Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*NIDA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*


*Page 1*

*1am*


LUBA

"Alhaji Alhaji"

"Ummm wai mai haka ne Luba bazaki barni nayi bacci na huta ba fisabillahi"?


"Taya zakayi bacci ka huta bayan ka ajiye mu? ai tunda ka ajiye mu kace mu biyu bamu isheka ba ai baka ga hutu ba Alhaji.

jiya da kake d'akin Hindatu ai ba bacci kayi ba kwana kayi Kuna abu sai da ka zagayo dakina zaka zo ka ringa baccin gajiya Alhaji tashi ka bani hakkina"

"Luba dan Allah ki bari sai da safe kafin na tafi aiki wlh kaina ma ciwo yake ni kwana biyun nan ma bana iya komai wlh sabida gajiya"

"Eee kwarai baka iya komai fa shiyasa jiya naga ka dade baka fito daga d'akin hindatu ba,dama kasan bakada kwarin rike mata uku ka Kara aure ai tunda har kaga zaka iya nima bazan iya daga kafa a tauyeni ba bana Jin bacci ka bani hakkina"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Alhaji salis yace tare da mik'ewa zaune Yana kallon luba da ke zaune dirshan a tsakiyar gadon ta ma yaye bargon daya rufa sai wani girgiza take yasan ba wani bukata da take tsabar rigama ce ba inda yake samun bacci mai dadi da nutsuwa sama da dakin Aisha amma indai kwanan hindatu da Luba ya zagayo haka zasu sako shi a gaba kamar su kashe shi ya rasa wanan masifa da me tayi Kama

"Luba nace miki kaina ciwo yake ki bari da safe kafin na tafi aiki nifa ba injin bane ba"

"Alhaji jiya bakace wa hindatu kanka ciwo yake ba sai da kwanana ya zagayo dan ka raina min hankali ka bani hakkina sai ka sha baccinka"


Ya riga yasan halin Luba indai baiyi din ba bazata tab'a barinsa yayi bacci ba.


"Tunda na gaya miki bazan iya komai ba Kika dage sai kiyi luba"


Kansa ta fada ba dan ransa naso ba ko Yana da wani bukata ba yayi.


Yana jin tana masifar ita daya ya mata kad'an ai ba daya yakeyi a d'akin Hindatu ba yaja tsaki tare da juya mata baya daya ga ma zata dame shi ya sauka daga kan gadon yayi kwanciyarsa a kasa nan da nan bacci yayi awon gaba dashi.


Hayaniyar da ya ringa jiyowa daga Palo yasa ya bude ido yaga gari yayi haske ya mik'e da sauri Yana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun gari fa ya waye wanan wane irin masifa ne"

Kullum sai hindatu da Luba sunyi fadan daya zame musu farilla ya rasa wanan masifa Kamar suna ganin hanjin junansu ace karfe shidda na safe har sun fara fada.

Bai fita waje ba ya fada bandaki yayi wanka a gurguje yazo ya tada sallah,Yana sallah ma hankalinsa na wajen palon dan har lokacin Yana jiyo zage zagen da sukeyi yasan har makota ma ana Jin hayaniyar su.

Yana sallamewa yayi waje da sauri Yana bude k'ofa takalmin da hindatu ta jefowa Luba ya sauka a kansa.

Ya dafe kansa Yana sallati

"Na Riga da na kafu a gidanan wlh ba yanda zakiyi dani luba mutuwa ce zata rabamu mumunar banza mumunnar wofi ni bansan ma mai Alhaji ya gani a jikinki ya auroki ba Alhaji ma yace hakuri yake yi dake"

"Ke da sadakarki aka bashi ko lefe fa baayi miki ba ni kuwa ki tambayi kowa kiji ba karamin kudi ya kashe a auroni ba tsabar kwantan da kikayi sadaki ma yafe Masa akayi sabida tsabar kin rasa mai aurenki"



"Ya isa ya isa haka"



Alhaji Salisu yace a tsawace Yana mulmula goshinsa dake Masa zugi "Wanan wane irin balai da masifa ne da asusuban nan zaku fara masifa wai wanan wane irin rayuwa ne Hindatu Nagaji Luba na gaji Wai ku yarane?ace da manyan yayanku ku addabeni ku hanani sukuni,ba dama na dawo gidanan na tab'a samun kwanciyar hankali dan balai idan na doso gidana haka zan ta fargaba a wane dalili? Haka kuka ga Aisha nayi domin Allah bazakuyi koyi da ita ba to wlh Nagaji idan kuka kaini bango ko duniya kuka haifa min wlh sakinku zanyi kowace ta Kama gabanta"

Ya koma daki a fusace har Yana tuntube

Luba taja tsaki tana "Ai baka ga komai ba tunda ka auro wanan mai zubin samudawan Ina zaka taba samun kwanciyar hankali"

"Hindatu kuwa dakinta ta shige tana masifa kasa kasa.

Wajen karfe bakwai da rabi yaran duk Suka fito cikin Shirin tafiya makaranta dan bangarensu daban da na iyayen matan an ware musu dakinsu daban mazan ma dakinsu daban Afrah itace babba a Mata tana matakin karshe a secondary ita take kula da sauran kanen nata, inka d'auke Ashraf da Abubakar da suke karatu a A b u zaria.

Basu tsaya neman abinci ba dan sun san sai dai a biyo su dashi indai Luba ce da girki d'akin Aisha suka nufa da suke cewa Hajiya Umma Kamar yanda Suka Saba sai da suka gaisheta suka fito Suka nufi kitchen Inda suke Jin motsin luba iya yayanta ta amsawa gaisawar ko kallon Afrah da yayan hindatu batayi ba a daidai lokacin da hindatu ta fito daga dakinta tana "Kuzo ku wuce ku tafi karku yi latti dan jarraba bazaa fito da wuri a dorawa yara abinci su ci su tafi dashi ba har sai sun makara"


Ta ja hannun kananan Suka yi hanyar waje duk sai da ta bisu da manyan biscuit ba Wanda ta ware dan ita bata kishi da yara kamar yanda Luba keyi sai da driver ya jasu suka tafi ta koma ciki.

A Palo tayi zamanta tana Jin luba na kanana haibaice habaice itama tana daga palon ta daga muryarta yanda Luba zata jita tace "tsabar kwadayi da san zuciya wata ta Kashe aurenta ta baro yayanta tazo ta auri mijin kawarta tur wlh da wanan cin amana ace "

Fitowar Alhaji Salis daga d'akin luba yasa Hindatu yin shiru a daidai lokacin da Luba ta fito fuska a had'e tana "Alhaji wlh kayiwa hindatu gargadi ta fita daga harkata"


Ko kallonsu baiyi ba ya nufi d'akin Aisha bashida burin daya wuce ma ya bar gidan daga luba har hindatu kaddara yasa ya auresu da tunda ya auresu yayi bankwana da wani abu Wai shi farinciki .

A hankali ya tura k'ofar dakin Aisha da sallama har a yau da aka tafi shekaru nauyinta da kunyarta yake ji.

Yana ji ta amsa sallamar ciki ciki har ya isa gefen gadon ta ya zauna ita Kuma ta cigaba da gugan da take.


Yasan ko zasu shekara a haka bazata tab'a ce Masa komai ba Yana bakin cikin yanda ya zama bakon karfi da yaji a wajenta tamkar ba Aisharsa Mai kaunarsa ba.

"Anjima zan tafi Abuja sai nayi sati uku kafin na dawo"


"Allah ya kiyaye hanya"

Shiru ne ya ratsa d'akin Alhaji Salisu yace "Aisha dan Allah dawo nan zamu yi magana"

Sai a lokacin ta dago ta kalleshi suka hada Ido ta d'auke kanta tana "Ina jinka daga nan"

"Aisha Abu baya wucewa ne a wajenki dan Allah kiyi hakuri nasan na miki ba daidai ba shekara goma tsakani da Allah kin kasa cire abinda ya faru a ranki"

Murmushin takaici tayi tana "Alhaji wai nikam kaji na fito na ce maka da wani Abu a zuciyata Kai kadai kake kidanka kake rawarka ni ba komai a raina"

"Wlh da wanan abin da kike min gwara ki fito kimin fada ki zageni kimin koma mene da ki kawo ido ki zuba min kin maidani tamkar hoto ki Kara nesanta kanki daga wajena wlh bana Jin dadin irin rayuwar da muke tunda yanzu har da zuria a tsakani an tasa Kuma ai sai ki cire komai a ranki"

"Ba komai a raina Kai kake damun kanka a yanzu banida wani damuwa nikam"

"Hmmm Aisha kenan to ni zan tafi na damka amanar gidana a hannunki dan Allah kisa min ido Kar suyi min hauka da suka saba,wlh sabida ke nake dawowa gidanan amma matan nan caza min Kai suke"

"Allah ya kiyaye"

Mik'ewa yayi ya ajiye mata kudi a gabanta Yana sai ya kirata a waya Yana fita taja tsaki batasan mai yasa ko kadan bata ganin farinsa ba duk kuwa abinda zai Mata.

Yana fita ya ci Karo da luba a bakin k'ofa ta cika tayi fam "Ranar girkin nawa ma Alhaji sai anci amanata tsakani da Allah ran girkinta kana zuwa dakina ka dade haka"?

"Dan Allah bani hanya na wuce"

Ya bangajeta tabi bayansa tana masifar Shiga d'akin Aisha da yayi ya dade ita dai idan amanarta akaci bata yafe ba hindatu kuwa na zaune a tsakiyar palon sai dariya take kasa kasa dan sosai take ganin haukar Luba ko lissafi ma bata dashi ai ko kwana zaiyi a d'akin Aisha a ganinta ko A bai dace tace ba.

D'akin Luba ya shiga dan ya dauki akwatin kayansa Luba kuwa ganinsa da akwatin Kaya yasa tayi turus tana "Alhaji ya naganka da akwati gafa abincinka nan a palo"

"Zanyi tafiya ne zuwa Abuja akwai aikin da zanje nayi sai nayi sati uku kafin na dawo"


"Alhaji yanzu tsakani da Allah ka rasa ranar da zakayi tafiya sai ranar da kake dakina"

"Luba bani hanya na wuce banida lokacin kananan surutu "
ya fice daga d'akin.


Yana fita ya tsaya a tsakiyar falon fuska a had'e Yana "Luba bana San tashin hankali Hindatu na hadaku da girman Allah karku min hauka a gida ku ba Yara bane ba,ku daina zubar min da mutunci a unguwa wlh idan dai har a ka kirani aka fadamin kun min hayaniya a gida wlh zan dauki mumunan mataki akan ku kunji na rantse muku"


"Nifa idan bata Shiga harkata ba wlh ko kallo bata isheni ba Alhaji ni iskanci ne kawai bazan d'auka ba dan ba dan ita kadai aka yo ka ba,
bata da burin daya wuce taga ta mallake ka ita kadai wanan ne dai bata isa ba"


Hindatu tace tana hararar Luba

Luba kuwa tayi kwafa dan ji take Kamar ta shako hindatu ba wacce ta mata Karen tsaye a rayuwa sama da hindatun har a yau burinta taga ta raba ta da Alhaji.

Alhaji Salisu bai Kare ce musu komai ba yasa Kai ya fice Luba ta rakashi har wajen motarsa sai da ya fice daga gidan ta koma ciki.


*AISHA*

Mace ce da ta koyi hakuri ta karfi da yaji ta koyawa kanta k'au da kai,a duk abinda mijinta Salisu keyi,ta kulle zuciyarta dake neman kamuwa da hawan jinin da mijinta ke k'ok'arin dora mata ta fahimci wani zubin namiji bai cancanci ki kashe kanki a kansa ba wani zubin Kuma basu San kunya ba sau tari takan zauna tayi nadamar sakin jikin da tayi da kawarta da ta Mata mumunan tabon da har ta koma ga Allah batajin zai gogu a zuciyarta a yanzu zaman 'ya'yanta kawai take da Kuma Neman Aljannarta ba dan wai akwai burbushin kaunar mijinta a ranta ba tasan Kuma koman daren dadewa Allah zai mata sakayyar cin amanar da ya mata yanzu suna da shekara Ashirin da biyar da Aure yaranta biyar Ashraf,Afrah,Abubakar Aliyu da Ummi.


LUBA...*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*


*Page 2*


LUBA

Mutane da dama suna ganin na aikata abin kunya nayi abin fade naci amana Wanda ni banga aibun abinda nayi ba tunda a musulunce ba haramun na aikata ba so so ne amma san Kai yafi,Ina san Jin dadi a rayuwata Ina san duk abinda nake so a rayuwata ya zama na samu,kina mace Ina mace ba abinda zaki gaya min Ina so naga na Zama mowa a wajen mijina ya zama ba matar data isa ta hada kafada dani Zan iya kashe ko nawa ne,Zan iya zuwa
Ko'ina Ina dan na samu cikar burina.



Waiwaye




Aisha

Zuciyata cike take da farinciki dawowar da uban yayana zaiyi.

Ya shafe shekara biyar a waje dan ya Karo karatun da yana dawowa zai zama cikakken likita Allah yasan nayi kewarsa Kamar na mutu Ashraf da Afrah ma sai murna suke Abbansu zai dawo,nasan ashraf da wayonsa a lokacin da ya tafi yasani Afrah ce dai take da shekara biyu lokacin daya tafi.

Salisu bashida komai a lokacin da mu kayi Aure dan zan iya cewa auren gata aka masa nima da yake a wajen yayana nake Yana kuma da dan rufin asiri Ina gama secondary school ya nemi salis daya fito da a lokacin ba wani aiki yake ba sai wani karamin chemist da yake dashi,da taimakon iyayen sa dai ya turo kudin aure gidanmu aka sa mana Rana wata shidda masu zuwa.

A lokacin cikin tsananin farinciki salis ya bugo katin engagement na raba wa kawayena,a lokacin banida aminiya sama da Luba da a lokacin makaranta daya muka yi jinin mu ya hadu da ita sosai ba Wanda baisan kawancen mu ba, har ana mamakin yanda akayi tamu tazo daya da ita dan ni Sam bana San hayaniya ita kuwa akwai zuciya da fada gata masifafiya masifarta yasa lokacin samari ma basu fiye zuwa wajenta ba.

A ranar da na bata labarin salis ya kawo kudin aurena mamaki ta ringayi tana mai salis yake dashi da zan aureshi ita har yanzu bata ga kalar Wanda zata aura ba.

Dariya na sa mata ina nidai Ina sansa luba ni dama nafiso na auri Wanda bashida komai idan munyi aure mayi arzikin tare.

Anan ta hade rai Wai taso muyi aure rana daya bazata so na rigata aure ba cikin dariya nace ta bada himma nan da wata shidda ta samo mijin aure ta tab'e baki tana ita dai taga Kamar nayi gaggawa.

A kwana a tashi ba wuya sai gashi mun fara kirga sattikan Aurena,duk wani shiri da Luba muke yi dan itace gaba wajen fito da anko duk da ba wani shiri take da salis ba amma da ta ga dai shi zan aura ta fara sakar masa fuska a haka har aka sha shagalin bikina Luba tayi k'ok'ari sosai dan ba karamin gudunmawa tayi min ba haka ma a gidansu anyi min gudumawa na Kuma ji dadi matuka.

Duk da na rigata aure ban canza mata ba,
wai dan ganin yanzu ni inada aure hasali kawancen mu kara karfi yayi,dan ba abinda nake b'oye mata game da rayuwar Aurena itama ba abinda take b'oyemin ba ta ma fiye zuwa gidana ba amma idan dai tazo zata wuni a gidana ko da salis ya dawo ma haka zamu hadu mu uku muyi ta hira duk abokanan Salis da suke Santa duk tak'i su a fadarta tafisan ta samu mai rufin asiri sosai,a haka na samu cikin Ashraf har na haihu nan ma sai da ta hidimanta min na ringa addua Allah ya gwada min aurenta nima na rama abinda tamin.

Na tafi shekara biyu da Aure na, aka kawo kudin luba murna kamar nayita rawa har salis na tsokanata akan ko a bikinmu banyi murna haka ba,daga yanda naga luba na shiri tana kuma facaka da kudi nasan ta samu irin wanda take so ta aura wato mai kudi,tamkar dai lokacin bikina nima haka na dage muka ringa shirya bikinta,har asusu na ringayi dan inaso naga na mata fiye da abinda tamin.


A wajenta nake jin labarin Wanda zata Aura Hamza a wani company Yan China yake aiki Kuma babba ne acan.

idan har sunyi Aure zata Masa magana ko zai iya samawa Salis aiki a companynsu.

Har a zuciyata naji dadi dan zanso Salis ya ringa aikin da zai na shigo Masa da kudi,dan a chemist din ma ba wani kudi yake samu ba,amma Yana iya k'ok'arinsa wajen kula damu duk da yayana bai barni haka ba yana yawan yimin aike.


A cikin irin aiken da yake min na yiwa luba gudunmawa sosai har da zannuwan gadona wajen biyu masu dan tsada da ban taba amfani dasu ba.

Gidan Luba yayi kyau sosai Iyayenta Kuma sunyi k'ok'ari wajen yi mata jere Luba an samu abinda ake so sai falli take,har tana cemin ita dai taga nayi gaggawa da ace banyi gaggawa ba da sai na samu mijin dayafi salis,nidai inasan salis Kamar yanda yake kaunata duk da gidan haya muke ban damu ba dan indai da rai da rabo Yana Kuma iya k'ok'arinsa wajen kyautata min.

A haka muka Sha bikin luba, kawancen mu ya Kara k'arfi fiye da baya.

Watan ta hud'u da Aure watarana tazo gidana naganta a firgice daga yanda na ganta nasan ba kalau ba Salis ma ko fita baiyi ba.

Tana zama ta rushe da kuka hankalina ya tashi anan na hau tambayarta mai ya faru dak'yar ta tsagaita Kukan da take take labarta min wai ta gano Hamza karya yayi mata Ashe mai gadi ne da kudin ajiya duk yayi facaka ya aureta yanzu haka jiya Yan sanda suka zo suka tafi dashi akan Mai company ya dage sai ya biyashi duk kudinsa ta Kara da "wlh ban taba tunanin Hamza makaryaci bane Aisha mai gadi fa kinsan kuwa gidan ma ashe hayane ba nasa bane"


Nidai sallati kawai na ringa yi ita kuwa ta cigaba da rusa kuka dak'yar na bata baki tayi shiru ta ringa rantsuwar sai Hamza ya saketa ita bazata zauna da mai gadi ba,a haka Salis ya fito ya same mu ganin yanda mukayi cirko cirko yasa ya hau tambayar mu mai ke faruwa

Shiru nayi dan Ina tunanin kamar sirrinta ne bai dace na fada masa ba,ita kuwa ganin banida niyyar magana yasa ta hau bashi labarin duk abinda ya faru,Salis kuwa ya hau sallati yana Yanzu Hamza na kulle shine tazo ta zauna ai Kamata yayi asan yanda zaayi a fito dashi a takaice a ranar salis bai fita shago ba haka aka ringa cuku cukun yanda za'a fito da Hamza dan Salis har wajen mai gidan sa yaje dak'yar dak'yar ya yarda akan a saki Hamza zai nemi rabin kudin ya biya shi inyaso ya cigaba da biya a hankali.

Duk salis ke bamu labarin yanda sukayi dan luba na gidana tace ita bazata ma koma masa ba so take ya bata takardar ta ta tafi gidansu kamar ba mijinta ba ta ringa auna masa zagi.


Luba sai da ta samu sati guda a gidana wulakanci kuwa haka ta ringa yiwa Hamza Kamar ba mijinta ba,sai da Salis ya samu Iyayenta suka saka baki ta yarda zata koma gidansu hamzan kafin ya samu wajen zama.

Ni tausayinta ma na koma ji dan ta saka damuwa a ranta sosai gashi tana d'auke da ciki.

Ba'a kwana biyu bata zo gidana ba,idan tazo haka zatayi ta mita tana tsinewa Hamza akan ya cuceta a irin wanan halin Nima na samu cikin a lokacin Ashraf ya tafi shekara uku.

Nidai zan iya cewa banida matsala komai dan Asirina kam a rufe yake dan banida wani matsala a gidan aurena daidai gwargwado salis na kyauta ta min.


Cikina wata biyar Luba ta haihu Sanin halin da suke ciki yasa na zage sosai wajen hidimanta mata Salis ma baa barshi a baya ba duk da bashida kudi.

Nidai nasiha da shawara ke rabani da luba da ta balain raina Hamza ni nasan da baya Santa da tuni ya saketa dan Abubuwan da ya mata ma duk sai da ta raina burinta ma kawai ta kashe auren.


A haka nima Allah ya saukeni lafiya na haifi Afrah a haihuwan nan Salis ya min hidima ba kad'an ba,tunda na haihu Luba bata tab'a d'auke kafarta daga gidana ba tun safe idan tazo sai dare take tafiya,kayan fitar sunan da salis ya siyamin take ta juyawa a hannunta tana "Kinsan kuwa tsadar atamfar nan Ina Salis ya samu kudi haka"?


"Kice atamfar nada tsada wai Ashe tunda nasamu ciki ya Shiga adashe shine fa Ina haihuwa ya karbi Adashen ni Ina nasan ma zanin nada tsada"


"Aikuwa da tsada yayi k'ok'ari gaskiya ni Ina naga arzikin Rabin atamfar nan ma wlh Hamza ya cuceni gashi yak'i sakina"

Zama nayi a gefenta Ina "kiyi hakuri Luba mai nema Yana tare da samu ai da ace baya nema sai ki fida rai amma tunda har Yana nema watarana za'a dace insha Allahu Kuma zakiji dadi tunda Yana kaunarki"

"Hmmm kinsan ko Napkin baya iya siyawa Sultan wlh ba irin rayuwar nan na tsarawa kaina ba"

Kwalla ya zubo mata ta share a daidai lokacin da Salis ya daga labule suka gaisa daga bakin k'ofa ya mikomin ledar daya shigo dashi ya fita.

Da zan ajiye ledar sai Kuma na bud'e ledar naga Kayan jarirai ne sai sarka da dankunne da mayafi kala biyu ganin tana ta kallon ledar yasa na fito da kayan ciki na nuna mata ta ringa juya kayan tana yabawa a cikin turamen zanin da aka kawo daga gidanmu na dauko daya na bata dak'yar ta karba tana da na barshi ita wanan haihuwar da nayi bata da abin bani.

Koda tazo tafiya ma sai da Salis ya bata kyautar kudi,na rakata ta tafi.


Ahaka akayi sunan Afrah banaso na sosa mata zuciyarta taji ba dadi Kaya kala biyu kawai na saka.


A haka rayuwa ta ringa tafar mana daidai gwargwado Ina k'ok'arin taimakawa luba indai ta kawomin kukanta zan k'ok'arta naga na share mata hawayen ta Afrah ta tafi shekara biyu wataran Salis ya shigo gidan da takarda a hannunsa cikin tsananin murna Yana nuna min sunansa ya fito a cikin wayanda suka ci scholarship da zasu fita Kara karatun da zai zama cikakken likita.

Ji nayi Kamar na zuba ruwa a kasa na sha dan murna dan duk Wanda yasan Salis yasan burinsa kenan yan uwa da abokanan arziki kuwa sai taya mu murna ake ciki kuwa har da Luba da ke fama da tsohon ciki duk ta fice a hayyacinta sabida damuwa da ta sa a ranta.

Duk kudin da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment