Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinta
da niyyar kafasu a jikin wuyan mubnaika
ba zato ba tsammani sai macijiyar taji an daka mata tsawa daga bayanta
cikin tsananin mamaki saita tsaya cak ta fasa yin mugun abinda tayi niyyar aikatawa
ta juyo domin taga wane mai tsaurin idon ne yake yi mata wannan tsawar
ba kowa baneba face wani kyakykyawan saurayi mai suffa da shiga irin ta mutanen daular larabawa
rataye da wata sharbebiyar takobi da kuma kwari da baka abayansa
mubnaika ma da take kwance saita juyo da fuskarta ahankali don taga abin dake faruwa
koda taga wannan kyakykyawan saurayi sai yaji nan take zuciyarta ta buga da karfin gaske kamar zata fasa kirjinta ta fito waje
kuma wannan ne karon farko data fara
jin irin wannan yanayi ajikinta
ba komai
ya janyo mata hakaba face ganin wannan
kyakykyawan saurayi wanda yake tsaye abayan wannan macijiya
kai da gani kasan cewa ya cika jarumi na gani na fada
mai tarwatsa maza kuma afagen kyau kuwa
ko acikin mata asami mace mai kyan sama sai an bincika
ga shin kansa kuwa ya sauka har gadon bayansa
idan ka ganshi saika zata cewa ya fito daga wani babban gida sarautar ne
fatar jikinsa kuwa tamkar ta jariri wajen
sheki da walwali kai duk inda kyau yakai wannan saurayi
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMEN BAKAR GABA
PART
20
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Nan take mubnaika ta kurawa wannan saurayin ido ko kiftawa ma ta kasayi
sai gani tayi ya dako tsalle daga inda yake
ya bayyana tsulum agaban wannan macijiyar
itama macijiyar saita juya ta fuskance shi
suka kachame da sabon azababben yaki mai cike da razanarwa
nan take mubnaika ta raina kanta a fannin
jarumtaka ta sallamawa wannan kyakykyawan
saurayi domin ta fahimci cewa ruwa
ba sa'an kwando bane saboda ta gani da idanunta cewa
duk sanda wannan bakon jarumi ya sami
nasarar sarar jikin macijiyar da takobinsa
duk da cewa takobin bata tasiri ajikinta
sai taga macijiyar ta kwallara ihu saboda
tsananin zafi da radadin da yake ratsa cikin tsokarta da kuma jijiyoyinta
har saida aka shafe dakiku dari biyu amma macijiyar bata sami nasara akan wannan saurayin ba
saboda tsananin zafin namansa da ulliyarsa
har saida takai cewa kogon ya fara tsattsagewa
yana ruguzowa kasa yana danne abubuwan
da suke kwance akasa kuma har a wannan
lokacin mubnaika tana kwance a kasa ba
zata iya mikewa tsaye ba saboda buguwar da tayi
koda bakon jarumi ya fuskanci cewa idan
har baizo ya dauketa ba to tabbas za'a iya
samun akasi wani dutsen yazo ya danne ta ta mutu
koda gama yin wannan tunanin sai nan take
ya shammaci macijiyar ya sannan ya daka tsalle ya gabzawa macijiyar naushi acikin kwayar idonta guda daya
sannan ya sake yin wani tsallen a saman ya
dira a inda mubnaika take kwance ya shureta
ya azata agadon bayansa ya daure. ta Tamau da
wani rawaninsa a wannan lokacin
macijiyar
tana ta matagugu sakamakon tsananin
zafi da zugin da take ji sannan macijiyar
ta fara rikida sannu ahankali ta rikide
ta zama wata mummunar aljana
mai
matukar ban tsoro amma babu ido guda
daya sai kurmin ido wanda yake zubar da jini
cikin karaji da kururuwa aljanar ta nufo shi gadan gadan
cike da mummunan nufi domin ta kamashi
tayi gunduwa gunduwa dashi koda ta kawo
masa cafka da hannunta sai ya daka tsalle
sama ya kaucewa harin nata ta cafki iska
cikin zafin nama ya kai mata wani wawan sara da takobinsa
koda takobin ta hadu da hannunta sai wata kara ta tashi
kamar ta haduwar karfe da karfe
nan take ta dinga kawo masa mahaukatan hare hare
da nufin ta kamashi ta tsinkashi biyu
amma sai abu ya gagareta saboda tsananin zafin namansa
da kuma karfin gudunsa ta kasa samun damar chafkeshi
domin wani lokacin idan yayi tsalle sai kaganshi kamar tsuntsu mai fuka fuki
saboda karfin tsallen nasa domin yaki yarda ta ritsashi awaje guda saboda yasan indai ya bari haka ta faru tasa ta kare
babu abinda zai baka mamaki face cewa duk wannan gumurzu da akeyi akwai mutum agoye abayansa
saida ya zamana sun rushe kogon gaba daya saboda gumurzun da suke yi
ya zamana cewa guri ya zama filine fetal
kuma har sannan babu wanda ya sami nasara akan wani domin jikin aljanar gaba daya makami baya hawa
sai sannan bakon jarumin ya fuskanci cewa
acikin idonta ne kawai makasarta yake saboda haka dolene ya dinga kaiwa idonta farmaki
ita kuwa koda ta fuskanci manufarsa sai taki ta bashi damar yin hakan
daga can saita sami nasara ta yanki
kafarsa guda ta dama da kaifin facenta harsaida jini
yayi tsartuwa daga jikin kafar tasa sannan ta shureshi
da hannunta ta dagashi sama tayi jifa dashi
harsaida ya fadi can nesa da rufda ciki
sannan tayi tsalle guda daya ta bayyana a inda yake
ta sake shurarsa ta sake yin jifa dashi akaro na biyu
amma sai jarumin ya juya jikinsa yaki yarda ya fadi kasa
ya dira a tsakiyar kanta sannan yasa takobi
ya caka mata acikin ragowar idon nata
nan take jini yayi fashe daga cikin idon
nata cikin zafin nama ya kara daka tsalle
daga kanta ya dira akasa sannan ya falafala da azababben gudu
alokacinda itakuma ta haukace da kawo
masa mugayen hare hare domin awannan
lokaci bataji kuma bata gani don haka duk inda taga dama kai farmaki takeyi saboda taga ta sami nasara akansa
cikin kankanin lokaci ya bar wannan
waje itakuma tayita magagin mutuwa har saida ta mutu
saida ya tabbata ta mutu sannan ya sami waje y ajiye mubnaika wacce awannan lokaci tayi doguwar suma
sannan yaje ya tsinko wata siririyar jijiyar bishiya bushashshiya
ya dinke raunin dake jikin kafar tasa
sannan ya zuba wani garin magani akan raunin kafar tasa
bayan ya gama da raunin jikinsa ne ya sake juyawa kan mubnaika
koda ya kalleta awannan lokaci sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske
tamkar zata tsaga kirjinsa ya fito
ba komai
ya haddasa hakaba face sai asannan ne ya kula da tsananin kyawun da allah ya bata tamkar itace tayi kanta
atsawon yawon da yayi aduniya ya hadu
da mata kala kala amma bai taba cin karo
da mace mai kyawunta ba kuma gata jaruma
tabbas wannan kyakykyawar budurwa ta kasance 'yar baiwa irin wacce yake da burin samu amatsayin matarsa
nantake ya dauketa ya dora akan cinyarsa
ya kura mata ido sannan ya dauko ruwa
acikin battarsa ya zuba mata afuskarta
take ta farfado daga suman da tayi
ahankali ta bude idanunta
koda tayi arba da shi sai ta zaune zumbur
ta na mai kallon fuskarsa cikin rashin yadda
tace kai wanene ?
kuma me ka aikata mini?
ka gaggauta sanar dani gaskiya inba
hakaba na yakeka harsaina hallaka ka ko kuma ka hallaka nice
dajin haka sai ya bushe da dariya yayi ta yi kamar bazai dainaba
sannan ya kalleta yace
yake wannan kyakykyawar budurwa
me kike zaton na aikata agareki inbanda abinda duk wani da namiji mai lafiya zaiyi idan yayi arba da wannan kyakykyawar surar jikin naki
koda jin haka sai mubnaika ta fusata
tazare wata gajeriyar adda a kugunta
ta kawo masa wani mummunan sara da nufin ta tsarga kansa gida biyu
take jarumin ya sunkuya ta sari iska
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME

DOMIN SAMUN CIGABAN SAI KU KASANCE DA SHAFIN HAUSAEBOOKS.COM.NG
BAKAR GABA
Kashi na biyar 5
Littafin Habibullah Muhammad kabara
Ebook created by Shuraih Usman
Published at http://Hausa brooks com.ng








BAKAR GABA
PART 21
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Cikin zafin nama shima ya zare tasa
takobin ya mike tsaye tsam yana kallonta yana murmushi
take ta sake afkowa kansa cikin mugun
nufi tana kawo masa mugayen hare hare
tamkar tsofaffin abokan gaba
shi kuwa sai ya kasance yana mai kare harin nata
fuskarsa cike da murmushi wanda yasa
mubnaika ta kasa tantance wanne irin murmushi yake yi mata
shin murmushin mugunta ne ko kuma
na raini ne saboda yana ganin kamar ba zata sami nasara akansa ba?
wannan shine tambayar data ayyana
acikin zuciyarta sannan tayi kwafa aranta tace
lallai dan saurayi ka yaudari kanka
domin dan hakkin daka raina shine yake tsone maka ido
yau saina baka mamaki
tana gama ayyana hakan sai ta daka
wani mahaukacin tsalle sama ta sake kai masa wani mahaukacin saran da nufin ta tsarge bayansa
inbadon ya sa takobinsa ya kare ba
ya kare da tuni ta aiwatar da nufin
dake cikin zuciyarta
da ganin haka sai shima ya sake yin wani tsallen
ya koma baya chan taku goma sannan ya
kalli mubnaika cikin wani irin tattausan murmushi yace
tabbas na yarda ke jaruma ce amma
ina mai shawartarki daki sake zage damtse
idan har kinaso ki aiwatar da nufinki akaina
don huce fushin abinda na aikata agareki
kafin ya gama rufe bakisa ta sake daka tsalle asama kawo masa wani harin
cikin zafin nama yasa hannayensa guda biyu ya daki kafafunta dasu
take ta rikito kasa mai makon jarumin
yaje shi ya kasheta tunda tayi yunkurin
kashe shi sai taga ya mika mata hannu fuskarsa cike da kwalla
don ta kama ta tashi tsaye nantake kuwa
ta kama hannun nasa tana mikewa tsaye sai ta shammace ta kai masa wani suka acikinsa
cikin bakin zafin nama ya juya ta soki iska
sannan yasa hannu ya rike ta baya da hannun sa hagu
hannun sa na dama kuwa sai ya ritsata
da takobi yadda ba zata iya kwacewa ba yace
haba yake wannan kyakykyawar budurwa saboda me kike
burin ki hallaka wanda ya zo gareki da alheri
koma dai wanne irin laifi na aikata miki
ai ya kamata ki gafarta mini saboda ceton
rayuwarki da nayi a hannun wannan hatsabibiyar
aljana dajin wannan maganar sai jikin ta yayi sanyi
ta saki addar ta kasa sannan ta
juyo itama ta kalli wannan jarumin
lokacin da taji kunya ta kamata kanta
a sunkuye cike dajin kunya tace
yakai wannan bakon jarumi
kayi hakuri abisa abinda ya faru nida kai
tsananin bakin ciki ne bisa zargin cewa
ka lalata mini rayuwa alokacinda nake cikin halin suma ne yasa
nayi maka haka amma sai yanzu na
fahimci cewa zargin da nake akanka ba gaskiya bane
amma ka sani bani kadai ba dukkan wata mace
idan irin wannan abu ya sameta dolene tayi yunkurin daukar fansa.
sannan kuma ina mai godiya agareka bisa taimakon da kayi mini ka ceci rayuwata daga wannan shu'umar aljana
kai kuwa wanene kai kuma menene ya kawoka wannan daji mai hatsarin gaske?
dajin wannan tambaya sai bakon jarumin yayi murmushi sannan yace
ni sunana marwan kuma bakone ni a
wannan nahiyar hanyace ta kawo ni nan
zan wuce domin gabatar da sana'a ta ta farauta
sai na zo giftawa ta bakin wannan kogon dutsen na tarar da bakin
gumurzun da kukeyi ke da wannan aljana
na dade a tsaye ina kallon yanayin fadanki
kuma nayi matukar jinjina miki domin kin cika
basadaukiya kuma jarumar jarumai wacce
ta chanchanci ajinjina mata
amma
kuma sai naga an sami akasi macijiyar tana nema tayi nasara akanki wannan daliline yasa na bayyana kaina agareta na hanata aiwatar da mummunan nufinta akan kyakykyawar budurwa kamarki
dajin haka sai mubnaika ta tari bakinsa tace
kada ka fadi haka domin kaine jarumin jarumai
kuma gagara badau saboda duk abinda ka fada akaina ka fini kyau, karfin damtse da iya yaki gaskiya dole ne na jinjina maka kaima
nan take ta mika masa hannunsa suka gaisa sannan tayi masa murmushi tace
nikuma sunana mubnaika sana'ar farautace ta shigo dani cikin wannan daji
duk da cewa ban sami abinda nazo nema ba
ina mai matukar farinciki bisa samun abinda zai maye mini gurbin abinda nazo nema
wannan nasarar kuwa da nayi bata komai bace ba
face ta samun abokin da zan dinga ganin haskensa acikin zuciyata
wanda zai dinga maye mini gurbin duk wani abu wanda na rasa arayuwata
kuma shine zai zamo fitila agareni
wannan abu kuwa ba komai bane ba face kai
nan take ta tsugunna akasa bisa gwiwoyinta tace
ni
tabbas na yarda dakai na yarda kai mutumin kirki ne zaka iya rikeni amana
ina fatan zaka yarda ka bani soyayyarka kamar yadda nima nake nuna maka tawa soyayyar azahiri na cire kunya da girmankai irin namu na 'ya'ya mata
idan har ka yarda dani to nayi maka alkawarin
ko mutuwa bata isa ta raba ni dakai ba
koda jin wadannan kalamai na jaruma mubnaika
sai nan take jarumi marwan yaji kamar an zare masa lakar jikinsa
ya kame kyam atsaye kamar gunki
sai wani siririn hawaye da ya digo daga cikin kwayar idanunsa
jikinsa ya fara karkarwa kamar mai jin sanyi
ba komai ya haddasa haka ba face jin dadadan kalaman soyayya daga bakin mubnaika
kawai sai ya rungume mubnaika yace
mene zaisa na ki yarda da wannan kyakykyawan tayi da kikayi mini
hakika nayi farinciki da kika shigo rayuwata
yake mubnaika tun kafin ki furta mini soyayya zuciyata ta tafi cikin shaukin begenki
tabbas na yarda soyayya ta kan iya mayar da mutum biyu su zama daya
idan har kuwa hakane to dani dake mun zama daya
zuciyata ta zama tsagin zuciyarki haka kema taki zuciyar
rayuwata kuwa daga lokaci zata kasance cikin tunaninki
tabbas na tsinci soyayya adaidai lokacin daya dace kuma koda zan tsinci wata to ina yi miki rantsuwa bazan dauketa ba
kece zaki zama abokiyar rayuwata ta har abada
daga wannan lokaci shida mubnaika suka zama masoyan juna kuma
suka shaku sosai duk farautar da zasuje
tareda suke zuwa bayan 'yan kwanaki
kadan sai suka yanke hukuncin yin aure domin samun dorewar soyayyarsu
nandai marwan ya tambayeta akan me take bukata amatsayin sadakin aurenta dajin wannan tambaya sai mubnaika tayi dariya sannan tace
ai sadakin zaratan masoya guda biyu kamar mu dolene ya zama abu mai matukar wahalar samu domin ranar aurenmu ta zama abar tunawa agaremu
cikin murmushi ya kalleta yace me kike da bukata
nayi rantsuwa da girman soyayyata agareki ko menene sai na kawo miki indai akwaishi acikin duniyar nan sai na kawo miki shi
mubnaika tace
abinda nake bukata agareka kawai shine
ka samo
mini kan dabbar da tafi kowacce dabba girma acikin dajin nan
idan har kayi haka to tabbas ka zama mijina
dajin haka sai marwan yayi murmushi yace
indai wannan ne karki damu ki bani sa'a biyar zanje na dawo
nantake kuwa ya debi kayan fadansa ya daura su ajikinsa sannan ya kalleta cike da alamar bege yace
na rantse harda soyayyar da kike yi
mini idan na fita sai nayi nasara koda
kuwa abinda zan farauto miki yafi karfina
domin shi karfin soyayya yafi karfin damtse tasiri acikin zuciyar masoya
wannan shine dalilin da yasa na tabbatar miki da cewa saina sami nasara
yana gama fadin haka sai ya falfala da azababben gudu na gaban kwatance
wanda saida ya baiwa mubnaika mamaki saboda yanzu ne ta gane cewa tabbas tayi dacen masoyi
domin marwan ya tara duk wata baiwa da mace take bukata
gashi kyakykyawa kuma jarumi sannan ga kuma karfin gudu
cikin lokaci kankani ya bace mata da gani
haka dai marwan yayi ta yawo a cikin dajin yana haduwa da manyan namun daji
amma abin mamaki shine duk irin dabbar
da ya hadu da ita sai yaga taki ta kawo masa farmaki hasalima saidai yaga ta juya baya aguje don ceton rayuwarta
abinda bai sani ba shine
duk dabbobin da suke cikin dajin sun jiyo sanda yake fafata yaki da wannan aljanar kuma sun jiyo karar ihunta a lokacin da ya kasheta
shine dalilin da yasa suke tsoron rabarsa
wannan shine damar da ya samu ya dinga bin dabbobin daya bayan daya
yana nazarinsu amma bai sami wata dabba ba
wacce yake ganin ta cancanci ta. zama sadakin aurensa da mubnaika ba
don haka sai ya yanke shawarar ya kara kutsawa yaje har karshen dajin
koda gama wannan tunanin sai ya kara
falfalawa da gudun tsiya bai tsaya ba
saida yazo bakin gabar wani katon teku wanda gabarsa ta biyo ta cikin dajin
ga igiyar ruwa nan tanata kadawa
har wani tsiri takeyi acikin sararin samaniya
babu hanyar da zakabi ka wuce face ka ratsa ta cikin tekun
koda yayi arba da wannan teku sai ya tsaya cak
shi baiyi gaba ba kuma baiyi baya ba
yana tunanin me ya kamata yayi
shin ya koma cikin dajin ne ya farauci dabbar data samu ya kaiwa mubnaika
ko kuma ya shiga cikin wannan teku tunda
har ta ratso ta cikin wannan dajin don haka itama ai tana daga cikin dajin
idan har yanaso ya auri mubnaika dolene saiya sayar da rayuwarsa
ya shiga cikin wannan tekun tunda har ya riga yayi mata alkawari to bai kamata ya canja shawara ba
koda ya gama wannan zancen zuci sai kawai
ya falfala da gudu sannan yayi tsalle yadda kasan kifi
ya fada cikin wannan tukun
da shigarsa cikin tekun sai gashi yana tafiya yadda kasan wannan babban kifi ba bil'adama ba
domin tafiya yakeyi tamkar yana gudu bisa kan turba
amma wani abin mamaki shine
tunda ya shiga cikin tekun sai yaga babu wata babbar halitta guda daya acikinsa
sai kananan kifaye wadanda ko kasuwa idan kaje basayin daraja sosai
wannan al'amari ba karamin bashi mamaki yayi ba
domin wannan ne karo na farko daya taba ganin irin wannan a rayuwarsa
sai ya tambayi zuciyarsa yace
to menene ya hallakar da dabbobin da suke cikin wannan tekun ?
amsar daya kasa baiwa kansa kenan
amma sai ya kudurce a cikin zuciyarsa cewa
koma dai wacce irin halitta cewa
tayi wannan aiki saiya nemo ta kuma ya kasheta da karfin tsiya
yana cikin wannan tunani ne kawai sai ya hango wani
abu a gabansa
kamar tsuburi kuma a wannan lokaci ya fara
gajiya da tafiya acikin ruwan dole yana bukatar ya samu ya huta
saboda tafiyar da ya sha
nantake kuwa ya tunkari wannan tsuburin ya samu ya hau kansa ya zauna sosai kamar yana zaune a makwancinsa ba tareda shakka ba
HAKIKA RASHIN SANI YAFI DARE DUHU INDA ACE YASAN MENENE WANNAN TSUBURIN DA BAIYI GANGANCIN ZAMA AKANSA BA
Koda ya zauna akan wannan tsuburin
Bai wuce dakika sittin ba sai ya ga wannan tsuburin ya dare gida biyu
take wata kofa ta bayyana mai kama da baki
cike da wasu zako zakon hakora marasa kyan gani in ba don marwan yayi saurin kaucewa ba da tuni ya fada cikin wannan wawakeken baki
ba komai bane wannan halittar ba face wata rikakkiyar jiminar ruwa
kuma itace ta kashe duk halittun da suke cikin tekun
dama tun lokacin da marwan ya shigo cikin wannan tekun ta kula dashi lambo tayi masa don ya kansa gareta
Anan alkalami na ya tsaya sai na sayo wani
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME BAKAR GABA
PART 22
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Lokacin da jarumi marwan ya kaucewa faramakin da wannan
dorinar ruwa ta kawo masa Saiya nutse acikin teku ita kuma saita
hadiyi iska Ba shiri ta juyo izuwa bangaren da yake domin ta hadiye farat daya
Cikin bakin zafin nama ya zare takobinsa ya kare harin nata
Nan take suka kachame da azababben yaki acikin ruwan
Babu abinda zai baka mamaki da kuma sha'awa sai ganin
yadda jarumi marwan yake iya fada da wannan dorinar
ruwa tamkar akan kasa yake ba wai acikin teku ba
Domin
har nutsu sukeyi shida wannan halittar na tsawon dakiku
sama da dari uku akasan tekun suna bakin artabu
Amma
saikaga ya sake tasowa sama domin shakar numfashi
Sannan kuma sai ya sake nutsewa akasan tekun idan suna fada
Babu abinda yake tayar masa da hankali da wannan
dorinar face ganin yadda take da tsananin karfin damtse da kuma zafin nama
Kuma bayan haka kaifi da tsini baya tasiri ajikinta
Kuma aduk sanda ya sari jikinta ko ya soketa da takobi
sai dai yaji wata kara ta tashi Kamar haduwar karfe da karfe
Idanuwanta kuwa idan ta budesu sai kaga suna haska
can kasan wannan teku tamkar an haska da fitila
Marwan ya tambayi kansa yace wannan wacce irin halitta ce ?
Tabbas wani shaidanin shahararren matsafin ne ya sana'anta ta
Don ya cimma wata muguwar bukatar tasa
To amma wannan wacce irin bukatace?
Tambayar da yayiwa kansa kenan kuma baisan amsarta ba
Yana cikin wannan tunanin ne yaji wannan dorinar ruwan ta
gabza masa duka da kafafunta na gaba take ya jishi kamar
an janyeshi da majaujawa ya nutse akasan tekun
Saboda
karfin dukan harsaida ya sha ruwa ta hancinsa da bakinsa
Yana cikin wannan halin ne sai ya ga ta biyoshi kasan ruwan
da nufin ta dira akansa ta karya masa kashu shuwansa sannan ta cikinye shi
Tabbas ya san cewa indai ya kuskura tazo ta sameshi anan kwanansa ya kare
Koda yin wannan tunanin sai ya mike zumbur ya bugi ruwa da dukkan karfinsa
Take yayo saman ruwan itama dorinar ruwan saita biyoshi nanfa suka kasa azababben tsere
Shidai burinsa kawai shine ya bar tsakiyar tekun yaje gaba
Domin acan ne zai sami cikakken kuzarin da zai iya fada da ita
Itama kamar tasan abinda yake cikin zuciyarsa don haka saita biyoshi da dukkanin gudunta
Wohoho hakika wahala bata da magani kuma duk wanda yake labarinta to tabbas bai santa bane
(harda ni da naketa suburbudo kuku karya kuma kuke saurarata)
Sai gashi ana falfala gudu kamar barawo da kuma me kaya
Kowa yana da burin cika burinsa
Abinda yake dada tayar masa da hankali shine
Duk lokacin da ya juyo bayansa sai yaga kamar baifi taku biyu ba atsakaninsu
Koyaya yayi sakaci ga barin gudunsa zata iya cimmasa
Wannan shine dalilin dayasa shi ya kara zage damtsen nasa
Cikin lokaci kankani suka iso bakin gabar tekun suna
Zuwa daidai wannan gabar sai kawai jarumi marwan
Ya tsaya cak ya juyo yana mai fuskantar wannan dorinar ruwan
Nantake itama ta tsaya cak domin tasha jinin jikinta cewa
Tabbas wannan jarumi akwai wani abu wanda ya boye acikin zuciyarsa
Kafin ta ankara sai taga shima ya falfalo da gudun tsiya izuwa kanta
Kafin ta ankara ya gabza mata wani mahaukacin sara atsakiyar
Kanta, take wata kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe
Saboda tsananin karfin saran sai da wani tartsatsin wuta ya tashi
Itama kuma taji kamar an sa wani katon dutse an kwankwatsa mata kanta
Nantake ta rusa wani irin mahaukacin ihu wanda yasa gaba daya tekun ta amsa kuwwa
Ruwa kuwa ya dinga ambaliya kamar igiyar ruwan zata tsinke ta tafi dasu gaba daya
Take dabbar ta shuri jarumi marwan ta falfala da gudu dashi zuwa cikin tekun
Cikin zafin nama yayi sauri ya mayarda takobinsa cikin kufe
Ya zare wata 'yar karamar adda ya ruketa da hannunsa na dama
Hannunsa na hagu kuwa yana ruke da wani kaho wanda yake kwaya daya tak a tsakiyar kanta
Nanfa suka kachame da sabon azababben yaki
Mafi muni fiye da karon farko
Inda ace kana nan lokacin da suke wannan bakin artabu sai kayi zaton cewa ba mutum bane marwan
Saboda wani lokacin sai dabbar ta nutse a can kasan teku
Bazata dago ba sai sun shafe sa'o'i masu yawa akasan ruwan domin taga ya mutu
Amma sai taga kamar ma kara masa kuzari takeyi
Ba komai ya jawo hakaba face tsananin horon da yake baiwa kansa tun lokacin da yake yaro karami
Ita kanta wannan jimina ta tabbatar da cewa yau ta gamu da gamonta
Saboda bai yarda ya sassauta mata ba munanan sara kawai yake zabga mata
Duk da cewa batajin yanka amma tana matukar jin radadin saran da yake yi mata acikin jikinta
Kuma yaki yarda ta saki kahon nata
Suna cikin fafawarne kawai saiya kula da cikin bakinta
Take yayi arba da wasu kwala kwan abubuwa kamar idanu
Koda yin arba dasu sai yace acikin ransa
Tabbas wadannan abubuwa sune ruhin wannan dorinar ruwa
Kuma acikinsu babu abinda yake gani face fuskar wani mummunan aljani
Sanye da hular mulki fuskarsa cike da kwarjini kai da kaganshi kasan cewa
Shine yake sarrafa wannan dorinar ruwan
Cikin sauri ya saki kahon nata sannan ya fara kai mata sababbin hare hare ta ko ina ajikinta
Koda dorinar ruwan taga tabbas yana wahalar da ita sai ta shammaceshi
Ta gabza masa wawan naushi da kafarta ta gaba
Saboda karfin naushin saida kafarsa ta dama ta karye
Take ya kwallara uban ihu sannan yayi sauri ya daka tsalle
Tamkar akan turba yake sannan ya dira akan bakin dorinar ruwan
Sannan ya saka hannunsa na hagu ya tokare hakoran bakinta na sama
Kafarsa ta hagu kuwa saiya tokare hakoran bakinta na kasa
Hannunsa na dama kuwa yana ruke da addarsa
Nanfa aka soma kokawa tsakaninsu
Ita tana ganin wannan ce damar data samu wacce zatayi kalaci da shi
Shi kuma yana tunanin yadda zai ya fasa wadannan
abubuwa masu kama da idanuwa Nan take dorinar ruwan
ta tattare karfinta gaba daya wajen ganin ta tauna jarumi marwan sannan ta hadiye shi
Shima kuma sai ya tattare karfinsa guri guda ya hana ta aiwatar da nufinta
Nantake damatsansa suka tattashi jijiyoyin jikinsa sukayi burdin burdin
Tamkar jijiyoyin bishiya rigar jikinsa kuwa saida ta yayyage kamar an sa kaifi an yanka
Cikin zafin nama ya daidai ci tsakiyar wadannan idanuwa
Ya jefa takobinsa daidai tsakiyar su,
Take takobin taje ta fasa wadannan idanuwa wani irin tiriri ya fito daga cikin su
Sannan jarumi marwan ya sakeyin wani tsallen ya fito daga cikin bakinta
Ya nutse acikin ruwan ya jira ta gama matagugun mutuwarta
Sannan ya dawo ya hau kanta ya saka takobinsa ta dinga
yanka wuyah harsaida ya rabu da gangar jikinta
Sannan
ya nutse a cikin tekun ya kama hanya ya fice daga cikin sa
Yaje ya rarrafa ya shiga cikin daji ya samo murtukekiyar jijiyar bishiya
Sannan ya koma cikin tekun ya dauro kan dabbar ya fito daga cikin tekun
Yana fitowa daga cikin sa ya fadi kasa yana numfashi
da kyar Saboda wahalar dayasha Ga kuma kafarsa guda
daya akarye ba'a gyara masa itaba har tayi tsami ta kumbura
Cikin karfin hali ya bude bakinsa da karfi tareda karanto wadansu Dalasiman tsafi
Take sararin samaniya tayi duhu wata irin inuwa ta mamayeta kamar za'ayi ruwan sama
Kafin cikar dakika biyu wani matashin aljani ya bayyana
Aljanin ya rissina a agareshi yace gani na amsa kira ya shugabana me kake da bukata?
Jarumi marwan yace
Yakai aljani lamakus ina so ne yanzu ka daukeni ka kaini
Inda sansanin mu yake tareda kan halittar nan
Cikin biyayya aljanin yace an gama ya shugabana
Take ya shuri jarumi marwan tareda kan dorinar ruwan ya tashi dasu sama kamar kiftawar ido haka ya bayyana a sansanin su
A wannan lokaci mubnaika tana zaune tana jiran dawowar sa
Har ta kosa ta zaci ya mutu ta fara zubar da hawaye
Koda taga aljani lamakus ya bayyana dauke da jarumi marwan kwance yana numfashi sama sama
Saita kwallara uban ihu sannan ta rugo da gudu tazo inda yake ta goyoshi agadon bayansa ta sauke shi daga

Please Login or Register in order to submit comment