Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

AMINATU
Na Humaida mrs Kamal
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook Publish by www.hausaebooks.cf

[08/01 5:31 pm] +234 810 669 8241: [9/24, 3:12 PM] Mrs kamal: [9/24, 3:12 PM]
Mrs kamal: _1_
*A'minatu*
Gudu tak'e ba tsayawa! tana haki amma idan ta waiga sai ta k'ara rugawa da
gudu har takai titi ba tare da ta sani ba.
sak'a kai kawai tayi ji tayi kauuu mota ya kad'e ta innalillahi wa inna
ilaihi rajiun shine Kalmar da da`n saurayin yak'e fada! ya dauk'e ta yasa cikin
mota yaja zuwa asibitin mallam aminu Kano suna zuwa aka shiga da ita!
hannun
sa yasa
yaga bata ko numfashi nan da nan ya k'ara rikicewa, Dr pls save her
life karka bari ta mutu wlh bansan taba.
Ya shiga tashin hankali sosai sai addu'a yake Allah yasa karta mutu, bayan an
shigar da ita Dr yafara dubata ciikin ikon Allah ya samu tafara numfashi yayi
hamdala.
Ya barwa wata kyakkyawar Norse ta cigaba da duba ta shi kuma ya fito, d'an
saurayin na ganin shi ya rugo da gudu xuwa wajen shi, Dr marwan yajikin nata?
" biyo ni office Suna shiga Dr marwan yace have a site! ka kwantar da
hankalin ka fu'ad zata samu sauki cikin yardar Allah sai dai ta bugu Dan haka
tana bukatar Hutu kaje gida ka dauko Wanda zai dinga kulawa da ita.
" ok Amma Dr Dan Allah ka taimaka min ka kulamin da ita yanxu zan dawo.
Tun kafin Dr marwan yayi magana ya bude kofa ya fice yaja otar da gudu zai
tsaga kasa SBD gudu waiyooo ni fu'ad yazanyi da raina shin wazan dauko ya duba
baiwar Allah nan? tunani ya masa yawa kansa ya cushe ya tsaya agefen titi yana
xubda hawaye SBD tausayin kansa daya kamashi! wayar da tayi Ringing shiya dawo
dashi daga duniyar tunani a hankali ya dauki wayar amma yakasa furta kalma
daya!
What??? Subhanallah meya same shi na shiga uku ne fuad ya zanyi da raina ya
Allah ka kawo min dakarfi ya bugi sitiyarin motar!
Wani zazzafan hawaye na bin kwancin sa .
Taku
*Humaida (Mrs kamal)*✍🏼
[9/24, 3:12 PM] Mrs kamal: _2_
*A'minatu*
Yasa hannu yana sharewa shikan shi yasan yazama abin tausayi yasa hannu ya
kunna motar ya fara tafiya ahankali har ya isa wani katafaren gida
Mai dauke da kayan alatu na zamani horn yayi maigadi yazo ya bude masa gate yana
shiga ya bude mota dasauri ko rufewa baiyi ba yashiga cikin gidan yana ya kiran
phatty! Phatty! tana saida ya karaso cikin falon ya ganta kwance tana tauna
cwigam.
Phatty, bakiji ina kiranki ba, haba fu'ad kai kasan banason haniya ko ihu
amma meyasa kakemin, kiyi hakuri kuskure ne, dama....dakata banason complain
indai abinci ne kai kasan bani da lokacin dafawa, ta juya ta ka'ra gishin gida'
ya mik'e jiki a sanyaye har yakai bakin kofa ya sake juya yana kallon ta cikin
sanyin murya yace phatty I need ur help kizo ki taimaka min nayi accident a
hanya yana hawaye yana mata magana.
Sai a lokacin tad'aga ido ta kalle shi cikin k',asaita tace ayya sannu ko jeka
watsa ruwa ajikin ka zakaji dadi.
Nooo phatty na kad`e wata yarinya yanxu haka tana asibiti inason ki taimake ni

kije ki zauna da ita pls
Arazane ta juya cikin zafi take magana kaikasan bazan iya ba banason haniya kaje
ka roki inna balaraba nasan zataje Dan tanada tausayi amma nibada ciwo ba na
zauna a asibiti.
Taku
*Humaida (Mrs kamal)*
[9/25, 6:34 PM] Mrs kamal: _3-6_
*A'minatu*
Phatty! Me yasa kike min haka I'm not ur husband, a yanxu umarni nake baki ba
Neman shawara ba idan har baki zo mun tafi asibiti kin kula da baiwar Allah nan
ba kada nadawo NASA meki a gidannan.
Abakin auren ki fu'ad ni zaka gayawa Abakin aure na ai kasan nida kai mutu
karaba muje zanyi amma da sharadi idan zaka biyani zanyi idan kuma baza ka biya
ba, ba inda zani, yi hakuri muje zan biya hijabin tasa suka wuce asibiti tana
shiga saida gaban ta ya fadi ganin yarinya kyakkyawa akwance Wanda shekarun ta
bazai wuce 18 years ba ta matsa kusa da ita tace sannu baiwar Allah.
Da kai ta amsa mata yanxu ya kikeji ajikin ki ahankali ta bude baki tace dasauki
saidai ina tunanin halinda nabar Ummi na, nasan yanxu tadamu tasan halin da
nake ciki Dan Allah ki taimaka min.
Wani irin taimako zan miki baiwar Allah? Inason kije ki fadawa Umma ta abinda
yafaru dani,
Keee

dalla dakata niba surutu nazo kimin ba .

Karki damu zan kibari ki kara jin sauki saiki min kwatancen gidan naku
musu bayanin komai.

zanje na

Ngd sosai amma ya sunanka meya sa kike tambayan sunan sa kedai ki warke ki
k'ara gaba banason shishhgi .
Phatty why?why?? Meya sa baki da hakuri
Hmmm fu'ad na kasan ina sonka yazama dole nayi kishi da kai Dana zauna da
kishiya gwara nayi yawo tsirara,
Haba Anty meyasa zakice haka ai kishiya abin sone ko uncle hmm nikam ya sunan
ki? Sunana Amina amma ana kirana da meenat ko ummu ammara.
Fu'ad meye naka

na tambayar ta katafi mana ka barmu nizan kula da'ita.

Zan tafi baizama lallai nadawo ba kisani jin tsoron Allah shine abinda nake
fad'a miki kullum kizama mace tagari a duk inada kika tsinci kanki Dan Allah ki
rikemin amana banda Tara k'awaye a gida my phatty yau zan barki baizama lallai
na dawo ba.
Uncle ina

zaka? Ina ruwanki da inda zashi .

Taku
*Humaida(Mrs kamal)*
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: _12-14_
*A'MINATU*
Tunda Allah ya hada su , suke son junan su musamman maryam Wanda komai
zatayi Abba na yana ranta Sam batason Bacin ransa ko kadan , dakyar mahaifin
ta ya yarda ta auri Yahuza sunyi aure cikin so da kaunar juna.....

Suna matukar kulawa da junan su basa

son abinda zai tabi dayan

su......

Bayan auren su da shekaru biyu aka samu cikina murna wajan iyaye na da
kakan Nina bazai misaltu ba, dukkan kulawar su ya koma kan mahaifiya ta basa
son bacin ranta Wannan kulawar da ake bata dayawa shi yayi sanadiyyar dasa
kiyayyar ta a zuciya inna Zainabu ta tsane ta gashi dai ba gari daya suke ba
amma inna Zainabu ta matsa saidai su dawo kano da zama Abba na baiso haka ba
amma yazama dole yayiwa iyayen sa biyayya......
Tunda suka koma kano da zama mahaifiya ta, tayi ban kwana da farin
ciki. .....
In kinga tayi murmushi to da mijin tane inkinga kwallan ta to tabbas da inna
Zainabu ne, Watarana suna zsune sukaji sallama suka amsa yaro ya shigo yace wai
ana sallama da *maryam Rano* abin ya bata mamaki tana mik'ewa inna Zainabu ta
mike tana tafiya ta ingijeta gefe ina zaki?, *shan shani I mai kafar yawoo*
dalla matsa kibani guri na wuce...
Haka ta matsa mata tunda inna Zainabu ta fita bata dawo da wuri ba bayan ta
dawo take CE Mata wai Sagir yana gaisheta da murnan ta tashi tana cewa INA
shike? Allah sarki Yaya sagir....
Hhhhh gwanda ma ki koma ki zauna SBD yariga ya tafi ga abinda yace nabaki
nima na figi tawa rabon kuma inason kisani daga yau nima nazama matar yayanki
sagir saiki hadiyi yawu ki mutu .....
Tunda taji wannan maganar Cikin ta yafara murd'awa da karfi ta kwalawa inna
Balaraba kira tazo ta shigar da'ita d'aki cikin yan mintoci ta haihu...
Murna kam anyishi Dan harda mutanin Nasarawa sunzo duk Tsanar da inna Zainabu
kewa Umma ta baihana ta nuna tana matukar sona ba....
Ta shaku sosai sa yaya sagir soyayya mai karfi sukeyi a tsakanin su amma duk
da haka bata kaunar wani Dan uwan Umma ta yazo wajan ta...
Taku
*(Mrs kamal*)
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: _6-9_
*A'MINATU*
Pls don't go! Ka tsaya tare dani I need ur care, meenat kada kidamu nafasa
tafiya har sai kinsamu lafiya na maidake gaban iyayen ki daga wajan zan wuce.
Ngd Allah yasa maka da Alkhairi,
Fu'ad meyasa zaka fasa bayan kayi niyya
Karka damu zan kula da'ita har ta warke dakaina zan mayar
ta.

da ita gaban iyayen

INA xuwa Dr marwan yana kirana, fitar shi da kadan yadawo tare da paper a hannu
ya kalli meenat yace yan mata lafiya ya samu ko? Kwarai kuwa saidai nakara
godewa Allah .
Yanxu Ku had'a kayan Ku gida zamu gida sai kiyi wanka ki huta kibamu

labarinki.

Hmmm labarina? Ayya dama kabar shi dayafi Dan banason tunawa,
Bayan sun gama had'a kayan su suka shiga mota yaja zuwa gida.
My phatty naji bakice komai ba tunda nafara magana me kakeso nace bayan ka
wulakan tani agaban agola, Wacece agolar? *A'minatu* na Sam ba agola bane kada
nakara ji kin kirata da wannan sunan Dan bashi akayan ka mata ba.
Suna isa phatty ta ban kad'e kofa da karfi ta fita tana wani irin huci. Ya juya

ya kalli meenat yace kada kidamu kinji haka take zata warware, yafita ya bude
mata motar itama ta fitooo direct gefen sa ya wuce da'ita yanuna mata toilet
yashiga ta watsa ruwa ya dauko kayan phatty yabata tasa ta gabatar da sallolin
ta.
Yana zaune a falo ya kifa kansa yaji sallamar ta yad'ago ahankali ya zuba
mata jajayen idon shi dasu ka kumbura saida ta tsoro ta ganin irin kallon da
yake mata.
Ahankali takarasa tazauna suka fuskanci juna
magana,

cikin San sayar murya tafara

" Uncle fu'ad shin zan iya sanin *Labarinka* SBD na lura kana cikin damuwa Dan
Allah kafadamin ko da taimakon da zan iya maka.....
*TAKU*
*HUMAIDA*✍🏼(Mrs Kamal,)
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: _10-12_
*A'MINATU*
*farkon labarin na!*
sunan k'aka na malam musa ba fulata nin gombe , amma ya dawo Kano da zama
anan ya had'u da mahaifiyar baba na inna *Balaraba* sanidiyyar wani mako
cinsu , basu taba ganin juna ba har aka daura aure....
Amma inna Balaraba bata tab'a nunawa iyayen k'in wannan had'in auren ba
koda a fuska ,Mahaifin inna Balaraba shi yane mawa malam musa aikin yi,na sayar
da zannuwa a *kwantin kwari*bashida da matsala mutum ne mai
rikon amana ga
ibada...
Tunda malam musa ya auri inna Balaraba basu tab'a fad'a ba har Allah yasa
tasamu juna biyu murna wajan sa bazai misaltu ba, haka iyayen ta, lokacin da
ciki yakai 9months ta haifo d'anta kyakkkawa kamar baban sa...
Ranar suna yaci sunan mahaifin ta *Yahuza* basu canza masa suna ba saidai
inna Balaraba bata kiranshi da sunan saidai tace masa d'an juma...
Bayan shekaru biyar tasake haihuwar mace akasa mata suna *Zainab* sun taso
cikin tarbiya da girmama juna Iyayen su sun basu ilimin Arabic sosai....
Mahaifina Na da shek'ara a shirin yabar garin kano zuwa *Nasarawa state*
wajan abokin baban sa anan yasamu ya ci gaba da karatun sa....
Inna Zainabu Nada shekaru 16 aka aurar da In takaice miki mahaifina yasamu
karatu sosai kuma Allah ya hadashi da wata baiwar Allah mai suna Maryam Rano
mahaifin ta hamshakin mai kudi ne...
Taku
*MRS KAMAL*
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *16-18*
*A'MINATU*
Hakane my son I know! Umma ta wacece a falon ki? Hmm kajimin shu'umin yaro
phatty cefa bakaga kamar kawun ka ba..
Hmm lallai girman mata ba wuya Sam phay ta girma haka shine kota gaishe ni
kila itama bata gane ka bane...
Ni zan tafi idan kashirya ka same mu a big parlour , OK *A habbak'i* ya UMMI!
*A habbak'a* ya ~fu'adul huffaz~tana fadan haka ta fita bayan nagama na fito ina

xuwa nasake cin karo da phatty saida naji gabana ya fadi SBD yanda naga yarinya
kara shiga raina tayi tabbas nasan zan daukowa kaina dutsen dala ba gammu..
A haka NA zauna
kowa ya watse aka
fu'ad, thank u my
Hmmm nifa bancika

muka gaisa dasu Abba harda phattyn bayan mun gama cin abinci
barmu mu biyu tadago ido ta kalle ni tace welcome back Yaya
sst how is ur study? i hope everything is moving smoothly!
son yawan magana ba kawai ka ware zanyi bak`i...

Meenat a taikace Ashe phatty samarin tane zasu zo a gsky tun daga wannan
ranar naji na tsane ta har zuciya na SBD phatty ta dauko rayuwar ya hudawa
sosai gashi ba Wanda ya isa ya Gaya mata magana taji...
Kwatsam muna zaune aka kira family meeting muka hadu dukkan mu bayan kowa ya
zauna aka fara bude taro da addu'a Baffa yafara nasiha bayan yagama inna
Balaraba ta amsa saiji nayi tace idan mai duka ya kaimu watan gobe wato watan
azumin tsoffi da kwana 11 zamu aurar da yaran nan su biyu da sauri phatty ta
da'go kai tana tambayar inna Balaraba...
Waye mijin nawa?, kibari idan Allah ya kaimu ranar zaki Sani Mara kunyar
kawai....
Bayan mun tashi daga wajan meeting na koma gida na dinga tunanin dawa za
had`ani aure da wannan tunanin na kwana....
Washegari Umma ta, tashigo d`akina tace fu'ad nazo nan ne Dan gargadeka akan
batun auren ka duk matar da aka baka ka karb`a hannu bibbiyu da addu'ar samun
zaman lfy mai d`orewa ka mana biyayya insha Allah rayuwar ka bazaka tabe ba....
My son promise me, Umma ta na mika mata hannu tace promise? Nace promise
lovely mom..

my

Yauwa my son may God bless u Amin....
Tun nadawo sau daya naje gidan su inna Zainabu ina zuwa tamin zagin
wulakanci na fita tun daga wannan ranar ban sake xuwa ba....
Da ranar aure ya xagayo aka dauramin aure da.....
*urs*
Humaida (Mrs kamal)
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *18-20*
*A'MINATU*
Aka dauramin aure da phatty tabbas banyi farin cikin haka ba amma idan natuna
yadda girman yiwa iyaye biyayya yake sai nayi murmushi nayi addu'a samun
kwanciyar hankali tare da zaman lfy mai dorewa.....
"Bayan 'yan biki sun kawo amarya kowa ya watse sai ita kada'i, ko kawayen ta
ba'a barsuba ina zaune nida abokai na phatty ta kirani tacemin anbarta ita
kadai a gida kuma tsoro take ji...
Na tashi muka tafi abakin k`ofa nace wa abokaina su koma abinsu ngd haka kuwa
akayi.....
Nashiga da farin cikina ina zuwa na shiga d'akin
nayi mata sallama ta amsamin acikin k'oto...

da na tabbatar phatty na ciki

" d'aga idon da zanyi dasauri na sauke su k'asa sanidiyyar abin da idona yagani
Wanda bai tab'a ganin irin shiba hankali na ya gushe bansan lokacin da ledar
hannu na ya fad'i ba dasauri na tinkari wajan da phatty take na rik'e Mata hannu
nace...
Phatty na meye haka "why ar u crying waya tabamin ke?"

Bakowa kawai dai banason rabuwa da inna tane shiyasa
Hmmm 'yan Matan inna yi hakuri kinji taso muje muyi alwala muyi sallah....
Waiyo Yaya fu'ad cikina ciki kuma bude min nagani don't worry dear yadaina "noo
phatty pls open it let me see ",
Hhhhh nace maka I can't.
Saifa kin budemin na dubaki kar wani Abu yasameki,
Hmmm *Meenat*bazan iya gaya miki sauran ba *sirrine* amma ataikace phatty bata
bari ko nafila munyi ba tunda wani Abu yashiga tsakani na da'ita shi kenan
narasa gane kaina banajin maganar kowa saina ta Dana inna Zainabu 😭😭...
Bana xuwa gun Umma ta abin yana cimin rai narasa dalilin haka in takaice
miki phatty bata bani kulawa Sam ,SBD tunda mukayi aure ko b'atan wata bata
tab'a yiba....
Bansan ta inda Zan bullowa lamarin ba, yanxu haka kiran da akamin
sukayi Allah yayiwa Abbana rasuwa .....

cemin

*meenat* zantafi bazan dawo ba zan gudu nagaji da bak`in hali irin na ta Gashi
natsani xuwa garin mu idan ba phatty ce tacemin natafi ba,pls meenat ki
rok`amin ita ta barni Dan Allah...
Basai ta rok`eni ba katashi katafi zan kula da'ita kafin ka dawo ko kuma na
maidata village dinsu kada kamin musu Yaya fu'ad kasan ban da mutunci zan iya
komai akan ka....
Ke kuma idan zaki cire rai gwanda ki cire kallon kitse kikewa rogo, kada
kiyi wasan auren min miji, *Mijin phatty* dagani sai makara gwanda kije kiyi ta
tallan nono dagan nan kila kyasamu mashin shini inafatan kingane....
My phatty kinsan cewa ni mijin mace d`aya ne daga ita bak`ari Dan haka ki
kwantar da hankalin ki kamar kina jirgin sama mai ya k`are yanxu zan maida
meenat gidan su daganan zan wuce...
Urs
*(Mrs Kamal)*
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *20-22*
*A'MINATU*
"Zancen kake so wai ance da gauro ya iyali.
Haba sweety na kasan dai bazan tab`a yin abinda zaisa kaji haushi ba zan rik'e
*Meenat*tamkar k`anwata karka damu zaka dawo kasa meta cikin k`oshin lfy .
OK ngd Sosai zo muje muyi sallama ko phatty ta suka kama hanya xuwa da`ki suna
xuwa fu'ad ya juya ya rungume ta phatty I need u Dan Allah kada ki hanamin
hakki na kinsan zanyi tafiya mai tsawo..
Haba Yaya meyasa kafiye jaraba ne nidai gsky I'm not in the mood kayi hakuri
saika dawo, tashafa gashin kanshi tana mishi wani Shu'umin murmushi wanda ita
kadai tasan manufar yin sa,
Haba baby na Dan Allah kitaimakamin_naji anawa,
Ga *ATM* dina kicire yanda kikeso saida ta dauki ATM card din ta amince tanata
dariyar mugun ta, haka yagama yayi wanka ya shirya har ya shiga mota yaji bazai
iya tafiya batare da ya sallami meenat ba, sallama daya yayi ta amsa yashiga
ya zauna kusa da'ita Meenat ko kuma nace y`ar kanwa ta Zan tafi fadamin abinda
kikeso nadawo miki dashi...
Banason komai ka gaida min su Umma da kowa da kowa Allah ya tsare yasa katafi
lfy kadawo lfy, kada ka manta da karanta *subhanallah walhamudullah wala`ila ha
illallah wallahu Akbar*yazama abokin hiran ka acikin mota kaji ko uncle....

Zakayi?"zanyi meenat ngd da tunatarwa Zan ta tuna zakin muryan ki ma kobakya
so,?
Eh banaso kai dai katuna zikiri Dan shi zai fi maka tunanin muryan matar aure...
What😳? " Matar aure fa kikace???? " Matar aure fa kikace???
kwarai kuwa matar wani!!!
Mika mata wani Leda yayi ya fice dasauri ya shiga mota xuciyar shi na radadi
yarasa inda zaisa ransa yaji dadi..
Tabbas nakamu da sonki bazan yarda na rasaki ba sai bayan raina meenat shin
wacece keee, meye asalin lbrn ki????
Kubiyo mrs kamal Dan jin yadda zata kaya...
*Urs*
Mrs kamal✍🏼
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *28-30*
*A'MINATU*
Ina shiga motar na hangi kyakkyawa na ya fita daga motar cikin sauri na fita
gudu nakeyi har saidai na isa gareshi kamar Zan rungume shi yayi sauri yaja da
baya.
keeee lafiyar ki kuwa koba bakya ganine?" Yi hakuri Adam da...... Da me yi
maganar ki sauri nake number wayar ka zaka bani, OK yasa hannu a aljihu yacire
card yabani hmmmmm basai na fada maka irin farin cikin da nake ciki ba ka
k'iyasta da kanka ina koma wa inda akayi parking motar mu amma banga komai a
wajan ba na dauki waya na dialing number Abba na amma akashe dukkan nakira
number su switch up..
Hankali na ya tashi matuk'a nasan fushi sukayi Allah yasa ba sun bane, dakin mu
na nufa shima a kulle...
A hankali nata ka xuwa dakin wata 4rnd din mu mai suna *ILHAM* ina xuwa itama
bata nan amma dakin a bude yake saidai nakasa shiga ciki na zauna awaje fito da
card din da Adam yabani nayi na sa number shi a waya ta nakira ji nayi an rik'e
ni my love waya tabamin ke da sauri na kubce hannu na haba Na'omi how many
times will I have to tell u, kullum saina gaya miki niba yar iska bace kuma
addina yayi hani da haka ki kya'leni naji da d'aya.
Wani mugun kallo ta jefamin hmmm shame on u amina, amma kinji kunya ina mai
tabbatar miki bazan loosing aikina ba, yau dai ko kiso ko kiki saina kaiki
wajan Gabriel...
Na'omi will u get out of my sight, ko saina miki ih....jinayi an rufemin baki
tun daga lokacin ban sake sanin inda kaina yakeba😭
Haba my heart kar kiyi kuka mana kicigava da bani lbr

daganan

ina takaiki?"

Bude idon da zanyi SAI ganina nayi a d'akin su Gabriel hhhhh hhhhhh Amina
kinganki a gabana ko na gaya miki inason ki why don't u love me 2 i want u 2 be
my wife meenat..
How can I be ur wife Gabriel bazan taba son kafiri Mara addini irin kaba, c'mon
baby relax zaki soni idan nakoma addinin ki?" May be!
Hmmm yau zan aika ta sukayi wani shu'umin dariya kafin yak'ara cewa yau zan
cika burina ya matso kusa dani yaka Mani ina fisgewa pls kasakrni bana so, I
can't amina "I love u" pls save my life allow me 2 feel ur warm body....

*Urs*
*Mrs kamal*✍🏼
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *26-28*
*A'MINATU*
Kamar yanda kasani sunana Amina Muhammad, haifaffiyar garin kano sunan
mahaifina Alhaji Usman naira fitattacen d'an kasuwa wannan muna zama G R A
sunan Umma ta Aisha macen kwarai mai amana ga rik'on da addini uncle in short
zan maka SBD kar ANTY phatty ta shigo tasameni ina waya....
Mu HUD'u suka Haifa Yaya Suhail ne farko sai yaya Rayyan, Aminatu da Dan autan
mu Ashfaq duk cikin su nice kadai Mace Dan haka nazamo ya'r gatan kowa a gida
bansan wahala ba saidai jin dadin Rayuwa
banyi karatu anan Nigeria ba....
"A Dubai nayi karatu bazan taba manta wa ba watarana muna zaune nida kausar
saiga wani kyakkyawan saurayi ya wucemu saida na firgita da irin halittan da
Allah ya mishi na nunawa kausar itama ta jinjina irin kyansa bayan mun koma
gida na kwanta barci mai zaifaru Dana k'ulle idona wannan saura yin nake gani
idan nabude idon nasake k'ullewa murnushin sa nake sake gani Abu kamar wasa
yafara zama gaske danko a class nake bana iyayin komai sai tunanin sa gashi
narasa inda zan ganshi na duba naduba har na gaji tunda ga wannan lokacin
karatu na yafara Jada baya bani da aiki sai tunanin kyakkyawañ saurayi tun
kausar namin fad'a har ta koma yimin nasiha SBD abin nawa yakoma bata
tsoro......
Akwai wani ranar da natashi da matsanan cin zazzabi ban iya xuwa class
ba,kausar ce ta tafi cikin hanyar ta na dawowa ta had'u da kyakkyawa na Dan
sunan da nasa masa kenan da gudu tazo ta kirani saidai kash!
Ina xuwa yana
Jan motar shi banji zafi ba SBD ganin shi danayi SAI naji na warke daga zazzabi
ranar murna da annashuwa bazai misaltu ba....
Har kyauta nayiwa kausar muna dawowa saida nayi sallah raka'a biyu Dan godewa
Allah da yasa nak'ara ganin kyakkyawa na.....
Tun daga wannan ranar sonshi yakara shiga ta koda exam yazo Dana dauki talarda
da niyyar karatu SAI naji na kasa haka muka rubuta jaravawa cikin rashin
kuzari.....
Ranar da muka rubuta final paper nayi kuka kamar raina zai fita SBD nasan zanyi
nisa da kyakkyawa na kwatsam Saiga qatada yazo wajen mu, da sallmar sa......
Queen meenat meyasa ki kuka y'ar gatan kow.....kafin ya k'arasa na mik'e zumbur
na ruga da gudu suka biyoni ina anan ma nataka rashin sa'a ina xuwa yana
shiga motar cak na tsaya ina kallon shi na Lula duniyar tunani maganar qatada
ne yadawo dani, dalla malama Adam din ne kikazo gani shine kika samu gudu wlh DA
nasan shine bazan zoba Qatada me akace?" Kasan shine a'a ganin shi kawai nakeyi
a skul dinnan amma naji ana kiran shi Adam.....
Kinsan wani abun mamaki?"duk kyannan nashi Ashe Dan Nigeria ne. Haba Qatada ka
dube shi dakyau kagani ya maka kama da mutanin Nigeria dalla malam kar kuskura
ka zagi kyakkyawa na, idan har kanason na dinga kulaka....
Oh! Ni kausar meenat kin d'aukowa kanki dutsen dala ba gammu yazayi kidinga
son abinda baima
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment