Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BA ma'ana BAISAN DAKEBA BAZAI TINAKI BA.
Sulalewa tayi 'kasa tana neman shi'dewa komai na
duniyar na juya mata Jitake kamar zuciyarta zata buga
Gaba 'daya zantukan nafisa sun hargitsata batamasan
wane tunani zatayi ba. Sai alokacin wani irin kuka mai
ciwo yazo mata ta 'kankame jikinta tanayi abunta sosai.
Yanda take kukan ne ya masifar kashe jikin nafisa dan
tana tunanin akwai abunda yafaru akan rabuwarsu.
Zama tayi kusada ita tanason ta rarrasheta amma yanda
nazli ke kukan tana bukatar abarta tayi abunta kodan
samun saukin radadin zuciya sbd kalar kukanta ya
bayyana zuciyarta tana cikin wani mugun hali. Tsoro
nafisa tafaraji ganin nazli na neman sha'kewa ahalinda
take ciki Ta dafata cikin tausayi tana shirin yin magana
nazli ta gwalo mata manyan idanunta dasukayi jajir sbd
kuka. Girgixa kai tayi murya ashake tace, Dan allah ki
fitar dani agidan nan yanxu, Banason bayanke dakika
ganni wani yaganni musamman haj xeenat Bakuma zan
iya jurar ganin meer 'dina yaganni amma baisanniba, Bai
tunaniba, 'Karshema yanamun kallon 'yar aiki Baxan iya
jure wannan ba Gwara natafi nakoma nayi jinyar
xuciyata dazata rayu da tsananin sonsa da damuwar
rashinsa 'karshe ta mutu da sonsa. Nazli kece wadda duk
masoyan alh da 'yayansa ke adduar su samu sbd nagani
nakuma ji ajikina kece zaki kubutar dasu daga sharrin
hajiya. Mikewa tayi tana nufar 'kofa nafisa tayi saurin
shan gabanta tace, Nazli ina cikin jikinki dakika tafi
dashi? Cikin kuka tace, Babushi ya xube. Garin yaya
yazube? Bansaniba nima Tun yaushe? Bazan iya
tunawaba Bazai yiyu ba sbd kinason tameer nasani
fiyeda kanki dan haka joda cikinsa dake jikinki ya zube
nasan bazaki taba manta ranar ba. Dan haka tun yaushe
ne cikin ya zube? Shekara hudu. Tafada da 'karfi tana
kuka dan duk tambayoyin na nafisa a jere take matasu
duk sun rudata dan dama aruden take. Ja baya nafisa
tayi tareda sakin ajiyar zuciya tace, Shekarar abunda kika
haifa hudu kenan nazli Dan banyarda da cikin yafitaba.
Rintse idanu tayi tana jingina da bango hawayenta naci
gaba da ambaliya. Gidan takeson bari danji take makar
zata 'kone tsabar ciwon zuciya. Cikin hawaye da sanyin
murya tafadawa nafisa komai tun bayan barinsu gidan
'karshe ta 'dora da fadin, Rayuwata ba 'daya daga cikinsu
wato meer ko waleed to tabbas batada amfani agareni.
Inasonsu fiyeda kaina, Inason meer tun bansan soba,
Inason duk wani abu daya dangaci meer 'dina shiyasa
nakeson waleed fiyeda numfashi sbd duk nakallesa
fuskar meer da jinin meee nake gani yana yawo ajikinsa.
Inason meer 'dina, Inason meer 'dina kuma meer 'dina
yana sona kaman yanda nake sonsa Amma wannan na
yanzu ba meer 'dina bane sbd meer 'dina bazai mantani
ba, Bazai daina sonaba, Meer 'dina ya mutu ya barni
daga yanzu zanyi takabar meer 'dina Nida waleed 'dina
munzama marayu mun rasa meer 'dinmu wannan
tameer ne yafi 'karfinmu. Kukan tausayinta nafisa keyi
tana lallashinta. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh gee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH
GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 151โ†’155
Kiranta fannah tayi ta hanyar landline 'din 'dakin nafisa
Nafisa tafada mata suka mike gaba 'daya zuwa can 'din.
Kaya dake gibge kan kujera ta nuna mata tareda cewa, Ki
'dauka ga kayanan zan siya miki wasuma sbd inaso ki
ringa wanka biyu ayini tareda canza kaya dan ki kasance
atsaftace koyaushe. Na yaba da tsaftarki amma inaso ki
'kara dan kiyaye duk abunda zai 'bata ran b 'dina. Ki
gyara 'dakina yanzu bari ni nashiga wanka. Bedroom
tashige tana tubewa tashige toilet. Nafisa ta kwasar mata
kayan sta fice itakuma ta gyare gurin cikin sanyin jiki.
Tana gamawa ta fito kenan yayi daidai dashigowar haj
xeenata dasu haj karima harsun samu fitowa daga
dawowarsu dan bata rahoton gurin boka dasukaje can
kanon. Zabura tayi da 'karfi taja baya tana nuna nazli
tareda ha'de wasu wahalallun miyau. Kallon rashin
fahimta suke mata haj bilki takalli nazli tamaido da
kallonta ga haj xeenat tace, Me aikin da fannah ce datasa
aka samo mata tun akano fa. Afirgice takallesu tace, Kun
kuwasan me kukayi barin wannan tsinanniyar tazo mana
da wannan Ta nuna nazli a rude. Haj karima tace,
Xeenatu kiyi mana gwari gwari mana munkasa gane me
kike nufi. Karima nazli ce fa matar shegen tsinannen
yaron nan. Meyasa kuka bari tazo da ita? Na shiga uku ni
zeenatu meyasa abubuwa ke neman tabarbaremun ne?
A kidime suke kallon nazli datati 'kasa da kai tana adduar
allah yasa su koreta yanzu basai gobeba tabar gidan dan
tabbas bazata iya rayuwa agida 'daya da tameer ba. Wata
wawuyar dam'ka haj xeenat takai mata ta shaqota tana
fadin, Zo tsinanniya munafuka kibar gidannan yanxu tun
wani daga cikin alh ko tameer basu gankiba duk da
nasan yanxu baisankiba ko kukuwa wlh nayi miki
mummunar kisa. Janta tafara tanajin wata irin tsanarta
kamar ta shaqeta ta mutu ta huta. Riqeta haj bilki tayi da
sauri tana ha'da zufa tace, Aa wannan ba itace mafitaba
agaremuba dan taga inda suke yanxu zata iya dawowa ta
baya ta tona asirin komai ta gudu kuma kunga basanin
inda takeba zamuyi bare mu 'dau fansa ko mataki
akanta. A ru'de haj xeenat tace, To meye abinyi dan
namatsu tun kafin shegiyar can ta fito taganmu ahaka
tayi zargin wani abin. Haj kareema tace, Mafita 'dayace
mu barta anan muna ganin duk wani motsinta da
abunda takeyi duk ranar data gudu ko ta tona mana asiri
wallahi saimun bashi guba ya mutu tunda shine abunda
tafi so fiyeda komai tunda allah ma yasa babu shegen
cikinta dayanzu masifar dazamu shiga saitafi haka.
Jinjina kai sukayi cikin gamsuwa da bayaninta haj xeenat
ta 'dora da fa'din, Kuma duk rintsi kadaki bari alh
yaganki kuma kadaki bari tsautsayi yasa ki nuna kinta'ba
ganinmu arayuwarki dan kuwa da kaina zan dama guba
na basa kina kallo yasha, Bake bashi, Ki tsaya amatsayinki
na me aikinsa da tsinanniyar qanwarsa. Idan kikayi
ganganci to kisani da rayuwarsa kike wasa dan yanzu
tana hannunki. Ficewa sukayi batareda sun tattauna
abunda yakawosuba. Kukandata risga adaren bai
fa'duwa sbd abun yazo mata ba yanda tasoba. Meyasa
koyaushe tameer ne abunda kowa ke amfani dashi gurin
quntatar da ita? Meyasa tameer yazama wanda zata
iyayin komai akansa har ayanzu dasuka zama duniya
daban daban? Tameer shine farin cikinta, Shine baqin
cikinta, Shine damuwarta, Shine buqatarta. Kuma shine
weak point 'dinta. Yanzu gashi once again zatayi rayuwar
wulakanci acikinsu akansa duk da baimasan tanayiba.
Amma koba komai zata zauna tayi gadin Koda garin haka
zata rasa rantane. Koda garin ya waye fuskarta ta
kumbura suntum ko gani sosai batayi amna haka taje
tayi gyaran dakin fannah tsaf. ******** Sannu ahankali
ta 'dan saba da fannah sbd tana janta ajiki sosai tana
kula da ita kamarba 'yar aiki ba. Wasu lokutan kiranta
take su zauna tana janta fira duk da ita bata sakewa
sosai. Abunda ta lura dashi shine tana tsananin son
yayanta sbd takanas ta 'dauketa takaita shago tayo mata
siyayyar turaka masu kyau da qamshi da kaya sosai duk
dan sbd kada yayanta shaki wari ko tsami idan tana
masa aiki. Itadai damuwarta duk kayan yawancinsu
dogayen rigunan kantine masu kyau da 'dan kama jiki.
Amma haka take sakawa atakure tana aikin. 'Bangarensu
haj xeenat kuwa ido sosai suka saka akanta.
โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ Duk inda nutsuwarta take bata
jikinta yau dan yau tameer zai dawo Tun safe aka bu'de
mata sashensa amma takasa shiga ta gyara saida nafisa
takama hannunta suka hau saman har cikin tsakiyar
palonsa kafin ta juya ta fita. Lumshe idanu tayi tana
tsiyayar hawaye. Komai na palon tsaf yake sai 'kamshi
dake tashi duk da 'dakin ya kwana biyu bakowa. Daqyar
ta lalla'ba kanta ta gyara palon da bedroom ta fesheshi
da airfreshner masu da'di ta kukkuna ac ta rufo qofar ta
fice. Girki na musamman sukayi hadda fannah 'din sai
farin ciki take ga aminiyarta meenah tuni ta iso taci wani
irin ado dan tarbar tavin ranta. Suna gamawa suka jere a
dining fannah tayi gurin wanka bayan ta umarceta da
itama taje tayi wankan dan driver yaje 'daukarsa daga
airport. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE
โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 161โ†’165 Cikin
rashin bawa xancen mahimmanci yace, Tunda kunaso
zan duba nagani. Mikewa yayi yabar gurin yana xuba
hannuwa a aljihun wandonsa. Dai dai xai shiga 'dakin ita
kuma ta fito 'daukeda glass cup din fresh milk sukayi
wani wawan karo Fresh milk 'din tazube ajikinsu gaba
'daya tayi baya da qarfi cikin tsoro aikuwa ta taka wadda
ta xuba a qasa santsin tiles yayi mata mummunan ja ta
tafi da qarfi zata xube Wata fixga yay mata ta fado masa
da qarfi saikuma suka zube gaba 'daya. Fannah dake
tsaye ta dariya ta kufce mata dan tun qarar faduwar cup
'din ta taso dan dubawa komai akan idonta yafaru.
Dariya take sosai kamar 'yar bby sbd ganin yayanta
kwance cikin madara har a fuskarsa ga nazli itama duk ta
6aci da madarar sai suka koma kamar wasu yara. Saurin
tashi tayi daga jikinsa ta bar gurin da sauri idonta na
qoqarin kawo ruwa dan haduwar jikinsu ya zaburo mata
da tsimin sonsa datake neman dannewa. Mikewa yayi
yana ha'de fuska yayi hanyar stairs dinsa. Gaban
madubin bedroom 'dinsa ya tsaya sai kwai yasaki
murmushi dan komawa yayi kamar yaron da yayi
'banna. Wanka yayi yayi sallar magrib yazauna palon
yakira fannah. Da sallama tashigo palon itama ta canxa
kaya tana 'daukeda tray 'din farfesun kifi da akayi masa
fannah na bayanta. Ajewa tayi tana mikewa fannah tace,
Nazli ki xuba masa saiki 'dauko ruwa da drinks ki kawo
masa. Riko hannunsa tayi tace, B pls get married, I really
want to see you happy kuma inason naga 'yan babys sun
fara kirana aunt. B pls do dis for me qnd marry my
friend meenah. Na yaba maka da ita and you knw i
always choose wats best for you. She's very nice, Kind
and gud..bayan wannan she really loves you. Kallon tv
yake yana saurarenta jin muryarta ta fara rawa kaman
xatayi kuka yasa ya juyo aikuwa hawayen take Jawota
yayi jikinsa yana cewa, Little youre askin for sumtin dat i
dnt really tink i can do for you. Marriage is not a joke or
sumtin simple. Its abt my future,my happiness my.....
Daz y i want you to get married b bcos i want to see u
live a happy life.. Pls pls b do this for me, Do this for ur
little sister. Zanyi tunani little but for now pls kibar
xancen okey? Kai ta 'daga cikin tana murmushi. Miqewa
tayi xuciyarta na bugawa da qarfi kamar zata fashe.
Kishinsa takeji yana kona zuciyarta ta fice da sauri tabar
palon ko ruwanma bata 'dauko masaba sai dai fannah ta
kawo masa. Sosai ya lura da yanayin data shiga amma ya
basar sbd baisan dalilin shigarta halinba. Kuka ta la6e ta
risga a 'daki har saida taji kanta na sarawa kafin ta
lallashi kanta ta fito. Da daddare harta kwanta fannah
takira wayarta data siya mata dan irin haka. Nazli pls ki
kaiwa b hot coffee yanxu yanacan yana jira. Kicin ta nufa
ta 'dora yanayi ta juye tadauka ta nufi 'dakinsa. Apalo ta
tarar dashi zaune da farar singlet da farin dogon wandon
bacci mai taushi yana aiki da laptop. Duqawa tayi ta aje
tray 'din akan center table 'din dake gabansa, Qamshin
turarenta ya daki hancinsa ya lumshe ido batareda
yakalli gefen datake ba. Mikewa tayi zata fice saitaji
tanason kallon fuskarsa ta juyo ahankali idonta tab da
hawaye. Juyowarta tayi daidai da 'dagowarsa idanunsu
suka shiga cikin na juna. Qurawa juna idanu sukayi
Tsantsar damuwa yake hangowa a idanunta yayinda ita
kuma take hango rayuwarta a idanunsa. Hawayene suka
gangaro mata ta juya da gudu ta fice tana toshe bakinta
sbd kukan dayazo mata. Qofar yabi da ido cikeda
mamaki Dan iya tunaninsa magana bata taba shiga
tsakaninsu ba amma yanayin yanda ta kallesa kamar
tasanshi yayi mata wani laifi. Shafo fuskarsa yayi yana
ayyanawa aransa akwai wata damuwa atare da ita.
********** Bayan 'dan lokaci ya amince da maganar
auren meenah badan yana sonta ba sai dan yanda
fannah ta damu sosai akan zancen dan shi sam beyi wani
tunanin xai iya samun lokacin kula mace bare soyayya
ayyukan gabansa ma kawai sun ishesa arayuwa.
Meenah,haj xeenat,haj kareema,haj bilki da fannah ji
suke kamar su taka kan jariri sbd farin ciki, tuni aka fara
shirin biki sbd har dad yazo ankai qarshen komai.
meenah tuni ta dawo gudan da xama dan idan ba ita ta
nemesaba baya bi takan zancenta saiya xama itake zuwa
fira 'dakinsa. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH
GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 166โ†’170
Zaune suke a garden 'din gidan yana waya dasu ammah
akan sha'anin bikin yace suyi zamansu basai sunxo ba
bayan bikin zasuzo tareda meenah 'din. Meenah dake
zaune taredashi tasaki wani murmushin farin cikin
samun cikar burinta dan yanda takeji ko kisa xata iya
akan tasamu tameer. Miqewa yayi sbd umminsa haj
nurat data karbi wayar zasuyi magana kasancewar yasan
batason auren da meenah yasa yatashi ya zagaya yana
wayar 'dayan hannunsa na sanye cikin aljihun 3quater
jins blue dake jikinsa da farar body hug. Yana cikin yin
wayarne yaringa jiyo sheshshekar kuka natashi ahankali.
Ignoring yayi yana cigaba da wayarsa. Sautin kukan
yafara yawo a kunnuwansa har baya iya fahimtar me
umminsa ke cewa, Ya rintse idanunsa yanason kukan
yadaina damunsa amma ina saima qara shigarsa yake
haryana dukan zuciyarsa. Bayan flowers 'din gurin ya
nufa sbd daga can kukan ke fitowa. Duqe take tasaka kai
atsakiyar qafafunta tana rero kukan. Bayanta ya kalla ya
gane 'yar aikin nance. Juyawa yayi yana 'bata fuska yana
jin haushinta aransa na yanda takeda damuwa takasa
fa'da ataimaka mata tunda tasan fannah zata iya taimaka
mata da koma nawane. Cak ya tsaya xuciyarsa na
tantama sbd sunansa dayaji ta fa'da cikin kuka.
Tameer,meer meyasa rayuwata take wahala haryanxu
akanka? Meyasa zan zauna dan ganin wannan baqar rana
agareni duk dakai farin cikine agurinka. Waleed 'dina zai
tabbata a maraya kenan shima baqar rayuwar danayi ita
xaiyi sbd rashin mahai.... Bata qarasaba kukanta yaci
qarfinta duk da bata bari sautinsa yafuta ba. Xuru yayi
qwaqwalwarsa a cunkushe dan baisan tunanin dazaiyiba.
Baimasan me zancen nata yake nufiba, To amma meyasa
sunansa yashiga zancen nata? Kodai bashi tameer 'din
ba. And waleed? Who is that waleed she's talkin abt? Is
he her hus... Juyawa yayi yabar gurin dan tuni kansa ya
fara sara masa. Baikoma takan meenah ba yawuce 'daki
kai tsaye. Da daddare data kawo masa fresh milk ko
kallonta baiyiba sbd bayason yaringa damun kansa da
abubuwan daba serious ba. Juyawa tayi ta fice jiki
asanyaye kamar mara lafiya. Bayan ta fita saiyaji yana
buqatar coffee sai bai nemi fannah ta turo masa ita ya
miqe yasauko dakansa dan yasa nafisa tayi masa sbd ita
'din ya lura kaman tana cikin tough time. Ba kowa
apalon dan haka ya nufi qofar 'dakin dan qwanqwasawa
Hannu ya 'daga zai buga maganar nafisa ta daki
kunnansa, Nazli pls kadaki bari ayi wannan auren ki fito
ki fa'da komai Ki bayyana musu waleed da gaskia sbd da
anyi wannan auren babu wata mafita dan kuwa burinsu
yagama cika akansu. Kuma dolene sir yasan gaskia wata
rana dan haka gwara ki sanar ma...... Cikin tsananin kuka
tace, Nafisa babu gurina arayuwarsa yanxu, Yana cikin
farin cikinsa bazan katse masashiba dan tarayyata dashi
ba abunda yaja masa sai wahalar rayuwa da
qasqantacciyar wahala. Kasa sauraron sauran yayi
yajuya yabar qofar 'Daki yakoma yakasa zama ya kasa
tsayuwa so yake ya gano me suke nufi amma bai ganoba
qarshema ciwo kansa yafara saiya kwanta kawai.
Tundaga lokacin yafara saka ido akanta sbd hankalinsa
ya kasa kwanciya akan xancensu duk da yanada tabbacin
wani tameer ne suke magana akai. ************** An
fara shagalin biki sosai dan dukiya alh zaida da tameer
suka sake musu anata shagali duk da dad bai dawoba sai
saura kwana 'daya 'daura auren. Shagali sukeyi sosai duk
da angon baida lokacinsu saisu ka'dai suke bidirinsu
sudai suga an 'daura auren. Duk iya yanda ta kama kanta
sosai ta danne xuciyarta hakan bata faruba sbd
muguwar rama tayi sbd tsananin damuwa da tunani dan
yanxu kukanma ya daina zuwa saidai idanuwanta su
ka'da suyi jajir. Fannah da kanta tasata agaba tace nazli
bakida lafiyane ko kinada damuwar zama damune? Kai
kawai ta girgixa mata. Kula da abincinsa yana kanta dan
tun fara biki fannah take jaddada mata hakan. Toilet
'dinsa take wankewa cikin cikin tsautsayi bakin taje
kunna tab saita kunna shower aiko ruwan sukaxo da
qarfi nan take suka jiqata jagab. Dan qaramin tsaki rana
kallon yanda ta jiqe gaba 'daya har gashinta. Sanin
bayanan bakuma kuma baya dawowa sai maraice yasa
ta Xame hijab 'dinta ta shanya a toilet din hakama
doguwar rigarta danso take kafin tagama sun 'dansha
iska. Bra ce fara qal ajikinta da farin under skirt tsaf dasu
kamar sabi sbd sosai fannah ke siya mata duk wani abun
buqata. Zaune yake a sit 'din baya yana sanye da suit
black masu red tie sai qamshi yake zubawa driver na
tuqasa. Wayarsace tayi qara ya duba saiyaga p.a 'dinsane
cikin qasaita ya 'daga wayar. P.a dinsa yace, Sir am sorry
walh meeting 'dinnan sun aiko wai sunada babban uxuri
an 'daga sai gobe kuma. Kasa magana yayi sbd haushi sai
kawai ya datse kiran ya kashe wayoyinsa gaba 'daya yace
driver yamaidashi gida yama fasa xuwa office 'din yau
gaba 'daya. A gate 'din farko yace driver ya ajesa ya
aikesa office shikuma ya taka ya 'karasa wanda hakan ya
hana sam tasan da yadawo. Dai dai qofar shigowa palon
yaci karo da fannah tana riqeda coke ahannunta tanasha
zata fita cikin sauri dan xuwa gidansu meenah sbd yaune
suke qunshi. Gaba 'daya coke 'din ta 6atasa Ya rintse
idanu cikin takaici kafin ya wuce da sauri yana ce mata
ta tafi kawai tunda yaga she's in hurry. Yana shiga
palonsa yasawa qofar key dan bayason adamesa wanka
kawai xaiyi ya huta. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na
MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo
171โ†’175 Yana shiga bedroom 'din ya kalli jikinsa yana
'dan yamutsa fuska dan yaso yana dawowa ya kwanta ya
huta amma yanxu saiya kuma wani wankan. Tu6ewa
yayi ya 'daura farin towel a qugunsa kyakkyawan jikinsa
da lafiyayyar fatarsa sai sheqi suke alamar hutu daya
ratsasu. Kai tsaye ya bude qofar toilet 'din yashiga tareda
rufowa. A firgice ta 'dago daga duqen datake tana canxa
ruwan cikin bathtub. "Ohh my god" ya fa'da yana kare
idanuwansa da hannunsa cikin wani irin tsoro da ganin
dirinta daya kusan tafiya da numfashinsa dan nan take
yaji wata sha'awa ta taso masa. Gabaki 'daya rikicewa
tayi tama rasa yazatayi ta fito dan wani santsi ke janta
yana maida ita tama kasa fitowa bare takai gurin
kayanta. Jin tasaka fitowa sai zamewa take yasashi
matsowa ya miqa mata hannunsa danshi amatse yake
data fice dan ya rikitu sosai ga qamshin turarenta daya
cika gurin. Qaf qaf tafara da idanu tana sake qoqarin
fitowa batareda takama hannun nasaba. Zamewa
tasakeyi shisaima tabashi daria ya saka hannuwansa biyu
ya 'daukota gaba 'daya aiko bai qarasa fitowa da itaba
santsi yajasu gaba 'daya suka fa'da cikin bathtub 'din
hannunsa ya bugi shower saiko ta fara sako musu ruwa.
Itace a qasa shine asamanta jikinsu ya ha'de sosai gashi
babu me kaya ajiki acikinsu Nan take suka shiga wani
yanayi sbd body contact dasuka samu. Qurawa juna
idanu sukayi basako qyaftawa duk da ruwan shower
dake xuba akansu. Hannu yasa ahankali ya matsar da
dogon gashinta daya jiqe ya 'dan hawo gefen fuskarta.
Cikin wani salo ya janye da gashin yana kallon tsakiyar
idanunta. Shafo gefen fuskarta yayi har xuwa wuyanta
cikin wani salo Taja numfashi ahankali tareda lumshe
ido. Kasa bude idonta tayi sbd fuskarsa dataji tana
matsowa xuwa tata. Da sauri numfashinta ke fita har
qirjinta na 'dagawa yana komawa. Qirjin ya qurawa ido
hankalinsa na qara ficewa daga jikinsa sbd ganinsu
farare tas acike tsaye acikin bra 'dinta suna daqawa suna
koma sbd numfashinta dake ja. Hannu yakai ahankali ya
shafosu cikin wani salo ai 'dauke huta tayi ta bude baki
numfashinta na fita ahankali ya maida kallonsa ga 'dan
bakinta bai tsaya komaiba ya shigar da nasa cikin nata
'din. Ahankali yake kissing 'dinta yana qarajin wata
fitinanniyar sha'awa na taso masa. Zare bra 'dinta yayi
yana ya jefar yana qara cusa bakinsa anata. Sam basusan
me sukeba dan kuwa tuni alamari yayi nisa. Qoqarin
rabata da pant 'dun jikinta yake ta dawo hayyacinta A
furgice ta zame tareda sakin kuka ahankali. Dafe kansa
yayi cikin tsananin kunya da takaici Dan baisan meya
hau kansa yatashi aikata hakaba. Dukkaninsu kasa motsi
sukayi sbd rashin kuxari Ita kuwa harda kunyar tashi
take yaganta tunda yayi wurgi da bra 'dinta. Saidaya
tattaro 'dan guntun kuzari ya mike ya fito ruwan ya fita
Saigashi da jallabiya fara tas ta maza da wani farin towel
ya miqa mata ya juya dan idan ba haka yayiba taci gaba
da zama gurin xai iyayin komai danko yanxu saidaya
yaqi shai'dan sbd baita'ba jin sha'awa kamar yau 'dinba.
Goge jikinta tayi tana rawar jiki kafin ta xura rigar daya
bata batareda ta tsaya 'daukar bra dinta ko sauran
kayanba ta fito kanta na qasa ta fice da sauri harta
tuntu6e. Tunda take saukowa haj xeenay ta hangota
amma ta kasa gasgata abunda idanunwanta suka hango
mata. Murza idanuwa tayi taga tabbas rigar tameer ce
ajikinta kuma ga kanta a jiqe sharkaf da ruwa. Wani
rikitaccen gumi ta sharce tana jinjina kai har nazli ta
shige 'daki. Lallai nayi sanyi tunda har nayi saken da irin
haka tafara faruwa. Wlh babu tsinanniyar macen data isa
ta haihu a zuriyar gidan nan tunda ban haihuba ko
meenah bazan bari ta haihuba kozanyi yawo tsirara bare
wannan shegiyar. zanyi maganin komai Kowama ya huta
kona samu nutsuwar zuciya. Adaren kasa bacci yayi sai
juyi yake dan baitaba tunanin shi 'din mai cikakkiyar
lafiya bane sai yau dan gabaki 'daya ya birkice buqace
yake. Ita kuwa zuru tayi akwance tana tunani me ciwo ko
hawayen takasayi sai radadin zuciya.
โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ Tunda wannan abun yafaru tafara
'boye masa. Bata shiga aiki saiya fice hakama abincinsa
tun bai dawoba take kaiwa ta aje ta ficewarta dan ta
tabbatar da sonda take masa zai iya rinjayarta duk da ita
tasan ba haramun bane to shifa? Yazai 'dauki abun?
*********** Yau gidan ba kowa saisu sbd yaune suke
bridal night amma fir tameer yaqi xuwa dan sam kamai
na auren baya kansa. Basusan dazai dawoba suka dawo
gidan cikin isa da qasaita. Nafisa haj xeenat takira a waya
tace tafa'da mata tana neman nazli yanxu. Fadawa nazli
saqon haj xeenat tayi sukayi shiru cikeda tunanin me
kuma zaifarune kaba komai yau batajin kanta daidai. A
daidai stairs suka tsaya nafisa tace, Nazli duk abunda
zasuyi miki kadaki yadda dasu dan zasuyita amfani
dakene suna biyan buqatarsu. Sawo kai yayi apalon cikin
qasaita kuma kunnuwansa sun 'debo mai zancen nafisa
na qarshe datace " yadda dasu dan zasuyi amfani dakene
gurin biyan buqatarsu" Komawa nafisa tayi ita kuwa ta
haye stairs 'din cikin faduwar gaba. Tana shiga suka
kalleta a wulaqance kafin haj xeenat tace, Ba 'bata lokaci
xamuyi ba abunda zamu da'da miki yanxu shine an
canxa shara'di. Ma'ana rayuwar fannah itace fansa ga
rayuwar masoyinki. ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ ja da baya tayi cikin muguwar
ki'dima tana kallon bakin haj xeenat datayi xancen. Haj
kareema ta miqe tsaye tace, Bari kada mu barki a
duhu.fannah mukeson kisawa guba taci ta mutu idan
kuwa ba hakaba to tabbas a daren farkonsa zaisha guba
ya mutu. Qwarai kuwa dan haka kiyi gaggawar xa'ba dan
tafiya xamuyi. Bushewa xuciyarta tayi tafara tunanin
yanxu lokaci yayi daya kamata ta ringa tunani irin wanda
su basayi sbd ku'butar da masoyanta daga sharrinsu dan
tanajin qaunar fannah kaman yanda meer ke qaunarta
amma zatayi wasa da tunaninsu dan tsirar dasu fannah.
Hawowa stairs 'din yayi dan xuciyarsa takasa nutsuwa
aiko yana riqe handle 'din qofar xai shiga yayi dai dai
data fara magana ya tsaya cak yana sauraronta. ZAN
BAWA FANNAH GUBA TASHA TA MUTU NIMA NA HUTA
DAN NAGAJI DA WANNAN WAHALALLIYAR RAYUWAR.
Cikeda farin ciki suka miqe suka shige uwar 'daka
batareda tunaninsu yabasu plan ne tayiba sbd sun san
zatayi komai kan tameer. Wani wawan jirine ya 'dibesa
yayi saurin dafa bango idanunsa suka ka'da sukayi jajir
Wata mummunar tsanarta ta rufesa, Qanwarsa dayafi so
dakomai ita zata kashe masa da guba. A fusace ya banka
qofar ya shiga. Tsaye take riqeda qullin gubar dasuka
bata sai wayarta dake hannunta tana shiein fitowa. Duba
palon yayi babu kowa sai ita ka'dai tana waya tana fa'dar
kashe fannah xatayi. Jikinsa har mazari yake ya shaqota
xatayi magana ya 'daga hannu ya sharara mata
kyakkyawan marin dayasa hancinta 6arewa da jini... TO
FAH..... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰ mamuh geee [7:39pm, 15/01/2017] โ“‚amuh
geee: ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜†
Husnah bbchoudiallo 176โ†’180 Damqo hannunta yayi
yafara janta zuciyarsa na tafarfasa. Ji yake inama baije
kunnuwansa suka jiyo masa itaba. Jan qarfi yake mata
ido jajir saidaya kaita tsakiyar palonsa ya wurgar da ita
ta xube a qasa idanuwanta jajir sbd tashin hankali
Kukama sam baiga gurin xuwaba dan abun yafi qarfinsa.
Cikin karaji yace, Ke wacece? Me kikeyi anan cikinmu?
Meye dalilinki nason kashemun fannah? Waya saki? Wa
kikewa aiki? Wa....... Jikinta rawa ya 'dauka tashin hnkalin
da bata ta'ba jiba ya dirar mata ta matso ta xube a qasan
kwance ta kama qafarsa a ru'de tafara fadin, Wlh bazan
ta6a cutatarda kai ba bare abunda nasan kana tsananin
so, Koba dan kai ba vazan iya cutar fannah ba sbd
halaccinta gareni, Dan allah kada kayi xargina walh
bazan iya cutar...... Cakumota yayi jikinsa har rawa yake
tsabar 6acin rai Fuskarnan tayi jajir Ya maqureta abango
da qarfi yace, Jst tell me d damn truth who the hell are u
before i do sumtin crazy. Duk tashin hankalin data shiga
abaya baikai mata wannan ba dan yau tameer ne
dakansa ke... Jijjigata yayi da qarfi kamar qato dan
uwansa Sai alokacin wasu hawayen baqin ciki da takaici
suka gangaro mata ba abunda takeso sama da mutuwa
alokacin. Sakinta yayi ta xube qasa a zafafe ya bu'de
fridge 'din palon ya 'dauko robar swan 'daya ya bu'de ya
finciki qullin gubar ya fazge ledar ya juye acikin ruwan
jikinsa sai cira yake Ya 'dago hannunta yasa mata tana
durqushe jagwaf sai hawaye take cikin baqin cikin
kasancewarta araye hartaga wannan baqar rana. Cikin
wata irin tsawa da karaji yace, Kince ba kasheta xakiyiba
then prof yourself and drink it. Qura masa ido tayi
hawayenta na qara gudu ga idanun sun ka'da jajir sbd
tashin hankali. Cikin tsakiyar idanunsa take kallo gaba
'daya ya juye kamar wani xaki. Prof me wrong and drink
it idan kuwa ba haka walh i wont spare you Hannun
police xan miqaki harsai kin fadi abunda yasa kikeson
kashe qanwata. Tabbas rayuwarta batada wani sauran
amfani gwara tasha ta mutu kowama ya huta

Please Login or Register in order to submit comment