You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
shurais abubuwanda ya samo a wannan karon
Bayan sun iso tsakiyar fada ne dakaru suka jera tarin akwatunan da aka zubo dukiya acikinsu
Wadanda babu komai aciki face zallan duwatsun lu'u lu'u da zinare na fitar hankali Ana tare su guri daya
Suna cikin wannan aiki ne kwatsam sai ga boka Zulhas ya bayyana fuskarsa cike da fara'a
Bayyanarsa keda wuya take duk wasu kofofi da tagogi na wannan fadar suka kulle kansu ruf ta yadda inbanda iska babu abinda zai iya fita ta cikinsu
Cikin mamaki sarki shurais yace ya kai zulhas menene ya kawo ka a wannan lokaci
Dajin wannan tambaya sai boka zulhas ya tuntsure da dariya daga can kuma yace
Ya shugabana hakika abinda kake nema a halin yanzu yana cikin wannan fadar taka
Ma'ana yarinya lasmira wacce zata zama Hanyar mallakar Karagar ajali a gareka
Ina mai rantsuwa da allon sihiri na cewa a halin yanzu tana cikin wannan fadar taka ba zata taba kubuta daga garemu ba a wannan karon
Domin da zarar nayi arba da ita ako. Wacce irin siffa ta kasance
Nantake ainihin siffarta zata bayyana a gareni
Koda jin wannan batu take sarki shuras ya tuntsure da dariyar farinciki sannan ya umarci boka zulhas daya nemo ta da kansa
Nan take ba tareda bata lokaci ba boka zulhas ya zaro wani sandan tsafinsa daga jikin kugunsa
Ya fara bi takan dakarun hubair yana nuna su da wannan sandar
Saidai duk wanda ya nuna da wannan sandar tasa sai kaga take sandar ta rikide daga launinta zuwa koren launi
Ita kuwa lasmira tuni hankalinta ya kara tashi fiye da ko yaushe ta fara kokarin neman hanyar kubuta
Domin duk taji abindasu boka zulhas da sarki shurais suka. Tattauna kuma ta tabbatar da cewa duk abubuwan da suke faruwa na binciken data tarar anayi abaya duk anayi saboda ita
Don haka cikin matukar razana ta fara tunanin hanyar da zatabi domin kubutar da rayuwar ta acikin zuciyarta
Bata san sanda ta fara zancen zuci ba wata zuciyar tace da ita kawai ta tashi ta gudu kafin bincike yazo kanta wata kila ta samu ta kubuta
Ai. Kuwa har ta juya da nufin yin gudun sai taga duk wata kofa da zata bi ta fita a rufe take
Wata zuciyar kuma tace mata akul dinki karki kuskura ki aikata wannan kuskuren domin ba zaki taba tsira ba
Abinda zaifi miki. Sauki kawai shine ki bayyana kanki a garesu sannan kiyi musu bayanin matsalar mahaifinki wata kila su tausayawa halinda kike ciki
Aikuwa tana gama wannan tunani take ta nufi inda inda boka zulhas yake kai tsaye ba tareda fargabar komai ba
WANNAN SHINE ABIN DAYA FARU GA LASMIRA LOKACIN DATA FADA TARKON MUTUWA HAR TA YANKE HUKUNCIN MIKA WUYA GA SARKI SHURAIM
+++++++ +++++++++ ++++++
Acan duniyar sama cikin Masarautar RUGTARUL BARZAK kuwa Boka HUBBAS ne yau da kansa kamar yadda ya saba aduk karshen karni guda yakanja ragamar duk hadiman aljanun dake duniyar sama zuwa fada ta goma sha biyun da aka ajiye KARAGAR AJALI Tareda SAIFUL LAIHAM domin bauta agaresu
Kuma duk lokacin da sukayi wannan bauta a wannan lokaci boka Hubbas yake sanin duk abubuwan da zasu faru a wannan karni gaba daya
A wannan lokaci fadar taayi tsit bakajin sautin komai acikinta. Face hucin numfashin aljanu
Acan karshen fadar kuwa KARAGAR AJALI ce a ajiye a samanta an rataye SAIFUL LAIHAM
Yayinda wata yanar sihiri ta lullubesu gaba daya wacce akoda yaushe wani tartsatsin wutane yake tashi daga jikin ita wannan yanar
Agaban karagar kuwa Boka Hubbas ne a zaune ya tankwashe kafar sa agaban ita wannan karaga yana mai nazari akanta tareda karanta wadansu dalasiman tsafi acikin zuciyarsa
Abayansa kuwa rukuni ne na jinsin bakaken aljanu da duk wani jinsi na duniya
Yana cikin wannan karatun ne take wani irin gagarumin haske mai matukar karfi ya fito daga jikin KARAGAR AJALI ya shige cikin idanunsa saboda karfin hasken baisan sanda ya runtse idanunsa ba
Ai kuwa nantake yaga gaba daya abubuwanda suke faruwa acikin duniyar kasa
Kamar ka ajiye kwayar gero akan faifai tundaga randa aka haifi su farhan har zuwa girmansu
Da kuma haihuwar Yarinya Lasmira har zuwa yanzu da take kokarin mika kanta ga Sarki shurais
Koda ganin wadannan al'amura take ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce tasa gaba daya duniyar sama ta dinga girgiza gami da tambal tambal ita kanta wannan fadar da suke ciki saidata hautsine
Ragowar aljanun dake tsugunne kuwa a bayansa basu san lokacin da suka zube akan kasa ba kamar zasu nutse a karkashin kasa saboda bala'i
A wannan lokaci a gabaki daya duniyar sama babu abinda bai fita daga hayyacinsa ya kuma motsa daga inda yake ba sakamakon dariyar boka Hubbas
Face Takobin SAIFUL LAIHAM DA KARAGAR AJALI wadanda su ko kwarzane babu abindaya same su
Saida boka Hubbas yayi dariya ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar
Ya juyo bayansa a lokacin da komai yayi tsit kamar mutuwa ta gifta a wannan karon. Ma ko kwakkwaran numfashi. Babu maiyi acikinsu saboda yadda suke matukar biyayya agareshi
Ya tsaya ya kare musu kallo tsawon dakiku kadan daga bisani kuma yayi gyaran murya sannan ya dora da cewa
Yaku hadimai na hakika akwai wani babban abu da yake faruwa acikin duniyar kasa wanda a halin yanzu ku baku san dashi ba
Inaso ku sani ba komai ne yasa kuka ganni ina wannan dariyar ba
Face ganin abinda mai girma KARAGAR AJALI ta sanar dani
Cewa acikin duniyar kasa har akwai masu ganganci da kasadar zuwa nan fadata domin su yakeni sannan su tafi da wadannan ababan dogaron namu
Ababan da muka kasance muna bautar agaresu fiye da dubunnan shekaru
Shin kuna ganin akwai mahalukin da zai iya yakata har ya shigo wannan fadar tawa a a duk cikin duniyoyin da ake dasu tsakanin sama da kasa?
Koda jin wannan tambaya take duk sukayi shiru aka rasa wanda zai bada amsa
Daga nan sai ya cigaba da cewa to ammafa ku sani a wannan lokaci akwai wata yarinya wacce KARAGAR AJALI da kanta take bata kariya
To ahalin yanzu wannan allon kariyar nata yana daf da karyewa ta fada hannun masu yunkurin zuwa wannan fadar tawa domin daukar karagar ajali
Saboda haka a matsayin mu na masu bada kariya ga duk abinda ya shafi KARAGAR AJALI dole ne mu kare duk abinda yake da alaka da ita
Yana gama fadin haka take yayi nuni zuwa ga jikin KARAGAR AJALI
Nantake saiga hoton rayuwar su sadauki farhan gaba daya ta bayyana ajikinta da dukkannin gwagwarmayar da suka sha arayuwarsu
Su kansu da sukaga wannan hoto basu san lokacin da suka fara yi musu dariya ba saboda raini
Sannan a wani gefen kuma saiga hoton Yarinya lasmira bayyana cikin ainihin siffarta
Koda wadannan aljanu sukaga irin kyawun da take dashi take suka rikice suna sambatu kamar zautattu
Har saidaya daka musu tsawa sannan suka dawo cikin hayyacinsu
Yace dasu bana nuna muku wadannan abubuwa bane domin kuyi min shashancin banza ba
Na nuna muku sune domin in baku aiki akansu
Da gama fadin haka sai yayi nuni izuwa wani daga cikinsu yace
Ya kai marganu inaso yanzu yanzu ka tashi ka shiga duniyar kasa ka dauko min lasmira ka kawomin ita kada ka bari wani abu ya taba lafiyarta
Kuma karka kuskura ka bari wani daga cikin wadannan mutanen dana nuna muku ya sami damar guduwa da ita koda kuwa zaka hallakar da gaba daya duniyar kasan , ka tabbata ka dawo nan fadata dauke da lasmira
Dajin wannan batu take Aljani Marganu ya fadi yayi sujjada agareshi cikin kakkausar murya yace angama ya shugabana !!!!!!
Nantake ya bude manyan fukafukansa sannan yayi nutso acan kasan karkashin kasa cikin a zababben gudu domin cika umarnin mai gidansa
Wato sarki a duniyar tsatsuba mai mulkin duniyoyin sama sannan mai bada kariya ga KARAGAR AJALI da SAIFUL LAIHAM
SHIN WANNE HUKUNCI SARKI SHURAIS ZAI DAUKA AKAN LASMIRA IDAN TA MIKA KANTA GARESHI?
WANENE ZAI MALLAKETA TSAKANIN SARKI SHURAIS DA BOKANSA ZULHAS?
INA LABARIN SU SADAUKI FARHAN DA SARAUNIYA NAUWARATUL HASNAL DA KUMA SADAUKI MUFRAN DA SAFRAN?
YAUSHE NE GIMBIYA HUSNAILA ZATA ISO BIRNIN MISRA?
SHIN ALJANI MARGANU YANA SAMUN DAMAR DAUKE LASMIRA YA MIKATA ZUWA GA UBAN GIDANSA WATO MAI CIKAKKEN IKO BOKA HUBBAS?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A LITTAFI. NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR
09133502477
LIKE ,COMMENTS AND SHARE
+++++++++++KARAGAR AJALI 9
++++++++++PART A
LBR
+++++++++HABIBULLAH KBR
TYPING
+++++++HABIBULLAH KBR
lokacin da yarinya lasmira ta kusanci boka Zulhas cike da kwarin gwuiwa tana zuwa gabansa sai ta rissina agabansa tana mai cewa
Yakai wannan boka idan har wani laifi na aikata agareka ko kuma iyayena suka yi maka wanda ya janyo sanadiyar barinsu daga cikin al'umma ina mai nema mana gafara agareka karka wahalar da kanka nice yarinyar da kake nema
Tana gama fadin haka saita runtse idanunta kwalla na zuba daga cikinsu tana jiran hukuncin da zai yanke akanta
Koda ta shafe wasu dakiku taga baiyi mata wani abu ba sai ta bude idanunta
Kawai sai taga ko kallon inda take baiyi ba yaci gaba da bincikar mutanen dake gabanta ba taredaya kula ba
Don haka sai ta wuce inda sarki gulbas yake domin tayi masa bayani da kanta
Azatonta boka zulhas bai yarda da ita bane koda tazo daf da sarki Shurais take sai kafafunta suka harde ta tafi gadan gadan zata fada kansa
Nantake ta kwallara ihu saboda tsananin razana
Bisa mamaki koda ta fada kansa sai taga ta ratsashi ta wuce kamar yadda haske yake ratsa gilashi ta fadi kasa ba tareda yaji ko kwarzane ajikinsa ba
Kuma shima a sannan ko. Inda take baisa idonsa ya kalla ba
Wannan al'amari sai ya kara daure mata kai fiye da koyaushe har ta kara mika hannu a karo na biyu don ta taba jikin sarki Shurais sai taga hannun nata ya kara ratsa jikinsa ya wuce a karo na biyu ba tareda yako juyo inda take ba
Sai a wannan karon ta gane dalilin daya sanya tunda ta baro gida babu wanda ya binciketa
Domin duk kansu sun zama makafi agareta idanuwansu basa iya ganinta ko taba ta harda shi kansa boka zulhas dukda cewa tsafinsa ya tabbatar masa cewa tana cikin masarautar
Saboda ganin haka bata san lokacin da farinciki ya kamata ba
Har wata 'yar karamar dariya ta kwace mata amma. Data tuna lokacin data bata wajen aikin buya na Tsawon rayuwarta sai taji bakin ciki ya turnuke ta kamar ta fashe da kuka
Daga bisani kuma sai abin ya fara bata mamaki ta tambayi kanta tace shin menene yasa ita take iya ganinsu amma su basa iya ganinta?
Amsar tambayar data kasa baiwa kanta kenan daga karshe ta yanke hukuncin zama bai kamata ba kawai ta fice daga wannan masarauta ta tafi aikin dake gabanta
Tana gama wannan tunani kawai saita kama wuce ta gaban boka zulhas ta nufi kofar fita daga gidan sarautar duk da tasan bata da karfin da zata iya bude ta
Amma ba zata tabbatar da hakan ba dole sai ta gwada tunda masu iya magana suna cewa sai an. Gwada ake sanin na kwarai
Don haka sai taci gaba da tunkarar wannan katuwar kofar da aka rufe gidan sarautar wacce aka sana'anta ta da zallan bakin karfe mai matukar kauri da kuma tsawo
Wanda saboda girman ta sai dakaru sama da dari sun hadu sannan suke iya budeta ko kuma rufe wa
Da zuwan ta bakin wannan kofa sai takai hannunta kai tsaye da nufin dafata
Nantake taga hannun nata ya ratsa ta cikin wannan kofar , koda ganin haka ba tareda bata lokaci ba kuwa sai ta dannan kanta gaba daya cikin wannan kofar
Yin hakan keda wuya sai ganinta tayi ta bayyana a wajen wannan fadar
Shi kuwa boka zulhas har yanzu yana cikin wannan fadar yana ci gaba da binciken da yakeyi ba tareda sanin cewa wacce yake bincike akanta ba har ta fice gaba daya
Lasmira bata tsaya bata lokaci ba ta nufi hanyar da suka baro cikin gari
A amma a wannan karon sai gaba daya taca tafiyar da take taki sauri kamar an ninninka tazarar tafiyar da sukayi abaya kafin suzo gidan sarautar
Ba komai ne yasa take ganin nisan tafiyar ba face a lokacin da take cikin ayarin sarkin kasuwa Hubair ya kasance yana amfani da sihirin tsafinsa a wannan karon domin gajarce musu nisan tafiyar dake tsakaninsu
Saboda haka kafin ta bar iyakar gidan sarautar har yamma tayi
Adaidai lokacin data isa gidan sarautar ne rana ta fadi tana isa kasuwa ta tarar gaba daya an dade tashi babu mutum ko guda daya face face masu gadi
Da karnukan dake zagaye kasuwar na masu gadi , haka ta gama zagaye kasuwar bata sami wani mutum guda wanda ya kasa hajarsa
Don haka bisa dole ta sami guri ta kwanta zuwa wayewar gari
Kwanciyar ta keda wuya kuwa sai barci mai nauyi ya dauke ta
Ta gabanta masu gadin kasuwa suka dinga shawagi amma babu mai ganinta
Sai bayan duhun dare ya rabane tana tsaka da wannan barci nata kawai tayi wani mummunan mafarki wanda yayi matukar razana ta kasancewar wannan ne karon farko a rayuwarta data taba yin mummunan mafarki kamar wannan
Bakomai ta gani a cikin wannan mafarki nata ba face ta tsinci kanta acikin wani mummunan daji mai matukar bantsoro
Tana tsala gudu acikinsa domin ceton ranta inda abayan ta kuwa tawagace ta manyan sarakuna suna biye da ita
Sunata yakar junansu jini yana fallatsi akan kasa
Kowanne daga cikinsu burinsa kawai shine yaga ya kamata a raye da karfin tsiya
Ita kuwa ta ci Gaba da gudun da takeyi tareda ta tsaya ba
Tana cikin gudun ne kwatsam taga kasa ta tsage wani wawakeken rami a bayyana a samanta sannan ta fada cikinsa tana mai rafka kururuwa alokacin da shi kuma ramin ya rufe kansa
Koda tazo daidai nan a wannan barcin nata bata san lokacin data farka daga wannan mummunan mafarki tana rafka ihu da kururuwa
Tunda ta farka daga wannan barci bata sake komawa ba saboda fargaba
Sai ya zamana juyi kawai takeyi a inda take zaune tare da tunanin halinda mahaifinta yake ciki data baro shi cikin matsanancin ciwo ga kuma yunwar da take damunsa wacce ita kadai zata iya yi masa lahani ko kuma ta janyo a sarar rayuwarsa gaba daya idan har bai sami abinci ba
Tana cikin wannan tunani ne kawai ta hango wani farin ingarman doki ya nufo inda take
Kafafuwansa na tafiya a saman iska agadon bayansa yana dauke da akushi mai dauke da abinci da kuma wata karamar batta cike da maganin da lasmira ta fito nema
Koda zuwan wannan doki daidai inda take sai ya sauko kasa tareda tsugunnawa yace
Ya shugabata maza ki. Hau gadon bayana in kaiki ga mahaifinki domin a halin yaxu dakiku kadan suka. Rage a rayuwarsa matukar bai sami abinci da kuma maganin wannan ciwo dake jikinsa ba
Ni kuma a yanzu ina dauke da dukkan abubuwan da kike nema kuma zan sadaki dashi kafin cikar wadannan dakiku
Dajin haka ba tareda tsoron komai ba kuwa lasmira ra haye bayansa domin a yanzu tayi imani cewa tsautsayi ma yanzu tsoron haduwa da ita yake saboda ganin abubuwan da suka faru da ita
Zamanta keda wuya sai wannan dokin ya ruga da azababben gudu ya nufi hanyar fita daga birnin misra
Hakika gudun da wannan doki. Yake kana gani kasan ya wuce na al'ada saidai kawai kace gudu ne na karfin sihiri
Suna zuwa daf da kofar birnin misra
Take dokin ya daka mahaukacin tsalle sai gashi ya tsallake wannan katangar dukda tsananin girman da take dashi
Sai gashi dokin cikin abinda bai wuce dakiku goma ba ya iso kogon da Almajiri Ruzyal yake kwance koda isowarsu wannan guri take dokin yaja tunga ya tsaya cak tareda tsugunnawa ta sauka daga kansa
Sannan ta dauki kuttun maganin dake bayansa tareda abincin ta ruga cikin kogon ta tashi mahaifin nata ta dura masa wannan maganin abaki
Tareda bashi abincin dake cikin wannan akushi faruwar hakan keda wuya take yayi wata kwakkwarar atishawa sannan idanunsa suka dan lumshe kadan
Acan bakin kofar wannan kogo kuwa bayan lasmira ta shige cikinsa take sai wannan farin ingarman doki ya rikide zuwa siffar wani dattijon aljani wanda kana ganinsa kasan cewa ya fito daga jinin masu sarauta
Kawai sai ya tsaya daga bakin kofar kogon ya kurawa Ruzyal
Ido
Jim kadan sai ruzyal ya bude idanunsa ahankali suka hada idanu
Take yaji duk ciwon dake damunsa ya warke kai hatta idanunsa ma da suka dade da makancewa sai da suka bude a wannan lokaci
Nantake farinciki mara misaltuwa ya turnuke lasmira basu san sanda suka rungume juna ba.
Tare da zubar da hawayen farinciki saida suka jima suna rungume da juna ba tareda sun saki ba
Suna cikin wannan haline kawai wannan aljanin ya danno kansa ya shigo cikin kogon
Da ganin wannan aljani take ruzyal ya razana har zai janye jikinsa daga na lasmira
Sai yaji kamar an daddaure jikin nasa
Koda wannan aljani ya shigo cikin kogon sai ya dubi ruzyal yace yakai abu lasmira ka sani banzo nan gurin domin cutar dakai ba
Nazo ne domin sanar dakai wani sirri wanda kai baka sanshi ba
Don haka ka kwantar da hankalinka kuma ka saurareni
Da farko dai ina so ka sani a halin yanzu duk wannan tattaunawa da zamuyi dakai lasmira bazata iya jin abinda zamu tattauna dakai ba
Kai bama iya jinmu ba hatta maganar da zakayi min ba zata iya ganin motsin bakinka ba
Ni dai sunana Dauwaz kuma hadimi ne ni ga sarauniya Azimatul marwan wacce ke mulkin birnin RUHUL SAIWAN
Dajin. Wannan batu sai Ruzyal ya dubeshi yace yakai dauwaz naji bayaninka amma me kakeso ka sanar dani a halin yanxu
Kodajin wannan tambaya sai marganu yayi murmushi daga bisani yace
Gaggawar me kakeyi bayan aikina ne sanar dakai komai da aka umarceni
A halin yanzu duk. Duniya mu hudune kadai muke da ikon ganin lasmira
Wato. Daga ni sai kai, sannan kuma wani hamshakin boka wanda yake mulkin duniyoyin sama wato Hubbas da kuma ita Azimatul marwan kanta
Babban abun kuma da nake son sanar dakai shne lasmira 'yarka ce amma ba 'yar matarka ba
Kodajin wannan batu sai Ruzyal ya tuntsure da dariya daga bisani kuma yace wannan wacce magana kake ?
Anya kuwa kana cikin hankalinka taya za'ayi matata ta haife ta akan gabana sannan kuma kace wata ce daban ta haifeta, To wacece ainihin mahaifiyar tata?
Dajin wannan tambaya sai yace
Yakai ruzyal hakika rashin sanine yasa kake wannan maganar
Domin acikin kaddarar matarka babu haihuwa acikinta koda kuwa zata sadu da gaba daya mazan duniyar nan
Sannan abu na gaba shine bakowa bace asalin mahaifiyarta ba face Sarauniya Azimatul marwan
Ka sani tunda sarauniya azimatul marwan take bata taba samun haihuwa ba
Tayi aure da sarakunan jinsin mu na aljanu ba adadi amma ko sau daya bata taba samun ciki ba
A karshene binciken tsafinta ya nuna mata matukar tana son samun haihuwa dolene saita kwanta da bil'adama matalauci sannan kuma makaho zata sami haihuwa
A lokacin data gano wannan sirri tayi matukar bakinciki domin in takaice maka saida taji kamar ta kashe kanta amma data ga dole bata da wata mafita face wannan zabin bisa dole ta hakura
Tun daga wannan dare a kullum da daddare idan kazo kwanciya da matarka ni nake zuwa na lullubeta da bakin kyallen sihiri wanda zaisa ta dogon barci
Ita kuma sarauniya Azimatul marwan saita rikide zuwa siffarta sannan ta kwanta a makwancinta kuyi saduwar aure tare
Haka aka yi ta aikatawa har saidata sami juna biyu dakai
A randa ta haihune sai ta ajiye maka lasmira ta barta domin ta girma dakai a matsayinka na mahaifinta
Ina so. Ka sani ba komaine yaja mutuwar matarka ba face kishi
Domin a sanda aka ajiye maka lasmira alokacin ne ta farka daga dogon barcin da takeyi
Don haka yayinda taga lasmira sai tayi zaton kaci amanarta ne
Wannan ne ya janyo bugawar zuciyarta,
Yakai Ruzyal amadadin uwargijiyata Azimatul marwan ina mai baka hakuri akan abin da muka aikata maka
Bayan haka inaso ka sani tun daga randa aka haifi lasmira akullum nine wanda yake kula da cinku da kuma shanku acikin wannan daji
Saboda haka ne yasa zakaga lokuta da dama idan ka fita bara kana samun abinci da wuri. Ba tareda kasha wahala ba
Kai wasu lokutan ma kasha ratsawa ta tsakiyar guggun barayi da 'yan fashi da zarar sun tunkareka nine wanda ke shiga tsakaninka dasu na tarwatsa maka su da karfin tsiya ba tareda ka. Sani ba, haka ma manyan dabbobin daji wadanda sau da dama suna zuwa nan bakin wannan kogon amma basu taba tunanin shigowa ba
To saidai ka sani yanzu lokaci yayi da zaka rabu da lasmira domin samar da farin ciki gareta da kuma kwanciyar hankali agareka
Banzo nan ba a halin yanzu sai domin tafiya da ita
Idan har aka barta tare dakai babu makawa mutuwa zakayi haka itama
Kai ni kaina a wannan lokaci bazan iya kareta ko kuma kai daga bala'in dayake neman kunnowa ba
Domin yaki za'a kwafsa wanda ba'a taba yin kamarsa ba a duniya miliyoyin rayuka zasu salwanta a wannan lokaci
Amma bayan an gama wannan yaki lasmira zata sami matsayin da wata halitta bata taba samun kamar sa ba sannan kuma zatu tsawon rai fiye da sauran mutane
Har zuwa sanda KARAGAR AJALI zata shigo cikin wannan duniyar tamu
A sannan ne lasmira zata sami damar hawa karagar mahaifiyarta Wato sarauniya Azimatul marwan ta mulki duniyoyin aljanu da mutane na wannan duniyar tamu
Sannan ta zama sarauniyar kyawawan duniya wacce ba za'a sake haifar mai kyanta ba
Ya kai ruzyal kayi hakuri abisa rabaka da Lasmira da zanyi a wannan lokaci
Amma haka shine maslaha agareka da kuma hanyar daukakar ita wannan diya taka duk da cewa
Kai ba zakayi tsawon rai ba har zuwa lokacin da zata sami wannan daukakar dake tunkaro ta ba
Kuma zan tafi da lasmira ne bata hanyar tilastawa agareta ba
Zan tafi da itane cikin siffarka domin tafi samun kwanciyar hankali da kasancewa tare dani
Kodajin wannan bayani take jikin sa yayi sanyi kawai kwalla ta zubo daga idanunsa
Ba tareda bata lokaci ba ya janyo lasmira jikinsa ya kara kankameta yana mai zubda hawaye yace
'yata lasmira kiyi hakuri dani awannan lokaci zan kasance ina matukar kewarki
Inaso komai daren dadewa ki dawo wannan guri ki ziyarce ni domin anan zaki zo ki iske kabari na
Jin wannan magana sai hankalinta ya tashi ta kasa gane me yake nufi har ta bude baki zatayi masa tambaya
Sai. Yayi mata nuni data fita waje zaizo ya sameta
Ba tareda gardamar komai ba kuwa ta tashi ta fice daga kogon
Nantake aljani Dauwaz da ruzyal sukayi bankwana sannan Dauwaz ya rikide ya koma siffar Ruzyal ya fito waje ya kama hannunta suka nufi hanyar komawa cikin birnin misra
Suka bar ruzyal acikin kogon yana lekensu kwalla na zuba daga cikin idanunsa saboda sanin cewa wannan ne gani na karshe da zai sake yiwa 'yarsa lasmira
Bayan sun kama hanyar komawa birnin misra ne lasmira ta dubeshi tace ya abbana menene kuma zai kaimu cikin wannan birni
Baka san hatsarin dana shiga ba acikin garin nan ni dai a yanzu bani da burin komawa cikinsa
Dajin wannan batu sai yace ki kwantar da hankalinki yake 'yata kowacce nasara arayuwa tana tareda jarrabawa
Ke a yanzu kika fara ganin kalar taki jarrabawar
Yana gama fadin haka sai yayi shiru da bakinsa ba tareda ya kara ce mata uffan ba
A wannan karon kai tsaye suka shige birnin misra ba tareda wani daga cikin dakarun ya gansu ba
Basu zarce ko ina ba sai cikin tsakiyar birnin suka sami wata rumfa suka zauna acikinta kuma har a sannan gari bai fara wayeba ko ina a garin yayi tsit babu sautin mutane
Zamansu keda wuya a wannan lokaci wani irin barci mai nauyin gaske ya dauke lasmira
Ta baje akasa har tana zabga minshari, yin barcin nata keda wuya take aljani Dauwaz yayi girgiza daga inda yake nantake ya bace bat daga gurin kai kace bai taba wanzuwa ba
Haka dai lasmira taci gaba da kwanciya a wannan guri har safiya tayi hasken rana ya dallare idanunta
Koda farkawarta da taga bata ga Ruzyal ba sai hankalinta