Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KABILARMU
Marubuciya
Maman shakur
Aisha muhammad
Publish:- http://fb.com/hausaebooks

KABILAR MU 1to10
Posted on February 3, 2016 by mamanshakur
[2/1, 6:37 AM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU 🌺🌸🌺
1
zaune suke shi da friends dinsa a gidan shashancinsu. duk suna ta shaye shaye
abinsu da ciye ciye, shi kam ya daura kafa daya kan daya a centre table ya
jinginar da kansa kan kujera idonsa lumshe kamar me bacci, bude kofa akayi wasu
friends dinsu biyu suka shigo da wata yarinya tana kuka sosai,tana tittirjewa
tana “plz kuyakuri,ku tausayamin,plz ku tausayama rayuwata,dan Allah karkumin
komi”, kuka take jikinta ko ina na rawa, duka samarin suka fashe da dariya banda
wanda idonshi ke lumshe har alokacin,daya daga cikin wanda ya dauko ta ya cire
mata hijab ya yar akasa yasa hannu yana shafa mata fuska yace”who told u munsan
Allah?ku musulmai ke bautama Allah bamu ba, and if u called his name again bayan
mun gama amfani dake saina yankaki”yana magana yana zare mata ido,ta rike
bakinta ta cigaba da kuka sosai, ta taushe bakin ta amma dukda haka kukan na
fitowa, sauran suka fashe da dariya harda tafawa,mutumin ya juyar da ita yasa
hannu zai zage mata riga yarinyan ta kwalla ihu tana kuka sosai mutumin ya wanka
mata mari….Wanda ya lumshe ido ahankali Ya bude idonshi yadaura su kan
abokinshi,akasalan ce yace” wot do u think u are doing Dave?trying to rape dis
small gurl or wot?”, Dave yace “but OLIVER am in d mood, muna bukatan mace, dont
stop us plz Oliver”,cikin daga murya yace” if u are in d mood,get amateur 4 ur

self, kabar yarinyan nan ta tafi right dis minute,tacika min kunne da ihu 4 god
sake”, ya ballamai harara yace”i mean it Dave let her go, right dis minute”,Dave
ya saki yarinyan ya koma yaja kujera daya ya zauna yana huci, sauran ma duk suka
daure fuska alamun basuji dadin yanda yahana su shanawa ba. yadan kalli yarinyan
ta gefen ido,yanda take kuka sosai jikinta na rawa ko ina,ya kauda kanshi da
sauri dan ya tsani yaga mace na kuka tadamai da hankali yake, komawa yayi ya
jingina da kujera ya lumshe idonshi sanan yace “u can go”, da sauri yarinyan
tadau hijab dinta tafita daga dakin da gudu.
Mikewa yayi, ya kwashi wayoyin shi,da car keys yafara tafiya harya kai bakin
kofa ya juyo yace”disgusting, I don’t know wot d heck u guys saw on her body,me
zakuyi da karaman yarinya?me take dashi?mai zata baku?u bunch of fools” yay
tsaki ya kada makulle ya bude kofa yafita.
ERAJ kiyi sauri ki gama wanke wanken kar Malam ya zanemu yau kinsan munada
nahawu,Eraj ta turo baki tace “nidai wlh banison nahawu ko kadan ya cika ban
wuya…. wata mata Fara bazata wuce 40 ba tafito daga daki tace “Eraj kedawa kike
surutu?,bazakiyi sauri ki gama bako saikinyi lattin islamiyya”,tace “Amma nida
Rahma ne”,Rahma da sauri tace “Amma ina wuni”,Amma tai murmushi ya mamanku
Rahma?tace” lpy lau Amma,tana gaidake. Amma tace “kinga Eraj zata saki latti ko,
tace “bakomi Amma namaso na tayata amma taki,wai zan jika kayana”,Amma tace
“Eraj barmin wanke wanken tashi ku tafi”,da sauri ta tsame hanunta ta mike, ta
shiga dakinsu Amma ta kwanta tana karatun wani littafin adduo’i, Eraj tazo ta
tsaya agaban ta tace “Amma dan budemin zip nakasa”, Amma tace wai yaushe zaki
girma Eraj kullum saina zage miki zip din kaya”, Eraj ta buga kafa akasa cikeda
shagwaba tana uhm uhm,ni bazan girma ba,banason na girma”, Amma ta dungureta
tace” juya joor,see her mouth”,Eraj tai dariya tajuya Amma ta zage mata zip
din,doguwan rigan ta cire gaban Amma “”ni m shakur dake dauko muku rahoto saida
taban kunya””ta dauko kayan makaranta tasa abunta tadau jaka da sauri tace “Amma
natafi”,Amma tace “adawo lpy tabi yar nata da kallo idan da sabo ta saba Eraj
agabanta take cire kaya tasa wani batare datai lullubi ko wani abuba,murmushi
tayi ta kwanta tacigaba da karatun ta, Eraj tasamu Rahama a tsakar gida taja
hanunta da gudu tace”muje kafin afara tsaron latti”.
Maman Abd Shakur😘
[2/1, 8:40 AM] Aishat muhd:

🌺🌸🌺KABILAN MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺
2
Karfe 6 suka tashi daga makarantan, suna tafiya suna hira sama sama, Eraj ta
zaro ido waje tace” nabani! Da sauri Rahama tace “maiya faru?”tace Wlh na manta
banyi assignment din Biology naba,kuma malamar muguwa ce”,Rahama tace “toya
zakiyi?”Eraj idonta ya ciko da hawaye tace “I dont know,tace muyi diagram of
flame cell harda label kuma banda text book, Amma tace zata saimin amma har
yanzu bata samu kudi ba”, Rahama tai murmushi tace “guess wot?”Eraj tace “dis is
not tym crack jokes Rahama,wlh gobe zansha duka”,Rahama tace dalla inada
biology text book yanzu, jiya baba yasaimin da sauri Eraj ta share dan guntun
hawayen ta ta kankame Rahama u are d best friend ever,Rahama tace”Eraj kan hanya
fa muke ana kallon mu da sauri Eraj ta saketa tace “muje gidanku na karba naje
nayi”,gidansu Rahama taje ta karbi textbook din koda ta isa gida an idar da
sallan magrib.
Salla tafara yi ta cire kaya sanan ta dauko jakan makaranta tace”Amma Rahama ta
aramin textbook nayi assignment da akabani a school”Amma ta shafa gashinta
dayakai har tsakiyar bayanta tace “Eraj karki damu idan nasamu kudi zan saimiki
duka textbooks kinji my baby”,Eraj ta daura kanta ajikin Amma tace “Amma
bakomi,i understand”,Amma ta dagota oya maza ki gama assignment din gobe da
sassafe ki kaimata textbook din.
Washegari da asuba Amma ta tasheta tayi salla suka karanta al qur’an, bayan sun
gama ta gyara daki tayi sharan gida Amma ta dama mata koko taje tai wanka tasa
uniform yellow long sleeve shirt, sanan ta daura royal blue sket tai tokin dan
ka’idan makaran tansu kenan,tasa karamin white hijab dinta iya kafada, tadau
covers dinta da white socks tasa ta goya jakan makaranta tafito tsakar gida tana
gudu Amma dake gaban murhu tajuyo tace “zonan Eraj”,ahankali tazo ta tsaya tace
gani Amma, Amma ta daure fuska tace”ban hanaki gudu ba,by d way kinma sha kokon
dana dama maki?Eraj ta turo dan bakinta tana girgiza kai, batare datace
komiba,Amma tace wai mesa bakison cin abinci ne, wuce kije kisha kafin na saba
miki”, tajuya idonta ya cika da kwalla taje ta zauna tasha kokon da kyar dan

bataso tafito tace “Amma nagama sha”,Amma tace “yauwa ko kefe oya tafito Allah
bada sa’a kiyi karatu da kyau ba ruwanki da mazan class kinjiko my baby”, Eraj
tai dariya tace “to Amma bye-bye” tafita da sauri dan school bus dinsu ya iso ta
shiga suka wuce.
Bayan fitan ta Amma ta sauke ajiyan zuciya ta kashe rushin takoma daki tadau
hijab dinta tasa tafito ta kulle kofar gidansu. tafiya kadan ya kaita gidansu
Rahama ta shiga da sallama lokacin maman Rahama na kitchen tace”marhaban dasu
lale Amman Eraj yau kece agidan namu shigo shigo” Amma tai murmushi tabita suka
shiga daki,ta kawoma Amma breakfast Amma tace wlh nakoshi nagode.
Maman Rahama ta matso kusa da ita tace “Amman Eraj da matsala ne na ganki wani
iri meke damunki?”
Amma ta sauke ajiyan zuciya tace”M Rahama nazo neman rance ne,rancen dubu biyar
inaso nakai Eraj asibiti ne”,M Rahama tace “subhanallahi Eraj batada lpy ne?
jiya naganta tare da Rahama a gidanan da yamma maiya sameta?Amma tace “ba ciwo
take ba M Rahama,asibiti nakeson na kaita adubamin ita nadamu shekara 16 amma
har yanzu bata fara al’adaba,yarinya na ss3 abun yadamen duk sa’oin ta sun fara,
inason na kaita asibiti idan ciwo take dashi tun wuri munemi magani”, M Rahama
tace “amma akwai wasu matan da haka Allah yake halittan su basayi” Amma cikeda
damuwa tace nasani amma ko shine gwara na kaita I should seek medical
advice,narasa mijina banason sake rasa yata ita kadai garen”, M Rahama tace” Ina
bayanki aminiyata”ta mike ta shiga dakinta tafito da wasu yan dubu daddaya gudu
uku tace wlh su kadai gareni ki karba kuje asibitin haka dashi In sha Allah Eraj
bata da wani matsala,Ammi tace nagode M Rahama Allah bar zumunci ta karba,tai
mata sallama ta tafi gida.
Maman Abd Shakur😘
[2/1, 9:46 AM] Aishat muhd:

🌺🌸🌺KABILAN MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺
3
Wuraren karfe daya lokacin ana short break taji cikinta na mugun ciwo da sauri
ta tsugunna akasan kujeranta,yarinyan dake kusa da ita tace “Eraj Ibrahim
menene, baki da lpy ne?” Murya chan kasa tace “Mermu banda lpy ne”, da sauri
Mermu ta tsugunna kusa da ita cikeda damuwa tace “meke miki ciwo?”,tace “tun
muna assembly cikena ke ciwo kadan kadan yanzu naji yakara ciwo sosai”, tafaeshe
da kuka ta rike cikin” Mermu tace dadina dake Eraj shegen son kuka”, tashi muje
school clinic adubaki”,ta kama hanunta da kyar ta iya tashi, amma saime zasuka
gani duk kasan kujeran yabaci da blood, Eraj ta zaro ido tace “Mermu me wanan
daga jikina ne?nabani ta rirrike Mermu”, Mermu tace “zauna u can’t go outside
ahaka,Allah yataimake kima babu kowa a class bari naje clinic na duba idan Allah
yahada ni da kind Dr zai biyoni adubaki anan”, Eraj ta zauna akan kujera ta
fashe da kuka ahankali ta kifa kanta kan table tana rike da maranta.
Clinic din school din nadadan tazara, dan bangare daban suka gina clinic
din,Babban clinic ne manyan likitoci aciki. Direct office din Dr Tara tatafi
wanda take in charge of any matsalan ko ciwon Female student din school din amma
kafin ta shiga secretary ta ta tsayar da Mermu tace Dr Tara has travelled but if
u need anything go to office number 4. Mermu tace Tnx tajuya ta tafi office
number 4, kasan 4 din taga anrubuta Dr Oliver. Aranta tace waye kuma Dr Oliver?
duk yanda akayi new Dr ne dan bantaba ganinshi ba kojin sunanshi bama,ta sauke
ajiyan zuciya ohhh I hope he is good and kind Dr.
Ahankali ta daura hanunta kan kofan tai knocking, tayi kusan sau uku sanan taji
ance come on in. Ta bude kofan ta shiga ta tsaya jikinta na rawa saboda wani
kwarjini daya mata dukda bai dago fuskanshi ba, saida yagama danne dannen laptop
sanan ya dago kanshi yace “yes”. Mermu dake watsa da yatsan ta ta dago kanta ta
kallai da kyar bakinta ya iya fadan good… go..morning sir.. tunda take anya ta
taba ganin kakkyawa irin wanan kuwa? matashine yanada kauri gashi Fari, ga fadin
kirji,yanada manyan idanu da dogon hanci yana da dogon saje saida baida gemu ko
kadan,lips dinshi pink sosai kaman bature.yana sanye cikin dogon wando baki sai
royal blue long sleeve shirt ya daura lab coat fari asama, wani katon sarkan
cross ne awuyanshi wanda ya sauka har kirjinshi daga gani kasan da gold aka
kerashi,yayinda kunnenshi daya ya makala dan karamin dan kunnen gold mai kama da
dan makale. Ganin taki magana tana kallonshi yasa yacigaba da danne dannen
dayake. Da sauri tace sorry sir.
Ya sake dago kanshi akaro nabiyu yace mekike so?,uhm sir a student is sick and
she needs medical attention..yace so?ta danyi tari adan tsorace tace” tana

class, yace “go and get her”,ta dukar da kanta tace ta bata kayanta saisa takasa
zuwa,yamata wani mugun kallo so ni kikeson naje har class nadubata,da sauri tace
no sir, ya nuna mata kofa yace “get out of my office”, da sauri Mermu tayi
hanyar fita, har zata bude kofa tajuyo tayi fuskar tausayi sir plz she is
undergoing a lot of pain, she is crying,she needs medical attention plz plz
plz.
Yajima kafin ya mike tsaye daga bisani yace”less go” tana gaba yana tafiya na
kasaita students sai kallonshi suke wani Dr ne wanan?
Suna shiga ajin ta kaishi gaban Eraj da kanta kekan table sai kuka take,suka
tsaya agabanta, Mermu ta taugunna tace”Eraj Dr is here,tashi kimai bayanin yanda
kikejin ciwon” students duk suka shigo class wasu na leke ta window kawai dan
suga me wanan kakkyawan likitan yazoyi a class. Eraj ahankali ta dago kanta
idanunta sunyi ja sunyi luhu luhu, gashin gaban goshinta sun kwanta sunyi lub
dasu, ta kalli Mermu tana jan kuka tana share hawayen ta da bayan hannun ta,
tana dan turo baki, Dr Oliver hanunshi yasa a aljihun wandonshi yana kallon ta
yay shiru yama kasa magana, Mermu tace “bazakiyi magana ba Eraj kin tsaya kina
wani kukan”, dago kanta tayi hawaye na gangara daga idanunta na dama ta sauke
idanunta akan Dr Oliver tace “good morning..s…I..sir”.
Maman Abd Shakur😘
[2/1, 9:32 PM] Aishat muhd:

🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺
4

Muryanta ne yafara rawa saka makon yanda taga yana kallonta,gashi ya cika mata
ido,kuka ta cigaba dayi ta rike cikinta,ahankali ya tsugunna agabanta ya kalli
fuskan ta yace”shiiii”,ya daura yatsan shi akan bakinshi yana kallonta, hadiye
kukan tayi da sauri tana wiki wiki da ido,Yace”tell me ya yake miki ciwo?”, tai
raurau da ido sanan ta bude baki ‘cikina ne, and uhm uhm saikuma takara fashewa
dawani kukan,takasa fada. Dukar da kanshi yayi ya fuzar da iska,only inda ace
zatasan yanda kukan mace kesa hankalinshi yatashi da bata yiba,barin ma nata
dayake ji har ranshi.Daure fuska yayi ‘ inkina so nabaki magana just keep quiet
kidena min kuka,kindly stand up,mutafi clinic nabaki magani.hadiye kukan tayi
ta mike tsaye,saita koma ta zauna da sauri ganin yanda kujeran yabaci, tabude
baki zatai bara kuka ya balla mata harara ta hadiye kukan, mikewa yayi ya bude
boturan lab coat d jikinshi ya cire, hannunshi biyu yasa ya dagota da sauri ta
daga jajayen idonshi ta kalleshi,shima kwayar idonta yake kallo,ta sauke nata da
sauri, lap coat din ya daura akan kafadanta yace “put dis on,cover ur sket”
yajuyo yacema Mermu clean up dis mess,ya kalli Eraj less go,yay gaba, da sauri
ta gyara lab coat din ya rufe duka bayanta har gwuiwa yakai mata, ahankali take
tafiya har tabar ajin aka bisu da kallo, da kyar take daga kafa saboda wani irin
ciwo datake ji. Yana gaba tana baya har sukakai office dinshi ya bude suka shiga
bai cemata ta zaunaba taga yadau waya yana dannawa,ahankali ta tsugunna ganin
tana neman faduwa ta cusa kanta acinyoyin ta tana kuka kasa kasa,wanan wani irin
likita ne mai wulakanci?yana ganin ina ciwo ya shareni,wai inama Dr Tara?.
Jitayi anbude kofan office din saikuma taji kaman ankulle,bata damuba ta cigaba
da kukan,kafadanta ya rike ya dago ta,da sauri ta matsa baya tana kallonshi taga
ita yake kallo,mika mata abu yayi acikin leda, yanuna mata bathroom din office
din yace go and change, kadan kadan take tafiya harta zo gabanshi ahankali ta
mikamai hannu, dan murmushi yayi yasa mata acikin hannun tajuya da sauri ta
shiga inda yace mata, sabon school sket ne aledan,da pad da wando,da sauri ta
shirya kanta tadau tsohon sket din tasa aleda saikuma taji tanajin kunyan fita,
ta tsugunna abayin tana mukurkusu ahankali take kiran ‘wayyo Ammana,cikina zan
mutu kizo.
Jinta dayayi shiru yasa ya mike daga kujeran dayake, batare da tunanin komiba ya
bude bayin ya shiga, ya daure fuska yana kallonta mekikeyi abayi?ta kwalalo ido
muryan ta narawa tace dama yanzu zan fito, yajuya yafita tabi bayanshi ya nuna
mata kujera yace zauna, ahankali ta zauna tana cije lebe,ido ya kura mata
aranshi yace so pretty everything fits her “, allura ya ciro daga drowan
magunguna,Eraj tana ganin allura ta mike tsaye tajuya da gudu tayi hanyar kofa,
tsayawa yayi chak yana kallonta tsabagen rudewama takasa bude kofan tafashe da
kuka sosai tana bubbuga kafa, tace no,plz-plz-plzzzzz karakamin allura’,uhm
uhm,tana girgiza kai dukta rude.

Maman Abd Shakur 😘
[2/1, 9:38 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU 🌺🌸🌺
5
Tausayin ta ya kamashi ya ajiye alluran akan table yazo gabanta ya rike mata
hannu yace “bakison Allura?”,Da sauri ta girgiza kai tana goge hawaye, yace
“cikin baya na miki cewo ba”, tasake girgiza kai,yace! “mesato bakison namiki
allura ya dena ciwon?”, ta turo baki tai shiru, jan hanunta yayi tabishi luu
yakaita gaban table din ya dauko magani da Eva water agora yace “sha”, karba
tayi tafara zuba ruwan abaki sanan tazuba tablet din ta hadiye kaman zatai
ammai. Daukan alluran yayi, tajuya zata gudu fizgota yayi da hannu daya ta fado
jikinshi ta kwala ihu wayyo Amma na zaimin allura, matseta yayi ajikinshi ya
tsira mata alluran abayan ta, ihu tafasa tana kuka ajikinshi, buga bayanta yake
kadan kadan ko minti biyu ba’ayi ba ta bingile da bacci,alluran maganin ciwon
mara ne amma tanasa bacci. Daukan ta yayi ya daura kan gadon marasa lpy dake
office dinshi.
Jawo kujera yayi ya zauna gaban gadon yana kallonta gashin gaban goshinta
akwance, hancinta dogo, round face gareta ga karamin bakinta wanda zaka zaci
spoon bazai iya shigaba,kwanto da kanshi yayi kusa da fuskanta yace “u are damn
pretty gurl,u are an angel created 4 me”,lips dinshi yakai ya sumbaci goshinta
kadan ya daura hanunshi kan nata ya matse ya kulle idonshi. Karan wayanshi yasa
ya bude idonshi fuskan Eraj dake bacci ya kalla yayi murmushi ya cire hannushi
daga kan nata ya tashi ya koma kujeran shi ya zauna sanan ya daga wayan Hello
mother don’t tell me u have already start missing me,I just got here yesterday,
yadan yi shiru sanan yay murmushi yace d area is cool mum, no need to worry,
sunyi posting dina zuwa wani private school clinic, saikuma yay shiru chan yace
ok I will mother,bye take care.
Har karfe uku Eraj bata tashiba,har aka tashi yan makaranta bata tashiba,yayinda
Dr Oliver ke zaune kusa da ita yana kallonta. Wuraren karfe hudu ta tashi
ahankali take bude idonta har suka washe, taga babu kowa a office din amma
tanajin motsi abayi, agogo ta kalla taga hudu tayi ta zaro ido tace “nabani Amma
yau zatamin fada”, saukowa tayi daga gadon tasa takalman ta tayi hanyar
fita,hartakai kofa ta hango katon sarkan cross dinshi akan table, murguda baki
tayi tace “katon arne kawai, to wlh kabar ganin sarkan cross dinan naga uban me
zakasa,yana wani sa sarkan cross angayama mu arna ne”, tai kwafa tadau sarkan ta
tura a poket din gaban rigan makarantan ta. tajuya da gudu tabar office din,
ajinsu taje ta dau jaka sai gida. Koda yafito yaga bata nan baiji dadiba yaso
yacigaba da kallon kakkyawar fuskanshi, saida yagama komi ya shirya zai tafi
gida yafara neman sarkan shi yasa yay yaga,amma yaga ba ita babu alamunta.babu
abunda yazo ranshi sai Eraj, folding hanunshi yayi akirji yay murmushi yace
“dolenki gobe kiban kayana if not”yay kwafa, car keys dinshi ya dauka yatafi
gidan shashan cinsu.
Maman Abd Shakur 😘
[2/2, 12:50 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU 🌺🌸🌺
6
Wuraren biyar takai gida saboda gidansu da nisa sosai da school, gashi school
bus yariga yatafi gida. da sallama ta shiga gidan Amma ta daure fuska ‘daga ina
kike?Tun dazu nake jiranki ki dawo na kaiki asibiti’, Da gudu tafada jikin Amma
tana kuka,Amma ta rude tana kallon jikinta tace “maiya sameki?me akaimiki a
school?”,cikin kuka tace “cikina ke ciwo shine aka ban magani akamin alluran
bacci sai dazu na tashi……nan taba Amma labarin ciwon nata.
Amma tai murmushi ta shafa kanta ‘kidena kuka to,ba cuta bace,baiwa ce daga
yanzu ki dinga kula da kanki,dukda nasan baki wasa da maza amma karki yarda ko
hanunki namiji yataba,sanan duk randa kikaga ya tsaya saikiyi wankan tsarki
kinji,ai an koya muku a islamiyya ko?Ta girgiza kai, ‘yauwa to, je kiyi wanka ki
sa wasu kaya kizo kici abinci. Tashi tayi ta cire kayan tadau zani ta daura
tafito ta tafi bayinsu donyin wanka.
Lpy suka kwanta wuraren taran dare ita da Amman ta,wuraren karfe biyun dare ciki
yace bansan me bacci ba, yawani murda mata da sauri ta tashi ta zauna kan
gado,wani irin mugum ciwo cikin ke mata kuka tafara tafara tashin Amma-AmmaAmman,ahankali Amma ta bude ido ta lalubo yar toculan su ta kunna ta haska
fuskan Eraj taga hawaye shabe shabe harda majina arude Amma tace “Eraj
menene?”,Da kyar ta hadiye kukan tace “Amma cikina zan mutu,ciwo yakemin

Amma”,da sauri tahau jikin Amma tana kuka, Amma na jijjigata tana tofa mata
addu’a.
Daidai lokacin Dr Oliver ya farka daga bacci shima ya daura hanunshi kan
kirjinshi yana kokarin saita numfashin shi, juyo da kanshi yayi ya kalli karuwar
dake kusa dashi a kwance tsaki yayi ya tashi ya fito sitting room ya zauna kan
kujera ya daura kafafun shi akan table, lumshe idonshi yayi ya dafe kirjinshi ‘I
can feel it,she is in pain ‘ bude idonshi yayi cike da damuwa yace’but meke
damunta ko cikin ne?, kaman zaiyi kuka yace “my pretty angel sorry gobe inkinzo
school zan baki drugs kisha,bazai kara miki ciwo ba”.
Ganin bacci yaki daukan shi har karfe 3:30,kuma yanaji ajikinshi har alokacin
batai bacci ba tana cikin ciwo. tashi yayi ya dauko bible dinshi ya tsugunna ya
daura hanunshi kan bibble din yana mata addu’oin su.
Hankalin Amma yatashi Eraj ta tasata agaba tana kuka tana mukurkusu,jitake kaman
ta dauke mata ciwon, Amma ta dinga jijjigata tana shafa mata maran da hannu
ahaka wuraren 5 din asuba bacci ya kwasheta cikin yadan lafa, Amma ta kwantar da
ita ta lullubeta da bargo, sanan tamike tafita tai alwala dan gabatar da salla.
Dr Oliver a wurin shima bacci ya kwasheshi kanshi akan bibble.
Maman Abd Shakur 😘
[2/2, 12:57 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺
7
Gari nayin haske Amma ta dauko kudin da M Rahama tabata aro tasa hijabi tafito
kofar gida daidai lokacin school bus dinsu ya iso da sauri Mermu tafito ta gaida
Amma,tace “Amma Eraj fa?bazata bane yau”, Amma tace “bata da lpy bazata samu
daman zuwa ba,yanzu ma tana bacci”,Mermu tace “idan mun tashi zanzo nadubata”,
Amma tace “koma bus kina batama sauran lokaci”,ta dagama Amma hannu ta shiga
tafada ma driver yaja motan sukai gaba. Amma ta wuce inda zata wani babban
pharmacy ta tafi alokaci bama su bude ba sai takwas haka Amma ta zauna har
takwas tayi suka fito da sauri ta shiga tai bayanin matsalan, macen ta bata
magunguna tamata bayanin duka Amma ta biya kudin 2,500 sauran chanjin tasiyo
kayan tea da bread koda tadawo gida bata tashi ba kitchen ta shiga ta hada mata
ruwan tea din dayasha kayan kamshi ta zuba a flask takai daki ta ajiye.
Karfe goma nasafe ta tashi,Amma ta taimaka mata tai wanka ta gyara kanta sanan
tabata maganin tasha da kyar sanan tasha tea.
Sai wuraren 11 nasafe yakai clinic din saboda yanda makara,office dinshi ya
shiga ya zauna babu wacce zuciyarshi keson gani sai Eraj, telephone din office
din ya dauka yakira principal din makarantan ya dau wayan shiyafara gaida Dr
Oliver good morning sir, bai tsaya amsa mai ba yace “inason gani student I dont
know her name but naje class dinsu naga ss3 B take”, principal din ya mike yace
“za’a nemo maka ita yanzu sir”,ya katse wayan da kanshi ya tafi SS3 B din, yace
“wacece taga Dr Oliver last jiya?”,kowa ya nuna Mermu, ta zaro ido principal
yace “biyoni”, tabi bayanshi har office din Dr Oliver, yay knocking Dr yace su
shigo, kafanshi nakan table yana daddanna waya saida yagama bata lokacinshi
sanan yadago kanshi ya kalli principal batare dayace komi ba,principal da sauri
yace “sir gatanan itace?,so kake a zaneta kona koreta daga school din?”, Dr
Oliver yadan tabe fuska ya nuna mishi hanyar kofa yace “no need u can go”,da
sauri principal yafita. Mermu da sauri tace “good morning”, bai amsa mataba ya
cigaba da danna wayanshi batare da ya dago kanshi ba yana danna
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KABILARMU
avatar
fadila-9

6 months ago

Reply

Bana gajiya da karanta wan'nan littafin Allah ya karamiki basira ya kareki daga sharrin makiya

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to fadila-9

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment