An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DUNIYA MAKARANTA 1 (Hikimomi 1-250) Rubutawar Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto 1 Bugawa da Yadawa: Bugu na biyu 1437H/2016 Haqqin Mallaka @ Mawallafi mansursokoto@yahoo.co.uk isbn 9960-49-972-3 2 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Gabatarwa Yabo da godiya da’iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama su dawwama ga fiyayyen halitta, shugaban Annabawa kuma jagoran Manzanni Annabinmu Muhammadu, da iyalansa da Sahabbansa baki xaya. Waxannan kalmomi na fito da su ne daga cikin Alqur’ani da Hadisai da maganganun masu ilimi da basira da fahimtar rayuwa na da, da na yanzu. Na kuma rubuta su ne musamman don amfanin kaina game da darussan da wannan rayuwa take xauke da su. Kuma tasharmu mai farin jini ta Wisalhausatv ita ce take da yaxa su a kullum safiya ta Allah domin amfanin jama’a. Haka kuma ana yaxa waxannan kalmomi masu amfani a shafinmu na Minbarin Malamai wanda yake group ne na faxakarwa a Whatsapp wanda ya qunshi darussa da fa’idoji masu amfani.1 Babu shakka, wannan littafi ya samu karvuwa a fitowar sa ta farko wanda ya sa har aka yi ta maimaita buga shi sau da dama, wasu kuma suna raba shi a wuraren tarurruka da bukukuwan aure da makamantansu. Wannan ya daxa ba ni qwarin guiwa wajen ci gaba da fito da waxannan Hikimomi masu amfani. Ga shi yanzu wannan bugu na biyu zai fito a tare da littafi na biyu. Bayan haka kuma in sha Allahu za mu buga littafin “Abokin Fira” wanda yake bayyana darussan “Duniya Makaranta” a cikin qissoshi na tarihi masu ban sha’awa da sa nashaxi da ban al’ajabi. Baban Ramla A Sakkwato 27 ga Safar 1437H 1 Waxanda suke son shiga wannan zaure za su iya aika lambobinsu ta Whatsapp zuwa ga 08064661666. Haka kuma masu buqatar wannan littafi suna iya bugawa ko su aiko saqo zuwa ga wannan lamba: 09030606028 3 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 1. Sauqi yana tare da tsanani. Mai haquri yana cim ma daxi. Mai kyauta ba ya rasawa. Kowa ya ji tsoron Allah, Allah zai yi ma sa mafita. Manta da damuwa ka fuskanci rayuwa. Kowa ka gani a duniya akwai abin da ya dame shi. 2. Idan za ka yi alheri ka gaggauta shi, ka sirranta shi, sannan kada ka yi gori. Wannan shi ne halin mutanen kirki!. 3. Idan ba ka iya yin sadaka daga abin aljihunka to ka yi sadaka daga cikin haqoranka. Murmushi ga fuskar xan uwanka shi ma sadaka ne. 4. Ba kowane aiki ne qarfi yake yi ba. Wani aikin haquri ne yake yin sa! 5. Yaro akwai lokaci da qarfi amma babu kuxi. Dattijo akwai kuxi da qarfi amma babu lokaci. Tsoho akwai kuxi da lokaci amma babu qarfi. A rayuwa in ka samu wani abu ne za ka rasa wani. Cikakkiyar ni'ima kawai tana aljanna. Ya Allah ka ba mu aljanna. 6. Maqiyanka mutane uku ne: Mai qin ka, da mai qin masoyinka, da mai son maqiyinka. Mai son uwa dole ne ya so xanta. 7. Macce ce ta haife ka. Macce ce ta yi rainon ka. Macce ce kuma uwargidanka. Ta ya ya za ka raina macce? 4 8. Uwa ita kaxai ce take manta kanta a addua, ta shagaltu da yi ma xanta. Mu so iyayenmu. 9. Abubuwa uku ne su ke kawar da bala'i: Sadaka da Addu'a da Sada Zumunta. 10. Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa: Magana da Lokaci da Mutunci. 11. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudun su ake yi. Wasu kamar magani suke, akai akai ake buqatar su. Wasu kuma kamar abinci suke, a kullum dole ne a neme su. Yi qoqari ka zama wanda a kullum ake neman sa saboda amfaninsa. 12. Idan ka kwanta ba ka sani ba wane ne zai tashe ka? Iyalanka ne ko Mala'ikan mutuwa?! Zama cikin shiri a kullum don kada a riske ka. 13. Ana yin da-na-sani ne a kan magana, amma ba a cika yi a kan kawaici ba. Kama bakinka duk lokacin da ba ka tabbatar da amfanin magana ba. 14. Kada ka damu da masu qulla ma ka sharri, duk iya qoqarinsu ba su wuce zartar da qaddarar Allah a kan ka. 15. Alamomin tsoron Allah guda biyar ne: a. Fadin gaskiya b. Cika alkawari c. Riqon amana d. Jin tausayi da e. Kyautata ma mutane. 5 16. Rayuwa kamar kasuwa ce. Ka zagaya ka tsinci duk abin da ka ke so. Idan ka zo fita za ka biya duk abin da ka xauka. 17. Wanda bai iya karatu da rubuta ba jahili ne! Amma wanda ya fi shi jahilci shi ne wanda ya san gabas amma kuma ba ya salla!! 18. Idan ka mutu an rufe labarinka, amma abubuwa uku suna rayuwa a bayanka: a. Ilmi da b. Haifuwa da c. Aikin alherin da ka shuka 19. Abokai iri uku ne: - Mai son ka don abinka. - Da mai sonka don kanka. - Da mai son ka don kansa. Irin wannan yana tare da kai ne idan ka samu. Idan ka rasa zai yi ko-sama-ko-qasa. 20. Idan ka yi fushi ka kama bakinka. Domin ba kai ne za ka yi magana ba a lokacin, Shexan ne! 21. Kada ka bar aikin yau ka ce sai gobe. Gobe ai ta mai rabo ce. 22. Kada ka zolayi masu aikata zunubi. Dukanmu muna cikin suturar Allah ne. Amma ka yi ma su nasiha da lafazi kyakkyawa. Duk masu laifi ba su kai Fir'auna ba, kuma duk masu wa'azi ba su kai matsayin Annabi Musa (Alaihis Salam) ba. Amma Allah ya ce da shi: Ka gaya ma Fir’auna magana mai laushi, wataqila zai karvi wa'azi ko ya ji tsoron Allah. 6 23. Huda-huda tsuntsu ne da ya kawo rahoto, ya isar da saqo, ya nuna kishin addininsa. Kada ka bari tsuntsu ya fi ka son Allah da kishin addininsa. 24. Abu Jahali cikakken Balarabe ne, mai kuxi, kuma Baquraishe. Amma yana wuta. Bilal talaka ne, kuma bawa ne, baqar fata. Amma yana tare da Manzo a aljanna. Aikin kowa shi yake fisshe shi. 25. Idan namiji bai ji daxin aure ba zai yi tunanin qara mata ne don ya samu jin daxi. Idan kuma ya ji daxi zai yi tunanin qarawa don ya qara jin daxi. Mata ku yi haquri. Qarin aure xabi'a ce a cikin mazajenku. 26. Ba zaka iya yin hukunci na gaskiya a kan mutum ba, sai idan ba ka da buqata zuwa gare shi. Wanda ya miqa hannu bai miqe qafa! Idan baki ya ci dole ne ido su ji kunya!!. 27. Maganar gaskiya ba lalle ne ta zama mai daxi ba, amma tana da kyau da amfani. 28. Duk lokacin da zunubinka ya fara damun ka to, ka riga ka kama hanyar tuba. 29. Zuciyarka ita ce adireshinka. Harshenka shi ne ma'auninka. Gyara zuciyarka sannan ka kula da harshenka. 30. Haquri iri biyu ne: Haqurin abin da kake so idan ba ka same shi ba, da haqurin abin da ba ka so idan ya same ka. 7 31. Idan kana tafiya babu takalma watarana za ka gamu da wanda yake tafiya ba qafafu. Kalli wanda ka fi shi a kullum sai ka gode ma Allah! 32. Rana a cike take da wuta mai zafi a cikin ta, amma haskenta ne take ba mu. Ba abin da kake da shi ne yake da muhimmanci ba, abin da kake bayarwa. 33. Yana da kyau ka yafe idan aka yi ma laifi. Abin da ya fi haka kyau shi ne ka manta da laifin da aka yi ma ka. 34. Ba za ka sauka tashar nasara ba sai ka hau motar haquri da qoqari da sadaukarwa. 35. Wani ya iya karanta komai amma bai iya fayyace abin da ke cikin zuciyarsa ba. Yana gane aibin kowa amma bai iya ganin nasa. Laifi tudu ne, sai ka take naka ne kake hango na wani. 36. Wanda duk ya yabe ka da qarya watarana sai ya zage ka. 37. Namiji ba ya raki! Jarumi ba ya ja da baya!! Fara ko ta mutu akwai idanu!! 38. Da yawa na nesa da kai zai amfane ka, na kusa da kai ya cuce ka. Kusancin zuciya shi ke da amfani ba na gangar jiki ba. 39. Duk qofar da ka gan ta a rufe tana da mabuxi. Kada ka saki baki kana jiran ta buxe da kanta! 8 40. Komai a duniya yana da mabuxi. Mabuxin ilimi shi ne tambaya. Mabuxin nasara haquri. Mabuxin arziki tsoron Allah. Mabuxin zaman lafiya adalci da gaskiya. 41. Hattara da mabuxai guda uku: - Fushi, mabuxin azaba. - Tsoro, mabuxin fitina. - Kwaxayi, mabuxin wahala. 42. Babban mabuxin alheri shi ne Istigfari. Idan ka yawaita shi matsalolinka za su kau, damuwarka za ta gushe, sauqi daga ubangiji zai zo maka. 43. Kafin ka yi tambaya ka yi tunanin amsar da za a ba ka. 44. A cikin mutane akwai wanda ya cancanta ka jira shi komai daxewar sa. Wani kuma sam bai cancanta ko da ka waiwaye shi ba. 45. Komai ya fi kyau idan yana sabo amma ban da imani. Shi kam ana qara daxewa yana qara kyau da qwari. 46. Duk yadda ka yi sai wani ya zage ka. Manta da mutane ka yi komai yadda ya kamata! 47. Mutane da yawa ba su iya bayyana uzurinsu. Rinqa ba su uzuri ba sai sun faxi ba. 9 48. Duk abin da za ka yi ka yi shi da zuciya xaya. 49. Kowa ya iya haquri ya iya komai. 50. Idan Allah ya ba ka lafiya ya ba ka komai. 51. Kada ka damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba. Kada yau ta sha ma kai, domin gobe ma rana ce. 52. Yafe ma wanda ya cuce ka ni'ima ce. Tuna abin baqin ciki da damuwa wahala ce. Manta alheri butulci ne. 53. Babban zunubi ne ka ci naman wanda ya mutu. Ba za ka iya gaya ma sa a nan duniya ba, shi kuma ba zai yafe ma ka ba a gobe qiyama! 54. Kafin ka roqi Allah abin da ba ka da shi, ka fara gode ma sa a kan abin da kake das hi, don shi ne ya ba ka. 55. A da can mutane ba su da asibitoci amma suna da lafiya. Ba su da yawan kuxi amma suna da arziki. Ba yawan makarantu amma akwai ilimi. Ba hanyoyin sufuri da na sadarwa amma akwai sada zumunci. Ba su da yawan ni'imomi, amma suna da jin daxi. Ko ka san dalili? "Albarkar abu ta fi yawansa". 56. Babbar alamar girman kai ita ce ka raina mutane ko ka ki karvar gaskiya. “Mutakabbiri ba ya shiga aljanna”. 10 57. Ba kowace faxuwa ce matsala ba. Da yawa wanda zai faxi amma idan ya tashi ya sheqa ba ka iya cim ma sa. 58. Idan ka saka kuxi a account ko ka cire kana samun alert na abin da ya rage ko ya qaru a cikin jarinka. Ina ma ace duk lokacin da ka yi qarya ko sata ko ka ci naman xan uwanka za ka samu alert na yawan zunubinka? Ko kuma idan ka yi sallah ko azumi ko sadaka za ka samu alert na yawan ladar da ake ba ka? A kullum ka aikata savo ko xa'a haka tana faruwa, amma Mala'iku ne suke lissafa ma ka suna rubutawa, kuma za su haxa rasitinka gaba xaya a ba ka gobe qiyama, a buga total, a fitar da sakamako, sannan a yanke hukunci. Allah ka sa muna shiga aljanna. 59. Kada ka cuci wanda ya cuce ka. Sharri kare ne, ko ya yi nisa sai ya dawo ma mai-shi. 60. Abu mafi sauqi wajen tunkuxe cuta shi ne ka manta da an cuce ka. 61. Idan ka ga mutum yana tsarguwa da shiga cikin jama'a, shi maha'inci ne. Idan ka ga mutum yana fushi a wurin jayayya to, maras hujja ne. Idan ka ga mutum yana faxa, ba shi da abin faxi. Mai gaskiya ba ya tsoron jama'a. Mai hujja ba ya fushi. Mai abin faxa ba ya faxa! 62. Fulawa tana koya mana fara'a da murmushi. Tururuwa tana koya mana aiki. Zuma tana koya mana tsari. Zakara yana koya mana sammako. Kowace halitta da tata gwaninta. 11 63. Wanda ya fi kowa jin daxi a cikin mutane shi ne wanda bai damu da sha'anin mutane ba. 64. Ba duka wanda ka ke so ne yake amfanin ka ba. Ba kuma duka wanda ka ke qi ne yake cutar ka ba. Wuqa ko tana da laushi yanka take yi, magani kuma tare da xacinsa ana samun waraka a cikin sa. 65. Da zarar ka ji qarar wayarka ka san wani yana son magana da kai ne. Kamar haka ne da ka ji kiran sallah ka san ubangijinka na neman ka. Kada ka sanya karva kiran mutane ya fi ma ka muhimmanci a kan kiran Allah. 66. Sirri kamar dafi yake a cikin zuciyar Macce. Idan ba ta fito da shi ba sai ya kashe ta. Yana da kyau ka san inda za ka voye asirinka!. 67. ‘Yan uwan Annabi Yusuf sun yi niyyar kashe shi, Allah bai kashe shi ba. Sun so su qasqanta shi, Allah ya xaukaka shi. Su ka vatar da shi don mahaifinsu ya manta da shi, ya daina son sa, amma sai Allah ya qara masa son sa. Aka sayar da shi a matsayin bawa amma ya zama Sarki. Kada ka damu da sharrin xan Adam. Allah gatan Bawa. 68. Akwai miliyoyin halittun ubangiji waxanda ba su da aljihu, ba asusun ajiya a gida ko a banki. Amma ba su daina cin arziki ba. Kwantar da hankalinka. Arzikinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi halaliya, don ba ka wuce arzikinka. Saurin nema ba ya kawo samu. 12 69. A Hotel ake rubuta cewa, "idan mun burge ka ka faxa ma duniya. Idan mun vata ranka ka faxa mana". Wannan shi ne yadda ya kamata ka yi hulxa da kowane musulmi xan uwanka. 70. Abu xaya ne kyakkyawa wanda ko makaho yana iya ganin sa. Shi ne kyawon hali. Ka zama mai kyawon hali ba sai ka faxi ba mutane da kansu za su yabe ka. 71. Da dare kowa yana rufe qofarsa ne don tsoron mutane. A lokacin ne kuma Allah ya ke buxe qofofinsa don karvar mutane. Ko kana qwanqwasa qofarsa ta hanyar salloli da zikiri da addu'oi da tilawa a wannan lokaci? 72. Kada jin daxin wani ya tsone ma ido. Ba ka san abin da ya rasa ba kafin Allah ya ba shi ni'imar da yake cikin ta. Kada damuwarka ta tada hankalinka. Ba ka san alherin da za ta jawo ma ka ba. Haquri maganin zaman duniya. 73. Idan ka makara a wajen aiki kana jin kunyar shugabanka. Idan ka makara zuwa masallaci ko kana jin kunyar Allah? 74. Idan yaro ya yi wayo kyawonsa a sa shi makaranta. Idan ya girma kyawonsa a gan shi a masallaci. Macce ita kuma kimarta idan ta girma tana a gidan mijinta. 75. Kamilin mutum shi ne wanda ya tara ababe guda uku: Ga kyauta, ga dadin zama, ga kuma yawan ibada. 13 76. Rinjayar mai qarfi ba shi ne gwaninta ba. Gwani shi ne wanda ya iya bakinsa, ya rinjayi zuciyarsa, sannan ya ji tausayin na qarqashinsa. 77. Idan ka ga tururuwa ka xage qafarka don kar ka take ta, za ka gamu da rahamar Allah don ka ji tausayin wata halitta daga cikin halittunsa. To ya ya ka ke ji idan ka tausaya ma xan Adam mai daraja a wurin Allah? Ina kuma ace wanda ka tausaya ma musulmi ne mai fuskantar gabas ya yi sallah? 78. Zunubi da savon Allah suna cike da shu'umci. Sukan sa ka da-na-sani, ko su ja maka hasara, ko su hana ka riba, ko su mantar da kai wani alheri, ko su zubar da girmanka, ko su bayyana aibinka, ko su jawo rinjayar maqiyinka a kan ka, ko su tozarta dukiyarka. Ga shi kuma suna ja maka fushin Allah da tozarta a cikin jama'a. Nisanci zunubi don ka zauna lafiya. 79. Matsalolinmu a yau guda biyu ne: Mu yi aiki kafin mu yi nazari, ko mu yi ta nazari ba aiki. 80. Idan ka taimaki wani saboda Allah kada ka jira ya yi maka godiya. Yardar Allah ta fi yardar mutane. 81. Yana da kyau ka damu da damuwar xan uwanka. Abin da ya fi wannan shi ne ka taimaka ma sa domin ya fita damuwa. 82. Kyau iri uku ne: Akwai kyan jiki, akwai kyan hali, akwai na zuciya. Kyan zuciya shi ke sada ka da Allah. Kyan hali yana sada ka da mutane. Kyan jiki kuwa a kullum sai ya ja ma ka fitina. Duba tarihin Annabi yusuf Alaihis Salam. 14 83. Abin da ka koya da farko a cikin addini shi ne abin da za a tambaye ka a cikin qabarinka. Ba tarin ilimi ke da muhimmanci ba. Amfanin ilimi aiki da shi. 84. Magana tsuntsu ce. Idan ta fita ba a iya kamo ta. Ka iya bakinka don kada ka kwana cikin da-na-sani. 85. Wanda ya fi kowa girma shi ne wanda bai ganin girman kansa. Wanda ya fi kowa xaukaka shi ne wanda yake amfanin mutane. 86. Mace ta gari tana neman yardar Allah da biyan buqatar mijinta. A gidanta ba qazanta, a jikinta ba cuta, a waje ba a jin muryarta. Daga nesa idan ka hango ta ba ka gane ta saboda kamalar suturarta da kwarjinin hijabinta. Muguwar mace ita ce mai yawan kiran ciwo, mai gajiyar haquri, mai kaushin magana, mai dogon harshe, mai kukan qarya, mai tona asirin gida. 87. Mutum yakan qosa da quruciya, amma idan ya girma zai dawo yana begen ta. Yana qarar da lafiyarsa wajen neman kuxi sannan ya sa kuxi yana neman ta. 88. Wahaltattun mutane a duniya su biyu ne: Wanda Allah ya kawo lokacin abu ya ce ba za ayi shi ba, da wanda Allah bai kawo lokacin abu ba ya ce sai an yi shi. Ka yarda da hukuncin Allah, shi ne zaman lafiya a gare ka. 89. Babbar hasara a lahira ita ce ka samu ladarka a cikin littafin wani, ko ka samu zunubin wani a cikin littafinka. Kada ka zalunci mutane. Kada ka 15 shiga cikin haqqinsu. Idan ka yi haka za su washe ladarka ko su lafta ma ka zunubinsu. 90. Masoyinka shi ne wanda yake kare ka idan aka aibata ka. Maqiyinka a kullum fatar ya ke yi ka tozarta. 91. Rayuwa taqaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon guri ya xauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci wataqila shi zai zamo mabuxin aljanna a gare ka. 92. Sau da yawa mu ke kuskuren fahimtar mutane. Ma'aunin da ba ya kuskure shi ne ka ajiye kanka a matsayin wanda kake yi ma hukunci. 93. Idan ba ka son a soke ka kada ka ce komai, kada ka aikata komai. Duk wanda ya motsa dole ne sai an soke shi. 94. Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya kafin ta bar shi, ya gyara qabarinsa kafin ya shige shi, ya yi sallah a cikin jama'a kafin su sallace shi, sannan ya yi ma kansa hisabi kafin a gurfanar da shi a ranar hisabi. 95. Ba ka sanin daxin lafiya sai idan ciwo ya same ka. Ba za ka san daxin zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin daxin haxuwa ne idan rabuwa ta zo. 96. Idan kwalba ta fashe za a ji kukan fashewarta ne sau xaya amma za a taka ta sau goma. Haka mummunar magana ta ke idan aka faxe ta, za a ji ta sau xaya, amma za ta daxe tana zungurar zukata. 16 97. Aboki guda xaya ne zai taya ka kwanciyar qabari. Shi ne aikinka. Aikata alheri don ka samu aboki na qwarai a wannan kogo da ba shi da makawa. 98. Abu uku su na vata lokaci ne: Da-na-sanir abin da ya wuce kuma ba zai dawo ba, da neman yardar mutane gaba xaya kuma ba za ta samu ba, da haxa kanka da wanda ya fi ka kuma ba za ka cim ma sa ba. 99. Wanda ya fi ka wadata ba lalle ne ya fi ka arziki ba. Wadatacce shi ne wanda yake samun biyan bukatunsa. 100. Idan ka ga mutum yana sukar xan uwansa bai lura da nasa laifin ba. Ko sukar xan uwanka da ka ke yi shi ma aibi ne. 101. Wani aboki yana bin ka don ya koyi alherinka. Wani kuma yana bin sawunka don ya kama laifinka. Rinqa hattara da abokai. 102. Wani mutum idan ka yi ma sa alheri zai saka maka ne da sharri. Idan ka amfane shi zai cuce ka. Idan ka sa shi inuwa zai jefa ka a rana. Kada ka damu. Ka ci gaba da yin alheri, kowa halinsa ya ke yi. 103. Da yawa mutanen da muka san su, muka yi hulxa da su a yau sun riga mu gidan gaskiya. Idan yau mu ne, wata rana ba mu ne ba. 104. Idan ka ga mutane suna tururuwa zuwa gidanka abin buqatarsu ne Allah ya ajiye a wajenka. Idan ka rasa shi kowa zai kama gabansa. Kada ka 17 nemi hutu daga taimakon jama'a. Xaukakarka ita ce buqatuwar su zuwa gare ka. 105. A wuri uku ake sanin halin mutum: Idan aka ba shi aure, ko aka yi ciniki da shi, ko aka yi tafiya mai nisa a tare da shi. 106. Ba kowane lokaci ne mutane za su fahimce ka ba. Qaramar qwaqwalwa ba ta gane manyan kalamai. Babban kifi sai babbar gora. 107. Ana sanin darajar mutum ne ta hanyar halinsa ba ta hanyar matsayin gidansu ba. Gina kanka da kanka. Ka daina gadara da matsayin gidanku. 108. Da yawa waxanda ke ce ma 'ya'yansu: "Ina son ka zama Likita" ".. Ka zama Injiniya" ".. Ka zama Malami". Mutum nawa ne su ke ce ma xansu: " Ina son ka zama mai albarka, mai taimakon jama’a"? 109. Kada ka damu da cewa qarya ta miqe qafa. Tabbas qarya za ta gushe. Kada ka damu da tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana? Lalle za ta bayyana komai daxewa. Abin da ya kamata ya dame ka shi ne, mine ne matsayinka; a kan gaskiya ka ke ko a'a? 110. Rayuwa a kullum cikin canji take. Yaro zai girma, babba ya tsufa, mai lafiya ya yi ciwo, wani mai ciwo ya warke, rayayye kuma ya mutu. Lokacin da ka samu sannan wani zai rasa. Idan ka faxi wani ne zai tashi. Rungumi hukuncin Allah a cikin amincewa da yarda. 18 111. Alamun mai riya guda uku ne: A fili yana sallah, a voye yana wasa. Idan an gan shi an ga mumini, idan ya kevanta ya koma fasiqi. Bakinsa ya fi zuciyarsa qarfi. Allah ka kare mu daga sharrin riya. 112. Abu uku ba a wasa da su: Addininka, da qasarka, da mutuncinka. Abu uku ba a faxar su: Arzikinka da Iliminka da yawan shekarunka. 113. Ba kowace magana ce ake ba da amsar ta ba. Ko shiru magana ce. 114. Sana'arka arzikinka. Annabi Dawuda maqeri ne. Annabi Zakariyya kafinta ne. Annabi Idris maxunki ne. Annabinmu makiyayi ne. Nemi na kanka. Zaman banza babbar cuta ce. Arziki kuma zomo ne. Zomo ba ya kamuwa daga kwance! 115. Yi murmushi idan ka ga mai son ka, zai ji daxi. Yi murmushi idan ka ga mai qin ka, zai ji tsoro. Yi murmushi idan ka ga wanda ya bar ka, zai yi da-na-sani. Yi murmushi ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Murmushi kwarjini ne ga namiji, ado ne ga fuskar macce. 116. Makaho idan idonsa ya buxe karya sandarsa yake yi. Wani ma qona ta zai yi da wuta. Haka xan Adam yake da saurin manta alheri da qin tuna baya. Duk wanda za ka taimake shi yi ma sa don Allah. Idan kana jiran godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki. 117. Wawa ne yake faxin abin da zai aikata. Mai kuri shi yake bayyana abin da ya aikata. Mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa. 19 118. Gishiri da Sukari kalarsu xaya ce. Banbancinsu yana bayyana ne idan aka xanxana. Haka mutane su ke; sai an gwada akan san na qwarai. 119. Zama da mutanen kirki yana qarar da kai ababe guda shida: Son Allah, da bin Allah, da ambaton Allah, da gudun duniya, da son lahira da barin girman kai. 120. Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su. Akwai kuma ma su qin ka duk yadda ka kyautata ma su. Kowa da kiwon da ya karve shi. 121. Marar gaskiya kamar mai yagaggen wando ne, duk inda zai zauna sai ya rinqa kame-kame. Mai gaskiya a natse yake zamansa. 122. Ana gane mumini ne a wurare guda uku: Idan ya samu ya gode ma Allah, idan ya rasa ya koka ma Allah, idan ya shiga damuwa ya koma ma Allah. 123. Abubuwa uku idan suka haxu da wasu uku ba su da magani: Talauci idan ya haxu da kasala. Qiyayya idan ta haxu da hassada. Jahilci idan ya haxu da girman kai. Allah ka sa mu gama da duniya lafiya. 124. Abubuwa uku ba su da tsada: Ilimi da Lafiya da Sadaki. 125. Idan kuxi suka fara zance dole ne gaskiya ta rufe bakinta. 20 126. Tsare gaskiya ba ya hana rayuwa jin daxi. Qarya da zalunci da cin amana ba su kawo samu. 127. Abu biyu idan kana da su kai Sarki ne: Lafiya da wadatar zuci. 128. Duk abin da ya sa ka damuwa idan ka yi nazarin sa ya tava sa ka murna. A duniya babu abin murna na din-din-din sai dai a aljanna. 129. Qaramin yaro da Fensir yake rubutu. Idan ya girma sai ya koma ga Biro. Dalilin haka shi ne, kuskuren yaro mai sauqin gogewa ne. Goge kuskuren babba kam akwai wahala gare shi. 130. Mutane iri biyu ne: Wani yana rayuwa ne don ya ci, wani kuma yana ci ne don ya rayu. Koka gane bambanci tsakaninsu? 131. Zunubin da ya sa ka yin da-na-sani da komawa ga Allah ya fi ibadar da ta sa ka girman kai da xagawa! 132. Sarakunan da suka yi mulkin duniya duk sun tafi ba su san daxin duniya ba. Ba wutar lantarki, ba ruwan Firijin, balle kuma Fanka da AC. Ba su hau keke ko Mashin ba, ballantana motoci da jirage. Ba su san abin da ake kira Tarho ba ballantana wayar tafi-da-gidanka. Duk hasken gidajensu a wancan lokaci bai wuce na Kyandur da Fitila mai amfani da kalanzir ba. A yau kai Sarki ne amma ba ka gamsu da abin da ka samu ba. Idan kana da mota ta maqwaucinka kake kallo. Idan kana da gida na wani ke ba ka sha’awa. Oh! Allah Sarki. Xan adam da guri yake mutuwa. 21 133. Idan ka kasa gane wurin da ka yi shuka kada ka samu damuwa. Watarana ruwan sama ne zai nuna ma ka. Haka rayuwa take. Yau da gobe babbar makaranta. 134. Hattara da hawaye guda uku: - Hawayen iyaye da - Hawayen maraya da - Hawayen wanda ka zalunta. Kowanen su hawayensa na iya nutsar da kai a cikin tekun bala'i. 135. Mala'iku suna da hankali ba su da sha'awa. Dabbobi suna da sha'awa ba su da hankali. Xan adam ne Allah ya haxa ma sa guda biyun. Idan hankalinka ya rinjayi sha'awarka ka bi sawun Mala'iku. Idan sha'awarka ta zarce hankalinka ka shiga sahun dabbobi. 136. Karatu akwai wuya, ilimi akwai daxi. Nema akwai wuya, arziki akwai daxi. Zama da jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici. Haka duniya take, yaro vata hankalin dare ka yi suna! 137. Allah ya yi mana kunnuwa biyu da idanu biyu amma ya yi mana baki guda xaya saboda ya fi son mu yi kallo, mu yi saurare fiye da yadda mu ke magana. 138. Idan na qwarai da mugu suka haxu kowa ma yana iya gane bambanci. Amma a tsakanin na qwarai da wanda ya fi shi, da mugu da wanda ya fi, wannan sai masu hankali ke iya rarrabewa. 22 139. Ba a sanin matsayin saurayi sai ya yi aure. Ba a sanin halin talaka sai ya wadata. Ba a sanin gaskiyar xan Siyasa sai ya kai ga muqami. 140. Ba kowane wayayye ne mai ilimi ba. Ba kuma kowane mai ilimi ne yake da wayewa ba. Idan Allah ya ba ka ilimi nemi sanin duniya da zamanin da kake cikin sa, sai ya zama kana da haske a kan haske. Idan kuma kana da wayewa da sanin duniya matsa kusa da malamai ka qara sani, sannan ne wayewarka za ta amfane ka. 141. Idan kana son ganin yadda duniya za ta kasance a bayanka, ka duba yadda take a bayan mutuwar wani irinka. Za ka ga yadda masoya ke manta masoyansu, rigima ta harxe tsakanin magadansu. Wanda bai manta ka kawai shi ne Allah mahaliccinka. Manta da kowa ka nemi yardarsa. 142. Wanda ba ya sallah an haramta ma sa jin daxin duniya. Sannan zai gamu da wahalhalu a wurare guda huxu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin qabari da ranar hisabi. A duniya ana xebe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a qyamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wulaqanci da yunwa da qishirwa. A cikin qabari Allah zai quntata ma sa, a hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumarci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a baqanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla dalla, sannan a haxa shi da Zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai, Sallah ita ce ginshiqin addini. 143. Idan kana jin kaxaici ka tuna Annabi Adam Alaihis Salam. Ya zauna a duniya shi kaxai ba kowa. Idan ka sha wuya a wajen wa'azi da karantarwa ka 23 tuna Annabi Nuhu Alaihis Salam. Shekarunsa dubu ba hamsin yana wa'azi. Idan 'yan uwanka sun cuce ka ka tuna Annabi Yusuf Alaihis Salam. A cikin rijiya su ka jefa shi. Idan mahaifinka na tsanar ka a kan riqon addini ka tuna Annabi ibrahim Alaihis Salam. A kan haka ne ya sha wuya a hannun mahaifinsa. Idan ciwo ya addabe ka ka tuna Annabi Ayyub Alaihis Salam. Har sai da ya ji qamshin mutuwa a kan cuta. Idan matsalolin rayuwa sun dabaibaye ka, ka tuna Annabi Yunus Alaihis Salam. Kifi ne ya haxiye shi amma ya samu kuvuta a dalilin ambaton Allah. Idan an yi maka qazafi ka tuna iyalin shugabanmu ma'aiki Sallallahu Alaihi wa Sallam. Kwana hamsin tana cikin sunu da takaici sai da Allah maxaukaki ya wanke ta. Matsaloli da wahalhalun rayuwa ba su ne qarshen xan Adam ba. Manya ma sun gamu da matsaloli kala-kala. Abin damuwa shi ne matsalarka ta zama sanadin rabuwar ka da Allah mahaliccinka. 144. Abu biyu neman ka suke yi: Arziki da ajali. Arzikinka ba zai wuce ka ba, kai kuma ba zaka wuce ajalinka ba. Kada ka wahalar da kanka wajen neman abin da ke neman ka. Kada ka ji ciwon abin da ka rasa, idan naka ne zai dawo ma ka, idan ba naka ba ne dabararka ba ta kamo shi. 145. Idan duniya ta aure ka sai ta kwashe alherin mutane ta yava ma ka. Idan kuwa ta sake ka sai ta kwashe alheranka ta jefa ma wasu. 146. Lokaci kamar walqiya ne; ba ya jira. Ko ka ci moriyar sa nan take ko kuma ya tafi ya bar ka. 24 147. Wanda fuskar mata take ba shi sha'awa mata daya ba ta isar sa. Amma wanda kyakkyawan hali yake so xaya ma sai ta ishe shi. 148. Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauqi daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi. 149. Duk lokacin da fitila ta yi sama haskenta ya fi yaxuwa. Idan Allah ya daukaka ka, yi qoqari ka zamo fitila mai kawar da duhu da damuwa daga mutane. 150. Urwatu bn Zubair, ya gamu da jarrabawar ciwon Cancer a qafarsa. Da magani ya gagara sai aka yanke shawara aka cire masa qafar ga baki xaya. Amma a wannan dare bai fasa karanta abin da ya saba yi na Alqur'ani da Zikirin ubangiji ba. Duba ka gani, sau nawa ne qaramar matsala ta durqushe ka daga ibada? 151. Kyawon hankali ya riqa tunani. Kyawon harshe ya riqa faxin gaskiya. Kyawon Budurwa kunya. Kyawon Yaro biyayya. 25 152. Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi. Idan ka wadatu daga mutum za ka zama tsaran sa. Idan kuwa ka buqatu zuwa ga mutum, to dole sai ka zamo bawansa. 153. Tuntuven harshe ya fi tuntuven qafa zafi. Na qafa saurin warkewa yake yi, na harshe kuwa illanta mutum yake yi har qarshen rayuwarsa. 154. Ilimi ya fi kuxi, kuma ya fi mulki. Kai, har lafiya ma ya fi ta. Kuxi da mulki da lafiya duk suna gushewa. Amma Ilimi yana nan tare da mai shi ba su rabuwa. 155. Abin al'ajabi da lura: Masallatai suna cika ne bayan isowar liman, amma filayen qwallo suna cika tun kafin zuwan ‘yan wasa. 156. Kada lamarin duniya ya dame ka. Duk abin da ke cikin ta na Allah ne. Kada sha'anin arziki ya dame ka. Domin daga wurin Allah yake fitowa. Kada ka samu damuwa a kan gobe, domin a hannun Allah take. Abin da ya kamata ya dame ka shi ne, neman ka samu yardar Allah. 26 157. Karan dawa yakan sunkuya ne idan yana xauke da alheri. Idan yana fanko sai ka gan shi tsaye qyam. Ba kowane mai xaga kansa ne ya cancanci jinjina ba. 158. Mumini yakan yi adalci ko yana a cikin fushi. Yakan yi gaskiya ko yana a cikin matsi. Yakan daidaita ko yana a cikin damuwa. 159. Idan ka kwatanta kanka da rayuwar mawadaci ka lura ya fi ka, to ka duba yanayin ibadarka ko kai ka fi shi? Domin kada ya yi maka bugu biyu; ya ci nan kana kallo, a ranar lahira kuma ya shige aljanna ya bar ka. 160. Gurgu na gaskiya shi ne wanda ba ya zuwa masallaci, makaho na gaskiya shi ne wanda ba ya duba Alqur'ani. 161. Idan ka xauka cewa, ba ka yin kuskure to wannan shi ne kuskurenka na farko. Duk mutum xan tara ne, bai cika goma ba. 162. Kada ka bari girmanka ya faxi a kan kalma guda xaya da za ka sosa qaiqayin bakinka da ita. Kada ka bari tuntuve guda ya zubar maka da mutunci. 27 163. Kada ka sa ranka cewa mutane duk za su so ka. Zukatan mutane a kullum cikin Canji suke; abin da suka so yau, shi suke qi gobe. 164. Qauyanci shi ne ka yi kuri da babbar riga ko fankaceciyar mota ko danqareren gida a birni alhalin iyayenka na qauye suna cin busasshiyar gurasa. 165. Duk kyawon da kake taqama da shi duniya ke cinye shi. Duk kyawon da kake bukata, a lahira an yi tanadin fiye da shi. Me ya sa muke son duniya muna manta lahira? 166. Aiki kaxan mai xorewa ya fi yawan surrutu mai wucewa. 167. Mutane uku ne suke kewaye da kai: 168. 169. shi. Mai son ka tsakani da Allah. Wannan ka mutunta shi. Da makusancinka amma yana qyashin ka. Wannan ka yi hattara da 170. Sai maqiyinka wanda ba ya voye jin haushin ka. Wannan ka roqi Allah kariya daga sharrinsa. 28 171. Mai wa'azi ba shi yake hisabi ba, amma yana tunatar da kai cewa akwai hisabi a gaban ka. 172. Kada ka bayyana murnarka a gaban wanda yake cikin damuwa. Kada ka faxi yawan dukiyarka a gaban talaka. Kula da damuwar jama'a yana cikin alamun Imani. 173. Idan kana cikin jira, lokaci zai yi tsawo. Idan kana jin tsoro lokaci zai yi sauri. Idan kana ciwo lokaci zai yi nauyi. Idan kana cikin nashaxi lokaci zai gajarta. Lokaci da yanayi a tare suke tafiya. 174. Abu uku ba su amfani idan aka rasa abu uku: - Rayuwa idan babu lafiya - Da kuxi idan ba a kyauta - Da magana idan ba aiki. 175. Shan toka da tsare gida sukan sa a qosa da kai. Yawan raha da sakin jiki kan jawo maka wulaqanci. Ka lizimci tsakiya a komai, shi ne alheri. 29 176. Gaskiya ta fi tasiri idan aka sha wahala a kan ta. Sirri ya fi daxin ji idan aka inganta voye shi. 177. A kan pillow Sarki yake kwana. Haka shi ma talakka. Amma babu wanda zai ji daxin bacci sai wanda yake da kwanciyar hankali. 178. Mutakabbiri kamar mutum ne a qololuwar dutse; yana kallon mutane qanana a qasa, suna kallon sa xan karami. 179. Ba dole ne ka faxi duk abin da ka sani ba, amma yana da kyau ka san duk abin da kake faxi. 180. Tunaninka naka ne. Amma magana da zaran ka furta ta, to ta fita daga ikonka. 181. Duk wanda yake saurin amsa tambaya, lalle ne sai ya yi kuskuren bada amsa. 182. Duk wanda ya gudu daga aiki ya gudu daga hutu. 30 183. Kana da girma a idon mutane matuqar ba ka nemi abin hannunsu ba. Da zarar ka nema shikenan girmanka ya faxi. 184. Kuxi ba su da amfani sai an kashe su. Idan an kashe su kuma ba za su dawo ba, sai dai a sake nemo wasu. 185. Mai hasada ba ya haxuwa da abu xaya, ba ya rabuwa da abu xaya: Mai hasada ba ya rabuwa da kwaxayi. Ba kuma ya haxuwa da qoshin zucci. 186. Aikin da Allah ya fi so duka shi ne ka faranta ran mumini, ko ka yaye ma sa damuwa, ko ka biya ma sa bashi, ko ka raba shi da yunwa. 187. Wanda duk ya haxiye fushinsa Allah zai rufa asirinsa. Wanda kuwa ya biya buqatar xan uwansa Allah zai tabbatar da qafafunsa a kan siraxi. 188. Idan farce ya yi tsawo shi muke yankewa ba yatsan ba. Haka ne idan muka yi savani, kawar da shi ya kamata mu yi ta hanyar tattaunawa ba ta hanyar yanke alaqar da ke tsakaninmu ba. 31 189. Idan kana son sanin yadda ake gudun duniya ka zauna kusa da qaramin yaro ko kuma tsoho mai hankali. Na farkon bai san duniya ba. Na biyun kuma ya riga ya sallame ta. 190. Kiyaye ladarka kamar yadda kake kiyaye shexarka. Watarana shexarka za ta qare. Kuma daga nan ne ladarka za ta fara aiki. 191. Mutane biyu ne suka ci moriyar duniya: Wanda ya rubuta abin da ya kamata a karanta, da wanda ya aikata abin da ya kamata a rubuta. 192. Kada ka xauka cewa, duk wanda ya yi shiru kurma ne. Wani ya yi shiru ne yana jiran lokaci. Wani ya yi shiru ne don yana nazari. Wani kuma kawaicinsa shi ne maganarsa. 193. Abu uku sanin su zai amfane ka: - Duniya ba a tabbata a cikin ta. - Kuma babu hutu a cikin ta. - Sannan ba a tsere ma zargin mutane. 194. Idan za ka yi bacci kada ka manta abu uku: Alwala, da karanta Ayatul Kursiyyu, da kwantawa a hannun dama. 32 195. Mai hankali ba ya neman hutu a duniya. Yana tanadin ruhinsa wanda zai je sama bayan mutuwarsa, fiye da yadda yake tanadin gangar jikinsa wadda idan ya mutu za a rufe ta a cikin qasa. 196. Yawan jayayya alamar girman kai ne. Yawan surrutu alamar tavuwar hankali ne. Kawaici ado ne. Kyauta halin girma ne. Yafiya xaukaka ce. Yabon kai jahilci. 197. Sanin da ya fi kowane sani amfani shi ne ka san kanka. Ladabin da ya fi kowane ladabi amfani shi ne ka tsaya matsayinka. 198. Wanda ya wayi gari yana da abinci, ga shi kuma a cikin qoshin lafiya da aminci, a garinsu akwai kwanciyar hankali da kawaici, wannan ya gama haxa ni'imomin duniya. 199. Mantuwa ga xan Adam ni'ima ce. Ba domin mantuwa ba da rayuwa ta gurvace. 33 200. Wanda ya kame harshensa, ya kiyaye farjinsa, ya shiga taitayinsa, ba zai tava yin da-na-sani a duniya ba. 201. Ikon Allah: A da mutane suna rayuwa babu mota, babu wayar tarho, ba ruwan fanfo. A yau kuma mutane suna rayuwa babu qauna, ba mutunci, ba zumunci. 202. Masu hikima sun ce: Rayuwa ta tambayi mutuwa, me ya sa mutane suke so na, amma ba su son ki? Sai mutuwa ta ce, saboda ni gaskiya ce mai xaci. Ke kuma qarya ce mai cike da ado da xaukar hankali. 203. Idan ka xauki Alqur’ani Shexan yakan fusata. Da zaran ka buxe shi sai ya fashe da kuka. Kana yin Bisimilla zai faxi qasa warwas. Da ka shiga cikin karatu sai ya suma ya fita hayyacinsa. Mu yi qoqari mu rinjayi Shexan. 204. Mai hankali yakan gane ko wane ne kai daga maganar da kake yi a kan mutane ba daga maganar da mutane suke yi a kan ka ba. 205. Rayuwa gidan jarabawa ce. Da haifuwar xan Adam za a yanke masa cibiya, zai ji zafi yana kuka. Idan an naxe shi a tsumma zai samu takura, ya quntata yana kuka. A wurin shan nono zai gamu da wasu wahalhalu da 34 rashin jin daxi. Bayan haka zai sha wahalar fitar haqora, sannan faxuwarsu da sake fitowarsu. Idan an cire shi daga shan nono zai samu damuwa da baqin ciki wadanda ba su misaltuwa. Idan lokaci ya yi za ayi masa kaciya ya sha wata wahala sabuwa. Daga nan zai fara sanin wahalar tashin safe, da zuwa makaranta, da tsananin wasu malamai da tsarguwar wasu manyan xalibai, da takurar wasu abokai. Bayan ya girma akwai hidimar aure da zaven abokin zama a gaban sa. Sai rainon yara da hidimar tarbiyyarsu. Neman abinci, da gida, da abin hawa, wata damuwa ce babba. Idan tsufa ya zo akwai wahalar curutoci da jinya da raunin jiki. A tsakanin haka yakan gamu da ciwon kai, da ciwon ido, da ciwon kunne, da zazzabi, da sanyin mura, da waxansu curutoci daban daban. Idan ya zo mutuwa akwai jinya, akwai wahalar fitar rai. Sannan kwanciyar qabari da tambayar Munkaran da Nakiri. Bayan busa qaho akwai tsayin qiyama, da tsallakar Siraxi, da awon ayyuka. Mazaunin xan Adam na qarshe shi ne gidan aljanna ko na wuta. Kai, xan Adam! Ba ka da hutu sai ranar da ka yada zango gidan aljanna. Tashi ka nemi samun tsira. 206. Idan aka cuce ka, ka buxa baki ka ce: Allah ya isa, to fa ka xage kyas xinka ne daga kotun qasa zuwa ta sama. 207. Idan kana son sanin muhimmancin lafiya ka ziyarci asibiti. Don sanin daxin 'yanci ka je gidan yari. Wanda bai gane muhimmancin rayuwa ba ya je maqabarta. 35 208. Agogo yana zagayawa ne a kan kowace sa'a. Haka rayuwa take zagayawa da mu a kan yanayi daban daban. Yi haquri idan yanayinka a yau bai yi daxi ba, wataqila gobe ne za ka yi dariya. 209. Duniya kamar littafi ce; shafukanta yawa gare su. Wanda bai yawata ba zai san shafi xaya ne kawai na duniya. 210. Kibiya sai an ja ta baya sannan ake harba ta. Kai ma xan Adam wani lokaci kana buqatar ka ja da baya don cim ma buqatarka. 211. Idan ka qi gaskiya za ka faxa vata. Idan ba ka ji nasiha ba, za ka yi da- na-sani. Wanda bai ji bari ba ya ji hoho! 212. Abu huxu su ke maganin abu huxu: - Maganin gajiya bacci. - Maganin wahala hutu. - Maganin musiba haquri. - Maganin qiyayya kyauta. 36 213. Duk wanda ka haxu da shi akwai rawar da zai iya takawa a rayuwarka. Wani zai taimake ka, wani ya nemi taimakonka, wani ya so ka, wani ka so shi, wani ya amfane ka, wani kuma kai ka amfane shi. 214. Haifuwar namiji ba zavi ba ce, yin Allah ne. Amma zama Namiji qoqari ne, sai wanda ya dage. 215. Fahimtar sabon abu ba shi ne matsalar xan Adam ba. Babbar matsalarsa ita ce barin abin da ya saba. 216. Mai fushi da mai dariya, mai murna da mai kuka, duk ba za su hana duniya tafiya ba. Hutar da rayuwarka kada ka sa damuwa ta hana rayuwarka ci gaba. 217. Savani a tsakanin miji da mata ko 'yan uwa ba shi ne matsala ba. Babbar matsala ita ce mayar da savani dalilin adawa da gaba. 218. Kukan yaro qaramin abu ne yake jawo shi. Idan ka ga babba ya koka to lallai kam matsala ta vaci. 37 219. Sallah abincin zuciya ce. Idan abinci bai wadaci jiki ba yakan lalace. Haka ita ma zuciya idan ba a samu sallah mai kyau ba sai ta lalace. 220. Komai yakan fara a qarami ne sannan ya girma. Amma ban da abu xaya, shi ne; Musiba. Ita kam da girmanta take farawa. A hankali a hankali sai ta fara ragewa, har ta vace gaba xaya. 221. Duk abin da ya yi yawa zai rage qima in banda abu xaya, shi ne; Ladabi. Shi kam duk ya qara yawa sai ya qara daraja. 222. Duniya gonar lahira ce. Abin da ka shuka a nan shi za ka girba a can. 223. Kurma yana son ya ji muryar jama'a. Makaho yana so ya gan su. Bebe yana son yin magana da su. Duk Allah ya haxa maka wadannan a cikin "ji" da "gani" da "harshe". Ka gode ma ni'imomin Allah. 224. Ba za ka iya barin miki a jikinka yana tsiyaya ba. Haka ne bai dace ka zauna dumu dumu a cikin zunubi ba ka tuba ba. 38 225. Da yawan matsalolin da suke raba kanmu xayan biyu ne: Ko dai abin da ake nufi ba mu fahimta ba, ko kuma wanda muka fahimta ba shi ake nufi ba. Kyautata ma xan uwanka zato a kodayaushe, sannan ka nemi qarin bayani idan ba ka gane ba. 226. Kada ka yi dariya sai a kan dalili. Kada ka shiga cikin abin da bai shafe ka ba. Kada ka tambayi abin da ba ka da buqatar sa. Kada ka zauna da wanda ba ya voye asiri. Kada ka yi maganar da ba ta da amfani. 227. Ba matsala ba ce idan kana bin Allah amma ba ka samu biyan buqatarka ba. Tabbas watarana za ka samu. Babbar matsala ita ce kana savon Allah amma yana ba ka duk abin da kake so. Watarana idan ya damqe ka ina mai karvar ka? 228. Abu biyar ana gane su daga abu biyar ne. - Ana gane daxin bishiya ne daga 'ya'yanta. - Ana gane haqurin macce ne idan mijinta ya shiga halin talauci. - Ana gane mai imani idan ya gamu da jarabawa. - Ana gane mai kyauta idan ya samu wadata. - Ana gane gaskiyar xan siyasa idan ya ci zave 39 229. Wanda ya samu ababe biyar sai a masa san-barka: Macce ta gari, da xa mai ladabi, da aboki na kirki, da maqwauci na qwarai, da malami mai faxin gaskiya. 230. Ababe uku suna xaga darajar mutane uku: - Ilimi yana xaukaka qasqantacce. - Tsentseni yana xaga darajar mai ilimi. - Kunya tana qara qimar 'ya macce. 231. Abu uku suna vatar da wasu uku: - Kuxi suna voye aibi. - Gori yana rufe daxin kyauta. - Tsoron Allah yana voye son zuciya. 232. Ababe uku suna qarfafa wasu uku: - Lafiya idan ta haxu da arziki. - Bacci idan ya haxu da qoshi. - Dare idan ya haxu da ambaton Allah. 40 233. Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauqi daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi. 234. Babban mabuxin alheri shi ne Istigfari. Idan ka yawaita shi matsalolinka za su kau, damuwarka za ta gushe, sauqi daga ubangiji zai zo maka. 235. Rayuwa ta karantar da mu cewa, duk abin da yake xorewa sai an sha wahala wajen samun sa. Abin da duk aka same shi da sauqi kuwa ya fi saurin kubcewa. 236. Ya fi kyau ka haska kyandur guda xaya a kan ka la'anci duhu sau xari. 237. Duk abu mai daraja rufe shi ake yi. Daddaxan abinci a kwano ake sa shi. Ayaba da gwadda da kankana da abarba da Aful da Mangoro duk a lulluve mahaliccinmu ya yi su saboda darajarsu. Haka ne 'ya mace take, tsadarta ke sa ta yin lullubi. 41 238. Idan ka ga mutane suna yabon ka akwai alherin da suka gani a gare ka. Akwai kuma wani aibinka da Allah ya voye daga idanunsu. Ka gode ma Allah a kan suturar da ya yi maka. 239. Ladan yana Kiran sallah. Rediyo yana Kiran sallah. Kwamfuta tana yi. Agogon hannu da na bango duk suna faxa mana lokacin sallah. Amma duk da haka muna makara zuwa masallaci. Allah ya shirye mu. 240. Abokai na gaskiya suna da wuyar samu, suna da wuyar bari, suna da wuyar mantawa. 241. Maigida bango ne, mutan gida su ne allo abin jinginawa. 242. Halin ‘yan Adam akwai mamaki. Sai su ce Allah suke so, amma suna sava masa. A kullum suna la'antar Shexan amma kuma suna biye masa. 243. Zamani ya canza: A da idan ka zagi wani kowa sai ya kau da kansa. A yau idan za ka ci naman xan uwanka har ruwan wanke baki ake ba ka. 42 244. Mai sadaka ba kashe kuxinsa ne yake yi ba. Yana shigar da su ne a wani asusun ajiyarsa. 245. Abu nawa ne Allah ya ba ka baka roqe shi ba? Ka tabbata idan ya hana ka abin da ka roqa to, akwai dalili. 246. Da shekara Arba'in ake ce maka “Baba”. Da su kake yin furfura, ganinka ya fara ragewa, lafiyarka ta fara ja da baya. Da su kake gano daraja da matsayin naka iyaye. Idan ka yi Arba'in ya dace ka sake nazarin rayuwarka, ka shirya da ubangijinka, ka nemi gafarar zunubinka, sannan ka gyara aikinka. Allah ya bamu ikon gyara. 247. Mafi munin hali ga xan Adam shi ne Rowa. Abin da ya fi ta muni shi ne ka ba mutum sannan ka yi ma sa gori. 248. Idan ka qi gaskiya don gudun xacinta, ka xanxani qarya don kwaxan zaqinta, watarana sai ka nemi maxaci don ka wanke cikinka. 43 249. Abu biyu ne suke sanya aure ya yi qarko: - Idan ba ka da gaskiya ka amsa rashin gaskiyarka. - Idan kana da gaskiya ka yi shiru. 250. Duniya kamar inwarka ce; duk inda ka tafi za ta bi ka, amma idan ka tafi neman ta za ta riqa gudu, kuma ba za ka tava cim ma ta ba. Alhamdu Lillah Mu haxu a fitowa ta biyu cikin yardar Allah 44 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels