Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciya cewa Allah ne fa ya bata Rayha kuma shiya amsa abinsa kuma komi akai mata Allah baya bacci tabbas subar su da Allah tun a nan duniya Allah yake fara hukuncin sa su basuda k'arfin shari'a dasu kam amma ai akwai Allah yanzu kawai abinda Rayha take so shine addu'a.


Sosai nasihar limamin ta shigeta sai dai har yanzu kuka take kamar k'aramar yarinyar,




Tofa tashin hankali sai da aka zo fita da gawar Rayha su duka uwa da y'a da kyar aka b'anb'are su suna kuka kamar ransu zai bar jikinsu Momy fad'i take inshallahu wadda sukai miki wannan cin kashin tun a duniya basai anje rahira ba Allah zai fara saka miki bamu yafe ba Ubangiji Allah ya isar mana, haka take ta maimatawa tana kusa da gawar gawar aka d'auka ganin cewa gadan-gadan za'a fita da ita Aamah da takasa jurewar cewa fa shikenan ita da k'ara ganin Rayhanta mutuwa mai yankan k'auna rigijif akaji fad'uwar Aamah a sume............✍️


















*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️














Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
























*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*












*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






PAGE1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣






__________________✍️ Washe garin ranar aka tashi da labarin mutuwar Sulaiman matar sa kuwa kwata-kwata bata cikin hayyacinta tofa mutane da yawa sun d'iga ayar tabbaya akan wa'inna Abokai har an fara k'ananun maganganu kala-kala wasuma cewa suke ai k'ungiyar asiri suka shiga shine suka bijire ake masu d'auke d'ai-d'ai,




Tofa maganar mutane tasa sun k'ara shiga rud'o da tashin hankali shida Mustapha da Aliyu wadda duk cikin Abokansu su TAKWAS su kad'ai suka rage sosai suka shiga tashin hankali inda suka tattauna cewa kar su k'ara yarda da kowa sana su rik'e d'an hannun nan da kyau dan kuwa ta ko wacce suffa zata iya zuwar musu dan Aliyu ya basa labarin zuwar mai da tayi lallai Mustapha ya k'ara shiga rud'o da dana sani sosai, Mustapha da kyar ya bud'e baki yace "koda na mutu Aliyu na tabbata zaka rik'e min yarona da kyau Amana Dan....... Da sauri Aliyu ya dakatar dashi da cewa baya son irin wannan maganar dan Allah ya daina.




Mustapha kuwa tashi yayi kawai yana girgiza kai ji yake tabbas shima ya kusa mutuwa jiki a sanyaye ya shiga gidansa ganin kayan Al'ameen na school zube a k'asa da alama ya dawo school kiransa ya fara yi "Al'ameen!! Al'ameen!!!" Yana sama ya amsa da "na'am Abbee gani nan sakkowa" jin shuru bai sakko ba zai sake magana yaji ihun Al'ameen cike da tashin hankali yake kiran sunansa kuka yaron kawai yake ya kasa magana da sauri Mustapha har yana tuntub'e ya hauwara saman shigarsa d'akin yaron wani abun birki yaja zuciyar sa tayi wata mahaukaciyar bugawa zubewa yayi k'asa ganin Al'ameen Amreeta ta zama sharb'eb'iyar macijiya ta nannad'e yaron ta saita kansa sari kawai ya rage ta kaimai da sauri baikin sa har yana kyarma yace "kiyiwa Allah ki rabo da yarona karki cutar dashi ba abinda ya sani" ya idasa maganar yana fashewa da kuka Amreeta kuwa wata dariya ta saki tace "ashe kunsan Allah kunsan dashi kuma kuka cuci bayinsa har wani kai kasan imani a nan sana kuma indai kana son d'anka a raye to ka cire wannan d'an hannun inba haka ba zan kashe shi a madadinka" cikin tashin hankali yake kallon d'an hannun da d'an macijiya ya basa innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai yake mai-maitawa,




Wata uwar tsawa ta daka mai "zakayi abinda nace ko kuwa baka son rayuwar d'an nakahhhh" ta ida maganar a tsawace har hannunsa na kyarma yakai hannunsa zai zare d'an hannun yana cewa "a'a a'a dan Allah ki bari zan cire" cirewa yayi ya wallar dashi wata irin dariya ta kece da ita tana sulalewa ta rabo da yaron bata wani bata lokaci ba tayi salle ta kaimai sara a dai-dai wuyansa ta b'ace ta bar gidan kwata-kwata,




Zubewa yayi k'asa yana sakin wata k'ara da sauri Yaron ya matso kusa dashi yana kuka da ihu yana girgiza Abbeensa kukan yaron yasa har waje ana iya ji,


Haka kawai Aliyu na zaune yaji yana so yaje gidan Mustapha dai-dai yana shigowa yaji kukan yaron a sama da sassarfa ya k'ara sa ganin abinda ke faruwa ya matuk'ar tada mai hankali da sauri ya k'ara so yana kama hannun Mustapha yana girgiza sa hawaye yake yana cewa "ya zakai min haka kaima karka tafi ka barni kagafa ni kad'ai na rage karka tafi kaimahhhh" ya idasa maganar yana fashewa da kuka kamar k'aramin yaro, Mustapha kuwa dake gab'ar mutuwa ya kama hannun yaronsa Al'ameen ya sashi a na Aliyu yace "Aliyu ga yaro na na baka shi halak malak ka rik'e min shi da amana nasan zaka iya tabbas nasan Allah yanzu bazai bata iko a kanka ba saboda baka da laifi ko a wajan Allah tabbas ina ji a jikina zaka kub'uta daga kaidin wannan maciji in...... Tari ne ya sark'esa jikinsa yana chanza kala idanuwansa sun fara kafewa aman kunfa da yake jikinsa ya sake rai yayi halinsa wata irin runguma Aliyu yayi ma Mustapha yana fashewa da kuka shi kansa Al'ameen kuka yake dan kuwa yasan mutuwa tunda ana masu wa'azi a isilamiya cewa duk wadda ya mutu bazai dawo ba ya tafi kenan inya tuna wannan abun sai ya k'ara sakin kuka mai tab'a zuciya shikenan bazai K'ara ganin Abbeensa ba da sauri Aliyu ya rungume Al'ameen suna kuka a tare kyar suka sanarwa mutune aka kaisa gidansa na gaskiya wajan fita da gawar sa kuwa da kyar aka b'anb'are Al'ameen ba wadda bai tausaya masu ba shida Aliyu sun tasu tare amma yanzu ba ko d'aya, Aliyu bayan an dawo kaisa a zuciyar sa ya yanke shawarar barin garin.............










**************** Rigijif akaji fad'uwar Aamah a sume da sauri mutune sukai kanta da kyar aka samo likita ta farka tana kuka kamar zata shid'e ganin haka likita yayi mata allurar bacci dasa mata k'arin ruwa ita kanta Momy ganin bata cikin nutsuwarta yasa itama aka sa mata k'arin ruwan mutune tausayin su fal a ransu dan ita kanta makarantar abinda yasa suka shigeta suna da k'ok'ari sosai hakanne yasa tun a secondary hukumar makaranta ta biya masu zuwa wannan school d'in dan basuda kud'in da zasu iya biya masu kud'in wannan makarantar tabbas k'addara ce ta kaisu wannan makarantar.




Bijay kuwa dashi aka kai Rayha yayi kuka harya gaji ba wadda yake ganinsa sai akai Addu'r uku yana garin sana ya koma Ruman domin shirin d'aukar FANSA dan bazai tab'a yafe masu ba har suyi rayuwar jin dad'i.






Bai sauka a ko ina ba sai gidan su Shamsu Abokin Abdallah dan takansa zai fara Abdallah hukuncin sa na dabanne, ganin irin gidan mai kyan gaske da matakan tsaro a zuciyar sa yace taya za'ai kuwa a hukunta su suna y'ay'an jiga-jigai,




Hango wani d'an aiki yayi zai shiga part d'an Shamsu da abinsha dan ba'a dad'e da sallamo su daga asibiti da sauri ya b'ace ya sauka kusa da d'an aikin jin kamar mutum yana binsa da sauri ya waiga ganin ba kowa yasa ya cigaba da tafiya Tafiyar dai ya k'ara ji a bayansa da d'an fad'a-fad'a yai waigo nufinsa ko wani cikin y'an aikinne ke binsa yana so yayi mai wasa wani abu Bijay ya fesa mai danda nan ya tafi dogon bacci chan wani lungu ya ajiyesa ya dafe kansa ya dawo suffar d'an aikin sak da d'an hanzari ya d'au abinda shan wadda za'a kaima Shamsun d'auka yayi yana kallon abin shiyi ne wani abu ya d'akko a jikinsa yasa a shayin danshi bazai sa masu dafinsa a'a saiya basu wahala a rayuwa inya so daga baya su mutu,




Shiga yayi yana zaune yana kallon boll kamar ba abinda ya aikata jin an bud'e k'ofa yasa ya waigo ganin d'an aikinsa yasa ya tsine baki yace "ajeshi nan" yana nunamai wani teburi dake kusa dashi ajewa yayi kamar yadda yace sana ya d'an tsaya a kansa cike da isgilanci da raina talaka ya buga mai wata uwar tsawa cewa "kai miye na tsawa kuma kama hanya ka fice min daga gani sai wari kake ma" wani munafikin murmushi Bijay yayi yana juyawa ya fice kwata-kwata daga gidan,




Shi kuwa Shamsu yana kallon boll yana murna wadda yake so sunci yakai shayin bakinsa duka ya shanyi saboda dad'i da gama shan shayin ya fara tari amma duk da haka ihu yake na kallon boll d'in jikinsa ne ya fara wata irin mika yana lallauyewa ya zube a k'asa bakinsa ya karkace hannuwansa sun lauye duk jikinsa ya shanye ihu yake yana k'ara wa ganin abinda yake faruwa dashi anya shine kuwa da sauri ahalin gidan sukayo parta d'insa jin ihunsa cike da tashin hankali ganin abinda yake faruwa da sauri aka kwashesa sai asibiti Daddy d'insa kuwa duk ya rud'e dan mahaifiyarsa ta rasu babban asibitin garin aka kaisa cikin sauri aka amshe sa iya bincike likitoci sunyi bincike amma basuga komai ba tashin hankalin iya tashin hankali Daddyn Shamsu ya shiga likitoci sunmai bayani sufa basuga komai ba kawai shanyewar jikinsa ya shanye wadda bazai K'ara moruwa ba sai dai zasu rik'e sa asibitin su d'ora sa a magani aga abinda Allah zaiyi Daddy sosai ya shiga rud'a ni ba kad'an ba haka aka ci gaba da jinyarsa ana basa mgani amma sauki sai wajan Allah kam jiki na nan a lallauye baki ya karkace har miyau ke jalala ya zama musaki tuburar.




Kamar yauma bayan an basa magani kowa ya fita daga d'akin jinyar Bijay ya shigo d'akin a matsayin likita zama yayi yana murmushi kallonsa kawai Shamsu keyi ba bakin magana dan ko magana ba iyawa yake ba shafa fuskarsa yayi yana cewa "saka makonku kenan sai kuma na Allah in kunje can ai nasan bazaka manta da Rayha wadda kuka cutar da rayuwar ta ba kukai sanadiyyar mutuwar tahhhh" ya ida maganar da k'arfi har gadon da Shamsun ke kwance na girgiza Shamsu kuwa fitsari ya saki nadama ce ta dirar mai marar anfani kuka yake hawaye kawai ke zuba ga baki dake mutsi yana so yayi magana amma inah Bijay kuwa ya k'ara cewa "ai kaida magana har abada kaida tashi ma sai dai kaga wasu nayi" bat Bijay ya bace ganin abinda ya faru yasa jikin Shamsu k'ara rikicewa na'ururi jikinsa suka fara k'ara da sauri likitoci suka shigo ganin numshinsa na gaf da d'aukewa taimakon gaggawa suka fara bashi amma ina numfashi ya tafi saboda abinda ya faru zuciyar sa ta bugu likitoci suna share zufa suka fito lokacin Daddyn Shamsu ya k'ara so bayanin da likitoci suka mai ba k'ara min girgiza yayi ba da kyar aka samu ya dawo hayyacinsa aka d'auki gawar sa sai gida mutanan gidansu da ma'aikata kuwa wasu sunji mutuwarsa wasu kuwa ko a jikinsu dan kwata-kwata bashida kirki haka dai aka kaisa gidansa na gaskiya daga shi sai halinsa..........✍️
















*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️


















Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
































*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*












*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






*PAGE D'IN K'ARSHE1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣*






___________________✍️ cikin k'ank'anan lokaci Aliyu da kuma d'ansa na yanzu Al'ameen ya gama had'a kayansu inda saura kwana biyu subar garin da yawan mutane na zomai gaisuwa






Kamar yauma bayan wasu sun fita Al'ameen na zaune akan ciyarsa duk ya zama abin tausayi, tashi yayi yana kallon Aliyu yace "Daddy ruwa zansha" (da yake haka Aliyun yace daga yau ya rink'a kiransa da Daddy,




Da sauri Aliyu cike da k'aunar yaron ya tashi ya zaunar dashi yaje d'akko mai ruwan dawowar da zaiyi ya hangi kamar gilmawar mutum da hanzari ya yunk'ura zai rungume Al'ameen yaga tashin abu sama ya nufi inda Al'ameen yake Allah yaba Aliyu sa'a har yana fad'uwa ya k'ak'k'ame Al'ameen a jikinsa waigawa yayi ganin wata narkekeyar macijiya sai uban huce take tsalle zata k'ara yi ta kaima yaron hari dan bata da ikon tab'a Aliyu saboda karinyar da yake da ita.




Sai dai Allah mai rahama ne da yake Aliyu bashi hakki akan duk abinda ya faru, tsallan da tayo ta afkama window dake kallon waje, window d'in ya tararratse duk ya caketa (kunsan maciji indai wani abu yayi mai rauni to tabbas ba lallai ya tashi), to haka ta kasan ga Amreeta dan fad'awar da tayi duk gilas d'in window ya caketa sai kuma tayi rashin sa'a ta fad'a akan wasu k'ayoyi masu mugun tsini,




Da sauri Aliyu ya fita yana kallon yadda duk k'ayoyin suka caketa shida Al'ameen kallon abun suke kamar almara, kwance take akan k'ayoyin sau wani irin huce take fiddawa na tsananin azaba rikid'ewa take a hankali har ta zama suffar mutum cikin tsoro Aliyu yaja baya Al'ameen dake jikinsa ya k'ara k'ak'k'ame sa,




Ita kuwa dake gab'ar mutuwa tana kallonsu tana murmushi tace "tabbas baka da laifi zan tafi nabar wannan duniyar da farin-ciki na cika burina na d'aukar wa mutanan da sukafi soyuwa a gurina *FANSA*" daga kanta tayi sai ta rink'a hango Khausar d'in ta da Mijinta suna mata murmushi sanye da fararan kaya suna mik'o mata hannu, Murmushi tayi ta k'ara kallon Aliyu da cewa "ka gani suna kira nazo su tafi dani inda suka tafi" tana murmushi yaga ta muk'a hannunta gani yayi ta bace bat a wajan kamar ba'ayita ba.




Ba k'aramin sauke ajiyar zuciya Aliyu yayi ba lallai Allah yana sonshi da rahma sujadda yayi ta godiya ga Allah daya karesa,




Aliyu bai fasa barin garin ba dan kuwa Washe gari yabar garin da d'ansa ya sauka a garin da masoyiyarsa take wato Aliya garin KANO Take da zama yazo da uwar kud'in sa yasai gida madai-daici inda baiyi k'asa a gwaiba ya nemi auran Aliya ba'a wani ja lokaci ba aka basa auranta.




Bayan aure da kwana biyu zaune suke ita da Aliyu Al'ameen nakan jiyarta zai zuba mata shagwaba yake inda Aliyu ya gama bata labarin irin abubuwan da suka fuskanta a rayuwa har kuka tasha jin wannan labari mai rikitarwa cike da kwanciyar hankali suke zamantakewarsu gwanin sha'awa inka kallesu da Al'ameen baka tab'a cewa wai basu ne iyayansa ba sosai Aliyu ya samu cigaba a rayuwarsa inda dukiyar Al'ameen ta mahaifinsa yana tattalamai yadda ya kamata inya girma yayi hankali ya basa abinsa zaune suke lafiya da matarsa Aliya data gansa cikin damuwa to yana tunowa da Abokansa ne zatayi iya bakin k'ok'arin ta wajan kawutar mai da damuwa rayuwarsu sun abin birgewa da Soyayya mai tsayawa a zuciya..................














****************** Tofa koda Abdallah yaji mutuwar Shamsu lokacin yana masha'arshi tare da wata karuwarsa yad'an ji mutuwar kad'an ya jigaba da sha'aninsa ita kuwa karuwar sai k'ara wani narkemai take dan tasan abin ta kunsa mai dan kuwa d'auke take da cutar nan mai karya garkuwar jiki baccin nan d'auke take da wani mukuguwar cuta dake gabanta,




Tunda yayi ma'amula da wannan karuwar tasa gabansa ya kama k'aik'ayi gaban kowa yana iya zura hannu a wando ya kama kartar gabansa yana lumshi ido saiya gama kuma wani rad'ad'in azaba ke ziyarceshi haka zai kama kuka tuburar koya tub'e kayansa a gaban kowaye, Tofa nan mutane suka zancen koya haukace ne wasu daga cikin su kuwa har video sukai mai ana dora a duniya innalillahi wa'inna ilaihir ahalin Abdallah bare Abbansa ya shiga tashin hankali Mamarsa kuwa yanke jiki tayi ta fad'i ganin videon d'anta a duniya tunb'ur haihuwar uwarsa yana susar gaba da alama bai san ana videon ba.




Abu fa sai gaba-gaba yake dan kuwa saida aka dangana da asibiti to a asibitin ma dai sun d'ora sa a magani amma ina dan gabansa mazakuntarsa ta kunbura tayi sumtun ga kurajen sun fashe ga wani aban d'oyi da wajan ya farayi inda Bijay duk yana kallon miyasa meshi lallai ya k'ara yarda Ubangiji baya son mugunta gashi tunkan ya d'au mataki ta Allah ta sameshi duk da haka saida ya ziyarce sa har asibiti a matsayin likita ya basa Maganin daya ba Shamsu dan kuwa Aliyu na iya magana saidai yana cikin mawuyacin hali tofa bayan Bijay yaje ya basa wannan magani yasha da rashin sanin waye ya basa tashin hankalin da ahalin Abdallah suka sake shiga shine shanyewar jikinsa baki ya saki yana jalalar da yawu ga hannu a babbank'are Bijay kuwa ya bacewa cike da tsananin murna na sakama Rayha Ubangiji yayi tun kan aje ko Ina.




Jikin Abdallah fa in gabansa ya tashi k'ak'ayi ba sauk'i gashi jiki ya shanye birgima yake kamar mahaukaci yo gara ma wani mahaukacin dan kuwa d'ankin da yake wani irin mugun wari yake wadda yasa mutane da yawa in suka shigo da gudu suke guduwa tsananin warin da d'akin yake mutane da yawa sun gujeshi ciki harda y'an uwansa daga iyayensa su kad'ai suma sai sunkai zuciya nesa suke shigowa in sun shigo ba wani dad'e wa suke iyayi ba to Mamarsa kuwa tun sadda ta fad'i hawan jini ya kamata bata iya komai asibitin ma kansa ganin sai korar masu mutane yake yasa suka sallame sa ba shiri koda aka kawosa gida can aka ware mai wani d'aki inda kowa bai shiga can wajajan masu aiki ko abinci za'a basa sai dai a warga mai ga gabansa sai k'ara ruwa yake har wasu tsutsotsi sun fara fitowa ta gabansa zuwa wannan lokaci yasan cewa alhakin Rayha ne ke bibiyar sa a yanzu ya gwammace mutuwa da rayuwa kullum cikin rok'on Allah yake daya d'au ransa dan mutu ai hutu ce da wannan bala'in da yake ciki duk da yasan koya tafi lahilar wani jan aikinne a chan






Zaune su Momy suke da Khausar daka kalle su kasan farin-ciki yayi k'amari a rayuwarsu dan har yanzu basu dawo dai-dai ba Momy data g damuwar tayi yawa ta tashi ta kunna tibi dan rage damuwa dan rabonsu da wani kallo harsun manta tashar labarai ta kai dai-dai an hasko gawar Abdallah Allah yayi masa rasuwa bayan tsawon jinyar daya sha zaro ido Momy da Khausar sukayi ganin SAKAYYAR da Allah yayiwa Rayhansu lallai Allah buwayi ne gagara musali godiya suke ga Allah ga wasu irin zafafan hawaye na zuba ta idanuwansu tunuwa da Rayha Aamah tace "Momy kinga ni ko tun a duniya ma kenan" ta ida maganar cike da marin cikin wannan abu Momy kuwa hawaye take na tsananin godiya ga Allah daya sakawa d'iyarta tun a duniya.




A wajan gidan su Abdallah kuwa da yawa farin-ciki suke da mutuwarsa dan duk ya ishesu da wari a cewarsu dama akan k'aya suke dan da kyar aka samu masu mai wanka sun dod'e hanci da kyar da kyar suka k'arasa mai duk da sun dod'e hancin haka aka sallace sa aka kaisa gidansa na gaskiya daga shi sai abinda ya shuka.




Kai jama'a muji tsoron Allah mu daina biyewa sun zuciya da rud'in duniya
miyasa dad'in da bai tab'a tsallake shekara ɗari na a duniyarka zai rud'eka ka manta da dubbunan shekarun dake gabanka na barzahu kawai?, miyasa dad'in dake k'alilan na duniya zai rud'eka ka manta da ranar hisabi ranar da bata da kwatankwaci ko misali😭?, ga dai Abdallah ji karshan sa, akwai ranar rarrabe gaskiya, ranar tonon silili, ranar da uwa ke gudun d'anta, ranar da d'a ke gudun iyayensa, ranar da kanka kawai ka sani, ranar bud'e b'oyyayun sirrika😭 (Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un) y'an uwana! Y'an uwana! Mi muke tunani haka da zurfine? Mi muke buri haka da yawane? Mi muke fatan samu haka da yawane? Mi muke k'ok'arin mallaka haka da yawa ne? Mi yake canjamu haka da yawane? Mi yake rud'armu haka da yawa ne? Mi muke tak',ama dashi haka da yawa ne ji Abdallah duk dukiyar sa data babansa yanzu tana ina ina tak'amar take? Da mi muka dogara haka da yawa ne? Suwa muke tunanin ko zaton sun tsaya mana haka da yawa ne? Ina mukabar imaninmu tafiya haka da yawa ne? Ina muka bar zukatanmu haka da yawa ne?😭😭.


“🙏🏻😭Ya rabbi ka gafarta mana badan halinmu ba”.




Allah ka tsaremu da mummunanr k'addara ya Ubangiji Allah ka tseratar da zukatanmu da gangar jikinmu aikata sab'onka ya Ubangiji..............






Alhmdllhi Alhmdllhi Alhmdllhi




Allah na gode ma daka bani ikon kammala wannan d'an tak'aitaccen labari nawa Ubangiji Allah darasin dake cikin wannan book Allah ya bada ikon anfanuwa dashi illar dake ciki kuwa Allah yasa ayi watsi da ita




Ina k'unar ku Masoya na irin sosai d'in nan a duk inda kuke fad'in duniya.




Sai kun sake jina a wani sabon book nawa in sha Allahu.




*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*




PHONE NUMBER_08130479973






Email address_ [email protected]
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment