Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamakin yadda
talatu take dago masa hannu
tare da kara masa kwarin gwiwa
duk da yake kuwa ita ya biyo don
ya kamata ya mayar da ita gida
.
Ita kanta tasan ita yazo nema
amma ganin ana dambe dashi
kuma shine dan uwanta wada
tafi sani a garin yasa take goyon
bayanshi tare da sabbin
kawayenta wadanda suke zaune
tare a benci daya
Amadu yaji tsigar jikinshi ta
tashi yaji sabon karfi ya shigo
masa Idan har ya yarda shagon
sadi ya kashe shi to ya bayar da
talatu don kuwa tuni yasa ta
bayar da labarinshi a wajen
kawayenta cewar dan garinsu
ne kuma ita yazo nema
juyawar da Amadu yayi ne yaba
shago damar kawo masa wani
dukan ya sameshi a hanci
Amadu ya girgije bai yarda ya
fadi ba yaja baya ya kalli shago
wanda yake huci yana gyara
hannu hancin Amadu ya fara zubar da jini yana tsaye Garban
kauye ya garzayo yasa riga ya
gogewa Amadu jinin aka raba
damben kafin a sake juyowa
turmi na biyu
Ganin nasarar da ya samu ne
akan Madu baligi sai shagon sadi
ya koma gefe yana kirari
makadan suka sa kidansa ya
fara rawa yana wasa da
hannunsa 'yan tsirarun mutane
da suke sonshi suka fara ihu
suna yi masa tafi amma da yake
mafi yawan sunfi son Amadu
baligi gidan yayi sanyi babu
hayaniya sosai
.
Amadu ya juya ya sake kallon
talatu wacce ranta ya baci ganin
shago ya bata masa hanci
Amadu yayi mata murmushi
talatu ta sake dago masa hannu
Idan har yabar shago ya
kasheshi ya kunyata dimbin
masoyansa da suka cika gidan
musamman talatu wacce kadan
ya rage ta fashe da kuka amadu
baligi yaji ya canza ra'ayinsa a
dan lokaci kankani dole ne ya
kashe shagon sadi kome zai faru
ya faru" bazai taba kunyata
dumbin masoyansa ba dake a
wannan gida
Bayan sun huta sai aka basu fage
don su dawo su sake raba raini
da shago yaga shi yake samun
nasara sai ya sake tasowa
Amadu ya kawo masa duka a
kwibin wuyansa Amadu ya
tokareshi ya hanashi karasowa
da hannun kafin shago ya
sarrafa jikinsa ne yayi wata
hikimar Amadu yadan zunguri
hancinsa" wanda hakan yasa
shago yayi baya kamar zai fadi
har mutane sun fara ihu da
murna" sai shago ya dake a
jajirce" to amma kowa yasan yaji
dukan" mutane suka dawo
hargowa suna kiran sunan
Amadu baligi muryar talatu ta
kere muryar mutanen dake a
kusa da Amadu baligi" yaji tana
cewa
Yayana Amadu ka dage.....
Yaya Amadu ka kashe shi
.
Wannan muryar ce ta sake zaburar da Amadu baligi yayiwa shago bakandamiyarsa lokacin
da shago ya wartsake ne sai
Amadu yayi fitar sauri ya takewa
shago kafa ya hanashi ja da
baya akan lokaci a lokaci guda
yasa bakandamiyarsa ya daki
muka-mukin shagon sadi baya
bukatar ya tsaya kallon irin
faduwar da yaron zaiyi yasan a
duniya babu mutumin da zai iya
shanye wannan dukan" Amadu
ya juya ya fara dagawa
masoyansa hannu wadanda suke
hargowa kamar zasu fasa gidan
Shagon sadi ya dade a sume
kafin ya fadi kasa a sandare
kamar kifin miya" sadi ya bude
baki a rikice yana kallon cin
amanar da amadu yayi masa
Garban kauye ya rugo a guje ya
dauki amadu duk da nauyinsa ya
dagashi sama mutane suka fara
zubo da ruwan kudi 'yan kore
suna kwasa suna tarawa Amadu
Garba ya fara zagayawa dashi
mutane suna dafa kanshi a haka har saida suka zagaye filin talatu tare da kawayenta sai
tsalle sukayi suna tafi cikin murna tana basu labarin Amadu
yayanta ne
.
An kai minti ashirin ana murna a
gidan kafin a gyara filin" Garba ya tattaro
KAZAR KARFIN
da kuma kyautar da Amadu ya samu ya
damka mashi yana dariyar farin ciki sannan ya dauki makirfon yayiwa mutane godiya sannan
ya tabbatar masu kudu ce tayi
kisa a wannan ranar ba arewa ba""
Harare da Iro bahago suka shigo
cikin fage suka dauki shagon
sadi wanda bai farfado ba
sukayi waje dashi mutane suka
basu hanya ana tayi musu ihu da
gwalo sadi ya tashi daga kan
bencin ya shigo cikin fagen yana
murmushi yaje har gaban Amadu
baligi ya dafashi yace dashi
"Na tayaka murnar nasarar da ka samu
ya kalleshi har cikin idanunsa
sannan ya kara da cewa
"kada ka mance da alkawarin da
na dauka akan idan kaci amanata.......
Muna nan muna
jiranka zakazo hannunmu bayan ka gama murnar
.
Ya juya a fusace ya tafi yabar
Amadu tare da masoyansa da masu son su gaisa dashi...
.
INTERVAL....
.
TAKUN FARKO KENAN....KAZAR KARFI--> 19
.

.
Wadansu kuma suna so su dauki
hoto tare dashi duk abinda
akeyi hankalin Amadu yana kan
talatu ya nunawa Garban kauye
ita yace kada ya bari ta bace
masa ita yazo nema suna cikin
haka ne saiga Balan dubarudu ya
keto mutane ya shigo ya kama
Amadu yana murna Amadu ya
nuna masa talatu wacce take a
cikin karuwan da suke akan
benci yace da Bala Gata can bala
mutane bazasu
barni in tasa ta ba ka tafi da ita
gidanku zanzo in dauketa idan
na gama sallamar mutane Bala
yaje ya sami talatu ya fara yi
mata magana Garban kauye ya
dawo wajen Amadu baligi suka
samu da kyar suka fita daga
fagen sun kai awa daya suna
fama da hayaniya da mutane
kafin su sallami makada da
sauran 'yan koren da suke aiki a
gidan damben Amadu ya kullo
kudinsa a buhu suka dawo gida
tare da garban kauye
Har zuwa lokacin bai mance da
gargadin sadi ba inda yake cewa
....IN HAR BAKA CIKA MANA
ALKAWARINMU BA SAINA KASHE
TALATU KISAN
WULAKANCI..
.
BAßI NA BAKWAI
.
Bayan Amadu baligi ya huta a
gidan Garban kauye sai
hankalinsa ya koma kan talatu
yanemi jaka ya zuba kudinsa a
ciki ya kirga dubu hamsin ya ba
garban kauye ya mayar masa da
kazar karfinsa daya sa masa ya
kuma bashi dubu goma kyauta
Garba yayi masa godiya ba
kudin da ya bashi sukafi
damunsa ba ya riga ya share
masa hawayensu a garin ya fitar
dasu kunya tunda dai ya kashe
musu wannan yaron wanda ya
gallabesu kwana da kwanaki
Amadu yayi bankwana da Garban
kauye wanda ya dage kan sai
sun nemo mai mota wacce zata
mayar dashi gida Amadu ya
nuna rashin amincewarsa yace
ya gode yasan ya tono rigima a
tsakaninsa da sadi baya son
ganin ya shafi kowa a cikin
mutanen garin ba wanda yasan
abinda sukayi shi da sadi bai
fadawa kowa ba
Amadu ya garxaya gidansu bala
don ya dauki talatu su koma gida
da zuwanshi ya sami Bala a kofar
gidansu a kishingide
cikin jini makwabtansu
wadanda suka damu dashi sun
cire masa riga anje nemo mai
babur a kaishi asibiti jikinsa duk
raunin sara jini sai zuba yakeyi
.
Amadu ya durkusa ya dafashi a
kidime
Bala ya akayi..... Me ya faru..... Wa
yayi maka haka?
Bala ya dago kai da kyar ya dubi
Amadu yace dashi
"Su sadi ne suka tareni suka
kwace talatu daga wajena a
lokacin da na taho da ita daga
gidan wasa zanzo da ita nan
gidanmu" yace in fada maka idan
kana sonta kaje ka samesu acan
bayan gari a wani daji da muke
cewa
MAI KWATAMI...
Bala ya cije baki saboda azabar
dake damunshi wani mutum
dake a wajen a tsaye yace da
Amadu baligi
kaje ka fadawa 'yan sanda halin
da ake ciki wadannan 'yan
damben ba mutunci ne da su ba
Kai Amadu kada kaje ka fada
musu su kassara ka a banza kaga
dai abinda suka yiwa Bala
Amadu yace da mutumin
Wannan rigimace tsakanina da
su abin bai shafi 'yan sanda ba
nina san dalilin da yasa suka yi
min haka ni suke so su gani don
haka zanje in samesu a
bayan garin ina ne
MAI KWATAMI ?
Mutumin yasa Amadu baligi a
hanyar mai kwatami yace ya
mike hanya zaije har inda suke
Amadu yasa kai ya tafi ba wani
fargaba a lokacin gari ya fara
duhu an kusa kiran sallar isha'i
ba kanshi yake ji ba talatu yafi ji
saboda a dominta yazo wannan
gari" gashi abokan adawa sun
kamata sunyi garkuwa da ita
.
MAI KWATAMI.
.
MAI KWATAMI wani karamin daji
ne dake bayan garin dubarudu
tafiyar kilomita daya daga wajen
ana iya hango kyallin rufin
gidajen garin a nesa kuma ana
iya jiwo sautin dake da kuma
kukan jakuna ko haushin
karnuka lokaci-lokaci
Babu gonaki a dajin mai
kwatami kananan itatuwa ne
irinsu kayar dundu da kuma
tsamiya da faru kasancewar
wajen baya rabuwa da tsuntsaye
da rana dajin yakan cika da yaran
garin dubarudu wadanda
suke zuwa harbi da gwafa ko
kuma su ajiye keji don tsuntsaye
su fada ciki ya rufe dasu
Da zuwan Amadu baligi wajen
tun kafin ya karasa ya hango
dandazonsu sadi kare garke
yana zaune a tsakiyarsu su kuma
suna a tsaye Amadu ya gane
hakan ta hanyar dosashin jan
tabar da sadi yake sha wacce ke
kara yin haske duk lokacin da ya
zuketa a cikin daren saida
Amadu yazo dab da inda suke
sannan yaga talatu a daure
tamau a jikin wata kututturen
icce a kusa dasu ga alama tayi
kukanta tuntuni harta gama
kafin Amadu yazo
.
Sadi kare garke da yaransa sun
hangi Amadu tun daga nesa
kafin ya matso kusa dasu da
zuwanshi wajen sadi ya mike ya
tarbeshi da cewa
Barka da zuwa jarumi dama kai
nake nema yau kazo inda bazaka
taba komawa gida da rai
ba
Amadu wanda yake rike da jakar
kudinsa a hannu yace
kun bani kunya bansan ku
matsorata bane kuma kananan
yara saida na samu labarin kun
kama mini kanwata ni zaku
kama idan kun isa ba karamar
yarinya zaku tsare ba a daji
wacce batayi muku laifin komai
ba
.
Tun kafin sadi ya mayar masa da
martani Iro bahago ya taso a
fusace zai fadawa Amadu sadi
ya dakatar dashi da hannu
Saurara Bahago Zan Baka Damar
.
BARKAN KU DA JIMIRIN
SAURARON WANNAN QAYATACCEN
LABARIN MAI CIKE DA
NISHADANTARWA
FADAKARWA
WA'AZANTARWA
DAKUMA
BOYAYYIYAR SOYAYYA...KAZAR KARFI--> 20
.

.
SADI ya juya ya sake fuskantar
Amadu babu wadataccen haske
a wajen don haka ba wanda
yake iya ganin munin dake
tattare da fuskar kowa
Sadi yace da Amadu
Kaci amanata Amadu ka karya
mani alkawari ka bata mani
yarana biyu dukansu suna
asibiti yanzu zamu dauki fansa
wannan dalilin yasa muka kama
talatu saboda mun san ta haka
ne kawai zamu kama ka kazo
inda muke ka samemu
Amadu yace da sadi kare garke
Gani nazo na sameku din
amma ina tabbatar muku yadda
nazo da kafafuna a kansu zan
koma tare da kanwata bazaku
iya cin nasara akaina ba
Sadi yayi dariya
kayi kuskure Amadu saboda
dambe kawai ka iya anan ne
kake da ido fiye damu mu kuwa
bayan dambe akwai abubuwa da
yawa da muke iyawa wadanda
zamu iya kare kanmu dasu a ko
ina
Sadi ya hade rai yace da iro
bahago a fadace
shiga ka nuna masa abinda bai
iya ba Bahago
kamar dama jira yake yi a
taboshi iro bahago yayi kukan
kura ya fadowa baligi ya
rumbabeshi suka fadi kasa tare
Amadu ya saki jakar kudin gefe
guda ya mayar da hankali akan
fadan dake gabanshi
.
Iro Bahago yana da karfi don
haka sun dauki lokaci suna
turmushe juna a kasa ya kasa
tureshi Amadu ya tokari iro
bahago da gwiwar kafarshi ya
sameshi a ciki wanda hakan
yasa dole ya dafe cikin nasa ya
saki Amadu sadi da ragowar
yaransa suna tsaye suna kallon
Amadu ya mike ya haye kan iro
bahago ya naushi wuyansa
Iro yayi makararriyar tsuwa ya
koma lagwaf ya saje da kasa
Amadu ya tashi daga kanshi don
ya sumar dashi kuma bazai
fardado da wuri ba
tun kafin Amadu ya huta sadi ya
fizgo yaransa biyu MIKO da
RAGIJE ya turawa Amadu su da
fadawarsu suka kamashi da
kokuwa basu yarda ya sarrafa
hannuwansa ba suka murdeshi
da karfi suka tausheshi suka
kaishi kasa miko ya murde
hannuwansa ta baya Ragije
kuma ya shake wuyansa suka
tankwarsa shi
Ganin irin rikon da kartin biyu
suka yi masa yasa talatu ta fara
kuka tana a daure a inda take
sadi ya fara dariyar mugunta ya
kalleta yace
tukunna ma yarinya zamu zo
kanki ki jiramu
.
Kafin sadi ya gama tsorata talatu
ne Amadu yayi kururuwa ta
tashida kartin biyu ya watsar
dasu suka fadi yayi saurin cire
hannuwansa ya daki miko a
fuska wanda saida yayi kuli-kulin
kubura a sama sau biyu
sannan ya fadi kasa baya
numfashi Ragije ya cire hannu
shima ya daki Amadu a fuska
wanda dole tasa ya fadi kasa
wanwar
to amma a saboda zapin nama a
lokacin da Ragije yayi sufa zai
tausheshi sai Amadu ya mirgina
ya goce ya bashi wuri Ragije
yayi karo da dutse ya fasa hanci
Amadu yasan hakan bai ishe shi
ba yasa kafa yana a kwancen ya
tokareshi a habarshi ya cilla
dashi can gefe guda ya hadu da
iro bahago suka ci gaba da
sumarsu tare
Sadi ya rude da yaga Amadu ya
sumar da yaransa uku saura
hudu suka rage wadanda ya
taho dasu ya dubesu su dukansu
yace dasu a fusace
Me kuke jira dashi kuna kallonshi
yanayi mana illa ? ku
tarar masa mana ku cinyeshi
danye.
.
Sauran kartin hutu Wurure da
Gwanyo da martai ajali sai kuma
shagon ajagu suka fadawa
Amadu baligi kamar kuraye sun
sami akuya a daji Amadu yasan
bazai iya karawa dasu su duka
ba a lokaci daya zai iya amsar
mutum biyu yayi fada dasu
amma bazai iya ja da mutum
hudu ba a lokaci guda
Don haka sai yaja baya bai yarda
sun cakumeshi su duka ba ya
rika kai musu duka dai-dai da
dai-dai idan ya sami sa'ar
wannan ya mangara sai ya
komawa waccan ya buga sai yaja
baya ya ruga idan wani ya taso
mashi sai ya nausheshi
Sun dade a haka suna bugi in
buga basu sami nasarar yiwa
Amadu tarko ya fado tsakiyarsu
ba a haka sai da ya galabaitar
dasu suka gaji da ya tabbatar
karfinsu ya ragu sosai sai ya fada
tsakiyarsu yanzu kam zai
iya amsarsu su duka hudun
tunda dai sun dawo kamar karfin
mutum biyu
Shagon Ajagu ya fara bazarwa a
kasa ta hanyar tokareshi da
kafa a kirji sannan ya duka a
lokacin da warure ya aiko masa
da tasa kafar kafin kafar warure
ta gama yawo a saman
ne ta dawo kasa Amadu ya
kama daya kafar ya goceta
warure yayi sama kamar toton
masara duk da girmansa koda
ya fado kasa baiyi yunkurin sake
tashi ba don kuwa akwai
yiwuwar kashin bayansa ya
motsa sosae
.
Martai ajali ya fadowa Amadu
suka nufi wata kayar dundu
suka afka ciki Amadu yaci
maganin tsini don haka kayar
bata raunatashi ba martai ya
makale a cikin kayayoyi yana
kokarin banbare kanshi da kyar
ganin haka sai Amadu ya sake
danneshi ciki sosai ya barshi a
haka ba tare da ya jigatashi ba
koba komai martai zaisha wuya
kafin ya iya ciro kanshi a cikin
kayoyin da suka sossokeshi
Saura Gwanyo wanda tuni ya
gama razana amma saboda
karfin hali bai fasa garzayowa ya
cakumi Amadu ba sai da suka
hadu Amadu yaji zafi a gefen
cikinsa ya ture gwanyo gefe
guda yaja baya ya taba inda yaji
zafin da hannu ya shafo jini sai
a lokacin ya fahimci aikin
wukane
.
Amadu yasan wuka bata kamashi
to amma..
.
AMMA ME KUMA ?
HABA UBAN BALIGA ME YAKE
SHIRIN FARUWA NE HAKA ?
21 Loading
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWA
KAZAR KARFI--> 21
.

.
SAI da suka hadu Amadu yaji zafi a gefen cikinsa ya ture
gwanyo gefe guda yaja baya ya
taba inda yaji zafin da hannu ya
shafo jini sai a lokacin ya
fahimci aikin wuka ne
Amadu yasan wuka bata
kamashi to amma dai yaga
kwallin balati a hannun gwanyo
yaja daga saiya daina mamaki
don kuwa wani mafarauci daya
bashi lakanin wuka ya taba fada
masa wani sirri dake tattare da
balati yawanci da ita mata suke
yanka kayan miya a gida A
cewar mafaraucin duk taurin
mutum ko maganin me yaci da
ka dauko wukar da mata ke
yanka albasa ka danna mashi zata wuce kamar ka sami
kubewa ko kankana!
Gwanyo ya sake garzayowa rike
da balati Amadu ya goce ya
kauce gefe daya ya hambari
gwanyo a baya ya kara masa
gudu gwanyo yaje ya hadu da
itacen tsamiya ya watse kasa
goshi yana zubar da jini kamar
an bude famfo tuni ya saki
wukar tasan inda dare yayi mata
.
Tun kafin Amadu ya juya bangaren da SADI yake yaji ihun
talatu a lokacin ne yaga tuni har
sadi ya kwanceta ya shake
wuyanta da hannunsa daya ya
hadata da jikinsa yana rike da
guntuwar bindigarsa a daya
hannun wacce ya tsorata Amadu
baligi da ita a daren da ya
gabata ka tsaya a inda kake idan ka
motsa daga nan zan harbeta
kaima kuma zan harbeka yanzun
nan
Sadi ya gargadi Amadu da
kakkausar murya
Amadu ya tsaya a waje daya yana
kallonsa
Sadi ya daka matsa tsawa
"Ina KAZAR KARFIN da kaci a wajen wasa dazu ? naga ka taho
da ita yi sauri ka dauko min ka
jeho min
ya sake dannan kan bindigar a
goshin talatu tayi kara mai
razanarwa Amadu ya daga
hannayensa sama ya juya inda ya
ajiye kudin da yaci a wurin
damben ya duka ya dauko su da
hannu daya a cikin jakar ya juyo
inda sadi yake tsaye rike da talatu
"jefo min jakar ka koma baya...
Kada ka sake matsowa inda nake
zan harbeka kai da ita
Amadu ya tattara karfinsa waje
guda yayi saitin fuskar sadi ya
cilla masa jakar kamar kibiya
jakar ta sameshi fas ta bugi
idanunsa yayi baya kamar zai
fadi bai san lokacin da ya saki
talatu ba
Amadu ya tashi cikin sauri ya
fitar da kafa daya ya doki sadi a
daidadi tafin hannunsa dake rike
da bindigar sadi ya jefar da ita
saboda karairayewa da yatsunsa
sukayi sakamakon dukan da
Amadu yayi masa
.
Talatu ta kauce gefe daya a
tsorace ta tsaya baya tana kallon
fadan Amadu da sadi kare garke
kamar yadda taga sauran fadace-
fadacen da suka wakana a
gabanta sadi yana kwance a
kasa kafin Amadu ya dira kanshi
tuni har ya jawo kaho ya kaiwa
Amadu suka ta gefen hannun
Kahon yayi saitin idonsa daya
Amadu yaji zuke" to amma duk
da tsinin kahon bai sami idonsa
ba ya sami gefen fuskarsa
kahon bai hudashi ba saboda
wannan alkawari ne a tsakaninsa
da tsini sai dai yaji zafi sosai
saboda dafin dake tattare da
zafin dukan
Amadu ya fadi baya sadi ya tashi
a fusace kamar bai nakasa ako
ina ba" yayi tsalle ya dira akan
Amadu baligi ya shake wuyansa
da karan hannuwansa ya
danneshi
Amadu yayi kokarin mikewa ya
kasa ya fara tirje-tirje a kasa
talatu ta fara kuka don kuwa
yanzu ne Amadu yake shan wahala
.
Amadu ya tattara karfinsa waje
guda ya fara bude rikon sadi ya
naushi kirjinsa sadi ya kife baya
kamar an jefar da diron mai
Amadu ya tashi da kyar saboda
ya galabaita" da kyar yake iya
numfashi
Sadi ya mirgina cikin sauri ya
jawo bindigarsa Amadu ya
kabeta a hannunsa ya nuna
Amadu da ita yaja baya don ya
sami damar da zai harbeshi
sosai Amadu bai nuna alamar
ya tsorata ba a wannan karon
sadi ya dora hannunsa akan
kunamar bindigar ya harba bindigar amma bata tashi ba
sadi ya sake danna kunamar
bindigar taki tashi Amadu yayi
masa murmushi yace dashi Ka daina wahalar da kanka sadi
bazata tashi ba tun farko dama
ina sone mu gwada karfi ni da
kai shiyasa na nuna maka na
tsorata da bindigarka
Sadi ya saki baki a tsorace ya
tashi ya sake komawa baya ya
nisanta kanshi da Amadu
wanda ya taso ya biyoshi
Sadi yace dashi a fusace
Na yarda kafi karfina yanzu.....
Amma zan sake yin shiri na
musamman a kanka saina ga
bayanka Amadu ka guji haduwata da kai a lokaci na gaba
.
Yana gaba fadar haka ya ciro
wata laya yasa a bakinsa ya
cizata ya bace bat!!
kamar walkiya ko sama ko kasa
Amadu yayi ajiyar zuciya ya juya
inda talatu take tsaye
ta tambayeshi a tsorace
Ina yake Amadu ina yaje ? kada
ya fito ya kashemu bamu sani ba
Amadu baligi yayi mata murmushi
Bazai sake fitowa ba talatu yaji tsoro ya gudu amma zamu sake haduwa watarana Idan kere
yana yawo zabo yana yawo ai za'a hadu
yace da ita cikin sauri
zomu tafi gida duk ke kika jawo min wannan wahalar
dama na fada miki ko ina kika
shiga a duniyar nan saina biki na
mayar dake gida kin sha wasa
nake yi maki ko talatu
.
Yarinyar ta fara neman afuwar
Amadu tana kuka
Don Allah kayi hakuri yaya
Amadu wallahi bazan sake guduwa ba daga yau ka yafe min
Amadu yace da ita....
.
ME KUMA YAKE SON FADA MATA ?
.
KU BIYO NI DAN JIN YA ZAKA ƘAYA
. . . .KAZAR KARFI--> 22
.
LAST PAGE--> THE END
.
@ YARIMA A. GANGARIYA
.
Amadu yace da ita
shinkenan! Mu tafi gida ko ba
komai a dalilinki ai gashi na wasa
jinina na rabu da samun wannan damar kada kiso kiji
farin cikin da nayi don in ba ana
haka ba sai jinin mutum ya
kwanta ya mutu
Amadu ya dauki jakar kudinsa ya
tasa talatu suka tafi suka bar
dajin tare da karti bakwai din da
ya bazar dasu fululu a wajen
wata kila su farfado su dawo
haiyacinsu a kwanaki biyu masu zuwa sunci sa'a don kuwa
hannun Amadu baligi gudumace
lafiyayya a boye ba tare da kowa ya sani ba
Tun sanda ya fara dambe ya
nemi lakanin gudumar makera
dake dukan mutane aka kamar da hannunsa yake aiki
shi kadai kawai yake iya ganin
gudumarsa amma ba hannunsa ne yake irin wannan ta'asar ba
.
KAMMALAWA
Ina yiwa daukacin jama'ar da
suka bibiyeni a wanga dan
guntun labari kuma suka bani
karfin gwiwa ta hanyar comment
ALLAH yayi muku albarka ya
kuma albarkaci rayuwarku
.
Wadanda kuma burinsu kawai su
karanta labari ba tare da sun
mika comment nasu ba suma ina godiya gare su matuka wayanda kuma basa son ganin rubuce-rubucena sai dai
suyi hakuri ba tare da goyon
bayansu ba Allah ya sanya mun
karasa wannan labari lafiya
.
BaZan cikaku da surutu ba bara
in karkata birona In koma bakin Zaren labarin" saboda nasan kun
kagu kuji karshen labarin Amadu
baligi da kuma talatu
.
Da komawarsa gida lokacin da
Alhaji Danjuma yaga 'yarsa talatu
ta dawo gida Amadu baligi kuma yana shirin tafiya saiya
rikeshi ya kara yi masa godiya
sannan ya rokeshi ya taimaka
masa ya auri talatu tunda dai su
tafi karfinsu amma shi zai iya riketa
"Idan baka aureta ba bamu san
yadda zamuyi da ita ba ka
taimaka ka aureta Amadu da zaran ka tafi zata sake guduwa
.
Amadu yace dashi
"to Alhaji kaga bani da daki ban
shirya yin......"
tun kafin ya karashe korafin
Alhaji Danjuma yace
zanje insa a gina maka dakin da
zaku zauna" kai in kana da fili na
amince zan gina maka gidan da
zaku zauna" ka taimakeni"
.
Amadu ya sake cewa
"matsalar bani da kudi a hannuna ne yanzu Alhaji
Alhaji Danjuma yace
"Banason ka kawo komai ko
kayan lefe bance kayi ba ka
kawo sadaki duk abinda Allah ya
hore maka ka kawo zan amsa
.
Amadu ya sake cewa
Bayan anyi auren ne Alhaji bani
da sana'ar da zan rike mata yanxu saboda.....
Alhaji Danjuma yace
zan rika aiko maka da abinci da
kudin da zaku rika kashewa iya
bukatunku kai da ita idan ba kai din ka aureta ba hankalinmu
bazai kwanta ba bazata zauna ba
.
GODIYA
Ina kuma gaishe da daukacin
jama'ar dake biye dani awannan labari musamman ma members dakuma jajirtattun Admins dake group dinmu mai albarka na
"TASKAR GIDAN LITTAFI" Ƙarkashin Jagorancin Jajirtattun Shuwagabannin mu dakuma ilahirin members
Wanda bisa tallafinsu wannan labari yazo karshe
.
Kada ku gajiya ku biyoni har
yanzu birona aiki Yake bazan
dage ta ba daga bakin aiki ba har
sai nazo karshen wannan labarin na
KAZAR KARFI
.
Amadu baligi ya amince da yaji
saukin yakai sauki da ya koma
gida ne ya sanarwa iyayensa ya
sami mata zai aura su kansu sunji dadi don kuwa a yadda
Amadu baligi ya baci da neman
mata ba wanda ya zaci zai taba
yin aure a duniya don haka tanan ana iya cewa SAM bARKA!
.
Anyi haka da wata biyu aka
daura auren Amadu da talatu
Idan ya ajiye kara bata isa ta
tsallaka ba saboda tsabar
biyayya" Idan kuma yace ta zauna a guri to ko kwana zatayi
bazata motsa ba a wajen sai yace
ta tashi
Aikin gida kuwa ba kama
hannun yaro sai ya bari manyan
wandunansa sunyi datti sannan
ya tattarosu ya watso mata su ba
kudin sabulu da ruwa zata wankesu fes!
surfe da hannunta take yi kuma
a dutsen nike take yin markade
baya bayar da kudin nika
to dama dai ance maganin shege
dan banza dole Amadu baligi zai
iya riketa" da wani mutumin
arziki ta aura da yanzu tana can
tana gasa masa gyada a tsakiyar
kai
.
Bana gajiyawa da nuna farin
cikin akan zuwa karshe wannan
labari" tabbas akwai manazarta
da suke bibbiye dani a wannan labari
na kuma yaba da kokarinsu
Godiya nake musu mai tarin
yawa sai kuma Allah ya sake sadamu a wani sabon labarin
mai SUNA........
.
Bari in sake karkata birona
saboda babu dalilin da zai sanya
in bata muku lokaci saboda akwai sauran labarin
.
Alhaji danjuma yayi zaton idan ya
rabu da talatu shikenan masifu
sun daina fado masa to amma
tunda talatu tayi aure sai kuma
matansa suka dawo suka fara
bugi in BuGA
kwari ta dauki tabarya ta
rotsawa amarya kai aka je kotu
akayi shari'a ya kashe kudi
.
Anyi haka bada dadewa ba
annobar faduwar motoci ta
sameshi" ba ayin wata sai
motarsa tayi hadari ba'a jima ba
duk motocin suka balbalce suka
kare da aka gama aikin gona an
tara buhuhhunan a sito sai
gobara ta tashi a ciki ba'asan ko menene musabbabinta ba
.
Bala'i dai yayi ta rafkowa dukiyar
Alhaji Danjuma tako ina daga
wannan sai wannan aka rasa
mafita
:
ABINDA BAI SANI BA SHINE
ZAKKAR DA BAYA SON FITARWA NE
TAKE FITAR DA KANTA BA TARE DA
YA SANI BA"
.
KARSHE....
.
DAGA FASIHIN MARUBUCIN NAN
SHAFI'U DAUDA GIWA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment