An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [14/11 10:11] 'Dan Malam: FALALA DA MARTABAR SAHABBAI #Shimfiďa: Da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da amincin ALLAH su 'kara tabbata akan Manzon ALLAH S.A.W cikamakin Annabawa shugaban manzonni. ALLAH yace: An tsinewa waďanda suka kafirta daga Bani isra'ila (zuriyar Annabi Yakub A.S) da harshen Annabi Dawood A.S da na Annabi Isa ďan Maryam; saboda sun kafirce kuma sun wuce gona da iri. Sai ALLAH ya cigaba da cewa: (Saboda) sun kasance basa hani ga juna akan munanan ayyuka idan aka aikata, lallai makoma tayi muni akan waďannan abubuwan da suka kasance suna aikatawa (ma'ana dukkanin su da masu aikata waďannan ayyukan da waďanda basa hani ga aikata su) a duba ko wane littafin tafsirin waďannan ayoyi wato Sura ta biyar (Suratul Mai'da) daga aya ta saba'in da takwas zuwa ta tamanin da ďaya (Q5:78-81). Waďanda ayoyi dasu na kwana don jiya nayi muqabala da wasu ýan uwa akan son zuciyoyin su dangane da abunda ya shafi bid'o'i waďanda ake 'kir'kirowa a addini. Dalilin da suke bayarwa su da maluman su shine: Mai yasa bamu ta6a fitowa mun soki birthday wanda kullum ake kan aikatawa ba? Dalilin mu anan shine: Birthday yahudanci ne kuma ai a matsayinka na musulmi mai imani, idan kana karatu baka bu'katar sai an fito an ce maka wannan kafirci ne wanda bashi da asali a musulunci. Manzon ALLAH S.A.W yace: Mumini madubin mumini ne, idan yaga aibu a gurin ďan uwansa, ya gyara. Idan don ALLAH muke yin addinin, dole mu dinga kar6an gyara daga gurin juna. Da dalili ake addini ba da son zuciya ba. Ka karanta kuma ka ďauki sakon da yake 'kunshe a cikin wannan rubutun don idan baka karanta ba, nayi imani cewa waďanda suka fika zasu karanta kuma su amfana. Duk da cewa 'Karshen duniya ne kuma duk iya salo na da'awar mutum ba yanda zaiyi idan ALLAH bai shiryi mutum ba, wannan ba hujjace ta 'kin kira ga gaskiya ba. ALLAH ya koyar da ManzonninSA ciki har da Manzon ALLAH S.A.W akan cewa: Ba zaka iya shiryar da wanda ALLAH baiyi niyar shiryar dashi ba. Misali: Mu duba 'Dan Annabi Nuhu A.S, matar Annabi Luď A.S da baffan Annabi S.A.W wato abu 'Dalib. Kuma mu dawo ta ďayan 6angaren mu duba rayuwar matar Fir'auna (kafirin da yafi ko wane kafiri kafirci a tarihi). ALLAH ya buga misalai dasu a gurare daban daban a Qur'ani kuma Manzon ALLAH S.A.W ya bada labarin su a hadisai daban. A musulunci, mun yarda bayan Annabawa, babu masu darajar sahabban Manzon ALLAH S.A.W kuma wajibi ne duk mai imani ya yarda da hakan. Idan muna karanta tarihin su kuma muna amfani da abubuwan da muka karanta, zamu ci riba duniya da lahira. ALLAH da KANSA ya yabe su da cewa: Mazaje ne waďanda kasuwanci da siye da siyarwa baya shagaltar dasu daga ambaton ALLAH; suna cike da tsoron ranar da zuciyoyi da da idanuwa zasu raunana (Ranar Qiyama) to dayake ba Tafsiri nake ba, bana son in ja da yawa tunda dama shimfiďa ce duk da akwai abubuwa masu yawa da nake son kawowa amma a hankali inshaa ALLAH zan isar da sa'kon. ALLAH ya san zuciyata na dalilin wannan rubutun kuma ina ro'kon ALLAH ya bani ikon 'karasawa lafiya kamar yanda na fara da sunan ALLAH, ALLAH ya bani ladan tare daku. ALLAH KA rabamu da riya da ribatar Shaiďan.. (1) MUS'AB BIN UMAIR (Farkon jakadan Musulunci) Mus'ab ďan Umair ya taso a gidan wadata da jin daďi don mahaifiyarsa ta kasance daga cikin mutane mafi kuďi a Makkah. Ya kasance ďan gayu wato babu matashi a Makkah wanda mata suke labarinsa kamar Mus'ab bin Umair saboda ga kyau, ka kuďi ga mulki don mahaifiyarsa ta kasance daga cikin masu faďa aji na wancan lokacin. A lokacin, farkon Manzoncin Manzon ALLAH SAW ne kuma a lokacin, musulunci bai fara 'karfi ba don Manzon ALLAH SAW da sauran sahabbai farkon musulunta suna zaune ne a "Daru Arqam bin Arqam" suna ibadah a 6oye. Wata rana, Mus'ab bin Umair ya ji labarinsu inda yazo don cin mutuncin Manzon ALLAH da sahabbansa inda ALLAH ya shiryar dashi ya kar6i musulunci a maimakon haka. Ya fara yi a 6oye har wata rana yazo shiga wani mai suna Uthman bin Taiha ya gansa yaje ya gayawa maman Mus'ab wato Khunais bint Malik wanda dama tayi fice ne a mugunta don kusan duk makkah ana tsoron sharrinta amma tare da haka, ALLAH ya jarebeta da son ďanta 'kwaya ďaya wato shi Mus'ab. Bayan an kai mata labari, ya dawo gida sai yaga duk manyam mutanen makkah an taru ga mahaifiyarsa a cikin su. Suka zazzage shi suka ci mutuncinsa wanda har sai da maman nashi tayi masa wani naushin da sai da yaga taurari. Bayan wannan, an kulle shi amma sai da ya san yanda yayi ya bar gidan ya koma Daru Arqam wanda wannan yayi daidai da lokacin da Manzon ALLAH SAW ya tura sahabbai 'kasar sarki najjashi wanda ba musulmi bane amma baya bari a takurawa musulmai a 'kasar. A lokacin sai suka tafi tare dashi har zuwa wani lokaci wanda bayan sun dawo, ya 'kara zuwa gurin mahaifiyarsa inda yace mata: Kinga wannan takobin, Na rantse da ALLAH duk wanda kika sa ya kamo ni saina raba kansa dashi. To dama tasan halin shi tsaf zai iya. Daga 'karshe yace: Yake mahaifiyata! Ki kar6i wannan addinin da yake na gaskiya lallai ni ina sonki da rahamar ALLAH. Sai tace: Na rantse da taurari ba zan kar6a ba. Haka kawai girma na ya zube a banza?! Tana ji tana gani haka suka rabu da hawaye. Mus'ab bin Umar ya gwammaci rayuwar wahala akan wanda jin daďi duk don ya samu yardar ALLAH. Wata rana, sahabbai suna ganinsa sai suka fashe da kuka suka ce: Kalli yanda Mus'ab ya dawo wanda da kowa yasan irin jin daďin da yake ciki amma yanzu kalli kayan da yake sakawa!. Manzon ALLAH SAW yace: Ni naga Mus'ab a Makkah a lokacin ba wani matashi wanda yake jin daďi kamar sa. Manzon ALLAH SAW ya tura shi Madina don yayi kira ga musulunci kuma ya koyar da addini inda anan ya samu ďumbin nasarori don manya-manyan mutane a madina sun musulunta a sanadiyyar shi inda kusan duka mutanen Madina suka musulunta a wancan lokacin. Ya samu gaggarumar nasarar da ba'a kwatantata da wata a wancan lokacin. Ha'ki'ka ya isar da sa'kon ALLAH wanda Manzon ALLAH SAW ya aiki shi dashi tare da gaggarumar rinjaye. Lokacin ya'kin Uhud, bayan shaiďan ya samu rinjaye akan musulmai inda bayan sun bar kan dutsen uhud, kafirai dalilin da yasa kafirai suka samu galaba a kansu. Lokacin da Mus'ab ibn Umair ya fahimci cewa ya'ki ya canja kuma akwai matsala, sai yayi kukan kura yayi kabbara ya 'kara himma har takai ga sun zama ýan tsiraru daga cikin waďanda suke kare Manzon ALLAH daga harin kafirai waďanda basu da wani buri da ya wuce na ganin bayan Manzon ALLAH S.A.W a wannan lokacin. An sare masa duka hannuwa biyu inda daga karshe yayi shahada tare da sauran manyan jarumai waďanda sukayi shahada a ya'kin uhud wanda hatta Hamza anan yayi shahada. Bayan an gama ya'kin, Annabi SAW tare da sauran sahabbai sun zo ďaukan gawawwaki don binnewa da yiwa shahidai ban kwana inda aka tsince shi a cikin su sai Manzon ALLAH SAW yayi hawaye inda yace: Munyi hijra tare don ďaukaka kalmar ALLAH, lallai sakamakon mu yana ga ALLAH. Annabi S.A.W ya cigaba da cewa: Daga cikin mu akwai waďanda suka bada gudunmawa iyakar 'karfin su amma sun koma ga ALLAH ba tare da sun ci gajiyar wahalar ba (ma'a basu riski lokacin da addinin yayi 'karfi ba) yace: A cikin su akwai Mus'ab bin Umair. Aya ta 23 ta cikin sura ta 33 (Q33:23) ta sauka ta dalilin wannan. ALLAH yasa mu dace. Daga 'karshe wannan kamar sharen fage ne na tarihin sahabbai shiryayyu wanda gudunmawa ta ce, duk mai son sanin cikakken tarihin, ya duba waďannan littattafan: Albidaya wan nihaya na Al-hafiz ibn Kathir, Qasasus sahaba da sauran ingantattun littattafan sira na manyan malamai. Zamu cigaba da tarihin sahabi na gaba a cikin jerin rubutun inshaa ALLAH ko gobe idan na samu lokaci. Ayi sharing don Manzon ALLAH SAW yace: Duk wanda yayi nuni ga aikin alkhairi yana da lada kamar wanda yayi. ALLAH KA sanar damu abunda zai amfane mu! ALLAH KASA addinin nan ya zamo hujja gare mu ba hujja a kanmu ba!! Don gyara ko jan hankali ko tambaya, ga nombobi nan kamar haka: 08067396502 (WhatsApp). 08169965350 (Kira kawai). ©Aliyu Abdullahi 'Dan Malam [14/11 10:11] 'Dan Malam: FALALA DA MARTABAR SAHABBAI (2) Wani ya tambayi Manzon ALLAH SAW alamomin tashin Qiyama inda bayan ya bayyana alamomin ta, sai sahabbai suka tambaye shi akan me ka umarce mu dashi idan mun riski lokacin da waďannan alamomin zasu bayyana? (Wato kamar dai don mu sukayi tambayar don zuwa yanzu, alamomin da yawa sun bayyana. Yawancin 'kananan sun bayyana, waďanda suka rage sai dai manya kamar su bayyanar yajuju da majuju, dare biyu, bayyanar Dajjal da sauran su. Tun Manzon ALLAH SAW yana da rai yace: An aikoni Qiyama tana gab da zuwa.) Manzon ALLAH SAW yace musu: Kuyi ri'ko da Sunnah ta da Sunnar Khalifu na shiryayyu. A nan nake so mu gane wani abu ďaya don lokacin da muke yiwa ýan uwa nasiha akan wata bid'ar da suke kai, sun fara wasu tambayoyi masu hatsarin gaske kamar haka: Tunda mun ce Maulidi bid'ah ne to haďa Qur'ani ma bid'ah ne kenan tunda ai Annabi SAW bai yi ba kuma bai ce ayi ba. Amsa: Ina ka ajiye hadisin nan da na kawo a sama? Baka san yanda akayi tsakanin manyan sahabbai musamman Umar da Abubakar ba a lokacin da aka kawo maganar cewa akwai bu'katar tattara Qur'ani zuwa wani kundi guda ďaya ba? Ko baka san dalilin haďa Qur'anin bane?. Tambaya ta biyu da suke yi itace: To ai Tafsiri ma bid'ah ne kenan tunda Manzon ALLAH SAW bai yi ba kuma sahabbai shiryayyu basu yi ba. Amsa: Kaje ka duba tarihin Abdullahi bin Abbas wanda tun yana yaro Manzon ALLAH SAW ya masa addu'a yace: Ya ALLAH ka fahimtar dashi addini kuma ka bashi ilmin fassarar Qur'ani. To dayake addu'ar Manzon ALLAH SAW bata tashi banza, a cikin sahabbai sai da ya zamana kusan babu wanda ya fishi ilmin fassarar Qur'ani. Tabi'ai sunfi sahabbai ilimi saboda sahabbai su suka koyar da tabi'ai inda su koma tabi'ai sukayi karatun ta hanyar amfani da damar da suka samu wajen koyon komai daga sahabbai. Sahabbai basu san komai da Manzon ALLAH SAW ya koyar ba amma tabi'ai sun koyi duk abubuwa daga sahabbai daban daban tunda ko a cikin sahabbai akwai abunda wasu suka sani wanda wasunsu basu sani ba. Misali: Abu Hurayra yafi kowa rawaito hadisan Manzon ALLAH SAW tare da cewa daga baya ne ya musulunta don ko manyan ya'kuna bai samu damar halarta ba don kwata-kwata bai wuce shekaru biyu tare da Manzon ALLAH ba kafin Annabi SAW ya koma ga ALLAH. Shi yasa idan wata rana ya karanto wani hadisin, sai sahabbai su ce: Kai Abu Hurayra! Kasan abunda zaka dinga gaya akan Manzon ALLAH. Ga misali: Wata rana Abu Hurayra ya karanto hadisin da Annabi SAW yace: Duk wanda musulmi ya mutu yaje aka yi sallar gawa tare dashi kowa aka kai ma'kabarta aka binne gawa tare dashi, yana da lada daidai da Qiraďi biyu (Kamar girman dutsen uhud sau biyu) Sai wani daga cikin sahabbai yace: Kai Abu Hurayra! Yaushe Annabi yace haka? Sai ya kama hannun sa sukaje gurin Aisha wato lokacin Manzon ALLAH SAW ya koma ga ALLAH. Sai Aisha tace: Tabbas nima naji. Abunda yasa Abu Hurayra ya tara hadisai sama da duka sauran sahabbai shine: Ya kasance yana bin sauran Sahabban da suka yi rayuwa tare da Manzon ALLAH har gida domin samun ilmin hadisan da aka yi lokacin da baya nan kuma bayan da ya kar6i musulunci, bai da sana'a bal ma kullum yana fadar Manzon ALLAH SAW inda yake cin abinci na sadakar da aka kawo. Ta haka ya tara hadisan da sauran basu tara ba kamar yanda zan kawo cikakken bayani akan haka idan nazo kan tarihinsa nan gaba idan ALLAH ya yarda. Abunda nake nufi a ta'kaice shine: Ku duba duk tafsirai ku gani ko maganar waye. Idan wani malami daga cikin magabata ya gayi wani abu wanda ba Manzon ALLAH SAW ne ya gaya ba kuma ba sahabban shi ba, zaka samu fahimtar su ce wanda suka samu ta sanadiyyar yawan neman ilmin su. Misali: Imam Malik yayi karatu ne a gurin wanda yayi karatu a gurin Abdullahi ďan Umar, imam shafi'i ďalibin imam Malik ne, imam Ahmad bin Hambal ďalibin imam shafi'i ne. Anyi wani fitaccen malamin hadisi mai suna Abdullahi bin Mubarak wanda babban ďan kasuwa ne da yake kasuwanci saboda tafiye tafiye da yake yi wajen kar6o hadisan Manzon ALLAH SAW. ALLAH ya sani magabata sunyi iyakar 'ko'kari wajen sau'ka'ka mana addinin nan don mu fahimta wanda Tafsirai suna daga cikin aikin da sukayi don amfanin mu. ALLAH yasa mu dace. SALMANUL FARISI (Mai neman hasken gaskiya) Ga yanda ya ba wani babban sahabi labarinsa: Na taso a wani lardi da ake kira "isfahan" a inda ake kira Jai, na taso naga ana bautar wuta a gidan mu, babana wanda na kasance mafi soyuwa a cikin ýaýansa sa ya horar dani akan bautar wuta wanda kullum aikina shine kar in bari wutar ta mutu. Babana yana daga cikin mafiya dukiya na garin. Wata rana ya aikeni zuwa ďaya daga cikin manyan shagunan shi inda a hanya na haďu da wasu christoci suna bauta a cocin su. Abun ya burgeni inda na shiga na shagalta da kallon bautar tasu har takai bai je gurin da aka aike ni ba kuma ban koma gida ba har rana tazo faďuwa.. Lokacin da yazo tafiya sai ya samu wannan fada na cocin yace mishi: Ina son shiga addinin ku don yafi namu kyau. Sai ya koma gida inda babansa ya tambaye shi sai ya gaya masa kamar yanda da ya gayawa wancan fada ďin. Sai ya kulle shi har bayan wani lokaci inda bayan ya samu dama, sai ya tura ga wancan fada (pasto) ďin inda ya bukaci cewa idan aka samu masu tafiya syria (tunda yace mishi a can ne ake addinin yanda ya kamata) ya sanar mishi. Bayan ya gaya mishi ranar da fatake zasu tafi, sai ya ku6uto ya same su suka tafi. Bayan sun je, sai aka haďashi da wani babban fada wanda ya zauna a gurin shi har zuwa lokacin da yazo mutuwa inda a lokacin da yake jinyar ajali, sai Salmanul farisi yace masa: Idan ka mutu gurin wa zanje? Sai yace: Akwai wani a guri kaza, ka je gurinsa. Yace: A lokacin da wannan fadan ya mutu dama nasan halinsa don idan aka kawo abubuwa don a rabawa mutane, tarawa yake baya bayarwa. Bayan mutuwar shi, Salman Alfarisi yayi tafiya mai nisa inda yaje gurin wani fada ďin. Yace: Na biyun kuma ya kasance mutumin kirki inda shima da yazo mutuwa, ya tura shi gurin wani. Haka aka dinga yi har yazo gurin na 'karshe wanda da yazo mutuwa sai yace mishi: Ya kai yaro na! A iya sani na, masu yin addinin nan dagaske sun 'kare amma mun karanta a littafin mu (na injila) cewa lallai akwai wani Manzo wanda zai fito daga 'kabilar Qurayshawa a cikin wani gari da yake da Dabinai (wato makkah) mai suna Ahmad (wanda sunan shi kenan da yazo a injila). Ka je idan ka haďu dashi, akwai alamomin guda uku da zaka tabbatar shine kamar haka; Na farko baya cin sada'ka, na biyu baya cin kyauta, na uku akwai wani tambari wato na alamar Annabta a tare dashi. Bayan wannan malamin ya mutu, dama Salmanul Farisi yana kiwo sai ya kaďa awakinsa inda ya haďu da wani fataki ya musu kwatance da abunda wannan malamin ya mishi kuma yace zai basu duka awakin. Sun fara tafiya har sun kai wani gari inda suka ci amanarsa suka siyar dashi. Wanda ya siye shi ya ďauke shi ya kai shi garin su yana mai aiki inda shima wani ďan uwansa wata rana yazo gurinsa ya siye shi ya tafi dashi dashi Madina wanda a lokacin Manzon ALLAH S.A.W yayi hijra daga makkah zuwa madina. Yayi aiki a gonar wanda ya siye shi ďan 'kabilar banu Quraidha. Wata rana yana aiki saman bishiyar dabino a yayin da megidansa yake shan iska a 'karkashin bishiyar, sai ďan yar uwarsa yazo yana cewa: Ana ta surutu a gari wai wani ya 6ullo wai ALLAH ne ya aiko shi. Salmanul Farisi yace: Ina jin wannan sai da na faďo saura kaďan na faďo akan Megidana sai ya ďauke ni da wani wawan mari wanda sai da naga haske sannan yace: ka koma aikin ka. Na cigaba da aikin har rana ta faďi inda na samu dabinai na tafi zuwa ga Manzon ALLAH SAW na gaishe shi nace ga sada'ka na kawo. Manzon ALLAH SAW bai ci ba sai yacewa sahabbai su ci da sunan ALLAH. Na tabbatar da alama ďaya kenan. Washe gari ma nayi haka amma sai a wannan karon nace ga kyauta inda Annabi SAW yaci sahabbai ma suka ci. Sai alama ta uku wanda wannan lokacin yayi daidai da dawowa daga ya'ki inda naje nayi kamar ina neman wani abu alhalin tabon nake nema, da Manzon ALLAH SAW ya fahimci haka, sai ya buďe min na gani. Ina gani sai na fashe da kuka na ba Annabi labarin inda Manzon ALLAH ya nemi da sahabbai su siye ni su ýanta ni kuma akayi haka. Ali ďan Abi Ďalib yana masa alkunya da Luqman (Mai hikma) don mutum ne mai hikma tare da ilmi saboda tarin ilmi da gogewar rayuwa da ya samu sakamakon gwagwarmayar da yayi. Manzon ALLAH SAW ya tabbatar cewa: Duk wanda yayi imani da littafin injila kuma ya kar6i musulunci yana da lada iri biyu. Salmanul Farisi yayi rayuwa mai tsayi don sai a lokacin khalifancin Uthman ya koma ga ALLAH. Tun a lokacin Umar ana bashi Albashin da ya kai dirhami dubu biyar inda yake sada'ka da dirhami dubu huďu da casa'in da tara. Dirhami ďaya ne yake ajiyewa wanda dashi yake siyo kayan haďa kwandon dabino wanda bayan ya haďa yake ciyarwa dirhami uku, yana bada sadaka da dirhami ďaya daga ciki, yana rayuwa da dirhami ďaya sa'annan yana siyo kayan haďa wani kwandon da dirhami ďaya. Ya mutu a gida inda lokacin yana jinyar mutuwa, Sa'id bin Abi waqqas yazo duba shi sai ya ga yana hawaye. Sai yace: Ba ina kuka ne don wani abu ba sai don Manzon ALLAH SAW ya bani shawarar cewa in nemi duniyarnan kamar matafiyin da yake tafiya a kan hanya. Sai Sa'id ibn Abi waqqas ya duba bai ga komai ba na jin daďi a gidan (don lokacin da zai gina gidan sai da ya gargaďi mai ginin akan ya gina mishi wanda kawai zai kare shi daga sanyi da rana kuma wanda zai dinga tuna mai da qabari ma'ana wanda idan ya ďaga kai, ba zai iya mi'kewa a cikin sa ba.) Sai Sa'id yace: Ka mana wasiyya! Sai yace: Kuji tsoron ALLAH akan waďanda ALLAH ya baku shugabancin su (iyalanku) idan baku da su, kuji tsoron ALLAH akan shugabancin da ALLAH ya baku na mutane. Lallai addinin nan zai 'kara samun cigaba bayan mutuwa ta, idan hakan ya faru, kuyi amfani da iya abunda zai isheku na daga dukiyar "baitul mali". Da yazo mutuwa, sai yace matarsa ta kawo mishi ajiyarsa. Sai ta kawo wani turare inda ya saka a cikin ruwa kuma yace: Zan haďu ga abokai (Mala'iku) waďanda ba abunda suke so sai 'kamshin turare. Sai yace ta bashi guri inda bayan ta dawo, sai ta tarar da gawarsa. A nan na kawo 'Karshen tarihin wannan babban sahabi mai falala wanda idan mukayi aiki da rayuwar shi, zamu samu cin nasara duniya da lahira. Domin gyara ko tambaya ko neman 'karin bayani, ga lambobi kamar haka: 08067396502 (WhatsApp) 08169965350 (Kira kawai) ©Aliyyu Abdullahi 'Dan Malam [14/11 10:11] 'Dan Malam: FALALA DA MARTABAR SAHABBAI (3) Idan a 6angaren imani ne da daraja da falala ko kusa da tabi'ai baka kai ba balle sahabbai waďannan a musulunci dole mutum yayi imani da cewa bayan Manzon ALLAH SAW, babu waďanda suka kaisu imani domin su da gaske suka yi addinin ba da kame-kame ba kuma ba da son zuciya ba. Sun so Manzon ALLAH SAW iyakar soyayya ta hanyar kare martabarsa, taimaka masa da tsayuwa tare dashi a halin 'kunci da tsanani amma yau saboda bid'ah tazo ta ci 'karfin imanin mutane har ta kai ga sun fara tunanin yin abubuwan da sahabban Manzon ALLAH SAW da magabata basu yi ba wanda idan imani ne da ilimi irin na wancan lokacin, sam babu ko kashi goma cikin ďari a wannan zamanin. Iyakaci muyi nasiha amma shiriya na kar6an nahihar ALLAH shi yake bayarwa don hatta Manzon ALLAH SAW sai da ALLAH yace mishi shiriya a hannun ALLAH take ba a hannun Manzon ALLAH SAW ba bal shi bai kasance ba sai Manzon ALLAH mai isar da sa'kon ALLAH wanda dama ALLAH ya za6eshi kuma ya aiko shi da littafin da yafi na sauran Manzonnin kuma ALLAH ya bashi darajar da bai ba wani ba daga cikin Manzonnin ALLAH. An fara ďaukar sahun wasu daga cikin christoci ta hanyar kai Manzon ALLAH matakin da bai kai ba don wasu har ta kai ga suna jinginawa shehunan su matsayin Annabi SAW ko ma sama da haka. Wasu ma saboda tsabar 'kin gaskiya sai su dinga isgilanci wa ALLAH don duk wanda aka mai nasiha akan wata bid'ah har takai ga yace idan ita ita zata shigar dashi wuta to idan ya shiga zai cigaba. Ai kaga wannan ba mu yake wa isgili ba ALLAH yake don ai wuta ta ALLAH ne kuma duk wanda yake ganin abunda aka 'kirki bayan Manzon ALLAH SAW da sahabbansa da tabi'ai daidai ne, lallai alama ce ta ta6ewa. ALLAH yasa mu gane BILAL BIN RABAH (Mawadacin Jarumta) Duk lokacin da Umar (ALLAH ya 'kara masa yarda) zai ambaci Abubakar (ALLAH ya 'kara masa yarda) yana cewa: Shugabanmu wanda ya fanshi shugabanmu wato Bilal. Fansar Bilal da Abubakar yayi yana ďaya daga cikin falalolin sayyadina Abubakar a musulunci don Bilal ba 'karamar gudunmawa ya bayar a duniyar musulumci ba. Bari mu shiga daga cikin tarihin wannan gwarzon.. 'Kaddarar Bilal tasa ya kasance daga cikin bayin wasu mutane daga ka'bilar "Juma" dake Makkah wanda mahaifiyarsa ta kasance baiwar waďannan mutanen. Bilal ďan Rabah Ba'ki ne wanda yake aikin bauta na kiwo da sauransu kafin rana tsaka ALLAH ya aiko Manzon ALLAH SAW wanda daga bisani ya kar6i musulunci bayan ya ďauki lokaci yana samun labarin addinin wanda musulunci ya zamo abun surutu da hiran ýan gari sanadiyyar da yasa iyayen gidansa suka fara azabtar dashi da nau'ika iri-iri na azaba a matsayinsa na bawa mara gata kuma a matsayin addinin musulunci na addinin da mutanen Makkah (Qurayshawa) suke tsananin 'ki a daidai wannan lokacin. 'Kabilar juma sun kasance daga cikin ka'bilu mafi Alfahari a garin makkah saboda haka suke ganin ai zubar musu da mutunci ne ace bawansu shi ya bi addinin Muhammad a cewar su. Suka fara ďanďana masa azaba da niyyar lallai sai ya bar addinin musulunci ya koma addininsu na kakannin wanda Bilal duk azabar da suke gana mishi sai dai yace: 'Daya! 'Dayya (ALLAH! ALLAH!!) har takai ga sun fara tausaya mishi sai suka fara cewa: Kaga muma mun gaji da azabtar da kai, kace Lata da Uzza kawai sai mu sake ka. A lokacin magana ma bata fitowa amma duk da haka sai yayi yun'kuri yace: "ALLAH! ALLAH!!" Dalilin da yasa ba zasu iya kashe shi ba shine bawa kusan yafi komai daraja a gurin su a matsayin su na ýan kasuwa masu kasuwanci wanda bawa abu ne mai daraja tunda da kuďi suka siye shi. Ana haka wata rana Abubakar yazo wucewa inda ya ga Bilal ana ta gana mishi azaba a cikin rana inda yace: Kuna azabtar da mutum don yace ALLAH ďaya ne? Sai Ummayah bin khalaf (Uban gidan Bilal) ya mishi iho yace: To ka kawo kuďinsa mana. Bayan Abubakar ya biya sai Umayyah bin ka'ab yace: Gashi! Na rantse da lata da uzza!! Idan da ka'ki siyan shi a farashi mai kyau, ko dirhami ďaya zan siyar maka dashi. Da kamar Abubakar ba zai ce komai ba amma sai yayi tunanin idan yayi shiru, kamar an ci mutuncin ďan Uwan sa na musulunci ne a gabansa amma ya kasa komai. Sai Abubakar yace: Na rantse da ALLAH idan da ka'ki siyar mini dashi sai a dirhami dubu, zan siye shi. Abubakar ya ýanta shi nan take ya zama cikakken mutum mai ýanci kamar sauran mutane wanda ya bashi damar kasancewa daga cikin na gaba-gaba daga cikin sahabban Manzon ALLAH SAW. Bilal ďan Rabah ya samu matsayin da sauran manyan sahabbai suka nema basu samu ba na Ladanci wanda yana da falaloli na musamman a musulunci. Daga cikin falalar Bilal a matsayinsa na Ladan shine Manzon ALLAH SAW yace: Bilal me kake yi ne? Naji takun ka a Aljanna. Sai Bilal yace: Na kasance duk lokacin da na kira sallah, ina yin raka'a biyu. A ya'kin Badr Bilal ya kashe Umayyah bin khalaf wanda da ya janye kansa daga zuwa ya'kin inda wani abokinsa yaje ya same shi a bakin Kaba ya zuga shi suka tafi. Bayan Ummayya bin Khalaf ya ga ya'ki ya canza, sai yaso yayi amfani da wata dama don ya ku6uta daga kisa ta hanyar cewa shi ya zama ya zama fursunan Zubair ďan Awwam amma haka yaci tura. Bayan Manzon ALLAH SAW ya koma ga ALLAH, Bilal baya iya kiran sallah kamar da duk da ya kasance mafi murya daga cikin sahabbai. 'Karshen kiran sallar da yayi shine a lokacin khalifancin Umar lokacin da ya kai ziyara syria wato inda Bilal ya koma sai mutane suka nemi da ya saka Bilal ya kira sallah, a lokacin Abubakar kuwa da ya matsa masa akan sai ya cigaba da kiran sallah cewa yayi: Idan a da ka ýanta ni don kanka, zanyi abunda kake so. Idan kuma ka ýanta ni don ALLAH ne, ka barni kawai (don bazan iya cigaba da kiran sallah ba). Sai yace to me zakayi? Sai Bilal yace: Naji Manzon ALLAH SAW yana cewa: Mafi kyawun aikin mumini shine jihadi a hanyar ALLAH. Sai Abubakar yace: To me kake so? Sai yace: Zanyi jihadin jaddada addinin ALLAH har sai na mutu. Malaman tarihi sun rabu anan inda wasu suka ce ya tafi ya yita jihadi har 'karshen rayuwar shi inda wasu suka ce ya amsa ro'kon Abubakar inda ya zauna har lokacin khalifancin Umar inda ya ro'ka aka bashi damar tafiya syria. ALLAH yasa mu dace Domin gyara, 'karin bayani ko jan hakali: (08067396502) WhatsApp ©Aliyyu Abdullahi 'Dan Malam An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels