Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 1
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
babban kogon dutse ne mai cike da kayan tsafi iri iri daban da wanda ido bai taba gani.
acikin kogon dutsen an aje wani gunki jingine ajikin bangon kogon.
agaban ana kiran wannan gunki da suna sarkus.
agaban gunkin kuwa wani boka ne durkushe awurin idanun sa arufe.
ga dukkan alamu karance karance yake irin nasu na matsafa.
ga wani kosko akusa dashi hayaki yana tashi .
daga can kuma sai ya bude idanun sa yana waige waige yana duban aljani daya bari acikin kogon.
amma baya nan.
zumbur ya tashi daga in da yake zaune ya shiga yawo akogon ya na neman sa amma shiru kamar maye yaci shirwa.
da ya gaji da neman sa ne ya fara kwala masa kira! kana ina ne aljani mardis!
kana ina!
duk da haka shiru.
hakan yasa ya zauna yai shiru.
kwatsam ba zato ba tsammani sai ya ji an bushe da wata irin dariya. dariya data cika kogon gaba daya da amsa kuwwa!
amma bai ga wanda yake wannan dariya ba..
can kuma sai yaji an yi tsit da barin yin dariyar.
da wata irin babbar murya ake magana.
cikin fushi ake maganar ana fadin.
yakai boka hurujul mahas ina so kasani lokacin rabuwar ka da wannan aljani yayi.
ni ne nan na dauke shi.
sunana aljani jaras ibn safazi.
ba wani bane ya turo ni na dauko shi face.
mai gidana aljani bazagas na dajin jahur.
aljani bazagas ya sani na sato wannan aljani naka ne ba don komai ba sai domin yana so yayi masa wani aiki daban. wanda ni kaina ban san shi ba.
ina so kasani wannan rabuwa da kayi da aljanin ka.
ka rabu dashi kenan basa ka same shi ba.
saboda wurin shugaban aljanun duniya za a kaishi.
kai kan kasan duk wanda ya je wurin aljani bazagas da wuya ya dawo.
da ma ni nazo ne domin na aiwatar da aikin aljani bagazas kuma na aiwatar.
abin da ya rage mini yanzu shi ne na kaiwa aljani bagazas wannan aljani naka domin ya cimma bukatar sa akan sa?
boka hurujul mahas ya daga murya yace.
shin ko zan iya ganin wannan aljani nawa mai yimin hidima shekaru da shekaru.
ka bayyanar min dashi zamuyi maganar.
ka sani cewa idan har ka raba ni da wannan aljani nawa.
ka cuce ni. saboda mun shaku dashi mun zauna dashi shekaru masu yawa?
aljani ya kara bushewa da dariya sannan ya yi tsit yace.
ai yanzu bakin alkalami ya riga ya bushe baza ka kalli wannan aljani naka ba yanzu saboda ya riga ya shigo hannuna.
yanzu haka na rufe bakin bazai iya yin magana ba. har sai na kai sa in da ake bukatar sa.
boka hujurul mahas ya daka wa wannan aljani tsawa tare da fadin.
kai wannan aljani ina mai gargadin ka ka maido da wannan aljani idan kuma ba haka zaka shiga babbar matsala.
kai ba kai bama har wanda ya turo ka.
zan tanadi mara kyau agareku matukar ba kayi gaggawar bayyanar da aljanin nan ba.
hanya daya ce zaku bi ku tsira daga mummunan tanadin zanyi muku. shi ne kawai ka maido da wannan aljani.
koda boka hujurul mahas yaji haka sai ya kara busheya da mahaukaciyar dariya
kamar ba zai daina ba sannan ya tsuke bakin sa ya dakawa boka hujuru mahas tsawa yace.
kai bil'adama ka iya bakin ka kasan da wa kake magana.
fadan irin wannan maganar ga aljani bagazas ba karamin tashin hankali ba ne agareka.
rashin sanin ko wanene shi shiya sa kake fadan irin wannan maganar.
matukar kana so kana ka tsira da rayuwar to ka janye maganar raba ka da wannan aljani naka.
ina son kasan wani abu daya.
idan kana jin gobara daga kogi to shine aljani bazagas!
idan kana jin guguwar annoba to shi ne aljani bazagas.
acikin munanan hadarurruka to aljani bazagas ya wuce yanda kake tunani sanin ko wanene masifa ce.
zan tafi na barka.
kuma inaso ka kiyaye abinda na fada maka.
yana gama fadin haka
sai bar cikin kogon.
yabar boka hujurul mahas ya na kai kawo acikin kogon.
nan take boka hujurul mahas yaje wurin tarkacen kayan tsafin sa ya shiga bincike ta yadda zai gano hanyar da zai bi ya kwato wannan aljani amma babu bai gani.
sai daga baya da ya tsananta binceke ya gano hanya daya ce wadda zai bi don ya kwato wannan aljani nashi.
wannan hanyar kuwa itace.
dole sai ya nemo wani mashi na sihiri. wanda ahalin yanzu bokaye da aljanu da sauran sarakuna suke so su mallaki wannan mashi.
to yanzu ya za ayi ya samo wannan mashi wanda zai iya yakar aljani bazagas kuma ya mulki duniya gaba dayanta.
nan fa ya kama tunani shi kadai.
daga karshe ya yanke shawara dole sai ya fita daga cikin wannan kogo yashi ga duniya ya kara ilimin tsafi ta yadda zai mallaki wannan mashin sihiri?
yana gama aiyana haka ya fara tattara kayan tsafin sa. ya daura gurayen tsafin sa ajinkin sa.
ya fara karanta wasu dalamisan tsafi. nan take ya bace bat daga cikin kogon tamkar bai taba wanzuwa ba.

*** acan dajin aljani bazagas kuwa***
daji ne wanda ido bai taba ganin sa.
aciki dajin ne gidan aljani bazagas yake . amma idan kashi go baza ka taba sanin akwai gida adajin ba saboda akarkashin kasa gidan yake.
aljani bazagas yana cikin fadar sa ya na kaikawo.
yana jiran isowar wannan aljani daya tura ya sato masa aljani mardis.
yana cikin kai kawon ne kwatsam sai ga wannan aljani da ya aika ya bayyana dauke da aljani mardis akafadar sa........
in karasa muku ne.
sai na ji ku

By ABBAS
With Shuraih 99%
ρðšтєđ вч
Shuraih Usman
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 2
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~


aljani bagazas ya juyo.
ko da yayi arba da aljani jafas sai tare da aljani marsdis rungume akafadarsa sai ya bushe dariya kamar bazai daina ba sannan hade fuska yace.
yakai aljani jafas ina so ka kai wannan aljani dakin tsafi na ka aje shi kafin ya farfado ina so juwar masa da kwakwalwa da yadda zai manta da komai hatta wanda yake hidima awurin sa wato boka hurujul mahas.
ya zamana cewa ya dawo yana min kallon boka hujurul mahas?
nan take aljani jafas ya cika umarni yakai aljani mardis dakin sihiri..
shi kuwa aljani bagazas ya kyalkyale da dariya sannan ya bace.
sai gashi ya bayyana acikin dakin sihirin nasa
ko da yaga aljani jafas akwance shame shame akasa sai ya kara bushe dariya sannan ya murtuke fuska ya dauko wani koskon sa na tsafi ya kunna wutar tsafi.hayaki na tashi.
sannan ya shiga kewaye aljani mardis idanunsa arufe yana karanta dalamisan tsafi.
sai da ya gama sannan aje koskon gefe guda ya zubawa aljani mardis ido ya kallon sa.
adai dai lokacin ne aljani mardis ya farfado ko da ya tsinci kansa awannan dakin wanda bai saba ganin sa ba sai ya kama waiga waige.
yana kallon cikin dakin .
sannan ya dubi aljani bagazas wanda yake masa kallon boka hujurul mahas yace.
ya shugaba na ya akayi muka zo nan wurin ko dai mun kaurane daga wancan kogon dutsen. ni nasan na kwanta barci.
ko da aljani bagazas lura da cewa sihirin ya fara tasiri akansa.
sai ya bushe da dariya yayi tayi kamar bazai daina ba.
daga can sai ya murtuke fuska ya juyawa aljani mardis baya yace.
akwai abinda zaka shi yasa muka dawo nan.
kuma rashin cimma wannan buri dana sa agabana babbar matsala ce. kuma nayi bincike na gano kai ne za ka iya yimin wannan aiki. saboda kaifin tunaninka da basirarka da kwazon ka.
ina so kaje birnin zamar.
wato birnin sarki maharu.
ko da jin haka sai aljani bagazas ya tashi zumbur daga zaune da yake. ba komai ne yasa ya tashi ba face sanin sarki maharu.
ba shi da mutunci ga zalunci.
kai hatta birnin baya bari baki su shigo.
don haka ne ya saka dakaru ko ta ina a birinin shi mutun da aljan suna gadi saboda tabbatar da tsaro.
kai saboda mummunan tsaron da sarki maharu ya bayar.
har waje wajen birnin dakaru ne abaje ko ta ina su na kai kawo don ba da tsaro.
sarkin maharu yana da kyakkyawar 'ya ta gaban kwatance.
wanda idan ka kalle ta sai ka rantse cewa babu wata mace da ta kaita kyau duk fadin duniya.
saboda hakane sarki maharu yake bata kyakkyawar kulawa.ko ku da baya so ya sauka ajikinta.
aljani mardis ya dubi aljani mardis yace . birnin zamar fa kace naje.
ba ka da labarin sarki maharu ne irin zaluncin sa da irin mummunan matakan tsaron da ya aje agidansa na dakarun mutane da aljanu.
aljani bagazas ya yi magana ba tare da ya juyo ba yace.
na sani kuma kai kadai ne za ka iya yin wannan aiki amatsayin ka na sadaukin aljani.
ina so ne kaje birnin zamar.
akwai wani mashi na sihiri awurin sarki maharu shi nake so ka sato min ka kawo min shi nan wurina.
akwai wani dalili daya sa ni bazan je da kaina ba.
na samo labarin cewa wannan mashi yana hannu sarki maharu.
kuma duk wannan ya mallaki wannan mashi idan har yayi wata daya ahannun sa to shi zai mallaki duniya gabadayanta.
mutane duniya su dawo gareshi ya zama dole kafin sarki maharu ya cika wata daya da wannan mashi to mu tabbatar mun rabashi dashi.
ka sani cewa ba mu kadai ba ne muke da muradin wannan mashi akwai sarakuna da manyan bokaye wanda suma burin su suga sun mallaki wannan mashi.
matukar idan bamu mallaki wannan mashi da wuri ba to fa akwai babban ruguntsumi agaba saboda sarki maharu ya kammala abinda zaiyi da wannan mashi har wata daya ya cika to mun shi babbar 'ukuba ya zama dole ka aiwatar da abinda na saka ka da wuri wuri amatsayi na na wanda yake saka hidima.
ina so ka sani baka da sauran wani hutu kawai sauri ka fara shirin tafiya birinin zamar domin raba sarki maharu da wannan mashi na sihiri............
kuyi comment da wuri.
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 3
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
aljani mardis ya sunkuyar da kansa na dan karamin lokaci yayi tunani kafin ya dago da kansa ya dubi aljani bagazas yace.
naji ya shugabana zan tafi saboda abinda ka fada na cewa zamu shiga mummunan hadari idan har bamu raba sarki maharu da wannan mashin sihiri ba.
to yanzu kana ganin mu idan muka samu wannan mashi ta yaya zamu rike shi har wata daya. ba tare da wasu sun kawo mana farmaki ba. kasan cewa dole yanzu matsafa su dukufa wajen neman wannan mashi.
domin su mallake shi.
ina ganin kamar wasu ma suna kan haryar zuwa wurin sarki maharu su rabashi da wannan mashi. duk da nasan baza su iya ba.
.
aljani bagazas yace.
ai shi ne nace kayi gaggawar tafiya saboda gagarumar matsalar da take tasowa nan gaba.
ina so muyi muga mun samo wannan mashi mun cimma bukatar mu akansa.
duk abinda zai faru abirnin zamar zan dinga kallonka ta madubin tsafi na.
idan naga abin zai fi karfinka zanzo na kawo maka dauki.
amma ina so kai ka fara zuwa.
aljani mardis yace ina so ka hada ni da dakaru wadanda za sumin rakiya.
izuwa birnin zamar.
aljani bagazas ya bushe da dariya yace wannan ba matsala bace.
ka fita waje zaka wadanda dakaru na jinsun ku na aljanu sai ku tafi tare dama tuni na tanadar maka su.
ko da jin haka sai aljani mardis ya fita waje sai gashi yayi arba da wadannan dakaru na jinsin sa.
nan take aljani mardis ya bude fuka fukan sa ya tashi sama suma sauran dakarun suka tashi sama su bishi abaya.
su dukan su suka luluka acikin gajimare suna zabga gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya.

****al'amarin boka hujurul mahas kuwa***
tun lokacin daya bace daga kogon dutse bai bayyana ako ina ba sai acikin wani daji in da gidan wani shaharen boka yake .
lokacin da boka hujurul mahas ya shigo wannan daji sai yayi murmushi kawai sai ya fara tafiya acikin dajin.
sai da yayi nisa da tafiya acikin dajin yazo tsakiyar dajin sannan ya fara karanta wasu dalamisan tsafi.
faruwar hakan kenan sai ga wata mararrabar hanya guda uku ta bayayyana.
nan take boka hujurul mahas ya tsaya yana nazarin hanyoyin guda uku ya rasa wacce zai bi acikin su wacce zata kaishi izuwa gidan boka saljan.
ko da ya ga kasa gane hanyar da zai bi sai ya dauko wata sanda ta tsafi ajikin sa.
ya karanta wasu kalmomi irin nasu na matsafa ya tofa ajikin sandar sannan ya sake sandar ta tsaya cak acikin iska kawai sai sandar ta fara tafiya ta taba hanya farko. sannan ta wuce hanya ta biyu.
ko da ta taba hanya ta biyu sai ta tsaya cak. ta kasa gaba ta kasa baya.
ko da boka hujurul mahas yaga haka sai yayi murmushi .
ya tabbatar da cewa wannan itace hanyar.
kawai sai ya dauki wannan sandar tasa ta tsafi ya shiga wannan hanya ta biyu.
maimakon ya tsinci kansa agidan boka saljan sai ya kara yin arba da wasu hanyoyi guda shida agabansa.
nan take ya tsaya yana karewa hanyoyin kallo yana nazarin ko wacce hanya .
amma ya kasa gano hanyar da zai bi.
hakanne yasa ya dauko wannan sandar tasa ta tsafi .
ya karanta dalamisan tsafi kamar dai na farkon hayoyin da ya wuce.
amma ya na sake sandar sai yaga ta fadi kasa.
sihirin sa yaki yayi tasiri.
al'amarin daya dugunzuma hakalin sa kenan.
ya sunkuya ya dauki sandar ya karasa gaban hanyoyin yana kare musu kallo.
yanzu acikin wadannan hanyoyi guda shida wacce zan bi. ya tambayi kansa amma babu amsa.
hakanne ya sa ya dubi hanya ta biyar kawai sai ya shige kai tsaye .
yana shiga kofar ta kulle kanta.
al'amarin daya bashi tsoro kenan.
kawai sai ya cigaba da tafiya yana waige waige.
ya na cikin tafiya sai tsintar kansa yayi acikin kusugumin daji daban .
abin da ya bashi mamaki kenan.
sai yanzu ya tabbatar da cewa yabi wata batacciyar hanya wadda ba itaba.
kawai sai juya da baya da nufin ya fita yabi wata hanya.
kwatsam!!
sai yayi kicibis da wani jibgegen zaki mai tsananin girma da kwarjini wanda sai an hada manyan giwaye guda biyu kafin suka girman shi.
ko da ya yi arba da wannan zaki sai yayi baya da gudu

BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 4
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
ya bar zakin atsaye awurin ya cigaba da gudun.
shi kuwa zakin ya tsaya a inda yake yana kallon boka hujurul.
daga can kuma sai ya bace bat.
sai gashi ya bayyana agaban boka hujurul mahas.
cikin zafin nama boka hujurul mahas ya zare takobin sa alokacin da zakin ya yi tsalle ya kawo masa farmaki.
da azama ya kare harin zakin.
nan take suka cigaba da bakin gumurzu.
ana fara wannan artabu boka hujurul mahas ya lura da cewa wannan zakin yafi karfin sa.
ko da ya fahimci cewa zakin zai iya hallaka shi farat daya.
kawai sai yayi amfani da karfin sihirin sa.
ya tashi sama.
ya cigaba da kaiwa zakin sara da suka ko ta ina.
al'amarin daya rikirkita zakin kenan.
ya gane cewa wannan hatsabibin mutum ne.
nan da nan zakin ya kara bacewa.
ko da boka hujurul mahas ya ga haka.
sai kara karanta dalamisan tsafin sa domin zaki ya bayyana.
amma zakin yaki ya bayyana.
kawai sai boka hujurul mahas ya dira kasa.
yana haki.
ya cigaba da waige waige. alokacin da ya fara jiyo gurnanin zakin ko ta ina a harabar wajen.
nan fa hankalin boka hujurul mahas ya dugunzuma. ya tabbatar da cewa ya shigo sarkakiya.
ya fara nadamar bin wannan hanya da yayi.
" yana cikin wannan tsayuwar ne yaji wannan zakin ya bayyana ta bayan sa.
kafin yayi wani yunkuri na kare kansa tuni zakin ya daka tsalle ya mangare shi.
sai da boka hujurul mahas ya jujjuya sau hudu.
sannan ya kife a kasa.
awannan lokacin tara tara yake ganin komai?
nan take zakin ya kara yin wani gurnani ya nufi in da boka hujurul mahas yake kwance.
ko da boka hujurul mahas ya ga zakin ya dufafo shi kai tsaye sai ya yunkura domin ya tashi amma jiri ya hana shi ya ya tashi.
nan fa ya kara firgita da nufin zakin.
gashi kuma tara tara yake ganin zakin.
saura kadan zakin ya zo inda yake .
ko da yaga zakin saura kiris yazo inda yake sai yayi amfani da takobin hannun sa.
kawai sai ya harbawa zakin nan take wuka ta cake a idon zakin.
nan take zaki ya tsaya cak a inda yake.
zumbur boka hujurul mahas ya tashi tsaye ya mike duk da cewa jiri na diban shi.
hakan bai hana shi yayi tsalle ba ya zare takobin daga idon zakin.
wani irin gurnani zakin yayi.
sannan ya shammaci boka hujurul mahas ya kara bige shi.
wannan karon sai da boka hujurul yayi sama yayi katantawa sau uku sannan ya fadi kasa ya baje a wurin sumamme?

*** lokacin da boka hujurul mahas ya farfado daga suma da yayi.
sai ya tsinci kansa awani kerarren gida mai kyau da walwali. ko ina ka duba a tsakar gidan an shimfida kilisai masu taushi awurin. ga kuma an zuba lu'u lu'u da mujani acikin gidan.
a firgice boka hujurul mahas ya tashi zaune.
wani mutum ya gani tsaye akansa yana kai kawo.
ga dukkan alamu dai sarki ne.
acan gefe daya kuwa zaune bisa kan kujera wata kyakkyawar budurwa mai tsananin kyau na ban al'ajabi ta sha ado mai rikitar da duk wani da namiji da yayi kuskuran kallon ta.
ko da suka hada ido da boka hujurul mahas sai boka hujurul mahas yaji zuciyar sa ta buga.
kawai sai budurwar ta sakar mishi murmushi.
sai shi ya mayar mata da martanin murmushin.
shi kansa yayi mamakin yadda yana boka amma 'yar sarki kamar wannan tayi masa murmushi.
ko dai ta kamu ne!
ya tambayi kansa.
wai tsaya tukunna awannan dalili za a kawo shi wannan gida mai kyau haka.
domin jin wannan dalili sai ku biyo mu don a fayyace muku komai?

sarkin da yake tsaye akansa ya juyo ya dubi wasu kuyangi yace ku tafi dashi yayi wanka ya sha magana.
idan kun gama komai sai ku dawo dashi nan.
cikin gaggawa kuyangin suka cika umarni.
ko da sarkin yaga kuyangin sun fita sai ya juyo ga wannan budurwa da take zaune.
kawai sai ya kyalkyal da dariya har da tafa hannu. ita ma wannan budurwa ta taya shi dariyar.
suka yi tayi kamar baza su dai na ba.
sannan sarkin ya tsaya da dariyar ya dubi wannan budurwar yace.
yake 'ya ta lushmat.
ina so ki sani.
wannan boka da kika ga na zo dashi. ina so na sa shi wani. Aiki
idan har ya yi min wannan to daga baya sai na yaudare shi ta hanyar nuna kirsa irin tamu ta sarakai.
akwai wani mashin sihiri shi nake so yaje ya kawo min.
kafin ya tafi zan shirya masa abubuwa na karya wanda sai na tabbatar ya yarda dani.
sannan idan ya kammala aikin.
zai ga sakamakon da zai biyo baya..
ki dai bari kawai ki sha kallo.
zan nuna masa yadda ake shirya makirci daban daban.
ko da sarki yazo nan.
azancen sa sai ya kara bushewa da dariya itama lushmat ta taya shi...........
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 5
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Bayan wani lokaci sarki yasa aka kira boka hujurul mahas.
lokacin yana zaune a turakar shi kadai bisa kan kujera.
sai ga boka hujurul mahas ya shigo.
ya durkusa ya kwashi gaisuwa.
sarki yayi masa iso domin ya karaso.
boka hujurul mahas ya karaso.
sarki ya masa nuni da wata kujera da take fuskantar tasa?
boka hujurul mahas ya zauna bisa kan kujerar.
sunkuyar da kansa?
sannan boka hujurul mahas ya budi baki yace.
yakai wannan sarki menene dalilin da yasa nazo nan fadar ka.
sanar dani dalilin.
saboda ba wurin ka na yi niyyar zuwa ba.
sarki yayi murmushi sannan yace.
sanin halin da zaka tsinci kanka na zuwa wurin boka saljan. shi ya sa na gaggawar dauko ka.
da farko dai ni sunana!!
MAJARUL DAUFUS.
wannan budurwa da ka gani 'ya ta ce tun tana kimanin shekara biyar tayi rashin uwa.
hakanne yasa muka ware gefe guda muke rayuwar mu ba tare da 'yan 'uwan mu mutane ba saboda.
tsananin bakin cikin rashin mahaifiyar wannan yarinyar.
mun dade acikin wannan gida dake dokar daji.
ina jiran wannan rana daza kazo gareni.
na gani kuma na kallah. duka acikin madubin tsafi na.
ka na rayuwa ne acikin wani kogon dutse kai da wani aljani na ka.
kun dade da wannan aljani yana bauta akarkashin ka.
sannan rana tsaka sai gani kayi an sace wannan aljani naka mai maka hidima.
nasan cewa kasan wanda ya dauke maka wannan aljani.
wato aljani bagazas.
sannan kuma bakasan aikin da aljanin ka zai yi wa aljani bagazas ba.
to ina so kasani cewa aljani bagazas ya tura aljani mardis ne ya karbo masa wani mashi na sihiri.
mashin sihirin yanzu haka yana hannun sarki maharu. saninka masifa'
na sani kaima ka futo daga wannan kogon dutse ne domin kaga kai ma ka mallaki wannan mashin sihiri.
shi ne ka tunkaro dajin boka saljan domin ya baka masaniya game da wannan mashi na sihiri.
to ina so ka sani muddin ka je wurin boka saljan game da maganar nashin sihiri don ya baka mafita.
to tabbas yaudarar ka zai yi.
kura da shan buga gardi da kwashe kudi.
hakanne yasa nayi gaggawar ceton ka awurin wannan mugun zakin da yake yunkurin hallaka ka.
idan ka lura wannan hanyoyi da boka saljan tanada babu alamun yaudara acikin su.
yana so kawai ka hallaka saboda baya bukatar ka awurin sa kai boka shi boka. shi yasa yayi maka haka?
sannan kuma badan komai ba yasa na ceto rayuwar ka sai don kawai.
ka samu hanya mai sauki ta damar mallakar wannan mashin sihiri.
zan taimake ka saboda tausayin ka da naji. wanda har ta saka ka zubar da hawaye.
ina so ka sani
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment