Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[04/02 à 08:22] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```

Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR*🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻

*GAJEREN LABARI NE...*✊🏻
*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*

```MRS SADAUKI 💫✍🏻```

_______________________


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*


*PAGE* 1-2


A guje ya nufi ƙofar gida ya na shirin fita Abbasi ya rufe ƙofar.Tsayawa yayi cak ya na zaro manya fararen idonsa wanda baƙin gawayin da ya shafe fuskarsa da shi ya ƙara fiddo hasken su,cikin murya mai taushi Abbasi yace "ina za ka je kuma Mahomet?"bai bashi amsa ba sai waigawa bayansa yayi ya na kallon Ammi hannunta riƙe da almakashi cike da tsoro ya koma bayan Abbasi ya na mai ɗora hannuwansa masu datti kan farar shaddar Abbasi.
"Ammi tunda bai so ki bar shi kawai"cewar Abbasi , Ammi tace "ba ka ganin duguzar ta yi yawa kamar wani mahaukaci ya bari na ɗan rage masa"daga can bisa ne Hajiya Atine ta bushe da dariya tace "yo da can mine ne in ba MAHAUKACIN ba?"kai Abbasi ya ɗaga ya kalli mahaifiyar ta shi ya na mai girgiza kai kafin ya juya ya kamo hannun Mahomet.
Ammi na gaba su na take mata baya har suka isa ƙurya gida inda a can part ɗin ta ya ke,su na shiga falo Mahomet ya ja ya tsaya bakin ƙofa ya na mai sake kallon almakashin hannun Ammi ganin hakan ya sa ta ajiye shi bisa table da gudu Mahomet ya nufi ɗakin sa ya shige yayinda Abbasi ya bi bayan shi.



Tsakiyar gado ya tsinkaye shi a zaune ya jawo bargo ya rufe dukan jikinsa ya bar fuskarsa a buɗe ya na kallon ƙofar shigowa.Ganin Abbasi ne ya sa shi dirowa ya na kallon shi,ajiyar zuciya ya sauke yace "mu je na wanke ma wannan abun da ka shafa a fuska bai yi ma kyau ba" kafaɗa ya maƙe tare da girgiza kai alamun bai so.
Abbasi yace "ba zan yi ma wanka mu je fuska kawai zan wanke ai ba ka yi dauɗa ba"cike da yarda da lafazin ɗan uwan na sa ya nufi toilet.Fuskar sa Abbasi ya wanke masa da soso da sabulu nan fah ainahin fuskar sa ta bayyana wacce ta ke doguwa siririya mai ɗauke dogon hanci har baka.Madubin da ke cikin toilet ɗin Abbasi ya nuna masa,kallon kansa yayi sai ya saki murmurshi dimple ɗin sa suka lotsa jajayen laɓansa sirara suka buɗe fararen haƙoransa suka bayyana.
Cike da dubara Abbasi ya raba sa da kayan jikinsa,yayinda Mahomet ya shagala da kallon kansa dan a duniya babu abinda ya ke so sama da madubi.
Pampo ya jawo ya fara yi mashi wanka ya na watsa masa ruwa irin yadda ake yiwa yara,Mahomet ya shiga ƙyarƙyata dariya ya na jin sanyin ruwan na shiga ɓargon jikinsa.
Man wanke kai Abbasi ya shafa masa nan fah aka fara daga dan kuwa babu abinda Mahomet ya tsana irin a taɓa gashin kansa,kamar wani ƙaramin yaro haka ya shiga rera kuka tare da ƙoƙarin zillewa Abbasi kuma na ta ƙoƙarin wanke masa kumfa.



Ko da aka gama wanka tuni Mahomet yayi fushi da Abbasi wanda kusan kullum haka su ke da zarar yayi masa wanka😂 mai ya ɗauko zai shafa masa amman ya ƙi bari sai ma gado da ya ɗale ya duƙunƙune.



Ganin haka ya sa Abbasi yin murmushi ya fito,a falo ya tarar da Ammi ta yi tagumi ta na ganinsa ta miƙe tace "duk shaddar ta ka ta ɓace da dauɗa halan wanka kayi mashi?" Abbasi yace "bai komi Ammi ai da na kai ta wajen wanki tsaf za ta dawo,wanka nayi mashi ya ƙi barin ma na shafa masa mai"
Ammi ta goge ƴar ƙwalla tace "Allah biya ka da mafificin alkhairi Abbasi yadda ka kula da ɗan uwanka Allah baka ƴaƴa masu jinƙai"yayi murmurshi yace "amen Ammi na gode zan tafi na canza kaya,a bashi maganin shi"da "Toh"Ammi ta amsa.



Gorar ruwa ta ɗauko cikin frigo ta nufi ɗakin sa,ya nan kwance ya rufe a bargo kamar sabuwar amarya.Ya na jin muryata ya yaye bargon ya zauna tsakiyar gado daga shi sai gajeren wando wanda Abbasi ya saka masa kafin yayi ƙoƙarin shafa masa mai.
Ledar maganin da ke bisa didilin gado ta buɗe tare da ɓallo masa magani ta basa,babu muso ya karɓa ya hanbaɗa baki sai da ya tatamna sannan ya karɓi gorar ruwan ya shanye tass.
"Ammi..."ya furta da muryar sa mai kamar ta ƴan shaye-shaye, kallonsa tayi ba tare da tace komi ya murmusa ya kuma cewa "Ammi ?"tace "umhum Mahomet ya jikin na ka?"sai da ya karye wuya har bada wani ɗan sauti kafin yace "da sauƙi zan yi sallah"cike da murna tace "dagaske Mahomet ?"kai ya ɗaga mata.
"Je kayi alwala to amman ka yi addu'a in za ka shiga toilet"bai ce komi ba ya sauka daga bed ya nufi toilet yayi addu'a ya shiga,bakin ƙofa ta tsaya ta na kallon yadda ya ke alwala daidai bai manta yadda ake yi ba dan rabonsa da yin Sallah an fi wata uku.
Doguwar riga jallabiya ta miƙa masa tare da shimfiɗa masa tapis,iƙama ya fara yi kafin ya ƙabarta ya fara karatu ya na yi ya na tsayawa saboda yadda zuciyar sa ke suya raka'a biyu kawai yayi salamce.
Juyowa yayi ya dubi Ammi wacce ke bakin gado,saitin zuciyar sa ya nuna mata da sauri ta nufo sa ta na tambayar "mi kake ji?"bai iya cewa komi ba sai lumshe ido da yayi....




★★★ *MAI JAN GERO*


Wani yanki ne daga cikin ƙauyen Tchadoua wacce ke garin Maradi jamhuriyar Nijar.
Ginin ciment ne wanda ya sha ya harshe tun daga waje har cikin gida.
Tun kafin ka shiga gidan za ka iya jiyo sautin kukanta tare da suratai na azaba irin na sargantatun yara.
"Alƙur'an tunda na fara sai kin bari na ida,yo ina dalili yarinya kamar jikanyar lasaru kullum kai a tsefe kamar chrétan (chrétienne😹)"Inna ke faɗa ta na mai sake matse kan Maryam wacce ke kukan kitso.
"Ai dai gashi na ne dan haka ki sake min kai nace ban so ko doli ne?ke da kika damu ba sai kije ayi maki ba"cikin kuka Maryam ke faɗar haka,Inna ta tuntsire da dariya tace "ai fah dai ko mi za ki faɗa sai na idasa" Maryam na kuka na ƙari Inna ta yi mata zane shidda (manyan kitso)ta na gamawa ta tureta daga gabanta tace "sai ki tashi daga gabana ja'ira ke yanzu hakan da na rufa maki asiri ba ki ji daɗi ba?"Maryam na turo baki ta goge ƙwalla ta fita waje.
Bokiti ta cika ta nufi banɗaki,wanka tayi soso da sabulu kafin ta fito.Hannuwa Inna ta shiga taɓawa ta na ce "laha ila...ke yanzu saboda gantali sabon kitson kika wanke?"Maryam ta turo baki tace "to shikenan sai na yi wanka ban wanke kai ba?"Inna tace "eh ta yaya za ki ƙin wanke kai tunda sabuwar amarya kike"ita dai Maryam ba ta kula ta ba ta shige ɗaki babu jimawa ta fito cikin riga da sket na atamfa ta kashe ɗauri.
"Ina zan tafi sayen awara"ta faɗa ta na mai ɗaukar tasa mai murfi,"a dawo lafiya"cewar Inna."To ki ban kuɗin"ta faɗa cikin marairaicewa "a'a ko sisi ba zan baki ba tunda ga abinci can tukunya na dafa"cikin gunguni tace "Ni ban cin wake kuma ai na faɗa maki"Inna ta miƙe daga zaunen da ta ke a kujera ta ɗauko radiyo da ke kan frigo tace "sai ki yi ai,wai an yi ma Ɗiya shegen miji yaushe kika fara tsanar wake?ina ce dai jiya alala kika yi"kwanon ta saki ƙasa ta koma ɗaki ta na kuka.


"Dawo ki karɓa ni ban iya jarabar ki ba, wannan masifa ban san inda kika ɗauko ta ba sai dai can dangin ubanki ni Ɗiyata (cewa da mahaifiyar Maryam) ba haka ta ke ba har mu ka rabu da ita lafiya "fitowa tayi ta karɓi kuɗin ta duƙa ta ɗauki tasar sayen awara kafin ta fice.


Ta na tafe ta na waƙa Habsou Garba "iyee babu kamar Niger🇳🇪dan ku san babu kamar Niger🇳🇪 tashin hankali Niger ba ta gada ba kwanciyar hankali ne mu ka gada....💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻"cak ta tsaya jin Rabe na ƙwala mata kira,daidai gabanta ya tsaya ya na gyara tsayuwa yace "sai ina Autar Inna?"sunne kai tayi ta kasa magana, murmurshi yayi ya kuma cewa "wai Mairo sai yaushe za ki barin jin kunyata?koko sona ne ba ki yi shiyasa kike ƙin yi mani magana?"da sauri ta ɗago kanta idonta suka faɗa cikin na shi.
Tatausan murmushi ta sakar ma shi tare da girgiza kai ta kuma sunne kai.Ajiyar zuciya ya sauke yace "to mu je na raka ki inda za ki je"cikin jin kunya tace "a'a na gode je ka gida kawai ka huta"farin ciki fal zuciyar sa yace "to aikin mi nayi da zaki ce naje na huta? wannan ɓotar da kike gani Baba ne yace na kawo mashi ita gida sam ni ban san yadda ake noma ba balle nayi shiyasa ni ke ta fafutukar yin karatun bokona saboda in samu aikin gwamnati inda za mu huta in mun yi aure"Muryar Inna suka ji ta na cewa "keee!Maryamu sayen awarar ne nan?"da sauri tayi gaba shi kuma Rabe ya shiga gidan su ya na tsinewa Inna da ta hana shi isar da saƙon sa gun masoyiyyar shi.



Maryam kuwa banda dariya babu abinda ta ke a fili tace "hege kaji ƙarya wai bai iya noma ba bayan ga ƙafafunsa nan sun yi futu-futu kamar mai sharar kasuwa,za ka ci ƙwal uban ka ne sai na tatse ka sarai ta yadda ko sunana kaji an ambata sai gaban ka ya faɗi" gidan da ake sayar da awarar ta shiga ta sayo ta dawo gida.
Sai da Inna ta yi mata dundu da baya sannan tace "ban hana ki sauraren wancan ɗan iskan ba?duk ƴan matan garin nan na shi ne ko wacce ya gani ya na so kamar kare shine kika wani sadda kai kamar malam da ɗalibi"
Maryam ta turo baki tace "haba Inna shine sai kin dake ni ?ai dai kin san babu abinda zan yi da wannan baƙauyen ni ɗan birni zan aura"Inna ta dafe ƙirji tace "iyeee!Maryama yanzu ke ce ke faɗar kalmar aure?laha ilah ƙarshen zamani ya zo to bari uban ki Salihu ya zo na shaida masa aure kike so ya yi maki kafin ki jawo ma mu abun kunya"
Maryam tayi rau-rau da ido tace "Ni daga ban ce ina son aure ba"Inna tace "a'a ga shi kuwa sai ƙara nanata kalmar kike"





★★★ *MARADI VILLE*



Tunda Mahomet ya sha ruwan addu'ar da Ammi ta bashi wata irin masasara ta rufe sa,sai karkarwa ya ke ya na rawar sanyi.
Ammi tagumi tayi ta na kallon ikon Allah yadda Mahomet bai son ko kallon kofin da tayi mashi tofi ciki.Ana haka sai ga Abbasi ya dawo cikin shiga ta ƙananun kaya,"subahanallah mi ke damun shi kuma?"Ammi tace "daga na karanta Ayatul Ƙursiyu da amanar Rasulu cikin ruwa na basa"Abbasi yace "sallah yayi ko?"Ammi ta gyaɗa kai shiru yayi ya na kallon Mahomet kafin yace "Ammi sai ni ke ganin ciwon Mahomet kamar ba na asibiti ba ne duba da yadda ya tsani duk wani abu da ya shafi Ayar Allah"Ammi tace "to mu bari har Daddyn ku ya dawo sai mu ji mi zai ce"Abbasi ya zauna kusan Mahomet ya fara yi mashi karatu ai kuwa ya fara zabura.....






Jikar Rabo ce 😎
[04/02 à 18:19] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```

Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR* 🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻



*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*

```MRS SADAUKI 💫✍🏻```

_______________________


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*

*Na manta ne uwanda suka riga suka ga 4-5 to 3-4 ne mistake ne nayi*

*PAGE* 3-4


Kunnuwan sa ya toshe ya na jin tsanar karatun da Abbasi ke rerawa,kafin ya miƙe tsaye ya na zara ido.Shiru Abbasi yayi dan gudun kar ya ɓallo masu ruwa dan ba ƙaramin aikin Mahomet ne ba ya zuba a guje.
"To zauna an gama karatun"cewar Ammi ,kai ya girgiza ya na kallon Abbasi wanda shi ma shi ɗin ya ke kallo.Kai ya jinjina alamun gaskatar maganar Ammi ,a hankali ya janye hannuwansa daga kan kunnuwan ya na mai sauke ajiyar zuciya.
Abbasi ya sosa ƙeya yace "Ammi na manta na gaya maki Daddy yace zai shigo zuwa jibi ƙila ma shigowar safe zai yi"
Ambaton sunan Daddy ya saka Mahomet wangale baki kamar wani ƙaramin yaro,ya shiga murna Abbasi ya murmusa yace "to yanzu ai ka tsaya a rage ma duguza ka ga in Daddy ya gan ka haka ba zai ji daɗi ba"kai ya girgiza cikin muryarsa ta maras hankali yace "sai dai in yi da kaina amman babu wanda zai taɓa min kai"
Ammi wacce ke zullumin zuci jin mijinta zai dawo tayi saurin cewa "Abbasi ɗauko masa almakashin ya gyara da kansa ɗin"


"Tawo mu tafi can tsakar gida "cewar Abbasi ,Mahomet ya bi bayansa sai da ya ɗauki almakashin sannan suka fita tsakar gida inda ba kasafai mutanen gidan ke zama ba.
Da taimakon Abbasi ya ragewa duguzar ta shi tsayi sai kuwa yayi kyau,dama ba'a jima da yi masa gyaran fuska ba.
Kakaɓe masa jiki yayi kafin ya kirawo mai gadi ya kwashe duguzar,Hajiya Atine da ke can gefe tayi saurin ƙarasowa inda suke ta na yamutsa fuska "miye haka Abbasi ?ka rasa wanda za ka yiwa aski sai mahaukaci Ɗan maƙiyiya ta?"rashin jin daɗin furucinta ya bayyana a fuskar Abbasi ƙarara yace "haba Hajiya yanzu wannan furuci ya dace da ke? wannan sam bai dace ba gaskiya sannan ki bar jifar sa da kalmar hauka domin Allah ne ya jarabe shi"ta taɓe baki tace "to ai shikenan Ammin mahaukaci ta zama uwar ka ƙarshen ƙauna kenan ko?sannan daga yau sai yau na haramta maka shiga sashen su"ta na gama faɗa tayi ƙuuu ta wuce ta na hararar Mahomet wanda ya ɓoye bayan Abbasi tun zuwanta.
Hawaye suka zubo masa ya na jin wani ɗaci can ƙasan ransa,a zuciyar sa sai ya ke jin shi tamkar mai lafiya amman da yayi tunanin haka sai yaji kamar an tsikare sa da ƙwalwa sai ya mance taƙamaimai shi ɗin wane ne.


"Wuce ka koma ɗaki kaji?"cewar Abbasi,kafaɗa Mahomet ya maƙe ya na mai riƙo hannun Abbasi yayinda ya fara motsa baki alamun ya na son yin magana amman ya kasa sai kukan da ya kubce masa.Jawosa yayi ya rungume sa tsam a jikinsa, Allah na gani ya na son ɗan uwansa sosai tare da son taimaka masa sai dai mahaifiyar sa ta tsani hakan.Bayansa ya shiga bubugawa ya na rarrashi kamar ƙaramin yaro kafin ya zaro wayarsa, Daddy ya kira amman bai ɗaga ba kawai sai ya aika masa text yayi masa bayanin abinda Hajiya Atine ta gindiya masa.
Can kamar minti goma haka sai ga Hajiya Atine ta fito ta na kumfar baki,tsabar masifa har tuntuɓe ta ke ta na harɗe ƙafafu.Gaban Abbasi ya faɗi ganin ta na waige-waige alamun shi ta ke nema dan tuni sun gusa daga gun da ya yiwa Mahomet aski,sun koma wajen piscine inda agwagi ke wanka.Kallon yadda Mahomet ke nishaɗi ya na kallon yadda agwagin ke ta ɓacal-ɓacal cikin ruwa,Abbasi ya shagala da kallon Mahomet bai san Atine ta hango su ba har ma ta zo gaf da shi.
Ɗauke sa tayi da mari tace "Ni ka yiwa gami da Alhaji ?har ka sa ya na min barazanar igiyar aurena akan wani banzar mahaukaci?"kwaratsin ta ya fargar da Mahomet zuwanta da sauri ya miƙe a zabure cikin rashin sa'a yayi glisser ya faɗa cikin ruwa kwacaaaa.


"Mahomeeee!"Abbasi ya furta da ƙarfi ya na mai miƙa hannu sai kuma ya tsaya cak jin furucin uwa mahaifiya gare sa.
Cikin sake jaddada masa ta kuma cewa "in har ka fiddo sa Allah ya isa nonona da ka sha ban yafe maka ba,ka bari in ya fito ka ja shi zuwa part ɗin su tunda wancan alƙawarin ya karye"



Ido taf da hawaye Abbasi ya kalli Hajiya Atine ya kuma juya ya dubi Mahomet da ke ta wutsilniya cikin ruwa ya na buɗe baki can Allah ya bashi fasahar tashi saboda dama ruwan bai da zurfi sosai dan dai kawai bai da hankalin da zai samu dubara ne.
Ya na fitowa Abbasi yayi Hamdallah ga Ubangiji ya nufe sa,faɗuwa yayi ƙasa ya fara kelaya amai sai kuma numfashin sa ya tsaya cak.A ruɗe Abbasi ya fara danna masa ciki nan ruwa suka ɓulɓulowa ta baki da hanci,sai da ya tabbatar duk ruwan sun fito sannan ya duƙa dan busa masa baki sai dai mi wani irin wari ne ya bugi hancin sa saboda an kwana biyu ba'a canza ruwan ba kuma duk sun yi kashi ciki.
Daurewa yayi haka nan ya buɗe bakin Mahomet ya fara busa masa iska,ba a ɗauki lokaci ba numfashinsa ya dawo jikin sa,sai dai ya kasa buɗe ido.A na cikin haka wayar Abbasi ta fara ruri,Hajiya Atine da ke tsaye bayan su ta kashe kunne jin Abbasi ya ambaci sunan Daddy.
"Ina cikin réunion ne shiyasa ban ɗauki appel ɗin ka ba, amman da na karanta text ɗin ka na ja ma mahaukaciyar uwarka kunne dan haka kar ka biye ta ka kula da ɗan uwan ka"Daddy ke faɗar haka a can ɓangaren,Abbasi yace "Daddy Mahomet ya faɗa cikin ruwan wankan agwagi kuma ya ƙi buɗe ido"yadda yayi maganar cikin rauni shi ya ɗaga hankalin Daddy,da sauri yace "ka ɗauke sa kuje asibiti mana,gobe zan shigo in shaa Allah"ƙit ya katse kiran.


Ya na shirin saka wayar aljihu Hajiya Atine ta fige ta tare da komawa ciki,bai kula ta ba ya gwada ciciɓar Mahomet amman ya kasa doli ya kirawo driver su ya taimaka masa.Har sai da suka isa asibiti ya tuna bai shaidawa Ammi halin da ake ciki ba,ya lalaba aljihu yaji babu waya ya dafe kai ya fito harabar asibitin yace ma Ado "Please je ka sanar da Ammi halin da ake ciki shaf na manta ban sanar da ita ba"Ado yace "sai ni ke ganin gaya mata ɗin zai iya zama matsala mi zai hana mu jira mu ji abinda Dr ɗin zai ce?"Abbasi ya girgiza kai yace "a'a gwara a sanar da ita dan tunaninta zai iya bata ko fita yayi"Ado na shirin magana Dr ya fito ya kira Abbasi .


Ɗakin da Mahomet ke ciki suka shiga,a zaune suka tarar da shi kan bed ya ƙi barin a saka masa ƙarin ruwa saboda a samu ƙarfin jikinsa ya dawo.Da lalami Abbasi ya ciyo kansa a ka saka mashi ƙarin ruwan da bai ɗauki minti goma ba ya ida,"ya kamata a cire masa wannan jallabiyar tunda ta jiƙe kar mura ta kama shi"cewar Dr Abbasi yace "ok yanzu da mun isa gida za'a cire"ordonnance Dr ya bashi ya jawo hannun Mahomet suka fito suka shiga mota Ado ya ja su.



A bakin get suka tarar da Ammi ita da mai gadi ya na yi mata bayanin abinda ya faru,ajiyar zuciya ta sauke ganin Mahomet ya fito daga mota bisa ƙafafun sa.
"Ammi ga mu mun dawo mu je ciki"cewar Abbasi,Ammi tace "eh yanzu mai gadi ke faɗa min,yaya jikin na sa?"Abbasi na riƙe da hannun Mahomet ya amsa mata da "alhamdullah"su na masu shigewa part ɗin ta.




★★★ *MAI JAN GERO*


Banda murƙususu da matsar ƙwalla babu abinda Maryam ke yi tun safe,ta rasa yadda za ta yi ciwon ciki mai azaba ke damun ta shiyasa ma ta tafi makaranta ba ta daɗe ba ta dawo gida ta tarar kuma Inna ba ta nan ƙila ta shiga makwabta kasancewar ba ta rufe gidan ba sai ɗaki.



Ta na nan kwance taji marar ta haɗi da cikinta sun murɗa lokaci ɗaya,da sauri ta ɗauki buta ta shige banɗaki ta fara zawo🤣 zuwa can kuma ta fashe da kuka ta kiran ta shiga uku sakamakon ganin jini da tayi sai zubowa ta ke.
Ta na kuka haka ta wanke ta fito,ciwon ma sai ta neme sa ta rasa sai tunanin yadda za ta cewa Inna ta ke.Tashi tayi ta koma banɗaki ta duba pant ɗin ta tare da shafowa ,jinin ta kuma gani ai kuwa ta ƙara sautin kuka ta fito ta fara zagayen gida sai da ta gaji ta zauna ta rabka tagumi.Tsawon lokaci ta na zaune sai taji damshin ruwa kamar ya jiƙata,tashi tayi ta kwance zane nan ta shiga tashin hankali ganin ya ɓace wani uban ihu ta buga wanda yayi daidai da shigowar Inna.
Da sauri ta nufo ta tana cewa "ke lafiyar ki?"
"Wayyyo Inna shikenan nayi abun kunya na haifi ɗan shege, wayyyo Inna na haihu amman ban ga jaririn ba"
Ƙirji Inna ta dafe sai kuma idonta ya sauka kan zanen da Maryam ta jefar ƙasa,da sauri ta ɗauke sa tace "jinin mine ni ke gani?"baya Maryam tayi tace "wlh Inna nima haka na gan shi tun safe ni ke jin ciwon ciki shine yanzu na haihu"mi ina za ta yi in ban dariya ba saboda ta gane jinin al'ada ne Maryam ta fara......



Jikar Rabo ce 😎
[06/02 à 14:49] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```

Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR* 🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻



*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*

```MRS SADAUKI 💫✍🏻```

_______________________


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment