Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KISAN BOKO-01

Nazir Adam Salih (Nas)

TABA KA LASHE

Wani tela ya auri wata Masifaffiyar mata mai fadan tsiya kamar karya. Ance basu fi shekara da aure ba amma fadansu yakai sau saba'in da doriya

Don me zakice na auri aminiyar ki?
Sanin kanki ne duk duniya babu wacce nake kauna kamar ki shin bazaki aureni bane? Saurayin telan ya tambayi Uwargijiyarsa.

Zan aure ka mana. Amma kana da wani aibu.
Aibun da babu mai wanke ma shi har sai ka auri babbar aminiyata NADIYA. Kafin ni nasamu kwanciyar hankalin da zan aure ka daga baya...............

NAZIR ADAM SALIH (Nas)

DAGA NAZIR ADAM SALIH
KIBIYAR AJALI✅
ME YAFI KUDI✅
TA LEKO TA KOMA✅
BIRNIN SARAUNIYA✅
NAIRA DA KWABO❌
ACI BULUS✅
MUTUWAR KASKO✅
ALAKAKAI✅
WA NA KAMA?❌
HINDU✅
RUHINA❌
DARE DA RANA✅
KARYA LINZAMIN SHAIDAN✅
CUTA TA DAU CUTA✅
ISKA MAI KADA RUWA❌
BINDIGAR KWALI✅
DAMISAR TAKARDA❌
AZIZA⭕
TSOHON ALKAWARI✅
KAI DA JINI❌
ALJANI YA TAKA WUTA✅
SAI MUTUWA❌
KUDI DA MACIJI✅
KISAN BOKO✔️
MURMUSHIN ALKAWARI ✅
KURA DA KAN RAGO.✅

DON
Abokina Muttaka (Baggio) Gwammaja.
Da
Abdullahi Musa Madda
Da
Assadik Muhammad
Wanda ya taimaka wajen gyara littafin.

KISAN BOKO
Nazir Adam Salih (Nas)

Copyright © nazir Adam salih (Nas) 2006
Hakkin mallaka (h) Nazir Adam Salih NAS 2006

TARIHIN DABA'INSA
An fara buga shi a kamfani KAMNAS PUBISHERS DAKATA A SHEKARAR 2006 (1427)

GARGADI
Ba'a yarda wata kungiya ba ko wani mutum ya juya wani bangare na wannan littafin ta hanyar wasan kwaikwayo da majigi ko kuma wani abu daban saida tabbataccen izinin marubucin hakanan duk wani abu dayayi kama da halin wani mutum acikin labarin nan don Allah gafarce ni akasi ne kawai aka samu domin labarin kagagge ne NAGODE.

ADIRESHI
Abubakar Saddik islamiyya dakata Kano
Akwatin waya 4792.

KISAN BOKO
Nazir Adam Salih
(NAS) 2006

BABI NA DAYA 1
Awata kasa awata jiha awata unguwa awani katon gida acikin wani faffadan dakin shakatawa dake kallon lambu wata mata ce zaune tayi tagumi haka nan ta zurawa katuwar akwatin gilashin idanu wacce ke dauke da dan karamin teku da wasu yan kananan kifaye kirar nasara sunata wasa abinsu kai kace masu rai ne ba robobin wofi ba azahiri idan ka dubi matar saika rantse da Allah dan karamin tekun bogin dake gabanta take kallo amma a badini bashi take kallo ba hakanan ba kawar ta dake zaune kusa da ita take kallo ba zuciyarta na can cikin duhu tana ta lalube.
Laluben abinda take zargin kanta da cewa Meyasa bata lalube shi ba tunda sauran haske?

Kai NADIYA meyayi zafi haka kikayi jugum kamar anyi miki mutuwa? Irin wannan tunani haka tunda kuruciyar ki kawar ta ce ke magana.

Nadiya ta mike tsaye akwai alamun damuwa karara a fuskarta ta nufi wani dan karamin firji dake dab da tekun Tangaran din ta bude shi kana ta dauko wani dan karamin kofin Tangaran da wani abu aciki ruwa ruwa ta dan kurba ta runtse idanu kadan kamar mai hadiyar magani saita ta mayar da kofin cikin firjin ta rufe lokaci guda kuma ta nufi gindin katuwar tagar gilashin dake kallon lambun alfarmar dake bayan gidan tafara girgiza kai cikin takaici.

Haba AMIRA wacce irin kuruciya kuma ga matar datayi shekaru talatin da uku aduniya?
Amira ta dubeta cikin mamaki tace
Kina nufin kenan kice dani ke tsohuwa ce?

Nadiya ta girgiza kai.
Bahaka Nake nufi ba Amira abinda nake son ki fahimta shine a irin shekarun da muke ciki ayanzu mun fi karfin a kira mu da yan mata masu kuruciya saidai ko iyayen mata shekara talatin da uku fa Amira! Ayanzu haka halin da ake ciki ya'yan sa'annin mu sun isa aure amma mu gamu nan.... Tayi shiru bata karasa ba.

Kodayake gara ma ke Amira kin yi sa'a kin sami miji bara nayi miki murna wallahi da auren da kikayi Amira ta tura baki gaba tace.
Eh to yafi babu amma meye wani abin murna ga auren tsoho?

Kinyi sa'a ma ke da kika auri tsohon Amira ta harari Nadiya sannan saita fashe da dariya.

Bana son iskanci nadiya meye abin sa'ar a auren tsoho? Sanin kanki ne da inada tarin dukiya da kayan alatun duniya kamar ki babu abinda zaisa na auri tsoho Nima wallahi kudi na bi ta danyi shiru alamun damuwa suka dan bayyana a fuskarta.

Ai ke Nadiya da sauki ma damuwar ki kadan ce dubi fa yanda kike gidanku akwai kudi kema da kudi yan uwanki da kudi mahaifiyar ki da kudi mahaifin ki Allah ya jikan sa shima cikin kudi ya mutu to yanzu in banda abin ki Nadiya me kika nema rasa da har zaki bi ki uzurruwa kanki abanza?

MIJI shine abunda na nema na rasa amira wannan shine kawai ya rage min MIJI ba. Shekara talatin da uku aduniya babu miji.
Amira ta girgiza kai lokaci guda kuma ta bude jakarta ta dauko wani dan karamin mudubi mai shan zuciya tafara kallon fuskarta a jiki.
LALLAI shekaru sun fara ja tace cikin zuciyarta sa'ar da ta kalli fuskarta taga ta dan fara tauyewa cikin sauri ta ajiye Mudubin cikin damuwa ta dubi Nadiya tace.
ME KUDI BASHIDA HAUSHIN KOWA.

Nadiya idan kikaga dama kina iya auren kowane irin mutum ne tunda dai kinada kudi ko dan dole basai kin takura shi yayi auren jari dake ba Wallahi Nadiya idan nice ke ina iya auran yaro dan shekara ashirin. Amira tayi shiru tana duban fuskar Nadiya. Lokaci guda kuma tana kokarin taga ko abunda tace yayi tasiri.

Can sai Nadiya tayi ajiyar zuciya sannan saita baro jikin tagar ta matso kuwa da inda amira take zaune ta zauna ahannun kujerar tace da ita a tausashe.

Gaskiya ne duk abunda kika fada amira tabbas in har ina son auren jari zan iya yi dan ayanzu haka ma a asibitin danake aiki akwai wani saurayi daya nace min amma na rigaya na san karya yakeyi bani yake so ba kudina yake kauna.

To Meyasa ke bazaki aure shi ba yaro ne ko tsoho? Amira ta tambaya. Nadiya ta dubeta wani irin tsoho kuma saurayi ne Wallahi na ma girme shi domin nasan yayi da yawa shekara talatin.

Indai hakane ashe da gangan kike ta uzzurawa kanki da tunane tunanen banza ba sai ki aure shi ba kawai tunda saurayi ne ko mummuna ne?

Nadiya ta girgiza kai tace.
Kyakkyawa ne amira kyakkyawan gaske wanda hakan shiyasa bana son hada wata alaka dashi domin na tabbata da bashi da labarin arzikina babu abinda kyakkyawa kamar sa zaiyi da babbar mace kamar ni......KISAN BOKO-02

Nadiya ta girgiza kai tace.
Kyakkyawa ne amira kyakkyawan gaske wanda hakan shiyasa bana son hada wata alaka dashi domin na tabbata da bashi da labarin arzikina babu abinda kyakkyawa kamar sa zaiyi da babbar mace kamar ni.

Haba Amira dubeni fa da kyau yadda na lalace kyawuna duk ya gushe jikina ya saki wallahi akwai sa'ar danake jin kunyar kallon Mudubi domin tun hoda tana rufa min asiri har itama ta gaji ta bari.

Nadiya tayi shiru idanun ta sukayi Rau Rau suka cicciko da kwalla kamar zatayi kuka.
SO nake na sami wanda yake kaunata tsakaninsa da Allah Badon kudina ba..... Zuciyarta ta karye muryarta tafara rawa.
Kuma zan so ace saurayi ne.... Ba.... Tsoho ba amira.... Wallahi kullum na tuna da auren babban mutum sai inji duk duniyar tayi min zafi domin tun ina karama sosai budurwa yar shekara sha bakwai nake mafarkin auren saurayi domin jin dadin aure yafi tabbata idan budurwa ta auri matashi dan uwanta sai gashi Rudin zamani yasa na makara.

Nadiya tafara zubar da hawaye sannan taci gaba da cewa lokacin ina sakandire Amira... Inada wani saurayi TIJJANI babu yadda baiyi ba akan ya aure ni naki bakiga wulakancin danayi masa ba saboda naga ya mace akaina nace dashi ni bazanyi aure ba sai na gama karatuna na likita.
bazan taba mantawa ba amira da daddare ne acikin lambun can da kike hange daga nan. Kinga fararen kujerun can guda biyu anan ya durkusa gabana yana rokona harda kwalla yana neman na hakura muyi aure yayi min alkawarin cewa idan na aure shi zai kyale ni na cigaba da karatuna amma fau fau fau naki... Nadiya ta fashe da kuka.

Haba Nadiya me yayi zafi haka harda su kuka wannan idan da maza zasuji mu ai ba karamin abin kunya bane shi aure ai nufi ne na Allah idan yaso saiki ga kin sami saurayin da kike so wanda ke kaunar ki tsakaninsa da Allah ya aure ki.

Nadiya ta share hawaye ta girgiza kai tace.
Anya kuwa amira yanzu kina ganin yadda nake din nan kuwa akwai wani saurayi da zai iya kaunata tsakani da Allah.? Ban ki ta taki ba dai idan akace zai so ni don abun hannuna amma haka kawai ya so ni ni kadai.....
Kai abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa amira ta bude baki kamar zatayi magana sai kuma ta fasa domin bata san abunda zata ce wa kawar Tata ba tarigaya tasan cewa duk Abunda Nadiya tafadi gaskiya ne domin ita kanta abun na da sauki da babu abunda zai sa ta auri tsohon nan.

Kawayen biyu sukayi shiru na yan dakiku kawunan su a sunkuye sannan sai Nadiya tace
Ni Daman tun muna jami'a amira jikina yafara bani cewa zamu sha wahala kafin mu samu irin mazan da muke so suke son mu. Amira ta dubeta cikin mamaki..
Meyasa kikace haka.?sabdoa wata magana danaji wasu samari suna fada a shekarar mu ta karshe a jami'aKISAN BOKO-03

Meyasa kikace haka.? sabdoa wata magana danaji wasu samari suna fada a shekarar mu ta karshe a jami'a

Me suke cewa? Amira ta sake tambayar nadiya akaro na biyu idanunta akan fuskar nadiya.

Abinda suke cewa shine wai mun yi musu tsufa su yanzu sun fi son suyi kawance da yan mata yan aji daya sabbin dauka.

Wannan zancen banza ne Amira tace da kawar tata a fusace.
Mata nawa ne a lokacin namu da suka sami mazan aure a acikin mazan ajinsu? Ai ba zasu kirgu ba nadiya.

Amma kuma zancen gaskiya amira idan kika lura zakiga duk kusan matan da suka sami maza Awannan lokacin sunfi mu kurciya nesa ba kusa ba domin sun shiga jami'a ne tun suna da kananan shekaru kuma karatun su bashida tsayi kamar namu ki tuna fa aikin likita na karanta kusan shekaru shida zuwa bakwai kai sun kai takwas ma harda yajin aiki amira tayi shiru na tsawon lokaci bayan da nadiya ta gama dogon bayanin ta sannan saita Mike tsaye domin wannan dogon bayani na kawar tata duk ya gama gundurar ta.

To Allah ya kyauta tace sa'ar data mike tsaye sannan saita dada da cewa
Wato yanzu dai a takaice kina son kice dani ke kin yanke kauna da samun miji saurayi kenan?

Nadiya ta dago kai ta dubi amira sannan saita saki wani bushashshan murmushin yake akaro na farko tun sa'ar da suka fara hirar takaicin.

Amira kenan wallahi idan kina wani zancen sainaji kamar ba dake mukayi zaman jami'a ba ke abunda baki gane ba shine wannan yan banzan samarin masu tsabar iya sa riga da wando da muke burin aura sunyi bala'in raina mu kullum hankalin su yana kan kananan yan mata shin bakiji ba har wani sunan shegantaka suke kiran mu dashi ba?

Suna kuma kamar yaya wane suna ne wannan? Nadiya ta dubi amira sannan saita rufe idanunta ta fashe da dariya.
Nima wallahi amira kunyar fadar sunan nake yi.

Ke kinga bana son iskanci dan Allah fada min kinji nadiya.... Dan Allah fada min wane suna suke kiran mu dashi? Nadiya ta dubi amira sannan tayi kasa-kasa da murya tace wai KISAN BOKO suke cewa irin mu amira ta rike baki cikin kaduwa.
KISAN BOKO? Mune kisan bokon? Nadiya ta mike tsaye ta matsa kusa da amira haka suke kiran mu amira saidai hakuri wallahi basuda kirki....

Basuda mutunci zakice amira tace a fusace yan iska suma ai kisan bokon ne.

Kwarai kuwa nadiya tace sannan ta dubi amira ta dada da cewa.
Yanzu daga nan ina zakije gida zaki koma kokuma shagon dinkin naki zaki koma? Amira ta girgiza kai sannan ta dubi agogo.

Kinsan nafi zuwa da rana lokacin da suke tsakiyar aiki amma yanzu gida zan koma kina ganin har shida ta kusa amira tabi kan tattausan kilishin dake dakin ta nufi kofa kafafun ta kamar zasu nutse aciki saboda taushi.
Kamata yayi ma ace muje ki ga shagon dinkin nawa nadiya. Amira taci gaba da cewa nadiya ta bita abaya tana kada dan makullin mota a hannu.

Muje to na mayar dake gida idan zamu wuce ta bakin kasuwar basai ki nuna min inda shagon yake ba ko ba'a bakin kasuwa yake ba? Amira ta harari nadiya tace.
Bangane in zamu wuce na nuna miki shi ba kina nufin ganin nesa zakiyi wa shagon nawa?
Amira ta girgiza kai tace.
Bazata yiwu ba nadiya nifa Daman neman taimako ne yakawo ni gurinki ta danyi shiru.

Ki shirya tunda gobe Lahadi bazaki je aiki ba sai mu tafi da rana ki ga yadda tsarin shagon yake domin agaskiya nadiya.... So nake ki karamin jari kinga yanzu kekunan dinki bakwai ne aciki so nake na kara guda uku su zama goma kenan gaba daya sai na sake karo madinka kuma inda hali ma inason nafara sayar da shaddodi da atamfofi a shagon amira ta sake yin shiru sannan saita tausasa murya tace.
Bafa dole bane nadiya kiyi min kawai abunda zaki iya... Mijin nawa ne baya banbaruwa tauri ne kamar naman kai nadiya ta fashe da dariya sannan sai kuma ta zubawa tsohuwar kawar tata idanu lokaci guda kuma irin taimakon da kawar tata tayi mata a zamanin zaman su na jami'a ya fado mata tabbas ya kamata ta agaza mata.

Haba amira don dan wannan ma kin tsaya kina ta wani dogon bayani ai da tun zuwan ki ma kin fada da sai mu wuce banki na baki duk abinda kike bukata ta dan yi shiru tana duban agogo
Kinga yanzu har shida tayi abunda zamuyi shine idan kinje gida yau saiki yi lissafin duk abinda kike bukata idan nazo gobe sai mu je shagon Naki na gani sannan na baki cakin in yaso ranar (Monday) saiki karɓa nan da nan fuskar amira ta washe.

GODIYA Nake nadiyata bansan abunda zanyi aduniya ba idan babu ke nagode nagode Allah ya saka da alheri.

Bakomai amira menene amfanin zaman taren idan ba'a amfani juna ba? Muje na kaiki gida.
Kawayen biyu taka ahankali suka fice daga dakin suna hira cikin raha sannu ahankali suka tattaka takan wata yar karamar matattakala ta farin dutse wacce gefen ta ke dauke da jerin sahun shuke shuke ma'abota fure mai kamshi suka nufi inda filin ajiye motoci na gidan yake daga inda suke tafe suna iya hango wasu dirka dirkan jiminoni suna zagayawa a farfajiyar gidan zakalan-zakalan abinsu suna mika dogon wuya.

Nashiga Uku amira tace sa'ar da taga daya daga cikin jiminonin ta nufo inda suke Nadiya ta fashe da dariya.

Ke ba abinda zatayi miki ina ruwan ki da ita jiminonina ne wannan me zuwan sunanta ZANKALA waccan kuma dake jikin bishiyar can sunanta SANTALA amira ta rike baki cikin mamaki lokaci guda kuma ta rike kafadar nadiya a tsorace.

Oh su nadiya manyan gari in banda rigima irin taki ina ke ina irin wannan zankala zankalan halittu dubi fa wuyan ta idan ta mike shi kamar zai taba sama.

Nadiya ta fashe da dariya ta mari kafadar amira tace shegiya har yau baki daina karya ba.

Ahaka suna tafe suna wasa cikin raha har kawayen biyu suka isa inda dunkulalliyar motar tata take sai sheki takeyi acikin dan abunda ya rage na daga hasken yammacin.

Nadiya........ Amira takira sunan kawar ta muryarta kasa-kasa Adaidai lokacin da suka karasa jikin motar nadiya ta juyo kadan lokaci guda kuma ta bude gaban motar bangaren direba ta dubi amira tace.
Na'am ya akayi Amira? ta dan yi jim sannan tace.
Akwai wani saurayi inda zaki iya son sa dana nuna miki shi nadiya ta dubi amira cikin tsananin mamaki sannan saita mayar da kofar motar ta rufe ta jingina ajiki tace.......KISAN BOKO-04

Akwai wani saurayi inda zaki iya son sa dana nuna miki shi nadiya ta dubi amira cikin tsananin mamaki sannan saita mayar da kofar motar ta rufe ta jingina ajiki tace.

Ban fahimci abinda kike nufi ba.
Amira ta gyara dan sirrin gyalen dake yafe a akanta kamar rawani kana tace muryarta na sarkewa.
Wani saurayi ne kyakkyawa nadiya inda zaki iya kaunar sa danayi miki murna nadiya ta rike baki cikin mamaki.

To in banda abin ki amira tayaya zan so abunda ban taba gani ba kuma ban da haka ma ai tambayar bawai ta ina son sa bace tambayar anan itace shin zai iya kaunata tsakani da Allah?

Amira ta gyada kai tace.
Ina tsammanin in har akayi dace ya ganki Yakuma kauna ce ki to tabbas tsakanin sa da Allah ne tunda dai shi baisan da matsayin arzikin ki ba

Nadiya ta dauke wuta kanta a sunkuye na kusan rabin minti sannan saita dago kai.
Tayaya to kike tsammanin daga ya ganni zai kaunace ni? Dubeni fa ki gani ba karamar yarinya bace me yiwuwa ma baifi sa'an kanina na biyu Marigayi ABDULMALIK ba saidai ko mu nuna masa kudi. Kinsan kuwa abunda bana so kenan.

Amira girgiza kai cikin sauri tace.
Bakya bukatar nuna masa kudi abunda kike bukata kawai shine idan na nuna miki ai zan yi kokarin na gabatar dake a gare shi amatsayin kawata domin muna bala'in mutunci dashi ke kuma saiki san yadda zakiyi ki faranta masa kiyi masa hira mai dadi kija hankalinsa da kalamai masu dadi kinga..... Nadiya ta katseta ta hanyar girgiza kai.

Haba Amira irin wannan abu haka saikace littattafan soyayya kema kinsan ai bazata yiwu ba abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa kawai daga naga mutum daga nayi masa zance mai dadi sai ya kauna ce ni bayan ko ganina bai tabayi ba kuma in banda abin ki ma amira ni yanzu wane dadin zance ke gareni da har zan iya ribatarsa dashi? Sanin kanki ne duk tsawon rayuwar yammatacina banida wani saurayi sai dayan nan jal danaki aura to wane zance ma ni na iya? Cikin damuwa amira ta matsa kusa da nadiya ta dafa kafadarta tace.
Abin kawai danake so dake shine idan na hadaku dashi ki kyautata masa ki nuna yar kulawa agare shi Nadiya ta rike baki gamida yar dariya cikin tsananin mamaki.

Oh! Yau na shige su na kyautata masa ko? Na faranta masa ko? To mijina ne ko kuwa me?
Bahaka bane nadiya amira tace cikin kaguwa ke macece abinda nake so dake shine kiyi amfani da kissar mu ta mata ki hilace shi akwai abinda yasa kikaji inata ce miki ki kyautata masa ki kyautata masa!!

Menene yasa? Amira tayi ajiyar zuciya kana ta dubi nadiya tace saurayin danake baki labari baifi wata hudu da aure ba kyakkyawa ne kamar yadda na fada miki tun farko amma ina tabbatar miki da cewa tunda nake jin labarin mata yan uwan mu ban taba jin labarin masifaffiyar mace kamar amaryar sa ba domin da kunnena ran nan Naji yana baiwa Abokan sa labarin cewa acikin wata hudu da sukayi da aure fadansu kusan saba'in da bakwai kusan kullum a masifa suke.....

Amira tayi shiru tana mayar da numfashi idan kika bi ahankali nadiya zamu iya amfani da bakin cikin matar dake damunsa mu kwace shi domin da kunnena Naji yana cewa nan da wata guda idan bata sauya hali ba sakinta zaiyi domin wai ya gaji da masifar ta wannan shiyasa kikaji nace dake idan mun hadu dashi ki kyautata masa kinsan ance mutumin da ruwa yaci ko tsinin takobi ka mika masa karɓa zaiyi.

Kawayen biyu sukayi shiru gamida duban juna na yan dakiku.

Ni dai amira wannan al'amari naki yafi kama da labari amma yanzu anya haka ta yiwu a gaske?
To mu gwada mu gani mana ai a rashin tayi akan bar araha. Amira ta sake wani tattausan murmushi.

Yaya naga duk kin rude har kin fara gumi?
Nadiya ta saki murmushin yake tace toh Ai abin naki ne kamar a fim.

Kada kice haka kibari tukunna sai kin ganshi wallahi kyakkyawa ne nadiya ta dubeta cikin dariya sannan tace.

Sai wani zuga shi kikeyi to idan gaskiya ne Meyasa ke baki ribace shi ba ya aure ki din ba?
Ko me baki son auren saurayi sai tsoho?

Amira ta girgiza kai gamida hade fuska tace.
Kada kiyi min muguwar fassara nadiya lokacin dana hadu dashi nayi aure...... Ta dan yi shiru sannan sai tace zo mu tafi ki kaini gida idan bakya so ba dole bane Daman wai kokari nake Nima na taimaka ko ma gusar da abunda ke damun zuciyar ki.

Nadiya ta bude musu motar suka shiga sannan ta tuka motar suka nufi babbar kofar tangamemen gidan wani dogon maigadi mai tankwararriyar hula kamar makami ya taho Aguje ya bude musu kofa
Koda suka hau titi suka fara tafiya sai nadiya ta lura da cewa kamar amira ta dan yi fushi domin taga har suka fito daga gidan bata ce da ita kala ba.

Wannan shiyasa nadiya ta dan sassauta murya idanuwanta akan titin tace da amira saurayin da kike maganarsa dan uwan ki ne? Amira ta girgiza kai sannan tace yana daya daga cikin madinkan dana dauka haya domin aiki a shagon dinkina sunansa TIJJANI nadiya ta dan rage gudu kadan sannan ta dubi amira tace
Ina son irin sunansa kuwa sunan nada dadi amira tayi ajiyar zuciya sannan tace DAN MA BAKI GANSHI BANE.

********* ****** ******** ********* ***********

Bazaka fita ba Wallahi bazaka fita ka barni ni kadai ba nagaji da wulakancin ka matar tace dashi lokaci guda kuma ta matso ta damki kwalar rigar sa tana jijjiga shi kamar zata karya wuyansa ta jefar da kan.

Kada kiyi min haka BATULA yanzu ashe neman abinci yazamo wulakanci?

Haba Tijjani duk fa abunda kake yi awaje ana bani labari wato yan iskan matan da kake tarawa a wajen sunfi ni kima kenan? Kullum saika tafi ka barni tun safe bazaka dawo ba sai tsakiyar dare wai kai ga TELA ko? To bari kaji wallahi ko kaine sakataren majalisar dinkin duniya yau ba zakaje ko ina ba kana nan tare dani ta dada
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment