Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga murya samira ta tambayeta,itama ta dubeta ta mayar mata "kamar yadda kika kunnuwanki suka ji nace"da sauri ta nunata da yatsa "baki isa ba wallahi kinyi kadan don yadda kike buqatarsa nima hakan take.....ke bari ma nayi miki dalla dalla...yadda kike a matse ni nama fiki matsuwa"ta fada tana wani gayara zama,sai kuwa cece kuce ya barke dama kadan kowacce take jira 'yar uwarta ta tabo ta,sak yayi yana kallonsu,sai ya zama kamar wani mutum mutumi,babu wadda tayi masa wani abu na azo a gani a matsayinsa na matafiyin da yayi wata judu bai cikin iyalinsa yanzu ya dawo musu,shegiya shinkafa fara sol da yaji babu wadda ta turo masa tace gashi,amma aqalla ai ko tsakar dare ya dawo idan da tunani sa tashi su sama masa wani abu ko drink ne,to amma ga drink din ma jibge a freezer dinsa su dauko ma su hada masa da cup suce masa gashi babu wadda ta iya yin hakan,babu wani welcoming na arziqi,amma ko wacce burinta ya kwanta da ita ya biya mata buqata kamar wani inji

Ganin abun nasu ma shirin wuce makadi da rawa don har an fara 'yar lakace lakacen hanci yasa ya dakatar da su ta hanyar daka musu tsawa don idan ba tsawar ya musu ba yadda suka kacame babu wadda zata iya jiyo shi"bana buqatar kowa cikinku,duk ku tashi ku bani waje,tunda ku baku iya kwantarwa da mutum hankali ba saidai ku tayar masa,ko kwana daya banyi ba cikin gidana amma kun fara samin bacin rai?" Tuni samira ta miqe,salima ta rausayar da kai tana cewa "amma aliyu ......." "amma me?Please stay away" ya fada yana nuna mata hanya,samira ta sheqe da dariya tana cewa "ato saiki taso ai mu daye,ki daina naci haka kowa sai ya riqe kwadayinsa tunda yace bai yi" wani banzan kallo alin ya watsawa samiran yana cewa "kin sanni,kada ki bari muyi arangama dake bani da kyau!"tasan hakan kuwa tuni tayi gaba salima ta bita a baya,yan jiyo kici kicin kokawarsu a bakim part din nasa,yayi banza da su

_*12 PM*_

Sha biyu na dare ya dinga gwada maqullan hannunsa a qofar har ya samu na qofar tata,ya tura ya shiga ya haska makunnin fitila ya danna dukka qwayayen suka kama bangaren ya cika da haske,qamshi falon yake tamkar tana nan,kamar bata yi tafiya ba na tsawon watanni hudu ba,hakanan komai akillacensa,kai tsaye ya shige bedroom dinta,shima dai kamar falon cikin qamshi yake da tsafta,gadonta a dame yake komai ajere,pant da brassier dinta ne kawai a gefan pillow,ya qarasa ahankali ya haye gadon hadi da kwanciya pillow din ya janyo hadi da rungumeahi tsam tsam a qirjinsa,qamshi pillow din yake kamar a shafa masa turare ne,ya sake miqa hannu ya dago pant and brassier din farare qal ya zuba musu ido,a hankali ya mannaau a hancinsa yana sheqar qamahin turarenta na shamsul imaraat

A hankali ya shiga sosai cikin zurfin tunani,yanayinta,halayenta,dabi'unta,haquri irin nata kawaici da yakanah,bai taba ganin ta tana fada irin nasu samira ba,bai taba ganinta tana koda sa'insa da daya daga cikinsu ba,duk wata sabga tasu bata ciki,shi da kansa alokutan baya har haushi yake ji idan yaga bata damu da fadan kishi ba,ashe so ne?,ashe haushi yake ji yana ganin kamar bata sonshi ne?

Juyi kawai yake samar gadon,jinsa yake tamkar wani maraya,wani irin kewa yakeji mai zafi da radadi tana kamashi,ya riga da ya saba da kwana jikinsu na gogayya da na juna,ya saba da sheqar qamshinta,sosai ya sake rungume pillow yana sakin numfaahi sama sama,yafi awa biyu kafin wani wahalallen bacci awon gaba da shi ,ko cikin baccin ma bata qyaleshi ya huta ba sai da ta jawo masa yin wanka,ya dawo bakin gadon yq zauna yana tsane jikinsa da towel dinta,idanunsa ya sauka kan wani dan kyakkyawan madaidaicin frame da yake zaune dirshan bisa side bed,yasa hannu a hankali ya dauki hoton ya zuba masa ido yana kallonta,murmushi take yi sosai,fararen haqoranta jerarru reras sun bayyan,yar lobawar dake tsakiyar habarta ta fito sosai,ya sanya bakinshi saitin lips nata yayi kissing,murya qasa qasa yace "I love you"ya dan manna hoton a qirjinshi

Sai da yayi sallar asuba sannanya baro bangaren har ya fito ya manta bai dauko hoton ba ya koma ya dauko abinsa,kan side drower dinshi ya kafa sa,yana shiryawa yana kallon hoton har ya kammala shirinsa tsaf cikin shadda fara tas mai asalin tsadar sai maiqo take da daukan idanu,yayi masifar kyau saidai fuskarnan na kirtibe,qarfe bakwai ga fito ya soma da sashen samira don itace a damansa,yana tura qofar ta bude alamuna bude ta kwana,kai tsaye ya zarce bedroom din ta don yasan tana ciki,yana tafiya yana bin falon da kallo tamkar dakin ajiyar shirgi haka ta maidashi

Dai dai ya sameta saman gado hannu can qafa can,gajeran gashinta maras tsawo wanda bai hadu da mace mai gyara ba duk ya hautsine ya tashi yayi cako cako kamar bishiyar qaya(don ko baki da tsawon gashi matuqar ke mai gyara ce to zai bada sha'awa,amma komai tsawonsa indai ba gyara abin qyamata zai zama),sosai iyyu ya tsani irin wannan kwanciyar tata,don kuwa insha Allahu kuka hada gado daya da samira to ranar fa ka shieya zaka daku da hannu da qafa,haka kullum yake fama da ita,shi yasa ya gwammace ya matseta a jikinsa ayi baccin haka

Ya dan taba qafarta yana kiran sunanta,saidai kamar gawa ko motsi bata yi ba bare yasa ran zata tashi jan minsharinta kawai take,yasan hali dama bata motsa din ba kuwa har sai da ya dage ya daki daki qafar da hannu sannan ta miqe a zabure tana cono baki gami da mutsitstsika ido,sai da ta gama mutstsike idanun sannan ta dubeshi,ganin aliyyu a tsaye ya sata shiga taitayinta,addu'a take cikin ranta Allah yasa maganar laifinta yazo yayi mata,don tasan halinshi shirunsa ba abu mai dadi yake haifarwa ba,fuska a murtuke yace "hala ko sallar asuba bakiyi ba?" Nan ta hau kame kame "zan....zanyi....yanzu ne na tashi ai..." "good" yace da ita cikin takaici yana gayada kai,ya juya zai fita "zan fita sai na dawo" "to" tace kaar wadda aka tilasta ta sai ta fadi hakan,Allah Allah take ya fitan taja bargo ta koma barcinta,bata sani ba shi din ma Allah Allah yake ya bar dakin,don zarnin bandakinta dake cikin bedroom din shi ke busowa har cikin dakin gadon,sai taga kuma ya juyo hadi da cewa "bani key din motarki da wayarki" cikin marairaita tace "don Allah kayi haquri bazan sake ba" a zafafe ya kalleta "will you keep quiet or not? Da baki iya bada haqurin ba kenan sai yanzu?common bani key da phone nace"nuni tayi masa kan hargitsatstsen dressing mirror dinta,ya juya ya kalli kan madubin saboda hargitsewarsa ma shi bai hango wata waya ba ballantana maqulli "ok...ni zanje ma na dauko miki ko?" Dolenta ta sauka daga kan gadon ta dauko ta miqa masa tamakar zata yi ihu,ya amsa ya fice da sauri ba tare da yace mata qala ba don zarnin sake busowa yake,kuma ko yace ta gyara ba zata yi din ba don sau nawa yana fama da ita kan hakan sai tave masa yau fa sati daya kacal da wanke shi ba wani dadewa yayi ba

Salima ma na bisa gadon a nade bacci na dibarta sama sama,ita din ma sai lokacin bakwai da wani abu ta yi tata sallar,saidai yana sallamar ta amsa gami da miqewa zaune kan gadon,murmushi take masa wanda hakan ya sanyashi rage daurin fuskarsa"kar daiace har ka fito" ta soma cewa,ya kalleta yace "eh"yana mamakin yadda basu iya gaisuwa wa mijinsu ba,babu wadda ta fado masa sai fadilan,duk safiya sai ya gaidashi kamar yadda ya zame mata qajibi sannu da zuwa da adawo lafiya duk da sai yaso yake amsawa amma hakan bai dameta ba haqqinta take saukewa, "amma yaci ace yau a gida zaka wuni ko" ta sake shigowa da wani qorafin "a hakan kuna batan ran babu wani caring bare a faranta maka"yayi zancqn cikin zuciyarsa,a fili sai yace "maiduguri zani zuwa anjima zan dawo insha Allah"cikin tuhuma tace "maiduguri?gurin wa?...." "stop your suspicion,sai na dawo" ya katseta, "madalla"tave tana binsa da cike da kishi har ya fice

Cikin motarsa qirar 4matics fara ya zabi yin tafiyar shi kadai,bayan yin addu'o'in matafiyi ya kunna motar ya fice daga gidan cikin tsammani mai yawa da fata na gari akan kanshi

*mrs muhammad ce*👑

📘📘📘📚📚✍🏻✍🏻
[10/16, 2:10 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

7⃣&8⃣

Cikin kwankin kullum cikin kuka take kwana take wuni,a haka ma an samu sauqi saboda takan kaucewa idon anty hauwa don kada ta dinga jin ba dadi,damuwa sosai ta yiwa zuciyarta yawa,tana jimantawa kanta yadda soyayyar aliyu ta gama illata ta,saidai bata barin damuwar ta tsawaita mata da yawa ba ta tsananta yin addu'o'i,da taimakon hakan ta soma samun kyakkyawar nutsuwa cikin ranta,koda yaushe cikin kula da ita anty hauwa take bata barinta ta zauna ita daya bare ta damu sosai,sau da yawa anty hauwan idan tana bata haquri kunya fadilan keji "nifa babu wanda yayimin laifi don Allah anty ki daina bani haquri,kunya hakan yake bani wallahi"

Yara kam murna suke anty fadila ta dawo gidansu sunata tsalle,idan akace babu makaranta to suna liqe da ita wani lokacin har sai anty hauwan ta kore mata su tace su barta ta huta,ita kam dadi take ji idan tana tare da yaran saboda dama can mai son yarance ita,sosai mamansu taja kunnensu da kada su sake su gayawa kowa cewa anty fadilan tana nan gidan saboda yadda taga suna rawar qafa zasu iya subul da baka

Ita kanta tayi mamaki qwarai yadda ta soma ragewa kanta damuwa kan aliyun duk da yake ba abun mamaki bane addu'a ai tafi qarfin wasa,sosai tayi yaqi da zuciyarta,bata bari bacin rai ya rusata ba,da zarar ta soma tunane tunane zata datseshi ta hanyar daukan qur'ani ta karanta,idan ta gama kuma ta shiga shafukanta na sada zumunta,komai anty hauwa ta hanata yi,duk da hakan fadilan taqi yarda don kullum tare suke shiga kitchen yin lunch ko dinner,wani lokaci kuma ta shirya mata yaran da safe

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Gudu sosai ya dinga yi shi daya cikin motar,cikin ikon Allah ya sauka lafiya,saidai tun daga yadda su ya gana ke faman tambayar fadilan ya sare da al'amarin ya tabbatar bata garin ma baki daya bare gidan,sallah kawai yayi ya baro garin,bai damu da yawan tafiyar da yasha ba bare ya nemi hutawa har yaci abinci,juyin duniya ya gana tayi ya tsaya yaci abinci amma qeme me yaqi,ya bata haquri bayan ya ajjiye musu kudade masu dama yace yana da abubuwan yi masu yawa a kano,haka ya kamo hanya ya taho,gudu na ban mamaki ya dinga shararawa ba qaqqautawa,sai da yaji tuqin na neman gagararsa sannan ya samu wani shago kam hanya ya siyi yoghurt yasha,bai fasa gudun nasa ba wanda ikon Allah ne kawai ya kawoshi garin kano lafiya
🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Kwana hudu bai cikin daidanshi,matansa mata ne marasa kulawa,tabbas sunga canji sosai tattare da shi amma babu wadda ta damu da tambayarsa mene damuwarshi,momi kam ganin baice komai ba yasa ta tsuke bakinta ta qyaleshi don ta sani ida dai ya soma zurfin cikin nan nasa bai gayawa kowa komai sai lokacin da yaga dama

*G*idan anty hauwa shine gida na qarshe da hankalinsa ya kai kai,anan ya tattara dukkanin fata da tsammaninsa,duk da wata zuciyar na tantamar mai zaya kaita can bayan ko gidansu bata je ba?,qarfe biyar da shirin na yamma ya gama shirinsa cikin qananun kaya da sukayi matuqar yi masa kyau

Suna kitchen ita da fadilan suna hada abincin dare sunayi suna hirarsu,yara suka jiyo wadanda suka bari a falo suna kallo da yake alhamis ce suna cewa "ina wuni uncle....ina wuni uncle" gaban fadila yayi mummunar faduwa ta saki mirfin hannunta da take shirin rufe miya da shi,"shikenan yau zan amshi takardar rabuwa da shi" abunda zuciyarta ke gaya mata kenan "anty aliyu ne"ta fada tana kallon anty hauwa dake tace shinkafa "aliyu?" Ta fada tana kallon fadilan cikin kasa kunne,"ina zuwa" anty hauwa fada bayan ta ajjiye tukunyar hannunta ta fice da sauri,komawa fadila tayi jikin drawer ta jingina bayan ta hatde hannayenta a qirjinta tana jiyo sweet voice din sa,batasan me yasa take jin qunci a qirjinta dalilin gaya mata da zuciyarta ke yi takardar sakinta aliyun ya biyota da ita

Ruwa aliyun yace ma anty hauwa ta bashi,duk ruwan dake freezer din falonsu ya qare sai lemo,da hanzari anty hauwa ta miqe ta hau sama ta dauko masa a parlour din abban kausar don bata son ya shiga kitchen din,ji yayi bazai iya jiranta ba don haka ya miqe ya shige kitchen din,a hankali fadila ta bude idanunta da a da ke a lumshe,cikin jikinta take jin tahowar tasa,nan da nan tayi wuri wuri da ido tana neman maboya,a asukwane ta shige bayan qofar wadda a kusa da ita freezer din take

Kai tsaye ya qaraso ya dage freezer din ya sunkuya yasa hannunsa ciki,cak ya tsaya da qoqarin ciro ruwan da yake yi,sai yake jin qamshinta cikin hancinsa,irin qamshin da ya ji cikin bargo pillow da undies dinta,sakun murfin yayi ya soma kallen kallen kitchen din yana neman ta inda qamshin ke fitowa,ko ina ya kai idanunsa sai yaga babu kowa,tuni fadila tayi surrender bayan qofa numfashinta kamar zai dauke musamman da taji ua jingina a bayan qofar ya kuma qin barin gurin,yafi minti uku cikim kitchen din yaqi fita din qamshin turarenta na ahlamul arab kawai yake ji,hat sai da anty hauwa ta shigo hankalinta a tashe tana tsammanin ya ga fadilan,sai ta tadda shi a tsaye kawai jingine jikin qofar hannayensa harde a qirjinsa,"ina ka shiga ga euwan can na kaimaka" "ok" kawai yace ya gewayeta ta fice daga kitchen din itama ta rufa masa baya

Ta maida yara dakinsu daga ita sai shi a falon,zuba masa ido tayi sosai tana kallonsa canji qara ta hango tattare da alin,fara'arsa ta sake qaranci sosai,tsiyayar lemon kawai yake yi yana dirkawa cikinsa,yadda bai tanka ba itama bata ce kamzil ba har sai da ya tashi da roba biyu ta ruwa da lemo,ya dago kai ya kalli antin hadi da sakin ajiyar zuciya "ni wai uncle meke damunka?tunda kazo naga kamar a hargitse kake?"wata ajiyar zuciyar ya kuma saki "fadeelah nake nema mummyn kausar" kamar gaske ta nuna alamun rashin fahimta sosai "kamar yaya?fadilan da kuke tare,yaushe dududu sumayya ta ke gayamin kun dawo daga china zaka ce ita kake nema kamar wadda ta bata" "bata tayi....bacemin tayi"ya fadi yana jingina jikinsa da kujera,yayin da fadila dake labe cikin kitchen ta zaro ido jin cewa wai nemanta yake "yayimin me? Me zayayimin ne?"ta tambayi kanta ba tare da tasan amsar tambayar ba

Ya dora cikin wata iriyar murya "tayi tsammanin bana sonta ne bayan nima na dade ina sonta,tayi zatin maqiyinta ne ni alhali duk duniya babu mai sonta kamar ni...ta dauka ina zaune da ita ne bisa dole bayan kan son raina nake zaune da ita.....anty ta yimin gurguwar fahimta,ta gujeni a lokacin da na qara zurfi cikin qaunarta....ta gujeni a lokacin da dukkanmu ni da ita muka fi buqatar kasancewa da juna"ita kanta anty hauwa baki ta saki tana tsammanin ba aliyu bane,aliyyun da tunda take tare da shi zata iya cewa bata taba ji ko ganin yana kwatanta qaunar da yakewa wata diya mace ba aduniya koda uwar 'yarsa,fadila kam dake cikin kitchen duburburcewa tayi,sai jikinta ya fara rawa qafafunta suka gaza daukarta ta lallaba ta ja jikinta ta zauna kan kujerar roba bakinta rufe da tafin hannunta yayin da hawayen da sukayi kwana da kwanaki tana qumshe su yau suka samu qofa.

Lallai ma yaudararta aliyu keson yi?,dama shi din shahararren mayaudari ne,shine a yanzu zai furta cewa yana sonta?wanne irin zama ne basu yi ba baice yana son nata ba sai ayanzu?sai yanzu da ya kwanta da ita?,ya tabbata kenan jikin nata yake so kamar yadda tayi zato tun farko? (Illar zato),sha'awarta yake kenan ba qauna yake mata ta cikin zuciya ba?,kuka ne sosai mara sauti ya kufce mata yayin da shi din ma ke can zaune dirshan gaban anty hauwa yana fayyace mata irin zaman da sukayi da fadilan,kunne sosai ta saka tana jinsa duk da yake tamkar tishi yake mata,duk yadda fadilan ta fada hakanne harda wasu abubuwan da fadilan ta boye ta qi fada

Kafin ya kammala tuni har qwalla ta cika idanunsa duk da bata gai ga zubowa ba amma qiris take jira,soyayyar 'yan uwan taka sai Allah tuni tausayinsa ya kamata don zata iya dafa qur'ani kan aliyyu bai taba shiga makamancin wannan halin ba akan wata mace,ta karanto gaskiyarsa qarara,don dama ko ada bai iya qarya ba tun yana qaraminsa,zai gaya ma gaskiya ne ko za'a tsireshi don haushi,to saidai bata jin kuma zata shiga haqqin fadilan ta karya alqwari da ta daukar mata don aliyyu nata ne,bata jin zata sarayar mata da haqqinta tunda nata din ne,ita ke da iko da abunta,ita kadai tasha haqurinta ita kadai tasan me ta hadiya

Cikin sanyin jiki da qunar rai yace"wai anty roqona take na saketa,tana tsammanin sakin nata abu ne mai sauqi har irin haka a gurina?" Ya kada kai yana cewa"bazan iya ba,bazan iya furta wadan nan kalmomi gareta ba koda duka duniya zata taru a kaina" dole ka sake ni aliyyu dole mu rabu ,bani kake so ba jikina kake sha'awa" ta fadi haka qasa qasa cikin kuka mara sauti,ya miqe "zan tafi tafi tunda kema bata gunki zan ci gaba da nemanta",tuni ya juya ya fice daga gidan,tausayin dan uwan nata ya kamata don tasan wahla kawai qanin nata zaici gaba da sha tunda fadila na tare da ita

Kifa kanta tayi kan cinyarta ta sake sakin wani sabon kukan mai dan qaramin sauti,wani qunci zugi da radadi data rasa na meye take ji cikin ranta,anty hauwa ta kama hannayen fadila tana kallin qwayar idonta "fadila.....fadila,naga abubuwa da dama cikin qwayar idanun aliyu,naga soyayya naga qauna cikin cikin idonsa irin wadda ban taba gani ya yiwa wata 'ya mace ba,kinji komai da kunnuwanki no need na maimaita miki"

Kada kai fadilam keyi,"anty na yarda aliyu na sona a yanzu bazan qaryata ki ba,anty amma ba ni fadilan yake so ba wani abu dake gareni yake so,tun yaushe anty....tun yaushe nake tare da shi nake kyautata masa bai taba cewa yana sona ba sai yanzu?sai yanzu da wani dalili ne ya jawo hakan?...Thank god aliyu na sona yanzu anty,saidai ......is too late anty I already displaced him from my heart,na goge cikin kundin rayuwata zan rayu da shi" kalmar ta fito daga bakinta hade da hawaye

Sai dariya taso kama anty hauwa amma ta gimtse,with confidence fadila ke fadin maganar saidai qwayar idanunta kadai ta ta qaryata ta,bata sani ba ita kanta qaunar aliyyu tayi mata illar wadda take huduwa tun daga zuciyarta har zuwa idanunta da bakinta,bata da abunyi anty hauwa ta sani wani daci ne da fadilan ta dade tana guntsa taje fesarwa idan ta hanata kuma bata yi mata adalci ba,tasan cewa kokwanto ne yasa fadila fadin wadannan maganganun amma ba har cikin zuciyarta bane,ta kuma gama gasgatawa wani irin salon rikicin soyayya ne ya kunno kai kawai tsakaninta da aliyyun,sanoda haka sai kawai tave mata "shikenan fadila kici gaba da addu'o'inki ki yi ta istihara,Allah ya zaba abinda yafi alkhairi"

Har anty hauwan ta kai bakin qofa fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"am sorry anty idan maganganuna sun bata miki rai" murmushi ta saki "don't mind,banji komai ba araina fadila" murmuahi itama tayi mata tace "na gode" haka Allah yayi fadila bata aon bacin rai ko yashin hakai ko kadan kamar yadda bata son taa ta batawa wani rai ko ta shiga haqqinsa

Kwana biyu yama cikin wannan hali,duk wasu harkokinsa na gida dana waje yaqi maida hankali kan kowanne,daga qarshe dai kasa jurewa yayi gani yake kamar su suka boye masa fadila,yana ganin da wani yashin hankalin gwara wani,da ya rasata gwara a yanke masa duk wani hukunci da za'a yanke masa idan yaso su bashi ita,ya gaza jure kewarta komai nasa ya yi missing dinta,

🔅🔅🔅🔅🔅

Tsakiyat uncle abba da momi ya zauna ya warware masu abinda ke faruwa kamar yadda halayyarsa take fadin gaskiya,momin ce ta saki salati mai nauyi yayin da uncle abba yayi shiru gami da yin tsai da ransa,sai a lokacin ne kuma hankalinsa ya soma tashi momi tayi shiru ne tana jiran jin umarni ko me mijin natazaya fada?,yayin da uncle abba ya rasa me ma zaya ce din?,sama da minti biyar kafin ya dago yace "tashi kaje aliyyu" cikin firgici ya dago kai yana kallon uncle abban,ya sake maimaita masa"ka tashi kaje nace mu zamu nemota" alhaji yaje fa kace?" Momi ta fada cikin fushi,a nutse uncle abba ya kalleta "to maimunatu mai zai zauna yayi min?,yaje kawai tunda ya gama nasa aikin ko,mu kuma ba sai muyi namu ba?"

Tasan sarai halin mijin nata saboda haka ta gamsu da abinda yace "gaskiyane"shi kam aliyyu yadda bai tanka ba sabida rudani haka ya kasa tashi kansa na sunkuye jinsa yake kamar wani mutum mutumi,har sai da uncle abban ya gaji da ce masa ya tashi shi da momin suka taahi suka bar masa falon

Da azahar momi ta dauki wayarta ta kira anty hauwa kamar yadda uncle abba ya ce ta ce mata yana son ganinta ko zuwa najima ne,sai kuwa aka taki sa'a suna cikin gaisawa kausar ta soma qwala kiran "anty fadilah!anty fadila!!na kasa daukowa"nama ne tace ta ciro mata cikin fridge sunce suna son dambun nama to naman ya riga yayi qanqara,tuni momin ta tsaya da amsa gaisuwar "maijidda wace fadilance a gidanki?" Cikin son boye boye tace "am ....fadila ce ta zo mu gaisa,dazun aliyun ya sauketa" "mu kuma dazu aliyyun ya bar nan yana cigiyar ta ba"momi ta katseta "aljanu ke miki wasa da hankali ko gida biyu su aliyun suka rabu?" "A'ah momi ai" "kinga dakata shi aliyun ya riga da ya sanar da babaku komai da kansa,dama maganar da na kira ki kenan akai,saboda haka idan anyi magariba ki dauko ta kuzo"

Hawaye bibbiyu fadilan keyi"anty me yasa kika sanar musu anty,munyi alqwari dake anty,me yasa suka sani?" "Fadila aliyyu da kansa yakai kansa gun abba,momi kuma ta san kina gidan nan dazun da kausar ke qwala miki kira" "me yasa aliyyu zai min haka?,don me yasa zaije ga uncle abba?,me yasa baiyi sakin cikin rufin asiri ba?,so yake kowa sai ya ga laifinshi kenan?"sai lokacin tayi dana sani,tayi data sanin da ta fito tun ranar da yazo gida anty hauwan ya bata takardarta ba tare da kowa yaji ko ya gani ba,suna sake doso unguwar bugun zuciyarta na daduwa,tabbas da kafin su yi nisa naty hauwan ta gaya mata inda zasu babu shakka ba zata ba sauka zatayi,gaba daya jikinta rawa yaje ta kasa nutsuwa sai da anty hauwan ta riqeta sannan ta iya shiga falon.........

*mrs muhammad ce*👑

📘📘📘📚📚✍🏻✍🏻
[10/16, 2:11 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

9⃣&1⃣0⃣

Umminta ta gani da mominta zaune kujera daya,uncle abba da abban nata kuma na kujera daya,sai iftihal dake zaune dare dare kan cinyar abban nata,duk kansu suka amsa sallamar,sosai taji dadi cikin ranta don rabon da tasa iyayen nata a ido har ta manta,sai dai hararar da ummin nata ta watsa mata ita ta sagar mata da gwiwa,anty hauwa ce ta fara gaida su sannan itama ta gaidasun,sama sama ummin ta amsa mata don har gwara abbanta,cikin salubewar jiki ta koma gefan kujera ta rakabe

Aliyyu ne ya shigo cikin sallama yana sanye da shadda dinkin tazarce kansa babu hula,da gudu iftihal tayo gurinsa,hannunta kawai ya iya riqewa bayan da ta gaidashi,gaida su yake saidai abba da umminta ne kawai suka amsa masa,yana shirin samun guri ya zauna uncle abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "kai....dakata ba zama na kiraka kayi ba...ungo nan" ya miqa masa farar takarda da abun rubutu "rubutawa yarinya sakinta tunda Allah yasa mun ganta" da sauri ya daga kai ya soma rarraba ido cikin filin falon yana neman inda fadilan take,can ya hangota a takure a gefan kujera kanta a qas

Gaba daya idanunsa suka rufe,tuni ya manta da cewa akwai wasu wai iyayensa a falon ya durfafeta,idanunsa qir bisa kansa,wani shauqi mai cakude da matsananciyar qaunarta yake fisgarshi,sai da yaje daf da ita uncle abba ya daka masa tsawa wadda ta sashi dawowa cikin hayyacinsa "qaniyarka nace dawo nan" inji uncle abba yana masa nuni da gabansa inda zai zauna din bayan daquwar da ya

Please Login or Register in order to submit comment