Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yatsine tana cuna baki gaba, ba tare data amsa masa kalmomin yabonsa ba ta maida murtani da faɗin, “Kai yaya, dama zakazo ɗin amma kaki kirana ka sanarmin kuma? Gashi nacema su Nafy su jirani a gidansu saimu tafi tare?.
Murmushi yaɗanyi duk da yanda tai masan ya bashi mamaki, “Yi haƙuri Samie na, banzo danna hanaki ƙyautata zaman tareba, nazone dama na kaiki basai kinsha wahalar jiran abin hawaba?.
Yanzu kam sosai ta juyi ta kallesa, cikin waro masa manyan idanunta tace, “Ka kaini kuma yah Ahmad? Da wane motan??.
Huci yaɗan fidda mai ɗaci, dan ta fara ƙokarin janyo fusatarsa da wannan salon rainin wayon data ɗakko, amma kasancewarsa sonta na ɗawainiya dashi saiya sauke numfashi da ƙokarin hadiye dukkan fusatar tasa ya saki murmushi a karo na babu adadi.
“Banda abunki Samina ina naga mota, wannanma mashin ɗin Sufiyanu ne na aro danna sauƙaƙa miki wahala?.
“Tofa, to ALLAH yay mana maganinta ita wahalar, karka damu na hutar dakai, kaje kawai zamu tafine dasu Nafyn tunda kaga na musu alƙawarin binsu dan ALLAH?.
Wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi, sam baya ƙaunar alakar Samina da su Nafyn gidan ɗan-majillisa, amma ya kula yanzu dukkan hankalinta yana ga mu'amulantarsu. Ganin zata tafi yay saurin tsaidata ta hanyar faɗin,
“Okey to babu damuwa tunda kin samu abokan tafiya, ga wannan kozaki buƙaci wani abu a wajen?.
Har tayi niyyar wucewarta saita dawo baya jin ya ambaci kuɗi, babu kunya tazo ta amshe kuɗin dayake miƙomata canzazzu ƴan hamsin-hamsin rabin bandir ɗaya.
Godiya tai masa cikin ladabi, ta tura kuɗin a jakarta tare da sakar masa murmushi duk dan dai hankalinsa ya kwanta da barinta ta wuce ita kaɗai.
Ta ɗaga masa yatsun hannunta guda biyu alamar bye cike da wani salo.

Da kallo kawai ya iya binta tamkar wani soko, ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya yana nufar roba-roba mashin ɗin dayazo dashi kalar jaa, hawa kawai yay ya zauna yana kallonta harta ɓacema ganinsa, yanda take tafiyarta cikin yauƙi da yanga sai sonta ya kuma nunkuwa a ransa, yanason Samina so irin mai tsanani ɗinnan, dankuwa dashi ya girma a zuciya tun baima gama sanin ma'anar SO ɗinba.
Ya ɗauki kusan mintuna talatin a wajen kafin ya hau mashin ɗin yabar anguwar da tunanin ina ya dace ace yaje, dan shidai a yanzu ya koma majalisar abokansa dariya zasuyi masa, yanda ya fito yana ɓare-ɓaren jiki zaije yakai Samina, sai gashi Samina ta watsa masa ƙasa a ido, bayan kuma dama kullum abokansa na nuna masa yanzu Samina ta canja, ta fara fin ƙarfinsa amma sam yaƙi fahimtarsu balle ya yarda da batunsu.
Yawo yaytayi a gari, sai da ya fahimci man ciki yayi ƙasa kafin ya koma gida.
Ya iske abokansa na hada-hadar shiga sallar magriba a massallaci, dan haka shima yay haramar yin alwala domin samun jam'i.
Bayan an idar duk suka fito ɗai-ɗai zuwa majalisarsu da suka kafa a ƙofar gidan su Yakubu abokinsu, saboda baranda dake wajen, shikuma yakubu yanada shagon littatafan hausane da yake bada rancin da saidawa.
Hannu suka shiga bama juna suna gaisuwa, Ahmad ya miƙama Sufyanu key ɗin mashin ɗin yana faɗin, “Broth nagode, ALLAH ya bada ladan zuminci?.
Amin suka faɗa a tare, yayinda Sufiyanu dake amsar key ɗin ke faɗin Sharukhan ɗinmu nazata fa sai dare zamu ganka ALLAH, Amma kunyi saurin dawowa kaida gimbiyar taka?.
Murmushin yaƙe Ahmad yayi kawai, ya kishingiɗa kusa da Musa yana bama Sufiyanu amsa da, “Ai ba yaune ainahin bikinba fa, kamu sukayi yau shiyyasa, sai jibinema ɗaurin auren, kasan mata da shegen son bidi'a, shiyyasa a kullum ake ƙara nisanta talaka da samun aure cikin sauƙi?.
Cikin damuwa Rabilu yace, “Maganarka gaskiyane wlhy Ahmad, ba gamunanba, acikinmu nan wanene bai isa aurenba, kuma duk munada ƴammata amma babu kuɗin yin auren, to wai muma fa kenan dakeda sana'oi munkuma ɗanyi karatun, inaga waɗanda basuda sana'ar babu karatun kumafa?.
Salisu daya zabga tagumi ya wani marairaice fuska yana harɗe kafafunsa dake lilo a ƙasan benci, “Abokai wlhy bidi'oin biki suna taka rawar gani wajen ɗora mata a burin auren mai hannu da shuni, tana kuma jefa rayuwarsu a garari harma da ƙara yawaitar fyaɗe, yanzu irina masu ƙarfin sha'awa idan baka danne zuciyarkaba ai tuni zaka afkama ƴar wani ka jefa kanka a halaka da ƴan uwanka a damuwa ko?.
Lumshe idanu Ahmad yayi a hankali, dan maganar Salisu ta sosa masa inda ke masa ƙaikayi, yace “Uhumm? kawai ba tare da ya ƙara komaiba.
Hakane ya saka Sufiyanu da Yakubu dake kusa dashi kallonsa.
“Sharukhan yaya dai??.
Ameenu da tun ɗazun baice komaiba ya faɗa yana kallon Ahmad ɗin shima.
Buɗe ido Ahmad yay da suka canja launi zuwa jaa, yay murmushi kawai yana girgiza kansa.
Hakanne yasaka su cigaba da hirarsu akan matsalolin aure da burikan da mazan da ƴammata ke dorawa saboda son gasa da masu kuɗi keyi lokacin bikinsu.

Sallar isha'ice ta tadasu a majalissar, dukansu suka dunguma zuwa massalaci, akabar waɗanda zasu sake alwala irinsu Ahmad.
Bayan sun idar da salla zama sukai islamiyyar da suka tsarama kansu kamar yadda suka saba a kowanne dare, malam Sulaiman ne malaminsu, wato limamin massalacin, bayan ƙarin karatu yay musu nasiha kamar yanda ya saba.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai suka fito, kowa daga nan gida ya shiga domin cin abinci.

Tsakanin gidansu Ahmad da majalissarsu gida biyar ne, hakan yasakashi takawa a hankali suna tafiya shida Salisu da shima gidansu ke maƙwaftaka da nasu Ahmad, suna isowa kowa ya shige.

Gidansu Ahmad gidane na talakawa irin masu ƙaramin ƙarfinnan sosai kamar yanda kukaji tun a farkon labarin, ginine irin na zamanin daya shuɗe, duk da dai yana mulmule da suminti har jikin bango, amma kallo ɗaya zakaima gidan ka fahimci ingantaccen ginin daya samune yasaka sumintin daɗewa bai zabtareba, saika shiga soro biyu kafin ka iso ainahin tsakar gidansu, amma a shiga farkon gidan zakaci karo da turken awakine da mahaifansu mata ke kiwo, sai kejin kaji daga gefe wanda baida nisa sosai da ƙofar banɗakinsu.
A shiga farkon gidan ɗakunan kakanninsu da aka zagaye da katanga zaka fara iskewa, sai sashen Baba Iliyasu daga bangon gabas, sai sashen Baba Yusha'u mahaifin Samina daga can Bangon arewa, suna kallon sashin kakanninsu, sai sashen iyayen Ahmad a bangon yamma suna kallon sashensu baba Iliyasu.
Tsakar gida zaka fara tararwa, sannan kabi siririyar hanyar da zata sadaka da ainahin sashen da matan Baba Hamza mahaifin su Ahmad suke.
Ya shafa kan tunkiyar daketa ɓara kuka saboda rashin ganin ɗanta kusa da ita, “K dan ALLAH ki rage ihunan, tunkiyarnan sam baki da hankali akan ƴaƴa, inama ya shiga shima uban ɓarnar? Ahmad ya ƙare maganar yana leƙa ƙasan kejin kajinsu kozai gano ɗan jaririn ragon tunkiyar.
Can kuwa ya hangoshi kwance, dan haka yasa hannu ya zaƙulosa ya kai gabanta ya ajiye kafin ya shige ainahin cikin gidan da sallama.
Mahaifiyarsa da ƴar kunya ke tsakaninsu saboda shine na fari a gabanta ya fara cin karo tana ɗibar ruwa a tulun dake ƙasan barandar ɗakunansu cikin kofin silba.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tamkar batama gansaba, sai ƙannensa dake zaune a tabarma da fitila a gabansu sun baza littatafaine suka amsa masa, sai kuma Ayyah matar babansu ta farko dake riƙe dashi a ɗakinta data amsa itama daga cikin ɗakinta.
Ya gaida Gwaggo data gama zuba ruwan harta ɗora a tiren data shirya abincin babansu tana shirin ɗauka zuwa ɗakinsa, sau ɗaya ta amsa ta ɗauki tiren tai gaba abinta, yaɗan bita da kallo yana kauda kansa a lokaci ɗaya.....
Ayyah dake fitowa ta katsesa da faɗin, “Ɗan albarka ka dawo??.
Murmushi yay mata yana ƙarasawa gabanta da cewa, “Eh Ayyah na, ina yini??.
“Lafiya lau ɗan albarka, kaga tashi ga abincinka nan yau miyarka nasaka akai dole a gidannan, maza kaci karya huce, ga manshanu nan dana soya maka ɗazun?.
Cikin faɗaɗa fara'arsa ya miƙe yana faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi Ayyah na, ya jiƙan malam ya ƙara muku nisan kwana da lafiya?.
Amin ta faɗa ita da ƙannensa.
Baba dake daga can ɗakinsa duk suna jinsu shi da gwaggo, ba yaune suka fara ganin hakanba, dan soyayyar Ayyah da Ahmad ALLAH ne kawai yasan iyakarta, amma ba mutumba, inhar ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba itace ta haifesaba.

Saman tabarmar da ƙanwarsa Sadiya ta shinfiɗa masa ya zauna, tuwone na jar masara dayaji dahuwa ta ma'iya, sai miyar tafasa da akayita da gyaɗa sai ƙamshi takeyi, ya buɗe kwanon langa ɗan ƙarami da manshanun ke a ciki ya zuba, tare da barbaɗa yajin daddawa da shikuma ke a robar cingam.
Laumar farko daya kai ya lumshe idanu saboda daɗin da miyar tayi, Zainab dake ajiye masa ruwa tai ƴar dariya ciki-ciki, “Yah Ahmad kaji miyar ta haɗu ko??.
Idanunsa ya buɗe ya ɗaga mata kai kawai batare da yace komaiba.
Ayyah dake ƙoƙarin kunna redio ɗinta tai saurin faɗin, “To akku, ki tashi masa akai yaci abincinsa cikin salama?.
Baki Zainab ta kumbura tana barin wajen, hakan yay dai-dai da shigowar Mudanseer ƙanin Ahmad ɗin.
Sallama yay suka amsa, ya ajiye ledar hannunsa gaban Ayyah yana cewa, “Ayyah gashi nan inji Yaya Maryama, tace gobe insha ALLAHU zama tazo gidan?.
“Karma tazo? Ayyah ta faɗa rai a jagule.
Ɗago ido Ahmad yay ya kalli Ayyahn, kafin ya maida kan Mudanseer dake ƙoƙarin zama kusa dashi.
“Miya faru kuma da Yaya Maryaman??.
“Yaya abinda kasani kullumne dai, faɗa suka sakeyi da kishiyarta shikuma jakin ya daki yaya maryama ɗin, amma sai batazo ta faɗaba tai shiru, sai ɗazunne Inna Haule tazo da zancen gidannan?.
Shiru Ahmad yay kamar bazai tankaba, ya tsame hannunsa daga abincin da yakeci yana ture kwanon silbar gefe, miƙewa yake shirin yi Ayyah tace,
“Ɗan albarka dama ka zauna kaci abincinka, itafa ta zaɓama kanta wannan rayuwar, mizaisa ku zauna kuna ɓata ranku a banza, maza koma ka zauna ka karasa ci?.
Komawa yay ya zauna, danba tarbiyyarsu bace jayayya da maganar manyansu, Mudanseer ya ɗauki ruwan dake gaban Ahmad yasha tare da wanke hannunsa, cikin kwantar da murya yace, “Yah Ahmad babu tayine? Bayan ga ƙamshin manshanu inaji ya cikan hanci ɗan gatan Ayyah?.
Hararsa Ahmad yayi, amma baice komaiba, hakanne ya saka Mudanseer ɗin yin murmushi ya saka hannu suka cigaba dacin tuwon, wanda a yanzu Sam Ahmad baya wani ci sosai saboda damuwar halin da ƴar uwarsa take ciki................✍?




_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*



*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(4)*


.............Har suka kammala babu wanda ya sake magana, Ayyah natajin redionta, su Zainab kuma na Assignment ɗin makaranta.
Ahmad ne ya fara tashi, bayan ya wanke hannu ya shiga ɗakin Ayyah, kusan mintuna biyar sai gashi ya fito hannunsa ɗauke da ƙananun kaya, dukda ya zama saurayi har yanzu kayansa na ɗakin, dukda kuwa sunada nasu ɗakin a ƙofar gida, takalman daya fita dasu ya ziro hannu ya ɗauka ya maidasu cikin ɗakin, sannan ya saka silifas ɗinsa dake gefe a wanke.
Ficewa yay daga gidan batare daya cewa kowa uffanba.
Ayyah taɗan rage sautin redio ɗinta tana kallon Mudanseer dake kwashe kayan da sukaci abincin.
“Mudan banso kayi maganar yarinyarnan gaban ɗan albarka ba, yanzun nan saiya saka abun a ransa kasandai halinsa?.
“Wlhy nima Ayyah sai bayan na faɗa na gane nayi kuskure, dan sai sauke ajiyar zuciya yake?.
Ayyah tai shiru cikin damuwa.

Ahmad kuwa yana fita ɗakinsu dake a soro na farkon fita daga gidan ya shiga, ya canja kayansa kafin ya ciro wayarsa da screen ɗin yay rugu-rugu saboda azabar lalacewa yashiga neman Number Samina, harta yanke ba'a ɗagaba, ya sake kira a karo na biyu nanma babu amsa.
Bai gajiyaba ya cigaba da kira, sai da yay mata kira na takwas ne ta ɗaga kamar a fusace.
Sautin kiɗan daya jiyo yana tashine yasakashi saurin faɗin, “Wai Samina kina nufin har yanzu baku koma gida bane??.
Guntun tsaki ta saki yanda bazai jiba, daga can tana murguɗa baki da harar wayar, “Ai yanzu zamu tafi? ta faɗa a cinkin sanyin murya dan tsabar munafunci.
Kansa ya dafe yana gyara zama akan yololuwar katifar barcinsu, “Haba Samina, kinsan kuwa ƙarfe nawa yanzu? A matsayinki na mace ace kina waje har kusan sha ɗayan dare? Kina nufin da anan gidan kike zakikai wannan lokacin baki dawo bane? Koma shiyyasa kika tafi can ɗin danki samu lasisin yin yanda kikeso?!!?. Ya ƙare maganar a tsawace.
Sosai ta firgita, jikinta na ɓari cikin in ina ta shiga fadin, “To yaya amma kuma ni ba wani abu nakeyi mara ƙyau ba fa, Nifa wlhy wannan bin ƙoƙwanton da abokanka suka koya maka bana sonshi, ni dai subar haɗani dakai gaskiya, ahaka kake tunanin zamuyi aure babu yarda a tsakaninmu??.
Leɓensa na ƙasa yaɗan ciza yana cewa, “K banason iskancifa, ni kike faɗama wannan banzar maganar...??
Batama bari ya rufe bakinsaba ta katse wayar ta koma cikin rawa.
Innalillahi kawai ya shiga ambatawa da ɗunbin mamakin Samina, anya kuwa itace ma ta ɗaga masa wayar nan? To amma ai muryartace, kansa ya dafe cikin tsagwaron mamaki da damuwa.

Har Mudanseer ya shigo Ahmad bai saniba, Mudanseer dake tsaye kansa ya sake maimaita kiran sunansa a karo na uku,
“Yah Ahmad!!?
Aɗan firgice ya buɗe idanunsa dake a rine da duhu, tashi yay zaune sosai yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, “Mudanseer yaushe ka shigone??.
Zama Mudan yay kusa dashi cikin damuwa, “Yah Ahmad tunfa ɗazun na shigo, inata maka magana amma baka ko motsaba, halan zancen Yaya Maryam kasaka a ranka, kokuma yauma gimbiyar taka tayi wani tutsun??.
Guntun murmushi Ahmad yay yana kallon ƙanin nasa, yaɗan taɓe baki yana ɗage kafaɗu, cikin ƙoƙarin kauda maganar Samina yace, “Mudanseer, dolene halin da yaya Maryam ke ciki ya dameni, bansan miyasa ta kafe akan wannan rayuwarba, inajin takaicin yanda a kullum mijinta ke mata dukan kayan wanki amma bazata faɗaba, shin wai ita wane irin sone har haka a tsakaninsu da bazata rabu dashi ba?.
“To ni wlhy Yah Ahmad nama kasa fahimtar wannan al'amarin nasu, kaga kuwa yanda yaji mata wani mugun ciwo a hannunta?.
Babu shiri Ahmad ya miƙe tsaye yana faɗin, “Ciwo kuma? Amma ta zauna bataje asibitiba??.
“Wlhy batajeba in gaya maka, sai da naje na tasata gaba ƙyamis ɗin Shamsu, dama kuɗin ɗinkine ɗazun Farida ta kawo ina jira ka dawo na baka sai Ayyah taimin aike wajen yaya Maryam ɗin na iske halin da take ciki?.
Cikin tsagwaron takaici Ahmad ya jingina da bango yana lumshe idanu zuciyarsa na masa wani irin zafi, tsawon mintuna uku suna a haka kafin ya fice daga ɗakin yabar Mudanseer shima da nasa tunanin.
Shagon da suke ɗinki ya buɗe ya shiga, ta kowanne fanni ya rasa abinda ke masa daɗi, da ɗan hasken screen ɗin wayarsa yay amfani wajen haskawa ya nemo fitilar da suke kunnawa a shagon idan babu wuta, da yake suna cajinta da hasken rana ne, tayi ƙau da haske saboda ranar da aka zuba yau.
Ya sagalata jikin ƙusar da suke ajiyewa ya zauna a kujerar da tazama tasa, dan babu mai hawa wannan keken sai shi.
Ɓacin ran da yake cikine yasashi duƙufa kan aikin wasu kaya daya yanka tun jiya da hantsi, ɗinkin yake amma sam zuciyarsa bata wajen, tana can a tunanin Samina, ganinfa bazai iya daurewa ba saiya ja tsaki yana take keken ya tsaya da aiki, wayarsa ya ɗauka ya sake kiranta, ƙin ɗagawa tayi harta tsinke, ya ajiye wayar a wani yanayi.
Kamar zai haƙura sai kuma ya dai sake kira, tana gab da tsinkewa ta ɗaga.
Kafin yayi magana tace, “Na koma gida, harma na kwanta barci Hubby na, dan ALLAH kayi haƙuri ɗazun wayarce ta mutu ashe babu cajine?.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke murmushi na neman kuɓce masa, Murya a sanyaye yace, “To sannu da zuwa?.
“Uhumm? ta faɗa daga can.
Shiru sukayi su duka, jin hakanne yasa Ahmad cewa “Kiyi barcinki sai da safe, nima ɗinki nake ɗan ragewa?.
Kamar bazata amsa ba, sai kuma tace, “Ɗinki a daren nan Yah Ahmad??.
Murmushi yayi mai sauti saboda jin daɗin nuna kulawarta gareshi wadda ta daɗe batai hakanba, yace, “To Samie na ya na iya, na kwance ai baiga gariba?.
“Hakane Yah Ahmad, amma dai kaje ka kwanta kaima, sai da safe?.
“Nagode My Samie? yay maganar a hankali tamkar mai raɗa.
Itako daga can baki taɗan taɓe tana ajiye wayar da maida hankalinta ga Ma'aruff sabon saurayin da tayi yau a hotel ɗin da sukaje wajen kamun ƙawarsu, shine ya kawota har gida a mota, koda suka iso sai suka zauna hira bata fitaba duk da kuwa dare yaja, dan kusan sha biyu ma.

Kallonta Ma'aruff yay yana ɗan ɓata fuska, “Shi kuma wanene wannan??.
Ta ɗago manyan idanunta ta kalleshi da wani fari, “Karya dameka, yayana ne?.
“Yayankine amma kika nuna damuwarki a kansa harda kashe masa murya??.
“Wannan duk farfaganda ce dan a rabu lafiya?.
Shiru yay baice komaiba, ganin hakan yasa ta ɗakko masa wata hirar.
Da yake shima ɗan duniyane sai ya basar da zancen suka ɗora hirarsu.


______________★★★★___________

Ahmad kam kalaman Samina ne suka ɗan sanyaya ransa, ya jingina da bango yana lumshe idanu, shi kansa baisan iya adadin son da yakema Samina ba, bashi da burin daya wuce a yanzu ya mallaketa matsayin matarsa ta aure.
Yayi zurfi a tunani ya tsinkayo muryar Baba na faɗin, “Amadu! Kai Amadu shin barci kakeyine a shagon wai??.
“A'a baba?. Ahmad ya faɗa da sauri yana miƙewa tsaye.
A ƙofar shagon yaga baba tsaye, “Sannu baba, wani abu kake buƙata??.
“A'a babu komai, na fitone zan rufe gida saina leƙa ɗakinku naga Mudan ne kawai a kwance, shiyyasa nai tunanin ko kana nan, nakumaji ba ɗinkin kakeba ashe??.
Shafa kansa yay yana faɗin, “Eh wlhy baba, ɗinkin dai na fara sai kuma allura ta karye na tsaya sakawa, ashe babu mai ƙyau a shagon ma sai mun nemota da safe?.
“To ALLAH ya kaimu, ka rufe kaje ka kwanta hakanan, kanaji jiya sai da ɓarayi suka shiga gidan Alhaji mamman?.
“Wlhy kuwa baba, haka nima nakeji ɗazun da safe, ALLAH ya rufa mana asiri to?.
“Amin ya rabbi? baba ya faɗa yana juyawa gida.

Komawa cikin shagon Ahmad yay ya kashe fitilar sannan yazo ya rufe shagon ya koma cikin gida bayan ya rufe gidan.
Uzirinsa ya shiga bayi yayi, yay alwalar barci daya sabarma kansa kafin ya nufi ɗakinsu.

Mudanseer na ɓararraje a katifarsu yana jan nasharin barci, Ahmad ya shinfiɗa abin salla a gefe yana girgiza kai, salla ya tayar yay sha'i da wutiri, bayan ya kammala yay addu'oinsa ya cire

Please Login or Register in order to submit comment