Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ki bi sannu" murmushi Fulani Zaliha tayi ta ce, "In sha Allah Yaya kinsan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi" Fulani Zaliha zuciyarta ɗaya ta faɗi haka ita kuwa Fulani Maryama juyowa tayi amma sai ta wayence da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce. "Kinyi gaskiya kuma nasan da haka amma duk da haka tsugunne bata ƙare miki ba amma fa shawara ce na baki." tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin.

Tun daga ranar Fulani Maryama bata ƙara shiga sashen Fulani Zaliha ba, kuma zuciyarta fes ta fita daga ɗakin saboda yadda da dukkan alama haƙanta ya cimma ruwa. Shirye-shirye ake ta gudanarwa na shagalin suna daga sassan ɓangarori na cikin masarautar. Ranar suna Mai martaba ya raɗawa Jariri sunan Saifullah suna kiransa da Saif, anyi shagali sosai ɓaki daga garuruwa suka kawo ziyara wajen taya Mai Martaba murnar samu Ɗa namiji a karo na biyu.

Anyi taron suna angama lafiya kuma daga ɓangaren Mejego da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya. Bayan wata uku Mai Martaba ne zaune a fada shi da Waziri, ga duk wanda ya dubi yanayim Mai Martaba zai fahimci tsantsar damuwar da yake ciki, amma da yake namiji ne jajirtacce farat ɗaya bazaka fahimci ainihin yanayin da yake cikin ba. Waziri ya ɗuƙar da kai cikin sigar girmamawa yace. "Allah ya taimaki takawa ya ƙarawa Sarki lafiya, Muna zaune aka aika da saƙon kiranmu" Sarki Aminullah ya jinjina kai sannan ya ce.

"Waziri wani abu yana damunmu kuma babu wanda muka aminta da mu tattauna dashi sai kai" Waziri ya ɗago yace. "Wannan haka haka yake" Sarki yace. "Mun lura da yaron wajen Zaliha kamar bashi da wadatacciyar lafiya, kuma na lura da yanayin Mahaifiyarsa ita kanta ta fahimci haka sai da tana shakkun sanar dani. Waziri ina san maganar nan ta zama sirrin saboda kunnuwa da idanun Fada suna bibiyar halin da ake ciki, banasan a fuskanci halin da yaron nan yake ciki inasan ka nemo min mai magani a sirrance ta yadda babu wanda zai fahimci halin da ake ciki."

Waziri ya numfasa yace. "Allah ƙadiran alamanyasha'u gaskiya akwai matsala babba dukda kasancewar ba shine Yarima ba, amma sirrantawar yana da matuƙar fa'ida. A cen garin Zaria akwai wani mai magani dana sani yana bada magunguna sosai, dan haka insha Allah zan shirya naje na karɓo maganin sai a jarraba da ikon Allah za'a dace." Mai Martaba yace. "Waziri me zai hana ya gayyato mana mai magnin ina ganin kamar hakan zaifi" Waziri yace, "Duk yadda kace haka za'a aiwatar da kai da kaya duk mallakar wuya ne" Mai Martaba yace. "A shirya tafiya gobe aje a gayyato mana shi" Waziri ya amsa daga nan ya fice daga fadar."

Da daddare Fulani Zaliha ce zaune a turakar Sarki ta zuba uban tagumi, Sarki Aminullahi ya kalleta yace."Me yake damunki Zaliha" idanunta ne suka ciko da ƙwalla muryarta na rawa ta ce. "Mai martaba Saif ne nake lura da yanayinsa bashi da ƙosasshiyar lafiya, na lura fa ko gani kamar ba ya yi, gashi har yanzu kansa baya tsaiwa hatta irin gwarancin yarannan banji yana yi ba, abu ɗaya kawai nasan yanayi idan na kira sunansa zan ga yana ɗan motsawa." Fulani Zaliha na kawo nan a zancenta ta rushe da kuka. Rungumeta yayi ajikinsa tsam kamar wani zai ƙwaceta ya fara rarrashinta, yana buga bayanta harta lafa da kukan sannan yace. "Ina lura da halin da kike ciki kuma na fahimci duk abinda kika gayamun, dan haka na aika a kira mai magani a sirrance inasan ki zama jaruma karki bari magauta su ga kukanki, Insha Allah Saif zai samu lafiya ki kwantar da hankalinki." Haka dai Sarki yayi da lallashin Fulani Zaliha har ta sauko ta daina kuka.

Bayan kwana biyu Mai magani suka ƙarasa ta ƙofar baya suka ƙaraso ɗakin sirri wacce take bayan gari, Saif na hannun Mai martaba mai maganin ya shigo hannunsa ɗauke da wata jakar fata ta magunguna, yana zuwa ya ƙurawa Saif kallo nan take ya fara tsanyara wani irin kuka, jinjina kai yayi ya ce. "Tabbas ancutar da shi da guba mai tsanani sai dai zan iya taimaka muku da yardar Allah koda kuwa bazai warke gabaɗaya ba." Mai maganin kwance jakarsa ya farayi nan take ya dafe ƙirjinsa ya fara wani irin kakari kafin wani lokaci ya yanke jiki ya faɗi ƙasa matacce.


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[13/10/2021, 18:53] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 6


Hankali a tashe Waziri da Mai martaba suka kalli juna ganin abinda ya faru da mai magani, ƙanin Mai maganin da ke gefe da sauri ya faɗa kan ɗan uwansa yana kuka, Mai Martaba cikin al'ajabi haɗe da tashin hankali ya kalli Waziri yace. "Waziri a ji da bawan Allahn nan bamasan a tara mana jama'a, ashirya tafiya ƙasar Zazzau a sirrance batare da wasu sun sani ba, zan aiko da takarda akaiwa da iyalansa tare da kyautuka masu yawa." Yana gama faɗa ya juya ya fita ta ƙofar baya cikin jimami" Lokacin da Mai martaba ya ƙarasa cikin turakarsa dare yayi sosai babu komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabbobi, Fulani Zaliha na tsaye sai safa da marwa take yi da ka ga yanayinta zaka fahimci tana cikin damuwa, tana jin motsin Mai Martaba da sauri ta ƙarasa ta tarbeshi gabanta sai faɗuwa yake tunaninta ɗaya wacce amsa Mai martaba zai bata.

Ganin Mai martaba tayi ya shigo cikin shigar da yayi ta ɓadda kama, sanye yake da kayan bayi fuskarsa naɗe da rawani sai Saif dake rungume a ƙirjinsa, har kusan gware sukayi da Fulani Zaliha ta ɗan ja da baya tana kallan yanayinsa, a hankali ya taka kan lallausar shinfiɗarsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Fulani Zaliha zama tayi a gefensa ta ƙarɓi Saif dake hannun Sarki Aminullah yana shan ɗan yatsansa, kallan ɗan nata take zuciya a karye ta ce. "Allah ya taimakeka har dace ba ko?" Sarki Aminullah yace. "Mai maganin Allah yayi masa rasuwa" a hargitse ta ɗago tana kallansa bakinta na rawa ta ce.

"Mai Martaba ɗazu kace Mai maganin yana ɗakin sirri yana jiranka" Sarki Aminullah yace. "Zaliha lamarin Ubangiji yafi gaban komai, yana gabda haɗa magunguna Allah ya karɓi rayuwarsa." Fulani Zaliha ta jinjina kai ta ce. "Allah ya fimu sanin dalilin faruwar haka. Amma gani nake larurar Saif anya babu sihiri a ciki?" Kallan da Sarki Aminullah ya yi mata ne yasa ta haɗiye wani yawu tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce.

"Allah ya huci zuciyar Takawa a gafarceni ban faɗi haka saboda ɓacin ranka ba" Sarki Aminullah yace. "Zaliha karna ƙara jin makamanciyar irin wannan maganar daga bakinki, kina nufin yafi ƙarfin Ubangiji ya jarrabceshi da wani ciwo ne? Karki bari shaiɗan yayi tasiri a zuciyarki har ya kaiga kin fara zargin abinda ba haka bane" Fulani Zaliha kukan da take ɓoyewa ne ya ƙwace mata, wani irin kuka take me tsuma zuciya Mai martaba jin kukanta yake har cikin zuciyarsa, takowa yayi a hankali ya karɓi Saif ya kwantar da shi sannan ya rungumeta yana lallashinta, sai da ya ga ta tsagaita da kukan sannan yace.

"Zaliha dole na gaya miki gaskiya koda bazata miki daɗi ba saboda gujewa faɗawa ga halaka, zato a musulunci haramin koda ya kasance gaskiya abinda nake so da ke ki cigaba da kai kukanki gurun Ubangiji, shi zai magance mana duk abinda yake damunki, karki nufi kowa da sharri sai kiga Allah ya kare ki duk wanda ma ya nufe ki da shi koda yana nasara wata rana mugun abinsa zai koma kansa saboda ramin ƙarya ƙurarre ne. Allah ya fimu sanin dai-dai amma ni bana zargin akwai wanda zai iya cutar da abinda kika haifa a cikin masarautar nan, ki riƙi ibada kamar yadda nasanki da ita Allah zai kawo mana waraka cikin ƙudurarsa." Fulani Zaliha goge hawaye tayi tana gyaɗa kai Sarki Aminullah ya cigaba da kwantar mata da hankali.

Fulani Maryama banda zarya babu abinda take yi a soron baya cikin shigarta ta baɗɗa kama, motsin tafiya taji da sauri ta matsa cen kusurwar bango ta maƙale kamar ba kowa a gurin. Shigowa yayi yana ɗan dube-dube murya ƙasa-ƙasa yace. "Allah ya taimakeki" da sauri Fulani Maryama ta fito ta ce, "Ya ake ciki Ɓoyayyiyar Fuska?" Mutumin yayi murmushi mai sauti yace. "Allah ya taimakeki tabbas kin tabbata murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, tuni ya riga da ya mutu har lahira" Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Lallai ka tabbata lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi" Mutumin da take kira da ɓoyayyiyar fuska yace. "Ya gara ta kanyi da dutse..." Fulani Maryama tayi dariya mai tsauti ta ce. "Sai kallo, kallonma daga nesa" suka bushe da dariya lokaci ɗaya, Fulani Maryama ta sunkuyo ta ce. "Kasan idanun Masarauta na lura da shige da fice sai wani lokaci idan mun ƙara haɗuwa" tana faɗar haka ta juya fice ta ƙofar baya.

Tun daga ranar Mai martaba ya cigaba da neman masu magani amma wani abun damuwa duk wanda aka ɗauko sai dai ya faɗi take ya mutu, wani kuma a ranar da aka shirya za'a gurinsa za'a je a samu labarin ya mutu ko kuma ya kwanta matsananciyar jinya. Tun Mai martaba bai fara damuwa ba har abun ya fara damunsa, daga ɓangaren Fulani Zaliha duk ta rame saboda damuwa. Sarki Aminullahi tun yana neman masu magunguna a ɓoye har ya fara nema a fili, masu magunguna daga sassan garuruwa suke zuwa domin kawo nasu maganin amma babu nasara, nasara ɗaya aka samu masu Maganin sun daina mutuwa sai dai idan sunzo babu wani canji da ake samu daga jikin Saif. Haka aka dinga tsegungumi a cikin masarautar musamman yadda mutane suka lura da yadda Sarki Aminullahi ya ɗora soyayya akan Saif. Hakan ba ƙaramin ɓatawa Fulani Maryama rai yayi ba da sauran Matan Sarki Aminullah, sai dai su basu wani damu sosai ba dan sun san har abada babu shi babu karagar mulki.

Haka aka cigaba da tafiya har Saif ya shekara guda a duniya amma ko zama bayayi, hatta kwanciya sai Mahaifiyarsa ta juyashi, Fulani Zaliha ta riga da ta tabbatar da Saif baya gani sai dai ji da kunne tana yi masa magana take fara jujjuyawa, har zuwa wannan lokacin Sarki Aminullah bai ƙosa da nemawa Saif magani ba amma babu wata nasara ko cigaba da ake samu.


Jakadiya ce ɗurƙushe gaban Fulani ta ce. "Barka da hutawa giwar mata uwar Yarima hasken talakawa, an aika kina nemana" Fulani Maryama cikin Isa da ƙasaita ta ce. "Yau zamu kaiwa Marduska ziyara" A firgice Jakadiya ta ɗago tana kallan Fulani Maryama amma ta kasa furta koda kalma ɗaya ne" Fulani Maryama ta cigaba da cewa.

"A yanzu nake san zuwa basai anjima ba" bata saurare ta ba ta wuce cikin ɗaki ta ɗauko Yarima Salma ta miƙa mata tace. "Zamu je domin biyan buƙatata ina ƙara jan kunnenki Jakadiya bakinki ƙanin ƙafarki ina tausaya miki azabar da zan aiwatar miki muddin sirrina ya fito daga bakinki" wuri ta miƙa mata sannan ta fara ambatar kalmomin da Boka Mardusk ya bata ta dinga ambata aduk lokacin da take san ziyartarsa.

Durƙushe suke gaban Boka Marduska ya kalleta sannan ya wage ƙaton bakinsa yana ɓaɓɓaka dariya bakyan gani sannan ya ce. "Maryama buƙatarki ta biya" Kin fito da ƙudurun a juyar da hankalin Sarki daga kan Zaliha da Ɗanta Saif ko?" Fulani Maryama ta gyaɗa kai Boka Marduska yace. "Wannan dai ta biya sai dai wata buƙatar kuma" Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Tsafi ya dafa ka daɗe kayi ƙarko irin na dabino, hatsabibancinka ya dauwama har ƙarshen duniya" tana rufe baki ta ɗire masa jakar kuɗin da ta taho dasu sannan suka miƙe zasu tafi har sunje bakin Ƙofa yace. "Sai dai kiyi haƙuri Maryama wannan karan makusancinki zamu ɗauka a tukwicinmu lamarin bazai miki daɗi ba." Yana rufe baki ya ɓace daga gurin gabaɗaya.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[15/10/2021, 12:18] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 7


Wani abu ne ya tsargawa Fulani Maryama tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta nan take jikinta yayi sanyi, a sanyaye ta kalli Jakadiya murya a raunace ta ce. "Jakadiya ina jin tsoron wanda Boka Marduska zai ɗauka, tsoro nake kar wani mummunan abu ya faru da Yarima Salman" Jakadiya cikin zuciyarta ta ce. "Ya rabbi samawati kasa jinin Salman ne tukuwicin da Boka zai ɗauka, yooo dama duk wanda ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa" jin Jakadiya tayi shiru yasa Fulani Maryama ta ce.

"Jakadiya magana nake fa kina ji na" Jakadiya ta sauya fasalin fuskarta zuwa yanayin damuwa ta ce. "Allah ya taimakeki ba dan kar kalamaina za suyi kaushi ba da nace ki gaggauta yin istigifari saboda Salman Kainuwa ne dashen Allah, domin Jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa babu wanda ya isa ya cutar da Salman da yardar Allah shine Sarki me jiran gado." Fulani Maryama ajiyar zuciya ta ce. "Jakadiya shiyasa duk cikin masarauta babu wacce nake ƙauna kamar ke saboda ke kike kwantar mun da hankali a duk lokacin dana tsinci kaina a wani hali" tana gama faɗar haka ta fara karanta kalaman data saba sannan suka koma masarautarsu.

Washegari da asubar fari saƙo ya iso musu daga Masarautar Gombe na rasuwar Mahaifin Fulani Maryama wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya, Dattijon arziƙi ne shekarunsa Tamanin da bakwai. Jam'ar ƙasar Gombe ba ƙaramin jimami sukayi ba na rashin adalin Sarkinsu marigayi Sarki Abdullahi bn Abdurrahman, lokacin da Mai martaba Sarki Aminullah ya samu wannan saƙon ba ƙaramin jimami yayi ba, tunaninsa ɗaya yadda zai sanarwa da Fulani Maryama rashin mahaifinta musamman da ya tuna yadda take matuƙar ƙaunarsa.
Fulani Maryama tun da gari ya waye ta ga Salma cikin ƙoshin lafiya damuwarta ta lafa amma a daren ranar ko baccin kirki batayi ba, saboda fargabar abinda zai faru batasan waye Boka zai ɗauka daga cikin ahalinta ba. Tana zaune Yarima Salman na ta ƴan wasanninsa Jakadiya ta shigo da sallama, ga wanda zai ƙarewa Jakadiya kallon tsaf zai fahimci tana cikin farinciki tana shiga ta sauya fasalin fuskarta cikin damuwa ta durƙusa ta ce. "Barka da kyakkyawar safiya uwar gijiyata Mai martaba ya umarceni da sanar dake yana jiranki a turakarsa." Buɗe ido Fulani Maryama tayi da mamakin kiran da Sarki yake mata ta ce. "Jakadiya kinji sabon labari ne?" Jakadiya a zuciyarta ta ce. "Mugun labari ma kuwa amma idan kinje kyaji da kanki" a fili Jakadiya ta ce. "Ranki shi daɗe babu wani sabon labari da ya iso fada a wayewar garin nan"

Fulani Maryama miƙewa tayi gabanta na faɗuwa ta wuce har taje bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Ki kira Binto ta kula mun da Yarima ina dawowa" Fulani Maryama bata jira cewar Jakadiya ba ta fice. Jakadiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo a hankali ta ce. "Fulani Maryam kenan ai duk wanda ya sayi tsintsiya yasan zatayi shara da sannu zaki fara girbar abinda kika shuka" ta ƙarasa gaban Yarima Salman ta waiga hagu da dama sannan ta dungure masa kai ta ce. "Kai kuma Falalu sai zare idanu kake kana fala-fala da kunnuwa, ko waɗannan fatalin kunnuwan naka ya isa a gane basu da alaƙa da Mai martaba." tana jin ya fara kuka ta ɗauke shi tana cewa. "Yarima babban gwarzo badai ƙyuya kake ba ke Bintoto zo maza Fulani Maryama ta tafi gurin takawa" bata rufe baki ba sai ga Baiwar ta shigo da sauri, Jakadiya cikin masifa ta ce. "Ke dalla ki dinga nutsuwa yarinya sai rawar kai kamar taci sadakar miji." Jakadiya dangwara mata Yarima tayi ta miƙe ta ce. "To gashinan ki kula da shi dama aikinki ne ni kinga wucewa ta"

Fulani Maryama zaune ta samu Sarki bayan ta gaisheshi ya amsa sannan yace. "Maryama kinsan dukkan mu daga gurin Ubangiji muke kuma gurinsa zamu koma, yarda da ƙaddara me kyau da marar kyau wajibi ne ga duk musulmin ƙwarai kuma duk wanda kikaji anwayi gari da mutuwarsa to Ubangiji ya fi mu ƙaunarsa shiyasa ya ɗauke bawansa." Fulani Maryama ta gyaɗa kai jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya cigaba da cewa."A ɗazu aka aiko ɗan aike daga ƙasar Gombe cewa Allah ya yiwa Mai martaba rasuwa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Ubangiji ya kyauta namu zuwan" Tun Sarki Aminullah bai rufe baki ba Fulani Maryama ta rushe da matsanancin kuka, ana cikin haka sauran Matan sarki suka ƙaraso ganin yanayin da Fulani Maryama take ciki ya sanyaya jikinsu. Zama sukayi cikin ladabi suka gaida shi sannan ya ci gaba da cewa.

"Dukkan Mai rai mammaci a yanzu ba kuka ya kamata kiyi masa ba yafi buƙatar Addu'arki, Mai martaba mutum ne mai karamci da dattako dan haka Addu'a ya kamata muyi masa Allah ya jiƙansa ya gafarta masa dan haka ku shirya zamu kai gaisuwar rashin mahaifin Maryama Ƙasar Gombe nan ba da jimawa ba." Jiki a sanyaye Su Fulani Zaliha suka yiwa Mai martaba da Fulani Maryama ta'aziyya sannan suka miƙe kowacce ta shige sashenta. Fulani Maryama tana kuka tana haɗa hanya ta tashi ta nufi ɓangarenta zuciyarta fal damuwa da jimamin rashin Mahaifinta.

Fulani Maryama bayan ta gama shiryawa ita kaɗai a ɗaki ta fara magana. "Wannan masifa da me tayi kama saboda Allah a ce wai tsiyar Boka Masduka akan Mahaifina zata ƙare alhalin ni babu wata tsiya da naga ta sauya, aikuwa wallahi ba zanyi rashin mahaifi a banza ba kowa yaci tuwo dani miya yasha." tana rufe baki ɗau jakarta ta rungumi Yarima ta fito, lokacin da suka fito ita da baiwarta a lokacin tuni Sauran Matan Sarki sun fito tsayuwarta babu jimawa sai ga Fulani Zaliha ta fito rungume da Saif a hannunta. Mai martaba na fito daga turakarsa ya ƙare musu kallo Fuska a ɗaure ya kalli Fulani Zaliha ya ce. "Ina zaki da yaron hannunki?" Fulani Zaliha bata kawo komai a ranta ba ta ce. "Allah ya taimake ka gurin rasuwar da ka bada umarnin zuwa"

Sarki Aminullah yace. "Ki mayar da shi ciki" a firgice ta ɗago da kai ta ce. "Bangane ba ranka shi daɗe" Sarki Aminullah yace. "Abinda na faɗa da farko, ya za'ayi mu tafi da nakasasshen yaro cikin jama'a" idanun Fulani Zaliha ne suka ciko da ƙwallah nan take ta fara hawaye, Mai martaba bai jira cewarta ba ya wuce ya barta a gurin. Babu wacce ta tanka mata haka suka wuce suka barta a gurin, Fulani Maryama dukda tana cikin halin jimami hakan bai hanata jin zuciyarta fes ba saboda ko ba komai tasan batayi asarar mahaifi a banza ba. Kafin ta ƙarasa tuni Mai martaba ya shiga cikin motarsa itama ta wuce motar da su Fulani ta suka shiga, suka ɗauki hanyar tafiya. Motar da suke ciki mota ce irin ta wancen lokacin me shige da fasalin Ladi ba ɗuwawu, tafiya sukayi me nisa har suka ƙarasa ƙasar Gombe.

Kwanan su ɗaya a masarautar Gombe suka juyo gida duk wanda yaga irin kukan da Fulani Maryama take yi sai ya matuƙar tausaya mata, Fulani Zaliha kuwa duk a ɗaɗɗare take kasancewar ta lura da Mai martaba kamar fushi yake da ita, ko gaishe shi tayi ciki-ciki yake amsawa a haka har suka dawo gida zuciyarta a dagule musamman idan ta tuna da abinda Mai martaba ya gaya mata. Tun daga ranar kuwa Sarki Aminullah ya daina shiga sabgarta da ta Saif, shi da ita sai dai kadaran kadahan babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu, ko turakarsa ta zo da Saif zai ce mata ta mayar da shi. Haka Fulani Zaliha ta ci gaba da ƙunsar baƙin ciki idan abun ya yi mata ciwo sai dai ta shiga ɗaki tayi kuka me isarta, cikin dare kuma bata fasa kaiwa Allah kukanta ba haka ta duƙufa ba dare ba rana ta fauwalawa Allah lamuranta. A haka rayuwa ta cigaba da gangarawa har aka shefe shekara biyar sai a wannan lokacin cikin ƙudura ta ubangiji ta fahimci Saif ya fara koyon zama dukda har ya kai waɗannan shekarun bata fasa koya masa zama ba, kuma bata fasa kaiwa Allah kukanta ba. Babu wanda ta gayawa kuma a ranar da ta ga haka ba ƙaramin murna tayi ba, a cikin ƙasa da wata huɗu zaman Saif yayi ƙwari dan a yanzu tana iya zaunar da shi ta tafi aikin gabanta, har sai da zamansa yayi ƙwari sannan wata rana suna zaune da Mai martaba ta sanar masa. Ga mamakinta sai ta ga bai yi wani murna ba dama kuma batayi tsammanin zai nuna jin daɗin nasa ba, tun da yadda ta lura ba wani ji yake da shi ba ko dan shi nakasasshe ne oho, saɓanin Salman da yanzu duk inda Mai martaba yake yana gefensa. Shikuwa Saif sai ya shafe sama da sati biyu basu haɗu da Mahaifinsa ba, saboda ko kaɗan Baya ƙaunar Fulani Zaliha ta raɓo shi da shi. Sarki Aminullah shi kansa abinda yake yiwa yaron yake damunsa sam baya jin daɗi a ransa wani lokacin abun har damunsa yake yi, sai yayi kamar yace a kawo masa Saif sai kuma yaji sam baya ƙaunar ya raɓe shi, a wannan lokacin Saif na da shekara shida yayinda Salma yake da shekara bakwai a duniya, Fulani Maryama babu wani abu da yake damunta a yanzu saboda bata da wani abu da zai ɗaga mata hankali, tun da ba ita kaɗai ba hatta sauran mutanen da ke cikin masarautar sun san fifikon da Sarki Aminullah yake yi tsakanin Saif da Salman.

Lokacin da Saif ya kai shekara goma lokacin ya ƙara girma sosai kammaninsa dana Sarki Aminullah ba ƙaramin ƙara fitowa sukeyi ba, a wannan lokacin cikin ikon Allah ya fara jan ciki a haka yake zuwa duk inda yake san zuwa a sashen mahaifiyarsa, dan ma ta hanashi fita saboda bakin mutane da ƴan tsegumi yana fita ake dandazon zuwa kallansa, da ƙyar Fulani Zaliha ta shawo kan Mai martaba aka samo me koya masa karatu, da farko Sarki Aminullah faɗa ya rufe ta da shi lokacin da ta sameshi da magananar. Sai da ya gama sauraronta yace.
"Haba Zaliha ke meyasa kin fiye fitina yaron da yake a nakashe ta yaya zai iya koyan karatu?" Fulani Zaliha ta ce. "Allah ya taimakeka hakan ba yana nufin zamu barshi haka babu ilimi ba tunda yaron nan ba ciwon hauka yake yi ba kuma babu abinda ya samu ƙwaƙwalwarsa, Allah ne ya hallitoshi haka ba dan baya ƙaunarsa ba, yaron nan ba kurma bane duk abinda nake faɗa yana jina kuma wata baiwa da yake da ita duk inda na aikeshi a ɗakina kome nace ya ɗauko min zaije ya ɗauko min, kana

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

1 Comments On ANYA BAIWA CE
avatar
kabiru-6

1 year ago

Reply

Uhmm

Please Login or Register in order to submit comment