Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]


*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________



*Assalamu alaikum*

Godiya ga Allah maɗaukakin sarki daya kawomu wannan rana na fara sabon littafi.
Dama an ce rana bata ƙaryah saidai uwar ɗiya taji kunyah. Barkanmu da wannan rana mai albarka,dafatan An wayi gari cikin ƙoshin lafiya.


*GARGAƊI*


Ban yadda wani ko wata ya kwafamin littafi ba ta kowacce siga,sannan akwai halayya da ɗabi'u a cikin wannan littafin wanda basu dace ba,dafatan za'a ɗaukesu a matsayin darasi mai isarda saƙo.
Sannan abu na ƙarshe ayimin afuwa idan wani yaci karo da abinda yayi daidai dashi,banyi niyyar yin hakan ba sam.
Nagode sosai ayi karatu lafiya......




Page 🖤01🖤


.........."zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi"
Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici.
"Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!"
Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane.
""Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24"
"Toh ranki ya daɗe"
Ta faɗa tareda zubawa dagudu. Bayan barinta wajen sake maida hankalinta tayi kan hafsa,wadda take ta nishi amma babu alama haihuwar tana kusa,gashi kuma jininta ya hau sosai babu dama suyi mata cs.
Girgiza kanta tayi cikeda tausayawa,dan duk wanda yakalleta a wannan halin yasan ba ƙaramar wahala take sha ba sosai.
"Sannu kinji,bari yazo ya duba koda akwai matsala,dan ni gaskiya bamu taba ganin irin wannan ba tunda muke anan asibitin,komai ƙalau amma kan yaron yaƙi motsi tunda yafara fitowa?"
"Nurse to ki sake yimin allurar naƙudar mana,inaga yanxun a dace wataƙil"
"Ahah kiyi hakuri,a iya daga jiya da daddare zuwa yanzu mun yi miki allura kusan biyar,bazayyi ki sake ɗaukanta ba yanxu,tana da haɗari sosai.
Baridai doctor yaxo muji mai zaice,inshaaallah zaki haihu lafiyah,kada ki damu,Allah yana tareda ke"
Karfafa mata gwiwa ta cigaba dayi akan lamarin,duk ita kanta ta sare da irin wannan case ɗin.
Waje ta leƙa suka haɗa ido da HAJIYAH ZEENAH,wanda tun ɗazu take zirga zirga a wajen.
"Ya ake ciki nurse,ta haihu ne?"
Jijjiaga sister suwaiba tayi,shekararta ashirin kenan tana karbar haihuwa,amma wannan kam yacaza mata kai matuƙa,.
"Har yanzu dai hajiya lamarin jiya i yau,ni har na fara tsorita ma da abin,gashi tana naƙuda amma kuma babu haihuwa babu alamunta"
"Kai innalillah,ni banma san mai zanyi ba,ga IYAH SAYYADA ma,saida akayi da gaske kafin ta hakura da zuwa asibitinnan,nasan tana can ta ɗagawa kowa hankalinsa,sannan gata itama yarinyar tana shan wuyah sosai......to maizai hana ayimata cs,shi mijin baya ƙasar,amma kuma ƙaninsa yana nan ai sai ya saka hannun"
"Shima hakan bazayyi yiyu ba Hajiya,domin jininta yana at risk,a kowanne irin lokaci zai iya zama matsala"
Suna cikin maganar ne likitan ya iso wajen da coat a jikinsa,da alama zuwansa kenan.
"Ya akayi sister suwaiba,naji ance kina nemana a ɗakin haihuwa,wane abune haka daya gagareki?"
"Uhm sir babbar matsalace sosai,yarinyar kwana uku kenan tana naƙuda,gashi tana last stage,amma kuma jinjirin ya gagara fitowa,idan muka saka hannu kuma saiya koma da baya,sannan da alama kaman yaron bashida rai"
"Oh to a shirya shiga operation mana,bazayyi yu a barshi a cikinta har yanzu ba ai"
"Uhm uhm sir jinin yana over tension fah,operation bazayyiyu ba shima"
"So do you like us to watch her die(so kike mu zuba mata ido ta mutu) dolene muyi wani abun,maza muje na ganta yanzunnan.
Naji kince mrs.JABEER .A.JAAN ce koh"
"Eh hakane doctor,yana shirin tahowa yanzunnan"
Juyawa yayi yana duba file ɗin ta suka haɗa ido ta hajiya Zeena,waccce gabaɗaya damuwa a tattara akan fuskarta.
"Barka dai ranki ya daɗe"
"Yawwa barka doctor,ya kamata kuyi wani abun,idan ta kama fita da ita ne ma sai a shirya yanzunnan ta private jet"
Karki damu hajiya,zamu yi iyah koƙarimmu akan matsalar.
Daga haka suka shige site ɗin da Hafsan take kwance.
Wayar tace tayi ƙara,hakan yasa ta koma inda su LAYLAH matar ƙanin mijinta (facalah)suke a zaune.
"Hello ina jinka ABDULMALEEK ya ake ciki?"
"Hmmm ummah ina hanyar zuwa asibitin,kuma tare mukeda Iyah Sayyada,tace wai dole saitazo taga jikinta,na kawota ko muyita wani wajen?"
Jan ajiyar zuciya Hajiya zeenah tayi kafin tace.
"Shikenan babu komai ka kawotan,idan ka kaita wani wajen ma,kasan bazata haƙura ba"
Sauƙe wayar tayi tana kallon Lylah wacce take danne danne a wayah.
"Lylah Iyah Sayyada tana zuwa,yakamata ki ɗora alamar tausayi akan fuskarki,inba so kike kuyi ba"
Tabe baki Lylah tayi tareda cewa.
"Nina gaji da zaman wajennan wlh,kawai akan wata zata haihu a ce saikazo ka zauna,da muka zauna ɗin uwar me muka tsinana a wajennan ne,in matsalar wanine a sakoka,idan taka ce kuwa kai kake magance abinka"
"Toh yanxun wannan habaicin dani kike kokuma da mijinki dayace kizo? Bar ganin ina cikin jimami ki sami dama akaina,kinfi kowa sanin halina banida daɗi,batun zama kuma babu wanda ya riƙeki ki tashi ki bar wajen,daɗin ta ma kema naki ahalin ba ƙalau suke zaune ba,shanyayyen ɗanki ma ya isheki"
"Ehhh naki shanyayyene,amma dai surukata ai bata kashe kishiyoyinta koh,matsala kan ai tana gindinki,surukarki tazame miki alaƙaƙai,kowa shaidane ita ta kashe kishiyarta,wannan ma kar ace komai,dan biri yayi kama da mutum".............."
"Lahhhh ha ila ni Sayyada Tatin,yanzu mai zan gani,maizan gani haka,ƴar jikartawa tana ciki rai a hannun Allah,ku kuma kuna nan kuna saida hali.......ke Zeenatu,wato surukarki batada lafiya ma amma bazaki daina ɗiban rashin arziƙi ba koh......"
"Amma iyah Sayyada itah fah ta fara,kuma......."
"Dallah rufemin baki ni,saina kunyi abu nayi magana kununamin ku ƴan zamanin nasara ne,kalleku tula tula daku,ƴaƴanku na ƙasar masu jan kunne suna holewa,nikuma ƴar jikata ƙwaya ɗaya ta ni kaɗai take da,an kasa yimata gatan magani,sai paracetamal ake bunka mata dan rashin imani"
Dukkan su jugum sukayi suna jinta,ta riƙe ƴar ƙafar data ke mata ciwo tana ta zuba kaman ƴaƴan kanya,idonnnan sai fici fici nashi takeyi,kaman na ƙwarƙwata.
"Habba Sayyada kiyi shuru mana,wai bakya ganin yanda kika tara mutane sai kallonki suke ne,ni wlh dana sani dana barki kin cigaba da kukannaki ban kawoki ba"
"ABDULMALEEK ya faɗa yana zuya fuska"
Duka ta kai masa a gadon baya tareda cewa.
"Gyauton uwarka data ke tsayennan Audulolo,a gidan ubanwa nayi kukan,ko sharri zakamin dan ka rainani?"
Daga haka bai sake cewa komai ba ya koma gefe yana kallonsu,ta kama uwarsa ta matar baffansa sai tsefesu take a dandazon mutane.
"Mai me Kakah ma yagani ma a wannan matar ya aura har ta haifi ubanka oho,mtsww ba dama ka fita da ita saita zubarmaka da ajikinka a gaban abokanka"
Gyaran muryah likitin yayi hannunsa duk jini,ga gumi akan fuskarsa.
Sakin baki sayyada-tatin tayi tana kallon jinin dayake hannunsa,
"Kai.....ɗan saurayi,yanzu wannan jinin danake gani a hannunta na hafsatuna neh,mai kayi mata kaji mata ciwo haka?"
Saurin cire safar hannunnasa yayi tareda ɗorata akan tiren da nurse ɗin take binsa dashi
"Ahh iyah ba haka bane,jinin haihuwa ne kawai"
Ɗora idonsa yayi akan Hajiya zeena,tareda yimata Alamar yanason magana da itah.
"Am Iya bari muyi magana da Hajiya yanzu nan"
"Mai zaka faɗamata,faɗaminnan ni kakarta,duk nan wajen nafi kowa ƙaunar ta da son ta rayu"
"To Iyah a halin yanxu gaskiya,bamu sam mai zamuyi ba,dan wani abin mamaki ma,ta daina magana saidai bin mutane da ido,sannan gabobin jikinta munaji suna karyewa kass kass a duk sanda ta ɗan motsa,da alama kuma bata cikin hayyacinta....."
"Yimin shuru haka baƙin jakada,ya isheka haka,wayyooo hafsatuna shikenan,sun haɗu sun cinyemin ita,saida nace bazan bashi ita ba matarsa mayyace,amma suka ƙeƙasa ƙasa su a dole wai yana sonta,kuma tana da hankali.
Gashi nan sun kaita wannan la'ananniyar matar tasa tacinyemin itah,bazan taba yafemuku ba wayoo ni Tateen ƴar mai Gaskiya"
Share hawayenta take da gefen gyalenta,tana kuka amma bakinta ya gagara yin shuru.
Buge likitan tayi tareda cewa.
"Dallah matsa na wuce naje na ganta,marasa imani kawai"
Turus tayi a bakin gadon,ganin yanda jikinta ya koma kaman babu gabobi,ta kwance take da tulelen ciki kaman gawa,dan yanxu kamma babu damar nishin da tayi ɗaxun.
Faɗuwa Sayyada-tateen tayi tana burburwa a kasan tile ɗin ɗakin,kaman sabuwar ƴar bori.
Sai ƙiran sunan LUBAN take da su hajiya zeena da Lylah tana tsine musu.
Abdulmaleek neh ya shigo ɗakin tareda dafa kafaɗunta,suma su Hajiya zeenah shigowa sukayi suna kallon yanda kamannin hafsan suka sanja daga yanda suke.
Madeenah ce da Maleekah ƴayan hajiya Zeena mata(ƙannen Jabeer babban yayansu,sai kuma Abdulmaleek &Abdulkareem su ƴan biyune,sun gama karatunsu wannan shekarar,ABDULMALEEK engneer ne,Abdulkareem kuma doctor ne na ƙwaƙwalwa,yana housemanship a india.
Sai mai binsu Madeenah,tana 300 level a University of abuja,ita kuma Maleeka a 100 level,suna zuwa su dawo).
"Allah sarki zainabuna ma(Mahaifiyar Hafsa,kuma kanwar baban su ABDULMALEEK),haka ta mutu a haihuwa,aka haifamin ita,sai gashi itama suna so ta tafi ta barni a lokacin haihuwar"
Likitanne yashigo da sauri shida nurse din suka fara shiryata zuwa ɗakin tiyata,
"Kiyi haƙuri hajiya,zamu shiga da ita tiyata,saboda mun gano abin cikinta bai mutu ba har yanzu,saidai amma kiyi haƙuri,dan iya ba lallai takai labari ba,amma duk da haka muna buƙatar addu'arku"
Dagata sukayi tareda ɗorata akan wani sabon gadon kaman gawa,suka nufi ɗakin tiyatar,suna barin wajen Sayyada-tateen ta ƙara gudun kukanta,kaman wata ƙaramar yarinya.
"Shima jabeerun sai naci bantan ubansa,dan tsabar ran yarinyar nan bai dameshi ba,shine ya ɗaga kafa daga dawowarsa shekaran jiya har ya koma yau da sassafe koh hmmmm,bamai zugashi ai sai wannan mayyar kuɗin,a son kuɗi zakiyi komai"
Ta faɗa tana nuna Hajiya zeena,wacce ta ɗauke kanta tana tabe baki,dan inda sabo sun saba ma........

Kwana uku baya..........


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤02🖤


Ƙwana uku baya............


________________"Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za'ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba.
Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita.
JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan, saidai idan nina haifa shine zai gani,amma idan baniba babu wata ƴa kuma.wannan alƙawarina ne ni LUBNAH ƴar URWATU"
"Shikenan yanda kika ce aikin bazai gagara ba,saidai kafinnan zaki ajiye nairah Miliyan ɗaya da rabi kafin a fara aikin,dan zubar da cikin a yanzu zayyi wuyah,saidai a bari idan yakai matakin haihuwa sai a hanashi fitowa,koya kika ce toh"
"Hmmm idan hakan zaifi ayi hakan,amma ni da son samuna ne kafin na koma gida na sameta anyi filla filla da naman jikinta,babu wani abu dazai nuna itace,vazaka gane bane boka,natsani na buɗi idona na ganta a cikin gidannan,da wannan tsinannan cikin tana turashi,nafiso a kasheta irinnna waccar matar,kafin ma takai ga wani samun ciki"
"Kai......!! Tsiyata dake lubna gaggawa,inkika bi a sannu,kuma kina bawa Aljanu jinin da suke buƙata,babu abinda bazaki samu ba,har matakin zaman ki na CEO ma duk zai cika nan da zuwa gaba.
Idan aka kawar da itama rufe idonsa za'a yi daga kan duk wata ƴa mace da take doron duniyar nan,ke ɗai zai dunga kallo a duk inda idonsa ya sauƙa"
"Shikenan nidai duk yanda zakayi ma kayi"
"Amma fah akwai ƙa'idoji da dole saikin kiyayesu,na farko;dolene kijata a jiki,ta yanda zata yarda dake har ki dunga sanin ya take ciki,na biyu kuma akwai wata ƴar tsana da zan baki,ki tabbatar kin saka jininta a jiki,lokacin da tazo haihuwa ki dunga karya jikin tsanar,zai zamo tamkar jikinta kike karyawa,daga lokacin da kika karyata tayi laushi,ita kuma sannan zata fuskanci tata mutuwar tareda abin cikinta"
"Naji wannan bayani naka,za'ayi yanda kace ba matsala,lokacin dazata dunga ihu sannan zuciyata zata wanke da zama min da tayi a cikin gidana.
Nagode gaskiya yau da gagarumin abinda ka bani,zan tafi,dan yau zai dawo daga taron daya tafi England"
Tashi lubna tayi daga ƙasan da take zaune tareda kaɗe zaninta tana murmushin samun nasara.
Hanyar fita daga wajen ta nufah mai matuƙar bada tsoro,amma hakan ko a jikinta,dan akan kishin mijinta babu abinda take ganin zai iya saka mata zani yarabata dashi.
Saida ta ɗanyi tafiya mai nisa kafin tazo wajen inda ta ajiye motarta,Wai hausawa suna cewa SA KAI YAFI BAUTA CIWO.
Saida tayi tafiya mai nisa kafin ta shigo garin abuja,direct JAAN ESTATE ta wuce da baƙar motar ta.
Nufar babban get ɗin tayi cikeda ƙasaita da izzah,wanda hakan a jininta yake.
Titin dazai kaita apartment ɗinsu tabi,wanda take ɗan ciki kaɗan da bakin babban get ɗin.
Saida ta wuce nasu Hajiya Zeena kafin ta iso nasu part,shima da get ɗinsa mai zaman kansa,yana ɗauke da part biyu,amma a haɗe suke ta tsakiyah,inda side ɗin Jabeer yake.
Ba hanyar nata part ɗin ta nufah ba,da alama wajen Hafsa zataje.
Fuskarta a murtuƙe take saboda tsanar baiwar Allahn,amma haka ta danne saboda zancen boka ta saki fuskarta kaɗan.
Da sallama ta shiga tangamemen falon,mai adon Green da purple,yayinda nata kuma yake fari da ja.
Haushi ne yakamata ganin kayan Alatun da mijinnata yasaka mata,tafison komai yazama ita kaɗai take dashi bada wata matar ba.
"Assalam ƙanwata kina cikine""
Hafsace ta fito daga ɗaki da doguwar riga a jikinta marar nauyi tana tura zungureren cikinnata.
Kallon Lubna take da mamaki,dam yanda taga murmushi akan fuskarta abune da bata taba gani ba a faɗin rayuwarta,a ranta addu'oi take jerowa duk wacce tazo bakinta.
"Lafiya ƙalau Anty lubna,sannu da dawowa ya hanya"
"Hanya ƙalau,har zan shige nace bari nazo naga ko lafiya kike,nasan babu kowa a gidan saike kaɗai,ga Honey ma bayanan,an barki ke kaɗai ga ciki"
Ƴar dariyah Hafsa tayi,har sannan bata share tantamar inaga antynnata ba lafiyar ta ƙalau ba,dan in ana neman rashin imanin matar to a tambayeta"
"Ayyah ba komai anty,akwai Alawiyyah ai ƙanwata,tana taimaka min da abubuwa,Hajiya ma kuma tana shigowa akai akai"
Mintsine bakin lubna tayi tareda cewa "munafukar tsohuwa" a ranta.
"Ohh kinga shaɗaf na manta da hakan,dama saidai ta hakan ai,akwai abincine ki bani,yanzu na fawo gashi banci komai ba"
"Ah....ehhh barina duba kitchen ɗin,ki zauna akan kujera naje na dawo"
Murmushin yaƙe Hafsan take dan kwata kwata abin bayyi mata a gaske yake faruwa ba.
Bayan tabar wajen tashi lubna tayi tana kalle kallle a cikin falon,yaune zuwanta na farkon wajen da niyyar arziƙi,saidai tazo tayi tijara ko kuma kashedi,dan haka har tazo ta tafi bata gane mai yake wakana a wajen sai yanzu.
Tana cikin kalle kallenne Hafsa ta dawo ɗauke ta plate a hannunta,ta rufe da wani a sama.
Karba lubna tayi tana murmushi tareda cewa.
"Yawwa nagode ƙwanta sosai,amma zan iya tafiya dashi saina kawomiki plate ɗin?"
Ɗaga mata kai Hafsa tayi cikin ladabi.
"Lahhh ki tafi dashi Anty babu komai"
Daga haka lubna tajuya ta fita da plate ɗin abincin a hannunta.
Tana shiga part ɗinta ta buɗe kwandon shara ta zubashi a ciki,tareda jefa plate a ɗin a wajen wanke wanke tana kaɗe hannu kaman ta dauki kashi.
Ɗaya daga cikin masu aikinta ta ƙwalawa ƙira.
"Bishirahhhhh!!!!!"
"Naaama ranki ya daɗe"
Ta karisa magana tana zurowa da gudu.
"Gyaran gidannan bayyimin ba kwata kwata,ku tabbar kun sake gyarawa kafin magriba"
Bayan ta wuce wacce aka ƙira da bishira ta samu waje ta zauna,tareda sakin wata ajiyar zuciya,banda neman na halali mai zai sakasu aiki a wajen wannan dujal ɗin.
Bayan ta fito daga wankane taji ƙarar motoci suna shigowa cikin apartment ɗinnasu.
Shafe shafe tafarayi,dan tasan mai gidanne yadawo daga taron shekara da sukeyi da sauran companies..
Har lubna ta gama shiryawa ana ta ƙiran Sallah amma bata ga Jabeer ya shigo ba,abinne yafara bata haushi,dan tasan yanzu haka yana sashen Hafsa,saboda ita tana da ciki ita kuma batada shi.
A bangaren J.J kuwa yana fitowa daga motar muhimmin ƙira ya shigo wayarsa,ana nemansa da gaggawa,dan haka a take ya ɗau ƙaramar motarsa personal ya koma.
Bashi ya dawo gidanba sai bayan isha.
Sallama yafara a bakin falon lubnan,amma shuru bata kulashi ba har ya shigo cikin ɗakinta.
A zaune take akan kujerar dressing mirror tana danna waya,tacika tayi famm kaman zata fashe.
Mamaki abin yabaww J.J,dan yasan babu abinda yayi mata kafin tafiyarsa,hasalima sanda ya fita daga gidan bata nan ta tafi gidan ƙawarta batareda yasani ba,shine ma yakamata yayi fushi,amma kuma wai itace dayin fushin.
"Lubna inata Yin sallama kinaji kaman ba musulma ba?"
"Hmmm banyi niyyar amsawa bane,dan tsabar rashin adalci wato,tun ɗazu kashigo gidan amma kana wajenta,ita gamai haihuwa koh,sai nayi magana tsofi suce banida haƙuri"
"Ke suwaye tsofin,iyayena koh? Yayi miki kyau,wai yaushe zaki sanja haline kam,dawowa ta fah kenan,yanxune ma nashigo gida,hmmm ALLAH ya shiryeki,banida lokacinki tunda lafiyarki kalau fine,na sauƙe miki haƙƙinki,saida safe"
Yana gama faɗin haka ya bar sashennasa cikin bacin rai,tasashi kuwa sarai,idan yayi zuciya da ita ta ƙwammaci ya mareta daya tura mata aniyarta,dan sai yayi sati bai kalli inda take ba.
Tsuka taja duk da taji tsoron fushinnasa,dan Allah ne kaɗai yasan irin yanda take so tajishi a tareda ita,dan ita kanta shida ce shiɗin jarumin namijine a ta kowacce fuska,badai mace ta rainashi ba,saidai ma ta gaza.
Dama ƙarin haushinnata kenan,ba a sashenta yake ba,shiyasa take wannan kumbure kumburen.
Hafsa tana kan sallayah ya isa ɗakin cikin fushi.
Sallama tayi tareda sake masa murmushi lokacin da suka haɗa ido.
Shima murmushin yayi mata,duk wani bacin rai da lubna tayi masa sai yaji yana sauƙa.
"Ka dawo lafiya ya hanya?"
"Alhamdulillah,ya zaman gidan da lafiyarku"
"Muna lafiya kalau,barina kawo maka abinci"
"Ahah ki barshi,barina yi wanka tukunna"
Tashi yayi ya rage kayan jikinsa tareda shiga banɗaki.
Kafin ya fito ta fitar masa ƙananna kaya marasa nauyi.
Da safe suna cikin yin break fast lubna ta shigo sashen riƙeda plate ɗin jiya a hannunta.
Tasha wani matsatstsen lace kalar zinare da baƙi riga da skirt,ba laifi tanada yar ƙiba,amma kuma bayada kunkumi sosai mai cika ido,sannan ba fara bace,saidai sanadiyyar mayuka na zamani,tayi fari tass kaman fatalwa.
Wani shu'umin murmushi tasake mai,dauke da ma'anoni kala kala.
Hafsa ce ta gaishe da ita tareda yi mata bismillar abinci,Jabeer kam ko kallon ta bayyi ba,sauri yake yagama cin abinci yafita wajen aiki.
"Ayya wai break fast,naga kam kuna cikin nishadi sosai,plate ɗin jiya na dawo miki dashi"
Ta faɗa tamkar mutuniyar kirki. Jan kujera tayi babu kunya a kusada Jabeer ta zauna tareda yimasa kallo ƙasa ƙasa.
Hafsa tana kallonsu amma ta kawar da kanta tareda zubawa Lubna itama abincin.
Bayan kamar minti biyune Jabeer ya ɗago ya zabgawa lubna harara,saboda yanda take ɗaga ƙafar wandonsa da kafarta ta ƙarƙashin tebur ɗin.
Har ya buɗe baki zayyi magana ganin bata daina ba ya fasa,saboda yanda Hafsa ta ajiye cokalin hannunta tana rike cikinta.
Tun kafin Jabeer ya taimaka mata,lubna ta riƙeta tareda yimasa magana ya ɗakko key ɗin motarsa.
Cikin sauri suka nufi asibitin da itah da gaggawa,sai bayan sun isa an shiga da ita ɗakine tukunna suka samu damar ƙiran Hajiyah zeenah,wanda cikin ƙankanin lokaci ta tashi hankalinta,sai gata itada Laylah,matar baffansu ABDULLAHI. Sayyada-tateen kam ba'a sanar mata ba,saboda kowa yasan halinta da surutu da ɗaga hankali.
Safa da marwa suka fara a bakin labor room ɗin,itadai luban kallonsu kawai take,duk sanda suka nuna damuwa ƙara bata haushi suke,musamman yanda jabeer yafasa tafiya ko ina,kowa addu'ar ta sauƙa lafiya yake,ita babu wanda ya kula da ita.
Ƙara wayarta tayi a cikin jaka,wanda hakan yasa ta nufi wani dan waje gefe da inda suke tsaye.
"Hello Hajiya na ɗebi miki jinin,yanzu zan fito daga ward ɗin,sai ki bini zuwa nurse section na baki"
"Okay babu matsala"
Tana kashe wayar tayi murmushin mugunta tareda kallon inda hafsan take kwance,fitowa nurse ɗin tayi kanta a sunkuye ɗauke da test tube na jini ta nufi sashen su,babu wanda ya kulada ita,domin kowa yayi zaton abu zata kai wani wajen.
Lubna tana ganin hakan ta bi bayan nurse din,saida sukaje inda babu kowa kafin ta tsayah,
"Yawwa gaskiya kinyi ƙoƙari sosai,ai dama yanda kika faɗa cewar kin bata maganin naƙuda tasha da safe,shiyasa na shiga sashen domin na biyosu asibitin.
Aikinki ya cika,na tura miki miliyan ɗaya acct ɗin yanda mukayi nagode ni barina na tafi"
Lubna ta faɗa bayan ta karbi jinin tasaka a jaka.
"Kwanan ki ya ƙare Hafsatuwa kema kaman ɗayar,nariga na faɗamuku,duk wacce ta rabeshi to kabarinta ta tona,koda kuwa wacece".......!!!!!

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]







*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________






Page 🖤03🖤




Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah.
Lylah ce ta kulada ita tace.
"Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?"
"Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan"
"Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan"
Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi ba.
Dariyah ƙasa ƙasa Hajiya Lylah tayi,da alama show ɗin yayi mata dadi sosai.
A daddafe tana nishi ta nufi motar ta,hadda tsayawa ta huta kana ta cigaba da tafiyah.
Saida tabar layin asibitin kafin ta saki shewa tareda ciro wayar ta a jaka.
"Kee Dallah ki tsaya nayi magana,nasamo mahaɗin yanzunnan,naji kincemin kinaso kiga yanda zan gama da ita,to ki hanzarta,dan ba'a son tafara naƙuda tukunna,idan ta haihu to aikin bazayyi yiyu ba"
Kashe wayar tayi tareda ƙarawa motar wutah tana waƙa.
Bata ja wani lokaci ba ta isa gida,kasancewar basuda nisa da asibitin.
A bakin ƙofar gidan ta samu motar Yaseerah ƙawarta tana jiranta,bodyguard sun hanata shiga,ta bar ID parmission dinta a gida saboda sauri.
Horn Lubna tayi musu tareda nuna musu motar Yaseerah lokacin da tazo shiga.
Tafiya take tana binta a baya har suka isa apartment ɗinsu.
Direct
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment