Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yinku irin sosai ɗin nan, musamman yadda kuke comment.😘😘😘

*I hearttttt you my besty KHADIJAH S MUHAMMAD*💞

*25*

Sallama ya yi tare da shiga cikin falon, shirun da ya ji shi ya bashi damar sanin babu kowa a falon, don haka sai kawai ya kama hanyar bedroom ɗinsa, kasancewar tun a hanya ya ga an shiga sallah sai shima ya wu ce toilet ya dauro alwala, ba zai iya zuwa masallaci ba, don haka cikin bed din ya tada sallarsa, yana zaune har aka kirayi ishsha aka shiga, bayan ya idar da sallar sai ya koma falo yana mamakin rashin jin motsin Aneesa a gidan.

Bai zame ko ina ba sai bed ɗinta, yana tura kofar ta buɗe can kuryar gado ya ganta ta kudundune cikin bargo, duba ɗaya zaka mata ka tabbatar babu lafiya.

Ganin Dr ai da sauri ta ya ki ce bargon ta nufe shi da dan sassarfa, jikinsa ta faɗa ragafff, saurin tallafeta ya yi yana faɗin

"Subhanallah! My Anee mai ya sameki?"

Ɗago jajayen idanunta ta yi wanda kallo ɗaya zaka mata kasan ta ci kuka

"Hamma daga ina kake?" Ta yi tambayar dai dai da zubowar hawayen da ta ma'kale.

"Ina gidansu Nenne tun safe bana jin dadi." Ya bata amsa yana gyara mata zama a jikinsa.

"Sorry Hamma ai ban san kana gidansu Nenne ba da nazo, hankalina ya tashi da rashin ganinka na kira wayarka duk baka ɗauka ba!"

"Ban kula ba da yake wayoyin duk suna silent ne."

"Please Hamma karka kuma tafiya ka daɗe, ko baka da lafiya ka dawo gida zan fi son haka."

"An gama Madam." Dr ya yi maganar tare da ɗan sakin murmushi.

"Mu je falo ka ci abinci." Aneesa ta yi maganar tana tashi.

Tashi ya yi tana rike da hannunsa suka nufi dining inda ta shirya masa abinci

******
"Kai Alhamdulillah! Wallahi Alhaji na yi matukar farin ciki da jin wannan maganar, Allah ya amsa addu'a ta, ya haɗa Auta da miji na kwarai mai cikar mutunci da hankali." Cikin tsantsan farin ciki Ummi ke wannan maganar.

Shima ɗin Abba zama ya gyara ya ce "ai wato Hajiya wani hani daga Allah baiwa ce, kin ga yanzu babu wanda ya yi zaton haka, amma gashi Allah mai rahama da jin kai ya yi mana canji na Alhairi, addu'ar zaman lafiya kawai zamu ke yi masu."

"Haka ne Alhaji Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyaba."

"Amin." Abba ya amsa.

Suna cikin hiran ne Meesha da Meena suka shigo, Meena zama ta yi a kasa tana gaida su Ummi ya yin da Meesha ta je kan kujerar ta yi kwanciyar ta, ko kallon su Ummi bata yi ba.

"Meena kin kuwa san dawa aka daura auren Auta?" Ummi ta tambaya.

"A'a Ummi" Meena ta bata amsa.

"Ai kin san Dr da yake dubata ko?"

Cikin sauri Meena ta amsa da "Eh!"

"To da shi aka daura auren, bayan rashin mutunci da Alhaji Mansur ya yi mana." Ummi ta k'arasa maganar cikin takaici.

Wani farin ciki ne ya ziyarci Meena jin da Dr aka daura auren Ameesha, wannan abu yana daga cikin burin Meesha sai gashi dama ya samu, sai dai kash Meesha bata san wainar da ake to yawa ba."

"Amma fa Ummi na yi farin ciki sosai Ubangiji ya sa hakane mafi Alhairi."

"Ameen." Ummi ta amsa.

Tashi Meena ta yi tana faɗin

"Ummi bari na tafi sai da safe."

"Allah ya tashemu lafiya."

Bayan tafiyar Meena, Ummi ta umarci Meesha ta shiga bedroom ɗinta. Kin tashi ta yi sai ma kallon Ummi da ta ke yi

"Uwata ta shi ki shiga ciki ki yi sallah sai ki kwanta." Abba ne ya yi maganar yana da ga inda ya ke zaune.

Tashi ta yi tana turo ƙaramin bakinta, mamaki ya kama Ummi ta ce

"Ikon Allah ko dai yarinyar nan da abun da ta ke bukata ne?"

"Babu komai rabu da ita, yanzu zata wuce."

"To Allah ya kyauta." Ummi ta yi maganar bayan wucewar Ameesha.

****

Da mamaki sosai Nenne ta ke kallo Bobbo jin maganar da yake faɗa mata. Wani jin dadi wanda rabonta da shi tun ranar haihuwar Asmad sai yau da ta ji wannan labari ta kuma jin irinsa.

"Alhaji dama ka taɓa zuwa nema masa aure ne?" Nenne ta yi tambayar cikin mamaki.

Girgiza kai ya yi ya ce "a'a ko ɗaya kawai zuwa wajen ɗaurin auren na yi, dama kafin na tafi sai da muka tattauna da Hafiz, yake sanar min halin da ake ciki, na tausaya ma Asmad sosai haka na tafi wajen ɗaurin auren bani da cikakken nutsuwa, bayan mun je sai baƙon lamari ya bullo, ganin uban yarinyar yana gaf da shiga wani hali sai kawai na yake shawarar a daura da Asmad ɗin, cikin karamin lokaci aka daura." Bobbo ya dire maganar murmushi kwance a fuskarsa.

"Masha Allah! Allah ya tabbatar da Alhairi, na yi farin ciki sosai."

"Ameen." Bobbo ya amsa.

"Amma fa har yanzu Asmad ɗin bai sani ba."

"Hhh! Ka ce *Auren bazatta* ka yi masa?"

"Sosai kuwa."

"To ai shi kenan, muna godiya da hakan, sai yaushe kuma zata tare?"

"Sai bayan sun dawo daga Egypt tukun, don ana son a kaita don duba lafiyarta."

"To Allah ya taimaka, amma ni dai gobe zan je ganinta."

"Allah ya kaimu."

*****

DR ne zaune a bakin gadonsa hannunsa a kan haɓarsa, tunda garin Allah ya wu ye sallah kawai ya yi ya zauna ya soma tunanin Meesha, duk lokacin da ya tuna ya rasata bugun zuciyarsa ke ƙaruwar, ƙaramin tsaki ya ja tare da cusa hannunsa cikin sumarsa.

Ƙaran wayarsa ta dawo da shi cikin nutsuwarsa, kallon wayar ya yi tare da sa hannu ya dauka

"Assalamu Alaikum Nenne ina kwana?"

"Wa'alaikumus salam Asmad lafiya lau ya ƙarfin jikin?"

"Alhamdulillah! Na samu sauki sosai, har masallaci na je."

"Madallah! Allah ya kara sauki, ina son anjima kazo kai da Aneesa."

"Ameen! Insha Allahu zamu zo."

Daga haka su ka yi sallama, Dr kwanciya ya yi tare da lumshe ido cikin wani yanayi mai wuyar fassara, a haka bacci ya dauke shi bai farka ba sai ƙarfe tara. Yana tashi toilet ya nufa wanka ya yi yana fitowa ya shirya cikin wani riga da wando kayan sun amshi jikinsa, ya yi kyau sosai falo ya fita inda ya ke tunanin Aneesa na ciki, ilai kuwa tana zaune a falon cikin kwalliyar ta mai kyau, tana ganin Dr ta saki murmushi ta ce

"Hamma ka yi kyau."

Murmushi ya mayar mata shi ma sannan ya amsa da "na gode."

"Mu je ka yi break kar ka makara." Aneesa ta yi maganar tana fara tafiya. Bin ta a baya ya yi har kan dining din ya zauna ta zuba masa abin da ta haɗa, sannan ita dinma ta zauna

"Ki yi break fa yanzu fita za mu yi mu je gidan su Nenne ." Yana maganar ne yana ci gaba da cin abincinsa.

"To." Aneesa ta amsa kirjinta yana bugawa, haka kawai ta ji hankalinta ya tashi. Sam jikinta babu kwari ta kammala break ɗin, gyale ta dauko suka kama hanya.

Suna shiga mota aka soma kiran Dr ana sanar masa akwai mara lafiya emergency, don haka cikin sauri ya k'arasa da su gidan, lokacin da suka isa gidan Bobbo ya fita, a gaggauce Dr ya gaida Nenne ya fita.

Bayan fitar Dr ne Nenne ta gyara zama tare da kallon Aneesa,

"Aneesa! Nenne ta kira sunanta.

"Na'am Nenne." Cikin nutsuwa ta amsa.

"Kina jina ko? Duk abin da zan sanar maki ki yi haquri domin ya zama dole ki sa ni, ki yi haquri ki dau dangana."

Gyada kai ta yi har yanzu kanta a kasa yake.

"Aneesa jiya aka daura auren Asmad, amma aurensa ba yana nufin cin mutuncin ki bane, babu wani cin zarafi tsakanin ki da Hamma ɗinki, in har wani abu ya biyo baya ki sanar min." Nenne ta fada cikin karfafawa Aneesa gwiwa.

Girgiza kai Aneesa ta ke yi cikin mummunan faduwar gaba, hankalinta ya yi mugun tashi da jin maganar Nenne, addu'a take Allah yasa ba gaske ne abin da ta ji Nenne ta faɗa ba, a fili ta bayyana

"No! Ba haka bane." Ta yi furucin cikin tashin hankali.

"Karki tada hankali ki hakuri Aneesa."

Da sauri Aneesa ta tattaro nutsuwarta, ta tuna a gaban Nenne take, murmushi ta yi wanda da gani kasan gara kuka da shi

"To Nenne Allah ya sa Alhairi." Allah kaɗai yasan ta yadda Aneesa ta haɗa wadannan kalmomin.

"Allah ya maki albarka ya zaunar da ku lafiya."

"Ameen." Kawai Aneesa ta amsa, sai ta mik'e kamar wacce aka tsikara.

"Ina kuma zaki je?"

"Umm Nenne dama zan yi baki ne, shi ne zan koma in dafa masu abinci."

"To ai shi kenan, amma da naso ki wuni mana tunda baƙi ne sai kin kuma zuwa."

Sam Aneesa bata wani tsaya sauraron abin da Nenne ke faɗa ba, kawai ta sa kanta ta yi waje.


_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*wannan shafin sadaukarwa ne gareki AYSHA WARIZI ki yi yadda za ki yi da shi in yaso ma ki hana kowa ya karanta, indai gaisuwa ta ta sameki Alhamdulillah ina maki fatan Alhairi da nasara a rayuwar ki*_

*Hak'uri nake baku akan rashin ganin post ɗina kullum, hakan nada nasaba da halin da na tsinci kaina, ku taya ni da addu'a Please.*

*Masu kirana da masu yi min text message ina godiya da kulawa, Allah ya bar zumunci*

```Nafee Ankerh korafi```☹

*One in town my Besty, ke kam kin zama jinin jikina k'aunar da nake maki daga Allah ne, Allah ya barmu tare har karshen rayuwa*😍😍

*26*

Sallama ya yi tare da karasawa tsakiyar falon, abin da ya bashi mamaki shi ne yadda bai ji an amsa masa ba, duk da akwai mutum a falon bai damu ba don haka sai ya taka zuwa kan kujera tare da furta "wash! Madam na gaji fa."

Ko daga kai bata yi ba balle yasa ran zata masa magana, Zama ya yi kusan na minti uku yana kallonta tare nazari halin da ta ke ciki, a iya tunaninsa bai mata wani abu wanda har ya bata ranta ba, hasalima cikin farin ciki suka fita har ya barta gidan Nenne.

Tashi ya yi daga inda yake ya matsa kusa da ita yana faɗin

"My Anee me na yi ne? Ya yi tambayar yana kai hannunsa jikinta. Da sauri ta janye jikinta tare da watsa masa wani mugun kallo na tsana zallah

Ta ce "Kar ka taɓa min jiki Hamma.

Da kyar ta hado kalmar domin yadda zuciyarta ke wani irin tafasa, ji take kamar ta shakeshi ta huta.

Da mamaki ya ke kallonta ya ce

"Aneesa me ya faru? Me na yi maki da har zan kai hannuna jikinki ki goce?"

Buɗe ido ta yi tana kallonsa da mamaki mai cike da takaici "wato baka san me ka yi min ba, lallai ma Asmad ɗin nan ka mugun raina min hankali." A zuciyarta ta ke wannan maganar amma a fili sai cewa ta yi.

"Ba kai min komai." A takaice ta yi maganar.

"A'a Aneesa ban yi maki komai ba ki ke fushi da ni, dole akwai dalili Please me ya faru?"

Wannan tambayar tasa na rainin hankali ta bata ranta fiye da jin labarin aurensa, kwafa kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, sai ma mik'ewa da ta yi da niyyar shiga bedroom ɗinta.

Da sauri ya janyo ta ta faɗa jikinsa, hannu yasa ya rungume ta tsam kamar wani zai rabasu.

Kokarin fisge jikinta take tana faɗin "Please Hamma ka barni wallahi na tsaneka ni zaka ciwa amana, me kuma zaka faɗa min?"

Bai damu da maganganun da take faɗa masa ba, shi dai burinsa ya ji laifin da ya aikata mata har ta dauki zafi haka. "Aneesa ki nutsuwa ki faɗa min abin da na yi maki don ban san laifina ba."

Kuka ta rushe masa da shi ta ce

"Hamma ashe kaima kana cikin masu karya da cin amana, Hamma menene bana yi maka da zaka saka min da kishiya?" Da karfi ta k'arasa maganar.

Shi fa maganar ta ma dariya ta sashi amma sai ya dake ganin yadda ta ke kwararar da hawaye "anya kina cikin hankalinki kuwa? An yi maki kishiya? Kuma wa ya faɗa maki?

Dariya ta yi duk da akwai hawaye a idonta, domin dai maganar Hamman ɗinta ya bata mamaki "wato wa ya faɗa maki an yi maki kishiya?" A fili, ta maimaita kalmar ta ce

"Nenne ce ta sanar min kuma kasan dai ba zata min karya ba, ashe dama jiya kana can tare da Amarya ne shi ne da ka dawo ka shirga min karyar baka da lafiya hmmmm! Hamma kenan, yanzu ma kazo ka tsara ni ne bayan ka je wajen matarka, wallahi Hamma na tsaneka." Ta k'arasa maganar tare da rugawa da gudu ta shiga bedroom ɗinta.

Sororo Dr ya yi maganar Aneesa suna masa yawo a kunne "Aure kuma Nenne ta fada mata?" Ya yiwa kansa tambayar da babu amsa. Jagaf ya zauna akan kujera tare da dafe kansa, shi yama rasa tunanin da zai yi, wayarsa ce ta fara ruri don neman a gaji, jiki a saɓule ya kai hannu tare da dauko wayar ganin Number din Hafiz yasa shi ɗauka.

"Ango! Hafiz ya faɗa daga ɓangarensa.

Buɗe ido ya yi tare da gyara wayar a kunnensa ya ce

"Kai fa sai a hankali, wani irin Ango kuma?"

"Ango ka ke mana ko ka manta?" Hafiz ya k'arasa maganar cikin dariya.

Mtss ya ja tsaki ya ce
"Kai wallahi ka faye zolaya da yawa fa, angon Aneesa ba."

"A'a na Ameesha dai." Hafiz ya faɗa.

"Da a ce haka zata faru da nafi kowa murna, amma kash sai dai Ameesha ta min nisa tana karkashin wani." Cikin zuciyarsa ya ke maganar.

Amma a fili sai ya ce
"Please bar maganar nan karka sa na shiga wani ha..." Tun bai gama maganar ba Hafiz ya yi saurin katseshi da fadin

"Kai abokina kana nufin har yanzu baka san an daura auren ka da Ameesha ba?"

Wani irin mik'ewa ya yi daga zaunen da yake ya ce

"Me ka ce?"

"Yes an daura auren ka da Ameesha." Hafiz ya yi maganar kai tsaye.

"Please bana son haka, idan wasa kake min ka daina Ameesha dai ina sonta so na gaskiya, amma na hak'ura da ita." A zafafe Asmad ya k'arasa maganar.

"Haba Dr ya ina faɗa maka maganar gaskiya kana karyata ni, ka je ka tambayi Bobbo ko Nenne zasu sanar ma shekaran jiya da kai aka daura auren Ameesha." Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa.

Da kallo Dr ya bi wayarsa, cikin zuciyarsa yana mamaki da tunanin maganar Aneesa da ta Hafiz, Aneesa ta ce Nenne ta sanar mata, shi kuma Hafiz ya ce ya tambayi Nenne, abin da ya daure masa kai shi ne "ɗazun da zai dawo gida sai da ya biya ta gidan don ya ɗauko Aneesa a tunanin sa tana can gidan, kuma bai ji Nenne ta sanar masa da makamanciyar wannan maganar ba, kai shi kam bai yadda da wannan maganar ba."

"Yanzu me abin yi?" Ya yi wa kansa tambaya.

"Ka fara zuwa ka lallashi Aneesa tukun." Wata zuciyar ta bashi amsa.

"A'a kar ka je domin kuwa a yadda ta ɗauki fushin nan ko ka je bata sauraron ka." Wata zuciyar ta yi saurin tunasar da shi.

"To mai zan yi, menene mafita?" A fili ya yi maganar.

"Wajen Nenne da Bobbo." Wani bangare na zuciyarsa ta bashi amsa.

"Yes! Sosai ya ji ya yi na'am da shawarar da zuciyarsa ta bashi. Cikin kwarin gwiwa ya mik'e yana fita motarsa ya ɗauka tare da bata wuta sai gidansu Nenne.

Ko tsayawa kyakkyawan fakin bai yi ba, ya fita daga motar, cikin gida ya nufa da sassarfa a wannan gaɓar sallama ma ta gagareshi da Nenne ya yi karo ta fito daga hanyar kicin.

Kallonsa ta yi tare da girgiza kai ta ce

"Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau Nenne." Ya bata amsa.

"An ya kuwa lafiya, kalli fa ta yadda ka shigo?"

Sosa kai ya fara da keys din hannunsa ya ce

"Allah Nenne babu komai, dama dai tambayar ki zan yi?"

"Tambaya?" Wacce irin tambaya kuma? Ko da yake zauna in ji me ke tafe da kai?"

Zama ya yi tare da lankwashe ƙafafunsa ya sun kuyar da kai, sai dai me tambayar da ya ke niyyar yi ta ki fitowa. Ita dai Nenne zuba masa ido ta yi tana sauraron abin da zai ce, ganin ya yi shiru sai ta gyara zama ta ce

"Asmad wai kuwa ka je gidansu Ameesha kuwa?"

Ɗago da kai ya yi yana kallonta ya ce

"Gidansu Ameesha? Me zan je yi mata bayan yanzu tana inuwar wani, ko kin manta na ce an daura auren ta da wani?"

"A'a ban manta ba, sai dai yana da kyau ka lek'a domin duba a wani hali ta ke, saboda wannan ɗin ya rataya a wuyar ka ne."

Da amaki ƙarara a fuskarsa yake kallon Nenne bakinsa har yana rawa ya ce

"Ya rataya a wuyana? Nenne ban gane nufin ki ba?"

"Eh! Haka nake nufi, yau kwana biyu da Ameesha ta zama a karkashin inuwar ka, ma'ana dai Maryerm Taheer wato Ameesha ta zama mata a gare ka."

Kallon Mahaifiyarsa ya yi a karo na barkatai, ganin yadda ta dire maganar sam babu alamar wasa ya sa shi ya yadda, ai da sauri ya tashi tare da yin sujada ga Allah don nuna farin ciki, yana ɗagowa ya zubawa Nenne ido kallo ɗaya zaka masa kasance wa yana cikin zallar farin ciki, musamman yadda fuskarsa ta nuna.

Kasa furta komai ya yi sai wani fara'a da murmushin da ke k'arasawa fuskarsa kyau ya yi, cikin zuciyarsa kam godiya ya ke ga Allah. Muryar Nenne ya ji tana faɗin

"Kaga yanzu dai ka tashi ka je gidan nasu domin duba wani hali take ciki."

"To." Tare da mik'ewa yana faɗin Nenne sai na dawo.



_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:00 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)*


*SANGARTA*


©
*ZULAIHEART RANO*


*_Bismillahir Rahmanir Rahim._*



*_Allah ina rokon ka don karfin ikon ka, kabani iko kamar Yadda na fara rubuta littafin nan lafiya Allah kasa in kammala rubutawashi lafiya_*



*1*



Zaune yake cikin kasaitaccen falonsa wanda aka tsara su da manya-manyan kujeru ne na alfarma. Kallo daya zaka yiwa falon ka san ba karamin dukiya aka narka ba. shi kansa kafet din falon ba duka gidaje ake samun irinsa ba sai gidan wane da wane.

Hannunsa ya mika tare da dauko jaridar Leadership daga kan wani kyakykyawan teburin dake kusa dashi, ya bude tare da soma karantawa. Cikin wata irin tafiya take taka steps din tana saukowa fuskarta dauke da murmushi, jikinta sanye da wata rigar bacci wandda bata gama rufe mata cinyoyi ba, kanta ko dankwali babu. Kai tsaye wajensa ta nufa. Shi ma tunda ya hangota fara'ar fuskarsa ta karu. Bata zame ko'ina ba sai inda yake zaune, ta zauna tare da dora kanta saman kafadarsa, cikin shagwab'a tace
"Abbana barka da safiya"
Murmushi ya yi yace "Barka dai uwata, fatan kin tashi lafiya?"
Dariya ta yi tace " Lafiya lau Abbana."
"Madallah, fatan babu wata matsala?" Ya yi tambayar yana kallonta.

"Innalillahi.... Ni Halimatu! ke kuma Amesha kina daukan maganata kuwa? sau nawa ina maki maganar ki daina fitowa a haka?" Maganarta da suka ji kamar daga sama ne ya hana ta ba Abban nata amsar tambayarsa, duk suka juyo ga mai maganar.

Turo baki tayi tare da kunkunai "To ni Ummi wai shikenan mutum ba zai sake ba shi da gidannsu?"
Dakuwa Ummin ta watsa mata tare da daure fuska tace "za ki tashi kije ki suturta jikin ki kosai na bata maki rai?"

Ganin fuskar Ummin ba wasa yasa ta mikewa cikin takaici. Abbanta yace "Haba Hajiya! me yasa kullum sai kin rika takurawa Yarinyar nan ne? Ko baki san har yanzu karamar Yarinya take ba?"

Wani takaici ya rufe Ummi ta ji kamar ta gaurawa mijin nata mari "Haba Alhaji, ta yaya zaka ce kar na yiwa Ameesha fada in ta yi ba dai dai ba? Yarinyar nan fa kullum kara girma take yi amma babu hankali a tare da ita. Ji fa irin kayan da take fitowa falo dasu, by mistake ayi bako ta fito haka ai kunya zamu ji....."

Ya dakatar da ita da hannu "Look! Hajiya ban son dogon turanci, gida dai nawa ne kuma Ameesha gidan ubanta take, don haka babu mai takura mata. Ke kullum baki da abokiyar fada sai yar cikinnki? wallahi wani in ya shigo sai ya yi tunanin bake kika haife taba, musamman da kullum fada kike mata. Kuma kina maganar bako, ai ba mai shigowa falon nan sai da izini. Gidan nan duk muharramanta ne, basai ta rika sa kaya masu nauyi ba."

Takaici ya rufe Hajiya, Wanda har ta kasa furta komai, sai aje masa cup din coffee din tayi ta nufi bedroom dinta. Tabbas ta san duk wani abu da Ameesha takeyi da izinin mahaifinta, don shine baya kaunar a fadi laifin Yarinyar. Allah ya sani ina iya bakin kokari na wajen bama Yarinyar tarbiyya, amma taki daukan duk wani nasiha ta, ta fada a ranta.

Ameesha tana shiga bedroom dinta toilet ta zarce ta sallo wanka. Tana fitowa ta zauna gaban dressing mirror ta soma tsantsara kwalliya. Tana gamawa ta shirya cikin wata bakar doguwar riga, mai masifar kyau, tayi rolling dankwali a kanta. Iya kyau dai kam Ameesha tayi, kamar a sace a gudu. Kyakykyawa ce sosai yar shekara goma sha takwas. fara ce amma ba sosai ba. Ta samo asali da kyau ne wajen mahaifiyarta, komai nata irin na mahaifiyar ne. *MARYAM TAHIR* kenan inkiya kuma Amesha Yarinya yar gatan Abbanta.

Wayoyinta ta kwasa daga kan gado ta sanya takalminta mai kyau, sannan ta fita falon don yunwa take ji sosai. wani murmushi ta saki ganin har a lokacin Abbanta na zaune a falon
"Wow! Babyna kinyi kyau."
Abban ya fada yana nuna farin ciki.
Dan turo baki tayi ta ce "Na gode Abban Ameesha. Abba so fa nakeyi naje saloon a wanke min kai" Cike da shagwab'a ta karasa maganar.
"Ok babu damuwa my baby. Yanzu dai je ki fara yin break don nasan kina jin yunwa. In kin gama sai ki tafi."

"Abba nifa ba kudi a hannuna, ka ban kudin da zanyi amfani da shi"

"Sai dai kije da ATM Card don banda wasu kudi masu yawa a gida" Ya bata amsa a lokacin da yake kokarin mayar da hankalinsa ga jaridar da ke hannunsa.
"No Abba, Gaskiya ba zan iya bin layin ATM ba, mutum yaje ya yi ta tsayuwa" Ta yi maganar kamar zata yi kuka a daidai lokacin da Hajiya Halima mahaifiyar Ameesha ta iso inda suke.

"Yawwa Hajiya muna da bukatar kudi in kina da su a hannu" Alhaji Tahir ya fada, yana rufe jaridar.

"Wani irin kudi kuma Alhaji?" Hajiya ta tambaya cikin nuna rashin fahimta "Baby ce zata saloon kuma wajena babu kudi a gida, ki bata 30 thousand naira kila su ishe ta"

Zaro ido Ummi tayi tace "Alhaji dubu talatin fa kace! Da su zata wajen saloon din?"

"Eh, saboda zata biya ta yiwo shopping. ko kuma dai bata fifty zaifi"

Jinjina kai tayi tare da cewa'
"Ai bani da su"

"Zan maida maki kudinki Hajiya"

Juyawa tayi ta nufi bedroom dinta, tana Kara mamakin halin mijin nata.

Ameesha kam sai da ta kammala break din tsaf, kana ta baro dining tabke din. Wajen Abban ta taje tace "Abbana na gama"

"Ok je ki amshi kudin wajen Umminki, 50k ne ai zasu ishe ki ko? Sai ki siyo yan abubuwan bukata da abinda ya rage."

Daga kai tayi kafin ta nufi bedroom din Ummin. Ta

Please Login or Register in order to submit comment