Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Qaddarata S3 na Yar Mutan Kankia



_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


_Allah sarki buwayi gagara misali godiya ta tabbata agareka ya ubangijin talikai Allah kayi tsira ga fiyayyen halitta annabi Muhammad da iyalansa sahabban sa baki daya,ameen._


```Tom jama'a kunsan ance rayuwa cike take da kalubale da kuma QADDARARORI Kala Kala, ko wani bawa da tashi qaddarar maikyau da akashin haka, cikaken musulmi shine yayi imani da qaddara maikyau da marar kyau shine cikan imani, to haka rayuwar Amina charanci take kunji yanda labarinta ya kasance tun daga ALKALAMI SEASON ONE kukaji BAKIN JININA YA JAMAN SEASON TWO to gamu a cikin QADDARATA SEASON THREE kenan, sae ku cigaba da biyoni ni YAR'MUTAN KANKIA dan jin yanda Qaddarar Minal charanci zai ta kasance😢, Allah ya bamu ikon yarda da qaddara Amin👏```


```Note kuyi hakuri masu yi man magana ta private da masu comment banda lokaci Ina busy ga karatu shiyasa ban cika baku ansa ba kuma inajin dadin comment din sosae a cigaba da yi hakan na sani nishadi sosae```

*Ya Allah nagode maka da kabani ikon rubuta littafin nan yau 27/9/2021 cikin koshin lafiya da kuma cikin aminci kayafe mana kurakuren dake ciki🙏.*


_NO EDITING_


S3/E1&2




*******Ita rayuwa da kuke gani kowa da tasa Qaddarar,kuma ba yanda bata zoma ɗan Adam saidai ba kowa ke cin jarabawar da ubangiji ya daura masa ba,ni kuma haka tawa Qaddarar tazo mani ban shiryaba,batareda na fargaba,hawayen idanuna kullin suna kwaranya a idanuna idai bansan dadin rayuwa ba,narasa komai nawa,idan nace komai ina nufin farin ciki.

Farin ciki shine cikar kowane burina na Adam arayuwa saidai QADDARATA ta nisantani da duk wani farin cikina!.....

Amina Caranci kenan wadda duniya tai mata daurin goro rayuwa tai tsanani agareta komai ya rikici mata da tarin danasi,kunci,tashin hankali,fargaba,da kidima duk wadan abubuwan su suka taka rawa a cikin Qaddarar ta!


******_CIGABAN LABARI_



Allah mai kowa mai komai shike tsara komi a yanda yaso kuma sadda yaga dama,yau nice cikida farin ciki na anshi Certificate dina na Medicine nagama da sakamako mai kyau,harnayi Intership a sabitin Murtala dake kwaryar birnin Kanon Dabo.

Ina gamawa nahau shirin tafiya NYSC dina a ENUGU can nayi Camp dina na kusan tsawon wata daya daga can nayi relocation zuwa gida Katsina a FMC nasamu nayishi nasamu alkhairi a tsakanin Intership dina Dda NYSC dina,a haka nagama alhmdullh na samu Expriences sosai,yanzun aiki nike nema gadan gadan cikin ikon Allah.


Koda nadawo gida dan zaman da nayi gidan mu banda wata damuwa,musamman wajen mahaifina yana ciki gaba da bani duk wata kulawa daya kamaya uba yaba ya'yan sa hakama Mama tana iya bakin kokarin ta akaina.


Bayan kwana biyu ina zaune tsakar gidan mu ba lula a cikin nazarin rayuwa da yanda take zuwar mani in yau da dadi gobe sai ahankali,wayar hannuna ce ta hau ruri da ido nabi Screen wayar dake hannuna Iphone7 sunan Abdallah ya bayyana.

Fuskata dauke da murmushi na ɗaga wayar cikeda da zolaya nace.
Angon karni anata jiran tsammani ya aminiyar tawa."

Murmushi yayi mai sauti yace.
Amaryar kamshi barkan mu da arziki ansamu baby girl."
Wani uban tsalle na daka da hamdala abakina har saida Baba ya fito jin karata yana lfy.

Amsa ban iya bashi ba tsabar dadi,da kyal na tattaro natsuwa ta nayi kan Baba bansan na rungume shiba nace.

"Husna ta haihu Baba."
Masha Allah,eyeh su Mamana an zama manya wannan murna har haka barka Allah ya raya."

Sai lokacin na sunkuyar dakaina inajin nauyin mahaifin nawa bisa labbana nace ameen.

Ina shigewa dakina,lalubo number Fatash nayi duk da munrabu da gaisawa da ita zuwa yanzun alakarmu tai sanyi hatta Ya Hussein shima munja baya da juna duk da son shi ba abinda ya sauya a cikin zuciya ta saidai abinda nasani Qaddara itace ta raba tsakanin mu.

Dagawa tayi murya kasa kasa kamar mai kuka ko bacci,bandamu sa yanayin taba nagaya mata sakon Husna ta haihu.

Itama tayi murna,nan muka gaisa sama sama na kashe wayata duk da zuciya ta nasan ta tambaye ta Ya Taufiq amman bakina ya gaza tambayar ta har mukai sallama na yanke wayar.


Bayan kwana biyu muka shirya harda mama da Antyn su Asma'u da yan uwa sai gidan Asma'u mukai mata barka ranar farin cikin da muka shiga bai misaltuwa tunda naje narike baby sai da gaske nike badata a dauka,tinda nai tozali da jinin Husna sai Allah ya jarabceni da kaunar yarinyar har cikin zuciya ta sai nike ganin kamar kaunar da nikema Husna ne ya dawo kan yarinyar.


Ranar haka muka wuni har la'asar sannan muka nufo gida Caranci.


_*Noted:-Kafin inci gaba da wannan labarin inasan in sanar daku labarin Qaddara ta,akwai Fiction musamman inda aka tabo Taufiq,shima ba dukaba rabi da kwata is true saidai kadanne fiction,amman duk abinda ya shafi Amina ba fiction a ciki duk true ne hope kungane nufina,infact duk page din dakeda fiction zan sanar daku nagode*_


Ranar Monday ina zaune a falo ina kallon film din Tarkon Kauna na tashar arewa24 nida kannena hankalin mu kwance,wayana ta hau ringing,dauka nayi ina dubawa saidai new number ne kamar ba zan dagaba sai kuma na dauka,da sallama abakina.

Doctor Amina Yusuf Caranci ce online.?"
Yes am the one."
Okay gobe kizo asibiti interview FMC Katsina kizo da wuri."


Wani irin farin cikine ya lulube mani kasan zuciya ta,alhmdullh na iya furtawa.

Allah yakaimu lafiya.
Dakin mama nafada sai farin ciki nikeyi,kallo ɗaya Mama taimin tagane tsantsar farin cikin da nike ciki.

Wane albishir din ne aka zomani dashi Aminatu.?"
Rungumeta nayi nace.
Mama FMC sun nemeni gobe inje interview."

"Kai masha Allahu, gaskia bansan da wane baki zan fara godema Allah SWT ba saidai muyima Annabi Salati Allah yasa albarka ya kaimu lafiya,amman duka duka yaushe kikai CV dinki.?"

Wlh Mama nima nai mamaki kamar dai jira,amman nayi farin ciki,sosai."

Allah abin godiya duk daba abin mamaki bane,aishi Allah ba yanda baima bawan sa kyauta ta inda baiyi zatoba,kinga Allah yai maki gata da rabon ki gama karatu gashi har kinsamu babban rabo Allah yasa albarka."

Ameen Mamana tafi takowa.
Nikam nakasa zaune nakasa tsaye dan murna,fatana Baba ya dawo insanar mashi abin alkhairin daya sameni.


Koda Baba ya dawo anyi sallar isha'i yana gama cin abinci yafara kallan NTA News,da sallama bakina na shigo cikin falon shi.

Maido kallan shi yayi kaina shima murmushi yaimani mai nuna tsantsar so da kauna dake tsakanin ɗa da mahaifi.

Daganin bakin Mamana akwai magana a cikin shi,mike tafe da Mamana.?"
Sadda kaina nayi kasa saidai inata smile.
"Baba FMC sunkira Interview."

Alhmdullh Allah abin godiya Allah yasa albarka ya'ta gaskia bansan irin farin cikin da nikejiba a raina,Congratulation Mamana."

Thank you Sir am proud of you Babana."
Dariya yayi yanajin dadi,cigaba da yimani bayanj yayi akan aiki da rikon amana da kula da patient da duk sauran abubuwan daya kamata ki rike akan aikin ki.


Haka dai yaita yimani nasihohi har zuwa tara nakoma dakina,waya na dago da niyar ingayama Ya Taufiq sai kuma nafasa ganin dare yayi,nabari saida safe kafin in sanar mashi.


Washe gari da safe tunda wuri naje fcm duk abinda yaka mata anmani kuma duk na tsalleki komai succesful ,congratulation akaimani nadawo gida zuwa upper week zanci gaba da aikina,haka na dawo gida cikin aminci mai tarin yawa.

Da yamma kiran Husna nayi na shaida mata nasamu aiki,tatayani murna sosai,har Abdallah saida yatayani murna.

Inagamawa nakira Ya Taufiq kira na ukku ya daga cikin sanyayar muryar shi mai sakani sukuni dajin dadin.

"Princes how are you kin gujeni ko Minal.?"
Sihirtattar ajiyar zuciya na sauke kamar bansan magana nace.

"Aaa kana raina Ya Taufiq,albishirin ka.?"
Goro."
Fari ko ja.?"
Fari kyal mai kyakkyawar aniya kamar ki."

Nasamu aiki."
Alhmdullh ina kika samu aiki .?"
Fcm ne,department of Theater&Surgery."
"Amman natayaki murna Congratulation my cute baby."
Thank you so much my hope."
Murmushi yayi,muka taba fira kadan da haka mukayi sallama ina cikin farin ciki marar misaltuwa.


********Bayan kwana ukku,muka shirya zuwa sunan Husna,kaya na musamman na shiryama Baby da maijego saida nayi akwai guda na kaya,sannan nai mana kala Ukku anko nida Asma'u,shadda Lace,sai atamfa super mai masifar kyau,nida kanwarta muka tafi daren sunan.

muna zuwa mukahau preparation abinda za'aci na sunan,dayake nida Abdallah kusan kullin muna waya aikin mu mi za'aci tun kan inzo duk abinda ya kamaya nasa anware ankai aikin shi,abinda ya rage kadan ne,muna gamawa aka gau yimana lalle(Henna)
ranar wuni mukai muna fira nida Husna zan icewa kusan daren a zaune mukayi shi.

Washe gari da safe kuwa aka radama yarinya suna Aminatu,duk da suna mahaifiyar Abdallah kenan amman kusan ni akaima takwara,domin kuwa ko dangin shi da sukazo kowa cewa yake ina takwarar take sai anunani ana aikuwa sunyi kama da babyn.

Kowa dai yanata zolayata dadi kam wajena bai faduwa,yan caranci duk sunzo suna yan uwa da abokan arziki anci ansha masha Allah.

Kusan kaya iri daya muke sawa nida Asma'u da wanda nayo mana sai wanda taimana guda biyu iri daya,kayan da basuyi iri daya ba bai wuce kala biyu amman komai tare mukeyi gwanin burgewa,bakataba cewa Asma'u ba cikinmu daya ba,dan ta zame mani yar uwata ta jini,bakaramin shakuwa ke tsakanin muba saiya zama yanzun datai aure munfi da shakuwa da junan mu.


Ina zaune kusa da Asma'u sai Rukayya anata pictures din suna ina rike da Amina anata hotuna wayar Husna tai ringing Ahmad Idris (A.I.D) ya bayyana jikin screen din wayar,duk da kaina bai hakaito komai ba hakanan naji gabana yadan fadi kadan dagawa tayi tana Dr barka da yamma."

Yawwa mai jego gani a kofat gidan yanzun na iso."
Okay bari Minal ta shigo dakai."
Kallan tuhuma nike mata.

Dr Ahmad ne dan Allah ki shigo dashi falon Abdul."

Kallan bakida aikin yi nai mata.
Kamar ya waye shidin malama ban zuwa."
Hmm wato kedai Amina bakida kirki Allah shikenan bari mai gidan ya shigo dashi.

Uhmm kawai nace mata naci gaba da sabgogin gabana.

Bada jimawa ba,Hauwa'u ta shigo dakin da muke.
"Antyn wai Yaya yace ace maki bakon yana falon shi...toh shine abinda Husna ta amsa ta,mike tana miko mani Minah.

Tashi muje sai akawo mashi drinks ko.?"
Ke wlh ban zuwa waike wace irice kinyi bako baku fara gaisawa ba kawai sai in kwashi kafa inbiki,kije in kun jima ko lemo kila yasamu arzikin shi wajena.!"


Ohni Asma'u yau mi tawan kejine wannan ruwan rashin kirki Allah ya shiryeki Minal."

Ameen saidai ya kara dan ashirye nike."
Hmm kedai kikasani,taja gyalenta tayi falon Abdallah.

Nikam chart nike na saki posting din pic din suna sai viewing akeyi ana comment.

Masu Woow masha Allah nayi masu Allah yaima baby albaka nayi kowa da abinda yake cewa.

Thank you all narubuta nayi posting saboda DM din dayawa.

Zansauka kenan naga comment Ya Taufiq,hannuna na kyarma na bude.

"U re the best among the stars my Queen tauraruwar mata,i miss u tawan,Allah yaraya little Minal."

Wata siririyar ajiyar zuciya na sauke ina smile a fuskana.

"Thank you my king u re the hero handsome miss u too."

Emojis ya turomani na tsantsar jin dadi haka mukaci gaba da chat cikeda tsantsar kaunar junan mu datarin kewae juna,kiran Abdallah ya shigo wayana hakan yasa na sauka online ina dagawa...


"Angon jego."
Kizo falona kuma kitaho da drinks."
Okay,nace tashi nayi na dauki tray ina daura 5alive akai sai ruwan roba,samun dan karamin flat nayi na zuba snacks a ciki na tafi falon Abdallah.

Da sallama baki ina hankalina kwance kaina na kasa,amsa mani sallamar akayi take naji mummunan faduwar gaba ya dira a cikin zuciya ta,jin muryan daya daki dodon kunnena,a sanyaye na dago kaina na aza bisa fuskar.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️

_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E3&4



Dr Ahmad,wanda ya kafeni da idanun sa ko alamun keftawa baiyi,nima shi nike kallo daga bisani na sauke kaina kasa harna isa wajen shi,bisa center table na aje tire din, ina barsarwa kamar ba wani shock da jikina yayi dan kuwa wani irin nauyin shine ya rufeni tuno rashin mutucin da nai mashi harda barazanar kisa,zama nayi na maida kallona kanshi.

"Dr Ahmad how are you.?"
Am fine ,nice to see you again Aminatu."
Thanks.
Nace ina maida kallona bisa screen din wayata
Shiru ya kaure falon Abdallah ke cewa.
"Honey muji su gaisa ko.?"

Ya mike yana kama hannun Asma'u,nima tashin nayi zan bisu don banga anfanin gaisawar da zamuyiba tunda ba wata alaka a tsakanin mu.
Ki tsaya ku gaisa ina kuma zaki.?"
Kallan mamaki nikebin Abdallah dashi wanda yai maganar yaba hade fuska irin umurni yake bani,bude baki nayi zan mashi musu sai kuma na kasa sakamakon kallan daya sake jifana dashi sai yai mani kwarjini sosai dan dole na koma na zauna,suka fita tareda matar sa.
Shiru ya kaure wajen kowa da abinda yake sakawa.

"Gimbiya ta,nayi missing dinki ban tunanin zan daina daunar ki Aminatu bare in cireki a raina,ina sonki.!"
A raunani ya ida zancen nashi.

Wani kallan up and down nai mashi batare da raini ba, kawai ina mamakin karfin hali irin na Ahmad kaida akace ba'asonka har iyayen ka suka janye zancen auren daya shiga tsakanin mu,taya zaka dawo da wani labarin kuma.

"Nagode nima ina maka fatan alkhairi."
Numfashi mai zafi ya fesar yana dafe kanshi yace.

"Nasan baki sona Amina amman ni ina kaunarki har gaba da abada dan haka bazan maki tilas ba saidai inaso kibani dama ta biyu,mu dinga waya dan Allah."

Batareda naji komai araina ba nace.
Aaa Ahmad kayi hakuri bansan abun daya wuce ya dawo agareni son daka nuna mani ya watadar,na gode maka."
Shiru yayi yana nazari ya kuma cewa.

"Ina neman wannan alfarmar dan Allah Amina ki bari koba kullin ba muna gaisawa sannan dan Allah kitai maka mani idan kina bukatar wani taimako,awajena ko wane irine kofa abude take Amina inasan naga na kyautata maki ko yayane wala da kudina,lokacina ko kuma da karfina,na rokeki kada kice Aaa."

Shiru nayi narasa mi zancema Ahmad nidai Allah yasani bawai na tsane shi bane bansan alaka ta sake hadamu dashi gudun abinda zaije ya dawo,nidai bansan ya zanyi da lamarin nan ba.

Waving face dina yayi na shiga tunani,dawo da kallona nayi kanshi ganin yanata begging dina ya hade hannayen sa alamun roko,hakanan naji wani irin tausayin shi,ya kamani araina.

Shikenan na amince nima inafatan idan kana bukatar taimako kaimin magana matsawar baifi karfina ba zan maka."

Murmushi ya saki mai nuna tsantsar jin dadin shi.
"Inaida alfarma awajenki da yawa gimbiya ta kinsani ni mai barane agareki."
Uhmmm minene fada in maka idan inada hali."

Kina dashi da izinin Allah,inasan ki kasance dani akoda yaushe,ma'ana ki dinga daukar kirani kullin safe da dare ina gaisheki."
Rasa abin cewa nayi saidai jinjina kaina da nayi alamun gamsuwa.

Godiya yai mani muka hau fira kadan kadan."
"Na dauka kinyi aure Amina na shiga rudani da tsananin tashin hankali saidai Asma'u ta tabbatar mani baki aure ba sannan nasamu sukuni araina."

Hmmm aikuwa banba amman na kusa yi insha Allah,Amman kai kayi auren ko.?"
Aaa wlh banba ina nan dai."
Allah yakawo ta kwarai.
Bai amsani ba,duk mukai shiru kowa yana tunani aran shi,mikewa nayi.

"Zan shiga ciki inatayin baki nagode da karamci."
Shima mikewar yayi yace.
"Ameen gimbiyata nikeda godiya da wannan tsadaddan time din da aka bani."
Never mind .
Fita nayi na shiga side din Asma'u mukaci gaba da hidima nan aka hau kidin kwarya,sai biyar na yamma yan Caranci suka fara azamar tafiya harda su Mama dagani sai kanwar Asma'u da Antyn su sai Yayar Mamar su aka bari,sai washe gari idan anyi soye zamu wuce gida.


Hussein Pov.......


"Mum dan Allah kidaina yawan kawo zancen nan ba abinda zai sauya Qaddarata nasan koma minene haka Allah yaso haba Mum.!"
Ya ida maganar yana aje spoon dake hannun shi da alama abinci zaici.

"Hussein kenan karfa ka manta nima uwace zanso ingan ka kayi aure,shekarunka sunja yanzun fa kwanan nan zakaji Aisha ta kuma haihuwa ya'yan ɗan uwanka ukku duk da na ciki huɗu haba Taufiq saidai kace ansaka maka hannu ina dalilin wannan bala'i nagaji wlh.!"

A dagule ta ida maganar idanun ta duk sun kada tsabar fargaba da zullumi.
Fesar da numfashi yayi mai zafi yace.

"Mum ya kikeson inyi da raina wajen Abba ba dadi kema so kike in rasa gata wajen ki? Kidaina maganar wai saman hannu akayi bazan aminta da wannan zancen ba kawai dai komai lokacine."

Eh daman ai komai lokacine amman hardakai Hussein,ka nemi matar aure kawai."
Kallan mamaki yake ma mahaifiyar tashi yana maimaita zancen bisa labban sa.

"Hardake Mum kema kince inbar Minal kenan?"
"Kwarai kuwa Hussein domin ba zaka sameta ba,mahaifin ka yaki yarda kanasan ya tsinema aurenka kasamu ya'ya marassa albarka.?"

Girgiza kanshi kawai ya iya domin kanshi ya dauki charji.
Inko har hakane ya zama dole ka hakura da Amina duk da kasancewar ta yar kanina amman hausawa nacewa duk fadan dayafi karfin ka,ka maida shi wasa,dan haka kanemi matar aure,inabaso kake ka mutu bakai aure ba Hussein.!"

Mum dan Allah kibini a sannu kimani uzuri wlh nima ina bukatar auren nan saidai har yanzun lokacina ne baiyiba."

Karya ne Hussein lokacin ka yayi,mace nawa ke sonka daga dangin mahaifin ka har zuwa ya'yan abokan mahaifin ka dana kawaye na,sudin ba mata bane!?"

Mum pls Minal nikeso miyasa bazakuyi sporting dina ba,almost shekara nawa ban fidda mataba,amman kun kasa yimani uzuri nasan Minal Qaddarata ce wlh da yanda zanyi dana fiddata araina baki daya Mum ki fahimce ni narasa yanda zanyi wajen yima mahaifina biyayya duk irin kaunar daya nuna mani arayuwa amman na gaza bin umurnin sa."

Kai Taufiq idanma bacci kake kafarka tinda wuri kilan kana bukatar kaga uwarka ta zama bazarawa inko har baka bukatar hakan dole ka rabu da Aminatu,tunkan ubanka ya yanke mummunan hukunci dan duk abinda Sarki keyi wannan karan lamarin shi ya ta'azzara nagaya maka.!"

Mikewa tayi tabar wajen,shiko kamar andasa shi,ya tisa abinci gaba yana kallo idanun shi sun kada sosai,banda numfashi mai zafi ba abinda yake shidewa,kanshi na sarawa ga tsananin kaunar Minal a ran shi.


******Washe gari already angama soyen naman suna inda Abdallah yaima Husna manyan raguna guda ukku,haka aka raba shi,aka warema mai jego da angon jego sai dangin ta da nashi,duk abinda yaka mata angama ware shi harda na yan unguwa saida akayi la'asar sakaliya muka fito zamu tafi gida.

Kamar kada mu rabu haka mukaji aranmu driver Abdallah ya dauko mana motar aminci aka kaimu har gida gwanin dadi.

Lokacin fara zuwa aikina yayi tinda sassafe na kimtsa zuwa Katsina mota nahau na tafi ana saukeni nahau napep har asibiti.

Ina zuwa nayi sign muka hau aiki da kwararrun likitoci suna kara guiding dinmu aiki muke sosai wani ka tsorata wani kuma bakajin komai,ranar farko CS nafarayi duk sai naji wani iri danma muna yawan Practical a makaranta shiyasa muka dan saba da abubuwa iri iri na harkar lafiya.

Alhmdullh aiki yai aiki inata sabawa da abokan aikina harna shiga wata ukku dafara aikina watan akai mana wani irin mahaukacin salary da arias dayake tinda mukafara ba'aimana albashiba,sai wannan karan shiyasa muka samu kudi fiye da kima,murnar danayi bata wasaba.


Koda naji alert Mama nagaya mawa tasa albarka,Baba nadawowa na sanar mashi.
"Masha Allah Mama Allah yasa albarka yasa su zama alkhairi agareki."

Ameen Baba amman mikake gani za'ayi dasu."
Eh ina ganin tinda kinga kudin nan dayawa ki kasasu gida biyu kashi daya kisai motar hawa kinga bin motar haya ba dadi,sai sauran ki rabasu ukku,kisan ance albashin farko na dangine sai kiyima kowa ihsani sauran saiki aje tsaran lalura tayau da gobe."

Murmushi nayi wato duk wannan raban da Baba keyi basu a ciki kenan
Babana kenan badai tawalu'uba shidai indai abin mutun ne bai dame shiba,sake murmushin nayi

To Baba haka za'ayi,haka na rabama mutane kudi musamman dagina har Baba da Mama nai masu transfer masu nauyi saidai suka samani albarka sunajin dadi,Husna naima transfer taji dadi kwarai har Fatash naba dayake ita ko aikin bata faraba sai tagama Masters dinta tukunna,sannan naima Ya Taufiq transfer da kyal nasamu Fatima ta turomani acct number din shi dare nayi banjima ba na kwanta da zummar gobe da safe inje nida kawuna insayi mota,kiran wayar Ya Taufiq ya katse mani baccin dana fara dagawa nayi murya sanyaye na gaida shi,cewa yayi.

"Princes sakon dana gani na minene.?"
Cikeda zumudi nace.
"My first salary kasa albarka Yayana."
Shiru yayi sai kuma yace.
Allah yasa albarka amman bazan karbi kudin nan ba gaskia."

Marairaicewa nayi kamar ina gaban shi na shagwabe fuska,Pls my hero karkace haka am beg of you."

Hmmm shine abinda yayi,tareda sauke nauyayyen ajiyan zuciya yace.
"Thank you very much my hope, yanzun miye planing dinki.?"
"Mota zan siya."
Okay good girl wace kala.?"
Inasan Matrix tana mani kyau sosai."
"Okay amman kisayi Corolla LE ko kuma EOD kamar zasufi kyau da tsada."

Dariya nayi ina cewa wai tsada a raina a zahiri kuwa cewa nayi.
"Hmm Ya Taufiq kenan nikam inani ina mota masu tsada baka ganin nidin talakace."
Shima dariyar yayi yace.
"Karki damu ba abinda zai gagara tawan indai kinaso zaki mallake ta."

Gano inda ya dosa yasa na katse shi ta hanyar cewa.
"Aikuwa gobe za'akawo mani motar ma dan har kudi duk natura."

"Okay dan banda mahimmaci shine bazaki fara shawara dani ba har saida kika gama yanke decision sannan zaki gaya mani.?"
"Ayyah sorry ba haka bane kasan zan gaya maka aimun afuwa."

"Aaa ba wata afuwa nima bazan kuma gaya maki abinda nai niyar yiba tunda aminci bana Allah bane."
Kashe kiran yayi waishi yai fushi da murmushi nabi wayar zama nayi na dauki wani littafi na cigaba da karatuna ina nazari littafin theater nikeyi da surgery har saida biyu tayi nayi nafila na kwanata bacci ya daukeni ana kiran sallah na mike na shiga toilet nayi alwalla natada sallah.


Yauna kamar kullin ina office aiki nike bil hakki da gaskia ranar Wenesday munfi samun patient sosai ina duba wata marar lafiya dake fama da cutar yoyon fitsari irin yan kauyen nan ne,telephone dina yai ringing nasan aikin office ne dagawa nayi Dr Siddi ne yace.
"Dr Caranci akwai Emergency Theater yanzun ki shirya nan da 15mint za'ayi aikin.?"

Okay nace,ina ida duba patient din nasanar aikin gaggawar ya taso mani dole,haka aka yanke layin ganin likitan da patient din keyi.

Fita nayi nashiga Dept na saka rigar aiki da handglove aka shigo da matar da za'aima aikin CS cikin gaggawa nida Dr
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment