Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*Mallakar*
_AUTAR MANYA_🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿️ *1*


Daƙarfin gaske ya bugi ƙaton table ɗin dake gabansa wanda yake shaqe da tarin takardu, sannan ya ɗago rinannun idanunshi waɗanda suka cika da zallan ɓacin rai marar misaltuwa ya zubasu akan p.a wanda yake gurfane agabansa cike da ɓarin jiki dana zuci.

"Me kake son kacemin _P.A_ kana nufin aikin da mukai ya lalace"!! yafaɗi maganar fuskarsa cike da tarin bakin ciki marar misaltuwa.

Wanda aka kira da p.a ne ya qara rissinar da kansa a qasa tare da kallon uban gidan nasu cikin rawar jiki.

"Wallahi tallahi nima ɗazu habu wakili yake sanar dani cewar aikin da mukai a Ɗawisu l.g ya lalace sannan kuma ansamu wasu ɓata garin samari sun haura cikin makarantar ƴammatah ta ɗawisun har sunyiwa guda uku fyaɗe" yakai maganar yana sadda kansa a qasa batare daya kalli uban gidan nashiba.

Rintse idanunshi yay harna wajan mintuna biyar kafin ya warasu yana bin _p.a_ dasu cike da tarin ɓacin rai ya ɗaga masa hannun alamun yabar masa office.

Cike da sassarfa _p.a_ ya miqe ya nufi hanyar barin office ɗin.

Tare da qara rissinawa yace. ALLAH ya taimaki _Megirma *MAS*!_ yakuma huci zuciyar ka mutumin qwarai fari mai farar zuciya sukari bakai farin banza ba yaro mai jini ajika wanda duniya take yayi ALLAH yacigaba da dafa maka adukkan lamuranka yasa maqiyanka suzama fadawanka!!

Yana kaiwa nan yaja masa qofar office ɗin ya fita sanin halin _mai girma *MAS* mutum marar son yawan kirari ko fadanci.


Da sauri ya koma da baya ya faɗa saman kujerar office ɗin nasa ya ɗaga kansa sama yana kallon rufin p.o.p office ɗin cike da bakin ciki yana ayyana yadda zewa ma'aikatan daya baiwa wannan contract ɗin rashin mutunci danshi mutum ne tsayayye sam baya son, son zuciya shiyasa baya zama da duk wani mutum marar amana.

Cike da qwarin gwiwa ya ɗauki wayarsa wadda take yashe a saman table ɗin yafara neman layi.....

Ringing biyu aka ɗaga daga can ɓangaren tare da cewa."ALLAH ya taimaki _Maigirma *MAS*........"

Bai tsaya jiran cigaba da maganar na cikin wayan tashiba yafara magana cike da ɓacin rai "Haba sardauna yaya zakuyi mana haka mu baku aiki amman kuyi mana almun dahana kasan dai halina kuma kasan waye ni natsani rashin gaskiya arayuwata wannan dalilin yasa waccan tafiyar ban baku aiki ko ɗaya ba" yakai maganar yana komawa ya lafe a saman kujerar daya ke kai.

Cike da bakin ciki wanda aka kira da sardauna ya mayar da abinda ya taso masa zuciyarsa tare da qaqalo murmushin qarya sannan ya soma bawa _Maigirma MAS_ hakuri tare da cewa shima bai san haka yaransa sukai aikinba amman gobe monday zeje yagani,


Batare daya tanka masa ba ya katse kiran cikin rashin jin dadi.

Kiran sakataren sa yay a waya ya sanar masa. ya cewa _p.a_ ya kai masa jaka mota ya tashi. Cikin muntuna biyar ya haɗa tarkacan sa yabar office ɗin ransa duk ajagule.

Dagudu gourd's ɗinshi suka rufa masa baya tare da saurin bude masa marufin wata shegiyar mota ya faɗa cikin gajiya yana gyara links ɗin hannun rigarsa.

Acikin mintunan da basu wuce goma ba motarsa tabi hanyar babban titin cikin garin ƊAWISU.


Gabaki ɗaya kowa yaga yadda manyan motocin bayan motar daya ke ciki, suke gudu yasan babu lafiya dan haka jama,a sukaita matsawa suna bawa motocin hanya waɗanda aqalla zasuyi guda goma.


Bai sanar da ƴan jarida ko wani cewar ze fita ba dagashi sesu habu p.a da sauran gourds ɗinshi haka suka nufi cikin garin ɗawisu.

Wanda zuwa lokaci kaɗan zancan zuwan bazatan da *ƊAN MAJALISA MAI GIRMA SANATA MUHAMMAD ANWARR SAMEER ( MAS )* yay cikin garin ɗawisu ya gama cika gari wanda yasa ma'aikatan sardauna constuructions suka shiga ɗimuwa

Abakin tafkeken qaton gate ɗin makarantar *ƊAWISU BORDING SCHOOL* ya dakatar da drivern sa da kansa ya buɗe marufin motar tare da ziro da santala santalan fararen qafafunshi waje.

Cikin azama duk wasu masu bashi tsaro sukayo caa! akansa tare da rufa masa baya wanda ya taka da qafafunshi har cikin makarantar.

Da gudu - gudu principal ɗin makarantar tayo wajansa wadda zancan zuwansa ya kaɗa mata ciki zubewa tai agabansa tana kwasar gaisuwa sannn ta miqe tai masa jagora har wajan aikin daya bayar na kwangilar sola.

Zagaye yay sosai acikin makarantar sannan ya koma can wajan office ɗin principal inda aka miko masa farar kujera ya zauna akanta.

Da rikitattun idanunsa waɗanda suke kama dana maijin bacci ya dubi. p.c yana jefa mata tambayoyinsa masu kama dana ɗan jarida akan yadda akai har garada suka hauro cikin makarantar batare da malamai ko ita sun luraba wanda alhakin kula da students ɗin akansu yake.

Gumine ya tsurgo mata sannan ta soma basa haquri akan wannan lamari tare da shaida masa qaddara ce babu yadda zasuyi.

Taune qasan laɓansa yay yana jin tsigar jikinsa tana miqewa babu abinda yafi tsana a duniya kamar zina babban abinda yake ɗaga masa hankali yaji anyiwa ƴammata ko yara fyaɗe wallahi jiyake inda zega waɗannan garadan da babu abinda ze hana ya kashe tsinannu.

Ɗago idonsa yay ya kalli p.c sannan ya nemi data turo masa dukkan wasu masu ɗankwali na cikin makarantar da kuma mamomin ɗakuna dan yana son sanin asalin yadda lamarin ya faru.

Cike da sauri p.c ta baxa sakonsa sannan ta koma ta tsugunna agabansa tana jimanta abun aranta.


Hostel!

Dagudu wata baqar budurwa mai ɗan tsaho ta, taho wajan wata farar yarinya mai ɗan tsaho kaɗan marar jiki wadda take ɗaure da ɗaurin kirji ajikinta tana wanke hause ware masu kalar blue.

Cikin haki ta karaso gabanta.
Ɗaka mata duka tai tare da cewa.
"F.K kizo kece shugabar makaranta wallahi *ƊAN MAJALISARMU* yazo akan zancan haurowar da yaya gardi yayi kuma ya nemi da akira duk wasu masu ɗan kwalin cikin makarantar nan yanxu haka p.c tana can tana nemanki ashe kekina nan kina wanki.

Wadda aka kira da f.k ita ta ɗago da sauri tana kallon wadda take mata maganar cike da sanyin hali "kai lebour ni wallahi harkin bani tsoro wallahi canake wani gardin ne ai wannan murya haka"

Dariya lebour tai sannan ta kalli F.K malama nasanki da sanyin jiki sefa kinyi da gaske sabida kiran gaggawane dan ALLAH kada ki tsaya wannan yangar taki.

Tsaki F.K tai sannan ta tsame hannunta ta wanke ta nufi hanyar ɗakinsu.

Kwanarsu taje ta dauki qaton hijabi har qasa sannan ta dubi walida wadda suke kwana ɗaya da ita cikin nutsuwa "walida zanje kiran p.c dan ALLAH ki tsaman idomie ta kada ta jiqe takai maganar a nutse" wadda ke zaune daga gefe tana karatu ta ɗago ido ta kalli f.k.

"Waidaman feenah baki ci abincin nan ba tun ɗazu nifa narasa kanki tunda muka dawo daga wannan hutun naga kin sauya sanyin jikinki ya qaru kodai su baffa ne suka kuma...." kallon walidan tai cikin basarwa "nidai idan naxo mayi magana dan ALLAH ki tsaman" takai maganar tana futa daga cikin kwanar tasu.

Hanyar area class tai cikin sanyin jiki wai ahakama tana sauri.

Adai dai bakin office ɗin p.c taji sautin bugun zuciyarta yana qaruwa fiye da nada wanda qaddara tasa ta gamu dashi batare data shirya ba.

Addu,a tacigaba dayi hartaja qafafunta zuwa bakin office ɗin.

Seda ta kutsa kanta sabida yawan jama,a ga security's kota ina ga malamansu haka ta samu ta qarasa wajan da aka ce musu su taru ta tsugunna tana saukar da kanta a qasa.

Yawan bugun zuciyarta da rawar jikinta dasuka tsananta sune suka saka babu shiri ta haɗe jikinta waje ɗaya tana tsukewa kamar maijin shigar sanyi.

Kafin taji wani daddaɗan mayen kamshin turare ya cika mata hancinta wanda take tunanin ina ta sanshi?

Ɗago kanta sama tai wanda adai dai wannan lokacin shima yake neman waje akan kujerar da aka ware masa dan ya zauna.

Cike da tsoro ta ware idanunta duka waje meya kawosa nan?".......



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*Mallakar*
_AUTAR MANYA_🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿️ *2*


Lumshe manyan idanunta tayi tare da sake warasu akansa tana jin wata iriyar nutsuwa ta shigeta kafin taji sautin bugun zuciyarta yafi nada qaruwa sosai ta shagala da kallonsa wanda takejin kamar ta dawwama a haka tana kallonsa batare data gajiyaba.
Cikin zuciyarta kuma matsanancin mamakine fall tayaya yazo cikin makarantarsu? ita data gansa a ƊAWISU GENERAL HOSPITAL har takai masa files ɗin kaka, anya kuwa shine kodai aljanine tayaya yazo a ƊAN MAJALISAR SU? Kuma ta gansa a matsayin likita wannan lamari ya cuɗa mata kanta ya hanata sukuni tabbas tana da tarin tambayoyi aranta amman babu mai bata amsarsu dan haka ta kuma jan jikinta ta tsuke tana ayyana koma dai waye shi ita taji ta gani!!
Ta cikin wutsiyar idanunta take kallon yadda yake motsa ɗan madai daicin bakinsa yanawa ɗaya daga cikin masu tsaronsa magana wadda ba lallai na nesa dashi yaji miyake cewaba.
Mintuna kusan goma suna tsugunne kafin taga p.c ta miqe tsaye tanawa baba vise magana wanda kafin hankalinta ya dawo kanta taji yana kiran sunanta.
"Nafeesa Kabeer" taji baba vise ya kira sunanta yana kuma umartarta data matso gaba ana son ganinta.
Cikin rawar jiki f.k ta miqe daman can ita bamai yawan magana bace ba sannan kuma batada sakewa acikin mutane tun fill azal balle yanzu dataga taron maza damasu ɗammara wannan dalili yasa tafara karanto addu,oi cikin bakinta harta samu ta qarasa gaban p.c ta sake tsugunnawa.

P.c ce ta umarceta akan ta matsa gabansa wanda faɗin hakan da p.c tai yakusan sakata ta ɗimauce bada ban qarfin addu,aba da tabbas seta faɗi a wajan.
Cike da sanyin jiki dana zuciya ta qarasa gabansa wanda yake zaune akan kujera ya ɗora qafa ɗaya kan ɗaya gefensa masu tsaronsa ne duk sun riqe bindigogi se wasu mutane daban dake bayansa suma a tsaye.

Agabansa ta tsugunna tare da mayar da kanta a qasa tana zana qasar gabanta da yatsun hannunta tana jin wani sanyi yana ratsata ga wata iriyar faɗuwar gaba data qaru acikin kirjinta.
Wata qwalla ta matso mai zafi tare da saka gefen hijabinta ta share a fakaice tana kallonsa yadda yay kamar bai san da ɗan adam a wajanba seda taga wani mutum ya risina yay masa raɗa a kunnensa sannan ya ɗago ya jefeta da wani shu'umin kallo mai kama dana raini da qasqanci.

"Ke"! yafaɗa muryarsa a daqile kamar wani basarake cike da saurin jiki p.c ta daka mata tsawa "ke nafisa ba magana ake maki ba" cikin sanyinta ta ɗago idanunta waɗanda suka soma yin jaa! sabida damuwar data taso mata ta diresu akansa tana kallonsa batare data tanka masa ba kuma batare data ɗauke idanunta daga kan nasa ba.

Cike da mamaki _mai girma MAS_ Yake kallon yarinyar gaban nasa wanda take yaji wani ɓacin rai ya ziyarcesa jiyana mata magana ta mayar dashi kamar wani wawa tsaki yaja kaɗan tare da lumshe idanunsa waɗanda yake jifanta da kallonsa na rainin hankali dasu kafin ya furzar da iska mai zafin gaske ganin tana son ta ɓata masa lokaci.
"Ke wace irin wawiya ce ana maki magana kinyiwa mutane banza hala bebiyace"! ya faɗi maganar muryarsa adake!!
F.k wadda ta shagala a kallonsa lumshe idanunta tai cikin muryarta mai dadin sauraro mai kama data mai jin sanyi ta fara magana "ALLAH ya baka haquri banji kaba" tana faɗin maganar taja bakinta tai gum jikinta duk ya dauki rawa sakama kon wani wawan kallon wulaqanci daya mako mata.

Ɗan tsaki kaɗan yaja cike da halin ko in kula yafara yi mata bayani akan yadda zasuna kula da ɗakunansu suna tsare kansu batare da sun jira malamai sunzo ba a yayin da garada suka hauro masu.
Cikin tattausan lafazi yake mata bayanin wanda idan ka kallesu seka rantse wata magana suke ta soyayya.
Abinda yafi bata mamaki yadda taga duk magana ɗaya seya lumshe idanunsa sannan yake faɗinta dalla dalla kuma yake mata maganar yadda zata fahimta sedai kuma ta lura kamar yanada ɗan saurin magana kaɗan.
Har yay yagama bayanin nasa bata fuskanci komaiba illa wata karin damuwar daya kuma jefata aciki tare da shiga ruɗun rashin makama akansa haka ta miqe jiki na rawa tai masa godiya tabar wajan.
Kafin ta qarasa wajan da aka tsaidasu taji maganganu sun karade wajan akan yay masu kyautar maqudan kuɗi.
Sallamarsu akai akan su tafi se an nemusu, inda shikuma ya miqe aka rufa masa baya ya nufi wajan ganin aikin daya zuba ai acikin makarantar.

HOSTEL

Tana tafe tana haɗe hanya kamar wata zararriya haka ta qarasa cikin ɗakinsu akwanar su ta yada zango tare da tube hijabin jikinta, da gudu walida tazo ta rungumeta "wayyo shugabar makaranta naji abin alkairi _mai girma MAS_ yabamu kyautar kuɗi masu yawa sannan yasa a dauke waɗanda akaiwa fyaɗe a fitar dasu waje aga lafiyansu mudai ALLAH yasa a rarrabamana kuɗinnan kinsan halin malaman nan kowa kansa yake gyarawa"
Ganin kamar f.k bata hayyacinta yasa walida taɓata "F.k lafiyanki kuwa?" ɗago kanta tai ta kalli walida da idanunta waɗanda sukai jawur! sannan ta mayar da kanta saman gado ta kifa tana kuka kamar babu gobe...
"Subuhanallahi Nafeesa kabeer lafiyanki?" walida ta kira complt sunanta, tare da kai hannunta ta ɗagota ta jawota jikinta tana rarrashinta "Dan ALLAH feena badan niba kigayamin abinda yake damunki bana son wannan zurfin cikin naki na fuskanci tunda muka dawo wannan hutun kin rage walwala ko muqamin da aka bakine bakyaso ko agidane su baffa sukai maki wani abun?" ko idanun kakane ciwonsu suka motsa?" walida ta jera mata wannan tambayoyin tana jiran amsarsu.
Seda tai kukanta mai isarta sannnn ta ɗago fuskarta tai jawur idanunta ya qara girma.

"Walida na shiga uku!! walida zuciyata batamin adalciba takaini inda zan wahala takaini inda za,a wulaqantani wallahi walida sonshi nake da gaske!!!
"Miyasa aduk sanda zan gansa seya gayamin baqar magana miyasa duk sanda zan gansa senaji kamar na mutu walida sonsa ze kasheni idan na rasu kicewa kaka akan sonshine" takai maganar cikin gushewar tunani tana kuka kamar zata shiɗe.
Cikin damuwa walida ta ɗagota "feena waye wannan ki gayamin a ina yake waye mai sa,a dayay nasarar samun kamilar mace kamarki?" takai maganar tana tallafo feena ajikinta.
Jada baya feeanah tayi tana jan numfashinta.
"Walida baya sona kuma nasan baze taɓa sona ba naganshi tun kafin nasan shiɗin ƊAN MAJALISSARMU ne naso shi tunkafin nasan shiɗinne walida na haɗu dashi ranar talata da safe acikin ƊAWISU HOSPITAL naje kai files ɗin idanun kaka sabida munji sanawar za,a tallafawa marasa lafiyar idanu mutum ɗari a wannan rana shine da mukaje muka samu shiga aka bani file ɗin kaka nakaiwa babban likitan wajan daxe ɗauki hoton idanun dasauransu naje office ɗin wanda naga anrubuta *DR. ANWARR S.* ajiki da manyan harufa da sauri na tura qofar office ɗin danna shigar da, qafafuna sedai kash nai rashin sa,a domin hango wani haɗaɗɗan kamilallan mutum danai zaune da glass a idanunsa yana rubutu da sauri da sauri da tulin takaddu a gabansa,ban tsaya kare masa kallo ba sedai gani guda nai masa yasami nasarar sace zuciyata, dirin tashin masifarsa acikin dodon kunnena shiya saka na yada file ɗin na gudu daga wajan ."shinke mahaukaciya ce daxaki shigomin office babu permision!! naji saukar amon daddaɗar muryarsa da sauri akaina yana surfan masifa wallahi walida tunda na baro asibitin haryau ban kuma ganinshiba se yau kuma kullum senayi mafarkinsa" takai maganar tana cigaba da kukanta.

Sannan ta cigaba.....
"Seyau kawai na gansa wai ashe shine ɗan majalissarmu mutumin danaji kowa yana yabonsa da fadar alkairinsa amman nikam senaga kamar ya tsaneni yauma seda ya kirani da wawiya, walida yaya zanyi nasanshi na shaqu dashi harma ya soni sannan ina son nasan tayaya ya zama ɗan majalisarmu bayan ni a likita na sanshi.........!!



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_

🌹 *ƊAN MAJALISA*  🌹
              ( Love story  )                    


*Mallakar*      
   _AUTAR MANYA_🌹   

~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_

                         🅿️ *3*


Kuka! Take kan jiki kan qarfi hartana jin numfashinta yana kokarin ɗaukewa, cike da tausayawa walida ta saka hannunta ta ɗago ta daga jikinta sannan ta soma magana.
"Dan ALLAH feenah kiyi shuru hakan nan mana akan namiji kike asarar hawayenki, wanda baima san kinayi ba, haba feenah kefa macece mai aji mai kamun kai mai ilimi da nutsuwa wadda take ganiyar quruciyarta akan me zaki zauna kina kuka akan sa" walida takai maganar tana goge mata hawayen dake sauka akan fuskarta.
"Walida dole nai kuka! idan ban kuka mai kikeso nayi?" shin wai kuka! a so qaryane?" tayaya bazanyi kuka akansa ba alhalin kukana shize saka naji sanyi acikin zuciyata" takai maganar tana janye fuskarta daga hannun walida.
Gabaki ɗaya ta riga tagama karyawa walida zuciyarta babu abinda walida take se hawaye ayayin dataga aminiyar tata tana kuka akan son wanda baima san da zamanta ba sam.
"Naji feenah na yarda so ba qarya bane ba, kuma so yana saka mutum yay fiye da kuka ma, amman ina horonki da kiyi haquri sannan kiyi addu,a matukar ALLAH yay zaku zauna waje guda dashi babu mai hanawa, dan ALLAH kibar kukan nan haka kisaka dangana aranki muyi karatunmu sosai batare da matsala ta afkuba".
Walida takai maganar cike da nuna kulawa ga aminiyar tata.
"Naji walida zanyi shuru na daina kuka amman tunani kam yanzu ma na soma wallahi nikadai nasan yadda zuciyata take masifar sonshi" takai maganar tana share hawayenta.
Cike da murna walida tace,"na yarda wallahi harnaji dadi dakuwa zaki ɗagamin hankali insha ALLAH zesoki so kamar yadda kike masa kuma da yardar ALLAH idan ya nazeer yazo kawomin provision zan ɗan tambayesa akan koze sanshi tunda ba ɓoyayye bane agarinnan" haka walida taitawa feena tattausan kalamai masu kwantar da rai harta samu ta miqe taje ya haɗa indomien data barwa walida ta tsame mata.
Koda ta zauna cin indomien kawai hango kyakykyawar fuskar gayen take wadda take qara dulmiyata acikin tafkin sonshi da begensa.
Tana gama cin indomie ɗin ta fita taje ta ɗebo wankin data gama ɗazu ta dawo kwanarsu tana ninke hause ware ɗin cike da sanyin jiki.



************

Cike da qarfin gwiwa yake taka qafafunsa waɗanda suke zube a cikin wani irin azababben takalmi mai rufaffan sama, cikin nagarta da qarfin da ALLAH madaukakin sarki yabasa yake duba ayyukan daya bawa kamfanin SARDAUNA CONSTRT. wanda zasu zubawa makarantar kwana ta ƴammata dake cikin qaramar hukumar ɗawisu wadda take cikin jerin qananan hukumomin dayake wakilta na'urorin hasken sola da kuma gyaran banɗakunan da zasuyi waɗanda aka sauya musu shadda da sauran, su..............................Rai bace ya juyo yana kallon habu p.a cike da ladabi da biyyayya p.a ya rissinar da kansa a qasa yana faman baza idanunsa kamar wanda za,a cewa katt! ya arce.
Fuskarsa hartai jawur abinka da farin mutum cikin kakkausar murya ya qara duban p.a a karo na biyu "wannan wani irin sakarci ne p.a haka na baku nace ku basu?" yafaɗa cikin wata iriyar murya kamar ba tasaba.
"I say! haka na baku tayaya nace ku gyara masu toilet's sakamakon kokensu danaji akan idan ruwa ya sauka
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment