Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi kankanta.

Uwani ta daga girar idanunta sama ta tabe baki tace Ah to laifin ka ne ai daka barni ahaka.

Indararo ya yi mata murmushi yace kada ki damu ba ga ni nazo ba kedai dauko mana tabarma don Allah kizo muyi wata shawara don abin nan da muka shirya akwai matsala.

Uwani taji gabanta yafadi.
Matsalar me?

Indararo yace ke dai dauko tabarma mu koma waje sai mu tattauna a zaune.

Uwani ta dan yi jim tana dubansa cikin damuwa sannan saita dauki tabarmar ta fita waje.

Indararo ya bita abaya mai hannu dayan nan shima ya bishi abaya yana cewa ranka ya dade ni a sallame ni na tafi.

Indararo ya lalubi aljihunsa ya dauko wata tsohuwar naira hamsin har ta kode dakyar ma ake ganin zayyanar dake jiki ya mika masa yace ga wannan babu yawa kabari sai mun sauke kaya idan na dawo ma hadu.

Mutumin ya karba sannan ya wuce babu ko godiya.

Uwani ta dubi Indararo cikin damuwa bayan da suka zauna akan tabarmar suna fuskantar juna tace inajinka kace akwai matsala ni Wallahi harka sa kirjina yafara ciwo.

Indararo ya dubi bangaren da yan cacar ke zaune suna ta kada kati abin su sannan ya kaiwa wani sauro dake ta yawo akan doron wuyansa duka da hannu ya dubeta yace....UWAR MUGU-13

Indararo ya dubi bangaren da yan cacar ke zaune suna ta kada kati abin su sannan ya kaiwa wani sauro dake ta yawo akan doron wuyansa duka da hannu ya dubeta yace kai wajen nan naku sauro yayi yawa wallahi.

Uwani ta Harare shi tace Ni don Allah ka bar maganar sauron nan kafada min abunda ke faruwa.

Indararo ya dan yi jim sannan ya dubeta yace maganar alkawarin jarin da zan baki ne ake neman a samu matsala ya danyi shiru yana sosa doron wuyansa.

Kinsan Daman ba tsabar kudi nayi niyyar baki ba'a saboda gaskiya abinda kike bukata sunada yawa to sai nayi niyyar idan mun dauko lodin ridi na biyo ta nan sai mu san yadda za'ayi ki Samar mana wani dan kauye anan baya inda zan boye motar daga fuskar jama'a kingane saiki samo buhuna mu dinga tsakuro ridi kadan kadan daga cikin buhunan dake cikin motar mu muna zubawa har sai mun cika miki kamar buhu goma nasan idan kika sayar zaki sami jari mai dan kauri.

Uwani ta gyada kai tace kwarai kuwa to ai wannan babu wata matsala don nan bayan mu na kadan akwai wani lungu da za'a iya boye motar agurin babu kowa duk sababbin gidaje ne da ake gininsu ba'a tare ba.

Indararo ya dubeta cikin damuwa yace to ai ba'a nan gizo ke sakar ba.

Uwani ta dube shi to ina jinka.

Ah kin gane kinsan idan muka dauko kayan Ridin nan sai an hada mu da Wakilin kamfani wanda shi zai ke kula da kayan don kada wai mu sata to wani lokacin idan aka hada mu da su mukanyi musu dabara to amma shi wannan da aka hada ni dashi wallahi na rasa yanda zanyi da dan iska saboda irin yaran nan ne yan boko masu muguwar akida...kin gane tunda muka zo yaki ya motsa ko nan da can ne ballantana mu san dabarar da zamuyi masa mu dauke motar bai sani ba.

Wani tattausan murmushin yaudara ya kubuce abakin uwani ta dubi Indararo tace to shi dan boko an fada ma ba ya son mata ne?

Indararo ya dubeta cikin murmushi a rude yace ban fahimce ki ba uwar mugu.

Uwani takai masa duka da hannu ya goce sannan tace kaga wallahi wannan sunan yafita daga bakinka bana son iskanci ta danyi shiru Indararo yana dariya.
Ai indai yana son mata mun gama dashi.

Indararo ya girgiza kai yace gaskiya ayadda na ga yanayinsa bai min kama da masu neman mata ba.

UWAR mugu ta fashe da dariya tace Haba Indararo ya kake magana kamar wani sabon dan duniya? Ka gane cewa har kullum akwai mai neman mata sannan akwai mai son mata yanzu ashe har akwai wani namijin da zai ce baya son mace ko kuma ya gagari mace?

A'a bance dake da akwai namijin daya gagari mace ba abin da nace shine yaron bai min kama da mai neman mata ba irin wannan namu ba.

To ba sai mu sa shi yafara ba.

Tayaya?

Uwani ta dubeta shi da murmushi tace zaka iya kawo min shi nan? Indai yazo nan nagama dashi.
Kafin Kuzo zan kawo wacce ko waliyi ne shi wallahi saita tafi da hankalin sa.

Indararo ya fashe da dariya yace ke uwar mugu na fuskanci bakisan yan boko ba yaron daya saba ganin mata yan birni masu iya ado yaushe kike tsammanin wata gajarabul din karuwa zata dauki hankalinsa? Kedai ki sake dabara don nasan yanzu Hakama idan ya ganta sai ya yi kyankyaminta.

Uwani tayi murmushi tace
Mata suna suka tara Indararo kada kayi la'akari da irin matan da muke kawo muku akwai masu aji suna nan aboye mu muka san inda suke.

Indararo ya dubeta cikin kaduwa yace amma da kinsan da su din kike hadamu da gajoji.

Uwani ta fashe da dariya tace kaidai wallahi ba zaka girma ba ta danyi shiru sannan taci gaba ka ga tashi kaje ka zo min dashi nan bari ni kuma na yi mata waya ta shirya wallahi indai ya ganta mun gama dashi wata yarinya ce in fada ma kyakkyawa yadda kasan mayen karfe haka take fizgar maza.

Indararo yace cikin damuwa to ai bakisan wata tsiya ba yaron dan taurin kai ne yanzu haka idan nace yazo bazai zo ba saboda kafin nazo nan saida na nuna masa cewa yazo zan nema masa daki anan cikin gari ya kwana don cewa nayi dashi Barayi ne a hanyar amma wallahi yaki yana can yayi shimfida a gefen motar ya kwanta matsiyacin harda kunna kyandir yana karatun wani dimemen littafi irin na turawa saikace dan gidan Alhuda-huda.

Yaci abinci.? Uwani ta tambayi Indararo

A'a wani guntun biredi naga yana ci da lemo.

To koma kace yazo yaci abinci da nama kace dashi ba wani dadewa zaiyi ba.

Indararo ya dan yi shiru sannan saiya Mike tsaye cikin damuwa yace bari to naje na gwada Allah dai ya amince kekuma sai kiyi sauri kiyi mata waya tazo.

Kada ka damu yanzun nan zan kirawo ta ai rashin jini rashin tsagawa zaka ganta ne kaima wallahi sai ka so ta.
Ta mike tsaye sannan saita dube shi tace kai duk fa wayon amarya sai an sha manta jeka kazo min dashi ba dan boko ba ko alli ne ubansa yazo nan mun gama dashi.

****** ******* ****** ******** ******* **********

Acan bakin titin akan dakali akofar wani tsohon gida da ruwan sama ya rushe rabin sa Usman ne kwance akan tabarma yana munshari littafinsa daya fara karantawa Agefe guda.

Lokacin da suka karaso Usman yayi mamaki sa'ar daya ga duk ilahirin gurin iya ganinsa babu komai sai.....UWAR MUGU-15

Indararo yayi ajiyar zuciya kadan ya rage ya rusa ihu don farin ciki.

******** ******* ******* ******** ******* ********

Usman na zaune akan tabarma a kofar shagon uwani ya jingina bayansa ajikin bango yana nazarin irin jama'ar Dake gurin lallai tafiya mabudin ilmi ce.

Usman yafada cikin zuciyarsa abunda yabashi mamaki sa'ar daya ga gashi karfe sha biyun dare ya gota amma jama'a sai dada shigowa layin sukeyi daga can nesa da shi kadan tabarmi ne kashi uku ko wacce tabarma da jama'a zaune suna kada kati ayadda Indararo yace masa wai anan suke kwana suna caca.

KOWA dai da kiwon daya karbe shi wai makwabcin mai akuya ya sayi kura ni kam in banda karatun jarrabawa banga mai zai sa na raba dare ban kwanta ba? Usman ya sake fadi cikin zuciyarsa sannan ya sake jingina da jikin bango. Barcin dake idanunsa ya gushe ahalin yanzu abunda kawai ke damunsa yunwa domin Indararo yagama kwadaita masa cewa zai ci abinci har da nama da man shanu wannan kalami shiyasa cikinsa yafara kugi.

Usman ya dubi kofar shagon abincin da Indararo yashiga cikin kaguwa wai me yakeyi ne haryanzu aciki? Ya tambayi kansa.
Lokacin da suka zo Indararo bai yarda sun shiga tare ba suna zuwa saiyace dashi ya zauna akan tabarmar dake shimfide a kofar shagon abincin ya jira shi zai shiga ciki ya aiko masa da abincin.

Usman ya zauna adaidai lokacin da wata doguwar mata ta fito daga cikin shagon da daurin dan kwali agaban goshi Usman ya lura da cewa yar duniya ce domin tana fitowa yaga takai wa Indararo duka ta dura masa ashariya sannan ta dube shi tace sannu da zuwa kanina. Usman ya amsa mata ciki ciki domin ya tsani irin wannan matan.

Usman yaji cikinsa ya sake kugi yayi kamar ya tashi ya shiga cikin shagon ya tambaya saidai ya gimtse sannan ya lumshe idanunsa yaci gaba da zaman jira wannan abinci dai ko dutse ne ake dafawa ya kamata ace ya dahu ya fadawa kansa.

Salamu Alaikum.
Wata zazzakar murya ta daki dodon kunnen Usman tun kafin ya bude idanunsa yaji kamshin wani abu kamar man shafawa kamar kuma na turare ya daki hancinsa Usman ya bude idanunsa yace Amin Wa'Alaikumussalam sannan ne to suka yi ido biyu.
Wata mace ce mai matsaikacin tsayi mai dogon hanci da tsini kamar alkalami idanunta dara dara dauke da farantin abinci tsaye a kansa.

Usman yana kallon ta yaji numfashinsa ya dauke gashi shi dai acikin duhun dare ne amma saida ya lura da cewa matar jazur take kamar tsada.

Matar ta durkusa a gabansa ta ajiye farantin abincin sannan ta haskake shi da murmushi tace.
Yayana ga abincin... Kayi hakuri ka sha zaman jira.

Usman ya dubeta baki na rawa yace A'a babu komai wallahi ai ba wani dadewa akayi ba.

Matar ta zauna akusa dashi sannan ta bude daya daga cikin kwanukan dake kan farantin soyayyiyar kaza ce aciki.
Matar ta dube shi tace zaka fara cin naman ne kokuwa na zuba ma shinkafa da makaroni.?

Usman ya dubeta jikinsa na rawa cikin damuwa domin tagama ruda shi tunda yake arayuwar sa wata mace bata taba zama kusa dashi sosai kamar haka ba domin ko maganar da takeyi ayanzu yana iya jin numfashinta yana bugun fuskarsa.

Bakomai duk wanda ma kika fara zubawa shi zan ci.
Matar ta kashe masa idanu sannan tafara zuba masa abincin cikin farantin tangaran.

Daga Kano kuke ne? Ta tambaye shi da murmushi.

Usman ya gyada kai kamar kadangre yace eh yayi shiru shi kam zamanta akusa dashi duk ya gama ruda shi.

Inason zuwa Kano wallahi bantaba zuwa ba

Haba dai?

wallahi da gaske nake da zan sami wanda zai kaini dana bi shi watarana.

Usman yayi shiru domin yaji abin yafara wuce tunaninsa.

Matar tagama zuba masa abincin ta turo masa gabansa sannan ta mike Tsaye ta dube shi.
Bari na baka guri kaci abincin ka in ka gama saika kirawoni aciki na dauke kwanukan ta dan yi shiru sannan tace sunana ALIYA.

Faran cin abincinsa keda wuya sai Usman yaji duk ta koshi...UWAR MUGU-16

Matar tagama zuba masa abincin ta turo masa gabansa sannan ta mike Tsaye ta dube shi.
Bari na baka guri kaci abincin ka in ka gama saika kirawoni aciki na dauke kwanukan ta dan yi shiru sannan tace sunana ALIYA.

Faran cin abincinsa keda wuya sai Usman yaji duk ya koshi abin yabashi mamaki domin daga lokacin daya dora idanunsa akan Aliya saiyaji duk yunwar dake damunsa tabar cikinsa meke damuna ne.?ya tambayi kansa tambayoyi dayawa suka dabaibaye masa zuciya shin wacece wannan kyakkyawar?

Usman ya tambayi kansa sannan saiya dubi karuwan dake can gefe dashi kadan zaune a tsakiyar maza suna ta caca ga taba a hannun su.

Usman ya bijiro siffofin Aliya cikin zuciyarsa sannan yayi wa kansa tambaya mai tsada. Anya kuwa Aliya ta kasance daya daga cikin wadannan matan? Ga mamakinsa saiyaji yafara fargabar jin amsar wannan tambaya ko kusa ko alama Usman bai so ace Aliya na daya daga cikin mata masu sayar da mutuncin kansu. Awannan lokaci sai wani tunani mai kwantar da hankali yazo cikin zuciyarsa. Aliya yar gidan matar nan ce mai abinci. Wannan tunani yayi masa dadi akalla dai da'ace Aliya ce ke irin wannan muguwar sana'a gara ace mahaifiyar ta ce wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshinsa sa'ar da wata sabuwar tambayar kuma ta darsu a ransa. Idan wannan mata mai abinci ce mahaifiyata to wanene kuma mahaifinta?

Har ka gama cin abincin? Muryar Aliya ta katse masa tunaninsa.
Usman ya juyo firgigit ga mamakinsa saiyaji yana mai farin ciki da dawowar ta.
Na koshi Usman yace bakinsa na rawa.
Aliya ta sake zama adab dashi ta dubi farantin abincin dake gabansa cikin mamaki tace a'a ai baka ma ci komai ba kai bawan Allah lafiyan kuwa?
Usman ya gyada kai yace Daman fa ba wai yunwa nakeji ba.
Aliya ta gyada kai tace hakane ta sunkuyar da kai Kana ta sake dagowa ta dube shi.

Naga alamar duk a gajiye kake ko?
Usman ya dubeta ya gyada kai akwai wani abu a sautin muryar ta dake masa dadi hakanan idan ta kalle shi saiyaji wani farin ciki ya lullube shi. Allah kenan Usman yace cikin zuciyarsa jiya war haka bai taba tsammanin har abada zai sami wata mace ba da zama da ita zaisa shi farin ciki bayan Samira ba ayanzu dayasa wannan Aliya agaba sai ya ga ashe dai duk kyawun nan na Samira da iya zancen ta bakomai bane face shashancin zuciya irin tasa.

Yanzu daga nan ina zaka? Muryarta ta sake katse masa tunani.

Usman ya dubeta yace to ban dai sani ba amma ina jin direban da muka zo dashi nan zai sama min inda zan kwana kafin asuba muyi gaba
Aliya ta dube shi tace in babu damuwa me zai hana mu tafi nabaka gurin kwana.?

Usman ya dubeta cikin mamaki a zuciyarsa yana cewa wannan tana nufin wai na kwana a gidansu ne?

A ina kenan?

Nan baya ne babu nisa.

Usman yayi shiru yana tunani can sai ya dubeta yace to bari na fadawa direbana ko?

Aliya ta ta mike tsaye ta dube shi da murmushi tace kada ka damu tun kafin nafito nafada masa cewa zamu tafi tare nakai ka inda zaka kwana.
Usman ya Mike tsaye ya dubeta sai yaga ta kara kyau.

Aliya ta matso kusa dashi daf har shi yana iya jin hucinta tace zo mu tafi dare yana dada yi gara ka sami isashshen barci kaga gobe da asuba akwai tafiya dayawa a gabanka.

Usman ya dan ja da baya cikin damuwa domin yaga ta matse shi sosai wannan wace irin rayuwa ce ya tambayi kansa.

Aliya ta dubi kofar shagon ta daga murya tace yayata mun tafi saida safe.

To kanwata uwani ta amsa daga cikin shagon.
Aliya ta wuce gaba Usman ya dan yi jim zuciyarsa na wasi wasi.

Yayata... Usman ya nanata abinda Aliya tace da mai abincin wato ashe ma kanwa ce agurin ta ba 'ya ba kamar yadda ya tsammata tun farko Usman yabi bayanta da sauri.

Aliya ta waigo ta dubeshi sannan ta kashe masa idanu tace a tausashe mu tafi ahankali muna hira ko?

Usman ya gyada kai ba magana.

Daga can cikin shagon abincin Indararo da uwani uwar mugu sun make suna lekensu Usman koda suka ga Aliya ta tafi da Usman sai suka dauki shewa suka tafa.

Wane mutum inji mutuwa uwani tace.

Kai amma fa yarinyar nan ta hadu wannan da za....
Kai don Allah rufawa mutane baki me zatayi da tsoho kai ba gashi sai sanko.

Indararo ya fashe da dariya.

BABI NA HUDU
Karfe uku da yan mintuna na dare yan cacar dake kofar shagon uwani uwar mugu tuni tun nade tabarmarsu kowa Yakama Gabansa ba don sun gaji ba sai don sun sami labarin wai anyi fada jiya anan kusa dasu don haka kowanne lokaci daga yanzu ana tsammanin yan sanda zasu zo kame...UWAR MUGU-17

BABI NA HUDU
Karfe uku da yan mintuna na dare yan cacar dake kofar shagon uwani uwar mugu tuni tun nade tabarmarsu kowa Yakama Gabansa ba don sun gaji ba sai don sun sami labarin wai anyi fada jiya anan kusa dasu don haka kowanne lokaci daga yanzu ana tsammanin yan sanda za su zo kame.

Wannan al'amari yayiwa Indararo da uwani dadi Daman abinda suke so kenan don haka tashin yan cacar keda wuya sai Indararo Yakoma can bakin titin ya tuka motar zuwa cikin lungu tun kafin ya karasa uwani tasa wani mai gadi ya bude masa kofar wani katon kango wanda aka zagaye ba'a fara gini acikinsa ba don haka Indararo na zuwa saiya shiga da motar ciki nan da nan mai gadin ya mayar da kofa ya rufe.

Wasu karti gudu uku yan zaman banza da uwani ta tanada suka fito daga cikin duhun sannan suka fara sauko da buhunan Ridin duk wanda aka sauko dashi sai a tura wani karfe aciki mai kwararo irin wanda ake amfani dashi wajen ganin samfur daga an soka shi jikin buhun sai ridi yafara zubo wa sannu ahankali ana tatsar buhunan kadan kadan har aka tatsi buhuna goma.

Wannan sun ishe ki? Indararo ya tambayi uwani yana kallon ta cikin duhun dare.

Eh to amma dai ina ganin da za'a kara samun koda buhu biyu ne da ba haka ba saboda kaga shi kansa maigadin sai na sallame shi don wallahi yayi mana mutunci kaga in ba don shi ba da sai mun tafi can cikin kauye kafin mu sami inda zamu yi aikin nan ko?

Hakane Indararo yace sannan ya dubi kartin yace ku sake tatso Mana buhu biyu sannan ya juya ya fuskanci uwani da murmushi yace ya bayanin Mariya.?

Uwani ta Harare shi tace kai fa ka cika gaggawa ai duk wacce kace ita za'a kawo ma Indararo ai ni ka gama min komai.

Dakyau uwar mugu shiyasa nake son ki yana gama fadin haka sai ya ruga aguje tun kafin ma uwani ta bishi da duka.

****** ******* ******** ****** ****** ************

Usman yana biye da ita abaya sumu-sumu kamar tunkiya har suka isa cikin gidan koda suka shiga sai Usman ya tirje sannan ya dubeta cikin kaduwa sa'ar daya ga jama'a jimgim a farfajiyar gidan sun kunna fitilar kwai ga tabarma a tsakiyar su suna caca.

Aliya ta juyo ta dube shi da murmushi tace shigo mana yaya ka tsaya? Usman ya dubi jama'ar Dake zaune sunata kada karta abinsu basu ko dago kai ba ballantana ma su kalle su ganin haka shiyasa Usman ya dan saki jiki har ya bita abaya suka shiga cikin dakin

Aliya ta dube shi sa'ar data ga yana nazarin dakin ahankali kai kace wani malamin kimiyya ne yake nazarin wata sabuwar kwayar halitta.

Saidai fa hakuri dakin nawa ne babu wani abun kirki aciki ta dan yi shiru tana dubansa a daidai lokacin da ya juyo ya dube ta da murmushi yace bakomai yafi dai na kwana awaje kare yana sunsuna ni kamar danyen nama.

Aliya ta bushe da dariya kaidai wallahi baka rabuwa da abin dariya wai kamar danyen nana cab.

Ta numfasa bayan tagama dariyar sannan ta dauke kai gefe guda domin ta lura da cewa gaba daya idanun Usman akanta suke to ka zauna mana kayi ta tsayawa kamar soja?

Usman ya zauna akan katifar dake shimfide a tsakar daki gamida murmushi Aliya ta zauna akusa dashi sannan ta mike kafafu.

Dubi idanunka Usman duk sunyi ja barci kakeji ko?

Usman ya gyada kai ai dole naji barci don ban saba doguwar tafiya irin wannan ba ya dan yi shiru yana ci gaba da satar kallon kyakkyawar fuskarta.

Ai naga alama Aliya tace tana dubansa sannan saita dago idanu ta kalle shi da murmushi tace
Na fahimci kamar kai bako ne ma a irin wannan aikin ko.?

Me kika gani?

Aliya ta sunkuyar da kai tana wasa da yan yatsunta tace gani nayi Sam-Sam bakayi kama da irin mutanen da su Indararo ke zuwa dasu ba ka gane su zaka ga irin koda yaushe acikin datti suke kayansu dukun-dukun da bakin mai amma kai naga rigar ka da Wandonka ma har da karin guga kaidai dan gayu ne a takaice.

Usman ya fashe da dariya yace kedai kin sa min ido.

Allah ba wani sa ido gaskiya ce kawai Aliya tace sannan ta mike tsaye ta nufi kusa da wani kwanon tagulla ta dauko wani abu cikin bakar leda ta dawo ta zauna kusa dashi tana kallonsa cikin murmushi. Zaka ci?

Usman ya dubi ledar cikin mamaki yace me.?

Idan matambayi ta danyi dariya kaidai kawai ka amsa min zaka ci.?

Usman yafara dariya kuma don dai kawai ni na fi kowa kwadayi sainace zanci abunda bangani ba?

Aliya ta gyada kai tace cikin shagwava eh mana don Allah nidai kace eh zakaci kaji? Ta langwabe kai cikin shagwaba.

Hakan datayi sai kawai Usman yaji ta burge shi tabbas tafi Samira iya hira yafadi cikin ransa kaita fi Samira komai ma ya sake fadi sannan saiya gyada kai yace toh Shikenan zanci.

Ka yarda zaka ci ko menene?

Usman ya gyada kai yace na yarda nasan dai ai bazaki bani Abunda zanci na mutu ba ko?

Aliya ta rike numfashi Haba Usman me kuma yakawo zancen mutuwa ana zaune Ƙalau da inada abinda zai kara ma kwanaki aduniya ma da shi zanbaka tana gama fadin haka saita kunce jakar ledar dake hannunta sannan ga mamakin Usman sai ta fito da wani irin biskit dogo mai madara a tsakiyar sa ta mika masa da murmushi.
Gashi naka ne.

Usman ya karɓa cikin jin dadi da mamaki a zuciyarsa yana fadin ashe dai irin wadannan mata masu zaman kansu sun iya soyayya haka basa son yin aure?

To kaci mana ka rike sai kallo kake yi kamar wani hoto muryar Aliya ta katse masa zancen zuci.

Usman ya jefa biskit din a baki ya tauna lallai mai zaki ne yafada acikin zuciyarsa yanzu haka wani ne yabata yasake fadi cikin zuciyarsa ga mamakinsa saiyaji wani abu ya soki zuciyarsa sa'ar da tunanin mu'amalarta da wani yazo masa zuciya.

Aliya ta mike tsaye
Bari na kawo ma lemo.

Usman ya girgiza kai cikin sauri yace A'a ki barshi wallahi cikina ya cika da ruwa ko kin manta ne ban dade da gama cin abinci ba.?

Aliya ta tsaya tana kallon sa ta lumshe idanu tace kana nufin bazaka cinye biskit din ba Kenan?

Usman ya girgiza kai yace me zai hana amma sai gobe idan mun kama hanya zan ke ci kadan kadan acikin mota.

Aliya ta zunkuda kafada sannan ta dawo ta sake zama kusa dashi.

Usman ya jefa biskit din abakinsa sannan ya dubi kyakkyawar fuskarta numfashinsa sama-sama yace Aliya... Yayi shiru bai karasa ba...

Fadi mana ya kayi shiru? Usman ya gyara zama sannan ya sunkuyar dakai yace....UWAR MUGU-18

Usman ya jefa biskit din abakinsa sannan ya dubi kyakkyawar fuskarta numfashinsa sama-sama yace Aliya... Yayi shiru bai karasa ba...

Fadi mana ya kayi shiru? Usman ya gyara zama sannan ya sunkuyar dakai yace Gaskiya bazan boye miki ba... Aliya Allah yayi miki kyawun halitta.

Aliya ta dube shi cikin mamaki sannan tayi kamar zatayi masa murmushi saikuma ta fasa ta dube shi da fuskar katako tace ba wani nan tsokana ta kake yi.

Allah da gaske nake kema ai kinsani saidai Idan bakya kallon Mudubi.

Aliya tayi dariya tace Allah ko?

Usman ya gyada kai Allah kuwa irin kyawun ki daban yake acikin mutane sai an tona.

Aliya ta dago kai cikin gaggawa ta dube shi cikin mamaki tace wai da gaske har cikin zuciyar ka abinda kake nufi kenan?

Usman ya gyada kai.

Aliya ta sunkuyar dakai tace to nagode Naji dadi.

Matasan biyu sukayi shiru na tsayin lokaci suna kallon juna tambayoyi marasa adadi na ta kai da kawowa acikin zuciyoyinsu.

Usman yana cewa ga doki har doki amma kofaton na sakaina.

Aliya tana cewa wannan da gani dan boko ne babu abinda zaiyi dani.

Usman ya fara bata shirun ya dago kai ya dube ta. Yaya kikayi shiru.?

Aliya tayi dariya ta sunkuyar dakai tace bakomai.

Kedai fadi gaskiya.

Aliya ta fashe da dariya adaidai wannan lokacin ne to wayar ta ta dauki ruri cikin sauri ta dauko wayar daga kasan mararta kusan a fusace tace yanzu haka wannan dan iskan mai shegiyar... Kalmar ta makale akan fatar bakinta bata karasa ba lokacin data ga ashe ma ba wanda take tsammani bane.

Au ashe ma bashi bane wannan ba ma suna har na fara masifa tace tana kallon Usman cikin murmushi sannan saita kara wayar a kunnen ta tace Hello waye?

Akayi shiru na yan dakiku daga can daya bangaren sannan sai wata taattausar murya tace da ita baki gane ni ba ne?

Aliya ta tsuke fuska cikin mamaki ta dubi Usman wanda yayi tsit yana sauraronta baiyi mamaki ba domin yasan irin wadannan mata basa rabuwa da amsa wayar maza.

Bangane ka ba Wallahi babu suna ta yaya zan gane ka bayan ba ganinka nake ba.?

Amma dai inda alkawari ai ya kamata ki gane muryata Aliya.

Akace da ita daga can daya bangaren.

Mamaki ya sake bayyana akan fuskar Aliya jin cewa

Please Login or Register in order to submit comment