Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace sosai ma dalibatace itada meenat da ita zan aura



Laila da suby suka dau salati suna kallon kallo

Hajiya rukayya kuwa zufa yajikata sharkaf
Saboda rashin gaskiya



Hakeem yayi murmushi gefen baki
Ya kalli husnah yace baby kinsanshi daman tace a copper ne a school dinmu

Yace daga bawani Abu takalli bash ta kalli meenat da jikinta yake bari

.tace bakomai bayan wannan
Bash yace karkice haka asmau nasan ban kyauta miki ba
amma Dan Allah karkice ba komai a tsakaninmu


Cikin bacin rai husnah ta kalleshi tace dan Allah malam dakata karkasake min maganar wani alaka

A ina nasanka da harwani Abu yashiga tsakaninmu bayan malami da dalibarsa



Bashir yazube gaban prof yace wallahi ba a hayyacina nafasa aurenta bansan meyake faruwaba

A lokacin ba abinda nake gani sai amina


Hakeem ya kalli husnah yace daman shine Wanda kike bani labari amina ma itace kawarki da kike bani labari



Tunda akafara maganar kuka baizowa husnah ba sai yanzu

Ta fashe da kuka data tuno da abinda suka mata

Dagudu tabar falon

Hakeem yakai kallonshi ga amina yace ke inason kifada min gaskiyar abinda kefaruwa bana son kimin karya kinsan halina



amina tafashe da kuka ta kalli bashir tace Dan Allah uncle kayafemin


Hajiya rukayya tace ke karkice komai tashi kitafi daki

Hakeem yace ba inda zakije sai kin amsa min tambayata

Cikin kuka meenat ta kwashe komai tafadamusu


Kunyar duniya hajiya rukayya da su hajiya suwaiba da laila sunshashi agun


Bashir yadago idonshi kaman garwashin wuta ya kalli meenat yace amina kuncuceni duniya da lahira

Ninasan dama duk abinda na aikata wa asmau
Ba a hayyacina na aikata ba


Ba abinda zance saidai nace Allah ya isa tsakanina dake da kakarki


Ya kalli Hakeem yace kamin aikin gafara wallahi bazan iya zama da amina a matsayin mataba

Nasaketa saki uku kuma a hayyacina nasaketa

Bana bukatar ta a ruyuwata

Ya tashi yay ficewarsa daga gidan baki daya



Hakeem yace kunga abinda kukajawa kanku ko
Yanzu wannan wani irin abin kunya ne haka

Yayi mun dai dai wannan shine hukuncin da yadace da ita

Kuma kunga dayake Allah ba azzalumin bawansaba ne kuncuci husnah kuna Ganin kunci bulus ko

To kunga aikin Ku saigashi duk abinda kuka yi nikuwa tanadi
Dan kuwa samun mata irin husnah a yanzu sai antona


Dole bash yamiki abinda yafi haka
Banga laifinshi ba Dan asarar mace kaman husnah bakaramin asara bane


Ya tashi yayi dakin husnah ya kullo kofar yanashi baiganta a faloba

Direct yawuce zuwa bedroom dinta

Ya hangota kwance kuka sosai takeyi kaman Allah ya aikota

Ya karasa yazauna dab da ita yakamo hanunta yace baby look in to my eyes


Husnah takasa kallonshi
Yace kukan mekikeyi
Tace bana son tuna abinda suka min ne

Saboda nashafesu a tarihin rayuwata
Yace idan hakane kidaina kuka

Kokinsan nigata suka min da bashir ya aureki ina zansameki baby
Kodaya banji haushin su ba
Saima godewa Allah da kuma hajiya rukayya
Duk abinda ta aikata karshe kan 'yarta yadawo


Dan haka kidaina kuka bana son kukan ki kinjiko
Tadaga kai sama yahau bed din dakyau yajanyota jikinshi yana shafa bayanta yace kokinsan bashir yasaki amina yanzu


arazane Husnah ta tashi tace meyasa zaisaketa bayan komai yawuce


Allah yabani Wanda yafishi
Baikamata yayi hakaba wannan ai cin amanar soyayya ce


Hakeem yamaida ita kan kirjinshi yace ai dama soyayyarsu bata Allah da annabi bane
Naji dadi dayawa amina wannan sakin


Hakan shizaisa tagane abinda yake dai dai
Tadaina bin zugan kakaninta Dana uwarta


Idan amina ta nutsu tagyara halinta
Zan maida ita makaranta insaku tare kucigaba da zuwa school dinku kamar yadda kuke da



Husnah tayi murmushi ta kara rungumeshi sosai tace idan kamana haka zamuji dadi sosai Allah yasaka da alkairi

Allah yakara daukaka da arziki mai amfani yakara mana lafiya yabaka ikon ciyar damu da halak
Yakara wa su mummy da daddy Nisan kwana da lafiya



Hakeem cikin tsananin son matarshi ya kara kankameta sosai a kirjinshi yace adduoinki agareni suna sani nishadi
Dani da su mummy duk muna alfaharin samun ki cikin rayuwarmu



Husnah tace Dan Allah sweet karkace zaka matasawa meenat

Kabarta na tabbatar zatayi nadama abinda tayi


Hakeem yace kedai kice kina bin bayan kawarki ko
Husnah tayi murmushi tace tun bayan rabuwata da meenat bansake wata kawaba daman nima bamai son tarin kawaye bane


Naso meenat zuciya daya itace dai tadaukeni da guda biyu


amma koyanzu takeson mucigaba da zumuncin mu
Ina son haka saboda ina son meenat sosai



Hakeem bai barta tacigaba da maganartaba yahada bakinsu guri daya

Nan fa wasa yacanja salo


Gashi ankusa kiran magriba kuma ba itace dashiba

Tayi kakorin kwatar kanta amma takasa tashiga hanun maza sosai Hakeem yafara fita a hayyacinsa yana kokarin rabata da kayan jikinta

Husnah tayi tunanin idan tabari fa ba takyauta Dan anshiga hakkin uwargida


Cikin kuka Husnah tafara wash Allah cikina cikina

Cikin sauri Hakeem yafara tambaryata meyasameta tace cikina nane yake ciwo

Dasauri yasauka daga kan bed din Dan dauko magani husnah naganin yafita ta tashi dasauri tashiga bathroom
Tasaka key


Yadawo yaga wayam bata kan bed murmushi yayi yace zan kamaki


Kifito nayi alwala kinga zantafi masallaci Husnah tace naki wayon kaje dayan bedroom din kayi acan


Murmushi yayi yasan idan zai biye mata bazata budeba





Meenat zaune gaban uwarta da kakanta kuka sosai takeyi


Laila tace duk abin ma ai kaina yadawo niyakama ta ace ina kukan bakeba

Hajiya rukayya kuwa cewa tayi share hawayenki Dan yasaki ke
ai bashine karshen mazaba


Dan haka kiyi shiru miji sai kin ce bakya so
Keda ba mummuna ba


Meenat tace wallahi ina son shi gashi harsaki uku yayi min
Yazanyi nayi rayuwa ba bashir


Husnah kincuceni bazan taba yafe miki ba sai na dau fansar abinda kika min


Laila tace dakuwa kincika 'yar halak mekishin kanta ban amince kibarta tasha ruwaba agidan nan zanso kizama kece kishiyarta baniba uwarki zan nuna mata ina da kamarki


Hajiya suwaiba tace gaskiya ne idai kujininane ban amince kubar maganar nan ba
Tunda saboda ita aka sakeki
Itama inason saboda ke ubanki yasaketa



Nan sukaci gaba da mummanar shirunsu



Hakeem yafito daga dakin husnah yayi waje batareda ya kallesuba




Husnah kuwa sai da ta tabbatar yafita kafin tayi alwala tayi sallarta hade da adduointa
Ta dauki alkuraninta tafara karantawa har aka kira isha
Kafin ta ajiye tayi sallarta



Tana idarwa ta ninke kayan sallarta tashiga bathroom tay wanka kafinta fito tashirya cikin wasu Riga da skirt din atanfa dinkin yayi matukar zama ajikinta tafesa turararukanta
Tayi parking din gashinta
Tadaura Dan kakwalin ta das kaman wacce aka dasa akanta

Tasake gyara dakinta kafin tafito falonta

Daman kafin Hakeem yakirata tagama abincinta mai rai da lafiya
Couscous ne tadafa fari da miyar kaza

Sai zobo drink mesanyi
Wanda yasha flavour masu kamshi
Da yakan kamshin


Nan tadauki plate tadeba abincinta tasa miya

Tadauki Dan karamin glass jug tazuba zobonta aciki
Taduki karamin cup tayi waje
Main falon gidan taje center table tajawo ta ajiye kayan abincin ta akai kafin tazauna zaman ci


Bakowa afalon sai TVdake kunne


Can saiga su sunfito gabadayansu kowa tanemi kujera tazauna



Husnah tace barkanku da fitowa
Duk zuba mata tsaki


Husnah ta kallesu tace to Ashe abin nan
To Allah yasauwake

Tacigaba da cin abincinta

Can sai mai aikin laila tace anty nashirya dining din

Laila tace jeki kawasu nan muna a nan zamuci

Husnah tayi murmushi batace komaiba




********

Bayan wata hudu meenat tadade da gama iddarta da kusan watadaya kenan


Kuma a kano tayi iddarta yau take shirin komawa Kaduna gidan ubanta

Dan tadau matakin datake da niyar dauka akan husnah


Tuni driver yadukota zuwa kaduna

Laila tuni tasa angyara wa meenat dakinta
Komai yaji
Ita kawai dakin yake jira


Husnah kuwa yau ta tashi da kewan gidansu ne
Tunda tayi aure sau biyu taje
Kuma bai barta takwana ba
Yau tafita girki tana zaune kusa Hakeem tana mishi rigima ita sai yabarta taje takwana biyu agida kuma yau takeson tafiya


aikin dayakeyi a computer ma kasawa yayi
Ajiyewa yayi gefe yakamota yace baby bakya tausayina kinsan bazan jure rashinki kusadani bako

Husnah tasake shagwabewa
Tace aishiyasa nace natafi yau jibi da yamma insha Allah sai na dawo

Kaga yau dagobe bani bace da kai antyna ce


Hakeem yace kedai kimin wayo ne kawai tashi kishirya
Sainasa driver yakaiki
Jibin zanzo na daukoki yau muna da meeting ne

Inkuma zaki bar tafiyar sai gobe to saina kaiki da kaina

Husnah tayi saurin cewa a a kaje meeting dinka kawai

Yayi murmushi yace wato murna kikeyi zaki barni harna two days ko


Husnah tasa hanunta a kumatunshi tace mezaisa nayi murnar barin minjina abin alfaharina


Hakeem yashafa cikinta Yakama ta muje aduba min kefa
Ina son yara baby yaushe zaki Haifa min yara masu kyau kamarke murmushi husnah tayi tace nikuma masu kaman kai nakeso su dauko


Yace dagaske kikeyi tadaga alamar a

Yace sai kidage sosai kinsan abin kokarine

Tabashi full attention dinta Dan yamata bayanin yadda kokarin yake

Yace kina son sanin yadda zakiyi 'ya'yan my suyi kama dake tace a


Yace OK yatashi yacire singled din jikinshi itadai husnah dai kallonshi takeyi da zuciya daya bata kawo komai aranta ba


Gani tayi yacire mata Dan kwalinkanta aikuwa ta gane meyake nufi
Cikin shagwaba tace wallahi nabar maka suyi kama dakai kawai


Hakeem yace a a kibarni kawai nayi kokarina Dan insamu mai kama dani kuma kice kinyafe

ai kokarin danake nufi kenan
Kibani hadin kai sosai kigani inbazaki samu masu kama dani ba



Husnah dai talura da gaske fa yake

Tace shine abinda kake bukata yace yes my Queen

Tace OK ina zuwa barinsha sha ruwa a fridge zanbaka mamaki yace really tace yes

Bani minti daya naje nadawo


Tasamu tamishi wayo tagudu shiru shiru bata dawo ba yatashi tafita zuwa part dinta

Yaga har ta fito daga wanka ma tana drying gashinta da hand drayer


Hanu yasa a kirji yace kimin lefi kinshiga min aiki tunda kinsan ina gida aikina nane namiki komai


Husnah tadago suka hada ido tasan bakaramin aikinshi bane yasata sake wanka yanzu

Karasowa tayi cikin shagwaba ta kwantar da kanta a kirjin tace na tuba my prince Dan Allah karka bata min wanka na wallahi dokin ganin umma yasa nake sauri


Hakeem yace ban yarda ba saikin min Abu daya

Tace mezanma
Yace kekisani murmushi husnah tayi tasan idan yafara haka rigima yake nema

Tace OK kan bed tahau taga Kansu yazo dai dai tahada bakinsu guri daya

Sosai take kissing dinshi Dan tasan abinda yake bukata kenan
Batayi aune aune ba taganta yakwantar da ita duk yadda taso yakyaleta yaki
Sai daya samu nutsuwa kafin yabarta
Cak yadauketa tare sukayi wanka suka shirya

Dakanshi yahada mata kayansawarta kala biyu cikin wani Dan karamin jaka mai kyau da sha'awa




~~~~~~~~~~

Husnah kwance falon ummanta kanta akan cinyar umma suna hirarsu

Anty kubra ta shigo falon tace kinsan Allah husnah kikiyayeni fa zaki karyamana cinyar umma ne katuwa dake


Husnah tayi murmushi tace to kwana nawa bangantaba banga ya shamsu ba

ai dole na damu nayi kewarsu saura ya shamsu zaizo shima yasameni yamin alkawarin zai dinga zuwa sosai yana ganina Amman bai cika ba



Husnah tace wallahi danwake zanci da dambu da kuma tuwan alkama

Kubra ta rike baki duk acikin ki kekadai tace sosai makuwa


amma dai yanzu tuwon nake bukata tukun

Anty kubra tace OK bani minti na muna da miya daman tuwon kawai zanmiki



Husnah tace yauwa matan yaya daga ke bawata


Husnah taci tuwo sosai umma da kubra sunyi mamakin


Umma dai murmushi tayi itakadai tasan dalilin murmushinta


Duk abinda takeso shi ake mata agidan su
Yaya shamsu kafin yadawo sai yatambayeta abinda take sha'wa ya taho mata dashi


Ranar da zata tafi tun azahar YOUNG PROFESSOR ABDUL HAKEEM ABUBAKAR

Ya isa kano gidansu husnah yazarce direct danshi jinshi yake kaman bashi da lafiya Dan kwana biyun datayi bata nan



Saida yaci abinci agidan shida ya shamsu kafin suka wa ummu sallama suka fito suka dau hanya


Hakeem yakasa boye zalamrsa akanta saida. Yayi parking a gefen titi
Komeyasa oho



Suna isa Hakeem yayi parking yazago yabude wa husnah kofa duk abinda kefaruwa a idon meenat da suby Dan suna lambun gidan suna hutawa

Takaici Yakama meenat tace wallahi anty suby danasan husnah zata auri daddy Dana wallahi da banbar hajiya taje gurin maganin ba

Yanzu gashi nibada bash itakuma da auren ubana har bayaganin kowa sai ita


Suby tace ai wallahi zamu koya mata hankali basu rufe bakiba Hakeem yadauko bag din husnah da Yakama hanunta suka shiga ciki


Suna zama husnah ta ce wayyo Prince zansha nun tsamiya zansha kuma nagaji dayawa beside ni idan nayi ma balle nashaba

Cikin sauri yazauna kusada da ita yace kobakida lafiya ne Dan naga kincan minfa sosai

Hanu takai ta lakuce hancinshi tace nidai ba abinda yake damuna
Kawai kasamomin kunun tsamiya

Waya yadaga yakira Ahmed yace kana gidane yace a
Hakeem yace kasa Aisha ta min kunun tsamiya zanzo na dauka

Kafin Ahmad yayi magana Hakeem yakashe wayarshi Dan yasan sai yamishi tsiya


Hakeem yajuya yaga hartafara bacci a mota gabadaya ma baccin tayi

Tashi yayi yamatsa kusa da yakura mata ido sosai

Can zuciyarshi tace anya yarinyar lafoyarta kalau kuwa


Yadauki waya yakira family doctor dinsu macen yace tazo da kayan aikinta
Yafada mata abinda yake zargi tace OK tagane gatanan zuwa


Hakeem cikin tsananin farin ciki yayi sujjadar Allah yatabbatar mishi da abinda yake zargi



Next page

Your comments is needed fans


Love all


πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“–πŸ“–πŸ“–πŸ“–πŸ“–πŸ“–
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN 🌹: πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—
πŸŽ—πŸŽ—
πŸŽ—
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Story & written
By
The special writer


UMMU AFAN

πŸ–ŠπŸ–ŠπŸ–ŠπŸ–ŠπŸ–ŠπŸ–ŠπŸ“š



🌹FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION🌹


🌹🌹 (F.C.T.W.A)🌹🌹



🌹HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION🌹




πŸŽ—I DEDICATE THIS PAGE TO YOU Aisha Ibrahim ina matukar jin dadin comment din ki wallahi keep it up ina alfahari dake over my sister πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸŽ—





πŸŽ—AKWAI LOKACI πŸŽ—





πŸŽ—PAGE 143 to 145πŸŽ—




Bayan gwaje gwaje da likita tawa Husnah ta tabbatar mishi husnah tana dauke da cikinshi



Cikin tsanin farin ciki hakeem yace alhamdulillah Allah nagode maka da cika min burina cikin gaggawa


Allah kasauketa lafiya likita tayi murmushi tace gaskiya wannan babyn zaiga gata prof irin wannan doki da murna haka


Yayi murmushi tare da rungume husnah ajikinshi tunda likitar tafada cewan ciki ne da ita
Ta rufe Idan kaman me bacci
Ita kanta takasa sanin meyasata jin kunyar




Hakeem yace wa likita kizuba ido kiyi kallo aranar da Queen dina ta haifamin baby a ranar zan yi abinda za bakowa mamaki
Kuma kema fa baza abarki ba zaki ga goron albishir a account din ki


Likita tayi murmushi tace kai amma nagode Allah yafito mana da wannan babyn lafiya


amma Yakama ka kawota hospital gobe Dan mumata scanning a tabbatar cikin wata nawa ne Dan kasan lokacin da zakafara tsammanin babayn ka


Hakeem yace ai bazan bari sai gobe ba yanzu zamu biki muje Nagani da idona

Doctor tayi murmushi tace ina jiranku to

Hakeem cak yadauki Husnah zuwa bedroom yasamata kataton hijabinta

Sannan kuma ya sunkuya wai ta hau baya

Husnah taga dagaske yakeyi fa
Taware tace a a Dan Allah Prince kabarni maka ganin bamu kadai bane


Hakeem yace ai ni mutane da maganarsu bai cika damuna ba ko agaban mummy zan iya goyanki ballantana 'yata


Husnah tace naji inkai bazaka ji kunya ba aini zanji
Ta kwasa dagudu tabar dakin
Yafito hankalinshi a tashe yace Dan Allah baby kidaina gudu karki samin baby yagaji


Husnah tatsaya cak taki juyowa
Ya tako ya iso har gurinta yajanyota jikinshi yace oya mutafi ko kinga doctor tana jiranmu a waje


Cikin shagwaba husnah tace tun ba aje ko ina ba kafara nuna min iyakata ko
Shine zaka ce wai kar babyn ka yagaji
Wato ma bani bace damuwarka babyn ne ko


Cikin murmushi Hakeem yajuyo da ita suna fusakanta juna yace Haba baby kema kinsan you are my one and only

Taya za ayi nace bandamu damu da lafiyarkiba

ai dake da abinda yake cikin ki
Inkincire mummy da daddy to kune rayuwata kune komai nawa



Husnah tace nidai banyarda ba
aikuwa sai ganin prof tayi gwiwa biyu agabanta

Cikin sauri itama tayi kasan takama hanunshi tace la nifa wasa nakema

Yayi murmushi yaja hancinta yace kinji tsoro kenan tace sosaima wace dasa zuciyata kneeling a kasa ai dole tsoro yakamani yayi murmushi yatashi yadagota cak

Dakyar tabashi hakuri yabarta ta tayi tafiya da kanta




Bayan scanning da akayi wa husnah aka ta babbatar musu da tana dauke da cikin sati bakwai wato getting to two months kenan



A gurin Hakeem yadauki wayarshi yakira mummy da daddy yasanar dasu


Mummy kaman tayi tsuntsuwa tazo taga 'yarta husnah haka take ji

Tayi murna sosai haka ma daddy

Dan mummy hafsat kam ma cewa tayi tundaga can zata fara sayayyar kayan jarirai




Daga hospital sai gidan su Aisha da Ahmad Hakeem yayi dasu


Suna zuwa kuwa Aisha takawo mai kunun tsamiyar dakan yazauna kan carpet ya hada mata sosai tasha kuwa duk sunyi mamaki


Ahmad yace amma natayaka murna abokina Allah yaraba lafiya


Aisha da itama haihuwar ko yau ko gobe

Tayi murmushi tace Allah sarki 'yar kanwata Allah yasaukemu lafiya ko


Husnah tace anty nifa bani da komai


Wasa fa yaya yake muku
Aisha da dariya yaso barke mata tace sosai Nagani kuwa

Wannan tulun kunun da kika shanye ai kowa yasan bake kadai bace


Husnah tayi murmushi tace ai saboda ina sone shiyasa

Hakeem yace sannu da kokari madam kema kina fama da kanki mun hada kida aiki

Tace bakomai wallahi bana ma son zaman

Nan Ahmad da Hakeem sukafita



~~~~~
Bayan sati biyu duk wannan abinda kefaruwa na maganar cikin nan baizo kunnen su Laila ba



Husnah zaune a falonta mai kamshi da sanyun Ac


Kaman daga sama taji murya kaman na anty kubra

Da sauri ta tashi taduba anty kubra ce kuwa tasha kyau cikin wani tsaddan less Dan shima ya ashamsu yanzu kudi yazauna mishi sosai shiyake juya dukiyar husnah Wanda tabashi ragamar komai a hanunshi


Kuma shiyazama manager a company Hakeem


Husnah tayi tsalle ta rungume anty kubra tace wayyo anty na wallahi naji dadin ganin

Anty kubra tace kai Husnah bakida hankaline wayafa miki meciki tana tsalle haka husnah tarufe ido tace anty nifa banida komai


Kubra tace ai Allah zata sake magana husnah taja sukayi part dinta


Laila dake zaune jin abinda anty kubra tace
Ya mugun daga mata hankali sosai

Tace kai ina karya ne wallahi ba zaki taba haihuwa gidan nan ba matsuyaciya


Meenat ce tafito daga part dinsu
Dauke da glass cup a hanunta na drink

Sai mummynta na hawaye
Sai Takaraso a tace meyafaru kuma mummy

Suby tace wannan 'yar talakawar ce wai cike ne da ita

Meenat batasan sanda tasaki cup din hanunta ba
Tace karya takeyi wallahi bata isa ta haifi wannan Dan iskan cikin nata agidan nan ba


Tayi hanyar dakin husnah suby tayi saurin tarota tace inazaki

Meenat kibarni naje anty suby wallahi sai namata dukan dazaisa cikin yazube inga tafadi


Suby tace idan kikayi haka daddynki zai dauki babbar mataki akanki

Kibari mubiyo musu tabayan gida
Ina tabbatar muku husnah bazata haifi cikin nan ba

Nan dai suby taringa basu shawarwari


Husnah takawo wa anty kubra gashashshan namar kaza da drink saikuma fruit



Ta zauna kusada anty kubra
Anty kubra tace anya wannan husnah ummace kuwa
Kinganki kuwa kinyi fresh dake kaman ba mai cikiba

Husnah tayi murmushi kafin tayi magana wayarta yayi kara tana dubawa taga Prince ne cikin shagwaba ta amsa sallamar

Anty husnah baki kawai tasake tana kallon husnah yadda tazage tana soyayya da mijinta ba alamar kunya cikin kawarewa da iya wa Hakeem yace to ya antyn mu
Husnah tace LA ya akayi kasan tazo yayi murmushi yace karkidamu ki isar min da gaisuwa na kafin mukaraso yanzu

Husnah tace kukaraso kaida wa kuma
Yace naki fada yayi murmushi yace bani baby na muyi hira naji abinda take bukata

Murmushi husnah tayi tace anty nan
Yace kibani baby muyi hira
Taga dagaske yake
Tayi murmushi ta kashe wayar






Sai da tagama taga anty kubra tazuba mata ido

Kubra tace anya wannan Husnar ummace kuwa towai Husnah ina kunyar ne wannan soyayya haka
ai sai kisa yakasa aikin


Husnah tayi murmushi tace anty kenan wallahi tun inajin kunyar ya Hakeem wallahi har na daina

Dan shi baruwanshi ko agaban waye baya kunyan nuna min soyayya


Anty kubra tayi murmushi tace to ai gwamma dai da kika nuna mishi kema kwararriya ce fanni kula miji kar kiyarda kece zaki kunyar wasu


Husnah tace wallahi anty kaman kinsan ni
Wallahi Allah yagani tsoro suke bani kawai nuna musu nakeyi kaman bana jintsoronsu
amma wallahi suna ban tsoro

Anty kubra tace ai karkisake Susan kina tsoronsu



Wato ita meenat din har yanzu bata sadudaba duk da irin jarabawar data gani na rayuwa

Husnah tayi murmushi tace wallahi anty sai abinda yakaru inda kikasan zata kasheni agidan nan haka take min

Dam tana tsoron daddynta ai da abinda zata min dayafi haka daga ita har uwarta

Anty kubra tace ai sai kigodewa Allah ma mijin ki nasonki
Husnah tayi murmushi tace ai ni wani zubin har tsoron nuna min son dayakeyi gabansu nakeyi



Anty kubra tace inbanda abinki ai hakan shine zaisa duk sukone da ruwan jikinsu

Nan dai anty kubra tayi ta bata shawarwari zaman duniya






YOUNG PROF da Ahmad da ya shamsu sukayi sallama suka shigo falon


Masu falon ne hakimce abinsu
Suby da meenat suka gaishesu amma banda madam laila


Direct dakin husnah suka shiga
Wani kamshi ne yadoki hancinsu yasa farin ciki a zuciyar Hakeem yasan kadan daga aikin husnah bata zama ba kamshi



Husnah cikin tsananin murna tace LA yaya shamsu daman harda kai kukazo shima ya shamsu
Cikin tsananin farin cikin ganin 'yar kanwar tashi

Yayi murmushi yace ai daman mamaki nakeson baki

Sosai husnah take murna ganinsu


Hakeem yace lalle ma baby wato kinga ya shamsu kin manta dani ko

Ahmad yayi dariya yace kai Dan uwa wasane ballantana su biyu kawai

Kokaima dakana da kanwa haka zaka nuna jin dadin ganin ta alokacin da kuka hadu bayan kun Dade Baku haduba


Young prof yayi dariya yace wayafada maka duk shakuwarsu

ai yanzu munfi shakuwa Dan nasan kozaba zatayi yanzu
Ya mu'allim zata dauka

Ya kalleta kobahakaba Queen dina

Husnah tashi tayi tabar gurin zuwa dining Dan hada musu komai






***********

Hajiya suwaiba tawa bokanta magana akan aikin datakeso yamata
Shine yabasu tabbacin sai sun zo dakansu baya son aika


Shiyasa da hajiya rukayya da hajiya rukayya suka shirya tafiya zuwa karbo maganin daza a wa husnah cikin yazube kuma ta haukace tabi duniya


******

Bayan wata daya da sati biyu
a yaune ake sa rai da dawowar su daddy da mummy


Husnah tagama gama hadawa su mummy abincin su mai rai da lafiya kusan kala hudu banda drinks kala kala
Da su farfesun kaji gasunan dai



Hajiya suwaiba da hakiya rukayya sundawo wajen satinsu uku kenan yau suke son aiwatar da nufin su akan husnah



Husnah da Hakeem sungama shiryawa kasancewar ranar girkintane


Har sunfito zasuje air Port dauko su mummy Sai taji kanta yasara mata tadafe kan nata

Hakeem dake bayanta yayi saurin karasowa yakamata

Yace yadai Queen tace kai nane yake ciwo
Yace o to sannu kinji kizauna kawai zanje na daukosu

amma barin kawo miki magani kisha kafinko

Duk wannan abinda me faruwa a idonsu meenat

Hajiya rukayya takashe mata ido daya

Meenat ta tashi da sauri tace daddy kaje kawai zan kawo mata maganin

Kaman daga sama yaji maganar abakin amina

Kafin yayi magana wayar daddy ya shigo wayar Hakeem

Hakeem yace sun sauka baby
Husnah tace badamuwa kaje kadauko min mummy na nafi bukatar ganinta akan

Please Login or Register in order to submit comment