufe fuskarta tana dariya. Yace aah!aigaskiya nafada. Tace nagode tana dariya. Yace toya shirye-shiryen komai lafiya ko? Tad'anyi farrr! da idanunta sannan tace iee toh!!lafiya lau,maganar tata cike dayanga Wanda dama abinda yafi daukar hankalinsa kenan. Tace sai dai abinda ba'arasaba,haka 'kanana wad'anda dole saimun bukaci kud'i,kasan hidimar aure bawasa bace. Yace to shikenan bamatsala indon wannan ne zanturo maki,don banaso asamu matsala kwata-kwata. Tace insha Allahu aiko mai yana tafiya dakyau,kaga shima gyaran gidan ankusa kammalawa. Yace e nagani gaskiya yayi kyau sosai. Suna cikin fira saitaga yakauda kansa gefe guda yayi wani murmushi Wanda takasa gane manufarsa,hardai tace Alhaji mekakeyima dariya? Yayi saurin maido hankalinsa akanta cikin razana cikin rawar murya tareda yin wata dariya ta rashin gaskiya, yace inadariyane idannatuna dacewa yau saura sati daya burina yacika,kizama amaryata,don a yanzun jinake tamkar bantaba aureba akankine zanfara. Nan take farin ciki yamamaye zuciyarta,tace shiyasa wani lokacin idan inataredakai sai inji tamkar bada tsofo nake tareba,hakan shiyasa nake karajin sonka. Yace kai!kai!!kaih!!!baricewa tsofo!don yanzun jinake tamkar Dan shekara talatin. Sukayi dariya sosai,sukayi firarsu cikinnishad'i,anan yake sanar da ita cewa gobe zaikoma Kano,bazai dawoba sai ana igobe d'aurin auren, don haka duk abinda take bukata tayi magana donya kammala da wannan 'bangaren. Nantasanar dashi duk abinda suke bukata ,yace zaituro mata ta account, dama matsalar dai batawuce takudi,sukayi sallama yatafi. Bazana cemaku Alhaji mansur tsofo bane kamar yadda bazankirashi da yaroba,domin dai ahaife ya haifi Mariya, saidai kyakyawan mutumne sosai,Wanda kuma yakeji dakudi! Yanemi auren mariyane dukda take 'yartalaka,saidai kuma komai nadawainiyar bikin yazamana akansa,mafiyawa daga cikin hidimar shikeyi. Anan garin zai zauna da ita,dukda bagida gareshi ananba,amma dayake yaso abin saiya kama hayar gida mai kyau. Idannacemaka duk dukiyar da akazuba acikin dakin Mariya shine yazubata kada kayi mamaki,don koda Dana su aciki kadanne,hatta gyaran gidan iyayen Mariya da akeyi shine yadauki dawainiyar abin. Dukda dama ita mariyar marainiyace ,tun tana karama mahaifinta yarasu,to saidai mahaifiyarta mai mugun son abin duniya,donda karfin gwiwarta Mariya keson Alhaji mansur, don da mariyar tafara zillewa akan batason Alhaji mansur din, don ita yayimata manyantaka dayawa,kuma gasaurayinta Wanda takeso. Amma inah!!!mahaifiyar ta tayi tsalle tace ita samm!batasan wannan ba,indai ba bakin ciki zatayimataba,tana ganin ga inda zata huta itama tahuta,zatace ta'kishi,shi saurayinnata meyakedashi? Don haka Mariya idan zaki kwantar da hankalinki muci arziki mubarsa to kibi abinda nakeso ,indai dakud'i wake duban wani tsufa? Ahankali dai ta lallashi 'yarta harta amince da Alhaji mansur din,duk dadama shima yariga yasakarmasu bakin aljihunsa sosai,yawanyimata kyauta day akeyi daga ita har mahaifiyar tata,yasa itama takamu da sonsa,duk dadai soyayyar badon Allah bace, kudinsa kawai akeso. Shikuwa tsofon saurayin ta Wanda yadad'e yanasonta,kusan uwaka ubaka akarabu dashi badon dad'iba,don kuwa kudi sunriga sunrufe masu ido,domin kuwa suna wankar Alhaji mansur. HASHIMU kuwa tsofon saurayin ta ba'arabu dashi tadad'iba,donya nuna ranshi ya 'baci sosai,da tsakaninsa da mariyarne kawai suke hayaniyar,yana nunamata bata kyauta maiba abinda tayimasa. Nandanan saitafarayimai rashin kunya,tanad'an gaygayamasa magana haka,har mahaifiyar ta JUMMAI tajiyosu,saita kirasu gaba d'aya harcikin d'akinta,yashiga ya gaishe ta cikin girmamawa,sai tace: Mariya yanakejin kamar kuma hayaniya azaure? Tace mamammu hashimu ne wai akan maganar aurennan nawa,yace shifa bayyaddaba,domin shiyafara nema,ya aza'azo daga baya ace ankasashi? Mama jummai takalleshi sosai tace:abinda nakeso ingayamaka shine,shifa aure nufin Allah ne,bar ganin kadad'e kana nemanta,idan Allah bai hukunta Kaine zaka auretaba dole kahakura kabarta, kuma kada kace ba'ayimaka adalciba, nice idannabaka 'yata banyima kaina adalciba!domin bawanda zaiga arziki irinna Alhaji mansur yazo Neman auren 'yarsa,sannan yahana yaba talaka kamarka!toma inbanda abinka Hashimu INA kaga abinda zaka auri Mariya? Yabude baki zayyi magana tadagamai hannu,taredafadin dakata hashimu!! Nasan abinda kake bukata,iyakadai kace abaka abinda kakashemata,wato kudin ka,wannan dukme saukine awurinmu ,kaje kayo lis,tundaga ranar daka fara kashe mata kudi harzuwa yanzun konawane za'abiyaka! Yagirgiza kansa hawaye nazuba a idanunsa,yace bahaka baneba mama,inason Mariya, bazan iya rabuwa da itaba,duk Wanda yace zairabani da ita yacuceni............. Tadakamai tsawa,taredafadin da Allah ya isheka! rufemana baki!!tunda aiyazama dole karabu da ita!!tare kukaxo duniyar?kaje nika lissafo duk abinda kakashe mata abiyabaka!!!! Yace mama bana bukatar kudinku,ita kawai nakeso. Tace to aidama bacewanayi kudimmuba!!kudin ka mukace kalissafa,Mariya ta kuma tafi karfinka!gadai mai halidai bazamu dauka muba talaka ba!kaji nagayamaka!!kanannade guntun talaucinka kafita!!!! Wannan magana tabata masarai,yadago kai yakalleta,yace to shikenan, Allah yabimin hakkina, INDAI KUDINE GAKU GASUNAN!!!sai kunga sakayya!mutum bazayyi Abu don Allah ba,saidon abin duniya!! Sannan yakalli Mariya yace balaifinki bane,nasan kinasona ,kudine suka rufe maki ido,da kuma shawarar mahaifiyar ki,don haka indai baku sauyaba ZAKUGA WULAKANCI!!Auren kudi auren wulakancine da kaskanci,indai badon Allah Akaginasaba,kuma kusani Alhakinama bazai barkuba,don banyafeba!!KUMA ZAKUGANI!!!! Cikin sauri mama jummai tamike tsaye,taredafadin,babu abinda zamu bani sai Alkairi!!kuma aniyarka tabika!kuma duk abinda yasamu 'yata agidan aurenta Kaine!!kaibama abinda zai sameta,mezaka iyayi?dommu munfi karfinka!!!! Haryafita tana masifa,sannan tajuya takalli Mariya,tace kekuma tsayuwar mekikeyimani anan?yaunaga yaran zamani!toko kinasonshi bazaki aure shiba!!! Donbakiyimin wannan bakin cikin wallahi!!a ah!!hakanan ga inda zamusamu arziki sai azauna ayimana wata sagegeduwa!!!to duk nasan maganinku. Sannan daga baya takara komawa talallashi 'yarta dacewa: Kinga yanzun Mariya ba'a auren soyayya ,auren soyayya yanzun auren wahalane,daga zaran anyi auren wannan soyayyar takare,dakinje gidansa bashida ko sisi,akan kudin cefane isashshema saiku fara kai ruwa ranadashi, Inko kika auri mai kudi babu ruwanki da wannan matsalar, muyanzun ba gashi munfara futawaba,hatta kudin auren ki duk a jikinsa zamusamesu,kinhad'a da wannan sullutun! Don haka kikwantar da hankalinki ,kije kishiga cikin arziki da daula,harnima danake agefe insamu. To wannan shine yadda mama jummai takatse soyayyar Mariya da hashimu, taba Alhaji mansur, duk dayake shi Alhaji mansur din dattijone,amma tunda yanada kudi aiba matsala aganinta. Haka akatsaida biki da Alhaji mansur, kamar yadda tafada kuwa kayan dakin Mariya duk a jikinsa suka samu kudin nan,banda wadanda suke amsama hakanan, WANNAN KENAN. Alhaji mansur kuwa baibaro kano ba sai ranar juma'a ana yagobe za'adauka aurensa da Mariya. Nan gidan su mariyar kuwa shagali ake sosaiba, tunda duk 'yan uwansu sun hadu wurin bikin,sai ranar akakawo lefensa,shima yayi kyau sosai,abokinsane kawai yakawo lefen. To abin yaso yadaurema mutane kai,tayaya za'ace kawo lefe mutum d'aya? Saikace dai yanayin abin amunafince,sai mata akarika Dan 'kana nan maganganu,saikace angon bashida kowa! Mama jummai ko sai washe baki take,don ita wannan bai dametaba,tundadai ankawoma 'yarta kaya masu yawa,koma shiyakawo dakansa INA ruwanta!saita fara yada bakakan maganganu. Ai indai bakin cikin akeyimana asamun arziki!to kamar munsamune,talaucidai banakai 'yata inda zata sha wahala,shikuma wancan din (HASHIMU) da ake cewa yana kwance yanzun bashida lafiya,toyagajima yawarke. Tadafa kafadar yayarta,tace kiganemin nan lariya!aa sai in dauki 'yata inkaita ga talauci,gadai arziki ina kallo,wai tsofon saurayinta shine akazo ake sanar dani bashida lafiya,to aiyama gaji yatashi,don gobe iwar haka mariyama tana dakin mujinta,kuma duk matsalar data samu auren 'yata bazan yaddaba!!! Lariya tace haba jummai yakike irin wannan maganar kamar wata karamar yarinya,abinda yawuce aiya wuce,tundadai baki bashi 'yarkiba bashikenanba,saikibishi da Addu'ar samun sauki,bakiyimai mummunan zatoba. Mama jummai tace yaya lariya idanba tsaye-tsaye nayiba abinnan saiya gagareni,abinda matasan samarinnan suka ganeyi yanzun kenan,saisu hana yarinya zaman aure,saboda anyi biyu anan makwabtammu nagani,gayarannan suna zawarci,saisu hana yara zaman lafiya agidan mazajensu. Aida kikaga inata wannan kumfar bakin inafada,ba'abanza nakeyiba!inayine don intauna tsakuwa aya taji tsoro!don duk abinda yasamu yarinyata agidan muji tayadda zanyi ba!! Kinsanni sarai yaya lariya! Lariya tace to Allah madai shikiyaye,kiyi shiru hakanan kada idanun mutane yadawo kammu. Washe gari ranar asabar aketa shirye- shiryen auren Mariya da Alhaji mansur. Hashimu kuwa NA zaune bisa gadonsa,sai abokansa guda biyu da suke zaune kusa dashi,suna bashi hakuri,taredayimai nasihohi,akan duk abinda kaga baisamu mutum ba dama Allah bairubuta zai samesaba,kuma rabonka baya ta'ba ku'bucemaka,munsan abinda akayi maka daciwo,amma idankadaure watarana abin zaizama kamar ba'ayiba,ka kwantar da hankalinka hashimu,karika cin abinci. Hashimu yace nagode, tareda kallon agogon dayake manne ajikin bangon dakin,yace karfe sha d'aya da rabi za'adaura aurennanko? Daidainan kuka yakwacemai tareda sarkakken tari,dagyar suka samu suka shawo kansa,har bacci yadan daukesa. Baccin dabai wuce na mintuna gomaba,daidai sanda yafarka,sayya fara tuna abinda yafaru tsakaninsa da Mariya tuntana karama,dayadda yake dawainiya da ita. ***** ****** ******** ******* Baba kabiru shine mahaifin Mariya,dattijon kirkine,baita kadaice yahaifaba,tanada yayye maza da mata,amma itace karama. Tsakanin gidansu danasu Hashimu babu nisa, tunsuna kanana basusan menene soba suka shaku da junansu,tare suka tafiya makaranta,tare da 'yan uwanta,shine yake taremata fad'a dayake bataji,har suka fara dagawa,yanabata kula sosai. Har mama jummai watarana dai wata rana tace:Hashimu kikanaso inbaka autarnan ta wane? Yadayyi dariya,tareda ajiye takalman Mariya daya dauko mata daga waje,tabatosu saboda tsabar rigima. Mama jummai tace kazo kazauna asamaku tuwo tunda kuntaso makarantar. Dayake yayi wayau,sayyace nakoshi nabarma Mariya taci yahada danawa,alokacin shi zaikai shekara goma sha Hudu,itakuwa bata wuce shekara takwas ba. Bayan kwana biyu kuwa,suna zaune atsakar gida harda malam kabiru,kamar dawasa saisukaji Hashimu yace,mama rannan kince zaki bani Mariya, to idan mungirma nidai inasonta. Akasa dariya gaba d'aya, sunadauka shirman yarintane,sai malam kabiru yace to Allah yanunamana girmannaku,indai kanaso aisai inbaka,mama jummai tayi dariya tace kaji shiriritar yarinta,kaih!!Allah dai yashiryamana. BAYAN SHEKARU HU'DU Lokacin Mariya Nada shekara goma sha biyu, rashin lafiya tasamu mahaifinta baba kabiru,ananan yayi jinya sosai,donduk saida 'yankadarorinsu suka 'kare wurinneman magani,suka zama basuda cinyau basuda nagobe. Hashimu shike zuwa yayo buga-bugarsa abinda yasamo yakawo masu,duk dalilin son dayake yima Mariya,kuma daga gidansu hashimunma ana taimaka masu sosai, dakayan abinci,alokacin Hashimu din baiwuce shekara goma sha takwas ba. Abin mamaki kuma mama jummai tanada 'ya'ya sanari,har wadanda suka girmi Hashimumma,amma dayake mashiriritane,basa ta'buka komai,tayi fad'an -tayi fad'an harta gaji,saiyazamana Hashim din yafiyemata su,don hatta aikace-aikacen gida basasonyi,kamar irinsu AIKE- 'DEBO RUWA-DA KAI NI'KA,wani lokacin tafiso taba Mariya tayimata. To dalilin hakane yasa wannan aikin yasoma dawowa kan Hashimu,domin bayaso yaga Mariya nayin wahala,duk lokacin dayaganta da kaya abisa kanta sayya tsaya ya karba,yakance: Haba Mariya gadaini,saiki zauna kina wahala,kawo inkaimaki,ai irin wannan aikin baikamacekiba,keda nakeso kizama 'yar Hutu sosai,saidai innemo inkawo maki. Tayi dariya tace hashimu sokake kashagwa'bani sosai. Yace Mariya duk ranar Dana aureki saina maidake 'yargata,tamkar wata sarauniya haka zan mayardake,saboda tsantsar son danakeyimaki. Tace kai Hashim kaidai wannan so yanashan ambata abakinka,dazayyi 'korafidai dayayi. Yace shiyasa kekuma banta'bajin kinfurtamin irin wannan kalmarba. Tace aiwadda kake fadama ta isa tawakilci tawadin datakan. Yace to shikenan Mariya Allah yanunamana lokacin da za'ace gashi yaukinzama matata,yace kinsan wani abu? Tace saika fad'a. Yace jiya nasamu aiki a gareji zanrika zuwa koyon aiki,kinga ainasamu Sana'a,kuma duk wata wahala dake cikin aikin zan jajurce,badon komaiba saidon infarantamaki rai anan gaba,donya zamana inada saba'ar dazan rikeki,kema kiji dadin rayuwa kamar kowace mace. Tace toh!Allah yataimaka. BAYAN SHEKARA 'DAYA Jinyar baba kabiru tayi tsanani sosai,hashimu shine dakansa yadaukeshi yakaishi Asibiti,haka d'awainiyar kudin maganinnan duk a jikinsa,mama jummai saigodiya takeyimai,taredasamai albarka. Tana zaune bisa wata kujera gefen gadon Asibitin,baba kabiru nakwance,hashimu yashigo rike da leda ahannunsa,kayan marmarine yasiyo,ayaba-kankana-,lemo,yamikoma mama jummai,takarba tana godiya,shikuma yana kara tambayar yaya jikin baba? Tace dasauki, yagaishedashi. Baba kabiru ya amsa masa tare dacewa ainasamu sauki Hashim, Allah kuma yasaka maka da Alkairi,yabaka abinda kakeso duniya da lahira. RUDANI 1 page 5 NA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA 09162526909 Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen, sannan m-kabiru yayunkura zaitashi,Hashimu yataimaka mai yatadashi zaune,sai tari yad'an sarkeshi,bayan yalafa yace: Jummai lallai naga soyayyar da hashimu keyima Mariya iya gaskiyarsa yakemata ita,to in Allah yaso idan inada tsawancin kwana,zandage inga aurennan nasu yayuwu,idan kuma babuni araye,kiyimin Alkawarin cewa zaki cikamin wannan niyyar tawa,sabodaninasan hashimu bazai cutar da itaba,inakuma hangen mata jin dadi tareda kwanciyar hankali gameda aurenta dashi,toko bayan rayuwata kicikamin wannan 'kudurinnawa. Mama jummai tace in sha Allahu malam za'acika maka wannan ballantanama da rayuwarka za'ayi wannan Abu. M-kabiru Yakama hannun hashimu yace kari'kemin 'yata amana dazaran ka aureta,kada kaci amanarta,kada kawulakantamin ita,Nina baka Mariya jummai kece shaida,saikuma Allah daya haliccemu,kada asa'bamani wannan alkawari. Hashimu yace baba nayimaka Alkawarin zarike Mariya tsakanina da Allah ,bazan cutar da itaba, bakuzanbari acucetaba,nayi maka wannan alkawari baba. Mama jummai kuwa Addu'a kawai take tana fadin Allah yatabbatar da wannan Al amari,aini zammafi kowa farin ciki,yarinya tasamu indai mza'akula da ita. Bayan wannan Abu yafaru,hashimu yakara jin tsantsar son Mariya acikin zuciyarsa,yakara ganin darajarta dakimarta a idanunsa, wani irin so yakeyimat,Wanda shikansa yakasa gane kansa,yakara sanin darajarta. Bayan sati biyu dawucewar wannan Abu, baba kabiru yarasu,akayi 'yankoke-koke akahakura. Duk wasu aike da akesa Mariya hashimu yahana,yace tunda tafarazama budurwa, adaina aikenta kamarsu 'dibartuwa kaini'ka,tadai zauna tayi aikin cikin gida,yayyenta maza kuma suyi Aiken,idan bazasuyiba shizai rika zuwa yayi Aiken. Totundaganan dasafe kafin yatafi aiki sayyazo gidan yaji idan sunada aike yayi masu kana yatafi,idan kuma yadawo wurin aini mzaikara zuwa yayi masu Aiken,idan kuma yayyenta sunyi shikenan . Akwana atashi aikin Hashimu yanadad'a'karfi,garejin gyaran motoci yakeyarinta,yanasamu sosai,yanayima Mariya hudima. Don son abinduniyama irin mama jummai,wataranama itaketambayar yabata wani Abu,kotacema Mariya idan Hashimu yazo kice yabaki Abu kaza,wani lokacimma har mariyar taji kunya takasa tambaya,sai mama jummai tayimata dagaske. Takancemata, to inbanda bakida wayau!inbaki samuba yanzun saiyaushene zaki samu abin hannunsa?sana'arnan dasukeyi kudinefa sukesamu ba 'yan kadanba,to inba ki sabamai da amsar abin hannunsa ba kezaki kare awahala!kuzauna kina wani tausayin namiji,imma zaki zage kizage!banaji ance yasayi filiba? Mariya tace e yasiya. Mama jummai tace ah toh!!nidai nagayamaki,kudi sukesamu agarejinnan,don haka kima saki jiki kirika karbar abin hannunsa,inbaki koyamasa hakan ba saiyaushe?shifa namiji tun awaje akegane halinsa. Mariya tace aiko mama Hashimu yanayimana bakin kokarinsa. Mama jummai tace toshineme?don yanayimana kawai kuma saimuyi shiru! Sai abinda yadauko yabamu,mubamuda wata bukatar tadaban?to 'yar talkarnan danake doramaki yahana,yanzun badole awurinsa zamu samuba. To ahaka sukarika samun abin hannun Hashim, kuma baitaba nuna gajiyawarsa akan abinda sukeyimasaba,kuma baudaina iya bakin kokarinsa akansuba. (Mai karatu kada kamanta kana karanta littafin RUDANI na Fatima Dahiru funtuwa (Binta) 09162526909) Lokacin da Mariya yakai mshekara goma sha biyar arayuwarta,lokacin tana S S 2 a secondary. WATA RANAR ASABAR dayamma suna zaune Mariya natankaden garin tuwon yamma dazasuyi. KWATSAMM!!!! Sukaji sallama mai sallamar tashigo,duk dadai ita Mariya batason ta'ba,cikin sauri mama jummai tamike ,tareda fadin OYOYO LALE MARHABUN DA HAJIYA TANI!!yau kuma kece agarimmu? Kai maraba-maraba!tadauko tabarma tashinfida mata. Mariya tagaisheta cikin girmamawa. Mama jummai tace saukar yaushe? H-Tani tace aiko yau kwanana biyu,danazo jiya akegayamin rasuwar mujinki,Allah yajikan malam kabiru. Mama jummai tace Ameen. H-Tani tayi masu gaisuwa sosai,Mariya takawo mata ruwa,H-Tani takar'ba taredafad'in sannu 'yammata. Mariya ta amsa sannan tawuce taci gaba da aikinta. WACECE WANNAN? Take tambayar mama jummai. Mama jummai tayi dariya tareda fad'in 'yarkice Mariya gatanan tayi girma baki santaba. H-Tani tace masha Allah,tayi girma sosai,tagama makaranta ne? Mama jummai tace aa tanadayyi dasaura. H-Tani tace gata kyakykyawa barakallah,niko jummai danaga yarinyar nan ,harkinsa nayi sha'awar kibani ita,intafi da ita tanemo maki abinduniya. Mama jummai tace anya!gaskiya bazan baki itaba,don itanake gani inajin dad'i,sauran 'yan uwannata duk ba zuciya. H-Tani tace aiyara yanzun duk sai ahankali,saidai fatan Allah yashiryamana,to aike dama jummai irin wad'annan masu zuciyar su akesawa sunemi kudi. Mama jummai tace to aikuma karatunfa? H-Tani tace yome akedakaratu jummai?duk bagamasu takardunnan munaganiba,kaidai katashi kanemi nakanka kawai,aikine zannema mata kukanku kunhuta dawannan wahalar, kinsan Allah jummai don dubu ashirin dubu talatin saidai kiga anayomaki aike dasu. Mama jummai tace Allah Hajiya Tani!!? H-Tani tace to kedai zauna ainad'aka bayyi kallon nawajeba,dazaki shiryata kibani ita intafi da ita Kano,saikinyi mamakin yadda zata zama da abinda zata samo. Mama jummai takara nanatawa da karfi, DUBU TALATIN fanajikince! H-tani tace kwarai kuwa,barima kiga infara baki wani Abu,nandanan tazage Jakarta taciro rafar kudi 'yan hamsin-hamsin harna dubu goma,tamikama mama jummai. Jiki narawa mama jummai takarba kudin taredafadin,Al'amarin nan nakifa Hajiya tani dagaske ne. H-tani tace aah!yodafa,kedai kinji shawarar danabaki,don haka kishiryata inzan koma muwuce. Mama jummai tace to yaushe zaki koma? H-tani tace ieetoh!!nanda kwana biyu. Mama jummai tace saidai matsala ta daya,wannan saurayinnata Hashimu ,idan yaji bazai bariba. H-tani tace yo waye kuma hashimu? Mama jummai tace saurayintane Wanda zata aura aiko anyi Alkawarin aure dashi tun mahaifinta nada rai ,bakiga irin dawainiyar dayakeyimanaba,lallai natabbatar bazai so tafiyar nan tataba. H-tani tace yoshima idan yaga tacanza tayi kyau zaifi kara sonta,kuma 'yarki takara farashi. Mama jummai tace hakane kumafa,Allah yataimaka nasan yadda zanyi dashi. H-tani tace ahtoh!!kidayyi shawara. Haka suka tsaida maganar cewa Mariya zatabi Hajiya Tani Kano acewarta zata nemammata aiki Wanda zata rika samun kudi sosai. Mama jummai taja kunnan Mariya akan kadatasaki tasanar da Hashimu abinda kefaruwa,harsai bayan tatafi,itatasan yadda zata gayamasa. Washe gari ana igobe zasu wuce Kano,Hashim yazo wurinta,duk da mama taja kunnanta akan kadatasanar dashi saida tafada mai, amma saice masa tayi unguwa kawai zata tayi sati biyu. Hashimu yace har sati biyu Mariya?to Allah yadawo dake lafiya,kinsan Alkawarin DA nakeso kiyimani? Tagirgiza kai. Yace don Allah Mariya duk inda kikaje kitsare kanki,kitsare mutum cinki,karki yadda dasamarin bariki,nabaki amanar kanki harkije kidawo,nikuma inanan zantayimaki Addu'a kice kinyimin wannan Alkawarin. Tace Hashim nayi maka Alkawari da duk rintsi duk wuya zankare kaina da mutumcina,bazan ta'ba bari wani mummunan Abu yasameniba,duk inda kuma natafi ,kana tareda ni acikin zuciyata,in sha Allahu yadda natafi haka zandawo maka,alkawarine nayi maka,hashimu INA SON KA,inasonka sosai,daidainan tasa tafukan hannayenta tarufe fuskarta...................... ********* ********* ********** ******* Firgigitt!!!hashimu yafarka daga nannauyan tunanin daya tafi,nandanan hawaye suka 'kara kwararowa daga idanunsa,cikin sauri yatashi zaune,yaga dakin babu kowa. Ashe abokannasa suntafi,atunaninsu barci yasamu,lokaci guda yakara kallon agogo,karfe goma sha d'aya da mintuna ashirin da shidda,ya mike dasauri yayi waje ko takalmi babu akafarsa. Kaitsaye hanyar gidan su Mariya yanufa,yana tafiya kamar anzaremai lakka. Mutane ne tunjum awurin,hakan shi yakara tabbatar mai dacewa lallai yau yarasa Mariya ,kanshi yaci gaba da juyawa,yana ganin sama nakomawa kasa,yana kallon kowa badaidaiba,hatta hayaniyar da akeyi awurin sama-sama yakejinta. Daidai lokacin dayaji ance FATIHA!! Alamar andaura auren Mariya dawani bashi ba,saidai faduwa yayi awurin sumamme,akayo kansa,akadaukesa,wadanda basusan komai gamedashiba,saisuka dauka lalurace kawai,wadanda kuma suka Sani kowa nafadin albarkacin bakinsa. Koda akagayama Mama jummai saicewa tayi,yama gaji yatashi,wahalalle kawai!! Bikifa yayi biki,anyi shagali sosai,maroka-makad'a-mawaka sunzo sun baje kolinsu anan wurin, amarya kuwa tayi kyau harta gaji. Misalin karfe biyar nayamma akakai amarya d'akinta,biki yasoma watsewa. Bayan sallar isha'i,suna zaune cikin daki bisa gefen gado,bayan sungama sallolinsu. Yace amarya yaudai burina yacika,duk wani Abu dakikeyimin ada yanzun yakare,yanzun sai inyi yadda nakeso. Tace to kagodema Allah daya ganar dakai haka tunda wuri,domin tabbas zina mummunar hanyace,kuma kazanta. Yace hakane,shiyasa nakejina cikin farin cikin daban ta'ba jina acikinsaba,abinda nadade INA nema yau gashi Allah ya mallakamin shi har d'kina. Tayi dariya. Azuciyarsa kuma yace yausaina kawar da sha'awarki danadade tana wahalar dani azuciyata,afili sayyace kici abincin mana,kici kikoshi sosai donnasan lallai kina jin yunwa,Sam!nasan hidima batabarki kin sake kinci abinci ba,Niko bazan yadda amaryata takwana dayunwaba. Ya tsiyayi mafara mai kauri kofi yamikamata,yanata lallashinta sosai,saida takoshi sannan yakauda kayan. Washe garima agida yawuni,suna d'ibar soyayyar su,itakam ganinsa take tamkar wani saurayine tasamu,don yadda yake kulata yake tarairayarta,ga uwa uba kuma ya iya soyayya. Tana kwance kandoguwar kujerar falon ta,shikuma yanatsugunne yana matsamata kafa,suna fira jefi-jefi. Yace Mariya lallai inakara godema Allah daya mallakaminke amatsayin Matar aurena,jinakeyi kamar intazama dake kada intafi Kano inbarki. Saita wani yatsune fuskarta,cikin yanga tace:ashefa bani kadai bace matarka, hakane katunamanifa,yaushe zaka tafi kanodin? Yace sati daya zanyi anan inkoma can. Tace Allah yakaimu, Yace kamar kar intafiko? Tace Nina isa!kace lallai da madam tayi hukunci,to inkaje yaushe zakadawo? Yace yadda kikeso aihakan za'ayi. Tace kokuma yadda hajiyar ka taceba. Yace kinganki,hajiyar nan tafita bakin ki. Tace Abokiyar zaman tawa? Yace a'a wadda kukahada muji daya da itadai,amma aibawuri daya kuke da itaba. Tace to amma aikasan..................... Yace don Allah dakata akauda zancen hajiyar nan,banaso kina tadoshi. Saitaji farin ciki yamamaye zuciyarta,atunaninta bayaso anatada mashi zancen hajiyarne saboda yasameta,yafara sharewa da itane,azuciyarta tace naci gari!lallai nasan yanzun tamkar nikadaice azuciyar Alhaji, saita karajin takara wani isa. Shiko abangarensa bahaka bane,duk sanda yatuna da hajiyarsane saiyaji kirjinsa nadukan uku-uku,saboda baysamma tayadda zaisanar da ita cewa ya kara aureba,yasan kuwa idantasani ba irin tashin hankalin DA bazai ganiba,shiyasa yaki sanar da ita,harsai duk abinda zaifaru yafaru, yanaso idanyakoma Kano yasan yadda zaiyi yasanar da ita Karin aurennasa,cikin hikima,sannan yayi hakuri,yadauki kowane irin hukunci zatazo masa dashi,don idan yasanar da ita kafin auren ,zata iya sanadin da za'afasa wannan auren,shiyasa yabarta harsai amarya tashigo d'aki tazama Iyakaci tagama kurarin fadanta ta hakura. Yana jin faduwar gabansane aduk lokacin daya tunata ko aka ambaceta,don baisan irin tashin hankalin dazasu fuskantaba,idan taji yayi aure,kuma yarasa wadda zai aura sai MARIYA!!! Kaih! Gaskiya akwai matsala!!! Domin idan harta Sani............................ Mariya ce takatsemai tunani dacewa,lafiya naga kayi shiru?kamatsamin kafafuna ciwo sukeyimani,zurga-zurgar bikinnan nayi wahala sosai. Tana wani kara shagwabemai,don ganitake bashida kamarta,shiyasa saiwani rawar jiki yake akanta,tace azuciyarta Ashe haka masu auren dattijan maza suke morema aure?suyita shagwabarsu suna watayawarsu shikuma yana tarairayarka,domin duk abinda zakayi yarinyace awurinsu,komai kayi aikin kuruciyane,yayta wani lallashin mace kamar yasamu baby ,idan kuwa har haka zanci gabadarayuwa da Alhaji mansur lallai bawadda tafini Saar aure amata. Tad'ago fararan idanunta takara kallonsa taredafadin nagode,tajanye kafafunta tasaukesu kasa,shikuma yadawo kusa da ita yazauna,tareda yin saurin kama hannayenta dasu kaji kunshin amarci,yadan murzasu taredayimata kiss ahannayen,yace Mariya zanshiga wanka,yayi saurin mikewa saboda yaga lokacin Sallah yakusa,yafada kewaye yasanyama jikinsa ruwa. Rayuwa mai dad'i da farin ciki suka kasance acikinta tsawon kwana biyar,gaba d'aya alokacin hankalinsa ya kad'a zuwa Kano,don yakosa yaje ayita takare,don kada watarana tasani dakanta,yakuma rasa amsar dazai bata awannan lokacin, don haka duk ys'kagara kwana bakwannan sucika yatafi. Itakuwa Mariya tana zaune a dressing mirro tana tsala kwalliyar da ita kanta tasan tayimata kyau sosai, saiwani kara gyarawa take ,don atunanta hankalinsa NA kanta. Shiko yana can yana tunanin tayadda zaifara sanar da matarsa wannan lamari,shin da wadanne kalamaima zayyi amfani ne yadda zata fahimceshi? Daidai lokacin Mariya tamatso daf!dashi,tana fadin yakuma kaga kwalliyar yau? Cikin karfin hali yace gaskiya kinyi kyau,irin wannan kwalliya haka,aibazanso inrikayin nisa dakeba,Allah yayi halitta kyakykyawa anan amaryata,wannan kwalliya yadda kikayi kyau haka kuwa,aidole inbiya. Cikin murna tayi tsalle tareda fad'awa cikin jikinsa,shikuma yadageta sama yana juyawa da ita. Daidai lokacin da kunnansa yajiyo wata murya daga waje tana cewa: Tabbass!!!Hajiya nanne!donninan dakike ganina ganauce bajiyauba!lallai mujinki anan gidan yakawo Amaryar tasa! Baisan alokacin dayayi saurin sauke Mariya kasaba,sobodajin muguwar faduwar gaba dayayi,cikin sanyi jiki yanufi kofar falon donya kara tabbatar ma kansa shin abinda kunnuwansa suka jiyo masa gaskiya ne? Daidai kofar falon yala'be,saiyaji Matar nakara shaidamata,tana cewa: Kaih!!lallai namiji maciyin amanane!wata kan yazo nan yakama gida yatareda yarinya har tsawon kwana biyar,kekuma kina can yabaroki!yananan yana holewarsa da yarinya!!!kaih!!!Namiji!Namiji!! Namiji beba!!!yatarwatsa maki farinkici wallahi!!!! Alokacin kuwa H-Amina tagama cika,zuciyarnan tata kamar tafashe,cikin zafinnama kuma iya karfinta tahau dukan 'kyauran dakin,don tama kasa magana,sai huci kawai take,burinta kawai taga Alhaji mansur din,tanadukan kofar iya karfinta, irin dukannan da akecema koka bude ko inkarya kofar. Tunda yaji haka cikin sauri yanufi wurin Mariya,jikinsa har 'bari yake,gaba daya yagama jikewa da zufa,cikin rawar murya yakecewa. Mariya yimaza-maza kishiga bayi kirufe,karki kuskura kibude!wallahi Hajiya Aminace gatanan tashigo gidannan. Mariya tabude baki zatayi magana. Yace bana bukatar maganar ki yanzun,kiyi abinda nace kawai!!kishiga kirufe!kozata kwana acikin gidannan toki kwana akewaye,don idan tahadu dake,duk abinda yasameki kekijawo! Tuni zufa tagama jikesa,cikin hanzari yake kara turata cikin bayin,tashiga yajawo yatufe. Sannan yayi namijin 'ko'kari yace bari infita,ni inyaso tayagani. A hankali yabude kofar,idonsa cikinnata,yakara shiga wani mummunan RUDANI dalilin wani irin kallo dayaga tayimasa. Cikin tsawa tace INA yarinyar!!! Ahankali yafito yajawo 'kyauran shima yasa mukulli cikin hikima yarufe,yamaida d'an mukullin cikin aljihunsa. Yace Hajiya ce? Taharareshi,tace lallai Alhaji mansur yayi kyau!!!wata kan ga 'yar iska kabaro Kano!!kazo nan kayi aure!! Yace Hajiya kifahimceni wallahi.............. Takatseshi dacewa maganar infahimceka duk batasoba!don yanzun ni babu abinda zaka gayamin infahimceka!!donkariga kagama tarwatsani!!nace nanne Abujar? Yace hajiya ki.................... Tace tambayar kafa nake nanne Abujar?? Oho!! Wata kan kacemin zaka aiki Abuja!! Shine kazo nan ka kara aure bada saninaba!!to daga kai har ita yau kunshiga uku kun lalace!!don duk Wanda yatsayamaku saina dauki matakin danayi niyyar indauka anan!!! Kabude Mani 'kofa inshiga injawo yarinyar nan inkarairayata!!don yau koni ko kai ko ita sai anrasa d'aya!!! Yace dakata Amina kiyi hakuri. Tace kacucenine zakace inyi hakuri!!ni bamma sanshiba!!tad'aga murya da karfi tace,ka bud'emani 'kofar koko sai haukana yatashi!!!! Tajefar da jakar hannunta gefe guda, tacire gyalanta tayi d'amara dashi,tad'ora hannunta aka tafasa kururuwa,yayi saurin rufemata baki da hannunsa. Yace lafiyarki Amina? Tace banida ita!indai akan zancen kishiyane kakirani da komai, Donni yanzun badamuwata bane intara maka mutane!kowa yasan irin cin amanar dakayi Mani!!donba tsoro nakejiba!bakuma kunya nakejiba!!don mubar abin magana niduk dayane awurina!! Kafin ka Ankara mutane sunfara shigowa gidan donjin ko lafiya, don kururuwar dasu kaji tayi. Itakuma alokacin ta'kara farashin fad'anta,tana hargowa,don kowa yaji irin cin amanar da mujinta yayimata. Inbanda cutama irintaka!harni zaka yaudara!!dacewa zaka tafi aiki!to Allah yatona asirinka!!kamarni zakaci amana!kayi kuskure babba daka rasa yarinyar da zaka aura sai Mariya!!kabudemin kofar nan inshiga injawota!inyimata rugu-rugu anan wurin!!don wallahi hankalina bazai ta'ba kwantawaba inba gawarta nagani ba!!Nina gayamaka kuma kasan zan iya!! SAINA KASHE MARIYA!!!!! Duk gaba d'aya hankalin kowa yayo kanta,ana lafiya-lafiya. Tace babu lafiya!yau sainayi maganin maciyan amanata!tarike kofar tana girgizawa iya karfinta. Alhaji mansur yajanyeta yana fad'in kiyi hakuri kikoma Kano, inanan zuwa nima yanzun zanbiyoki,ni banason tashin hankali. Tace ba kasan tashin hankali kuma ka nemosa?aikaida kwanciyar hankali aduniyarnan harsai yazamana babu d'aya daga cikinmu!amma muddin inada rai!kanada rai!!Mariya tanada rai toka dingi gamuwa da tashin hankali kenan har iyakar rayuwarka!!don Allah nikarabu dani inyi maganin la'ananniyar yarinyar nan!!! Alhaji mansur yana riketa tana fizgewa,tuni kallabinta yarabu da jikinta,saboda tsabar masifa. Wani bawan Allah yana wurin yace:haba Hajiya da girman ki,baikamata kina irin wannan abinba,saiki zuddama kanki mutumci,kisa kuma yarinyar nan tarainaki,tundadai aurene anriga andaura,hakuri yakamata kiyi,duk DA shima bai kyautaba,daya kara aure baisanar dakeba,lallai yayimaki laifi,amma tunda hakan tafaru,kiyayyafama zuciyarki ruwan hakuri,saikiga abin yawuce kamar ba'ayiba,kuma sainaga yarinyar nan dakike fad'a akanta 'yar cikinkice,don ahaifedai kin haifeta. Alhaji mansur yace ah!toh!tareda langa'bar da kansa gefe guda. Mutumin yacigaba dacewa,amma kizo kina tada hankalinki,kinatada jijiyoyin wuyanki akan wannan 'yarficiciyar yarinyar,ki zauna kina mugun kishi da ita,wadda bata wuce 'yar cikinkiba,duka yau kwana biyar da auren ko amarcimma basu gama Ciba kinzo kintada masu hankali. Tace dakata da Allah hakanan!!nikarka 'kara 'bata Mani rai!shibaisan yarinyar bace ya aureta!sainice zanji kunyar yin kishi da ita!! Har kake gayamin kwana biyar da aurensu!aiba saika gayamin cewar mujina yakwana biyar da wataba!! Kuma tunda yayimin wannan cin amanar saina dauki mummunan hukunci akansa!!sannan tajuyo ga Alhaji mansur. Tace nizaka daudara!ni zaka ha inta!!nizakaci amana!!kayi babban kuskure,yau kuma INA cikin gidannan ba inda zani saidai afidda gawata!! Wani can gefe yace:bawanda zai fidda gawarki da kafarki zaki fita! Tawaigo tayo kansa kamar mahaukaciya,tana fadin inko aka kasa fidda gawata to za'afidda gawar Amaryar Alhaji!!don bazan yadda tana Raye INA rayeba!inayimata kallon wadda tata'ba kwana da mujina!! Itace saboda tsabar masifa hartayi hanyar kofar gida tana zazzaga bala'i,shiko Wanda yafad'i wannan maganar tuni yayi waje baima bari ta iskoshiba,gaba d'aya idonta yarufe tsiya kawai takeyi. Koda tadawo cikin gida babu Alhaji mansur, Ashe yayi wuf!yabar gidan shima dayaga hankalinta yayi wani wuri,yasan dai duk abinta bata iya 'balla 'kofar nan tashiga. Tadawo tana huci tana kumfar baki,tana zage-zage,dadai taga babu abokinyin saita lafa. Ahankali mutane kowa yafara kama gabansa,domin da gidan harya cika da mutane. Wadda takawota gidan tadafa kafad'arta tace kibarshi kawai kishirya kikoma Kano,Nina tabbatar yau d'innan basai gobeba zai biyoki,idan yaje saiku can care, kiji kuma irin fad'in bakin dazayyinaki. Wani dattijo dayake tsaye acikin gidan,Wanda shikadai yarage baifitaba,yace gaskiyarki kuwa takoma,tunfarkoma da batazoba tajirashi idan yaje saiya lallasheta,yayi mata dadin baki,hakanma dayafiye mata,dabata wahalar da kantaba kuma dayafi lada. H-Amina takalleshi tagadai dattijone amma data gayamasa magana. Kawar tata tace to shikenan baba mungode,dai dai lokacin datake daukoma H-Amina Jakarta da takalminta,tana fadin muje kawai!Allah yakiyaye!yadai gama dake kawai!!takamo hannunta sukayo waje,tasaka mata jakar acikin mota, tana cewa ki isa Kano din Nina tabbatar yau sayya biyoki,aikin tadamashi hankali. H-Amina tace rabu dashi dani yake magana,sannan tace kishigo inmaidake gidanku sannan inwuce. Tace to,tashiga tazauna kusa da ita,sannan H-Amina taja motar suka tafi,donta sauke ta gidanta itakuma tawuce Kano. (Karka manta mai karatu kana tareda Littafin RUDANI 1 Wanda fateema Dahiru funtuwa Binta ta wallafa,dafatan yana nishad'antar dame karatu, 09162526909) Bayan sun wuce wasu samari keta tattauna maganar,anan kofar gida,d'ayan yace Auwal gaskiya duk Wanda yasan me akecema adalci yasan ba'ayima matarnan adalciba,haba maza muji tsoron Allah mana,don Allah yabamu damar mu auri mace fiye da d'aya aikuma sai ayi masu adalci,tayaya za'ace zaka kara aure amma baka sanar data gidaba?saidai taji agari,wai harma katare da mata kwana biyar,dolene ranta ya'baci. 'Dayan yace kamal aikuma tunda abin yafaru dasaitayi hakuri,tundadai babu abinda zata iyayi,yanzun bagashiba tagama kurarin tatafi,kuma aurennan,to ribar metasamu aciki?inbanda 'batama kanta lokacima datayi. Kamal yace ammadai duk dahaka wallahi maza saimun gyara,idan zaka 'kara aure,kasanar da matarka,tonifa inaso inkara aure,koda yafara fushin tagaji tabari kafin Amaryar tashigo tayi tahakura,kaga sai abin yazo mata da sauki,amma bawai kwatsamm!!taji kawai harma antare ,kaima kasan akwai matsala. Itama yarinyar dazaka aura din saika sanar da ita,tonifa inada mata da 'ya'ya kaza to kunga duk sai adaidaita kafin lokacin auren,Allah dai yakiyaye yashigemana gaba. Saida suka fara tafiya sai H-Amina tace wallahi Halima mujinnannawa yabani mamaki! Kamar ni zaici amanata!amma ba komai!! Halima tace Namiji!Namiji!! Namiji macucine!!mayaudari!!kaih!!maza suna sheke ayarsu!bakuma abinda kemasu ciwo!humff!maza mutananmu. H-Amina tace kirabu dashi sayya gane yata'boni,dani yake zancen!!zaizo yasameni har d'akina. Halima tace kinunamasa kuskurensa!!!! Wannan aicin amanane ta gaske!!kaih! aimu mata munada ha'kuri! Kiduba kigani H-Amina inkece komagana yaga kinayi dawani inhankalinsa yay dubu saiya 'baci!amma shi har ya iya auren wata yaje yakwana biyar da ita baisanar dakeba!!wannan cin amana aiyayi yawa!!! Humf!!bari tunamin Halima, nan jinake kamar zuciyata tayi bunduga!koyazo wurinnawama mezaicemin?bacin aikin gama dai yagama. Halima tace yo yalallashekimana. H-Amina tace keyanzun kina ganin har akwai wata kalmar dazayyi amfani da ita wurin shawo kaina?ai duk duniyarnan bata! Halima tace kisama ranki hakuri karkije wani ciwon yazo yahaye maki,kikwantar da hankalinki Hajiya. Haba Halima donbake akayima abinda akayimanibane shiyasa kike fad'in haka. Halima tace gaskiya nefa,kuma kinsan wani Abu Hajiya,yau inda ace matane keda ikon auren maza fiye da d'aya, nina tabbatar sai anyi ya'ki!kenifa idan naji ance anyima mace kishiya tausayi take bani,sai ince araina waiya takeji lokacin dataga anata biki anshigo dawata amatsayin Matar mujinta!!kaih!!lallai in ba'a tausayamanaba,nifa shiyasa tunda naji labarin aurennan ,naji ance a asirce zayyi aurennan,matarsa ta gida bata saniba nakasa sukuni,naga innice mujina zayyimin haka yazanyi?kawai saina shiga bincike,nagane mutumin kanone,nashirya naje da tambaya harnagano Inda kike,tunda nidai kinga bansankiba,inba dalilin hakaba,shiyasa nayi maki wannan 'ko'karin nazo nasanar dake,don kisan halin dakike ciki,to yanzun dai kinga dill!!. H-Amina tace ainagode,Allah yasaka maki da Alkairi,naji dad'in wannan kokarin dakikayimani,koba komai nasan matsayina awurin mujina. Halima tace karki yadda kisa damuwa azuciyarki,kizo hawanjini Yakama ki,don ba'kin cikin najimiji ba abinda bayasawa,DA kinga mace da ciwon zuciya,ko wani hawan jini,ba'kin cikin d'a Namiji ne kawai,aina tausaya maki sosai, daidai nan tayi parking din motar ta 'kofar gidan su Halimar,tareda fadin aibaki tausayamin bama tukunna tunda bakisan WACENIBA KUMA WAYE ALHAJI MANSUR SANNAN WACECE MARIYA??????? Halima takara gyara acikin motar datake shirin fita,tamaida hankalinta akan H-Amina, don taji amsar wadannan tambayoyi daga bakinta. ***** ******* ****** ******* ******** SUNANA AMINA YAKUBU,ni haifaffiyar garin kanoce,mahaifina shahararren d'an kasuwane,yanada arziki sosai,don intakaice maki labarin nikadaice 'ya awurinsa,tareda mahaifiyata Hajiya Asma'u,wanda muke kiranta da mommy,duk wani gata dajin dadin duniya nasameshi,iyayena basa hanani duk wani abinda nakeso, koda kuwa su abin bazaiyi masu dad'iba,saboda farin cikina kawai sukeso. Inason sana'ar mahaifina ta kasuwanci,don haka nima danazama budurwa sainayi nufin in zama 'yar kasuwa kamar mahaifina,dukda mommy tana gayamin aure shine kawai darajar 'ya mace,amma Abbana yayadda da abinda nakeso,don haka idanna taso makaranta sai inbishi intayashi aiki. Ahankali haryasakar min dayawa daga cikin ragamar kasuwancin nasa,koda baya kasar ni INA kula da abubuwa sosai,tare dasauran ma aikata. Lokaci kad'an nazama BABBAR yarinya,maiji da naira!gani da hannun kyauta,shiyasa nakeda masoya sosai, inahawa mota irin wadda nakeso,haryazamana tamkar nice keda kammafoninsa,don yanzun hatta wata cinikayya dazata kaishi 'kasashen waje niyake turawa. WATARANA dasafe nafito zani aiki,INA cikin tafiya a motata,sainaga wani mutumi yatsaida wani mai adaidaita sahu yanayimai fad'a,tareda an she mukullun 'kur'kurar,shikuma saurayin yanata bashi hakuri. Tokasancewar ni macece mai taimako da tausayi,kawai saina tsaya don inji musabbabin rigimar,nayi parking din motata dai dai indasuke,nace: Sannunku lafiya daiko? Mutumin yace Hajiya yaronnanne naga bazamu shirya dashi ba,yau sati uku kenan bai kawomani balance ba,shine yazama dole in an she keketa,tunda naga ba sana'ar yakeson yiba! Nace yokai bawan Allah meyasa ba kakaimasa kudinsa?in anahaka aibaza'aci gababa,todayake sauri nakeyi,kawai sainacema mai keke napep din nawane kudin ka? Yace sati ukune,naira dubu A shirin da d'aya. Naciro kudinnabashi,sannan nakalli saurayin nace kaikuma don Allah arika kiyayewa,naja motata natafi. Bayan wucewar wannan Abu kamar da sati uku,wata rana nataso daga aiki,abin tsautsayi wani mai mashin yabugarmin amotata,yayi Mani 'barna,dalilin haka sainabiya da ita wurin gyara,gashi maraice yafarayi,don haka nanzanbarta insamu abin hawa inkoma gida. Inanan tsaye saiga wannan mai keke napap din Wanda nabiyama bashi kwanaki,yatsaya yagaisheni,nalura dashi sosai ,kawai saina tsaida shi nahau,nafadamasa inda zai sauke ni,har ina tambayarsa yanzun dai kana biyan kud'in bamatsalako? Yace e amma saidai injin yatsufa dayawa. Nace tokabar sana'ar mana,kayi karatun bokone? Yace e nayi. Nace to gobe kazo kasameni anan gida,nanyasaukeni na idasa shiga cikin gida,nabarsa yanata zabgamin godiya. Washegari yazo,cikin sa'a kuwa NA bashi aiki a d'aya daga cikin ma'aikatun mahaifina. KINJI YADDA NA HA'DU DA MANSUR. Halima tace Ta'bd'ijan!!ya akayi kika aure shi?? H-Amina taci gaba dacewa,bayan yayi kamar wata shidda yana aiki dani,saiya goge kyawunshi yafito, nice nace inasonsa dakaina,duk danaso insamu matsala da rashin yadda daga wurin iyayena,amma daga baya kuma nice nayi nasara,sakamakon iyayena basa musantamin abinda nakeso,donhaka dasukaga nadage saisuka hakura suka barni da za'bina. Kyawun halayyarsa da iya mu'amala da mutane shiyaja hankalina agaresa,bansamu wata matsala daga gareshiba alokacin dana kaimai zancen soyayyata,lokaci kad'an muka fahimci juna. Wata rana,inagaban motata INA kokarin shiga don tafiya gida,mansur yanufoni dasauri,cikin fara'a yana fad'in. Sarauniyar mata!d'awisu sha ado!!farar mace alkyabbar mata!! Ranki shidad'e harkin fito? Cikin fara'ata nace nafito,tareda bude motata nacemai shigo muyi magana,yabude shima yashigo. Sannan yace Amaryata nanda sati uku!mace d'aya tamkar da Hudu,kin tare gaba kin tare baya!kinmamaye dukkan ilahirin zuciyata!kinyimata kawanya da soyayyar ki,kinrufe ko ina daidai da kafar allura bakibariba,ballantana wata tasamu gurbin zama acikinta,ked'aya tilo uwar gida kuma amarya agidan Alhaji mansur manager! Babu sauran wuri dagake anrufe kofa,babu sauran d'aki agidan Alhaji mansur barewata tayi tunanin shigowa,sannan yakalleni sosai yace Amina yaya dai? Nayi murmushi cike dajin fad'in wad'annan kalamai nasa,nace Alhaji mansur idandasabo nasaba da irin wannan kod'awar taka,amma kodayaushe kake karantominsu sai injisu tamkar sabbi,in kasance cikin jindad'i da fara'a,sai intsinci kaina inamayyin murmushi idankanayimin irin wadannan kalaman,kuma koda acikin 'bacin rai nake dazarar kazo shikenan kawankesa. Nagodema Allah dayayi had'uwata dakai,ya mallakamin kai amatsayin mujina,koba komai nasan zankasance acikin farin ciki na har abada,samun jajaurtaccen namiji mai sauya tunanin d'iya mace alokaci guda wannan BABBAR nasarace awurin kowace mace. Sannan babban cikar burina gashi zangama rayuwata nikadai awurin namiji kamarkai,wannan wani abin alfaharine awurina,yadda natashi agidammu nikadai nasamu gata,haka zan rayu awurinka niadai batare da gatan yagoce maniba. Yace tayaya za'ayi mace kamarke ahad'a soyayyar ta dawata?idan namiji ya aikata hakan tamkar yayima kansa gi'bine,kinga ne abinda nakenufi? Idan mutum yahad'aki dawata duk ranar dayayenke wasu kwanaki donyakaima abokiyar zaman ki,tamkar yayankema kansa wani jindad'i,yatauye kansa sosai awannan rana. Harcikin kaina naji maganar tayimin yawo,yawani kara tsunami,inajinkaina lallai ni watace tadaban. Nace inasonka mansur!! Yace nima inasonki Amina. Fateema Dahiru funtuwa 09162526909 Mukagama firarmu sannan yafito motar yashiga tashi yatafi. Munyi aure da Alhaji mansur irin auren soyayyar dana saki jikina dashi akan lallai bawata saini din,kamar yadda kullun yake kara shaidamin. Shekarata talatin da biyar dashi a yanzun haka,haihuwata bakwai tare dashi,INA cikin jindad'i da kwanciyar hankali sosai ,kuma arzikimmu kodayaushe kara gaba yake,,don yanzun mansur yafita daga karkashin aAbbana,yabude nasa,don haka gashin kansa yakeci yanzun. Nimacece mai kishi!kamar yadda yakecewa,natare gaba natare baya,bana yadda kowace mace inganta da mujina,inba dawani kwakwkwaran daliliba. NA kasance INA bibiyar wayarsa akowane lokaci,duk da inajin nayadda dashi, amma saboda tsaro,kuma koda yaushe yanakara gayamin inkwantar da hankalina,indai maganar aurece aishiyariga ya auru,bawata macen dazai kara gani taburgeshi. Rannan naje shiga dakinsa,kawai sainayi kicibis!dashi yana waya da mace. Nace Alhaji menakeji haka? Cikin sauri yakauda wayar daga kunnansa,taredayin wata irin dariya,yace lafiya dai Hajiya? Nace a'a nikainake tambaya,nakejin kamar muryar mace awayarka? Yataso ahankali yakama hannayena,yace to inbanda abinki jin muryar mace awayata wani sabon abune? Nayimai wani irin kallo nace banganeba, Yace to amma atsayina name kasuwanci,mai harka da mutane kala-kala aidole kiji muryar koma wacece. Nayi saurin fizge hannuna daga nasa,nace to anzo wurin!!dama inajiran haka!nagaji!Alhaji mansur nagaji!!harka kowace irice indai zata had'aka cud'anya da mata tonayafeta!!gara abarta kwata-,kwata!Donni bazan amince dawannan ba!! Yace kintaba ganin inda kasuwanci yakasance ahaka?ace sai anware wasu junsi wadanda sukadaine za'ayi mu'amala dasu?haba Amina jimana" kikwantar da hankalinki, yanzun yawancin kasuwancimma matane,uwum!don Allah ki yadda dani mana. Nace nifa indai harka da matane zan iya cewa kasuwancinma abarshi!! Yace wannan ma datakirani awaya ba 'yar nan bace,daga Lagos take,zanyi order wasu kayane. Nace wai Alhaji mansur suwa kake nemamma kudinnanne? Yace kemana da 'ya'yanki. Nace to zan iya cewa abar Neman kudin!kadawo kazauna cikin gida kullun intasaka gaba inakallonka,Donni gara muzauna ahaka zaifiyemin kwanciyar hankali! Wannan maganar saida ta bashi dariya,yakara janyoni jikinsa,yana fadin,aiko watarana dakanki zaki koreni,inzodai intaremaki acikin gida,habawa aikemadai kinfadane. Amma gabadaya narasa gane irin wannan kishinnaki,kuma azaman damukayi dake fiye da shekara talatin ayya kamata ace kin sanyaya zuciyarki,kin tabbatar dacewa nibazanyimaki kishiyaba,domin dazanyi datuni nayi,don Allah Amina kirage wannan zafin kishin naki. Humf!nayi ajiyar numfashi,nace hakane,amma wani lokacin ne idan raina ya 'baci akan kishinka bansamma inayin wani abinba,don gaba d'aya idona rufewa yake. Yace tokibudeshi kinjiko?uwar gidan Alhaji mansur!kuma amarya!babu wata bayanke,zinariya sarauniyar mata,haka yacikani da kirari kamar yadda yasaba,harsaida yaga nayi dariya, sannan yace: Wohoho! Sarkin kishi,amma balaifinki bane,laifin soyayyatane datayimaki wawankamu,Nikuma nasan dole sai anason mutum akeyin kishinsa. Nace aigaradai daka gane hakan,saida yakwantarmin da hankali sosai. Shiyasa nakeson Alhaji mansur, domin shi mutumne Wanda ya iya lallashin mace,ya iya tarairaiya,ya iya kalamai,kuma kodayaushe jinsa yake tamkar wani saurayi,yasan kaina dayawa,Kowane irin bacin rai nashiga yasan yadda zayyi ya lallasheni,gashi da kissa kamar mace,shiyasa kullun nake karajin sonsa,nakekuma kishinsa,amma duk dahaka saida Yazagaye yaje ya auri wata !! Halima Tabbas!! Danasan dawannan labarin kafin aurennan saina lalatashi!!bayadda za'ayi inbari ayishi,nasan shiyasa ya boyemani. ( mai karatu kana karanta littafin RUDANI 1 na fateema Dahiru funtuwa Binta 09162526909) ****** ******* ******* ******* ******** Hankalina yanatashi idannatuna irin kalamai masu dad'i dayake yawan fad'amani akunnena,sai intunacewa ya auri wata tsawon kwana biyar itama yana karantamata irinsu akunnuwanta,yatonamani asiri!!! Daidai nan tari yasar'keta,tareda fitar wasu zafafan hawaye dasuka jika kuncinta. Halima tahau lallashinta tana fad'in,kiyi hakuri karkitadama kanki hankali,donshi namiji babu ruwansa!sayya tarwatsaki!!yahaddasamaki ciwon zuciya,bakuma abinda yadamesa,kaih!Namiji dai!Namiji dai mayaudarine!!wallahi yacuceki!!kwana biyar kanata sharholiyarka da Amarya bakasanar da uwar gidaba!Hajiya idan kikaga mace da wani hawan jini ko ciwon zuciya sanadinsa Namiji ne!kidauki duk matakin daya kanata akansa!inagoyon bayanki!!natabbatar kuma yau dinnan saiyabiyoki har Kano. H-Amina tace to mezayyimin? Halima tace yomezayyimaki inbanda kalaman yaudara,dama can tunfarko yaudararki yake,ayya gama dake kawai!!saidai kisaurareshi kawai. Daidainan taduba agogon motar ta,tace yamma tayi ,yakamata inwuce banason inyi dare sosai ahanya. Halima tace AF!to aibakigayamin WACECE MARIYA BA. H-Amina tace kibiyoni bashin wannan, duk ranar damukasake haduwa Zangaya maki,yanzun lokaci nakuremani. Halima tace gaskiya kin bani labarin dazai dademani azuciyata ,Allah dai yakiyaye,sannan tafito daga cikin motar. H-Amina kuma tadauki hanyar komawa Kano, daga manumfashi. BAYAN AWANNI UKU Mariya ce ketakai dakomowa acikin falon ta, hannunta rike dawaya,tana latsawa,zuwa can ta kangata akunnanta,harya yanke ba'ad'agaba,tacigaba da kewaye a falon, tana kwata tanatsaki,rannan nata abace,dagani cikin masifa take,tatsaya wuri daya tana karkada kafarta,tace wainid'in!!!humf!ba'asanniba wallahi!! Sannan takarakiran number datake nema,harta kusa yankewa sannan aka daga. Tace mamammu tund'azun inata Neman ki awaya baki dagaba. Mama jummai tace mariya bani gidan yanzun nashigo,wayar kuma nabarta tana charge, lafiya daiko? Mariya tace bata!mamammu ba lafiya! Gaba daya nakosa inganki!ingayamaki damuwa ta!don Allah mamakitafo yanzun! Mama jummai tace wani Abu yafarune mariya? Mariya tace aa nidai mama kawai saikinzo,maganar bata wayabace. Mama jummai tace incedai bayaronnan bane Hashimu? Mariya tace mama kedai kizo kawai,bawanda nakeso ingayama damuwata saike,kiyi maza-maza don Allah kizo kada inhuce! Mama jummai tace to shikenan Mariya kibani mintina talatin ,don inbiya tawani wuri tukunna,sannan inzo. Mariya tace mama dadai kinfara zuwa nandin. Aa Mariya kibari inda zanfara biyawadin yanada muhimmanci sosai ,sannan takatse kiran,tana karayin kwata,tace lallai kam!!dani ake magana!! Itakuwa mama jummai cewatayi,heee!lallai kam dama nasan ba abinda zaihana yaronnan bai dauki matakiba!amma dani yake magana,in yasan wata aibaisan wataba,wata kan yarikitamin yarinya adakin mujinta!yahanata zaman lafiya,wata'kila ture yayimata,akebata tsoro agidan,baridai inje ingani,don gara inyi maganin abin tunda wuri,shiyasa yanzunma kafin in isawurinta saina biya wurin bokana nakaimashi bayani,donyadaukar Mani mataki akan yaronnan (Hashimu) donbashakka bakowa bane shine,tadaga matashin kanta tadauko kudi,ta 'kirgi naira dubu goma tafita da ita. Batazame ko inaba saiwurin mai maganinta. Tace boka akwai matsala!yanzun yarinyar nan mariya takekirani,tace inyi maza-,maza inje gidan ta akwai gagarumar matsala!Nina tabbatar yaronnan bazai barta hakananba,shiyasa nazo kataimakamin,asamu yarinyar nan tazauna d'akinta lafiya, inba hakaba kuwa zamuga samu muga rashi. Boka yace kikwantar da hankalinki, tunda kikaxo nan komai yabiya,maganar zaman lafiyar 'yarki ad'akin mujinta an gama!! Bawanda ya isa yatadata!indai nikina tareda ni. Tace kuma boka sonake amantar da hashimu cewa yatabason yarinyarnan. Yamanta da ita kwata-kwata!don inbahakaba nima bazaibarni inzauna lafiya ba,don ranar bikintafa har somewayayi. Boka yace indon wannan ne ba matsala,yadauki 'yansaddabarun dazai bata yamika mata,itakuma ta karba tana farin ciki,tafito dasamu adaidata sahu tahau batazame ko inaba sai gidan 'yarta mariya. Tashiga tanata sallama bataji an kar'baba,tayi tsaye kofar falon tana sallama taji shiru,don haka saita shiga azatonta ko mariyar tashiga kewayene,tasamu kujera tazauna,shiru bataji motsin mutum ba. Saitadau waya takira number mariya,harta gama ringing ba'ad'agaba ,tace aah!towai lafiya?yanzunfa takirani inakuma tajene?takara hakuri kamar na mintuna goma don jiran mariyar waiko wani wuri tashiga amma shiru takeji, don cikin gidamma babu alamar mitsin kowa,saita mike tsaye tana kwala Kira, Mariya! Mariya!!mariya!! Taji shiru,kawai saita shige dakin. Kwance taganta abisa gado male-male cikin jini,gakuma wukanan ajiye agefenta. Mama jummai tafasa wata gigitacciyar kara,tareda fadin mariyaah!!!! Lailahaillallahu Muhammadurrasulullahi sallallahu alaihi wasallam!!!mariya!!!tasa hannu tajuyo da ita,sai tatafi yaraf! Almar babu rai ajikinta. Nashiga uku mariya waye yakasheki?? Tafasa kuka sosai tana Neman dauki,tayo waje aguje donta shaidama mutane,tana ataimaka mata. To dayake unguwar babu mutane sosai,gidaje ko INA arurrufe,inbanda hayaniyar da H-Amina taxo tayi dazun,tatara mutane,to yanzun kuma kowa Yakama gabansa,bakowa alayin. Donhaka tanufi kofar wani gida,tana bubbuga get din gidan . Cikin sauri mai gadin gidan yafito,takara fashewa da kuka,tanayimai nuni da gidan da mariya take tana cewa: Don Allah kataimakamin ankashemin 'yata a can gidan!! Ganin tanunamai gidan kuma tafad'i kisa,yayi saurin dafe kansa yana salati,yace yanzunnan matarnan saida ta aikata wannan danyen aikin?mumin zacima tatafi!!yanzunnan saida tatsaya takashetadin? Cikin kuka mama jummai tace wacece? Yace kishiyarta mana ,Matar mujinta,dazun tazonan taita hayaniya,tatara mutane,tana cewa saita kasheta, nandai aka lallasheta mumund'aukama tahakura tatafi,Ashe saida tadawo takasheta. Mama jummai tace kishiyartatace tazo gidannan? Yace kwarai kuwa,don akwai wad'anda sukaganta dayawa,hartana ikirarin saita kasheta,kibari inshiga insanar danasu gidannan don suji abinda hayaniyar dazun ta haifar,yawuce cikin gidan da gudu-gudu yana salati. Nandanan saigashi yafito tareda masu gidan,cikin sauri. Koda sukazo mama jummai tazame kasa tanata kuka iya karfinta. Hajiya (Matar gidan) tace kece mahaifiyar amaryarko? Sannan tayi salati,tareda fadin sukau wasu matan inazasukai rayuwarsu da irin wannan kazamin kishin? Takasheta kikaceko? Mama jummai tace wallahi takasheta!!bamu dade dagamayin waya da itaba,tacemin inzo akwai matsala! Ashe bazamu hadu da itaba! Hajiyar tace gaskiya tsakani da Allah wasu matandai suna bada Kansu,inazamukai rayuwarmunewai?mezamu samu aduniyarnanne wai? Sannan takoma ga kallon maigidanta tace Alhaji asanar da jami'an tsaro,don sushigo suga abinda yafaru. Shiko dama yananan yarasa wurin tsayuwa,duk yadaburce,yadauko wayarsa donya Samar da 'yan sanda. Hajiyar taci gaba dacewa: Nikinganninan mu ukune awurin mujimmu,amma ba'atabajin wata hayaniya tafito damu wajeba,muna zamanmu lafiya, da mujinmu,amma ita daga anyimata kishiya daya kawai,duk tazo ta hargitsamana unguwa!tatada hankalin kowa, muna zamanmu lafiya, kaih!!wannan ba'kin kishi nata Allah wadaransa!gashinan zata jama kanta muguwar nadama! Kisan kai!!kisankai saboda kishi? Kaih!wannan mata wallahi tabada mata! Zatayi danasani! Mujin datake takama dashi karshenta tarasashi har abada! Zaman gidan yari yasameta!! Kinga mujinnata da take kishi akansa saima ya auri mata Hudu inyaso,oohni!!Nafisa yaunaga tashin hankali!! FatimaDahirufuntuwa 09162526909 Kafin kace miye wannan unguwa takuma cika fiye da dazun, kowa NA fadin albarkacin bakinsa,wadanda basuga hayaniyar da H-Amina tayiba dazun sunata tambaya,wadanda ko suka Sani sunata kara bada labarin abinda H-Amina tazo tayi dazun, jama'a nata Allah wadai da irin wannan bakin kishinnata. Cikin mintuna A shirin da faruwar wannan Abu saiga motar 'yansanda,kaitsaye suka shiga ciki,don suga gawar,daga busani kuma sumikama likitoci ita suwuce da ita Asibiti. Haka akayi wannan yammaci acikin tashin hankali a wannan gari na manumfashi,musamman ayankin da abin yashafa. Jama'a nata fad'in kishiyace tazo har gida takashe kishiyarta! Ankira number Alhaji mansur yadaga wayar: Hello. Yace inajin ka. Shikuma yace Alhaji kana inane? Alhaji mansur yace inamota,don yanzumma nakusa kaiwa Kano. Tokayi maza-maza kadawo don kabar tashin hankali agidanka. Cikin kaduwa Alhaji mansur yace meyafaru? Mutumin yace uwargidanka tazo takashe Amaryar ka, gashinan yanzun unguwa tacika!har jami'an tsaroma gasunan sun halarci wurin,don haka kome kake kayi maza-maza kadawo. Alhaji mansur yaja wani mahaukacin birki,cikin kaduwa,taredasakin wayar dake hannunsa tafad'i,cikin gigita yace: Hajiya Amina takashe Mariya?? Nandanan yaji zufa tayankomai,tareda fad'in subuhanallahi!!wannan wane irin tashin hankaline? TAYAYA ZA'ACE HAJIYA-AMINA CE TAKASHETA??? Wannan kuma wane irin balaine?nida nasan yanzun H-Aminama takai Kano . TAYAYA ZA'AYIMATA WANNAN SHARRIN??? Sayya juyo da motarsa yadawo dabaya,yanufo gida,zuciyarsa cike da sake-sake,lokaci zuwa lokaci yana ambatar. Hajiya Amina! Hajiya Amina!!wannan wane irin bala'ine? Saibayan magariba sannan yaiso,koda yazo unguwar nanan cike,cikin sauri yaketa kutsakai cikin gidan da aka hana kowa shiga,inbanda lokitoci da jami'an tsaro da suke aikinsu acikin gidan. Duk da ana kokarin taresa saida yayi kokarin shiga cikin gidan, har yasamu yashiga dakin da gawar take. Wasu mutane daga waje nafadin meyasa ake kokarin hanashi shiga gidan? AISHINE MUJIN!wadanda basu sanshiba suna fadin dama shine?aiko shine!!akansa ne akayi wannan rigimar,anata nunashi anacewa aishine!aishine!!harya shiga cikin gidan. Yanashiga yatarar da gawar Mariya kwance bisa gado, lokacin da likitoci ke 'ko'karin daukar ta. Yanazuwa yafada jikinta yarungumeta yana fad'in Mariya don Allah kitashi kada kimutu!idan kuma kin mutu Mariya maza kitaimaka kutashi kisanar dasu WAYE YAKASHEKI!!! Cikin kad'uwa da kuka yake fad'in wadannan maganganun. Kitashi kifad'amasu Wanda yakasheki! Kamar daga sama yaji wani yace ba ance kishiyarta tazoba?to ai ita takasheta, Alhaji mansur yayi saurin sakin mariya tareda kallon mai maganar,yace tayaya za'ace Aminace takasheta, Alhalin nasan Amina ma tuni takai Kano, gaba daya duk ya gigice. Cikin 'yansandar wani yace kofir usman! Cikin sauri ya amsa da yes sir! Atafi anemomin H-Amina acikin awanni A shirin da Hudu akawota. Yace angama tare da Sara mai. Sannan yadafa kafad'ar Alhaji mansur, yace kakwantar da hankalinka,kafad'amana inane zamu samu H-Amina matarka? Cikin kaduwa yace bazata iya aikata kisankaiba. Dan sandan yace bamunce lallaine ita ta kashetaba,bincike zamuyi. Alhaji mansur yabasu Address din gidansa dake Kano. Sannan Spector 'yan sanda yace ma Usman kutafi tareda sergeant hasana atafo da ita. Alhaji mansur najin anfad'i haka,kawai sai yafad'i kasa sumamme ,nanfa shima aka had'a dashi anufi Asibiti, ita kuma gawar mariya akanufi da ita inda ake Adana matattu,zuwa kwana biyu kafin agama bincike. Nandanan wannan labarin yakarade garin manumfashi,don haryaje kunnan kawar Hajiya Amina, (wato halima)lokacin da halima taji wannan labarin hankalinta yayi mummunan tashi,,don haka cikin sauri ta dauki waya takira Hajiya Amina. Alokacin isarta gida kenan,rannan nata 'bace ,tanata fad'anta itakadai,da 'yanzage-zagenta akan muguwar cin amanar da maigidanta yayimata,sannan harma yake sanar da ita cewa yana hanya a yanzun,tomema zaizo ya gayamin?banda yariga ya aikata abinda yayi niyya,amma gara yazo ayita takare,don lallai yau sayya fuskanci hukuncina! Yazodin dani yake magana!! Daidainan wayar dake cikin jakarta tahau ringing, atunaninta Alhajintane,sai taki d'agawa. Ind'aga to ince mashime?mayaudari kawai!aizakazo kasameni har gida! Har wayar tayanke batama dauko tadubaba. Itakuwa halima nacan takasa zaune takasa tsaye,tanaso H-Amina tadauki kiran,dontasanar da ita abinda kefaruwa. Takirata yakai sau biyar har tayanke ba'ad'agaba,sai kawai tayanke shawarar tatura mata Text message, tarubuta tatura mata. Itakuma can sai cewa tayi kaih!wannan fitina taka tayi yawa,watakan yaga bazan d'aga kiranba,shine yaturo sako,baridai induba,aidai baisannaduba ko bandubaba,iyakaci koyazo yatambayeni ince nidai banganiba,sannan tadauki wayar taduba,an rubuta kamar haka: H-Amina munfa 'ballo ruwa! Muna cikin tashin hankali! Yanzun aka shaidamin cewar anje har gida anyima kishiyarki kisan gilla Kinga kuwa dole ayi zargin mune........ Batama idasa karantawa ba tayanke cikin sauri,takira number Halimar, bugu d'aya tad'auka,tace: Halima bangane abinda kikenufiba! Halima tace gaskiya nake gayamaki! Don yanzunma 'yansanda suntafo ne Manki,kingakau akwai matsala. H-Amina tayarfar da wata zufa data Yanko mata,tace to yanzun yazamuyi Halima tace kigudu kinemi wani wuri Ki'buya,in an kwana biyu ki haure Kibar kasar,inko bahakaba lallai a Kwai matsala. H-Amina tace ba inda zani,don duk in da naje dole zandawo,kuma guduwar me zanyi?TUNDA BANINA KASHETA BA,idannagudu aisai ayi zargin lallai Nina kasheta din,tunda kuma nibani nakashetaba!ba inda zani suzodin. Halima tace to nidai guduwa zanyi don gaskiya natsorata sosai. H-Amina tace karki gudu halima don Zaki jamana,za'ace mune muka aika ta,badai iyakaci bincike bane?koba Da'de kobajima gaskiya zatayi halin ta,don haka karki gudu,sannan ta Yanke kiran. Awannan Daren H-Amina agigice takwana,atsorace dataji motsi saitaji kamar 'yan sandanne zasushigi,haka takwana zarya acikin d'akinta ,tana kullawa tana kwancewa,batada mafuta. Acikin Daren tasanar da iyayenta abinda kefaruwa,dazuwan datayi manumfashi tayi rashin mutumci,sannan cikin kuka tace: Abba wallahi banina kasheta ba" Inda nasan kwanan yarinyarnan sunku Sa karewa dabamma wahalar dakaina najeba!ammanina tabbatar yanzun ba Wanda zai iya fitar dani daga wannan Zargin sai Allah, kuma gashi nataka Shari'arsa,naje har gida naci mata mu tunci,daga ita har mujinnawa,ta'kara fashewa da kuka,tace Allah kaga ha lin dana shiga,Allah kafitar dani,ba Wanda zai iyayimin haka saikai Allah Allah nasan na aikata laifi,kuma nakar 'bi laifina,Allah kayafe Mani,Allah ka nunamani ban isaba,dakayi Mani wan nan hukuncin cikin gaugawa,kuka yaka ra kwace mata tareda fad'in Allah kafi tar dani!! Mahaifin ta Alhaji yakubu yayi salati, yace wannan wace irin jarrabawabace?dukdakema kinada laifi,babu abinda bamu fadamaki abaya akankirage wannan zafin kishin na ki, toyau ga abinda yajawo maki. Awannan dare har gidan iyayenta ba'asamu runtsawaba,don kuwa ita mahaifiyar tama tafowa tayi gidan 'yartata,nan suka zauna tare,duk yaran basusan abinda kefaruwa ba. Sai Al amenn babban dan H-Amina Wanda ayanxun yakeda shekara TALATIN da biyu, farine dogo dashi,kamanninsa daya da mahaifin sa,yarone mai hankali tuntasowarsa,yanada natsuwa sosai. Inda yakammala degree dinsa,yafara aiki a Asibitin malam Aminu Kano,shiyarone mai hazaka sosai ga nutsuwa. Cikin sallama yashigo falon, tunda yaga yanayin dasuke ciki,yasha jinin jikinsa,ya'kara so ahankali taredafad'in mom lafiya?. Tadago kai takalleshi cikin tashin hankali,sannan tace Al ameen daddyn Kane yayi aure. Cikin karfin murya yace: daddy kuma!? Tace hakane Amaryar tana manumfashi,shine naje nanuna raina ya'baci,natafo,wai yanzun anje antadda Amaryar ankasheta,shine akace nice,a yanzun haka 'yansanda nanan hanyarsu tazuwa sutafi dani. Yace sutafi fake mommy? Tagyad'amai kai alamar e,tareda share hawayen dasuka zubo aidonta. Yace to amma mommy................. Tad'agamai hannu tareda cemai ya isa!kada kace komai Al ameen,kai d'anane,kuma sanin kankane Addu'ar 'ya'yazuwaga mahaifansu kar'ba'b'biyace,don haka ita kawai nake bukata awurinka,don ba abinda zaka iya taimakamin dashi yanzun face ita. Nandanan shima yaji hankalinsa yatashi,zargin kisan kai?wannan ai babban Case ne,yo amma mommy ita meyasa taje gidan?duk dadai nasan mahaifiyata tanada zafin kishi. Hajiya tace tashi katafi d'akinka ,kaitayimata Addu'a. Yatashi jikinsa asanyaye,yakoma dakinsa,kai tsaye gadonsa yafad'a,hawaye nazuba a idanunsa,yadauki filo yarungume. Yace azuciyarsa yanzunnan tafiya za'ayi da mommy station? Akan zargin kisan kai? Daddy meyasa kayi mana haka?meyasa kakara aure mommy batasaniba?kuma dukda kasan zafin kishinta? Kawai sayya tuna da wata rana suna zaune shida mommysa afalo. ***** ***** ****** ******* ******** Yace mommy nikau intambayeki? Tace inajin ka . Yace wai meyasa kikeda tsananin kishine haka?sai inga duk lokacin da wani yayimaki maganar kishiya sai inga duk kin canza. Tayi murmushi tareda 'ballar Apple din dake hannunta,tace yarone kai ba kasan komaiba game dawannan,sai nan gaba tukunna,kodayake kai Namiji ne bazaka fahimtaba,amma ko 'kanwarka Asiya ba tayimin irin wannan tambayar ba,tundadai ita tayi aurennan. Sayyace nikuma mommy bazan biyema matataba,inkiyin aure,ni mata biyu zan aura. Tace inma Hudu zakayi ina abinda yadameni,sai inyi maka Adduar Allah yataka riko. Sayyayi dariya yace ammani bansan abinda yasa Daddy mu yazauna da mata d'ayaba. Tace Al Ameen tononama kakeko?inawasa dakai!to abinda yasa daddyn ku yake zaune dani nikadai,saboda nikadai din naishesa! Yace haba mommy bahakabane,idanna zauna INA lissafine,sai inga duk abokan daddymu shikadaine keda mata d'aya. Tace wata kan tooh!har lissafanima kakeyi?kan anan kana lissafi!to tashi kabani wuri!takaimai jifa da filon dake hannunta,yagoce ,yatashi dagudu yana dariya. ( Fatima Dahiru funtuwa Binta 09162526909) Aah!kajini da yaro,shiyasan me akecema ki shine? Hada wani zaka hada mata biyu,to Allah dai yatayaka riko,yabaka ikon yin mata biyun,don yanzun aurennan nazamani inba mata biyu ko uku kahadaba ba kagane anasonka,Allah yacika maka burinka,yataka riko,Allah kuma yahada maka kan matayenka,Allah yabaka masu sonka da gaskiya, sannan tad'auki rumot ta canza tashar datake kallo. ******* ****** ****** ****** ******** Koda yagama wannan tunanin idanuwansa sunjike da hawaye,yanzunnan mommy akezargi data kashe kishiyarta? Nandanan yadauki waya yakira kanwarsa dake aure yasanar da ita. Asiya itama hankalinta yatashi sosai,tareda fadin meyasa daddy zayyi masu haka?meyasa zayyi aure bamu saniba?itama tafashe da kuka. Washe gariko ko karyawa sunkasayi,kowa zugudum-zugudum,kamar anyi masu mutuwa,suna sauraron shigowar 'yansandan da akace zasuzo daukar mommy, dasunji motsi saisuji kamar sune. Tun safe dama Asiya sammako tayo,idanunnan nata jawur!suna zaune afalo kowa yabuga uban tagumi. Asiya tace mommy nikau sai inga ,daki zauna anan azoatafi. Azo atafi dake cikin tozarci da wulakanci,dake kikaje kikakai kanki. Kowa yad'ago kai yakalli Asiya,lallai kam kinkawo shawara mai kyau,hakanma zaikara tabbatar dacewa ba ita tayi kisanba. Kawai saita mike da nufin tatafi wurin motarta don taje manumfashi, Asiya kuwa cikin kuka tace mommy sainabiki. H-Amina tace Asiya kiyi hakuri in Allah yayadda zandawo,kedai kici gaba tayimin Addu'a. Dai dainan wasu 'yansanda mata guda biyu suka shigo, dauke da zabgegiyar onka ahannunsu,ba gaddama dama jiransu suke. Akadaura mata kafa da hannayenta aka kuma ratayo mata wata awuyanta. Al Ameen tunda yaga mamansu acikin irin wannan yanayin baisan lokacin daya fashe da kuka mai tsananin rikitarwaba,gaba daya kowa kukan yakeyi. Salim Dan autanta yarugo da gudu ya mamuketa,yana fadin don Allah mommy kada atafi dake"shikenan bazamu kara ganinkiba mommy? Tace kayi hakuri salim zandawo,kaitayimani Addu'a kaji. Wannan 'yarsandar tajanyeshi daga jikin mamansa ,sannan suka tasa keyar H-Amina sukayi waje da ita,nanfa akaita 'yan koke-koke gidan kamar anyi mutuwa. Har wajen motar police din suka biyosu,suna kuka,'yan sandar kokulasu basuyiba sukaja motar sukayo hanyar manumfashi. MASHA ALLAH Anan nakawo karshen littafi na daya,saimun hadu alittafi na biyu domin jin yadda zata kasance. Daga mai debemaku kewa akodayaushe. 'Yar mutan funtuwa Fateema Dahiru funtuwa Binta Gawanda yakeson cigaban wannan littafin ya tuntubeni ta wannan number 09162526909. Dad'an tugwicinka kad'an zaka samu cigaban wannan kayataccen littafin. Don Allah kada mutum yadauki number ta inbaitashi siyan littafin ba,yayi hakuri harka yashirya siye. Kusani littafin na biyu na kudine. Littafan marubuciyar BABBAR HUJJA 1&2&3 KWATAR KAI 1&2&3 RUDANI 2&2 WATA SAKAYYAR...........1&........ Dukkansu na siyarwane,kaidai inka shirya katuntubi wannan number WhatsApp kawai banda kira 09162526909 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels