Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BOYAYYEN AL'AMARI
Na SEEMALUV
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
T


‎khaleesat haiydar hausa novels*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*© ```Written```By*_Seemaluv_*Bismillahir Rahmanir Rahim...Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin K'ai...*01*A zaune Safna take saman tabarma rik'e da razor a hannun ta tana cire kumban k'afar ta, Sai Umma wacce take ta kara kaina a tsakar gida ' sai kuwa k'an nanta guda biyu Rumaisa da Anisa wad'an da suke wasan guje guje a tsakar gida.Safna ita ce babba a cikin su ' don kuwa zata kai kimanin shekara 20 cir, Rumaisa kuwa shekaran ta 17 Anisa 10.Safna, Rumaisa da Anisa marayu ne ' Mahaifin su yarasu sakamakon rashin lafiyan da yayi mai tsana ni.Hakan yasa karatun Safna ya tsaya cak tunda ta gama secondry school ' bata samu damar zuwa gaba ba, Kasan cewar matsalar rashin kudin da sukefama dashi.Rumaisa da Anisa kuwa ' a makarantar Primary suka tsaya, ba tare da sun cigaba ba ' sai makarantar allon da suke zuwa anan k'ofar gida.Rumaisa ita ke fita k'ofar gida tana suyan wara, A haka har tayi ciniki susami abinda zasuci.Ita kuwa Safna aikatau take zuwa mak'otan su, wani lokaci haka zata gama aikin ranar baza'a bata abinciba.Umma ce keta d'awainiya dasu da dad'i babu dad'i, Hakan baisa tayi wani auren ba ' wani lokuta ma 'yan uwanta ke d'an harhad'a mata kayan abinci."Safna ya kamata ki tashi ' ki tafi wajen aikin ki rana nayi".Inji Umma."Umma ranar ma tayi wallahi ' yanzu ina zuwa fad'a zasu rufeni dashi, Suda basu da uzri"."Baki da wani uzri ai lafinki ne ' bakison zuwa da wuri, Yanzu dai ki tashi ki d'auki hijabin ki ki wuce"."To shikenan Umma".Safna ta fad'i haka tana k'ok'arin tashi."Safna zan biki".Cewar Anisa."A'a kiyi zaman ki gida".Safna na fad'in haka ta mik'e tare da janyo hijab d'inta maroon colour dake saman k'ofa, Ta sanya ta fice.Haka ta kama hanya ' harta isa kusa da gidan ta had'e da k'awar ta tana fitowa ciki."Sumayya ya garin ne".Cewar Safna.Harare hararen da Sumayya takeyi ne ya d'aure ma Safna kai."Lafiya kuwa"."Lafiyar ta kawo haka!"."Tooo! Allah ya baki hak'uri sai anjima".Safna tana fad'in haka ta k'arasa cikin gidan, Kai tsaye ta wuce d'akin hajiya domin su gaisa.Bayan ta shiga ne Safna ta iske suna magana da babban d'anta.Haka ta zuk'unna har k'asa ta gaishe ta, Bayan sun gaisa ne ta tashi zata fita Hajiya ta tsaida ita."Safna tsaya tukunna"."To".Ta fad'a tare da komawa ta zuk'unna, Hajiya bud'e jakarta tayi ta ciro kudi kimanin dubu 2 ' ta mik'awa Safna, Haka Safna ta mik'a hannu ta amsa ba tare da tasan na menene ba."Safna ' wannan kud'in sallama ne, Bakison zuwa dawuri kuma bakison wanke mun kwanoni da kyau ' saboda haka na yanke shawarar cenja ki" ."Subhanallah! Hajiya don Allah kiyi hak'uri ki dawo dani ' wallahi Allah ina miki aiki dakyau, Yaune kawai na makara".Tana fad'in haka hawaye na zubo mata a ido."Nifa ba kuka nace kimun ba, Saboda haka tashi ki fita"."Hajiya kiyi mata afuwa mana".Cewar d'anta."Bana son iskanci kaji ko?"."Allah ya huci zuciyarki".Safna kuwa ganin bata da niyyar hak'ura ne yasa ta tashi ta fita, Harta kama hanyar fita taji motsi a kitchen alamar ana wanke wanke."Bari inga wacce aka cenja".Ta fad'a a zuciyar ta.Tana k'arasawa wajen taga mahaifiyar k'awarta wato sumayya, Mamaki ne ya cika Safna ' hakan yasa ta juya da sauri tabar wajen.Haka Safna ta baro gidan cikin wani hali ' tafiya kawai takeyi tana share k'wallar dake idon ta, Har ta isa gida cike da sallama a bakin ta.Umma ta iske ita kad'ai a tsakar gida tana surfa dawa."Wa'alaiki-salaam Safna, Lafiya kika dawo?".Matso murmushi tayi ta sakar mata ' amma sam fuskarta babu walwala, Tukunna ta k'arasa kusa da Umma wacce tayi kasak'e tana kallon ta."Am... Umma ga wannan inji Hajiya".Safna mik'awa Umma kud'in tayi, Umma ta lura idanun ta cike suke da hawaye."Tooo Kud'in aikin ki aka biyaki da wuri haka?"."A'a Umma, Kud'in sallama ce".Nan gaban Umma ya fad'i tayi sauri ta jinginar da tab'arya jikin bango, Gami da dafe k'irji."Uban me kikayi? Iyi Safna wane laifin kika aikata? Sata kikayi mata?".Jin an abaci sata ne ' yasa Rumaisa fitowa daga d'akin su cikin sauri, Ita kuwa Safna hawaye kawai ke mata zarya a fuska."Haba Umma! Ya za'ai kici taimata sata? Bayan kinsan halayen Yaya Safna kaf...".Idanun Umma ne suka ciko da k'walla, Rumaisa tasahannu ta sharewa Safna hawaye tare da janyo tabarma suka zauna."Yaya Safna meya faru?".Nan Safna ta fad'awa Umma duk abinda ya faru, Umma waje ta samu ta zauna cike da ajiyar zuciya."Yanzu abunda Hajiya zatai mun kenan?"."Umma karki damu ' insha Allah zan fita in nemi aiki,Kuma insha Allah bazamu tagayyara ba"."Rumaisa ina Anisa?".Inji Safna."Tana Bacci".Mik'ewa Safna tayi idon ta akan Umma wacce duk damuwa sun bayyana a fuskar ta."Umma ki bani koda dubu d'aya ne cikin kud'in, Domin zan hau adaidaita sahu ' inshiga cikin gari"."Hm... Yanzu idan kinje ina zaki nufa?".Cewar Umma."Umma manyan kanfanoni(Companies) zan fara bincikawa ' ni koda share share ne su bani"."Hm... Meyasa baki tunanin k'asa da wannan? Meyasa baza kije gidaje ba? Safna ina ganin kamar neman aiki a kanfanoni zaiyi maki wahalar samu".Rumaisa ce tayi saurin kutsa baki cikin maganar."Haba Umma fatan alkairi kawai zamuyi mata"."Hakane Rumaisa".Umma na gama rufe baki ' ta zari dubu ta mik'awa Safna, Ta karb'a sannan tasa kai ta bar gidan cike darashin sanin inda zata fara nufa.Bayan Safna ta fito ne ' tayi sa'a tasami adaidaita ta shiga."Ina muka nufa?"."Cikin gari zamu shiga ' kawai kaita kewaye da wajajen manya manyan ma aikatun nan".Haka mai adaidaita sahu yaja napep d'inshi Safna na ciki, Har suka isa cikin gari.Mai napep zagaye ya dunga yi da ita ' tana k'arewa kowacce ma'aikata kallo kasancewar Garin babban gari ne ba k'arya. Safna wani k'ayataccen company ta hango cikin garege d'inshi motocin ma'aikata ne birjit iyakar ganin ka.Hakan yasa Safna yin saurin tsaida mai adaidaita sahun."Bawan Allah mu tsaya anan, Nawa ne kud'inka?".Tayi tambayar tana k'ok'arin saukowa daga napep d'in."Gaskiya malama bisa adalci ' dubu d'aya zaki bani"."Haba kaikuwa? Har dubu d'aya? Ina laifin d'ari ukku? Kaga fa dubu d'ayan nan ita kenan mun, Kuma wajen nan zan iya kaiwa yamma"."Shikenan kawo d'ari biyar ' gaskiya iyakar abunda zan iya ragewa kenan".Inji mai Napep.Safna mik'a mashi dubu d'ayan nan tayi, Shi kuma ya bata cenjin d'ari biyar sannan ta juya ta doshi cikin company d'in.*DEDICATION..._My Family!_*....*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**2-3**_Pure Moment Of Life writers_*© ```Written```By*_Seemaluv_**2-3*Safna tafiya takeyi tana kallon yanayin Company d'in, Har ta isa bakin k'ofar shiga ciki ' jitayi ana."Hey! Hey!!!".Hakan yasa ta tsaya cak ' cike da fargaba, Wasu securities guda biyu sukayo kanta."Madam! How can we help you?".Nan bakin Safna ya hau rawa ' kasan cewar turancinkad'an kad'an take iya maidawa."Am... Sunana Safna ' nazo neman aiki ne a job".Nan securities d'in suka fara dariya tare da k'are mata kallo."Madam, ba'a d'aukan aiki anan, saboda haka ki tafi ki nemi wani wajen".Cewar d'aya daga cikin su."Don Allah koda shara ne zanyi muku ' sai ku rik'a biya don Allah".Tana gama fad'in haka suka rufe security door d'in, Hakan yasa Safna juyawa ta matsa daga wajen ' ta nemi waje ta zauna tana k'arewa motocin da ke wajen kallo.Bata ankara ba taji iskar hadari ta taso ' hakan yasa tabarin wajen cikin hanzari, Ta shige cikin wani garden wanda aka k'ayatar dashi matuk'a.Safna kujera ta samu ta zauna ' tare da d'aura kanta saman table, Haka akaita tsugaga ruwan sama ita kuwa tuni bacci ya kwashe ta a wajen.*35 MINUTES LATER*Safna taji ana buga table d'inda ta d'ora kanta akai, Hakan yasa ta farka daga baccin tare da d'ago kai domin taga waye.Wani Mutum ta gani sanye da suit a jikin shi ' Chocolate colour, Zubin masu kad'i."Who are you?".Nan nefa Safna ta kauda kanta daga kallon da take mashi ' ta koma kallon sama don duban hadari."Ashema angama ruwan!"Shima juyawa yayi ya dubi sama."Oh yes angama, and am advising u, koma wacece ke kibar wajen nan ' kafin nakira securities".Ai nan Safna ta mik'e tsaye gami da zaro ido."Don Allah ka taimaka mun! Wallahi aiki nazo nema ido rufe, Sir koda Shara ne zanyi muku sai ku biyani".Kujera yaja ya zauna, sannan yace."Hope kina da takaddun ki a hannu?"."Eh dasu nazo".Miko mata hannu yayi ta bashi takaddun nata ' ya duba tsaf sannan ya mik'a mata."Kamata yayi kije ki cigaba da karatun ki ' inyaso saiki dawo mu baki aiki"."Sir nidai a taimaka mun insamu da secondry schoolcertificate d'in"."Well... Is ok if that's what you want, Ammm are you good in making Coffee?"."Coffee?"."Yes Ruwan bunu"."Amm.. A'a...".Bata kaiga k'arasawa ba ya katseta da cewa."Then saikije ki koyo ' domin shine zai zama aikin ki dazaki rik'ayi a wannan Company"."OK! Na gode"."Am KAMAL ABUBAKAR ni ne mataimakin mai wannan Company ma'ana (P.A), You can call me Sir Kamal Ok?".Ta d'aga mashi kai alaman To."Sir, Yaushe zan fara aikin?".Murmushi yayi mata ' ganin ta cika sauri."Ai zaki fara ' har saikin gaji"."Hmm"."Yanzu tashi zakiyi ' ki biyoni mu shiga Office d'ina, Domin insamu wasu informations a tsanake.""Har ina ne wajen?".Kamal sauri yayi ya d'ago kai ya kalleta."Office d'ina mana!"."Hmm... Nidai da dai zamu iyayin komai anan"."What!? You are not serious!, Look inada aiki sosai a gaba na ' so ki tattara inaki inaki kibar wajen nan".Kamal tashi yayi cikin b'acin rai zai bar wajen tayi saurin rik'o gefen rigar shi, Gami da zubewa k'asa."Sir Kamal! Am sorry, ka taimakamun don Allah ' na yarda muje cikin office d'in naka amma kuma inaso ka rik'e Allah ya zuciyar ka"."It's Ok".Haka Safna ta bishi suka shige cikin ma'aikatar securities da sauran ma'aikatan kallonta kawai sukeyi, Ita kuwa Safna wurga idanu kawai takeyi tako ina har suka isa cikin Office d'in.Kamal a kujerar shi yaje ya zauna ' gami da zaro takarda, Sannan ya d'auki pen daga desk d'in shi, Zaifara rubutu kenan ya ankara ashe a tsaye take har yanzu."Madam!".Ta d'ago kai ta kalleshi tare da cewa."Sir!"."Zaki iya zama".Safna waje ta samu ta zauna ' sannan ta maida kanta k'asa Kamal
ya cigaba da rubutu.Sai da ya kammala ne ya d'ago kai ya kalleta tare damik'a mata takaddan."Am..ansa wannan ' zaki dawo ranar monday! Wannan takaddan itace zaki nunawa securities idan kinzo, Understand?"."Yes"."Good! But before then, Ya kamata inji sunan ki ' infact you have to introduce yourself to me now!"."Ok, Sunana Safna Habib! Ina zaune ne ana k'auyen GATORIYA, Kuma ni marainiya ce mahaifina ya rasu' sai mahaifiya ta wacce take d'awainiya damu..."."Ya Salaam! Allah yaji k'anshi"."Amin"."Insha Allah zaki sami aiki Safna ' Zanyi magana da Ogana kinji?"."Nagode"."Shikenan! Zaki iya tafiya yanzu".Safna tashi tayi rik'e da takaddan ta ahannu, Tabar Office d'in cikin hanzari tana fita suka ci karo da wani har suna bangazar juna.Wani Handsome guy ne ' mai kamala shima cikin suit, Fari ne zubin larabawa ' da bloothode d'in shi sanye a kunne, Matashi ne d'an kimanin shekara 30."Whattaaa!!!".Abunda taji ya furta kenan tajuyo cikin tsoro ta kalleshi."Kayi hak'uri don Allah"."What? Are you blind? Wacece ke? Daga ina? And who gave you the permission to...".Bai k'arasa ba tayi saurin katseshi da cewa."Ha'a bana baka hak'uri ba? Hmm".Tana gama fad'in haka ta juya ta wuce.Mamaki ne ya cikashi ganin yadda ta juya ta wuce without begging."Wace yarinya ce wannan? She don't even have manner, i will surely find out ' mtsww".Yana fad'in haka ya juya tare da sanya hannun shi cikin aljihu ya wuce.*DEDICATED TO MY FAN'S**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**4-5**_Pure Moment Of Life writers_*© ```Written```By*_Seemaluv_**4-5*Safna tana fita daga company d'in ta tsaya bakin titi domin samun abun hawa, Bata wani b'ata lokaci ba ta tari mai keke napep tai mashi kwatancen inda zai kaita ' kasancewar K'auyen su da cikin garin bashidanisa.Farin ciki ne cike ranta ' don kuwa ya kasa b'oyuwa afuskarta."Bawan Allah d'anyi sauri mana".Cewar Safna.Haka tasa mai keke-napep ya karawa keken shi gudu, Ita kuwa sai godewa Allah takeyi da k'osawa taga Umman ta.*AROUND 5:00PM*Safna ta isa gida ' nan ta sallami mai keke-napep sannan ta shige gida, Safna shiga tayi d'auke da sallama a bakinta ta iske Rumaisa tana jan ruwa a rijiya.Jin sallamar yasa Rumaisa d'ago kanta ta kalli Safna, Cikin jindad'i da nuna farin ciki Rumaisa ta aje gugar a gefe tayo kanta."Yaya Safna, sannu da dawowa ' Allah dai yasa antaki sa'a".Murmushi kawai Safna tayi gami da cewa."Umm! Ina Umma take?"."Umma tana d'aki tare da Anisa"."Ok".Safna da Rumaisa d'aki suka shige cike da sallama Umma ta amsa."Alhamdulillah Safna ya hanyar?"."Umma hanya lafiya k'alau, yana barku?"."Lafiya k'alau Safna, Allah dai yasa anci nasara!"."Insha Allah Umma".Cewar Safna.Bakin gado ta samu da zauna ' sannan ta cire hijab d'inta ta aje gefe, Tukunna ta cigaba da cewa."Umma! Kinga wannan takaddar?".Tayi mata nuni da takaddar dake hannun ta."Eh k'warai"."To mataimakin Ogan wajen ne yayi mun rubutu aciki ' yace kuma indawo ranar litinin da takaddar tabbas zan samu aiki"."A wane waje kika nema?".Cewar Umma."Umma a babbar ma'aikata ce (Company)"."Kinga Safna banason abunda zaije yajawo matsala?".Rumaisa ce tayi sauri ta shiga maganar."Haba Umma? Insha Allah babu wata matsala!"."To Shikenan! Allah ya shige mana gaba"."Amin"."Umma? Ina abinci na don nadawo da yunwa wallahi".Cewar Safna."Tuwo ne da miya gayacen ' ki d'auko kwano ki d'iba".Tashi Safna tayi gami da cewa To ta nufi wani d'an d'aki wanda anan ne suke aje kwanoni, Nan ta d'aukikwano ta dawo d'aki ta zuba tuwon taci.Bayan ta gama ne Umma tace."Safna?".Ta d'ago kai ta kalleta tare da cewa."Na'am"."Wai wannan ma'aikatar ta mecece?"."Umma ma'aikar tumatirin gwangwani ne"."To Allah yasa adace!".Rumaisa wacce ke gefe tana kallonsu ta amsa da amin.Safna suna cikin haka ne aka kira sallar magrib, Cikin nutsuwa gaba d'ayan su suka tashi sukayo alwala sannan sukayi sallah.Bayan sun idar ne Rumaisa ta tada Anisa domi itama tayi sallar.Atak'aice dai basu kwanta bacci ba saida sukayi sallar isha'i tukunna.Haka rayuwa tacigaba da juyawa ' da dad'i babu dad'i haka Safna da Umma ke fad'i tashi don ganin rayuwarsu ta inganta.*3DAYS LATER...*Yau take lahadi, Safna da Rumaisa tunda sassafe suka tashi suka fara aikin cikin gida ' kamar yadda suka saba, Sannan Umma ta tashi ta had'awa Rumaisa waran da zata sayar a k'ofar gida domin susamu su sami abinda zasu ci.B'angaren Kamal kuwa zaune yake cikin Office d'in shi yana danna laptop kira ya shigo cikin wayar shi, Ganin Oga ne yasa shi yin saurin d'agawa."Sir?"."Yes come to my office right now!"."Am on my way Sir".Kamal yana gama fad'in haka wayar ta yanke hakan yasashi tashi cikin hanzari ya nufi office d'in Oga.Kai tsaye ya shiga ciki ' ya sameshi a zaune saman kujerar shi ya juya baya."Sir, Am here".A hankali ya juyo ya kalli Kamal."Good! Zaka iya zama".Kamal zama yayi cike da ladabi."Kamal, Ina fatan komai suna tafiya yadda akeso?"."Eh sosai kuwa"."Good, there is a lady ' da naga ta fito daga office d'inka kwana biyu da suka wuce!"."Ohh Safna?"."I don't know!!!".Ya fad'i haka cikin fad'a da tsawa, Hakan yasa Kamal jin fargaba a cikin zuciyar shi."What did she think of herself? Who is she to you?!"."Sir am very sorry!"."Sorry for what? Me tazo nema?"."Oga, Aiki tazo nema with secondry certificate ' Sir please a taimaka mata marainiya ce! And is like itake d'awainiya da gidansu...."."So? What does that suppose to mean?"."Sir please ' yarinyar tausayi ta bani, Please koda coffee ne saita rik'a had'a maka ana biyanta sallary"."What??? Coffee? Did you just said Coffee? How? Wannan kucakar yarinyar? No no no! No way!!"."Sir! Bantab'a neman abu wajen ka ba narasa, Yakamata ka duba"."It's ok i will think about it! But mind you idan ma wannan ne ' then it would have to be competitive"."Hmm Okay Sir! Thank you... "."You may leave now! ".Kamal tashi yayi yabar office d'in cike da ladabi."Inhar Sunana *FAUZAN IMRAN!* then i will have to teach that what so called Safna ' a leason!, I will teach her how to respect her elders ' batada ladabi ko kad'an".Yana gama fad'in haka ya d'ora hannun shi saman laptop ya cigaba da advertising products d'in shi".*DEDICATED TO MY FAN'S*B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

© ```Written```
By
*_Seemaluv_*👄

*6-7*

Yana cikin hakan ne ' yaji ana knocking k'ofa, Nan take ya bada iznin shigowa.
Wata mace ce kyakkyawa slimly ajin farko ta shigo d'auke da murmushi a fuskarta, Shima ganinta yasashi sakin wani murmushi.
K'arasawa tayi ciki taja kujera ta zauna, Sannan ta aje handbag d'inta a saman desk.
"My Man!".
"Sweet-Suhailah, Zakizo shine baki kirani a waya ba?".
"Ehen, Am just missing you shiyasa! Kuma time d'inka kawai nakeso".
Ta fad'i haka cikin shagwab'a.
"You see?, Shiyasa naso ki kirani first kafin zuwanki ' and now ina abu mai muhimmanci kingani!".
"Akwai abu mai muhimmanci da yawuce ni? For God sake Fauzan ' meyasa yanzu nake rasa gane kanka ne?".
"You know what? Am a little busy now! Kije gida zanzo ind'auke ki mu fita".
Yana fad'in haka idonshi na kan laptop, Haka ta tashi ta d'auki handbag d'inta ta fice ranta a b'ace.
Wace ce Suhailah?, 'yace ga Alhaji Muktar. Ita kad'aice wajen mahaifinta, Mahaifiyar ta Allah yayi mata rasuwa tun tana k'arama.
Hakan yasa Alhaji Muktar shagwab'a ta matuk'a! Kasancewar shid'in mai kud'ine.
Haka company d'in Mr-Fauzan ya cigaba da yalwata da samun k'arin fasaha.
Mr-Fauzan saida ya tabbatar yayi announcing cewa ' zaiyi k'arin ma'aikata wad'anda suka kware a fannin had'a coffee.
Yana gama hakan ya rufe laptop d'inshi, Sannan ya d'auki wayarshi k'irar iphone7 da car-key d'inshi ya fito daga office d'inshi ' da alama gida zai koma.
Yana cikin tafiya cikin isa ' suka had'e da P.A Kamal shima yana fitowa daga nashi office d'in, Nan ya dakata cikin ladabi irin nasu na workers.
"Sir are you leaving?".
"Yes of cause ' yanzu nakeso in koma gida".
"Ok sir."
Nan Mr Fauzan ya juya ya fita daga company d'in.
Bayan fitarshi ne ya bud'e motarshi yashiga tukunna yaja cikin class ya nufi gida.
*Wane ne Mr-Fauzan?*, Mr-Fauzan mutum ne mai kud'i! Kuma mutum ne maison iyayen sa, Ya kasance d'an gata kuma shid'in kyakkyawa ne hakan yasa 'yan mata keson shi duk inda yaje, Amma saidai kash Mr-Fauzan mutum ne mai wulak'anci musamman akan mace.
Mr-Fauzan d'ane ga Alhaji Imran ' haka zalika d'ane ga Hajiya Saratu, Alhaji Imran da Hajiya Saratu 'ya'ya biyu suka mallaka arayuwarsu ' Mr-Fauzan da Khairat wacce take da shekara 19, Hakan yasa suka sami gata da duk wani abunda suke buk'ata na rayuwa!.
Kasancewar Alhaji Imran mai kud'ine cikin garin Kaduna yana cikin jerin mutanen da ake kwatance dasu, Amma saida Hajiya Saratu macece wacce bata k'aunar talaka ' batason talaka ya tab'e ta sam.
Mr-Fauzan yana yin packing ya fito cike da kuzari ya shige cikin gida, Da Mummy ya fara had'a ido wacce ke zaune a babban parlor saman kujera ' sai Khairat dake kwance ta d'ora kanta bisa cinyar Mummy.
Mr-Fauzan sallama yayi suka amsa tukunna ya sami waje ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya.
"Son da alamun kasha aiki a office d'in nan yau Right?."
Inji Mummy.
"Eh Mummy sosai kuwa."
Nan ya kalli Khairat wacce hankalinta ke kan wayarta k'irar iphone6+ ' tana chatting abunta.
"Ke bakisan kice sannu da dawowa bako?."
Cikin k'unk'uni tace.
"Sannu da dawo...."
Ta k'arashe maganar cike da zunb'uro baki.
Abunne ya bashi haushi ya zaburo zaikai hannu ' tare da cewa.
"Ke ni kikema k'unk'uni?."
Mummy ce tayi saurin shiga maganar da cewa.
"A'a banason haka! Karka sake! Daga dawowar ka?, Tashi ka wuce part d'inka Mairo tana nan zata kawo maka abincin ka."
Mr-Fauzan tashi yayi gami da cewa.
"Mum! Zaki jawa yarinyar nan tasha wahala a banza."
Harya kai bakin steps Mummy ta dakatar dashi.
"Son?."
Cak ya tsaya ya juyo ya kalleta.
"Na'am."
"Dawo inason magana dakai."
Dawowa yayi ya zauna a gajiye ' sannan Mummy taci gaba da cewa.
"Suhailah bata dad'e da barin nan ba! And tazomun da complain akanka, Son meyasa kakeyin haka?."
"Ohh Mummy k'arata ta kawo maki kenan?."
"Look Son! Banason haka ' kuma inaso ka gane Suhailah iyayenta suna da kud'i, Wace yarinya zaka kawo wacce zata fita? To bari kaji ingaya maka ' gwara tunda wuri kaje ku shirya da ita, Domin ni zuciyata ta ruga ta aminta da ita."
"Haba Mum, Nifa ba k'aramin yaro bane i know what am doing!..."
Yana fad'in haka ya tashi yayi tafiyar shi.
"Ohh haka zaka fad'amun? To bari Daddynku ya dawo zaka maimaita ai."
Mr-Fauzan yana shiga part d'in shi ya wuce bedroom d'inshi direct ya fad'a
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

8 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment