Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta saki ihun da a ganinta shi kad'ai ya rage mata dan ta kusa fashewa.
Kuka takeyi jikinta na rawa fuskarta da idanunta sun canja launi har zafi suke mata. Hakan bai hanata dainawa ba dan ta sani wannan shine mafarin kukanta a nata duniyan.
HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA

NA MaryamerhAbdul

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

08. Na tuba

Tsaye take a tsakiyar makaranta tana kallon yanda 'yan ajinsu ke kai-kawo a farfajiyar makarantar. Fuskarta cike da annuri bayyane da murna da farincikin da take ciki.

Mintuna 40 kenan da fitowarsu daga d'akin jarrabawa, tayi hotuna har ta gaji tayi niyyan tafiya gida. Yau dai ta gama zana jarrabawar Neco saura degree tunda ta samu jamb nata.

A hankali ta fito bakin titi ta tsayar da adaidaita sahu ta mik'e hanyar gida tana jinta kamar tana firewa sama dan dad'i.

A bakin k'ofa ta had'u da Umar, ko kallonsa batayi ba ta shige gida tana mai mamakin nacinsa. Yaci ace ya yi zuciya ya barta ko dan k'in kulashi da takeyi.

"Da guntun wandonsa a wurin, ala dole shi Ustaz"
Ta fad'a a k'asan mak'oshi had'e da jan tsaki tana mai shiga falon gidan ba tare da sallama ba.

Zayyan kad'ai ta gani a falon, hakan yasa ta d'auke kai tayi hanyar d'akinta. Bata san lokacin da ya isota har ya janyo hannunta  tare da damk'ewa ba.

"Ke wai meh ke damunki ne? Duk kin wani canja kin zama salihar k'arfi da yaji. Wallahi da babban murya nake ja miki kunne ki daina guduna dan zakiyi mamakin abunda zan miki"

Bai jira amsarta ba ya saketa ya fice ya barta tsaye. Hawaye masu zafi taji saman kuncinta

"Meh laifinta dan ta kame kanta? Meh laifinta dan ta zab'i hanyar tsira? A da tayi wautar komawa rayuwar da suka koya mata amma a yanzu Zaid ya koya mata darasin da har ta mutu bazata manta ba. Tun ranar da ta tabbatar da Zaid ya yaudareta ta fita daga hanyar namiji, ta duk'ufa kan karatun da dashi kad'ai ta dogara, karatun da Alhaji ya sa ta shi kad'ai zai sa tayi masa fata na gari, amma bayan nan babu abunda zai sa tayi masa addu'a a rayuwarta"

"Lafiyanki kike kuka?"
Muryar Anty Hajara ya katse mata tunaninta. Juyowa tayi ta rungumeta tana mai sake fashewa da kuka a kafad'unta.

Cikin rawar murya Anty Hajara ke tambayarta abunda ya sameta. Bata iya amsawa ba sai da ta d'au lokaci
"Na tuna da Baba ne, Anty Hajara inaso inje wurin mamana tunda na gama exam yau, ko sati biyu ne in dawo"

Murmushi Anty Hajara tayi tana mai d'agota daga jikinta.
"Shine zaki tsaya kiyi ta kuka? Har kin tsorata ni na d'auka wani abu ne ya faru"
Shafa gefen fuskarta tayi tana mai cigaba da cewa
"Ki shirya jibi sai ki tafi, zan sanar da ita a waya da kaina"

"Nagode sosai, Allah ya biya ya k'ara girma"
Murmushi suka sakarwa juna kowa ya wuce nasa d'akin.

*****

Wasa-wasa yau watanni biyar da gama makarantar Surayya. Rayuwarta cike da kwanciyar hankali take tafiyarwa ba tare da damuwar komai ba, matsalarta d'aya ta saba da kashe kud'i, ta ina zata samu kud'ad'en da take kashewa a da dan ya fara damunta matuk'a.

Dalilin nan kad'ai yasa ta amince da soyayyar Umar, ba dan komai ba sai don tunanin samun na kashewa daga garesa, sai dai abun ba kamar yanda tayi tunani ba, dan Umar baya bata isassun kud'in da take buk'ata, kuma bazata iya tambaya ba gudun raini.

A hakan dai take tare dashi har lokacin da ta samu gurbin shiga FUTY, inda ta fara karantar English and linguistics.

A nan ta had'u da Fu'ad nata har ta karb'i soyayyarsa, bai sha wahalar samun kanta har ta fara bashi kanta a duk lokacin da ya nemi hakan ba, dan yayi mata alk'awarin aurenta.

Had'uwarta dashi bai sa ta daina sauraran Umar ba, dan bayi da wani anfani a wurinta, a nata ganin kuma bazai rageta ko k'areta da komai ba. Fu'ad ya cike mata dukkan gurbin da take neman mai cike mata, ya wadatar da ita da dukkan abunda 'ya mace zata buk'ata, yana zubar mata kud'i kamar bai san darajarsu ba.

Sai dai duk sharholiyar da takeyi babu wanda ya sani a gidansu bare a sab'a mata.

~~~~~~~

Cigaban Labari

Sati biyu da samun sak'on Fu'ad, Surayya ta canja kamanni kamar mara lafiya, tayi kuka kamar ranta zai fita. Tun tana k'iransa baya d'auka har ya kai ga ya fara rejecting, daga k'arshe kuwa ya kashe wayarsa gaba d'aya dan damunsa da take yi.

Kwance take a gadonta idanunta luhu-luhu a lumshe. Wayarta da yake gefenta ta janyo ta bud'e ta shiga wurin k'ira.

Umar Ustaz ta dannawa k'ira. Ringing biyu ya d'auka sallamarsa ya cike dodon kunnenta. Runtse idanunta tayi hawaye suka biyo gefen kuncinta

"Hello kina jina?"

Ya furta jin shirun da tayi. Yawu ta had'iye sannan ta iya amsa sallamarsa ta gaishesa.

Bata yi dogon zance ba ta fad'a masa shawarar da ta yanke
"Inaso ka turo ayi maganar aurenmu"

Sakanni masu yawa sun gota ba tare da ya amsa ta ba, hakan yasa ta ciro wayar daga kunnenta ta duba, ganin har yanzu yana layi ta sake mayarwa
"Kayi shiru, baka shirya aurena bane?"

"A'a Surayya, na kasa yadda da abunda kika sanar min ne, da gaske kina nufin in turo magabatana ayi maganar aurenmu?"

Idanunta ta juyasu sannan tace
"Eh, da gaske nake"

Sai sannan taji ya furta alhamdulillah can k'asa sannan yace mata
"Nagode sosai Surayya, ki sanar da naki magabatan sati mai zuwa insha Allah, nagode sosai"

Hawayen da take k'ok'arin hanasu sauk'a ne suka zubo dan jin yanda yake murna, ji tayi kamar ta mayar da hannun agogo baya ta amshi soyayyarsa tun lokacin da ya nuna ra'ayinsa ba sai yanzu da ta gama fand'arewa ba. Kasa rik'e kukan nata tayi ta katse wayar ta shiga kuka kamar anyi mata mutuwa.

~~~~~~~~~

Wa zai iya cankar abunda zai faru?
Labari yanzu ya fara tafiya, ku biyoni...

MaryamerhAbdul
HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA

NA MaryamerhAbdul

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

09. Aurena

Kamar yanda addini ya gindaya, Surayya cikin wattannin da aka sa na aurenta tayi istibra'i, ta karb'i k'addarar rayuwarta ta karb'i shawararta na auren Umar hannu biyu.

Wattani shida da aka sa ya shud'e, yau Jumma'a ake d'aura auren Umar Faruq Samaila da Surayya Abdussamad, bisa sadaki naira dubu saba'in.

Alhaji mijin Anty Hajara shi ya bada aurenta(liwalinta), Mahaifiyar Surayya tun ana sati d'aya saura biki ta dawo gidan da zama. Zayyan bai damu da aurenta da za'ayi ba, hasalima tunda ta turo Umar gida ya fita sha'aninta, yana wuya su had'u sai in ya zama dole.

Biki yayi biki, anci an sha kowa yayi murna an taya ta murnar aurenta, ciki harda sauran yayyunta da har yanzu Allah bai kawo musu mazaje ba. Cikinsu babu wanda ya nuna kyashi ko bak'in ciki, sun jinjinawa kamewarta da kuma shawarar da ta yanke farat d'aya.

*****

Watanni biyar da auren Surayya, duk wani jin dad'i da mace ke nema a gidan aurenta babu wanda bata samu wurin Umar. Takan yi mamakin yanda yake kula da ita duk da bai sameta matsayin cikakkiyar mace ba.

A nata tunanin ta d'auka daga ranar da ya kusanceta zata ga sauyi a tare dashi game da kulawa da zallar soyayyar da yake nuna mata, sai ya bata mamaki dan babu sauyi ko kad'an. Hakan yasa ta sakankance tana d'iban soyayyarta son ranta. A ganinta bai gane yanda ya sameta bane kasancewarsa sabon shiga.

*****

Tsananin ciwon kai ke addabarta tun daren jiya, ta sha magani amma sai k'aruwa yake yi, ga zazzab'i da amai da take ta zabgawa tun safiya.

"Tashi muje asibiti"
Yana mai mik'a mata hijabinta ya fad'i hakan
"Ka bari sai anjima in munyi la'asar, bazan iya tashi ba yanzu"

Bai mata magana ba ya sanya mata hijabin tare da d'aukarta a hannunsa ya isa da ita cikin motarsa. Sai da ya gyara mata zama yanda bazata takura ba sannan ya koma mazaunin direba ya kama hanyar asibiti.

Kai tsaye likita ya nemi ayi mata gwajin shigan ciki tare da d'iba jininta dan gwadawa.

"Emm Surayya, kinga ana nemana wurin aiki, in sakamakon ya fito ga kud'i ki hau adai-daita ki koma gida"

Idanunta da ke rine ta d'ago tana kallonsa,
"Yau Saturday fa, wani aiki kuma?"
Kallonsa takeyi dan ta kasa gane yanayin da yake ciki, tsoro ne ko rashin gaskiya?
"Lafiyanka?"
Ta sake tambaya tana mai k'are masa kallo, cikin muryar rashin lafiya take maganar.

"Ogana ke nemana, karb'i dan Allah. Muyi magana ko a waya ne in ban dawo da wuri ba"
Karb'an kud'in tayi bata sake masa magana ba har ya fice cikin sauri.

Mintuna talatin da tafiyarsa likita ya nemi ganinta a ofishinsa. Murmushi ya sakar mata ya nuna mata kujerar da zata zauna.
"Ina mijinki?"
"Ya d'an fita, lafiya?"

Kallon takaddun teburinsa yayi sannan ya sake dawo da dubansa gareta.
"Ba sai yana nan ba zan iya baki sakamakon bincikenmu kenan?"

Kai ta gyad'a alamar eh idanunta bai d'auke daga kallonsa ba.

"Mrs. Umar, inaso ki kwantar da hankalinki, ki sani cuta ba mutuwa bane, ki sa a ranki cewa bazaki mutu ba sai lokacinki yayi. Farko dai sakamakonmu bai nuna kina d'auke da juna biyu ba, amma gwajin jini da mukayi ya nuna mana cewa you're HIV positive, zamu d'aura ki kan magunguna mu baki katin da zaki na zuwa every month dan karb'an magani"

Firgici da tsoro ya hana Surayya magana, jikinta rawa yakeyi tana mai kallon likitan dan gaskata abunda kunnuwanta ke saurara.

Zufa tuni ya jik'a saman hijabinta, sauran maganganun likitan bai shiga kanta ba bare ta fahimcesu.

"HIV? K'anjamau kenan fa? Ta ina na samo aids? Fu'ad? Yes sai dai Fu'ad, amma kenan in ina dashi na sawa Umar mijina?"

Tuna hakan yasa ta toshe bakinta da hannunta hawaye masu zafi na sauk'o mata, duk maganganun da takeyi a zuciyarta takeyi.

Karb'an sakamakon tayi ta kama hanyar waje, tuni ta nemi cutan da take ji ta rasa, tashin hankalin da take ciki ya wuce ciwon kan da take ji.

Wuri ta samu a harabar asibitin ta zauna, tunaninta tuni ya toshe ta rasa meh ya dace tayi. Kuka ta shiga yi tana mai da na sani da kaicon rayuwa irin nata.

Bata san iya lokacin da ta d'iba a wurin tana aikin kuka ba sai da taji dirin mota ya tsaya gefenta tare da tsinkayo muryar mijinta.
"Lafiyanki Surayya? Meh kikeyi anan? Kinsan k'arfe nawa? Ana k'iran maghrib fa"

Sai sannan ta duba yanayin garin taga duhu ya mamaye inda take. Kallonsa tayi tana mai tausaya masa, rik'eta yayi ya sa ta a mota tare da karb'an takardar sakamakon nata ya koma mazaunin direba sukayi hanyar gida ba tare da wani ya sake magana daga cikinsu ba.

~~~~~~

Thank you all
MaryamerhAbdul na sonku kwarai
HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA

NA MaryamerhAbdul

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

10. GWAJI

"Fu'ad ka tabbata da abunda kake fad'a min?"
Tana maganar ne a hankali idanunta na manne da k'ofar kitchen d'in da take ciki. Hannunta dukka biyu take rik'e da wayar a kunnenta fuskarta sai yoyon zufa yake.

"Wai meh yasa kike ma tambayana ne? Na fad'a miki ni am negative, just last week ma nayi donating jini, k'arshen bani dashi kenan. In kina da aids ma ki binciki wad'an da kikayi mu'amala dasu bayan ni, dan ni kam Alhamdulillah na tsira daga wannan tarkon"

Yana jin yanda take kuka amma ya katse wayar, toh meh zai mata? Can mata da wanda ya sa mata cutar ta. Kusan shekara d'aya da rabuwarsu amma zata k'irasa tana masa wannan banzan tambayar?

*****

Ahankali take girgizashi tana ambaton sunansa. "Alhaji k'arfe sha-d'ayan har ya gota"
Ganin bayi da niyyan motsawa yasa ta fara girgizashi da k'arfi tare da k'iran sunansa cikin d'aga murya.

Ahankali ya iya bud'e bakinsa ya fara magana, bata iya jin komai cikin maganarsa ba dan rikicewa tayi da ganin irin karkarwar da yake yi. Da gudu ta mik'e tayi hanyar d'akin Anty Hajara.
"Yaya, ki zo ki ga abunda ya samu Alhaji, karkarwa yakeyi ko magana ya kasa, na tsorata nikam ban gane masa ba"

Da hanzari ta fito daga bayan gida tana k'ok'arin d'aura zaninta.
"Amarya lafiya? Inace lafiya mukayi sallama jiya kuka kwanta? Ko kun kwana bayi da lafiya ne?"

A hanyarsu ta iya amsata
"Asuban nan fa da muka idar da sallah yace in tashe sa k'arfe sha-d'aya, lafiyansa lau wallahi bansan meh ya same shi ba farat d'aya"

Hawayen da ke gangaro mata ta goge da bayan hannunta. Biye take da Anty Hajara a baya tana mamakin abunda ya samu mijinta a iya awannin da ta fita daga d'akin dan had'a masa abin kari.

"Ki nemo wani daga cikin yaran nan mu kai sa asibiti, jikin nasa yayi tsanani Amarya nima ya tsoratani"
Hannunshi ta rik'e cikin nata tare da ambaton Sannu tana k'ara gyara masa jibgegen bargon da yake jikinsa. Sosai yake karkarwa kamar yana cikin fridge.

Mintuna biyar K'annen Zayyan da sauran yaran gidan wad'an da basu aiki suka shigo d'akin. Dak'yar suka iya d'agosa yana takawa ahankali har suka isa mota.

Anty Hajara da maza biyu cikin yaransa ne suka bi motar, Amarya da sauran suka koma ciki suna mai yi masa fatan samun lafiya.

*****

"Surayya"
"Na'am"
"Wai lafiyanki? Meh haka duk kin d'aga hankalinki kina ta ramewa a banza? Toh ai in cutan bai kashe ki ba ke kya kashe kanki, ki nutsu ki san meh kikeyi dama"

Kallonshi ta tsaya yi cike da mamaki, sati d'aya yanzu da jin sakamakon gwajinta, tayi ta jiran lokacin da mijinta zai tambayeta inda ta samo cutar amma yayi biris kaman bai san da sakamakon ba.

Toh yau dai gashi yazo mata da wani salon wanda ta kasa ganewa.
"meh maganansa yake nufi? Bai ji haushin sa masa cutan da nayi ba kenan, wait, sa masa kuma? In ni na sa masa kenan Fu'ad ne ya sa min kuma ya tabbatar min bayi dashi"

Runtse idonta tayi har ya fice daga d'akin bata iya ce masa komai ba, ta kasa gane abunda ke faruwa da rayuwarta, ta ina ta samo k'anjamau? Bayan Fu'ad da Zaid babu wanda ya tab'a kusantarta a rayuwarta gaba d'aya, toh ko dai cikin su Alhaji da Zayyan ne wani ya goga mata? Dan tabbas taji ana iya d'aukan cutar ta yawu, doguwar sumba na iya janyo canjen white blood cell tsakanin juna, toh ko dai ta hakan ne?

Da sauri ta kad'a kanta alamar a'a tunowa da tayi jiya tayi waya da Anty Hajara kuma ta tabbatar mata har lokacin ba'a tabbatar da cutar da ke damun alhaji ba, da k'anjamau ne da zata sanar mata.

"Zayyan kenan? Toh ni yaushe rabona dashi da har zan samu a wurinsa?"
Ta furta hakan a fili hawaye masu zafi na kwaranya daga idanunta. Lab'b'an bakinta na k'asa ta ciza tana mai kad'a kanta ahankali dan cushewar da tunaninta yayi.

"Umar? Kenan a wurin Umar na samu? No, bazai yu ba, Umar baya neman mata kuma Ustaz ne taya zai samo wannan cutar? Na tabbata Zayyan ne, duk da jikinsa bai nuna mai k'anjamau ba amma shine, yes, ya zama dole in nemesa inji ko yana da wannan cutar".
Duk zancen nan a zuciyarta take yi.

*****

"What? Are you insane? You most be stupid Surayya, ni kike kallon tsabar idona kizo har cikin d'akina kina tambayana ko ina da k'anjamau? Baki da hankali ne? Naga alaman tunda kika auri wannan gidahumin kika rasa tunaninki"

"Zayyan ya isheka, nazo nan ne dan in tabbatar da zargina, ka sanar dani yaushe rabonka da gwajin HIV? In kasan ka kai shekara toh ka gaggauta zuwa asibiti dan ka tari cutar tun kafin tayi maka illa"

Bata jira zancensa ba ta juya zata fice daga d'akin.
"Surayya kinsan meh kike cewa? Kin fa rud'ani? Meh kike nufi?"

"Na dai baka shawara, in ka samu sakamakonka sai ka nemeni in maka k'arin bayani"
Bata juyo ba tayi masa maganar, hakan yasa tana gamawa ta cigaba da tafiyarta cike da nutsuwa zuciyarta na harbawa kamar zai b'allo ya fito daga k'irjinta.

Can d'akin Anty Hajara ta koma dan sanar da ita ta gama su wuce asibitin duba jikin Alhaji.
A hanyarsu ne Anty Hajara ke sanar da ita 'yan mata uku na gidan sun fito da mazajensu har an fara maganar aure. Sosai ta taya su murna amma sai ta tsinci kanta da bada shawarar ayi gwajin jini kafin ayi auren.

"Meh yasa? Baki ma san mazan ba bare kice suna da halin banza"
"Ai Anty ba sai kana da halin banza za'a duba lafiyarka ba, yana da muhimmanci sosai a wannan zamanin ayi gwaji kafin aure, duk da ahalin maza wani lokacin har da na matan kan fusata a duk lokacin da aka nemi yin gwajin, yakamata a gane cewa yin gwajin ba shi zai nuna ba'a yadda dakai ba, ana cutan mata da yawa da wannan cutar a rashin sani Anty"

"Hakane, kinyi gaskiya Surayya, insha Allah zan bada shawarar haka in Alhaji ya d'an samu sauk'i, kin kawo shawara mai kyau, Allah ya dad'a kare mu daga hannun azzalumai marasa tausayi"
Ameen kawai ta iya furtawa dan zuciyarta ya karye, rayuwarta yazo k'arshe tayi asara har abada. Dak'yar ta iya mayar da hawayen idanunta.

~~~~~~~~~
Dan! dan!! dan!!!
Labarin ba mai tsawo bane dama na sanar daku, kada kuyi mamaki in gobe nace muku k'arshe😂


Wasa nake, har yanzu da sauran tafiya.
Ku fad'a min ra'ayinku game da wannan shafin, meh ra'ayinku game da yin gwaji kafin aure?
Ya mazauna wurinku suke d'aukan wannan shawarar na gwaji kafin aure? Nidai sarkin garinmu ya hana d'aura aure sai da gwaji, duk malamin da ya d'aura aure ba tare da gwajin HIV ba yana fuskantar hukunci mai zafi tare da tara.
Zan so jin ra'ayoyinku.
Thank you so much

MaryamerhAbdul
HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA

NA MaryamerhAbdul

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

11. ZALIHA

"Ya za'a ce ba'a san meh yake damunsa ba? Meh anfanin kawosa asibitin in har su likitocin da kansu bazasu iya sanin meh matsalarsa ba bare su basa magani. Sun dinga k'ara masa ruwa kenan suna masa allurar bacci, haka akeyi? Ni ban yadda da asibitin nan ba ma, canja asibiti kawai zamuyi wad'an nan basu san meh sukeyi ba"

Zayyan ne ke wannan batu yana tsaye a bakin k'ofar d'akin mahaifinsa tare da Anty Hajara, Amarya da k'anin Alhaji mai suna Salihu.

"Nima dai abun nan yana d'aure min kai Zayyan, sati fa da kwanaki babu wani sauyi bare a fad'a mana tak'amaimai cutarsa"
Kad'a kai Anty Hajara tayi tana mai cigaba da cewa "abun nan akwai d'aurin kai".

"Yanzu dai duk ba wannan ba, zayyan ka tafi da matan gida ni zan ga likitan da kaina mu san abun yi, gaskiya yana cikin ciwo in akayi la'akari da maganganunsa, haka kawai ya dinga bada wasiyya kenan yana cewa mutuwa zai yi"

Hawayen da ya taru a idanunsa ya goge ya cigaba da cewa
"Ban tab'a ganin yaya cikin irin halin nan ba, d'azu ce min yayi ya gwammaci mutuwa da abunda yake ji cikin jikinsa, wannan wani irin cuta ne?"

Duk jikinsu a mace suka bar wurin, kowa da abunda yake ransa game da ciwon Alhaji, wasu na tunanin sammu akayi masa dan wani abun nasa kamar hakan. Komai na jikinsa ciwo yake a nasa fad'an, ji yake kamar ana soka masa allura a dukkan jikinsa, wani lokaci kuwa kamar ruwan zafi ake kwara masa.

*****

Sosa kai Zayyan yayi yana tunanin k'aryar da zaiyi musu dan ya wuce karb'an sakamakonsa, dalilin zamansa a asibitin kenan na tsawon awanni.
"Dan Allah barin d'an duba abu anan kafin mu wuce"
Amsawa kawai sukayi da toh suka shiga motar nasa suna zaman jiransa.

Wurin gwajin jinin ya shiga zuciyarsa na harbawa, ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba tun ranar da Surayya ta tunkareshi da maganar k'anjamau, shi lafiyan jikinsa k'alau ta ina zai samu? Shakkun da yake dashi kad'ai yasa shi zuwa gwajin nan, amma ba dan haka ba hankalinsa a kwance yana sharholiyarsa da mata yana jin dad'in rayuwarsa.

Bai wani zama ba aka bashi sakamakonsa likitan na cewa "its negative"
Murmushi ne ya kufce masa tare da cafke hannun likitan yana girgizawa yana hamdala a ransa. Kaman anyi masa albishir da gidan aljannah yake ji.

Da hanzari ya fito murna fal ransa, bakinsa ya kasa rufuwa ya isa wurin motarsa, sai da ya danna kid'a sannan ya fizgi motar ya bar harabar asibitin. Duk wannan a salon murnarsa kenan.

*****

"Umar magana fa nake, bani da kud'i a hannuna kuma kasan makaranta zanje, tun d'azu fa kai nake jira kaga har zanyi latti"
Ta k'arashe maganar tana duba agogon hannunta.

Ko kallonta bai yi ba ya ciro d'ari biyu ya mik'a mata sannan ya cigaba da aikinsa a komfutarsa(computer)

Karb'a tayi tana kallonsa, ganin ba magana zai mata ba yasa ta fara magana
"D'ari biyu ne zai kai ni makaranta ya dawo dani? Kuma kada inci ko in sha abu? Ka manta kud'in da kake bani na sati ne? In ma ka daina bani na satin ne ai sai ka k'ara min ko d'ari biyar ne in sha abu in naji ishi"

"Dan Allah ki b'ace min akaina, haba! Sai mitan tsiya kika koya. In bakya so bani kud'ina"
Ya mik'a hannunsa dan ta bashi d'ari biyun.

Baki bud'e take kallonsa, mamakinsa bai barta ba. Ganin da gaske kud'in yake so ta mik'o masa yasa ta sa a jaka ta bi gefensa ta wuce.
"Na tafi"
Ta furta can k'asa, bai ce mata komai ba ta bar gidan tana mai takaicin sauyawarsa.

"Ba laifinsa bane, dole yaji haushina tunda na k'ak'aba masa cuta, na ma yi sa'a bai hau ni da duka ya hana ni makarantar ba"
Ta furta a fili tana mai share hawayen da ke sauk'owa daga idanunta.

*****

"Kinsan Allah sa'arki d'aya kina da aure, da sai na mugun ci miki mutunci akan tashin hankalin da kika sani....."

Sheshshek'ar kukanta ne ya dakatar dashi, ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli sunan nata da yayi saving sannan ya mayar kunnensa.
"Dan uwaki kukan meh kike min? Dan kinji haushi bani da cutar shine kike kuka? Wai tsaya, ko kece kike dashi shine kike son k'ak'aba min"

Cikin sheshshek'a ta iya cewa
"Dan Allah ka k'yaleni Zayyan, na baka shawara meh laifina da zaka dinga zagina? Tunda baka dashi kayi hamdala ka tuba ka bar halin da kakeyi tun kafin lokaci ya k'ure maka, wallahi ina fad'a maka hakan saboda ni nasan illar bin son zuciya. Kuma ka sani, mazinaci baya auren salihi sai mazinaci d'an uwansa, a ganinka zaka tsira ko ka b'uya wa fad'ar Allah? Ni dai nawa shawara kuma na baka, wad'an da suka rasa wannan daman shikenan ta wuce musu har abada, kada ka bari ka zama cikinsu"

Bata jira maganansa ba ta katse wayar, yanayin maganarta yasa zuciyarsa da dukkan jikinsa sanyi, tunani d'aya yazo ransa
"Meh yasa take irin wannan maganar? Anya bamu cuci Surayya ba?"

*****

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Hannunsa dukka biyu ya dafe kansa dashi yana maimaita wannan kalmar.

K'arar bud'e k'ofar d'akin yasa zuciyarsa ta k'ara hautsinewa. Kasa d'ago kansa yayi har ta iso inda yake ta tsaya a gefensa tana masa kallo daga sama har k'asa cike da tsantsar raini. K'arar chewing gum(cingam) da ke bakinta ke fita cas-cas-cas, hannunta rik'e da k'ugunta.

"Toh da ka shigo nan ka zauna ka d'auka bazan iya binka bane? Wallahi ka fa raina ni, naga alamar baka nemi zaman lafiya cikin gidanka ba, kuma tabbas tunda ka auri mace kamar ni toh ka saya da kud'inka. Da Zaliha kake zancen"

K'afansa ta take ta wuce ko a jikinta, huci take kamar namijin zaki har ta fice banko masa k'ofar ta rufe kamar yanda ta shigo.
Har lokacin bai iya d'ago kansa ba dan ciwo mai rad'ad'i da yake masa.

~~~~~~~~

Waye kuma Zaliha?
Waye mijin nata?
Ya tabbata ba Zayyan ne ya sawa Surayya HIV ba, waye kenan? Umar? Ta ina ya samo in shi ne? In ma ba shi bane to waye?

MaryamerhAbdul
HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA

NA MaryamerhAbdul

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION



Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment