Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[10/14, 20:00] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Intelligent Writer's Asso.*


*DEDICATED TO: My Mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are I so much luv u my mommah*


*Wannan littafin ba Sabon Novel bane Tsohon Novel dina ne na Dawo dashi,saboda zan sake gyarashi,na fadadashi domin masoyana wadanda basu karanta ba Dama wadanda suka karanta...Ina godiya sosai domin kun nuna min One love💝kuna ma kan nunamin SON SO FISABILILLAH..*


*Typing 1 january 2019*



*Chapter 1*

*Kaduna*

  ⭐Da gudu wata mota 320 kirar toyota,ta shiga cikin wani private hospital mai suna *S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL*


Cikin Hanzari matar tabude motar tafito tayi cikin asibitin da gudu tana fadin"ku taimakamin kada y'ata ta mutu ku taimaka min.." Nurses suka biyota aguje da gadon daukan marasa lafiya,wata matashiyar budurwa ce aka fito da ita daga cikin motan tareda wata dattijuwan mata,tsirtsetsen cikin keta wutsul wutsul alamar yana gab da Fitowa Ihu take zabgawa iya karfinta tareda wasu maganganu marasa ma'ana Da Hanzari suka gungurata sai labour room,Hajiya karima takalli Momma tace"To ai sai kira d'anki shafaffe da mai ya taho ya girbi abunda ya shuka" tafada dawani irin izgilanci,Momma tayi murmishi irin nata kan tace"Ayyah Hajiya zai zo ba"a gabanki namai waya ba kan mufito,insha yanxu zai zo kila wani abun ne ya tsaidashi"Tafada tana duban Hajiyar yamutsa fuska tayi zatayi magana kenan Kamshin turaren azzaro visit yafara musu maraba ko ba'a fada musu ba sunsan mamallakin kamshin.


Momma takara fadada fara'arta daidai lokacin da suka kariso maza biyu ne cikin shigar suit Black and ash,rigar likitancine saye acikin su,Daya daga cikinsu ya Karisa yana Fadin"Momma Har kun iso?


Cikin fara"a tace"mun iso Babana kashiga sun shiga da ita ciki"mtswssss tsakin daya katsesu kenan suka juya atare suna kallon Hajiya kari datake zabgamusu Harara,tace cikin kallon raini"Kaga mallam ba mgana zaka tsaya yi ba yata nakeson nasan Halin data ke cike,tundazu anshiga da ita bawani labari"Tsam dukkansu sukayi da rai kafin momma tayi karfin halin zame Hannunta tana Fadin"Babana Hanzarta kashiga ga Halin da *SAKINATU* take ciki.

cikin takaici da bakin ciki ya juyo wow!! abunda na Furta kenan dogon bufullatani mai cikar zati da kamala,yanada tsawon da dan kibam murjewa,dogon Hanci ya mallaka tareda madaidaitan dan bakinsa pick kamar yana shafa janbaki idanunsa,bakin gashin kansa yakwanta ye luf dashi,zagayayyen sajensa yakaramasa kwarjini Fari ne tas mai jaja din nan abun burgewa goshinsa dauke da tabon salla wanda yake kara masa kima a idon mutane,wani siririn gilashine mai karama Fuskarsa kyau sanye a idanunsa,kallo daya zakamai ka fahimci tsayayyan Namiji ne mai cikar zati da Haiba

*DR SAFWAN SALE SAFANA* kenan likitan daya kware gurin kula daduk abunda yashafi mata wato gynea Doctor wanda ke tare dashi *DR TAHIR* ne Abokine kuma Amini garesa kuma abokin aikinsa dasuke aiki akarkashin asibitin shi Dr safwan din.


Sai da ya isa kusa da ita yadan ramkwafa yace cikin dakakkiyar murya"Barka da zuwa Haji......."

"wai shi na tambayeka"ta katseshi "yata nake bukatar jin Halin datake ciki anshiga da ita tundazu naji shuru'"

takareshe fada tana wani jijjiga kamar wata yar daba,yadade tsugunne kafin yamike cikin sanyin jiki,ya Nufi kofar labour room din yasa Hannu a handle din kenan Wata murya cikin karaji da azaba yaji tana fadin

"Allah ya isa tsakani na dakai safwan,kayi min ciki kabarni da wahala,kacemin Haihuwa babu wuya...Gashi....Gashi kabarni da wahala  kai babu abunda kasani sai ci🙈kamar tuwo wlh bazan sake yadda dakai ba" cikin bakin ciki da Nadama yasaki Hannun kofar ya juya ya Fara Tafiya duk suka bishi da kallo Hajiya kari tace cikin daga murya"Kai safwan ina zaka ko bakajin ihun da sakina takeyi ne....".Ina ko waiwayowa baiyiba saima kara sauri dayayi har yabace daga gurin.


Cikin Takaici Hajiya kari tadaga Hannu sama tana Fadin"wayyo ni karima nashga uku"kan ta isa kusa Da momma tana Fadin"ke wata irin uwace kinaganin wulakancin da d'anki yayi ma y'ata ammh kin gagara mai magana,saboda yagama cin moriyar ganga ya dirkamata ciki ko"?

Takareshe Fada Tana zaremata ido,Momma tayi mirimishi daya zaman mata jiki kam tayi magana Dr Tahir yarigata dacewa"Am....Hajiya kiyi Hakuri i promise u sakina Zata Haihu lafy"yana gama fadar  haka ya bude Kofar Labour Room din ya Shiga.



Dakyar Dr safwan ya karisa office dinshi cikin kunan rai,toilet yafada yasakarma kansa shower ko kayan jikinsa bai cireba Haka ruwan keta kwararamai yafi minti talati ahaka so yake yarage radadin dake addabansa,Haka ya Fito ruwa na diga ta ko'ina ajikinsa kan kujrerar dake office din yafada yana maida Numfashi.


Har abada baisan yaushe zai zama mutum a idanun sakina da mahaifiyarta ba,baisan yaushe sakina da Mahaifiyarta zasu daina cimai mutumci  ba shida mahaifiyarsa ba,baisan sai yaushene zata darajasa ta kallesa amtsayin miji ba bai sani ba,bai sani ba,yafada da karfi idanuwansa sun canza launi.


Yafi minti Hudu acikin wannan yanayin kafin ya sake Bude idanuwansa,gabadaya Zuciyarsa ta gama cika da wani kunci kansa na sarawa lokaci daya jijiyoyin kansa suka Dago,kansa ya Dafe lokaci daya yana Share Ruwan Dake Diga daga saman kansa,kafin ya sake komawa ya jingina da jikin kujeran yana maida Numfashi a jere kamar wanda yayi gudun tsere.


Runte idanunsa yayi yana ajiyar zuciya Lokaci daya yana Saukar Da Numfashi Daga ganin yadda yake yi zaka fahimci yanayin Dayake ciki na bacin rai da dacin Zuciya,idanuwansa ya bude yana bin Kofar shigowa da kallo lokaci Daya Abubuwan da suka Faru abaya suka fara dawowamai daki daki kamar alokacin Abun ke Faruwa tamkar yana kallo cikin magijin talabijin.


*Domin samun kasancewa cikin masu karanta Sanyaya biyu na Mr Bello da Matar Naseer kan 350 duka biyun Single 1 kuma 200 vips kuma 400 ne Duka biyu kuma 600 ne Muna maraba daku masoyanmu Sai kunzo*


Commets,share,like and vote....


*Anitha..*
[10/14, 20:00] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*DEDICATED TO:My mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*

*02*

*SHEKARUN BAYA*

" *DR SALE HABULE SAFANA* shine cikakken sunan Mahaifin Dr Safwan wanda d'ane ga marigayi Justice Habule safana kafin Allah yamai Rasuwa,yayi gwagwarmaya agwannati har kawo mutuwarsa

Dr sale habule safana Haifaffan garin safana ne dake jihar katsina,yana da shekara bakwai aduniya Allah yadauki ran mahaifinsa,Mahaifiyarsa Hajiya Maryam wacce suke kirada Hajiya mama ita tadinga kula da danta har yagirma,Yayi sakandiri sch dinsa a barewa college dake zaria anan kuma yahadu da Aminsa kabir kankia ganin sun fito daga jaha daya yasanya abotarsu tafi tafiya daidai.

Bayan sun kamallah makaranta suka Fada ABU ZARIA a inda Sale ke karantan medicine shikuma kabir political science,ammh duk da haka suna Haduwa in basuda lectures,Haka rayuwa tacigada da tafiya Har kabir ya kammala digirin dinsa ya dora masters dinshi shikuma alokacin sale yatafi Bautar kasa.

Sale a garin adamawa yatafi bautar kasa kuma achan Allah yahadasa da mahaifiyar Safwan Hadiza,Hadiza mahaifaffiyar Adamawa ce bafullatanan asali, marainiya bata uwa ba uba sai kanin mahaifinta wanda yariketa mai suna Baffa Sani Hadiz bata zurfafa lilimi ba iyakarta sakandiri ammh masaniya littafan Addinin muslunci tana da ilimi fiye da tunanin mai karatu bai kammala bautar kasa ba Allah ya kulla aurensu tareda jajircewan Hajiya mama.

Lokacin da'akayi bikin kabir kankia na kasar spain yaje yin phd dinsa,sai da yadawo yaji amininsa yayi aure hakika ya tayasa murna kwarai matuka samun mace irin Hadiza,Macece kyakyawa dogowa mai dogon Hanci da gashi,Bayan kammala bautar kasarsa yafara aiki da Aminu kano,Yaso ya dauki iyalansa sukoma kano da zama Hajiya mama taki amincewa dole yasa yabarsu nan safana yana zuwa musu weeked

Bayan kammala karatun kabir kankia yafada siyasa kadangadan akuma lokacin iyayensa suka masa aure da yar uwarsa Karimatu,karimatu tun tana karimar shegiyar makirace,gata bawani kyau ba bakace mummuna ga gajarta,tun tana yarinyanta take bala'in son auren mai kudi bata shiri da takala,gata da kyashi da hassada ga bariki kala kala dan dai babu yadda zai yine yasa yahakura ya amshi karima.





Yafara rike mukamin sakataren gwannatin janar katsina akuma lokacin Hadiza ta haifi Safwan Hakika tunganin Farko da karima tama Hadiza taji ta tsaneta saboda tafita kyau uwa uba hankali Natsuwa da tarbiya kai akomai tadarata shiyasa lokaci guda kyashi ya shigeta,batawani sakarmata sai kiga tawani yamutse yamutse kamar taga kashi shiyasa Hajiya mama ganin Farko tace"Kabiru ina karoro wannnan ruwan yan Duniyan"kai tsaye agabanta mirmishi kawai yayi itakuma karima tadago tana karema Hajiya kallo ta kasan ido.





safwan yazo cikin gata,badewa mahaifinsa ya tafi london karo karatu sai da ya shekara uku kana yadawo lokacin yazama consultand,Safwan nada shekara biyar iyayensa suka kaisa Nigeria turkish.tunda Hadiza ta haifi safwan bata kara Haihuwa.





Haka dai Rayuwan ta cigada juyawa cikin nasara da kwanciyar Hankali lokacin da Safwan ya kammala secondry sch dinsa lokacin Da Allah ya karbi ran Mahafinsa hatsari yayi ahanyarsa tadawowa daga kano hakika matuwar Dr sale Habu safasa ta girgiza yan'uwa da abokan arzika,Alhaji kabir yaji mutuwar Amininsa matuka sai dai Hakuri






Hajiya da Hadiza wacce Safwan kekira da Momma suka dau dangana suka maida Hankalinsu wurin kula da safwan,Lafawar abun yasa yadage kasar malesia zuwa karatun medicine sai da ya shafe shekara sha kana yadawo lokacin yazama cikakken likitan mata.








Shima din da Aminun kanon ya fara aikin kan chukun chukun bude asibitinsa ya kammala da taimakon Dady Alhaji Kabir kanki wanda yake matsayin kwashinan ilimi ta jahar katsina.







Koda bude asibitin ya kammala baida na aiki da Aminu kano ba Saida ya tattaro Su Hajiya suka dawo garin kaduna kana ya maida Hankalinsa kan asibintinsa,Dr tahir Aminsane wanda suka Hadu a malesia course daya suka karanta,kuma yan kasa daya shiyasa abotarsu tayi karfo Shiyasa bayan ya kammala asibitin ya Nemosa don Atafi tare







Alhaji kabir bai yada iyalan Dr sale ba yana kokarin ziyartarsu in yasamu dama,duk abunda suke bukatu tunkan suyi mgana yake kawo musu Hakika shi mutumin kirkine sai dai Karima tanajin bakincikin abunda yake musu dan dai bayya zatayi duk da yanxu ta mallakeshi sai abunda tace yakeyi





*WACECE SAKINATU*

SAKINAT KABIR KANKIA shine cikakken sunanta yace ga kwamishina Alhaji Kabir kankia da Hajiya karima wacce ake kira Hajiya kari,yayansu hudu salmace babba tana aure a portharcort wani controller ne sai laila dake auren wani dan kasuwa a kano,sai Sakina daga ita sai Ummi.


Gabadaya ya"yan Hajiya kari laila da sakina,sune suka dauko halayyanta wanda ma harsun gyasheta Salma ce da Ummi kadai suka fita dabam,dukkansu suna da degree sakina business admistration takaranta Tana son taga tazama yar kasuwa tana juya kudi ahannunta shiyasa tana dawo daga london bayan ta kammala masters dinta Mahaifinta ya tallafamata,tafara odar kaya daga dubai zuwa Nigeria irinsu dogayen riguna da takalma da jaka,kayan maza kai duk abunda yadanganci sawa da kwalliya,cikin lokaci Allah yasa abun albarka cikin shekara biyu sakina ta bunkasa tayi kudi tuni takeda dankara dankara shaguna a kano,kaduna,katsina,zamfara,da gombe,Sakina boutique and costimetics,sakinat shoes,etc.



Gabadaya Hajiy Kari bata kula da tarbiyan yaran ba kwamishina baya zama so komai na Hannunta,shiyasa sakina tataso tun tana karama bata kunya ga raina na gaba da ita bata da kunya ko kadan bata iya girmama nagabada da ita ba.



Sakina bawata kyakyawa bace ta azo agani bakace gajera ammh saboda shafen nan na yaran zamani yasa takoma Fara,Wani gajeran hanci gareta tana da dan tudun baki,kan nan kamar Hammatar dan iska kullum cikin gashin doki take,tanason mu'amala da abun mai kyau duk da ita din bamai kyau bace,Sakina bata kaunar talaka ko kadan shiyasa danginsu na kanki kowa yasanta da rainin arziki shiyasa kaf suka fita harkansu sboda Hajiya kari inrin matan nan ne masu kyashi arziki daga ita sai mjinta da yayanta.


Sakina yar gayuce ta karshe kullum cikin shigar alfarma zaka ganta,to tazo kaduna duba shop dinta taji zazzabi ya rufeta tana Hanya shine tafada asibitin Dr safwan ganin farko tamai yasace zuciyarta wanda dagashi har ita basusan juna ba saboda kowa ba kasar nan yayi karatunsa ba,Ada ta dauka wasane sai da takoma gida kana ta tabbatar da takamu da son Dr safwan,tayi kokarin tayakiceshi ammh hakan ya faskara,abinciken da'aka matane tagano dane gun Aminin Abbanta.


Da tama hajiya kari magnar kin bada goyan baya acewarta baida qualities din auren yarta,ammh sakinat taki hakura,taci gaba da shisshigemai da kissa da kisisina,Da hajiya taga yarta taki hakura yasa tashiga tafita har soyayyah mai zafi ta kullu atsakaninsu,Lokacin da kwamishina yaji labari yayi matukar farinciki dasamun suriki irin Dr safwan,kuma yakara zumunci tsakaninsa da amininsa duk da baya raye.



Da Hajiya mama taji lbr tadaga tsalle tace bata yarda ba saboda sanin mugun halin Hajiya kari ammh Dr safwan ya tubure dole tasa ta amince ita daman momma batada matsala cikin lokaci kankanin komai ya kammallah Amarya tatare a gidanshi dake kaduna,mai dauke da shashi biyu daya na momma da Hajiya daya shine mallakin sakina





Sunkwashi amarci na tsawon wata guda kafin halayyan,Sakina sufara bayyana.









Commet
And
Share
[10/14, 20:00] Sis Janafty: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HYlSeJb3pcr33n3fhabu5h


*NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
  
*DEDICATED TO My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


*03*

------Hallaya ta farko data fara bayyana shine kazanta da lalaci,kafin Hajiyarta tasamo mata masu aiki Sai dai shi Safwan inyagaji da ganin kazanta ranar karshen mako yazage ya tsaftace gidan tun yana mgana har ya zuramata ido.

Girki kuwa baida darajar da sakina zata girkamai abinci to tama iyane banda indomie bata iya dafa komai ba,kullum sai dai masu aiki su jagwagwala su ijeye sai da kullum yana aikin rab'awa sashin Mommah yanacin abinci, gashi batason zaman gidan kullum tana Hanyar katsina ko kano,Ko yamata mgana baji takeyi ba shiyasa ya zuramata ido.

Raininta har Mommah bata kyaleka ba yimata take dayake Mommah macece mai Hakuri da kawaichi Mommah irin matannan ne masu mugun Hakuri ko zagin ta kayi sai dai tama mirmishi,ashekaru bata wuce48 ba,shiyasa sakina tayi bala'in rainata tadinga daka mata tsawa,Hajiya mama ce take shakka domin itace big problem dinta agidan Safwan.

...Hajiya mama Dattijuwa ce yar kimanin shekara saba"in aduniya,Bata daukan raini ko kadan irin tsofaffun nan ne wanda komai ke ransu gameda kai saisun fada maka sai dai kamutu tanada faran faran da jama'a dason mutane tun tana safana macece takowa makotanta kuwa kamar yan'uwanta Haka ta daukesu,tanada fada in aka tabota gata wani lokacin da ashisshigi koba"ayi da"ita ba,saita tsoma kanta,shiyasa Sakina ta tsaneta saboda tana mata katsalandan a al"amarinta game da Mijinta Safwan.

Wani lokacin Hajiya ke tarema mommah tacima sakinar mutumci intaga tana mata Rashin kunya,inkuwa dukkansu suka bata haushi tasharesu saboda Takaichin yadda Mommah ke zama Sakina namata yadda Taga dama kuma tana matar Danta ,Safwan yarasa yadda zaiyi da sakina daya tashi daukan mataki mommah tahanasa.

Ranshi bai kara baci da Sakina ba saida tayi Rashin lafiya tafara, zubar jinin,Dubar farko ya fahimci taje anrufemata bakin mahaifa dayake Allah ba'a mai dabara sai ga ciki ya bulla agefen mahaifan bai mata mgana ba, sai da yayimata operation yamaida cikin,cikin mahaifa ya sallamota suka koma gida,Sakina taga bacin ran Safwan wanda bata taba gani ba mgana har kunnin kwamishina shima yacimata mutumci ba'a son ran sakina ba tacigaba da renon cikin jikinta domin ita atsarinta babu Haihuwa Allah shi kyauta,Shawaran Hajiyarta da laila ne sunfada mata karta yarda yamaida ita akuya tadinga zazzagamai ya"ya karshen tadurkushe ta zama Tsohuwa shikuma ya auro wata.

SAFWAN yaci sunan mahaifin momma ne shiyasa bata iya fadar sunansa sai dai da babana, Mutum ne mai Hakuri saboda Nonon Momma ya tsotsa,shekararsa ta haihuwa 30 yanada kawaichi da dattako mutum ne mai Nagarta kallo daya zakamai kakirasa ustaz ammh social ne yana da zurfafan bincike a bangaren ilimin addini duk da matsayinsa na likita yahaddacce Qur'ani tun yana shekara sha hudu aduniya saboda jajircewan mommah agaresa, da sauran littafai irinsu,muwadda malik,sahihul bukhari,iziya,sira,fiqhu,dadai sauransu,yana da tsantsane da addinsa matuka mutum ne mai yalwar fara"a,yana bala"in kaunar mommansa saboda itace ginshikinsa da kakarsa Hajiya mama.


Abangaren kaya yafison manyan kaya atsarinsa yafison yasanya shadda gezner da yadi mai stantsi ammh saboda yanayin aikinsa yasanya yake surkawa da suite ammh duk Ranar jumma"a kowa yasani shigar manyan kayan ne atsararinsa.Yana da zuciya da fushi wanda yakan dade kafin yayi irinsa fushin kuma in yayi fushi da abu na har abada yakeyi,bangaren abinci yafison abincin gargajiya,irinsu dambu,fate,fankasau,tuwo miya kubewa da dai sauransu.


Aurensa da sakina babu abunda yakaru dashi sai ci baya tunbayan aurensu matsaloli suka dunga kunno kai saboda sanyinsa yasa ta rainasa bai isa yamata mgana taji ba shikuma baisan hayaniya da kwakwazo dat why yake yakyaleta uwa uba yana ganin mutumci mahaifinta,A yan"uwanta kaf bamai darajashi sai salma da ummi Hajiya kuwa da laila dama sune aminan sakina duk abunda sukace shi takeyi,ko bangaren auratayyah bazai iya dora komai ba domin sai inyarasa yadda zaiyi ne yake neman sakina,saboda baya samun gamsuwa bata iya komai na fanni bama miji kulawa ba,gashi bata rabo dama kanta pixsing kullum suka gama saduwa da juna sai yakoma yana jinyar kansa saboda tsabar yakusan dayake sha,ita bata damu danashi bukatan ba nata kawai tadamu dashi tayimai sharf kamar kayan wanki yaci yatashi bawani salo balle kukan kissa,ita ba abunda tasani sai ci ta kwanta sai gayun kawai awaje ammh aciki sai takaichi.



Ko Rainan cikin sai abunda yagani sai yayi sati bai nemata ba ammh duk ranar daya nemata bada son ranta ba sai yakusa kuka saboda takaichi itadai sakina ba abunda tasani sai harkan kasuwanci ko dan kayan gyaran jiki bata damu data sha ba dan tagyara kanta ba a"a ita abunda tasama gaba shine agabanta,shiyasa bai rabo da azumin litini da alhamis Domin kare kansa daga halaka.


Kullum ta kalli cikin jikinta sai ta zageshi aranta,Haka tacigaba da renon cikin,cikin bakinciki da danasani saboda mahaifinta yace wlh yaji lbrin wani abu yasamun ciki kashinta ya bushe,ga bakincikin tadaina fita ko'ina tunda cikin ya tsufa,kullum cikin zuwa Hajiya take tana duba yarta acewarta,babu mai kula da ita,gashi ta ranma mommah saboda sunganta bamai karamniya bace.



Ranar da Sakina tafara naguda tun Safe Dr safwan yatafi asibiti,kuma da safe ya bartaa tana barci,itakuwa Hajiya daman sunyi waya,da ita tafadamata batajin dadin jikinta shiyasa tun safe,tasa dereba ya daukota suka kamo  Hanya koda ta iso ta iske sakina tafara jigata,shiyasa da Hanzari tafito da ita zasu wuce asibiti,Itakuma momma tafito tazo taduba sakinar sai taci karo dasu,cikin azama ta isa tana tambayan lafiya"harara kawai Hajiya kari ke zabgama mommah takasa bata amsa,da sauri Momma tace Hajiya bari  in dauko mayafi insanar da hajiya muje"Ko kallonta batayi ba koda ta isa,shashensu ta iske Hajiya mamq cikin daki take fada mata"Tabe baki hajiya tayi kan tace"Allah raba lfy nikin gama barci nakeji in kinfita kirufemin kofar"

daga haka tashige ta barta nan mommah takira Dr safwan take fadamai gasunan zuwa da sakina zata Haihu,yashiga rudu yace su hanzarta,Koda tafito Hajiya na kokarin sanyata cikin mota tataimakamata suka sanya suka nufi asibitin tanaji Hajiya kari takira yarta laila tanafadamata abunda ke faruwa tana zagin Mommah din da danta wai sun bar Sakina agida zata mutu sai da ita tazo Daga katsina,mommah kuwa sai dai kawai tayi mirmishi ta kauda kai.

Shine dalilin kawota asibitin da abunda yafaru.


WANNAN KENAN







Commet
And
Share
Vote.
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_


*DEDICATED TO My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*04*


-----Tura kofar office din akayi tareda shigowa,Dr tahir ya kariso yana mai karewa Dr safwan kallo wanda ke kwance ruwa nadiga ajikinsa duk ya jika kujera kwaya dayan datake cikin katob office din,cikin azama Dr Tahir ya isa garesa yana Fadin"Dr Safana wht wrong with u"?

yafada yana mai dafasa,ajiyar zuciya Dr safwan ya sauke yana mai sauke gwaron numfashi bayan tsawon lokacin daya dauka yana tuna iya tsawon lokacin daya dauka yana kunsan bakincikin sakina da uwarta.


Ya dago idanunsa jajir kamar garwashi yana bin Dr Tahir da kallo,kallo daya Dr Tahir yama safwan yaji mugun tsausayinsa ya tsirgamasa hannu yasanya yana jijjiga kafadarsa yana fadin"Dr Safwan Dan Allah Dan Annabi kayi.....!"

"Nagaji Nagaji Tahir wlh Nagaji"ya katsesa cikin kunar rai da kosawa"koda yaushe kaida momma kalmarku daya inyi hakuri shin bakuda wani abunda zaku iya gayamin sai kalmar Hakuri eye"?

yafada yanawani zaremai ido idanunsa sun tara kwallah,cikin sanyin jiki Tahir ya karisa kusa dashi yana riko hannunsa,yana fadin"Babu...Babu safwan babu wata kalma data dace dakai bayan Hakuri,nasanka kacigabada da hakurin daka saba Allah nasane dakai"shuru Dr safwan yamai yana kallonsa kamar yana karantan wani abu atareda shi,kara damke hannunsa yayi yana jijjigawa alamar lallashi cikin kasala ya zare hannunsa ya isa ga wata durowa dake cikin office din akafe ya bude sai ga wasu jeren kayan sun bayyana kai tsaye ya ciro su yakama Hanyan toilet Dr Tahir yayi zuru yana kallonsa sai dayaga yana shirin shiga toilet don kana yace

"ta sauka lafiya an sami DR SALE SAFWAN SAFANA Da sauri ya juyo yana kallonsa kan mirmishi ya subuce masa zaiyi mgana kenan Dr Tahir ya rigasa dacewa"Both momma and bby are in good Health yanzu ma zan basu sallama su koma gida" gyada kai yayi kafin yace"thanks so much Dr....."!

"Zan maidasu gida"Abunda tahir ya katsesa dacewa kenan kafin yafice mirmishi kawai Dr safwan yayi kafin ya girgiza kai yafada toilet.

***

Dr Tahir ya tura kai Dakin da"a ka kawo sakina bayan angyarata,ita da bbyn nata,Momma ta amsa sallaman tana Fadin"Attahiru sannu da kokari "

"Yauwa mommanmu Barkanmu fa"Yafada shima yana mirmishi karisawa yayi yana mai kara kallon babyn wanda kamar Dr yayi kaki,momma tadago tana Fadin"kaga danku ko,kungirma yanZu inashi baban nawa yazo yaga dansa mana"Tahir yace zaizo yanzu momma bari nadubata in babu matsala inmai daku gida"

Momma tace"Alhamdulillah..."Gurin sakina ya karisa wacce ka zaune kan gado tana shan ruwan shayi yayinda Hajiya kari ke gefenta tana faman buge bugen waya"cikin mirmishi yace"Sannu madam munfa gode"Kallon raini ta watsama Tahir kan tace"Dole kace kungode kun hadani da aiki kun gudu"Yasan da wanda take shiyasa yace mata"is ur duty ai madam kema kinsani Haihuwa na matane ba maza ba kuma meye ribar auren soyayyah,A Haifi ya'yan soyayyah"yakareshe Fada yana dariya kasa kasa tunda yafara mgana Hajiya kari dake waya take zafgmai Harara yana kallonta ta kasan ido aransa yace'oho dai
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment