Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zabinki??,duk aikin daza'ayi miki zabi biyu ake baki,kike daukar daya. Lokacin dazan fanɗarar da yarinyar nan nasaka mungun halinta ya zaga duniyah,saida na cemiki shin na tura mata aljanu ko kuma na kasheta? Kika zabi na juyah tunanin ta,haka ma ga mahaifiyar ta,muncemiki mu kasheta komu nakasa ta,kika zabi a nakasa ta.
Jaririn da aka haifane kaɗai kika buƙaci a kasheshi mu kwashe jininsa,kuma munyi miki hakan"
Cikin rawar murya da shiga ha'ula'i Inna laari tasake ƙasƙantar dakai tareda cewa.
"Tabbas nina zaba kam,saboda a lokacin so nake su wahala basuyi mutuwar sauƙi ba labarinsu ya shafe,sona ke suyi dasunsanin shiga cikin gona ta nida mijina,amma yanzu ita yarinyar baza'a iyah kashemin itaba?"
"Wai meyasa kike manta sharadin da muke bakine,kinsan fah duk abinda kike mana na sakarci ƙyaleki mukeyi saboda jikin ƴar uwarki dakika bani nake amfani dashi ta fitowa a gaban ku.....idan na kashesu yanzu to fah duk abinda yake jikinsu kanki zai dawo dukka,shin kin yarda da hakan"
Saurin girgiza kai tayi tareda cewa.
"Ahah ranki ya daɗe banason hakan,shikenan babu dama a kawar dasu yanxu,dana sani da tunda aka kashesu ma"
"Hhhh karki damu munji barazanr da tayimiki,kuma inamai tabbatar miki dagaske takeyi zata aikata,yarinyar tana da ƙarfin ruhi,duk da baƙin Aljanu suna riƙeda ragamar tunanin ta,wani lokacin takan iyah turasu baya,amma zamu kafeta a garin dazata ce mu hanata dawowa harsai kinsamu abinda zamu umarceki ki samo.
Da sune kaɗai zamu iya amfani mu kasheta,batareda aikin damukayi musu yadawo kanki ba"
"Yawwa nasan babu abinda zai gagareki a faɗin duniyar nan(Azubillahi),to shikenan a kafeta a garin,nikuma koma menne zanyi ƙoƙarin samowa kafin ta dawo"
"Wata bishiyace datake rayuwa a Sahara,tanayin aƙalla shekara ɗari biyu a raye,sannan takanyi fure duk bayan shekara biyu,wannan shekarar tayi furenta,kuma nayi amfani dashi a wasu,dan haka dole saidai kijira zuwa nan da wani furen bayan shekara biyu tukunna"
Kana ganin fuskar inna laari kasan abinda aka faɗa bayyi mata,saidai babu yadda zatayi dole tayi jiran hakan. Koƙarin kawar da zancen tayi ta hanyar cewa.
"Uhm nace ba maganin farin jinin innayi fah har yanzu ba'a samu ba"
"Wannan kuma nan da wata shida zanyi miki magana,akwai abinda na shiryah akan ta,inajinta tamkar ƴa nima,ko kinmanta da ƙoƙarin dalasimaina aka samu cikinta....sannan kuma akwai alƙawarin damukayi dake gameda ita tun kafin haihuwarta.....!?
Shuru inna laari tayi tana zazzare ido,wanda yake nuna ta tuno wani abin tashin hankali daya faru da ita,saidai duk da hakan bata tanka dan tasan maganar matsafiyar gaskiyane......(toh fah yaya takene?)
"Hhhhhh nasan bazakice komai ba,saidai abu daya nakeso ki sani shine ba'a tsallake maganata koma waye,sannan ba'ayin yarjejeniya dani a saba,batun wanccar yarinyar kuma ki zuba ido gobe zata bar garinnan,ba jibi ba kaman yanda tace"
Jingina kanta tayi bangon ɗakin tana ɗan jijjiga haidar dayake kan cinyarta,baccine yafara daukarta,can cikin bacci taji ana cewa.
"Kibar garinnna bamason garinnan saikin bar garinnan zaki bar garinnan............hhhhh mutafi bazamu zauna ba"
Buɗe ido tayi tareda tafe kunnuwanta guda biyun wanda maganar take shiga ciki,ta haddasa mata barazanar fashewar kanta da kuma ciwon kai mai tsanani.
Cize baki tayi har fatar bakinta tana fashewa saboda sakata datayi tsakanin haƙoranta.
"Ku dakata haka ya isahhhh!!!!!"
Tafaɗa da ƙarfi a cikin kanta ba'a zahiri ba,dan hakane kaɗai ta koyi control ɗin muryar datake zugata a cikin kanta wani lokacin.
Jin maganar bata daina bane yasa ta ajiye yaron dayake kan cinyar ta a gefe. Zaman dirshan tayi a tsakiyar gadon tareda rufe idonta kana kuma ta dunƙule hannayenta.
Tunani tafarayi tayanda zatayi blocking maganar da akeyi mata.
"Kudaina damuna kuna takurawa rayuwata,nasan turoku akayi domin ku fitar dani daga garinnan,saboda naje nayi mata gargaɗi koh,hmmm ashe dai tana tsorona. Babu wanda ya isa fitar dani daga cikin garinnan har saidai idan nice nayi niyyar tafiyah"
Bombee tafaɗa cikin kanta cikeda taurin zuciya,wata ƴar dariyah ce ta jiyarci kunnanta mai kamada munafurci.
""""Haaaar idaaan muka cuutarr da wannnanan.....yyyyaaaarooonn maa baaazaaaki tafiiiibaahhhhh hhhhhhhhhhhh""""
Aka ƙarisa maganar cikin dariyar mugunta.
Saurin buɗe ido Bombee tayi tareda saukeshi akan ɗannata farincikin rayuwarta.
Aikuwa taga alama,dan lokaci guda ya callara ƙara tareda saka kuka a zabure.
"Ahah kubari kada ku tabashi zan tafi,amma fah sai gobe ba yanzu ba,dan yanzu dare yayi"
Haɗiye yawun baƙinciki tayi tareda cigaba da jijjigen ɗannata,dan kana gani kasan batayi niyyar tsayawa da wasan ba,saidan ya hau kan rayuwar ɗantane,ta yarda komai suyi mata akan su tabashi.
"Matsorata kawai,mai yin barazana da wani abun ma yana tsorone"
Bombee tafaɗa a hankali kan fatar bakinta.

Washagari da sassafe Bombee ta shiryah ita da yaronta suka kama hnayar barin garin gembu cikin motarta,saboda ko badan itaba tana tsoron rayuwar ɗan ta,yanzu babu abinda yake cikin ranta sai muradin rabashi daga cikin garin,saboda tasan sun riga sunsan shine masomin karya lagonta a yanzu.

Lubnah ce a kwance akan gadon ta na gidansu tana danne danne a waya, hankalin ta yayi nisa wajen hirar dasuke da ƙwayenta. Ƙara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinne yasaka jan tsaki tareda kawar da dogayen kitson attach ɗin take kanta,kana ta juyo ta kallo ƙofar.
"Miye kuma,ba yanzu kika sharw ɗakin kika fita ba?"
"Ahah hajiya ba wannan bane,wata mai aikice ta zo nemanki daga Gidan mijinki"
Saurin tashi tayi ta zauna tareda fitowa wajen,dan tasan bazata wuce Bishirah ba,dan dama kafin tahowarta jiya tasaka ta kawo mata rohoton duk abinda yafaru a gidan.
Aikuwa ita ɗince tana zaune a ƙasan carpet ɗin falon,tasaka hannunta tana wasa da zare zaren carpet ɗin.
Muryar Lubnah ce tasakata saurin ɗagowa tareda gyara zamanta kaman mai shirin karbar gafara.
"Yaya mai ya faru bayan tahowata daga gidan"
Lubnah tafaɗa bayan ta zauna akan kujerar dake gefenta,cikeda zumuɗin son jin abinda ya faru.
Bishirah bata kai ga magana ba wata dattijuwar mata tashigo falon,tadan manyanta,Barr Na'imah Hashim kenan,mahaifiyar Lubnah.
(Sorry a baya nace mahaifinta ne brr amma mahaifiyar ta ce,shi mahaifinta General ne babba a barikin sojoji Gen Abdu Manga)
Duk da ta manyanta,amma kanaganinta zaka san cewa anyi boko harda bokoko ma. Itama zama tayi a kujerar dake facing ɗinsu,laptop ɗin dake gefenta ta dauka ta ajiye a kan cinyarta,tareda gyara ɗan karamin glass ɗin dake idonta.
"Wannna kuma wacece Daughter?"
"Uhm mommy wacce nasaka ta dunga kaomin rahoton abinda yake faruwa ce,yanzu tazomin inaga da wani labari ne,ke ina jinki mai ya faru bayan na taho?"
Gyara zama Bishirah tayi jin an bata lasisin yin magana.
"Ai wato hajiya dazu naji wani zance wai an gyara anihin sabon part ɗin yallabai na gidan,a can wai amarya zata zauna,har yau ma'aikatanta sunje sun ƙawata part ɗin yadda take buƙatarsa. Sannan wai tunda wacce Hajiya ta taho da ita ba amaryar bace,amaryar bata zo ba sai gobe zata iso tukunna,kuma naji ance hajiya ma shakkarta take,yanda takeyin nan nan da yaran da suka zo dasu"
Zaro ido Lubnah tayi lokacin da mummunan labarin ya doshi kunnnenta,sabon part??? Ita bata koma part ɗin ba tsawo zamanta gidan sai wata kucaka data zo yanxu itace zata buɗe wajen?
Lubnah ta faɗa a ranta cikeda takaici.
Tashi kije zan biyaki idan na dawo,yanzu banida kuɗi a hannuna.
Tashi Bishirah tayi ta rawar jiki tabar gidan bayan tayi musu sallama.
Lubnah kaman jira take,tana ganin tafita tasaka kukan sakarci.
"Ahahahha mommy kingani koh,Allah zan kashe wannan uwar tasa daga ita har wacce ta aura masan,nagaji da kaicinsu danake sha gaskiya"
Hmmm karma ki soma,saboda bakida hankali kina ganin in wata matar tasa ta mutu baza'a zargeki ba ne,meyasa mahaifiyar sa bata aura masa Wannan yarinyar ba(Jawaheer),sai suka aura masa wata can daga wani gari,wacce bata san mai yake faruwa ba,saboda suna so itama ki kasheta ne,wanda baya zarginki ma daga lokacin yafara idan yaga mata uku sun mutu a jere. Kinga lokacin dazasu ɗaureki da igiyar da bazaki iya kuncewa ba,sai su aura masa ita suyi zaman ƙalau an kawar dake,dama suke shayi zan tsayamiki a shari'ah,amma daga lokacin da kika kashe wannan da kuma uwar mijinki to fah abin nima zaimin wuyah. Sauyah salon zamanki dasu zakiyi yanzu,karki kashe kowa,yanzu kiyi amfani da kissa bayan zulungum ma,ki tafiyar da abu tayanda babu mao zarginki,sannan idan sukaga baki kashe wannan ba,to zasuyi ƙoƙarin Jawaheer ma,wanda nasan kinfi tsanarta,a nanne zaki tafiyar da ita a boye batareda kowa ya sani ba,ke daka Kashe mutun shikenan gwanda ka haɗashi da abinda sai ya ƙwammaci ya mutu ma"
"Eh kuma fah hakan mommy to yanzu yakike ganin zanyi kenan"
"Keba mace bace,bakisan yanda zakiyi komai sai kisa kawai,saboda matsoraciya ce ke,bakya tunkarar abu saidai kaimasa hari ta baya,halin ubanki ne sakk dake"
Lubnah taji haushin maganar mommyn tata,amma kuma tasan gaskiya ta faɗa,ita bata jurar bin abu a hankali,takanyi duk abinda zuciyarta ta raya mata ne.
"Toh.... Toh...kinaga fah nadawo gidannan ma har yanzu bai zo nemana ba,taya zan koma kenan?"
"Haka dai zaki ƙare,nace miki komai yafaru ki zauna a gidanki kiga mai akeyi,sannan ki kasa ki tsare amma kinki ji,saiki dawomin kina min kukan sakalci waike kin gaji,kinada kafafu biyu ai kiyi amfani dasu mana ki koma"
"Toh mommy yakike so nayi,aure fah wai ya ƙara,kuma nace yasaketa yaƙi sakinta,idan nayi masa magana bayajin maganata,kaman yanda abbah yake jin taki,narasa yanda zanyi dashi,sainayi da gaske wani lokacin nake samun kansa,gashi inasonsa banison wata a kusada shi,kiji wani sabon tsirin wai a sabon part zata zauna"
"Ke ma saiki koma gobe da wuri ko rigata komawa,ko wanda tazaba kikeso dole tafita kishiga tunda kece babba a gidan,yanzu kiyi shiri ki koma gobe da safe,da badan akwai abinda nakeson haɗamiki ba,da a darennan ma zaki koma"
"Yawwa mommy,zaki kaini wajen bokanyarki,ni wancan zulungum ɗin yanzu bani sonsa sosai"
"Ahah ni kaɗai zanje bazaki bini ba,har yanzu bakiyi wanann girman ba na ganinta,sannan kinsan kafin ki yakice zulungum a jikinki zaki daɗe,tunda yasan yana samu daga gareki,kuma karki damu shima aikinsa yana ci sosai,kece ma zaki bawa wasu labari"
"Ni naso yazo dakansa ya ɗaukeni,baya wai na koma dakaina ba,bari zan ƙira Yaseerah tazo mu tafi tare da safen,kutt harma wani ta zabi part banida masaniya"
"Hmmm dama ki tsayah kallon ruwa,shidama kwaɗo ai ƙafa zayyi miki"
Barr Na'imah tafaɗa tareda cigaba da abinda take a labtop ɗin gabanta.

Har Hilyaan tafara bacci da daddare taga ƙiran Bombee,dagawa tayi tareda yimata sallama.
"Hello inace dai lafiyah,ko haidar ne ya hanaki yin bacci kai?"
"Ina cikin abuja yanzu haka,na sauƙane a hotel,da safe zan shigo gidan,dan haka kituro min address ɗin zanyi installing ɗinsa a kan Motata zuwa safe"
Tashi Hilyaan tayi ta zauna cikeda mamaki tace.
"Abuja kuma,meyasa kika taho yau ina sai gobene zaki dawo"
"Menene kuma na razanar shin ban isa sanja ra'ayi bane saikin tuhumeni iyee,ko akwai abinda baku gama bane kike tsoro"
"Ahah mun gama komai,mun zabamiki part ɗin dayake gefen lambun wajen,ta ƙofar baya zaki shiga,sannan yanada girma daidai gwargwado,mun shuka wasu fulawoyi ma wanda bazasuyi wata biyu ba zasu girma,amma dan Allah meyasa kika taho yau,ko kin matsu kai kiga angonnaki ne?"
"Hilyaan zan.......kidaina shiga hnacina fah da zancen rijalun ɗincan tamm,batun dawowata basai kinjiba daliline boyayye,wai hadda fulawa kaman nace muku ina buƙata?"
"Kai anty maryam nifa dama nasan zaki ce haka,amma ki bari saikin gani da idonki,ina tsoron shiga fah Bad side ɗinki,anyi komai yanda ya dace. Matar tasa ma naji ance wai batanan tunda taji zancen ƙarin aurensa"
"Tafiya kuma,batasonsa ne ta tafi tabarshi,ko kuma taji tsoro? Ashe ma ƙaramar ƴar isaka ce"
"Amma nikuma nafi zaton ko tafiya tayi tasake shiryowa zama dake,tunda ance bata ragawa kishiyoyinta"
"Hmmm ba shiryawa ba intanaso ta ɗauko mai yimata aikin ma su dawo gidan,hakan bai shafeni ba,tun bansan kaina ba ake bankamin,dan haka an shanin na warke,ki bari ina shigowa cikin gidan da safe"

To matan fah zasu shigo a tare kenan,ku jirayi na gaba domin haɗuwarsu a bakin ƙofar jaan estate.😂😂😂




_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK 2_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]




Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31


Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________





Page 🖤5••6🖤





"Wai luby lafiyah kika tasoni da safennan wai zaki koma gidannan,haba bansanki da wannan,wannan ba girmanki bane mana big elegant woman"
"Kimin shuru Yaseerah eh haka naga dama,komawa zanyi,dama ai bashi ya koreni ba nice dakaina na taho"
"Kutt wannan yajin fah ko sati bakiyi ba shine zaki koma,naga wani lokacin har wata kinayi a gida,ko kai dagaske dan kina tsoron wannan matar ne kada ta mallakemiki miji"
"Kaii wai Yaseerah da wanne zanji ne,dake koda mijina,ko kuma da mommy tada koroni iye,koma mai zai faru kekam ki zuba ido mana kigani,inda tani ce da tuni na kasheta tun kafin ta shigo cikin gidana"
"To meyasa kika fasa hakan"
"Mommy ce ta hanani mana,a cewarta sunyi hakanne domin na kasheta su sakani cikin tarko,idan inaso na kawar da ita saidai na yi amfani da kissa da kuma aiki a boye,wanda ba kowa zai kulada abinda na aikata ba,kaman haɗata da wani ciwo,saka mata wari ko kuma saka wa Jabeer tsanarta,ke yanda nakeji ma koda ban kasheta da asiri ba zan yi hayar ƴan fashi wanda zasu shigo suyimin daga daga da ita....."
Tana maganar ne numfashinta yana cikowa saboda tarin baƙin ciki da tsanar amaryar mijinnata da take cinta.
"Kinga ki kwantar da hankalinki haka mana luby,batun kawar da ita wannan dolene,tunda har tayi nasarar shiga rayuwarki,bazamu taba barta ba,yanzu dai mu shiga gidan muga sabon part ɗin daza'a kaita,nasan wannan tsohuwartata ce tayi hakan saboda tana tsoron abinda zakiyi mata."
"Nasan dama shine dalilin,sannan a cikin wajen a kwai part din dayafi girma,yaɗan shiga cikin lambun gidan,sannan yana ɗan nesa da sauran parts ɗin,kaman anyishine domin babbar matar dazata zauna a wajen,wanda nce kenan mamallakiyarsa"
"To yanzu idan mukaje kuma taɗauki wannan part ɗin fah,ya zamuyi mata kenan"
"Hhhhh har tambaya kike ma mai zanyi mata,kaff gidannan banga mai sakani barta ta zauna a wannan wajen ba,da banyi niyyar zama a wajen ba,amma tunda naga tace anan amaryarsa zata zauna,nima a can zan zauna,kuma wannan part ɗin nakeso"
Ƙarisa maganar tayi cikeda shirin abinda zata aiwatar idan ta shiga cikin gidan.

Daidai isowarta ƙofar gidan,wanda take da tabbacin shine gidan da take nema,saboda nan Gps ɗin motarta ya nuna.
Kashe ƙarar motarta tayi tana kallon get na shiga estate ɗin. Ko ba'a faɗawa mutum ba daga ganin mashigar zai tabbatar da cewa wajene babba kuma ƙawatacce sosai.
Ƙara horn ɗin da ake mata da motane yasaka ta ɗauke kanta daga kallon mashigar ta maidashi kan motar dake gabanta.
Farar mota ce mai kyau tashiga taro ta faso kai ta shigo wajen,har Bombee tayi niyyar jan motarta baya domin bata damar shigewa,saikuma taji ana ta jera horn akallah kusan biyar,tun ma kafin ta motsa motar tata.
Komawa tayi ta zauna shuru ta zubawa motar gabannata ido,batareda tasake motsawa ba,jira take taga wanne shafaffe da mai ne yake tunanin zata yimasa abinda yake so ta ƙarfi.
Bayan kaman a ƙalla minti biyar,wanda zuwa sannan lubna tayi horn yafi sau a ƙirga,jan tsuka tayi tareda bugar sitiyarin motar da hannunta,idanuwanta har sunyi ja dan baƙinciki.
"Wai wannne ɗan***** ya taremin hanyar shiga ne,waye mai kuma yake taƙama dashi"
"Inaga saidai ɗan gidann mana,abin da rainin hankali kam a ciki,amma bari naje na duba"
"Ahah yi zamanki basai kinje ba,daga gani baɗan gidan bane,domin bansan mai irin ƙirar motar nan ba"
"Ahh a yanda suke kam ko jiya zasu iya order sabuwar mota,kokuma Abdulkareem ne kai ya dawo?"
"Ba Abdulkareem ba inma Abdullahi ne dakansa bazan ɗauki wannan rashin mutuncin ba,yaushe har lagona ya karye suke wannan wasan dani"
A zuciye lubna tafito daga motarta ta tunkari inda Bombee take zaune a cikin tata motar."
Kwantar da sit ɗin drivern tayi tareda yin miƙa,lokacin da taga lubna ta tunkaro inda take,dama jira take daga wanene a cikin motar da har zai mata waɗannan horn ɗin kaman ya samu dabba akan hanya.
"Ohh dama kece mai yimin horn ɗin mrs Jabeer? Banyi tsammanin haɗuwar mu yanzu ba,wow very interesting and nice meet"
Bombee tafaɗa cikeda nishaɗi kana ta karisa maganar da hamma.
Ƙwanƙwasa glass ɗin kusada ita taji lubna tayi,nan ma saida tayi shan ƙamshi na ɗan wani lokacin kafin kafin ta sauƙe glass na motar.
In ana magana takaici ranar Lubnah ta shaƙa,da taga macece ma cikin motar,kuma dan iya shege a kwance ma take batada niyyar tada motar,wato ƙalau motar ma take da gangan taƙi tayar da ita ta matsa mata.
"Wacece keee!?"
Lubnah ta faɗa tanayiwa Bombee kallon ƙasa da sama,wacce idon yake rufe kaman bada ita take ba,inda bata buɗe mata glass ba sai tayi tsammanin bacci take,ji take kaman ta saka hannuwanta ta cakumo wuyanta tacikin motar.
"Mai kike taƙama dashi da har ina miki magana kina ji iyee,waye ubanki cikin garinnan,koma menene alaƙarki da gidannan bai dameni ba,amma ki sani ko ƴan gidan nafi ƙarfin su rainamin hankali ballantana kuma keh"
A kasalance Bombee ta buɗe idonta tajuyo ta kalli Lubnah,a yanayin data juyo cikeda jan magana,sai ya ƙara fito da ainihin Kyawunta.
Gaban Lubnah ne ya buga datayi arba da fuskarta,sai taga kaman ta taba ganin mai kama da ita,amma ina ga kamace,ta faɗa a ranta.
"Ku mutane kunada damuwa,dole saini ƴar wanice kafin zanyi abinda naga dama,akwai wanda aka hanashi motsi yanda yake sone,to meyasa sai ƴan wanene zasuyi yanda sukeso,sha kuruminki ni ba ƴar kowa bace,amma tunda kikayimin horn fiyeda ɗaya kafin na matsamiki,to a lokacin na yanke hukuncin sai kinyi minti talatin kina tsaye kafin ki shiga gidannan,in kinga na matsa a wajennan to lokacin dana yanka ne ya cika,ko kuma mota mai haƙora kika ɗauko ta dauƙe motata,amma idan biyunnan wani bai faruba,tsayuwar banza kikeyi a wajenann,dan abinda kike bazai sakani sanja ra'ayina ba,gwanda ma ki koma motarki ki zauna"
Bombee tana kaiwa nan ta bayaninta ta maida glass ɗin motarta ta rufe.
Wata jijjiga Lubnah tayi,tama rasa mai yake mata daɗi,wai wannan yarinyar ce take mata magana haka,tukunna ma wajen wa tazo a cikin estate ɗin,yanayinta ne yasa tayi tunanin wataƙila baƙuwar Lylah ce,sai kuma wata zuciyar tace ta ƙira securtyn gidan.
Allah sarki bawan Allah,chiep securityn yana ɗagawa lubna tafara balbaleshi da masifah,ta inda take shiga bata nan take fitaba.
"Uban me kukeyi,menene ma aikinku a gidannan,maza kazo da kanka ka gani,wata banza ta hanani shigowa ciki,da saka motarta a bakin ƙofa,kuzo kuyimin waje da ita"
"Ranki ya daɗe kiyi haƙuri bari muduba CCTV camera,inaga kuma wajen wani tazo a cikin gidan,kada muyi mata magana yazama matsala"
"Matsala... Ina ruwana da wajen wa taxo tunda ta nuna min ta isa dan tasamu shiga wajennan sai tasan matsayinta yanzunnan,ku zaba shin fitar da ita daga baƙin ƙofar nan ko kuma Aikinku?"
Ai tun kafin Lubnah tasake cewa wani abun yayi saurin cewa.
"Aikina na ɗauka Hajiya,gani nan zuwa dakaina yanzunnan basai anjima ba"
Kashe wayar tayi tana jiran isowar tasu kaman yanda suka faɗa.
Yaseerah ce ta fito itama daga motar tazo inda lubna ke tsaye tana jijjiga kaman an jona mata wutar lantarki.
"Ƙawass mai yafarune,waye a cikin motar ko baci tayi?"
Duk maganar datake Lubnah bata kulata ba,har sannan tana sama,ƙarar fitowar motar securityn ta jiyo,saidai suma bayadda zasuyi su fito,dan Bombee ta tare hanyar fitowar daga waje.
Sagern Hudu ne ya fito daga motar,wanda shine shugaban security na estate ɗin gaba dayah,wajen motar Bombee ya nufah tareda ƙwanƙwasa mata ƙofah.
Zugewa tayi tareda haɗe fuska tace,
"Wai menene kuka dameni,idan kukayi haƙuri ma minti talatin na cika zan matsar da motata,basai kun takurawa rayuwata ba"
Kallon mamaki ya bita dashi tareda cewa.
"Kee wacece ke,shin tukunna ma mai kikazoyi gidanann,danni ban taba ganin mai kamarki ba a wajennan"
"Kai kai wai duk gidannan haka kuke ne,kowa inzai buɗi baki wacece ke,dole saini watace zanyi haka,kenan ban isa ɗaukar mataki ba idan akayimin wani abun?"
Tsawa Lubnah ta dakawa sagern hudu daga inda take tsaye,
"Lallabata ma kakeyi,yanzunnan kuyi waje da itah,ko tsoronta kukeji kai"
Sagern hudu yanajin maganar Lubnah ya ƙara ƙaimi tareda ficcina ƙananun idanunsu.
"Kinga madam koma me kike takama dashi ki fito daga motar nan yanzunnan,a matsar da motar"
"A kuda kuke so na matsar da mota meyasa kuma zan fito?"
"Ahhh wannan kuma madam daga baya kenan,dole zaki fito ki faɗamana menene dalilinki na zuwa nan wajen"
Shuru Bombee tayi bata bashi amsa ba,daidai lokacin da ta ƙayyade suna cika taga hannun sagern hudu yana shirin cakumo kirjinta,cikin zafin hannu ta riƙe a hannunsa tareda yimasa kallo mai ɗauke da alamar tambaya.
Idonsa tagani yana kallon kan ƙirjinta,tashi daya ta gane ba iyah niyyar fitowa yake da ita daga motar ba,harda wani mungun nufinnasa ma.
Yatsun hannunsa guda biyu na ƙarshe ta rike ta malƙwasa,nan da nan yabada ƙarar ƙass ta ƙaryasu.
Ƙarar azaba ya saka tareda fizge hannunsa yaja gefe yana kallonta cikeda mamakin karfin dayaji ta saka masa.
Key tayiwa motar ta bata diri,hanyar get ɗin ta nufah inda sauran securityn suke tsaye,nufarsu tayi da niyyar bi takansu ta shiga gidan.
Da farko basuyi tunanin zata cigaba da tafiya ba duk da sun tsayah....amma ganin tsakaninsu baifi taki ɗaya ba,kuma bata da niyyar tsayawa yasaka su bajewa da gudu,ɗaya kam har yatsansa t taka na ƙafah.
Tsalle yafara ya ihu tareda bin motar tata da kallo,wanda har ta bace a cikin gidan.
Saida ta ƙule tukunna sagern hudu ya juyar da kallonsa ga Lubnah,wacce itama tatsayah tana kallon abinda Bombee tayi.
Hannunsa yasake ɗunlewa tareda cewa.
"Hajiya kiyi haƙuri bari mushiga cikin muga wajen wa tazo,karki damu yanzu zamu koreta"
Bai tsaya jin abinda zatace ba yashiga motarsu suka shiga cikim gidan.
Itama Lubnah ganin cizon yatsa bazai kaita ya sakata shiga tata motar itada yaseerah suka bi bayansu.
A bangaren Bombee kuwa hankali kwance take tafiyah akan titin dake cikin estate din,har ta isa ga bakin part ɗin su Hajiya zeenah,dan shine a farko daga an shigo da kuma na su Lylah daga ciki kaɗan.
Parking motarta tayi a wajen da taga wasu motoci,wayarta tafitar tareda dannna sunan Hilyaan.
Ringing biyu da daga tareda yimata sallama daga ɗaya bangaren.
"Kinga babu bata lokaci sonake na kwantar da yaronnan,ya gaji da kwanciyar mota ga bayanin daɗi,ki fito ki nunamin part ɗin dazan zauna,ko kimin kwantance idan wani abu kike,zan wuce daga nan"
"Lahh anty maryam harkin shigo wai,kina ina kenan a cikin gidan?"
"Uhmm ina bakin wani part wanda shine na farko idan aka shigo ciki"
"Ohh part ɗin Hajiya zeenah kenan,muna ciki ai barina sanar mata da isowarki,mijinnaki ma yana wajenta yanzu ya shigo gaishe da ita"
"Kinga ni Hilyaan bana son wannan maganganun wanda naga kin koya tun zuwanki wajennan,inma wani abun suka baki kika sauya ni bai dameni ba,kawai ki fito ki nunamin masauƙina inason na huta,badan hotel ɗin dana sauka ana event a wajen ba maizai fitar dani da safennan kamar na ciwa wani bashi?"
"Sorry sorry Ogah ganinan fitowa yanzu nan karki damu"
Bayan kashe wayar Bombee a ƙalla tayi tsuka sunfi uku,ƙarar motoci taji sun faka a kusada ita,sa alama mutanen ta ne na bakin get suka iso.
Tana kallonsu dukkansu suka fito daga motar,shikam sagern hudu har sharce yake,saboda azabar data haushi na gurɗiyar yatsunsa guda biyu.
Fitowa itama tayi daga cikin motar tana kallon Lubnah wacce take tsaye tana zabga mata harara kaman zata cinyeta da ido.
"Ohh wato ke baƙuwar matar nan ce,no wonder kikejin haushina duk da bansanki ba mana"
Lubnah tafaɗa tareda yin murmushin gefen baki .
"Amma kaman banice dajin haushinki ba,ina fah kece kika dau da zafi daga farko,kuma har yanzu ma kinanan dajin haushinnawa,shin bakya ganin kallon da idanuwanki suke yiminne madam luban,ko aikamin kallon suke batareda izininki ba kai........ohhh kuma akan kawai na hanaki shigowa ciki sai lokacin dana shata sun cika,abin burgewar kuma saida suka cika kika shigo ɗin,common ƙaramar dokata kin kasa karyawa inaga babba kuma.......chchchchchc am feel sorry for you"
Bombee tafaɗa cikeda sigar zolayah,harda wani cuna baki kaman na kifi,hakan datayi ne lokacin ɗaya mutum zai dauka innocent ce.
"Sannunki da isowa"
Hilyaan tafaɗa fuskarta ɗauke da fara'a lokacin da suka iso wajen da take itada khamees.
Daga kai Bombee tayi wa Hilyaan kafin ta kalli khamees cikin kame fuska,kaman ba ita ke zolayar Lubnah yanzu ba.
"Barka da isowa yakk ya hanya"
Khamees ya faɗa cikin girmamawa,murmushi Bombee tayi masa tareda cewa.
"Hanya normal ne kasan dawar,ykk hope komai ya tafi normal koh?"
"Yeah komai kalau,amma nayi mamakin isowarki da safe haka"
Wani rolling manyan idanuwanta tayi,wanda hakan yasake bawa ƙwayar idanuwant show up,kafin tace.
"Jiya na shigo garin,so na tsayane a hotel badan hayaniyar dasuke yahanani sakewa ba,da bazan shigo yanzu na sai yamma"
Hajiya zeenah ce dake tsaye tayi magana cikin dan ɗaga murya yanda kowa zaijita a wajen,harda su Bombee da suke magana itada mutanenta.
"Toh amaryarce ta shigo da wuri haka,hala a gari kika kwana amma?"
Tsayawa tayi da maganar da suke da khamees ta ƙarisa inda Hajiya zeenah ke tsaye itada su Madeenah,harda

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

3 Comments On BAƘAR AYAH BOOK 2
avatar
ummi-ummi

1 year ago

Reply

My Allah bless you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ummi-ummi

Ameen

avatar
ummi-ummi

1 year ago

Reply

Ayya next of chapter 4 pls

Please Login or Register in order to submit comment