Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_


```ALHMDULLIHI ALLAH abun godiya da ya bani ikon cigaba da posting din labarin DA'IMAN ABADAN BOOK TWO (SANADIN SHI),fatan zaku bani hadin Kai kamar yanda kuka bani a baya...yanzun aka fara wasan fa🥰```

*Daga tafiya hutun sati biyu ya zama complain oooni Jameey🤔 daga groups har DM maganar kenan yayi yawa yayi yawa to mun dawo ko satin d'aya ma ba ku bari munyi ba🤧,sai a cigaba da gashi sai dai Babu posting Saturday and Sunday Thank myluv's💋🥰*

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba,ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*1-10*

Abincin aka kawo masu na saukar amarya.masace da sinasir sai miyar ganye da taji kafar sa.sai kuma wata miyar kabewa ta aka wadatata da zallar hanta.wata kular kuma soyaiyen naman kaza ne a cikin sai kuma dayar ragadadar kan ragone.sai catoon din ruwa da kuma na lemuna kala kala.haka aka kawosu aka ajiye gabansu.
Sai sannu da zuwa Meelat take masu ta rasa Ina zata ajiye su dan dadi Meelat kanwar Najeeb ce uwarsu d'aya ubansu d'aya anan cikin abuja itama take aure.sai kuma Sema ita kuma kanwar Moha ce.kamar yanda Moha da Najeeb suka taso Kai daya haka ma Meelat da Seemarh haka suka taso.tare ake masu komai har hatta course d'aya suka karanta a turkey B.S.C.NURSING,kuma rana d'aya aka yi masu aure.
Meelat da kanta ta zuba masu abinci sai da ta fara kai ma Zubaida sanann ta zuba ma Zulaihat ta kai masu sai sannu take masu.yanda tayi masu kuwa sunji dadi dan har nuna sukayi.ita dai Zubaida ta samu ta dan ci kadan dan yanda take jin yunwa ba zataji zata iya kyale abincin ba gashi kuma kamshi sai tashi yake

Ita kuwa Zulaihat yanda aka ajiye mata abincin haka ta zuba mashi ido tasa sa hannunta a ciki ba dan bata jin yunwa ba,tana jin yunwa abunda ke yunwa sai dai bata jin zata iya cin wani abu a halin da take ciki.
Ta kasan ido take kallon movement din kowa tana ankare da komai.tana ankare da yanda yan'uwanshi suke cikin walwala da farinciki tana mamakin yanda ya fita zakka a cikin yanuwanshi.duk fuskar da ta kalla sai taga annnuri a samanta kamar dai fuskar Dr Moha,amman shi ne kadai ya banbanta da halin yan uwanshi bashi da annurin fuska ko kadan.

Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin yanda zatayi rayuwa da shi da irin wanann halin mai wuyar sha'ani.gani take bata iyawa dan ba zata iya dauka ba.ji take kamar tabi yan kawo amarya su koma tare dan ita bata iyawa.komai ya kwance mata tama rasa ta ina zata fara da wanann mutumin marar mutunci da tausayi.
Furzar iskan bakinta tayi tana cewa a cikin zuciyarta.."zan iya yes zan iya zan koya maka hankali zan baka mamaki Najeeb zan nuna maka Da da yanzun akawai banbanci na shirya zama da kai da ko wani irin hali kazo dashi kuwa."

Dangin su Najeeb basu bar shashen da aka sauke amare ba sai da goma tayi sanann suka yi masu sallama suka tafi.dan kuwa Shuraima makale kafad'a tayi tace ita a wajen Zulaihat zata kwana ba yanda ba'ayi da ita ba amman taki yarda har da kukanta ganin tana kuka yasa Zulaihat saka baki akan a bar mata ita.
Daman bata son tafiyar yarinyar duk da ba wata magana take mata maitsawo ba amman tana dan yaye mata wani pain din,ajiyar zuciya Yaya Seemarh tayi tana barin Shuraima dan ba yanda zatayi,amman taso ta biyota suma su Zubaida sun samu su dan sake suyi fira da yan uwansu tun dai gobe zasu tafi.flight din rana zasu bi
Bayan tafiyarsu Zubaida ta fara tashi dan shiga wanka dan daman a takure take. Tana fitowa Zulaihat na shiga wankan bayan ta fito sauran yan rakiya suka shiga kowa yayi shirin bacci,dan kafin su gama shiryawa har Shuraima tayi nisa a bacci.gyara mata kwanciya Zulaihat tayi tana kureta da kallo.tana bala'in kama da Najeeb dan dai kawai Najeeb ya dan fita haske da kadan.ita tana da duhu sabanin shi da yake da haske shine kawai banbanci, Addu'a ta tofa mata sannan itama ta kwanta tana yin Addu'ar baccin itama.

Ita kowa Zubaida waya tayi da Moha dan sun dade suna wayarsu yana mata ya gajiyar biki da kuma Allah ya albarkaci aurensu ya basu zaman lafiya ya kuma kauda fitina,basu bar wayar ba har sai da bacci ya dan fara fisgarta sanann ya kashe wayar ya barta ta kwanta itama.
Najeeb tunda aka daura auren aka kawosu bai sata a Ido ba,kuma bai nemaita ko a waya ba,shi hidimar gabanshi kawai yake dan baka cewa shine aka kawo ma amarya,dan fuskarshi sam bata nuna a wani situation yake ciki ba akan auren nashi..Koda ya shiga cikin gidan part din Hajja haka danginta na wudil da su kazo bikin suka kama yi mashi tsiya wai kamar ba ango kodai auren dole akayi mashi?shi dai sai dai yayi murmushi kawai dan ciwon kai ma yake fama dashi.

Part dinsu ya koma ya kwanta ko ya samu relief yana cikin Bacci Khalid ya shigo ya tada shi yace ya tashi ya fita anan za'a sauki amare sai angama walimar da za'ayi gobe za'a kaisu gidansu,ba haka yaso ba yaso kawai a sauke su a idu estate.haka ya tashi yayi wanka yayi covering din duk abunda yake bukata ya abar part din..bai sake dawawa gidan ba sai dare kuma Koda ya dawo yana kallon yanda Moha yake waya da Zubaida yana nuna mata soyayya da taitali da kula,ko a jikinshi ko dan kishin nan babu bari shima ya kira tashi matar babu,ruwa kawai ya watsa yayi kwanciyarshi ya cigaba da baccin shi.

*Washe gari*

Suna tashi Aunty Maimuna kanwar mamar Zulaihat tasa suka shiga wanka suna fitowa ta fiddo masu wata Holland wax mai kyau wanda Umma ta dinka masu tace su saka,ko mai basu shafa ba kayan kawai suka saka suka daura dankwali dauri mai kyau sannan suka fasa turare..bayan su Aunty Maimuna sun fito wanka suka shirya sai ga Aunty Meelat da Aunty Seemarh sun shigo masu da breakfast dinsu.
Butter yam ce suka soya masu sai kuma,Fish ball da kuma cous-cous plantain da Kunun semovita da yaji kayan kamshi rasa bakin magana Aunty Maimuna tayi dan al'ajibi da mamaki wa'anan iyayen abinci da aka kawo masu kamar ba gobe...godiya sukayi suna mamakin karanci da dattako irin na wa'anan mutane.basu da k'amar tallaka ko su nuna sunfi mutun suna da sakin fuska da son mutane dan tunda suka zo ake hidima dasu kuma duk shigowa da iyayen angwaye zasuyi sai sunce sun gode da aure da aka basu.

A gaskiya kam su Zubaida sunyi dace da mutanen kwarai masu mutunci da dattako.komai na mutanan gidan abun sone da birgewa ga hadin Kai kamar ciki d'aya suka fito baka gane dan wanann da dan wanann duk d'aya suke.sai dai ta kama ake gane su ta kamarma ba sosai ba dan rabin jikokin da iyayensu maza suke kama yan kadan ne suke kama da matan duk da duka yaran gidan su goma ne gidan su Najeeb suna da hudu.Najeeb ne babba sai Jamila suna kiranta (Meelat) sai Khalid Shuraima ce auta.a bangaren su Moha kuma su shidda ne.Moha ne babba sai Simatu suna kiranta( Seemarh) sai Khadija suna ce mata (Khadi) sai Ummul Salma (Salma) sai Ummulkhari(Khari) sai kuma Abdullah(Babbo).

Yawan gidan kenan,kuma iyayen sun hada kan yaransu gwanin sha'awa da burgewa.bayan sun gama cin abincin Khadi ta shigo ita da Salma da yake twins ne su daman.har kasa suka duka suka gaida su Aunty Maimuna sanann suka ce.
"Aunty Zubaida daman Aunty Meelat tace muzo mu gaya maku ku shirya anjima kadan mai makeup zasu zo suyi maku makeup."kallonsu Zulaihat tayi tana cewa.."Salma makeup kuma.?"d'aga mata kai Salma tayi murmushi dauke a fuskarta tace.."eh Aunty Zulaihat ko kin manta anjima za'ayi walima.?" Dan murmushi tayi itama tana kad'a kai tace.."hakane kuma,amman ni dai idan ba damuwa ba sai anyi man ba." Waro Ido waje Khadi tayi tana cewa."rufamana asiri Aunty Zulaihat so kike Yaya Najeeb ya balla mana kafar baya ko.?" Anshewa da cewa Salma tayi.."wallahi rashin maki wanann kwaliyar masifa ce a wajen Aunty Meelat tabb har bansan mai zance ba Yaya Najeeb yanda ya shirya ma bikin nan azo walima yaga ba'ayi maki makeup ba ai sunanmu sorry."

Tagumi Zulaihat ta buga tana kallon yanda suke ta karma dan kawai tace bata bukatar kwaliya.baiji dadin halinshi ba kam tunda har kannenshi bai daga ma kafa ba kenan?ta aiyana a zuciyarta lumshe ido tayi tana budewa tace."karku damu ba abunda zaiyi maku tunda nice nace bani bukata ai."

Girgiza kai Salma tayi tana cewa.."mudai gaskiya a'a ki rufamana asiri dan Allah Aunty bari ma na tashi muje ma kafin masu makeup din suzo." Dan bata fuska tayi tana cewa."nidai ai na gaya maku dai ko.?" Dariya sukayi suna ficewa daga part din kawai,dan sun lura bata san halin mijinta ba, shiyasa take cewa haka suna zaman zamansu ta ballo masu august ba da su ba kam,Koda suka koma part din Mom suka tadda su Aunty Seemarh suna ta shirya yanda walimar zata kasance.zama sukayi suka gaya masu yanda sukayi da Zulaihat sun kuma nuna masu ba yanda basuyi da ita ba amman fir tace ita bakuta.
Murmushi Meelat tayi tana cewa.."ku rabu da ita kawai bakunta ce ke damunta,na lura tafi Aunty Zubaida bakunta da rashin son magana." Dariya Seemarh tayi tana cewa.."tun jiya nike mamakin halin Aunty Zulaihat wallahi kusan shegen halinsu d'aya da mijinta na rashin son magana."..."Kinga kenan hadin yayi sai suje can su karata dan daman ba mai iyawa da wanann halin nashi sai ita din tunda a haka ta yarda da auren shi." Cewar Meelat tana dariya haka suka kama labarin Zulaihat harda Zubaida ma har wajen 3pm lokacin sun gama tsara komai da komai.basu bar part din Mom ba sai da masu makeup sukazo sanann Seemarh da Meelat suka fito dan kai su wajen amare su fara nasu aikin kafin lokaci yayi dan basu san ayi african time a walimar.

Da sallama suka shiga room din da suke zaune,ansawa sukayi suna masu sannu da zuwa, zama sukayi suka gaisa suna tambayar babu matsala dai ko?da eh suka ansa sannan Meelat ta fara cewa.."Aunty Zubaida ga masu makeup din nan su iso nasan dai kunyi wanka sai su fara aikinsu ko.?"

Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."to mungode Aunty Meelat Allah ya bar zuminci." Murmushi itama Meelat din tayi tana cewa."Dan Allah rufaman asiri karda ki sake ce man Aunty karda kije man hukunci a wajen su Yaya." Ita Zubaida abun dariya ya bata sai da ta dan dara tana cewa.."haba Aunty Meelat maiye dan nace maki Aunty?ai ke Auntyna ce dan kin girmaini sosai fa." Murmushi tayi tana cewa.."duk da haka dai ya yafe maki ki kirana Meelat,kuma ai ke matar Yaya ce fa." Murmushi kawai Zubaida tayi bata sake cewa komai ba,dan marairaice fuska Zulaihat tayi tana cewa.
"Dan Allah Aunty Seemarh ba sai anyi man wanann kwaliya ba nikam nagode."kama baki sukayi suna kallonta dan har sun manta da su Khadi sunce masu tace bata son makeup ,kara basu mamaki tayi tana cewa.."Haba mana Aunty Zulaihat tsakani ga Allah taya za'ayi kice baki son kwaliya sai kace ba hidimar bakinki ake ba?Dan Allah kiyi hakuri ayi maku Koda yar simple ce."

Girgiza kai tayi tana cewa.."Dan Allah nima kuyi hakuri kawai dai kwaliyar ce naji bani son yi shiyasa." Cikin shagwabar ta ida maganar ,dariya sukayi a tare suna cewa.."aikuwa dai sai anyi maki kwaliyar nan gaskiya idan kuma kika ki yarda yanzun nan zan kira Yaya Najeeb na gaya mashi kince baki son kwaliya kinsan dai halinshi." Kasa tayi da kanta tana cewa.."nidai nidai dan Allah ku barni da maganar makeup din nan." Ba magiyar da basuyi mata ba akan tayi hakuri amman taki ji,har sai da Zubaida ta saka baki akan ta yarda da ayi mata amman ta makale kafad'a tace ita fah Aa,kawai a daura mata dankwali kawai taji zata yarda ayi mata,amman banda kwaliya suna cikin wanann dramar Seemarh ta tura ma Najeeb massage ta gaya mashi hamar da suke da Zulaihat,bayan ya gama karantawa yayi reply dinsu da su tafi kawai gashi nan zuwa.

Kwance yake a lokacin da ta gaya mashi, kallon time yayi yaga har hudu tadan wuce tashi yayi yana tsaki,kallonshi Moha yayi yana cewa.."lafiya dai ko.?"sake sakin wani tsakin yayi yana cewa.."Ina fa lafiya,yarinyar nan ce wai tace ita bata son ayi mata makeup ba yanda su Seemarh basuyi da ita ba,amman ta kafe ita bata so shine Seemarh ta gaya man yanzun." Gargiza kai Moha yayi yana cewa.."Ina ruwan Zulaihat uwar yan rigima.yanzun ya za'ayi.?" Tashi ya ida yi yana cewa.."ya fa za'ayi banda naje mata yanzun nan,kasan dai halinta idan ta kafe waje daya dai ko.?" "Hakane kuma amman dan Allah idan kaje ka bita a sannu karda kayi mata wanann gadarar taka." Tsaki kawai yayi yana daukar key din motarshi ya nufi lifecamp estate.

Cikin mintinan da basu wuce goma ba suka kawo shi lifecamp samun waje yayi.yayi parking din motar shi bai tsiya biyawa ko wane shashen ba,direct part dinsu ya dosa dan daman already yasan a can aka sauke su.koda ya shiga cikin sa'a bai tadda kowa a parlorn ba hakan yayi mashi dadi dan baya bukata asan da zuwan nashi har ya tafi,tunda ta taso shi rashin jinta da kafiyarta sune suka kawo shi a wajen.kwafa yayi yana mai shiga a room din Khalid dan yasan ba kowa ciki dan daman a room dinshi aka sauke su room din Moha kuwa kallo daya yayi mashi ya gane anan ciki za'ayi makeup din.
Yana shiga ya samu gefen gado ya zauna yana cire hularshi,wayarshi ya lalubo yana danna ma Seemarh kira,tana can room din Moha suna fama da Zulaihat akan tayi hakuri ta yarda amman taki,dan da taga sun matsa mata sai ta fara yi masu kuka,suna cikin dramar ya kira wayar dauka tayi tana gaishe shi ko ansa gaisuwar tata baiyi ba yace.

"Ina room din Khalid dan turoman ita." Da to ta ansa ya kashe wayarshi sai tsaki yake dan har yanzun ciwon kan bai sake shi ba,gashi tana neman daura mashi wani ita kuma, Seemarh tana kallonta tace.

"Kinga ko Aunty Zulaihat gashi nan ai ko,yanzun dai tashi kije Yaya Najeeb nacan dakin Khalid yana jiranki." Take taji wata yar'juwa na neman kwasheta sai da ta rintse idonta sannan ta bude tana kara kwabe fuska tace.."wani Yaya Najeeb din.!?"Yanda tayi tambayar a tsorace ya basu dariya,sai da suka dara sannan tace.
"Wane Yaya Najeeb kuma bayan mijinki,ki tashi kije karda ki kara ma kanki wani laifin dan shi bai son jira da bata lokaci." Matse hawayen fuskarta tayi tana sharewa sannan ta tashi bace masu komai ba ta dauki hijab din Aunty Maimuna ta zura har kasa tana neman hanyar fita,rikota Meelat tayi tana girgiza kai tace.
"Haba malama mai kuma ya kawo ki saka hijab sai kace zaki isilamiya kuma."kamar daman tana jira sai kawai ta rushe masu da kuka bata ce masu komai ba.rufe baki Seemarh tayi tana cire mata hijab din tace.."wai Allah haka daman kike Aunty Zulaihat da saurin kuka,aiko Yaya Najeeb yana da aiki a gabanshi kam." Ita dai da Ido kawai take binsu tana kukanta duk da sautin kukan bai fita sosai,wani dan veil ta dauko ta yafa mata tana fasheta da turare sannan ta kama hannunta suka fito.

Dai dai bakin kofar ta tsaya tana yin nocking sai da ta buga kusan sau ukku sannan ya bada ikon shigowa,bude mata Seemarh tayi tana juyawarta dan tasan hali karda ta shiga ya zama laifi indai a wajenshi ne to shi laifi bai da wuya,kana iya ganin kana yin komai dai dai shi yazo yace bakayi dai dai har ma ya hauka da fada wanann halinshi ne.
Da sallama ta ida shigowa ta turo kofar ta kuma dakare a bakin kofar tana kallon gefe,kuma hawayen fuskarta basu daina zuba ba,shi kuma bai dago ba bai kuma motsa ba,wayarshi kawai yake latsawa bai ko kalli inda take ba,bai nuna yasan da shigowar mutun ba ,duk da kuwa ya ansa sallamar da tayi amman can cikin zuciya ya ansata.

Ta kusa shafe minti biyar a wajen tsaye ganin bai da niyar taka mata yasa ta bude baki tana cewa.

"Gani."

Nan ma banza yayi da ita ya cigaba da hidimar gabanshi,sai da tayi maganar da kamar two minutes aka kwankwasa kofar matsawa tayi daga bakin kofar tana cinno baki gami da share hawayen fuskarta,can taji yace.."yes come in." Wani kukane taji yana neman subuce mata ,gyalen jikinta ta tura a baki tana rushewa da shi,tsab yake jin kukan nata tunda ta shigo da kuma kara mashi volume da tayi, lumshe idonshi yayi yana ajiye wayar a size dinshi yace.
"Zo nan ki zauna." Yanda yayi maganar babu wasa a fuskarshi yasa itama ta kama kanta dan ita yanzun wani sabon tsoranshi ya kara shigarta tun daga ranar da aka daura masu aure,jiki a sabule take jan kafafun nata har ta iso inda yayi mata nuni da ta zauna ta zauna,kanta kasa sai ajiyar zuciya take saukewa ,dogon tsaki yaja yana nunata da yatsa yace.

"Zakiyi mana shuru ko sai nayi ball dake?Mai akayi maki zaki kama yi mana kukan banza da wofi?maza share hawayen nan ko na karyaki pieces wallahi." share hawayen tayi tana shanye kukanta tana mai yin kasa da kanta,tausayi ta bashi yasan daman wannan kukan gamashi a wajenta ba yanzun bane,rabuwa da iyaye ba sauki bane balle ma yanda suka saba da Umma tunda suka taso tare suke basu taba rabuwa ba sai ta sanadin aure dole kam a daga masu kafa su danyi kukansu, amman ita nata kukan ya zarce misili aita abu daya ba ko gajiya kuma ba'a gudun ciwon kai.

Kamo hannunta yayi yana girgiza mata kai cikin cold voice yace."kukan ya isa haka madam,and baki gudun ciwon kai.?" Shuru tayi bata ce komai ba sai ajiyar zuciya da take ba dai tace komai ba,Shima bai sake cewa komai ba har mai makeup ta shigo ita da Seemarh nuna masu waje yayi yana tashi yace.

"Gata nan kuyi abunda ya dace." Murmushi kawai Seemarh tayi tana ba mai makeup izinin fara aikinta,cikin ikon Allah kuwa ta fara dan daman time ya kusa dan 5pm za'a fara walimar,Shima ganin an fara har an danyi nisa ya tashi ya tafiyarshi ya bar masu wajen.tunda aka fara batace komai ba kuma bata kallesu ba sai ma kulle idonta da tayi ta sakar masu fuskar sunyi yanda suka gadama da ita,

★★★

Koda ya koma bai tsaya surutu ba da abokansu ya fada toilet yayi wanka ya shriya sanann ya zauna yana kallon Kb yace.."wanann kallon fah." Tuntsirewa da dariya Kb yayi yana cewa.."A'a bakomai ai in ana sallah ba'a magana,fatan dai ka baro amarya lafiya." Tsaki yayi yana daukar wayarshi ya fara latsawa dan ya fahimci inda maganar Kb ta dosa,kuma shi baida ra'ayin yin ta,dariyar shakiyancin suka cigaba da yi mashi suna cewa ya cika fitina da yayi hakuri ai yau dai za'a kawo mashi ita yayi yanda yake so ba sai ya bita har can ba dan rashin hakuri da tsabar jaraba irin tashi.

Sai dai ya girgiza kai ko kuma ya balla ma Moha harara idan suka hada ido dan yasan babu magulmacin da yace yaje can gida sai Moha dan gabanshi ya tafi ba kuma sunan basu Kai da zuwa ba balle yace.sai da suka gaji dan kansu sannan sukayi shuru..karfe biyar da rabi suka fito dan tafiya wajen walima,dan shrda sukayi hama da Najeeb sanann ya yarda zai bisu,dan shi kam cewa yayi walima ta mata ce mai zai kai maza a wajen?sai da sukayi da gasken gaske sanann ya tashi ya kara yin wanka ya shirya suka nufa gida,da yake a gidansu za'ayi walimar dan suna da babban filin da zai dauki mutane sama da mutum 500 ba tare da sun takura ba.

★★★

Masha Allah!Amare sunyi kyau mai suna kyau kuwa dan kwaliya aka tsara masu ta gani da fada.dan sosai masu kwaliyar suka natsu ko wace ta tsara ma wanda tayi ma kwaliyar bajinta kamar a daukesu dan kyau.lace ne black mai ratsin pitch color a cikin,sosai laces din yayi masu kyau,da yake dinkin teabubu ce akayi masu sai kayan suka kara masu girma suka maidasu manyan mata,duk da kwaliyar ba mutan daya tayi ba,amman ba zaka ce ga ta wanda tafi kyau dan kallo daya zakayi masu su bude maka Ido ka kasa fidda gwani a ciki.
Gidan ya cika tam da jama'a dan su Mom ba karamar gaiya sukayi ba,da yake daman bikin babu wani event da akayi tun daga kanon har abuja dan amare cewa sukayi basu bukata.koda ma sunce ayi wa zaizo masu? suda ba kawaye garesu ba,to nan ma abujar basuyi komai ba sai walimar nan da za'ayi a yau,dan ba karamin shirya mata Mom tayi ba,ta kashe kudi bata san adadi ba,tun daga kan abincin da za'aci har zuwa sabeniyas din da za'a raba zuwa da dauko masu decorations da kuma photography din da zasu dauki hotona a wajen ita ta dauko su,ita kuma Ammie masu wa'azi ta dauko wanda zasuyi dan short wa'azi na 20-30min.
Wajen ya tsaru iya tsaruwa dan sai da kowa ya samu kujerar zama ,daga sama kuma aka tsara wajen da amare da anguna zasu zauna,sai da kowa ya gama zama aka natsu aka maida hankali wajen daya sanann Mom
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment