Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*

*No. 1⃣*


"Bissmillahi Rahmani Rahim"
Da sunan Allah mai rahama maijin kai...



Mikewa tai azabure tare da kallan agoggon bango na dakin dasauri tamike ganin takusa makara, mamaki take yanda bacci yadauketa akan sallayar datai sallar asuba, kaya ta cire tai saurin fitowa tsakargida taja ruwa a rijiya tafada toilet, wankan minti 5 tai tafito tafada daki tazura doguwar riga baka tasa hijab fari tare da daukar nikaf dinta da jakar makarantarta, dama ita sam kwalliya bata dameta ba.
Dakin ummanta tashiga azaune taganta tana ninke kaya tashiga da sallama tare da gaidata ta amsa cikin daure fuska Salmah kam tasaba da wannan hali na ummanta dan yanzu abin baya damunta, mikewa tai tare da cewa umma banga Abba ba koya fita ne? Kara hade rai umma tai tace ki wuce kigaida Goggo dan shikam ya fita tadan tabe karamin bakinta tare da karasawa dakin goggon ranta duk ba dadi, sam batasan matar.

Sallama tai Goggo dake kwance ta amsa mata cikin gadara salmah tashiga tare da gaida ta goggo ta amsa tare da cewa yawan banzan za'a tafi? Salma tadaure tace goggo nidai makaranta zani😞.
Goggo tai tsaki tace oho dai tunda ke da kamal kunfi karfin iyayenku ai sai kuyi tayi tace goggo yaza'aikifadi haka? cikin zafin rai goggo ta mike zaune tace karya aka muku? Wayasani ma ko kamal din yamanta dake yayi auransa acan kasar dayake ke ya barki nan kina yawon nuna jiki😏? Idanun salma suka ciciko da kwalla tadaure ta mike tace natafi makaranta goggo tace ke kika sani munafuka mudai kika kuskura kika dauko mana abun kunya sai kinsha mamaki, Salmah tai saurin yin waje tana share kwalla umma tagani a tsakar gida alamar duk zancen dasukai taji dasauri ta wuce dan tasan umma baxata taba sa baki a wannan maganar ba, nikaf ta daura takarasa waje.



Titi ta fita tasamu bus din dazatai Buk tahau, acikin mota kanta kawai ta jingina a kujera tana tunanin wannan al'amari wai ace tsakanin ta da mahaifiyarta bawata shakuwa? Wai 'yar fari😟? Ita atunaninta tin yaushe aka dena wannan abun? Intayi magana sai Abba yace mata uwarta ai bafullatanace tai wata ajiyar zuciya tare da dauko hoton kamal cikin jakarta takuramai ido aranta tace yaya yaushe zaka dawo? I really miss you, lissafin kwanan wata tashigayi yaci ace yaya kamal yadawo dan ayanda yafada mata randa sukai waya saura 3wks su taho to yanzu gashi taga harda durin kwana 5 😞 lalai yaya kamar bai matsu yaganta ba? Rabonsu da juna tun shekara 3 dasuka wuce, maida hoton tai ganin sun iso tafito daga motar ta shiga makaranta.

Lalai yau tayi late cikin hanzari tafara tafiya sam bataji motsin mota a bayanta ba sai da motar tazo daf da ita dasauri ta juyo cikin razana tare dayin gefe amma ina motar gudu takeyi gashi kamar dan koyo ne ke tuka motar sam ba'a seti take tafiya ba motar sai data gogi jikinta hakan yasa tafadi kasa tim🙆🏻

Tabi motar dakallo idanta taf da kwalla dan mutane sun taru suna kallanta abin haushi bawanda yataimaka mata, ahankali motar tafara yowa baya sai alokacin takalli number motar Prince 1 ne rubuce a jiki.
Sai da motar tazo daf da ita dan harta runtse ido tadauka murkusheta za'ayi jin shiru yasa ta bude idanta ahankali kafar mutane uku tagani ahankali tafara dago idanta har ta dure su akan nagaban wanda tasani shine Prince Salman dan tanaganin rashin mutincin dayake yi a school din wani wahalalen yawo ta hadiya.
Salman yakashe mata ido sannan yace limamiya bakya gani ne? Aranta tace limamiya? Yacigaba kosai muntaimaka miki da glass ne? Salmah tamakamai harara sannan tadaure tace ku bugeni maimakon kubani hakuri sai kuce me? Amir dake baya yai wata dariya yace hakuri? Oh prince kagane metake nufi ai😆? Salman yace ohh ai kaji halin talakawa sannan yaciro bandir din dari biyar yacilla mata yace sune matsalarki I know😏

Najib dayai shiru abaya dan shi yake koyon tukin motar azahiri shikam baijin dadin abinda ke faruwa amma yazaiyi?

Salma tai wani murmushi tare da daukan kudin sannan takaraso kusa da Salman ta mikamai ganin yaki amsa ta daura akan motar sannan ta matso kusa da salman tace maza irinku masu daukan mutane banza sannan suke tunanin kudi na maganin komai suna matukar bani tausayi😏 tana gama fad'ar haka ta juya tafara tafiya, mutanen dake gun suka shiga gulma, ran salman yagama baci yamaimaita afili Tausayi? Sannan yakalli kayan jikinta yaga gaba daya kayan datasa basu wuce kayan 2000 ba amma takalleshi tace yanabata tausayi?

Dasauri yakara kusa da ita ta baya ya fizgo hijab dinta, jikintane yafara rawa ganin bata taba shigowa makarantar ba nikaf bama bare hijab ahankali hawaye yafara gudu a idanta salma yadawo ta gabanta dasauri ta tsugunna tare da kankame jikinta, ya firgita ganin yanda Allah yamata kyau amma rashin mutuncin dake idananunsa sun rinjayeshi yatsugunno kusa da ita sannan yace tausayi? Nidake yanzu waye mai kalar tausayi? Hawaye kawai takeyi yai wata dariyar mugunta sannan yace banza 'yar tallakawa ya mike yafara tafiya tace kai da kake d'an masu kud'i fin wasu kai? Tsayawa yai chak sannan ya juyo yace ke kinsan niko waye ma? Tace why should I know? Yace be careful dan zan iya ruguza miki rayuwarki mark my word ya juya ya tafi.

Amir yashiga tafamai yace woo Man kana burgeni, salman yai tsaki yafada mota yace najib zokaja cikin sanyin jiki najib ya shiga.

Salma kam suna tafiya tadau hijab dinta tasa da nikaf dinta tamike tare da kallan agogon hannunta shikenan tayi missing lectures dan kusan 40mins kenan dashiga class ahanakali take tafiya tana jin wata muguwar tsanar salman jitake daza'a bata wuka ace anmata uzuri takashe mutun daya data tsana a duniyarnan to lalai ba shakka salman zata lumawa wannan wukar😡.

Salma kam yaci alwashin sai ya nunamata shi basa'an yinta bane dan tunda aka haifeshi bawanda yataba fadamai maganar banza irin wannan banzar yariyar dabai masan ta ba, Amir yakalla yace adubomin ko ita wacece, Amir yace wannan yarinyar? Salman yace yes I can't live her like this.
Amir yace angama prince....


Nace hmmm abin babba ne[truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.2⃣

Salmah kam karkashin wata bishiya tasamu tazauna dan tarasa dalili tunda ta taho ake binta da kallo, cikinta taji ya murda tasani yunwace ke damunta hakan yasa tadauko jakarta tabude tashiga irga kudin ciki ~N~350 ne aciki ta ciro dari ta mike tai hanyar shop, har alokacin mutane na binta da kallo cikin rashin damuwa takarasa tare da mikama mai shop din kudi tace abani buns sai dai me? Kafin mai shagon ya amsa taji an wafce kudin ahankali ta juyo dan ganin wannan rainin hankalin wani saurayi tagani cikin mamaki ta dauriya tace malam mekenan? saurayin yace indai kinasan siyan abu anan to lalai ne ki kwabe wannan munafikin abinda kikasa muga mai kika nunama prince har ya tsugunna kusa dake tace me kake nufi da kalamanka? Yace oh kindauka bamusan manufarki ba? Salmah ta runtse ido tadaure ta juya batare da ta amshi kudin ba, jitai an mazan gun sun kwashe mata da dariya, ahankali take naga kafarta dan jin kafar take tamata nauyi.


Sai datai tafiya mai nisa sannan tasamu guri tazauna kwalla ya cika mata ido,
tunda tafara zuwa makarantarnan bata tunanin wani yasanta banda mutanen datake gaisawa dasu yau gashi anjayo mata duk inda ta wuce ana binta da kallo😰hoton kamal tadauko tafada afili yaya kamal kadawo plz😔 jitai ance lalai salmah soyaya har a skul? Tadago danta gane mai muryar tace zee ashe kin shigo, zee tazauna tare da cewa salmah meya hadaku da prince? Tace au kema harkinji? Zee tace hmm ni fa muna zaune munajiran Professor mannir kawai wani ya shigo class da gudu yace yan class kunsan salmah ai kawar zee? Sukace eh mai nikaf yace to tanacan ana show itada prince ya cire mata hijab da nikaf😂 nan yan class sukashiga dariya tundaga nan nafito nemanki banganki ba,
Salma tai murmushin yake tace zee kodai inhakura da makarantarnan? Injira kamal yadawo inmunyi aure sai inkarasa.
Zee tace haba salma akan wani can zaki durkushe rayuwarki? Kinsan prince yakai 2yrs a skul din nan kuwa? Tace haba? Zee tace hmm amma kinsan me? Haryanzu fa a level 200 yake salma cikin mamaki tace haba dai? Baya jaa ne? Zee ta kwashe da dariya tace inafa? Ance blanksheet fa yake submitting😝.

Salma tace blank? To ya akai ya wuce level 100 zee tace ance wai da shugabar makarantar taso tadinga bashi mark sai dai shi dakanshi yace mata bayaso karta karamai haka, salma tace meyasa😳? Zee tace oho ba wanda yasan dalili, tadan tabe baki tace shiyasani zee tace waje iskanci cikin fanko😜nan sukasa dariya.


Salman kam bai dade a skul ba ya wuce yawansa dan dama ba lectures yake shiga ba sai wajen magrib ya shiga gida ya ajiye mota yai bangarensa bayi nata gaisuwa yana isa daki yai wanka yazura doguwar riga yafito tareda bayinsa dake kuladashi yai bangaren fulani zuciyarshi taf take da bakin ciki suna isa harabar gun yacema bayin su jirashi yashiga, ahankali yakarasa kofar dankin bayin dake kula dagun suka budemai yashiga sai dai bakowa a kilisar da fulanin ke zama yai shiru zuciyarshi na bugawa da karfi.


Wata baiwa ce tazo tace tana daki bari insanar mata, yace a'a bari in karasa tace to ranka ya dade, ahankali yakarasa dakin yakai hannu zai kwankwasa yaji maganar Ishaq (yayansa ne agun mahaifinsu) yanacewa yau ma dai kamar kullum salman yawansa yaje, fulanice ta saki dariya tace ka tabbatar dai kana kula da takunsa dukda kaini dan sarki nafarko bai zama lalai ka gaji sarki ba ehe.


Ishaq yace haba ummi yaxakina fadar haka ke kina tunanin wannan shashashan Abba zaiba mulki? Yaranda banda yawo ba abinda yake? Haryanzu yakasa gama karatu? Tai dariya tace kasan sarki na tausayinsa ganin bashida uwa, ishaq yace tab aikin banza kenan to sau nawa yana zuwa gaida sarkin amma baya amsawa?

Ahankali salman yafara yin baya idanshi yakada yayi jaa dakinsa ya koma yai saurin dafa kansa da kirjinsa jiyake kamar zai mutu dasauri ya bude drawer yad'auko magani ya hadiya yashiga karanta *INNALLILAHI WA INA ILAIHI RAJI'UN* ahankali yafara jin nutsuwa tana zuwa mai.


Salmah zaune a tsakar ta zuba tagumi ga kwanukan wanke wanke a gabanta da alama shi takeyi tashiga tunani, abinda salman ya mata take tunani tai ajiyar zuciya aranta tace da yaya kamal nanan munyi auranmu da duk haka bata samen ba jitai an daka mata dundu a baya tadago cikin mamaki goggo tace kinci gidanku, wanke_wanke zakimana ko tunanin wancan dan iskan? Salmah tace goggo wai meyasa kika tsani yaya kamal? Ba dan uwan Abba bane? Tace oho ko dan uwa nane mai yadameni? Kedai kinji asara kannenki duk sunyi aure ke kinfi karfin iyayenki, salma tace nima da yaya kamal nanan ai...jitai an kwabe mata baki goggo tace mara kunyar banza kawai ke baki da aiki sai zancen kamal duk mutanen dasukazo neman auranki kim koresu shima Alhaji ai duk laifinshine aikin banza, tana zuwa nan tai gaba salma tabita da ido itakam bakomai zatajira kamal dinta truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄





*NA AYUSHER MOHD*

*NO. 3⃣*



Motsin bude kofa taji salma ta mike da sauri dan tasan Abba ne takaraso inda yake ta rusunna tare damai sannu da zuwa ta amshi ledar hannun sa, cikin murmushi ya amsa yace andawo? Tace eh Abba, nan yakarasa daki itama tana biye dashi.

Falo yashiga itakuma tai dakim goggo ta mika mata ledar sannan tai falo gun Abba, azaune taganshi umma nakusa dashi, Abba yakalleta yace salma ya akai? Tace Hmm Abba dama......tafad'a tana kallan fuskar umma, Abba yakalleta sannan ya kalli umma yace ko in fito? Tad'anyi kasa dakai, Abba yamike umma tad'aure tace hb Alhaji? Yace ke kinjiki ai yarinya nasan magana da mahaifinta, menene a ciki?

Abba ya fito salma ta biyoshi tana kallan umma na harararta suna fita tace Abba kunyi waya da yaya kamal? Yai murmushi yace jiya daddadare dai ya kirani😊.
Salma tasaki murmushi tace Abba yaushe yace zai dawo? Yace hmm lalai salma tadamu yayanta yadawo tunda harta fara tambaya, salma ta rufe ido tace Abba karatu yafara tsauri inaso insamu mai koyamin ne🙈.....

Abba yai murmushi yace hmm banyarda da wannan wayan ba nida nakeso yana dawowa musha biki😀 dasauri tad'ago sai kuma ta ruga daki da gudu, yabita da kallo tareda murmushi yana san yarinyar duk cikin 'ya'yanshi yafi shakuwa da ita kasancewar uwarta bata shiga harkarta hakan yasa shine ke zama abokin hirarta tun tana karama.

Salma kam gado tafad'a tashiga ajiyar zuciya na farin ciki itakanta takosa tai auren nan ko dangin mahaifiyarta zasu daina mata fad'a.

Shekararta 22 amma tarasa dalilin dayasa idan kowa yake akanta kodayake kannanta 2 sunyi aure suna gama secondary, kaninta namiji kuma na makarantar kwana ta Gezawa.


Wahsegari ta shirya yanda tasaba tafito ta tafi makaranta, 12 suka fito daga lectures itada zee wajen wata kujera suka zauna, zee tafara tambayar salma akan karatun dasukai yanzu, salma sosai tashiga yima zee bayani wani guy ne yazo yace wai ana magana da limamiya, cikin mamaki zee tace limamiya? Antaba kiran macce limamiya dama? Yace haka akacemin nidai taje inji prince, yana kaiwa nan yai waje.


Zee takalli salma tace don't tell me ke ake nufi? Salma tai tsaki tace dalla share d'an iska, zee tace salma karfa asamu matsala dan prince inya tsani mutum har korarsa yanasawa ayi, Salmah tai tsaki tace keni duk wannan abun bai damenba menamai wai? Shine yaci mutuncina? Zee tace tashi mubar gun nan daga gani yaganmu ne.

Mikewa sukai suka fara tafiya, salmah jitai an ja mata hijab dasauri ta juya tare dacewa wani irin iskanci ne.....kalamanta sun katsene ganin mazan jiya su uku Amir na rike da hijab d'inta, cikin zafin nama ta fizge sannan tace meye hakan kakeyi? Amir yace tambaya kike?
Tace eh laifi ne? Mena muku wai?
A tunanina kune kuka min abu amma na nuna ya wuce to why are u bothering me? 😠 tafad'a tana hararra salman duk da cikin zuciyarta taf yake da tsoro amma ta riga tasa aranta bazata juri wulakanci ba.

Zee kam tagama tsorata ahankali tafara ja da baya, prince ne yakaraso inda take daf da ita hakan yasa tad'an matsa dan tanajin sautin numfashinshi, kara matsowa yai kusa da ita , zuciyarta sai bigawa take sai datakai jikin bango ya kara matsowa tadaure tace me kakeyin hakan? Yace dazu kin tambaya me kikayi shiyasa nake kokarin baki amsa, tadaure tace to d'an matsa yace in naki fa? Tai shiru.

Salman yace abinda kika fad'a jiya shine dalilin dayasa nadawo yau kikace maza irinmu nabaki tausayi? Mamaki ya kama salma itakam sam ta manta ta fad'I haka to meye inta fad'a karya tayi? Jin salman tai yace meye abin tausayi agareni? Bayan ubanki ba d'an kowa bane? Ta dago ido cikin b'acin rai tace arziki shine komai kake tunani? Yace ke yar gidan Amadu mai gini kishiga hankalinki sannan kiyi gaggawar janye kalmarki ta tausayi agareni wannan shine last warning dina......


Salma mamaki yakamata wato bincike yasa ayi akanta? Tadaure tace kalmace bazan janyeba tunda ba karya nai ba😏gini kuma da mahaifina ke ye ai baiwace wani sana'ar yi ma bashi da ita🙄 tuni zuciyar salman tagama dugunzuma ba abinda yatsana a duniya irin ace ana tausayin sa jiyai kansa yafara sarawa, hannu yad'aga alamar zai mare ta dasauri ta runtse ido ko meya tuna sai yafasa tare da juyawa dasauri.

Salma tabishi da harara Amir ya nunata da hannu sannan ya nuna idansa da hannu tasan meyake nufi wai they are watching me tace oho aikine bai isheku ba.


Salman kam toilet yashiga dasauri ya dafe kirjinsa ya d'auko maganinsa ya had'iya ahankali yafara jin numfashinshi na fita dai_dai........[truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.4⃣


Salmah kam suna tafiya gun ta tsugunna ta shiga maida numfashi ta dade ahaka kafin ta mike ganin mutane tai agun suna kallanta ta dauke idanta tare da kallan agoggon hannunta, gani saura 15 mins su shiga next lectures gashi ko sallah batai ba yasa tai saurin wucewa, tana dubawa ko zataga zee.


Salman yauma sai magrib yashigo gun mai martaba ya wuce, ya dade kafin sarki yabashi izinin shiga, cikin nutsuwa ya shiga mai martaba yakalli fadawan gun yace kubamu guri suka amsa tare da mikewa.

Sarki ya kalli salman yace matso nan, cikin sanyin jiki salman ya matso kusa da sarki tare da sake gaidashi ya amsa fuska a d'aure, sannan ya cigaba haryanzu baka da aiki sai tsokanar mutane a makarantar ko? Salman yai kasa dakai Yace Ranka ya dade ba........
Cikin b'acin rai sarki ya katseshi yace anfad'ama duk abinda kake a makarantar bana sani? Ka kasa maida hankali kai karatu sai bin kawayen banza da wulakanta mutanena, sannan kana kallo kaninka Nazir yai aure amma kai banda shegantaka bakada aikin yi😠.
Salman kam idansa ya kad'a yai jaa batare da sarki yajira amsarsa ba yace wato yanzu rashin mutuncin ka ya kai wani mataki daka fara wulakanta mata ko? Salman yad'ago cikin mamaki sarki yace ina nan ishaq yazo yasanar dani ka cirewa wata hijab a makaranta ko karya aka ma? Gaban salman ne ya fad'I amma yadaure yace a'a, sarkj yace nagode salman kacigba da bakanta min rai.


Salman yai shiru zuciyarshi na rayamai kabada hakuri, can wata zuciyar tace ka manta me suka ma? Jin bashi da niyar bada hakuri yasa sarki yace dama kai bakasaba yin laifi kabada hakuri, tashi Kaban guri, ga mamakin sarki gani yai salman na kokarin mekewa ranshi yakara b'aci yace kakuma tabbatar ka fito da matar aure nan da wata 1 dan bazan d'auki iskancin da kakeji dashi ba, salman yace Abba wata 1 ai......dasauri sarki ya katseshi yace wlh ka fita daga idona ka sani bana magana 2 dan haka ka kiyaye.

Salman yai tsaye yakasa magana kuma ya kasa wucewa, wani bawa ne ya shigo yace ranka ya dade *Ishaq* na neman iso, sarki ya d'agamai kai alamar yashigo, dasuri ya juya, bai dade da fita ba ishaq ya shigo ganin salman yasa yasaki wani murmushi😏 tare da tsugunnawa ya gaida sarki, cikin sanyin murya ya amsa ishaq yace salman yanaganka a tsaye? Salman ya kalleshi sannan ya d'auke kai tare dacewa sarki nabarka lafiya, sarki bai amsaba salman kam da sauri yai waje.

Ishaq yace Abba Allah yasa dai d'an kanin nan nawa ba laifi yama ba? Inkuwa laifi yai ina bada hakuri a maimakon shi, sarki yace kyale sokon yaro zanyi maganinsa, sannan kafad'ama fulani ta fara nemo yarinyar dazai aura dan in bai kawo wace zai auraba nan da wata 1 to ba shakka aure zan mai.

Ishaq yace to ranka ya dade, sannan shima ya fita zuciyarshi fal farinciki lalai yau sunada karamin party.



Salmah kam tagama aikin gida takoma d'aki ta d'auko littafinta kenan taji yaro na sallama sai dai kafin tafita goggo ta fita tace yaro ya akai? Yaron yace wai ana sallama da salmah inji Muftahu tace muftahu? Wanne kenan? Yace muftahu mai babban shagon can tace au toh nagane, je kace gatannan yanzu zata iso, yace to tare da yin waje.

Goggo ta taho dasauri tana washe baki takaraso dakin salmah dake zaune duk taji abinda sukai da yaron, goggo tace tashi 'yar nan alkairi yasamemu😁 salmah tace name fa? Goggo tace gidan ku kina nufi bakiji me mukai da yaron can ba😠? Salmah tace au nad'auka sa'a yake nema( kanwarta da akai aure wata 4 dasuka wuce).

Goggo tace kaji min 'yar rainin hankali sa'ar datai aure za'azo nema? Tace kin manta ne goggo kwanaki.....ta katseta rufemin baki yar iskar banza to ke ake nema kuma muftahu ne mai katan shagon can salma tad'an tabe baki tace goggo kinsan fa ni yaya kamal nakeso, goggo tace lalai dalla rufemin baki kamalo ba kamalu ba kinsan Allah salma😠 tashi kafin na fasa miki baki.

Kasa tai dakanta tare da jan hijab dinta tai waje tana turo baki.



Muftahu kam ansha shadda da hula ga motarsa Civic ya ajiyeta yana tsaye ya juya baya, yanajin motsin kofa ya juyo yana murmushi takalleshi tare da d'auke kai tace ina wuni? Yacw lafiya lau *Salmat*😊 tace salmat? Yace eh mana ni haka zan dinga kiranki ta juya kai tare da yin shiru, yace salmat plz nazo da magana mai girma hope zaki fahimceni? Ta juyo tare da kakaro murmushi tace am sorry muftahu nasan kasan inada Wanda zan aura.


Muftahu yace salmat, kamal ba baida niyar auranki, inba haka ba shekararsa nawa acan? Kaf 'yan layin nan gulmar abin suke mahaifinki yabarki kina jiran d'an uwansa bayan kila shi yamanta daku.
Salma kam ranta yagama b'aci batare datace komai ba tai hanyar gida ta bude kofar tai dakin ta da sauri tafad'a kan gado ahankali hawaye yafara zubo mata.
..[truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.5⃣

Tanajin motsin umma a waje amma abin haushi ko tazo ta tambayeta meya faru, Abbanta nadawo wa tamike da sauri taje tagaidashi umma da goggo nazaune bayan ya amsa, goggo tace dazun korar muftahun kikai shima? Salma tai kasa dakai, Abba yace wai ke Basira meyasa bakyaji? Na dade da fad'a miki bana san kina takurama salmah, ko kin manta matar da kamal ce? Tace yahkuri Alhaji ganinai tanata zama a gida ba kamal ba labarinsa.

Abba yace kada ki manta yanda muke da mahaifin kamal mu 2 ne a d'akin mu shine yayana kuma baki
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment