Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 1&2*

Yanayin garin na Kano yau cike yake da ni'ima, sai iskace mai sanyi take kad'awa a ko ina sakamakon hadarin da ya wuce, kowa ka gani yana harkokinsa cikin farin ciki da walwala.

A cikin unguwar ta Hausawa wata farar mota 'kirar........... ta tsaya 'kofar wani kyakkyawan gida, sau biyu matu'kin motar ya matsa horn mai gadi ya bud'e masu get sai matu'kin motar ya shiga ciki.

Bayan ya samu guri yayi parking wasu matasa ne guda biyu masu kama da juna suka fito, sai dai daga dukkan yanayi d'ayan zai girmi d'aya, babban ri'ke yake da yaro d'an kimanin shekaru biyu a hannunsa.

Daga bayan motar kuma wata mace ce ta fito sai wata 'yar budurwa da ba zata wuce shekaru sha biyar zuwa sha shida ba, sai wasu yara mace da namiji da suka fito duk daga bayan motar.

Cikin d'oki wannan 'yar budurwa tayi hanyar cikin gidan da sauri, d'aya a cikin mazan nan yana mata magana "ke Amatullah wa zaki bari da d'iban kayan" amma ina ko sauraronsa bata yi ba ta shigewarya cikin ginin gidan ta barsu a wurin.

Bayan shigewarta ne babban ya dube shi tare da cewa "ai kaima kasan Amatullah da Hajiya, yadda take d'okin ganin tan nan ban ce ta ji abinda kake cewa bama."

Murmushi kawai ya yi yace "barni da ita kawai Yaya, ai zan shiga gidan na same ta ne."

Daga haka ya zagaya ya bud'e booth ya fito da babban trolly da kuma 'karama, dole shine ya d'auki babban matar kuma ta d'auki 'karamin suka shiga cikin gidan gaba d'aya.

Ita kam Amatullah tana shiga cikin gidan da gudu ta nufi dattijuwar matar da ke zaune kan d'aya daga cikin kujerun da aka 'kawata parlour'n da su ta fad'a jikinta tana cewa "nayi kewarki Hajiyanmu."

Cikin fara'a dattijuwar tasa hannu tana 'ko'karinta ture ta daga jikinta tare da cewa "shiyasa kike 'ko'karinta karyani ki sa 'ya'yana garari, tashi min daga jiki ke da bakya girma."

Gyara kwanciya Amatullah tayi tana cewa "wata nawa ban hau cinyarki ba, kawai ki barni na more."

Sallamar da akayi a ba'kin 'kofar parlour'n ne yasa Hajiya ba ta ce komai ba ta mayar da hankalinta ga masu shigowa fuskarta d'auke da fara'a tana yi musu sannu da zuwa.

Haidar da ya shigo daga ''karshe ya hango yadda Amatullah tayi d'are-d'are a cinyar Hajiya, ai kuwa ya zabga mata harara tare da cewa tashi daga jikinta kafin ranki ya 6aci, uwar 'yan son jiki baki da aiki sai na zama a jikin mutane."

Zum6aro baki tayi yayin da Hajiya tace "to kai ina ruwanka? Jikinka ta hau ko nawa?

Ai kuwa nan Uncle Bashir da ke zaune shida Aunty Habiba suka sa dariya "Uncle yace kai matsalarka kenan Haidar baka gani ka 'kyale sai ka tanka, ka san dai ba'a shiga tsakanin Hajiya da Amatullah, duk wanda ya shiga kuwa shi zai ji kunya."

'Kara had'e fuska yayi yace "ai dama kai da Hajiya ba kwa son laifin Amatullah duk abinda tayi bakwa so a kwa6e ta, shiyasa takewa mutane sangartar da ta ga dama.

Gaba d'ayansu dariya su kai, ganin yadda yayi da fuska kamar 'karamin yaro.

Suna cikin gaisawa ne me aikin Hajiya ta fara shigo da abinci, abinda zai baka tabbacin dama an san da zuwansu.

Zuruf Amatullah tayi ta mi'ke ta isa gaban warmers d'in ta fara bubbud'ewa don ganin abinda ke ciki, ai kuwa tana ganin alkubus fuskarta ta cika da farin ciki da fara'a, tace "yauwa Hajiyata shiyasa nake yinki."

Nan take ta d'auki plate ta fara serving d'in Uncle Bash, ta kai gabansa ta ajje sannan ta zubawa Aunty nata, sai ta zubawa sauran yaran.

Ta mayar da kallonta gurin Haidar tare da cewa "Uncle Haidar a zuba maka?"

Harara ya zabga mata tare da cewa "a'a karki zuba, tunda kinyo guzirin abincin ne kin taho da shi."

Hajiya tace "wai me yasa kai ba'a yi maka gwaninta ne? Yanzu daga tambaya sai ya zama laifi? Ai sanin tsurfarka tayi, yanzu idan ta zuba ma in baka ga dama ba cewa zakai baka saka ta ba.

Ita dai Amatullah bata 'kara magana ba ta zuba masa abincin ta kai gabansa ta ajje, sannan ta d'ebi dai-dai wanda ta san zata iya ci ta zauna a gefe ta fara ci.

Bayan kowa ya gama cin abincin ta tattare kwanukan da su kai amfani da su, ta mayar kitchen, tana dawowa parlour'n ana kiran sallar la'asar wannan yasa mazan mi'kewa suka fita don yin alwala su tafi masallaci, su kuma matan kowacce ta nemi inda zatai alwala don gabatar da tata sallar.


*Ummu Aisha*
[8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 3&4*

Tun bayan da suka fita babu wanda ya dawo cikin gidan sai dai jin 'karar motarsu su kai, alamun dai dake nuna sun bar gidan, su kuwa su Amatullah kowacce parlour ta dawo har Hajiya, nan suka zauna ana ta hirar yaushe gamo, sai labari suke bawa Hajiya.

Wajen biyar da rabi na yamma Hajiya ta d'auko mukullai ta bawa Amatullah tace su je ita da Baba Mairo (wato mai aikin Hajiya) su share gidansu, ba sai an jima sun koma a tsaya sharewa ba.

Babu musu Amatullah ta kar6i mukullin, ta jira Baba Mairo suka fita, Muhammad 'karamin yaron Aunty Habiba sai rigima yake zai bi ta, ita kuma tace "babu in da zanje da kai, haka kawai ka hana ni aiki da 'kiriniyarka.

Gidan da suka shiga a Jere suke da gidan Hajiya, sai dai shi a rufe yake saboda babu kowa a gidan.

Duk da ba wani dad'ewa sosai sukai da barin garin ba, amma sun sami gidan yayi 'Kura sosai, kasancewar babu kowa a gidan, sun sha aiki sosai don sai da sukai sallar magriba sannan suka gama komai, suka rufe gidan suka koma gidan Hajiya.

Bayan sallar isha Alhaji Babba suka shigo gidan yana kan gaba, yayinda matsan 'ya'yan nasa ke biye da shi a baya.

Kai tsaye parlour'nsa ya wuce, ai kuwa da sauri Amatullah ta mi'ke zata bishi, sai Haidar ya kama harararta tare da cewa " Allah yasa naga 'kafarki a parlour'n Alhaji ki ga yadda zamu yi da ke, daga dawowarsa ba zaki bari ya huta ba zaki je ki takura masa."

Hajiya da ke fitowa daga d'aki tace "wai Haidar ina ruwanka da takwarata ne? Ka d'aurawa yarinyar nan zani da tsanani a gidan nan fa, wallahi za mu sa 'kafar wando d'aya da kai."

Aunty Habiba da ke zaune tana sauraronsa tace "ina ganin kishi yake ta zo zata tare masa fada tunda shine auta, yanzu kuma zata 'kwace duk kulawar da kuke bashi ku mayar kan......."

Kafin ta 'karasa ya katseta tare ta da cewa ashe kin gane inda matsalar take, idan yarinyar nan ta zo daga Hajiya har Alhaji mantawa suke da ni, komai sai dai kiji sun ce ita."

Bashir da har ya kai hannunsa jikin 'kofa zai bud'e yana son zuwa parlour'n Alhaji don su gaisa ya juyo ya ce "amma dai kai anyi babban banza mai kishi da 'yarsa."

Hajiya ce ta cewa Amatullah "kinga takwarata tashi ki je ku gaisa da Alhaji tun kafin ya fara cigiyarki."

Ai kuwa da sauri ta mi'ke don dama kad'an take jira.

Tana shiga bata zauna ko ina ba sai gefensa, sannan ta gaida shi, shima cikin sakin fuska ya amsa mata, abinda ke nuna akwai 'kauna da sha'kuwa tsakaninta da shi, nan yake tambayarta karatunta, ta bashi amsa da "Alhamdulillah."

Can ta d'anyi 'kasa da murya yadda Uncle Bash dake zaune a parlour'n ba zai ji abinda take cewa ba tana magana, dattijon ya d'ago kai yana kallonta sai kuma yasa hannu ya dungure mata kai, "ai dama nasan aikin kenan, tun da Kura ta zo, wai Sa'adatu yaushe ne zaki daina kwad'ayi?"

'Bata fuska tayi kamar mai son yin kuka, cikin muryar shagwa6a tace "ni dai ka daina ce min kura."

Shima ya bata amsa da cewa "sai ki daina zuwa cinye min kilishi."

A hankali tace "ni dai don Allah ka bani."

Hannunsa ya nuna mata zuwa inda yake ajje a cikin wani bocket mai kyau, ta tashi taje gurin ta bud'e d'an bocket d'in, tana bud'ewa ta ware takardar da kilishin ke ciki ta d'ebi son ranta, sannan tayi godiya ta fita fuskarta d'auke da farin ciki.

Tana fita parlour Hajiya ta ganta ri'ke da kilishi tace yauwa kurar Alhaji ta zo, yanzu zaki fara cinye masa kilishi, da sauri ta nufi hanyar d'akin Hajiya, ganin yadda Uncle Haidar dake waya yana hararar plate d'in hannunta, don ta tabbatar idan ya gama wayar tana nan sai ya kwashe kusan rabi, tunda dama haka suke da shi, kuma tayi magana yace zai d'auki mataki a kanta tun da shi 'kanin babanta ne.

Tana shiga d'akin ta samu guri ta 6oye abinta, sannan ta zauna tana cin kad'an da ta rage, ai kuwa bata dad'e ba saiga Muhibba ta shigo kiranta wai ta zo su tafi gida, sauran wanda yake hannunta bawa Muhibbar suka fito tare.

Idon Uncle Haidar a kanta, cikin had'e fuska yace 'ke d'aukko min plate d'in da kika fito da shi daga d'akin Alhaji."

Tace "na cinye fa Uncle, kad'an na d'ebo dama."

Ya 'kara had'e fuska tare da cewa "wai yaushe na fara wasa da ke?"

Muhibba da ke cinye guntun kilshin hannunta tace "Allah Uncle ta cinye, ka ga ni taba wa sauran ma, dole babu yadda zaiyi ya ha'kura, Hajiya dake sauraronsa tace " kai dai Haidar zanga ranar da zaka girma, idan so kake kaje da kanka ka kar6a mana, amma sai dai idan yarinya ta kar6o ka 'kwace mata."

Shiru yayi baiyi magana ba, nan su Amatullah suka tattara gabad'ayansu suka tafi gida tare da yiwa Hajiya sallama.
Suna zuwa gidan wanka aka yiwa yaran tun da gidan a gyare yake babu inda ba'a gyara ba, sai aka shiryasu cikin kayan barci, Baba Mairo ta kawo abincin da dare nan aka bawa yaran suka ci, sannan suka kwanta saboda gajiyar hanya.

Zuwa 'karfe tara da rabi kowa ya kwanta yayi barci kamar babu kowa a gidan,sai iya Aunty da Amatullah kawai da suka zauna a parlour suna hira, shigowar Uncle Bashir ne yasa Amatullah yi musu sai da safe ta shiga d'aki, sai da ta fara yin shafa'i da wuturi sannan tayi addu'o'in kwanciya barci ta kwanta.


___________________________________________________________


Washegari tun da asuba da suka tashi sukai sallah kowa ya koma ya kwanta, amma banda Amatullah, don bayan ta idar da sallah sai ta zauna karatun Qur'ani, kafin ta kammala zuwa lokacin gari yayi gaske sosai, sannan tayi addu'o'inta da azkhar, ta fito parlour ta fara gyarawa, sai da ta share tayi mopping, ta d'auko bunner ta saka turaren wuta sannan ta koma d'aki.

Nan ma bata zauna ba, toilet ta shiga ta wanke tas, tana fitowa Aunty Habiba na shigowa d'akin cikin kwalliya, abinda ke nuna alama ta dad'e da tashi daga barci itama.

Fuskarta d'auke da murmushi tace "Amatullah sarkin aiki, yanzu ko hutawa ba zaki zauna kiyi ba, saboda gajiyar hanya? Da sassafen nan mutum ya tashi ya kama aiki kamar engine."

Amatullah tace "kai Aunty, wai ina aikin yake ne?, kuma nifa wallahi bana jin gajiya, tafiyar da ba' a mota muka yita ba."

"Ai shikenan, ke dai ba kya son zama haka amma dai ya kamata ace kin d'an kwanta tun da kin san zai yi wahala ki samu damar hutawa idan ba dare ne yayi ba."
Aunty da kanta ta tashi yaran tayi musu wanka, ita kuma Amatullah ta shirya su, sai Muhibba kawai da tayi da kanta, sannan Amatullah ta shiga daga 'karshe, kafin ta fito har Muhibba ta gama gyara d'akin yayi fes kamar babu wanda ya kwana a ciki.

Itama shiryawa tayi cikin dogur rigar shadda, d'in kin ya zauna a jikinta, ba 'karamin kyau tayi ba, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin 'kamshi, ban da 'kamshi babu abinda take.

Tare suka fito parlour da Muhibba da take zaman jiranta, suna fitowa suka gaida Uncle dake zaune a kujera da kofin tea a gabansa, don Uncle Bashir mutum ne da baya wasa da cikinsa indai akan abinci ne.

Kai tsaye dining suka nufa, inda suka gano Aunty da sauran yaran a zaune suna karyawa, suma suka sami guri suka zauna, kowacce ta zuba abinci suka fara ci.

Bayan sun gama sai da suka kwashe komai suka wanke, sannan suka fara shirin barin gidan, don zuwa gidansu Aunty Habiba, ita kuma Amatullah zata je gidansu itama.



*Ummu Aisha*
[8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 5&6*


A 'kofar gidansu Aunty Habiba da ke unguwar tudun yola ya tsaida motarsa, gabad'aya yaran da d'oki suka shiga gidan, sai iya Muhammad ne kawai Aunty ta ri'kewa hannu suka shiga tare Bashir na biye da ita a baya.

Su Amatullah suna shiga gidan suka sami Umma mahaifiyar Aunty tsaye a tsakar gida tana bawa almajirinta kud'in cefanen da zata aike shi, da gudu Muhibba ta je ta rungume ta tana murnar ganinta.

Itama nan take fuskarta ta cika da farin cikin ganinsu cikin 'koshin lafiya, tare suka juya zuwa d'akinta da ya kasance ciki da falo, a parlour'n suka zauna kan carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin tsaf dashi, kasancewar Umma mace ce mai tsananin tsafta.

Suna cikin gaisawa da Amatullah su Aunty suka shigo bakinsu d'auke da sallama, dukkansu guri suka samu suka zauna, sannan Uncle ya gaida surukar tasa cike da girmamawa.

Bayan sun gama gaisawa ya mi'ke da nufin tafiya, ya kalli Amatullah tare da cewa "ki taso mu tafi."

Nan take ta mi'ke, tana tashi Muhibba ma ta mi'ke da tace "nima can zan tafi."

Umma tace "a gaisad'a, nima na huta da shegen son jikinku daga ke har yayar tak kamar 'ya'yan mage."

Amatullah da har takai bakin 'kofa ta juyo tace "kwantar da hankalinki Umma, kema zamu dawo yi miki naki yinin, kuma cinyarki ce dai sai mun more."

"Kya more ma gani 'yar nema."

Haka suka fita, Muhibba ce ta shiga gaba, sai Amatullah ta shiga baya, Uncle ya tada motar, har suka je inda suka nufa babu wanda yayi magana.

Yana danna horn maigadi ya bud'e musu 'kofar, ya ja motar ya shiga ciki, daga Amatullah har Muhibba da gudu suka shiga cikin gidan kowacce na d'okin shiga gidan.

Kallonsu kawai yayi ya girgiza kai, sannan shima ya fito ya rufe motar ya bi bayansu zuwa cikin gidan.

A parlour ya taradda su tare da sauran yaran gidan, kasancewar ranar asabarce babu islamiyya ga kuma hutu babbar sallah da akayi, sai murnar ganin juna suke.

Hayaniyarsu ce tasa Mami dake d'aki fitowa don taga me ya saka su irin wannan hayaniyar, tana fitowa idonta ya sauka akan su Amatullah.

Duk da farin cikin ganin 'yar tata da tayi amma sai tace, "kin fi ga haka Amatullah, in dai ke ce zanga ranar da zaki girma, daga shigowarki duk kin cikawa mutane kunne da hayaniya.

Turo baki gaba Amatullah tayi, cikin shagwa6a tace "ni yanzu me nayi daga zuwa na? Ni kamar ma ba ki kewata ba."

Harararta kawai Mami ta yi ta maida hankalinta kan Uncle Bash da ya sami guri ya zauna yana kallon dramer da suke, guri ta samu itama ta zauna sannan suka gaisa cikin mutuntawa ga juna kamar yadda suka saba.

Tambayarsa tayi Habiba da sauran yaran, ya amsa mata da cewa "suna lafiya, yanzu na kai su can gidansu."

Sun ci gaba da hira har zuwa lokacin da Daddy'n Amatullah ya fito daga 6agarensa, fuskarsa d'auke da murmushin ganin 'kanin nasa.

Zama yayi shima suka gaisa, aka ci gaba da hirar da shi, ganin haka sai Mami ta tashi ta shiga kitchen tare da kiran Amatullah, aikin abincin rana suka fara, su kuma sauran yaran suna can a parlour suna ta wasansu.

Har suka gama abincin rana su Daddy suna zaune a parlour'n basu tashi ba, Amatullah ce ta fito ta fara shirya table lokacin kuma su Uncle Bashir suka mi'ke don zuwa masallaci saboda lokacin sallar azahar da ya yi.

Tana gamawa itama d'akin 'kannenta taje ta yi alwala don yin sallah, kamar yadda sauran yaran kowa ya tafi yin sallah.

Bayan sun dawo daga masallaci suka zauna suka ci abinci sannan suka fita tare. Nan su Amatullah suka yini har dare cikin farin ciki.

Kowane lokaci Mami ta kalli Amatullah tana godewa Ubangiji da irin uwar ri'kon da ya bata, da farkon lokacin da Habiba ta nemi a bata ri'kon Amatullah har a zuciyarta bata so hakan ba, duk da ta tabbatar 'yarta bazata wula'kanta a gidan Bashir ba, babban abinda yake saka ta a damuwa shine, matan zamanin nan ba kowacce mace ce take son a ra6i mijinta ba.

Amma dole ta danne zuciyarta ba tare da kowa ya fahimci bata so ba, tana kallo maigidanta ya d'auki Amatullah da ta kasance babbar 'yarsu ya bada ri'konta a hannun 'kaninsa.

Yanayin yadda yarinyar take rayuwarta da walwala shi zai tabbar da cewa bata da wata matsala a gidan, ga kuma sha'kuwa dake tsakaninsu da Auntyn tata.

Wannan yasa ba 'karamin mutuncin Habiba take gani gani ba a idanunta.

Kuma zumunci sosai suke a tsakaninsu, ko sa6ani suka samu da Bashir Mamin Amatullah take kira a waya ta sanar mata duk da nisan garin dake tsakaninsu, ita kuma zata kira Bashir suyi magana, har sai sun sasanta.


___________________________________________________

Sai bayan anyi sallar isha Uncle ya zo d'aukar su Amatullah, amma 'kememe Muhibba tace ba zata bi su ba, saboda ganin 'kawarta Kausar, dole haka suka tafi suka barta a gidan.

Ba da mota ya zo ba,kasancewar gidan a bayan layinsu yake, da 'kafa suka tafi har gida, suna zuwa ya tsaya a waje, sai da ya ga shigewarta cikin gidan sannan shi kuma ya shiga gidan hajiya.

A parlour ta same su zaune Ammar na kallo, shi kuma Muhammad yayi barci an kwantar da shi a kan kujera.

"Sannu da gida Aunty."
"Yauwa ya Aunty Bilkin da yaran?"
"Suna nan lafiya, tace tana gaida ke."
"Ina amsawa"

Sun d'an yi shiru na wani lokaci sannan Amatullah tace "Muhibba ta 'ki dawowa wai a gurin Kausar zata kwana, shine Uncle yace a rabu da ita."

Murmushi tayi tare da cewa "dama nasan za'a rina tun da suka had'u da Kausar ai Aunty Bilki ta had'u da gamonta, bari-bari kawai ya isheta."

"Ai kuwa wallahi yauma haka akai ta rabon fad'a, Muhibba iyayi Kausar kuma son girma kamar gyambo, kuma da anyi fad'an za'a jone aci gaba da wasan tare."

"Yo dama meye 'kuruciyar? Ai shiyasa ake cewa wanda ya shiga fad'an yara ya ji kunya."

*Wallahi kuwa." Cewar Amatullah.

Aunty tace "tashi muje kitchen mu gyara cefanen da Uncle d'inki yayi, saboda abinda zai iya lalacewa."

Tare suka shiga kitchen d'in, nan suka zage suka gyara kayan cefanen, sai da suka tabbatar komai sun ajje shi a muhallinsa sannan suka kashe wutar kitchen d'in suka fito.

Nan ma basu zauna ba, Amatullah ce ta sa6i Muhammad da yayi barci zuwa cikin d'aki, itama Aunty sai ta tashi Ammar da barci ya kwashe yana kallo zuwa cikin d'akin.

Sai da ta yiwa yaran addu'o'in kwanciya barci ta tofe musu a jikinsu sannan ta kashe musu wutar d'akin ta fita tare da yiwa Amatullah sai da safe.



*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 7&8*


Washegari da aiki sosai suka tashi a gidan kasancewar ranar jajiberi ce, dama sun zo gida nedaga garin porthercout inda Uncle Bashir yake aiki don gudanar da bikin babbar sallah kamar yadda suka saba duk shekara.

Daga 'karamar sallah har babba babu
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment