Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alkawarin,bazan taba bari ta cuci yayana ba, idan da boka ta dogara, ni da Allah na dogara, in sha Allah sena lalata duk wani shiri nata" daidai lokacin sadiq ya shigo dakin...

"Keh mara kunya, ki tattara kayanki yanzunnan zan maidaki gida, tunda baki da kunya, kuma ki shirya abinda zaki fadawa umma, dan sena gaya mata abinda kikayi" bata cemasa komai ba, ta dauko jakar kayanta ta fito, a tsaye suka sami bintu a falo

"Sadiq ina buk'atar mukullayen motocin gidannan" tafada tana hara rar khadija "ki bude bedside dina,suna ciki ki dauki wadda zaki fita" wani wulakantaccen kallo tayi mai "Ehh nasan inda suke ai, hada na hannunka nake buk'ata"tafada tana nuna key din hannunsa "ok da wannan kikeson fita? To gashi, bari nina dauko wani" yafada yana mik'a mata key din, karba tayi "kaga,ku hau napep kaje ka kaita ka dawo, kullum seka fita a mota ne" baice mata komai ba ya juya ya kalli khadija datayi mutuwar tsaye "wuce mutafi"

Fita sukayi ya tarar musu napep suka dauki hanya... Harsuka isa gidan abin bintu yana ran khadija, tunda take bata taba ganin shedaniya irinta ba... Suna shiga suka samu umma tana bacci,kamar a mafarki taji sallamarsu,rungumeta tayi "ummana nayi missing dinki sosai" itama Umman rungumeta tayi "nima haka khadija ta, gidan duk babu wani dadi, dama yanzu naketa tunanin na kirashi yadawo min dake" sadiq ne ya katse hirar tasu "umma barka da yamma,ya gida"

"Lafiya lau, ya bintu" gaban khadija ne yafadi dataji an ambaci bintu "tana nan qalau, tana gaidaki" bana amsawa, tunda taki zuwa ta gaidani" sunkuyar da kai yayi "zatazo umma, aiyukane sukayi mata yawa,yauma naso muzo tare, to wannan mara kunyar yarinyar tayimata rashin mutunci" zaro ido tayi tana kallon khadija "bangane rashin mutunci ba"

Kwashe komae yayi ya fada mata, amma seya boye laifin bintu "ita khadija ce tayi haka" gyada kai yayi "wallahi kuwa umma, shiyasa na tattaro ta nadawo da ita, tunda tace bazata taba yin shiru ba"

"Ehh kayi gaskiya, gwara daka dawo da ita, kuma keda zuwa gidannan kunyi sallama, tunda rashin kunya neyake kaiki" kuka tafarayi "wallahi Allah umma....rufe mun baki mara kunyar banza, na hanaki shegen surutunnan amma kink'i ko, to zanyi maganinki, tashi kibani waje" ta mik'e da gudu ta shiga daki tanata kuka...

"Kayi hakuri sadiq, yarintane yake damun yarinyar nan, idan kaje gida kabawa bintu hakuri dan Allah" mik'ewa yayi yana fadin "to umma bakomai, zataji in sha Allah" ya wuce ya koma gida....

Basu dade da fita ba ta kwashe mukullayen motocin gaba daya da takardun tayi gidansu, hajiyar ta bawa tace ta ajiyesu a wajenta, dan kada wata matsalar ma ta taso mishi yace zai siyar,nan fa hajiya ta dage tanata bata muguwar shawara, akan kartabar Sadiq da komai, seta tabbatar ta yasheshi tass sannan ta dage yasaketa.....

Data gama da gidan hajiyar gidan hajiya turai ta nufa, ranar ita kadai tasamu a gidan babu kowa, nanfa bintu tasake kwashe komai itama tafada mata, hajiya turai ta jinjinawa shawarar da hajiyarsu bintu ta bata

"Gaskiya hajiya tayi miki dabara, dan wallahi ko tsinke kada kibarshi dashi, kinga kina futowa, wallahi kodan abin hannunki da gudu za'a aureki" seda tayi shewa tace "bari kedai, wallahi ni dan saurayi ma sabon jini nakeson aura,inji dadina son rai" suka tafa hannu "aikuwa zaki samu,idanma kina so akwai wani yaro, bakigansa ba ya hada komai, gashi bawani shekaru ne dashi ba, tuntuni nake harinsa, sedai ni kinsan bana son harka da kana nan yara ne,gashi bawani kudi kake samu ba,sedae su suci naka, da tuni na d'ana shi wallahi" gyara zama bintu tayi "haba hajiya, ai ni kawai yanzu zaki had'a mu nafara d'anawa, dan abari ya huce, sheke kawo rabon wani,idan kudi ne, karyaji komae, wallahi indai zanji dadi babu matsala" suka sake tafa hannuwa, hajiya turai kuwa take ta dauko waya ta kira number, bugu biyu ya dauka

"Hajiya turai tamu, idan naga kiranki to tasamu" seda tayi dariya tace "aiko samu ne babba ma kuwa, kaidai kawai kaxo gida ina nemanka yanzu" da sauri yace "to gani nan hajjaju"

"Yanzu zaki ganshi, dan nasan kina ganinsa angama, irin namijin da kikeso ne, yafi mijinki komae" d'aga gira tayi "wa? Nifa kidena cewa mijina, dan ni tuni nadena daukar kaina a matsayin matarsa, nagama yayinsa,sabuwar rayuwa kawai hajiya"

Suka kwashe da dariya "wai ni ina kawarki saratu" tabe baki tayi "waya sanmata ne, ni tunsanda muka rabu kota kirani taji yanaje gida, shiyasa na watsar da ita"

"Badai tasamu kan mijinta ba, kirabu da ita, zata nemeki ne inta dagule mata, dan naga ba fitacciya bace" daidai lokacin Small daddy ya shigo gidan, wato yaron da hajiya turai ta kira...

Dogo ne sosai, fari,yana da dan kauri, ga pinks lips dinsa, dagani bai wuce shikaru ashirin da biyar ba.. Falon ya shiga yazauna, kiranta yayi a waya ya shaida mata ya iso..

"To kitashi ki sauya wannan kayan, kisaka kananan kaya, dan komae naki ya futo, sannan ki boye mishi shekarunki, kinsan yaran suma sunfi son yara, sannan ki tabbatar mishi auren dole akayi miki so kike ki kashe auren kifito ki aure shi, yanajin haka kekuma zaki samu abinda kikeso"

Fitowa sukayi, bintu sanye take da wasu matsatsun riga da wando, rabin kirjinta duk sunyi waje, kai babu ko dan kwali, sai juya duwaiwaka takeyi tana turo kirji gaba, ita a dole seta jawo hankalin small daddy... Waiyazubillah abinda batayiwa mijinta na sunna, amma gashi a banza tanayiwa wani dan iska😭😭 Allah ka shiryemu...

Tunda suka zo suka zauna idonsu akan bintu yake, dan gaba daya tatafi dashi...itama bintu hakan, jitake kamar ta janyosa jikinta, gaba daya ya kwanta mata...hajiya turai tace "to small daddy,wannan kawar tawace, zan hadaku, sunanta bintu, gata dai, zan tashi nabaku waje, setayi maka bayani, na yarda da kawata bata da wata matasala...

Tana futa bintu ta koma kusa da small daddy tazauna,sai kwarkwasa takeyi "sannunka, kamar yanda hajiya tayi maka bayani, sunana bintu, matar aure ce ni, amma auren dole akayi min tunda yarintata, yanzu idan zaka amince dani, zan kashe aurena, nafito muyi aure da kai idan zaka amince" tunda take magana yake binta dawani kallo irin na haramci "bintu ai duk namijin daya kalleki, zaiso kasancewa dake har abada, abu dayane zai hana ki aurenki yanzu"

"Mainene shi? Kudi, gaskiya banida kudin da zan iya aurenki, bani dawata sana'a makaranta nakeyi"

"Karka damu small dad, kudi ba matsala bane, indai kana sona karkaji komai, komai kakeso zanyi maka" atake yakai mata wata runguma, tuni tayi accepting, tun a wajen suka fara tambadewa....


*Deee💘*


*🌚GANTALALLIYA🌚*

*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*

*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*

*A. W. F*

*I.G:Arewa writers forum fans*

*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/

*Wannan shafin na sadaukar da shi ga HAJIYA HINDATU, a gaskiya babu abinda zancemiki sai fatan alkairi akodayaushi, samun mace irinki a wannan lokaci abune maikamar wuya,mai halin yan aljanna, Allah ubangiji yaraya miki yaranki yasa kifi haka Ameen ya rabbi I heart you dear, muna mugun tare❤💯*

True life story

41-45

Sundade suna aikata ba daidai ba a falon hajiya turai, harseda suka gaji dan Kansu sannan suka rabu da juna..small daddy ne ya kalli bintu yace

"Gaskiya bintu ke duniya ce, ina ma ace tuntuni nasanki, wallahi da babu macen da zan kula barema harna kusanceta, gaskiya kin hadu"

"Karka damu small da, ai yanzu muka fara, kaidai kawai ka rike alkawari, duk sanda nake buk'atarka zan nemeka, kaima kuma, duk sanda kake da buk'ata ta ka kirani kawai"

Da kyar suka rabu da juna, tashiga ta dauko Jakarta, dubu ashirin ta mik'a mishi tace yayi hakuri, batasan zasu hadu yauba, yana karba sukayi sallama ya wuce, ita kuma ta koma dakin hajiya turai...

"Gasiya hajiya small dad ya hadu, na dade banji dadi irin na yau ba, ashe da cutar kaina nake danake zaune da sadeeq bai iya tabuka komai ba"wani dan iskan murmushi turai tayi

"Ai nafada miki, yaron ya san takan mace, sai dai kuma bana so kiwani dade dashi, kawai kid'ana kiwuce wajen, tunda bawani kudi zaki dunga amsa ba,saidai shi yaci naki"

"Wallahi hajiya na yarda yaci kudin, indai zai dunga biyamin buk'ata ta, ke nifa bari nafada miki, wallahi ko hajiyata bata isa tarabani da small daddy ba, ni idanma duka dukiyata yake buk'ata wallahi zan mallaka mishi, indai zai kasance tare dani"

"Lallai bintu small daddy yatafi da ke, to Allah ya barku tare, indai kina sonsa ai ba matsala"

Suna gama hirarsu bintu tayi shirin tafiya gida, tafe take a hanya tanata tunanin small daddy.... A d'aki ta iske Sadeeq ya zuba uban tagumi,yana jin shigowarta ya mik'e da sauri

"Swthrt sai yanzu, ina kika shiga haka duk hankalina ya tashi banganki ba?" Ko kallon inda yake batayiba ta wuce ta ajiye Jakarta, ta zube a gado..

"Haba swthrt ina magana...kaga kayimin shiru, dan Allah ka fita kabani waje nagaji"

"To kiyi hakuri barinayi miki tausa" dak'a mishi tsawa tayi "kaga kafita nace bana son surutu" tana fada ta koma ta kwanta, shikuma yafita yabar mata dakin yayi nashi dakin...yana futa ta mik'e ta sa key ta rufe kofar, ta koma ta dau waya, missed calls din small daddy tagani rututu, da sauri ta kirashi suka kusan kwana suna waya...

Bangaren su Umman sadeeq kuma,tunda yatafi tabi khadija daki tana mata fad'a

"Wato khadija kinzama mara kunya ko? Matar yayannaki zaki kalla kice mata bata da tarbiya"

"Ummana wallahi dan bakisan meyake faruwa bane, sam anty bintu bata kyautawa yaya,yanda na kulama saitayi fuciwarta se sanda taga dama zata dawo, Allah umma yaya yana cikin wani hali, idan shi yana jin tsoronta,mukuma bai kamata muzuba musu ido ba taita azabtar mana dashi, kalli fa yanda yadawo kamar wani tsoko, to wallahi sema kinga yanda yakeyimata, kamar ita takawosa duniya, dazuma ina ji tana waya da hajiyarta wai zasu...... Keh rufe min baki,ina rabaki da surutu kina cigaba ko, ina ruwanki da rayuwar da yakeyi da matarsa, ko ance miki ana shiga tsakanin miji da mata ne, khadija kifita a idona fa, tohm"

Takarasa maganar a tswace, khadija kuma sai kukan rashin fahimtarta da umma batayi ba takeyi, a ganinta da umma zata yarda sai su had'a kai su ruguza duk wani shirin bintu. Tunani ta shiga yi, bayan umma tafita daga dakin, cen kuma ta tsaida kukan datake yi, wata dabara tafado mata, a fili tace "yawwa hakan zanyi kawai, dan wallahi ko umma zata kasheni wlh sena lalatawa bintu komai, kuma asirinta seya tonu" tana fada ta mik'e tayi kitchen, dan yunwa takeji....

Akwana atashi bintu sun shak'u da small dadi sosai, dan har mota ta bashi, a cikin motocin sadeeq, sauran kuwa duk ta siyar, sai ta hannunta datake amfani da ita, shikuma sadeeq ko oho, idan wata yar futa takama shi, saidai yahau adaidaita sahu, ya zama mijin tace, duk abinda bintu tace mishi shiyake, gaba daya duk yabi ya lalace, yarame yayi bak'i,bashida wajen zama sai wajen masu gyaran machine din unguwarsu, mutane kuwa duk sanda yafito andunga nuna shi, masu zagin bintu sunayi, masu Allah ya shiryeta, wasuma tsine mata sukeyi,dan babu wanda baisan ita ta jefa shi cikin wannan halinba....ita kanta ummansu sadeeq tafara damuwa da halin da danta yake ciki, babu yanda ta iya tunda tasan anruga an asirce mata danta, addu'a kawai takeyi, takuma saka malamai sutayasu da addu'a Allah ya karya abinda sukayi.....

Haka rayuwata dunga tafiya, a kwana a tashi khadija ta kammala karatun secondary dinta, tayi kyau ta girma ta zama cikakkiyar budurwa, dan babu ranar daxata futa samari basu biyotaba, sai dai ita bata ko kallon inda suke, barema harta kulasu...

Wata rana ne, da yammaci umma ta aiketa ta siyo musu kuka, sanye take cikin hijabi iya gwewarta,tana tafiya cikin nutsuwa, harta isa gidan tasiyo, tana kan hanyarta ta dawowa ne, wani mayen saurayi ya dunga binta,babu yanda baiyiba akan ta shiga motarsa yakaita gida amma tak'i, shima kuma yak'i dena binta, harseda tashiga gida...

Dukda ta shiga gidan bai tafi ba,tsayawa yayi yarasa tayanda zaiyi yasamu ta fito,yana tsaye saeyaga wani yaro, "yawwa dan yaro dan Allah shiga gidannan kace ana sallama da yarinyar data shigo yanzu" dayake yaron yaga fitar ta yasan khadija yake nufi "tab, ai malam idanma zaka hakura ka hakura, indai khadija ce, wlh bama zata fito ba,bare harta saurareka" yana gama fad'a yayi gaba, dan saurayin yasake binsa da gudu

"To dan Allah kayi min sallama da wani nata, ko yayanta ko mahaifinta"

"Mahaifinsu yarasu, yayanta kuma yayi aure bama anan yakeba, sai dai mahaifiyarta" da sauri yace"Ehh dan Allah ka kira mahaifiyarta kace tayi bak'o" yaron ya amsa masa da to "ya shiga ya sanar da sakon, umma tace ya shigo daga ciki, yana fita yafad'a mishi, cikin jin dadi ya dauko kudi ya bashi sannan ya shiga gidan.........

Ina bawa masoyana hakuri akan rashin jina da bakuyi jiya ba, ayyukane sukayimin yawa, gibema bazakujini ba,sai Allah ya kaimu jibi, saboda zanyi tafiya zuwa maradi, in Allah ya kaimu lafiya zakujini jibi in sha Allah kutayana da Addu'a Nagode.

DEEE💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*

*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*

*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*

*A. W. F*

*I.G:Arewa writers forum fans*

*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/

*Happy, Happy Birthday! Sister bilki I hope the day has been blessed with the presence of those you love most, and many magical moments! On your birthday, today, I wish you a year with loads of fun, excitement and beautiful memories.*
*Happy Birthday!once more again I hope its filled with love, laughs, and family..🎉🎊♥*

Dan ALLAH ina rok'on wayanda suke biyoni private na tura musu novel, dan ALLAH kuyi hakuri ku dunga tambaya a groups, karkuga bana responding, wallahi abubuwan yawa suke min, karku dauka wulakancine wallahi ba haka bane,Allah yasa kun fahimceni.😊

Wannan shafin sadaukarwane ga dukkanin masoyana na DEEE FAN'S CLUB ina godiya da soyayyar da kuke nuna min, nima ina sankon sosai da sosai, ALLAH ya barmu tare one Love❤


True life story

46-50


Cikin falon umma tayi mishi iso, seda suka gaisa, sannan yafara yi mata bayanin abinda yakawo shi

"Hajiya ni sunana usman surajo,dama ina hanyar dawowa daga kasuwa ne naga wata yarinya data shigo yanzu, to nayi kokarin ta tsaya muyi magana amma tak'i yarda, hakan yak'ara tabbatarmin da tarbiyyarta,, shiyasa ta k'ara burgeni,naji bazan iya ba senazo har gida nasami manyanta"

"Gaskiya ne,naji dadin yanda kayi, dan yarinyar nan duk saurayin da zai tsayar da ita a titi bata sauraronshi, watakila hakan dakayi, kasamu kudaidaita, amma kafin nan,kai dan ina ne?

"Ni dan asalin garin kano ne,ina tare da iyayena a unguwar taludu, kwanan nan nafara kasuwanci a kasuwar kwari, ina saida atampopi da lessina, shiyasa banyi aure ba tuntuni, amma tunda yanzu Allah yabani Sana'a kuma Alhamdulillah ina samun alheri, shiyasa hankalina ya jikkita kan aure, hajiya in har zaki bani yarinyarki, wallahi a shirye nake"

"To naji duk bayananka, sedae wani hanzari ba gudu ba,zan kira yayanta,zan fada mishi komai, inyaso seyayi bincike akai, yanda mukayi, seka dawo rana ita yau in Allah ya kaimu"

"To babu komai hajiya, amma dan Allah ina neman alfarma, kidan turo mun ita mu gaisa yanzu, kafin nadawo"

"To ba komai bari na turo maka ita" tashi tayi ta shiga ciki, a zuciyarta kuma sae yabon halin saurayin take, dan ita yanayinsa ya burgeta.... Da kyar ta lallaba khadija ta tafi wajensa, da sallama ta shiga tana tura baki, waje tasamu nesa dashi ta zauna

"Ina wuni" tafada tana turo baki "lafiya lau yan mata, ya gida" yafada yana kallonta yana murmushi "lfy" kawai tace ta sunkuyar da kai, shuru sukayi na yan muntina, kafin ya miko mata wayarsa yace

"Gashi,dan Allah ki taimaka kisaka min number ki,zamu dunga gaisawa kafin nadawo lokacin da hajiya tace" seda ta ja lokaci, sannan ta karaso inda yake ta karbi wayar, tana fara saka mishi number wayarta kira yashigo wayar.....

Ganin hoton mai kiran ne yasata zero ido, da kuma sunan dayakejiki, a fili tafada "Anty bintu! Kasanta ne" tafada tana nuna screen din wayar, har kiran ya tsinke,jikinsa ne ya hau rawa, gumi yafara keto mishi, cikin en'ena yace "ehmmm ammm wata abokiyar kasuwancina ce" a fusace tace "abokiyar kasuwancinka shine zaka sakamata sweet love" kasa ce mata komai yayi, itakuma hawayene suka dunga bin kuncinta, a fili ta dunga fadin

"Yanzu Anty bintu har saurayi gareta tana matsayin matar yayana,wannan wacce irin masifa ce, wallahi dole na tashi tsaye na farfado da yaya daga wannan masifar da bintu ta jefa shi, tun kafin ta kwaso wata cutar tazo tasaka mishi, dolenema ya rabu da ita koyanaso kobaya so" ta k'arasa maganar cikin d'aga murya....

"Haba khadija, kiyi a hankali mana, bakya tunanin idan mahaifiyarku taji hankalinta ya tashi.....kayimin shiru, mayaudarin banza mayaudarin hofi, ba hada kai ba ake haduwa a ci amanar yayana, nima kaxo zaka yaudareni, to Allah ya tona maka asiri, kuma sekayi nadama, Allah bazai barka ba" ta fashe da kuka

"Dan girman Allah khadija ki tsaya ki saurareni, wallahi sharrin zuciyane, amma wallahi nayimiki alkawarin daga yau babu ni babu bintu, amma sena fara tayaki kin cika burinki, wallahi Allah khadija da gaske nakesonki, bani da burin cutar dake a zuciyata, tunda naganki naji wani masifaffen sonki,ki taimakeni, zanyi miki bayanin komai kafin mu bullowa hanyar da zamu kwatowa yayanki hakkinsa"

Shiru tayi da kukan kafin tace "kayi alkawari zaka taimakeni mu ceto halinda yayana yake ciki" matsowa yayi kusa da ita "wallahi Khadija nayi miki alkawarin zanyi iyakacin bakin kokarina"

"To shikenan, kaga yanzu kar umma taji abinda muke cewa, kaje kawai saimuyi waya gobe, inyaso ko wani wajen ne ma hadu mu tattauna"

"To babu matsala Allah ya kaimu" sukayi sallama, koda ta koma umma taga yanayinta ya chanza, bata kawo komaiba,a tunaninta haduwarne bata sonyi.....

To wai waye wannan saurayin ne?

Small daddy ne, saurayin bintu, ko ince kwartonta, tunda suka hadu da bintu, kud'ad'en datake bashi, sune ya hadasu ya fara kasuwancinsa, dan motar data bashi ma siyar da ita yayi, yakuma sake karbe ta hannunta,dan komai ya buk'ata babu gardama take bashi.....tunda yafara kasuwancinsa yafara dauke mata wuta, dan sai sunyi zasu hadu, seya kawo mata uxuri, dan neman hanyar da zae rabu da ita kawai yakeyi,dan soyake ya gyara rayuwarsa...... Ita kuma bintu ba karamin tashin hankali ta shiga ba,kullum cikin kiransa take, wani lokacinma har kuka takeyi, gidan hajiya turai kuwa hartagaji da kai mata k'ara, dan babu abinda take cemata se "kawai ki manta dashi" sabida haka ne yasa ma ta daukewa gidan hajiya turai wuta, kullum tana kofar mata wajen hajiyarta....


Da tunanin khadija ya tafi gida, yana kuma danasanin tambadewar da sukayi da bintu, gashi yanzu yazo yana danasani, yayi imani da Allah komai zaiyiwa khadija bazata taba ganinsa da mutunci ba,gashi Allah ya jarrabeshi da sonta, yayi alwashin gobe seyafadawa khadija komae, tun farkon haduwarsa da bintu har karshe ko zae samu sauki a ransa...... Da wannan yakarasa gida, saedae kasa bacci yayi, daya rufe idonsa yake ganin khadija.....

Washegari da asubar fari khadija ta tashi, tunda tayi sallah bata koma ba, zama tayi tana ta tunanin abinda bintu takeyi, a zuciyarta ta dunga fadin "anya kuwa bintu zata shiga aljanna? Haka taita tunaninta harta gaji ta shiga kitchen ta had'a musu abinda zasuyi breakfast....

Suna cikin cin abincinne umma tace "khadija, idan kingama abinda kikeyi, zan aikeki gidan yayanki, tun jiya nake kiranshi a kashe, kuma bance kije kiyi rashin kunya ba, kinjiko? Seda ta hadiye abinci bakinta "to umma"

Daidai lokacin da suka gama ne kiran small daddy ya shigo, da sauri ta mik'e ta bar falon, seda suka gaisa sannan yace mata karfe nawa zasu hadu, ta fad'a mishi ummanta zata aiketa gidan yayanta, seyace to zaizo ya dauketa sae suje, bata amince ba,seda kyar ya shawo kanta ta amince....


Karfe 12 na rana daidai yazo ya dauketa suka tafi,suna tafe a hanya ya kwashe komai tun farkon haduwarsu da bintu yafad'a mata, babu abinda ya boye mata.... Wani nauyi kanta yayi tunda yafara magana, wani bak'in ciki da tsanar bintu da hajiya turai suka taru a zuciyarta, harma dashi small daddy yabata haushi ba kad'an ba, sedai bata nuna mishi ba..... Nesa da gidan ya ajiyeta yace taje ta futo yana jiranta, tana fita kuwa kiran bintu ya shigo wayarsa,kamar karya dauka sai kuma ya dag'a, yana dagawa tace

"Haba Cwt, menayi maka ne inata kira tun jiya kak'i dauka, meyake faruwa ne? Tabe baki yayi sannan yace "wlh baby ina cikin wani matsala ne, zan zo na dauke ki anjima, nafada miki koma menene kinji karki damu" sauke numfashi tayi "to Cwt senajika" ta kashe wayar tana jin dadi....

Khadija kuma tunda ta shiga gidan ta ganshi kamar kango, hatta mai gadi an sallameshi, babu mota ko d'aya, mamaki baigama cikata ba seda ta shiga falon taga babu kujeru babu kayan kallo, sallama ta dungayi taji shiru, gidan harwani amsawa yakeyi, ga k'ura ko ina, k'asan tail's dinma duk shatin kafafune sabida tsabar k'ura.... Dakunan ta hau dubawa amma bataga kowa ba, hakanne ya tabbatarmata babu kowa, haka ta futo tayi wajen motar small daddy...

Gaya mishi yanda ta tarar da gidan tayi, baiyi mamaki ba,dan yasan halin bintu, gida suka nufa,nan itama ta bashi labarin abinda tasani daga cikin halin bintu, hada zancen saida kadarorin sadeeq.... Bak'aramin tausayawa sadeeq yayi ba,ya kuma cemata karta damu, in sha Allah komai zai daidaita.....

"To yanzu ya kake ganin za'ayi, ta ina zamu fara" seda yadanyi tunani sannan yace "yanzu dai ta kirani tace tanason gani na, kuma nace mata ina cikin matsala,abinda za'ayi shine, anayin magariba zankirata mu hadu, zan langwabemata nace, wasu kayan kudi ne akayimin tallansu, idan har na siya ba karamar riba zanciba, amma kudine babu, kayan zasu kai million 1 da rabi.....kinga zata fara tunanin hanyar dazata samu kudin, na tabbata yanzu bata da su a hannu, idan ta fara wannan tunanin, nikuma sena bata shawarar ta dauko mun duka takardun gidajen sadeeq dana gonakinsa, sai mu sami lawyer na karya mu raina mata hankali dan naga bawani ilimine da ita ba ba ganewa zatayi ba, ina tunanin wannan shine plan na farko, yayi ko?

"Gud, abinda kafada yayi daidai, amma a ina zamu sami wanda zai hau lawyer? Kar aje a sami problem fa" murmushi yayi kafin yace "uhmm karki damu, ina da wanda zaiyi bashida matsala" daidai lokacin suka isa kofar gidan ya ajiyeta ta shiga gida, shima ya yi nasu gidan........

Deee💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*

*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*OMG!!! FROM WHERE I AM GOING TO START SELF?😍 AM OUT OF WORDS😷 MEMBER'S DIN PML A GASKIYA BABU ABINDA ZANCE DAKU SAI GODIYA DA FATAN ALKAIRI, ALLAH TUNDA NAFARA RUBUTA NOVEL BANTABA GANIN MUTANE MASU SON JUNANSU DA HADIN KAI IRIN NAKU BA, ALLAH UBANGIJI YAK'ARA MANA SO DA KAUNAR JUNANMU, MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA TSARE MU DA K'UNGIYAR MU🙏🏻 AM PROUD OF YOU GUY'S😍.*

*DEDICATED TO MY 2 LOVELY💕 SISTERS, BEELKEEY SHUWERH AND SUHANA, NO NEED FOR DOGON TURANCI, YOU KNOW I HEART♥ YOU GUY'S, AND I REALLY APPRECIATE WHAT YOU DID TO ME, I WILL NEVER FORGET YOU IN MY LIFE😍 ANA TARE #ONE❤.*


TRUE LIFE STORY.

51-55

Tana shiga ta tarar da umma tana bacci, band'ak'i ta shiga ta yi alwala tayi sallah, har yamma tayi sosai, taga umma bata da niyyar tashi, d'akin ta koma ta soma tashinta.

"Umma kitashi haka, yamma tayi fah" a hankali umma ta bud'e idonta "a'a yaushe kuma kika dawo"? Zama tayi tana fad'in "tund'azu fa nashigo nasamu kinata bacci"

"Wallahi kinga, ina gama karatu bacci ya kwasheni, ya kukayi da yayan naki to"? Gyara zama tayi "ai umma babu wanda nasamu a gidan, kuma gidan a bud'e amma bakowa" tashi zaune umma tayi "bangane babu kowa gidan ba,kuma a bud'e"

"Uhmm umma wallahi da gaske, duk d'akunan nan babu kowa, kuma umma kinsan me"? Girgiza kai tayi, kafin tace "inajinki" k'asa tayi da murya "umma wallahi gidan kamar k'ongo haka yadawo,

Please Login or Register in order to submit comment